.......Hidimar biki ta kankama gadan-gadan, dan har bak'in nesa sun fara isowa, a ranar alhamis aka gudanar da sister's and brother's day Wanda mune k'annensu muka shirya musu da yayinmu maza. da farko a tsakar gidan innaro aka shirya, saboda su Abba bazasu barmu mu saka kid'aba a gidanmu, gashi mun gayyato k'awayenmu ne, sai abokan su yaa Nasser danasu Anas. daga baya kuma sai muka canja shawara saboda samun wani fili damukayi can k'asan layinmu, filin a zagaye yake da katanga an saka gate. Tunda safe suka fara shirye-shiryen gyara wajen, kasancewar sai 4pm za'a fara, mudai makaranta muka tafi nida fauziyya da Munubiya, dan munada lectures, amma sauran duk k'in zuwa sukayi, barema su Siyama amare.
Around 3pm muka dawo gida, yauma kam da alama wasu bak'in sun iso, dan gidan Yakuma cika da yara da 'Yar hayaniya.
Mun tarrar innarmu tana d'akin abbanmu, dan haka mukayi wanka muka fara shirin tafiya wajen taron, ko abinci bamu nemaba, dagani har munubiya mun iya makeup, kasancewar mama Rabi'a tasakamu wajen koya muda Ayusher lokacin damuka gama secondary, a d'an tsakanin kafin fitowar results d'inmu, taga damuyi zaman banza gamma muje mukoya wata 'Yar sana'ar, tunda bamusan inda rayuwa zata kaimuba. Ko gama shiryawa bamuyiba Rahma tashigo kiranmu inji su Aunty Rahaima, dan mune zamu musu kwalliya.
Mun tarar dasu duk sunyi wanka dama mu suke jira, zaman musu kwalliyar mukayi, ni nafarama Aunty Hauwa'u, yayinda Munubiya takema aunty Ramlah.
Kiran Ayusher yashigo wayar munu...., ta d'aga tana fad'in 鈥渒in isone?鈥?.
Bansan mitace mataba daga can, naji tace, 鈥渒izo muna 6angaren su Aunty Ramlah鈥?.
Babu dad'ewa saiga Ayusher itama, ta gaggada su Aunty's d'in, sannan muma tabamu hannu muka gaggaisa cikina musabaha.
鈥渓ah dear nifa harna fidda ran zakizo ALLAH鈥?.
Ayusher tace 鈥渒ibari kawai, wancan jarabbaben ne yasakani aiki, tuwo mama tayi da rana, kinsan kuma bayaci shi, shinefa ya tsareni wai saina masa sakwara, harfa nayi shirin tahowa鈥?.
鈥渦hm ai lamarin yaa marwan saishi, matarsa dai taga banu wlhy, shi anya ma yata6a budurwa kuwa?鈥?.
Dariya duk muka sanya a d'akin, aunty Hauwa'u tace, 鈥渁i marwan akwai miskilanci wlhy shima, nifa zan iya cewa mun ta6a magana dashi kuwa?鈥?.
Ayusher tace, 鈥測o aunty ai wannan kowama haka yake masa, komu muka gaidashi sai yaso yake amsawa, kullum mama cikin masa fad'a take amma abanza wlhy?鈥?.
Nann dai hira Yakoma kan yaa Marwan da mutane masu muskilanci irinsa, Munubiya ce mai kareshi, (dama ita suna d'an d'asawa, nice dai kamar muna ganin hanjin juna dashi danma ina tsoronsa ).
Kasan cewar mu uku ne sai kwalliyar tai sauri, dan danan muka kammala, nida munubiya mukayi tamu muma, simple makeup mukayi, amma komai iri d'aya, dama haka mukeyi, komai namu kullmun iri d'ayane.
Munyi k'yau, 6angarenmu muka koma mukayi shiri cikin blue d'in skirt da pink d'in Riga kamar yanda aka tsara sai veil shima blue.
Na jujjuya ina kallon kaina a mirror, 鈥渒ai jama'a nikam bazan iya fita hakaba gaskiya鈥?.
Ayusher dake kwance tana danna wata tad'ago ta kalleni, 鈥渒ai amma kuma wlhy kayan sun miki k'yau, kinganki kuwa? dan ALLAH ki barsu, kiyi rolling veil naki kawai鈥?.
鈥渒ai ba munaya kad'aibafa, nima bazan iyaba, after dress zan d'ora wlhy鈥?.
Dariya Ayusher tayi, ta tashi zaune tana ajiye wayar, 鈥渨aiku miyasa k'auyawane sister's, naga a ke6antaccen waje za'ayi?鈥?.
鈥渁mma kuma dai ai akwai maza kema kin sani鈥?.
鈥渢o alaranmiya, Ku saka, amma kafin Ku saka d'in nidai kuzo miyi hotuna鈥?.
Gaskiya koni nasan munyi k'yau, kasancewar mud'in fararene, kalolin duk sai suka kar6i jikinmu blue & pink. Wanda bai saniba saiya ce mu 'yan uku ne har Ayusher, dan muna matuk'ar kama da juna, sai dai Ayusher tafimu haske da d'an jiki.
Sai da mukad'anyi hotuna sannan muka fito. Innarmu tace kunyi k'yau, amma dan ALLAH kar inji wani yayi abinda za'ace gashi-gashi, Ku kama kanku da mutuncinku kunga dai acikin anguwane, idon kowa akanku yake鈥?.
Mukace to innarmu insha ALLAH. mun fita tana binmu da addu'a.
A k'afa muka taka har wajen taron, tunkan mu k'arasa muke jiyo tashin kid'a. wajen dank'am yake da 'yanmata da samari, k'awayen amare da namu muma, sai 'yan uwa kuma da abokan su yaa Nasser, dama shi ya Hameed bai gayyaci kowaba, yace ya bar mana mu k'anne (shidama ba auren farko bane).
Tunda muka shigo akai mana caa da idanu, wasu tsantsar kamarmu ce tajawo hankalinsu kanmu, wasukuma burgesu mukayi, wasu kuma gulmarmu sukeyi da zaginmu, to dama shi taro ya gaji hakan, ballemu da ake ganinmu k'ask'antattu agidanmu, kamar kowama yafimu komai.
Amare suma duk sunyi k'yau cikin tasu shigar ta Riga da wando pink gaba d'aya, sai suka d'aure k'ugunsu da blue d'in belt, suka d'aura jacket blue.
Snacks ne kawai akad'anci a wajen da drinks, sai pictures da'aka d'auka da video, 'yan mata sunata casar rawarsu da samari, mudai muna daga gefe zaune muna shan kallo. mun rarraba gifts d'in damuka tanada, bawani Abu bane masu tsada. silifas d'in wankane sai brush, MacLean, soson wanka da sabulu d'ad'd'aya aciki, gifts d'in nan mun shiryashine kawai dan tsokana dama. gabda magriba taro yatashi lfy, kowa ya kama gabansa. muma gida muka koma.
鈽呪槄鈽呪槄鈽?
Washe garima saida mukaje makaranta, sai dai 11:30 muka fito lecture, ALLAH ya taimakemu muka samu taxi da wuri.
Sanda muka dawo har 'yan jere sun dawo, kowa dangin mamarsa sukaje jerensa, shiyyasa mukaji tsitt babu gutsiri tsoma.
Muna dawowa ko wanka bamu tsaya yiba mukaci abinci muka tafi shagon auntynmu data koyar damu makeup domin yin k'unshi da saloons.
Cikin farin ciki ta tarbemu, dan mun rabu da ita cikin mutunci bayan mun iya aiki, Aunty salamah batada damuwa, inkaga tana maka fad'a to baka fahimtar abinda take koyar dakai ne, kwazon damuka nuna alokacin yasa takeji damu over. Tana kiranmu 'yan ukun ta.
K'unshi aka mana mai k'yau da gyaran kai, (dan d'aurema k'arya gindi irinnan aunty salamah harda mana gyaran jiki馃槉, wai tanaso muma musamo mazajen aure馃檲).
Kowa ya gammu yasan munyi k'yau sosai.
Amakare mukaje gida, dan mun tarar amare nata jiranmu mu musu kwalliya, 'yan gidanmu harsun fara k'ananun magana, wai wulak'ancine yasa muka fita ai, kuma muna kallon lokaci yana k'urewa mukak'i dawowa. hakan da innarmu taji yasata kiranmu tana mana fad'a, hak'uri muka bata dacewa gamunan a hanya.
Masifa mukaitayi nida Ayusher, munubiya na bamu hak'uri, wlhy badan innarmu ba da bazanyi kwalliyar nanba yau.
Babu zancen mu huta muka hau musu kwalliyar. aikam ranar k'in fita wajen kamun nayi da akayi a tsakar gidanmu, kwanciyata nayi, innarmu taitamin fad'a kuwa.馃槙
Washe garin asabar d'aurin aure, dakam gidanmu yacika tab, 6angarenmu dai da sauk'in mutane, sai mama Rabi'a kawai da matan abokan Abbanmu.
K'arfe goma aka d'auro auren yaa Hameed da amaryarsa, sai yaa Nasser shima da yaa Shafi'u.
Na 'yan matan kuwa sai k'arfe 1:30pm. K'ofar gidanmu yacika dank'am da jama'a ta ko'ina, 'yan siyasa tawagar senator halliru da abokan su Sa'eed, hakama mijin aunty Rahaima d'an siyasane, dan haka harda governor a mahalarta taron d'aurin auren.
Har aka gama d'aura aurarrakin ina d'akinmu kwance, ko wanka banyiba, garama munubiya da Feena da Ayusher su duk sunyi, amma suna d'akin basu fitaba, sai balkisu k'awarmu da itama tazo mana.
Hira suketayi, nikam dai ina kwance kaina namin ciwo.
Gidanmu babu masaka tsinke, tako ina jama'ane, amare ansha k'yau, su siyama baki har k'anne an auri 'ya'yan sanata, hakama iyayensu sai burga sukeyi, ranar munga gasar dressing wajen iyayenmu mata kam, kowacce so take ace itace uwar amarya datafi kowa fita.
Innarmu kam babu ruwanta, shiga d'aya tayi ta atanfar da Abbanmu yamusu Na fitar biki, sai da yamma ta canja da less.
Aranar kowaccensu tayi yini. Baza'a kai amareba sai washe gari, saboda anason agudanar da dinner waje d'aya, amma an kawo nasu yaa Shafi'u sudai.
Yau d'inma dai mune muka musu kwalliyar su dukansu, kafin k'arfe 8pm afara kwasar mutane zuwa wajen daza'a gudanar da dinner d'in.
Gurin yayi k'yau sosai, yayinda aka shirya ma amare da anguna hi table.
Sai dai kuma wata sabuwa, ba duk angunan bane suka halarci wajen dinner d'in, nan fa aka fara 'yan gulmace-gulmace tsakanin dangin iyayenmu mata, tuni labari harya kai kunnuwan iyayenmu mata dasuke zaune a gida.
Amaren da babu angunansu sunsha kuka, wad'anda kuma dama sukasan angunan nasu ustazaine bazasu zoba basu damuba.
Haka dai aka gudanar da dinner d'in zukatan wasu babu dad'i, tunkan agama ma wasu sukaita tafiya gida abinsu. K'arfe 11 aka tashi.
A wajen dinner kam nayo saurayi mai suna Fu'aad, hakama munubiya da Ayusher dun sunyi, Fu'aad k'yak'yk'yawa dashi masha ALLAH, duk da dai bawani sake masa nayiba ya burgeni.
Su Ayusher sunata tsokanata, nidai ban kula suba.
Washe gari da safe kuwa saida abin yazama fad'a, wai ankama wasu suna gulma akan rashin zuwan sauran anguna, kuma dangin momy Hadiza ne, aikam sosai aka zuba rikici, har saida abbanmu ya tsawatar.
Aranar aka shirya kai amare, dole sai dai a rarrabu, tun la'asar aka fara kawo motoci, baba k'aramine yabada shawarar ahad'a tafiyar kawai gaba d'aya, su aunty Hauwa'u suma su siyama rakiya, sannan suma haka.
Haka kuwa yayima wasu iyayenmu mata dad'i, dan kobabu komai saji yanda gidan kowacce ya kasance.
mun fara kai su Siyama da Zarah, wad'anda babu alamun kuka a idanunsu, gidajensu jere da juna, sunyi k'yau masha ALLAH, kayan gado dai duksu Abba sukayi, kuma kud'insu d'aya, saidai kowa da za6insa, kayan kitchen ne kowa uwarsa tayi da sauran tarkace, ananne kowa ya ware ido dan aga kwazon uwar mutum, nidai agareni babu makusa, gidansu Zarah duk yayi.
Mun ajiyesu tareda k'awayensu, mukuma muka tafi kai sauran.
Daga Nan sai gidan aunty Rahaima, itama masha ALLAHU wlhy, saidai mak'iyi, gidanta yayi k'yau, sai dai tanada kishiya.
Saikuma gidan aunty khaleesa, itama dai d'in zamm zamm wlhy, daga nan sai aunty Ramlah, wlhy itama yayi d'as, itama tanada kishiya. Aunty Hauwa'u ce k'arshe dan itace babba, itama gidanta yayi k'yau sosai.
