har wannan lokacin su JJ nayawo acikin daji ganin mangoron dasukayi ayashe da alaman wurinda suka zauna shiyabasu tabbacin suna cikin dajin har yanzu dan haka sukaci gaba da nemansu ganin dare yayi yasa suka yada zango dan su huta se tsinema yaransa yake akan duk su sukaja mishi wannan wahalar
ba yanda ahmad baiyiba ba dayansandan akan suci gaba da nemansu tunda sunada torchlights amma sunce gaskiya sun gaji zasu huta gobe suci gaba
zaune asma'u take tasa AK agaba se kuka take tana tofa mai duk addu'ar datazo mata
Jikinsa yayi zafi rau gashi yana sauke nunfashi ahankali kana ganinsa kasan baccin wahala kawai yake dan da kyar yake Jan nunfashinsa
ganin jikinsa nakara zafi yasa ta tafita waje tadibo ruwa aroba sannan tamatso kusa dashi ahankali tafara balle buttons din rigarsa tana kallonsa cike datausayi hawayenta nadiga akan kirjinsa har tagama sannan tafara kokarin cire masa rigar cikin dabara gudun kar ta tasheshi
Har tagama cire masa rigar baisan tanayi ba
tsoma rigar tayi cikin ruwan tana dora masa akan goshi nan take ruwan robar yadau dumi seda tacanzo wani taci gaba dayimasa hakan har jikinsa yarage zafi sannan ta shanya rigar ajikin runfar
wurinsa tadawo ta gyara masa kuanciyarsa tadafa kansa tamishi addu'a
Sannan takoma gefe tazauna tana gyara daurin kafarta daya warware tun jini nazuba har ya daskare awurin seda tawanke ta kara gyara daurin sannan tafita tayo alwala tazo tafara jero sallolin da ake binta har tagama tashiga jero nafilfili tana rokammasa sauki awurin ubangiji tana rokon allah yakubutar dasu daga hannun wa'innan mutanen yamaidasu gida lafiya har alfijiri ya keto tana zaune batayi bacci ba seda tayi sallar asuba sannan tasake matsawa wurin AK ta taba jikinsa murmushi tayi jin ba zafi ajikinsa kuma nunfashinsa yafara daidaita
jin zai motsa yasa tayi saurin janye hannunta tamatsa baya
Gyara kuanciyarsa yayi yacigaba da baccinsa mai cike da mafarkai iri iri marasa kan gado
komawa tayi daga gefe ta kuanta nan take bacci yadauketa
hasken rana ne yadaki fuskar AK ahankali yabude idanuwansa yana bin runfar da kallo lokaci guda yana tuna abunda yafaru jiya
Murmushi yayi da yahango asma'u gefe akuance ta takura wuri guda tana bacci
ahankali yatashi zaune yana bin singlet din jikinsa dakallo tashi yayi yadauki rigarsa dayagani arataye yasaka sannan yafita waje
Roba yadauka yadibo ruwa arafi yayi alwala sannan yadawo cikin runfar yayi sallolinsa dayagama yayi addu'oinsa
sannan yamatsa kusa da asma'u yana duba kafarta daya kunbura yana so yataba kafar amma yana tsoro yatasheta yajima adurkushe kusa da ita yana kallon yanda take bacci kana ganinta kasan atsorace take
tashi yayi yafita daga cikin runfar yana bin wurinda suke da kallo
asma'u tajima tana bacci se wajan la'asar tafarka zunbur tamike tana kallon tabarmar da AK ke kuance amma bata gansa ba zunbur tamike zata fita kenan ta hango anyi rubutu akasa da mayyan harrufa kusa da inda takwanta
Durkusawa tayi tana karanta
DON'T GO ANYWAY I WILL BE BACK SOON
murmushi tayi tana shafe rubutun cikin siriruwar murya tafurta da wani Abu yasameka jiya zan mutu ina nadamar rashin sanar dakai cewa ina sonka amma nayi alkawarin yau zan Sanar dakai dan bansan mezai faru damu nan gaba ba
tashi tayi tafita waje tayo alwala tayi sallah sannan tayi addu'ointa taroki ubangiji ya kamusu karshen wannan wahalar
Rike cikinta tayi tanajin wata azababbiyar yunwa na damunta gashi tarasa inda AK yaje cikin wannan dajin jin kamar motsin mutun yasa tayi saurin mikewa atsorace taleko waje
ganin AK datayi zaune abakin rafi yasa tasauke wata nannauyar ajiyar zuciya tana murmushi ta nufo inda yake
Dagowa yayi yana kallonta da murmushi afuskansa yace kin tashi
Kusa dashi tazauna tana dafa kafadansa tace ya jikinka
Mangoron dayawanke yamika mata yana fadin naji sauki tundazu yunwa ta tasheni bashiri natafi neman abinci
Murmushi tayi tana kai mangoron bakinta tace thank you
kafanta yariko da hannunsa yadora kan cinyarsa yafara kwance daurin yana mata sannu
dagowa yayi yana kallonta yace kidaina taka kafan kinga ya kunbura sosai yanzu kibarshi haka yanashan iska kar yazame maki babban ciwo
Shiru tayi batace komai ba tacigaba da shan mangoronta tana kokarin hada kalmomin dazatayi anfani dasu wurin gayamasa abunda ke ranta
Wanke hannunsa yayi shima yadauki mangoron yafara sha suna kallon ruwan dake gabansu bawanda yasake magana
Sun jima ahaka secan yadago yana kallonta da murmushi afuskansa cikin sassanyar murya yace
Kinkosa ki koma gida ko ?
girgiza kai tayi tace nayi kewar gida amma I like it here
"Why
dagowa tayi tana kallonsa suka hada ido lokaci guda suka tsinci Kansu awani irin yanayin dasuka kasa fassara ma'anarsa
Cikin murya mai kaman rada tace ABI aduk lokacinda nake tare dakai banadamuwa da kowane wuri muke cikin dadi ne ko wahala duk hakan baidameni ba indai zan kasance kusa dakai ada nadauka sabone ko shakuwa amma daga baya natabbatar dacewa abunda nakeji shi ake cewa SO
Bansan yaushe kuma a ina nafara sonka ba amma abunda nasani kawai shine sonka yajima azuciyata
ABI so dayawa mutane suna tsoron fito da sirrin zuciyarsu ne saboda gudun kar su rasa kulawar dasuke samu daga wurin wa' inda suke so
Ni kaina abunda nake tsoro kenan amma bazan iya ci gaba da boye sonka araina ba
tunda tafara magana yake kallon kwayan idanuwanta ko kiftawa bayayi yana hango tsantsar kaunarsa acikinsu
Kauda kansa yayi cikin wani irin yanayi dayayi mai kama da mafarki
Hannunta tasa ta janyo fuskarsa saitin tata idonta cike da hawaye cikin sassanyar murya tace
ABI I am not asking u to love me
base kasoni ba kawai kabarni naci gaba da sonka and please kar kacanza mun nariga nasaba dakai idan kayi nesa dani bazan iya jurewa ba
tana kainan ta tashi tanufi runfarsu aguje tana sharan kwalla
Da kallo yabita har tashige runfar bai kauda kansaba lokaci guda kalamanta namai yawo akwakwalwa yana tuna rayuwarsu tabaya da wadda sukayi acikin dajin nan
mikewa yayi tsaye yasa hannayansa a aljihu yana safa da marwa awurin yarasa meyake damunsa awani hali yake ahin shima yana sonta ko kuwa
yana cikin haka kamar daga sama yaji maganar yaran JJ akusa dasu
saurin juyawa yayi aguje yanufi runfarsu
Zaune ya iskota kan tabarma ta takure wuri guda tana jin haushin kanta datagayamasa tana sonsa yanzu tasan shikenan abunda take gudu ne zai faru zai janye jikinsa daga gareta
Saurin karasawa yayi wurinta ya durkusa agabanta cikin rada yace chitti gasunan sun iso kitashi mugudu
atsorace tamike tsaye tana zare idanuwa
riko hannunta yayi aguje suka fito daga cikin runfar sedai kafin sugudu JJ sun iso wurin shan gabansu yayi ya saitasu da bindiga yana kwashewa da dariyar keta yace
Dakata mana AK ina kuma zakuje ai gudu yakare daga yanzu zaku huta muma muhuta da wahalar bibiyarku
Cak sukatsaya suna kallonsa ba alaman tsoro atare dasu
cike da takaici AK yace to mekake jira kaharbemu mana
Wancan karon ma sakacinka ne yasa muka gudu to yanzu ma inkayi wasa guduwa zamuyi
kuma kasake nabar nan wurin to daganan nine zanfara nemanka kana guduwa idan kuma nakamaka bazaka taba samun damar dazakayi kwakkwaran motsi bama bare kayi yunkurin guduwa
Kallon yaransa yayi suka tuntsire da dariya seda sukayi mai isarsu sannan ya saita bindigarsa kan AK yana kirga uku
Kuka asma'u take tana kankame AK ajikinta se rokonsu take karsu kasheshi amma banda dariya ba abunda suke dai daga cikin yaran yasaitata da bidiga yana fadin kar kidamu yan mata ai tare zaku tafi bahaka kuke soba
rungumota AK yayi akirjinsa takara kankamesa dakarfi tana runtse idanuwanta
JJ na kirga uku yadora yatsansa kan kunamar bindigar zai harba kenan yan sanda suka iso wurin tare da ahmad
nan fa aka fara musayar wuta tsakanin yan sandan da su JJ
Tundaga nesa ahmad ke kwalama AK kira yana fadin su gudu
tsaye AK yayi cike dafarin ciki yana kallon ahmad se washe baki yake yakasa motsawa gashi se harbi ake da bindiga amma ko ajikinsa
Jan hannunsa asma'u tayi dakyar yabar wurin suka ruga aguje sukayi wata doguwar hanyar dasuka gani
Sunyi tafiya mai nisa kafin suka iso wata kasuwar kauye da mutane dayawa awurin kowa na harkan gabansa
tsaye sukayi awurin suna maida nunfashi
Cike da takaici AK ya kalli mutanen wurin yana jan tsaki yace yanzu duk wahalar da mukasha ashe akwai dubban mutane anan wurin amma ko tsuntsu bamu gani ba
[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣5⃣5⃣
hannunta narawa takarbi result din tana dubawa tajima azaune awurin hawaye natsere akan kuncinta dakyar tamike tsaye tana neman faduwa saboda jirin dake dibarta
saurin mikewa doctor yayi yana fadin easy madam are u alright
Bata kula saba tafita daga office din tana Jan kafa kamar wacce aka zarewa lakka
zama tayi acikin motarta tadafe kai cikin rawar murya tace what....what... have I done ...I am ...such a fool
garin ya nabari haka tafaru wane mataki dady zai dauka akaina ya AK zai yi idan yasan ina dauke da *cikin da banashi ba*
fashewa tayi da kuka tana fadin *SALIM* kacuceni yanzu yazanyi ni aysha nashiga uku
Tajima tana kuka kafin tayi saurin daukar wayar ta takira wata number
Tajima tana ringing kafin yadaga cikin muryan bacci yace
Baby kintuna dani yau shine zakimun kiran asuba na....
Katseshi tayi da fadin salim kana ina ne we have a problem
Dariya yayi yace anzo wurin dama ai bakya nemana se kinada matsala
fashewa tayi da kuka tana fadin salim please it's a serious problem I am .....
Saurin tashi zaune yayi yana fadin ohh my god baby are u crying
Shiru tayi batace komai ba taci gaba da kukanta
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon agogon dakin yace ok ni... ina gida yanzu zakizoni ko inzo insameki
tada motar tayi tana fadin a'a ganinan zuwa yanzu
daidai wani katafaren estate tayi horn mai gadin yaleko yana ganinta ya washe baki yana fadin ahhh beautiful barka dazuwa ....
Harara tamaka mai tana jan tsaki tace kai dallah open the get for me I don't have time for u nonsense
Budemata get din yayi tashiga tana gama parking tafito da gudu gudu take hawa stairs
ahawa nabiyu tatsaya dadai wani hadadden apartment tayi knocking
bata jima atsaye ba aka bude kofar
wani dan kyekkyewan saurayi ne atsaye yana mata murmushi
( salim kenan saurayin aysha ne tun tafiyar dasukayi London itada sarah tahadu dashi tun tana wulakanta shi har tafara kulashi saboda tako ina yahadu yasan duk wata hanya dazaibi yashawo kan mace ya iya soyayya gashi yana sakemata kudi kamar hauka
Kwararen lawya ne maizaman kansa yanada kudi daidai gwargwado gashi shikadai ne awurin babansa shiyasa yazama dan gata duk abunda yakeso shi akemai
Wata rana aysha tazo gidansa tana kuka saboda damuwar rashin kulawar AK dabata samu
Garin lallashinta ne har suka wuce gona da iri shine wanda yafara saninta ya'mace kuma daga ranar ciki yashigeta
Idan yamata maganar aure setace tana so se ta mallake dukiyar AK gaba daya sannan zata aureshi saboda shine burinta da na iyayenta
tun bayaso har tanuna mai irin ribar dazasu samu tagayamai kadan daga cikin kadarorin AK tun daga lokacin shima yafara kwadayin dukiyar )
kauda kai tayi tana share kwalla
Janyota yayi ciki yana rungumeta yace baby I missed u so much
Turesa tayi tawuce Palo tazauna tana rabka uban tagumi
Karowa yayi kusa da ita yazauna yana fadin come on baby banason ganinki haka gayamun damuwarki kinsan uwarki ta haifeki ne dan kikawo matsala nikuma uwata ta haifeni dan na magance maki ita
hararansa tayi tace kafara ko???
Dariya yayi yana shafa kai yace sorry namanta ne yanzu gayamun meyake damunki
ciro result din tayi daga Jakarta tana nuna masa tace salim inacikin babbar matsala dama na gayamaka banajin dadi to yanzu haka daga asibiti nake doctor ya tabbatar mun inada ciki
shiru yayi yana kallon result din nadan lokaci sannan yadago yana kallonta yace
look aysha nafasan halinki idan kina bukatar kudi ba abunda bazakiyi ba idan kinsan karya kike to garama kifito kigayamun sannan kinsan ko nawa kike so zan iya baki but don't play games with me
riko hannunsa tayi tana kuka tace salim allah dagaske nake idan baka yarda ba muje tare dakai kagani
Dafe kai yayi yana tunanin ta inda zai bulloma lamarin kamar daga sama yaji tace
Salim nidai tsoro nakeji gaskiya muje acire cikinnan
Saurin dagowa yayi yana nunata dayatsa cikin kakkausar murya yace
Kar ma kifara aysha bakida hankali ne zubarwa fa kikace
to wallahi kinji narantse kar ki kuskura kizubar mun da ciki kinji ko ina son abuna
rungumeshi tayi tana fashewa da kuka tace salim tsoro nakeji idan dady yasani zai kasheni sannan kuma .....AK idan yagane inada ciki zai rabu dani kaga bazai aureni ba bare har mucimma burinmu
Shafa kanta yayi yana fadin stop crying baby nothing bad will happen kin manta ina tare dake yanzu dai zauna muyi magana
Zaunawa tayi tana ci gaba dakukanta
Share mata hawaye ya shigayi yana fadin ya isa haka kidaina kuka mana ko kinaso wani abu yasami babynmu ne
girgiza kai tayi tana shafa cikinta hannunsa yadora kan nata yana murmushi yace love u my baby
tashi yayi yanufi kitchen bayan dan lokaci yafito rike da fresh jus acikin glass cup yamika mata
Kusa da ita yazauna yana sauke ajiyar zuciya yace yawwa to yanzu kinsan ya za'ayi
Girgiza kai tayi tana ijiye cup din hannunta akan table takureshi da ido takosa taji mezai fadamata
murmushi yayi yace ya zancan AK anganshi kuwa ?
