_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._*
馃憠馃徎1鈨?
*Matsanan cigar* hayaniyar dake tashi agidan ce taja hankalina, cikeda bak'in ciki natashi daga barcin safen dana koma, fitinar gidanmu dabance data kowane family House dana Sani kona ta6a jin labarinsa a rayuwata, haka gidan namu yake kullum tamkar kasuwar 'yan danbe, daga matan gidan zuwa 'yan mata da yara tamkar muna ganin hanjin juna, saika rantse badaga tsatso d'aya muka fitoba.
Kururuwar danaji maman Safara'u ta kurma yasani kuma jan dogon tsaki, sai kuma najiyo muryar gwaggon haleema Na fad'in 鈥渒ai amma wannan lamari baiyi dad'iba, kekuwa maman biyu ya kamata ki canja wannan halin naki, dan tabbas inba wani abu kikayiba babu yanda za'ayi yaronan Sadeequ yadage shi cikinsu *MUNAYA* yakeso, duka yaushe aka gama maganar nan akan shafi'u amma shine zaki koma kan Sadeequ kuma yanzu?鈥?.
gaba nane ya fad'i, cikin zaro idanu waje nace, 鈥渁shema mu akanmu fitinar take yau?鈥?. yink'urin sakko nake daga gadon Munubiya tashigo tana share kwalla, binta nayi da kallo harta fad'a saman gadon ta kwanta rufda ciki tareda fashewa da kuka mai ban tausayi. Hakan Yakuma tabbatar min lallai mud'inne dai ake hargowar akanmu. a fusace Na dirgo daga gadon na nufi k'ofar fita, (ko kad'an banida hak'uri, musamman akan cin zarafin mahaifiyarmu da akeyi agidan lokuta da dama idan irin hakan ta taso), taku biyu nayi naji an damk'oni, najiyo cikin masifa dan nasan Munubiya ce.
鈥渨lhy ki sakeni kafin nafara huce haushina akanki munu! yau saina gyarama kowacce 'yar iskar mata zama agidannan dan kutu.....
Bankai ga k'arasawa ba Munubiya tai saurin rufe bakina da tafin hannunta.
Kici-kicin kwacewa nafarayi amma nakasa, dan bak'aramin ruk'o taminba, raina yak'ara 6aci ainun danjin irin rashin kunyar da Safara'u ke zubama innarmu a tsakar gida, bansan na wancakalar da Munubiya gefe ba nafice da gudu.
Babu Wanda yaga fitowata sai dai saukar sautin marin dana zubama Safara'u a farar fuskarta sukaji.
Hakan yaja gidan yay tsit na wucin gadi, sai kuma hayaniya takuma 6allewa, Safara'u da mamarsu sukayo kaina danufin duka....
Tsawar da baba k'arami ya bugace tasaka kowa dakatawa tsakanin ni dasu, hakama matan gidan sai suka fara jan k'afafu danufin barin wajen.
A tsawace yace, 鈥渒ar wadda tabar wajen!!鈥?.
Tsitt kakeji gidan yayi, tamkar bashi bane d'azun ya cakud'e da hayaniya tamkar ana biki ko suna.
Jarabar gidanmu ba bak'on Abu bane a anguwarmu, danta rigada tazama tamkar ajininmu take (yo ajininmu mana zance) tunda kullumne babu fashi sai anyi hayaniya, kodai matan gidan kokuma mu 'ya'yan gidan. Babu mai d'agama wani k'afa koda na second d'ayane kuwa, yanzun zakaji gidan shiru, anjima k'ad'an kaji an doka gangar shaid'an, musamman ma fad'an yara dayafi komai saurin had'a fad'an matan gidan da a kulum, a rana sai ayi fad'a biyar akan yara kawai, innarmu ce kawai da Maman Fauziyya keda k'ok'arin K'aucewa irin wannan fitintunun dasuka zama tamkar shan ruwa acikin gidanmu.
Baba k'arami yafara fad'a tamkar zai ari baki, inda yake shiga bata nan yake fitaba, kowa yayi tsit yana saurarensa, (saboda kasancewar masifaffe shima) sai da yayi mai isarsa sannan yajuya yafita yana fad'in nida Safara'u mu sameshi falonsa. harda iyayenmu mata.
Duk abinnan da akeyi innarmu na kicin tana had'a Karin kumallon safe, kuma kalma d'aya bata tofaba a zancen nasu, datasan ma zan fito bazata barniba nima.
A falon baba jafaru yanemi jin ba'asin tushen fitinar, cikin d'aga muryar da hargowa maman Safara'u tafara fad'in 鈥淎lhaji wlhy kashiga tsakanina da maman biyu a gidannan, idanfa tanama sauran matan gidannan Yanda taske so, suna barinta nibazan bartaba, tasanni tasan waye ubana ehe, kum.......
Hannu yay saurin d'aga mata, 鈥渒inga Suwaiba nifa ba wannan ne yasani kiranku ba, sonake naji minene ya kawo hayaniyar?鈥?.
Cikin jin haushin an tareta tace, 鈥淎lhaji akan yaronnan Sadeequ ne, kowa yasan wajen Safara'u yake zuwa a unguwarnan, amma jiya da yamma sai ya aiko kiran Munaya, dayake ALLAH yatashi tonon asirinsu sabida bayaune na farko ba sai d'an Aiken ya kwatsa maganar a tsakar gida, babu dai Wanda yace komai, dan azatonmu ba Sadeeq d'in Safara'u baneba, goshin magriba saiga Safara'u tashigo tana kuka. Na tsareta da tambaya da k'yar tacemin cikinsu 'yan biyu tagani da Sadeeq a zauren gidan Malam halilu suna hira da dariya, kuma hardama mata gwalo akayi. Saboda na gaskata zancenta na sake aiken Rahma taganomin da idonta, harma taji Sadeeq d'in nafad'in ai koma miza'ayi bazai auri Safara'u ba, cikin wad'an nan munafukan yaran daba ganesu akeba zai aura, saboda darene yasani d'inne maganar a raina har safiyar yau d'inan, amma wlhy Alhaji da k'yar na iya barci nida Safara'u jiya.
鈥渉ummm鈥? kawai nafad'a ina dafe kaina, saboda jin Yanda aka canja maganar.
Babak'arami ya kalleni yace, 鈥淢unubiya ce ko Munaya?鈥? (dan basa ganemu saboda tsananin kamata da hassana ta).
Zuciyata cikeda bak'in ciki nace, 鈥淏aba Munaya ce鈥?.
鈥測auwa Munaya, ina 'yar uwarki?鈥?.
鈥淭ana ciki baba鈥?.
Baba ya kalli Safara'u daketa matse kwallan munafurci tun d'azun yace, 鈥渒! Safara'u tashi kiramin Munubiya 鈥?.
Batareda ta amsaba tatashi tafita, mintuna kad'an saigata sun dawo tareda Munubiya datasha kuka idanu sukayi luhu-luhu. tsaki naja a raina ina hararta ta gefen ido, rashin jarumtar ta na bani haushi, ta cika hak'uri da sanyin hali tamkar innarmu.......
Maganar baba ce tadawo dani daga tunanin dana tafi. nad'ago ina kallonsa saboda kiran sunana dayayi, muryar a dake na amsa da 鈥渘a'am baba鈥?. kallonsa ya maida kan Safara'u yana fad'in 鈥渨acece acikinsu kika gani tareda Saddik'un?鈥?.
Binmu da kallo Safara'u tayi, cikin matse kwalla tace, 鈥渂aba niba ganesu nakeba, sai sun banbanta min Kansu sannan鈥?.
Baice komaiba dan shima yasan da hakan, (ta hallaya ne kawai kowa ke banbantamu agidan, hatta da innarmu kuwa). Baba yabimu da kallo alamar son sanin wacece acikinmu.
Da sauri Munubiya tace, 鈥渂aba nice鈥?.
Nima na kar6e da fad'in 鈥渂aba k'arya takeyi nice jiya Sadeeq ya aiko kira, kuma babu wata alak'a dake tsakaninmu, hasalima ya kirani ne akan Safara'un, sune dai suka maida zancen haka鈥?.
Daga Safara'u har mamanta harara suka ballamin, babu ragi nima na rama kuwa.
Baba ne yakatsemu da fad'in 鈥渕iya faru to Munaya?鈥?.
Janye idona nayi daga Kansu na maida gareshi, kaina ak'asa Nace,
鈥渂aba ya kirani ne yana tambayata minene abinda Safara'u tafiso a rayuwarta, dan yanason yabata gift na birthday d'inta, kuma soyake yayi mata bazata. shinefa nake lissafa masa muna dariya saboda ina cewa ya had'o mata da gyad'a soyayya dan ita mayyarta ce, a dai-dai lokacinne kuma na hangota zata shigo gida, nifa dama tsokana namata gwalon, Ashe ita ta d'aukeshi wani Abu. Kuma wlhy Rahma k'arya takeyi, lokacin data fito tareda yaa Hameed ta ganni yana bani kayansa nakai masa ciki shi zai shiga masallaci salla. Wannan shinefa abinda yafaru, shine suke cewa nakwace mata Sadeeq, har ana cin zarafin innarmu da farar safiyar nan鈥?.
Ajiyar zuciya innarmu ta sauke a hankali, taji dad'i daba abinda suke zargin baneba.
Wata uwar harara baba jafaru ya watsama maman Safara'u, 鈥渒ai Suwaiba kedai ALLAH ya gyaraki, dan ALLAH kuringa bincike akan Abu idan yara sun fad'a muku, tokinji dai abinda yafaru, kekuma Safara'u dayake bakida tarbiyya har bakinki yana iyama Ai'sha rashin kunya ko, ki tabbatar saina saka Abdulhameed yacimin ubanku keda Rahama yau a gidannan. Ai'sha kiyi hak'uri dan ALLAH 鈥?.
Innarmu ta yink'ura zata mik'e tana fad'in babu komai babansu, ALLAH ya kauda fitinar gaba鈥?.
鈥淎min鈥? muka fad'a muma muna mik'ewa mukabi innarmu a baya.
Koda muka fito, sai matan gidan suka zubo mana ido suna kallo tamkar yau suka fara ganinmu, a raina nace munafukai, haka zaku k'are.
Ran innarmu ya6aci matuk'a a wannan karon, amma kasancewarta mutum mai hak'uri da shanye damuwa sai bata nunaba.
Nida Munubiya kam kasa shanye 6acin ranmu mukayi, munsan koma wace irin wulak'antawa za ai mana agidan *KAKARMU* ce taja mana, itace tabada kowacce iriyar k'ofar tozartamu, idan kaga abubuwan da ake mana saika d'auka ba jinin gidan baneba, tunda muka taso a haka muka tsinci kanmu, hakama mahaifiyarmu a wannan halin muka risketa tana fuskantar k'ask'anci da wulak'anci daga Kakarmu da matan Abban mu, harma da matan k'annensa, bamuda 'yanci irin na 'ya'ya, mahaifiyarmu batada kima irinta matar gida (Uwargida), hakan yasamo asaline dalilin................鉁嶐煆?
馃憥馃徎
Tofa masu karatu dalilin mi? Dani daku duk muna buk'atar jin wannan dalili a bakin MUNAYA!, saiku kasance dani danjin Yanda wannan labari mai d'unbin harmutsi da tsalle-tsalle zai kaya, miye manufarsa? ina kuma ya dosa?.
Amsa d'aya zan iya baku.馃憞馃徎
*_LABARIN MAI TSAWONE_*
saikun kasance dani a hankali zancigaba da warware muku lauje cikin nad'i.
ALLAH yasa zaku bani had'in kai, tabbatarwata shine yanda zaku kar6i wannan labarin.
Dan haka kumuje zuwa馃ズ鉁嶐煆尖湇馃徏
Zamu cigaba Monday insha ALLAH, wannan d'and'anone.
Sannan wannan karon zandinga typing ne Monday to Friday kawai insha ALLAH, kunga banda weekend kenan馃槉.
One luv馃グ
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu馃槶馃憦馃徎._*
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎3鈨?
.........Fad'a sosai innarmu tamin akan Marin Safara'u danayi, sannan ta d'ora da nasiha kamar yanda tasaba, wani kam yashiga kunnena, wani kuwa tabaya yabi, dan harga ALLAH Na daina zama kowa yana taka mana mahaifiya a gidan.
Innarmu tace, 鈥渒u shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Ku tafi gidan mamanku Rabi'a Ku k'arasa hutunku, banason zamanku a gidan nan tunda fitina yake kawowa鈥?.
A sanyaye Munubiya ta amsa da 鈥渢o innarmu鈥?.
Amma ni saina tunzuro baki gaba ina k'unk'uni, dan banason tafiya ko ina, canma saboda d'an mama Rabi'a d'inne Marwan, ko kad'an bama shiri dashi, saboda masifarsa. 鈥渒ai innarmu, yanzu dan ALLAH saboda wasu can bazamu mik'e kafa yanda mukeso ba agidanmu, duka fa hutun sati biyu ne kacal, amma saimunje wani waje?, ni wlhy inkika barni babu mai k'ara mana koda kallon banza a gidannan, harma innaro bazan bartaba.........鈥?
Maficin danaga innarmu tajawo yasani tashi da sauri nabar gurin, Na tabbata shirin bugamin takeyi. Munubiya ta saka dariya tana kallona, 鈥渒e ga rashin arzik'i ga tsoron tsiya, dukan maficin kikema wannan gudun?鈥?.
Harara Na balla mata, 鈥測o k'ya fad'i haka mana tunda ba jikinki baneba, tsoro kam kinsan waye matsoraci acikinmu ai鈥?.
Munubiya ta ta6e baki 鈥渘aji dai, koma mizaki ce kije kiyita cewa, inama kayana dakika saka jiya? na wanke, dan dasu zanje鈥?.
Wayar innarmu Na d'auka ina dannawa, batareda na bata amsaba Na nuna mata laundry basket d'inmu.
Innarmu tace, 鈥渢o Aljanar waya ajiyemin kafin ki k'ararmin kud'in ciki, ina taki?鈥?.
鈥渒ai innarmu, please mana, zan kira Ayusher nefa nasanar mata muna zuwa gobe, ALLAH wayata babu ko nera aciki Munu ta cinye min jiya鈥?.
鈥渒iji tsoron ALLAH munaya, Nina cinye mini kud'in waya? bake kika kira Balkisu ba da kanki?鈥?.
鈥渢o dana kirata sai nace kuyita surutu har kud'ina ya k'are鈥?
innarmu Na shirin yin magana muka jiyo kururuwar kukan Safara'u da Rahama. dariya Na k'yalk'yale da ita, ina fad'in 鈥渙, ALLAH ga yaa hameed can yana gwajin kwanji a jikin gayu鈥?.
Harara innarmu ta ballamin, saikuma tamik'e tana shirin fita, nasan kar6arsu zataje, nai saurin fad'in 鈥渒ai innarmu, kid'an barsu su lallasu mana鈥?.
Dakk'uwa ta watsomin tareda fad'in 鈥淜'aniyarki Munaya鈥?.
Dagani har Munubiya dariya muka sanya harda tafawa kuwa.
Ba'a rufa mintuna 3 da fitar innarmu ba muka fara jiyo hargowar Maman safara'u (dama ita bata magana a hankali) Yaa hameed takema masifa akan dukansu safara'u dayakeyi, maman su yaa hameed babu hak'uri, itama tafito suka fara cacar baki, yaa hameed kam ficewarsa yayi bayan innarmu ta kwaci su Rahama a hannunsa da k'yar. kafin kace mi gidan yakuma kaurewa.
