Da yamma aysha taraka sarah gidansu asma'u taje Neman khadeeja
Bayan sungaisa dasu Umma khadeeja tarakosu har waje
Juyowa sarah tayi tana kallonta da murmushi afuskanta tace to deeja nizan tafi se kinzo gobe
kauda kai tayi tana daure fuska tace allah ya kaimu
ahasale aysha taja hannun sarah tana fadin wai sarah meyake damunki ne kintsaya karamar yarinya tana daddaure maki fuska kar allah sa tazo
Kwace hannunta tayi tana daka mata tsawa tace aysha ya isa haka karkimanta matsayinta awurina so behave ur self
Dariya khadeeja tayi tadawo gaban aysha tatsaya tana fadin
malama dafarko dai inaso kisan bani nagayyace Ku gidanmu ba so dole zaku Bini aduk yadda nakarbeku ku idan kinga bazaki iya ba hanya abude take
Sannan tajuyo wurin sarah tace ke kuma sarah ina so kisan cewa koda gaba daya mutanen duniya zasu yarda da canzawarki to ni khadeeja bazan fada tarkonki ba
Saboda nasan people like u won't change easily
nasan kina da wata buyayyar manufa akan wannan fuskar mutuncin dakika ara
nunata tayi dayatsa tace
let me worn u sarah if u dare do something terrible to me or my sister I will make ur life a living hell that's my promise
tana kainan tajuya tabarsu atsaye suna binta da kallo har tashige ciki sannan sarah tajuya jiki asanyaye tashiga mota aysha tabita tana jan dogon tsaki
AK na zaune apalo asma'u tashigo tana kwasan gyalenta tawuce takusan shi zata shiga daki hannunta yakamo yajuyo da ita gabansa yana fadin zo nan hajajju ina so in tambayeki wani abu
zaunawa tayi daga kasa suna fuskantar juna takure shi da ido batace komai ba kallon kallon suka farayi nadan lokaci kana yaja nunfashi yana Sosa kai yace mema zan tambayeki ?
tashi tayi tana fadin bari natafi inada abun yi idan katuna seka kirani
Janyota yayi yazaunar da ita yana fadin a'a dawo natuna nace wai me kika gayama sarah ne har tayi saurin gane abunda najima ina kuatanta mata
murmushi tayi tace ni nama manta abunda nagayamata kawai dai magana namata kuma banmasan zata dauki abunda nafada ba
kankance ido yayi yana kallonta yace um um chitti a iya sanina sarah ta tsaneki bata sonki amma ya akayi lokaci guda tafadi magana mai dadi akanki anya kwa ba magic dinnan naki kika mata ba kuwa ni kikoyamun yanda ake nama grany tafarayin duk abunda nakeso
Dariya tayi tace wane magic kuma nidai bawannan ba gaskiya ABI bai kamata ayi bikin khadeeja anan gidan ba duk da sarah tahakura amma bazataji dadi ba
zaiyi magana kenan sukaji sarah nafadin
Ba abunda zanji sister anan zamuyi bikin kanwarmu kamar yadda Yaya yafada
Juyawa sukayi suna kallonta da murmushi afuskansu
Karasowa tayi kusa da AK tazauna tana kallon asma'u tace bama wannan ba sis kushirya gobe da daddare nahada dan kwarya kwayan party wa ahmad da khadeeja saboda inaso musanar da abokanansa da kawayanta zancan bikinsu kuma natayasu murnan cimma burinsu
kallonta AK yayi cike da tausayi yace kintabbata ba wata matsala sarah can u bear it ?
Dafashi tayi tana dariya tace Yaya come on I am not a kid ko kuma Baku yarda nahakura bane
murmushi sukayi suna kallonta basuce komai ba
da daddare har Sarah ta kuanta aysha ta iskota rai bace tace sarah ni nakasa ganeki wai ina sarahn da nasani wacce bata hakura da abunda takeso bare abunda nasan kinfi sonshi fiye da komai aduniya yaushe kika dawo hakane ko kema sallon yaudarar asma'u yayi tasiri akanki ne
Daure fuska tayi tana kallonta tace aysha waini wacece dabazan gyara rayuwata ba ko kafiri yakan musulunta yazama nagari bare ni me kika daukeni ne to nagaji da abunda kike mun kar ki kara mun wannan banzar tambayar kinji nafadamiki
ahasale tafita tana banko kofar dakarfi
washegari dasafe AK d nabangaren grany yana breakfast kan dining asma'u nagefensa azaune tana kokarin zuba kunu akofi amma takasa saboda hannunta da yayanke wurin girki
inna ameena nazaune daga gefe tana kallonsu
karasowa tayi wurinsa tana murmushi tace AK kaga asma'u tayanke dazu ahannunta kazubamata kunun mana kabata
kwarewa yayi yayi saurin daukan ruwa yakora yana kallonta da mamaki yace inna me ...mekikace ....nabata kunu fa
daure fuska tayi tace yo miye ba matarka bace kai gaka ahaka kamar zakayi soyayya amma ashe ko wayewar ma bakayi ba
Harara yajefa ma asma'u yana fadin to dabana nan waye zaibata kunun ko dolene ma setasha kunu
tafa hannu inna ameena tayi tana salati tace oh ni ameenatu menakeji haka kamar gwaranci abakin AK
amma wallahi kabani kunya se anyi magana kuce mana yan zamanin da to mudai bahaka mazan mu ke mana ba
Kallon asma'u tayi tana fadin baiwar allah shiyasa da daddare sena koreki kike tafiya allah kadai yasan me yake miki
labace baki asma'u tayi kamar zatayi kuka tace inna infadamiki wani Abu
Zaunawa inna ameena tayi kan kujera tana fadin inajinki asma'u menene
"Jiya ma haka ya.....
bata karasa ba yayi saurin fadin
OK fine....zan bata abar zancan
gyada kai inna ameena tayi tana fadin dadai yafi maka inba haka ba yanzu nakira grany asma'u tafadi komai agabanta
Kofin kunun ya fizge ahnnun asma'u yana ji kamar yarusa mata shi abaki seda yafaki idonsu ya ciko cokali da barkono ya zuba cikin kunun ya juya yana murmushin mugunta yakai kofin bakin asma'u yana fadin enjoy ur self baby !!!
Kurban farko taji kunnanta ya amsa saboda yaji
saurin janye bakinta tayi tana kallonsa
Murmushi yayi yakara kai kofin bakinta yana fadin drink it badai kunu kike soba
kallon inna ameena yayi yace kinga ai halin matan kenan tace kunu yanzu kuma nafara bata tana nuna bataso
hannunsa asma'u takama takai kofin bakinta tana shan kunun kamar ba komai aciki
Da mamaki yake kallonta seda tayi rabi sannan takai kofin bakinsa tana lashe baki tace to kaima kasha darling!!
zaro ido yayi yana kokarin kauce bakinsa inna ameena tace kai kasha mana yau naga sakaran yaro
asma'u zatayi magana kenan yayi saurin kama hannunta ya kai kunun bakinsa ya kurba
saurin hadiyewa yayi ya kauda kai gefe yana huddo harshe
Kallonsa inna ameena tayi da mamaki tace wai yanaga kana Abu kamar dayaji akunun ne
dariya asma'u tayi tace inna yaji ya....
bata karasa ba yayi saurin katseta dafadin kaji inna kuma mezai kawo yaji cikin kunu waima banaji grany nakiranki ba kitashi kije mana zamu kula da kanmu ai
Gyara zamanta tayi tana fadin ba inda zani se kungama kaidai sha kunun
Juyowa dakansa asma'u tayi takara kai kofin bakinsa tana murmushin mugunta
Ganin yakasa jure yajin kuma bayaso inna ameena tagani yasa yayi saurin tashi yabar wurin yana shakan iska yana fiddo harshe
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Cigaban 1⃣2⃣0⃣
tashi asma'u tayi tabishi tana dariya daki ta iskoshi zaune yana guma ruwan sanyi abakinsa
Dariya tayi tace ai shi dama ramin mugunta kamata yayi ka ginashi gajere gashi yanzu kai kafada ciki
Harara ya watsamata da ruwa abakinsa yace Gagagagagga
Dariya tayi har da rike ciki tace ni banajin mekake fadi amma bari nataimaka maka
Fita tayi ba adau lokaci ba tadawo da manja acikin dan karamin bowl yatsanta ta tsoma aciki tana fadin bude bakinka
Kauda kai yayi yana girgiza Kai
"Bude mana shafa maka zanyi zai rage maka zafin yajin
Ruwan bakinsa ya hadiye zaiyi magana ta tura yatsanta cikin bakinsa ta shafo man jan aciki
Saurin tashi yayi yanufi bayi yana yamutsa fuska
Fita tayi daga dakin tana dariya
Da daddare aka fara party kowa yazo cikin abokansu ahmad da kawayen khadeeja sarah senan nan take dabaki aysha ko haushi yagama cikata se masifa take tana hantarar kawayen khadeeja
apalon gidan ake komai wurin yayi haske kamar darana kowa naharkan gabansa ga daddadan sawti natashi khadeeja da ahmad sunyi matukar kyew kamar prince and princess se alokacin kowa ke ganin dacewarsu abokanansu se kodata suke suna fadin tafi ahmad kyew saura suga amaryar AK ita kuma yatake sunsan se tafi kanwarta kyew
AK nazaune adaki yana jiran asma'u
Can anjima tafito tana sanye da doguwar riga tasha katon gyalenta se kokowa take dashi
Tagumi yayi yana kallonta har zata fita tawaigo ganin bai tashi ba
tace muje mana ai nashirya
kallonta yayi sama da kasa yace muje ina ai da injera dake ahaka gara nazauna banje ko ina ba
dawowa tayi gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta da mamaki tace me kuma nayi nifa nan karshen fitowata kenan
tasowa yayi yazo kusa da ita yana fadin wai ke chitti anya kwa a abuja nan aka haifeki yanzu saboda allah kodan yafa gyalen nan na yan mata baki iya ba allah inaga ko grany tafiki iya dawri mai kyew
Labace baki tayi kamar zatayi kuka tace to ni ban iyaba ya zanyi ka kira mun khadeeja to tamun
" ni kuma kawai se aganni nakira khadeeja wai zatama matata kwalliya haba chitti abokanaina zasu mun dariya
komawa tayi bakin gado tazauna tana fadin to shikenan tunda hakane ba inda zanje kawai katafi
Shuru yayi nadan lokaci kana yajanyo drowan dressing mirror din yana fadin badai akwai kayan kwalliyar ba zo kidanyi ko yayane mugani
Kin tashi tayi seda yajanyota ya zaunar da ita sannan yayi tsaye kusa da ita yana kallonta
Tureshi tayi daga wurin tana fadin to katafi bazan iya yi kana kallona ba
fita yayi daga dakin yana murmushi seda yadan jima sannan yaleka yana fadin wai haryanzu baki gama ba
juyowa tayi tana kallonsa yayi saurin ja dabaya yana salati yace chitti mezan gani haka to ai dawannan gara babu
muka fita haka ai watsewa za'ayi abamu waje ya salam!!!
Langwabar dakai tayi tace to ni gaskiya ban iyaba nama fasa fita kawai kacemusu bana jin dadi
Karasowa yayi wurinta yace je kiwanko fuskarki kizo namiki dakaina natabbata sena fiki iyawa
Tashi tayi tana dariya tanufi bayi tana fadin ashe kwa zamu kuana anan bamu gama ba
tana shiga bayi ya fiffito dakayan kwalliyar yana karanta yanda ake anfani dasu koda tafito yagama tsab yaware wanda zai bukata gefe guda tana zama ya nannande hannun rigarsa ya shigayimata simple make up yana yi tana mai dariya bayan yagama da fuska yakoma bayanta ya warware ribbon din data daure gashinta dashi kallonta yayi tajikin mirror yace chitti umma bafulatana ce ko buzuwa
Dariya tayi tace bakatapiya ce
Shima dariyar yayi yagyara gashin yamata parking mai kyew sannan yagyara mata gyalen
ba'adau lokaciba yagama yana murmushi yace to duba kiga
Mamaki tayi bakadan ba ganin yadda tacanza lokaci guda la lips din nan sunsha janbaki tayi kyew bakadan ba
Juyowa tayi tana kallonsa da mamaki tace ABI dama ka iya ne
girgiza mata kai yayi yamikar da ita yana fadin bantaba yiba se akanki yanzu muje kinga ahmad najirana amma dan allah bakinki alekum nasan ki talkative ce saura kigayama khadeeja ni namiki kwalliyar mushiga uku
suna fitowa kallo yakoma Kansu nan take aka hau tapi ana shewa da gudu khadeeja tazo tarungume asma'u tana dariya tace ammah kinganki kuwa gaskiya yau kinyi kyew bakadan ba
Juyowa tayi takalli AK sukama juna murmushi janta gefe khadeeja tayi tana fadin ammah zo gayamun miye sirrin nidai nasan baki iya make up ba
Hannaye taware tana fadin bansaniba ba
Khadeeja zatayi wata maganar ta kwace hannunta tabar wajan tana murmushi
Da kallo tabita tana fadin this is the beginning of ur love story sis
Karasowa ahmad yayi kusanta yana fadin deeja kina ganin abunda nake gani kuwa
Dariya tayi tace ohh ni tarzan ashe kaima ka iya gulma
Dariya yayi yace deeja asma'u da AK sun bala'in haduwa
"wallahi inama suna son junansu dase sunfi kyew
"Zama suso ne ai naga andawko hanya
tunda suka fara magana sarah ke kallonsu tana sharan kwalla kusa da ita aysha tamatso tana fadin sarah wai meyake damunki ne ni nasan wallahi karya kike kice kin hakura da ahmad yanzu gashi kinkasa juran ganinsu tare bare kuma ace sunyi aure
Barin wurin tayi batare datace mata komai ba
Khadeeja da ahmad sunzo wucewa kan stairs kenan kawai taji anturata dakarfi zata fadi kasa ahmad yayi saurin janyota tafado kansa da gudu asma'u da fa'iz suka karasa wurinsu suna tambayar lafiya
Rike kanta tayi tana runtse ido arude ahmad yadauketa yakaita bangaren AK
Kan 3sitter yakwantar da ita yana tambayar bataji ciwo ba
Dafe kanta tayi tana kallon asma'u tace ammah ba faduwa naje yiba turani akayi
Damamaki suka kalleta suna fadin turawa fa khadeeja to wa zai turaki
Murmushin takaici fa'iz yayi yana kauda kai yace ya wuce wannan busassar yarinyar aysha ai naga lokacinda tabi bayan Ku dazaku haura sama
azabure ahmad yamike zaifita asma'u tarikoshi tana fadin a'a ahmad barshi kawai zanmata magana dakaina ba laille ne yakasance ita bace saboda banga dalilin dazaisa tanemi hallaka khadeeja ba
girgiza kai ahmad yayi yace ammah bakisan suwaye wa innan matan ba zasu iya yin komai wayasani ko tana taya sarah kishine nasanta bata da mutunci
aysha ce tasigo dakin sarah tana tafa hannu tace Weldon sarah nice try natabbata nan gaba bazakiyi kuskure wajan aikata lahira ba
damamaki sarah tajiyo tana kallonta tace kamar ya ban...gane ...akan wa kike magana ba
Dariya aysha tayi tana zama kan kujera tadaura kafa daya kan daya tace sarah karki manta da aysha kike magana ba AK ko asma'u dazaki iya deceiving ba ko kinaso kicemun bake kika turo khadeeja daga sama ba
Shiru Sarah tayi tana kauda kai da hawaye a fuskanta
murmushi aysha tayi tace karkice mun a'a saboda da idona naga lokacinda kika turata kuma naga lokacinda kika zuba wani Abu a jus dazu kika bama nura yakai mata amma kafin yakai glass din yafadi yafashe kinji haushi har kika mareshi daga nan nafara samiki ido dan nasan dole akwai abunda kike shiryawa
sarah nasanki kamar yunwar cikina I know u will never change for good
Saitin window sarah takarasa ta tsaya tana kallon waje cikin muryar takaici tace
Kwata kwata yaushe tashigo rayuwarsa wacece asma'u bare wata kanwarta lokaci guda yamanta ni kanwarsa ce ya dauki farin cikina yadanka ma wata baare
Hawayen fuskarta tashare tana cije lebe tacigaba dafadin
sunyi wawta dasuka yarda cewa wai ni sarah nacanza
Dariyar keta tayi tajuyo tana kallon aysha tace banso kowa yasan abunda nake shiryawa ba amma bakomai tunda kece kika gani ba wani ba aysha ina ma ahmad sonda ni kaina bansan yanda zan fadeshiba
Tunda AK yariga ya yanke cewa Ahmad zai auri khadeeja to tabass zai aureta
amma kuma ai setana raye zai aureta ko idan har nacigaba da nuna adawata akansu to dazaran wani Abu ya sameta ni za'afara zargi shiyasa nafito dawannan hanyar
Nuna kanta tayi dayatsa tace idan har ni sarah ban auri ahmad to ba wacce ta isa ta aureshi
sedai idan bana nunfashi adoron kasa
asma'u ce taturo kofa tashigo sauri juyawa sukayi suna kallonta
Murmushi sarah tayi tace ohh hello sister karaso mana
Karasowa asma'u tayi fuska ahade tace nasan cewa faduwar khadeeja ba haka kawai bane someone is behind it
atsorace suka kalli juna sannan sarah takalli asma'u da damuwa tace to waye zai yi kokarin cutar da khadeeja akan wane dalili
kallon aysha asma'u tayi tana fadin aysha ce ta turata dalilin kuma shinazo inji daga gareta
Azabure aysha tamike tana fadin what nonsense
alama sarah tamata datayi shiru sannan takalli asma'u tace kintabbata itace ?
"To waye zaiyi hakan inba itaba
Juyowa sarh tayi tana kallon aysha cikin daga murya tace how dare u
akan wane dalili zaki aikata wannan shirmen idan ma kina tunanin kishi kike tayi to u are westing ur time saboda ni khadeeja matsayin kanwa nadauketa idan kika kara aikata makamancin wannan to ba abunda zai hana namikaki ga police
Kasheta kike so kiyi
baki bude aysha ke kallonta cike da takaici tama kasa magana
dafa sarah asma'u tayi tana murmushi tace kibarta kawai sarah basai takai ga police ba mutuncin gidan nan ne zai zube
sannan tajuyo tana kallon aysha tace wannan yazama na farko kuma nakarshe idan kika kuskura kikayi na biyu to ina tabbatar maki cewa u won't get another chance to do the last one
Tana kainan tafita tana banko kofar dakarfi
juyowa aysha tayi tana kallon sarah da mamaki tace miye haka kikayi akan me zaki dawra mun alifin da ba ninayi
ba
Zama sarah tayi kan kujera tana dafe goshi tace I am seeking tried of this girl wallahi ba karamin dakewa nakeba kafin natsaya agabanta ina mata magana
jdagowa tayi takalli aysha tace wai yakukayi da AK ne akan zancan barinta gidannan meyake jira da ita
tsaki ausha tayi tana zaunawa bakin gado tace na tambayeshi yatsaya mun kame kame wai muduba grany..... batada lafiya .....yana bukatr hujja kafin yasaketa
dariyar mugunta sarah tayi tana kuantar dakanta kan kujera tace hujja ko ???