Kauda kai tayi tana fadin sundawo jiya
Kusanta yamatso ya juyo dafuskanta yana fadin kawo kunnenki to kiji
wata magana yamata akunne tayi dariya cike dafarin ciki tace wow!!! salim shiyasa nake sonka akwaika da brain kaga daga nan hankalin AK zaidawo kaina munayin aure kuma se insa yaimaida dukiyarsa kan sunan danmu daga nan kuma se.....
dariya sukasa suna tafa hannu ta rungumeshi tana fadin thank you dear
Shafo cikinta yayi yana murmushi yace gaskiya yau kin zomun da albishir mai dadi kinada kyewta mai tsoka
ture hannunsa tayi tace to saura garin rawar kafarka kabari aharbo jirginmu
Kara maida hannunsa yayi kan cikinta yana langabe kai yace allah sarki AK uwata ta haifeni dan inmaki ciki shikuma uwarsa ta haifesa dan yazama uban dan sannan yakai bakinsa kan cikinta yana fadin kai kuma baby uwarka zata haifoka dan ka kawo mana kudi
mikewa tayi tsaye tana kaimasa duka da pilo tace u will never change salim kafa girma yanzu u are going to be a father yakamata kanatsu
dariya yayi yana mikewa tsaye yace baby bari inzo inkaiki wani hadadden wuri kigani antanadeshi ne kawai dan masoya
murmushi tayi tace ai kai kam kahadu tawannan wajan shiyasa nakasa hakura dakai
Janyota yayi jikinsa yana rungumota tabaya yakai hannunsa kan cikinta bakinsa daidai kunnanta cikin rada yace ohh tanan wajan kawai nahadu ko se antabayi baby yaraba mana gardama
hannunta takai baya tana shafo sumar kansa tace kahadu tako ina my Romeo shiyasa nakosa nagama da wa'iccan muyi aurenmu
Dariya yayi yasaketa yawuce daki yana dan tsalle yace ohhh I can't wait for that day to come inganki amatsayin matata harda dan babynmu
kamar yadda suka zo jiya haka ma yau suka taru gida yacika da yanuwa tamakar gidan biki se raha ake ana murna ya yinda gefe guda khadeeja da ahmad suka tasa AK da asma'u gaba akan se sunbasu labarin abunda yafaru atafiyar su
se wasan buya suke tsakaninsu kowa bayason bada labari daga karshe guduwa AK yayi yabuya adakin sarah
Asma'u kuma tajima dashiga dakin grany sun rasa inda tayi tana fitowa daga bayi kenan taga khadeeja akan gado juyawa tayi zata fita taga ahmad abakin kofa ya harde hannaye yana murmushi
komawa tayi bakin gado tazauna tana fadin ok fine naji zan Baku labarin amma karwanda yamun tambaya harse nagama
Karasowa yayi cikin dakin yazauna kan kujera suka sakata agaba suna saurare
labarin tafara basu kanta akasa tana murza yan yatsunta har tazo wurinda nunfashin AK kedaukewa sannan ta tsaya tana kame kame
Kara matsowa kusanta khadeeja tayi tana fadin se meyafaru ya akayi nunfashinsa yadawo
hararanta Ahmad yayi yana danne dariyarsa yace ke batace karmu tambayeta ba
sanann yakalli asma'u yana fadin manta da ita aunty cigaba dabamu labarin
Sosa kanta tayi idonta arufe tace se..... Nataimaka masa....
katseta khadeeja tayi dafadin dame kika taimaka masa
Hararanta tayi tace bansaniba allah se infasa bada labarin
Sorry ....tafada tana gyara zamanta
Kallon ahmad tayi tace ai kai kagane ko ?
Dariya yayi yace sosaima ba irin yadda innunfashin mutum yadauke ba se kasa bakinka ka....
Katseshi tayi dafadin badai ka ganeba to miye kuma nase kafada
shiru sukayi suna kallon juna shida khadeeja kamar su tuntsire da dariya amma suna danneta dan sunkosa suji ko tafadamasa tana sonsa
Cigaba tayi dabasu labarin har wurinda tagayama AK cewa tana sonsa
Ihu sukayi cike dafarin ciki khadeeja tafada kanta tana fadin wow ammah gaskiya kinyi kokari dama ina wajan inga yanda abun yakasance
Dariya ahmad yayi yana nikewa tsaye yace to shikuma meyace
sunkuy dakai tayi cikin sassanyar murya tace baice komai ba kuma dama ban fada dan inji mezai ce ba kunga ko yanzu abunda nake gudu ne yafaru tunda bama zama waje guda bare muyi fira ko yamun magana
Fita ahmad yayi yana fadin karki damu komai zai wuce zaku saba ai ki shirya shima ya kusa cewa yana sonki
da daddare bayan kowa ya watse AK yana zaune apalon masa yanason shiga bangarensa amma yanajin kunyar haduwa da asma'u se dannan waya yake yana duban agogo
aysha nadaga gefe takira nura tabashi glass cup din jus tace yakaima AK yace inji grany
yana zuwa yamika mashi karba yayi yana murmushi yakafa kai seda yashanye shi tas sannan ya ijiye cup din
Baifi minti 5 ba kansa yafara juyawa saurin dafe kai yayi yana salati yazo tashi amma yakasa saboda jirin dake dibarsa
Karasowa palon aysha tayi takamashi tanufi dakinta dashi Sam baisan duniyar dayakeba tana zuwa takwantar dashi kan gado
Seda tacire masa kayansa kap tabarsa dagashi sai boxer sannan tarufa mai bargo takoma gefe tana sauke ajiyar zuciya
can cikin dare asma'u tafarka amma bataga AK ba kuma ba alamr yashigo dakin bare har ya kuanta
Tashi tayi tafito Palo nan ma wayam daki to koma ta zunbulo hijabinta tasauka kasa
Duk inda take sa ran zata gansa taduba bata gansa ba takira wayansa kuma taji tana ringing akan kujerar Palo
cike da damuwa ta koma bangaresu tana addu'ar allah yasa lafiya
Zaunawa tayi anan Palo dan Sam taji baccin yafita idonta se safa da marwa take tana duba agogo """"
[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: Cikin baccinsa yake jiyo sheshshekar kuka sama sama kamar amafarki
ahankali yafara bude idanuwansa yana dafe kai saboda nauyin dayayi masa cike da mamki yake bin dakin da kallo har idonsa yakai kan aysha dake zaune gefensa daga cikin bargo tana rusa kuka
saurin tashi yayi zaune yana kallon ikon allah bakinsa narawa yanaso yayi magana amma yarasa mezai furta
sauka yazoyi daga kan gadon yaga kayansa akasa saurin komawa yayi yazauna yana fadin wai meyake faru.....
Katseshi tayi dafadin dole katambayi meyake faruwa bayan kagama biyan bukatarka
kallonta yayi dajajayen idanuwansa cikin rawar murya yace kamar...ya...banganeba ....aysha wai menake adakinki ne awannan lokacin kuma akan gadonki and why are u crying
Fashewa tayi da kuka cikin daga murya tace ba abunda kake adakina zaka tambaya ba abunda kayi adakina zaka tambayeni kukan kuma inayinsa ne saboda kacuceni ka zalinceni ka lalata mun rayuwata ka....
Katseta yayi yana daka mata tsawa yace shut up dallah what kind of joke is this ..
"I am not joking AK u raped me
saurin matsawa yayi yana kallonta cike da tashin hankali jikina har rawa yake ga kansa dayake Sara masa jinin dayagani kan gadon shiyakara rikita masa lissafi
cikin rawar murya yace me....but...how garin ya haka tafaru abunda bantaba yiba ba halina bane ko amatan banza ma bare ke kanwata
Cikin sheshshekar kuka tace nima bansani ba jiya ina kuance kawai naji kashigo mun adaki duk yadda naso inmaka bayani baka saurareni ba dakarfin tsiya ka turani kan gado nayi kokarin in kwaci kaina amma nakasa ...
takarashe maganar tana fashewa da kuka
jiri ne yadibesa yaja dabaya dabaya ze fadi yayi saurin rike kujera zama yayi akai yana dafe kansa wasu hawaye masu zafi suka gangaro kan kuncinsa kokari yake yatuno abunda yafaru amma yakasa abunda yake iya tunawa kawai shine lokacinda yake zaune apalo yana danna waya daga nan kuma baisan meyafaru ba se yanzu dayafarka yaganshi anan
ya jima ahaka kafin da kyar ya iya dago kai yana kallonta yanaso yayi magana amma Sam yakasa bude bakinsa tashi yayi yadauki kayansa yasaka batare dayace komai ba yafita daga dakin
Tana ganin yafita tamike cike dafarin ciki tafara rawa tana murna
tafiya kawai yake amma Sam baya cikin hayyacinsa jiki asanyaye ya nufi bangarensa
Yana tura kofar asma'u tamike azabure tanufosa tana fadin ABI are u alright daga ina kake naduba ko ina banganka ba gashi har asuba tayi allah yasa lafiya
wuceta yayi kansa akasa batare dayace komai ba yanufi daki
Shan gabansa tayi tana riko hannunsa cikin rawar murya tace ABI meyake damunka ya naganka haka kaga.....
Kwace hannunsa yayi yana damko kafadunta cikin kakkausar murya yace
Akan wane dalili kike tambayar daga ina nake dole ne se kinsan Inda naje da inda nakuana kar kimanta har yanzu bakida wani matsayi awurina so stop acting like my wife ....
yana kainan ya turata dakarfi ya wuce daki yana banko kofar dakarfi
kan kujera tafada tana binsa da kallo idonta pal kwalla tana mamakin meyake damunsa ne haka zama tayi anan palon taci gaba da kukanta lokaci guda maganarsa namata yawo a kunne
bayi ya wuce direct ya sakar ma kansa shawa idonsa arufe hawaye nazuba akan kuncinsa lokaci guda yaji ya tsani kansa wai yarasa wacce zai ma fyade se kanwarsa tajini
dakyar yasamu yayi wanka ya shirya ya nufi masallaci acan ya zauna seda gari yawaye sanann yanufo gida yafara shirin zuwa office
yana wurin dressing mirror yana fesa turare asma'u tashigo rike da coffee dinsa
batare data kallesa tawuce ta ijiye kan bedside drawer sannan tafita
Dakallo yabita har tafita sannan yasauke ajiyar zuciya yana ji bai kyewta abunda yamata dazu ba
bayan yafito dakin aysha yafara lekawa tana bathroom zama yayi akan gado yana jiranta
Tana fitowa tagansa azaune nan take ta hade fuska ta wuce drowan kayanta tana share kwallan munafunci
tashi yayi yakarasa wurinta cikin sassanyar murya yace aysha I am really sorry ni kaina bansan ya akayi haka tafaru ba amma ki yi hakuri ki rufamun asiri banaso kowa yaji maganar nan kuma namiki alkwarin duk yanda za'ayi zan yi kokarin ganin anyi aurenmu nan bada jimawa ba
banza tayi dashi tanufi dressing mirror yakara binta yana bata hakuri seda kyar ta hakura
Tana murmushi tace shikenan insha allahu ba Wanda zai ji kuma nayafemaka ai kasan ina sonka ....
takarashe maganar tana kokarin rungumeshi yayi saurin juyawa yafita yana fadin thank you ga magani nan na ijiyemaki kici abinci kisha
Da kallo tabisa tana murmushin mugunta tace zan rufamaka asiri har lokacinda cikina zai bayyana daga nan kuma ur name is sorry
cikin kuanakinan haka AK yadawo so silent ba um ba um um tun ba aluraba har aka gane kowa yafara tambayarsa sedai yace ba komai tsakaninshi da asma'u kwa ido ne dan har yanzu basu fara gaisawa ba .......lol
Sedai zuwa wannan lokacin ya tabbatar ma kansa cewa yana sonta amma bayada kwarin guywar gayamata sedai koda bazai iya gayamata damuwarsaba to yana son ganinta akusa dashi yana Satan kallonta hakan ma ya isheshi
Itama tadamu sosai dayana yinsa amma seta dangantashi da cewar datayi tana sonsa ne ya janyo hakan saboda haka tayanke shawarar janye jikinta daga garesa amma taga hakan ba wani saukin dayakawo
yanzu aysha hankalinta ya kwanta saboda AK yana kulata ko baya gida yana kiranta awaya yaji ya take
Asma'u tadamu matuka da halin da AK ke ciki zaune take tana kuka kawai tayanke shawarar zataje office tasamesa suyi magana
Yamanta da duk abunda tafada dawasa take ba dagaske bane dan haka sudawo yanda suke da matsayin abokai
Sedai wannan ranar takasance bakar rana awurinta seda tayi nadamar zuwa company
Saboda anan taji aysha da uncle jamilu na maganar plan din dasuka shirya dan mallake dukiyar AK daga karshe intakama ma su kasheshi kuma su kori kowa nagidan har taji aysha nafadin
Dady itama sarah daka gani dukiyar nan takeso saboda naji da kunnena tace daga ranar da tashiga hannunta gabadaya zata kori kowa daga gidan haka ma inna ladidi itama dukiyar takeso shiyasa ta aiko bashir yana aiki anan .....
Bata tsaya tagama jin karshen maganar ba ta baro company din ko AK din ma bata ganiba
[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: baki da hanci suka saki suna kallonta wasu kuma gulma nacinsu se fadin suke wannan kamar madam Asma'u
badan wannan shigar tata ba daba abunda zai hana muce itace dan gaskiya kamar tabace
Bakin takalmi ne akafanta (cover shoe👢) tana sanye da wando tight light blue se T-shirt dinta fara tadoro dark blue din jacket maidan tsayi daidai guywa tayi rolling dabakin gyale fuskanta yasha make up tana sanye da bakin glasses afuskanta wanda shi yakara fito da ainahin kyawun fuskarta
lafiyayyen agogon fata ne daure ahanunta se wani dan karamin zoben azurfa makale ayatsanta
tsayawa fadar haduwar wannan yarinyar bata lokaci ne kana ganinta zaka rantse ba yar Nigeria bace ko daga yanayin shigarta kawai ka kalla kasan kudi sun zauna
Glasses dinta ta cire ta sakala shi awuyan rigarta ko kadan ba alamun far'a afuskarta
Kallon ma'aikatan gidan tayi daya bayan daya sannan ta nuna wani dayatsa cikin siriruwar murya tace
Kai zo nan
Jiki narawa ya nufi wajanta yana washe baki ya durkusa har kasa yana gaidata
batare da ta amsa gaisuwarsa ba ta Tamika mai makullin motar tana fadin kashigo mun dakayana ciki
cike da kasaita take takunta kamar bata son taka kasa har ta isa dab da kofar palon sannan taja birki ta tsaya
Hawayen fuskarta ta goge sannan tamaida glasses dinta seda taja dogon nunfashi ta furzar sannan tasa kai cikin gidan
zaune suke gaba daya apalon gidan suna fira aunty sadiya da fitowarta kenan daga kitchen rike da plate din dambun nama bata San lokacinda ya subuce mata ba yafadi kasa ba
gaba daya suka juyo dan ganin meke faruwa sedai lokaci guda sukayin saurin mikewa tsaye suna kallon abin al'ajabi
Nunata sadiya tayi da yatsa baki na rawa tace wa...... Wa nake gani haka kamar asma'u
Kallon kallon akafara tsakaninsu sannan suka jiyo suna kallonta anrasa Wanda zaice wani Abu
ahankali take takunta kanta asama tana bin palon da kallo har ta iso wurinsu sannan ta tsaya tana binsu da kallo daya bayan daya fuskarta ahade ba alamar annuri
karasowa wurinta grany tayi tana kallonta sama da kasa cikin rawar murya tace a....asma'u kece?.... ina kika shiga har tsawon wata guda muna nemanki ?