Munubiya tace, 鈥渒ai jama'a ko breakfast ba'ayi agidanba har antafi wrestling zagaye na biyu鈥?.
Na fad'a saman gado ina Dariya, danni mamaki 'yan gidanmu nakeyi da bala'insu. wayar Innarmu tayi ringing, da Sauri Na duba sainaga Abbanmu ne, cikeda d'oki Na amsa tareda masa sallama sannan Na gaidashi.
Yace, 鈥淢unubiya ina maman takune?鈥?.
鈥淎bba ba munu bace, nicefa鈥?.
鈥渢o to munaya ce? hayaniyar mi nakeji haka agidanne Munaya?鈥?.
K'yafta min ido da zungurina Munubiya tashiga yi wai karna fad'a masa (dayake a Hans free nasaka wayar, tana jin komai) amma saina harareta da murgud'a baki nace, 鈥淎bba Mama Ce da maman safara'u suke fad'a鈥?.
Tsaki yaja da fad'in 鈥淎LLAH ya shiryesu to, ina maman taku ne?鈥?.
鈥淎min Abba, Innarmu tana can wajen rabon fad'an ai鈥?.
鈥渟hike Nan, idan tashigo kice takirani muyi magana鈥?.
鈥渢o Abba bye鈥?.
Yace, 鈥渙k dear bye鈥?. Sannan ya yanke wayar.
Ina yanke wayar Munubiya ta kaimin bugu, Na kauce ina dariya 鈥測o da bakina a hanani fad'ar gaskiya鈥?.
鈥渂a hanaki akayiba, amma kinsan idan Allura ta tono garma mune tushen fad'an ai, kinkuma san halin Abba da d'aukar zafi kamar baba k'arami鈥?.
鈥渢ab, ta k'are musu dai suda suka takalo wlhy, jarababbu dangin masifa鈥?.
鈥渒ina ciki kenan tunda kema dangin kine ai鈥?.
Dariya muka Sanya nida munubiya.
*washe gari*
Tafiyar mu gidan mama Rabi bai yuwuba, saboda dawowar Abbanmu, da innarmu ta sanar masa a waya zamuje can muk'arasa Hutu sai yace a'a muyi hak'uri mu zauna, Dan akwai bak'in da zaiyi a k'arshen sati (weekend), kuma yanason dukkan yaran mukasance muna nan.
Innarmu tace shikenan.
Wannan dalilinne ya hanamu tafiya Hutu, dama ni ba so nakeba, Munubiya ce keta zakwad'in tafiyar.
Yau ta kasance alhamis, tunda safe muka tashi da himmar wanki nida Munubiya, ina sharar sashenmu Munubiya na fidda kayan wankin, yayinda Aryan da Aiyan keta tara mana ruwa daga fanfo zuwa banbu.
Ina gama sharar na wanke hannuna na k'arasa bakin fanfo inda Munubiya ke k'ok'arin jik'a kayan. zama nayi bisa d'an dakali da akayi wajen saboda irin hakan, wanki ko wanke-wanke da sauransu, waya nake latsawa ina nemo mana wak'a, dan muji dad'in wankin, maganar aunty khaleesa kawai mukji a kanmu tana fad'in,
鈥渒! Munaya tashi kije ki gyaramin d'akinmu, akwai wani zanina nan ki d'akkosa ku wankemin鈥?.
Banza namata ban d'agoba, sai Munubiya ce tace, 鈥渢o aunty khaleesa鈥?.
Shirun danayi ina kuma tamke fuska yasata gane nice munaya, Dan haka ta kalli Munubiya dahar tatafi, 鈥渒 Munubiya!... dawo, bakece zakiyiba, k! Dan uwarku Munaya tashi kije kimin鈥?.
Da sauri Munubiya tace, "Aunty khaleesa ai nice munaya, waccan Munubiya ce鈥?.
Hararta tayi, 鈥渕ai dani 'yar iska to, ko kina tunanin ban ganeku nima d'in?鈥?.
Banyi niyyar d'agowa ba, amma jin abinda tafad'a yasani sakin guntun murmushi, nasan k'arya takeyi tace tana ganemu kai tsaye, yanzu ma dan kawai na nunu halin nawane shiyyasa tagane nice, kawai tafad'ane dai, mai da kaina nayi nacigaba da abinda nakeyi.......
Wata ashar ta lailayo ta makamin, tareda zaburowa tamkar zata dakeni, dai dai nan sallamar innaro ta karad'e tsakar gidan. mu duka kallonta mukayi, nikam kallo d'aya namata na d'auke kaina, (dan nikam natsani kakarnan tamu) Munubiya da aunty khaleesa suka gaidata, nikam a d'age nace 鈥渋na kwana鈥?.
鈥渒in yima uwarki Ai'sha dan Ubanki鈥?, cewar innaro ta na nunani da d'anyatsanta manuniya馃憠馃徎, tacigaba da fad'in 鈥渘i zakima gaisuwa a haka? kamar wata sa'ar uwarki?, aiko Aisha da ubanki basu isa sumin gaisuwa hakaba balle ke haihuwar yanzun鈥?.
Baki na la6e, ba tareda na kalleta ba natashi nahau wankin, Munubiya kuma tawuce danta gyarama su aunty khaleesa d'akinsu. abinda nayi na nuna halin ko in kula saiya kuma tunzura innaro, ta fara hayagaga da matse kwalla wai naci zarafinta.
Wannan yasaka matan gidanmu da yara fara fitowa d'ai-d'ai suna kallonmu (dan al'adar gidanmu ce hakan, da anji kaya-kaya kowa zaiyo waje yaganema idonsa abinda ke faruwa).
Dady ya k'araso da sauri yana fad'in 鈥淚nna miya farune haka da kuka? Keda waye?鈥?.
鈥渨annan shed'aniyar yarinyar mana鈥? tayi maganar tana nunani 鈥渨aini yarinyar nan zataima d'ibar albarka saboda uwarsu kullum tana aibantani a gurinsu, shiyyasa duk sun rainani....鈥?
Baki bud'e nake kallon innaro da sherinta. wlhy wannan tsohuwar bazataga Annabi ba........
Maganar Dady ta dawo dani daga mamakin innaro. Yace, 鈥淢unaya ce ko Munubiya? miya farune keda inna?鈥?.
Dady yanada sauk'i, ba kamar Abbanmu da baba k'arami ba sun fishi zafi.
Nace, 鈥渄ady Munaya ce. wlhy babu abinda namata, kawaifa daga shigowarta duk muka gaidata, shine kawai ta hau zagina wai ban gaidata da k'yauba.......鈥?
鈥渁mma ai gaisuwar rashin tarbiya kikai mata鈥?. 鈥榗ewar Aunty khaleesa鈥?.
Dady zaiyi magana Aunty Ramlah tace, 鈥渨lhy Dady ba haka bane, duk abinda yafaru akan idona yafaru, dan nafito zan d'iba ruwa a fanfo鈥?.
Dakuwa Innaro ta mata, 鈥渒inci uwarki hadiza, kema ashe munafukace ban saniba, to ko hadizar ta haifama Ai'sha ne ke?鈥?.
Fakar idon Dady aunty Ramlah tayi ta dallama innaro harara, sannan tace, 鈥測o daga fad'ar gaskiya, nidai wlhy Dady abinda nagani nakuma ji kenan鈥?.
Girgiza kai Dady yayi, sannan yace, 鈥渒iyi hak'uri Inna, Munaya tayi kuskure amma bazata sakeba. Munaya zoki bata hak'uri鈥?.
Ban musaba nazo har gabanta nace tayi hak'uri, bata amsamin ba, saima hararata datayi kawai. nima saina bar wajen nakoma kan wankina.
Dady Yakama hannun innaro suka shiga falonsa, matan gidanmu duk suka bar wajen, basuso wasan yak'are a nanba, sunso ace cin mutuncin innaro yasauka har kan innarmu.
Innarmu dake tsaye daga k'ofar falonta tanajiyo abinda ke faruwa dukda katanga ta shiga tsakiya, ta girgiza kai kawai tana komawa ciki da fad'in ALLAH ya k'yauta.
Ina wanki ina zubda hawaye, sosai raina ya sosu yau akan abinda Innaro tamin, dukda bawai yaune karon farko da hakan ya faruba, sai dai na yau yamin zafi ainun, har inaji natsani zaman gidanmu, a fili na furta ALLAH kabamu miji muyi aurenmu mubar gidannan鈥?.
Munubiya dabansan tazo wajenba naji ta amsa da Amin sweetheart, wlhy koni yanzu addu'ar danake mana kenan, sai dai banason mutafi mubar innarmu a wannan halin dasu Aryaan鈥?.
鈥渉akane Munu..., karki damu, insha ALLAH munayin aure d'auke innarmu zamuyi ko Abbah ya yarda kobai yardaba wlhy!!鈥?. 鈥榯a k'arashe maganar a harzuk'e鈥?.
Murmushi Munubiya tayi, dan tasan ran 'yar uwar tata yakai k'ololuwar 6aci.
Har muka gama wankin innaro na gidan bata tafiba, bamusan uwarmi takeyiba. dayake girkin gwaggon Haleema nema ranar. ina tsaye a bayan flowers d'in d'akinmu ina goge glass d'in windows naga Abdul yafito d'aukeda tire an jera sabbin kuloli akai, nasan Abbanmu baya gari, dan haka nace, 鈥淎bdul wazaka kaima abinci haka?鈥?.
Yace, 鈥淎unty zan kaima innaro tana falon dady鈥?.
Kai na jinjina masa kawai nace jeka, cigaba nayi da aikina ina fad'in 鈥渟hidai munafurci ai dodone, maishi yakeci鈥?.
Koda na koma ciki sai nake bama Munubiya labari, innarmu dake bayanmu bamu saniba tace, 鈥渢o ina ruwankine wai Munaya?, nifa banason gutsiri tsoma wlhy, wai sai yaushene zaku daina jamin fitina a gidanan ne?鈥?.
A sanyaye mukace kiyi hak'uri innarmu鈥?.
Batace komaiba tashige d'akinta, muduka da kallon tausayi muka bita, dukda tasan ita ake tauyema hak'i amma bata ta6a nuna itace mara laifi, kullum ta amince itace a k'asan kamar yanda kowa ke kallonta agidan.
鈽呪槄鈽呪槄鈽?
Washe gari Abbah yadawo da yamma, duk munyi murnar ganinsa, shima kuma hakan take a garesa.
Sai da daddare suka tara iyayenmu mata meeting shida Dady da baba k'arami.
Abbanmu yay gyaran murya sannan yace, 鈥渄ama wani abune yasaka muka taraku, maganace akan yaranmu mata, Ramlah da khaleesa da Rahaima da Hauwa'u kowa yasan sun fida mazajen aure harma an tsaida bikinsu nanda bayan salla鈥?.
Duk suka amsa da eh.
鈥測auwa to Alhmdllh, yanzu munada sauran yara 'yan mata agidanan ak'alla su 8, kuma duk kusan Kansu d'ayane, dukda su Ramlah sun girmemusu, to wani uzirine yataso na tilas zamu had'awa auren wasunsu danasu khaleesa. shin ko akwai wad'anda a cikinsu sukeda tsayayye? domin a fiddasu?鈥?.
Da sauri maman safara'u tace, 鈥淪afara'u nadashi, dan harma yanason turo iyayensa, amma nace ta dakatar dashi sai angama na yayyensu鈥?.
鈥渢o Alhmdllhi, sai kuma wa?鈥?.
Umma Ruk'ayya ma tace, 鈥淔iddausi tanada tsayayye itama鈥?.
鈥渕asha ALLAH, to bayansu fa?鈥?.
鈥渕amansu yaa hameed tace, 鈥渁i inaga sukenan kam Abban Hameed鈥?.
鈥測anzu su 6 kenan suka rage? to dama Alhaji halliru d'an majalissar datta6ai, nasan duk kunsan abokinane shak'ik'i? to shine yanemi alfarmar nemama 'ya'yansa maza biyu auren biyu daga cikin 'ya'yana, d'aya d'ansane na cikinsa, d'aya kuma d'an yayarsane tarasu tabari yacigaba da rik'onsa. to harga ALLAH nasan yaransa sunada tarbiyya dan haka na amince, amma dukda haka saida nasake dogon bincike akan yaran saboda yaron yanzu ka haifeshine baka haifi halinsa ba, to Alhmdllh suma basuda wata matsala, dan haka mun yanke magana dashi akan suzo saisu za6a acikinsu, wannan shine dalilin dayasa muka taraku kenan鈥?.
Hummm yaufa anzo da Sabon al'amari a gidan namu, nanafa iyayenmu mata suka hau tsugunne-tsugunne, kowa burinta ace d'iyarta aka za6a, harma da iyayensu safara'u dakeda mijin a hannu, ganin sunji gidan maik'one kowacce tafara k'ok'arin gani da fatan 'yarta ta kasance acikin gidan, aiko sai shirye-shirye kowa keyi a asirce, aka fara gyara 'ya'ya.
Mudai a 6angarenmu babu abinda innarmu kemana, hasalima inda taji maganar anan ta barta, komu bata sanarma ba, sai abakin Fauziyya mukejin komai.
Yanda ake shirye-shiryen bak'i takowanne 6angare saika d'auka 'ya'ya. Shugaban k'asane zasuzo, ni abinma mamaki yabani dan kowanne d'aki da nasu shirin, dayake kowane d'aki akwai budurwa d'aya, mu 8ne, su shida kowanne d'aki 1 kenan, saimu mu biyu a d'akinmu, 'ya'yan abbanmu mu 4 kenan, na baba k'arami 2 na Dady 2, gashi biyu za'a za6a acikinmu amma saika d'auka mu duka za'a za6a saboda shirye-shiryen da iyayenmu keyi.
Ranar Asabar (Saturday) kenan takama zasuzo, dan haka muduka 'yan Matan 8 baba k'arami yace muhad'u muyi girkin tarbarsu.
Ni Munaya, Munubiya, Safara'u, Fauziyya, Haleematu, Fiddausi, Zarah, Siyama.
A kitchen d'in 6angarenmu muke girkin, dukda dai iyayenmu sun d'an saka mana hannu wajen tsara kalolin abincin daya dace a tanada. Ni abunma haushi yabani, yanda naga 'yan uwana NATA rawar kai, sai wani k'alk'ale-k'alk'ale akema abinci da drinks na gargajiya damuka had'a.
A raina nace Kodai sune iyayen cin tsiya, ai bazasuci ko quarter d'in abincinnan ba, wannanma ai almabazzaranci ne wlhy, mutun biyu kawai amma anmusu abinci wajen kala 6, banda kuma kayan ciye-ciye irinsu snakes da nau'in nama da aka sarrafa zuwa daban-daban. haka dai muka gama aka kai falon baba k'arami aka shirya, sannan kowa takoma 6angarensu danta kimtsa........鉁嶐煆?
Anan ne za'ayi kece rainin馃憣馃徎馃槃馃弮馃徎鈥嶁檧
Guys kumuje zuwa馃槈馃憥馃徎
One luv馃グ馃グ
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*馃憦馃徎馃槶
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
_Ban yarda wani yaymin amfani da labarin nanba tako wace irin hanya, idan hakan tafaru ban yafeba gsky, ALLAH yabani ikon fad'ar abinda zai amfanar dani da Ku, ya tsare harshena daga fad'ar abinda zai cutar damu baki d'aya._
*_ALLAH ka gafartama mahaifina da dukkan sauran musulmai dasuka kwanta dama, kabama marasa lafiyarmu lafiya馃憦馃徎._*
馃憠馃徎2鈨?