To ni zan bashi hujja just wait and see
grany ce kawai zata bani matsala
Cike da farin ciki aysha tace idan ma grany ne bakida matsala saboda naji tace gobe zasuje Kaduna itada inna ameena amma kuana 2 kawai zasuyi
Murmushin mugunta sarah tayi tace good
Ina wannan Alin cousin dinta dakika ce yana damunki awaya
yamutsa fuska aysha tayi tace yana nan miye
Tashi tayi tafita tana fadin ki tabbata kunyi fira mai dadi dashi ayaw har ya yarda cewa kin amince dashi gobe zan gayamaki sauran plan din
Dakallo aysha tabita tana murmushi har tafita sannan takuanta tana fadin bakida kyew sarah ni kuma zanci gaba da binki ahaka har nacimma burina na auren AK daga nan kuma I will show u the worst part of me
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na(Maryam Mhd)
1⃣2⃣5⃣
Washegari dasafe sarah ta isko asma'u apalo kusa da ita tazauna tace sister dan allah wata alfarma nakeso kimun
murmushi asma'u tayi tace ina jinki menene
Rada tamata akunne asma'u tayi murshi tace OK badamuwa amma mezai hana kigayama AK ainasan bazai hana ba
Rungumeta tayi tace thank u sister amma banaso Yaya yasani nafiso semun daidaita tukunna
tashi asma'u tayi tanufi kitchen tana fadin to bari nadora yanzu kar yazo bamu gamaba
tana tashi aysha tazo tazauna kusan sarah tana fadin wow good acthing sarah naga kamar ta yarda ko?
"eh amma ina fata dai kinyi abunda nace
Nuna mata wayar ta tayi tana fadin kalla kiga garan har ya amince shima naga alama kamar dan hannu ne har da fadin wai inaga ba matsala idan yazo badasanin AK ba
Dariya sarah tayi suka tafa
Kowa nazaune apalo grany suka fito cikin shirin tafiya AK yayi jigum kamar zaiyi kuka se tsokanarsa asma'u keyi tana dariya
Amir yaron inna ladidi se yawo yake da camera ahannunsa yana musu video
Tashi sukayi gaba daya zasu raka grany airport ganin asma'u batada niyyar tafiya yasa AK yace chitti muje mana
Langwabar dakai tayi tace ABI kuje kawai banajin dadi bazan samu damar zuwaba
kureta yayi da ido nadan lokaci sannan yace anya kuwaaaa ni banga kinyi kama damara lafiya ba
Jan hannunshi sarah tayi tana fadin Yaya muje mana tace batajin dadi dolene
Sallama suka mata suka tafi bayan kowa yashiga mota suntafi aka bar aysha da sarh atsaye jikin motarsu kamar zasu shiga suna ganin kowa yatafi sarah taja hannun aysha suka koma ciki suka labe awani daki batare da asma'u tagansu ba cikin rada sarah tace aysha kintabbata zaizo kuwa
"eh mana yacemun yana hanya fatana dai kawai AK yadawo kar yakwapsa mana
"Karki damu nasan zai dawo
Suna nan atsaye Sega Ali ya shigo gidan se shan kanshi yake yana shafa saje
Dariya sukayi suka tafa hannu
kiran aysha yayi awaya tadauka cikin muryanta mai jan hankali tace sweetheart ka iso
"eh baby kina ina ne nakosa naganki
danni inba naganki akusa dani ba bazan yarda wai dagaske bane
Tabe baki tayi tace I am in my room can u meet me there
" tsalle yadaka yana cije yatsa yace why not baby just tell me where is the room
dariya tayi suka tafa da sarah sannan tamai kuatancen dakin su asma'u tace yasameta acan
Dakallo suka bisa har ya haura sama sannan suka fito suka shiga dakin aysha sarah tace idan muka tabbatar yashiga se murufe kofar kinga idan AK yadawo ba abunda zai hana yagansu tare daga nan kuma .....
Kinsan sauran
ahankali yatura kofar yashiga sedai yaga bakowa adakin zai juya kenan yaji motsi a dressing room
Komawa yayi ya kuanta kan gado yana fadin come out baby i can't wait to see u!!!!
asma'u na dressing room tana sa kaya batasan meke faruwa ba tana fitowa tagansa rigingine kan gado
cak ta tsaya tana kallonsa kamar amafarki tama kasa tantance mafarki takene ko gaske Alin datasani ne ko maikama dashi daga ina yake meyakawosa dakinta
tana nan tsaye taji anturo kofa atsorace suka kalli kofar suduka
Nunfashinta ne yakusa daukewa ganin AK tsaye bakin kofa kamar gunki se rawa jikinsa keyi ga idonsa daya rikide yayi ja kamar gawta
sorry.....
Yafada cikin wata iriyar murya yana barin dakin dakyer yake tafiya danwani jiri ne ke dibarsa
wasu zafafan hawayene suka zuboma asma'u cikin rawar murya tace Ali meyakawoka dakina mekakeyi anan Ali wannan wane kalan tumasanci ne kayi haka
atsorace yamike tsaye yana fadin asma'u mekike nufi kar kicemun nan dakinkine nashigo dan allah
Girgiza kai tayi tafita daga dakin tana sharan kwalla
apalon kasa ta isko AK azaune yadafe kai matsowa tayi kusansa adan tsorace tace ABI I....
Dakatar da ita yayi tahanyar daga mata hannu yace no don't say anything
Saboda komai zaki fada bazai maki anfani ba chitti u why ..........just leave
Juyawa tayi tana fashewa da kuka
karo sukaci da Ali yana sakkowa zaiyi magana tadakatar dashi cikin rawar murya tace
Bansan meyasa kayi hakan ba amma kasani idan har wani Abu yasami aurena I won't spare u
tana kainan tawuce da gudu tashige bangaresu
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: bayanda batayi da AK ba akan ya yarda da ita amma yaki cikin sheshshekar kuka tace ABI wai me kadaukeni ne
Taya kake tunanin zan aikata abunda tun ina gidanmu banyishi ba se yanzu dayagiyar aure ta haw kaina why will I do that
Dagowa yayi yana kallonta da jajayen idanuwansa cikin kakkawsar murya yace ni ne zantambayeki mekika daukeni asma'u da ace bani naganku da idona ba wani yagayamun dabazan taba yarda dashiba amma kinbani mamaki bansan dalilin dayasa kika kasance haka ba amma kisani na ysaneki banason ganin fuskar ki kije.....
atsorace takai hannu ta toshe mai baki cikin tsananin kuka tace a'a a'a ABI dan allah karkamun haka
katausayama ummata wallahi zata iya rasa ranta
ABI kayarda dani wallahi bantaba aikata irin wannan kazamin aikin ba bansan meyakawoshi dakina ba I am confuse ni kaina bansan meyake faruwa ba
Bige hannunta yayi daga kan bakinsa ya mike tsaye yana juya mata baya yace
Sanin kanki ne cewa koda ina sonki bazan iya cigaba dazama dakeba karma kiyi tunanin kishinki nake a'a kawai ina takaicin yanda kika ari rigar mutunci kike aikata abunda kikaso kowane mai laifi daya musanta lafinsa yana bukatar abashi dama yagabatar da shaida
Juyowa yayi yana kallonta yace to nima zan baki dama just 24 hours kikamun wata shaida dazata nuna baki aikata abunda nake zarginki akai ba yana kainan yaraba tagefenta yawuce yana fadin karki manta awa 24 kawai nabaki idan har suka cika baki kawomun shaida ba to karma kijira se nakoreki dakaina dan bazaki ji dadi ba
Dakallo tabisa har yabacemata sannan takuantar dakanta kan kujera tana rera dan marayan kukanta mai ban tausayi
sarah dake labe tana lekenta ta wuce daki tana kwashewa da dariyar mugunta seda tayi mai Isarta sannan aysha tace sarah nifa binki kawai nake a plan dinnan amma bangane Kansa ba
Dariya tayi tana zama kan kujera seda tajima tana dariyar keta sannan tanatsu tafara magana kamar haka
idan baki manta ba kintaba gayamun cewa kinji lokacinda asma'u ke ba AK labarin wannan Alin yaso ya aureta which means tsohon saurayinta ne
Su maza suna wani hali Wanda koda basa son mace to dazaran andaura musu aure da ita zakiga suna kishinta
Shikuma kishi yana daga cikin abubuwan dakesa maza saurin sakin mace musamman irin wannan
Nabukaci dakija hankalin Ali ajiya saboda inaso ya yarda cewa kinasonsa dan musamu yamana aiki cikin sauki
danatabbatr ya amince zai zo yau to se nafara tunanin hanyar dazanbi nahana asma'u fita raka grany batare dakowa yasan ni nahanata ba
Shiyasa naje nasameta dacewa akwai wani saurayina dazaizo yau kuma banaso kowa yasan dazuwansa inaso tazauna mumasa girki dasauran su ba bata lokaci ta amince
lakacinda taki tafiya raka grany nahango rashin yarda da ita karara a fuskan AK kuma hakan shiya taimaka aikina yazo dasauki
Bayan Ali yazo muka turashi dakin asma'u naso ace munje munkulle kofar dakin sekowa yadawo ya iskosu tare bansan meyadawo da AK dawuriba amma duk dahaka komai ya je daidai
Dariya aysha tayi tana tafa hannu ta jinjina ma Sarah sannan tace to ya ake ciki yasaketa ne
girgiza kai tayi hade da tashi tafara kaikawo adakin tana fadin baisaketa ba bansan meyasa yake tausaya ma wannan ummar tata ba
yabukaci takawomai shaidar dazata wanketa amma nasan ko mezatayi bazata taba samun shaida ba ina mai tabbatar miki dacewa nan da gobe dole tabar gidannan daga nan kuma senaji da khadeeja
dariya aysha tayi cike dafarin ciki aranta tana fadin Weldon sarah kinmaida mun aikina mai sauki batare Dana wahala ba
AK yana fita wurin ahmad yanufa yazayyane masa kap abunda yafaru har lokacinda yabama asma'u
damamaki ahmad ke kallonsa har yagama bashin labarin sannan yamike cike da takaici yace AK badai kana nufin kayarda asma'u zata aikata abunda kake zarginta dashiba bansan wacece itaba amma I am 100% sure bazata taba aikata haka ba
"oh to zanmata karyane ko kuma ni makaho ne incemaka da idona nagansa haba ahmad
adakina fa nagansa akan gadona she was standing there looking at him kuma kacemun wai bazatayi hakan ba
To gayamun meyakaishi dakina meyake akan gadona idan ziyara yakamata meyasa basu zauna apalo ba haba ahmad nifa ba sakarai bane
ajiyar zuciya ahmad yasauke yana zama kusa da AK cikin sassanyar murya yace
inaganin kamar dama yayi hakan dawata manufa ne maybe yanajin haushin auren datayi ne.... ko kuma har yanzu yana sonta ...badai banza ba AK amma baikamata kazargi asma'u ba tunda baka kamasu suna aikata hakan ba in fact bama wuri daya kagansu azaune ba so u have no right to accuse her
girgiza kai AK yayi yana dafe goshi yace ahmad bazaka gane bane saboda bakai ne ahalin danake ciki ba
Murmushi ahmad yayi yace are u jealous
"No I am not kawai dai ina kokarin kare mutuncina ne
Daddare asma'u tashigo dakinsu sedai cak tatsaya tana kallon yanda AK yayi watsi dakomai nadakin gabadaya yabirkita dakin bedsheets da pililluka duk yawatsar dasu gefe
Azaune tagangosa kan kujera yakuantar dakansa idonsa alumshe kamar mai bacci amma yana shafa goshinsa ahankali
adan tsorace take takunta har ta isa kusansa cikin rawar murya tace ABI are alright ?
azabure yamike yana damko kafadunta dakarfi seda nunfashinta yakusa daukewa saboda tsoro
matseta yayi jikin bango har tana jin bugun zuciyarsa
Hannunsa daya yasa ya damko kugunta yamatseta dajikinshi dayan hannun kuma ya zagayo dashi bayan wuyanta
Nan take jikinta yafara rawa muryanta har rawa take saboda tsoro
Kokarin kwace kanta tafarayi tana fadin ABI what are u doing let go of me please
Bakinsa yakai saitin kunnenta cikin rada yace meyasa zan kyaleki .....niba mijinki bane....tunda har zaki iya bari wani yatabaki why not me.....I see u can feel my touch why don't u like it
Tureshi tayi tana shigewa dressing room ta fashe dawani irin kuka mai cin rai
tajima tana kukan secan cikin dare tafito amma bataga kowa adakin ba ahankali ta tura kofa taleka Palo
Kuance tahangosa kan 3sitter da alama ba bacci yakeba dan har yanzu yana murza goshinsa
Komawa tayi tafara tattare dakin kamar wacce aka zarewa lakka banda kuka ba abunda take
bayan tagama tazauna abakin gado tana rungume pilo jin kanta take awani irin yanayi datakasa banbance wane iri ne tarasa meyasa take fargaban rabuwa da AK kuma tasan hakan yazama dole tunda batada wata shaidar dazata gabatar mashi dazai hana yasaketa gobe
[19/07, 17:03] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣3⃣0⃣
daren ranar haka asma'u tayishi banda kuka ba abunda take har garin allah yawaye idanuwanta sun kunbura sunyi ja
lokaci guda har tarame
bangaren Ali ma haka yawuni ya kuana cike da damuwar rashin sanin halin da asma'u keciki gashi tunjiya yakeso yagayama AK gaskiyar abunda yafaru amma yaki sauraronsa
har saida su inna suka fahimci akwai abunda kedamunsa ba tambayar dabasu masa ba amma yaki yace komai
kasa hakuri yayi safiya tayi ana gama sallar asuba yanufi gidansu asma'u
haduwa yayi da AK yafito daga masallaci yana ganinsa yakauda kai kamar bai gansa ba
yana kokarin shiga gida yayi saurin shan gabanshi yana hada hannayensa yace AK dan allah katsaya ka saurareni tun jiya nake bibiyanka kabani dama nama bayanin gaskiyar lamarinnan
dagowa yayi yana kallonsa da rinannun idanuwansa cikin murya mai kaman rada yace
mezaka gayamun Ali wane bayanine zakamun Wanda ban saniba darajar su inna kakeci narufama asiri amma idan katakuramun wallahi se Insa adaureka ...
yana kainan yayi gaba yabarsa atsaye yana binsa dakallo
Yajima atsaye yana kallon get din gidan jiyake kamar yashiga yaga halin da asma'u take ciki amma yana tsoron abunda zai biyo baya hakanan yahakura ya juya yana takaicin abunda ya aikata
yana isa gida yakira khadeeja tasamesa afilin gida damamaki tace Ali lafiya wai meyake damunka ne
shakan iska yayi yafurzar sannan yace deeja yau kunyi waya da asma'u ?
girgiza kai tayi tana fadin a'a lafiya
"I don't know amma dan allah idan bakya komai kidan lekata mana kiga yatake
matsawa tayi kusa dashi tana fadin Ali bangane naje nadubata ba meyasameta
zaiyi magana kenan sukaji anturo kofa atare suka juya ganin asma'u yasa khadeeja tayi saurin isa wurinta cike da damuwa take kallonta tace ammah meyasameki yanaganki haka bakida lafiya ne
Karasowa wurinta Ali yayi cikin rawar murya yace asma'u are u ok ina kiran wayarki kinki dagawa I was so worried ina fata dai ba....
bai karasa ba yaji saukan lafiyayyen marin dayahanasa karasa magamarsa
atsorace khadeeja tadafe kuncinta dan yanda taji marin bazata tadauka ita aka mara
cin kwalar shi asma'u tayi cikin sheshshekar kuka tace Ali menamaka zaka mun haka meyasa tunda baka shafamun bakin painti ba seda nayi aure meyasa.....
Takarashe maganar tana sulalewa akasa tadora kanta akan kafarsa tana fashewa dawani irin kuka mai ban tausayi
lokaci guda itama khadeeja tafara kukan durkusawa tayi kusa da ita tana dafata tace ammah meyasameki meyake damunki ne yaushe kika fara boyemun damuwarki ..
