.......Mun d'anji sanyi a ranmu, ganin kiran bamu kad'ai baneba, hardasu Safara'u Ashe, waje muka samu muka zauna, sannan muka gaidasu.
Fiddausi kad'ai ake jira, itama babu jimawa sai gata ta shigo da sallama, duk muka amsa, ta gaida su Abba.
Falon yay tsit Na mintuna biyu, sannan Abbanmu yay gyaran murya, kallonmu yake mu duka cikin nazari, ganin muduka mun hallara yace 鈥渕un kiraku nan ne saboda dalilin abinda yafaru kwanan nan, hankalina yakasa kwanciya da zamanku a gabanmu, mun yanke shawara nida 'yan uwana zamu aurar daku duka kawai, kowace saita cigaba da karatunta a d'akinta, muma hakan zai sama mana kwanciyar hankali. dan haka kowacce saita sami mai zuwa wajenta ta sanar masa munason ganin magabatansa inhar da gaske yakeyi鈥?.
gaba d'aya muka amsa da to abba kanmu ak'asa.
Wasunmu murna suke da hakan, amma banda ni da Munubiya, dan bamuda wasu tsayayyu a hannu, bawai samarinne bamu dasuba, a'a wad'anda zamu kawo amatsayin Na aurene matsalarmu.
Maganar Dady ce ta katsemin tunani, danaji yana fad'in su sutashi suje, amma ni Na tsaya.
Haka suka fice suka barni, duk tsoro yakuma cika zuciyata. bayan fitarsu baba k'arami yanuna min gabansu alamar Na matso.
Tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki haka natashi Na isa gabansu, na zauna kaina ak'asa.
Baba k'arami yace 鈥淢unaya!鈥?.
Muryata Na rawa Na amsa da 鈥渘a'am baba鈥?.
Ya gyara zamansa sosai, 鈥淢unaya na sanki bak'ya k'arya, kifad'a min tsakaninki da ALLAH miye had'inki da Galadima?鈥?.
Gabanane yafad'i daaam!, nai k'ok'arin had'iye kukan daya taho mini 鈥渨lhy Baba banida had'in komai dashi, hasalima ban ta6a saninsaba sai awajen hawan sallah, shima ba ganin fuskarsa na ta6a yiba, sai kuma randa mukai karo dashi a filin idi ina neman su kamal, kuma wlhy aranar hak'uri kawai nabashi, koma amsamin baiyiba yatafi, ni banma san shibane alokacin鈥?.
鈥渁mma miyasa aka buga hotonku kuna cikin plaza d'insa?鈥?.
鈥淒ady kuyi hak'uri, tabbas nasan munyi laifi anan, amma Ku yafemin, dan nasan da bamuje plaza d'inba a daren da k'ila hakan bai faruba, amma wlhy abinda yafaru shine...................., cikin nutsuwa ta zayyane musu komai, saidai batace Munubiya ce zata fad'inba, tace itace.
Koda basuga ainahin abin da idonsu ba sai zukatansu sukayi sanyi, baba k'arami yace 鈥渢o ALLAH ya k'yauta, wannan akwai wani Abu daban dabamu saniba acikin lamarin, ALLAH ya warware komai cikin sauk'i鈥?.
Duk mukace amin.
Dady yace, 鈥淢unaya! bisa hak'uri damukaita bama yaya kin sami sassauci akan sati 2 daya ce ki fidda miji, yanzu saiki nutsu ki kawo kamar sauran 'yan uwanki, insha ALLAH bayan babbar salla zamu aurar daku gaba d'aya kawai, ALLAH yayi muku albarka kinji, kucigaba da kare mutuncinku, sannan Ku koma zuwa makaranta tunda abin ya lafa鈥?.
Kai na gyad'a sannan nayi godiya.
Na iske innarmu da Munubiya jigum-jigum a falo suna jiran dawowata, nasami waje na zauna jikina a sanyaye.
Innarmu tace, 鈥渕iya faru kuma?鈥?.
Guntun murmushi nayi INA share kwallar data zubomin, 鈥渂abu komai innarmu, sun tanbayeni gaskiyar abinda yafaru ne, sannan since sun janye maganar sati biyu nafiddo miji da sukace nayi. nima za'a had'a danawa zuwa bayan salla kamar su Munubiya, kuma since mukoma makaranta鈥?..
Daga Munubiya har innarmu ajiyar zuciya suka sauke, 鈥渢o Alhmdllhi, ALLAH yabaku mazaje na gari鈥?. 鈥榗ewar innarmu鈥?.
A zukatanmu muka amsa mata da amin.
Washe gari.
Mukayi shirin zuwa makaranta, gudun abinda zaije yadawo sai muka saka nik'af dagani har Munubiya kamar yanda innarmu tabamu shawara muyi.
Alhmdllh tunda muka fita bamuci karo da abinda ya Sosa zuciyarmu ba, saboda fuskokinmu arufe suke.
A ajima babu Wanda ya shaidamu sai Bilkeesu, nanma dai munyi mun fito lafiya babu wata damuwa. amma saboda a d'ar-d'ar Muke bamu wani sakeba, ana fitowa lectures muka nufi gida.
Haka muka cigaba da zuwa makaranta kulum fuska arufe, ko cikin anguwa za'a aikemu saimun saka nik'af, dan yanzu fuskokinmu sunrigada sun zama sannanun fuskoki....
鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄
Yana gama kimtsawa yafice, ko abincin da Samha ta shirya nasa bai sauraraba, kai tsaye yanufi Hospital d'i. da Abie ke jinya.
da jakadiya yafara cin karo tana rik'e da Khaleel a hannu, khaleel yakwace yataho da gudu yana fad'in 鈥淯ncle oyoyo鈥?.
Hannayensa ya bud'e masa yafad'a jikinsa, ya shafa kan yaron yana fad'in 鈥渕y boy ykk?鈥?.
鈥渓afiya Uncle Sam... yaushe kadawo?鈥?.
Murmushi Galadima yayi, yad'an ja kumatun khaleel 鈥渢o maganatu yau na dawo鈥?.
Dariya yaron yayi, zai sake joho wata maganar Galadima ya d'ora yatsansa akan bakin yaron alamun yayi shiru. Shirun kuwa khaleel yayi dan yasan halin Uncle Sam.. saraii.
Jakadiya ta rissina tana gaidashi, amsawa yayi fuskarsa da 'Yar fara'a, ya tambayeta ya jikin Abie.
鈥渏iki Alhmdllh ranka ya dad'e鈥?.
Kansa kawai ya jinjina mata yay gaba rik'e da hannun Khalel.
Da sallama ya shigo d'akin da Abie ke jinya, d'akine babba kamar Bana asibitiba, daka gani Kasan anyisane saboda manyan mutane irinsu, Momma na zauna akujerar gaban gadon da Abie ke kwance, gadon Kansa bawai ainahin gado bane na asibiti, duk wasu na'urori ne ajikinsa, da alama sune suke taimakama jikin Abie d'in, k'umba Momma ke yanke masa.
Aunty Mimi na zaune bisa kujerun da aka shirya a gefe tamkar falo, System Ce agabanta tana danne-danne.
Sallamar Galadima yasata d'agowa tana murmushi, 鈥淢y k'ani oyoyo鈥? tafad'a tana ture system d'in daga cinyarta.
Murmushi yamata shima, cikin maganarnan tasa ta k'asaita maikama da anmasa tilas yace 鈥渕y dear aunty barkanki鈥?.
Hannu tasa tad'an bigi damtsen hannunsa, cikin wasa tace barka zakace ba bagyka ba鈥?.
Shafa Inda tad'an bigesan yakeyi yanda 6ata fuska kamar wani k'aramin yaro, 鈥淎LLAH akwai zafi aunty Mimi, wai har yanzu ban girma da buguba awajenki?鈥?.
鈥渢ab ai da sauranka, sai randa kayi aure zan daina鈥?.
Bakinsa ya ta6e yak'arasa inda Momma take yana fad'in, 鈥渁iko k'yadad'e baki barinba kenan鈥?.
Momma dake murmushi saboda drama d'in tasu ta kalli Abie da shima fuskarsa take a washe alamun yayi farinciki da ganin d'an nasa.
Gabansa yaje ya durk'usa, saitin Face d'insa, ya saka hannunsa cikin NASA fuskarsa d'auke da murmushi yace, 鈥渕y Abie barka da rana鈥?.
Da idanu Abie ya amsa masa, dan sune bakin maganar yanzu.
Yakuma masa magana da ido alamar yaka barosu?.
Murmushi Galadima yayi na takaici, sannan yace, 鈥渕ai martaba na gaidaka, shima zaizo nextweek鈥?.
Farin cikine Yakuma fad'ad'a a fuskar Abie, dasu sukasan yanayinsa, sukad'ai zasu iya fahimtar farin cikinsa ko damuwarsa, musamman ma Momma.
Momma dake kallonsu tayi murmushi, Galadima ya maida kallonsa gareta, 鈥淢omma na yana sameku?鈥?.
鈥淎lhmdllh Muh'd, yaka barosu?鈥?.
Baki yad'an ta6e sannan yace 鈥渓fy lau, ya jikin Abie?鈥?.
鈥渏iki Alhmdllhi, dan randa ka tafi yatsun hannun damarsa sund'an motsa鈥?.
Da Sauri Galadima yace 鈥渄a gaske Momma?鈥? yay maganarne yana kallon hannun Abie d'in, sannan cikeda farin cikin ya sumbaci hannun yana fad'in Alhmdllh ala kulli halin, ALLAH yabaka lafiya my sweet Abie鈥?.
Lumshe idanu Abie yayi farinciki na k'ara fad'ad'a a face nashi, aunty Mimi da momma da jakadiya suna kallonsu cikeda tausayi suka amsa da amin. khalel yata6a kafad'arsa, juyowa yayi yana kallonsa. yaron yakai hannu yana sharema Galadima hawayen dasuke kwance a kumatunsa. galadima yajawosa ya rungume yana sumbatar kan yaron, fuskarsa d'auke da murmushi.
鈽呪槄鈽?
Yau mune k'arshen tafiya school, saboda lectures d'in yamma ne damu, Fauziyya kuma batada lafiya bazatajeba.
Kasancewar abubuwa sun kuma lafawa yau sai bamu saka nik'af ba, amma yana rik'e a hannunmu idan mun shiga cshool zamu saka.
Mun fito bakin titi muna jiran taxi ko napep saiga wata bak'ar mota wulik ta faka agabanmu, dagani har Munubiya d'auke kanmu mukayi gefe.
Mai motar ya sauke glass d'in yana kallonmu, sallama yayi mana, Munubiya ta amsa, nikam koma kallo bai isheniba.
Ganin haka saiya bud'e motar yafito, matashin saurayine bak'i k'yak'yk'yawa mai yawan fara'a. Yace, 鈥渉aba 'yan mata, babu fad'a miya kawo gaba鈥?.
Cikeda tsiwa nace 鈥渟ai aka cemaka mu 'yan matane? to matan aurene鈥?.
Murmushi yayi, sannan ya gyara tsayuwarsa, 鈥渄ear hakan ma dakikayi yakuma tabbatar min da Bahaka baneba鈥?.
d'an hararsa nayi na d'auke kaina, danni yanzu maza duk haushi suke bani wlhy.
Dariya yayi, 鈥渙h sweety karkisa na sume mikifa a titinnan鈥?.
Ganin yana neman shiga hancinmu yasani jan hannun Munubiya muka bar wajen, k'yalemu yayi Yakoma mota ya zauna. har muka sami abin hawa yana kallonmu. haka yayta bin mai napep d'in har k'ofar makaranta, daga nan kuma bamusan ya akayiba mudai muka shige.
Kwana biyu da faruwar haka muna wanki a tsakar gida saiga ya Anas yashigo, ya kallemu yana murmushi, twins cikinku waye mai saurayi mai bak'ar mota?鈥?.
Mu duka kallonsa mukayi, gwaggon Haleema da maman safara'u dake aiki a tsakar gidan suma duk suka kallemu.
Da sauri Munubiya tace 鈥渕unaya Ce yaa Anas鈥?.
鈥渒ije to yana jiranki a k'ofar gida鈥?.
harara na dallama Munubiya 鈥渨lhy Munubiya k'arya dai babu k'yau鈥?.
Dariya tayi tacigaba da wankinta, 鈥渒itashi kije kina 6ata masa lokaci鈥?.
Hijjab na d'auka nafita danufin zuwa na sauke masa masifa na dawo.
Gwaggon Haleematu da maman Safara'u suka bini da kallo cikin wani yanayi. oho ni bammasan sunayiba.
Jingine da motarsa na gansa, sanye yake da shadda ruwan zuma, harda hula, sa6anin ranar damuka gansa da k'ananun kaya, kwarjini yamin nakasa masa masifar danayi niyya, namasa sallama sannan nace 鈥渕iya kawoka k'ofar gidanmu? waya nuna maka ma?鈥?.
Yad'an murmusa, 鈥渕iyake kawo saurayi gidansu budurwa?鈥?.
鈥渙ho maka鈥? Nafad'a cikin kauda kai gefe.
鈥渒imga baby sorry, mu ajiye wannan drama d'in, ni bada wasa Nazo nanba, tun randa na ganku keda 'yar uwarki kuka rikatani, nasa a raina duk wadda ALLAH yabani cikinku tamin, bansami kwanciyar hankaliba saida na binciko gidanku, sunana Haidar Mustapha鈥?.
Shiru nayi ban tanka masaba.
Yay murmushi yana matsowa kusa dani, 鈥減lease mana baby, kimin magana?鈥?.
Da k'yar ya sami na amsashi sannan nima nafad'a masa nawa sunan. abinda na fuskanta da haidar shi mutumne mai sauk'in kai, sannan ko kad'an banga alamun yaudara ba tattare dashi.
Cikin kwanaki kad'an mungama sabawa da haidar, sabawa maiban mamaki, wadda nikaina har mamakin kaina nakeyi wlhy.
Alokacinne kuma yaa Marwan shima ya nuna yanason Munubiya, wayyo zokuga farin ciki wajen iyayenmu, tamkar su zuba ruwa a k'asa susha dan dad'i.
Wannan Abu fa ya bak'anta ran 'yan gidanmu, sunso ace munyi kwantai, har agama sakama 'ya'yansu rana mu babu mazaje a hannu, amma ALLAH ya fisu ai.
Kud'in Munubiya aka fara kawowa gidanmu, daga nan saina Safara'u. nima saiga iyayen Haidar sunzo, ranar har kukan dad'i mukayi muda innarmu, duk wani masoyinmu zai tayamu murna akan wannan al'amari, dan ba'a ta6a tunanin zamu iya samun mazaje da wuri ba saboda abinda yafaru.
Sauran 'yan uwanmu ma duk ankawo kud'ad'en aurensu, dandanan aka tsaida ranar aure, watanni uku kacal, bayan salla babba da wata biyu.
Zuwa yanzu kam hankalinmu ya kwanta, sai dai matsaloli na gidanmu da basa k'arewa, saikuma abinda yafaru tsakaninmu da Galadima, wani lokacin mukan fuskanci tozarci daga wasu jama'a idan mun fita, tunma muna zama muyi kuka har zukatanmu suka fara dakewa.
Galadima kam bamu sake koda jin d'uriyar saba, hakama Fu'aad, tunima Haidar ya mantar dani wani Fu'aad gaba d'aya.
Ahaka babbar Salla tafara gabatowa. Masu shiri natayi, nikam dai babu mu aciki, dagani har Munubiya munyi alk'awarin babu inda zamuje sai gidan mama Rabi'a........
Munshiga bikin salla lafiya, inda iyayenmu sukayi layya kamar yanda kowacce shekara suka saba, itama innaro anmata, babu inda mukaje wannan karon, su Safara'u dai ansha yawo, ranar suyar nama kuma saiga dukkanin amare sunzo yawon salla, abin tamkar had'in baki, kowaccensu tayi 6ul-6ul da ita, harma damasu tsarabar ciki.
Kowacce jinta take a sama, mijinta yafi na kowa, iyayensu kam anata baza hak'wara da tink'aho ana zuba mana habaici.
Babu Wanda ya tanka musu acikinmu, dan innarmu ta hana.
wajen Ayusher mukejin wai babu Galadima a hawan salla wannan karon, hakan bai dameniba, danni baya gabana, nama manta dawani Galadima can.
Bayan gama bikin salla da kwanaki uku saiga wani tashin hankali.
Iyayen Haidar sunzo wai abasu kayansu sun fasa, ance musu ni 'Yar iskace.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Yau munga tashin hankali muda innarmu, kuka da hawaye innarmu keyi itada mama Rabi'a, haka aka had'a kayansu aka basu.
Innaro tashigo tafara tata tsiya babuji babu gani, sai zuba cin mutunci takeyi ga innarmu, 'yan gidanmu natajin dad'i, jisuke kamar anmusu gafara da fasa aurennan nawa, aganinsu yaza'ayi 'ya'yansu suna auren masu kud'i nima na auri mai kud'i, ai bazai yuwuba..