...........Zan iya ce muku fitinar gidanmu ta farone daga tushe, dan kuwa ginannen abune tun zamanin k'uruciyar iyayenmu...
Malam Faruku shine kakanmu, matarsa d'aya Marwa'natu (Innaro), 'ya'ya hud'u suka Haifa a duniya, maza uku mace 1. Auwal, Hameesu, Saffiya, Jafaru.
ALLAH yayi Innaro mace mai mugun son abin duniya, arayuwarta tanason ace komai daga gareta aka fara ganinsa, kokuma wajen 'ya'yanta, sun tsayama 'ya'yansu duk sunyi karatun addini dana boko, sai dai Safiya iyakarta primary aka mata aure. Sukuma mazan duk sunkai matakin babar makaranta (jami'a). wannan yasaka Innaro d'aukar burin duniya ta d'ora akan 'ya'yan, harma matan dazasu aura.
Auwal shine yafara kammala karatunsa, dan haka Malam faruku mahaifinsu yace ya fiddo matar Aure.
Bai wani tsaya Jan rai ba ya gabatar da Ai'sha amatsayin wadda yakeso.
Kai tsaye innaro tace sam bata aminceba, d'anta bazai auri d'iyar buzayeba kuma 'Yar iska, Auwal yayi lallashin yayi rok'on akan fahimtar da ita sonda sukema juna shi da Ai'sha, amma Sam tak'i saurarensa balle ta fahimcesa.
Da farko Malam faruku yasaka musu ido, azatonsa innaro zata sakko cikin sauk'i, amma ganin yanda ta kafe akan bakanta saiya sanya baki da tambayarta dalilin k'in amincewar.
Kai tsaye tace batason su Ai'shar ne, Dan ba'asan asalin suba, sannan kuma 'Yar iskace, shima kuma yasani ai. cikin hikima Malam yaso fahimtar da ita halin k'addara kowa da irin tasa, itama Aishar bayin kanta bane ba, amma tak'i saurarensa shima. ganin abin zai tasamma rashin mutumci yace to aure tsakanin Auwalu da Ai'sha kamar anyi an gama. A wannan lokacin ba k'aramin birkicewa innaro tayi musuba, amma Malam faruku yace tayi tagama, dan hujjarta batada muhimmancin dazai haramta auren Auwal da Ai'sha. babu 6ata lokaci kuma aka fara shirin bikin.
*Wacece Ai'sha?*
Ai'sha d'iyace gawasu buzaye 'yan k'asar Niger wad'anda k'addarar rayuwa ta jawosu zuwa k'asar Nigeria, su biyu kacal iyayensu suka Haifa, Aisha itace babba, sai k'anwarta Rabi'atu, wurjanjan suka shigo k'asar Nigeria, sun fara rayuwane awata tashar mota, inda anan tsautsayi ya fad'ama Ai'sha wani mara imani yamata fyad'e anan cikin tasha da daddare, randa abin yafaru Malam faruku yaje tashar zai bada sak'o akaima wani d'an uwansa dake garin Maiduguri, ya taras anata cecekuce atashar, yayinda Ai'sha da iyayenta ke rungume da d'iyarsu sunata kuka da kururuwa.
Malam faruku yatambayi abinda ke faruwa daga wajen mutanen dasuka zagayesu suna kallo, babu 6ata lokaci matashin saurayi yafad'a masa komai.
Hankalin Malam faruku yayi matuk'ar tashi, danshi mutumne mai kishin al'umma, anan ya d'auki Ai'sha da iyayenta suka nufi asibiti, saboda jinin daketa zuba daga jikinta (Dan bazata wuce 15 ba sannan), duk wata kulawar da yakamata anbama Ai'sha a asibitin, har tsawon kwanaki hud'u tasamu lafiya sarai, kamarma komai bai faruba, sai dai tabo Na zuciya da aka bar mata itada iyayenta. tun suna zaman asibiti Malam faruku ya fiskanci iyayen Aisha basuda wajen zama, dan haka yak'udiri niyyar taimakonsu.
Akwai wani d'aki k'arami ciki da falo dake gidansa, saiya zagaye musu shi da Katanga yamasa gyara.
Tunda aka fara aikin innaro ta tada hankalinta, duk zatonta aure zai k'ara, ganin tana neman tara masa k'asa ya zaunar da ita yamata bayani dallah-dallah, maimakon ta kwantar da hankalinta tunda ba kishiyar bace saima takuma tadashi, tace bazata zauna da iyayen Aisha ba.
Malam faruku yace bata isaba, Dan gidansane babu mai hanashi ajiye Wanda yakeso akuma lokacin dayaso.
Dole badan innaro tasoba su maman Aisha suka zauna agidan, sai dai ko kad'an basajin dad'in zama da ita, kullum gori da cin mutunci take musu, su Aisha kam basuda sakat awajenta, saita koma sakasu aiki tamkar boyi-boyinta. Malam faruku ne ya koyama mahaifin su Aisha sana'a, har shima yasamu rufin asirin rik'e iyalensa dai-dai gwargwado, amma ko kama k'afar Malam faruku baiyiba, lokuta da fama ma shine ke taimakonsa dawasu abubuwan Na rayuwa, musamman d'inkin sitturar su Aisha da wasu matsaloli Na yau da kullum dasukan taso. tun zuwansu gidan Auwal yafara k'aunar Aisha, duk da mahaifinsu ya Sanar musu da komai akan k'addarar da ta fad'ama Aishan kuwa, shekararsu biyu suna soyayya, tun Aisha Na d'ari-d'ari dashi saboda tsoron abinda aka aikata mata har tazo tasaki jikinta dashi, sai dai babu Wanda yasan suna soyayyar sai Rabi'a k'anwarta.
Ana haka kuma Auwal yazo da zancen Aisha zai aura.
To haka dai akayi auren Auwal da Aisha badan innaro tasoba.
Wannan kuma yasakata d'aukar Karen tsana ta d'orama Aisha, kullum cikin zagi da cin mutuncin Aisha take, sosai tazamar mata Uwar miji mai kishi da sarakuwa, ga gorin datake mata akan ita 'Yar iskace, babu wani fyad'e da'aka mata, taje tayi iskancinta an fake da fyad'e an dawo an lik'ema d'anta da asiri, tujara dai iri-iri dai ta innaro.
Aisha tanada hak'uri, ko kad'an abinda innaro kemata bai hanata girmamata ba da bata matsayi irinna uwa, amma innaro bata gani.
Watan aurensu 7 kacal innaro ta samoma Auwal wata yarinya mai suna Mero, mero d'iyace ga wani matashin d'an kasuwa, tun alokacinma ana lissafashi a masu kud'in yankin balle yanzu daya zama shahararre, Auwal bayason Mairo, amma dolensa ya aura saboda innaro tace zata tsine masa.
Shigowar Mairo Yakuma k'untata Aisha a gidan, dan tunkan ta shigo innaro tagama 6ata sunan Aisha dana iyayenta awajensu mairo, shigowar mairo da wata 1 kacal kuma tasamu ciki, wannan fa yakuma k'ara ta6ar6arewar al'amura, gashi sannan ALLAH ya yalwatama Auwal d'in babu laifi, harma yasayi wasu filaye uku shida 'yan uwansa anan cikin anguwar kusada su innaro, amma ba'a ginaba, dan babu kud'in ginin lokacin.
A wannan lokacinne kuma k'addara ta afkama iyayen Aisha, ranar wata alhamis da daddare aka maka ruwa Na tashin hankali, Wanda yay sanadin fad'awar d'akin dasuke ciki suka rasu.
Aisha da Rabi'a sunshiga matuk'ar tashin hankali, hakama Malam faruku, innaro kam ko'a jikinta.
Rasuwar iyayen Aisha yasaka rabi'a k'anwarta dawowa hannunta da zama, akuma lokacinne Hameesu shima yace Rabi'a yakeso da aure. tashin farko innaro ta taka masa birki da kukarin zata tsine masa kuwa. dole yabar maganar auren Rabi'ar yasamo wata Ruk'ayya ya aura.
A lokacinne Mairo ta haihu namiji, zokaga murna wajen innaro da mairo, Malam ma yayi murna, hakama Aisha, dukda innaro tace Na munafurcine. ranar suna yaro yaci Abdulhameed, koda wasa mairo bata ta6a yarda Aisha ta d'auki hameed ba, dan innaro tahana, Auwal yayi fad'an shida Malam harsun gaji.
Rayuwa tacigaba da tafiya tsawon shekaru, zuwa sannan su Auwal sun had'a hannu sun gina filinsu, kowa da 6angarensa, gidanmu yafara yawaita da 'ya'ya, dan matar Hameesu ma ta haihu Namiji Shafi'u, hakama matan gidanmu sun k'aru, dan jafaru ma yayi aure, hakama Hameesu yak'ara aure shima, ga iyayenmu sun kuma bunk'asa, dansu wuce buk'atun yau da gobe, dai-dai gwargwado akwai rufin asiri agaresu, alokacin kuma sai Auwal yakuma auro ta uku, auren iyayenmu yakoma tamkar gasa wajen za6o 'ya'yan manya, dan kuwa Aisha ce kawai d'iyan talakawa acikinsu, tana zaunene kawai da k'arfin ALLAH dakuma Na Malam faruku, saikuma soyayyar mijinta Auwal, amma da dan ta innaro ne da tuni Auwal ya saketa.
Akwaima randa fada ya had'a mairo da Aisha akan Rabi'a ta doki hameed saboda yamata rashin kunya, dukan da mairo taima Rabi'a saiya sa Aisha kasa hak'uri a ranar ta tanka mata, nankuwa mairo tafara zuba mata gori da cin zarafi, da innaro tazo danjin ba'asin rigimar saitace dole Auwal yasaki Aisha, dukda kuma mairo ce mai laifi, Auwal yayta magiya amma innaro tace yaza6a ko ita ko Aishan, babu yanda zaiyi yasaki Aisha saki d'aya alokacin. Hankalin Aisha yatashi matuk'a, dan batasan inda zasu dosaba, tunda basuda kowa a Nigeria, ga innaro tsaye akanta tace atake saita bar mata gidan d'a.
ALLAH ya tak'aita abunne dai-dai sanda Aisha ke fitowa rik'eda hannun Rabi'a kuma saiga Malam faruku yadawo daga kasuwa, nanfa ya tambayi ba'asi, Aisha tasanar masa komai, maidata yayi gidan, yakuma saka Auwal ya maida aurensu atake awajen, sannan ya tabbatar masa ko bayan babu ransa yasake sakin Aysha bai yafeba, kuma inhar innaro tasake sakashi ya saketa itama abakin aurenta.
Wannan shine dalilin dayasa auren Aisha da Auwal bai sake rawaba. rayuwa kuma tacigaba da shurawa. Matan gidanmu 7.
Auwal matansa uku, Aisha (innarmu) Mairo (mama) Sadiya (gwaggon haleema)
Hameesu nada biyu, Ruk'ayya (umma) Hadiza (momy)
Jafaru Nada biyu shima, Suwaiba (maman safara'u) Hafsatu (maman Fauziyya).
Kowacce ta haihu acikinsu, amma banda Aisha, wadda saida sukayi shekara 20 da aure itada Auwal sannan ALLAH yabata ciki, zokiga murna wajen Auwal da ahalinsa, saidai banda matan gidanmu da innaro, dan aganinsu duk sunfi Aisha matsayi, (maman fauziyya) Ce kawai babu ruwanta, dan suna d'asawa da Aisha sosai, ita kad'aice bata raina innarmu ba, dan Yaya ma take cemata.
Babu irin wahalar da Aisha batasha agidanba acikin shekarunan, kullum cikin mata gorin haihuwa dana talauci ake, harma dana batada asali, tundaga kishiyoyinta har matan k'annen mijinta basu raga mataba, kowacce jitake ina wuta tasaka innarmu a gidan, dama ga d'aurin gidi daga innaro suna samu. innarmu bata cemusu komai, saidai tashiga d'aki tasha kukanta, 'ya'yan maman fauziyya ne kad'ai ke shigowa d'akinta, amma sauran duk an hanasu, gashi ta aurar da Rabi'a tuni, itama harta haihu uku ma.
to saikuma ga Aisha da ciki rana tsaka, bayan tagama fidda ran haihuwarma gaba d'ayanta. cikin ikon ALLAH cikinta yakai haihuwa, ranar data haihu saiga 'yan biyu k'yawawa kamarta duk mata, A zahiri matan gidanmu suna k'untatama innarmu ne saboda yanda innaro tagama 6ata Aisha awajensu, a bad'ini kuma suna k'in Aishane saboda tafisu k'yau da komaima Na halittar jiki, (dan cikakkiyar buzuwa Ce) mai k'yawu Na asali, dirarriyar macece doguwa, fara tas, gashin kai, idanu da komai ALLAH yabatasu. Sa6anin su daba haka sukeba. cikin ikon ALLAH kuma saigashi ta haifo 'ya'yanta masu tsananin kama da ita.
Hassana (Munubiya) da Hussaina (Munaya) wad'anda suke matuk'ar kama da juna, kamar Munaya da Munubiya ta 6aci matuk'a, ko Aisha saitayi da gaske take banbancesu, saida suka fara girmanema ake d'an banbantasu tawajen halayya shima ba kowaba, amma Aisha ita tana ganesu kai tsaye a sanan.
Munubiya tanada hak'uri tamkar Aisha, duk wahalar dasukesha wajen yaran gidan bata iya ramawa, saidai tasha kukanta tashare hawaye. sa6anin Munaya da take fitinanniya, bata bari a cuceta, koda anfi k'arfinta saitabi tawata hanyar tarama kuwa, wannan yasaka matan gidan da yara sukafi tsanarta, sai dai kuma basa iya banbancesu itada Munubiya, sometimes Munaya takanyi laifi akama Munubiya a daka, itakuma Munubiya bazata ta6a fad'in ba itaceba.
Ganin hakan yasaka Aisha yima Munubiya shaida saboda aringa banbantasu, amma Munaya Na k'yalla ido tagani sai itama tayima kanta irin ta Munubiya komai da komai, idan sau dubu akama Munubiya shaida ajiki Munaya ma zataje taima kanta, hakama Munubiya takanyi idan anyima munaya, hakan yasa Aisha ta hak'ura kawai harma suka Shiga makaranta, nanma rikicin Munaya bai k'areba, dan saima abinda yay gaba, tajawo fad'a akama Munubiya adaka, hakan kuma bazaisa gobe ta fasaba.
Shekarar su goma Aisha takuma haihuwar 'yan biyu duk maza, Aryaan da Aiyyaan, tundaga lokacin kuma bata sakeba.
Sai dai Munaya da Munubiya suna matuk'ar k'aunar junansu over abinma har saiya Baka mamaki, sannan suna k'aunar mahaifiyarsu da k'annensu, Munaya ce kan shiga idan ana cin zarafin mamansu, amma ita Munubiya saidai taita kuka.
Yanzu haka zancen danake muku shekarunmu 19 nida Munubiya, muna matakin farko a jami'a, munzama 'yan mata, k'yawunmu da tsananin kamarmu da innarmu yasake fitowa, mun fita daban a gidanmu, dan mukad'aine kamarmu daban, Ayyan da Aryan ma duk Abbanmu suka kwaso, wannan yasaka suke kama da 'yan gidanmu.
Tabbas bamajin dad'in zaman gidanmu, saboda k'unci da hantara damuke fuskanta muda mahaifiyarmu awajen Innaro da matan gidan, harma dawasu yaran gidan 'yan uwanmu, amma wasu muna shiri dasu sosai, musamman ma mazan yayyenmu manya, dansu babu ruwansu da gutsiri tsomar cikin gidan.