Jin shiru yasa takara matsowa tana kureta da ido tace wai kodai ba asma'u bace
Ganin batada niyyar bata amsa yasa tajuya tana kallon bashir tace kai je kakira mana Abidi yazo yatayamu ganin ikon allah ....
bata gama karasa maganarta ba AK yashigo palon aguje dan tuni ma'aikatan gidan suka sanardashi zuwanta
Nufo inda take yayi da sauri sauri har yana tuntube yana dariya mai yar sauti yace chitti kece kika dawo haka wow gaskiya kinyi kyew amma wannan shigar ai se ta tsorata mu
yana isowa dap da ita ya tsaya cak yana kallonta tundaga kasa har sama cike da mamki azuciyarsa yana fadin kodai ba chitti bace wannan
Amma jikinsa yana bashi tabbas itace saurin rungumeta yayi dakarfi kamar zai maidata ciki cike da farin ciki yake fadin
Chitti dama kina raye Ashe zan kara ganinki me yasa kika barni alokacinda nafi bukatarki
Koma ina kikaje meyasa baki gayamun muntafi tare ba
Muryansa ne takarye yana kara matseta ajikinsa kamar zai yi kuka
yace chitti u have no idea how difficult it was for me to live without u
nasan namiki laifi but I am sorry bazan karaba zan dawo yanda muke da I promise kuma dama ina so ingayamaki chitti l lo.........
baikarasa ba ta tattaro illahirin karfinta gaba daya tasa hannayenta biyu ta turasa baya dakarfi har saida yakusa faduwa bashir yayi saurin tarosa tabaya
😱Shocking!!!
Zaro ido sukayi gaba daya suna kallon Abu kamar film dan haryanzu basu yarda ba wai dagaske asma'u ce tadawo ba
kara nufota yayi yana fadin chitti yau ni kike turewa haka nasan fushi kike dani har yanzu amma nace kiyi hakuri idan bazaki hakura ba u can punish me bu please don't ever leave me again
Glasses dinta tacire tana nunasa dayatsa cikin kakkausar murya tace kar kasake katabani *AK* ko kamanta cewa banada wani matsayi awurinka ne I am jus a stranger to u saboda haka u have no right to touch me
baki ya saki yana kallonta cike da mamaki yama kasa magana
Wannan wane kalan iskanci ne haka kananin mutane zaki daukemu idan kinmanta mutuncinki ai bazaki manta cewa shi mijinki neba ....uncle jamilu yafada cike da bakin cikin sake ganinta arayuwarsa
Juyowa tayi tana kallonsa fuska adaure sanann ahankali takarasa inda yake tsaye tana nuna AK da yatsa cikin murya mai kaman rada tace
Wannan tsakanina dashi ne ba girmanka bane shiga abunda bai shafeka ba so stay out of it idan zaka iya kallo kayi idan bazaka iyaba kuma se kabar nan
Fizgota aysha tayi ahasale tace malama ki iya bakinki duk fitsarar dakika koyo ta tsaya kansu amma kar kisaka babana aciki
Kuace hannunta tayi tana murmushi tace baban naki yakamata ki gayama ya iya bakinsa baniba
baki suka saki gaba daya suna kallonta cike da al'ajabi
cike da takaici inna ameena tace ke wai ma tukkuna wacece ke dan ni har yanzu banyarda asma'u bace dan ba abunda kuka hada banda kama
Saurin juyowa asma'u tayi tana tafa hannu tace good question inna kab cikinsu bawanda yamun wannan tambayar seke ?
yanzu kuwa zakuji koni wacece
Asma'u Mahammad Magaji ko kuce Asmy Magaji
sannan ina farin cikin sanar daku cewa I am the new owner of the hausawee properties ma'ana namallake duk wata kadara da ajiyayun kudi na AK hausawee
Wani irin wawan jiri ne yadibe jamilu se akan kujera tim nan take zufa ta hau karyomai kamar yashiga kasan shower
saurin dafashi aysha tayi tana mai alamar ya natsu sannan ta tsiyayi jus a copi ta mika mashi
What nonsense... AK yafada yana daka mata tsawa
toshe kunnenta tayi tana runtse ido nadan lokaci sannan tabude idanuwanta tana nufo wurinsa cikin sassanyar murya tace
Easy man ai abun bai kai haka ba idan kabini ahankali zaka fahimci komai
juyo da ita grany tayi afusace ta wanketa da lafiyayyen mari saurin dafe kuncinta tayi tana kalkon grany da mamaki tace grany ni kika mara
"An mareki idan akwai abunda yafi mari ma ya cancanci amaki ke bakiji kunyar furta wannan kazamin furucin agabanmu ba to idan ma wasa kike kidaina dan mu ba abokanan wasanki bane mara kunyar banza kawai
karasowa AK yayi yadafa kafadarta yana fadin yi hakuri grany mudan bita asannu kamar yadda tace inaga daga karshe zamu gane tasamu matsalar kwakwalwa ne shiyasa take wannan abun
Dariya bashir yayi yana fadin kai amma wannan haukar da dadin kallo take Yaya
akwatinta tanufa taciro wasu kardu tana murmushi Tamika ma AK tana fadin ga wannan shizai tabbatar maka da abunda nafada ba hauka bane
Karban takardun yayi yafara dubawa nan take jiri yafara dibansa seda yazauna kan kujera dagowa yayi yana kallonta da jajayen idanunwansa bakinsa narawa amma yakasa furta koda kalma daya
Saurin kauda kanta tayi ta koma gefe ta zauna kafa daya kan daya yafara magana kamar haka
nasan zakayi mamakin ganin abunda nafada gaskiya ne kuma kana so kasan ya akayi sa hannunka yazo kan takardun batare da saninka ba
AK kayi wawta matuka da kayarda cewa haka kawai nake zaune dakai bayan nasan cewa baka sona bana sonka
gaskiya ada nayi niyyar rabuwa dakai amma daga baya nayi wani tunani meyasa zan tafi nabar wannan tarin dukiyar batare Dana dibi kasona ba shiyasa nahakura naci gaba dazama dakai ahaka har zuwa lokacinda nacimma burina
Daga lokacinda nagane illahirin takardun kadarorinka suna wurin grany daga lokacin
nayi iya kokarina wajan cusa yardata azuciyarta har takai ta amincemun nashiga ko ina abangarenta ta wannan hanyar nayi nasarar sace takardun kai kuma nayi anfani da wata hanyar nasa kayi signing dinsu batare dasaninka ba
sanin cewa idan har zan rike dukiya irin wannan ina bukatar experience hakan yasa nashirya tafiya coast zuwa America batare dakowa yasaniba har natsawon wata daya gashi yanzu nagama cikin Sa'a nadawo zan kula da dukiyata yanda yakamata .....takarashe maganar tana kwantar dakanta kan kujera hade da lumshe ido
Tsit palon yayi tamkar anyi ruwa andauke bakajin komai sai saukar ajiyar zuciyoyi daga kowane gefe
AK kam tamkar gunki haka yadawo dan ko yatsarsa yakasa motsawa har yanzu yakasa yarda da abunda kefaruwa yakosa yafarka daga wannan rikitaccen mafarkin mai ban takaici wai chitti ta yaudaresa
Dafasan da bashir yayi ne yadawo dashi hayyacinsa dagowa yayi yana kallonsu daya bayan daya kamar baitaba ganinsu ba har yazo kan asma'u sannan da kyar ya bude bakinsa cikin wata iriyar murya yace but u said u love me
Dagowa tayi tana kallonsa sannan ta kwashe da dariya tace it's all part of my plan so karma kasa abun aranka
Shiru yayi baice komai ba yana kallon takardun hannunsa
Zunbur uncle jamilu ya mike cike da masifa yace kai ina walkahi bazai yiwu ba haba Abu sekace wasan yara tayama za'ayi ace wai keda kikazo jiya jiya har kin mallake gaba daya dukiyar ai baki isa ba wallahi
toshe baki aysha tayi jin katobarar da ya abka
Kallonsa asma'u tayi da gefen ido tana wani malalacin murmushi tace ohh kenan dama akwai masu neman dukiyar bani kadai bace
Zaunawa yayi yana share zufa dan se alokacin yagane subutar baki yayi
Tashi tayi tsaye tana kallon AK tace AK I know it hurts amma ya zakayi se hakuri karike wa innan takardun awajanka original din yana wajena idan kuma bakayarda ba zaka iya kai abun kotu I am ready for it
tana kainan taja akwatinta tayi bangarensu tana fadin I need to have some rest dan allah duk mai magana yajira zuwa gobe dasafe
Baki bude suka bita da kallo har tahaye sama sannan suka jiyo suna kallon juna tafa hannu inna ameena tafarayi tana salati tace oh ni ya'su jama'a kutayani ganin wannan abin al'ajabi
Zaunawa grany tayi rike da wayarta tana Neman numban Umma tace nidai gaskiya wannan Abu ya dauremun kai bari mu kira ummarta inmu tamana wasa da hankali ta rainamu ai bazata ma uwarta ba ko?
Umma nadauka tasanar da ita asma'u tadawo cike da mamaki tace grany asma'u fa kika ce
Tabe baki grany tayi tace aha'ab ai se kuzo kuga ikon allah
Shidai AK tunda ya zauna bai tashi ba ganin abun yake kamar almara wai chitti ta malakke dukiyarsa kuma wai karya take bata sonsa dafe Kansa yayi aransa yana fadin inna lillahi wa inna ilaihiraji'un
ba'afi minti talatin su Umma da khadeeja suka shigo gidan cike da farin ciki tanufo grany tana fadin grany ina asma'un take dagaske asma'u tadawo ina aka ganta
Shan gabanta aysha tayi tana fadin Umma yarki ba bata tayi ba kuma ba wani Abu yasameta ba tafiya tayi har na tsawon wata daya batare da sanninku ba
Cike da mamaki Umma take kallon mutanan palon dasukayi cirko cirko suna kallonta
Juyowa tayi tana kallon aysha tace tafiya kuma kamar ya ina taje
dariya aysha tayi tana tafa hannu tace ke uwarta baki sani ba taya za'ayi ni insani
Juyo da ita khadeeja tayi ahasale tace ke kisan abunda zai rika fitowa da bakinki kar kimanta da mahaifiyata kike magana
kwace hannunta tayi tana fadin ohhh Ashe dai ba dadi to awurin yayarki nakoya
Dawo da kallonta tayi kan Umma tana girgiza kai tace Umma dama tarbiyar da kike ikrarin kin bama yarki kenan kullun kina yabonta she is nice she have a good heart yarki diamond yarki gold to yau munga asalin wacece ita
katseta Umma tayi dafadin ke karki mun rashin kunya kinji ko
karasawa tayi wurin grany tazauna tana fadin grany wai meke faruwa ne ya naganku haka
ajiyar zuciya grany tasauke tashiga bata labarin abunda yafaru
Juyowa tayi tana kallon AK cike da mamaki tace kun tabbata asma'u ce kuwa dukiya fa kukace asma'u dako kudinta ma bai dameta ba bare har takai ga malakke wannan dumbin dukiya kuma wai ta mijinta kai gaskiya.....
Katseta uncle jamilu yayi yana share zufa yace to karya zamu maki kenan badai kinyi karatu ba to ga takardunan ahannun AK duba ki gani kuma wallahi bazata sabu idan shi ya kyaleta to ni bazan barta ba haka kawai shekara nawa ina ......
saurin taboshi sadiya tayi tana mai alama ya iya bakinsa
gyaran murya yayi yace ummm shekara nawa yayi yana wahala har yatara wannan dukiyar shine lokaci guda zata rabashi da ita kuma mubarta haka kawai
Umma dai har yanzu bata gamsu da bayaninsu ba nan take ta aika dai cikin ma'aikatan yakira mata asma'u
Seda tadauki tsawon lokaci sannan ta fito wannan karan idonta yayi jajir daganinta kasan taci kuka
Tunda daga nesa Umma da khadeeja suka saki baki da hanci suna kallonta har ta iso palon ta tsaya cak tana kallonsu
Saurin karasowa khadeeja tayi ta rungumeta tana kuka tace ammah ina kika shiga mukayita nemanki bamu ganki ba meyasa zaki tafi kibarmu kin kwsan halin da muka shiga na rashinki duba kiga yanda Umma tadawo kullun batada lafiya saboda tunaninki
Shiru tayi batace komai ba tana kallon Umma sama da kasa
ahankali Umma takaraso wurinta tana kallon shigarta da mamaki tace asma'u meyasameki haka ya kuma naganki da wannan shigar ina kika tafi batare da kinsanar damu ba
Kauda kai tayi batare datace komai ba
riko kafadunta Umma tayi tana kureta da ido tace asma'u meke damunki ne anya kuwa lafiyarki kalau ko dai abunda grany tafadamun dagaskene wai kin.....
Katseta tayi dafadin Umma kinsan dai grany bazata maki karya bako to dagaskene
Shocking.....😱
Kallon kallon aka fara tsakanin mutanen palon banda AK da ko dagowa baiyiba bare ya kallesu
Kallon khadeeja Umma tayi sannan takalli asma'u tana so tayi magana amma takasa
Riko hannunta khadeeja tayi cikin rawar murya tace ammah meyake damunki ne ....Umma ...kike ..yima magana haka kai tsaye
juyowa asma'u saitin Umma amma kanta akasa dan takasa hada ido da ita cikin dakewa tace Umma wannan fa ba wani Abu bane kawai dukiyar na mallaka amma kuma ni bance zan koresu daga gidan ba kawai dai.....
Hannu Umma tadaga zata mareta khadeeja ta rikota tana fadin a'a Umma kibarta kawai ni na tabbata akwai abunda yake damunta amma ko za'a akasheni bazan yarda cikin hayyacinta take ba something is wrong with her
Nuna ta Umma tayi da yatsa cikin kakkausar murya tace to wallahi bari kiji idan ma hauka kike ko kwaya kika sha to kisani ni nafi karfin ki tozartani nabaki nan da gobe ki mayar masa da dukiyarsa inba haka ba kuwa sedai kinemi wata uwar ba niba .....
tana kainan ta juya afusace tafita daga gidan khadeeja nabiye da ita
juyawa asma'u tayi aguje ta koma bangarensu tana shiga ta turo kofar hade da sulalewa awurin tafashe da wani irin kuka mai ban tausayi kuka take sosai har nunfashinta nadaukewa seda tayi mai isarta sannan ta tashi tana dafe kai ta wuce daki jacket dinta ta cire tarike ahannu ta tsaya gaban dressing mirror tana karema kanta kallo wasu sababbin hawaye nazubowa daga idonta tajima atsaye kafin ta wuce bathroom tayo alwala tazo ta zunbula hijabinta tayi sallah tajima azaune tana adduo'inta kafin ta tashi takoma kan gado tazauna tafara aiki a laptop dinta
bayan fitar Umma uncle jamilu ya mike afusace yanufi bangarensa sadiya da aysha sukabi bayansa
Daga nan kowa ya watse jiki asanyaye wasu kuma naji kamar su mutu dan bakin ciki
AK natashi wurin ahmad yanufa ya zayyane masa duk abunda yafaru
Dafari bai yardaba seda AK yanuna masa takardun sannan ya tabbatar cewa dagaskene cike da mamaki yace ammah har yanzu abun yana dauremun kai I mean...... why will she do that ?
ajiyar zuciya AK yasauke yana kuantar da Kansa kan kujere yace bansan meyasa tayi hakan ba amma I am sure she is hiding something tabbas ba banza ba chitti bazata taba yaudarar wani bama bare ni kawai dai dalilinta nayin hakan ne bansaniba
"To yanzu miye abun yi
"Ba wani abunyi ahmad ko ina akaje tafimu gaskiya saboda akwai sa hannuna akan takardun so banida ikon dazan kwato dukiyata amma abunda yafi bani haushi shine gaba daya komai yakoma kan sunanta hatta kudina na bank da da komai nawa ya daina aiki lokaci guda tamaidani fakiri wallahi yanzu dubu dari kawai nake magani itama a ranar da ta tafi nacirota zan yi wani Abu da ita namanta
Tagumi ahmad yayi cike da al'ajabi yana nazarin wannan al'amari amma shi kanshi bai yarda cewa asma'u zatayi haka ba yana zargin akwai abunda take boyewa ba banza ba
Tashi AK yayi yanufi hanyar fita yana fadin muje muyi sallah daga can muje wurin su Umma mudubata I know she must be worried
awurin Umma suka wuni ranan suna kuantar mata da hankali sannan suka tabbatar mata da cewa akwai dalilin dayasa asma'u ta kwace dukiyar AK ba banza ba kawai dai subita ayanda tazo asannu zasu gane dalilinta nayin hakan
[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: AK yana zaune office din ahmad kamar kullum wayarsa ce ahannunsa yana dannawa
tsaki ahmad yayi cike da takaici yace
Friend wai meke damunka ne kwana biyu gaba daya kacanza kafita hayyacinka bakada aiki sedanna waya sekace wani bakauye
Baidago ya kallesa ba bare yasa ran zai tankasa
Karasowa yayi wurinsa yazauna cikin sassanyar murya yace
Base kafada ni nasan akwai abunda yake damunka idan kana ganin bai zama dole nasani ba fine u can keep it to ur self amma dan allah karage wannan damuwar tana damuna
murmushi yayi yana ci gaba da kallon wayarsa bai ce komai
Dafe kai ahmad yayi yana salati sannan yadago yana fadin wai dan asma'u tace tana sonka ne kake wannan abun
Girgiza kai yayi har yanzu dai yana kallon wayarsa se murmushinsa da yakaru har ana ganin fararan hakoransa
Cike da takaici ahmad ya kwace wayar yana fadin wai uban me kake kallo awayar nan ne dayake......