Nidai aganina babu wadda mahaifiyarta batayi k'ok'ari ba wlhy, amma hakan bai hana sauran gumtso gulmarmakiba aka taho da ita.
Kasancewar duk babu Inda muka zauna aka taho gida da wuri, harzamu wuce Fu'aad daya d'akkomu yace bari yashiga Birnin gayu plaza damu.
Nace a'a muwuce gida kawai, kar aga kowa yadawo mu bandamu, gashi lokacin har 8:30pm ya wuce.
Ayusher ce tace indai bazamu dad'eba ashiga, saimuce muna gidajen su siyama mu, mun zauna jiran anguna.
Kamar dai nace a'a amma nayi shiru, saboda naji munubiya da feena suma sun bada goyon bayan mu Shiga, sannan Fu'aad yace bazamu dad'eba.
Ya kalleni murya k'asa-k'asa yace, 鈥済inbiya bakice komaiba?鈥?.
Murya a sanyaye nace, 鈥渋ndai bazamu wuce 1hour ba muje鈥?.
鈥渋nsha ALLAHU my luv bazama mu kaiba鈥?.
A kasalance Na d'aga masa kai saboda agajiye make ti6is.
Haka yashiga wajen nidai zuciyata Na dukan uku-uku daban San Na miyeba.
Munshiga cikin plaza d'in, bansan takamaimai miyasa Fu'aad yace mushigo wajenba, tunda dai bawani abin ci ake saidawa a wajenba.
Mun shiga 6angaren kayan kwalliya, yace kowa yaza6i abinda yakeso.
Nidai nace masa a'a mun Gode.
6ata fuska yayi yana hararata, ya maida kallonsa gasu munubiya dake tsaye 鈥減lease dan ALLAH karku biye mata, kuje Ku d'auka鈥?.
Badan suma sunasoba suka amsa da to.
Ya kalleni yana fad'in 鈥渕ujeto ni na d'ebar miki鈥?. bance masa komaiba nabi bayansa ganin kamar yayi fushi, wayarsa aka kira, ya zaro daga aljihu, saida yad'an saci kallona yaga hankalina baya kansa sannan ya d'aga, murya k'asa-k'asa tamkar mai gulma yace, 鈥渘agama aikina鈥?.
Dawowa yayi wajena bayan ya katse wayar, da kansa yake za6ar mini duk abinda yadace.
Su munubiya ma sunacan suna d'auka, kamar ance munubiya ta bar wajen saita zagaya tabaya, a dai-dai wannan lokacinne shikuma yake tunkarowa shida wasu matasan samari guda biyu, da alama yana zagayene kowani abun daban. tafiya yake cikeda nutsuwa da sarauta, sai sautin takunsa dakakeji, tunkan su iso gareta k'amshin turarensa ya iso.
Waige-waige munubiya tafara, tanason tuno mai wannan k'amshin. bata ankaraba saijinta tayi tatafi suuuu santsi ya kwasheta.
Shi mutumne mai yawan tausayi da taimako, da sauri yayo kanta kafin taje k'asan, Dan yasan fad'uwarta a wajen babban had'arine, yakai hannu zai rik'eta itakuma ALLAH yabata ikon dafe wasu tarin baskets dake wajen. Cikin runtse ido da sauke ajiyar zuciya ta furta 鈥淎lhmdllh鈥?.
Janyewa yayi daga rankwatowar dayay kanta tamkar zai rungumeta, batareda yace uffanba yafar wajen.
Muduka akan idonmu komai ya faru, wad'anda suke tare dashine sukaima munubiya sannu, mukuma muka k'araso da sauri gareta muna tanbayarta babudai wata damuwa ko?.
鈥渂abu komai Alhmdllh鈥?. 鈥榯afad'a tana gyara tsayuwarta鈥?.
Nace, 鈥渒unga kuzo mu tafi hakanan, wlhy inajin tsoron agane bama gidansu siyama鈥?.
Duk suka amsa da gsky mu tafi, da k'yar muka yarda mukaje wajen biyan kud'in. yabiya sannan muka tafi.
ALLAH ya taimakemu ba'a mana fad'aba.
Duk cikinmu babu Wanda yakuma maida hankali akan abinda yafaru a birnin gayu plaza, saidai abin yakasa barin raina, kamar zuciyata tana cikin fargaba, amma bansan ta miyeba, ita kanta Munubiya wani sukuku nake ganinta, bandai tanbayeta ba Na share.
Washe gari Monday, muka tashi da shirin makaranta, saida muka gama gyara gidan tsaf sannan muka tafi harsu Ayusher, dayake lectures d'inmu Na yau sai 1:30pm ne. yauma sauran 'yan uwanmu bakowa yaje school d'inba ma har fauziyya.
Tun muna tsaye abakin titi muna jiran taxi naga wasu tsirarun mutane nabinmu da kallo. ban kawo komai arainaba muka samu taxi.
Driver ma yana tuk'i yana kallonmu ta madubi, sainaga kuma ya kalli takardar dake saman cinyarsa. d'an fara tsarguwa nayi, amma saina dake ina zaton irin dirobobin nanne masu shegen kallon tsiya.
Da muka sauka cikin makaranta ma bata sauya zaniba, kallonmu akeyi har ana nunamu, wasu da jaridu a hannu wasu kuma waya.
Munubiya tace, 鈥淢anaya bakiga abinda ke faruwaba tundaga fitowarmu gida zuwa nan ne?鈥?.
鈥渘agani wlhy Munubiya, bansan miyakawo wannan kallon k'urilla d'inba, dama bakiga kallon da direban can yake manaba ni da ke harya saukemu, ko sanda muke sallama dasu Ayusher idonsa Na kanmu kyam kuma yana kallon wata jarida dake cinyarsa鈥?.
Muduka kallon jikin junanmu mukeyi, babu wanda shigarsa tazama aibu acikinmu, sannan bama tareda wani abin kallo,
Hannun juna muka kama muka cigaba da tafiya cikin tsantseni da nazartar kallonda 'yan uwanmu d'alibai suke mana.
Tunda muka shigo cikin class sai duk aka zubo mana idanu, kuma anata k'us-k'us. yanzu kam hankalinmu yatashi sosai, wai mike faruwane? saikace yau mutane suka fara ganinmu? shin yaune muka fara shigowa makaranta?.
Bamu da mai bamu amsar tanbayarmu, muka nufi Bilkisu dake zaune itama tazubo mana idanu, ga jarida agabanta, kamar yanda muka gani wajen sauran 'yan department d'inmu, wasu narik'e da jaridu wasu wayoyi, sunyi group group kuma suna k'us-k'us.
Da sauri Na k'arasa zan d'auki jaridar gaban Bilkisu amma saitayi saurin d'aukewa............鉁嶐煆?
Babbar magana, shin mike faruwane? kallonmi jama'a kema su Munubiya? Sannan mi ake kallo a jikin jaridar da wayoyin kuma?馃う馃徎鈥嶁檧.
Nasan masu karatu ma wannan amsar suke son sani馃
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*馃槶馃憦馃徎
[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎9鈨?
.......K'yaleta nayi najuya sit d'in bayanmu Na fusge ta hannun wani guy, rubutun farko dage jikin jaridar a shafin farko na tsirama idanu.
*_BABBAR MAGANA, GALADIMA SAMEER RUNGUME DA MATASHIYAR BUDURWA A PLAZA 'DINSA SUNA SUMBATAR JUNA!!_*
sai kuma hoton dake k'asan rubutun shima har kala biyu, Na farko abinda yafarune na fad'uwar Munubiya a birnin gayu plaza, har Galadima yay yink'urin taimakonta amma tadafe baskets ko ta6ata ma baikai gayiba, amma abin mamaki da al'ajabi a hoton galadima ya rungume munubiya ne bakinsa akan nata.
Hoto nabiyu kuma ni da shi ne afilin idi lokacin damukayi karo har wayarsa ta fad'i, ko kad'an bai ta6aniba, ko waya daya kar6a a hannuna hannuna danashi basu had'uba, amma anan an nuna hoton yana rik'e da hannuna duka biyu muna kallon juna.
鈥淚nnalillahi鈥? nafara maimaita jikina har yana rawa, gawata uwar jufa data fara jik'a sassan jikina, lallai dolene duk inda muka gitta abimu da kallo.
Ju yowa nayi na kallo munubiya dake tsaye a bayana, itakam hawayema takeyi.
Jikina a sanyaye nakama hannuta muka fita daga cikin hall d'in, kallon da ake Manama ayanzu yafi na d'azun, Dan labarin sai kuma yad'uwa yakeyi yanzun.
Muna fitowa muka samu taxi sai gida.
Tunda muka sauka naga wasu gungun samarin dake layinmu a majalissarsu sun zubo mana idanu gaba d'aya, tuni zuciyata tafara tsitstsinkewa, kenan labarin harya iso nan?. Dagani har Munubiya jamukai muka tsaya, saboda ganin dukkan ahalin gidanmu tsaye cirko-cirko a tsakar gida, hardasu yaa hameed anguna, ga bak'i dabasu gama tafiyaba, innarmu kwance akan tabarma maman fauziyya namata fifita, ga Abbanmu kusada ita tsugunne yana shafa mata ruwa.
Jaridar dake hannun baba k'arami mukabi da kallo, bansan sanda wani kuka yatahominba nima, sa6anin da munubiya kawai keyin kukan.
Da gudu mukayi kan innarmu, amma sai yaa hameed ya daka mana tsawa, 鈥渒arku sake Ku ta6ata wlhy, idan bahakaba jikinku kuwa saiya fad'a muku鈥?.
Babu shiri mukaja burki, amma sai muka durk'ushe ak'asa muka fashe da kuka.
Innro tace, 鈥渒wayi kuka kuwa munafukai, ahiyyasa ai ANNABI yace a auri mace tagari, Dan 'ya'ya susami uwa tagari, yo wannan aimu ba sabon abu baneba agaremu, tunda dama halin uwarku kenan, itama saida tagama tambad'arta a titi aka k'ak'abama d'ana鈥?.
Rintse idanu nayi saboda yanda maganganun innaro ke sukar zuciyata. Dady yakatseta da fad'in 鈥渄an ALLAH inna kiyi hak'uri kibar maganarnan鈥?.
鈥渉ameesu barni nafad'i gaskiya, wannan abin kunya har ina, wai jikokinane yau aka buga ajikin jarida namiji rungume da d'ayarsu a titi鈥? ta face hanci tana share hawaye da bakin zani, 鈥淎LLAH ya wadaran irin wannan rayuwa taku kuda uwarku, kun jawo mana abunkunya, yanzu dawane ido duniya zata cigaba da kallonmu鈥? feeet, takuma fyace majina鈥?.
Mudai ni da munubiya muna durk'ushe rungume da juna Luna rairai kuka maiban tausayi dacin zuciya, yayinda 'yan gidanmu da sauran 'yan biki suketa k'us-k'us a tsakaninsu.
Isowar likita yasa aka kama innarmu aka maida falon Abba, a sank'ame take tamkar gawa....
鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?
*_GAGARA BADAU PLACE_*
Shirye-shiryen komawa India yakeyi hankalinsa kwance, Dan yau zai koma ga mahaifansa da 'yan uwansa dake can, jirgin k'arfe 8pm zaibi.
Yana gama had'a 'yan abubuwan dazai iya buk'ata yadawo falo ya zauna, sanye yake cikin farare k'al d'in kayan Adidas na training, dogon wando da Riga mai dogon hannu, yasaki hular abaya, kayan sun masa k'yau sosai.
Kallo d'aya yayma abincin dake kan center table d'in ya d'auke kansa, cikin k'asaitacciyar muryarsa mai cikeda isar masu mulki naji ya furta 鈥淪aykin k'ofa鈥?.
Kai kace anmasa dolene saiyayi maganar.
Da hanzari sarkin k'ofa yashigo falon, ya zube a k'asa 鈥渂arka da hutawa ya shugabana鈥?.
Kansa kawai ya jinjina, sannan yace, 鈥渨aye yakawo abinci nan ne?鈥?.
鈥測a shugabana bansan daga ainahin wane 6angare bane, amma bayin dasuka kawo daga 6angaren sarauniya Zulfah ne鈥?.
Baice komaiba ya d'aga masa hannu alamun yatafi.
Sai da yad'an rissinar da kansa alamar girmamawa sannan yamik'e, dokace agareshi shi bayason kirarin da akema 'yan gidan sarautar. dan haka basa yimasa shi, Saboda gudun 6acin ransa.
zamewa yayi yay kwanciyarsa akan doguwar kujerar ya lumshe idanunsa batareda yabi takan abincinba.
Sallamar sarkin k'ofa tasakashi bud'e idanunsa akansa, ya amsa sallamar bisa la66ansa, sarkin k'ofa yazube agabansa, cikeda girmamawa yace, 鈥測a shugabana yalla6ai Muftahu yace amasa iso gareka鈥?.
Alama yamasa akan yabada izinin ya shigo.
Fita sarkin k'ofa yayi. babu dad'ewa saiga Muftahu yashigo da sallama, Galadima yabud'e idonsa yana kallonsa tareda amsawa.