Gidanmu gidane tamkar gidan hayar daya had'a k'abilu daban-daban saboda yawan rikici, kullum cikin fad'a muke, ba iyayenba ba yaranba, kai kace muna ganin hanjin junane.
Gwargwadon iko akwai hali a gidanmu, dan iyayenmu sun rik'e gidanmu sosai da buk'atinmu, dukda yawa da ALLAH yabamu, bamu rasa ci da sha ba da situra, hakama matsalolin karatunmu, dan kai tsaye zance gidanmu gidan 'yan bokone, kullum cikin gasa da juna ake, burin kowa ace shine gaba, batun ilimin addinima kam Alhmdllh, dan tsaye iyayenmu suke akanmu, har gobe yaa hameed bai daina zama gaban malamai ba balle mu 'yan baya-baya. ak'alla yaran gidanmu munkai mu 43 kuma.
ALLAH yayma Malam jafaru kakanmu rasuwa shekara biyu kenan, innaro Ce dai tana nan daram, al'amuranta sai abinda yay gaba, dan har gobe bata k'aunar innarmu, kuma bata daina cin zarafinta ba agaban kowa da mata gorin rashin dangi.
Hakan yasa kullum cikin buri da k'udirin binciko dangin Innarmu nake, ko itama zata samu 'yancin kanta kamar kowa馃槩.
Wannan shine labarin gidanmu, sai ahankali zaku cigaba da fuskantar ainahin halayen jama'ar gidanmu da aiyukansu, harma da sunayensu馃槉.............鉁嶐煆?
To masu karatu, sai nace yanzufa za'a fara, saiku kasance dani danjin labarin *_RAINA KAMA.... kaga gayya_* dan akwai babban al'amari a gaba, bawai gidan su Munaya kawai labarin ya shafaba, akwai wani lauje cikin Nad'i daga d'ayan 6angaren labarin Na Raina kama.....馃槈 suga gayya ba馃憥馃徎馃槃.
One luv馃グ
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu馃槶馃憦馃徎_*
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎4鈨?
.......Daga ni har Munubiya babu wata kwalliya damukayi, hasalima ni ko mai k'in shafawa nayi, danayo wankanma sainayi kwanciyata na hau barci. sai wajen 1 munubiya ta tadani wai sun iso, dama lokacin duk fashin salla muke nida munu.... (zakusha mamaki idan nace muku dai-dai da prioud yakanzo mana rana d'aya nida hassana ta, kuma musami tsarki tare), tashinai ina yatsine fuska, dan naji haushin tadanin datayi, toilet nashiga domin kimtsa jikina, sama-sama nadinga jiyo maganar Ikram tana fad'in 鈥淎unty wai innaro tace kuzo鈥?.
Cikeda mamaki munubiya ta amsa da to. nima abin yabani mamaki, dan haka nafito da Sauri, 鈥渨ai Munubiya minake jiyowa ina toilet? 鈥?.
Maganarta d'auke da mamaki tace, 鈥渨ai innaro ke kiranmu鈥?.
鈥渘i da ke? kokuma mu duka?鈥?.
鈥渨lhy ban saniba munaya, sai dai munje d'in magani鈥?.
Innarmu tashigo d'akin tana cewa 鈥渨aishin Baku naji innaro ta aiko kira bane?鈥?.
Muka amsa da 鈥渆h innarmu, mune鈥?.
鈥渢o mi kuke jira, kuwuce kutafi mana鈥?.
Babu Wanda yay magana acikinmu muka fita muna mamakin wannan kira Na innaro.
Tun a k'ofar falon baba k'arami mukaga wasu k'yawawan takalma, ga wani k'amshi yacika wajen, wicewa mukayi batareda mun shigaba, dukda mun hango Zarah da Siyama da Fiddausi natahowa cikin matsanancin gayu, saika rantse fita zasuyi wani gagarumin biki.
A k'ofar gidama munci karo da motoci uku duk bak'ak'e wulik, sai dai ta tsakiyar tafi k'yau da d'aukar hankali, garadan samarine majiya k'arfi kusan su 7 tsaitsaye ajikin motocin, duk suna sanye da bak'ak'en suit, daka gansu kasan babu sauk'i, hakan yasa muka fahimci bodyguards d'in bak'inne.
Gida biyu ne tsakanin gidan innaro da gidanmu, dan haka muka Isa da wuri. a tsakar gida muka isketa tana shanyar lawashin albasa. muka gaidata.
Yanda ta saba haka ta amsa mana, amma tace mushiga ciki tana zuwa.
Kusan mintuna 40 muna falon innaro zaune, amma bata shigoba, hakan yasakani tunanin tabas akwai wani lauje cikin nad'i a kiran namu, tashi nayi nalek'a tsakar gidan ta window, amma bata nan. 鈥淢unubiya kinsan Innaro bata gidanan kuwa?鈥?.
Cikeda mamaki tad'ago tana kallona, 鈥渒amarya bata nan?鈥?.
鈥淢unu... Wlhy ko rantsuwa nayi babu kaffara aciki, akwai dalilin kawomu nan鈥?.
A sanyaye Munubiya tace, 鈥渒arki damu Sweetheart, ko mai suke nufi ALLAH ya fisu, dama naga mamansu ya hameed tafito d'azu bayan mungama girki, ai d'an hakkin daka raina shike tsolema ido, *_RAINA KAMA KAGA GAYYAFA_* inji masu iya magana.
Hakane dear.
Daga nan muka zauna shiru kowa da abinda take tunani, har barci ya sace Munubiya, nukuma nahau chart kawai.
A gidanmu kuwa su Siyama ne suka fara Isa falon, tundaga k'ofar falon daddad'an k'amshin turaren bak'in yafara rikitasu, sun shiga da sallama, yayinda sukuma bak'in suka amsa.
Gaskiya masha ALLAH dan kuwa matasan samarine k'yawawa masu aji da gayu, suna kama da juna, hakan zai tabbatar maka da cewa jininsu d'aya. sunci ado cikin wasu rantsatstsun shaddoji gizna, sai maik'o sukeyi, d'aya yafi d'aya sakin fuska.
Su Siyama sun gaidasu cikin shauk'i da zumud'in fatan kowaccensu ta kasance abar za6i.
Sun amsa musu cikeda jan aji da nazartar su, ahaka Fauziyya da Safara'u da Haleematu suka shigo suma, suma dai gaidasun sukayi. Fauziyya da Zarah ne kawai sukayi hankalin tashi su zuba musu ruwa da lemo, sannan suka musu bismillar abinci.
Mai d'an yawan fara'ar ne yamusu godiya, sannan yace, 鈥渢o ya sunan k'annen namune?鈥?.
Cikeda yanga kowacce tafara gabatar da kanta agaresu, yayinda sukuma suka maida hankali sosai wajen nazartarsu, bayan sun gama suma suka gabatar musu da kansun.
鈥淣i sunan Sulaiman, brother d'ina kuma Sa'eed, munji dad'i kwarai da gaske Na tarbar damuka samu daga gareku鈥?.
Murmushi duk sukayi suna nuna farin cikinsu suma, sund'an ta6a hira.
Babu Wanda yadamu da rashin ganinmu acikinsu sai Fauziyya, iyayenmu kuma basusan babumu ba, dansu suna falon Abbanmu suna hira.
Kusan awa d'aya sannan duk suka fito suka barsu dan sud'anci abinci.
Suna fita Sa'eed ya kalli Sulaiman a yatsine, 鈥渕y man nida yaran nan nakula sunada rawar kai, garama mai farin kayannan naga kamar tafisu nutsuwa (Fauziyya)鈥?.
鈥渨lhy gskyarka bro... Amma Kasan dolenefa mucika umarnin dad, tunda yayi rantsuwa akan dolene muza6a acikinsu, kai wlhy mun jama kanmu, ni dama tun maganar farko da dad yamana Na maida hankali naza6o da duk hakan bata faruba gareni鈥?.
Cikin ta6e baki Sa'eed yace, 鈥渨annan kuma kaika Sani malam. amma basuma 8 akace manaba?鈥?.
鈥渆h hakane, amma kamanta ance biyu acikinsu sunada samari鈥?.
A nanma bakin Sa'eed Yakuma ta6ewa. sun d'anci abinda aka ajiye musu, sannan su Abba suka shigo suka gaisa, cikeda girmamawa suka gaida su Abba, hakan yayima Dady da baba k'arami dad'i, sun kuma tabbatarwa yaran sunada tarbiyya, dama basa kokwanto akan zance yayan Nasu.
An musu rakkiya duka Sassan gidanmu, sun Haida iyayenmu mata. ganinsu Yakuma rud'ar da iyayenmu, kowacce addau'arta ALLAH yasa d'iyarta aka za6a, yo wad'annan zuk'a-zuk'an samari haka, ga kud'i ga ilimi, kowacce saida suka ajiye mata kud'i suke fitowa, har innarmu ma.
Tun aiko kiranmu Innarmu taji ajikinta da biyu aka turamu can, amma baiwar ALLAH hakan bai dametaba, tasan dai wata bata aurar mijin wani, dan haka ko'a fuska bata nunama wani bama cikin wad'anda suka je wajen bak'inba.
Saida Innaro takusa awa d'aya sannan tashigo gidan, yinai tamkar ban gantaba, Munubiya kam tanata barcinta, itama sai bata kulaniba tashige bedroom d'inta.
Shigarta baifi da mintuna 3 ba mukajiyo sallama a k'ofar d'akin, nice Na amsa, Basheer yafara shigowa, sai kuma Sulaiman da Sa'eed, irin k'amshin damukaji a k'ofar d'akin baba karami yasani d'agowa dan jinsa anan, hakan ya tabbatar min da sune sukazo gaida Innaro.
Tunda suka shigo idonsu ya sauka a kanmu, sun kasa d'auke kai daga kallonmu.
Cikeda jan aji nace, 鈥渋na yininku鈥?.
Duk suka amsa da 鈥渓afiya big girl鈥?.
Basheer yace, 鈥渒ai Aunty dama kuna nan Ku?鈥?.
Kallonsa nayi nace, 鈥渆h, ana nemanmu ne?鈥?.
鈥渁'a, amma dai ba'asan badaku akaje wajen bak'iba鈥?.
Hararsa nayi, saboda sanin halin shegen surutunsa, 鈥渕alam kaje ka kira musu Innaro ka zauna kana zubama mutane shegen surutu uwa aku鈥?.
Baki ya zum6ura sannan yanufi bedroom d'in Innaro.
Wanda tunda suka shigo yakasa d'auke kai daga kallona, saima zama dayayi kujeraf dake kallona yace, 鈥渙k dan bakwa buk'atar ganinmu kuka gudonan kenan? Sai kuma gashi ALLAH ya kawomu mun ganku, dama ance rabon kwad'o...... koko my man?鈥?.
Murmushi Sulaiman yayi, yace 鈥渉akane wlhy bro, hakanma dasukayi yamana dai-dai鈥?.
Magan ganinmu yasaka Munubiya tashi, Sulaiman yace, 鈥渟leeping beauty kin tashi?鈥?.
d'an waro idanu Munubiya tayi, sai kuma ta kalleni dan neman k'arin bayani.
Innaro takatsemu da fad'in 鈥渢oku kuna ganin bak'i basai Ku tashi Ku basu wajeba鈥?.
鈥渃ikin tsokana Sulaiman yace, 鈥渁'a Granny idan sun tashi wazamu kalla? Sun gudo wajenki dan karmu gansu kuma sai gashi ALLAH ya kawomu har gida鈥?.
Ba k'aramin k'ona ran innaro maganar tayiba (dama an kawomu nanne dankar bak'in su gammu balle su za6emu, amma kuma sai gashi sun gammu anan d'in. Anyi gudun gara kenan.....馃ぃ馃檴).
Bamu tsaya sauraren abinda innaro zata ceba mukayi fitowarmu zuwa gida.
Su Sa'eed sun gaida innaro, anan take tambayarsu kosun za6a acikin wad'anda sukaje gaishesu acan gidanmu.
Sa'eed yace, 鈥渆h mun za6a Granny, amma wad'annan dasuka fita yanzu鈥?.
Caraf innaro tace, 鈥渁i wad'annan anmusu miji shiyyasa su basujeba, sai dai cikin wad'ancan鈥?.
Bahaka sukasoba, amma yazasuyi, sai dai har sukabar gidan basu sanar da wa suka za6aba.
Koda muka sanarma innarmu cewa tayi babu ko mai, karma hakan ya damemu.
鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄
Har tsawon kwana 5 babu wata magana data fito akan suwa bak'in suka za6a, su Abba basuce da kowa komaiba.
Hankalin iyayenmu mata duk atashe yake, kowa takasa kunne taji wacece aka za6a, sai dai babu mai iya tunkarar iyayenmu maza da zancen, dan duk ba suga fuskar hakanba.
Satinsu guda da zuwa saiga bak'i sunzo wai an kawo kud'in aure.
Hankalin iyayenmu fa yakuma tashi, dan ganinsu wani munafurcin akayi shiyyasa aketa k'unbiya-k'unbiya. Nanfa suka shiga 'yan tsugunne-tsugunne Na gulma irinta gidan yawa.
Kwana biyu dayin haka su Abba suka sanar da cewa nida Munubiya sukace sun za6a.
Innaro ce tafara k'aryatawa, sannan tace, Sam bata aminceba, ina jikokin talakawa 'ya'yan bak'in haure suka kai matsayin auren 'ya'yan babban mutun irin sanata halliru, ai k'aryane sannan munafuncine, agabanta su Sa'eed sukace Zarah da Siyama suka za6a. (Zarah k'anwar ya hameed Ce, babanmu d'aya, Siyama kuwa d'iyar momy Hadiza Ce d'iyar dady).
Jin wannan zance yasa kowa ya fahimci akwai munafunci a lamarin, kowa yasan yanda mamansu ya hameed suke da momy Hadiza a gidan, kansu had'e yake. aikam matan gidanmu suka harzuk'a sunata yada magana, harma abin yaso yazama fad'a, innarmu ce batace komaiba, ita cewama Abbanmu tayi dan ALLAH amaida zancen auren kansu Siyamar tunda innaro tace dama su suka za6a.
Banza abbanmu yamata dan yasan innaro tayi hakanne danta k'untatama innarmu, amma tabbas dabakin su Sulaiman sukace 'yan biyunnan suka za6a, shin sai yaushene inna zata bar muzgunama Aisha da munanata a gidannan?, shekara kusan Arba'in ana Abu guda babu sassauci, tunda yake baita6a ganin rana d'aya da innarmu tama innaro koda kallon banzaba bare rashin kunya, sa6anin sauran matan gidan da basa kunyar ya6a mata magana koda ta habaicine.
Kwana kusan hud'u ana d'auki ba dad'i akan wannan zance, saboda akawo k'arshen maganar sai Abbanmu yace su Sa'eed suzo su nuna wad'anda suka za6a da kansu.
Hummm bamusan miya faruba, (konace mi innaro dasu momy hadiza suka k'ulla ba) munga dai sunta murnar zuwansu Sa'eed d'in, sai rawarkan had'a abincin tarbarsu sukeyi, dan ranar su biyu kacal sukayi, kuma abin mamaki wannan karon agidan innaro aka saukesu.
Bayan isowarsu dakamar mintuna 20 sunci abinci sai akace duk muje gidan innaro.
Su Haleematu duk sun rigamu tafiya, mune k'arshen zuwa muda Fauziyya, saidai muna shiga gidan Innaro ta samu mukabi ta k'ofar kitchen nida Munubiya kawai, Fauziyya kuma aka barta tashiga ta falo.
