...........Bansan yanda zan musalta muku farin cikin damuka tsinci kanmuba nida 'yar uwata Munubiya, abin kawai ba'a magana.
Duk da bata yarda zan zo d'inba amma bata fasa tanadar min duk abinda tasan inasoba, tarasa inda zata sakani dan dad'i, gaskiya gidan munu yayi k'yau sosai, gashi an cika ko ina da kaya, kasancewar harda nawa aka had'a mata, muna yin salla muka 6arke da hirar yaushe gamo, a haka yaa marwan yazo ya samemu, yaukam abin mamaki naga fara'a a fuskarsa, nace lallai aure yayi citta kenan, yanda yake bama Munubiya kulawa sai abin ya birgeni, kamar Na lashesu kuwa Dan dad'i. Haka muka yini muna tad'i har lokacin sallar la'asar yafita salla.
A lokacinne aunty Salamah tazo gidan, Ashe Munubiya ce takirata ta fad'a mata zamu tafi India yau da daddare, mun tarbeta da murna sosai, yayinda ita kuma taketa yaba wai munyi k'yau. mukaita rufe fuska alamar kunya.
Shawarwari taita bamu akan rayuwar aure da yanda zamu tattali mazanmu, babu ko kunya take 6aro mana komai, sai mune muketa sunkuy da kai, itakam ko a jikinta, ta rarraba mana wasu buks da ke d'auke da abubuwa masu amfani dazasu bada gudunmawa a zaman takewar aure, nidai bawai na d'auki nawa da muhimmanci baneba.
Wajen 5 tatafi, tafiyarta babu dad'ewa saiga Galadima da yaa marwan sun shigo, Ashe wai ya dad'e a k'ofar gida zaune, ya kira yaa marwan yace baya gida amma gashinan zuwa.
Shine yajirashi amota harya iso suka shigo tare. Sun gaisa da Munubiya a mutunce, ta shirya musu abinci, da yace yagode sauri yakeyi, amma munu ta marairaice wai yaza'ayi mijin 'Yar uwarta yak'i cin abincin gidanta, in baimasa baneba ta sake masa.
Murmushi yayi ya zauna yaci kad'an, yayinda mukuma muka shiga d'aki dan mu basu waje suci abincin, d'an kuskus d'inmu mukayi muma, takuma kwantar min da hankali akan auren nawa da wasu 'yan shawarwari, da nunamin fushinta akan abinda nace nama Galadima d'in, ta nunamin wannan ba tarbiyyar da iyayenmu suka bamu baneba, gaskiya karna sake irin haka, kuma nabashi hak'uri akan hakan, nace “to amma tayaya zan basa hakurin?”.
'Yar takarda ta d'auka tayi rubutun tabani wai nabashi.
Na kar6ane kawai badan ina tunanin zan bayar d'inba, duk da nasiharta ta shigine gaskiya, kuma nima tun a ranar nayi nadamar ce masa azzalumin gaskiya, Duk da nasan a cikin fushine Nima Na fad'a, Dan nashiga rud'ani sosai akan abinda yayimin daban zataba.
tabani kayan da aunty salamah takawo a Leda, batareda na dubaba na amsa.
Itama k'yauta mai tsoka yamata sannan muka fito, nida ita kowa yana sharar kwalla, bamason rabuwa da juna, amma yazamuyi? aure ya rabamu.
Daga nan gz yaa marwan muka nufa gaida mama rabi'a, namayi mamakin yanda yasanta, nankam tare muka shiga, su Ayusher suka rukunkumeni cikin tsantsar farinciki da kewa.
Bamu dad'e sosaiba itama ya ajiye mata alkairi muka fito, su Feena ma yabasu kud'i wai su sai kayan kwalliya, hakama Ahmad, yaa Fadeel dai mun tarar baya nan, yakoma inda yake bautar k'asa.
Nanma saida nayi kuka dazamu taho.
Saida muka shiga mota ina sharar hawaye sannan ya kalleni cikeda k'asaita yana ta6e baki, “ke wai bak'ya tsoron hawayenki su k'are ne?”.
Bance masa komaiba nacigaba da kukana, shima saiya shareni.
★★★***★★★
Koda muka isa Masarauta bamu wuce sashenmu kai tsaye ba, wasu 6angarorin gidan mukaje mukai musu sallama, harda sashen mama Fulani, yauma dai babu magana mai dad'i tsakaninta da Galadima, nifa lamarin nasu na d'aure kaina gaskiya.
Mai martaba kam munsha addu'a a wajensa, sannan muka fito.
Mun shiga sashenmu ana kiran sallar magriba, zan shige yace “kiyi azamar shirya kayanki trolley d'aya, karki wani kwashi kaya dayawa”.
Da to kawai na amsa nayi shigewata ciki.
*_7:30pm_* Muka bar masarautar, nida shi da Samha motarmu d'aya, muna baya tana gaba.
d'ayar motar kuma Sauban da aunty Mimi da khaleel ne aciki.
Mun sami rakkiyar Harun da Muftahu sai wasu k'alilan daga masarautar.
Tom nidai ba k'auyace a airport, dan banta6a shiga jirgiba, amma kunsan mutuniyar taku da Jan aji,? saina Fiske abina nima inajan citta tamkar wadda ta saba.
Duk abinda yadace ayi anyi mana, musamman ma ni danake sabuwar fita k'asar, harun yad'an sha cukuniya a kaina tunda rana.
9pm dai-dai jirginmu ya shilla a gajimare???.
Lokacin da akace asaka belt ban sakaba, sai shine ya jawo yasakamin batareda yace uffanba, yana jikin window nikuma ina gefensa, sai bayan mu khaleel da Samha, can baya kuma aunty Mimi da Sauban.