Cak ya tsayada maganarsa yana kallon photon asma'u dake kan screen din wayar da alama bacci ma take yadauketa photon yayi kyew sosai ga Zara zarn eyelashes dinta dasuka kwanta da dan karamin lips dinta da yayi kamar tasa pink lipstick kanta ba dan kwali gashinta duk ya bazu akan pilo sauran kuma akan fuskarta
Juyowa ahmad yayi da mamaki yana kallonsa baki bude yama kasa magana
Se can yayi yar dariya mai sauti cike dafarin ciki yace ohh my god friend are u in love ?
Hannunsa yasa yadan daki goshinsa kadan yana fadin I was so stupid ya akayi nakasa gane halin da kake ciki tun tuni
hannu AK yamika mai batare dayace komai ba ahmad yabasa wayarsa yana fadin friend kace wani Abu mana ur silent is killing me
tashi yayi yafita daga office din yana rike dawayarsa gam ahannunsa baiko kalli ahmad ba bare yayi magana
Da kallo ahmad yabisa rike da baki yace ohhh ikon allah kaikuma haka soyayyar tazo maka ni har ma kabani tausayi
komawa yayi yazauna kan kujerarsa yana Neman numban khadeeja dan yamata albishir
tafiya asma'u keyi akan hanya tana rangaji da kyar take daga kafarta hawayenta kuma har basa bare tana ganin hanya da kyew bata damu da sharesu ba dan gaba daya jikinta ya mutu lokaci guda maganganun da taji suna dawomata
ahankali ta furta meyasa ....meyasa
Sukeso suga bayansa bayan bayada wani buri da yawuce ya kyewtata musu duk wahalar dayake saboda su yakeyi baya samun isashshen bacci baya samun hutu baidamu da duk wani jin dadi irin namasu kudi ba kawai saboda baya iya yin komai se tare dasu amma burinsu shine sumallake abunda yasha wahala da guminsa yatara why....why...takarashe maganar tana durkushewa awurin hade dasakin wani kuka mai cin rai bata damu da mutanen dake kallonta ba dan ita kadai tasan halin da take ciki
Cikin kukan take fadin ina bazai yiwu ba bazan taba bari su cutar dakai ba se inda karfina ya kare I will fight for u ABI that's my promise
amma taya tana ina zan fara ko zan mutu ina rantsuwa ABI bazaka yarda da abunda zan fada ba ....
kanta takai kasa tana kankame jikinta cikin kuka tace ya allah kataimakeni I am helpless😭
bayan AK yadawo gida da yamma bangaren grany yawuce yagaidata se dube dube yake ta inda zai hango asma'u amma bai ganta ba hakanan yatashi yanufi bangarensu dan yasan tana can
Seda yafara leka dakin aysha ya iskota zaune da sarah suna fira daga bakin kofar suka gaisa ya wuce bangarensa
Murmushi sarah tayi tana kallon aysha tace sister wai miye sirrine naga kuana iyu Yaya yadamu dake ba kamar da ba
Dariya tayi suna tafa hannu tace ba wani sirri kinsan ance true love never end
Yana isa bangarensu yatura kofar yashiga da sallama sedai wayam ba kowa daki yawuce nan ma bakowa ahankali ya tura kofar dressing room har bathroom nan ma bakowa
Jiki asanyaye yadawo yazauna yana cire agogonsa duk se yaji baiji dadin rashin ganinta ba wayarsa yadauka kamar ya kirata se kuma ya ijiye yana fadin control ur self man kansa yadafe da hannu biyu yana cukurkuda gashinsa yace wai meyake damuna ne
wasa wasa har dare asma'u bata dawo ba tun yana hakuri har yagaji yakira wayanta amma akashe wayan khadeeja yakira tace yau Sam ma bataje gidan ba
Wurin grany yanufa itama tace bata San inda tajeba nan fa aka fara nemanta sama da kasa amma ba ita ba labarinta
Nan take gida yadauka ba asma'u yar karamar hauka AK yayi dan yarasa ta inda zai fara se safa da marwa yake yana neman numbanta amma baya shiga police station yaso yaje grany tace yayi hakuri har zuwa safe suga idan ba'aganta ba
cikin Daren ya kira ahmad suka fita nemanta se yawo suke sun rasa ta ina zasu fara nemanta
Haka ma khadeeja da fa'iz duk inda sukasan tana zuwa sunje amma ba'aganta ba
Har dare yaraba suna yawo amota da kyar ahmad ya lallashesa akan sukoma gida gobe dasafe sucigaba da nemanta
Badan yaso ba haka ya hakura suka kama hanyar gida
akan hanyarsu sukaga mutane sun taru ana kallon wani Abu
Tabo ahmad yayi yana fadin dakata friend bari muduba nan muga
Baijira amsa ba kawai yabude motar yafita cikin sauri yakarasa wurin mutanen yana tambayar meyafaru
Cike da tausayi wani mutum yace
Allah sarki wata yarinya ce mota takade yanzu suka nufi asibiti amma yarinyar kam gaskiya bance akwai sauran nunfashi atare da ita ba ....
Baijira yaji karshen maganar ba ya kutsa ta cikin mutanen yashiga ahmad nabinsa abaya
Jini malala awurin kai daga ganin jinin kasan da kyar yarinyar zata rayu
Nan take jikinsa yahau rawa durkushew yayi akan guywowinsa yana jiyo maganar mutanen wurin sama sama saboda tuni jiri yafara dibarsa baki bude yake kallon jinin
Ahankali yakai hannunsa yatabo jinin yana kallo lokaci guda wasu hawaye masu zafi suka ziraro akan kuncinsa
Dafa kafadansa ahmad yayi shikansa yakasa danne tashin hankalinsa cikin sassanyar murya yace AK control ur self ba lalle ne ya kasance asma'u ce tayi hatsarin ba
Dagowa yayi yana kallon ahmad da jayayen idanuwansa cikin rawar murya yace are.....are u sure ?
Shiru ahmad yayi yana kauda kai dan baisan mezai cemasa ba
Sun jima ahaka kafin da kyar ahmad ya dagosa yana fadin friend let's go home
Bin bayansa yayi suka tafi batare dayace komai ba amma har sukayi nisa yana waigen jinin dake kasa
Ahmad nagaba yana tafiya jiki asanyaye yana boye hawayen fuskarsa dan ba karamin tausayi AK yabasa ba fatansa daya allah yasa ba asma'u bace tayi hatsarin dan kwa in itace to gaskiya sedai suce allah yajikanta
Yana cikin wannan tunanin kawai yaji karan faduwan Abu abayansa saurin juyowa yayi dan ganin komiye
AK yagani akwance kamar gawa dagudu yakarasa wajansa yana kiran sunansa da karfi har saida mutane suka juyo
Durkusawa yayi kusa dashi yadagosa yana fadin heyyyyy friend....wake up miye haka .....katashi mana
Bubbuga gefen fuskansa yafarayi yana kiran sunansa dakarfi amma shiru cikin mutanen wurin ne akasamu Wanda suka taimaka masa yasaka sa amota se asibiti
Suna isa aka wuce emergency dashi har lokacin ba alaman nunfashi atare dashi
Nan take ahmad yakira gida yasanar dasu kan kace me har asibitin tacika da yan gida harda su Umma
Kuka inna take kamar karamar yarinya tana fadin bayin allah abun tausayi duka duka yaushe suka fita daga wata wahalar yanzu kuma ga wata shi wannan akwance ita waccan allah kadai yasan inda take
Ansha wahala kafin da taimakon allah aka shawo kan matsalar
Bayan anakaisa dakin hutu doctor yasanardasu cewa damuwa ce tamai yawa nan kowa yafara tofa albarkacin bakinsa kan canzawar AK cikin kuana biyu
bashi yafarka ba se dasafe bayan sallar asuba ahmad ne kawai zaune kusa dashi dan ba abarin mutun sama da daya sushiga in percent yana bacci
ahankali yabude idanuwansa yana bin dakin da kallo har yazo kan ahmad da yake faman jera mai sannu
Lumshe idanuwansa Lokaci guda yana tuna duk abunda yafaru
Saurin dago hannunsa yayi yana kallon jinin daya bushe akan yatsunsa
juyowa yayi yana kallon ahmad cikin dasashshiyar murya yace har yanzu batazo ba
Sunkuy dakai ahmad yayi yakasa cewa komai
"Kun gayamata cewa banada lafiya ...?
kagaymata cewa idan maganar da banayine yasa ta tafi to nadaina zan dawo yanda nake zan fara magana kamar da zan tsokaneta zan mata fira amma bazan iya rayuwa batare da ita ba tayi hakuri tadawo
tasowa ahmad yayi yazauna kusa dashi yana boye hawayen fuskarsa yace friend asma'u tana nan daranta ba abunda yasameta ba ita bace wannan yarinyar kadaina damun kanka kana bukatar Hutu
Riko hannun ahmad yayi yana fadin to idan ba ita bace tana ina meyasa har yanzu bata zoba duk lokacinda nashiga matsala she is always there for me to yanzu ya akayi ban ganta ba
kagayamata tazo kaji tell her that I am really sorry I feel lonely without her by my side
Tashi ahmad yayi yafita daga dakin yana share kwalla dan bazai iya juran ganin abokinsa ahaka ba
ta wurinsu grany ya wuce amma baice musu komai ba bin bayansa khadeeja tayi tana kiran sunansa
Saurin mikewa sukayi gaba daya suka shiga dakin
binsu yake da kallo daya bayan daya har yazo kan Umma sannan yasakemata lallausan murmushi yana mata alama da tazo
Karasawa tayi wurinsa tana sharan kwalla tace sannu abid
Riko hannunta yayi yana murmushi yace hmmm Umma kinsan me ?
Girgiza kai tayi wasu hawayen nakara gangarowa
Cije lebe yayi yana runtse ido yace ur daughter was a little disturbed
taga mun damu da ita shiyasa take bamu wahala ko
Daga mishi kai tayi bakinta narawa takasa cewa komai
Murmushi seda hakoransa suka fito lokaci guda hawaye na gangarowa daga idonsa cikin rawar murya yace ance uwa tana ji ajikinta idan wani Abu yasami yarta now tell me is she ok ?