Ganin asma'u takasa bata amsa yasa tamike tsaye tana jifan Ali dakallon tuhuma cikin wata iriyar murya tace mekamata tunda naganta awannan halin natabbata kamata abunda yafi karfin tunaninta
kauda kai yayi dan tuni kukan dayake dannewa yaci karfinsa cikin kukan yake fadin
deeja ni kaina bansan meyake faruwa ba jiya wannan yarinyar aysha tagayyaceni gidansu wai nazo tana son ganina ta amince dani dafari ban yardaba amma tunda ta turomun wasu banzayen pictures da videos dasuka sa narasa natsuwata kawai naji ba abunda nakeso irin na ganni kusa da ita amma wallahi banje gidan dawata manufa ba ...
katseshi asma'u tayi dafadin wannan zancan banza kake Ali idan har wurin aysha kaje dagaske meyakaika dakina akan gadon mijina what kind of rubbish is that
dafe kansa yayi yana fadin yes nasan nashiga daki amma bansan ko nawaye ba karki manta ni bako ne ita tamun kuatancen dakin tace mun natane nasameta acan amma ni bansan cewa dakinki bane kuma kema kinsan ba halina bane ...yana kainan yawuce cikin gidan rai bace
tunda yafara magana khadeeja kebinsa da ido tana jin zancan nasa banbanrakwai dan basosai ma takejin meyake fadaba saboda yanda maganar ke fita dakyar daga bakinsa
Durkusawa tayi tana share mata hawaye cikin sassanyar murya tace ammah dan allah kigayamun meyake faruwane ko naje nagayama Umma ne
a'a muje kirakani gida zan gayamaki...
fita sukayi daga gidan akan hanya take bama khadeeja labarin duk abunda yafaru har lokacinda AK yabata natakawo masa shaida ko tabar masa gida
takare zancan dafadin khady wasu lokutan baka sanin yakake ji agame damutum se karabu dashi bansan miye so ba bantaba yiba amma inada tabbacin abunda nakeji agame da ABI shine so kowa da yadda kaddarar soyayyarsa take zuwa masa arayuwa amma ni tawa inaga bata zomun a saa'a ba
ajiyar zuciya khadeeja tasauke datagama jin bayanin yayartata
cike da tausayi tace ammah inaga AK yabullo dawannan hanyar ne dan yasamu yarabu dake cikin sauki batare da anga laifinsa ba dama Yajima yana Neman hujjar dazata sa yasakeki to bare yanzu dayasameta ahannu gashi kuma grany batanan
kawai kisa aranki ba abunda zai faru sai alkhairi idan rabuwa kukayi ma kidauka hakan shine yafi maki alkhairi tunda dama can ba wani dacewa kukayi ba tunda bazaman aure kuke atsakaninku ba
Murmushin dayafi kuka ciwo asma'u tayi tana girgiza kanta tace khady bazaki gane bane nasan bazaman mata da miji muke dashiba amma kuma inason zama dashi ahakan duk danasan cewa hakan ba mai yuwa bane saboda banada wata shaidar dazata hana faruwar hakan
Shiru sukayi kowa da tunanin dayake aransa har suka isa gida seda khadeeja tarakata har bangarenta sannan tamata sallama akan se sunyi waya anjima
Tana fita tahadu da AK zai shigo nufota yayi yana fadin ohhh hi little sis yaushe kikazo
Tagefensa tabi tawuce batako kallesa ba bare yayi tunanin zata amsa masa
saurin shan gabanta yayi yana murmushi yace wait wait deeja ba fada me yakawo gaba ko baki ganeni bane nine fa ....
katseshi tayi dafadin Yaya wai ya kake acting kamar bakasan mekayi bane karo nafarko nahango rauni da kasawa a idanuwan yayata kuma duk tadalilinka
yaya bansan ya kagansu ba maybe atsaye ne ,azaune ko akuance wuri guda abu daya nasani shine koda mutanen duniyar nan gaba daya zasu taru su zargeta akan wannan abun to ni khadeeja (tafada tana nuna kanta dayatsa )
Zan shaideta akan bazata taba aikata makamancin wannan kazamin aikin ba
hawayen fuskarta tashare sannan cikin rawar murya tace Yaya gatanan kayimata abunda kaga dama amma kasani idan har wani abu yasameta tadalilin wannan case din to nmbanajin zan taba yafemaka
tana kainan tayi gaba abunta tana gyara fuskarta dayajike dahawaye
dakallo yabita yana murmushi har tafita sannan yawuce ciki
apalo yazauna yana kallo can anjima asma'u tazo zata wuce yakirata nan take taji gabanta yafadi dan tasan baiwuce zaimata tuni da lokacinda yabata bane
Jiki asanyaye takaraso wurinsa daga gefe tazugunna tana jira taji mezaice
Bring my coffee.... yafada batare dayakalleta ba
da mamaki tadago tana kallon fuskarsa bayabo ba fallasa juyowa yayi yakalleta suka hada ido tayi sawrin sadda kai kasa tana murza yan yatsunta
kureta yayi da ido nadan lokaci sannan yace matsalarki ta tashi daga kan ido takoma kan kunnene kome nace kikamun coffee dina ko bakijiba
saurin tashi tayi tafita ba'adau lokaciba tadawo dauke da coffee din sedai ta isko aysha apalon tana zaune kamar zata shigemai jiki se fira suke suna dariya
Mikamasa coffee din tayi tana daure fuska bata ma yarda tasake kallonsuba
Kin karban coffee din yayi ahnnunta seda yaga tana kokarin ijiyewa sannan ya karba yana kallon fuskarta yace yanaga kin dame fuska ne tunda saurayinki zai iya zuwa wurinki to miye dan budurwata tazo wurina
saurin juyawa tayi zata bar wurin yacabko hannunta cak tatsaya batare datajuyo ba shima kuma bai janyota ba cikin murya mai kaman rada yace inafata baki manta yanda mukayi dakeba
"ban manta ba
"zuwa gobe idan har baki kawomun ba zaki tafi gida
share hawayenta tayi da dayan hannun batare data juyoba tace
yaune ba gobe ba saboda haka yau din zantafi
Murmushi yayi shima batare da yadago yakalleta ba yace gobe zaki tafi saboda naga alama kinada bukatar Karin lokaci
shiru tayi batace komai ba dan tana bude bakinta kuka ne zaifito da kyar ta iya fadin free my hand
sakin hannunta yayi tawuce daki ta rufo kofar tana sulalewa awurin tasaki kukanta mai ban tausayi
cike da bacin rai aysha tace AK bangane ka karamata lokaciba ko shekara zatayi batada wata shaidar dazata gabatar garama kawai kabarta ta tafi
Juyowa yayi yana kallonta yace ya akayi kikasan bazata taba samun shaida ba tukunna ma ya akayi kika San inda maganar mu tadosa bayan nidai nasan bamuyita dakeba ko ita tagayamaki
Saurin girgiza kai tayi atsorace dan se alokacinma tagane subutar bakinda tayi
Da daddare asma'u tafara hada kayanta tana sakawa a akwati har wannan lokacin bata bar kuka ba rigar AK tagani acikin drowarta wacce ta taba sakawa a hotel dawkota tayi tadawo bakin gado tazauan tana tunano dramar dasukayi ranan rungume rigar tayi tanashakan kanshin turarensa hawaye na tsere akan kuncinta
jin anturo kofa yasa tayi saurin ijiye rigar tana share hawayen fuskarta
karasowa yayi bakin gado yana daga rigarsa yana murmushi yace ohh my favorite shirt kallon asma'u yayi cikin sigar tsokana yace ina data dai ba saceta zakiyi ba
kauda kai tayi batace komaiba
Ijiye rigar yayi saman akuatinta yana fadin ok I understand zakiyi missing dina shiyasa kike bukatar wani abu nawa dazaki rika tunawa dani ko
Runtse idonta tayi tana damke bedsheets dakarfin gaske aranta tana fadin yes zanyi missing dinka ABI amma bana bukatar abunda zai tunamun dakai saboda bazan taba mantawa dakaiba
Dawkan gyalenta yayi yana dariya yace nima kinga sekibani wannan lippayan taki dan inrinka tunawa dake ...yakarashe maganar yana labace baki irin nayara
kwace gyalenta tayi tana fadin bazan badaba mezakayi dashi kuma ba lippaya bane gyale ne
hannu yakai zai dauka tayi saurin rufe akwatin tana tureshi daga wurin tace ABI dan allah kabarni kar kakara tabamun kayana
Dariya yayi yace chitti tsaya mana miye nafada kuma muda zamu rabu gobe kinga kin huta dani kamata yayi yau mukuana muna fira tunda itace ranar karshe awurinmu
turasa tayi har bakin kofa tana fadin jeka banaso ko yanzu kabarmun abubuwa da dama dabazan manta ba ya isheni haka
bude hannayensa yayi yanufota yana fadin chitti I'm gonna miss uuuuu
saurin turasa tayi tana rufe kofa tana share hawaye tadawo tacigaba da hada kayanta
Dakin sarah yanufa ya iskota zaune da aysha suna fira zama yayi akaci gaba dafirar dashi
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣3⃣5⃣
washegari dasafe.....
daki tashigo rike da coffee din AK cikin flax da mug tadoroshi akan faranti har wannan lokacin tana hawaye jikinta gabadaya yayi sanyi kan bedside drawer tadorashi tana kallon photon AK dake ijiye awurin yana sanye da faran shirt da murmushi afuskansa yayi kyew sosai
ahankali takai hannu tadauki frame din tana murmushi tashafo fuskansa hawayenta nadiga akan frame din
rungume photon tayi akirjinta tana runtse idanuwanta hade da cije lebenta nakasa hawaye na tsere afuskanta
zama tayi bakin gadon tana kallon photon cikin rawar murya tace
ABI meyasa bazaka yarda daniba ABI nasaba dakai meyasa kake kokarin nisantani ga gareka lokacinda nafi bukatarka arayuwata
tayu natakuraka kana so karabu dani kodan ka auri wacce kake so
ABI it's very difficult for me to leave without u
Sarah ce taturo kofar dakin tashigo tana nunata dayatsa ta kwashe da dariya
saurin juyawa tayi da mamaki tana kallonta
karasowa tayi tadafa kafadanta sannan tasa yatsa tatabo kwallan dake kuncin asma'u cikin murya mai kaman rada tace
ohhhh abun ba dadi ko ?
nataba shiga wannan halin amma bawanda yadamu dahakan bawanda ya tausayamun bawanda ya rarrasheni
saboda haka kema kiji abunda naji
cike da mamaki tace sarah wannan wace kalan banzar magana kike gayamun
Dariya tayi tace kima gode allah kinsamu mai gayamiki banzar magana ni kallon banza ma bansamu wanda yamun ba
Idan baki manta ba nayi alkawarin senasa kin zubar da kwalla kamar yanda nayi I always keep my promises
ko baki fada ba nasani AK yasakeki saboda naga lokacinda yabaki takarda dasafe karki bata mana lokaci kitashi ki fice daga gidan nan kafin AK yadawo yasameki
Tashi tayi tafita daga dakin tana fadin idan kinje gidanku kyayi kukan da hujja
dakallo tabita har tafita tana takaicin hali irin na sarah
rungume photon tayi dakarfi tana fashewa dakuka mai cin rai tajima ahaka sannan da kyar ta tashi tana rike da frame din tasaka shi a akuatinta sannan tadauki farar takardar da AK yabata kafin ya fita tasaka ajakanta tana karema dakin kallo tafita kamar wacce batada jini ajikinta
ahankali take takunta tana janye da trolley dinta har ta iso palon kasa
azaune ta isko sarah da aysha suna jiran sakkowarta suna ganinta suka hau dariya suna gayamata bakaken maganganu
Dariya aysha tayi tana kallon asma'u taje sarah anya kwa bazamu duba akwatinnan ba kinsan halin yan can...
dariya sarah tayi tamike tanufi wurin asma'u tana fadin aysha ni bandamu da me tadauka ba kawai dai tabarmana gida shine damuwata
Jan hannunta tayi tanufi hanyar fita da ita itadai asma'u jikinta gaba daya yayi weak tamakasa magana ita abunda yadameta daban fatanta tasamu damar dazatama AK kallon karshe gashi rabonta dashi tunsafe
dakarfi sarah ta turata waje yar kara tayi zata fadi kawai tajita akan kirjin mutum
lumshe ido tayi tana shakar kanshin turarensa mai kuantar da hankali
Janyeta yayi daga jikinsa yana maidata gefe
su grany dake bayansa suka karaso dasauri suna tambayar meyafaru
Dagudu taje ta rungume grany tana fashewa da kuka
atsorace grany tarikota tana fadin asma'u lafiya menene ganin takasa bata amsa yasa tajuyo tana kallon sarah tace ke wai lafiya meyake faruwa ne
daidai lokacin khadeeja takaraso wurin tana riko asma'u tace ammah mesuka miki kike kuka kigayamun idan sun miki wani abu
karasowa sarah tayi ta finciko asma'u tana fadin karma ganin grany yasa kigara tunanin zakici gaba dazama anan gidan wallahi se kinfita tunda....
bata karasaba khadeeja tadauketa dawani wawan mari tana nunata dayatsa cikin kakkausar murya tace
Mind ur business winch gidannan ko rayuwarta ce aciki zata barshi saboda ba farin ciki acikinsa amma kibari mai gidan ya koreta bake ba
Kai wai meyake faruwane .....
Grany tafada tana daka musu tsawa
ahasale sarah tace grany barin gidan zatayi saboda AK yasaketa dalilin kamata dayayi tana cin aman....
Bata karasaba AK yadaka mata tsawa yana fadin sarah shut up
Juyawa sukayi gaba daya suka kallesa banda asma'u dakanta ke kasa tana murza yatsunta dakarfi har tana jin zafi
karasawa wurinsa sarah tayi tana riko hannunsa tace Yaya meyasa zanyi shiru bayan abune dayazama dole kowa yasani
Kuace hannunsa yayi cikin kakkawsar murya yace bai zama dole kowa yasani ba saboda duk abunda yafaru ba gaskiya bane kawai munzargeta ne akan abunda bata aikata ba
Saurin dagowa asma'u tayi tana kallonsa da mamaki
Haka ma sarah take kalkon asma'u da mamki tace yaya kamar ya bata aikata ba takawo maka shaidar ne
kallon grany yayi yafara bata labarin duk abunda yafaru sannan yakare dafadin
daga baya nagane duk plan ne shiryashi akayi dan afitar da ita daga gidan kuma bakowa bane yashirya se sarah
Yana fada yana nunata da yatsa atsorace tadago tana kallonsa da tsananin mamakin ya akayi yasan haka
Aysha kuwa jitayi kamar taruga da gudu saboda tsoro amma jin an ambaci sunan sarah yasa tasauke ajiyar zuciya tana lumshe ido
Juyowa sukayi gaba daya suna kallonta
Cike datakaici yace kinyi mamakin ya akayi nasani ko to kisani ita karya fure take bata ya'ya
Kwarai dafari nayarda cewa ta aikata hakan kuma nayi niyyar idan har bata kamun shaida ba zan saketa saboda Sam naji banason ganinta na tsaneta amma daga baya nasamu shaidar data nuna mun cewa sharri aka mata ke kika shirya komai dan kicimma burinki na korarta daga gidannan
Wayarshi yaciro daga aljihu yamika mata yana fadin gashi idan baki yarda ba zaki iya dubawa
Idan Baku manta ba ranar da su grany zasu tafi amir yana yawo da camera yana daukan video sarah takoresa daga wurin dan bataso yana daukanta
Shi kuma ganin haka yasa yaje dakinta ya ijiye camerar jiya bayan nadawo daga masallaci na iskoshi apalo yana kallon video din ranar dayadauka yana ganin nazauna yamika mun laptin din yace inkalla
Ban kulashiba saboda alokacin ina cikin damuwar abunda yafaru har zanrufe laptop din kawai naga abunda ya birkita mun tunanina lokacinda sarah take take bama aysha labarin yanda tashirya plan dinta
I was shocked saboda ban taba tunanin sarah zata aikata irin wannan kazamin aikin ba
Juyowa yayi yana kallon sarah cike da takaici yace I feel ashamed to call u my sister kin bani mamaki kinbani kunya sarah yaushe kika zama haka
fashewa tayi da kuka tana kallonsa cikin daga murya tace
Ni kaina bansan yaushe nazama haka ba amma komai nayi Kaine sila kasabamun komai nakeso kana mun amma lokaci guda da wannan tashigo rayuwarka kacanza mun kai dakanka kadawo kana ruguza mun farincikina wai dan kafaranta mata da yan uwanta kai kafi kowa sanin cewa duk abunda nakeso to zanyi komai dan ganin nasamesa
Saboda haka dole ne namallaki abunda nakeso kuma dole tabar gidannan saboda kasaketa
wurin asma'u tanufa tana jan hannunta tace wallahi dole kibar gidannan
Fizgota AK yayi yasaukemata lafiyayyen mari atsorace tadafe kuncinta tana kallonsa cikin sassanyar murya tace kamun duk abunda kaga dama amma koda zan rasa raina setabar gidannan
Hannu yamika ma asma'u yana fadin bani takardar
Tana mikamasa yawarware takardar yana nuna ma sarah
Ido tazaro tana kallon farar takardar daba komai aciki
" kingani saboda haka ba dalilin dazaisa tabar gidannan u can die if u want
saurin dagowa tayi tana kallonsa da jajayen idanuwanta dasuke zubar da kwalla
jadabaya tafarayi tana fadin AK kabani mamaki gaba daya kacanza mun yau Kaine kecewa namutu in inaso saboda wannan banzar
juyawa tayi takoma ciki aguje tana fadin AK natsaneka I hate u Ku dukanku senasa kunyi nadamar abunda kuka mun u won't get away With this
Saurin bin bayanta aysha tayi dan gudun kar adawo kanta
hannu grany ta tafa tana salati tace oh ni mairo wai ina sarah tadauko dabi'ar turawa ne gaba daya yarinya tacanza
cike da farin ciki khadeeja ta rungume asma'u tana tayata murna
Dariya inna ameena tayi tana kallon AK tace
To gaskiya kabatama matarka rai kacutar da ita se kabata hakuri
Kallonta yayi aransa yana fadin toh fah here comes the love teacher
daure fuska tayi tana fadin bada kai nakeba katsaya kana karemun kallo
karasawa yayi wurin asma'u yatsaya yana kallonta da murmushi afuskansa sassauta muryansa yayi yace
dagaske sena bada hakuri kin.....
baikarasaba yaji tarungumesa dakarfi kamar zata shige cikinsa
Cak ya tsaya nadan lokaci sannan ahankali yakai hannunsa bayanta yarungumota yana lumshe idanuwansa
Juyawa khadeeja tayi tana boye fuskarta ajikin inna ameena dariya sukayi inna tace kajita sekace batasan komai ba ai idan ma kunyar kikeji gara ma ki ijiyeta dan ahmadi bai San kunya ba
janyeta yayi daga jikinsa yana kallon grany yace
grany mukarasa mana kuhuta ga inna ameena ko jakan bata ajeba kodai dakudi acikine
saurin karban jakan khadeeja tayi tana fadin inna kikawo jakan kuje kawai zan biyoku da ita
dariya sukasa gaba daya suka wuce bangaren grany suna raha
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Suna shiga ciki khadeeja takira ahmad awaya tana basa labarin abunda yafaru bai ma tsaya yagama jin karshen labarin ba yakatse wayar cike dafarin ciki ya yanufo gidan
yana zuwa aka bude sabon shafin fira anan suka tsaida magana kan bikin ahmad daza'ayi bada jimawa ba dazaran ahmad yadawo daga tafiyar dazaiyi gobe tunda komai ashirye yake kuma magabata sunsan damaganar
su ahmad baki yaki rufuwa se Satan kallon khadeeja yake yana ji kamar ya rungumota dan farin ciki
agidan suka wuni ranan sedare ahmad da khadeeja suka tafi
bayan AK yarakasu yadawo bangarensa yawuce yana kallon dakin sarah datuanin halin datake ciki ahakanli yataka har yaje kofan dakin hannunsa yakai kan handle din kofar kamar yashiga sekuma yajuya yanufi bangarensa
yana shiga dakin ya isko asma'u tana maida kayanta a drawer
coat dinsa yacire yadora akan gado sannan yagyara tsayuwarsa yasa hannayensa a alijihu yana binta dakallo
daukan coat din tayi daga kan gado tamaidata wurinta
Ganinsa atsaye kamar gunki yasa tajuyo tana kallonsa fuska ahade tace what??
kauda kai yayi yana shafa bayan wuyansa yace nothing kawaidai inaso nabaki hakuri ne akan zarginki danayi duk dacewa kinyi kokarin fahimtar dani amma naki sauraronki I am really so.....