Ina lafe jikin kujera, yayinda shima yake kwance ya jingina bayansa, wani English novel ne a hannunsa yana karantawa, dama tun amota yake rik'e da kayansa.
Da akazo tambayarmu mi muke buk'ata Coffee kawai yace yacigaba da karatunsa, nima ta tambayeni saina girgiza mata kai alamar bana buk'atar komai.
Janye book d'in yayi yana kallona, saikuma ya janye ya maida kanta, harta bar wajen ya kirata, yace takawo min abinda su Samha sukace sunaso.
Bance komaiba nidai, shima saiya cigaba da karatunsa.
(*************)
Alhmdllh mun sauka kasar India, k'asar da nake gani a films, abin mamaki sainaga dogarawa ne sukazo tarbarmu, saikuma Akash dawani danaji Galadima yakira da beejay.
Bamu 6ata lokaciba mukabar airport d'in, a nawa tunanin sainaga rayuwar tasu kamar dai tamuce gaskiya, saidai banbancin sutura zuwa wasu mu'amullat haka, mutane sunata hidimarsu da kai kawo hankali kwance.
Masha ALLAH na fad'a yayinda muka isa gidan danake k'yautata zaton nasu Galadima ne. gidan kam yamin k'yau gaskiya, su beejay basu shigaba suna saukemu suka juya, mune muka Shiga hannuna aunty Mimi tarik'e, yayinda su Samha suke agaba.
Galadima kam mun barsa a harabar gidan yana waya.
Ai kaina bai gama kwancewa ba saida muka shiga falon gidan, hummm manyan k'asarmu sunajin dad'insu gaskiya, yo kanada irin wannan gidan a k'asar daba takaba to k'asarka kumafa?.
A falo muka zube bayi suka Shiga hidima damu, muna zaune a wajen Galadima yashigo, shima zaman yayi ya aza k'afa d'aya bisa d'aya, Sauban yazuba ruwa a cup yabashi, kar6a yay yana fad'in “thanks”.
Ya kalli baiwar datake shirya abinci daga can gefenmu, “k zonan”.
Da sairi ta ajiye spoons d'in hannunta tanufo inda muke, agabansa ta zube tace “gani ranka ya dad'e”.
“kisamu wata ta tayaki Ku gyara d'akin can nakusada Samha yanzun nan”.
“angama ranka ya dad'e”. tayi maganar cikeda tdantsar ladabi.
Aunty Mimi Na najinsa batace uffanba. Shigowar momma tasaka khaleel tashi da gudu yaje ya tarbota, itama Samha zuwata ta kwakwameta, tunkan ma afad'amin nagane mahaifiyarsu Galadima ce, koda yanda fuskar kowannensu ta washe da farincikin ganin juna.
Hankalinta Na kaina tana murmushi da fad'in “oyoyo d'iyata”.
Zamowa nayi daga kujerar na durk'usa har k'asa ina gaisheta, ta k'araso inda nake ta kama hannuna ta tadani nakoma saman kujerar, “zauna kinji, sannunku da zuwa, kinsha hanya ko?”.
Murmushi nayi ina duk'ar da kaina.
Galadima yace “wai Momma dan ALLAH duk baki ganmu baneba?”.
Kallonsa tayi cikin Hararar wasa, tace, “yo naganku bata taku nakeba”.
Su aunty Mimi dariya suka Sanya, yayinda Galadima yad'an 6ata rai yana fad'in “da tsohuwar Zuma dai ake Magani Momma”.
“a fad'arka ba, amma sabuwa ma aitafi aiki da dad'i”.
Nidai murmushi nakeyi, Dan wasan nasu ya burgeni, inason ganin family haka cikin farinciki, gaskiya sai sunfi jin dad'in zaman nan fiyema da masarautar sun can.
Gaishe-gaishe aka shigayi, kowa yana k'ok'arin bama Momma labarin yanda biki ya kasance, sai dad'i takeji da sanya albarka, nidai nida Galadima babu mai cewa komai.
Mik'ewa Galadima yayi, “bara nad'an watsa ruwa Momma”.
“to afito lafiya Muh'd”. ta kalleni nima, “d'iyata tashi kibi mijinki kiyi wanka kuzo ga abinci”.
Harya fara tafiya saiya tsaya, juyiwa yayi yana mata magana a yaren daban saniba.
Ta galla masa harara da masa dak'uwa, itama bansan mitace masaba. naga dai ya tura baki yaci gaba da tafiyarsa. ita kuma tace natashi naje.
(Wai ashe cayay mata ai yasa a gyaramin d'akin da zan zauna, shine tamasa dak'uwa tana cewa d'akin safa?, shi idan ance Araba mana d'aki saiya amince?, to tare zamu zauna, shine yakuma cewa ammafa d'akinsa ai ba kowa ke shigaba, tace tasani aii, muje nima sirrinsace ai, shinefa ya tura baki gaba).
Kamar an maken k'afafu haka nabisa abaya muna taka steps d'in benen, har muka isa k'aramin falo mai k'yau, komai farine a wajen, TV ce kawai takasance bak'a.
Falon yad'anyi k'ura alamun ba'a gyaraba (babu mai aikin dake hawa samansa, gashi kuma sunyi tafiya suduka, Momma kuma batada time d'in gyara masa d'aki).
Guntun tsaki yaja yana yamutsa fuska, d'an zaman danayi dashi na fuskanci bayason k'azanta komin k'ank'antar datti yata yamutse fuka kenan, bamu tsaya ananba muka shiga bedroom d'in bayan yabud'e, mayataccen k'amshinsa yana manne da d'akin, sai dai nan d'inma yayi k'ura, waya yazaro yayi kira, ashe Samha yakira, yace “k zoki gyaramin d'aki”.