Kwace hannunta tayi tafita daga dakin tana fashewa da kuka
Karasowa wurinsa grany tayi tana shafa kansa tace Abidi kazama jarumi mana idan kai kana haka mu kuma matan yazamuyi ka kuantar da hankalinka ba abunda yasameta kaji insha allahu za'aganta
Rungumesa sarah tayi tana gashewa da kuka dan ba karamin tausayi yabata ba
Hannunsa yakai yana shafa kanta se alokacin yagane halin da tashiga lokacinda tarasa ahmad baiga laifinta ba dan koshi yanzu ji yake ba abunda bazai iyaba indai asma'u zata dawo
Kuanan su biyu a asibiti aka sallamesu har lokacin AK baidawo hayyacinsa ba gaba daya yazama kamar mai tabin hankali maganganunsa kadai sun isa Susa mutun zubar da kwalla
Har wannan lokacin ba asma'u ba labarinta ahmad kullun yana zarya police station amma bawani labari mai dadi se antsinci gawar wata ansamu wata tayi accident ansamu wacce aka ma fyade har bayason zuwa dan kullun yaje se ranshi yabace
Kuance yake akan gado gefen da asma'u ke kuanciya idonsa alumshe kamar mai bacci amma yayi zurfi cikin tunani
Ahmad ne yashigo rike bowl din fruit salad aciki dan seda dubara yake cin abinci
Kusa dashi yazauna yana fadin Mr Romeo dan tashi kaci wannan mana
Banza yayi dashi yana gyara kuanciyarsa yabashi baya
Shiru yayi nadan lokaci sannan yace da wane suna ma asma'u ke kiranka .......miye ma
Murmushi AK yayi batare da ya juyo ba yace ABI
Dariya ahmad yayi yace ehhh haka fa ABI to ABI wannan fruit salad din ranar da asma'u zata tafi tayishi tasa a frig saboda tasan zaka bukace shi
Tashi yayi yafita yana fadin gashinan idan baza kaci ba zan turo nura ya dauka
Yana ganin ya fita ya tashi zaune yana murmushi yadauki bowl din yafara sha harda lumshe ido
haka dai yacigaba da jinyar zuciyarsa shi kadai yasan halin da yake ciki lokaci guda ya rame gaba daya yafita hayyacinsa ba inda yakezuwa daga bangaren grany se wurin Umma kullun firarsa bata wuce ta asma'u shiyasa yakeson zama da khadeeja dan tayita bashi labarin rayuwarsu shikuma yana dariya
kullun da tunaninta yake kuana yake wuni idan abun ya isheshi sedai ya shige daki yarungume kayanta yayita rusa kuka se yayi mai isarsa dan kanshi ya hakura wayarsa kuma sallace kawai kerabasu kullun tana hannunsa yana kallon photon asma'u
Zaune suke da ahmad apalo yana tayasa cin abinci
Cike da tausayi ahmad ke kallonsa yace AK kasan kana son asma'u meyasa baka gayamata ba
Murmushin dayafi kuka ciwo yayi yana hadiye lomar da kyar yace
nadamar danake ako dayaushe kenan nayanke shawar gayamata amma inaso in mata surprise in shirya komai yanda zai tsaya akwakwalwarta har karshen rayuwarta naso najiyamata dadin dako wace ya'mace keburin samu agidan mijinta
Ahmad bantaba sanin cewa inason chitti ba seda tabarni bansan a ina take ba awane hali take amma jikina yana bani tana raye
Dafasa kafadansa ahmad yayi cikin sugar lallashi yace
Nima ina fatan haka amma kacigaba da hakuri kuma mudage da addu'ar allah ya bayyana mana ita
Share kwallansa yayi yace shiyasa akace idan kanason mutum kagayamasa maybe lokacinda zakaso yasani ko zaka shekara kana ihu bazai jikaba
Kawai sonake naganta koda so dayane nagayamata cewa ina sonta
Shiru ahmad yayi baice komai yana ni dayasan inda take dako birnin seen ne se yanemota kodan abokinsa yafita daga wannan halin
abubuwa dayawa sun canza gaba daya farin ciki ya kawaracewa gidajen biyu ahmad da khadeeja kuwa tuni sun ijiye zancan urensu gefe
Kasuwancin AK gaba daya yakoma baya saboda kokadan ba abunda yake kaishi office ahmad kuma shikadai abun yamasa shima yana kokarin bude nasa companyn a Lagos so baicika zama ba kullun yana zirga zirga ga damuwar halin da AK keciki ko yana gari to kullun suna tare da AK
Su uncle jamilu sun samu abunda sukeso se yayi Kane Kane a company wadaka suke da dukiya son ransu
Aysha kuma tana nan tana renon cikinta tana jira lokaci yayi dazata fara aikinta
sarah ma gaba daya jikinta yayi sanyi da yanayin da yayanta yake ciki ko baifada mata ba yanzu tasan yana son asma'u shi yasa take tausayamasa dan tasan irin wannan yanayin narasa Wanda kakeso
Su Umma da grany kuma tun suna kuka har sun gaji sun fawwala wa allah komai amma kowane dare na allah se Umma tayi kukan rashin sanin halin da yarta take ciki
Khadeeja ma juriya kawai take amma gaba daya ta canza duk wannan rahar da masifar tata duk tadaina tadawo so silent karatu kawai sukasa agaba itada fa'iz sedai ko a aji ta tuna asma'u sedai kawai aga tana rusa kuka sedai tafita waje tayi mai isarta ta hakura tun fa'iz natayata har yagaji sedai ya lallasheta
💔💔🕐🕒🕓🕕🕖🕗🕘🕙🕚🕛💔💔
*Bayan wata daya....!!!*
wata safiyar lahadi misalin karfe 9 ruwan sama ya sauka gari yayi sanyi ga wani daddadan iska dake kadawa mai dauke da kamshin damuna
AK nazaune agarden ya harde hannaye yana kallon fararen tantabaru dake zagaye dashi kamar zasu hau jikinsa saboda sabon dasukayi dashi cikin wata daya kullun awurinsu yake wuni sallace kawai kefitar dashi se bacci
daidai wannan lokacin wata arniyar mota ash color kiran BMW sabuwa gal tayi parking aharabar gidan
Bakin glass din motar shi yahana agane Wanda keciki
gaba daya ma'aikatan gidan sunyi cirko cirko suna kallon motar baki bude sunkosa suga waye aciki
motar takai kusan minti goma da tsayuwa amma bawanda yafito daga ciki
Ahankali aka turo murfin motar kusan minti biyar tadauka kafin tafito daga motar tana tura murfin dakafarta tarufe motar sannan ta gyara tsayuwarta tana bin gidan da kallo
[19/07, 17:05] Hubbey Frd Ameena Kn: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣6⃣0⃣
cikin sanda tashigo bangaren grany tana leken palon ganin grany ne ce kadai azaune yasa ahankali takarasa cikin palon tayi tsaye daga nesa tana kallon grany idonta pal kwalla
Dagowa grany tayi tana kallonta nadan lokaci sannan............. tasaki wani lallausan murmushi tana fadin karaso mana asma'u
saurin karasawa tayi tafada jikin grany tana fashewa da wani irin kuka mai cin rai
Shafa kanta grany tayi cikin sigar lallashi tace a'a asma'u miye kuma na kuka ai ba haka mukayi da keba
Cikin muryan kuka tace grany bazan iya ci gaba da wannan aikin ba bazan iya jurar ganin ABI awannan halin ba kuma fa kinji me Umma tace wai sedai in nemi wata uwar ba ita ba
Katseta grany tayi dafadin zaki iya asma'u tunda fari nasan zaki iya shiyasa nasakaki kimanta da Abidi nasan shi yanada juriya da tawakkali ba abunda zai sameshi kuma naga alama bai yarda cewa yaudararsa kikayi ba ita kuma ummanki ranta ne yabace amma ba abunda zata miki kici gaba da aikinki wata rana dakanta zata yi alfahari dake
Shiru tayi tana share hawayenta sannan tadago tana kallon grany tace kin lura da uncle jamilu dazu kinga yanda yake subutar baki
Tabe baki grany tayi tace hmm bari kedai ai tun da kika shigo nakafesu da ido se alokacin nakara yarda da abunda kika fada mun godema allah dakika jiyo zancansu dasedai muje mu asalansa
Dariya asma'u tayi tace amma grany kince in nazo zaki bani labarin yanda ABI da bana nan
Dariya grany tayi har tafa hannu tace kedai bari asma'u ai ni naga ikon allah ke mutuminki Ashe yana sone yana kai kasuwa bawan allah da kinganshi lokacin se kin tausayamai
Fuskar tausayi asma'u tayi tace gashi naga duk yarame kamar ba shiba
"hmmm ba kin dawoba ai yanzu zai maida kibansa amma gaskiya kinyi kokari da inata tsoron kar aje kikasa yin abunda muka tsara shirinmu ya lalace
"Grany ai ba karamar dakewa nayi ba kafin nayi wannan acting din bama danaga Umma ji nayi kamar inzo dagudu in rungumeta
Kallon kofar dakin inna ameena grany tayi sannan tace ai gara da kika dake kinga daganan mutananki zasu fara shakkar ki dan na hango tsoro karara afuskarsu
Shuru tayi nadan lokaci sannan tace yanzu gobe insha allahu zan fara zuwa office nasan ansamu canji sosai kasancewar ABI da Ahmad basa zama kuana biyu duk yanda ake ciki idan nadawo zan sanardake
shuru sukayi nadan lokaci sannan grany tadago tana dariya tace yi fa hakuri dazu nawankeki da mari
Itama dariya tayi tana shafa kuncinta tace ba komai ai duk cikin aikin ne sannan ta tashi zaune tana riko hannun grany tace amma gaskiya dazafi nan gaba inzaki mareni kidan min signal dan nashirya dan gaskiya na tsorata dazu
Dariya suka sa gaba daya daidai lokacin inna ameena ta turo kofar dakinta tafito
Grany na ganinta tayi saurin kwace hannunta cikin kakkausar murya tace eh anmareki din ko zuwa kikayi kirama ne
alama tama asma'u da ido sannan taci gaba da fadin tanbayar ki nake ko zaki rama ne
tashi tsaye asma'u tayi tana kallon grany fuska adaure tace ba ramawa nazo yiba zuwa nayi inmaki kashedin kar ki kara kai hannunki jikina da nufin marina namaki hakurin nayau saboda rashin sani amma nan gaba kika sake banajin zan iya kyaleki
Tana kainan ta juya tafita ko kallon inna ameena batayi ba bare tasan taganta
Saurin karasowa inna ameena tayi cikin palon tana fadin nashiga uku ni ameenatu wai kenan dai dagaske yarinyar nan take tazama mara mutunci
tsaki grany tayi tana kauda kai kamar dagaske tace nayi nadamar aura ma abidi yarinyar nan ina tunanin namishi zabi na kwarai ashe na dauko abun zai cutar damune ......takarashe maganar tana sharan kwalla
Dafata inna ameena tayi cike da tausayi tafara lallashinta
ahankali ta tura kofar dakinsu tashiga tsaye tayi tana kallon AK dake kuance kan gado idonsa alumshe kamar mai bacci
Dagowa yayi yana kallonta nadan lokaci sannan ya gyara kuanciyarsa ya juya mata baya
kallonsa taci gaba dayi hawaye masu zafi na tsere akan kuncinta
Jin kamar ana kallonsa yasa ya juyo ahankali yana kallonta saurin kauda kai tayi tawuce dressing room
can anjima tafito sanye da kayan baccinta riga da wando takwanta agefen datake kwanciya da
yana jin ta kwanta yamike tsaye hade da daukan pilo yabar dakin
Da kallo tabisa har yafita sannan tarungume pilo tana fashewa da kuka mai ban tausayi har bacci yadauketa
washegari dasafe tana cikin dressing room tana saka kayanta a drowanta AK ya fito daga bathroom daga shi sai towel aqugunsa suna hada ido yayi saurin juyawa yakoma ciki yana fadin what are u doing here
Ci gaba da aikinta tayi tana fadin meye kuma zaka wani juya bayan kasha cire kaya agabana
daga cikin bayin yace daba ni agaban chitti nake cire kaya bakeba lady boss
Rigarsa tamika mishi tana fadin fito kabani waje wanka zanyi kar namakara
Kwace rigarsa yayi ahannunta yana fadin karki kara tabamun kayana with ur dirty hands
juyawa tayi tafara Ciro dogayen rigunanta daga drawer tana sasu adayan drowar
Saurin saka rigarsa yayi yafito yana fadin ke wai mezakiyi
Bata kallesa ba tace wai meyasa kakeson shiga abunda bai shafeka bane kayana zan saka awurin
Janyeta yayi daga wurin yana maida kayan cikin drowa yace kinemi inda zakisa fitsararrun kayanki nan drowar chitti ne dan haka baki isa kicire mata kayanta aciki ba kuma I can't share my closet with u
Se alokacin tadago tana kallonsa da murmushi tace karfa kamanta nan gidana ne inada damar dazan ijiye kayana aduk inda nakeso
lokaci guda fuskarsa ta canza yana kallonta ko kiftawa ba yayi yajima ahaka sannan yariko kafadunta dakarfi cikin wata iriyar murya yace bansan meyasa kika yi hakan ba amma kisani ko kadan hakan bai bata min rai ba abunda yafiyi mani zafi shine karyar dakika mun cewa kina sona idan kudi kikeso ko nawa kika tambayeni ni mai iya bakine saboda kinfimun komai arayuwata ada amma ayanzu bakida wata kima a idona u can do what ever u wont with my money amma kisani ina nan dake sena kwato dukiyata ahannunki nan bada jimawa ba....yana kainan yasaketa yana daukan kayansa a drawer ya wuce daki
Durkushewa tayi awurin tana toshe bakinta dan kar kukan ya fita seda tayi mai isarta ganin lokaci yana tafiya yasa ta wuce bayi tayi wanka sannan ta dawo dressing room ta shirya cikin wasu riga da wandon bakake sannan tadoro jacket irin tajiya ruwan toka tayi rolling da karamin gyale shima ruwan toka se takalmin kafarta kalan gyalen tayi kyew matuka kamar bala rabiya tana fitowa AK yabita da kallo tundaga sama har kasa aransa yana fadin wai dama haka chitti tahadu bansaniba ganin tana kallona yasa yayi saurin kauda kai yana daure fuska
Dressing mirror tanufa tafeshe jikinta da turare sannan tazana light make up shap shap tagama tadauki jakarta sauri sauri tanufi hanyar fita tana duban agogon hannunta
dakallo yabita har tafita sannan yaci gaba da abunda yake yana fadin zamuga yanda zakiyi aikin yarinya tunda angayamaki make up ne dazaki iya koyanshi cikin wata daya
tana sakkowa kasa ta isko gaba daya mutanen gidan azaune apalo ana jajanta abunda yafaru jiya harda grany acikinsu
tana sakkowa suka hau daure fuska suna tabe baki
Ko kallonsu batayi ba tahau kwalama masu aiki kira dagudu suka karaso wurinta suna mika gaisuwa
kallonsu tayi dayan bayan daya sannan tace
Bakomai yasa nakiraku ba sedan insanardaku cewa daga yau aikinku ya kare anan gidan mungode da zaman mutuncin da mukayi da Ku abaya amma ayanzu bama bukatar yan aiki anan gidan
Dafe kirji dattijiwar cikinsu tayi tana langwabar dakai kamar zatayi kuka tace madam meyafaru idan wani laifi mukayi amana hakuri zamu gyara amma wannan aikin dashi muka dogara dan allah ataimaka
Murmushi tayi tana dafa kafadarta tace ba kuyi komai ba baba kawai dai lokaci ne dayakamata ace kuma kun huta
Check taciro acikin Jakarta ta bisu daya bayan daya ta mikamusu tana fadin ga wannan ya isheku Ku kama kowace irin Sana'a kukeso se kuje kuyi allah yabada sa'a sannan idan kuna bukatar wani taimako awurina to zaku iya zuwa kusameni akowane lokaci
washe baki suka hau yi cike dafarin ciki suna mata godiya
Mikewa mutanen gidan sukayi cike da mamki suna kallonta cikin daga murya inna ladidi tace to yanzu da kika kuresu uban wa zaiyi aikin gidan
Karasowa tayi dap da ita tana murmushi cikin sassanyar murya tace nanfa gidana ne ni nakeda ikon sawa ayi ko abari acikinsa ina ganin girmanki dan haka kija bakinki kiyi shiru
Juyowa tayi takalli aunty sadiya sannan tamaida kallonta kan inna ladidi tana fadin bakuyi tsofan dayakama ace kun daina aikin komai ba saboda haka kuzaku kula da tsabatce gidannan ciki da wajansa
Dariya akasa gaba daya palon ana kallonta dan su kallon mai tabin hankali suke mata
Itama murmushi tayi tana kallonsu sannan takarasa wurin aysha da sarah tana kallonsu tace munada tika tikan yan mata kamarku bama bukatar masu girki saboda haka daga yanzu kuzaku rika yin girkin safe da yamma saboda yanda kuke dayawa bazan iya cidaku so uku arana ba
Kallon juna sukayi sannan suka kalleta suna kwashewa da dariya
Banza tayi dasu tana kallon grany tace ke kuma grany.....
Bata karasaba inna ameena takatseta da fadin ita kuma me rashin imanin naki har yakai ki kalli girmanta kice zaki sakata aiki
Murmushi tayi tana kallonta tace to ai bakijira kinji mezan ceba ....
kallon grany tayi taci gaba dafadin dake da inna ameena zaku kula da bangarenku idan taga zata iya setayi gaba daya ke kuma ki huta amma yakamata ace kinadan aiki saboda motsa jiki yanada kyew
Wani dogon tsaki uncle jamilu yaja yana gyara zamansa kan kujera
Juyowa tayi tana kallonsa tace ohh uncle ashe kana nan nibanma ganka ba ai se yanzu
Kallon bashir tayi sannan tamaida kallonta kan jamilu tace uncle kaida bashir kuna wasa da aikinku sosai yanzu karfe Tara amma banga kunada niyyar zuwa office ba
Kallon agogon hannunta tayi sannan takallesu tace yanzu zan wuce office idan har narigaku zuwa to wallahi kunji narantse zan sallameku a aiki
Zaro ido sukayi suna kallonta amma basuga alaman wasa a tattare da ita ba
Juyawa tayi zata fita sukayi saurin mikewa atare suka wuceta har zasu fita tace yawwa bashir zonan dawowa yayi ya tsaya agabanta yakosa tafadi abunda zata fada ya taxi dan uncle jamilu tuni yafita
Makullin motarsa takarba tana fadin a wuri daya kuke aiki banga dalilin dazaisa Ku dauki motoci biyu kufita dasuba
Zaiyi magana tadaure fuska tana fadin nakune ?