Zama yayi kujerar dake kallon Galadima, yace, 鈥測alla6ai barka da hantsi鈥?.
Murmushi Galadima yayi, ya tashi zaune sosai yana fad'in 鈥渕y man daga ina haka naganka ayikice? bakaje aikibane?鈥?.
Ajiyar zuciya Muftahu ya sauke, yacije le6ensa na k'asa yana mik'ama Galadima jaridar dake hannunasa, 鈥渘afita wlhy sainaci karo da wannan jaridar data fito a safiyar yau鈥?.
Cikin halin ko inkula Galadima yace, 鈥淢iye had'ina da jayidan to?鈥?.
鈥淜ayi hak'uri ka kar6a ka duba鈥?.
A shafin farko yay karo da abinda yasakashi sake kallon Muftahu, kai Muftahu ya d'aga masa alamar yacigaba.
*_ANYI WALK'IYA...., GALADIMA DA AIKA-AIKA A FILIN IDI_*
cikin hanzari yabud'e shafin farko, nankuma an saka.
*_BABBAR MAGANA, GALADIMA SAMEER RUNGUME DA MATASHIYAR BUDURWA A PLAZA 'DINSA SUNA SUMBATAR JUNA!!_*
sai hoton farko dana biyu, wad'anda suka d'aure kansa, danshi gaba d'ayama ya manta daduk abinda yafaru, tundaga na birnin gayu plaza harna filin idi d'in. d'agowa yay yakalli Muftahu sannan ya maida kallonsa ga dogon rubutun da akai akan sharhin hotunan. bazai iya karanta rubutun ahakaba, saiya fara waige-waigen neman medical glasses d'insa.
Fahimtar haka da Muftahu yayi yace, 鈥渋na yake in d'auka maka?鈥?.
Da hannu ya nuna bedroom d'insa ba tare da yace komai ba.
Mik'ewa Muftahu yayi yanufi bedroom d'in, babu dad'ewa saigashi yadawo, ya mik'a masa sannan yakoma inda yake da ya zauna yana fad'in 鈥渒o ka kawo na karanta maka鈥?.
Nanma baice uffanba yamik'a masa jaridar, kansa ya maida jikin kujerar ya jingina ya lumshe idanunsa.
Tiryan-tiryan Muftahu yafara karanto k'aryar da aka jera jikin jaridar, ko sau d'aya bai motsaba, amma yana saurarensa.
Muftahu yagama cikin sauke ajiyar zuciya, Amma tabbas wannan wata k'ullaliyace, ai ba abinda yafaru kenanba jiya a birnin gayu, ni nama rasa mizan cema wannan gidan jaridar wlhy鈥?.
Galadima ya bud'e idonsa dake a lumshe, ya kad'a yay jajur saboda 6acin rai, akan Muftahu ya saukesu batareda yace komaiba, tuno abinda yafaru a filin idi yayi kusan sati 4 kenan, tabbas sunyi karo da yarinya, wadda ayanzu haka ko fuskarta bazai iya tunawaba, dan ko'a waccan ranar kallo d'aya yamata, a jiya kuma ko ta6a yarinyar baiyiba ALLAH ya kareta daga fad'uwar dazatayi. jinjina kansa yayi cikeda 6acin rai da mamaki.
Muryarsa a sark'e yace, 鈥淢uftahu imason bayanai akan yayannan najikin jayiday su duka鈥?.
鈥渙k yalla6ai, amma ai yarinya d'ayace duba kagani鈥?.
Kar6ar jaridar yayi yakuma kallon hotunan, tabbas duk yarinya d'ayace, wannan ya sake tabbatar masa da an shirya masa hakanne.
Mik'ewa yayi yazari mukullin mota batareda yace ma Muftahu komaiba, ganin haka shima Muftahu saiya mik'e yabi bayansa.
Cikin sauri dogaren dake binsa inhar zai fita suka taso gareshi, amma saiya d'aga musu hannu.
yana k'ok'arin bud'e motarne Jakadiyya ta iso inda yake...
Cikin rissinawa tace, 鈥渂arka da hantsi galadima鈥?.
Bai iya amsa mataba, sai hannu daya d'aga mata kawai.
Kuma rissinawa tayi tace, 鈥淕aladima takawane yabani izinin in kirayeka鈥?.
Kallonta yayi zaiyi magana saikuma yay shiru ya maida motar yarufe tareda cillama Muftahu dake bayansa kyes d'in.
Muftahu ya cafe.
Komawa yayi 6angarensa yashiga wanka, kusan mintina 40 sannan yafito sanye da bathrobe fara k'al, bai wani d'au dogon lokaciba yay shiri cikin k'ananun kaya, yayi k'yau sosai, ya feshe jikinsa da turarensa masu matuk'ar k'amshi.
Wayarsa ce tashiga ringing, baibi takantaba yacigaba da hidimarsa, dama tun yana bathroom yakejin ana kiransa.
ta baya yabi inda bayi bazasu isheshi da gaisuwa gaisuwa d'innanba, dayake sarki yana gida, yau ana hutun zaman fada saboda tunawa da abinda yafaru da tsohon sarki (mahaifin Galadima Sameer) duk ranar litinin tana zama ranar daba'a zaman fadane...
鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?
Kowa ya ganmu yasan muna cikin rud'ani, da k'yar aka samu innarmu ta farfad'o, sai dai an hanamu mushiga mu ganta.
Gidanmu kam abin nema yasamu, hakama cikin anguwa, saboda yad'uwar labarin a social Media.
Muna zaune a falo duk mun zabga uban tagumi dagani har munubiya, idanunmu duksun kunbura saboda kuka, Ni ba abinda yafaru a jaridar ne yafi damunaba, halin da mahaifiyarmu ke ciki shine babbar matsalata, bamuda kamarta duk duniya, bazanso wani Abu ya sameta asanadinmu ba, bayan bak'incikin datake k'unsa agidanmu kuma.
Kamar anjeho mama Rabi'a itada ya Marwan suka shigo falon. mun tsorata kwarai da gaske, cikin daka tsawa mama Rabi'a take tambayarmu innarmu.
Hakanne ya tabbatar mana da suma labarin yaje musu. munubiya ce tabata amsa cikin kuka, sannan tace 鈥渨lhy mama sharrine, ba abinda yafaruba kenan n......鈥?.
Saukar marin datajine yasakata rufe bakinta 6am, kafin na tantance mai Marin nima naji saukar nawa.
Ko kad'an yaa Marwan baiji tausayinmu ba, saida yamana lik'is da duka, dak'yar Dady ya kar6emu a hannunsa, amma baba k'arami da Abbanmu casukai yama k'ara mana.
'Yan gidanmu duk sunfito cirko-cirko a tsakar gida, kowa na tofa albarkacin bakinsa, gashi akwai sauran 'yan biki dabasu gama tafiyaba.
Iyayenmu da yayinmu duksun taru akanmu, ana tambayarmu wacece daga cikinmu.
Kafin Munubiya tayi magana nayi saurin cewa 鈥渒uyi hak'uri iyayena, nice munaya a gaba d'aya hotunan, wlhy kuma tsautsayine, amma ba ainahin abinda yafaruba kenan鈥?.
Munubiya zatayi magana nayi sarin rik'e hannunta alamar kartace komai, 鈥渒arki d'aurama kanki abinda ba laifinkiba Munubiya, nice Munaya na aikata....鈥?
Itama cikin kuka tace 鈥渨lhy bake baceba, nice, wlhy nice鈥?.
Nima nace 鈥渨lhy nice鈥?.. ....
Tsawa Abbanmu yadaka mana, atare mukayi shiru yace 鈥渘asan dama Munaya kece, Munubiya bazata aikata wad'annan abubuwan ba, dukda kema d'in nayarda da tarbiyyar dana baki, amma bansan miya kaiki ga aikata hakanba, shiyyasa ranar idi mukaita nemanki, Ashe kinacan kina d'akko mana magana, tunda aure kikeso zan miki, nabaki nanda sati 2 kacal, inbaki kawomin mijiba zan had'aki dadu Wanda nayi niya鈥?.
Yana gama fad'ar haka yatashi ya fice, baba k'arami ma ficewarsa yayi.
Wani kuka mai tsuma rai muka kuma fashewa da shi, musamman ma ni danasan nasaka kaina a tarko, amma hakan shine dai-dai, bazan amince naga 'Yar uwata cikin bak'in cikiba, insha ALLAH koma minene zan jureshi, muniya tanada hak'urin dazai iya cutar da ita akan wannan lamarin, gashi baba yafurta in ban fiddo da mijiba zai auramin Wanda yaso, to idan hakan ta kasance kan Munubiya wane hali kuke tunanin zata shiga? Musamna dabamusan gidan dazamu iya fad'awaba tunda nasan abinda Abba yafad'a tabbataccene, dan shi baya magana biyu.
Dady ne yashiga lallashinmu, tareda mana nasiha da nuna mana illar abinda muka aikata, musaman ma ni. ya Marwan kam sai antayamin harara yakeyi shida yaa hameed.
Yinin yau kam kuka muncishi harmun godema ALLAH, mu duka kwance muke rijif da zazza6i, har akayi isha'i bamu kumajin motsin kowaba, mukuma muna d'aki kwance mu duka k'udundune a bargo.
Su Aryaan sunacan nanuk'e da innarmu dake 6angaren Abbanmu har yanzun, dan haka 6angarenmu saiya kasance tsitt. a ranar dai haka muka kwana babu lafiya nida Munubiya, babu mai iya taimakon wani acikinmu, ga yunwa ga damuwa ga ciwo.
Zuwa asubahi ko salla kasa gashi muyita mukayi, dan k'arfinmu yagama k'arewa...馃槶
鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?
Ya isa sassan mai martaba, bayan masu tsaron k'ofa sun gama kwasar gaisuwa suka masa iso.
Izinin shiga mai martaba yabashi.
Falone k'aton gaske, Wanda nikaina banmasan yanda zan musalta k'yansa da girmansaba, ga kujeru rukuni-rukuni, ko ina yagama d'umamewa da sanyin AC, gawani k'amshi na musamman.
daga can gefe na hango mai martaba kishingid'e bisa wani lallausan carpet da aka k'awata da tarin tum-tum, gabansa tirene dake d'auke da jug na glass cikeda zo6o, sai wani k'aramin kwano na tangaram Wanda bansan miye acikiba, saikuma k'aramar butar shayi awani tiren daban, da mug guda d'aya.
Fuskarsa d'aure take tamau alamar yana cikin 6acin rai, ga jarida a hannunsa.
Cikeda girmamawa Galadima ya zauna a gefen dardumar, ya tankwashe k'afafunsa sannan ya risina yana fad'in 鈥渂arka da rana ranka ya dad'e鈥?.
Mai martaba bai amsaba, sai ma cilla masa jaridar hannunsa dayayi.
Galadima yabi jaridar da kallo batareda ya d'aukaba.
鈥渒a d'auka ka duba mana, dan inason sanin gaskiyar zancen鈥?.
Kan galadima a k'asa yace, 鈥渢akawa nima yanzu Muftahu yakawo min nagani, nama fito zanje ga gidan jayidayne kiyanka ya isomin, amma wlhy Abba ba gaskiya baneba, ka.......鈥?
Da sauri mai martaba ya d'aga masa hannu cikin 6acin rai 鈥渕i kakeson fad'amin? kana nufin zasu buga abinda baka aikata bane? ai sunsan gidan daka fito, haka kawai bazasu maka sharri ba kodan gudun abinda zaije ya dawo. Sameer yanzun nan da mutuncinmu kaje ka aikata wannan son zuciyar domin ka 6atama wannan masarautar suna? Lallai kacika d'an halak, kuma kayi dai-dai, tabbas ka kafa tarihin dawani bai ta6a yin irinsaba a wannan masarautar, Dama Ashe kabud'e waccan plaza d'inne domin son zuciyarka? Yanzu da ace lafiyar Yaya k'alau wane irin hali kake tunanin zai tsinci kansa? Ina ganinka shiru-shiru Ashe kaid'in shaid'anine鈥?.
Runtse idanu Galadima yayi zuciyarsa na k'una da kalaman mai martaba k'anin mahaifin nasa, amma yagaza furta komai, sai idanunsa daketa k'are rinewa zuwa jajazur.
Har mai martaba yak'araci fad'ansa yagama Galadima bai iya furta komaiba, kansa ak'asa ko motsi baiyiba.
鈥渒atashi kabani waje, k'arfe 8:30pm akwai meeting, saika jira hukunci daga mama Fulani 鈥?.
Rissinar da kai Galadima yayi yace, 鈥淎LLAH ya huci zuciyayka, na bayka lafiya鈥?.
Banza mai martaba yay masa, yatashi yafice shikuma cikin k'unar zuciya.
Yana fita wayarsa ta fara ringing, ransa adagule yacirota da nufin kashewa gaba d'aya, saiyaga *_My dear Momma_* rintse idanunsa yayi ransa nakuma suya, yasan tabbas labari ya Isa gareta kenan, wannan wace irin masiface, mahaifiyarsa dake wata k'asa har ankirata an Sanar mata, ko halin datake ciki baza'a kallaba?. Kasa d'aga wayar yayi harta tsinke.