Cikin kuka nakira Haidar ina tanbayarsa miyasa zaimin haka, yasan tun farko ba sona yakeba miyasa yazo gidanmu har iyayensa suka shiga.
鈥渒 dalla malama yimin shiru, ni mahaukacine zan auri yarinyar da aka buga hotonta jikin jarida wani na kissing d'inta, ok da an 6oyemin za'a bani sauran wani Ashe ked'in karuwar Galadima ce, to ALLAH ya toni asirinku dagake har iyayen naki, ko a hanya muka had'u karki kuma nuna kin sanni ma鈥?.
Baki na bud'e da nufin maida masa murtani ya yanke wayar, nayi saurin kuma kira amma sai najita arufe.
Kuka na fashe dashi, bansan miya faruba sai dai najini ak'asa kawai.
Cikeda tashin hankali Munubiya tayo kaina tana kuka da girgizani.
Dandanan d'akin yacika dasu Dady, babu alamar rai atare dani, hakan yasa aka d'aukeni da gaggawa sai asibiti.........
鈽呪槄鈽呪槄鈽?
A 6angaren Galadima kuwa wasu ayyukane suka d'auke hankalinsa, gaba d'aya yayi busy saboda kamfaninsu na k'ok'arin fidda wata waya sabuwar k'ira.
Abinda ya faru kuwa a Nigeria ya watsar dashi gefe, saboda gargad'in da doctor d'insa yamasa akan yarage yawan damuwa, saboda ciwonsa yana k'ok'arin tashi.
Haka yadage yacire komai d'in, amma har yanzu yasaka amasa aikin bincike ta k'ark'ashin k'asa, sannan iyalan manager sun ku6uta suma, yabar Nigeria da sati biyu suka sakosu.
Gaba d'aya ya ajiye duk wani abinda yashafi Nigeria a gefe, ko bikin salla bai hakarta ba, sannan zuwan dayankan yi duk karshen wata ma ya daina, Momma batace dashi komaiba akan k'in zuwan nasa.
Dan lokacin da mai martaba (mahaifin momma) yazo sun tattauna sosai akan abinda yafaru, shine yace Galadima yad'an tsahirta da zuwa Nigeria nawani lokaci, idan komai ya lafa sai acigaba da bincike, dan wad'anda suka aikata sumafa baza suyi barciba, yanzu idonsu abud'e yake akan komai, amma idan anyi burus dasu komai ya lafa sai a d'auki mataki. Wannan yasa bai sake zuwaba, gameda business d'insa nacan kuwa Harun yana tsaye akan komai.
Fitowarsa kenan daga office zaije gida yad'an kimtsa sannan yaje asibi, wayarsa tashi ruri, zarota yayi daga aljihu ya duba, ganin Muftahu a kan layi saiya maida wayar cikin aljihu kawai batare da ya amsaba.
Hannu yabama beejay abokin aikinsa sukayi sallama akan saikuma gobe. yana k'ok'arin shiga motar kiran yakuma shigowa, shiga yayi ya zauna sannan ya d'aga, suka gaisa da Muftahu, ya tambayesa jikin Abie.
Shikuma ya amsa da Alhmdllh.
Muftahu yace, 鈥淎LLAH yasa ban takuraka ba? Inason muyi magana ne dama鈥?.
Kwantar da kansa yayi jikin kujera ya lumshe idanunsa, cikeda k'asaita ya furta 鈥渋na saurarenka鈥?.
Daga can Muftahu yay murmushi, sannan yace 鈥渄ama akan yarannan ne, d'aya daga cikinsu an fasa aurenta, wai Wanda zai auretan yace yafasa sabo...da sa... sa.... yakasa fad'a saboda maganar tamasa nauyi abaki鈥?
Galadina yace 鈥渒afad'a mana, kasanfa bana son kwana-kwana a magana ni鈥?.
鈥渨lhy maganarce babu dad'in ji, ca yayfa wai ita karuwarka ce, yanzu haka yarinyar tana asibitima鈥?.
Da k'arfi ya cije lips d'insa, zuciyarsa na suya, saikuma ya saki guntun murmushin takaci, yatashi zaune yana bud'e idonsa, 鈥渉umm Muftahu waye shi yaron dazata aura d'in?鈥?.
鈥渨lhy ban saniba nima鈥?.
鈥渙 right karka damu, zanyi tunani akan lamarin, ni bamma duba bayanai daka turomin akan yarinyarba fa, abubuwa sunmun yawane wlhy. amma masu bibiyar tata basuga wani abunda ya shafi waccan maganarba?鈥?.
鈥淕askiya basuga wani abuba sa6anin tunaninmu, ammafa bama yarinya d'aya bace ba, twins ne, kaduba bayanan kagani鈥?.
鈥渙k sai munyi magana kenan鈥?.
Bayan sunyi sallama yay shiru yana tunani a ransa, da gani kasan ransa a6ace yake, ya furzar da huci daga bakinsa sannan ya tada motar yatafi. idonsa yayi jajir saboda bak'in ciki, yanzun har takai wani yafasa auren wata akansa? waye yamasa wannan abin? miya masa ne da zafi haka ya tozartashi? wlhy yayi alk'awarin duk Wanda keda hannu akan wannan tozarcin da akai masa bazai d'aga masa k'afaba, dolene yayi dana sanin saninsa.
Da wannan tunanin ya k'arasa gida.
Babu kowa a gidan sai jakadiya, su Sauban suna makaranta, Aunty Mimi da Momma kuma suna asibiti, jakadiya ta rissina tana gaidashi, hannu kawai ya iya d'aga mata ya haye sama.
Binsa tayi da kallon tausayi, hakan da yayi mata ya nuna ransa a 6ace yake, danshi mutum ne mai girmama nagaba dashi, dukda tana a k'ark'ashinsu bai ta6a wulak'antata ba, wannan tarbiyar mahaifiyarsu ce kuma.
Koda yashiga rigarsa kawai yacire ya zauna a bakin gado, medical glasses d'insa yasaka sannan yajawo System yabud'e, Emailil na Muftahu ya shiga.
Dukkan bayanai da tarihin su Munaya ne awajen.
Gaba d'aya ya nutsu ga abinda yake karantawar, shi mamakima abin yabashi, sukuma wane irin gida wad'annan yaran suka fito haka? Wani abun yakan bashi dariya (sai dai yakanyi dariyar ne a zuciyarsa), wani kuma haushi, tsaf yagama karanta tarihin yaran masu kama da juna.
Ya mik'e yana zagaye d'akin da tunanin miye mafita, har yanzu zuciyarsa bata bar karanta masa da hannun wad'an yaran aka masa wannan abunba, sai dai shi kansa yana tambayar kanasa mizaisa su aikata? miye kuma ribarsu bayan suma hardasu aka tozarta?. yanzu kuma zuciyarsa na masa wani tunani daban bayan yaji tarihinsu.
Zuciyarsa na cigaba da tunzurashi akan yayi amfani da damar k'arshe wajen bincikensa, tunda yabi dukkanin sauran bai samu wani bakin zareba.
To amma kuma wannan ai ba tarbiyyar Malam bahaushe baceba, daga baya kuma idan komai yafitofa? wane kallo kuma za'a masa?, shinma zata iya fahimtarsa kuwa? dan irin wannan abun yakan farune a labaran films ko Novels, to amma wannan ce damarsa ta k'arshe ai kawai, dolene ya jefi tsuntsu biyu da dutsi d'aya kenan?.............鉁嶐煆?
Tirk'ashi, Nikam dai nakasa fahimtar wannan cirkud'ad'd'en tunanin na Galadima鈽?, fan's koku kun fahimta Ku fassara mana馃?.
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu馃槶馃憦馃徎_*
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎1鈨?4鈨?
.......An kai ruwa rana kafin asamu na farfad'o, ina farfad'owa kuma sukamin allurar barci domin nasamu Hutu.
Sai a lokacin hankalin iyayena yad'an kwanta.
Baba k'arami da yagama birkicewa akan shifa bazai yardaba, saiya maka iyayen Haidar a kotu. wannan wane irin tozarcine haka? sunzo sun kar6i kayansu, anbasu batareda anduba wulak'ancin dasukayiba, shine kuma dan rashin mutunci shi Haidar d'in zai jamusu 'yarsu ta salwanta, to shifa bazai aminceba.
Hak'uri Dady da Abbanmu suketa bashi suna tausarsa akan yayi hak'uri, su d'auki hakan matsayin k'addara kawai, indai mijine ALLAH zai bani wani ai. k'ilama shid'in ba alkairi baneba agareni dama.
Innarmu dai tun tana kukan zuci harya fara fitowa fili, mama Rabi'a nata tausarta.
'Yan gidanmu babu Wanda ya biyomu sai maman fauziyya, har innaro k'in zuwa tayi.
Ban farfad'oba sai gabanin magriba, lokacin su Abba na shirin tafiya masallaci, na bud'e idona ahankali, da innarmu na fara tozali, sai mama Rabi'a da maman Fauziyya a gefenta, Munubiya na gefen gadon danake kwance rik'e da hannuna ta kifa kanta ajikina alamar barci ya saceta ahaka.
Nan komai yashiga dawomin sabo a zuciya, fashewa nai da kuka mai tsuma rai, cikin dasashiyar murya nace 鈥渟hikenan innarmu, shima na rasashi, Haidar yatafi, yakuma ce har abada bazai ta6a dawowa gareniba, mi muka musu suka za6i mana wannan sharrin dabazai ta6a barin rayuwarmu ba? yarigada yazame mana tabo a tarihinmu, ya ALLAH ka gaggauta saka mana akan duk mai hannu akan buga jaridarnan, wlhy Haidar ban aikataba, sharri sukaimin, dan ALLAH karka barni, ina sonka wlhy, sosai nake sonka, dan ALLAH mama Rabi'a kuce masa sharrine, ban aikataba, Munubiya dan ALLAH karkubar haidar yatafi, ina sonsa wlhy.......鈥?.
Kuka Munubiya takeyi sosai, dan tunda na fara magana ta farka, dama barcin nata bawani nisa yayiba. Innarmu kam tashi tayi tafita tana share hawaye, maman Fauziyya na rik'e dani tana lallashi. Mama Rabi'a ma kuka takeyi saboda ganin 'Yar uwarta Na kuka.
A haka su Abba suka shigo suka samemu inata wannan sambatu, da rok'on akiramin Haidar, dan wani masifar sonsa nakeji a lokacin, fiyema da son Dana masa muna tare.
Duk saida nabama su Abba tausayi, Dady ya zauna akujera tareda rik'e hannuna.
鈥淢unaya ya isa haka kinji, kiyi hak'uri, ki yarda da k'addara, dama can ALLAH ya rubuta shid'in ba mijinki baneba, insha ALLAHU mijinki nanan zuwa soon. Ubangiji nason bayinsa masu hak'uri, wata rana komai zai zama labari tamkar ba'ayiba kinji鈥?.
Ahankali na fara sassauta kukan danakeyi, ina sauraren lallashin Dady, sai ajiyar zuciya danakanyi lokaci-lokaci.
Bayan doctor yazo ya dubani yace abani abinci nasha magani, sunaso nakuma samun isashen barci danna samu na kuma hutawa. Saboda jinina yahau gaskiya.
Hankalin su baba k'arami yakuma tashi, ace 'Yar k'aramar yarinya dani amma da hawan jini, (ALLAH yay gaggawar sakamin akan duk mai hannu akan wannan tushen matsalar).
Da k'yar aka samu nasha shayi, nasha magani barci yakuma kwasheni.
Sai kusan 10pm su Abba suka tafi gida, akabar Mama Rabi'a da Munubiya zasu kwana dani.
***掳鈥⑩€⒙?***掳鈥⑩€⑩€⒙?***掳鈥⑩€⒙?***
Yana shirin fita asibitin sai ga Momma tadawo gida, tun yana sakkowa daga benen ya hangota zaune afalo itada jakadiya, da alama magana sukeyi.
Takun takalmansa da k'amshin turarensa yasasu juyowa suka kalleshi gaba d'aya, ya k'araso cikin falon cikeda takunsa na asalin jinin sarauta cikakke. Kujerar gefen Momma ya zauna yana fad'in 鈥淢omma yaushe kika shigone?鈥?.
Idonta akan d'an nata tana nazartar yanayinsa tace, 鈥渂an dad'e da shigowa ba, nama zata barci kakeyi ai? danJakadiya tacemin tuni kana gida鈥?.
Guntun tsaki yayi yana lumshe ido, tare da kuma jingina kansa jikin kujerar, ahaka yace, 鈥渨lhy kuwa Momma, nad'an tsaya wani aikine aciki鈥?.
Idanu ta tsira masa domin hango damuwa k'arara a fuskarsa. 鈥淢uh'd mike faruwane? mike damunka?鈥?.
Idanunsa da har yanzu suke da sauran ja ya bud'e, yasaki murmushin gefen baki, 鈥渂abu komai Momma, mikika ganine?鈥?.
鈥渂akaso dai nasani kawai Muh'd鈥?.
Yad'an narke face alamar shagwa6a, 鈥減lease Momma ki yarda dani mana鈥?.
Girgiza kai kawai tayi tana murmushi, 鈥渢o na yarda dakai. yanzu sai ina?鈥?.
鈥渄ama zanje hospital ne, dan inaga zanje Goa gobe idan ALLAH ya kaimu, maybe kuma na kwanama鈥?.
鈥渙k. ALLAH ya kaimu to, dama muna magane da jakadiya akan akawo wasu sabbin bayin, kaga aikin yanama su Samha yawa a gidannan Muh'd, gakuma makaranta, idan suka fita kaima ka fita sai gidan yay shiru, gashi mukuma muna Asibiti鈥?.
6ata fuska yayi yana gyara zamansa, 鈥淎mma kuma Momma bakwa tunanin a kuma samun matsalar datafi ta baya? kiduba kiga dad'ewar da mukayi da wad'ancan, amma hakan bai hanasu munafuntar muba鈥?.
鈥淗umm Muh'd kenan, wancan karonma bawai dabararmu bace ta tsaremu, muyi hak'uri akawo koda guda 20ne, maza 10 mata 10鈥?.
鈥渒ai Momma, amma har 20 ma?, ina laifin 5 kawai, idan sukayi yawa gidanan hayaniya zaiyi yawane鈥?.
鈥渨ane irin 5 kuma Muh'd?, yanzu badan laluraba data kawomu nan ta ajiyeba konan da can ka isa matsawa batareda bayi ko dogaraiba, sha'anin gidan sarauta sai hak'uri, wlhy tunda aka kwashe bayinan gidan saiyayi wani iri, tamkar bana masu sarauta ba, yanzu haka kullum k'orafin Mimi kenan adawo da bayin gidanan鈥?.
鈥渕omma kenan saboda Aunty Mimi za'a maidosu?鈥?.
鈥渒usan haka to, saboda ita saboda buk'atunmu muma ko鈥?.
鈥渟hikenan, sai a dawo damasu min hidima idan naje ko?鈥?.
鈥渁'a baza'ayi hakaba, idan an kwasosu kaikuma idan kaje kuma fa? wad'ancan munriga da mun yardaba da amarsu, idan mun maidosu nan kafin mu samu masu amanarsu zamusha wahala,, amma idan nan aka kawo mana wasun zamu saka ido sosai akan su yanzu ai?鈥?.
Kai kawai ya gyad'a mata batare da yace uffanba. saikuma zuwa can yace 鈥渋naga nima next week zanje Nigeria 鈥?.
鈥淣igeria kuma Muh'd? mizakayi?鈥?.
鈥渕urmushin gefen baki yayi yana kallonta, kwantar da hankalinki Momma, 3days kawai zanyi na dawo, wani d'an aikine zai kaini, ko masarauta bazasu San najeba ma Dan ba a can zan saukaba鈥?.
鈥淎mma Muh'd baka kudin abinda zaije ya dawo? kuma kana ganin zaka iya Shiga Nigeria kafito batareda kowa yasani a masarautarku ba?鈥?.
鈥渒imin addu'a Momma, insha ALLAHU lafiya lau d'anki zanje ya dawo kinji, kuma zanyi taka tsantsan d'in yanda bazasu San najeba insha ALLAHU鈥?.
Murmushi Momma tayi, tace 鈥渢o shikenan, ALLAH yabada nasara akan abinda za'aje, yakuma tsare mana kai. amma nikam Muh'd yamagar yarinyar nan da aka muku 6atancinnan tare?鈥?.
鈥渂an saniba Momma, dan ni ba saninta nayiba fa鈥?.
鈥渁mma dai gaskiya ba a k'yautaba, yarinyarnan dukda anazargin da had'in kanta yakamata anemi iyayenta ai, amma ba ayi burus da lamarinta ba, kuma wannan aikin Kaine yakamata kayishi tunkan kabaro k'asar alokacin鈥?.