Hannunta takai bakinsa tana girgiza kai da murmushi afuskanta cikin sassanyar murya tace
ABI baka bukatar bani hakuri saboda ko kadan banga laifinda kamun ba in fact ka rufamin asiri hatta iyayena bawanda yasan da maganar ni yakamata nagodemaka akan alfarmar dakamun thank you thank you
Janye hannunta yayi daga kan bakinsa yana murmushi yace come on chitti stop being romantic baya maki kyew
kauda kai tayi tana daure fuska tace wai ni komai sekace baya mun kyew kabar ganina haka fa kanemi karainamun class duk abunda wayayyar mace zatayi nima zan iya ko aysha kar nake kallonta dan ba abunda zata nunamun
Dariya yayi yace ohhh really so u can do anything
dan kwali ta turo gaban goshi tana karkada kafa tace kwarai kuwa idan baka yardaba bet me and see
"Ok tunda kince zaki iya yin duk abunda aysha tayi let's see
Aysha tafara cewa tana sona kafin nace ina sonta can u do that ?
dressing mirror tanufa tana fadin kai bazan iyaba saboda me zanyi karya bayan bana sonka after all ni bantaba cewa inason wani ba so it's not easy for me
Dariya yayi yana zama bakin gado yace dama nagayamiki har yanzu dasauranki kidaina hada kanki da aysha ita tafada dagaske ke kuma pretending ma kinkasa
Dawowa tayi wurinsa tatsaya tana fadin ok fine I will do it ai ba wuya ne dashiba
tashi tsaye yayi yana danne dariyarsa yace ok kuma kiyishi in a romantic way bawai kai tsaye ba
gyaran murya tayi tana saita nutsuwarta kanta akasa tace I ....I...
Dariya yayi yace accept ur defeat chitti bazaki taba iyawa ba I said in a romantic way amma kina Abu kamar mara gaskiya u....u....u what?
"ni gaskiya bazan iyaba I need to practice it kafin in iya yanda zanyi
dariya yayi yace ok to kije kiyi gasace nasamaki
Zama tayi bakin gado tace gobe zan gayamaka nasan zanci amma mezaka bani idan naci
Kusa da ita yazauna yana fadin me kike so
Shiru tayi nadan lokaci sannan tace yawwa idan naci ka yarda zaka daina kirana chitti kuma kadaina tsokanata
Nayarda kuma daga lokacin zan daina raina miki class ...
yafada yana kwaikwayon Yanda takeyi idan tana kwaikwayon maganar aysha
duka takaimasa da pilon dake hannunta ya tashi yana dariya yafita daga dakin
washegari dasafe....
Har lokacin sarah bata fito daga dakinta ba tana zaune ita kadai ko aysha tahana tazauna da ita ba kuka takeba amma idonta yayi ja zuciyarta takeji kamar zata fito saboda bakin ciki
asma'u na bangaren grany bayan sun gama breakfast tacemusu zataje gida tagaidasu Umma
da mamaki inna ameena tace ya zaki tafi gida ina AK fa bashi zai kaiki ba
Shiru tayi batace komai ba
Tabe baki inna tayi tana kallon grany tace Yaya nifa yarannan nabani mamaki anya kwa sunma San miye aure kuwa
kauda kai grany tayi tana fadin oho ganemun hanya wai makaho yaje gulma
Ni tun ina mamaki har nasaba inaga wayewar ce tayi yawa
Zatayi magana kenan AK yashigo tun bai gama karasowa palon ba tace yawwa AK dama nemanka nake
"ai ni dama kullun acikin nemana kike to gani nazo fadi matsalarki
dariya tayi tace dama cewa nayi kadauki asma'u mana kudan fita lunching mana
zama yayi kusa da grany yana fadin
bakuyi abinci bane yau ko kuma isarta ne baiyiba
Daure fuska tayi tana jefamai harara tace kai wai meyasa ba amaganar arziki dakai ne dan fitar dazakuyi kudan shakata shine wani Abu
Sosa kansa yayi yana kallon grany yaga ba alamun wasa atare da ita
tashi yayi yafita yana kallon asma'u yace muje
ahanya shiru sukayi nadan lokaci bawanda yake magana
juyowa yayi yana kallonta cikin sigar tsokana yace are u practicing ?
Gyada kai tayi tana gyara zamanta tace yes kuma zan baka mamaki
Kallon titin tayi tana tana Sosa kai tace wai ina zaka kaimu ne
Murmushi yayi yace badai abinci kike nema ba zan kai 5 stars abincinsu yahadu
girgiza kai tayi tace a'a nidai banaso irin wurinnan abincinsu bawani dadi sai tsada
"to ba 7 stars bare nakaiki idan kuma akwai ayi kauyanku se muje
"Mu bamada wani 7stars simple restaurant mukeda and the food was delicious.....
Tafada tana lashe baki
Karya kuana yayi yanufi unguwarsu yana fadin nayarda muje amma dasharadi
Juyowa tayi tana kallonsa tace wane sharadi ne
"Idan abincin yayi dadi nizan biya idan kuma baiyi dadi ba kece zaki biya
Kauda kai tayi tana fadin a'a gaskiya ban yardaba saboda ko yayi dadi zaka iya cewa baiyiba
Hannunsa daya yadora saman kansa yana murmushi yace I promise ba cheating idan yayi dadi zan fada
Haka sukaci gaba dafiransu suyi fada su shirya har suka iso restaurant din abakin titi yake ga mutane dayawa awurin dariya yafara mata yana fadin kuuut chitti mezan gani haka badai layi zamubi abamu abincin ba
daure fuska tayi tafita batace komai
Biyota yayi yana dariya se kokarin boye fuskarsa yake abayanta wai kar mutane sugansa
bayan sun gama cin abincin suka fita se dariya takemai wai yasha santi
Seda suka biya wurinsu Umma da Momy se yamma sannan suka koma gida
Da daddare AK yana tsaye yasa asma'u agaba yana jira tafadi cewa tana sonsa ita kuma takasa se kaikawo take
harde hannayansa yayi yana kallonta yace chitti please kifada nakosa naji
hararansa tayi tace to wai ma meyasa kakeso kaji nace inasonka kodan kasamu abun da zakajin dadin tsokanata dashi
Dariya yayi yace kawaidai inason naji ne ina tune lokacinda aysha tafada it was awesome
Kauda kai tayi tace to kajuya se infada kasan bantaba yiba
"Come on chitti kawai kidaukeni a matsayin friend dinki ba boyfriend ba
Juyawa yayi zai fita yana boye dariyarsa yace idan kuma bazaki iyaba shikenan se kidaina hada kanki da aysha
Saurin rikosa tayi tana fadin a'a tsaya mana allah zan iya amma kar kamun dariya
bazan yiba .....
Yafada yana gyara tsayuwarsa
Matsowa tayi dap dashi tatsaya seda taja dogon nunfashi sannan tarufe idonta tana jin sonsa nakara shiga har cikin ranta
Kallonta yake yana murmushi dan shi kawai yanayi ne dan Neman tsokana just to have a good time amma badan dagaske yana so tace tana sonsa ba
bude idanuwanta tayi ahankali ta saukesu cikin nasa nan take taji gabanta yafadi tana jin wani yanayi amma tadake cikin wata lallausar murya tace
ABI how can I explain my feelings to u its pain its numbness its like I can see and hear only one thing and that is you!!!
I will never let you go no matter what situation we are in I love and care about u for ever
Sunkuy dakanta tayi kasa tacigaba dafadin
I wish I could tell about my feelings in the morning ,middle of the night when I eats during sleep in happiness and in sadness I just want to tell u that ....
I LOVE YOU !!!
tafada cikin murya mai kaman rada tana kallon cikin idonsa
tsaye yayi kamar gunki tunda tafara magana yake kallonta seda yaji ta tabasa tana fadin ya kaji to
ajiyar zuciya ya sauke yana tafa hannu yace bravo!!!
Chitti excellent
gaskiya kin hadu ina fata dai ba ji kikayi anfada ba ko a film ko book
Daure fuska tayi tana barin wurin tace allah ninayi dan bakasan dauriyan danayi bane kafin nafada shiyasa
Rikota yayi yace ohh to ainace yayi kinyi kokari to be honest kinfi aysha kokari gaskiya kincinye gasar
Dariya tayi tace ok to yamaganar deal dinmu zaka daina kirana chitti daga yau
Sosa kai yayi yana fita daga dakin yace ehhhh toooh gaskiya bansaniba bakina yasaba da chitti amma zan daina tsokanarki daga gobe
Baki bude take binsa dakallo har yafita
cikin kuana biyu aka fara shirye shiryen bikin khadeeja da ahmad har many a sungama magana antsaida daurin aure ranar juma'a
Tuni asma'u suka fara gyara amarya
Ango ma yadawo dashi ake komai ranar da yadawo AK da asma'u sukaje tarbanshi a airport
Bayan sunkaishi gida suka zauan apalo suna fira
anan yaciro wasu agogo guda biyu masu kyew iri daya namace da na namiji yabasu amatsayin tsaraba
Kin karba AK yayi wai bazaiyi Abu iri daya da asma'u ba
Seda ahmad yarokesa yana gayamasa agogon yanada anfani ahaka zaka dauka agogo ne kawai amma yana da wani Abu ajiki inda idan dayanku yashiga matsala yana dannan nan
Ko a ina kake dayan agogn zai fara kara yana nuna jan danja alamun dan uwanka yana cikin matsala he need ur help sannan arrow zai nuna maka direction din inda dan uwanka yake har ka iskosa
karban agogon yayi yana dubawa dan tabbas ya birgesa amma bai yarda zaimasa wani anfani ba
cikin aljihu yasaka shi ita kuma asma'u tun alokacin ta daura nata ahannu
Yana zuwa gida yajanyo drawer yasakashi aciki
Duk abunda ake sarah tana sane amma Sam bata nuna damuwarta ba kawai dai bata shiga har Kansu ne kullun tana dakinta ko palon kasa azaune gaisuwa kawai take hadasu da AK se jefi jefi sukan dan taba fira
amma har yanzu tana nan da alwashin ko zata rasa ranta bazata bar khadeeja ta auri ahmad ba
Bangaren aysha da iyayenta kuwa komai ya cakude masu gaba daya sunkasa gane kan lamarin kwarai AK yafara janye jikinsa daga aysha sukan dan yi fira ko yadauketa sufita amma ba kamar da ba sedai har yanzu yana nan da niyyar zai aureta koda bai saki asma'u ba
tsakaninsa da asma'u kuma shakuwa mai karfi tashiga tsakani da taiamkon inna ameena sukan zauna suyi fira na tsawon lokaci yagan gayamata matsalolinsa kuma tabashi shawara sedai tsokanar se abunda yaci gaba basa zama na minti Biyar batare da sunyi fada ba kuma shike janyo hakan dagangan saboda yana jin dadin yanda take biyemishi
Sonsa se Dada karuwa yake aranta amma har yanzu tana kokarin dannewa bawanda yasan da hakan se khadeeja da ahmad bangaren AK kuma ba wata alama da ta nuna yakamu da sonta sedai yashaku da ita matuka
Ba yanda khadeeja batayi ba kan asma'u tagayama AK cewa tana sonsa kafin lokaci yakure mata amma taki hakan yasa suka hade kai da ahmad wai indai bata fada ba to bazasuyi auren ba
ita kuma taki fada saboda tana tsoron idan tafurta hakan tarasa kulawar datake samu daga garesa
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣4⃣0⃣
sarah ce tsaye tare da wani mutum suna magana
wani photo taciro daga jakanta Tamika mishi tana fadin JJ katabbata ba'asamu wata matsala ba dan aikin bana wasa bane ka kula
karban photon yayi yana kallo cikin muryan mashaya yace wacce daga ciki
wankan tarwadan kayi ahankali tanada wayo ba kyala bace please kar asamu mistake
Dariya yayi irin tasu sannan yasaka photon aljihu yana fadin hajiya bafa yau nafara aikinnan ba to kawai kije zakiga mai kyew nidai kawai inji alert dan alqur'an banda mutunci
Kallonshi tayi sama dakasa sannan tajuya tana fadin base kafada ba nasan bakada shi shiyasa nazo wurinka
tana tafiya yakira yaranshi guda biyu yabasu photon yana fadin gayu gafa aikinmu nayau kuma ga dukkan alamu zamu samu mai tsoka dan naga yarinyar yar masu Jan wuya ce
dariya suka sa gaba daya suka hada baki wurin fadin kai kaga wasu zuka zukan yan mata
daya daga cikinsu yace oga wane kalan aiki za'amusu
a'a guda daya zaku kwamusu mana amma bance kuyi mata komai ba kudai kawai Ku kawota address din yana jikin photon daga baya
"angama oga wannan ai karamin aikin mune wa'yannan yan yaran ai mutun daya ma acikinmu ya ishesu amma wacce daga ciki
juyawa yayi yabar wurin yana fadin kyekkyewar cikinsu kuma kuyi ahankali kar kowa yaganku lokacinda zaku kamata
kallon juna sukayi sannan suka kara kallon photon dayan cikinsu yace
bala kaji yallabai wai kyekkyewar cikinsu to ai suduka kyewawa ne
Dariya Wanda aka kira da bala yayi yana dora yatsanshi kan photon khadeeja yace amma dai kasan wannan tafi gogewa ko haka sukaci gaba da jayayya kowa dawacce tafimashi kyew
Tunsafe asma'u taje dawko khadeeja daga gida kasancewar yau ne ake sa lalle
Har sunkawo bakin get zasu fito khadeeja takoma wai tayi mantuwa fita asma'u tayi tanufi mota tana jiranta
yaran JJ suna daga gefe cikin mota suna jiran fitowar yarinyar daga gidan saboda yanda sukayi da sarah kenan ganin asma'u yasa dayan wanda yace tafi kyew yayi saurin nufar inda take cikin sanda yana ciro handkerchief a aljihunsa yana zuwa tabayanta yakai hannu zai shaka mata handkerchief din kawai yaji ana kokarin fitowa daga gida saurin jadabaya yayi yalabe bayan mota yana kallonsu har suka shiga driver yaja suka tafi
dunkule hannu yayi yanaushe iska cike da takaici ya koma wurin dan uwansa dake cikin mota
anan suka kira JJ suka sanardashi yanda akayi nan take ya hau zaginsu kuma yamusu kashedin idan suka dawo batare da yarinyar ba sai ya aikasu barzahu
sanin zai iya yin hakan yasa ba shiri suka bi bayan motar su asma'u
sarah tana ganin su khadeeja takira JJ tafara masifa akan ba haka sukayi dashiba idan yasan bazai iyaba ya dawo mata da kudinta tanemi wani hakuri yabata akan komai zai tafi daidai kawai dai tayi kokarin turo yarinyar waje sukuma zasu cika sauran aikin
Bayan asma'u takai khadeeja bangaren grany ita kuma tawuce dakinta dan tashirya
Tsaye take agaban dressing mirror tana gyara fuskarta
AK yashigo cikin shirinsa tsap na kananun kaya yayi kyew matuka kusa da ita yamatso yadauki turarensa yafara fesawa
Dagowa tayi tana kallonsa tace ABI ya isa haka mana turare in yayi yawa hawa kai yake kuma ma da lalle namata ne kawai why are u dressing up
daure fuska yayi yace stop treating me like a child I know what I am doing
Dariya tayi tace ohhh fita zakayi ne
"eh ko inzauna baki gaji da ganina ba
juyowa tayi tana kallonsa baki bude tace waaaaa meye anan dabazan gaji daganiba
Dariya yayi yajera da ita a gaban dressing mirror suna kallon Kansu yace kalla da kyew kiga ba yabon kaiba amma kema kinsan kinfini.....bai karasaba yayi sairin fadin I mean nafiki haduwa
Dariya tayi tana tafa hannu tace ABI bakinka yanaso yafadi gaskiya kana hanashi kama daina yaudaran kanka dan kasan nidin dabance
dariya yayi yana kallon bayan rigarta yace ohhh naga alama duk cikin gayun ne kika bar zip abude
Saurin juyawa tayi tana taba bayan rigarta tajishi abude
Murmushin yake tayi tana kokarin jan zip din tace nakasa zipping dinshi ne
"zo in taimaka miki
"to amma karufe idonka tukunna
Juyo da ita yayi yana fadin dan allah can mezan gani abayanki
kokarin Jan zip din yake amma yakiyi dagowa yayi yana kallonta tajikin mirror yace chitti wai dole se wannan kayan kicanza wasu mana
"kaja dakarfi mana se kace ba namiji ba
bata karasaba yaja zip din da karfi yayi sama dashi
thank you ...
tafada tana fita daga dakin
Zaro ido yayi yana kallon abun zip dinta dake hannunsa ahankali ya furta I am in trouble
bayan mutane sun taru aka fara shagali gidan yacika da mutane hakan yasa sarah bata samu damar aiwatar da aikinta ba gashi Sam khadeeja taki bata fuska bare tasamu damar fitar da ita waje
asma'u na hidima da baki Sam bata lura da zip dinta daya fara budewa ba AK yazo yana magana da grany kawai ya hango zip din abude gashi da mutane dayawa awurin har da yan samari
Kusa da ita yaje ya tsaya daga bayanta yana kokarin boye wurin
juyowa tayi da mamki tace miye haka wani Abu kake so ne
Kara dawowa bayanta yayi cikin rada yace muje dakinmu
Zaro ido tayi tace what kamar ya muje daki wai ma bakace fita zakayi ba
hannunsa yadora kan bayanta yace kedai idan munje zan miki bayani
kokarin juyowa take amma yahanata ga mutane sun fara kallonsu ana gulma
aysha dake gefe tana hangosu tuni idonta yaciko da hawaye sarah kuma ko ajikinta abunda yadameta daban
"ABI kabari mana baka ganin mutane suna kallonmu ne
Barin wurin yayi yana fadin shikenan nabari amma kinemi wani Abu kirufe bayanki dan har bra....