Bai jira cewarta ba ya yanke wayar.
Bance masa uffanba nima nataka nawucesa, bina yayi da kallo dan yaga ina zanje?.
Zanin gadon na yaye duka, nacire rigar filaluwan tareda rumfar da akama gadon, shidai kallona kawai yakeyi, yana tsaye jingine da bango (baiyi tunanin zance zan gyaraba).
Knocking d'in da akayine yabada izinin shigowa, Samha ce d'auke da kayan tsintsiya, ta zubesu a k'asa tana fad'in “aunty kibarsa zan gyara”.
Kaina na girgiza nace “barshi Samha, nunamin kawai yanda zanyi, kije kema ki huta”.
Nunamin komai tayi, har inda bedsheets suke, tafice a d'arare da zaton Galadima zai hanata yace takoma ta gyara.
Amma saitaji baice komaiba, yama kauda kansa gefe kamar baisan munayiba.
Bathroom nashiga, nazage sosai na tsaftaceshi, Dana k'urarce kawai, duk abinda zaisa toilet k'amshi da tsafta nasakashi, saida naganshi need sannan nafito, ban iskeshi a d'akinba, Dan haka hankali kwance Nagyara bedroom d'inma nagama, nasaka kamshi sosai. falon nafito danufi gyarawa, sainaga Samha harta gama itama tana saka air fresheners masu dad'in k'amshi, da turaren wuta irin namu na gargajiya.
Sannu da aiki namata, itama tamin, Galadima yafito daga wata k'ofa yawucemu batareda ya tankaba, bedroom d'in yakoma.
Kallon Samha nayi nace, “saura wannan d'akin daya fito cikin ko?”.
“ai Aunty wannan d'akin dakansa yake gyarawa, babu mai shigarsa duk gidannan inba Momma da Mummy na da shiba”.
Cikin mamaki nace “miya sa to?”.
“d'akin sirrinsa ne aunty”.
Ban fahimci maganarba, bankuma tambayeta ba, ta tattara kayan damukayi amfani dasu tafice tana fad'in “aunty bara naje nayi wanka, dama wankan zanyi yakirani”.
Kaina kawai na iya d'aga mata, saman kujerar na zauna shiru ina nazarin maganarta, miye kuma ma'anar d'akin sirri? nashiga k'ololuwar nazari banyi zaton time yawuce hakaba, k'afata yad'an shura, nad'ago idona ad'an firgice na kallesa, haryayi wankan yana sanye cikin jajayen kaya na Adidas, sun masa k'yau sosai.
Juyawa yay zai sauka k'asa yana fad'in “kitashi kije kiyi wanka”.
Bai jira cewata ba ya sauka.
Nima saina tashi nayi yanda yace, d'akinsa sosai ya had'u gaskiya, harma bansan Yaya zan fasalta mukuba, nasan farin Abu namai tsaftane, lallai yanada tsafta, daga bedroom parlour zuwa bathroom nashi komai farine, bedroom d'inne kawai keda d'an sirkin Golden kad'an-kad'an shima.
Nidai ina wanka da d'unbin tunani, haka kawai naji kwad'ayin son Shiga d'akin sirrin nasa.
Koda na fito saina saka zani da riga na atanfa, ban shafa komaiba na d'auki turarensa na saka saboda neman magana?. ina tsaka da saka turaren Samha tashigo kirana.
Ajiyewa nayi na d'auki gyale nabi bayanta.
Falon k'asa muka sakko, inda aka shirya abincin saman wata lallausar darduma, duk suna a zaune har Momma, kusada Galadima daketa cin abincinsa ko kallon mutane bayayi Aunty Mimi ta nunamin wai na zauna.
Kamar nafasa kuka haka naji, Sauban dake gefen haggunsa yace, “auntynmu har yanzu amarcin bai k'are bane? kin shige d'aki kinyi bulum”.
Murmushi kawai nayi na k'asa ce masa komai, dan yabani kunya gaskiya, nakula kuma yanada yawan tsokana, aunty Mimi kam dariya tayi, yayinda Samha tarufe baki tanayin tata.
Momma tamasa dak'uwa, “o kai Sauban ALLAH ya shiryeka, kowama bazaka d'agama k'afaba?”.
Dariya ya kumayi yana satar kallon Galadima dayay tamkar baya wajen, yace “to ai gaskiya nafad'a Momma. dan ALLAH aunty ba haka bane?”.
“gaskiyarka fa Sauban”. Aunty Mimi ta fad'a tana dariya.
Momma tace “barsu kinji my daughter, ci abincinki”.
Kai na jinjina mata cikeda kunya.
Galadima dai har yanzu baice k'alaba, baima d'ago ya kallemu ba.
Haka muka ci abincin nidai duk a takure nake, kamar yanda yafara cin abinci haka yarigamu kammalawa, tashi yay yabar wajen, yakoma can saman wasu kujeru guda biyu ya zauna, laptop d'in dake saman table d'in wajen ya d'auka ya kunna, da alama shiya ajiye kayansa.
Bayan mun gama duk muka mik'e, kowa ya hau shirin zuwa asibiti duba Abie, time d'in barcin sane shiyyasa ma Momma tasamu tataho, jakadiya kawai aka bari a wajen, itama a waje, da yake in time d'in barcinsa yayi kowa fitowa yake daga d'akin a barsa shi kad'ai.
Galadima saboda aikin da yakeyi yace muyi gaba shima zai taho.
Momma tace “to matarka ta zauna ta jiraka, mudai mun tafi”.