鈥淣ima nayi tunanin hakan daga baya Momma, amma wlhy a time d'in hankalinane yatashi sosai, sai dai karki damu, a wannan karon zansa amin bincike akanta鈥?.
鈥渉akan yafi kam gaskiya, bara na kimtsa saimu wuce k'ila kafin mu tafi su Sauban sun dawo. antafi d'akko Khaleel kuwa?鈥?.
鈥渁i da sauran time Momma, kuma nifa yanzu nace aringa kawoshi a school bos, dan kinga mu ba kullum Muke gidaba, ga khumar har yanzu bai dawoba, inaga jikin mahaifiyar tasa yayi tsanani shima鈥?.
鈥渒ama tunamin wlhy Muh'd, yakamata koda kaida Sauban ne kuje Ku dubata, wannan shine adalci da zakama Wanda yake k'ark'ashinka idan wani Abu yasamu rayuwarsa鈥?.
鈥淗akane wlhy Momma, zamuje insha ALLAH, miye ma sunan k'auyen nasune?鈥?.
鈥渘ikam nad'an manta, amma bari zan tanbayi jakadiya kota rik'e鈥?.
鈥渙k tom shikenan鈥?.
Tunda Momma ta shige saiya maida Kansa ya kwantar jikin kujerar, yacigaba da tunaninsa datum d'azun yake cin zuciyarsa da ruhinsa. baya buk'atar shawara da kowa akan wannan maganar gsky. to amma koya fad'ama Harun?. kai a'a, inma fad'arne Muftahu yakamata ya sani, tunda shine ya d'ora akan aikin, kuma shi kad'ai yasan komai akan yaran, to amma ba komai ne Na sirrinsa Muftahu ya saniba ai. (zuciyarsa tace, to ai wannan baikai girman sauran sirrikanka ba, kuma abune daza'ayi Na k'ank'anin lokaci yawuce, tunda ka yanke shekara d'aya ne ko biyu), iska ya furzo daga bakinsa yad'an dafe kansa dayakejin yana Neman fara masa ciwo.....
鈽呪槄鈽呪槄鈽?
Washe gari natashi da d'an sauk'i, sai dai har yanzu hawayen sun kasa barin fuskata nida 'yar uwata Munubiya. mama rabi'a ce keta lallashinmu da mana nasiha, ahaka su Ayusher sukazo kawo mana break fast itada Feena, ya Marwan ya kawosu.
Daga gidanmu kam ko ruwan zafi babu Wanda yakawo har kusan 10, sai kuma ga Fauziyya itada Jameela k'anwarta, sukace inji mamansu, tace ayi hak'uri Mubarak ne shima babu lafiya.
Mukace mun gode ya jikin Mubarak d'in?.
Fauziyya tace, 鈥渄a sauk'i, tare suke da maman tasu, sunacan zasuga likita鈥?.
Anan su Fauziyya suka zauna ana hira dayake weekend ne babu school, kusan hirar duk akan abinda haidar yayine shida iyayensa, dagani har munubiya bamu saka musu baki, ni hirarma k'onamin zuciya takeyi.
Yaa marwan dake zaune a gefe yanata latsa waya tamkar baya jinmu yamik'e, kallon Munubiya yayi yace 鈥渮o mana鈥?.
Saida yafita sannan ta mik'e tabi bayansa, su Ayusher suka sanya dariya suna fad'in soyayya ruwan Zuma.
Nidai bance komaiba, saibin 'Yar uwata da kallon tausayin zama da wannan mai shegen miskilancin nayi. zama da irinsu yaa marwan sai mai hak'uri wlhy.
A ranar da daddare aka sallameni muka koma gida, sai dai 'yan gidanmu maman Fauziyya ce kawai tazo, amma ko innaro batazoba. sai bayan an sallamemu su Dady sukaji babu Wanda tazo dubani. kuma Maman fauziyya Ce kawai me kai mana abinci, dukda ba ranar aikinta bane haka take dafa mana su fauziyya sukai.
Aiko ranar sunga tsantsar bala'i, dan su Abba birkice musu sukayi suduka ukun, har Dady da ake gani mai hak'uri. ita kanta innaro saida tasha jinin jikinta ga 'ya'yan nata.
Nacigaba da samun kulawa wajen innarmu da 'Yar uwata Munubiya, duk hanyar dazasubi Dan samamin farin ciki ita sukebi, burinsu kawai suga Na manta komai, hakama iyayena maza, sai yazama kowa tausayina yakeyi acikinsu, yayunmu mazama babu laifi, suna nunamin kulawa dai-dai gwargwado.
Ahaka nafara rage wasu damuwoyin.
Satina d'aya kenan da dawowa daga asibiti, duk na k'ara ramewa Na fige, hakama Munubiya, saika d'auka tare muka kwanta ciwon.
Ahaka muka tak'ark'ara muka koma makaranta, ayanzu kam maganar gsky bana fahimtar karatu, saboda damuwace tsatstsage da zuciyata, nasanma nida aure kuma har abada, kowa yafito haka za'a sokeshi ya janye, ita dai 'Yar uwata Munubiya ALLAH ya taimaketa na gidane yace yana sonta, itama nasan da yanzu an soki lamarin, musamman daba banbancemu jama'a sukeyiba. Nagodema ALLAH da abinnan bai shafi rayuwar Munubiya taba sarkin hak'uri, tabbas danafi haka shiga tashin hankali, bansan yanda zan musalta muku k'aunar danakema 'Yar uwataba, ina sonta fiyeda zaton mai tunani, wlhy zan iya fansar da raina awajen kare nata, kamar yanda nasan itama zata iya yin hakan agareni.
Yau ta kasance juma'a, dagani har Munubiya bamuje makarantaba, saboda tatashi da ciwonkai, tun muna primary idan d'aya bai da lafiya d'ayan bazaije school ba, komin zare idon ko dukanmu da za'ai kuwa, wannan abinne yazame mana jiki har girmanmu gashinan.
Bayan nagama gyaran 6angarenmu innarmu tace Na shirya naje nakaima wata k'awarta sak'o.
Badan nasoba Na kar6i sak'onnan natafi, saboda banajin dad'in tafiya nikad'ai arayuwata, tunda nataso nayi wayo ko ina zamuje sai nida Munubiya ne, mawuyacine kiga d'ayanmu tafita batare da d'ayaba.
Tafiya nake tamkar zan fasa kuka, gani nake kowa nikad'ai yake kallo, sanye nake da jallabiya bak'a datasha adon honey color d'in duwatsu, Na nad'a Veil ruwan zuma shima, haka ma takalmana masu d'an tudu ruwan Zuma, sai lady's bag d'ina, ahankali nake tafiyar cikeda takuruwa, ahaka nazo bakin titi domin samin abin hawa.
Banfi tsayuwar 15minutes ba saiga taxi, ganin babu kowa a taxi d'ina kamar karna shiga, amma sainayi addu'a kawai nashiga, gudun karnazo nayi sakin Na hannu kamun na guje.
Munyi nisa da tafiya naga mai taxi d'inan yak'i d'aukar kowa, gashi anata tsaidashi, kumani bance masa drop na d'aukaba gaba d'aya.
Cikin dakiyar zuciya nace 鈥渂awan ALLAH miyasa bazaka tsaya ka d'auki mutaneba? bayan kuma gashinan anata tsaidaka鈥?.
Ta madubi ya kalleni yana murmushi, sorry hajiya, kekad'ai aka bani izinin d'auka ai鈥?.
Da mamaki nace 鈥渒amar ya?鈥?.
Dariya yad'anyi sannan yace 鈥渒arki damu da wannan, ina muka dosa yanzun dai?鈥?.
Yawu mai kauri na had'iye da k'yar sannan na fad'a masa inda zamuje.
Har k'ofar gidan ya ajiyeni, nabashi kud'i kuma yak'i kar6a, haryaja motar yabar wajen ina binsa da kallon mamaki, na sauke ajiyar zuciya nidai ina hamdala ga ALLAH dayasa na sauka lafiya.
A fili nace 鈥渒'ilama aljanine鈥?. saikuma nace 鈥渨ayyo ALLAH ya tsareni da hawa motar aljanu鈥?.
Da wannan tunanin nashiga gidan, tun a soro nake kwad'a sallama.
Daga ciki najiyo ana amsamin, tace shigo mana baiwar ALLAH.
Shiga nayi inda ake amsamin sallamar, dattijuwar macece da zasuyi sa'anni da innarmu, ba yaune karon farko dana fara zuwa gidanba, tun muna k'anana muke zuwa yawon da innarmu ko idan munzo suna ko biki, (inna lami k'awar innarmu ce, a anguwarmu take, tun zuwansu innarmu gidansu innaro suka k'ulla k'awance da inna lami d'iyar makwaftan su innaro. harkuma yanzu akwai zuminci mai k'arfi a tsakaninsu).
鈥渁'a a'a lalale marhabin da d'iyata, Munubiya ce ko munaya?鈥?.
Fuskata d'auke da murmuahi nace 鈥渋nna munaya ce, munu.... tana gida bata jin dad'i鈥?.
鈥淎yya ALLAH ya sauwak'a yabata lafiya, ya Ai'shar dasu Aryaan?鈥?.
鈥渓afiya lau take, tacema na gaisheku. ga wannan tace na kawo miki鈥?.
鈥渢o madallah, ina amsawa. ngd sosai kuwa鈥?.
Murmushi nayi kawai bance komaiba, sai zuwa can nace 鈥淎meera batanan? naji gidan shiru鈥?.
鈥渨lhy Ameera tafita d'azunnan gidan Mariya, amma nasan duk inda take tana hanyar gida yanzu鈥?.
鈥淎LLAH sarki, to a gaida min ita idan tadawo ni bara na tafi鈥?.
鈥渉aba dai Munaya, daga zuwa kice zaki tafi?, Dan ALLAH ki zauna yanzu zakiga Ameeran tadawo aii. bara kiga nasa miki ko kallone kisamu abokin hira鈥?.
Badan nasoba na zauna har ameera ta dawo, sosai tayi murna da ganina, dayake munsan juna, school d'aya mukayi a secondary, kuma ajinmu d'aya, nan muka zauna mukasha hirarmu, har ta soya mana wainar fulawa mukaci muka k'oshi abinmu.
Ban bar gidanba sai bayan an sakko masallaci, har titi ta rakoni, da k'yar muka samu taxi kasancewar anguwar tasu tad'an shiga lungu abin hawan yana wahala.
Saida muka hau titi na fad'ama driver inda zamuje.
'Yar dariya yayi yana fad'in 鈥渁ina sani hajiya鈥?.
Cikin fad'uwar gaba nad'ago na kalleshi, Dan naji kamar muryar driver n d'azun, ido na zazzaro waje da dafe k'irji dan ganin shine kuwa.
Na ware baki zan maka ihu ya jehomin farin Handkerchief a fuska. luuuu nayi da baya na kwanta a kujerar, tun ina ganinsa dishi-dishi har na daina gaba d'aya................鉁嶐煆?
Tofa jama'a ana wata ga wata wanene yasa a kwamushe Munaya馃檰馃徎馃槶?.
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu馃憦馃徎馃槶_*
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎1鈨?5鈨?
.......Tunda yafara tafiya bai tsaya ko inaba sai a wata sabuwar anguwa, shiru anguwar take babu yawan hayaniya, dan gidajenma tsilli-tsilli suke tamkar rugar Fulani, wani gida dakecan nesa da sauran gidajen yanufa, gidane babba mai k'aton bak'in gate, yay horn sau biyu akazo aka bud'e masa. a babbar harabar gidan yay parking, yana cikin motar bai fitoba har kusan 10 minutes bayan yagama waya yace ya iso.
Idanu na zaro waje saboda ganin Muftahu yafito daga wata k'ofa yanufo motar, gaba d'aya mamaki yahanani kwakwkwaran motsi harya k'araso.
Mai taxi yafito ya risina ya gaidashi, sannan yace nagama aikina Oga.
Murmushi Muftahu yayi, sannan ya lek'a Munaya dake barci kashir6an ta glass, janye kansa yayi sannan ya zaro wayarsa daga aljihu yay kiran wani.
鈥淯mh yalla6ai akwai 'Yar matsala fa, dan barci takeyi sosai, kona d'akkota鈥?.
Da sauri yace 鈥淣o ina zuwa, amma wannan driver dayay aikin yabar wajen, dan bana buk'atar ya ganni鈥?.
Murmuahi Muftahu yayi, tare da fad'in 鈥渁ngama ranka ya dad'e鈥?.
Muftahu ya sallami drivern daya kawo Munaya, yace zai kirashi ya maidata zuwa anjima, yaje yabar motar anan.
鈥渂abu damuwa Oga, saina jika鈥?.
Bayan tafiyar driver Galadima yafito, dama duk yana kallon abinda ke faruwa ta window.
Taku yake cikin tsantsar nuna jinin mulki dake yawo ajikinsa, ga wata izza ta zamowarsa cikakken namiji mai isashshiyar lafiya. fusakarnan babu walwala kamar kullum, ahaka ya k'araso wajen motar, Muftahu ya bud'e masa murfin inda Munaya ke kwance tana kwasar barcinta.
Kallonta yayi na tsayin mintuna uku, sannan ya janye idonsa ya rankwafo da kansa cikin motar, saida yad'an cije lips d'insa sannan yasaka hannayensa biyu ya tallafota ahankali ya fito da ita, tamkar 'Yar baby haka ya d'akkota acikin hannayensa, sai wani kuma d'aure fuska yakeyi yana kauda kai, kaikace anmasa dolene ya d'auketa.
Hannu Muftahu yasaka yatoshe bakinsa saboda dariyar dake Neman kwace masa.
Wai yau Galadima gudane d'auke da mace a hannu, mutumin da ko kallon mata bai cika yiba, inkaga yana walwala ko dariya wa mace to Momma ce ko aunty Mimi.
Jakarta ya d'auka shima yabi bayansa.
Ya iske harya shinfid'eta a doguwar kujerar dake falon, yana gyara hannun rigarsa daya nannad'e yana jan k'aramin tsaki, ganin Muftahu na murmushi saiya kuma had'e fuska, Muftahu ya ajiye bag d'in yana had'iye dariyar da k'yar saboda gudun yin laifi.
Hannu yamik'ama Muftahu.
Muftahu yabashi handkerchief d'in daya zaro a aljihu, rankwafowa yayi kanta ya d'ora Handkerchief d'in bisa hancinta, tsayin minti 2 ya janye.
Tari tafarayi, saikuma ta fara k'ok'arin bud'e idanunta tana lumshewa, Muftahu ya mik'o masa gorar ruwa mai d'an sanyi.
Cikin hannunsa ya tsiyaya kad'an ya shafa mata a fuska, ahankali ta fara bud'e idanun ta, shikuma yaja da baya yakoma ya zauna bisa kujerar mai zaman mutum d'aya.
d'ora k'afa yayi d'aya kan d'aya ya jingina kansa jikin kujerar ya lumshe idanu, saika rantse idonsa arufe suke, amma ya zubasune akan Munaya dake ta mutsu-mutsun tashi zaune.
Da k'yar ta iya tashi ta samu ta jingina da kujerar tana k'arema falon kallo, yayinda hawaye ke zirara a kumatunta.
Ruwa Muftahu ya mik'a mata, babu musu ta kar6a dan wata kishirwa takeji, tunda tafara shan ruwan bata ajiyeba saida ta shanye tas, nan wata zufa tafara karyo mata kuma.
Mik'ewa Muftahu yayi yak'ara gudun AC n.
Ahankali zufar tafara tsanewa, saikuma tad'anji k'arfin jikinta, Muryarta na rawa alamun kuka tace, 鈥淧lease Ku suwaye? miyasa kuka kawoni nan? dan ALLAH kuyi hak'uri karku cutar dani, karku lalatamin rayuwa dan girman ALLAH, Ku tausayama mahaifiyata, damuwar damuke ciki kad'ai ta ishemu, wlhy daku keta mutuncina gwamma Ku kasheni yafimin sauk'i鈥?.
Daga Muftahu har uban gayyar kallonta kawai sukeyi, ita ko kad'anma bata gane Galadima ba, saboda yayi sama da fuskarsa.
Muftahu ne yace 鈥渒i kwantar da hankalinki, kuma ba abinda yasa muka d'akkokiba kenan鈥?.
鈥渢o miyasa kuka d'akkoni? bawan ALLAH, mina muku?鈥?.
Muftahu ya juya ya kalli Galadima, amma saiyaga ko motsawa baiyiba, bashima da niyyar tanka musu.
Itama Munaya saita maida kallon nata ga Galadima, a kuma lokacinne yad'ago kansa zai gyara zama.
Wata razananniyar k'ara Munaya tasaki saboda tsorata, da Sauri Galadima ya toshe kunnensa, shima tsawar ya Daka mata wadda tasakata nutsuwar dole.
鈥渒!!! Dalla karki ciremana dodon kunni!!!!鈥?.
Dole Munaya tayi shiru jikinta na 6ari da k'yarma.