Tabbas duk Wanda yake gidan jaridarnan saiyayi Dana sanin saninsa arayuwa.
Kiran Momma ne yakuma shigowa, yanzuma bai d'agaba harya k'arasa sashinsa.
Sai da ya zauna sannan yafara k'ok'arin nemanta cikin suyar zuciya data ruhi...............鉁嶐煆?
To masu karatu, ko wanene da wannan aika-aikar? tabbas yau Munaya tabani matuk'ar tausayi daga ita har munubiya, kai harma Galadima.馃う馃徎鈥嶁檧
Kumuje zuwa danjin Yaya kuma zata kasance馃檰馃徎?.
Yanzufa aka fara wasan馃憣馃徎鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧馃ぞ馃徎鈥嶁檧
*_YA ALLAH ka gafartama iyayenmu馃槶馃憦馃徎_*
[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎馃敓
.......Maman Fauziyya ce taga shirun yayi yawa narashin gittawarmu ta aiko Kamal yagani muna nan, dan ita azatonta ko mama Rabi'a tawuce damu gidanta ne.
Da gudu yakoma ya sanar mata gamucan babu lafiya a d'akinmu.
ai bata tsaya jin k'arshen zancenba ta garzayo, halin data iskemu aciki itama hankalinta yakai k'ololuwar tashi, takira baba k'arami a waya tana Sanar masa, duk da haushinmu dayakeji hakan bai hanashi shiga tashin hankaliba shima. atare suka shigo da dady, shima abbanmu sai gashi yashigo.
Duk kuma jikinsu sai yayi sanyi, aganinsu yakamata su sauraremu ajiyan, amma duk da haka babu iyayen dazasuga wannan abun hankalinsu bai tsashiba, garashi d'an manyan mutanene, nashi mai sauk'ine, amma mune awahale.
Haka aka kira doctor yaduba mu, yace damuwace ta haddasa mana zazza6in, sai kuma yunwa.
Da k'yar maman fauziyya ta taimaka mana mukayi wanka da ruwa mai d'umi, sannan mukayi sallar asubahi. tea ma dak'yar muka shashi sannan mukasha magani, still kwanciya muka k'arayi, nan barci ya kwashemu.
Dadyne ya kalli 'yan uwansa, cikin damuwa yace, 鈥測aya Auwal yanzu bazamuyi wani yunk'urin bincike akan lamarinnan ba? ni dai sainake ganin kamar yarannan bazasu aikata hakaba, tsawon shekaru muna tare dasu, bamu ta6a jin makamancin abinan ba daga garesu, sainake ganin bai kamata mu yanke hunci ba akan abinda bamuda tabbas kuma cikin fushi鈥?.
鈥淗ameesu karka goyi bayansu akan wannan lamarin, babu yanda za'ayi abuga labarinan alhalin bai faruba, kaduba fa shi yaron d'ane ga Sarki, shinema Galadima, kodan tsoron abinda zaije yadawo ai nasan gidan jaridarnan saji tsoron buga labarin鈥?.
鈥渉akane yaya, amma baka ganin mak'iyanshi zasu iya amfani da wannan damar domin 6ata sunansa? maybe kuma su yaranmu tsautsayine ya gitta akansu鈥?.
鈥渕aganarka gaskiyane Jafaru, nima wlhy hakan nake tunani, amma yakamata mujira muji daga gidan Sarki, Dan inhar Dan 6ata sunan yaron akayi nasan bazasu k'yaleba, kuma zasu nememu鈥?.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke yace, 鈥渘idai koma minene gsky aure yakamata ayima Munaya, Dan nikam banta6a cin karo da abinda ya rud'ar daniba irin wannan, mahaifiyar yarannan wlhy batayi barciba jiya, kwana tayi kuka, kuna ganin dai irin cin zarafin da inna tadinga mata jiya a tsakar gida gaban kowa, shin minene laifin A'isha akan wannan lamarin? zata aiki su Munubiya ne akan suje su aikata hakan?鈥?.
鈥渒ayi hak'uri yaya, lamarin inna sai hak'uri, kasan dai halinta ai鈥?.
Haka sukaita tattauna yanda zasu 6ulloma lamarin.
鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?
Jiki a sanyaye ya danna kiran Momma, bugu biyu ta d'aga, cikin girmamawa ya gaidata, ta amsa itama cikeda kulawa kamar yanda ta saba. hakanne yad'an sakashi jin sanyi a zuciya, ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in 鈥淢omma ya jikin Abie?鈥?.
鈥淎lhmdllh Moh'd. wani mummunan labari yanzu Ummu Erfaan takirani take sanarmin?, sai kuma ga mama Fulani ma takira tanata fad'a. yanzu kuma Sauban ya nunamin wasu pictures wai an turo masane鈥?.
Rintse idanunsa yayi cikin k'unar zuciya, murya a sark'e yace, 鈥淢omma nima haka kawai nagani鈥?.
鈥渂an gane kaima haka kaganiba Moh'd, kagayamin gaskiya please, wannan ba k'aramin Abu bane bafa鈥?.
Da k'arfi ya cije lips d'insa tamkar zai hudashi da hak'ori, cikin wata murya dake nuna k'ololuwar 6acin ransa yace, 鈥淢omma wlhy bansan komaiba, yanay idi tabbas munyi kayo da wata yayinya hay wayata tafad'i ta fashe, jiya kuma yayinya takusan fad'uwa a plaza nayi yink'uyin taimakon ta saima ALLAH yasa bata fad'iba, kuma ko ta6a banyiba, shine kawai yau gidan jayiday nan suka maida pictures d'in haka fa鈥?.
Ajiyar zuciya Momma ta sauke, (dan tarigada tasan halin d'an NATA, duk da ba'a shaidar d'an yau musamman idan yabar gaban idonka) 鈥淢uh'd tabbas wannan k'ulline, amma kuma yarinya d'ayace ai鈥?.
鈥渉aka nagani nima Momma鈥?.
鈥測anzu mi sarki yace?鈥?.
鈥淢omma wlhy maganay babu dad'inji, hayma sun shiyya meeting a kaina鈥?.
鈥淗umm Muh'd wannan maganace mai girma, kuma tabbas domin 6ata sunanka ne da namu akayi, akwai kuma dalilinsu nayin hakan, ita wannan yarinyar kodai da saninta kokuma an shigo da itane saboda cikar manufarsu鈥?.
鈥淢omma su waye to?鈥?.
鈥淢asusan ganin bayanmu mana, sun biyo wannan hanyarne domin dak'ileka da ragema kaifi鈥?.
Wani naushi ya kaima k'aramin teble d'in gabansa na glass, nan take ya tarwatse. bai damu da ciwon dayajiba, cikin k'araji yace, 鈥渢abbas kafin suga bayana nizanga nasu!!! rayuwar mahaifina bazata salwanta abanzaba!! Saina wulak'anta dukkan masu hannu aciki kosu waye su wlhy billahi Momma! numfashina fansa akan mahaifina!!鈥?.
Dole Momma tacire wayar daga kunnenta saboda yanda Galadima ke magana cikin matsananciyar tsawa.
Saman kujera ya wurga wayar, batareda ya katse kiranba, afusace yafito daga 6angaren nasa, tsawa ya dakama dogaransa.
Gaba d'ayansu cikin rawar jiki suka nufi motocin da ke fake a wajen, ko jira abud'e masa baiyiba yabud'e yashiga.
Hankalinsu a tashe yake daganin yanayin shugaban nasu, sunsan tabbas ran 'yan maza ya 6aci yau, Dan kowa yasan rashin son hayaniya irinta Galadima a masarautar nan.
Saida suka fito daga masarautar a d'arare sarkin mota yace, 鈥渞anka ya dad'e ina muka dosa?鈥?.
Tamkar bazai tankaba, sai kuma can afusace yace, 鈥減laza!鈥?.
鈥渁ngama Ranka ya dad'e, ALLAH ya huci zuciyarka ya shugabana鈥?.
Banza yamasa bai tanka masaba, sai huci yakeyi yanna karkad'a k'afafu da taunar lips, idonsa yayi zajur saboda masifar 6acin rai.
A plaza ma tunda yashigo kowa ya fahimci yanda cikin 6acin rai, Dan ko kallon masu gaisheshi bayayi, mutane masu siyayya sai kallonshi sukeyi, dama wasu gulmace takawosu dansu k'ara ganema idonsu akan labarin da ayau yazaga ko'ina da ina. kai tsaye wani Office yashiga.
Cikin hanzari Wanda yake a office d'in yamik'e domin kwasar gaisuwa, sai dai yanayin ogan NASA yayi masifar rikitashi.
Bai saurari gaisuwarba yace, 鈥渋nason ganin abinda yafayu a CCTV tundaga safiyay jiya hay daye鈥?.
Jiki Na rawa guy d'in yace 鈥渁ngama ranka ya dad'e鈥?.
Kujera ya jawoma Galadima ya zauna, sannan yagyra zaman computers d'in wajen sosai, tariyo wa yafarayi cikin nutsuwa, saida yadawo Sunday morning 6pm sannan ya saki, tundaga bud'e plaza har zuwa masu share-share da goge-goge dasukayi aikinsu, har lokacin da masu sayayya suka fara Shiga da fita a plaza d'in, har an wuce yace 鈥渄awo baya kad'an鈥?.
A slowly yadawo bayan kad'an, har zuwa kan wasu samari biyu d'aya sanye da jallabiya d'ayan wandon Jeans da farar t-shirt.
鈥渒ayo zooming d'in yayannan dake tsaye sunan waige-waige鈥?.
Zooming d'insu yayi, sannan yasanya play yanna tafiya a slow.
Samarin sunata 'yan kalle-kallene, saikuma zuwa can d'aya yasaka waya a kunne yana magana da kallon cctv camera d'in dake hasko tsakkiyar plaza d'in Inda motoci ke Parking, saikuma ya janye idonsa ya maida kan motocin dakeJere a wajen. da ganin Kasan yana maganane, Dan d'ayan dasuke tare yanata gyad'a Kansa alamar gamsuwa da abinda d'an uwansa yake fad'a.
Galadima Na zaune shiru, idonsa nakan computers d'in yana nazarin gayun har aka wuce Kansu, baice uffanba yacigaba da kallon shigi da ficin jama har zuwa 8:11pm, daga nan Computer tayi d'iff.
Da Sauri Galadima ya kalli sarayin 鈥渕i yake fayuwane?鈥?.
鈥淩anka ya dad'e wlhy nima ban saniba, amma bara Na duba鈥?.
Danne danne saurayin yafara da 'yan dube-dube, babu wata matsala daga nan.
Kallon Galadima yayi yace 鈥渞anka ya dad'e babu wata Matsala daga nan, sai dai Idan daga cameras d'inne鈥?.
A tsawace yace 鈥渂angane mikake nufi daga cameyas d'inne ba!? Kenan hay shigowata jiya babu kenan!? kuma kana zaune a office amma bakayi complain ba tun ajiyan? mika aikata!!? mi suka baka ne domin tozarta ni!!? nace nawa suka baka Saleem!!!!?鈥?.
Kusan duk Wanda ke cikin plaza d'inan a yau yaji wannan hargagin Na Galadima.
Jikin matashin saurayin ne yafara rawa, ya zube a k'asa gaban Galadima saboda tsabar tsoratar dayayi da yanayinsa, tunda yake aiki a k'ark'ashinsa baita6a ganinsa cikin wannan yanayin irin Na yau d'inna ba, duk da labarin abinda yafaru yazo kunanensu, sunkuma ganin a jarida da social media baiyi zaton lamarin zaiyi zafi hakaba.
鈥渨lhy yalla6ai babu Wanda yakeda abinda zai sayeni na cutar dakai, Kaine ka ceci rayuwata daga garari, ka tallafi maraicina a lokacin da nake Neman lalacewa saboda rashin matallafi, kazama gatana nida mahaifiyata da k'annena, mizaisa nabiyema rud'in wasu akan 6ata maka suna....鈥?
鈥測a Isa haka!!鈥?. 鈥榞aladima yafad'a cikin tsawa鈥?.
Gaba d'aya Galadima ya birkice musu a plaza, yasa securitys d'in wajen da dogaransa sun kori dukkan masu sayya dake ciki, ya tartare ma'aikatan wajen a d'aya, ya tabbatar musu da in har munafukan cikinsu da aka had'a baki dasu basu fidda kansuba gaba d'aya sai sunyi dana sanin saninsa.
Kaf d'insu sun rud'e, sai rantse-rantse da k'ok'arin kare Kansu sukeyi, amma yak'i saurarensu, ganin zasu kuma dagula masa lissafi saiya basu suspension kawai aka rufe plaza d'in baki d'aya.
Motocinsa Na k'ok'arin barin wajen motar Muftahu tashigo.
Muftahu ya faka motarsa waje d'aya suka fito shida Harun, (shima Harun abokin Galadima ne makusanci, Dan zan iya cewama yafi sanin sirrin Galadima fiye da kowa a abokansa gaba d'aya, shi d'an waziri ne).