Kamar zaiyi magana saikuma yayi shiru, cigaba yayi da aikinsa harsuka fice, jinai kamar nace nidai zan bisu kawai. Amma na makaro, dan harma sun fice abinsu.
Ganinai tsayuwa ta isheni, shikuma d'an latsin baice na zauna ba, sai kawai naje na zauna d'ayar kujerar dake kallon tasa, nima na d'ora k'afa d'aya kan d'aya tamkar yanda yayi. nayi gefe da kaina cikin basarwa.
Daina danna System d'in yayi, ya d'ago idanu yana kallona, yayinda yake Murza hannunsa na haggu daya d'ora guywar a hannun kujera hannun yana sama, yinai tamkarma bansan yana kallona ba kwata-kwata.
cije lips d'insa yayi kad'an, ya janye idonsa ya maida ga system d'in, aransa yana mamakin izzar yarinyarnan, tabbas data fito gidan sarauta da anga mulkin tsiya.
Falon shiru babu kowa, tunda kuyangin suka gama hidimarsu duk suka koma 6angarensu dake can baya.
Kusan mintuna 40 yagama abinda yakeyi, laptop d'in ya kashe sannan ya mik'e, batare da ya kalleni ba yace “muje”.
Saida na d'an ja wasu seconds sannan na mik'e, saidama ya juyo ya kalleni, dan har yakai k'ofar fita.
Gyalena na maida saman kai nabiyo bayansa, a k'ofa na iskeshi tsaye, na fito shikuma ya daddana wasu madannai agefen k'ofar, Ashe wai security yasaka.
Ranar farko danaga yayi tuk'i da kansa, dogarin dasuke gate suka bud'e mana muka fice.
Tunda muka tafi ba Wanda yayma wani magana, shi yanata deriving d'insa nikam ina kalle-kalle abuna, mun Isa katafaren asibiti mai k'yawun gaske, inma badan sunanba da saika d'auka wani wajen shak'atawa ne, asibitin ya had'u gaskiya, har ciki muka shiga bayan security sun mana 'yan tambayoyi dakuma gaisawa da sukayi, naga alamar sun sanshi sosai, amma duk da haka saida akai searching d'inmu.
Abin ya birgeni gaskiya, inda aka tanada domin parking ya tsaya, ya kashe motar sannan muka fito kusan a atare, bai tafiba saida na zagayo, muka jera zuwa ciki, yanata gaisuwa da jama'a, ina mamakin yanda ya iya yarurrukansu, nikam dai saidai da turanci nake gaishesu, kuma ba kowaba.
Mun fara zuwa office d'in wani doctor, suka d'an tattauna akan cigaban da aka samu na jikin Abie, mun gaisa dashi yaymana murnar aure, murmushi kawai nayi, sai Galadima ne ya amsa masa.
Daga nan muka shiga d'akin da Abie yake jiyya, iyalansa su aunty Mimi duk suna zagaye dashi, nidai a raina danaga d'akin nace oni kamar ba Asibitiba?.
Tunda muka shigo fuskar dattijon dake kwance a gadon ta fad'ad'a da murmushi, kallo d'aya namasa naga kamanninsa dana hoton d'akin Galadima na Nigeria.
Gabansa muka k'arasa, Galadima ya durk'usa yarik'o hannunsa, nima saina durk'usa ina gaidashi da Hausa.
Momma ce tazo ta kamani na tashi, cikin wani yanayi tace, “d'iyata ai Abban naku baya iya magana kinji”.
Da sauri na kallesa, ya sakarmin murmushi, sai kawai na mayar masa hawaye nabin kumatuna domin tausayi, duk kallona sukeyi sukam, harda Galadima.
Kuma zamewa nayi na durk'usa a gaban gadon, cikin rawar murya nafara jera masa addu'ar samun sauk'i wajen ubangiji. duk suna amsamin da amin.
Murmushi yakasa barin face d'in dattijon, Wanda k'aunata take shigarsa har zuciyarsa, Momma takuma d'agoni a karo na biyu ta rungume tana lallashina.
Galadima ya had'iye hawayen dake Neman zubo masa shima, yafara gaida Abie dake murmushi, da ido ya nuna masani wai ya lallasheni mana.
Sai Galadima yayi murmushin jin kunya yana susar k'eya.
Murmushi Abie yayi sosai, har hakwaransa na bayyana.
Ban ta6a jin tausayin Galadima ba sai yau, dama haka suke cikin tashin hankali? Lallai dan ba'aga dariya a fuskarsa ba ba laifi baneba, nama yabama k'ok'arinsa yanda yake zirga-zirga tsakanin Nigeria da nan d'in.
Ahaka akaita firar dani bana fahimta, danshi Abie da idanu yake maganar.
Bamu baro asibitinba sai dare sosai, a can mukayi salloli dacin abinci.
Mun taho muka baro Momma a can, jakadiya ma ta biyomu, dama Momma kad'ai ke kwana a wajensa, shima ba kullumba, dan wasu ranakun basa bari a kwana dashi, a sati sau uku take kwana a wajensa.
**********
Tunda muka baro asibitin tsohonnan ketamin yawo a zuciya da ruhi, sai cud'awa nake da kwancewa, inason jin labarin masarautar su Galadima gaskiya.
Yanzun ma iza k'eyarmu aunty Mimi tayi muka wuce d'akinsa, muna zuwa bathroom yashiga, kusan mintina 25 saigashi yafito, da Alama wanka yayi, harya sauyo kayan barci aciki, dama da abinsa yashiga.
Nima tashi nayi nashiga da nawa masu kauri a hannu. Wankan nayi da shirin barci, sannan nasako hijjab na fito.