Yaja wani wawan tsaki, tare da janye hannayensa daga kunnensa yana harara Munaya. 鈥渒 wace irin shashashace ne?鈥?.
Sukda halin da take ciki saida ta watsa masa harara, amma bata iya cewa komaiba.
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya FASA, komi yatuna oho.
Komawa yayi inda yataso ya zauna, ya maida k'afafunsa yay crossing d'insu.
Shi dai Muftahu yana kallonsu yakasa cewa komai, bakajin motsin komai saina shashshekar kukan Munaya Dana k'arar AC.
Cikin kuka tace 鈥渕inamaka kasa aka kawoni nanan? ko sokake kakuma jamin wani sabon 6atancin bayan Wanda yafaru abaya? wane Abu na tare maka waishin aduniyarnan dan ALLAH bawan ALLAH?鈥?. takuma rushewa da kuka mai tsuma rai.
Bakinsa ya ta6e a zuciyarsa yake fad'in daganin yarinyarnan akwai tsiwa dai, saikuma uban tsoro kamar farar kura. banza yamata, azahiri idonsa a lumshe suke, amma kuma abad'ini yana kallon Munaya ne, kukanta Neman saka masa ciwon kai yakeyi, dan haka yay maganar cikeda izza da mulki.
鈥渒inutsu muyi abinda ya kawomu, inba hakaba zaki kwana anan gidan ne鈥?.
Da Sauri Munaya ta share hawayenta, 鈥渋ndai kukane na daina wlhy, kayi hak'uri ka sanarmin, dan ALLAH ka maidani gida kafin hankalin innarmu ya tashi鈥?. tak'are maganar da share hawaye.
Dariya taso bashi amma saiya gimtse, saikace ba itace tagama tsiwa ba yanzun.
Muftahu dai kasa hak'uri yayi saida yad'an dara, Galadima ya balla masa harara, hakanne yasashi yin shiru ya had'iye dariyar.
鈥渒in shirya tafiya kenan?鈥?. 鈥榞aladima yafad'a tamkar an masa dole sai yayi maganar鈥?.
Munaya tace, 鈥渨lhy na shirya ranka ya dad'e鈥?.
Yace 鈥済ood girl鈥? yana ta6e baki.
鈥渒i fad'amin waye yasaki aikin nan?鈥?.
Cikeda rashin fahimta Munaya tace, 鈥渨ane aikin?鈥?.
Shiru Galadima yayi bai tanka ba, sai Muftahu ne yaymata bayani dalla-dalla akan abinda yafaru a plaza kwanakin baya鈥?.
Cikeda k'unar zuciya Munaya tace 鈥渘i babu Wanda yasakani, saima tozarci da hakan ya jawo mana muda mahaifiyarmu, bansan komaiba, amma tunda al amarinan yafaru muka kuma tsintar kanmu a k'unci, kullum da irin abin kuka dazamu gani agidanmu, yanzu haka akan waccan abin maganar aurena sau biyu tana lalacewa, yanzu haka satina guda kenan da baro asibiti saboda tashin hankalin dana shiga a dalilin fasa aurena da cin zarafi dana fuskanta daga Wanda yafasa aurena nawa, wlhy Ku yarda dani bansan komaiba鈥?.
Muftahu ya juya yana kallon Galadima da idonsa ke a rufe, amma yana sauraren Munayar.
Kusan mintuna 3 sannan ya bud'e idonsa, akan Munaya ya zubasu, bazata iya jurar kallon kwayar idonsa ba dan haka tayi azamar janye nata, shima janye nasa yayi ya gyara zamansa. 鈥渒ince babu hannunki? amma miya kaiki plaza a wannan time d'in daya kamata duk yarinyar kwarai tana gidansu?鈥?.
鈥淢una bikine, bayan munkai amare mun dawo sai fu'aad yamatsa akan saimun shiga, ba dan nasoba nayarda, kuma bani kad'ai baceba, harda 'yan uwana su uku鈥?.
鈥渨aye shi Fu'aad d'in?鈥?.
鈥淪aurayinane, awajen bikin muka had'u dashi鈥?.
da sauri Galadima yace 鈥渕iye kamaninsa? kuma ya kukayi dashi bayan abin ya faru?鈥?.
A nutse Munaya tabasu labarin komai, sannan ta zano musu kamannin Fu'aad dalla-dalla, danma bawani kallon tsaf tamasa ba a cikin kwana biyun.
Muftahu yace 鈥渒ozamu iya samun Horton shi Fu'aad d'in?鈥?.
鈥渂anida hotonsa, dan bai yarda munyi ko photo d'aya ba awajen bikin, amma zamu iya samu a video d'in da akayi maybe awajen dinner? 鈥?.
鈥済aladima yace 鈥渁 ina zamu CD d'in yanzu?鈥?.
鈥済askiya wannan shine mai wahala, dan bansan taka maimai cikin angunan waye yasaka ayiba鈥?.
Galadima ya cije lips d'insa da k'arfi, sai kace zai hudasune.
Kusan mintuna 3 kowa baice komaiba, sai can munaya tace 鈥渒unji na fad'a muku gaskiya, Ku maidani kafin afara nemana鈥?.
鈥渮amu maidaki bisa sharad'i guda d'aya鈥?. 鈥榗ewar Muftahu 鈥?.
鈥渨ane sharad'ine?鈥?. 鈥楳unaya ta tambaya鈥?.
鈥淪harad'in shine zakuyi auren 1year keda Galadima鈥?.
Cikin zaro idanu waje munaya tace 鈥渒amar ya? ban fahim cekaba fa?鈥?.
鈥渋na nufin Auren yarjejeniya zakuyi na shekara 1 ko 2, ta wannan hanyarne kawai zamu iya kamo bakin zaren, sannan kekuma zaki sama ma iyayenki kwanciyar hankali, nanda kafin adadin da aka d'ibama auren yacika kinga komai ya wuce, saiya sakeki kiyi idda ki sami Wanda kikeso sannan kuje gida a d'aura miki aure dashi, Galadima ma zai iya sawa har auren a d'aura muku, daga baya sai kuje ya warwarema iyayenki komai, yakika gani?鈥?.
鈥渢abd'i, wannan wace irin maganace saikace labarin Novels ko films? to tayayama za'ayi hakan yafaru? bayan nama sanarma iyayena banida wata alak'a dashi鈥?.
Murmuahi Muftahu yayi, yace 鈥渄an wannan duk mai sauk'ine, kedai amincewarki kawai muke nema鈥?.
鈥渁mma dai kun maidani wawuya wlhy, to ban aminceba, gara na dawwama banyi aureba ai鈥?.
Baki Muftahu ya bud'e zai k'ara magana Galadima ya d'aga masa hannu alamar yayi shiru ya barta.
鈥渒inga tashi kije kawai, amma wannan maganar tazama iyamu ukunnan, idan najita awani waje saina zubar miki da hanjin ciki waje, duk shawarar dakika Yanke da zuciyarki zaki iya nemanmu daga nan zuwa kwana biyu kawai鈥?.
Da sauri Munaya tazaro idanu waje tana kallon Galadima.
Harara ya zuba mata yace 鈥渒arki cinyeni鈥?.
Baki ta zun6ura gaba tana k'unk'uni, bayajin mitake fad'a, sai motsin la66anta kawai yake gani.
Sai da aka rufemin iso sannan aka baro gidan dani, bankuma kwanceba saida motar ta tsaya, Wanda yake tare dani yacire k'yallen sannan yace na fita.
Ko kallonsa banyiba saboda tsoro nafice amotar da sassarfa.
Gudu-gudu sauri-sauri na Isa gidanmu, mutane sai kallona sukeyi, ALLAH ma yasoni babu kowa a tsakar gida, inaga matan gidan duk sun shige sallar magriba yaran kuma basu dawo daga islamiyya ba.
A 6angarenmu ma innarmu na d'akinta, hakanne yabani damar shigewa d'akinmu wuff, na iske Munubiya na barci itama, na sauke ajiyar zuciya mai k'arfi ganin ALLAH ya tsareni babu Wanda ya ganni, kayana nacire daketa kamshin turaren Galadima, bayi nashige nida kayan, nayi wanka sannan suma na wankesu na shanya a bathroom d'in.
Harna fito Munubiya bata tashiba, nayi sallar magriba sannan nafito wajen innarmu.
Da mamaki take kallona, 鈥測oni har ina shirin kiranki naji lfy baki dawoba had dare yarufa?鈥?.
Zama nayi ina murmushin yak'e, dan abinda yafaru tsakanina dasu Galadima d'anzu ya min kane-kane a zuciya. ganin abin nakeyi kamar a mafarki. 鈥渁yya innarmu ai tun d'azun nashigo, lokacin kina salla, harfa nayi wanka ma nad'an huta. tace tana gidaki, yaya jikin Munubiya?鈥?.
Jikinta Alhmdllh, tad'an watsa ruwa takoma ta kwanta bayan taci d'an abinci鈥?.
To Almdllh, ALLAH yak'ara afuwa.
Amin innarmu ta amsamin, daganan muka koma hirar gidan Inna lami.
Munkai tsawon lokaci afalon muna hira da innarmu, sai dai nifa bama fahimtar hirar nakeba, dan fili kawai nakeson samu nayin tunanin maganar su galadima.
鈽呪槄鈽呪槄
Tun bayan tafiyar Munaya Galadima yakoma kan doguwar kujerar yay kwanciyarsa tamkar mai barci.
Muftahu dake kallonsa yace, 鈥淎mma miyasa kace ta tafi? batareda ta bamu gamsashshiyar amsa ba kuma?鈥?.
Shiru Galadima bai amsaba tsawon mintuna uku, sai zuwa can yabud'e idonsa yana kallon Muftahu, baki yad'an ta6e 鈥渒arka damu kanka, tama yarda, amsa ce kawai bata bamuba, itama kuma zata bayarne, tuni naga yardarta cikin kwayar idonta, akwai abinda take shakku akansa shiyyasa tak'i amsa mana鈥?.
Kai Muftahu ya jinjina kawai, yasan tunda Galadima yafad'i haka to hakanne kuwa, amma sai yace 鈥渢o amma bamu bata koda number ba, tayaya zata sanar damu amincewar tata kenan?鈥?.
Murmushi kawai Galadima yayi baice komaiba.
Hakanne ya tabbatarma Muftahu murmushin Galadima shine amsar tambayarsa. Daga nan bai sake cemasa komaiba shima.
Falon yay tsit.
鈽呪槄鈽呪槄
Gaba d'aya a kwanaki biyunan banida wani sukuni, tunanin maganar yak'i barin zuciyata, a kowacce dak'ik'a zuciyata tunzurani takeyi akan Na amince kawai, dan banida wata mafita sai wannan, ni kaina inason sanin Wanda ya aikata mana wannan abun, sannan bana fata sauran 'yan uwana suyi aure su barni a gidannan, hakan ba k'aramin tozarci zai zamarminba, ga Munubiya tadage akan innarmu ta sanarma Abba itama ad'aga bikinta har saina samu miji nima ahad'a ni da ita, na nuna mata 6acin raina akan maganar amma abanza, tanuna Sam ita tana a kan bakanta, nikuma harga ALLAH ba zanso hakan ta kasanceba.
Ita kanta innarmu nakula danne zuciyata kawai takeyi akan fasa aurena, amma tana cikin matsananciyar damuwa.
Yanzu yazanyi kenan? Na amince ko karna amince? gashi ya gargad'eni akan kadda Na nemi shawarar kowa, ni kaina nama kasa sanarma koda Munubiya, kuma kullum cikin tanbayata take mike damuna? duk da ita zatonta akan maganar Haidar ne har yanzu nake cikin damuwar.
Yau dai kwanaki biyu kenan da faruwar abin, har yanzu kuma nakasa tsayawa a matsaya d'aya.
Kusan tashin hantsi muna tsakar gida a baranda muduka 'yan matan gidan, kowa da hidimar dayakeyi, sai wasu daga cikin k'annenmu dake wasa agefenmu, iyayenmu kuma Na daga can k'arshen barandar suma kowa da hidimarta, innarmu ce kawai babu tana gidan mama Rabi'a taje duba feena da jikinta yad'an motsa.
Tsayuwar mota mukaji a k'ofar gida, yara suka tafi da gudu dansuga wanene? azatonsu cikin su Dady ne.
Mintuna baifi 10 ba saigasu suna shigowa da ledoji, saikuma ga Zarah tashigo cikin kwalliyar kece raini, tana taku d'ai-d'ai, daka ganta kaga mai yaron ciki, cikeda muran muka hau mata sannu dazuwa, itako saiwani ciccijewa take tana kuma Jan kai, ita adole matar manya.
Abin kallo bai k'areba saida mamansu yaa Hameed ta iso da d'an gudu ta rungume Zarah a jikinta, duk mukai galala muna kallon wannan sabon salo.
鈥渕asha ALLAHU Zarah sarkin haske, kinganki kuwa, da anganki anga matar manya yarinyata, kai ai aure Ni'ima ce babba, duk wacce ALLAH yabama 'yarta miji matan gidannan ta godema ALLAH, Dan wlhy yana sonta鈥?.
Caraf Momy Hadiza ta kar6e da fad'in 鈥渨lhy kuwa Yaya, ai babu babban bak'inciki irin kanada gandamemiyar budurwa a d'aki tayi kwantai takasa auruwa, aimu sai godiyar ubangiji wlhy, babu ta inda ni'ima bata saukar manaba, Zarah zoki zauna ki huta kinji 'yar albarka鈥?.
Maman safara'u da gwaggon haleema da maman su Fiddausi suka kwashe da dariya.
Kowa yasan damu ake wannan gugar zanar, amma sai mukayi murmushi kawai bamuce komaiba, maman fauziyya ma batace komaiba, nama godema ALLAH da innarmu bata nan balle ranta ya 6aci.
Tsam namik'e nabar wajen zuciyata Na suya, Na danne kukan dake shirin tahomin...
Maman Safara'u tace, 鈥渢o yanzu ke bazaki iya danne zuciyarki ba saikin nuna hasaadarki a filin ALLAH?, to Ashe ranar auren 'yan uwanki mutuwa kuwa zakiyi?, dan kina gani za'a d'auke kowacce abarki agidan.
Wani k'arfine yazomin a zuciyata, Na had'iye kukana, najuyo ina kallonta ido cikin ido, wani murmushin takaici nasaki, sannan nace 鈥渕aman Safara'u ke uwace agareni, sannan innarmu takoya mana tarbiyyar girmama kowacce mace agidannan, badan hakaba dana fad'a miki maganar dabazaki ta6a mantawaba, kuma ba hassadar tasani tashiba kamar yanda tunaninki yabaki, natashine Na d'aukama Zarah ruwansha, naga tashawo rana kuma babu Wanda yayi yink'urin bata鈥?.
Ina gama fad'ar haka nabar wajen. tsit banji kowa yasake maganar ba, bansan miyasa ba, maganar tawace tasakasu yin shiru kokuwa oho.
Ina shiga falonmu Na fashe da kuka, anzo ga6ar da kawai zan amince da buk'atar Galadima, insha ALLAHU aranar datake fad'ar za'a tafi abarni, aranar nima zanbar gidan, Na gwammace nayi auren shekara d'ayan nafito.
Tunanin tawace hanya zanbi Na fad'ar musu Na amince na farayi, dan basu bani number ko wata hanyaba dazan iya nemansu, gashi kuma bazan iya gane gidan dasuka kainiba.
Tunawa dawata farar takarda nayi, wadda nagani a bag d'in dana fita da ita a ranar, kuma nasan ni bani Na ajiyeba.
Da Sauri Na d'auki bag d'in na zazage, saiga takardar tafad'o, na d'auka na bud'e, Number wayace ajiki kawai.
Jikina har rawa takeyi na d'auki wayata na kwafe number, sai kuma nakasa kira, na fara zagaye d'akin.
Motsi naji kamar na tafiya, da Sauri na shige bathroom d'inmu dan nasan Munubiya ce.
fanfo na kunna yanda zata d'auka wanka nakeyi.
Sha warar tura massage kawai na yanke. dan haka na rubuta
*_鈥渘a amince inhar bazai zama ka wulak'anta rayuwa taba鈥?._*
Haka kawai natura masa na cire kayana nafara wankan gaskiya...........鉁嶐煆?
鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧time d'in wasa yafara.馃じ馃徎鈥嶁檧
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*馃憦馃徎馃槶
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎1鈨?6鈨?
.......Zaune yake cikin wata runfar bunu dake harabar gidan, dagashi sai wando 3quarter da t-shirt mara nauyi, k'afafunsa hard'e saman table dake tsakkiyar kujerarun, an yisane da ainahin siminti kamar kujerun, sai dai anmusu ado da katifa a sama wadda inma bakayi kallon tsaf ba zaka d'auka na katakone.
Laptop ce ajiye asaman cinyarsa, yayinda idanunsa ke sakeye cikin siririn farin medical glasses d'insa Wanda har kana iya hango fafaren k'wayoyin idonsa aciki.