Tunkan su k'araso Galadima ya sauke glass d'in motar da kansa. kallo d'aya sukai masa duk suka tsorata, Dan basu ta6a ganinsa a irin wannan 6acin ranba, baice uffanba, sai nuni daya musu akan su shigo motar.
Basu musaba suka bud'e suka shiga, Muftahu a gaba, Harun yashiga baya kusada Galadima.
Bayan gaisuwa dasukayi garesa babu Wanda Yakuma cewa komai, Dan ko gaisuwar bai amsa musuba, hannu kawai ya d'aga musu.
Sun hau titi sarkin mota yace 鈥淩anka ya dad'e ina muka dosa?鈥?. 鈥榗ikin girmamawa da taka tsantsan yay maganar鈥?.
Murya a shak'e yace 鈥済idan Jayiday鈥?.
Sarkin mota bai fahimtaba, amma yana tsoron tanbaya, murya k'asa-k'asa ya tambayi Muftahu 鈥?.
Murmushi kawai Muftahu yayi yana girgiza kai, shiya shiga yima sarkin mota kwatance har suka Isa.....
鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?
Muna tsaka da barci saboda allurar da doctor yamana Innaro tafad'o d'akin, babu ko tausayi tashiga tashinmu cikin d'ad'd'aka mana duka a baya da cinyoyinmu.
Dagani har Munubiya a firgice muka tashi zaune.
鈥渒utashi munafukai, Ashe abin ba a iya runguma da kama hannu ya tsayaba harda ciki kuka kwaso mana?, tsinannun gayyar tsiya, wlhy dagaku har uwarku yau saikin bar gidanan, a yau d'inan idan ubanku bai saki uwarkuba kun tattara kun tafi saina tsine masa albarka, yazo yaza6a ko Ku ko ni yau agidanan. sai kuma tafashe dakuka, takama bakin zaninta datayo lullu6i tana sharar hawaye, 鈥渒ai ni dai Malam ya cutar dani akan had'a wannan aure da d'iyar marasa asali, ai gashinan ta Haifa mana bala'i da masifa, shikuma yatafi yabarni da kunyata, Malam kacuceni katafi kabar mana baya da k'ura. Wlhy yau sai A'isha tabar gidanan itada gayyar tsiyar 'ya'yanta, natsaneku daduk wandama zai soki A'isha, natsaneku wlhy, takuma fashewa da kuka.
Tuni matan gidanmu kowa yafito, wasu harsun shigo falonmu, wasu kuma Na daga k'ofar d'aki, harda tsirarin 'yan biki da sukak'i tafiya domin tsayawa kallon kwaf.
Cikin matan gidanmu ne wata taje tasanarma innaro wai bamuda lafiya munata amai duk abinda mukaci, anakiran likita ya dubamu yace duk munada ciki wata uku-uku.
Ni da Munubiya mun had'e kai muna kuka mai tsuma rai saboda tozarcin da innaro kemana muda mahaifiyarmu agaban bainar jama'a.
Dady da Abba k'aramine suka shigo sunama innaro magana akan bafa haka zancen yakeba, babu Wanda yace munada ciki.
Hayayyak'o musu tayi tana zaginsu, wai k'aryane suna kare Innarmu ne, aida likitan bai fad'aba baza'aje a sanar mata ba.
Cikin 6acin rai baba k'arami yace, 鈥渋nna waye yaje yafad'a miki wannan maganar to?鈥?.
鈥渃ikin matan gidanan mana, kuma daga bakin wadda nasan bazataimin k'aryaba鈥?.
Ran Dady ma a wannan karon ya 6aci, afusace yace, 鈥渋nna wacece acikinsu? Wace 'Yar isakar matace鈥?.
Nanafa matan gidanan mu suka shiga raba idanu akan juna.
Innaro tace 鈥渒arka kuma zaginta, idaba ayiba bazatace anyinba, kuma koma wacece bazan fad'aba, idan kuma ni kake zagi sainaji?鈥?.
鈥淎LLAH ya huci zuciyarki inna, ni yaza'ayi Na zageki鈥?.
鈥渒ai dai kasani sakarai鈥?.
Duk abinda ke faruwa Abbanmu da Innarmu Na saurare daga d'akinsa amma acikinsu babu Wanda yayi yunk'urin fitowa.
Kayanmu innaro tafara kwasa tana watsowa waje, wai saimun bar gidan.
鈥淚nnalillahi wa inna'ilaihirraji'un, wannan wane irin tashin hankaline?鈥?. 鈥榠nnarmu tafad'a cikin matsanancin kuka鈥?.
Rungumeta Abbanmu yayi shima yana k'ok'arin maida kwallar data cika masa idanu.
Ganin abin yana Neman wuce gona da iri baba k'arami yafita da hanzari, wani tsoho dake can k'asan layinmu yaje ya d'akko, tsohon abokin Malam faruku ne na k'ut da k'ut, shika d'aine zai iya takama Innaro burki kuma.
Aiko hakance ta kasance, tunda yashigo yay magana Innaro ta dakata da abinda takeyi tana huci da fidda numfashi.
Tsoho Malam Labaran yace, 鈥渉aba innar jafaru, da hankalinki da girmanki kike aikata wannan abin Na yara a gaban sirikanki da 'ya'yanki da jikokinki? Shin babu mai fad'a miki kijine wai kekam?鈥?.
Cikin sassauta murya tace, 鈥渕alam mai kanwa nasan bakasan ainahin abinda yafaru bane kaima, amma wlhy da dakanka zakace Auwalu yasaki marar asalinnan sukama gabansu itada 'ya'yanta am.....鈥?
Hannu ya d'aga mata, yagyara tsayuwarsa jikin sandarsa dake taimaka masa tafiya, naji komai innar jafaru, amma wannan hanyar da kuka biyo ba wai itace mai 6illewa ba, bincike yakamata ayi domin asan gaskiyar lamarin. dan haka zoki wuce gida, zuwa gobe zamu tattauna akan lamarin sannan kowa ya nutsu, mukuma jira abinda zai fito daga can gidan Sarkin鈥?.
Badan innaro tasoba tafice, hakama matan gidanan mu basuso wasan yak'are iya nanba, sunso a yau Innarmu tabar gidan da saki, sannan mukuma mahaifinmu ya koremu. Kowa taja k'afa takoma d'akinta cikeda takaici da addu'ar ALLAH yasa daga gidan sarkin suma su d'auki mummunan mataki akanmu.....
Maman fauziyya Ce kawai ta nuna damuwarta akan lamarin
鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?
Su Galadima ma sun isa gidan jaridar *Manuniya* tun sanarwar isowarsa ta kad'a hantar cikin ma'aikatan wajen, musamman wad'anda basuda laifi akan lamarin, tirsasu akayi.
Shi kansa manaja d'in wajen a kid'ime yake, dukya rikice yarasa matsugunni har Galadima da gayyarsa suka iso office d'in bisa jagorancin sakatare d'insa.
K'asa yazube kawai yana kwasar gaisuwa wajen Galadima, ko kallo bai ishi Galadima ba, cikin daka tsawa yafara magana...........鉁嶐煆?
Tofa masu karatu, ko manajan jaridar MANUNIYA zai amsa laifinsa? Kokuwa zai fad'i wad'anda suka sanyashine inba laifinsa bane shima? to koma dai shima da had'in bakinsa?. Wane mataki masarautar su Galadima kuke ganin zata d'auka akansa? Shin ina ma maganganun Momma suka dosa ne? Miya faru da mahaifin Galadima har suka koma k'asar India da zama?.馃槙
Kumuje zuwa my guys danjin yanda zata kaya. da amsoshin d'unbin tambayoyinkun nan.鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧馃ぞ馃徎鈥嶁檧
_Naga mutane basa fahimtar yaren yarima馃槀, yarima later R ne baidashi, bawai tsamin bakine dashiba fa, kun gane, naga wasu kamar suna zaton tsamin bakine dashi馃ぃ._
_Ngd da comments d'inku, kuna sakani farin ciki sosai, kuyi hak'uri da rashin amsawa ta, kunada d'unbin yawane wallahi馃槉馃グ馃グ馃グ馃グ. I love you wujiga-wijiga all馃榿鉁嬸煆?._
*_Ya ALLAH ka gafarta ma iyayenmu_*馃槶馃憦馃徎[4/22, 2:14 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
__________________________
*_Naga idi馃檰馃徎, Galadima fa ba tsamin baki bane dashi, Ku fahimta馃槀, bashida (R) ne, amma gashinan nayi gyara, ina fatan yanzu zakuna fahimtarsa馃ぃ._*
_______________________________
馃憠馃徎1鈨?1鈨?
.........Ba manager kawaiba, hatta da sauran jama'ar dake gidan jaridar saida suka tsorata da tsawar Galadima, su Muftahu ma tsorone ya kamasu, sunsan irin wannan matsanancin fushin gareshi babbar matsala ce ga lafiyarsa.
Aikam sai gashi ya dafe kansa, saboda yay wani mugun sara masa, da sauri Harun yajawo kujera ya kamashi ya zaunar, har yanzu dafe yake da kan nasa.
Muftahu ya furzar da hucin, matsalar da suke gudun ta d'akko hanyar faruwa kenan. kallon manaja dake durk'ushe har yanzun yayi,
yace 鈥渢ashi ka zauna鈥?.
Mik'ewa manaja yayi jiki Na rawa yakoma saman kujera, Muftahu da Harun ma suka zazzauna.
Cikin tsare gida Harun yace, 鈥渕anager ka nutsu, kabamu had'inkai wajan fad'ar gaskiya, inba hakaba wlhy zakayi nadama ne, ba kaiba hatta da ahalinka saisunyi nadamar kasancewarka acikinsu鈥?.
Manaja yashare guntun kwallar dasuka taru masa a idanu, a nutse yafara fad'in 鈥渁i tunkan jaridar jiya tafita nake acikin nadama, nayi dana Sanin kasancewata ma'aikacin jaridar da aka ci zarafin d'an Wanda yay tushen kasan cewata a wannan matsayin danake, da ace remote d'in rayuwata a hannuna yake, dana tariyo bayana jiya bata shigo rayuwata ba, amma Na.....鈥?
Muftahu ya katseshi cikin d'aga masa hannu 鈥渒aga manager, ba rayuwarka mukazo saniba, munason ka fad'a mana waye yasaka wannan aikin? nawa suka biyaka kamusu shi?鈥?.
鈥渨lhy tallahi yalla6ai basu biyani komaiba, kaga wacan jakar sune suka ajiye min ita, amma ko bud'eta banyiba. kuma babu wani ma'aikaci daya buga labarinan agidan jaridar nan da hannunsa. sune da Kansu adaren jiya sukayi komai, bayan sun had'emu waje guda da bindugu, kuma sunzo nannane dukansu fuska arufe, wlhy ko fuskar mutum d'aya bamu ganiba, yanzu haka sun kwashe muhimman documents dake ma'aikatar nan sun tafi dasu. kuma sunsan da zuwan yalla6ai gurinnan yau, Dan komai sunyishine a tsare kamar yanda mukaji suna hira a tsakaninsu鈥? manaja ya fashe da kuka, sannan yacigaba da fad'in 鈥渟aboda sunsan zakuzo nan yau, sunje gidana tun adaren jiya, sun kwashemin iyali da mahaifiyata, yanzu haka suna wajensu, sun tabbatar min inhar wani magana yafito abakina abakin ran matata da yarana hud'u da mahaifiyata sai k'anwata. wlhy ina cikin masifa, yau anan Na kwana, nakasa fita waje saboda banason jin 6atancin da jama'a suka gani a wannan safiyar akan yalla6ai. Wlhy Na rantse muku bansan komaiba鈥?.
Tunda manaja yafara magana kowa yay tsit, Galadima bai d'agoba saida yaji manaja ya ambaci iyalansa Na wajen wad'anda suka aikata aika-aikar. Idonsa yakad'a yayi jazur, sosai manaja ya tsorata da idanun Galadima, haryana tunani a zuciyarsa anya Galadima shi kad'aine, bashida aljanu kuwa?.
Komai Galadima bai ceba, ya tashi dafe dakai yafice daga office d'in, ma'aikatan wajen sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa, amma kallon kowa baiyiba yafice.
Dogaransa suna ganinsa suka mik'e da Sauri, Mota suka bud'e masa yashiga, suma su Muftahu suka fito da hanzari.
鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?
Tun daga fitar innaro sai gidan yay tsit, kowa ya kama gabansa zuwa d'akinsa, a can suka cigaba da gulmace-gulmacensu suda bak'insu.
Niko da Munubiya muka shiga raira sabon kuka, munubiya ta kamo hannuna ta rik'e anata.
鈥淢unaya dan girman ALLAH kibarni Na kar6i hukuncin laifina, nice Na aikata bakeba, miyasa zaki cema iyayenmu kece? kibari nafad'a musu gaskiya please 鈥?.