bai karasa ba tayi wata irin supper tashige gabansa tana fadin ya ....ya....kuma haka bayan kace kayi zipping dinsa
Matsawa yayi takara shiga gabansa tana fadin ina kuma zakaje tunda kai kabatamun kai zaka kaini na gyara
dariya yayi yace se kinroka kuma da girmamawa
langwabar dakai tayi cikin siriruwar murya tace ABI can u help me please nasan kanada kirki da taimako to nima kataimaka mun kaji
Dariya yayi yace se kince nafiki haduwa haduwa
bai karasa ba tayi saurin fadin haba ai fada ma bata baki ne yanda kake handsome dinnan ina zan hada kaina dakai
Now please muje kakaini daki
sun juya zasu tafi kenan inna ameena ta taresu tana danne dariyarta tace ina zuwa haka
Murmushi AK yayi yace inna daki zamuje akwai abunda zamuyi
kallonsu tayi sama da kasa tace naga alaaaaama to Ku koma bayanzu ba bakwa ganin da mutane ne
Langwabar dakai yayi yace inna please emergency ne yanzu zamu dawo
Dariya tayi tace ohhh bazaku iya jira har awatse ba
Zai yi magana kenan asma'u ta taka kafarsa cikin murya mai kaman rada tace u better keep quite daban abunda kake nufi ita kuma daban inda tafassara maganarka
basu kara cewa komai ba suka raba tagefenta suka wuce ita agaba shi abaya yadora hannunsa akan bayanta
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Suna hawa kan stairs suka hadu da aysha tana atsaye taharde hannaye tana kallonsu
Meyake faruwa ne.....
tafada tana kallonsu daya bayan daya
Murmushi yayi yana kallon asma'u yace ba abunda yafaru kidan bamu waje muwuce
Fashewa tayi da kuka tana fadin AK wallahi abunda kake mun yafara isata ina alkwarin da kadaukamun haka mukayi dakai kuana biyu kacanza mun to wallahi zanje nafadama grany duk abunda yake faruwa
Saurin riko hannunta yayi yanuna mata bayan rigar asma'u yace kinga daki zan rakata ta gyara tunda ni nabata mata
Idan kuma zaki rakata shikenan
Murmushi tayi tana kallon asma'u tace eh zan kaita amma nima zaka fita dani
Mezai hana je kidawo
Hannunsa yakai yaja kuncinta yana fadin baby u know I love u na
saurin barin wurin asma'u tayi tana jin wani azababben kishi na dukan zuciyarta
juyawa sukayi shi da aysha suka fita da dabara dan kar wani yagansu
anyi shagali komai yatafi daidai amarya tasha lalle tayi tsap ga umm tun tuni tafara aikinta wato gyaran jiki kuana biyu khadeeja tayi fresh kyenta yakara fitowa yau zata koma gida saboda gobe daurin aure jibi kuma suci gaba da sauran shagulgulan kamar su sisters day dinner walima da dai sauransu
har yanzu yaran JJ suna waje suna jiran fitowar khadeeja amma shiru sarah najin asma'u da Ummi zasu maida khadeeja tayi saurin gayamusu
bayan asma'u takai Ummi da khadeeja tafito zata tafi tazo bude motar tajita arufe zagayowa tayi wurin driver tana knocking kawai taji an toshe mata hanci da handkerchief din dayasha powder
Kokarin kwace kanta take amma takasa sun jima suna kokawa dashi kafin daga karshi tafadi asume
saurin fitowa dayan yayi Yakama mishi suka sakata amota
Seda suka bar unguwar sannan suka kira JJ nan yagayamusu inda zasu kaita cikin wani dokar daji inda suka tanadeshi dan irin haka
Tafiya ce mai tsawo kafin sukai
bayan AK yadawo da aysha da daddare yawuce daki amma baiga asma'u baidamu ba yayi shirin kuanciyarsa ya kuanta dan atunaninsa tana bangaren grany suna hidimarsu
Ganin karfe daya tayi yaji yafara damuwa da rashinta adakin tashi yayi har zai fita se kuma yadawo yadauki wayansa yakirata tana ringing ba adauka
Yana nan zaune har karfe biyu tayi fita yayi daga dakin yanufi bangaren grany
Koda yaje har sun rufe Yajima awurin yana tunanin yatashesu ko yakyalesu amma zuciyarshi nabashi wani Abu yasamu chitti
Buga kofar yayi ahankali can anjima inna ameena tazo tabude da mamaki take kallonsa tace AK lafiya meyafaru...
Shiru yayi dan baisan mezai cemata ba
Kallon bayansa tayi tana fadin ina asma'u ko wani abune yafaru
Saurin dagowa yayi yana kallonta da mamaki yace inna bangane ina asma'u ba kina nufin batanan
anan dai suka fahimci asma'u tunda takai khadeeja bata dawo ba
Komawa bangarensa yayi ya kuanta hankali kuance yana fadin to wai meyasa nadamu da rashinta akusa dani murmushi yayi yace koda yake nasaba da shirmanta ne
da asuba Abba yafito zaije masallaci kenan yaga motar gidan AK awaje bai kulata ba yawuce saboda kar yamakara salla
Yana zuwa masallaci kuma yamanta se wajan karfe 7 fa'iz yamatso kusa dashi cikin rada yace Abba dazu dazan zo masallaci naga motar AK awaje
dafe kai Abba yayi yana salati yace kaga ni nama manta tashi muje muga allah sa lafiya kila paci tayi suka barta anan
Seda safe yaran JJ suka isa wannan wurin acikin dajin allah ko duhunsa kayane suna zuwa suka Shiga da ita runfarsu suka daureta ajikin iccan runfar sannan suka sanar da JJ sun isa
Cike dafarin ciki yace musu sukula da ita gayanan kan hanya
Su Abba nazuwa suka isko driver amotar knocking Abba yayi amma shiru seda yasakeyi dakarfi sannan drivan yatashi yana date kai yana runtse ido
Saurin gyara zamansa yayi yana kallon inda bude kofar yayi yafito suka gaisa da Abba kansa adaure yake kallon wurin yana kokarin tuna abunda yafaru jiya
kallon juna Abba da fa'iz sukayi sannan Abba ya kalli driver yana murmushi yace sannu ko allah sa dai Lafiya naga alama kamar anan ka kuana
Saurin riko hannun Abba yayi yana fadin malam ina madam
da mamki Abba yace wace madam kuma bayan tun jiya ta tafi gida
Shiru yayi nadan lokaci kana yazauna akan kujerar motar yana fadin dan allah zan samu ruwan alwalwala
kallon fa'iz Abba yayi yace jeka kakamasa ruwan alwalan daga nan kace khadeeja tadamo masa kunu ko tea yadan sha
anan wurin yashinfida sallaya yayi sallah nan khadeeja takamasa tea mai zafi karban tea din yayi ya ijiye yana kallon Abba yace wato malam jiya ina cikin mota azaune ina jiran madam tafito kawai naji ankwakwasa kofa lekowan dazanyi kawai naji anfesa mun wani Abu to daga nan kuma bansan inda nakeba se yanzu shiyasa kaji natambaya ina madam
salati Abba yayi cike da al'ajabi yace allah ya kyewta to miye dalilin haka oho mun gode allah dai tunda basu maka komai ba
Inaga asma'u tafito tajika shiru tazata bacci kake ga dare yayi shiyasa tawuce gida
Karasawa wurin motar khadeeja tayi tana kure wurin da ido tace a'a wani Abu ne yasameta
kallonta sukayi da mamki zugunnawa tayi takasa tadauko sarkan asma'u dake yashe awurin cikin rawar murya tace tabbas wani Abu yasami ammah ga alamun inda tayi kokarin kwace kanta nan ga jakanta akarkashin mota
Azabure suka mike suna nufo wurin hankali tashe fa'iz yaje yakira su Umma nan fa aka fara salati su inna tuni anfara kuka
Nan take khadeeja khadeeja takira wayar AK seda takusa katsewa yadaga yana dariya cikin muryan bacci yace
deeja karfe 2:00 ne daurin auren ko nine angon ai kya barni indan yi bacci ko
Cikin muryan kuka takatseshi da fadin
Yaya ammah tana nan ?
azabure ya zauna bakin gado yana fadin banganeba kardai kice mun ba anan takuana ba tunjiya bata dawo gidannan ba ai
Sulalewa tayi awurin tana sakin wani irin kuka mai cike da tashin hankali
dafata fa'iz yayi yana kuantar mata da hankali Abba kuma yana rarrashin Umma da inna
bashiri AK yasaka kayansa ko wanka baiyiba yafito agurguje daga bangarensa haduwa yayi da sarah ta rikoshi tana fadin
Yaya ina zuwa haka da sassafe
kuace hannunsa yayi yafita yana fadin gidansu asma'u zani akwai matsala zamuyi magana anjima
dakallo tabisa tana murmushin mugunta har yafita sannan ta wuce dakin aysha da gudu tafada kan gado tana murna
atsorace aysha ta tashi tana tambayar menene
Dariya sarah tayi tace gaskiya yau ina cikin farin ciki nacika burina yanzu tunda ahmad yarasa khadeeja ai dole yadawo gareni
da mamki aysha tace wai meyafaru ne kike wannan murnan
Kamo hannunta tayi tana murmushi tabata labarin duk abunda yafaru
Zaro ido aysha tayi tace to yanzu mezaki mata
Dage kafada tayi tace oho ni yanzu nagama nawa duk abunda suka ga dama sumata ba matsalata bace
Komawa aysha tayi ta kuanta tana fadin gaskiya sarah bakida dama se yanzu nakara yarda zaki iya yin komai akan ahmad
Murmushi tayi tadauki wayanta takira JJ yana dauka tace aiki yayi kyew JJ anjima kadan zakaji alert dariya yayi irin ta rikakkun yane fashi sannan cikin muryan mashaya yace nagayamiki aikinki bazai kuana ba kedai kawai ki tabbata kin biyani shine kawai
Karkadamu tafada tana katse kiran
AK na isa wurinsu Abba aka tabbar cewa wani Abu ne yasamu asma'u nan take yakira ahmad yasanar dashi ba bata lokaci ya iso wurin
Nan take suka wuce police station suka yi repot abunka da masu dashi nan take aka shiga Neman asma'u ruwa ajallo har sanarwa akasa gidan TV da Radio
Kafin gari ya waye kowa yasan da batan asma'u hankalin kowa atashe wasu nakuka wasu na rarrashi
AK da ahmad kuwa tare dasu ake nemanta amma har rana tafarayi ba ita ba labarinta
JJ na isa qurin yaran suka bude mashi fuskar asma'u
Saurin ja dabaya yayi yana zabga ashariya
Kallonsu yayi da jajayen idanuwansa yace dan ubanku wane dan jahila ne yakamota acikin
saurin nuna dan uwansa yayi yana fadin oga shine yakamota dama nagayamasa ba ita bace amma yaki saurarona
Cikin rawar murya dayan yace oga kaifa kace kyekkyewa kuma wannan tafi kyew
Wankeshi yayi da wawan wari cikin kakkawsar murya yace kai jahilin inane dan tasha kawai bakaga waccan tafi faso gari bane shine zaku faukomun wannan karamin alhakin inyime da ita
Shiru sukayi kansu akasa suna bashi hakuri
Ahankali asma'u tafara bude idanuwanta har tasaukesu akan wa innan rikakkun mazan saurin ja dabaya tafarayi amma tajita adaure atsorace take kallonsu cikin rawar murya tace su....suwaye Ku....menake anan
kusa da ita yamatso yazugunna yanafadin sorry yan mata tsotsayi ne yahau kanki nuna mata photon yayi yace wannan mukaso kamawa shine muka kamoki inda kike kuma nikaina bansan wurin ba
zatayi magana kenan wayarsa tahau kara ganin sunan sarah yasa yafita daga qurin yana daga wayar
Cike da masifa tace JJ wane kalan aikin banza kamun ne
katseta yayi dafadin hajiya kidan rage muryanki dan allah banason ana cikamun kunne da ihu inace dai kinbani aiki ko to matsalar da akasamu aciki tawace kuma ni zan gyarata kibarni nayi aikina kar kidameni
yana kainan yakatse kiran yana kunduma mata ashar
Dakallo sarah tabi wayarta cike da takaici tace jimun da iska nizai nuna ma dabanci
dafata aysha tayi tana boye dariyarta tace take it easy sarah kinsan mutanan nan ba imani ne dasuba kar su miki wani abun
banza tayi da ita tana zama bakin gado hade da dafe kai
Fita aysha tayi tanufi bangaresu tana murna tasanar dasu abunda yafaru cike dafarin ciki sadiya tarungume ta tana fadin allah sa ma sukashe yar banza wallahi da munji dadi
Dariya uncle jamilu yayi yace sarah nabirgeni akwaita da banzan hali Indai taso Abu to setayi duk yanda tayi tasameshi
dariya aysha tayi tace ni kuma ina anfani dawannan damar ina biyan bukatuna gashi yanzu ina kuance tagama mun aikina natabbata yanzu AK zai dawo kaina tunda waccan dai nasan ba dawowa zatayi ba
Har dare AK da ahmad natare da police suna nemata amma ba labari da kyar ahmad yaja AK suka koma gida saboda dare yayi kan gobe zasu dawo aci gaba da nemanta
komawa cikin gari JJ yayi yabar yaransa hudu tare da asma'u yatafi da biyu akan zai je yaga abunda yakamata yayi
kallonsu yayi yana hura sigari yace kar Wanda yamata wani Abu zanje indawo kafin nan muga abunda abunda yadace idan maidata za'ayi to idan kuma aikata zamuyi duk dai dayane
kuka tafarayi tana rokonsu surabu da ita amma bai kulata ba yafita sauran yaran kuma suka koma gefe suna kora giyarsu suna fira
Jiki asanyaye AK yashigo gida saurin yaroshi grany tayi tana fadin Abidi ya ake ciki har yanzu ba labari
Zama yayi kan kujera yana dafe kai yace har yanzu shiru grany ni ina mamkin suwaye zasu mata haka dafari nayi tunanin kidnapers ne to amma kuma har yanzu ba'akira kowa daga cikinmu ba abun yana dauremun kai
Zama tayi kusa dashi tana salati tace allah sarki asma'u ko awane hali take oho
Allah yakareta daga sharrinsu ...inji inna ameena
Ameen ....suka amsa gaba daya
Daran ranan Sam AK baiyi bacci ba duk Inda yakalla tunanin asma'u kawai yake yakosa safiya tayi yaje nemanta
da sassafe ahmad yazo gidan zasu wuce tare da AK yana shigowa AK yamike dama shikadai yake jira bangarensa yawuce dan yashirya sutafi
Asma'u nazaune banda kuka ba abunda take se rokonsu take su kwanceta tayi sallah amma sunki wai tabari intaje lahira tayi
Dasafe dai cikin yaran yakamata wata busashshiyar waina da pure water ya ijiye kusa da ita bakinsa duk warin giya yace gashi kija yan mata cikin nawa nabaki badan haka bama bazaki ciki komai ba
Kauda kai tayi tanaji kamar zatayi amai
Kuance mata hannu daya yayi yadaure dayan abaya har yajuya yadawo ya kwance agogon hannunta yana murmushi yawuce wurin yan uwansa yana fadin gayu kunga wani dan ubansun agogo kuwa
Kuka tasa tana rokon yabata agogonta amma basu kulata ba dayan yafara tattaba agogon yana fadin alqur'an bantaba ganin agogo irin wannan ba
AK yafito daga dressing room cikin shirinsa na kananun kaya lite blue din gins da farar shirt
Har zaifita kawai yaji wani Abu nakara daga cikin bedside drawer
Kamar yashareshi se kuma yadawo yana janyo drawer yaga agogon da ahmad yabashi yana kara yana nuna Jan danja
Saurin daukar agogon yayi yana sakin wani sassanyan murmushi aguje ya fito daga bangarensa yana kwalama ahmad kira
azabure suka mike tsaye suna kallonsa agogon yamikama ahmad yana fadin friend kalla agogon dakabani natabbata chitti ce ke kirana agogonta yana hannunta
Cike da farin ciki ahmad yakarba agogon yadanna wani wuri sega arrow din yajuya yafara nuna direction
kwace agogon AK yayi yanufi hanyar fita yana fadin friend bari naje kai kaje kutaho da yan sandan zamu rika magana awaya
saurin rikoshi ahmad yayi yana fadin haba AK inazakaje kai kadai bakasan wa yanne irin mutane bane kajira muje tare mana
girgiza kai yayi yana kuace hannunsa yace a'a Ahmad bazan iya jiraba akowane lokaci nashiga matsala tana tare dani har sai taga nawarware to nima gaskiya bazan bata lokaci ba kafin nataimaketa kaidai kawai kazo da police
Riko ahmad grany tayi tana fadin ahmadi yanada gaskiya barshi yatafi allah yana tare dasu
rungumeshi ahmad yayi jikinsa asanyaye yace shikenan friend ka kula dan allah idan kaga wurin da hadari kar kashiga kajira se munzo kaji
To yafada yana juyawa yafita bin bayanshi aysha tayi har yafita tarikoshi tana fadin AK wai mekake shirinyi ne
Juyowa yayi yana fadin abunda yadace
fashewa tayi da kuka AK yaruwarka fa zakasa ahadari saboda asma'u to gaskiya sedai kazaba ko ita ko ni idan har katafi wurinta sedai kahakura dani
Shiru yayi nadan lokaci sannan ya kwace hannunsa daga nata ya juya yana fadin nabarki lafiya
Saurin shangabanshi tayi tana kuka tace AK dagaske tafiya zakayi
Gefen fuskanta yashafo yana murmushi yace aysha nasan kindamu dani shiyasa kike haka amma kiyarda dani ba abunda zai sameni insha allah
Yana kainan yayi gaba dakallo tabisa har yashiga mota yatafi sannan tajuya ahasale tanufi dakin aysha
tana shiga ta isko sarah na Neman JJ awaya hankali tashe yana dauka tace JJ wai kai wane kalan sakarai ne to kasani ga Yayana nan zuwa kuma wallahi kasake yakamaka kai kasani karma ka ambaci sunana
tsaki yayi yace to seme inyazo ke nifa banason takura kingane ko inace ko gama biyana bakiyi ba kinzo kin isheni da surutu kibarshi yazo mana alqur'an ana kamani sunanki zan fada banza yar tasha kawai
saurin katseshi tayi dafadin yi hakuri JJ raina ne abace yanzu kasan meza'ayi
Kawai kasaki yarinyar kubar wajan kafin ya iso kunji
dariya yayi yace ni banda matsala kawaidai kituran sauran kudina ni kuma zan sallameta
tsaki tayi tana katse kiran tazauna bakin gado tana share zufan da takaryo mata se tsinema JJ take
Juyawa aysha tayi tafita batare datace komai ba tanufi bangarensu
Haduwa tayi da jamilu zai fita aiki fadawa tayi kan jikinsa tana kuka
Rikota yayi atsorace yana tambayar meyafaru
Cikin kuka tagayamasa duk abunda yafaru da tafiyar AK wurin asma'u
zama yayi kan kujerar Palo yana cire hularsa yace ina bazai yuba gaskiya haka kawai muna gani munaji Abu zai rikice mana wallahi natsani yarinyarnan ga dukkan alamu AK yafara sonta
Sadiya dashigowarta kenan palon tace yana fara kulata kuma zata fara zazzago Ya'ya daga nan kuma muntashi aiki daga karshe ayi waje damu
Kallon aysha yayi yana fadin kinsan Wanda sarah tabama aikin
gyada kai tayi tana share kwalla
murmushin mugunta yayi yace jeki satomun numbansa amma karki bari tagane
Fita tayi cike dajin dadi tanufi dakin sarah da dubara tasamu tadauki numban JJ tadawo bangarensu
Karban numban uncle jamilu yayi yakira bugu biyu yadaga yana fadin waye ne
Canza murya jamilu yayi yafara fadin
Sunana basiru nasan sarah tabaka aiki akan kasace khadeeja bai mistake kasaci yayarta yanzu kuma tace maka kasaki yarinyar yin haka kuma hadari ne babba awajanka
Katseshi yayi dafadin to malam basiru kake ko wa ??
abunda kakira ka gayamun kenan ?