Gaba d'ayan hankalinsa naga aikin dayakeyi a laptop d'in, lokaci-lokaci yakan d'auki fresh milk na hollandia dake a cikin kofin glass ya kur6a ya ajiye. d'an k'aran da wayarsa tayi yasashi waigowa ya kalli wayar, saikuma ya d'auke kansa ya maida ga system d'in. Saida yagama duk abinda yakeyi sannan ya ajiye laptop d'in bisa table ya sauke k'afarsa d'aya k'asa.
Ruwa ya d'auka yasha sosai sanann ya ajiye ya d'akko wayar da sak'o yashigo d'azun yana k'ok'arin dubawa. sabuwar number ce, dan haka yabud'e cike da mamakin waye?.
*_na amince inhar bazai zama zaka wulak'anta rayuwata ba._*
Shiru yayi yana nazarin massege d'in, dan yakasa fahimta India ya dosa, Yakuma maimaita karantawa har sau biyu, ana ukunne yarinyar shekaran jiya tafad'o masa arai.
Murmushin gefen baki yasaki, tareda d'age girarsa d'aya yana ta6e baki da fad'in 鈥渋yimm!. kingama Jan ajin kenan? Well dama nasan zaki amince ai鈥?.
Wayar ya ajiye gefen table d'in, yazame ya kwanta a kujerar idonsa na kallon rufin bunun, yanzu dai yarinya ta amince, amma tayaya zai tunkari ahalinsa kuma da wannan batun? Mai martaba mahaifin Momma ne matsalar farko, saikuma k'anin mahaifinsa Sarki, Momma bashida matsala da ita inhar papi ya amince, yad'an cije lips d'insa yana lumshe idanu, dole yay gaggawar nemo mafita, dan bak'aramin aiki baneba agabansa, musamman daya zam duniya tagama saninsa da yarinyar a yanayin da bai dace da d'iyan bahausheba musulmi.
Ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfi, kafin yaja kuma siririn tsaki.
Zumbur yamik'e saboda wani tunanin daya zo masa a zuciya. waya ya d'auka ya lalubo wata number da aka rubuta my second Momy. kusan mintuna biyu yana kallon number d'in batare da yayi dailing ba, saikuma ya danna cikeda jimami.
Ringing uku aka d'aga daga can.
bayan yayi sallama aka amsa daga can tace 鈥渁'a yarona dama kana k'asar?鈥?.
Murmushi yayi tamkar yana gabanta, yad'an zame ya kwanta jikin kujerar yana shafa kansa. 鈥淪orry my mom, wlhy 2days kawai da shigowata, kuma babu ma Wanda yasan nazo, wani d'an aikine ya kawoni鈥?.
Dariya tayi daga can, cikin tsokana tace 鈥測o dama ai kai kullum cikin aiki kake katafila鈥?.
鈥渙h my mom sunan dakika samin kenan? to nagode鈥?.
鈥渁i shine yadace dakai, yaka baromin 'Yar uwa da jikin yayana?鈥?.
鈥淓verything Alhmdllh mom. wlhy nakiraki muyi wata muhimmiyar maganane, ALLAH yasa ke kad'aice?鈥?.
鈥渘i kad'aice yarona, inama bedroom kwancene, miya faru?鈥?.
鈥渦hmmm mom inason nayi a...鈥? saikuma yay shiru yakasa k'arasawa.
鈥渋na jinka mana鈥?.
鈥渁i mom maganarce bansan yanda zaki fahimceta ba, amma zancene inason nayi auren 鈥?.
Zumbur tamik'e zaune, saboda jin maganar tayi tamkar daga sama, dan bata ta6a jin makamanciyar wannan maganar daga bakin Galadima Sameer d'in ba, hasalima bata ta6a jin ance yanada budurwa ba, kullum cikin yimasa maganar aure suke yana basarwa da cewa akwai sauran time, shiyyasa koda maganar jaridar nan tafito kai tsaye ta k'aryata zancen. 鈥測arona wasa ko gaske dan ALLAH?鈥?.
murmushi mai sauti ya saki tareda ajiyar zuciya, har yanzu hannunsa na yawo bisa Kansa yana shafawa 鈥渕om da gaske nakeyi, aiban ta6a kawo miki irin wannan maganar ba鈥?.
鈥渉akane, to 'Yar wace masarautace ka samo mana?鈥?.
Sai da yad'an ta6e bakisa sannan yace 鈥渘o mom, babu kowacce masarauta鈥?.
鈥渢ofa, d'iyar waye to?鈥?.
鈥渂a 'Yar kowa baceba mom, yarinyar Nance dai da aka mana 6atanci tare鈥?.
鈥淪ameer ban gane mikake nufiba? kana haukane? Koma kafara shaye-shaye bamu saniba?鈥?.
tashi yayi zaune sosai, ya d'auki ruwa yad'ansha, 鈥渂an fara shan komaiba mom, inason ki fahimceni da k'yau, dan kece ta farko Dana fara sanarma maganar, sannan kinsan Ku ukune kuka iya Sanin damuwata kai tsaye aduk duniyarnan. nasan zuciyarki zata kawo miki abubuwa dayawa akan maganarnan, to duk ba haka baneba...............鈥?.
Anutse ya zayyane mata tarihin su Munaya, har zuwa maganar aurenta data lalace, yad'ora da fad'in mom banason nazama silar tawatsewar rayuwar yarinyar da bata jiba bata ganiba, ki fahimta mana, inason na bibiyeta ta hanyar auren Nata kozan sami wasu evidence akan case d'inan鈥?.
Ajiyar zuciya mom ta sauke daga can, 鈥渢o na fahimceka, amma ni mikakeso nayi yanzun?鈥?.
鈥測auwa momyna, sonake kisamu inno da mai martaba da maganar, amma kinuna kamar kece kikayi tunanin su Sani na auri yarinyar鈥?.
鈥渋yim nagane, kenan dai yazamto kamar kaid'in bakasan komaiba?鈥?.
鈥測es my mom, kin fahimceni dai-dai鈥?.
Murmushi tayi, 鈥渙k babu damuwa, kamayi sa'a zanje gidan anjima dama na duba inno datayi mura鈥?.
鈥渨ayyo 'Yar tsohuwarnan, karfa ta wuce bataga 'ya'yanaba鈥?.
鈥渒'aniyarka Sameer, aiko zan fasa kenan鈥?.
鈥渘o please, sorry mom, nabari, ALLAH ya k'arama ginbiya inno lafiya鈥?.
鈥渮an kamakane fitsararre鈥?.
Dariya yayi yana kissing d'in wayar sannan ya yanke kiran Yana cigaba da murmushi, yasan inhar inno da papi suka amince komai yagama yuwuwa, dan ko masarautarsu dolene kowa ya amince.
鈽呪槄鈽呪槄
d'aure nafito da zani ina goge ruwan goshina, Munubiya data zubamin ido tace 鈥渒uka kikayi ko sweetheart? 鈥?.
鈥渓ah a'a wlhy, aini basukai namusu kuka ba wlhy Sweetheart, dan haka kima share batunsu. nifa kitsoma nakeson muje wlhy, kaina yagama yin datti har d'an tsami-tsami yakeyi鈥?.
鈥渒ice kawai kin zama k'azama baby?鈥?.
janbaki na d'auka na wurga mata, tai saurin cafewa tana dariya. nima dariyar nayi ina fad'in 鈥渒in tsira yanzu, amma next time bazan barkiba鈥?.
鈥渉hhh idan na zauna ko? kinga shirya kawai muje wajen aunty Salamah mu wanke kai, daga can saimu biya muga jikin feena ma ko?鈥?.
鈥渙k, hakan yayi鈥?.
Shirina nayi cikin zani da Riga na wata oxblood d'in atanfa da ratsin milk, nakawo milk hijjab na saka batareda na d'aura d'an kwaliba, itama Munubiya irin kayan nawa ta canja. tsaf muka fito damu, saida Munubiya takira Innarmu ta sanar mata sannan muka tafi.
Mun tarar duk sunbar tsakar gidan, kowacce tashige 6angarenta, 6angaren su fauziyya muka lek'a domin sanarma mamarsu zamu fita.
bamu wani jimaba muka fito muka tafi.
Tunma a layinmu muka sami napep. har k'ofar shagon Aunty salamah ya saukemu..
Kamar yanda ta saba haka tamana tarba ta mutunci da d'oki. muma hakan ne daga garemu, dan muna k'aunar auntynmu data koya mana aiki, tace 鈥?'yan ukuna ina hasaanar to?鈥?.
Dariya mukayi, dan munsan Ayusher take nufi, mukace bama tasan mun tahoba amma daga nan gidansu muka nufa.
An wanke mana kai, sannan mukayi kitso bawani mai yawaba, aunty ce tace dole sai ammana kunshi ko kad'anne, dole badan mun soba aka mana Jan lalli sai bak'i daya zamo kad'an, bamu baro shagonba sai bayan la'asar, dan mund'an taya aunty aiki.
Kai tsaye gidansu Ayusher muka nufa, mun iskesu gaba d'aya afalo suna hira, Ayusher na tacema Feena tafarnuwa dazafa sha. yayinda innarmu da mama Rabi'a ke zaune kusada juna suna hira k'asa-k'asa. Aiyaan Ahmad da Aryaan kam hankalinsu nakan wasa a can gefe.
Yaa fadeel ne yafara fad'in 鈥渙yoyo 'yan biyunmu鈥?.
Dariya mukayi, sannan muka k'arasa cikin falon, bayan mun gaida iyayenmu muka gaida yaa Fadeel, sannan mukaima Feena ya jiki, ta amsa tana murmushi.
Ayusher daketa antaya mana harara Na kalla, 鈥渒ekuma lafiya kike wani hararmu?鈥?.
Harar takuma watsa mana tana mik'ama Feena kofin tafarnuwa, 鈥渂an saniba 'yan rainin hankali, tun k'arfe nawa kukace zaku taho amma sai yanzu?鈥?.
Munubiya tatashi taje inda take ta rungumeta, sorry habibati, wlhy mun biya shagon aunty ne munyi kitso, saikuma ta tsaremu wai sai munyi k'unshi, tamace a gaidaki鈥?.
鈥渒ai shine baku kirani mun jeba? wlhy nima kan nan nawa yana buk'atar kitso, tana lafiya鈥?.
Namik'e ina fad'in 鈥淪umul- sumul, mukuka dafa? ALLAH yunwa nakeji?鈥?.
Cikin tsokana mama Rabi'a tace 鈥渢uwo鈥?.
Na tunzuro baki gaba, kai mama wai keda innarmu kullum tuwo bakwa gajiya?鈥?.
鈥測o yaza'ayi mu gaji tunda shi mukaci muka girma, kajimin ja'iran yara, wai kukam bakuda mak'iyi sai tuwone?鈥?.
yaa Fadeel yace 鈥測o k'aton ciki yake saka mutane, ina dalili鈥?.
Dakuwa innarmu tamasa, 鈥済idanku Fadeel, mu miyasa bamuyi k'aton cikinba?鈥?.
Feena tace 鈥淎LLAH innarmu gaskiya yaa Fadeel yafad'a fa鈥?.
鈥渓allai Nafeesa, kema ina ganinki salo-salo Ashe k'yallece鈥?.
Dariya muka sanya gaba d'aya, akuma wannan lokacinne yaa Marwan yashigo da sallama.
Su Aiyaan sukaje da gudu suka taryoshi da amsar kayan hannunsa.
Waje yasamu ya zauna yana gaida su innarmu, muma muka gaidashi.
Ayusher datasan dokarsa ta yana shigowa a kawo masa ruwa ta kalli Munubiya, sis.... Please kibama yaa Marwan ruwa, ni nariga da na ta6a tafarnuwa鈥?.
Kamar munubiya bazata tashiba saikuma tamik'e saboda harara daya antaya mata, shi zatonsa ma nice, dan yasan Munu.... Akwai sauk'in kai.
Mama da innarmu kam hirarsu suketa zubawa kamar basusan mi mukeyi ba.
Babu dad'ewa saiga Munu... da k'aramin tire tazubo ruwa mai sanyi a jug, ajewa tayi a gabansa, ta durk'usa ta tsiyaya masa tabasa, sai da suka had'a ido ta janye nata da Sauri, alokacin ya fahimci Munubiya Ce, yana gama shan ruwan yadire kofin yana mik'ewa, 鈥渒i kawomin abinci d'aki鈥?. 鈥榶afad'a yana yin gaba abinsa鈥?.
Tad'an bishi da kallo sannan tamik'e takoma kitchen d'in.
Kallon juna mukayi nida Ayusher muna d'aga gira, yaa Fadeel daya gammu shima saiya saka dariya, k'asa-k'asa yanda su inna bazasuji ba yace 鈥渕uma ALLAH kabamu masu sonmo鈥?.
Muma ahankali mukace amin nida Ayusher.
Feena tace 鈥淎LLAH ya shiryeku, dama yajiku wlhy鈥?.
Yaa Fadeel yace 鈥渟aidai su susha duka, nikam ai bani dokuwa鈥?.
Nanma dariyar mukayi.
Da sallama tashiga d'akin, yana zaune bakin gado dagashi sai vest da dogon wandon kayansa bai cireba, wayace a hannunsa yake latsawa, ta dire tiren abincin a gefe sannan ta janyo k'aramin table d'in gefe gabansa, abincin ta zuba masa, har sannan bai kalleta ba, saida tagama zata tashi yace 鈥渨ato k saima ance kibani ruwa ko?鈥?.
Shiru Munu... tamasa, Dan batasan mizata ceba, yad'ago idanunsa irin nata (dan duk 'ya'yan mama Rabi'a kama muke da juna, saboda ita suka biyo, idan kacire Feena dake kama da babansu) yana kallonta, itadai kanta ak'asa tana wasa da zoben hannunta.
鈥渂aki jina ne?鈥?.
Ahankali tace 鈥渒ayi hak'uri to鈥?.
Shiru yamata bai tankaba, yaja abincinsa yafaraci anutse, baice ta tashiba itakuma bata tashinba, gashi bawata hira sukeyiba, ita tunaninma yanda zatayi zaman aure da yaa Marwan takeyi, Yaya za'ayi rayuwa tayi dad'i Dan ALLAH?.........
maganarsace tasaka ta d'ago ido tad'an kallesa, shima idonsa Na kanta. ta janye nata idanun.
Yakuma fad'in 鈥渘ace yaushe zakije kiga gidanki?鈥?.
Saitaji maganar wata iri, wai gidanta, gidansa dai, muryarta a sanyaye tace ai basai najeba鈥?.
Yace 鈥渒o?鈥?.
Kai ta d'aga masa alamar eh.
Yad'anyi wani munafukin murmuahi, Sanan yamik'e yanufi hanyar bathroom yana fad'in 鈥渒i shirya jibi zanzo na d'aukeki da yamma鈥?.
Bai jira amsarta ba yashige abinsa. tadad'e zaune tana kallon k'ofar toilet d'in, tamkar nanne zata ganoshi, saida taji motsin kamar zai fito sannan tamik'e da sauri ta kwashe kwanikan ta fice.
Bamu bar gidanba sai bayan sallar isha'i, yaa Marwan da kansa ya kaimu har gida.
_____________________________
Yana kwance a falon gidan daya zama mafakarsa, waya suke da momma akan yaushe zai koma? dan doctors d'in Abie nason ganinsa.
鈥渕aybe ma gibe ki ganni Momma dan nagama abinda ya kawoni鈥?.
鈥渟hikenan babu damuwa, amma kana ganin a masarautar ku babu Wanda yasan kazo?鈥?.
鈥渂abu Wanda yasani momma, hatta da Harun, sai Muftahu kawai鈥?.
Cikeda mamaki tace 鈥淢uftahu kuma?鈥?.
鈥渆h Momma miya faru?鈥?.
Tayi d'an jim sannan tace 鈥渂abu komai, amma ka dinga kula dai Muh'd鈥?.
Shima yad'anyi shiru yana nazarin maganarta, sai kuma yace 鈥渙k Momma insha ALLAH鈥?.
Yana ajiye wayar kuwa saiga Muftahu ya shigo, kallonsa Galadima yayi.
Muftahu dake shirin zama yace 鈥測alla6ai barka da rana鈥?.
鈥測kk?鈥?.鈥榗ewar galadima鈥?.
鈥渨lhy Alhmdllh, dama akan yarinyarne, kagafa har yanzu bamuji daga gareta ba鈥?.
Murmushin gefen baki Galadima yayi, sannan yabud'o massage d'in da Munaya ta turo masa yamik'ama Muftahu wayar.
Babu musu Muftahu ya kar6a, saida ya gama karantawa sannan ya d'ago yana kallon Galadima fuskarsa washe da murmushi, 鈥淎lhmdllh yalla6ai ta amsa Ashe?鈥?.