Girgiza kai yayi yana fadin a'a nakine
baijira mezata ceba yafita aguje ya isko uncle jamilu har zai tada mota yabude gidan gaba yashiga
Juyowa yayi yana kallonsa fuska ahade cikin kakkausar murya yace kai miye haka
janyo sit belt yayi yadaura yana fadin kai dai uncle muje kawai zamma bayani ahanya
tsaki yayi yatada motar suka fita aguje kamar masu shirin barin garin
wayar Asma'u ce tayi ringing tana dagawa tace kazo ....to kashigo kawai
Dariya aysha tayi suka tafa da sarah tana fadin yau ni ke kallon film ganin idona
Dariya sarah tayi tace jifa wai mune zamuyi aiki base taganmu bama bare mu mata girki
Murmushin mugunta asma'u tayi tana kallon kofa tace gali shigo mana
😳😳😳😳😳
zaro ido sukayi atare suna kallon Wanda yashigo palon cikin shiga ta rashin mutunci kana ganinsa kaga dan kwaya ga idonnan yakade yayi ja fuska ahade ba alamar far'a ko wasa atare dashi
Cike da isa ya karaso palon kanshi Asama yana bin ko ina da kallo
Murmushi asma'u tayi tana kallon su sarah tace wannan shine zai rika kula da aikinku idan bakuyiba dan allah to zakuyi dan wuya
juyowa tayi tana kallon gali tace gali katabbatar komai yatafi daidai duk wacce tama rashin kunya acikinsu kanada damar hukunta ta wacce taga bazata iya ba kuma zata iya tafiya ba dole
dariyar mugunta yayi yana binsu da kallo yace angama hajiya nayi na banza ma bare inda za'a biyani ai karki damu kije kawai
Murmushi tayi tafita daga palon dagudu gudu tashiga motarta tafigeta aguje tafita daga gidan
ahanya bashir se ihu yakema uncle jamilu kan baya gudu tukin ma ashe bai iya ba
Sunzo daidai traffic light uncle jamilu ya juyo cike da takaici Kai kafa isheni fa dan ubanka wayace kabata makullin motarka idan kaga bazaka iya ba kafitarmun amota inyaso ni innaje inga inta isa takoreni aikin banza kai
Kauda kai bashir yayi yana zunbura baki bai kara magana ba har suka isa
suna fitowa daga motarsu motar asma'u tashigo companyn kusan tasu tayi parking tana fitowa takallesu tana murmushin gefe tace allah yaaa taimakeku
Tagefensu tawuce tana maida glasses dinta tasa kai cikin company
Da kallo bashir yabita har tayi nisa sannan ya jinginu da mota yana sauke ajiyar zuciya yace ohhh thank God
Wani banzan kallo uncle jamilu ya watsamai sannan ya wuce ciki yana Jan tsaki
[20/07, 18:48] Hassan Atk: Da daddare asma'u nadaki kan kujerar dake gefen gadonsu tana aiki a computer
AK yashigo dakin yana satar kallonta ya nufi kan gado ya kwanta
Har yarufa ya hango coffee dinsa dake kan bedside drawer
Kallon asma'u yayi aransa yana fadin grany batada lafiya kenan ita tayi wanann coffee din
tashi zaune yayi yajanyo flax din ya zuba a mug sannan ya gyara zamansa yana Satan kallonta yaga ko dagowa ma batayi barema tagansa
Kurban coffee din yayi ya furzar yana yamutsa fuska yace
Wannan wane kalan coffee ne...... koma waye ya hada bai iyaba .....kuma kar yakara hadamun dan ba kowane kalan kazanta nakesha ba
dagowa tayi takallesa sannan sadda kanta tace kaga idan kana son kanka to karkayi wasa da coffee dinnan
ada sau uku kake sha arana yanzu kuma ni nake saya da kudina dan haka nayi niyyar baka so daya arana idan kazubar da wannan to kaida wani kuma se gobe warahaka now it's up to u
wani malalacin murmushi yayi yace haba ai wannan fada kawai kike dan bakinki yasha iska amma ai kema kinsan baki isa ki hanani shan coffee agidannan ba
Ci gaba da aikinta tayi tana fadin muzuba mugani inace kap makullan ahannuna suke ko..... to sedai kaje kasha awaje amma banawa ba ....ko kasiyo grany tahadamaka .....wannan duk bai dameni ba
Ni yanzu kaina kawai nasani duk abunda zan karu dashi shizanyi kowa kuma yaji da matsalarsa
"To meyasa dazu kika shiga damuwa da kika ga grany akuance
"Saboda nasan kudi zan kashe wurin sayan maganinta shiyasa amma ba wai ainahin rashin lafiyarta bane yadameni ko kai dakaga nadamu akanka ba tausayi kabani ba kawai dai rigakafi namaka dan naga alama kaima kana shirin jamun wani kashin kudinne....shi yasa nabaka ruwan sanyi dan kar jininka ya hau
Shiru yayi yana kallonta dan yanda tayi maganar ko kadan ba alamar wasa atare da ita
bayan kuana biyu......
Grany taji sauki amma har yanzu bata sakamar ma AK fuska kullun idan asma'u tadawo daga boye zataje ta dubata har Sudan yi fira
sosai aysha kesamun kulawa daga bangaren AK dan gaba daya hankalinsa yakoma kanta da abunda ke cikinta
yar dubu dari dinsa tuni aysha tagama cinyeta yadawo ba ko sisi hakan yasa yafara zuwa aiki tare da asma'u akan zata biyashi a kowace rana yayi aiki
Haka ta amince ta daukesa dan tasan saboda aysha yake Neman kudi kuma tanajin dadin aiki dashi sosai saboda yafita experience kuma yana bata shawarwari idan tabukaci hakan
a company kuma komai yana tafiya daidai aiki suke ba wasa asma'u takawo canji sosai a harkokinsu shi kanshi AK tana birgesa yanda yaga tana aikinta cikin natsuwa sodayawa yakan shagala wajan kallonta idan suna meeting kowani abun wani lokacin se antaboshi yake dawowa hayyacinsa
Kullun ahmad yana ba khadeeja labarin abunda yake faruwa harda cikin aysha seda yagayamata tana son zuwa wurin asma'u amma Umma tahanata sedai tayita rokon ahmad akan yakular mata da yayarta
abangaren asma'u kuwa Sam takasa yarda cewa cikin jikin aysha na AK ne dan haka tasamata ido sosai akan duk wani motsi nata
har wannan lokacin su Umma basusan abunda ke faruwa ba Sam asma'u bata zuwa gidan suma basa zuwa sedai kowane lokaci da tunaninsu aranta
uncle jamilu yasake yanata harkokinsa Sam yamanta da zancan kudin dazaibiya yana ganin ai tunda amma yarsa ciki komai ya wuce
ganin take takensa yasa asma'u ta kirasa awaya tana son ganinsa yazo office dinta
zaune yake akan kujera kansa akasa yana faman daure fuska
"Jamilu najika shiru ne inafata dai baka manta ba kuana biyu kawai yarage maka cikin lokacinda nabaka
Saurin dagowa yayi yana kallonta yace kamar ya ni bakiga abunda mijinki ya mun bane .....ko nine bansan ciwon kaina ba
Murmushin gefe tayi tana kallonsa tace wannan tsakaninku ne.... ni bai shafeni ba idan kaga dama kayi karansa ko kayi masa abunda yadace ba ruwana.... nidai kudina kawai nasani
Bakaramin tashin hankali yashiga ba ganin da gaske asma'u keyi tabbas zata yi karansa idan bai biya kudinnan ba shi kuma ko za'akasheshi baida ko kwandala kadararsa kuma koyasaida bazata wuce 1M ba ko kashi uku cikin kudinta basu kaiba
duk inda yake tunanin zaisamu kudin yanema amma ba wani labari mai dadi har wurin grany yaje tabashi rance sema tarufeshi da masifa tace abunda take jiyemasu kenan amma basa gani lokacinda AK kebasu kudi intayi magana se suga kamar bakin ciki take masu yanzu gashi da AK baida kudin gaba dayansu sunshiga matsala
Wurin aysha yazo yace taje wurin AK tace tana son kudi yasan duk inda suke zai nemo yabata
Zaune ta iskosa apalon kasa yana kallo kafin sutafi office
Kusanshi tazauna tana marairaicewa tace AK ......
bata karasaba yace menene .....
kauda kai tayi tace shikenan ma kawai nasan ko nafada ba bani zakayiba
"Kifada mana indai inada meyasa bazan baki ba
"Kudi nakeso akwai abunda zanyi
"to ai sekibari har indawo da yamma ko yanzu banada ko sisi
kukan shagwaba tafarayi tana buga kafa tace allah ni yanzu nakeso idan baka baniba kwa sedai inzubar da cikinnan tunda duk shi yakesa ina son abubuwa
Riko hannunta yayi cikin sigar lallashai yace cmon baby meyayi zafi nagayamaki kidaina cewa zaki zubar da cikinnan banaso badai kudi ba jirani ina zuwa
tashi yayi yanufi bangarensu ita kuma ta gyara zamanta tana binsa da kallo tace ai nasan bazaka rasa kudi ba
yana Shiga ya hadu da asma'u zata fito karo sukaci tayi saurin ja dabaya tana ina kuma zakaje muda zamu tafi yanzu
Wucewa yayi cikin daki yana fadin ba inda zanje yau kije kawai
Bin bayansa tayi har cikin dakin tana kallon agogo tace AK cmon yaufa munada meeting kuma lokaci yakure ka ijiye wannan rigimar taka idan mundawo sekayi
Kuantawa yayi kan gado yana kallonta yace nifa ba inda zaje hutawa zanyi ....dole ne se kinje dani da can dabana zuwa ya kikeyi
Juyawa tayi zata fita yayi saurin tashi zaune yana fadin zanje amma dasharadi
Juyowa tayi tana kallonsa tace me kenan..
"Zaki biyani kudin aikina na yau tun yanzu
wani malalacin murmushi tayi tace ...me kadaukeni ....ai ba haka mukayi da kai ba ....ni bazanyi cinikin kifi aruwa ba
Kuantawa yayi yaja bargo yana fadin to jiki Umma tagaida Aisha ....
Har tajuya zata tafi tasake dawowa wurinsa tana Jan bargon tace fine tashi naji zan biyaka amma se kagayamun mezakayi da kudin
tashi zaune yayi yana hada tafukan hannayansa wuri guda yace lady boss for God sake idan bazaki bani kudinnan ba kitafi kibarni inyi baccina wai ana dole ne
Jakanta ta ijiye kan kafafuwansa taciro kudi masu yawa tafara lissafo masa nasa sebin kudin yake da ido yana tayata lissafin har ta gama Tamika masa ya karba yana sakkowa daga kan gadon yafita cike da farin ciki
Binsa tayi da kallo tana murmushi sannan tadauki Jakarta tabi bayansa tana fadin wannan karfa ya gudu ina nan tsaye
Yana zuwa ya mikama aysha kudin yana murmushi kin karba tayi tana bin kudin da kallon raini sannan tadago tana kallonsa tace banganeba ......badai kana nufin iya kudin dazaka bani ba kenan ....ina maka maganar makudan kudi shine zaka ban wa'innan to inyi medasu
Kallonta yake cike da mamaki sanann yakalli kudin yana fadin wai da nawa kikeso to awurina aysha da dayanzu badaya bane kinga wannan kudin sune kawai mallakina anan gidan suma ko aikin banyiba tamkar bashi nadauko su kuma ke kanki shaidace
tashi tayi tana Jan tsaki ta wuce dakinta tabarshi atsaye rike da kudin juyowa yayi yaga asma'u atsaye tana kallonsa yayi saurin boye damuwarsa yana fadin miye kuma kinwani kafeni da ido ....lokaci guda kinjuyani daga attajiri nadawo faqiri .....go and celebrate
daure fuska tayi tanufi hanyar fita yabi bayanta yanaci gaba da masifarsa
Ganin lokaci natafiya kuma yarasa inda zai sami kudin yasa ya yanke wata shawara bari yayi anfani da sarah yasami kudin cikin sauki
Sarah nazaune Palo tare dasu grany wayarta yayi kara ganin sabuwar numba yasa taki dauka har saida aka sake kira sannan tadaga batare datayi magana ba
Daga dayan bangaren akace sannunki sarah aikinki na kyew kinacikin daula kina jin dadinki kinmanta cewa baki gama biyana kudina ba ko
cike da takaici tace ...bangane mai maganar ba waye
JJ .....akafada tadayan bangaren
Saurin mikewa tayi tamatsa daga gefe tana fadin lafiya zaka kirani kuma ni bansan kudin dakake magana akai ba saboda bakamun aikin da nasaka ba
Dariya yayi irin ta marasa mutunci sannan yace bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane .....dama nakiraki ne dan nagayamaki cewa... Nayi recoding duk wayar damukayi lokacinda kika bani aiki kuma ina tunanin lokaci yayi dayakamata AK ya saurari koda daya daga cikinsu ne
Saurin katseshi tayi dafadin no ....no JJ please don't this to me ....idan kudinka ne zanbiyaka amma dan allah kar kamun haka
Dariya yasake yi yace yawwa yar gari kinsan ance mutunci yafi kudi to bawasu kudi dayawa nake soba kawai dai 5M zan karba ahannunki dan indan rage zafi kuma nan da gobe nakesonsu inafata kingane
"What nonsense.... Wane kalan 5M haka mukayi dakai wannan ai shirmene
"Shekenan se nashigo anjima ....yafada yana kokarin katse kiran tayi saurin fadin a'a dakata JJ dan allah karkazo naji zan baka kudin but please Kadan karamun lokaci wallahi yanzu yayana bashida kudi
katse kiran yayi batare da yagama jin mezata fada ba cike dafarin ciki yace yes!!! ga hanya mafi sauki natsaya ina ba kaina wahala da tuntuni ma nasamu kudin
bin wayar tayi dakallo cike da tashin hankali tafara tunanin inda zata sami kudin
jin andafata tabaya yasa tayi saurin juyowa aysha tagani atsaye tana fadin lafiya dawa kike waya naganki atsorace
Kakalo murmushi tayi tana share zufan goshinta tace ba kowa wata friend dita ce
Kureta da ido aysha tayi tana fadin kawarki ce keneman 5M ahannunki ....sarah nifa kawarki ce muna gayawa juna sirrinmu kigayamun meyake damunki inga kozan iya taimakonki
Jan hannunta tayi suka nufi daki sannan tabata labarin abunda yafaru
Shiru aysha tayi tana tunanin tabbas babanta ne ke ma sarah barazana dan yasamu kudin ahnnunta amma bazata so sarah tasan hakan
Dago dakanta tayi tana kallonta da damuwa tace to yanzu sarah yazakiyi .....ko zaki je wurin AK kiga ko zaki samu
shiru sarah tayi batace komai ba dan tasan kana ganin AK kasan bai ijiye dubu 10 bama bare 5M
tashi tayi tafara safa da marwa adakin tana tunanin ta ina zata fara neman miliyan biyar kafin gobe da yamma
[20/07, 18:48] Hassan Atk: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣7⃣0⃣
tana shigowa kowa ya mike atsaye aka fara gaidata cike da girmamawa
Seda tazauna sannan kowa yazauna suka fara abunda ya tarasu
Sunkusan shafe awa 2 suna abu daya bayan daya take tuhumar kowanne akan wasa da aikinsu da kuma matsalar dahakan yajanyo wa harkan kasuwancin su
gaba dayansu kai yadau caji har ahmad bata ragama ba bare su uncle jamilu da kowa yatashi magana se yace laifinsa ne saboda shine mai kula da komai kasancewar AK da ahmad basa zuwa kuana biyu
Zuwa wannan lokacin ran asma'u yagama baci har wani ja idanuwanta sukayi jitake kamar tarufe uncle jamilu da duka dan takaici
shikuma ya takure wuri guda se zare ido yake banda kadawa ba abunda cikinshi keyi dan duk yanda yake kallon asma'u ashe tawuce tunaninsa dan gaba daya tambayoyinta sun gama ruda shi
juyowa tayi tana kallon daya daga cikinsu tace Mannir naga anciri wasu kudade masu yawa akan wai zaku dinka bedsheets wa sababbin collections din dazasu shigo .....