Saman gado na iskeshi yawani barbaje a tsakiya, alamar baya buk'atar wani ya hau.
Na ta6e bakina, a raina nace koma bakayi hakaba ai bazan ta6a had'a makwanci da kaiba, aikin banza kawai, naja tsaki a zuciyata.
Saman sofar d'akin na hau na kwanta, inata tunanin Abie da ma tsalarsa.
Kasa daurewa nayi, na kallesa nace, “ wai miye matsalar Abie (kamar yanda naji suna fad'a)”.
Shiru yamin, harma na zata yayi barci, sai can yacemin “ciwone dai kawai”. daga haka yaja bakinsa yay shiru.
Nima shirin nayi, dan bakuma nida abin fad'a, musamman yanda yabani amsar.
Nidai zan iya cewa barcina na daren ranar rabi da rabine, kewar 'yan uwana da bak'unta, gakuma matsalar babansu Galadima data k'asa Barin zuciyata.
Da asuba narigashi tashima, na fito toilet bayan gama d'aura alwala na iskeshi zaune bakin gado dafe da kai, k'ala bance masaba nad'au abin salla na shinfid'a, tashi yayi ya shiga bayin yana Jan tsaki a zuciyarsa, Shifa wlhy dukya takura, yasaba zamansa shikad'ai a d'akinsa, yanzu duk anzo an cika masa?.
Haryaje k'ofar toilet d'in yadawo baya, doguwar riga ya d'auka ya shige, saida yay wanka da brush sannan yayo alwala yafito sanye cikin jallabiya blue.
Turare yad'an fesa sannan ya d'au key d'in mota yafita, Ashe inda yake zuwa sallan can gaban gidanne, kuma daga sallar asuba yake wucewa asibiti ya kar6i Momma tataho gida itakuma, duk ranar weekend haka yakeyi, yanzu kuwa yana cikin hutune.
Da yake ina sallah yafita, banyi zaton yafita kenanba, bayan na idar saina d'an kwanta, maganar d'akin sirrinsa ce taita cin zuciyata, namik'e nafita, saida na lek'a falon k'asa naga babu kowa sannan nadawo, cikin tantama na murd'a k'ofar d'akin, sai naga ta bud'e, banyi zaton hakaba gaskiya, musamman danaji an kira d'akin dana sirri. (bakisan ya manta bane bai rufeba Munaya? dan harda security a d'akin).
'Dakin k'aramine bashida wani girma, gaba d'aya bangon d'akin zagaye yake da hotuna, sai Computers guda hud'u da kuje d'aya gabanta akwai deck's babba, wanda duk Computers d'in akansa suke, sai pens da yawa cikin wani d'an Abu, gefe kuma k'aramar loka Ce ta glass cikeda takardu, gakuma tarin wasu takardun kashi-kashi da akayi kamar files a seman decks d'in, matsawa nayi jikin bangon nafara kallon picture's d'in, hotunan mutanene daban-daban, harda wasu manya dana Sani a TV, mafi yawa yayi rubutu a k'asan kowanne photo, bana fahimtar rubutun gaskiya, danhaka nacigaba da kallon picture's d'in kawai, harda na mama Fulani,?
?
Kutu melesi hotona fa jama'a a d'akin sirri, naga idi, nakaranta rubuntun k'asan yafi sau goma ban fahimci komaiba, saiwasu lissafi-lissafi kamar mai rubutun Mathematics?.
Na Muftahu nagani a k'arshe, abinfa ya d'aure minkai, mu kuma ni da amininsa Muftahu miya kawomu d'akin sirri???.
Agogon d'akin na kalla naga 7am tayi, da sauri nafita gudun karya zo ya sameni.
Na rufe k'ofar a hankali nakoma bedroom d'insa, ajiyar zuciyata na sauke ganin bai dawoba.
Zama nayi na zabga tagumi ina tunanin ma'anar wad'ancan pictures d'in dana gani, danma a tsorace nake, ban nutsu tsaf naganiba???♀.
Ban sauka k'asaba saida 9am tayi agogon k'asar, na iske su Samha suna breakfast, harda Momma, na durk'usa har k'asa na gaidasu itada aunty Mimi, cikeda fara'a suka amsa.
Momma tace “ai nayi zaton barci kike, shiyyasa na hana a tadoki”.
Cikeda kunya nace “a'a na tashi tun d'azun”.
Aunty Mimi ta zaunar dani kusada ita, Sauban ya had'omin komai na breakfast d'in.
Yanzun ma a kunyace naci abincin, kunyata na burge Momma sosai.
Bayan mun kammalane Momma ta kama hannuna muka shiga d'akin ta, a bakin gado ta zaunar dani itama ta zauna, anutse ta kira sunana.
Hakan yasani maida hankalina a kanta nima dan nakula magana mai muhimmanci zamuyi da ita............??
*_tofa, mi Momma zata fad'ama Munaya kuma?._*?
*_Ya ALLAH ka gafartama Iyayenmu???_*
[5/3, 4:28 PM] ? M B A ?: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??2?9?
...........“Munaya taimakona nakeson kiyi akan mijinki”.
'Dagowa nayi na kalleta cikin tsantsar mamaki, saina sinne kaina alamar jin kunyar ta, nace “Umarni zaki bami Momma, domin ke mahaifiyatace”.
Murmushin jin dad'i tayi kamfin takamo hannuna cikin nata, “Alhmdllh Munaya, nagode da wannan karamci naki, yanzu nakuma aminta Muh'd yasamu irin macen danake musu addu'a shida d'an uwansa, ALLAH yayi miki albarka. nasan dukkanin yanda aurenku ya gudana”.