Yanda sukaita zumud'in kallonmu wancan karon a yau ba haka bane, gaba d'aya hankalinsu Na kan Siyama da zahra, abin ya bamu mamaki har sauran 'yan uwanmu.
Tunda mukaga haka duksai muka fice muka koma gida, su Haleematu harda kukansu, mukanmu zukatanmu sun sosu, dan harga ALLAH Sa'eed ya kwantamin arai.
Wanan lamari saida yajawo gagarumin fad'a agidanmu irinma wanda ba'a ta6a yiba, dan saida takai matan gidanmu da 'Yar tone-tone asirinsu yanda suke kulle-k'ulle wani lokaci akan innarmu da junansu.
Sosai ranar saida ran kowa ya 6aci, amma mamansu yaa Hameed da momy Hadiza su wasai sukejin kansu, koba komai sune a sama suke gani, 'ya'yansu zasuje gidan Hutu.
Abbanmu yasamu innarmu yayta bata hak'uri, dan tabbas yanada tabbacin akwai lauje cikin nad'i akan lamarin, tunda su Sa'eed da kansune suka Samar masa za6insu, amma gashi a wannan karon since su siyama ne ba 'yan biyu ba.
ALLAH sarki innarmu sarkin hak'uri, cewa tayi babu komai, dama can su Siyamar ne matansu, Dan haka tunran gini tun ran Zane, suma sauran ALLAH yabasu Na kwarai.
Sosai Abba yak'ara jin jinama hak'uri da tawakkali irin Na matar tasa, abin sonsa, wadda yakejin har duniya ta tashi k'aunarta dabance a ransa, yana sonta harma baisan yanda zai fassaraba, kullum cikin mata k'yak'yk'yawar addu'a yake akan ribar hak'urin datakeyi da kowa agidan har mahaifiyarsa. yana ganin Kimar Aisha sosai da girmanta, tunda suke babu rana d'aya dazaice gawani abun aibu data aikata masa, sai dai abinda ba'a rasaba saboda zomu zauna zomu sa6a, balle shekara kusan 40 ba wasabace.
鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽?
An tsaida bikin Siyama da Zarah dai-dai danasu aunty Hauwa'u, komai kuma ankawo, saura lefe da sadaki kawai.
Ahaka muka koma makaranta inata yak'in fidda Sa'eed daga raina, ALLAH ma ya taimakeni dama bawai yashiga irin cancikin nan baneba.
******
Yau lectures d'in safe garemu, dan haka mukayi shiri da wuri nida Munubiya, a tsaitsaye mukasha kunun da innarmu ta dama mana, Dan yau girkin mamansu ya Hameed ne, idan bata gadama ba sai takai 8 bata kammala ba, har yara saisun makara,
Aiyaan yashigo d'auke da lunch boxs nasu yana tura baki gaba. 鈥渒ai kuma lafiya kake cuno baki uwa na agwagwa?鈥?.
6ata fuska yakuma yi tamkar zai fasa kuka, ya zube lunch boxs d'in saman kujera 鈥淎unty ba mama bace tace wai yau batayi abincin dazamuje dashi makaranta ba, hakama fa jiya abincin dare ta d'umama ta zuba mana, amma damukaje school saigashi a kulan Haneep Indomi ne da kwai鈥?.
Aryaan ya kar6e da cewar 鈥淎LLAH kuma aunty namu tsami yayi kafinma muci, haka mukadawo da yunwa鈥?.
tausayi yaran suka bani, Munubiya tace, 鈥渒uyi hak'uri kunji 2 d'in inna, watarana sai labari ai鈥?.
Kansu suka jinjina mata sukace 鈥渢o aunty鈥?.
innarmu tana jinmu amma uffan bataceba.
Fita nayi batareda nacema kowa komaiba, wani shago dake can k'asan layinmu naje, nasiyo musu yoghurt da cake k'ananu, nahad'o musu da biscuits.
A harabar gidan Na iskesu harsun fito, sauran yaran sunata shiga school bos d'insu da ake kaisu makaranta. School bag d'insu nabud'e Na saka ma kowa nasa, sannan nace ayi karatu da k'yau kunji babys d'inmu鈥?.
Cikeda jin dad'i suka amsa min da fad'in 鈥渢o auntynmu鈥?.
Kumatunsu Na sumbata sannan na taimaka musu suka shiga motar suma.
Ina shigowa munubiya tamik'e tana fad'in 鈥渨ai ina kikaje? kinsanfa jarababben lecturer d'inanne zai shigar mana yau鈥?.
鈥渟orry sweetheart tashi muje鈥?.
Dubu 1 innarmu tamik'o mana, kar6a mukai muna mata godiya, muka fito tana binmu da addu'oin fatan alkairi.
Mun lek'ama su Siyama, kowacce sai tace batada lectures d'in safe, fauziyya da Feedausi ce kawai muka tafi, dansu duk department d'inmu d'ayane..........鉁嶐煆?
One luv馃グ馃グ
*_ALLAH ka gafartama iyayrnmu馃憦馃徎馃槶_*
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎5鈨?
...........Wajen 4pm muka fito daga cikin makaranta, mu 6 ne yanzu, sa6anin d'azu damukazo mu hud'u, bayan tahowarmu Safara'u da Haleematu suka taho suma, duk da mun rigasu gama lectures sai muka jirasu suka fito muka rankayo tare domin tafiya gida, bamu samu school bos ba, dan haka muka da6o sayyadarmu har zuwa babban gate, muna tsaitsaye abakin titi, tareda wasu daga cikin tsirarun d'alibai irinmu, tundaga nesa muka hango tahowar motocin da uban gudu, saika d'auka sukad'aine akan titin saboda gudun dasuke tsulawa tamkar zasu tashi sama. duk baya muka matsa, dan tabbas wad'annan suka sameka babu abinda zai hanasu takeka su wuce batareda sun damuba.
Tamkar wucewar iska haka suka dinga gittamu, jikake shuuuu!! shuuu!! shuuu!!.
Furicin wani mayshin saurayi dake jingine jikin motarsa yazo d'aukar wasu 'yan mata biyu dake gefenmu 'yan matan sunada jin kan masifa, ko'a makarantar bakowa sukema maganaba, department d'inmu d'aya dasu amma ko kallo basu isheniba, dan ko sallama bata ta6a had'ani dasuba..
Saurayin yabi motocin da kallo yana fad'in 鈥渢ab ashe *_GALADIMA!_* yashigo gari kenan?鈥?.
鈥淒a gaske yaa Usman?鈥?. 鈥榙'aya acikin 'yan Matan tafad'a cikin matuk'ar zumud'i鈥?.
Yace, 鈥渄a gaske mana baby, baga motocinsa kuna ganin sun wuceba鈥?.
Dan danan suka shiga murna, kai kace an musu albishir da aljanna ne.
Baki na ta6e inajan k'aramin tsaki. Fiddausi tace, 鈥渢o waye shi galadima d'in?鈥?.
鈥渙ho musu鈥?, 鈥榗ewar Munubiya鈥?.
Budurwar dake tsaye d'ayan gefenmu itada saurayinta suna jiran abin hawa suma tace, 鈥淕aladima d'an Sarki kenan, *Yarima Sameer!鈥?*.
鈥渉umm lallai kuce manyane, shiyyasa suke gudun da kosunbi takan talaka babu abinda za'ayi鈥?. 鈥榗ikeda 6acin rai nake maganar鈥?.
Dariya su siyama sukayi suna fad'in 鈥渢oke ina ruwanki?, k'asarfa tasuce, sai yanda sukayi da ita, tsakaninmu dasu saidai mu hangesu cikin mota ko ranar hawan salla鈥?.
Dogon tsaki nakuma ja tareda kauda kaina daga garesu na maida hankalina wajen tare wata taxi dake gabatomu.
A motama firar dasu Haleematu sukaitayi kenan, ta Galadima ne ko uwarmi ne ma Na manta. nidai uffan ban kuma tofawaba, hasalima haushi hirar tasu takoma bani, dan mai taxi d'in yasaki baki sai wani basu labarin Galadima d'in yakeyi dakuma kwarzan tashi, earphone na jayo a cikin lady's bag d'ina na manna a kunne danma nabar jinsu gaba d'aya.
Saida muka iso gida sannan Fauziyya dake kusa dani ta zungureni, d'agowa nayi Na kalleta sainaga duk sun fice, bance komaiba nafito nima.
Mun iske innarmu bata nan, saisu Aiyaan kawai zaune a falo suna kallo, shigowarmu yasasu tasowa da gudu suna mana oyoyo, muma mun taryesu da murnarmu, Munubiya tace, 鈥淎ryaan miyasa baku cire Uniform ba kukayi wanka?鈥?.
鈥測o aunty mun dawo munga Innarmu bata nanane鈥?.
Nace 鈥渋nnarmu bata nan? to ina taje?鈥?.
鈥渕uma bamu saniba aunty, munje kuma kitchen bamuga abinci ba, kuma yunwa mukeji鈥?.
Munubiya tace, 鈥測a salam, kujira ina zuwa鈥?.
Fita tayi, babu dad'ewa sai gata tadawo cikin damuwa, ina cirema su Aryaan Uniform, Na kalleta ina fad'in 鈥渕ike faruwa Munu...? Ina abincinne?鈥?.
Kwallar idonta ta share, ta zauna bisa kujera sannan tace, 鈥渘aje mama tace wai innarmu ta d'auka abinci tatafi dashi hospital, dan haka shine rabonmu鈥?.
Raina a 6ace na mik'e zan fita, da sauri munubiya ta ruk'oni, 鈥減lease Munaya, kibarta kawai, yakamata mu kira innarmu muji waye a hospital? Inaga wannan yafi komai muhimmanci nake gani akan abinda mamar tamana鈥?.
鈥淗aba Munubiya, wannan wane irin rashin mutunci ne, wai mi Matan gidannan suke tak'ama dashine? Idan suna tak'ama da Ubanninsu muma ai nan gidan Ubanmune ko, yanzu ace yarannan kamar su Aryaan su dawo school tun 3 amma ahanasu abinci, wannan wane irin zaluncine? Kisakeni kawai naje naci kutumar uban matarnan munubiya, wlhy sai dai yau Abba yace nabar masa gidansa鈥?.
鈥淎'a munaya, duk hakama bata tasoba, idan hankali ya6ata hankali ke nemosa, bai kamata mutaru muzama d'ayaba mu da su. bara kawai naje kicin d'in Na dafa mana wani abun mai sauk'i, kiyi hak'uri dan ALLAH, kinga innarmu bazataji dad'iba idan tatarar da faruwar hakan鈥?.
Badan raina yaso ba Na hak'ura, saman kujera nakoma Na zauna ina huci, nikad'ai nasan minakeji a zuciyata.
Munubiya tafita dan nema mana abinda zamuci, nikuma Na d'auki waya domin Kiran innarmu naji abinda tajeyi asibiti.
Harta katse bata d'agaba, nakuma kira akaro Na biyu sannan ta d'auka, gaisheta nayi da tambayar mitajeyi asibiti?.
Daga can tace min Nafisar mama Rabi'a Ce jikinta ya motsa yanzu hakama jini ake buk'ata amma an Gaza samu, gashi yaa marwan dayakan bata jinin baya nan yayi tafiya shida Abbansu.
Hankalina a tashe nace 鈥渋nnarmu ganinan zuwa yanzunnan insha ALLAH, kuna general hospital ne?鈥?.
鈥渆h muna nan鈥?.
鈥渙k insha ALLAHU ganina zuwa鈥?.
'Dakinmu nashiga da Sauri nad'an watsa ruwa a tsaitsaye saboda naji dad'in jikina, komai ban tsaya shafawaba Na zira doguwar Riga jallabiya Na fice da hanzari. A k'ofar fita falo naci karo da munubiya d'auke da babban faranti tazubo spaghetti tanata turiri.
namatsa baya da Sauri INA fad'in sorry, munubiya bara naje asibitin wajensu innarmu, wai jikin feena ne ya motsa kuma ana buk'atar jini, gashi yaa marwan sunyi tafiya da abba鈥?. Munubiya tace, 鈥渢oko Na juye mana abincin a kula mu tafi gaba d'aya?鈥?.
Nace, 鈥渁'a munu... Ki zauna dasu Aiyaan bara naje ni kad'ai, baikamata mubar wajen ba kowaba鈥?.
鈥渢o shikenan, yanda akayi ki ta6oni awaya, amma in kunkai dare zakuganmu muma, abincinfa?鈥?.
鈥渉umm munu bar abincinnan, banida wata nutsuwar cinsa, saina dawo鈥?.
Ban jira amsarta ba nafice. ALLAH ya taimakeni INA fita nasamu napep. Mintuna kad'an muka isa hospital d'in, kud'insa na biyashi nashige da hanzari ina k'ok'arin kiran innarmu.
Babu dad'ewa kuwa ta d'aga, nace mata gani acikin asibitin. Kwatance tamin na inda aka kwantar dasu 6angaren masu sikila.
A rikice na iske innarmu da mama Rabi'a, saboda jikin feena ya motsa mata sosai a wannan karon.
Nace, 鈥渕ama yanzu mi ake cikine?鈥?.
鈥淩ashin jininne matsala yanzu Munaya, sunce kuma anemoshi da gaggawa, to dama can jinin Fadeel baya yimata shiyyasama ko gwadasa ba ayiba, Marwan dake bata kuma sunyi tafiya da abbansu鈥?.
鈥渕ama ina zuwa, bani takardar da suka baku鈥?.
Mik'omin tayi nafita da saurina. dukna rikice inata kai kawo dan ganin ansami jinin, amma har magriba ta rufa ba a samuba, saboda jinin feena yanada wuyar samu, ana cikin kiraye-kirayen sallar isha'i saiga Ayusher ta iso itama, dama an barta a gidane saboda babu kowa, to takasa hak'uri tabiyo sahu, da ita muka cigaba da shiga da fita, saida aka fito sallar isha'i ALLAH yasa aka dace da samun leda 1, saura 1, dama biyu suke buk'ata. ana cikin d'aura mata saiga Munubiya ita dasu Aryaan da kulolin abinci.
Koda aka gama sakawa sai muka koma Neman d'ayar ledar data rage, yanzu harda munubiya muke tare.
Muna a lab d'inne muna shawarar ko a d'iba namu jinin idan zaiyi babu damuwa. Takun takalman damuka jiyo yasamu juyawa harda likitan da maganarsa takatse bisa k'ok'arin bamu amsa dayakeyi. wani ni'imtaccen k'amshine ya iso hancinanmu tunkan mamallakin turarenma yakai ga isowa inda muke. d'auke kaina nayi na maida ga mai d'ibar jinin.
Likitan naga yafara gyara kujera yana fad'in 鈥渄ama yalla6ai ya shigo gari yau? Ni nama manta yaune ranar dayake bada jini鈥?.
Bai samu mai bashi amsaba a cikinmu har tawagar Wanda yakira yalla6ai suka iso wajen.
Munubiya da Ayusher suka matsa gefe saboda wata uwar tsawa da masu take masa baya suka daka mana, nikam koma motsawa banyiba bare nasan ALLAH yayi ruwansu awajen, saima baki dana ta6e na d'auke kaina daga saitin dasuke.
Bulala d'aya daga masu jajayen rigunan ya d'aga da nufin zubamun.
鈥淲anda suke kira Yalla6ai dake zaune a kujerar da doctor ya ajiye masa ya d'agamasa hannu da Sauri, alamar karya dakeni鈥?.
Cikeda girmamawa yace, 鈥渁ngama zaki s.........鈥?.
Hannu Yakuma d'aga masa alamar baya buk'atar kirarin.