Kallonsa kawai Galadima yakeyi cikeda nazarinsa, yana mamakin yanda Muftahu ke d'okantuwa da wannan maganar auren, tunda yabashi damar binciken su Munaya bai barsa ya hutaba, haka kawai sai zuciyarsa ta d'arsa masa wani Abu, musamman idan yay dubi da yanda Muftahu ya nuna tsantsar farincikinsa dayace zai auri yarinyar na shekara 1. to koma dai miye, zai sanya masa idanu.
Muftahu yace, 鈥測alla6ai to yanzu ya za'ayi dasu mai martaba ne?鈥?.
Galadima dake latsa d'ayar wayarsa yace, 鈥渘o, karka damu da wannan, zan k'arasa komai kawai鈥?.
Kamar Muftahu baiso hakanba, amma saiyayi murmushin yake, 鈥渟hikenan ALLAH ya tabbatar da alkairi, yasa ayi damu鈥?.
d'ago ido Galadima yayi ya kallesa, 鈥渢o miye kuma na wannan doguwar Addu'ar? Saikace wani auren gaskiya?鈥?.
鈥淗akane kuma yalla6ai, sorry鈥?.
Shiru Galadima bai amsaba. falon ya d'auki shiru kowa da tunaninsa.
鈽呪槄鈽呪槄
Harda safe inata yawan duba wayata kozanga replay daga Galadima amma shiru, hardai munubiya tace 鈥渨ai miye bini-bini saiki duba waya?鈥?.
Kallonta nayi ina k'ak'alo murmushin yak'e nace 鈥渂abu komai fa鈥?.
Badan ta yardaba ta k'yaleni, cigaba mukayi da aikin da innarmu ta samu.
Aryaan yashigo yana kuka, muduka mukace miya faru kaikuma?.
Cikin kukan yace 鈥渂a Abdul bane ya dakeni, wai dan Zainab ta zubamin ruwa na rama鈥?.
Nace 鈥渋na Abdul d'in?鈥?.
鈥淪una wajen fanfo鈥?. 鈥榗ewar Aiyaan daya shigo yanzun鈥?. 鈥淎untynmu kuma wlhy sosai yabama Aryaan mari a fuska, sannan ya halbeshi ga k'afarsa har yafad'i鈥?.
Da hanzari nafice daga sashenmu, na iske Abdul da sauran yaran gidanmu a bakin fanfo suna wasa da ruwa, rankwashin Abdul nayi tareda murd'e kunnensa, 鈥渕i Aryaan yamaka ka dakesa dan k'aniyarka?鈥?.
Hannuna yadafe saboda zafin dayaji na murd'ar kunnen, cikeda tsiwa yace 鈥測oba Zainab ya daka ba danta watsa masa ruwa bata ganiba鈥?.
K'eyarsa na mangara, 鈥渢o ina ruwanka, Zainab d'in ba k'anwarsa baceba? kokuwa dan kai mama d'aya ta haifeku? daga yau kasake dukan wani acikinsu saboda yadaki Zainab ko Fahad saina lallasaka agidannan, masu shegen 'yan ubancin tsiya, iyayenku duksun 6ataku da k'in 'yan uwanku jininku鈥?. nak'are maganar dakuma rank'washinsa.
Aikam ya daddage ya kwantsama kuka, kaikace wani uban bugu namasa.
Kamar jira gwaggon haleematu keyi tafito tana tambayarsa miya faru?.
Fad'a mata yayi waina mareshi da murd'a masa kunnen saboda ya daki Aryaan, harda cewa na zageta.
Hummm tamkar dama kad'an take jira damu, har k'ofar d'akinmu taje tana zazzaga masifa da zagina.
Innarmu tafito tana tambayar miya faru? dan ita bama tasan an bigi Aryaan d'in ba.
Maimakon tama innarmu bayani saita koma kanta da cin mutunci, kamar innarmu tayi shiru amma yau saita kasa.
Ta kalli Goggon haleema tana murmushi, Sadiya bakinki yasan mizai fad'a, inba hakaba zan baki mamaki agidannan wlhy, bakinki ya tsaya iya maganar yara, idan kika kuskura iyayena suka kuma shiga a furicinki zakiyi nadamar sanina鈥?.
Innarmu nagama fad'a tashigewarta.
Galala gwaggon haleematu da duk matan gidanmu sukayi da mamaki, duk kuma sai shakkar innarmu ya shigesu, Ashe akwai ranar dazata iya maidama wani murtani acikin gidan?.
Murmushi nasaki, sannan nabama Munubiya dake kusadani hannu muka tafa, nace 鈥渉o innarmu, kina aljanna ina binki da addu'a, haka nakesonki agidannan, kiringa watsema kowa aniya鈥?. naja hannun Munu.... muma muka shige ciki.
Abbanmu dake kallon komai ta window d'akinsa yasaki murmushi yana girgiza kai, yasan gaba d'aya halayen Munaya nashine, yarinyar batada tsoro, amma yau Ai'sha ta birgeshi datama Sadiya haka, koba komai tasaka musu shakkarta azukatansu.
Aikan kowa jiki babu kwari taja k'afarta tashige d'aki tana gulma da zuciyarta.
Gwaggon Haleema kam ai saida Nusaiba taja hannunta sannan ta iya d'aga k'afarta.
Koda muka Shiga sai innarmu tahau mana fad'a akan dukan Abdul d'in da nayi, hak'uri kawai na bata danni yau raina fes, innarmu tafara maida murtani.馃槄
鈽呪槄鈽呪槄鈽?
Da k'yar ya iya bud'e idonsa ya janyo wayarsa dake ringing, batare da ya dubaba ya amsa yasaka a kunne.
鈥淎ssalamu alaika Muhammad kana lafiya?鈥?..
Zaram ya mik'e zaune tareda watstsayewar dole saboda jin muryar mai martaba mahaifin Momma papi.........鉁嶐煆?
To ko mai martaba zai amince da auren Munaya? duk da baisan kai tsaye auren yarjejeniya baneba馃?.
Karku manta Amincewar mai martaba itace ta kowa.
Muje zuwa my guys鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*馃槶馃馃徎鉁嬸煆?
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎1鈨?8鈨?
..........A Asibiti gado suka bani, sunata fad'an yanda jinina ya hau sama, su mamakima suke yi 'yar k'aramar yarinya dani amma inada hawanjini, shin miyayi zafi haka?.
Su Abba dai kasa cewa komai sukayi, dan su kansu abin na yata6a zuciyarsu.
Wannan karonma Mama Rabi'a da Munubiya ne suka kwana a wajena, washe gari da yamma saiga 'yan gidanmu wai sunzo dubani, bamuyi mamakiba Dan munsan ba domin ALLAH sukazoba, kawai sunzo ganin kwafne.
Duk suncika d'akin da surutu akan wai suna mamakin miya samin hawan jini?. daga mama Rabi'a har Munubiya babu wanda yabasu amsa.
Doctor ne yashigo yace sud'an ragu wasu su fita baranda dan ALLAH, duk fita sukayi harda mama Rabi'a aka barmu iya mu yaran kawai, dansu Fiddausi duk hadasu akazo.
Ina daga kwance kan gado ina sauraren hirar dasukeyi, wai safara'u da Halimatu ne sukaje gidan su Siyama tai tamusu yatsina da d'aukar kai, saikace ba 'yan uwanta ba, mijinta yadawo sukayi shigewarsu suka barsu afalo har yamma sannan suka fito, mai makon tabasu hak'uri sai cewa tayi wai dama basu tafiba馃ぃ.
Wannan abun daya faru shine yajawo rigima a gidanmu jiya da daddare, har saida su Abba suka tsawatar.
Murmushi kawai nayi Na gyara kwanciyata, a zuciyata ina fad'in maganinku ai, baku masu dangiba..........gabana yafad'i, saboda jin tamkar k'amshin turarensa. da sauri Na d'ago kai saboda jin su Fauziyya ma sunyi tsit daga surutun dasukeyi suna kallon bayanmu.
Wani yaam naji a raina domin ganin Galadima da tawagar dogaransa, sai wani dake gefensa amma ba muftahu bane, (Harun ne). Sanye cikin k'ananun kaya wad'anda suka fidda ainahin k'irarsa ta cikakken namiji, fuskarnan kamar kullum babu walwala.
Mu 4 ne kawai a d'akin, dan haka yana tsaye a gadon farko da alama tanbayoyi yakema matar dake jiyya a gadon. gani nai yasaki wani guntun murmushin gefen baki sannan ya kalli harun, bansan miya cemasaba nagadai yabaro wajen yana tunkaro gado Na biyu.
A hankali Na lumshe idanuna wani Abu Na tsikarar zuciyata mai kama da tsoro da rud'ani.
Sauran 'yan uwana kam sun zuba masa idanu tamkar zasu cinyesa, kowacce takasa furta komai a fili saida a zuciyarta take tattaunawa da yaba Galadima d'in.
Annanma yayi kusan mintuna hud'u sannan ya tunkaro gadon takusa damu, dan nice ta k'arshe. duk da akusa damu yake banajin miyake fad'a, saidai motsin la66ansa kawai nake gani, tabbas Galadima naji da Girman kai da mulki, kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da tsantsar sarauta da mulki dake yawo a jinin jikinsa....... tunda naga yanufo inda nake sai kawai narufe idanuna gaba d'aya.
Su Munubiya duk suka risina suna gaidashi.
Hannu kawai ya d'aga musu yamatso jikin gadon danake.
Tsantsar mamakine ya bayyana a fuskarsa, yad'anyi kamar zai nunani da hannu saiya kuma fasa, su safara'u kam duk sun zubo mana idanu suga yanda za'a kwashe.
Munubiya ce cikin k'arfin hali tace 鈥淢unaya ki tashi ana miki magana fa鈥?. daka ganta kasan a tsorace take maganar.
Shima juyowa yayi ya kalli Munubiyar domin jin kuma Muryata, maganar Muftahu ta fad'o masa arai dayace yaran twins ne, kuma ba'a iya banbancesu.
Suma Kansu dogaran NASA da Harun duk sunyi tsuru suna kallonmu, domin babu wanda baiga jaridarba a wancan lokacin.
Maganar sace tasaka kowa maida hankali a kansa, nidai har yanzun idona arufe suke, cikin basarwa da nuna halin ko in kula yace, 鈥測a jiki?鈥?. tamkar bayaso haka yayi maganar.
Nima cikin dakiya da shariyar kamar yanda yamin nabud'e idona nace 鈥淎lhmdllh鈥?.
Kamar yanda yake tambayar kowa nima haka ya tambayeni miye matsalata?.
Na d'a6e baki sannan nace 鈥渕asassara鈥?.
Harun ya kalla, danshi baima fahimci minake nufiba.
Murmushi harun yayi, danya fahimci bai ganeba, cikin gyara tsayuwa yace 鈥渢ana nufin fever鈥?.
Caraf fiddausi tace, 鈥渞anka yadad'e k'arya take hawan jinine鈥?.
Juyowa yayi ya kalli fiddausin da fararen idanunsa wad'anda suka nemi zautata, bai Ce komaiba ya janye ya maida kan Munubiya, 鈥淪ister naga drugs d'innan?鈥?. yafad'a kamar anmasa dole.
Ko kad'an Munubiya bataji maiya fad'aba, dan a saman la66ansa yayi maganar, tana shirin sake tambayarsa d'aya daga cikin dogaran ya maimaita mata a tsawace.
Nikaina saida Na bud'e ido saboda tsawar, Na bankama dogarin harara ina magana k'asa-k'asa yan da babu mai jina, kajimin shegen dogari, dan tace batajiba zakawani daka mata tsawa?, shi mizaisa bazai bud'e baki yayi magana yanda kowa zaijiba? Mutum sai azabar Girman kai mtsoww, koma R bai iyaba.
Duk maganar danake la66ana ne kawai ke motsawa, shikuma idon nasa nakan la66ana, dukda duba kwalin drugs dayakeyi, tsaf ya karanci duk maganar danakeyi. yayi wani munafukin guntun murmushi yana mik'ama Munubiya magungunan.
Juyawa yayi yama Harun magana, sannan ya juyo ya kalleni yana fad'in 鈥淎LLAH yak'ara lafiya鈥?.
Harara Na zuba masa batare da tunanin zai ganiba, amma sai caraf muka had'a idanu.
Janye idanunsa yayi a kaina yajuya yabar wajen yana cije lips d'insa da mamakin yarinyar nan da batada tsoro.
su Safara'u Na zuba masa godiya, duk da zukatansu Na mamakin yanda yanuna tamkarma bai sanmu ba.
Ko kallonsu baiyiba ya d'aga musu hannu, sukuma sunyine dama danya tanka musu.
Harun ya tambayi Munubiya wane doctor ne ke dubani?.
Ta Sanar masa.
Addu'a yaymin sannan yabar wajen shima.
Lumshe idanuna nayi zuciyata Na kaikawo, yanda Galadima yayi, saiya kuma tabbatar min da mafarki dai nayi kenan, bawai gaba da gaba ba yace muyi Auren Contract ba kenan.
Innalillhi, mike shirin faruwa danine ni Hussaina, hawayen dasuke neman zubomin nai k'ok'arin had'iyewa, Munubiya kanta tashiga kogin mamakin yanda Galadima yay tamkar ma komai baita6a faruwaba, shin kodai shi baiga abinda yafaru a jaridar baneba?....
Batada mai bata amsa, su safara'u ma magana suketayi k'asa-k'asa a tsakaninsu, alokacinne kuma matan gidanmu suka shigo.
Mamansu yaa hameed take tambayar wai wananan bashine Galadima ba na jikin jaridar nan?.
鈥渨lhy shine kuwa mama鈥?. cewar Fiddausi.
Haleematu ta kar6e da fad'in 鈥渕ama kinga yanda ya nuna kuwa? tamkar ma bai gane su twins ba balle ya nuna yama San abinda yafaru a bayabaya tsakaninsu鈥?.
Murmushin mugunta mamansu ya hameed tayi, 鈥測o ai dama saboda irin haka ake cewa Ku kare mutuncin kanku, danshi namiji komi yayi adone, sannan shi d'an manyan mutanene, ko kallonsa da abin babu mai sakeyi, amma Ku gashi har ana fasa aure, kamun kai dai dad'i gareshi ai dama, kum.......鈥?
Shigowar doctor tasaka maman su yaa hameed yin shiru, korarsu yayi gaba d'aya, yace subarni Na huta.
Basuso hakanba, dan shirya cin zarafinmu maman yaa hameed tayi.
Daganan gida suka wuce suna 'yan gulmace-gumacensu da dariyar mugunta.
鈽呪槄鈽呪槄鈽?
Galadima kuwa yana gama zagaye-zagayensa a asibitin na duba marasa lafiya gida suka wuce.
Bayanin doctor yabashi mamaki, wai wannan 'yar yarinyar keda hawan jini, itako miyayi zafi haka a rayuwarta鈥?. wani sashi na zuciyarsa yabasa amsa da (6atancin da akai muku).
Lips d'insa ya cije yana jan dogon tsaki, shikad'ai yasan burin daya d'auka akan dukkan Wanda yasamu da hannu a wannan lamarin.
Sun biya birnin gayu plaza yaga komai yana tafiya dai-dai, daga nan suka koma masarauta.
鈽呪槄鈽呪槄
Nima a ranar da daddare aka sallamoni, nadawo gida nacigaba da shan Magani, yayinda biki keta gaba towa kuma.
Har yanzu innarmu tana cikin damuwa dani kaina akan zancen aurena daba asan taka maimai angoba.
Zancen galadima kuwa ai tini na shareshi, dan nabarsa amatsayin mafarki nayi, musamman kuma dana bincika banga number wayan daya baniba, a wayata kuma tun randa na tura masa massege na gogeta dama gudun kar wani yagani.
Yanda 'yan gidanmu suketa rawar kai akan bikin saran 'yan uwanmu innarmu batayi, bazama ka ta6a d'auka itama zata aurar da 'ya'ya har biyu baneba.
Mama Rabi'a ce ke tsaye akan komai, sai aunty salamah datazo da magunguna ta d'id'd'irka mana, mu bamusan namiye ba, takumace mudinga sha, saikuma had'ad'd'en sabulun wanka da mai data had'a mana, ga wasu turare masu sirrin k'amshi, takuma gargad'emu daga yanzu muna saka hijjab duk inda zamuje da nik'af, domin fatarmu tasami nutsuwa kar rana ta maidamu gidan jiya.
Ni dai dagani har munubiya da to kawai muke binta, kuma duk abinda tace muyi munayinsa.
Abbanmu yakira mama Rabi'a yabata wasu kud'i akan tak'ara amana siyayyar kayan kitchen da 'yan uwa keyi, tunda ita innarmu bawasu dangi ne da itaba dazasu tara mata.
Sosai tamasa godiya, sanan tasanarma innarmu, ko babu komai taji dad'i, harma tamasa godiya itama.
Tafiya mama Rabi'a tayi da k'ud'in, washe gari suka Shiga kasuwa itada inna lami, kaya masu k'yau suka sissiya mana dai-dai gwargwadon k'arfinmu. aka adanasu gidan inna lami duka.