Dariya uncle jamilu yayi irin tasu tamanya sannan yace JJ nima fa dan ahnnu ne saboda haka aiki zanbaka
bansan konawa sarah tabaka ba amma zan linkamaka konawane ka kashemun yarinyar kafin AK yaje wurin
Dariya JJ yayi yana hura sigari yace angama yallabai irinku mukeso masu bamu aiki kai tsaye
dariya jamilu yayi yace kardamu JJ yanzu zakaji alert narabin kudinka sauran kuma ina ganin gawarta zakagansu
cike da farin ciki JJ yagayamasa kudin da account numban daza'a turamasa kudin sannan suakayi sallama nan take ya dibi yaransa suka nufi dajin da asma'u take
kallonsa aysha tayi da mamki tace dady meyasa kace sunanka basiru
Dariya yayi yace yarinya ai awannan harkar wawayene kawai ke fadan sunansu nagaskiya kinga yanzu koda wani Abu yafaru yansanda suka tuhumeshi zaice basiru ne yasashi to waye basiru??
Dariya sukasa gaba daya cike da farin cikin burinsu yakusa cika
gudu AK yake amota kamar zai tashi sama yana mamkin nisan dayayi amma har yanzu arrow din baidaina nuna hanya ba seda yakai inda motarsa bazata Shiga ba yayi parking dinta yafara tafiya akafa yana ma Ahmad kuatancen inda yake
Yayi nisa sosai adajin ahmad yakirasa awaya yace gaskiya ya jirasu gasunan zuwa sun isko motarsa awani wuri shi sam bai yarda da .....
Hello hello AK yafarayi dan baiji karshen maganar ahmad ba
Jin shiru yasa yadago wayar yaduba zaro ido yayi ganin wayar amace yakunna kuma taki tashi
Hannu yadora akai yana fadin namutu ni Abidi yanzu taya su ahmad zasu San inda nake cikin wannan dajin
Jiyayi kamar yakoma wurin motarsa se kuma ya tuna baisan halin da chitti take cikiba
Kallon agogon yayi sannan yayi shahada yabi hanyar dayake nuna masa
har yamma tayi amma AK baikaiba har yafara sarewa da lamarin yana tsinema agogon ahmad shikadai se magana yake gashi ya gaji fatanshi daya allah d
Sa ba banzan agogo bane wannan yabi ta karyan turawa zai kashe kansa
jin karan agogon yakaru yasa yayi saurin kallonsa dariya yayi cike da farinciki yanufi inda yanuna mai baiyi tafiya mai nisa ba yahango runfar du JJ kuma nan agogon ya nuna masa
Cikin aljihu yasaka agogon cikin sanda da dabara yakarasa wurin kwance suke suna bacci suduka bayan sunsha giya sun bugu
ahankali yake takawa har yatsallekesu yashiga runfar can gefe ya hangota azaune tacusa kai aguywa tana kuka saurin karasawa yayi wurinta yana murmushi cikin rada yace chitti!!!
kamar amafarki taji muryansa saurin dagowa tayi dan ganin koda gaskene
zagayowa yayi tabayanta ya kuance mata daurin kamar jira take tafada jikinsa tana fashewa da kuka rungumeta yayi nadan lokaci sannan cikin rada yace kinga tashi mutafi idan munbar nan wajan se kiyi kukan
dariya tayi ta tashi tana fadin ya akyi kazo nan Jan hannunta yayi yana mata alama tayi shiru
suna fitowa sukaga ba yaran JJ awurin zaiyi magana kenan yaji ansamai bindiga abayan wuyansa cikin muryan mashaya JJ yace sannu da kokari AK
hannayansa yadaga sama yana juyowa ahankali itama asma'u tayi yanda taga yayi atsorace jikinta se rawa yake
kara saita bindigarsa yayi yana dariyar keta yace kayi Babban kuskure daka shigo gonata doka tace idan har nakama mutum yayi kokarin guduwa to kisa ne hukuncinsa saboda haka
saita asma'u yayi da bindigarsa yana dariya yace kiyi addu'ar karshe yan mata
saurin shiga gabanta AK yayi yana kallon JJ yace
dakata dan allah kayi hakuri kabarta ta tafi lafina ne nizaka kashe ba itaba katausaya mata mana mace ce fa mezaka samu idan ka kasheta tukunna ma akan wane dalili ka kamata kafada konawa kake so zan baka amma kabarta ta tafi
Kallon yaransa yayi suka kwashe da dariya seda sukayi mai isarsu sannan yasaita bindigar kan AK yana fadin to ai kaima ba kyaleka zanyiba tunda har kaganni kuma kaga mabuyata to dele kamutu
janyo hannunsa asma'u tayi tadora bindigar kan goshinta cikin kakkawsar murya tace zaka iya kasheshi amma sedai kafara kasheni tukkuna
saurin janyota AK yayi tafado jikinsa yana fadin chitti mekikeyi hakane
Dariya JJ yayi yana kallon yaransa yace haba tundazu ina mamakin meyasa AK zai sadaukar da rayiwarsa yashigo wannan dajin saboda wata yarinya Ashe masoyane hahahhaha
juyowa yayi yana kallonsu yace Romeo da Juliette banada isashshen lokaci kuazabi wazan fara kashewa acikinku ko kuma ni nazaba
Shiru suakyi suna kallon juna hawaye nabin kuncin asma'u tana tuna halin da iyayensu zasu shiga idan suka ga gawarsu atare
Shima AK abunda yake tunani kenan
Dariya JJ yayi ya umarci yaranshi dasu rike mashi AK shikuma yasaita bindigarsa kan asma'u
Sam bata damu da bindigar ba hankalin nakan AK dake kokarin kwace kansa daga yaran yana rokon JJ dayarabu da ita
kallon juna suke lokaci guda suna tuna rayuwar dasukayi abaya hawaye nazuba akan kuncinta amma da murmushi afuskanta tana kallon AK
kallonta yake shima baisan lokacinda hawaye ya zubo mashi ba cikin rawar murya yace JJ dan allah na rokeka kabarta ta tafi idan ma zaka kasheta dan allah kafara kasheni tukkuna I can't watch her dying
dafe goshi JJ yayi yana kallon AK yace
aK kamun shiru ni idan ina aiki banason hayaniya
Kallon yaransa yayi yace gayu gaskiya tunda nake bantaba kashe masoya ba kuma gaskiya bazan iya barinsu sutafi ba dole ne su mutu ya za'ayi
dariya sukasa dayan yace oga to mezai hana kabani bindigar nagama musu aiki
Shiru yayi nadan lokaci sannan ya tuntsire da dariyar mugunta yace gawata dabara
Bishiyar kusa dasu yanuna musu yana fadin kudauramun yagiya ajikin waccan bishiyar zamuga idan dagaske bazai iya ganinta tana mutuwa ba
Nan take suka daura yagiya kamar yadda yace hannayensu yasa suka daure sannan suka nufi wurin bishiyar dasu
duk yanda AK yayi kokarin kwace kansa amma abun yagagara sarkin yawa yafi sarkin karfi ga bindiga ahannunsu ita dai asma'u tuni ta saduda tagama sallamawa kawai mutuwa zasuyi to meyasa zata dami kanta
Banda kuka ba abunda take se rokonsu take surabu da AK sukasheta amma ko kallonta basuyi ba
har dare yayi ahmad nayawo da yansanda adajin amma sun rasa ta inda zasu nemesu gashi wayan AK akashe ba yanda baiyi da yan Saddan ba akan suci gaba da nemansu amma sunki wai dare yayi bazasuyita shiga cikin daji ba zasu koma idan sun shirya zasu zo aci gaba da nemansu
Bayanda ya iya haka yahakura jiki asanyaye yakoma gashi khadeeja se kiranshi take tana tambayar yagansu sedai yabata hakuri yace zasu gansu
acan gida kuwa gaba daya hankalinsu yakara tashi ganin ahmad yadawo batare dasu AK ba Umma ma seda ahmad yakira doctor yamata alluran bacci gudun kar ciwonta yatashi Abba kuma tuni yafada amasallaci atayasu da addu'a
Khadeeja kwa banda kuka ba abunda take da kyar ahmad ya lallasheta tayi shiru
Haka ma bangaren grany da inna ameena abinci da kyar sukeci dan gaba daya gidan ba dadi
Ita kanta Sarah tashiga damuwar rashin AK dan tasan JJ bayada mutunci zai iya hadasu gaba daya yakashe gashi tana kiransa baya dauka daga karshema yayi blocking numberta
Aysha ma tadamu ganin AK baidawo ba amma da jamilu yakira JJ seyacemasa AK baijeba asma'u kuma yakasheta kawai yajira gawarta nanan zuwa
Se alokacin hankalinsu ya kwanta sukaci gaba da nuna fake damuwansu akan rashin dawowarsu
kama asma'u sukayi suka ratayeta ajikin yagiyar ga hannayenta adaure
Dai cikin yaran yana rike da kafafunta wanda daga yasakesu wuyanta zai sarke ajikin yagiyar
Kuka AK yake kamar karamin yaro bashiri yasa karfinsa gabadaya yakwace kansa aguje yakarasa wurinta yana kuka yana rokonsu dan allah sukwanceta
dariya sukasa gaba daya suna kallonsu
yaron dake rike da ita yace oga nagaji pah yasin zan saketa
karasowa JJ yayi kusan AK yana fadin zaka iya taimakonta ai dasauran dan lokacinda yaragemuku kafin wahala takarasaku
durkusawa AK yayi akan guywowinsa aka Dora kafafuwan asma'u akan kafadunsa tayi tsaye
Dariya sukayi dai cikin yaran yace oga kana ganin zai iya juran daukanta kuwa
"To ai hikimar abun kenan shi dakanshi zai kasheta idan kuma bai kasheta ba ita zata kasheshi
Haka zamu barsu su kwana har gobe idan basu mutu ba dasafe zamu kashesu kafin mu barnan
juyawa sukayi suka koma gefe guda suka fara shan giyarsu suna fira
Hawaye ne ke zuba akan kuncin asma'u kamar anbude panpo har suna diga sama kan AK
ahankali yadago kansa yana lekenta yace chitti yayyafi akene kece asama zaki fini sani naji Abu nadiga akaina
Cikin muryan kuka tace ABI why did u come
"aw abunda ma zakice kenan maimakon kigode mun nazo taimakonki shine zaki ce meyasa nazo ko
"To yanzu me zuwannaka ya anfanar ni bantsira ba gashi zamu mutu gaba daya
murmushi yayi yace bazaki mutu ba chitti kafin Nazo nan wurin seda nabiya wurin Umma namata alkawarin zan maidaki gida to koda zan rasa raina insha allahu se kinkoma gida karkidamu
sautin kukanta ne yakaru tace ABI ni nafiso namutu karayu akwai mutane dayawa akarkashinka ga grany da sarah wane hali zasu shiga idan wani Abu yasameka
"Kema ai kinada responsibility ga Umma ga inna da khadeeja kece mai kula dasu yazasuyi idan bake
Cikin sheshshekar kuka tace idan har kana nan bandamu ba nasan zaka kulamun dasu amma idan baka ni bazan iya komai ba ABI
runtse idanuwansa yayi dan tuni kafadunsa sun fara zafi cikin muryan wahala yace yanzu dai abar zancan meyasa kincika surutu ne kina gabar mutuwa ma bazakiyi shiru ba to nidai ki kyaleni inyi istigfari dan nafara hango barzahu
Shiru tayi hawayenta nakaruwa tana ji dama itace akasa dan tasan shikadai yasan meyakeji ahalin yanzu
Har dare yayi su AK na ahaka tuni yafara gajiya dan har wani jiri jiri kedibansa kawai taimakon allah ne da jarumta irin tashi yasa har yanzu yake durkushe awurin amma guywowinsa da kafadunsa jiyake kamar ana Sara mai gatari gashi yanada asma tuni yaji tafara kokarin tashi
asma'u ma haka tagaji da tsayuwa jikinta har rawa yake tun tana kuka har tagaji tayi shiru tana addu'a sedai jefi jefi AK yakan tsokaneta wani lokaci takulashi wani lokaci kuma sedai tafashe da kuka har takai lokacinda suduka sukayi shiru bamai magana """""
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣4⃣5⃣
Kokarin janye kafarta tafarayi daga kan kafadunsa tana fadin ABI
katashi katafi kabarni anan kawai koban mutu yanzuba anjima mutuwa zamuyi gaba daya dan natabbata bazamu iya kai safe ahaka ba kuma koda munkai ma kashemu zasuyi
Kaga damu mutu gaba daya gara kai katsira koba komai abun zaima su Umma sauki
Kokarin kuance hannayensa yafarayi yana fadin chitti miye haka kike kokarin yi stop moving ur legs dan allah u are hurting me kina so kikashe kanki ne idan natafi nabarki anan miye anfanin zuwana mezan gayama su Umma idan nakoma
Cikin Sa'a kuwa ya kwance hannayansa har takusa sauke kafanta yayi saurin rikosu cikin rawar murya yace
Chitti kinga na kuance hannayena kiyi kokarin kwance naki abun baida kwari sosai
Shiru tayi hawaye nacigaba dazuba afuskanta yana rike da kafafuwanta akan kafadunsa yana cigaba da lallashinta har tafara kwance hannayenta da taimakon allah tayi nasaran kwancewa sannan tafidda yagiyan wuyanta atare suka fadi awurin suna maida nunfashi
Cike da tausayi ta sunkuyo saitin fuskar AK cikin rada take jera mai sannu
Yajima ahaka kafin dakyar ta taimaka mai yatashi yana runtse idanuwa saboda azaban da kafadunsa da guywowinsa kemasa
Hannunta Yakama yana leken su JJ dake sharan bacci kaman matattu sunsha sunyi tatil
Cikin sanda suka fara tafiya seda suka dan yi nisa sannan suka fara gudu suna kara shiga cikin dajin batare da sunsan inda suka dosa ba
Sunyi nisa sosai asma'u taci birki tana fadin ABI gaskiya nagaji bazan iya cigaba da gudunnan ba mudan zauna mu huta mana
bai musa mata ba dan shi kanshi juriya kawai yake amma bayajin zai iya tafiya mai nisa bai fadi ba
Zaunawa sukayi suka jinginu da katuwar bishiyar dake wurin suna maida nunfashi sun jima ahaka kafin suka fara bin wurin dakallo se alokacin suka fahimci ba karamin daji suka shigo ba dan gaba daya wurin manya manyan bishiyoyi ne azagaye dasu kasan kuma ciyayi ne da ramummuka iri iri
Adan tsorace asma'u tamatso kusan AK cikin rada tace ABI nan ina ne
jinginar dakansa yayi jikin bishiya yana lumshe ido cikin dasashshiyar muryansa yace da a maiduguri muke dase ince wannan shine dajin sambisa
amma yanzu bansan mezan cemaki ba
shiru tayi nadan lokaci tana kallonsa sannan ahankali tadafa kafadansa cikin sigar tausayawa tace kanajin zafi ko
Dagowa yayi yakalleta suka hada ido sannan yaballe bottom din rigarsa yafito dakafadansa yana murmushi yace ba sosaiba nagode allah bakida nauyi sosai da yau namutu
Murmushi tayi da hawaye afuskanta tadora hannunta kan kafadarsa tana shafawa ahankali
Jinginar dakansa yayi jikin bishiya idonsa alumshe yana jin dadin shafawar dakate kaman tana Sosa mai wurin ne
juyo dakansa yayi yana kallonta ahankali yace kinajin tsoro ?
Gyada kai cikin rawar murya tace eh amma basosai ba
Kaifa?
Murmushi yayi yana kallon wurin dasuke baice komai ba
maidamasa wuyan rigarsa tayi tana maida masa maballan alokaci guda suna kallon junansu suna jin wani yanayin dasuka kasa fassara shi
Mutsa bakinta tafarayi ahankali tana ji kamar tagayamasa tana sonsa amma kuma tana tsoron mezai biyo baya
Suna cikin haka sukaji wani gurnani gurrrrrr
atsoarace suka kalli juna cikin rawar murya asma'u tace ABI did u hear that ??