Gabana yafad'i, a raina nace badai Na yarjejeniyar ba?.......maganarta ta katsemin tunanin.
“Mahaifina Sarki Abdul'fatah shine yasakashi aurenki saboda abinda yafaru daku, Wanda nasan k'addarar Muh'd ce kawai tashigo dake cikin lamarin. Kafin nafara neman alfarmar zan fara baki tarihin masarautar su Muh'd, da dalilin zamanmu wannan k'asar daba tamuba tsawon shekara 24 kenan”.
Kaina na jin jina mata, nace “to Momma”.
Zamanta ta gyara sosai yanda zataji dad'in fad'ar abinda ke a bakinta.
*_MASARAUTAR GAGARA BADAU A WASU SHEKARU DASUKA SHU'DE?_*
Masarautar gagara badau masarautace mai d'unbin tarihi, da mulkinta ya gudana hannun sarakuna masu yawa, a hasashen masana masarautar sarakuna a k'ala 51 ne suka mulketa harda Sarki na yanzu, wato *Sarki jalaludden Abubakar*.
Sunan masarautar awani shud'ad'd'en lokaci ba *gagara badau* ake kirantaba.
Tasamo sunan gagara badaune dalilin wani Sarki daya mulki masarautar a zamani mai shud'ewa.
Abaya mulkin masarautar basai ka mutuba yake barin hannunka, a'a, da zarar anyi yak'i kayi sakakin da aka ci masarautar tom dolenefa kayi murabus a nad'a wani kuma. kuma bawai cikin 'ya'yankaba, saidai asamo wani hazik'i a masarautar a nad'ashi sarautar.
Tom alokacin Sarki Hameesu Alasan sai aka kawowa masarautar wani gagarumin hari dayaso girgizata. Sarki Hameesu yanada wani d'a da ake kira da suna *Barde* amma asalin sunansa shine Salisu. lokacin da aka kawo musu harinnan ba'a cikin shiri sukeba, amma haka Salisu barde yay saurin had'a mayak'a suka tunkari wannan runduna, bak'aramin gumurzu akashaba, sojojin masarautar Sarki Hameesu duk sun salwanta, amma hakan bai tsorata Salisu ba, yacigaba da bata kashi shida wasu 'yan tsirarun mayak'a, ALLAH mai iko saigasu sunci wannan runduna data kawo musu hari.
Wannan nasara da Salisu yasamuce tasaka babansa Sarki hameesu sauka a kujerarsa aka nad'a salisu. tundaga ranar takoma *_MASARAUTAR GAGARA BADAU_* abin nufi annan salisu barde yazama gagara badau.
Bayan Sarki Salisu gagara badau sarakuna kusan goma sunyi mulki kafin Sarki *_ABUBAKAR_* kakansu Muh'd kenan, mahaifin su takawa.
Shima ya gaji sarautarne a hannun mahaifinsa Yusufa.
Rana d'aya aka nad'a Abubakar Sarki shida amininsa d'an sarkin kan karofi yarima Abdul'fatah, mahaifin Abubakar Yusufu abokine ga Sarki idres na ll, dan haka rana d'aya suka yanke shawarar yin murabus suka nad'a 'ya'yansu.
Sannan aka d'aura musu aure kuma a ranar da matan da su Sarki Yusufu & Idres suka za6a musu.
Gimbiya Marawuyya (mama Fulani) d'iyace ga waziri Sama'ila k'anin Sarki idris, a masarautar Idrees kenan, Sarki idres bashida d'iya mace, dan haka ya d'auki mama Fulani d'iyar k'aninsa yabama Abubakar d'an Sarki Yusufu a masarautar gagara badau, shikuma Sarki Yusufu ya d'auki Khadeeja (inno) yabama Abdul'fatah d'an Sarki idres.
To Ashe ita gimbiya Marayuyya (mama fulani) tana masifar son yarima Abdul'fatah ne, kuma yasani, amma ya nuna mata shi dama gimbiya Khadija (inno) k'anwar abokinsa Abubakar yakeso.
Tun daga lokacin gimbiya Marayuyya (mama Fulani) ta tsani Khadija (inno), ko wani Abu yahad'a masarautunsu bata mata magana, sai zagi da habaici.
Sukuma iyaye basusan gimbiya Marayuyya nason yarima Abdul'fatah ba, sukayi wannan had'in aure. (Iyayen mama Fulani ma sunso ta Auri yarima Abdul'fatah d'in domin sarauta ta dawo tasu)
Gidan sarauta idan an shata layi babu mai k'etarashi, dan haka gimbiya Marayuyya da iyayen ta dolen suka hak'ura da auren yarima Abubakar (tunda acanma suna saka ran gadar sarautar) haka aka kawota gagara badau. ita kuma Khadija (inno) aka kaita masarautar su Mama fulani.
Kusan atare duk suka haihu, saidai Khadija (inno) namiji ta Haifa, yayinda Marayuyya (mama Fulani) ta Haifa mace.
Duk da ba masarauta d'aya sukeba hakan yasaka mama Fulani bak'in ciki, dan aganinta inno taje zata gaje musu masarauta, ita kuma bata samu damar gaje tasuba. A haihuwa ta biyu kuma sai inno ta Haifa mace, mama Fulani kuma ta Haifa namiji. Alokacin kuma duk mazajen nasu suka k'ara aure, daga Sarki Abubakar har Sarki Abdul'fatah. kamar atsare haka sukaita kuma aure har suka cika mata hurhud'u.
A masarautar gagara badau Mama Fulani na zuba mulkinta a masarautar, yanda kasan itace sarkin, dayake shi Sarki Abubakar yanada hak'uri da sauk'in kai.