*_kwanci tashi_*
Babu wahala wajen ubangiji, yau gashi abinda kowa yake jira yazo, domin kuwa ankawo lefen Haleematu, gaskiya angonta yayi k'ok'ari, akwati 5 abinta, kuma kaya masha ALLAH, sai-dai hakan bai hana 'yan gidanmu gulmaba, washe gari kuma aka kawo kayan Safara'u da Fiddausi.
Suma dai kam saidai mak'iyi, amma jikin maman safara'u yayi sanyi, dan gaskiya kayan sauran duk sunfi nata. Itama dai akwati biyarne, amma kayan cikine basukai na sauranba.
Again washe gari saiga na Fauziyya da Munubiya, mama Rabi'a tasan komai dake wakana a gidanmu, dan haka suka dage sukaima Munubiya lefe na 'Yar gata, wlhy ba fariyaba lefenta yafi na kowa, ranar har kukan dad'i nayi, domin banyi zaton hakanba. itama dai fauziyya angonta yayi k'ok'ari gaskiya.
Tuni hassadar matan gidanmu tafito fili suka fara yada habaici wai an aro kaya anzo ana musu burga, da anyi aure sai ake maidawa d'ai-d'ai.
Dagamu har innarmu babu Wanda ya tanka musu, dan munsan yau dai mune aciki sune a kwana馃ぃ馃ゴ.
Rashin kawo nawa lefen kuwa ko a kwalar rigata bai dameniba, dan bama sanin mijin nayiba balle nadamu dawani lefen banza. saima Munubiya ce harda kukanta rurus akan wai saidai araba mana kayanta mu biyu.
Nifa dariyama tabani wlhy.
Ganin ni babu lefe yasaka su baba k'arami siyomin kaya masu k'yau na fitar biki har kala 10, aka d'inka min, sai takalma da bags da veils masu k'yau suma.
Habaici dai kam munshashi wa su innaro da matan gidanmu, danma ita innaro gwaggo Safiyya na hanata ne, da bamu san tijarar dazata zubarba a ranar kam.
A haka aka shiga satin biki, mu bamu wani gayyaci k'awayeba, daga Bilkisu sai su Ayusher, ashe Ayusher ta buga invitation na k'awaye suka raba itada Bilkisu bamu saniba.
Abin mamaki ranar kamu sai ganin k'awayenmu mukayi harna secondary.
munji dad'in hakan sosai kuwa.
A ranar kamun saiga wasu mata hud'u sunzo wai dangin miji nane, su mama Rabi'a sukayi musu tarba ta mutunci, ba a nuna musu komaiba kuma, dukda a yanayin shigar talauci da sukazo, saidai zund'e da gulma irinta 'yan biki. Matan gidanmu kam komai ya kaimusu dai-dai, sai dariya da yada magana a kaikaice sukeyi. Da aka kaisu su gaisa da innaro taita musu yatsine-yatsine, harda tanbayarsu waisu garinsu ba'a lefene? dabasu kawoma jikartaba?.
Basuce komaiba sai murmushi kawai da sukayi.
Washe gari kuma akayi k'unshi, mudai namu aunty Salamah ce tamana, tana tsaye akan komai namu tamkar yayarmu ciki d'aya.
A ranar kuma akaje a kaima sauran amaren jere, harda Munubiya, amma ni banda ni, tunda ba'asan ina za'aje ayiba.
Aranarma Munubiya tayi kuka, nidai ina k'ok'arin danne zuciyata, saboda nabama innarmu kwarin gwuywa karta tada hankalinta.
Aiko Alhmdllh ta dake tamkar komai baya damunta, tashige cikin abokan arzik'inta sunata harkoki. kowanne 6angare yacika da dangin matan gidanmu, abin tamkar fariya, namu 6angarenne kawai keda sauk'in jama'a, hakama gidan innaro yacika da danginta da dangin kakanmu.
Tunda aunty Salamah tagama yimana k'unshi da gyaran kai dana jiki sai muka nufo hanyar gida, saboda yaa marwan yazo neman Munubiya harsau biyu, sai kiran wayarta yake yana masifa saboda tare yake da abokansa. hakan yasa muka taho gida.
Gashi Yau zamuyi sister's and brother's day, duk da dai saima da yamma.
鈽呪槄鈽呪槄鈽?
Galadima dake zaune a makeken falon Ummu hasheem, yanata bin jerin akwatinan da kallo, ga wasu daga 'yan uwansa zazzaune sunata kuma kimtsa kayan, aunty Mimi ta kalleshi, 鈥渒unga zanma mantafa, my k'ani ina kayan dana baka kayo gaba dasune?鈥?.
Yatsine fusaka yad'anyi yana gyara zamansa, 鈥渘ifa nama manta inda suke, shiyyasa nace bazan d'akkoba ai鈥?.
Wata uwar harara ta watsa masa tace, 鈥渓allai bakada kai yaro, bar ganin matarka za'a kaimawa, suka 6ata biyana zakayi ehe鈥?
Murmushin gefen baki yasaki yana lumshe idanu, cikeda k'asaitarsa yace, 鈥淪amha! jeki bedroom d'ina ki duba, maybe suna can鈥?.
鈥渂ama kada tabbas kenan?鈥? cewar mom.
Bud'e idanunsa yayi yana murmushi, 鈥渘o mom insha ALLAH sunama can. ni yanzu kam kun sallameni natashi natafi? dan zansa aje a d'auko su Akash a airport 鈥?.
Ummu Hasheem tace 鈥渒aje kawai, dama dan kaga kayanne, tunda kuma kace komai yayi ai shikenan鈥?.
Mik'ewa yayi yana fad'in 鈥渢hanks you Ummu, nabarku lafiya鈥?.
Tunda yasamu yay escape sai ya sauke ajiyar zuciya, shi dariyama suke bashi dagasu har su papi, su Dan basu san auren shekara d'aya bane dabasu dinga wannan rawar k'afarba, sun wani zauna sun had'a uban kayan lefe, yad'an ta6e bakinsa kawai yana nufar sashensa.
Komai na gidan sarauta mai tsarine, dan haka kai lefen MUNAYA da suke shirin yima a tsare akayisa, (papi ne yace Subari sai yau ana gobe d'aurin aure sai akai, tunda gidan su munaya basusan kosu su wayeba).
An tsara iya wad'anda zasu kai lefenne.
Bayan an gama zuba akwatunan a wata farar mota mai k'yau sabuwa dal aka rufe, driver ne kawai zai shiga cikin motar.
Sai kuma motoci 6 da aka zaba wad'an da zasu kai lefen.
Motar farko dogaraine, ta biyu kuma kuyangi ne, sai guda biyu 'yan cikin gidansu Galadima ne su hud'u, ko wacce mota mutum biyu, sauran biyun kuma 'yan 6angaren masarautar su Momma, suma su hud'u, kowacce mota biyu. sai Samha datasa kuka saitaje taga matar Uncle Sam.
Aunty mimi harta korata da zare mata idanu saiga Galadima motocin na niyar tashi.
Da kansa yabud'e mata gaban motar da aka saka akwatinan yace tashiga nan, idan taje ta gaida masa matarsa.
Cikeda d'oki tace zataji Uncle Sam, bazaka bada komai akai mataba.
Kansa yad'an dafe dan yakula Samha na neman k'uresa, shikuma yafad'a mata maganarne domin yanason agaban jama'a yadinga yana tsantsar k'aunar Munaya, a bad'ini kuma suna zaman aurensu na contract, shiyyasa ko lefennan baiji tsadar kud'in saba yabud'e bakin aljihu aka zuba kaya masu azabar k'yau, gakuma kud'in da Mai martaba yabada shima, dakuma sauran k'annen mahaifinsa.
Hannu yasaka a aljihunsa yana duba kozai samu wani Abu, amma babu komai sai wata chocolates guda biyu, wadda ya d'akkota ne zaiba khaleel d'azun yama manta, mik'ama Samha yayi yace 鈥済ashi kibata鈥?.
Da dariya samha ta kar6a tace 鈥淯ncle ta gode to鈥?.
Kansa kawai ya jinjina mata ya shirin barin wajen.
motocin suna fita daga masarautar saiya sauke ajiyar zuciya kawai.
鈽呪槄鈽呪槄
Gidanmu ya cakud'e da hayaniyar da akasan gidan kowanne biki da ita, bare mu daya kasance har auren mutum 6, dukda sai gobene d'aurin aure kuwa, yara sunata wasansu da tsalle-tsalle.
A jere motocin suka shigo cikin anguwar, jama'a sai binsu da kallo sukeyi, dai-dai k'ofar gidanmu driver daya san gidan yay parking.
Babu Wanda yay mamaki a 'yan kawo lefe, domin kuwa dama labari ya karad'e masarautar cewar Galadima'yar talakawa zai aura.
Dogarawa da kuyangi suka fara fitowa, sannan suka bud'e motor da akwatina suka suka fara fitarwa. Nanfa jama'ar anguwa sukayi cirko-cirko suna kallon ikon ALLAH dan ganin akwatinan da aketa fitarwa daga mota.
Batare da neman isoba Kuyangin suka fara kwasar akwatinan suna shiga dasu gidanmu..............鉁嶐煆?
馃槀馃槀馃槀
Team innaro kufito mu caskale yau馃檴馃じ馃徎鈥嶁檧
鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧
Asha weekend lafiya馃槄鉁嬸煆?
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu馃憦馃徎馃槶_*
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu馃挅: *_Typing馃摬_*
*_HASKE WRITERS ASSO...馃挕_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_鈾AINA KAMA......!!鈾*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce馃馃徎_*
馃憠馃徎1鈨?7鈨?
.........Cikeda girmamawa yace, 鈥淩anka ya dad'e barka da dare?鈥?.
鈥渂arkan ka dai Muhammad. dama kashigo k'asar kenan?鈥?.
Gabansa yad'an fad'i, danshifa yama manta mai martaba baisan yazo k'asarba, dakiyar dole ya aro yace, 鈥渨lhy kuwa nashigo d'azun yin wani aiki, amma gobema idan ALLAH ya kaimu zan koma鈥?.
鈥渢ofa, gobe gobe? kuma gashi inason ganinka a goben鈥?.
d'an jimm yayi, irin tamkar baisan komaiba, cikeda shakku yace, 鈥渞anka ya dad'e lafiya dai ko?鈥?.
鈥渓afiya k'alau, wata muhimmiyar magana nakeson muyine鈥?.
鈥渢o shikenan, zanshigo insha ALLAH 鈥?.
鈥渢o madalla saina ganka鈥?.
Dafe kai Galadima yayi yana mamakin kansa, anya kuwa baima kansa d'aurin gorobo? koda yake idanfa yayi hak'uri shekara 1 ne ko 2 kacal, inma komai yafito kafin cikar shekarar zai sawwak'a matane, yad'an murmusa sannan yakoma ya kwanta abinsa cikeda tunani barkatai.
鈽呪槄鈽呪槄鈽?
Rashin reply d'in Galadima ya dameni, haka dai naita danne zuciyata dankar innarmu da Munubiya su fahimta, nacigaba da harkokina tamkar banida wata damuwa a zuciya, saima sallar dare damuka fara dagewa da tashi nida Munubiya, gakuma azumin damuka tashi dashi yau litinin.
Duk da innarmu ta fahimci inada damuwa batacemin uffanba, saidai tausayina na damun zuciyarta, tana dannewane kawai.
Munubiya kam tsaf tagama fahimta ta, amma itama saita nuna bata fahimci komaiba, taje tasamu innarmu da maganar son a d'aga bikinta again.
鈥渕unubiya ba wannan yakamata muyiba, addu'a yakamata muyima 'Yar uwarki, idan da rabo saikiga ALLAH ya kawo mata miji a cikin watanni 2nan dasuka rage kinji. nima nasan tana acikin damuwa, amma tana dannewa a zuciyarta saboda farin cikinmu. addu'ar dazamu mata itace tsantsar k'aunarta a garemu鈥?.
鈥渟hikenan innarmu, insha ALLAH zamu kuma dagewa da fad'ama ALLAH, itama ALLAH ya kawo mata ta hanyar da batayi zatoba, ya sakanka mata fiyeda sadaukarwar datayi, innarmu nasan sadaukarwar da 'Yar uwata tayine yasakata a wannan halin, ta sadaukar da farincikinta saboda ni, mizanyi na biyata nikam鈥?.
Murmushi innarmu tayi, tace, 鈥渁ddu'a鈥?.
鈽呪槄鈽呪槄鈽?
Washe gari yatashi ya shirin tafiya masarautar su Momma, Harun yakira yace ya nema masa ticket.
Cikeda mamaki Harun yace, 鈥測aushe kashigo k'asar Galadima?鈥?.
K'aramin tsaki yaja, dan shifa yama manta Harun baisan da zuwansa ba, Link d'in hannun rigar milk d'in shaddarsa yake k'okarin sakawa, cikeda dakiya yace, 鈥渏iya nazo da daddare, kuma inagama yau zan koma鈥?.
鈥渢ofa, amma baka cikin masarauta?鈥?.
鈥渘o a hotel Na sauka鈥?.
鈥渙k barato a nema ticket d'in, sai muzo mu d'aukeka鈥?.
鈥渒arka damu harun, banason kowa yasan nazoma, muhad'u dakai kawai a airport 鈥?.
Koda suka yanke wayar sai yaja tsaki, gaba d'aya yakoma mak'aryaci, abinda yatsana arayuwarsa fiye da komai kenan (k'arya) amma sai gashi shi yana zundumata, 鈥淎stagafurullh鈥? yashiga maimaitawa a zuciyarsa.
Tsaf yafito cikin shadda milk color (nakula yana k'aunar milk) d'inkin rigar 3quarter, harda su hula, yayi k'yau sosai, yafito ainahin sa na cikakken bahaushe kuma basarake, ya fesa turaraensa Na kullum, komai nasa dayazo dashi ya had'a a waje d'aya. sannan yakashe kayan wutar bedroom d'in.
Afalo ya iske Muftahu zaune yana jiransa, yad'anyi mamaki amma sai bai nunaba, yabashi hannu suka gaisa.
Muftahu yace, 鈥渮aka dawo ta nan kenan?鈥?..
Kai Galadima yad'aga alamar a'a, sannan yanufi kayan wutar falon yafara kashewa. saida yagama komai sannan ya kalli Muftahu alamar suje.
Murmushi kawai Muftahu yayi, danya lura yau miskilawanne aka.
Sun isa airport, lokacin shima harun harya je, mamakine ya kama harun Dan ganin Galadima tare da Muftahu, shima yanzu yana mamakin yanda Muftahu ke kuma kusanta kanshi da Galadima, baice komaiba yabashi hannu suka gaisa kamar yanda yabama Galadima.
Harun yanason suyi magana da Galadima amma ga Muftahu a wajen, sai kawai yashare akan sayi a waya kawai.
Basu wani dad'e a airport d'inba jirgin su Galadima yatashi.
鈽呪槄鈽呪槄
Yau hankalin kowa a tashe yake agidanmu saboda gwaggo Safiyya da aka kawo batada lafiya, dayake ba'anan kusa damu take aureba, tanacan wani gari daban, tun lokacin bikinsu yaa Hameed tamasu Abba complain akan batajin dad'i, amma kunsan maza darashin d'aukar Abu serious, sai basu maida hankalinsuba.
Ita kuma kunya tahanata kuma musu maganar, har aka gama biki ta tafi, ashe baiwar ALLAH ciwo nata cin jikinta babu Wanda yasani, tun tanayi a tsitsaye har takai ga kwanciya, yaranta sun kaita asibiti amma basuga wani canjiba, hakanne yasa suka maidota gida, Dan aganinsu dai su Abba sunfi mahaifinsu k'arfi.
Aiko suna isowa babu 6ata lokaci aka wuce da ita asibiti.
Dan danan aka fara bata taimakon gaggawa.
Muda innarmu ne kawai da innaro a asibitin, amma matan gidanmu babu wace tabimu, kusan mudasu baba k'arami muketa shiga da fita a asibitin dan ganin komai ya dai-daita.
Kusan yamma saigasu Safara'u lokacin ma gwaggo Safiyya tana barci, yaranta duksunyi jigum-jigum da innaro saboda tashin hankalin dasuke ciki.
Har dare ba'abar kowa yashiga wajen taba, sai su Dady kawai, ganin dare yayi akace mu muje gida kawai.
Haka muka tafi akabar innaro da aunty habiba d'iyar gwaggo safiyyar ta uku, itama tayi aure amma tafito, yanzu zawarci takeyi. saikuma yaa Anas da aka barmusu saboda ko wani Abu zai taso.
鈽呪槄鈽?
Tunda yafito daga jirgi ya hango tawagar masarautar kakannin nasa, yasan tarbarsa sukazoyi, inhar zaishigo haka sukeyo gayyar tarbarsa, saikace wani bak'o daban, gefe yayi da fuskarsa dankarsu gansa, sashen motocin da akan d'auka drop ya nufa, duk manyan motocine da aka tanada dama domin irinsu, d'aya yabud'e da Kansa yashige da sauri, alamar yayma driver d'in suje.