Kuma dazu danaje banga wata alama data nuna kuna sababbin dinkuna ba .....ko zaka iya gayamun inda kudin suka shiga
tunda tafara magana yake kallonta da mamaki har ta gama sannan yayi wata yar dariya me dan sauti yana fadin what....ma ni bansan da wannan zancan ba inba yanzu danaji kinfada ba ko lokacin AK yana nan bama fara dinki har sai kayan sun iso munduba sannan zamu San kalan dinkin dazamuyi
Runtse idanuwanta tayi tana kauda kai sannan tajuyo tana kallon jamilu tace jamilu .....
saurin dagowa yayi yana fadin ye....ye....yes ....ma
kureshi da ido ahmad yayi kamar yasani yajuyo suka hada ido ya zabgamai wata uwar harara bashiri yayi kasa da kansa yana kunshe dariyarsa
"jamilu naga sa hannunka akan wasu kayan da aka fitar se dai banga kudaden sun shigo ba ya akayi haka
Handkerchief ya zaro a aljihunsa yashiga goge zufar dake kan goshinsa yana kame kame irin namarasa gaskiya
tsawa ta daka masa tana dukan table din tace jamilu don't waste our time kagayamana ina kudin suka shiga
atsorace yadago yana kallonta cike da takaici jiyake da zai samu bindiga ba abunda zai hana ya bindigeta
lumshe ido tayi tana shafa goshinta cikin murya mai kaman rada tace jamilu ina kudin suke ......ko sun bata ne ....?
saurin gyada kai yayi yana fadin eh.....eh....bata sukayi ....ma
Kallonsa ahmad yayi yana kwashewa da dariya sauran ma suka tayasa dan yanda yayi maganar yabasu dariya
Ita kanta asma'u seda tadanyi murmushi sannan tadakatar dasu tana kallon ahmad tace
Ahmad tsawon wata biyu kenan ba ashigo da sababbin kaya ba inaso cikin satin nan kafito mana da zane .....kar kamanta satin nan nace
Murmushi yayi yace ok ma insha allah dama najima da farawa kawai dai ban karasaba ne
haka sukaci gaba da tattauna yanda zasu magance matsalolin da suka samu kuma sunji dadin yanda take Neman shawarar su akan komai sun yaba yanda takeda kaifin tunani da hangen nesa irin namanya shi kanshi Ahmad ta birgeshi yanda take aikinta cike da kwarewa
Koda suka gama meeting din ita tafara fita sannan kowa yafita suka koma bakin aiki se nuna uncle jamilu ake ana gulmarsa wasu kuma namasa dariya
yana ganin asma'u tashiga office dinta yabita ahasale ya banka kofar yashiga
Bata juyo takallesa ba tawuce direct kan kujerarta tazauna tana fadin shigo mana uncle dama nasan zakazo amma bandauka da wuri haka ba
karasowa yayi kusan table din yana huci yace ke ni zaki zubarma mutunci agaban mutane ....ko dan kinga ina ragamaki.... to bari kiji hawainiyarki ta kiyayi ramata tun muna mu biyu kidaina shigar mun hanci da kudunduni.....
wani malalacin murmushi tayi tana kirgiza kai tace borin kunyarne kazo zaka mun ....menayi maka nazubar da mutunci .....kawai dan na tuhumeka akan abunda kai kanka kasan cewa ka aikata shi ....kuma kamar yanda natambayi kowa haka natambayeka .....meyasa su basuji haushina ba se kai....saboda kasan ....
Shut up.......yafada yana daka mata tsawa
saurin mikewa tayi tsaye cikin daga murya tace jamilu kar kamanta da shugabarka kake magana so behave ur self .....kasan nasan cewa kai kasaci kudinnan so kake inzuba maka ido kome ......
Nuna shi tayi dayatsa tace naragamaka ne dazu saboda kar nazubarma da kima agaban wa'inda suke aiki akarkashinka amma kasani bawai na kyaleka bane .....girman laifinka yakai nakoreka a aiki nadaureka kuma nacika tara har sai kabiya duk abunda kadauka
Saurin dagowa yayi yana kallonta idonsa jajir jikinsa har rawa yake dan bacin rai
"zan baka dama takarshe dazaka tsira da mutincinka da kuma lafiyarka just one week.......nan dasati daya kadawo da duk abunda kadauka idan bahaka ba kuma sedai ince sorry for u jamilu dan ni kaina bansan miye makomarka ba
Now get out of my office......tafada tana nuna mai kofa
Kafeta yayi da jajayen idanuwansa ko kiftawa bayayi har natsawon lokaci sannan ya juya yafita afusace yana rufo kofar da karfi
aK ne yazo fita har ya shiga mota aysha tazo aguje tana kwalamai kira
Sauke glass din motar yayi yana kallonta yace aysha yadai
idonta ne yaciko da kwalla cikin rawar murya tace AK ....akwai matsala inaso zamuyi magana da kai
Tada moyar yayi yana fadin ok yanzu sauri nake kijira idan nadawo se inji ko miye by.....
har yafara tafiya da motar tayi saurin binsa tana fadin AK I am pregnant ....
Saurin taka birki yayi ya leko yana kallonta adan tsorace yace u said what..?
fashewa tayi da kuka tana mikamai result din ahankali yakai hannu ya karbi takardar yana dubawa
4 weeks pregnancy..... Ohh my god ......ya fada yana dafe kai saboda nawyin da yaji yayi masa ya jima ahaka kafin yadago da kyer yana kallonta se sharan kwalla take kamar dagaske
Jiki asanyaye ya fito daga motar yana fadin akwai Wanda yasan da zancan ne a gida
"a'a amma ni tsoro nakeji AK muje azubar gaskiya .....idan dady yaji kasheni zai yi
saurin dagowa yayi yana kallonta yace haba aysha da wanne zanji laifin ai se yamun yawa namaki ciki kuma inzubar .....bazan iya ba gaskiya
fashewa tayi da kuka tace to ni yanzu ya zanyi haka zan kare rayuwata kenan da canma baka aureni ba bare yanzu......
Riko hannunta yayi yana murmushi yace stop crying baby kima daina wannan zancan wayagaya maki bazan aureki ba daga ke har cikin dake jikinki ina sonku kuma zan aureki kodan yaronmu damuwata kawai shine bansan ya su grany zasu dauki zancan ba nasan mutunci na ne zai zube I idonsu amma yazanyi dole najure hakan kodan farin cikinki .....yakatashe maganar yana jan kumatunta
Dariya tayi cike da farin ciki tace bare ma zasu fahimcemu tunda sun San ba halinka bane
Kallon cikinta yayi yana murmushi yace I can't believe it wai namiki ciki batare da sanina ba so strange
Saurin kauda zancan tayi dafadin ummm bafita zakayi ba
hannunsa yasa aljihu yazaro kudi masu yawa ya mika mata yana fadin ga wannan ko zaki bukaci wani Abu idan nadawo zan karamiki but please take care of ur del and my baby idan kina bukatar wani Abu just call me ok
karban kudin tayi tana murmushi shikuma ya shiga motarsa yatada amma kana ganinsa kasan yana cikin damuwa dan dai kawai shi mutum ne dabaya son nuna damuwarsa afili
yana fita takira salim awaya tabashi labarin yanda sukayi da AK
Da yamma asma'u na dawowa daga office ta isko mutanan gidan sunyi cirko cirko apalo sun zubama kofa ido
Dining tawuce direct tahada tea tazauna anan wurin tafara sha sedai tana mamakin zaman me suke haka damuwar data gani afuskar grany shi yafi daga mata hanakli tana son sanin meyafaru amma batason shiga harkansu dan kar su rainata
can anjima AK yashigo palon jiki asanyaye ya nufo grany kansa akasa yana ji kamar yakoma amma ba hali
mikewa tsaye grany tayi tana nuna masa aysha dake gefe tana kuka tace Abid gayamun dagaskene abunda tafada ko karya tamaka dan baka aureta ba
saurin ijiye cup din hannunta tayi tana kallonsu da mamaki amma takasa gano inda maganarsu tadosa
Shiru yayi kansa akasa yakasa magana dan kunya jiyake kamar kasa ta tsage ya fada
"da kai nake magana kayi shiru
Kasa jurewa asma'u tayi ta taso fuska adaure tanufo wurinsu tana fadin meke faruwa ne
Saurin mikewa uncle jamilu yayi yana fadin ohhh madam ai dama nasan zaki so sanin meke faruwa amma bandauka da wuri haba ba
kauda kai tayi tana kara daure fuska dan tagane da biyu yayi maganar yanason rama abunda tamasa dazu ne
daure fuska yayi yana jefa mata kallo mai cike da tsana yace ya'ta tana dauke da ciki kuma bakowa bane yamatshi pace mijinki AK
What rubbish..... Tafada cikin rashin ba zancan mahimmanci
Dariya yayi yana kallon mutanen palon yace kunji wai rubbish ....sannan ya juyo yana kallonta fuska ahade yace kina tunanin zamu miki karya ne kome .....cikin ne baki yarda tanadashi ba ko kuwa mijinki ne bakiyarda shi yamata ba ....
kallon aysha tayi sanan takalli AK tace dagaskene cikin dake jinkita nakane
Se alokacin yadago da jajayen idanuwansa yana kalkonta yace Ba ruwanki a cikin wannan maganar tsakanina da family na ne bama bukatarki aciki
kallon grany yayi da jamilu cikin sassanyar murya yace grany....uncle....kuyi hakuri Ku gafarceni ni kaina bansan meyazo kaina har hakan tafaru ba kuma kunsan ba halina bane sharri shaida......
Katseshi aunty sadiya tayi dafadin sharrin shaidan ko .....ai dama haka kuke.....se kuncuci yarinya kuce sharrin shaidan ....to wallahi baka isa ba kai bakaji kunya ba karasa ......
katseta asma'u tayi dafadin yimana shiru awajan ke harkinada bakin magana..... duk abunda yafaru harda sakaci irinnaki ....kinsan cewa suna soyayya kuma suna zaune agida daya kamata yayi ace kinsa musu ido amtsayinki na uwarta amma bakiyi ba dan haka dole kiyi hakuri da duk abunda yafaru ki rungumesa amtsayin kaddara
jiyowa tayi tanakallon AK tace kai kuma kace matsalar danginka ne bai shafeniba to kar kamanta kudukanku akarkashina kuke dan haka dole nasan abunda kuke aikatawa ......kasan kana sonta meyasa baka aureta ba ?
saurin dagowa yayi yana kallonta cike da takaici yace I am not a kid nasan abunda nakeyi base kinfadamun ba
"Kai ba yaro bane amma bakasan mekakeyi ba ka kwasan abunda ka aikata kuwa wane hali ummata zata shiga idan taji wannan zancan kawai dan ina nuna rashin damuwata akanta baya nufin inason ganin wani Abu yasameta ne .....if something bad happen to my mother I won't.....
Katseta yayi dafadin se me.....mezakiyi duk bake kika jefani awannan halin ba na tabbata ranar da kika dauki sa hannuna wani Abu kika bani Wanda yakawar mun da hankali har nakaiga aikata wannan kazamin aikin
zatayi magana kenan sukaga grany tafadi kasa asume atare suka rikota suna jijjigata tare da kiran sunanta
Daukanta AK yayi yakaita bangarenta har kan gado ya kwantar da ita sannan likita yazo yafara dubata
asma'u nabakin kofar atsaye tana kallon AK dake safa da marwa cike da tashin hankali yama rasa yazai yi
juyowa yayi yana kallonta aransa yana fadin koma meyasa kika canza chitti baki mun adalciba ba kinsaba mun idan nashiga damuwa ke kike tsareni dole senafadamaki kuma kiyi supporting dina kibani shawara amma yanzu ke kike zama silar shigata damuwa u are with me but I still miss u
Dagowa tayi takallesa suka hada ido yayi saurin juya baya yana daure fuska
Takawa tayi ta isa wurinsa wurinsa ahankali takai hannunta tadafa kafadarsa tabaya
Saurin juyowa yayi yana kallonta itama shitake kallo batace komai ba taja hannunsa tazaunar dashi kan kujera sannan ta nufi dan karamin frig din dake palon
Shidai yazama tamkar kungi se binta yake da kallo yana hango real chitti dinsa atare da ita
Ruwa mai sanyi ta tsiyayo acopi ta mika masa
Karba yayi amma yakasa kai copin bakinsa se kallonta yake lokaci guda yana tuna rayuwarsu tabaya
hannunta tadora kan nasa sannan takai masa cup din bakinsa yafara shan ruwan ahankali still idonsa akanta yana kallonta
seda yashanye ruwan tas sannan tajanye hannunta tajuya zata bar wurin yayi saurin riko hannunta
Cak ta tsaya batare data juyo ba tana lumshe idanuwanta wasu yan siraran kwalla nazubowa akan kuncinta
Mikewa tsaye yayi yazagayo tagabanta yana fadin meyasa kike kokarin danne abunda ke ranki chitti please stop this drama I am tired of it
fitowar doctor ne ya katsemashi maganarsa saurin karasawa sukayi wurinsa yana fadin doctor meyake damunta ne is she ok
murmushi doctor yayi yace eh ba wani Abu bane kawai dai bata samun Hutu ne kuana biyu adan kula da ita dan allah kunsan jikin tsufa
sallama yamusu yatafi akan zai dawo gobe yasake dubata
dakin AK yashiga ita kuma asma'u tajuya tafita tana tunanin ta inda zata bulloma lamarin ga matsalar Company gata AK da aysha ga kuma grany akuance
[20/07, 18:48] Hassan Atk: 📚📚📚📚📚📚
👨👧 _DOMUN KANWATA_ 👩👧
Na( *Maryam Mhd*)
1⃣7⃣5⃣
Asma'u zataje bangaensu kenan tahadu da AK yana sakkowa daga kan stairs rike da bowl din fruits salad ahannunsa har ta wuce tajuyo tana kallonsa tace yawwa .....AK kagama aikin danabaka kuwa
Girgiza kai yayi batare daya waigoba yace No ....banma faraba
Saurin binbayansa tayi tana riko rigarsa tabaya tace to mekake jira bayan nagayamaka cewa gobe dasafe nake bukatrsu
Kokarin kwace rigarsa yafarayi yana fadin to wai azaune kika ganni ne kome .....badai aikina bane to karki damu ko karfe dayan dare nakai zanyi kayana
Shiga gabanshi tayi tana kallon bowl din hannunsa tace ina zakaje dawannan kaje ciki kasha mana ai bazai hanaka yin aikinba
"banawa bane aysha zan kaiwa kinsan masu juna biyu seda kayan marmari.......yafada yana shafa cikinsa at the same time yana kallon reaction dinta
ganin tayi shiru batace komai ba yasa yaraba tagefenta yana fadin dare yayi je ki kunata lady boss....idan kinjini shiru kirufe kofar kinsan masu ciki da rigima zata iya cewa sena sakata bacci sannan zan dawo .....
baikarasaba tayi saurin shan gabanshi ta karbi bowl din tana fadin kawo....kawo zan kaimata
Kallonta yayi yana murmushi yace are jealous
kauda kai tayi tana daure fuska tace what......no...meyasa zanyi kishi bayan bana sonka
tajuya zata tafi ya riko hannunta ya juyo da ita dakarfi har saida tafado jikinsa matseta yayi a kirjinsa suna kallon juna cikin murya mai kaman rada yace
idan bakya sona meyasa baki tafi kinbarni ba tunda kinsamu abunda kike so .....meyasa ba kya iya kallon kwayar idona aduk lokacinda zakimun kike mun magana .....meyasa se kin runtse idanuwanki kike iya kiran sunana ....kullun ke kike tashina abacci ki ijiye mun coffee dina kafin nafito daga wanka aduk lokacinda kika ganni cikin damuwa ba kya iya boye damuwarki akaina why......chitti har yaushe zaki rika wahalar damu ne..... ada munyi aure ne domun kanninmu amma ayanzu muna tare ne dan bazamu iya rayuwa batare da juna ba chitti ki.....
Kokarin kwace kanta tafarayi tana maida hawayen dake neman zubo mata cikin rawar murya tace miye haka kakeyi .....sakemun hannuna please... Na gayamaka bana sonka.... ina zaune dakai ne kawai saboda ina tausayawa grany bansan halin dazata shiga ba idan kuka bar gidannan ....kadaina bata lokacinka wajan tunanin inasonka ne shiyasa ......