Humm matan Sarki Abubakar duk basu haihuba, sai mama Fulani keta zubo 'ya'ya. Saikuma amaryar Sarki ta uku ta Haifa d'anta namiji, kusan tare da mama Fulani a haihuwa ta hud'u, duk da mama Fulani itace da manyan 'ya'ya mace 1 maza 2 hakan bai hanata shiga tashin hankaliba, saita shiga tsangwamar gimbiya bagobura da aibanta d'anta *Saifudden*, wani lokacin har shegantashi tayi, saida Sarki Abdul'fatah yazo har masarautar ya taka mata birki sannan.
Mama Fulani tasaka sauran matan Sarki Abubakar sun juyama gimbiya bagobura baya gaba d'aya, batada sakewa ko kad'an acikin gidan. Sarki Abubakar yasan komai dake faruwa a gidansa, amma saiyayi tamkar bai ganiba, bakuma Dan mama Fulani tafi k'arfinsa baneba, yadai zuba mata idanu kawai yaga iya gudun ruwanta.
Ahaka yaran suka taso, gimbiya bagobura ma bata sake haihuwa ba, sai mama Fulani ce takuma biyu, mace 1 da autanta namiji Hayatudden.
Saifudden da jalaludden sun tashine tamkar tagwaye, dukda Saifudden ya girmi jalaludden d'in dakusan 1? kuwa. danma mama Fulani na hana jalaludden sakewa da Saifudden ne. Kokuma Kamaludden da Shamsudeen suyita dukan Saifudden idan sun gansa tareda jalaludden d'in.
Ahaka Saifudden yatashi cikinsu a tsangwame har suka girma suka zama manya.
Saikuma wani Abu tashin hankali ya samu, a time d'in da mama Fulani ke ganin sarauta zata dawo wajen 'ya'yanta sai ubangiji ya nuna mata ikonsa.
Dan kuwa Shamsudeen da kamaludden sai sukayi had'arin jirgi zasuje umara duk suka rasu.
A time d'in a marine kawai ba a saka mama Fulani ba, amma hauka tuburan tafara a masarautar gagara badau. Saida aka had'a da addu'a sannan talafa, saita kullaci gimbiya bagobura, wai ita tama 'ya'yanta asiri suka mutu domin d'anta Saifudden yagaji sarauta.
Gimbiya bagobura zata tada hankalinta Sarki Abubakar yace tama kwantar da hankalinta.
Bayan mutuwar su Kamaludden babu dad'ewa aka had'a auren gimbiya Zakiyya d'iyar Sarki Abdul'fatah da Saifudden aure, shikuma lokacin Jalaludden da Rafi'atu d'iyar wani Sarki.
Aikam sai mama Fulani ta hau bala'i wai munafunci aka shirya. Babu Wanda yabi takanta akasha biki.
Gimbiya Zakiyya da gimbiya Rafi'atu kusan atare suka haihu a time d'in, gimbiya Zakkiya ta Haifa d'iyarta mace, saidai tana haihuwarta ko ganinta batayiba takoma ga ALLAH?.
Wannan shine silar aurena dana Saifudden.
Dan bayan rasuwar yayata gimbiya Zakiyya da kwana 7 aka d'aura min aure da yarima Saifudden, domin nacigaba da rainon abinda tabari.
Banason Yarima Saifudden, domin ina masa kallon *Mijin yayata* amma banida yanda zanyi, dole na aminta da auren domin yima iyayena biyyaya.
Nasha wahalar zama dashi, saboda shi hankalinsa yana kan yayata ne marigayiya, silar soyayyar danake nunama Habeefa (aunty Mimi) d'iyar da gimbiya Zakiyya tabarine ya siyamin soyayyar yarima Saifudden, a hankali har shak'uwa tafara shiga tsakanina dashi. Soyayar dayakema 'Yar uwata saita dawo kaina.
Sai daifa inashan wahalar mama Fulani, duk da kuwa itad'in (Gwaggona ce) tana amsa sunan k'anwar mahaifina, amma k'iyayyar datakema mahaifiyarmu gimbiya Khadija (inno) saita shafemu, duk da abaya tana ik'irarin son mahaifinmu Sarki Abdul'fatah kuwa. Kamar yanda yayata gimbiya Zakiyya tasha wahalarta a gidan nima hakane, saima tawa taso fin ta 'Yar uwata, bansan dalilintaba, wai Ashe dan ina tsananin kama da inno ne?.
“Ina fata dai kina fahimtata Munaya” ‘Momma tayi maganar tana kallona dana rabga tagumi inajin cakwakiyar masarauta.
Kaina na jinjina mata cikin damuwa.
Saitayi murmushi tacigaba da fad'in.
Mama Fulani taso d'iayarta ta farko gimbiya Mansura ta auri yayanmu yarima Abubakar, Wanda babanmu Sarki Abdul'fatah yayma amininsa takwara.
To saikuma hakan bata faruba, dan ita tata dabarar itada iyayenta, idan Yayana Yarima Abubakar ya auri gimbiya Mansura sarauta takoma hannunsu kenan, tunda yarima Abubakar shine magajin masarautar mu, kinga ai d'ansa ne zai gajesa kenan, idan tahad'a auren kuwa yazama jikanatane da masarautar nan gaba.
To saikuma tsarin nata bai yuwuba, saima nida yayata mukazo masarautar gagara badau tushen mahaifiyarmu mukayi kane-kane, gashi kowa yana Saran Saifudden shine zai gaji masarautar gagara badau alokacin, tunda manyan 'ya'yan Sarki Abubakar sun rasu, Saifudden kuma shine babba namiji a lokacin.
Shiyyasa takuma d'aukar karantsana ta d'aura mana muda gimbiya bagobura.