Kai ya gyada mata yana waige waige sekara shigema juna suke
gurnanin suka kara ji anyi atsorace asma'u tarungumeshi da karfi tana jero addu'a
Dariya yayi yana rike ciki yace chitti ba komai bane ciki nane fah
Kallonsa tayi da mamaki tace cikin ka fah ABI wannan fa kamar zaki ne ko damisa
janyeta yayi daga jikinsa yana shafa cikinsa yace cikina ne yunwa nakeji yau ba abunda naci tun jiya rabona da abinci
itadai bata yarda ba se bin wurin take da kallo tana karanto duk addu'ar datazo mata tun yana mata dariya har shima yafara tsorata dayanayin wurin yafara tasa addu'ar
Washegari dasafe dai daga cikin yaran JJ yafara tashi yaga ba su AK hankali tashe yatashi sauran yasanar dasu
afusace JJ ya hausu dafada kamar su suka kwancesu bashiri ya rarrabasu acikin dajin suje su nemosu hankali tashe suka bazu nemansu hardashi JJ kuma yayi alkawarin yana ganinsu zai kashesu kowa yahuta
tun safe ahmad yaje police station suka fara shirin fita Neman su
agidama haka sun dage da addu'a tun suna kuka har sun hakura sun barma allah gidajan biyu sunzama tamkar gidan mutuwa Sam ba walwala ba farin ciki acikinsu
lokaci guda khadeeja tarame tafita hayyacinta kowa yaganta seya tausayamata kowane lokaci suna waya da ahmad yana kara kuantar mata da hankali
bangaren sarah ma abun yafara damunta saboda bata San halinda AK yake cikiba dan tasan idan dai JJ yagansa bazai kyaleshi ba
aysha ma haka tana mamkin rashin dawowar AK tunda JJ yacemusu yakashe asma'u gashi kuma sunji shiru suna kiransa basa samunsa
Kuance suke suna bacci hankali kuance AK yadora kafansa kan cikin asma'u ita kuma tayi reran dayan hannunta kan kirjinsa
ahankali tafara bude idanuwanta tana bin wurin da kallo saurin tashi tayi tana ture kafan AK daga jikinta tafara tashinsa
gyara kuanciyarsa yayi cikin muryan bacci yace chitti bring my coffee kafinnan zantashi
Dariya tayi tana daddabashi tace wane kalan coffee kuma ABI kamanta inda muke ne
janye hannunta yayi daga kan kafadarsa idonsa arufe yace jiya nayi wani mafarki mai ban al'ajabi idan kin kawomun coffee dina se inbaki labari
Ganye ta tsinko tadora akan bakinsa tana dariya tace ba coffee sedai dambun nama inzakaci
saurin tashi yayi zaune yana kakkabe bakinsa lokaci guda yana bin wurin da kallo
Runtse idanuwansa yayi yakara budesu yanaso yatabbatar ko dagaske ba marfaki yayi ba
tashi zaune yayi dakyar yayi mika yana salati kamar daga sama sukajiyo
Tafiyar yaran JJ suna nemansu
atsorace suka kalli juna suna mikewa tsaye asma'u ta cakumo rigarsa cikin rawar murya tace
ABI... mun ..shiga uku za.....
Bata karasaba yaja hannunta aguje suka cigaba da gudu suna kara kutsawa cikin dajin seda sukayi nisa sannan suka fara tafiya suna Jan kafa kamar bugaggu ga kishi da yunwa dasuka addabesu karfin hali kawai AK yake amma tuni yafarajin asman shi na kokarin tashi
Tafe suke shi agaba ita abaya sekara kutsawa cikin dajin suke
Karasowa asma'u tayi kusa dashi cikin dasashshiyar muryanta tace ABI I am hungry
baijiyo yakalleta ba yace gani kici
Dariya tayi tace ai koda inacin naman mutane ba'abunda zanyi danaka dan dagani ba dadi zai yiba
Shiga gabanshi tayi tana rike cikinta kamar zatayi kuka tace
ABI dagaske yunwa nakeji kuana biyu fa ba abunda naci ko ruwa bansha ba
Kafadunta Yakama ya juyar da ita sukaci gaba datafiya yana fadin chitti ki kalli nan wurin da kyew kigani banda ciyayi da bishiyoyi ba abunda keda kwai
Idan bamuyi gaggawan barin wurinnan ba mune zamu zama kalacin namun daji
Saurin juyowa tayi tana fadin 😧namun daji fa kace kana nufin akwaisu anan
Dariya yayi yawuce gaba yana fadin awannan dajin miye baza'a rasa ba kima kula da inda kike sa kafanki kar ki taka maciji
saurin bin bayansa tayi tana riko hannunsa tace to wai aganinka suwaye wa'yannan kuma meyasa suka kamani
"Ke baki sani ba taya za'ayi ni insani
Shiru tayi batace komai sukaci gaba datafiya batare da sunsan inda suka nufa ba amma kowane da tunanin dayake aransa
Tuni ahmad da yan sandan suka shigo dajin sedai abun takaicin basusan ta ina zasu bi sufara nemansu ba hakanan dai suka rarrabu gida uku sukashiga dajin dafatan ganin su ko ko sukama yan daban
agida kuma tun safe grany da inna ameena suka je gidansu asma'u aka taru acan ana taya juna jaje da addu'ar allah yabayyana su
har yanzu JJ nacigaba da nemansu AK acikin dajin nan saboda yanada tabbacin bai isa sunfita daga dajin ba dan yanada girma sosai za'ajima kafin akai kyawyukan dake kusa dawurin
suna cikin tafiya asma'u tarangada ihu atsorace AK yajiyo yana duddubata yaga ko wani Abu yasameta
Tsalle tafara cike dafarin ciki tana nuna mai bishiyar mangoron datahango
tace ABI kalla kaga mangoro acan wallahi mangoro ne
tsaki yayi yana kallon bishiyar mangoron shi kanshi tabirgeshi bai San lokacinda yasaki wani lallausan murmushi ba suka nufi wurin
dutse yadauka yafara jifan mangoron amma yakasa samun koda guda dayane
labace baki tayi kamar zatayi kuka tana kallonsa tace ABI haka bazai yiba kahau mana katsinko
Baki yasaki yana kallonta yace nahaufa kika ce wannan katuwar bishiyar nasan miye akai haka kawai ke ki hau mana
tureshi tayi daga wurin tana fadin yo se in hau mana ai ba yau nafara ba bishiyar ma dako tsawo batada
Matsawa yayi yabata wuri tafara kokarin nawa se dariya yake yana tafa hannu yana fadin chitti!!!chitti!!!chitti!!!
Tafara hawa kenan tayo kasa zata fadi yayi saurin tareta tafado kansa suka fani kasa tare
Dafe bayansa yayi yana runtse ido hade dasakin yar kara atsorace ta riko gefen fuskarsa tana fadin ABI are u ok kaji ciwo ne ?
Bude idanuwansa yayi yasaukesu cikin nata suna kallon juna nadan lokaci sannan yatureta yana fadin
Dallah malama tashi sama na dama nasan dagangan kikayi
Saurin tashi tayi tana Sosa kai
Dakyar yatashi yana dafe baya yace dama zan samu naman dajin dazai cinye mun ke koba komai kashi hamsin na matsalolina zasu ragu
Nuna mai mangoron tayi tana lashe baki tace please ....
Bata karasaba yatattare kafan wandonsa yahaw bishiyan yafara tsinko mangoron yana jefomata
Ita kwa se dauka take tana Tarawa ga daya ahannunta tana sha
Lekowa yayi daga saman bishiyan yana kallonta yace to kijira insauko mana asha tare haka ake ni da wahala keda jin dadi
seda suka Tara mai yawa sannan ya sauko suka zauna awurin Sunasha suna fira
gutsuran mangoro yayi yadago yana kallonta yace
Chitti acikin namun daji wanne yafi hadari
Dgowa tayi tana kallonsa da mangoro abakinta tace me kadaukeni ne ABI ai kowa yasan zaki yafi hadari
Dariya yayi sannan yakai mangoro bakinsa yana lumshe ido yace
to shi zaki baida wani hadari saboda idan dai zaki iya dake nunfashinki kiyi kamar kinmutu to sedai yayita zagayeki ba abunda zaimiki kinsman bayason mushe yafiso yakashe dakansa sannan yaci
tunda yafara magana take kallonsa baki bude seda yagama sannan tayi dariya tace kaidai kawai sha mangoronka amma wane dauke nunfashi mutum zai iya yi ga zaki na kewayashi
dariya yayi yace to kindai fadi wannan fadi wani
Zari ido tayi tana kallon macijin dake bayansa cikin rawar murya tace ma.....maciji
Dariya yayi yace kaji wai kuma maciji yo miye hadari awurin maciji ai shi kina ganinsa kawai kiyi kokarin taka kansa se kisa hannunki ahankali ki kamo wuyansa kirike gam to kin gama dashi ba'abunda zaimiki
Mikewa tayi tana wurgi da mangoron hannunta atsorace tace ABI ....maciji....abayanka
zunbur yamike yana duba bayansa yana ganin macijin yadaga uban tsalle yabi tagaban asma'u aguje har yatafi yajiyo yaganta atsaye takasa motsawa se yarfa hannu take bashiri yadawo yaja hannunta suka bar wurin
seda sukayi nisa sannan suka tsaya ai kwa nan asma'u tahau kwasan dariya tana tsokanarsa banza yayi da ita yayi gaba yana jinyar kirjinsa dake masa azaba amma ko kadan bayaso asma'u tagane halin dayake ciki
suna cikin tafiya ta taka wata gundumemiyar kaya durkushewa tayi awurin tana sakin yar kara tana kallon kafar
Saurin dawowa AK yayi wurinta yana mata sannu
Hannu yakai zai taba kafar amma taki bari se rike hannayansa take tana kuka
bayanda baiyiba amma Sam taki yarda shiru yayi nadan lokaci sannan ahankali yakira sunanta cikin wata iriyar murya yace ASMA'U
seda taji gabanta yafadi dan har tamanta rabon dataji yakira sunanta dagowa tayi ahankali tana kallonsa carab suka hada ido lokaci guda taji tamanta ciwon dake kafarta
matso dafuskansa yayi dap datata har suna musayar nunfashi sannan yakai bayan hannunsa ahankali yashafo gefen fuskarta har zuwa lips dinta lokaci guda suna having eye contact
dayan hannunsa yakai ahankali kan kafarta yashafo tundaga kwabrinta harzuwa tafin kafarta sannan yazare kayar
Yar kara tasaki tana kankame hannunsa dakarfi
Murmushi yayi yaciro handkerchief a aljihunsa yadaure mata kafar yana fadin nafadamiki ki kula da inda kikesa kafarki kigodema allah ba maciji kika takaba
Sunkuy dakanta tayi kasa tanajin kunya takamata dan Sam batasan lokacinda yakai hannunsa wurin kayarba
dagata yayi tsaye yana fadin yawwa to tashi muga zaki iya takawa
Dingishi tafarayi tana langabe kai tace ABI mudan zauna muhuta mana
Girgiza kai yayi yace a'a chitti Hutu ba namu bane mutanan nan fa haryanzu suna binmu idan muka zauna anan kowane lokaci zasu iya iskomu
shiru tayi batace komai ba tana kallon kafarta dake zubarda jini
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: Dukawa yayi agabanta yana fadin haw ingoyaki
Dariya tayi tace goyofa inazaka iya goyona awannan halin
ganin dagaske yake yasa ta dane bayansa yagoyata sukaci gaba datafiya
Murmushi tayi tace ABI in tambayeka
"Ina jinki
"dawa dawa kayi missing acikin yan gida
Murmushi yayi cike dafarin ciki yace grany mana
"Uhm sewa?
"Se ahmad se inna ameena se inna se Umma se sarah se khadeeja se fa'iz se .......
Haka yayita jero yan gida ganin har yakai kan su amir yasa tace to banji kace aysha ba ?
dafe kai yayi yace ohhh namanta se aysha
Dariya tayi tace seda na tunamaka
Shiru yayi yana mamakin meyasa baya jin yayi kewar aysha ne shi har ma mantawa yake da ita
Murmushi yayi yace kema intambayeki
"Eh
Banda Umma da Abba da khadeeja dasauran yan gidanku wa kika fiso
Dariya tayi aranta tace kai nafiso ABI amma afili tace grany
"Se wa
"Se inna ameena
Shiru yayi nadan lokaci sannan ahankali yafurta sewa
"Se sarah ......
Haka tayita jerowa har akazo kan ahmad
alokacin AK yahasala jin bata ambaci sunansa ba sauketa yayi yana fadin sauakmmun abaya
Makalkaleshi tayi awuya tace haba ABI ban warkeba fa
Wucewa yayi yana fadin sedai kikira wa'yanda kike so su goyaki amma ni nagaji
Dariya tayi tabi bayansa tana dingishi har ta iskosa hannunta tadora kan kafadarsa suna tafiya tace wai fushi kayi ne to aini ban dauka harda mai tambayar ba
Daga kafada yayi yace meyasa zanyi fushi dama ai bance ki ambaci sunana ba
har wannan lokacin ahmad da yansanda nacikin dajin suna nemansu amma ko alamar su basu ganiba mutum biyu cikin yan sandan ne ma sukaga runfar su JJ da Inda aka daura yagiya ajikin bishiya nan take suka sanarda yan uwansu suka zo wurin
Da gudu Ahmad yakarasa wurin yarike yagiyar da hannunsa yana kallonta lokaci guda hawaye suka wankemai fuska
Dafashi dai daga cikin yan sandan yayi yana fadin kayi hakuri ahmad karkayi saurin karaya alamu sun nuna guduwa sukayi insha allahu ba abunda yasamesu muci gaba da nemansu
kiran grany yayi yagayamata su AK sun gudu daga hannun yan ta'addan amma har yanzu basu gansu ba
Cike da farin ciki tasanarda su Umma da sauran yan gida aka ci gaba da addu'a
da labari yasami aysha da jamilu ba karamin mamaki sukayi ba gashi suna kiran JJ basa samunsa sunkasa gane kan lamarin
suna cikin tafiya asman AK yatashi zo laga tashin hankali awurin Asma'u kamar zatayi hauka haka takeji
Tun yana tafiya ahankali har ya durkushe awurin yana nunfashi sama sama
durkusawa tayi kusa dashi cikin sheshshekar kuka tariko hannunsa tana fadin ABI meyake damunka ne dan allah karkamun haka ina zan sa kaina idan wani Abu yasameka kamanta kama Umma alkawarin zaka maidani gida ABI dan allah katashi
Damke hannunta yayi dakarfi yana kokowa da nunfashinsa cikin rawar murya yace chitti ru...wa .....ruwa...
Riko fuskansa tayi da hannu biyu cikin kuka tace ruwa kakeso ?
Kai yagayda mata yana runtse idanuwansa
kwantar dashi tayi awurin tana fadin to kuanta bari nakamaka ruwan kaji dan allah kajirani namaka alkawarin zan nemo maka ruwa
tashi tayi aguje tanufi cikin dajin Sam tama manta daciwon dake kafanta se jini yake amma bata San yanayiba
Tayi kusan awa daya tana yawo adajin taci kuka har tagaji tayi addu'a ba adadi da taimakon allah tahango wani dan karamin rafi da wata runfa akusa dashi da alama ta makiyaya ce
Aguje takarasa wurin tasamu wata yar roba tadibo ruwan aciki gashi roban afashe take se zuba ruwan yake hakannan dai tajuya aguje takoma tana bin sawunta inda tabiyo saboda jinin dake zuba dashi take gane hanyar databiyo
ahankali AK yafara bude idanuwansa har yagama bude idonsa saurin tashi yayi yana kallon gefensa baiganta ba azabure yamike yana kiran sunanta amma shiru
Nan take hankalinsa yatashi jinin dayagani akasa yafara bi yana kiran sunanta da kyar yake tafiya hannunsa daya akan kirjinsa yana ji kamar nunfashinsa zai dauke
Tundaga nesa ta tsinkayoshi yana tafiya aguje tanufi wurinsa tana kwala mashi kira da karfi ABIIIII
wani lallausan murmushi yasaki lokacinda ya hangota tana zuwa cikin karfin hali yakara saurin tafiyarsa har ya isa wurinta suka rungume juna dakarfin gaske kamar za'a rabasu
Cikin dasashshiyar muryansa da bata fita sosai yace chitti ina kikaje meyasa zaki tafi kibarni kin kwasan halin danashiga dana farka banganki ba
Kara shigewa jikinsa tayi cikin muryan kuka tace ABI I am sorry ruwa naje in kawomaka amma bazan kara tafiya inbarka ba I promise
sulalewa yayi awurin yana dafe kirjinsa
zaunawa tayi tana tallabosa tadora kansa saman cinyarta tana kokarin bashi ruwan amma yakasa sha
Se Jan nunfashi yake dakarfi kamar mai fitar rai
fashewa tayi dakuka tariko kansa tana fadin ABI katashi ga ruwan kasha naga wani waje acan wurin se muje muzauna kila musamu Wanda zai taimakemu
riko hannunta yayi yana murmushin wahala cikin rawar murya yace kukan me kike ba abunda zai sameni haka yakemun kidan jira anjima zai rage se mutafi amma kin tabbata ba gidan aljanu kika gano ba kuwa
Rungume kansa tayi akirjinta tana gashewa dawani irin kuka mai ban tawsayi sun jima ahaka kafin dakyar ta taimaka masa yatashi suka fara tafiya se jera mai sannu take har yagaji da amsawa
Koda suka isa wannan runfar yagama galabaita yar tabarmar datagani awurin tadauko tashinfida mai sannan ta taimaka mishi ya kwanta amma gaba daya tagama tsorata da halin dayake ciki
zama tayi akusa dashi tajanyo kansa tadora saman cinyarta tana shafa lallausan gashin kansa daya cukurkude kamar bashiba
Hannunta yakamo cikin rawar murya yace chitti I am sorry na yima Umma alkawarin zan maidaki gida amma inaga bazan iyaba I am dying saboda bantaba irin wannan ba
Fashewa tayi da kuka tana toshe mai baki tace a'a ABI dan allah kadaina fadan haka ba abunda zai sameka insha allahu kana son ruwa bari inje indibo maka
riko hannunta yayi yana tari hade da rintse ido cikin muryansa da bai fita yace a'a kibarshi banason ruwa kowane lokaci idan zanbaki hakuri akan wani abu bakyaso se kihanani ko kirufe mun baki
To yau kitsaya kiji mezan ce
Chitti nasan namiki laifi nabata miki rayuwarki na aureki badan allah ba bada kekkyewar niyya ba akan wata manufa tadaban banyi la'akari da makomar rayuwarki ba amatsayinki na ya mace
I am sorry chitti kiyi hakuri kiyafemun nasan ina damunki ina tsokanarki amma badan in bata miki rai nakeyiba sedan narage miki damuwar danajefaki aciki
Kuka take kamar ranta zaifita tama kasa magana se girgiza takai take tana kallonsa cike da tausayi tana ji dama itace ahalin dayake ciki da tafijin saukin radadin datakeji ahalin yanzu
hannunsa yasa akan bakinta yana fadin shshshsh
Kiyi shiru chitti kar wa innan samudawan su jimu
kinga ni tafiya zanyi nasan bazan iya cigaba ahaka ba kiyi kokari ki koma gida kinji kibama Umma hakuri kice nayi iya kokarina nakawoki amma nakasa kicema grany tayi hakuri kuma taringa shan maganinta akaikai ki kularmun da ita kinji nasan ke kadai ce zaki iya ga sarah nan itama ki kula da ita kinji kizabamata miji nagari Wanda yadace da ita kihadasu kinji nasan tanada taurin kai batajin magana amma tanada tausayi da saurin karaya ki koyar da ita halayanki masu kyew kinji
Murmushi yayi yanajin wani yanayi ajikinsa cikin dasashshiyar muryansa yaci gaba dafadin
Kicema inna ameena nace takoma wurin dan tsohonta tadaina takurama granyta kinji
Kicema aysha tayi hakuri nasan tanasona amma ina jamata lokaci naki aurenta kigayamata ina Neman albarkar grany akan duk abunda zanyi shiyasa ban aureta ba inaso se grany ta amince amma kice cikin samarinta tazabi Wanda yafi sonta aciki ta auresa
Khadeeja kuma kicemata nace takula da ahmad sosai tayimai biyayya tazauna dashi lafiya shima kice nace yariketa amana kar yacutar da ita
Kuma kicemasa karyayi wani aboki bayanni kinji idan yana bukatar wata shawara ko wani Abu yasameki kar ya yarda dakowa cikin abokananmu
Chitti kinada hali mai kyew kinda kirki kicigaba da haluri kinji idan namutu kar kizauna hakanan kisamu wani mutum nagari ki aureshi amma kar ki manta dani kinji ko
Rungumeshi tayi dakarfi tana sakin wani kuka mai cin rai tace ABI ya isa haka dan allah ba abunda zai sameka ABI katashi kaji tare zamu koma gida muci abincin grany mai dadi sannan inkamaka coffee dinka mai zafi kasha kaji ni bawanda zan aura ABI Kaine mijina dakai kadai zan rayu saboda kai nakeso I LOVE YOU!!!