Baki nakuma ta6ewa sannan na ra6a ta gefensu nafice, banga fuskar Yalla6ai d'in nasuba, saboda ya juyamin bayane ni, sananan shima tunda yashigo bai kalli kowaba a lab d'in, yanata aikin danna wayarsa, kuma baiyi magana ba, ko doctor da Norse's d'in da suka gaidashi hannu kawai ya d'aga musu, kuma ko d'agowa baiyiba yanata aikin danna waya kai kace zai danno hanyar zuwa aljannane aciki.
Waje na dawo nayi zamana ina cigaba da game a waya, su Munubuya dai suna cikin, bansan uwarmi suka tsaya yiba awajen.
Kusan mintuna 40 saigasu sunfito, takun takalmansu kawai naji, amma ban d'agoba, sai k'amshin turarensa daya cika illahirin wajen, saikuma gaisuwar da mutane keta faman zubewa sunayi masa, ko sau d'aya banji ya amsaba.
Tsaki naja inamaijin haushin wannan mutumin, to wayema shine? dayakema mutane wannan jinkan., motsooww aikin banza kawai.
Tabbas yaji tsakin da akayi, hakanne yasakashi d'ago k'yawawan idanunsa yakai duba saitin Inda yajiyo tsakin, akan *munaya* dake zaune bisa kujerun dake Jere awajen ya sauke su, sai dai baya ganin fuskanta sosai, saboda ta duk'ar da kai tana danna waya, kuma gyalen jallabiyarta yarufe mata Rabin fuska, ita kad'aice zatayi wani motsi awajen suji, dan tafi kusanci da Inda suke tsaye.
Janye idanunsa yayi kawai daga gareta, yay saurin d'agama bayin dake k'ok'arin tafowa gareni hannu. Cikin Wata tattausar murya mai aji dake cike da k'asaitar masu isa najiyo yana fad'in 鈥淏ayta kawai鈥?.
Cikeda girmamawa bawan yace, 鈥測a shugaba tsaki tayi fa鈥?.
Shiru yay kamar bazai tankaba, saikuma najiyo yace, 鈥渒asan dawa take?鈥?.
Bawan girgiza kai yayi alamar a'a.
Bai sake cewa komaiba yay gaba suka bishi a baya.
'Dago ido nai nabi bayansu da kallo, sainaga sun nufi 6angaren mata masu haihuwa.
janye idona nayi ina fad'in 鈥渒adaiji dashi Malam, kana fama da Girman kai kamar wani Sarki? Abinma dariya ko (R) bai iyaba, wai bayta鈥?.
Dai dai nan su Ayusher suka iso cikeda farinci, hannunsu d'auke da ledar jinin
Cikeda jin haushi nace, 鈥渨ai uwarmi kuka tsaya yi acikin lab d'inne?鈥?.
鈥淯warmu ta gode鈥?. 鈥? cewar Ayusher鈥?.
Munubiya kuma tace, 鈥渮aman namu aiko yayi amfani, tunda gashi mun samo sauran jinin ko鈥?.
Na kallesu da mamaki, 鈥渋na kuka samo jinin kuma to?鈥?.
鈥淕aladima ya bayar鈥?.
Cikin ta6e baki nace, 鈥渕iye kuma Galadima? A inama kukaga wani Galadima kome ma kukace?鈥?.
鈥渨anda yashigo muna cikifa, ai Galadima ne (Yareema Sameer d'an sarki)鈥?.
Ido na waro waje, 鈥渨ai kuna nufin wannan mai shegen girman kai d'in dama shine Galadiman? kenan munu.... shine yawucemu d'azu munfito makaranta?鈥?.
鈥渒warai kuwa sweetheart shine, kuma wlhy bashida Girman kai kamar yanda kike zato ko Sis.. Ayusher? 鈥?.
鈥淲lhy kuwa hakane Munu..., ashe duk k'arshen ko wane wata saiyazo asibitinan yabada jininsa gamasu buk'ata, gashi jinin nasa mai irin wahalar samu d'inanne irinna feena, kai mutuminnan yayi wlhy, Sarauta ba karya baceba, danyau naga tsantsar sarauta da mulki da k'asaita ajikin Galadima, yanzu haka zai zagayane yaduba marasa lafiya鈥?.
Harara na ballama Ayusher daketa zabga surutu uwa aku, na warce jinin daga hannun munubiya ina fad'in 鈥渋dan kun gama shirmen kwa taho鈥?.
Kallo suka bini dashi, Ayusher tace, 鈥淎nya yarinyarnan batada aljanu?, ke kowama bai mikiba?, yanzu nan duk had'uwar Galadima Munaya tana nufin bai burgeta ba kenan?鈥?.
Dariya Munubiya tayi, sis... Ayusher har yanzu baki gama fahimtar Munaya ba na lura, kyagama abinda yafi haka indai daga wajentane. Yanzu hakama tunda kikaji tace haka ko sau d'aya bata kalleshiba wlhy bare tasanma kalarsa. kinga muje kinji.
鈥渉umm aiko wlhy inabata kalleshiba anyi babu ita kuwa, ruwa ta shata kuma, yo kobabu komai aina bada koda labarine nace nata6a ganinsa ido da ido ko鈥?. 鈥榗ewar Ayusher鈥?.
Dariya kawai Munubiya tayi, taja hannunta suka tafi.
Sanda suka iso harma an fara k'ok'arin sakama feena jinin, dama wancan yak'are.
Duk muna zaune a k'ofar d'akin bisa kujerun wajen, Aryaan da Aiyaan duk suna jikin mama Rabi'a barci ya d'aukesu, fadeel na kusada innarmu yanacin abincin dasu Munubiya suka kawo, zama nayi kusada fadeel d'in na saka hannu nad'au cokalin dayake cin abincin ina fad'in bro... nimafa yunwarnan nakeji, rabona da abinci tun kusan 1 danaci a kafteriya na makaranta鈥?.
Kallona yayi yana cewa 鈥渟annu da k'ok'ari sis...., shiyyasa gakinan tsula guda bak'ya gaba bakya baya keda munu....鈥?.
Cokalin nakai zan kwala masa a kai ya kauce yana dariya, nima dariyar nayi na d'auki kular abincin na k'ara mana.
Muna cikin ci Ayusher ma tamatso tace zataci, munci mun k'oshi sannan muka gyara wajen, mama da innarmu ma sukaci, dan zuwa yanzu duk mun sami 'Yar nutsuwa.
Kusan 10pm saiga Abbanmu shida baba k'arami, duk muka gaidasu suka tambayi mai jiki, innarmu da mama Rabi'a suka amasa musu da sauk'i.
Har d'akin suka shiga, suka duba feena daketa barcinta, sannan sukace muzo mu tafi gida, za'a bar innarmu da mama Rabi'a su kwana.
Saida safe mukai musu muka fito, Fadeel ya d'akko Aryaan, baba k'arami ya d'akko Aiyaan.
Saida muka fara sauke Ayusher da Fadeel gida sannan mukuma muka wuce.
Mun tarar gidan tsitt alamun duk anyi barci, saidai masu wayar dare da samari irinsu aunty Ramla, saikuma masu charts.
Abbanmu da baba k'arami suka d'auki su Aiyaan, har d'akinsu suka kaisu sannan suka fita.
Muma shirin barci mukayi muka kwanta cikeda kewar Innarmu, muna kwanciya muka kirasu da k'arajin mai jikin sannan muka tafi duniyar barci muma, dagani har Munubiya babu mai wani saurayin da zamu 6ata lokaci wajen yin hirar dare...............鉁嶐煆?
Kumuje zuwa my guys馃ぉ馃憥馃徎
Gobe idan ALLAH ya kaimu baza kujiniba, inada wani d'an uziri, sai Monday idan ALLAH ya kaimu kuma.
https://chat.whatsapp.com/K1qwmMusX7ILDLATGSvfHJ
*_RAINA KAMA........ FANS CLUB_*
_Duk Wanda yasan yana karanta wannan buk d'in ya garzaya yanemi link Na RAINA KAMA FANS CLUB, a wannan gidan kawai zan dinga posting a halin yanzun, awannan karon bazan turama kowa buk ta PC ba, narigada nayi rantsuwa. Amma annan zaka iya samu da faro, sannan inhar ba'a tattaunawa akan novel d'in zanyi waje da mutum babu ruwana, kuma kar a turomin kowanne novels acikinsa Dan ALLAH, inba hakaba zan fidda mutum ko Yaya nake dashi馃檯馃徎, nabud'e gidanne saboda anan kawai zan dinga posting yanzu, sai wasu groups dabasu wuce 3 ba._
Ina fata zaku bani had'in kai please, inba hakaba ALLAH zai koma Na kud'ine saboda tsaro ba tsoroba馃槑馃ぃ
One luv馃グ馃グ
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu馃憦馃徎馃槶_*
[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
_____________
*_ASSALAMU ALAIKUM_*
_Jiya da daddare akaita kirana mutane Na tanbayata Yaya jiki, tun ban fahimci maganarba hardai nafara tsarguwa nayi tambaya. Dan sai kira kan kira ake jeramin, wata take sanar dani taga wani posting ne yana yawo wai za'amin CS. babu shiri nabud'e data naga mike faruwa, group d'in farko dana bud'e sainaci karo da wannan posting d'in mutane nata comments, nabud'e nabiyu ma hakan dai._
*_Assalamualaikum Alaikum,Dan Allah kuyiwa billyn Abdul(ma rubuciyan RAINA KAMA. Adua'baby ya mutu a cikin ta zaa cire Mata Shi yanzu_*
_sai daga baya nakejin Bily galadanci ce batada lfyar, amma wata ta maida zancen haka saboda sunan namu yazo d'aya, to ALLAH yabata lfy itama._
_sannan ina shawartar jama'a Dan ALLAH kuringa nutsuwa wajen tantance Abu kafin Ku yad'ashi, domin wadda tayi wancan write up d'in ta zaunane ta tsara nata son zuciyar, wadda tayi posting d'in farko akan ciwon Bily galadanci sunan Bily tasaka ba nawaba, itakuma ta canja nata tsarin tashiga ya d'awa, ALLAH ya shiryar damu, yakuma bama marasa lfyarmu lafiya._
*banyi niyar posting ba yau, amma ganin wancan write up d'in yana cigaba da yad'uwa yasani dole yi Dan na warware muku zancen.*
______________________________
馃憠馃徎6鈨?
.......Bamusan abinda yafaruba, mukaji 'yan gidanmu suna k'ananun magana da safe, wai girkin jiya na dare da mamansu yaa hameed tayi sai asararsa akayi, girkin yay d'anye yak'i dahuwa, kuma a gas tayi girkin bare ace iccen yabata matsala, gashi kuma normal gas d'in yake aiki.
Muna cikin yima su Aiyaan shirin school muka fara jiyo hayaniya, sai da muka gama musu shirin sannan muka fito, cirko-cirko muka iske 'yan gidanmu, yayinda mamansu yaa hameed keta zabga masifa. tana fad'ama abbanmu wai mune muka mata kwari shiyyasa jiya abinci yay mata d'anye danta hanamu abinci, kuma gashi yanzuma tasaka doya amai tak'i soyuwa.
Ni dariyama taso bani wlhy, wai mune muka mata kwari, to miye kwarinne ma datake magana a kai? danni bamma sanshiba.....
Maganar Abbanmu ta katsemin tunanina.
鈥? 'Yan biyuna kuzo nan naji kunji鈥?.
K'arasowa mukayi kusada abbanmu harsu Aiyaan, ya kallemu cikeda kulawa, 鈥渉aba 'yan albarka mike faruwa haka?鈥?.
Cikeda rashin fahimta nace, 鈥淎bba a ina?鈥?.
鈥渉aba twins d'in Abba, bakuji mi mamanku take fad'aba? abinci yamata d'anye jiya da yau鈥?.
鈥渁mma Abba Dan abinci yayi d'anye kuma sai ace mune? Kagafa jiya munama asibiti bamuci abincin dareba agida, darana ma mama hanamu tayi tace innarmu tatafi da kasonmu asibiti, haka muka dawo muka iske su Aryaan sunajin yunwa, sai Munubiya Ce tamana girki, kuma tayi takai mana wani asibitin, ni wlhy Abba bammasan wani kwari dasuke maganaba akai, wannan ai canfine, tunkuma zamanin da aka barsa鈥?.
鈥渃anfin uwarki, kujimin munafukar yarinya, inbakune kukayi muguntarba uwarwaye yayi, to wlhy ahir d'inku, ba 'yan biyu ba ko 'yan gomane ni ubanku zanci a gidannan.......鈥?
Afusace Abba yace, 鈥渢o ai gani, saikizo kici ko, ai gaskiyama yarinyarnan tafad'a, wannan canfine kawai, dan abinci yayi d'anye saikuma a fassarashi dawani Abu daban, haba Dan ALLAH, saikace wata mara ilimin addini? Karna sake jin wannan maganar, inba hakaba rankowa zai 6acine a gidannan鈥?.
Yana gama fad'a yabar wajen. muma ganin haka muka tasa su Aiyaan gaba muka koma 6angarenmu. duk da nakasa fassara mi mama ke fad'i hakan yamun dad'i, koba komai dai ai ALLAH yamana sakayya da hanamu abinci datayi muda wad'anan k'ananun yaran da basu da alhakin kowa.
Yanzuma munubiya Ce ta dafo mana indomi mukaci, sanan ta zubama su Aiyaan a kulolinsu Na makaranta, suna tafiya muma mukayi shirin tafiya School.
Bamu tsaya jiran sauranba mukayi gaba saboda zamu biya ta asibiti, kuma munsan acikinsu babu mai binmu, harmun fita saiga Fauziyya tabiyomu, itama zataje taduba feena d'in.
Alhmdllh munma tarar an sallamesu sunata shirin tafiya gida, mukaima feena sannu, ta amsa tana fara'a da tambayarmu ya makaranta?. mukace gatanan zamu tafi.
Bamufi mintuna 30 ba muka fito, Fadeel ya d'aukesu, mukuma muka wuce school.
A mota Munubiya take bama Fauziyya labarin ganin Galadima damukayi jiya a asibiti, ko sau d'aya ban saka musu bakiba har muka sauka.
鈽呪槄鈽呪槄鈽?
A wannan karon har mamansu yaa hameed tagama girkinta Na kwana biyu asarar abinci akaitayi, Dan kullum d'anye yake mata. hakan yasa taita sakin habaici agidan itada muk'arrabanta irinsu momy hadiza,.
Maman Fauziyya ta sanar ma innarmu komai tun randa taje duba feena agidan mama Rabi'a, Dan haka Innarmu tayi kunnen uwar shegu dasu, tamkarma batasan da ita sukeba balle ta nuna tama fahimci zancen nasu.
Innaro ma tazo tayi tata tsiyar San rai, tabi duk ta zagemu dacin mutuncin innarmu, koma fitowa innarmu hanamu yi tayi, har Innaro tagama tafice. Matan gida najin dad'i.
鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄
Haka rayuwar tacigaba da tafiya, yau da gobe kayan ALLAH har gashi azumi ya rage saura kwanaki uku kacal a fara, Dan haka musulmai NATA shirin tarbar wannan wata mai tarin albarka da falala.
Kasuwanni sun cushe saboda yawan hada-hada, duk da 'yan kasuwa sunyi taiyar tasu ta k'arama abinci kud'i, maimakon su sassauto bayin ALLAH su sami sauk'i (ALLAH ka shirya 'yan kasuwarmu subar wannan hali dai).