鈥淎'a Munubiya, wannan laifin nawane, karki manta ta sanadina abinnan yafaru, da ace Fu'aad bai kaimu plaza d'innanba da hakan bata faruba wlhy, munubiya farincikina fansane agareki, har abada bazan iya juriyar ganinki cikin k'unciba, Dan Girman ALLAH koda da wasa kar wani agidannan yaji banice Na aikata abunnanba koda kuwa innarmu Ce, namiki alk'awarin zan jure duk wata fitina dazata taso, zankira Fu'aad yafito muyi aure, duk da naso ace rana d'aya aurenmu zai kasance, amma haka ALLAH ya k'addara mana鈥?.
rungume juna mukayi muka kuma fashewa da kuka, cikin shashshekar kuka Munubiya ke fad'in 鈥渕i mukaima Wanda ya k'ulla mana wannan sharrin? mi muka tare masa agidan duniyarnan Munaya?鈥?.
鈥渂an saniba Munubiya, bansan waneneba? Amma nafi zargin gidan wannan jaridar, aganinsu sun sami babban labari, bara su buga suyi suna, Sun zaluncemu Munubiya, sun yad'a labarin abinda ba haka faruwarsa ta kasanceba, Galadima ko ta6aki baiyiba amma suka saka har yana kissing d'inki, wane irin zaluncine wannan? wlhy nima bai ta6a niba da mukayi karo a filin idi, amma ki duba hannunsa rik'e da nawa ajaridar, Munubiya banga laifin iyayenmu ba, kowanne mahaifa bazasu so ganin wannan mummunan abinba, kuma ko zamu kwana rantsuwa bakowa zai amince damu ba, INA tausayama innarmu, ada Yaya muka k'are ma a gidannan bare yanzu?, munubiya innarmu innarmu, banason innarmu tashiga mummunan hali akanmu, yazamuyi innarmu ta fahimcemu, koda ace kowa bai yarda damu ba inason innarmu fahimcemu munubiya.....鈥?
鈥淣a fahimceku 'ya'yana, tabbas nashiga tashin hankali da ganin hotonku a jarida, kuma a yanayin da kowace uwa ba zataso ganin 'ya'yanta a wanna halinba, kuma ace bazata shiga fiyeda yanayin Dana fad'aba, sai dai ni ba abinda naganine yasakani cikin rud'ani irin haka ba harna yanke jiki na fad'i, cin zarafin innaro ne.
'ya'yana nasan bazaku aikata koda makamancin hakanba, dan naji ajikina sharri akai muku.....鈥?
Da gudu suka sakko a gadon sukazo suka fad'a jikin innarsu suka cigaba da raira kuka harda ita kanta innar, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru.
Duk suka nutsu suka mata bayanin komai, har Munaya ta d'akko wayar da Galadima ya barta da ita a filin idi ta nuna musu.
Nanna INA ta kuma fahimtar akwai 6oyayyen al'amarin abinda basu saniba akan lamarin, kuma tafi zargin k'ullin Anma Galadima ne kawai, 'ya'yanta k'addara Ce ta sakasu cikin sark'ak'iyar, itadai Addu'arta ALLAH ya fiddashi da 'ya'yanta baki d'aya, saitaji yabata matuk'ar tausayima.
Suna cikin haka saiga mama Rabi'a dasu Ayusher, nanma aka kuma zaman warware zance, mama Rabi'a da inna suka kuma fahimtar komai yanda yake.
Nasiha suka Shiga yima 'ya'yan Nasu mai ratsa jiki, sannan suka nuna musu illar biyema samari batareda wani dogon tunaniba, duk sai jikin su Munaya yayi sanyi, sun fahimci bin Fu'aad dasukayi plaza shine yazama babban kuskurensu.
Sun nemi gafarar iyayen nasu akan hakan dasuka aikata, daganan suka Shiga tattauna maganar Auren munaya da Abba yakafe akan nanda sati biyu.
Sun Yanke shawara akan akira Fu'aad, inhar da gaske yakeyi to saiya fito kawai.
Akan wannan shawarrar suka zauna gaba d'aya.
鈽呪槄.鈽呪槄.鈽呪槄.鈽呪槄.鈽呪槄
Har suka Isa cikin masarautar Galadima baiko motsaba, yana tangad'i da layi yashige 6angarensa, daga Muftahu har Harun babu Wanda yayi yunk'urin binsa.
Tunda yaje yazube saman 3seater bai sake sanin inda kansa yakeba saboda matsanancin ciwon kai dake damunsa, da k'yar ya iya gabatar da sallar magrib da isha'i a lokaci d'aya, a saman abin sallar ya kwanta rigingine dafe da goshi, yana kwance shiba mai barciba shiba ido biyuba.
8:30pm dukkan mai ruwa da tsaki a meeting d'in ya hallara, hatta da sarki gaba d'aya, sai dai kuma babu Galadima babu dalilinsa har mama Fulani tafito.
(Babbar magana 馃槰) na fad'a a raina, saboda ganin tsantsar mulki da isa ajikin hamshak'iyar tsohuwa dazata iya kaiwa shekaru 77 a duniya, sai dai tsantsar hutu da gayu ya 6oye ziryan d'in tsufan nata, gata da k'aramin jiki kuma, daka ganta haka bafulatanar asali.
Tunda ta fito kowa a falon yamik'e tsaye saboda girmamawa a gareta, amma banda sarki, ya risinar da kansane kawai alamun girmamawa ga mahaifiyar tasa.
Saman kujera 2seater ta zauna cikeda izzar mulki, (saikace itace sarkin馃う馃徎鈥嶁檧) sai da ta gamaima kowa dake falon kallon tsaf sannan takuma kamewa, cikeda k'asaita tace, 鈥淪hi yana ina? Ko raini. Hankalin nasane ya hanashi zuwa?鈥?.
Kowa dake wajen yasan galadima take nufi, babu wanda ya iya cewa komai sai wani matashin saurayi dazasu iya zama sa'annin juna da galadima, ya gyara zamansa yana wani 6ata rai shima, 鈥淕ranny kinsan halinsa aii, ba ganin kowa da gashi yakeba a masarautar nan mtsoww鈥?.
Mama Fulani ta turo hanci ga bada, cikeda fushi ta bada umarnin a kira mata jakadiya.
babu dad'ewa saiga jakadiya tashigo, k'asa ta zube tamkar zatayi mata sujuda tafara fad'in 鈥淎LLAH yaja zamaninki ranki ya dad'e, kinga taki kinga tawasu, fatanmu kiga tawasun wasuma, Sarautar gagara badau a hannunki take, domin kaida kaya ai duk mallakar wuyane, duk mai shirin ganin barcinki ya tabbata shima bazaiyi nasaba, kece k'i gudu samaza gudu, jaruma mai dad'and'en tarihi, kin ajiye tarihin da babu wanda yake dashi a masarautar nan, koda kuwa mai martaba gagara badaune, ALLAH ya tsare gabanki ya tsare bayanki, mace mai kamar maza, mazanma a tafin k'afafunki suke ya uwar gijiyata鈥?.
Sosai kirarin jakadiya yayima mama Fulani dad'i, takuma kishingid'a a kujerar, cikeda izza tace, 鈥渋nason ganin Galadima yanzunan鈥?.
Angama damusa k'i sabo, cika umarninki wajabtaccene a gareni 'Yar sarki, matar sairi kuma mamar sarki, wata ran kakar sarki, ki huta lafiya babbar giwa鈥?.
Fita jakadiya tayi.
Ta isa 6angaren galadima, inda sarkin k'ofa yashiga domin yimata iso, halin daya isake shugaban nasa ya razanashi, amma haka yadake ya isar da sak'on jakadiya.
Da k'yar galadima yay masa nuni akan yabarta tashigo.
Babu dad'ewa saiga jakadiya, ta rusina cikin girmamawa ta gaisheshi, bata damu da rashin amsawar tashiba ta isar da sak'on mama Fulani. hannu kawai ya iya d'aga mata.
Kusan mintuna 7 da fitar jakadiya yamik'e dafe da kansa dayakejin tamkar zai fad'o k'asa, jiyay falon na juya masa, ya dafe bango da gyar kusan 2munute sannan yad'an lafa, haka yafito yana d'an tangad'i, wajen mota yanufa, dan bazai iya zuwa sashen mama Fulani da k'afaba, saboda akwai tazara sosai a tsakaninsu.
Da sauri sarkin mota yataso ya bud'e masa, shima shiga yayi mazaunin driver, sauran dogaranma suka shishshiga mota.
Da k'yar galadima yafurta 鈥渟ashen mama Fulani zamuje, sauran su zauna鈥?.
cikin girmamawa sarkin mota ya amsa, sannan ya sanarma sauran dogaran.
dukkan jama'ar dake falon idanu suka zuboma Galadima daya shigo dafe da kansa, baima kowa magana ba yasamu can gefe ya zauna, har yanzu hanunsa na saman kansa, muryarsa a shak'e yace, 鈥渂arkanku da dare鈥?.
Hakan yayi masifar k'ona ran mama Fulani, saboda ma ya rainata tare zai gaidata da kowa? kuma bazaizo gaban taba ma yabata girmanta?.
A falonma wasu sun amsa wasu basu amsa mishiba, shi baima San sunayiba, ta kansa kawai yakeyi.
Cikeda izza mama Fulani tace, 鈥渢o isashe, gaisuwar ma saina rok'a ko yaya鈥?.
Dukda halin dayake ciki bai hanashi sakin guntun murmushiba, ya janye hannunsa daga goshinsa, idanunsa dasuke matuk'ar jajur yad'ago ya kalleta, ba mama Fulani niba kowama a falon ya firgita daganin idanunsa, hakan ya tabbatar musu da bashida lfy kenan.
Ahankali Yakuma furta 鈥渂agykanki da hutawa鈥?.
鈥淎LLAH yarabamu da bak'in hali鈥? . 鈥榤ama Fulani tafad'a batareda ta amsa gaisuwar ba鈥?.
Baice uffanba ya maida kansa ya duk'ar, tareda kuma tallafe goshin yana ta6e baki.
Idanun Ummu Hasheem yacika da kwalla saboda tausayin Galadima, ko kad'an batasan bashida lafiya ba, dukda d'azun ta aika bayinta su duba matashi suka tarar yafita.
Mama Fulani kam baki ta k'ya6e tareda kuma hard'ewa a kujera, takai dubanta ga wani dake gefenta, Matawalle! ahad'amin video call da Zeenah yanzunan鈥?.
鈥渁ngama ranki ya dad'e鈥? Dan danan yahad'a video call bayan yakira wata number, wata kamilalliyar matace ta bayyana ajikin System d'in, tana sanye cikin shigar kamala, kallo d'aya namata Na hango kamannin Galadima tartare da ita, dukda kamar tafisa haske, hakkane ya tabbatar min da Momma ce.
Cikin girmamawa ta gaida mama Fulani, ita kuma ta amsa cikeda k'asaita sannan tafara magana kamar haka.
鈥渘asan kowa yasan miya taramu anan wajen?, bana buk'atar maimaita wannan shed'ancin a harshena, wanda kuma ya aikata yasan kansa, Dan haka hukunci biyune, yanada za6i aciki. Na farko tozarcin da yayama masarautarnan da zubar mana mutunci mun haramta masa auren kowacce yarinya data fito daga kowacce masarauta, na biyu ya gaggauta fidda matar aure acikin shekararnan kafin yaje yayma wata ciki a waje akawo mana d'an tsakar gida a masarauta, kokuma mu muza6a masa acikin bayin gidannan, hukunci na farko babu sasauci acikinsa kuma babu canji, Na biyu yanada za6i nemowa komu nema masa. Wannan shine tabbataccen hukuncin kotun fulani. Idan akwai mai abun fad'a sainaji?鈥?.
Kowa ya girgiza kai alamun a'a, wasu hukuncin bai musu dad'iba, wasuko yamusu fiye da zaton mai karatu.
A hankali Galadima ya yunk'ura yatashi batareda yacema kowa uffanba yanufi hanyar fita.
鈥渢o fand'ararre, daka tafi ba'a gama magana ba ai uwarka zataji, mara mutunci mai bak'in hali鈥?.
Juyowa Galadima yayi ya kalli mama Fulani, wani k'asaitaccen murmushi ya sakar mata sannan yay salute nata yafice abinsa鈥?.
Mafi yawansu saida suka zaro idanun mamakinsa, dama Kowa yasan galadima baya tsoron mama Fulani a masarautar, duk masifarta saima yagadama yake amsata, gaisheta kam saiya zo k'asar yatafi ma bata ganshiba. Iya kacinta tayi masifarta da sababi ta hak'ura, babu yanda ta iya dashi.
Murmushi kawai shima sarki yayi baice komaiba.
Mama Fulani kam kasa koda motsi tayi a kujerar saboda abin kunyar da galadima yayi mata gaban kowa, ta tsani shed'anin yaronnan mai ido a tsaitsaye dabaya shakkar kowa. Kwafa tayi sannan tatashi tabar falon tana tafiya cikeda mulki da izza.
Gaba d'aya suke fad'in ALLAH ya huci zuciyar sarauniyar sarakuna.
Duk abinda ke faruwa Momma naji kuma tana gani, amma dayake Galadima yana bayan laptop d'in bataga miyayiba, hasalima bataji ko sau d'aya yayi magana ba, hakanne ya tada hankalinta, mama Fulani Na barin wajen ta katse call d'in, waya ta d'auka takira number Galadima, amma harta tainke bai d'agaba.