dago fuskansa tayi tana kallonsa idonsa alumshe ba alaman nunfashi atare dashi atsorace tafara daddabashi tana kiran sunansa Amma shiru
Hannunta tasa tana bubbuga gefen fuskarsa cikin rawar murya tace a'a a'a ABI u can't do this to me dan allah katashi ABI idan kamutu ina zan sa raina wallahi nima mutuwa zanyi dan allah katashi ABI
Surutai kala kala take tana jijjigashi dakarfi amma shiru kakeji jadaba tafarayi tana toshe bakinta tajinginu da iccen runfar tana kallonsa se kuka take kamar ranta zai fita tajima ahaka can kuma tayunkura kamar antsikareta tanufosa da rarrafe tana kara kiran sunansa tafara danna mai kirji amma baimasan tanayiba
Sunkoyo dakanta tayi kan fuskarsa hawayenta na diga akan idonsa ahankali takai bakinta kan nasa tafara hura masa iska tajima tanayi amma taji shiru fadawa tayi kan jikinsa takara fashewa da kuka tana addu'ar allah yadauki ranta itama da wannan halin datake ciki
Kamar daga sama taji yafara tari kadan kadan saurin dagowa tayi cike dafarin ciki ta riko fuskarsa tana kiran sunansa
amma bai bude idoba kuma bai motsaba se nunfashinsa dake fita ahankali ""'"
[19/07, 17:04] Hubbey Frd Ameena Kn: surutai yaketayi shikadai jin shiru yasa yaduba gefensa amma baiganta awurin ba cike da mamaki yafara waige waige yana kiran sunanta
Can bakin wani shago yahangota tana daga mai hannu
Girgiza kai yayi yakarasa wurinta yana tambayar metake anan
Waya takarba ahannun mai shagon tamika mishi tana murmushi
saurin kai hannu yayi ya fizgi wayan yana dariya yace ohhh chitti gaskiya kin hadu bari mukira grany
Nunmaban grany yayi dialing seda takusa katsewa tadauka jikin asanyaye tayi sallama
Hannunsa yasa yatoshe bakinsa hawaye nazuba afuskansa tsabar farin cikin jin muryan grany dayayi yama kasa magana se mikama asma'u wayar yayi bayan yasa a handsfree
Har grany zata kashe wayar taji muryan asma'u na sallama
Zunbur tamike tsaye cike da farin ciki tana fadin wanake ji haka kamar asma'u
da mamki kowa yajiyo yana kallonta kowa yakosa yaji meyake faruwa ba
kallon kallon aka fara tsakanin aysha jamilu da kuma sadiya bakaramin tashin hankali suka Shiga ba jin an ambaci asma'u
Cikin rawar murya asma'u tace eh nice grany ya kuke ya ummata
Dariya grany tayi mai hade da kuka tafara kai kawo cikin palon tana fadin lafiryamu kalau asma'u Ku yakuke ina Abidi badai abunda suka muku ko
matsowa kusan wayan AK yayi cikin rawar murya yace grany!!!
dariya tayi mai dan sauti jin muryansa datayi batasan lokacinda hawaye ya wankemata fuska ba
"Abidi ya kake kuna ina ne
dariya yayi yana goge hawayen fuskarsa yace grany lafiyarmu kalau muna hanya yanzu zamuzo kigayama su Umma su....
Bai karasaba Asma'u taturo bakinta kusan wayar tana fadin grany yunwa mukeji kicema Umma tayimana kunun gyada ke kuma kiyimana tuwo inna ameena kuma tamana dambu yaji hanta sosai .....takarashe maganar tana lashe baki
ture kanta yayi yajuya mata baya yana fadin grany kihadamun coffee na mai zafi ki kara citta sosai saboda makogorona yabushe
Dariya grany take harda rike ciki rabonta da tayi farin ciki irin haka har ta manta
Kokowa suka farayi akan wayar kowa da abunda yakeso yafada seda katin ciki yakare sannan ya mikamata wayar yana fadin to ai gashi se kicinye ko duk awane cikin zaki saka abinci kala 7 oho
Kin karban wayar tayi takauda kai tana turo baki tace seda kacinyemasa katin se ka maida masa wayarsa
Juyowa yayi yana kallon mai shagon yana murmushin yake yace malan yi hakuri muncinye maka kati
Murmushi yayi yace ah ai ba komai dama nagayamata katin ba yawa
se alokacin asma'u tajiyo tana mai godiya sannan tace
dan uwa ina zamu samu motar dazata kaimu cikin garin abuja
dariya yayi yace to gaskiya yarinya sedai babbar motar dake kamana kaya idan kunaso yanzu se inrakaku muga in yayi lodi se yarage muku hanya
Juyowa sukayi suka kalli juna sannan AK yakallesa yana murmushi yace malan munaso sedai fa ba kudi ajikina ya za'ayi
fitowa yayi daga cikin shagon yanufi wata hanya yana fadin kuzo muguada sa'armu mugani amma gaskiya da kyar zai yarda dan bashida mutunci
Haka yayita musu surutu suna binsa abaya har suka isa wurin babbar motar da tacika makil da buhuhhuna
Sallama yama wani mutun yajiyo yana hura sigari batare da ya amsa sallamarsa ba yace ya akayi ne idan ma kayane kaje ba wuri se gobe....
dariya mai shagon yayi yana nuna su AK yace gali dama wa'innan bayin allah zaka taimakama ka rage musu hanya zuwa cikin gari
Juyowa yayi da jajayen idanuwansa yana binsu da kallo yace nima ai bawan allah ne nawa zasu biyani
Juayawa mai shagon yayi yakoma yana fadin gashinan kudaidaita zan koma nabar shago ba kowa
Kallon juna sukayi sannan asma'u ta sassauta murya tace gali taimakonmu zakayi ba ko kwandala ajinkinmu amma idan munje zamu biyaka konawa kakeso
Kallonsu yayi ya tintsire da dariya yana fadin yanmata kin ma rainamun hankali ki kalleni da kyew kinga nayi kama da Wanda zaku yawdara daganinku irin yarannan ne masu gudowa daga gidan iyayensu sushiga duniya ...
Yakarashe maganar yana zukan sigari yahura musu
Hannu AK yasa yana kabe hayakin sigarin yana yamutsa fuska yamatso kusan asma'u cikin rada yace chitti wannan dan jagaliyan yayi kama da dai daga cikin wa'inda suke binmu ko zamu hadashi da yan kauyan nan suci uba.....
Bai karasaba gali ya katseshi dafadin kai nifa tafiya zanyi kuna batamun lokaci idan bazaku ba gara ma kuware
tsaki AK yayi yana ji kamar ya haushi da duka
ganin zai shiga motar yasa asma'u tayi saurin riko hannun AK tana Nuna ma gali tace to ka rike wannan agogon jingina idan munje muka baka kudin seka bamu abunmu
Saurin kwace hannunsa yayi yana fadin ke bakida hankali ne kwasan tsadar wannan agogon zakice inba wannan dan ta'addan haka kawai
juyowa gali yayi afusace yanufo AK asma'u tayi saurin shiga gabansa tana basa hakuri sannan ta lallashi AK da kyar yaciro agogonsa taba gali
Sannan suka shiga gidan gaba suduka biyun yaja motar suka tafi
Fada akayi sosai tsakanin yaran JJ da yan sanda sedai bawanda aka kashe atsakaninsu kuma yaran JJ sunyi nasarar guduwa daga hannunsu guda daya suka kama JJ dakansa yaharbesa gudun kar yatona musu asiri
shidai ahmad damuwarsa su AK seyawo yake yana nemansu amma bai gansuba
Tuni grany tasanar dasu Umma wayar dasukayi dasu asma'u nan take gida yacika cike dafarin ciki kamar gidan bigi haka ake hidima kowa nakokarin girmusu abunda sukeso
Aysha jitake kamar tamutu dan bakin ciki ga wani bakon al'amari da yaziyar ceta na sauyin yanayin datake gani kwana biyu takasa fahimtar komai kuma taki zuwa asibiti saboda tana tsoron abunda result zainuna kar aje abunda take zargi yazama gaskiya
suna cikin tafiya AK se toshe hanci yake kamar zaiyi amai saboda saitin hamatan gali yake sedariya asma'u kemishi suna fira da gali shidai AK takaici ya isheshi ko magana bayason yi
Juyowa yayi yana kallon gali yace kai wai ina zaka saukemu
Baijiyo ya kallesa ba yace duk inda kakeso konan kace insauleka tsaba zan iya taka birki
tsaki AK yayi yace kai nafaga alama ka rainani dayawa bakasan koni wayeba ko?
dariya gali yayi yana kallon AK yace to waye kwa kai banda mutun dan uwana kuma dan kauye mai guduwa da budurwa
dariya asma'u tayi tana kallonsu batace komai ba
cike datakaici AK yace yanda make dinnan bansan ko kasan AK hausawee ba to nine
Baki bude gali ke kallonsa sannan ya kwashe da dariya harda dukewa yace kai amma guy dinnan ka rainamun hankali wai AK hausawee kodayake zaka iya fadan haka
Kaga nima akauyanmu salman khan ake kirana saboda yanda nake da kirar karfi
Dariya AK yayi har yana kuantoma asma'u yace wai salman khan amma wallahi zaginka sukayi baka saniba kuuuut
daure fuska gali yayi bai kara magana ba har suka iso inda zai saukesu sannan asma'u takarba wayansa takira driver tamai kuatancen inda suke
sun jima atsaye kafin kafin driver ya iso cike da fadin ciki suka rungume juna da AK yana mai barka
karban kudi yayi ahannun driver yamika ma gali yana kwace agogonsa daga hannunsa ya wuce mota
dariya gali yayi yana fadin eh dai jeka kana tunkaho da kudin budurwa gara ni gumina nakeci se gayu ba ko sisi
juyowa AK yayi ahasale yanufosa asma'u ta taresa tana dariya tama kasa magana
mota gali yashiga yana fadin hajiya allah kirabu dawannan yaron Sam Baku dace ba lashe money kawai
aguje AK yanufesa yayi saurin fadawa mota yatada yana daga ma asma'u hannu yayi gaba
Juyawa AK yayi yana watsamata harara yace to ai da kinbishi kuntafi tare kawai
Dariya take harda hawaye tanufi mota tashiga shima yashiga driver yaja suka tafi
suna shiga gari AK yafara washe baki yana kallon garin kamar dan kauye asma'u dai banda dariya ba abunda take yayi banza da ita kamar baisan tanayiba
kuantar dakansa yayi jikin kujera yana lumshe ido yace kai ba Inda yafi gida dadi
suna isowa gidan suka isko gaba daya mutanan gidan afilin gida ana jiransu kafin driver yagama parking suka fito aguje suka rungume juna se kukan farin ciki
Da kyar aka banbare khadeeja ajikin asma'u haka Umma da inna su grany ai ba amagana
Sunkusan awa daya ahaka kafin da kyar aka barsu suka karasa cikin gidan inda yasha gyara ba kadan ba se kanshin turaren wuta ke tashi ga kanshin girke girke kala kala
anan palon kasa suka zauna kan doguwar kujera sukasa grany atsakiya se Umma agefen AK inna kuma agefen asma'u khadeeja nazaune kan hannun kujera daga gefe se washe baki take
Kujeran kusa dasu kuma inna ameena ne da sarah dasu fa'iz se sauran mutane Abba kuma tundaga waje yakoma gida dan yaki shigowa ciki wai daga baya su samesa agida
tashi sukayi suka nufi dining kamar mayunwatan zakuna haka suka fara bude kuloli se dariya ake musu ko ajikinsu
Wayar khadeeja ce tayi kara tana dabuwa taga Tarzan cike da fadin ciki tadaga kiran tana fadin Tarzan albishirinka gasu amma sundawo suna gida yanzu haka
Dariya yayi yace dagaske kike to amma meyasa baki gayamun ba tun dazu ina cikin daji ina nemansu nayi fushi karki kara mun magana ....yana kai nan yakatse wayar yana murmushi cike dafarin ciki yakamo hanyar gida
abinci sukaci bana wasa ba seda sukayi tatil sannan suka dawo Palo aka ci gaba da fira
Ruwan dimi Umma tasa khadeeja takawo tagasa kafar asma'u lokaci guda suna basu labarin yanda abun ya kasance amma idan anzo wani wurin se suyi shiru suna sadda kai
tsakiyansu khadeeja tashigo cikin rada tace garama ku ijiye wannan kunyar agefe dan idan ahmad yadawo duk se kunbamu labarin abunda yafaru
kauda kai sukayi lokaci guda suka tuno abunda yafaru dazu
Saurin tashi AK yayi yana fadin ummm bari naje nayi wanka nagaji sosai
Dariya momy tayi tace ai gara kuje kuyi wankan kuhuta
Tashi su Umma sukayi suna musu sallama zasu tafi zunbur asma'u tamike tana fadin Umma Nima zanbiku muje
Kallonta sukayi da mamki inna tace jimun shashasha ina kuma zaki keda kika dawo yau kizauna kikula da mijinki bakya ganin yanda yadawo ne abun tausayi har kinfishi kumari da kyan gani
kallon juna sukayi da AK atare suka kauda kai yayi saurin wucewa bangarensa yana musu sallama
ba yanda batayiba amma sunki bari tabisu hakanan tahakura tazauna amma tana tunanin yadda zata kuana daki daya da AK dan se yanzu taji kunyarsa takamata
Shima haka abangarensa yana tunanin mezai cema asma'u idan takara gayamasa tana sonsa shi kunyarta ma yakeji yanzu yana tsaye apalo yana wannan tunanin yaji anturo kofa saurin juyawa yayi yana zaton itace jin muryan ahmad yasa ya juyowo dasauri suka rungume juna cike da farin ciki se dariya suke summa kasa magana
Sunjima ahaka sannan suka zauna kan kujera Ahmad yafara jera mai tambayoyi
Dafe kai yayi yace ohh ni wai yanzu sena kara maimaita labarin danabada dazu kaje wurin lhadeeja mana tagayamaka ai taji komai
Kauda yayi yana daure fuska yace banaso fada muke da ita nidai inzaka gayamun ka gayamun ai waka abakin mai ita tafi dadi
Gyara zama yayi yafara basa labarin abunda yafaru har wurinda suke zaune abakin rafi ya tambayi asma'u takosa taje gida ne...yana zuwa nan yayi shiru yana Sosa kai
Ahmad dayakashe kunne har da lumshe ido yana sauraronsa jin shiru yasa yabude idonsa yana fadin se tace me
Kauda kai AK yayi yana fadin se tace eh
jiyo dakansa ahmad yayi yana dariya yace ahh wallahi ban yardaba nasan bahaka tace wani Abu daban tafada gayamun metace u know I am ur friend naaaaa
Daure fuska AK yayi yana hararansa yace to kenan karya zan maka abunda tace kenan in kanaso inci gaba in bakaso kuma tashi katafi dama ni bacci nakeji
tashi ahmad yayi yana fadin bari inbarka ka huta amma kuma gobe ma ai zamuzo dole ma kubamu labarin abunda yafaru
tashi AK yayi ya wuce daki yana fadin kaida khadeeja dama jarida kukayi da yafiyemaku
dariya ahmad yayi yafita yana masa se dasafe
Haduwa sukayi da asma'u zatazo bangarensu tana ganinsa tajuya zata koma yayi saurin tarota yana dariya yace tsaya mana aunty munjima bamu haduba shine kuma kike guduna kamar kinga dodo
Washe baki tayi tana Sosa kai tafara kame kame
Dariya yayi yace karkidamu kitanadi amsoshin dazaki bamu gobe in allah yakaimu ina fata dai kin gayamasa kina sonsa dan har yanzu muna nan akan bakarmu indan baki gayamasa ba bazamuyi aure ba ....
Bata jira ya karasaba taruga aguje tashige bangarensu tana rufo kofar dakarfi
AK nazaune bakin gado yaji anturo kofa azabure ya kwanta yana tufa da bargo ya lumshe idanuwa kamar mai bacci
ahankali taturo kofar dakin tashigo tana lekensa
Ajiyar zuciya tasauke ganin yana bacci cikin sanda tawuce bathroom
Yana ganin tashiga yatashi zaune yajera pilullukan dasuke raba gadon tatsakiya sannan ya gyara kuanciyarsa yana lumshe ido
daren ranar aysha batayi bacci kuana tayi tana safa da marwa adakinta ga damuwar ta isheta ga batajin dadin jikinta ana gama sallar asuba tawuce asibiti bayan likita yadibi jininta yabama nurse tafita cikin minti 30 tadawo da result din yana dubawa yayi murmushi yace amm hajiya kinada aure ne ?
Kai tagirgiza mishi tana kafeshi da ido gabanta na dukan uku uku takosa taji mezai ce
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta yace idan bazaki damu ba inaso kidan kuanta anan zammiki scanning dan tabbatar da abunda kecikin result dinki
Gabanta ne yayi mummunar faduwa nan take idonta yaciko da kwallal jiki asanyaye tahau kan gadon duba marasa lafiya doctor yafara dubata
Yajima yana mata scanning din kafin daga karshe ya girgiza kai yakoma ya zauna yana yan rubuce rubucensa
Sakkowa tayi daga kan fadin tazo tazauna cikin rawar murya tace doctor menene
Dagowa yayi yana kallonta nadan lokaci sanann yamika mata takardar yana fadin gaskiya hajiya duk wasu gwaje gwajen damuka mini sun nuna kina dauke da karamin
*CIKI* na sati biyu!!!! 😱"""""
?????AK ne yamata 🤔
Kubiyoni taku Maryam Mhd danjin cigaban labarin
0 comments:
Post a Comment