A 6angaren gidanmu ma iyayenmu maza duk sunyi shirin, Dan dukkan wani abun buk'ata an tanadeshi, sai abinda ba'a rasaba dazai iya lalacewa idan an ajiye, wannan anbarsa yayunmu maza su ringayo cefanensa kullum kamar yanda aka saba.
Itama Innaro an ajiye mata dukkan abinda zata buk'ata, dukda kullum daga gidanmu ake kaimata abinci, safe yamma da dare, kuma dolene kowane 6angare sai sunkai nasu.
Muma a 6angarnmu munyi dukkan namu shirin, dukda abin zai had'e mana da zuwa makaranta, hakan yasa nake tausaya mana, gashi ana tsula rana mai zafi kuma.
Alhmdllh yau ta kasance Alhamis, kuma yaune ake saka ran ganin wata atashi da azumi washe garin juma'a.
Har zuwa 9pm kunnen kowa naga redio da talabijin, jira kawai Muke muji sanarwa daga sarkin musulmai. sai wajen 9:30pm sanan aka Sanar da ganin wata, duk wani Muslim yana cikeda d'okin fara azumin watan Ramadan da zamu Shiga goma ta marmari (inji hausawa馃槀).
Tun alokacin duk muka d'auki niyya, kasancewar girkin innarmu ne tayi shirin tafiya d'akin Abbanmu, muma tace mu kashe TV muje mu kwanta kar atadamu da asuba kuma muzo muna k'unk'uni.
Badan mun soba muka kashe mukaje mukai shirin barci muka kwanta da addu'ar abakunanmu.
Aiko da asuba dak'yar innarmu ta iya tashinmu mukai sahur, tea kawai muka shama, dama mu bama sahur da abinci nida munubiya, garama ita wani lokacin takan had'a da kunu ko fura.
Bamu kwantaba saida akayi sallar asubahi, still kwanciya muka kumayi, sai 8 innarmu ta tadamu, kasancewar yau saima 10 mukeda lecture, kuma zamu fito 12 ne.
Tunkan aje da nisa azumin yafara garani, dak'yar Na daure aka kammala lecture muka fito, amma badan Na fahimci komaiba nidai yau.
Su Munubiya sai dariya suke mini wai Raguwa, nidai ban kulasuba, Burina kawai naga mun Isa gida Na kwanta.
Tunda muka dawo school nazube a falo k'asan carpet, ban sake Sanin duniyar danake cikiba saida munubiya ta tadani nayi salla, Ashe harsu Aryaan sun sako masallacima inata barci, sallarma dak'yar nayita atsaye, INA kammalawa nakuma kwanciya.
鈥渙h ni Aisha, wai Munaya mikikeson maida kankine? yanzu azumin kikema langa6e haka? saikace yau kika fara azumi a rayuwarki?鈥?.
鈥淎LLAH innarmu bazaki ganeba, nidai ALLAH yasa akira salla da wuri鈥?.
Munubiya dasu Aiyaan suka sakamin dariya. 鈥淎unty yanzufa k'arfe 2 ma, sauran kusan awa 5 dawani Abu asha ruwa鈥?. 鈥楢ryaan yafad'a yana dariya鈥?.
Harara Na Dalla masa INA fad'in 鈥淎LLAH inbaka rife wannan bakin naka mai gajerarrun hak'oraba zaka dakune, Dan k'aniyarka kaiba yanzu kagama lodama cikinka abinciba?鈥?.
Aunty nimafa Dan innarmu bata tadamu baneba kawai, amma insha ALLAHU gobe zamuyi ko Aiyaan?鈥?.
cikin zumud'i Aiyaan yace, 鈥渆h mana, muma zamuyi bro鈥?.
鈥渒uma wlhy yaro bai Isa karyashiba, garama karku d'auka鈥?.
Munubiya tamik'e tana dariya, 鈥渋mm innarmu bara kiga naje nafara rage aikin, miza'ayi?鈥?.
鈥渒i fere doya kafin Na fito, Munaya tashi maza kuje, kekuma ki gyara kayan miya鈥?.
鈥渨ayyo innarmu ki tausaya min mana鈥?.
鈥渕ukuma mu kashe kanmu tunda bama azumin ko?鈥?. 鈥榗ikeda gatse tayi maganar鈥?.
鈥渁'a innarmu, bara naje kodaga zaune sainayi鈥?.
鈥渒imayi daga kwance, raguwar banza kawai, ai mijinki yashiga uku, wataran sai yadawo aiki baki gama abinciba鈥?.
Baki Na tura gaba sannan nafita.
Mun rage aiki sosai kafin la'asar, sai bayan sallar la'asar d'in 'yan Matan gidanmu suka shishshigo kitchen d'in kamar yanda aka saba, dama duk shekara gaba d'aya muke had'uwa a kitchen d'in 6angarenmu ayi abincin bud'a Baki, saidai saboda munada yawa akanyi time table saboda a rarrabu kowa da ranar da Zai taya mai aikin ranar.
Da yake aikin yawane dandanan muka kammala kafin 6, a can tsakar gida aka shinfid'a manyan tabarmi bayan an tsaftace wajen, duk azumi gaba d'aya muke had'uwa asha ruwa dama anan, kafin matar ya hameed ta rasu har itama anan suke zuwa suyi bud'a Baki.
Bayan mun had'u mun gama shirya komai kowa yanufi 6angarensu ya watsa ruwa kafin akira salla, dolene kaga jama'ar gidanmu aranar mu burgeka, babu fad'a babu hantarar juna, (yo kowa azumi yagama cin k'aniyarsa馃ぃ馃お).
Kasan cewar babu wuta ya kamal yazuba fetur a Gen... Ya tada, kowa yayi wanka saiyayi shirinsa da alwala yadawo tsakar gida ana jiran kiran salla, yara dabasuyi azumi baneba suketa shargallensu a tsakar gidan.
Yanda na zube a tabarman tamkar mara kashi yasaka yaa Shafi'u fad'in 鈥渒ai kekam anyi raguwar yarinya wlhy, nasan dai Munaya Ce, Dan Munubiya tafiki jarumta鈥?.
Dariya wad'anda ke wajen sukayi, yaa Naseer yace, 鈥済askiya mijinki yaga banu, yo idan yayi wasa dai bazai dinga cin abincin bud'a bakiba a gidansa鈥?.
Cikin dariya Aunty Hauwa'u ke fad'in 鈥渟ai ya d'auka mata 'Yar aiki ai鈥?.
Caraf maman Safara'u ta amshe zance... 鈥測o basai idan mai halin d'aukar 'Yar aikin bane, ana fama da masarar tuwo da shinkafa a jajibo mai aiki?鈥?.
Gurin tsit yayi kamar ruwa ya cinyemu, da alama kowa baiji dad'in furucin Na maman safara'u ba, sai mamansu yaa hameed ce tayi dariya itada momy Hadiza.
Ganin abin zai koma cin zarafin juna sai maman fauziyya ta d'ako wani zance, daga nan aka koma hirar d'inkin salla. babu dad'ewa ma aka kira sallar magriba, cikeda d'oki kowa yafara k'ok'arin cin dabino. tab aini kam bandani, tuni Na d'ebi ruwa mai sanyi nafara sha, Dan shine babban burina. a gida mukayi jam'i, baba k'arami yajamana limanci. da ganan kuma kowa ya maida hankalinsa wajen bud'a baki, harda su hajiya innaro馃槙, tayi kane-kane ita masu gidan 'ya'ya馃槒, koda wasa dagamu har innarmu babu Wanda yashiga sabgarta gudun gwalasa, har aka gama lafiya muka gabatar da sallar isha'i da asham. daga nan aka d'an ta6a hira kowa yahad'a kan 'ya'yansa zuwa 6angarensa.
haka muka cigaba da gudanar da ibadar azumin watan ramadan, tun ina ragwan taka harna fara daurewa, an gama goman farko aka shiga ta biyu (goma ta wuya馃檴 ).
Gaskiya nad'an wahaltu a tsakanin, ga makaranta ga aikin gidanmu dabaya k'arewa, ko wanke-wankema ya isheka, dukda had'uwa akeyi anayi kuwa.
Azumi yana 13 aka kawo kayan sallarmu, an bajesu tsakar gida kowa ya za6a, kala uku-uku ne dama duk shekara, atanfa, shadda, les, saikuma iyayenmu mata su k'ara mana gwargwadon abinda ALLAH ya hore musu.
Munada telolinnmu masu mana d'inki iya 'yan gidanmu kawai, shiyyasa bamuda matsala. Washe gari kuwa sukazo suka gwadamu, kowa aka saka sunansa ajikin kayansa da style d'in data za6a.
Innarmu ma sun saya mana itada mama Rabi'a, dan tunma kan azumi an kammala mana d'unkunanmu mudasu feena, (innarmu tana business itada mama Rabi'a) shiyyasa duk wani abun kwalliya Na 'yan mata bama rasashi, duk da dai 'yan gidanmu suna mana d'agawar sun fimu komai, saboda danginsu masu kud'ine, suna ganin kayansu sunfi namu tsada. hakan baita6a damunmu ba, dan aganina duk sutura sunanta sutura, yawan kud'in nawani bai d'ad'ani da k'asaba, to barema Munubiya da babu ruwanta.
Ana cikin haka muka shiga goman k'arshe Na azumi (goma ta d'okin sallah馃お馃槀).
Ranar wata weekend yayyanmu maza suka kwashemu domin za6o takalma da sauran tarkace Na kwalliya, dama duk ankai yaran suma kowa ya za6o, mu matasan 'yan matan muka rage dakuma yayyenmu su Aunty khaleesa.
Plaza ce babba mai k'yau da burgewa, kayansu Na manyane, amma yayyenmu dayake sunaso mufito suka kaimu can, sa6anin da da ake kaimu kasuwa kamar sauran yaran, su aunty khaleesa ne kawai ake kawowa nan saboda sune manyan 'yan mata, to yanzu muma mun shigo layi馃拑馃徎.
Sosai muka rikice da tsarin wajen, takalmane 'yan waje wad'anda duk inda kayi taku sai an kalleka ansan kagama Isa. Harda bags, kayan makeup, turarurruka da dogayen ruguna irinsu Arabia's gowns, gyalilla da kayan 'yan kunne, kananun Maya Na garari Na mata da maza, kai inaga babu abinda zakazo Baja sameshi awannan PLAZA d'inba kam鈥?.
Lallai an narka dukiya a wannan waje, ko plazan wanene? oho. munga dai sunan plaza d'in *BIRNIN GAYU!!*
鈥淟allai kuwa taci sunanta birnin gayu鈥?. 鈥? cewar Anty Ramlah鈥?.
Haleematu tace, 鈥渨lhy wannan ace plaza d'in mijinace to bazan maimaita kaya sau uku ba, hakama waya duk wata za a dinga canjamin鈥?.
Dariya tabamu, dan haka muka shiga darawa kuwa. kowa yad'auki abunda yakeso gwargwadon iko, yayyanmu suka biya da kud'in dasu Abba suka basu, sannan suka cika mana danasu kud'in, kowa yafito cikin farin ciki muna jera musu godiya, mun d'auki picture's sosai awajen kuwa. muna tafiya a mota nake cewa yaa Anas dan ALLAH wai Plaza d'in waye wannan?鈥?.
鈥渁i plaza d'in ta babban kwaroce k'anwata, plaza d'in *GALADIMA* ce鈥?.
shiru nai kamar banjishiba, danjin sunan wanda ya ambata, inada tabbacin kuma wannan mai girman kan tsiyar yake nufi kenan, yayinda 'yan uwana suka rud'e da firar galadiman.
d'an tsaki naja nace, 鈥渁shema Na mai shegen girman kai d'innan ne鈥?.
Kusan atare sukace ke a ina kika sanshi? dahar kikasan yanada girman kai鈥?.
Shiru namusu, sai Munubiya ce tashiga basu labarinsa da had'uwar damukayi a asibiti da shi, aikam duk sai sukabi suka rikice, harda masu fatan yazame musu mijin aure.
bansan miyasa duk hirar tasu ta k'untataniba, tabani haushi, saina maida hankalina ga kallace-kallacen jama'ar daketa kai kawo akan titi.
Har mukaje gida suna hirar Galadima sudasu yaa hameed dake basu labarin halayen kirki Na Galadima d'in, wai kuma bashida girman kai kamar yanda Na fad'a, kawai dai dan ban fahimcesa bane nima.
Nidai jinsu kawai nakeyi, amma badan Na yarda baida girman kai ba, tunda da idona Nagani ba labari aka baniba.馃槒ehe
Innarmu tayi mamakin wad'annan kanya, dan haka takasa hak'uri, har 6angaren samarin gidanmu taje tamusu godiya da fad'an d'awainiyar tayi yawa ai, ga hidimar biki Na tunkarosu.
Sunji dad'i sosai akan hakan da innarmu tayi, koba dad'i kowa yayi aikairi yanaso anuna jindad'i kuma amasa godiya.
Sukace tayi hak'uri, ai k'annensu ne, idan basu mana ba wazai mana, da samari suzo suna mana hidima su lalata mana rayuwa ai garasu sumana su kare mutuncinmu.
Sosai innarmu ma taji dad'in furicinsu, dan hakan ya nuna cewa su basu d'auki halayen iyayensu mataba Na raba d'aya biyu.
Salla nata gabatomu, yayinda aka fara 'yan kimtse-kimtse Na shirin bikin sallar, masallatai nata rufe tafseer, hakama gidajen redio dana talabijin..............鉁嶐煆?
*Kusaka yayan mahaifiyata a addu'arku, ALLAH yamasa rasuwa ranar alhamis馃槶馃憦馃徎, ALLAH ya gafarta masa, ya raya abinda yabari.*
_Bansan makaranta Raina kama.... kunada yawa hakaba wlhy, nazata ki rabin group bazaku kaiba馃檰馃徎, gashi yacika wasu basu sami wajeba kuma._
Na gaisheku k'yauta, ina fatan duk kuna cikin k'oshin lafiya kuda iyalanku馃馃徎馃槉?.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*.馃憦馃徎馃槶
[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎7鈨?
.......Yau ake saka ran ganin wata, dan haka kowane gida zaka iya jiyo kamshin miya dana nama, harma da kayan snacks.
Muma agidanmu kusan hakanne ta kasance, dan kowanne 6angare sunata hidimarsu, yau ko bud'a baki bakowa yasamu zaman yinsa ba.
Muma muna namu 6angare muna taya innarmu ayyukanta, dayake kowa yana miyarsane, da safe ahad'u ayi tuwo da masa da shinkafa, haka muke had'a kalolin abinci iri-iri saboda yawan jama'a da gidanmu kan tara a ranar salla, abokan yayunmu maza, abokan su abbanmu dawasu dangin iyayenmu mata.
Har wajen 10 munata aiki, sai kuma a lokacinne mukaji ana sanar da ganin wata.
Nannafa yara suka shiga murna gobe salla, Muma kanmu manyan murnar mukeyi. badan mun kammala aikiba muka kwanta.
Washe gari tun kiran sallar farko aka tadamu muka fara aiki, sai wajen 7am muka samu kanmu, a gurguje muka fara wanka da shirin tafiya idi, duk shekara dama 'yan gidanmu a masallacin da sarki yake salla muma mukeyi.
A gurguje duk mukaita fitowa saboda horn da yayyenmu suketa mana, yara an d'urasu a school bos d'insu Na makaranta, yayinda mukuma muka rarrabu a motar yayinmu datasu Abba dasuka bayar, tunda bakowa keda motarna acikin yayyen namu.
Dagani har Munubiya cikin shigarmu muke iri d'aya tamkar yanda muka saba a koda yaushe, dai-dai da kwalliyama iri d'ayace a fuskarmu, komai namu mukayishi iri d'ayane, wannan yasaka ake gaza banbancemu akoda yaushe.