Kira Na biyu ta sakeyi, hakan yay dai-dai da shigowar Galadima falon dafe da kansa.
Da k'yar ya iya d'aga wayar, muryarsa a shak'e yace, 鈥淢omma zan kigyaki anjima鈥? bai jira cewarta ba ya yanke wayar.
Hankalin Momma yakuma tashi, tasan ransa yakai k'ololuwar 6aci, da sauri ta danna kiran Harun, yana d'agawa ko gaisuwar dayake mata bata amsaba tace, 鈥淗arun maza jeka duba min Moh'd yanzunan鈥?.
Yanda yaji Momma Na magana shima kansa saiya kid'ime.....
鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?.鈽?
Ayusher tafita tasiyo min credit domin kiran Fu'aad.
Jikina a sanyaye nagama loda katin, tunani nakeyi shin Fu'aad zai kar6eni bayan yaji abinda yafaru a jiya zuwa yau? tunda komai akan idonsa yafaru. Na dad'e ina juya wayar a hannu kafin Nayi dialing d'in Number d'insa d'in, harta tsinke bai d'agaba, ban damuba Na sake kiransa da tunanin ko baya kusa da wayarne.
Bugun farko kuwa ya d'aga wayar...........鉁嶐煆?
Humm masu karatu, mi kuke tunanin zai faru tsakanin Munaya da Fu'aad a waya, zai kar6eta kokuwa sa6anin haka?.
Yaya zata kasance ga Galadima kuma?.
Wannan amsar tana a page 12 da zaizo muku ranar Monday馃槂馃憣馃徎.
Barkanku da juma'a.
Musha weekend lafiya馃馃徎馃グ馃グ.
Team *_INNARO & MAMA FULANI_*馃ゴ馃ゴ鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧.
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu._*馃槶馃憦馃徎
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠1鈨?2鈨?
.......Murya a sanyaye Munaya tace, 鈥淎ssalamu alaika鈥?.
鈥渨a'alaikissalam鈥?. 鈥榳ata murya ta amsa sa6anin Fu'aad鈥?.
鈥淯hhm 'yar uwa please, ko ina mai wayar dan ALLAH?鈥?.
鈥淢ai wayar kuma? ai nice mai wayar鈥?.
Wani iri munaya taji a zuciyarta, suka kalli juna itada Munubiya dan a Hans free tasaka wayar. alama munubiya tamata akan tayi magana. kai Munaya ta jinjina mata, sannan tace, 鈥渁yya 'yar uwa sorry dan ALLAH, wlhy wanine yabani number d'innan mai suna Fu'aad鈥?.
鈥淔u'aad!鈥?. 鈥榶arinyar ta maimaita daga can鈥?, saikuma tace 鈥渢o gaskiya 'yar uwa yabaki wrong Number, ni sunana Afnan, ina Katsina state ne鈥?.
Wasu hawaye masu zafi suka zubo a kumatun Munaya, 鈥渟hikenan ngd sis..., kiyi hak'uri鈥?.
鈥渘o babu damuwa鈥?.
Bayan Munaya ta katse wayar ta dafe kai tana hawaye, daga Ayusher har Munubiya basa Neman k'arin bayani, tunda sunji komai, Munubiya ta share hawayenta tana murmushin takaici, 鈥渒ibarshi karki sake kiranshi, nasan shine yabama yarinyar nan wayar akan tace wrong number ne, ya ALLAH ka kawo mana sauk'i a wannan lamari dai鈥?.
Tsaki Ayusher taja, ta kamo hannun Munaya 鈥渟weet sis..., please wannan karya zama abinda zai ta6a zuciyarki, ki d'auki hakan matsayin ba komaiba, kuma hakan da Fu'aad yayi yasani kuma tabbatar da zargin danake a kansa, ku duba yanda yazage saimunje birnin gayu plaza aranar鈥?.
Gaba d'ayansu zuba mata ido sukayi cikin wani yanayi.
Feena dake kwance tatashi zaune, 鈥渉umm aini wlhy tunda zancen jaridar nan yafito zargina yana kan Fu'aad ne, Na barine akirashi dama danna sake tabbatarwa鈥?.
Munubiya tace, 鈥渟isters nifa duk Na kasan fahimtar zancennan naku fa, zargi babu k'yau ai, miye ribarsa idan ya aikata hakan? dukama yaushe muka San juna dazai yi hakan a garemu? yarasa kuma dawa zai mana hakan sai galadima?鈥?.
Zama Ayusher ta gyara, tafara musu bayani dalla-dalla. 鈥渢ad'ora da fad'in kinsani ko saboda galadiman yayi?鈥?.
鈥渢o amma Dan zaima Galadima mu miye Na had'awa damu kuma?鈥?.
鈥渨annan amasar tana wajen Fu'aad sister 鈥?.
Hankalin Munaya yatashi ainun, itafa ko kad'an bata ta6a kawo Fu'aad acikin wad'anda take zargiba, amma maganar Ayusher tasata dogon nazari yanzu, duk da dai bawai tama yarda baneba kwata-kwata..
鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄
Lokacin da harun ya iso sashen Galadima bai wani jira isoba yashiga, kwance ya iskeshi bisa 3seaters sam6al, hannunsa d'aya dafe da k'irji, d'aya dafe da kansa.
Da sassarfa ya k'arasa gabansa 鈥淪ameer lafiya kuwa?鈥?.
Da hannu Galadima yamasa nuni da k'irjinsa da Kansa.
鈥測a salam, Sameer! Shiyyasa naketa cemaka kacire abunnan a ranka, kafasan matsalarka batason yawan takura da tunani鈥?. Wayarsa dake ringing ya Ciro a aljihu, Momma Ce ke kiransa.
Cikeda girmamawa ya amsa sallamar data masa, sannan naji yace, 鈥渨lhy Momma bashida lfy, kuma k'irjinsa yake complain akai鈥?.
鈥渙k Momma 鈥?.
Yana yanke wayar sai yayi kiran Dr Jalal.
鈥淛aalal please kana gida kuwa?鈥?.
Bansan wace amsa ya bashi ba daga can, naji dai yace, 鈥減lease kazo kaduba Galadima鈥?.
Babu dad'ewa saiga Dr Jaalal, damuwa sosai Nagano a fuskarshi saboda ganin halin da Galadima yake ciki.
Harun ya taimaka masa suka kaishi bedroom, sannan yamasa allurar barci.
Babu dad'ewa kuwa barcin ya kwasheshi.
Su duka ajiyar zuciya suka sauke, Dr jaalal yama harun sallama yatafi.
Yana fita Muftahu Na shigowa, gaisawa sukayi da Harun, sannan ya tambayi jikin Galadima d'in.
Harun ya amsa masa Cesar da sauk'i.
Anan sashen Galadima suka kwana, sai dai kowanne acikinsu da dalilin kwannan nasa.
*_Washe gari_*
Alhmdllh Galadima yatashi jikinsa da d'an sauk'i, yakuma ji dad'in ganin Harun da Muftahu a tare dashi. bai iya zuwa masallaciba sai a d'aki yayi salla.
Yana zaune akan sallayar yana azkar su Muftahu suka shigo, zama sukayi bisa Sofa suna jiran yak'arasa azkar d'in nasa.
Bayan ya k'arasa ya juyo garesu, hannu ya mik'a musu sukayi musabaha, suka tamyashi jikinsa.
Yace da sauk'i Alhmddlh, sannan yace, 鈥淢uftahu inason ticket, dan yau zan wuce India, ina buk'atar ganin doctor d'ina鈥?.
鈥渙k babu damuwa, bara na bincika idan akwai jirgi mai zuwa India daret鈥?.
Harun yamik'e yana fad'in 鈥渂ara ahad'a maka ruwan wanka to鈥?.
Kai ya d'agama harun, ya maida idonsa ya lumshe tareda jingina da Waldrop.
Muftahu dake latsa waya yad'ago ya kallesa, 鈥渂abu jirgin dazai tashi a yau, sai gobe 1:30pm鈥?.
Batareda ya bud'e idonsa ba yace, 鈥渂incika min ta Abuja ko legos. dan bazan iya kuma kwana a k'asar nanba yau, ina buk'atar ganin lilita鈥?.
Kai Muftahu ya jinjina ya cigaba da latse-latsensa a wayar, kusan mintuna 4 sannan yad'ago, 鈥渁n samu, amma zai biya Abu-Dhabi ya sauke Passenger's, daga nan zasuyi hutun kamar na 1hour鈥?.
Idomsa a lumshen yace 鈥測aushe zai tashi daga Nan?鈥?.
鈥?12pm, yanzu na saya maka ticket d'in zuwa Abuja, jirgin zai tashi 8am ne鈥?.
鈥淥k bara na shirya to鈥?.
Harun dake tsaye yana saurarensu yace 鈥渂ara naje Na watsa ruwa nima鈥?.
Shima Muftahu mik'ewa yayi suka fita tare.
Galadima yashiga bathroom, kusan mintunansa 40 sannan ya fito, dauriya kawai yakeyi, amma shi kad'ai yasan irin suyar da zuciyarsa ke masa. tsaf ya shirya cikin Suit blue, rigarshi ta ciki Orange, yayi k'yau sosai, yana zaune bakin gado yana saka takalminsa Muftahu yashigo da sallama.
d'ago idanunsa yayi akan Muftahu, sannan yatashi tsaye yana gyara belt nashi, 鈥測a maganar binciko yarinyar nan?鈥?.
鈥淣agama komai, inason kasami nutsuwane sai muyi maganar daman鈥?.
Galadima dake gyara 'yar sumarsa da bawani yatarata da uban yawa bane yace 鈥渙k, katura min komai zan duba, sannan inason kaje kuyi magana da commisshiner of police akan iyalan Manager d'innan鈥?.
鈥渙k yalla6ai angama insha ALLAH鈥?.
Sallamar Harun suka amsa gaba d'aya, ya zauna kan sofa sannan yace 鈥渁mma yakamata ma'aikatan plaza su koma aikinsu, naga jama'a kamar suna fassara abin dawani Abu daban kuma鈥?.
Murmushin gefen baki galadima yayi, ya ajiye Cumb d'in hannunsa yajiyo yana kallonsa 鈥渁ini yanzun kuma babu kuma ta sigar dabaza'a fassara ni ba, inaga akan mace kawai yarage jaridu su buga duniya ta ganni, so sukoma aikin su kawai鈥?.
Daga Harun har Muftahu kallonsa suke cike da tausayawa. Muftahu yace wannan d'inma kansu sukai mawa, kuma ALLAH bazai barsuba鈥?.
鈥渋nsha ALLAHU鈥?. 鈥榗ewar Harun鈥?.
Galadima baice komaiba, sai d'an kimtse kimtsen da ba'a rasabane ya k'arasa, su Harun kam suka fice suka bashi waje.
Baifi mintuna 10 ba yafito suka fice, bayan yatsaya da bayinsa na mintuna biyar, bansan miya fad'a musuba, naga dai sunata faman godiya damasa addu'a.
Aka bud'e masa mota yashiga, duk wanda yake k'ark'ashimsa saikaga fuskarsa ta canja alamun baya son tafiyar tasa.
Kai tsaye fada suka nufa, bayan motocin sun tsaya aka bud'e masa yafito.
Shi kad'ai yashiga fadan, cike take da dukkan masu ruwa da tsaki anata fadanci.
Saida ya gaida sarki, sannan ya zauna mazauninsa kusada sarkin, sauran fadawan suka gaidashi cikin girmamawa, shima ya amsa cikeda mutuntawa.
鈥測a adalin sarkinmu yau zan koma inda na fito, saboda inason ganin likitana鈥?.
Murmushi sarki yayi, sannan ya gyad'a kai bare da yayi maganaba.
Da sauri Dogarawa suka d'auka da fad'in Sarki yajika Galadima, Yakuma amsa, yana maka addu'ar sauka lfy kuma.
鈥渋na godiya da wannan alfarma鈥?. 鈥榞aladima yafad'a cikin rissinar da kai alamun girmamawa鈥?.
Sarki yad'an gyara zamansa, ahankali ya furta 鈥渒a gaidamin da d'an uwana da gimbiya Zeenah, insha ALLAH nima nextweek ina nan zuwa鈥?.
鈥渋na godiya ranka shi dad'e, insha ALLAH d'an uwanka zaiji鈥?.
鈥済yad'a kai kawai sarki yayi鈥?.
鈥淎n gaisheka galasima, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka, ALLAH ya kaika lafiya yabama adalin tsohon sarki lafiya, Alkairin ALLAH da ni'ima sukai a garesa, gaba dai gaba dai Galadima mai jiran gado, d'an sarki jikan sarakuna k.....鈥?.
Hannu ya d'aga musu alamar ya Isa.
Ya risinar da Kansa domin girmamawa ga fada sannan yamik'e suna jera masa addu'oi, yayinda shikuma yake amsawa asaman la66ansa.
Bai shiga sashen kowaba yay tafiyarsa, suna isa filin jirgi ko 20 minutes basuyiba jirgin su yatashi zuwa Abuja.
Muftahu da Harun da dogaransa suka dawo cikeda kewarsa.