Tacikin glass yake kallonsu yana murmushi, yanda suketa d'aga kai nason hangosa, suna fita daga airport d'in ya kwantar da kansa ajikin seat ya lumshe idanunsa yana tunanin wane hukunci mai martaba zai yanke akan maganar, shin ya amincene? Kokuwa?.
Driver yace, 鈥渙ga ina muka nufa?鈥?.
Bai bud'e idonsaba kuma bai d'agoba, yace 鈥済idan sarki鈥?.
Ta madubi driver n ya kallesa, 鈥測alla6ai ko kaine ma dai akazo tarba daga masarauta?鈥?.
Murmushi kawai yayi batareda yace komaiba.
Jin bai amsaba sai driver yakama bakinsa ya tauke shima.
Ganin shine yasa dogarai suka bari aka shigar dashi har cikin masarauta, tunda yafito bayi da hadimai keta zubewa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai yake d'aga musu, fuskarsa ad'an sake take, bai d'aureba baikumayi murmushi ko dariya ba kai tsaye.
Tuni an kar6i kayansa an nufi sashin inno dasu, shikuma yanufi fada, Dan yasan yanzu Sarki suna fadanci.
Cike fadar take da 'yan majalissar Sarki anata fadanci, bayan an masa iso yashiga da sallama, nanfa dogarai suka fara zuba masa kirari.
Hannu kawai ya d'aga musu ya rissina yana mik'a gaisuwa ga Sarki.
Sarki da fuskarsa tacika da fara'ar ganin jikan nasa ya amsa cikin lumshe idanu.
Nan dogarai suka d'au da fad'in 鈥渟arki ya amsa maka sarkin gagara badau na gobe, an gaida magajin sarki, galadiman gagara badau, ALLAH yabaka zamani irinna sarki gagara badau.
Galadima Yakuma rissinawa ya mik'a gaisuwa ga 'yan majissar sarki, suma cikeda fara'a suka amsa, kowa yasan irin tsantsar k'aunar da sarki kema jikan nasa a masarautar.
Atake anan sarki ya sallami kowa, fadanci yatashi saikuma gobe idan ALLAH ya kaimu, yau yanada ganawa ta musamman da jikansa.
Haka kowa yatashi yana musu addu'ar kasancewa cikin aminci.
Tareda Galadima sarki yashiga cikin gidansa, hannunsa Na rik'e da Na Galadima, ba sabon Abu bane hakan a masarautar, duk Wanda yakwana yatashi acikinta yasan matsayin Galadima azukatan masu masarautar.
Akatafaren falon sarki suka yada zango, babu dad'ewa da shigowarsu saiga jakadiya da kuyangi uku, kowanne d'aukeda babban tire, bayan sun dire komai suka zube suna kwasar gaisuwa wa sarki, sannan suka gaida Galadima.
Jakadiya ma ta rissina ta gaida Galadima damasa barka da zuwa masarautarsu.
Bayan fitarsu Galadima yakuma risainawa a girmame ya gaida sarki kakansa.
Cike da murmushi sarki ya amsa yana kamo hannunsa, 鈥淢uhammad Sameer! kana lafiya鈥?.
鈥淎lhmdllh ranka ya dad'e鈥?.
鈥淢asha ALLAH, ya kabaromin Zeenah ta da jikin babanka da 'yan uwanka kuma su Haneefa?鈥?.
鈥淢omma lafiyarta lau, hakama jikin Abie Alhmdllh, suma su aunty mimin haka鈥?.
鈥渢o Alhmdllhi, ALLAH yacigaba da jagorantar lamuranku ya albarkaci rayuwarku ta gobe da jibin jibima鈥?.
Murmushi Galadima yayi yana amsawa da amin.
Sarki da Galadima tare sukaci abinci, (tun yana k'arami dama idan yazo gidan hakance ke faruwa tsakaninsu) Sunci sun k'oshi sukayi hamdala ga ALLAH.
babu wani 6ata lokaci sarki yashiga masa bayanin kiran nasa akan maganar da Fateema (mom) tazo masa da itane jiya, shima ya zauna yayi nazari yagane hakan shine dai-dai, Galadima ya auri Munaya.
tur6une fuska Galadima yayi tamkar baisan komaiba, yace 鈥渞anka yadad'e ka gafarceni, ammafa ni bata minba ai鈥?.
Sarki yay murmushinsu Na manyan k'asaitattun masu ji da mulki, 鈥渂asai tayi makaba Muhammad, domin sanda Na aurama babanka Zeenah itama bai mataba, amma saboda biyayya dakuma tausayin d'iyar 'Yar uwarta ta amince tamin biyayya, to kaima hakan nakeso gareka, ka amsamin da to kawai saimu zauna lafiya, kasan magana biyu ba halina baceba ko鈥?.
Jinjina kai Galadima yayi yana kuma tankwashe k'afarsa, cikeda girmamawa yace 鈥淎LLAH ya huci zuciyarka ranka ya dad'e, Na amince da za6inka, ALLAH yabani ikon rik'ewa鈥?.
Cike da tsantsar farinciki Mai martaba ya rik'o hannun Galadima, 鈥淢uhammad ALLAH shiyi maka albarka, ya tsareka dadukkan sharri, ALLAH yabama mahaifinka lafiya kaji鈥?.
鈥渁min ranka ya dad'e, ngd sosai 鈥?.
Daga nan hira suka cigaba dayi cikin tsantsar soyayya da k'aunar juna, kowanne yanajin d'an uwansa sosaih a ransa.
Kusan atare suka yini, inno tun tana zuba idon shigowar Galadima harta hak'ura. Galadima bai shigo wajenta ba sai bayan sallar magriba.
Tundaga k'ofar sashenta hadimai keta kwasar gaisuwa, tuni labarin tahowarsa ta iske inno, hakan yasa ta k'imtsa da k'yau, ta sallami bayinta masu mata hidima.
Fuskarsa d'auke da k'ayataccen murmushi ya k'araso falon, bai zauna ko inaba sai jikin kakarsa, oh my sweet inno I miss you so much wlhy鈥?.
Kunnensa tad'anja kad'an, cikeda tsokana tace 鈥渕iskili kafi mahaukaci ban haushi, aini harna fara shirin yo bikonka daga turakar mai martaba鈥?.
Yayi 'Yar dariya yana fad'in 鈥渢uba nake ginbiyar papi鈥?.
鈥渏a'irin kaya, bazaka canjaba dai? ya kabaro iyayen naka da 'yan uwanka?鈥?.
鈥渒owa lafiya lau ranki ya dad'e鈥?.
鈥渢o Alhmdllhi 鈥?.
Nanma hirarce ta 6alle tsakanin kaka da jikanta, kan mace me nanma an cika masa gaba da kayan itatuwa, shikuma yana zubama inno shagwa6ar daya saba tana biye masa.
Masu jiran Galadima kuwa a airport saida sukaga kowa yagama fita ajirgi babushi sannan wani dogari yakira sarkin fada yake sanar dashi sufa basuga Galadima ba.
Sarkin fada yace 鈥測o kunacan kuna shashanci yaza'ayi Ku gansa, shi harma sun shige cikin gida da sarki 鈥?.
'yan uwansa ya sanarmawa suka tattaro suka dawo masarautar.馃ぃ
Dole a nan masarautar ya kwana, washe gari ya zagaya duka sashen sauran matan sarki ya gaidasu a mutunce. suma dai sunmasa tarbar mutunci kamar yanda suka saba, duk da dai taciki Na ciki. Sannan sai sassan iyayensa yayun momma da k'annenta, dukda dai bako ina yashigaba.
Yanzunma tare sukayi karin kumallo da maimartaba, sannan suka fita fada tare, da Galadima akayi fadanci yau, yana gefen adalin kakansa.
Washe gari da safe ya tattara inasa-inasa ya cane India, yabar tsofin da kewarsa, shima yatafi yana kewarsu.
********
Gwaggo Safiyya tacigaba da samun kulawa sosai, dukda dai tanad'an jin jiki, kullum matan gidanmu sukanzo sau d'aya, muma dai makaranta tasa bama yini a asibitin, amma kullum da safe mukanzo mu kuma dawo da yamma.
Matan gidanmu kam jarabar innaro tasakasu k'ok'arin zuwa kullum, dan tace wlhy duk Wanda bata zuwa saitayi Dana sanin saninta.
Wannan furuci ya d'an tsoratasu, dan kowa agidan yasan wacece innaro, idan kaga mutuncinku ya d'ore to kana cinna mata 'yan canji ta k'ark'ashin k'asane馃檴, amma kana hanata gobe bazai hana ta karta maka rashin m ba馃ぃ. (Ho innaro mu ta mutunci馃じ馃徎鈥嶁檧, ina yinki over ginbiyar Malam faruku馃槣馃檴)
鉀桂煆烩€嶁檧
Abin yafara tsoratani ganin har sati 1 dayin maganarmu dasu Galadima amma babuko labarinsu, tun ina saran yau gobe har na daina lissafin ma, ganin zan saka kaina a damuwa nacirema zancen a raina gaba d'aya, domin Na gama fahimtar maganar Galadima da abokinsa k'aryace, maybe ma mafarki nayi naketa shirmena kawai.
A tsaitsaye damuwa tafara ramar dani a tsaye, sai idanuwa da dogon hanci.
Tun ina daurewa har Abu yaso yaci tura, ciwon kai Dana k'irji suka fara zama abokaina.
Ranar data kama sati biyu cif saiga bak'i su Abba sunyi, babu Wanda yasan daga ina suke, kuma su Abba basuma kowa bayanin komaiba dangane da bak'in. saida sukayi kwanaki uku da zuwa sannan naji wai wanine yakawo kud'in aurena yana son abama d'ansa.
Lamarin yabama kowa mamaki, nanfa 'yan gidanmu suka hau dariyar mugunta wai kwantai dai ya tabbata kenan.
Gugar zanar dasuke tayine ya fusata innarmu, tasakama Abba kuka akan bata aminceba, yaza'ayi su d'auki aurena subama mutumin dabasu saniba, idan su sun gaji dani itafa tanason kayarta.
Lallashi duniya Abba yayi dan innarmu ta fahimta amma Sam tak'i saurararsa, wannan ne karon farko da yaga tsantsar fushinta.
Yarasa yazai mata, dan shima lamarin Na damunsa, yarasa minene yasakashi amincewa yabada auren d'iyartasa ga mutanen?, shi dai kawai tsohon yamasa kwarjinine wlhy, dan jiyay ko kad'an bazai iya musa masaba. dukda talakawane kamarsa, harma yana ganin yafisu abubuwa da yawa.
Lamarifa yayi tsamari a d'an tsakaninnan a gidanmu, dan innarmu takasa kwantar da hankalinta, hakama abbanmu, yayinda 'yan gidanmu sukejin Dad'i kamar su had'a fati.
Nikuwa uwar gayya ai ba'a magana ma, nakira number Galadima yafi sau 200 amma tak'i shiga ko sau d'aya, lokaci guda nagama fita hayyacina, 'Yar uwata kanta dukta lalace kamar itace cikin matsalar.
Innaro kam ciwon gwaggo Safiyya ne ya d'auke hankalinta, duk da dai su Abba sun mata bayanin kawo kud'in nawa, amma cikin halin ko in kula tace su basu kawai, idan sun barni agidan kuwa najawo musu abin kunyar dayafi nabaya, harma tashafi sauran kannena suk'i auruwa tamkar ni.
Wannan furuci ya Sosa zuciyar abbanmu, amma saiya danne saboda girman mahaifiya.
An sallamo gwaggo Safiyya da kwana biyu jikina ya birkice nima, dole aka kwasheni aka kai asibiti.....
*********
A 6angaren sarki kuwa bayan tafiyar Galadima da kansa yazo masarautar gagara badau, an masa tarba ta girmamawa domin shid'in babban abokine ga kakansu Galadima wato (marigayi sarki Abubakar na lll).
Mama Fulani kanta in kunga yanda take girmama sarki (Abdul'fatah idris) saikusha mamaki Ku d'auka ba itace mai ji da kanta d'innanba da tsantsar nuna sarauta(gaba da gabanta yo馃ゴ).
Sarki bai 6ata lokaciba ya sanar musu abinda yazo dashi, ganin tsantsar farinciki nayi ga mafi yawan jama'ar gidan, dan hukuncin sarki Abdul'fatah yamusu dai-dai, koba komai an k'ask'antar da Galadima d'in, Wanda yadace ace an sama masa d'iyar wani mashahurin sarki ya aura, kodan sarautar da ake da yak'inin shine yakama ta ya gada.
Murmushi papi yayi, saboda ganin farinciki zancensa a fuskokin wasunsu, yasan tabbas dawata manufa suke wannan farinciki, amma hakan bai damesa ba, domin shi da k'yak'yk'yawar niyya yayi. maganar sarauta kuwa sune suke ganin bazai iyaba saida wata d'iyar babban sarki, amma shi yanada yak'inin ko d'iyar shugaban talakawan duniya koda baiwace agidan Galadima ya aura sarauta ta ALLAH Ce.
Daga baya ya tsara musu yanda yakeso Neman auren ya kasance, bawai zasuje musu da rigar mulki baneba, yanason suje amatsayin talakawa domin ganin tarbar dazasu samu daga iyayen yarinyar, daganan zai gwada yak'inin tarbiyar gidan da mutuncin iyayenta.
A masarautar sarki ya kwana, washe gari sukayi shigar talakawa shida sarki jalaludden k'anin mahaifin Galadima, sai wazirin papi dana sarki, saikuma k'annen mahaifin Galadima biyu sannan aka sami tsohuwar mota suka tafi aciki bisa jagorancin wani dogari da sarki yasa yamasa binciken gidansu munaya.
Abinda basuyi zatoba shi suka samu, domin tarba ta mutunci da girmamawa suka samu dagasu Abba, duk da suna kallonsu talakawa fitik harma da yak'inin sun fisu komai.
Hakan ya burge sarki Absul'fatah (papi) shi kansa sarki jalaludden lamarin ya masa dad'i. Sun bada kud'in gaisuwar farko data biyu naira subu 30 kacal.
Sai bayan tafiyarsu sannan su Abba sukaita mamakin kansu anya mutanen bada wani siddabaru sukazo musuba? Yazama ayi basu sansuba amma suzo su kar6i auren 'yarsu? sukuma su basu babu musu kamar sun gaji da ita. (Niko nace kwarjinin sarauta suka muku abba馃槣馃槀).
Can kuma dasu sarki suka tafi sunata yabawa suma, sarki Absul'fatah dad'i dukya gama cikasa, lallai Galadima yasamu tsatson daya dad'e yana masa fata da addu'ar samu.
Momma koda papi yakira yamata bayanin bataji komaiba, saima addu'a data masa da kuma nuna farin cikinta akan lamarin, koba komai zataga auren Galadiman ta, amma saida tayi hawaye data tuna za ayi auren Galadima babu mahaifinsa, kamar yanda akayi na Haneefa (Aunty Mimi).
Data sanarma Abie saiya fad'ad'a murmuahinsa, yayinda hawaye ke zirara ta gefen idanunsa, ALLAH sarki iko da falala, tun yaronsa na shekara 5 a duniya yake a wannan halin, gashi har zaiyi aure, yagodema ALLAH da wannan jarabawa shikam.
A satin papi yaje India ma da kansa, yaduba jikin Abie dakuma maganar auren Galadima dayayi musu, nanma saida Abie yay hawaye, amma sarki Absul'fatah yayta masa nasihar yawan hak'uri da kar6ar k'addara, ya nuna masa sunada yak'inin zaici ribar can.
Abie yana son surukinsa kuma aminin mahaifinsa sosai, dan duk lokacin dazaizo dubashi da irin salon nasihar dazai masa wadda zai k'ara tasirantar da imani a zuciyarsa.
Galadima kuwa sai wani basarwa yakeyi irin shifa abin bai d'ad'ashi da k'asaba, kuma bayason abin, aurenma dole za ai masa, haka yaytaima Abie korafi yana shagwa6a.
Murmushi Abie yay tayi yana lallaahinsa da idanun.
Cikin tsokana sauban dake d'ayan gefen Abie shima yace 鈥測aa Sam to kawai ni abani kana, kaga na huta da zuwa tad'i k'ofar gidan kowa鈥?.
Wata uwar harara Galadima ya maka masa, wadda tasaka Momma da auty Mimi da samha da jakadiya dariya, shi kansa Abie murmushine ya fad'ad'a afuskarsa.............鉁嶐煆?
Wannan shine yafaru 6angaren Galadima munaya bata saniba.
Guys kuje zuwa kawai, k'ila zuwa dare kujini da bonus鉀桂煆烩€嶁檧鉀桂煆烩€嶁檧
ALLAH yabama munaya lafiya.
Barka da juma'a.馃槃鉁嬸煆?
0 comments:
Post a Comment