Mun Isa filin idi, inda muka taddashi dank'am da jama'a maza da mata, wasu harda iyalansu, kamar yanda muma muka taho baki d'aya harsu innarmu, mu mata muna 6angaren mata, yayinda mazan sukayi nasu 6angare.
Khud'ubar da aka gabatar tazamo mana mai ratsa jiki da 6argo, Malam yayita cikin tsantsar larabci, yayinda wani malamin ya fassara acikin harshen Hausa, saboda marasa jin larabcin irinsu o e馃檴.
Daga nan aka gudanar da sallar idi kamar yanda addini ya koyar.
Had'a kan yaran muka shigayi gudin karsuyi wani waje, sai dai hakan bata samuba, dan annemi Kamal da Haneep an rasa, nannafa muka shiga bulayin nemansu, duk mun rikice, gashi baba k'arami da Abbah sai fad'a suke wai sakacinmu ne.
Tamkar zan kifa haka nake tafiya da sassarfa ina kalle-kalle. ban ankaraba naji naci karo da Abu, tunkan inkai idona kansa k'amshin turarensa yabigi hancina. da sauri na ware manyan idanuna bisa kamilalliyar fuskarsa dake d'aure babu alamar yasan miyema dariya, janye idona nayi cikin fargaba da fad'awa kogin tunani, inban mantaba irin wannan k'amshin naji a asibiti wajen Wanda aka kira galadima a wacan ranar da feena batada lafiya.
Cikin yanayin tantama Na maida idona nad'an saci kallonsa...
Tsaye yake kyam tamkar dutshin da aka dasa waje d'aya, idonsa akan wayarsa dake k'asa a tarwatse, Wanda inada tabbacin karon damukacine yasaka wayar fad'uwa.
A rikice nace 鈥測a Salam鈥? tareda duk'usawa nafara harhad'a wayar.
A hankali ya durk'usa kamar yanda nima nayi, ya d'ora hannunsa akan wayar dana ke k'ok'arin sakama battery ya zareta daga cikin hannuna. bugun zuciyata yak'aru saboda tsoro gashi yak'i cewa uffan, nasan nice da laifi, kafin Na ankara ya sake d'oramin wayar bisa hannuna yamik'e yabar wajen.
Sororo nabisa da kallon mamaki da al'ajabi, sanye yake cikin farar shadda k'al, wando da riga harda malun-malun, ya murza hularnan da ake kira Minister bak'a a kansa, takalminsa da agogonsa duk bak'ak'e, duk da bawani k'are masa kallo nayiba fuska da fuska nasan tabbas yayi k'yau, kayan sun maidashi wani babban mutum. Ajiyar zuciya Na sauke saboda ya 6acema ganina, nabi wayar daya barni da ita a hannu da kallo, tomi yake nufi da hakan?.
Banida mai bani amsa, dan haka nacigaba da had'a wayar, sai alokacin Na lura da sim card d'insa dake kan wayar yacire d'azun lokacin daya kar6a kenan.
Jujjuya wayar nashigayi cikin tafin hannuna, wayace mai azabar k'yau ga k'amshin turarensa ya manne jikin wayar tamkar itama ana fesa matane. 'Yar tsagewane tayi kad'an daga gefe, amma daga hakan ni banga wata matsalaba, kenan yana nufin koyaya waya ta tsage a hannunsa tatashi aiki a garesa?. Nanma babu mai bani amsata. Cikin mak'oshi Na furta to wanene wannan d'in shikuma?鈥?.
鈥淕aladima!鈥?. 鈥榥aji wata murya tafad'a abayana鈥?.
Cikin hanzari najuyon dan inga mai bani amsar tawa. wayam naga babu kowa, sai alamar gittawar mutum mai jajayen kaya.
Goshina Na dafe inamai runtse idanuna, cikeda mamaki nace, 鈥渒enan shine wanda yabama feena jini? Galadima!鈥?.
Nafad'a cikin bud'e idanuna inabin inda yabi da kallo tamkar zan sake ganinsa, a hankali nakuma furta _鈥淕aladima!鈥漘.
鈥済aladima kuma?鈥?.
Najiyo muryar Safara'u a bayana, da sauri a cusa wayar cikin hijjabina Na mik'e, kallonta nayi cikin basarwa nace, 鈥測a angansu ne鈥?.
Tace 鈥渆h mana an gansu tun d'azun, saikuma aka koma nemanki, miya faru naji kina kiran sunan galadima?鈥?.
d'an guntun tsaki naja 鈥渘aji wasu 'yan matane suna fad'in wai INA zasuga Galadima, tunda ance yazo sallar idi. shine nikuma nake maimaita sunan Galadiman saboda takaicinsu鈥?.
Dariya Safara'u tayi, ke 'Yar uwa karkiga laifinsu wlhy, koni zan sameshi saina bar Sadeeq wlhy, yanzu fa Nima ake nunaminshi, dama haka yahad'u? Wayyo ALLAH yau naga tsantsar gwanzartakar sarauta ajikin bawan ALLAH nan, tafiyarsama kawai abin kalloce, inaga kuma yayi magana?, kai ALLAH yakai damo ga harawa...... kedai kawai........
Baki kawai Na ta6e, batareda nagamajin k'arshen zancen nataba nayi gaba abuna da mamakinta a raina, wai zata iya Barin sadeeq?, saikace ba'akan sadeeq d'in bane akaso cin zarafina da innarmu, amma yanzu saboda taga Wanda ya fishi bakinta yake furta haka.
Da gudu Safara'u tabiyoni. Kusan a tare muka k'arasa Inda motarmu ta tsaya, yaa hameed yafara zagina akan INA kuma naje Na tsaya?, hak'uri nabashi muka Shiga mota kawai, dan nasan shima d'in masifafene kamar su abbanmu.
Amotar ana fira amma ni tunanina yanakan had'uwarmu da Galadima ta yau, ga mamakin wayarsa daya bari yatafi a hannuna batareda yace min uffanba, kai wannan Bawa yanaji da k'asaita da mulki.
Har muka Isa gida bakina bai iya furta komaiba acikin hirar tasu. Mun tatar su innarmu ma harsun huta su, yara kan summa fara cin abinci.
Ban zauna faloba kamar yanda munubiya tayi, saina zarce bedroom d'inmu Na 6oye wayar sannan nacire hijjab d'ina nashiga bathroom Na wanke hannuna gudun kar wani yaji k'amshin turaren saina dawo falon.
Tuni gidanmu ya kacame da hayaniya, munubiya tazubo mana masa da fankasu zamu faraci Ayusher da Feena suka shigo da gudu, juna muka rungume muna murnar ganinsu, Yaa Fadeel & yaa Marwan suma suka shigo, sai mama Rabi'a dake take musu baya tana rik'e da hannun Ahmad.
Nan muma muka kacame da farin cikin ganin 'yan uwanmu wad'anda bamuda kamarsu, innarmu ta baje mana abinci da kayayyaki da dama dansu duk ta tanadesu, sai makwafta dasuke gaisawar arzik'i suma duk tabada ankakkai musu.
Bamusan hidimar da kowa keyi anasa 6angarenba, mudai namu muka sani.
Ayusher takawo bakinta saitin kunnena, ahankali ta rad'amin sweet sis.... Wlhy k'amshin turaren Galadima kikeyi, kinsan har abada bazan mance k'amshi nan ba鈥?.
Cikin dakiya Na d'ago kai Na kalleta tareda balla mata harara, 鈥淎yusher wlhy ki kiyayeni, a'a k'amshin turaren sarki kikaji bana Galadima ba k'arewa鈥?.
dariya ta sanya harda rik'e ciki, nikuma Na tashi Na canja waje ina mamakin Ayusher mai gani har hanji, duk dawanke hannuna danayi sosai amma ace wai har yanzun anajin k'amshin turaren?, kai shikam wannan dawane mayen turare yake aiki haka?鈥?.
Wajen 12 muka fito domin zuwa kallon sarki dazai wice yima governor barka da salla.
A wannan karan tafiyarmu daban data 'yan gidanmu, dan mafi yawancinsu duk sun fice gidajen kakanninsu, tacan masu ra'ayin zuwan suma zasuje.
Mukuwa mudasu yaa marwan muka tafi.
Acikin gari duk inda ka kalla jama'a ne keta kai kawo, musamman yara da 'yanmata da samari, kowa yaci kwalliya ta kece raini da garari (yo dama ai ance ba'a za6ar budurwa ran salla, saboda duk k'azantar mutum ranar saika sameshi cikin tsafta da gayu馃槀).
Dukda akwai rana hakan bai hanamu jeruwaba domin kallon wucewar mai martaba sarkinmu da jama'arsa.
Masu busa algaita da kid'an taushine suka fara wucewa, sai kuma ga tawagar sarki Na biye.
tawagar saiki Na wucewa sai ta Galadima, kamar yanda mukaji wasu gungun samari Na fad'ar cewa ga Galadima nan.
Kowa yasan dama tsarin haka yake, daga sarki sai shi.
'Daga idanuna nayin donson sake ganinsa a karo na biyu. yanzu kam ya canja shigarsa zuwa milk coulor d'in janfa da wando Na lallausan yadi, Wanda aka k'awatashi da d'inkin surfani Na ainahin gidan masu sarauta, ya d'ora Brown Na alk'yabba mai kwalliyar Milk Color, hakama rawaninsa daya zagaye fuskarsa ya kasance milk ne, takalmansa heir cover masu lankwasa daga gaba irinna sarauta, sukuma Brown. yanzun kam fuskarsa d'auke take da k'asaitaccen murmushi mai kama da anmasa dole, hannunsa d'aya dayake d'agama mutane yana d'aureda farin agogon azurfa, sai zabba biyu a yatsunsa Na tsakkiya Wanda nake k'yautata zaton azurfane suma.
Nanfa su Ayusher suka fara d'aukarsa hotonsa a wayoyinsu.
Tsaki naja ina hararsu, 鈥渕tsoww wahalallu kawai, dama kanku kuka d'auka yafi Ku k'are wajen d'ura hotunan Wanda baisanma da zamankuba a wayarku鈥?.
Kafin cikin su Ayusher wata tabani amsa, wasu 'yan mata dake kusadamu d'aya ta kar6e da fad'in 鈥渒 'yan mata kama kanki, kodai kema son nasa ne yakaiki ga kishinsa?鈥?.
Wata wawuyar harara Na buga mata, 鈥渒ekuma shasha waya sako bakinki?, kajimin ballagaza kawai, uwarmiye abin so a jikinsa dahar ya isa ayi kishinsa? Ke dai dabakisan inda ke miki k'aik'ayiba ita dakon wahala, dan nakula ke amatanma suffar mata maza ALLAH yayiki....鈥?
Gaba d'aya suka taso min da masifa tamkar zasu cinyeni d'anya itada k'awayenta..
Yaa marwan dake zaune saman mota a bayanmu duk yana saurarenmu yad'ago kai ya kalleni, yasan tabas Munaya ce, baya buk'atar k'arin bayani kuma ko tambayar wacece ita, tunda Na nuna halin nawa, yace, 鈥淜 munaya zoki shige mota鈥?.
Nasan halinsa sarai baya wasa damu, cikin tunzura baki gaba nazo nashige motar Na zauna, amma saina bar k'ofar abud'e k'afafuna awaje, banida buk'atar cigaba da kallon kuma, dan haka nabud'e data nashiga chart kawai ina cika ina batsewa masifa nacin raina, gashi kuma an hanani amayar da'ita,. sai antayama yaa Marwan harara nakeyi ta gefen ido baima San inayiba, gaba d'ayama sainaji dama banzo kallon hawanba.
Koda muka bar nan ba gida muka komaba, yawo yaa Marwan yaytayi damu gidajen dangin babansu, bamune muka dawo gidaba sai magriba, kowa yayi ti6is da gajiya.
Mun tarar innarmu da mama Rabi'a sunata shan hirarsu ta zuminci.
Sai kusan 10 suka bar gidan.
鈽呪槄鈽呪槄
Washe gari muma agidansu mama Rabu'a muka yini har innarmu, koda yakema fitarmu mukayi nida Munubiya, Feena, Ayusher, mukabar su mama agida dasu Aryaan.
Yauma mun zaga gari sosai, dan Ayusher takira mana wani saurayinta yazo ya kwashemu, yauma munje munga hawan sarki da la'asar, saidai yau babu Galadima a tawagar, hakan bai dameniba, dan nama manta da lamarinsa ni.
Kwanaki kusan biyar zuwa 7 munashan shagalin salla, munsha yawo tamkar bamuda mafad'i mudasu Ayusher, sai Fauziyya dakan bimu wani lokacin idan basu fitaba da mamarsu suma.
'Yan matan gidanmu kowa sabgar gabansa yayi, rana d'ayane muka fita gaba d'aya domin gaida danginsu Abbanmu da Innaro takafa ta tsare akan sai munje wai su Anty Ramla sunyo musu sallamar aure.
Kwanaki 10 cif dagama bikin salla muka koma makaranta.
Haka rayuwa tacigaba da shud'ayawa, yayinda 'yan gidanmu keta shirin bikin 'ya'yansu, shiri akeyi babu kama hannun yaro, kowa burinsa ace 'ya'yan d'akinsa sune Star's, kuma sunfi kowa komai.
Sati uku kacal bikin yarage, an kawo lefe daga gidan senator halliru, akwatina 24, siyama 12 Zarah 12.
Humm ai ranar munsha kallo Na al'ajabi wajen mamansu yaa Hameed da momy Hadiza, habaici da gugar zana da burga, kowa yashashi, har dai abin yak'ure mamansu haleematu da maman Safara'u suka tanka musu, kafin kice mi gida yagama kacamewa da hayaniya, kowa yana ya6ama kowa magana, saida suka gama cin zarafin junansu sannan sukayi shiru bisa tsawatarwar baba k'arami, dayake yana gida a lokacin.
An bar maganarne kawai amma badan ta k'areba, mudai a 6angarenmu ma innarmu hana kowa fitowa tayi, dayake weekend ne.
Suma sauran duk an kawo nasu lefan, Aunty Rahaima, Ramlah, Hauwa'u sai aunty khaleesa, suma dai Alhmdllh, komai sai dai mak'iyi, duk da basukai nasu siyama ba gaskiya. a wannan karonma dai saida akayi 'yan gulmace-gulmace a gidanmu, amma basu bari tafito sarariba.
Suma su yaa Hameed aka kai nasu lefan gidajen matan dazasu aura shida Ya shafi'u da yaa Nasser. suma iyayenmu sunyi k'ok'ari wajen had'a musu lefen girma, ankai kuma kowa Na sambarka.
Tun bayan gama kai lefe gidanmu yakuma d'inkewa da k'us-k'us na gutsiri tsomar gidan yawa, kowa yana gulmar kowa akan aga wace rawa zaka taka, su 5 masu aurar da 'ya'yan.
Mamansu yaa hameed zata aurar da 3, yaa hameed, aunty khaleesa da Zarah.
Sai maman Haleematu zata aurar da aunty Hauwa'u.
Sai Momy Hadiza zata aurar da Siyama da aunty Raihan.
Mama Ruk'ayya kuma zata aurar da yaa Shafi'u da yaa Naseer.
Maman Safara'u kuma Aunty Ramlah.
Innarmu da maman Fauziyya ne kawai bazasu aurar da kowa ba, dan haka suka zama 'yan kallo, sai idan mazajensu sun saka su acikin shawarane.............鉁嶐煆?
0 comments:
Post a Comment