Bata karasaba yasaki hannunta yana ja dabaya cikin daga murya yace karya kike asma'u aduk lokacinda nakalli kwayan idonki zallar so nake hangowa aciki ..... kawai dai kina danneshi ne saboda wani dalili naki .....
Tsayawa yayi yana kallon yanda take share kwalla cikin sassanyar murya yace chitti please nagaji da abunda kike mun ....I was blinded by ur love .....kinmun abunda yakamata ace naji haushi amma nakasa yin fushi dake bansan meyasa kika canza ba .....nagani kinyi kyew kin iya dressing kin iya make up u are so pretty amma .......ni wannan duk bai dameni ba .....ina so kidawo yanda kike da wannan asma'un dabata iya kwalliya ba ....bata iya sa kananun kaya ba ....ni ita nakeso she was the most beautiful and prettiest girl I ever seen in my life ....yakarashe maganar yana murmushi amma idonsa pal kwalla
juyawa tayi tana share hawayenta tanufi dakin aysha batare datace komai ba amma kuka ne kincinta aciki jitake kamar taje ta rungumesa tasaki kukanta ko taji sauki
tsaye yayi yana binta da kallo har tabacemasa sannan ya juya jiki asanyaye ya nufi bangarensu yana fadin bazan kara tambayarki ba kuma nima zanyi kokarin cire sonki araina nasaka na aysha tunda ita take sona kuma zan aureta inshafa maki lafiya silly girl .....dawanann surutan ya isa bangarensu yafara aikin data bashi
tazo daidai wurin dakin aysha kenan taga wucewarta tana waige waige tanufi hanyar fita
Saurin labewa tayi bayan kofa tana kallonta har tafita sannan tayi saurin bin bayanta har harabar gidan
Daga nesa ta tsaya tana kallon yanda suka rungume juna da salim har yana sunkuyawa daidai cikinta yamanna mata kiss tayi saurin ture kansa tana waige waige
Kallonsu take cike da mamaki dan ko ba afada ba tasan tabbas wannan shine uban dan duk yanda taso taga fuskansa takasa saboda wurin akwai duhu gashi yabata baya tajima azugunne tana lekensu ganin ya juya ai tafi yasa tayi saurin komawa ciki wurin dining tanufa ta ijiye bowl din dake hannunta sannan tadawo Palo ta tsaya
Aysha nashigowa taga Asma'u atsaye taharde hannaye tana kallonta fuska adaure ba alamar wasa atare da ita
Kauda kai tayi tana daure fuska tanufi hanyar dakinta zata wuce asma'u tafizgota ta wurgata kan kujera tana jifanta da kallon tuhuma
Sake da baki aysha ke kallonta cikin rawar murya tace ha'an...malama..miye haka ya zaki wani turani ko kinmanta halin danake ciki ne
"Cmon shut up .....bandamu da halin dakike ciki ba saboda banhada komai da abunda ke cikinki ba .....kuma inaso insan waye wannan dayazo wurinki cikin wannan Daren
Saurin dagowa aysha tayi tana kallonta atsorace dan batayi zaton taganta ba kame kame tafara irin namarasa gaskiya
Sunkuyowa asma'u tayi tana dafa kujerar datake zaune cikin murya mai kaman rada tace tun muna mu biyu kigayamun waye wannan saboda shakka babu shine uban dan dake cikinki
Zaro ido aysha tayi tana fadin what nonsense.... Are u daunting me ..?
"No I'm not .....saboda dama nasan cikinnan bana AK bane nayi shiru ne saboda banada wata hujja amma yanzu nagani da idona saboda haka kigayamun waye wannan mutumin da naganko tare
Wani wahalallen murmushi aysha tayi tana kallon asma'u tace wannan ai zancan banza ne .....baizama dole kisan waye wannan ba saboda bayada wata alaka da cikinnan .....kawai dai kice bakin ciki kike ji saboda naba AK kyewtar dake kika kasa basa amatsayinki namatarsa
nunata tayi dayatsa lokaci guda idonta yakade cikin kakkausar murya tace watch ur tongue...... kisan irin maganar dazata rika fitowa daga kazamin bakinki idan bahaka ba yanzu nagyara miki zama.....wai Ku wa'yanne irin mutane ne ....meyasa ko kadan ba kwa tsoron allah ne ....mutumin dabayada wani buri da yawuce yaga ya kyewtata muku kullun yana kokari yaga yajiyamuku dadi kuci mai kyew kusha mai kyew kusa sutura mai kyew .....kuma duk daga jikinsa kuke ciro kudin amma bakwada wani buri da yawuce kucutar dashi Ku wulakanta shi saboda me....don't u have any shame .....kirasa wanda zaki lakawa cikinki se shi .....koma wane dan iska ne yamiki shi tunda yanasonki meyasa bai aureki ba ....
katseta tayi dafadin dallah dakata mezaki gayamun ke har kinada bakin magana wace cutarwa ce baki mishiba tunda kika kwace dukiyarsa ai kingama wulakantashi kenan....
Kuma wallahi kifita daga harkata nalura kuana biyu kinasamun ido akan harkokina to ya isheki haka
Kafeta da ido asma'u tayi cike da takaici tama rasa mezatace mata kawai tajuya afusace tanufi bangaren grany
zaro ido aysha tayi tana fadin to mekuma zatajeyi wurin grany nashiga uku ...bin bayanta tayi cikin sanda har cikin palo ta labe daga bakin kofa tana sauraransu
Tafa hannu grany tayi tana salati tace ohh ni ya'su kice sharri tamasa .....haba nifa nayi mamaki shiyasa har yanzu banyarda cewa abidi zai aikata wannan abunba .....to ai yanzu bazama zakiyi ba tashi zakiyi ki gayamasa gaskiyar magana yama daina wahalda kansa akanta munafuka mai bakin hali irin na ubanta
saurin komawa dakinta tayi cike datashin hankali takira salim tana gayamasa abunda yafaru
Wata magana yagayamata tayi shiru tana sauraransa sannan ta ijiye wayar tana murmushi tanufi bangaren AK
Dagowa asma'u tayi tana kallon grany tace grany ina jin tsoro dawuya ya yarda dani kinfa san yanda ya kwallafa rai akan cikinnan ba lalle ne ya yarda cewa banasa bane
"Tashi dai kije asma'u ai yasan aysha bashi kadai take kulawa ba kinga zai iya yarda da maganarki ......kuma ai bazamu barshi haka ba yayita wahala akanta alhali munsan ba cikinsa bane
aysha nashiga palon tafara kuka saurin mikewa AK yayi yanufota yana tambayar lafiya
kara volume din kukanta tayi tana fadin ba matarka bace .....haka kawai tahau zagina wai ni yar iska ce nadauko cikin shege wai banada tarbiya .....kuma wai zata gayamaka cewa cikinnan banaka bane dan karka aureni kuma harda tarani tayi dakarfi har nabige da gado tana fadin wai seta kashe abunda ke cikina .......
wani malalacin murmushi yasaki yana fadin haba aysha .....nasan wacece asma'u bazata taba aikata haka ba kawai inaga baki fahimceta bane kuma kila ranta ne abace shiyasa amma ai ita ma tanason abunda ke cikinki kema shaidace duk abunda kike so tana sayamaki ......
kara fashewa tayi dakuka zatayi magana kenan asma'u tashigo kallon yanda aysha ke kuka tayi se duk jikinta yayi sanyi tana tsoron abunda zai biyo baya idan tagayamasa
ahankali takarasa wurinsa cikin sassanyar murya tace .....inaso zamuyi wata magana
Go ahead ......yafada yana kafeta da ido
shiru tayi nadan lokaci sannan tadago tasaci kallon aysha sannan tamaida kallonta kansa cikin rawar murya tace ....in ....private
"She is my wife to be kuma uwar Dana so zaki iya fadan komiye agabanta .....inajinki
riko hannunsa tayi tana fadin karya take maka AK cikin dake jikinta banaka bane she is just blackmailing u da tacimma wata manufa ta....
bata karasaba yayi saurin kwace hannunsa yana fadin enough!!! Ashe dama gaskiya tafada har ina karyatata ....kinbani mamaki Ashe dama son dakike nunawa cikinta duk yaudara ne ....wai meyake damunki ne asma'u dama haka halinki yake ko kudine suka sa kika canza halayenki masu kyew
Idonta ne yaciko da kwalla tana kallonsa cikin muryan kuka tace AK believe me gaskiya nake fadamaka ba cikinka bane wanann kawai......
hannu yadaga zai mareta se kuma yadakata yana dunkule hannunsa yanunata da yatsa yace .....ya isheki haka bana bukatar jin komai daga gareki cikinnan nawane inasonshi daga shi har uwarshi kuma dazaran ta haihu zan aureta .....zamu tafi gaba daya mubar miki gidan kiyi abunda kika ga dama dashi
Jan hannun aysha yayi zasu fita tayi saurin shan gabanshi tana kuka tace AK please listen to me kuskure kake aikatawa babba Wanda nan gaba zakayi nadamarshi
tureta yayi daga gabansa yana fadin ba abunda yashafeki dani najima dayin nadamar saninki arayuwata ....kuma bari kiji ....idan nakara jin wannan maganar abakinki ko abakin wani daban I will show u the other side of me ....yana kainan ya wuce yabarta atsaye tana binsu da kallo hawaye na tsere afuskanta
Juyowa aysha tayi tana murmushin gefe takai hannunta tashafo cikinta tana kashemata ido har suka fita daga palon
Durkushewa tayi awurin tanafashewa da kuka yace ABI why don't u believe me .....meyasa ka amince da mutanen da ke kokarin ganin bayanka ne .....oh allah kataimakeni ....abun yamun yawa da wanne zanji
Washegari dasafe kafin ta tashi har ya gama aikin databashi yayi shirin zuwa office yana fitowa ya hadu da sarah idonta jajir da alama bataga bacci ba gashi fuskanta dauke da damuwa
Wurinsa ta nufo tana boye damuwarta tace Yaya dama kai nake jira ...
Gyara tsayuwarsa yayi yana fadin to gani fadin matsalarki lil sis
Murmushi tayi tana Sosa kai tace Yaya .....dama ......wasu yan kudi nake bukata ahannunka kozan samu.....
Hannunsa yakai aljihu yana fadin bari mugani inaga baza'a rasaba wata kudaddiyar dubu daya yaciro daga aljihunsa duk ta kudundune seda ya bubbudeta sannan ya mikamata yana murmushi yace gashi je kisamo canji kiraba biyu kikamun sauran zansha coffee anjima
sake da baki take kallon kudin kamar zatayi kuka tace Yaya ....banganeba ....mezanyi dawannan nida nake naman 5M
Zaro ido yayi yana gadin 5M fa kikace sarah......kodai banjiki da kyew bane mezakiyi da kudi masu yawa haka
saurin juyawa tayi tanufi dakinta tana fadin barshi kawai dawasa ma nake maka
Binta yayi dakallo aransa yana fadin tabbas akwai abunda take shirin yi.....I won't forgive u if u did something stupid this time
dasafe sukayi meeting a company inda ahmad ya gabatar da hadadden Zane mai bala'in kyew amatsayin sababbin collections din dazasu shigo
bayan antashi takara jaddada ma uncle jamilu cewa karyamanta yaune ranarshi takarshe idan bai biya kudin ba zaiga sammaci
sedai ga mamkinta murmushi taga yayi yana kallon zanen dake hannun ahmad hakan yasa tayi zargin wani abu sedai takasa gano meyake shirin aikatawa
Sarah duk tagama fita hayyacinta gashi uncle jamilu se barazana yakemata duk inda take tunanin zata samu kudi tanema babu
fadawa tayi kan gado tana fashewa dakuka cike da nadamar abunda ta aikata yanzu gashi bakin halinta yajamata tashin hankali kuma Wanda tayi danshima batasameshi ba
ahaka aysha tashigo tasameta karasowa tayi kusanta tafara lallashinta seda tayi shiru sannan tace tashi inbaki wata shawara amma bansan kozaki iyaba
Saurin tashi zaune tayi tana share hawayenta tace allah zan iya fadamun menene
Kallon kofa aysha tayi sanann tamatso kusanta cikin rada tace naji ance company sun fitarda sabon zane
tsaki tayi tace to miye alakar wannan da matsalata ina ruwana da zanensu ni kiyamun ida zansamu kudin shine damuwata
Dariya ysha tayi tace to ai baki bari kinji karshen zancanba .....kinsan wanann zanen yanada matukar mahimmanci idan har kika sameshi to matsalarki ta kau saboda bakaramin tsada ne dashiba
"Kamar ya banganeba ......taya zansameshi .....kuma waye zai sayi Zane ahannuna har kina maganar wai zaiyi tsada
Duka aysha ta kaimata akafada tana fadin ke yanzu kanki bai kawo wuta ko kadan .....kinsan company dake Lagos suna dan takun saka da su AK saboda sun fisu kwarewa dasanin kan aiki kuma sun lunkasu customers shiyasa basa jittuwa idan har kikayi kokarin samo zanen to inagayamiki da gudu zasu sayeshi ahannunki for just one clap zaki samu 5M dinki cash ....
"Gaskiya aysha bazan iyaba sata fa kenan kuma idan Yaya yasan ni nadauka wallahi kasheni zaiyi
tsaki aysha tayi cike da takaici ganin plan dinsu zai ruguje tayi saurin fadin wane irin sata kuma ko kinmanta cewa yanzufa company bana AK bane na asma'u ne kinga kwa ai rama cuta ga macuci ibada ce
Murmushi sarah tayi cike dafarin ciki tarungume aysha tana fadin nagode aysha gaskiya shawarar nan tayi amma ina zansamu zanen
Murmushi tayi tana mata kallon gara wasai tace Zane yana office din ahmad se kisan yanda zakiyi kisatoshi batare da kowa ya ganki ba
nan take ta shirya tanufi office din ahmad aguje tafada office dinsa tana fadin wayyo Yaya ka taimakeni
Azabure ya mike cike da mamki yanufota yana fadin subhanallahi .....sarah menene dake dawa......
Dafe kujera tayi tana haki tace Yaya .....wa.....wasune suka biyoni suna..... nan waje....
zaunar da ita yayi kan kujera yafita da sauri dan ganin ko suwaye
yana fita tamike tana leken kofa tashiga bubbude drowowi tana Neman zanen sedai duk Wanda tadauka setaga ansa date din akayi zanen haka taci gaba da dubawa har takai ga sabon zanen tayi saurin daukoshi sedai tarasa inda zatashi saboda takardar tanada girma kuma bazata iya nadeta ba
Window takalla taga ba komai awurin se shukeshuke tayi saurin janye glass din ta wurga zanen waje daidai nan ahmad yashigo
saurin juyowa tayi tana kallonsa atsorace sedai murmushin dataga yayi shi yatabbatar mata cewa baiga abunda tayiba
Karasowa yayi wurinta yana fadin sarah kodai gamo kikayi ne naduba ko ina banga kowa ba kuma natambayi securities sunce ke kadai kika shigo
Sosa kai tayi tana murmushin yake tace to ni dai bansaniba amma wasu naga suna bina zasu kamani
Kujera ya nuna mata yana fadin to zauna bari nakira AK se musan abinyi
Zaro ido tayi tana girgiza kai tace a'a Yaya karka kira kowa karma kagayusu nazo nan .....bari kawai natafi sauri nake
Cike da mamaki yace sarah are u alright.... Ko inzo in rakaki gida ne
"a'a kabarshi kawai yi aikinka zan iya tafiya nikadai .....takarashe maganar tana fita daga office din
Dage kafada yayi yana tabe baki ya zauna kan kujerarsa yaci gaba da aikinsa
tana fita tazagaya cikin sanda tadauki zanen batare dakowa yaganta ba har tafita bawanda ya lura da abunda hannunta saboda securities din sun Santa ko kallonta basuyiba har tafita get """""
0 comments:
Post a Comment