Koda ya isa Abuja hotel yanufa kai tsaye, yakama d'aki danya huta, akwai kusan 3hours nan gaba kafin jirginsu ya tashi. Rigar suit d'insa yacire tareda tie d'in, sannan ya zame wandon da rigar cikin ya kwanta dagashi sai boxer da vest.
Juyi kawai yakeyi agadon, Dan barci yakasa d'aukarsa, abinda yafaru a kwanaki biyunnan yakasa barin zuciyarsa, yarasa wane irin hasashe zaiyi ga masu aikata masa hakan... Ringing d'in da phone nasa tayine yasakashi bud'e idanunsa, wayar yajawo yana kallon mai kiran. *_Sweet papi_* yagani ajikin wayar, yay saurin d'agawa kafin ta tsike.
Cikeda girmamawa tamkar yana a gabansa ya rissinar da kansa bayan yatashi zaune, 鈥淏arka da hantsi ranka ya dad'e鈥?.
Daga can aka amsa 鈥渄a yauwa Muhammad, ina fata kana lfy?鈥?.
鈥淎lhmdllh ranka ya dad'e鈥?.
鈥淭o masha ALLAH, dama mamanka Ce takirani takemin wasu bayani, duk da kafin kiran nata dama naga zantukan dake yawo a jaridu da yanar gizo, zuciyata bata yarda zaka aikata hakanba Muhammad, amma inason sanin gaskiyar zancen?鈥?.
鈥渨lhy ranka ya dad'e sunyi hakanne kawai domin 6atamin suna, amma ainahin abunda yafaru shine.............鈥?
Nan Galadima ya zayyane masa komai.
Murmushi mai sauti tsohon yayi, har Galadima Na jiyosa, sannan yace, 鈥渉ummm! to yanzu kai kana wace nahiya ne?鈥?.
鈥淚na Abuja zan koma India, saboda jikina yana Neman motsawa鈥?.
鈥渢o to, hakanma dakayi dai-daine, amma a kwantar da hankali, komai mai wucewane, komai kaga yafaru da d'an Adam rubutaccene a littafinsa, dama ita rayuwa tana tafiyane da k'addara, yanzu zan isa fada, bayan kasamu nutsuwa idan kaje zamuyi magana, duk da watak'ilma nashigo ganin mahaifin naka k'arshen watannan鈥?.
鈥渢o shikenan, ngd sosai, ALLAH yak'ara tsahon rai da lafiya mai amfani鈥?.
鈥渁min ya rabbi Muhammad鈥? cikin tsokana tsohon yace 鈥渒aga d'annema, duk kabi ka susuce akan k'aramin Abu, kazo Na sanmaka jarumtata mana鈥?.
Dariya Galadima yayai (karon farko danaga yayi dariya馃檴馃槀) cikin tausasa harshe yace 鈥渉aba dai, ai sai dai Na sammaka tawa, nifa sabon jinine, ta ina mai shekaru 80+ zai fi mai 29 jarumta?鈥?.
Daga canma Sarki dariya yayi, cikeda k'aunar jikan nasa, 鈥渦hmyim tunda kace haka idan kazo saimu gwada kwanji ai鈥?.
鈥渉hh tom kafad'ama inno ta tsumaka sosai, inba hakaba zatayi takaba鈥?.
鈥渏a'irin gora zan kamakane ai, ALLAH ya tsare hanya, ka gaida iyayen naka鈥?.
鈥渮asuji ranka ya dad'e, a gaidamin inno, tayi hak'uri wannan karon ban shigo naci tuwon taba, nazo k'asarne da uzurori dayawa, gashima banyi ko d'ayaba鈥?.
鈥渮ataji insha ALLAHU, babu komai, adage dai da addu'a watarana sai labari, *zakaran da ALLAH ya nufa da cara, ko ana mazuru ana shaho sai yayi jikana kaji*.
Murmushi Galadima yayi dan jin maganar kakan nasa, sukayi sallama cikeda k'aunar juna鈥?.
Ajiye wayar yayi yakoma ya kwanta fuskarsa d'auke da murmushi, yana k'aunar kakansa (mahaifin Momma) saboda shima yana nuna masa k'auna da kulawa, akan la66ansa ya furata 鈥淎LLAH ya k'aramaka tsawon rai my sweet papi鈥?.
Amin Galadima.
鉀桂煆烩€嶁檧bara nalek'o su munaya.
鈽呪槄鈽呪槄*鈽呪槄鈽?*鈽呪槄鈽呪槄
Bansan yanda zan musalta muku irin bak'in cikin danakeba a yau, tundaga kiran Fu'aad zuwa yanzu zuciyata sai suya takemin, banida wata walwala, sai dai ina dannewa kodan kwanciyar hankalin innarmu da 'Yar uwata Munubiya, dama tun randa abunnan ya faru bamu sake fita koda tsakar gidaba dagani har 'yar uwata, abinci sai dai innarmu kosu Aryaan su kar6o mana.
Habaici dai da gugar zana muna shanshi acikin gidanmu, innarmu bata cemusu uffan, nikuma mai maida murtanin damuwa ta hanani iya cewa komai, 'yan biki dai zuwa yau kowa yakama gabansa, yanzu dagamu sai mune agidan.
Sauk'inmu d'aya tun ranar innaro bata sake shigowa gidanba, inaga baba mai kanwa yahanata.
Babu Wanda yay mana maganar komawa makaranta, muma kuma bamuyi yunk'urin zuwanba, kullum dai innarmu NATA k'ok'arin ganin munkwantar da hankalinmu, a koda yaushe cikin mana nasiha take dayimana kwatance da rayuwarta itada mama Rabi'a, takan Nuna mana muhimmancin hak'uri da amfanin yinsa, koda baka ci ribarsa anan gidan duniyaba zakaci ribarsa a lahira inda kowa ke rububin tara ayyukan alkairi.
Alhmdllh muma mun fara rage damuwar kodan ganin farin cikinta, Abu d'ayane kecin zukatanmu shine maganar fidda miji da Abbamu yace nayi acikin sati biyu kacal, gashi kuma babu wani tsayayye a hannu.
Duk mun rame mun zuge nida munubiya, dama gamunan bawani aukin kirkiba, ahaka muka cinye satin da abin yafaru.
Yau ta kasance lahadi, wasu a yaran gidanmu sunata shirin ziyartar gidajen amare, kaf sa'aninmu 'yan matan gidan sunyi shirinsu, Fauziyya, Fiddausi, Safara'u, Haleematu, amma ban da mu, Dan kogaya mana mu shirya ba'ayiba, saima Fauziyya Ce data tashigo da safe gaida innarmu take sanar damu wai mushirya zamuje gidajen amare.
Dagani har Munubiya bamuce da ita komaiba, sai 'yar dariya damukayi.
Koda suka gama shirinsu basu nememu ba, sai Fauziyya Ce tashigo danta mana magana akan mufito.
Turus tayi Dan ganinmu babu wani shiri, hasalima muna falo zaunene, Munubiya ta kwantar da kanta bisa cinyata ina kwance mata kai, innarmu kuma Na zaune gefe suna waya da mama Rabi'a, sai Aiyaan da Aryaan daketa faman buga game.
Hira mukeyi da Munubiya akan wasu write-ups datake dubawa a Instagram da akayi akan maganarmu da galadima, cikin damuwa take karanta writeup d'in, shiyyasa bamuga shigiwar Fauziyya ba saida tayi magana...
鈥渨ai sisters kuna nufin ma ko shiryawa bakuyiba?鈥?.
Gaba d'aya muka kalleta, nayi murmushi ina fad'i 鈥渒iyi hak'uri Fauziyya, kutafi kawai, har yanzu fita bata kamacemu ba, dan abubuwa basu gama daidaitaba tukunna鈥?.
Cikeda damuwa ta gyad'a kai, jiki a sanyaye tace 鈥渟hikenan saimun dawo鈥?.
鈥渙k to Ku gaida mana amare鈥?.
Kanta ta jinjina nanama tana ficewa.
Munubiya tace, 鈥淎LLAH Sarki Fauziyya, itadai tana sonmu鈥?.
Nad'an murmusa ina taje mata Wanda Na tsefe, 鈥淢unu.... nima ina k'aunar Fauziyya wlhy itada mamansu, sune kad'ai suke sonmu agidannan, Na tabbata wannan fitar dama ba'a sota damuba, itace kawai taketa k'ok'arin taga munje d'in鈥?.
鈥渨lhy hakane sweetheart 鈥?. 鈥榗ewar Munubiya鈥?.
Innarmu dai tanata waya, Dan haka batace mana komaiba.....
鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽?
Lokaci na gabatowa yay shiri yabar hotel d'in, zuwansa airport babu dad'ewa jirginsu yad'aga, sun tsaya a Dubai Abu-dhabi sukayi hutun 1hour sannan suka nufi India.
Tunkan jirginsu ya sauka Sauban da Samha sukazo d'aukarsa.
Dan haka yana fara taka matakalar jirgin suka hangosa, cikeda jin dad'i suka nufo gareshi.
Duk da fuskarsa babu walwala hakan bai hanasu nuna farincikin ganinsa ba, shima dai yayi farin cikin ganinsu, duk da kwanaki 4 kacal kenan da barinsa k'asar.
Sauban ya kar6i bag d'in hannunsa yana fad'in yaya welcome鈥?.
Kansa ya shafa yana lumshe ido alamun amsawa.
Samha ma tace 鈥淲ellcom back Uncle Sam鈥?.
Ahankali ya furta Thanks you dear, ya school?鈥?.
鈥淎lhmdllh Uncle, ya kabaro Nigeria? 鈥?.
Murmushi kawai yayi batareda ya amsa mata ba, yasan surutun Samha bamai k'arewa bane, yana amsa wannan wata zata jeho masa.
Sauban ya bud'e masa back seat ya zauna, sannan yarufe shi yakoma mazaunin driver, Samha Na gefensa.
Idonsa ya lumshe ya maida Kansa ya jingina da kujera.
Wani madaidaici Gida suka isa, Wanda baza'a kirashi k'aramiba, sannan ba k'ato baneba, sai dai muce tsaka tsaki.
Samha ce tafita da kanta tabud'e gate d'in, Wanda ana ganin komai dake farfajiyar gidan ta jikinsa daga waje. Sauban ya ida shiga da motar, kusada wasu motoci uku yay parking, Samha data k'araso tabud'ema Galadima yafita.
Kusan atare suka shiga falon gidan, yana gaba suna baya.
Masha ALLAH nafad'a saboda ganin tsaruwar falon, sai dai shiru gidan alamun babu kowa a ciki.
Ya zube bisa rukunin kujerun farko dasuka kasance golden color and white. Isaka yad'an turo daga bakinsa sannan ya kalli Sauban dake shirin zama shima.
鈥測anaji gidan shiru? inasu Momma ne?鈥?.
鈥渄uk suna hospital, har jakadiya ma, zamu tafi d'akko kanema Aunty Mimi tatafi itama, dama ita kad'aice agidan saboda mu muna school 鈥?.
鈥淥k, ya jikin Abie?鈥?.
鈥渉ummm da sauk'i yaya鈥?.
鈥渕ik'ewa yayi yana guntun murmushi, tunda yafara girma yafahimci mahaifinsa Na kwance yakejin idan antanbaya Momma jikin Abie tana cewa da sauk'i, amma shi shekaru kusan 25 Abie Na kwance amma shifa baiga wannan sauk'inba, kawai suna dai fad'ane, sauk'i d'ayane zai iya cewa yagani shine magana da idanu da Abie keyi kawai.
Da wannan tunanin ya haye steps d'in benen, yana tafiya yana sasaauta tied d'in wuyansa. ahaka harya k'arasa d'akinsa.
Komai needs kamar yanda ya barsa, (kullum ne babu fashi sai Samha ta gyara d'akin) Komai a d'akin fari ne, sai golden dasuka kasance d'ai-d'ai. d'akin yayi k'yau sosai, sai tashin k'amshin turarensa daya manne yakeyi, gakuma na air fresheners, saiya had'u yana bada wani ni'im taccen k'amshi. kayansa yashiga cirewa d'ai-d'ai yana sagewa jikin hanger. wanka yashiga sannan ya gabatar da sallan data riskeshi a hanya .........
鈽呪槄*鈽呪槄*鈽呪槄*鈽呪槄*鈽呪槄
Da daddare muna zaune munacin tuwo saiga kiran Abba yashigo wayar innarmu, tana d'agawa yace ta turo masa mu.
To kawai tace ya yanke wayar.
Kallonmu tayi ad'an sanyaye, tace 鈥渋dan kun gama cin abincin kuje abbanku Na kira鈥?.
Daga ni har Munubiya sai da gabanmu yafad'i, jiki a sanyaye muka amsa da 鈥渢o innamu鈥?.
Kasa cigaba Dacin abincin mukayi, dole muka ajiye kawai mukaje muka wanko hannu..................鉁嶐煆?
馃ko wane kira kuma Abba yakema su Munaya馃槙?.
Barkanmu da dawowa鉁嬸煆?, ina fata duk kuna cikin k'oshin lafiya?馃槃馃馃徎.
To gashinan Na k'ara yawan page Masu k'orafi馃槃鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧
0 comments:
Post a Comment