Bayan haihuwar Haneefa babu dad'ewa gimbiya bagobura ta rasu, rasuwar data gigita yarima Saifudden kenan da Sarki Abubakar har ma da jama'ar masarautar gagara badau, amma banda mama Fulani da sauran matan Sarki, dansu hakanma dad'i yamusu.
Sanadin rasuwar gimbiya bagobura Sarki Abubakar ya kwanta ciwo, sai yayi murabus yace a d'aura d'ansa Saifudden a madadinsa.
Wannan Abu yama kowa dad'i a masarautar, amma banda mama Fulani dakejin tamkar tamutu dan bak'in ciki.
Saidai batada yanda ta iya, tanaji tana gani yarima Saifudden yazama Sarkin masarautar gagara badau.
Alokacinne kuma akace dole ya k'ara aure, dan Sarki baya zama da mace d'aya, gashi kuma ni ban haihuba har lokacin.
A rana d'aya aka d'aurama Sarki Saifudden aure da mata biyu. Nanfa mama Fulani tashiga jansu ajiki wai dan a kuntatamin, tana kuma koya musu yanda zasu kuntatama shi Kansa Saifudden d'in.
Sarki Saifudden nada shekara 9 a karagar mulki ALLAH yayma Sarki Abubakar rasuwa, mutuwarnan ta girgiza mahaifinmu Sarki Abdul'fatah sosai, dan saida aka had'a masa a addu'a.
Tun daga wannan lokacin masarautar gagara badau takoma hannun mama Fulani, dan sai yanda tace tanaso Sarki Saifudden zaiyi, dayake shi mutumne mai sanyin hali, baya ta6a sa6a mata.
Duk da haka wannan bai ishetaba, hattada yanda za'a gudanar da mulki saita tsara.
Har lokacin amaren Sarki Saifudden babu wacce ta haihu.
Cikin ikon ALLAH sai gani da ciki, babu kitumurmurar daba aima cikinnan nawaba d'anya zube amma ALLAH ya k'addara mijinki *Muhammad Sameer* saiyazo duniya.
Lokacin Dana haihu shekarar haneef 10 cif a duniya.
Muhammad shine jika namiji na farko da aka fara haihuwa a masarautar gagara badau, dan kuwa matar Jalaludden ma mata taketa haihuwa.
Daga nan nima ban sakeba saida Muhammad yacika shekara hud'u, yanda Saifudden yasha tsangwamar mama Fulani haka Muhammad ma yashata tun yana yaro.
Shima Sameer hak'urin mahaifinsa Saifudden ya gado sosai, dan ko abu aka masa saidai yayi kukansa ya goge hawaye, koni bazai sanarmawa ba, saidai in wata baiwa tagani ko Haneefa (aunty Mimi) su sanarnin.
Da *Ciwon zuciya* na haifi Sameer, dan haka kullum cikin kaffa-kaffa muke dashi saboda gudun samun matsala ga lafiyarsa, da yawa jama'ar gidan sukan masa abune wai dan zuciyarsa ta buga? ya mutu. sun manta rayuwa da mutuwa duk Na ALLAH ne.
Da sauri na kallo momma.
Ta d'aga min kai tana murmushin takaici, “hakane d'iyata, kullum burinsu kenan akan Muhammad tun yana yaro..
Ranar wata litinin da asuba Sarki Saifudden yafita sallar asubahi sai kawo manashi akayi cikin gida, wai yafad'i ana tsaka da sallah.
A lokacin kafafunsa ne kawai basa aiki, amma sauran jikinsa yana motsawa.
Nice naita wahalar jinyarsa, ga cikina yafara tsufa, sai jakadiya ke taimakona, amma sauran matan Sarki ko'a jikinsu.
A hankali ciwo yacigaba da girmama a jikin takawa, tun ana kafa har yadawo duka jiki, idonsane kurum ke aiki a lokacin.
A asibitin garinan muke jiyyarsa a time d'in, a asirce batareda jama'ar gari sun saniba.
Acikin wannan tashin hankalin na haihu Namiji, shine Abubakar (Sauban).
Nidai lokacin kawai ina rainon Sauban ne, amma rabi duk Haneefa ce (aunty Mimi) yayinda kulawar Sameer takoma hannun k'anwata Zaituna (mom), autarmu kenan, dan dole aka dawo da ita wajena tana taimakamin.
Na haifi Sauban babu dad'ewa aka maida sarautar Saifudden akan Jalaludden d'an gidan mama Fulani, saikuma lokacin jama'ar gari suka San Sarki Saifudden bashida lafiya ma.
Ko kad'an ban damuba, danni ta lafiyar mijina nakeyi ma.
A lokacin anta kananun magana akan zargin mama Fulani dawasu kuma manyan attajirai, dan akwai wani zaman sirri da sarki Saifudden yayi dawasu attajiran k'asar ana jibi abin zai sameshi, kuma anga yafito ransa a 6ace daga tattaunawar, alamar sun buk'aci wani Abu ya hanasu kenan. suma angansu ran nasu A 6acen. Nikam bamma maida hankali akan wannanba, mahaifina Sarki Abdul'fatah shine kawai tsaye akan ciwon Saifudden, saini kuma da jakadiya.
Masarautar kuwa ai duniya sabuwa. Matan Sarki Saifudden ma duk sun kama gabansu, sunce bazasu iyaba.
Shekararmu d'aya a asibiti babu wani canji, saima jikinsa dake neman fara ru6ewa saboda komai sai an masa. Baya iya d'aga koda d'an yatsane. (Tun farko likitocinmu na nan sun Sanar damu an masa allurar gubane, kuma guba mai had'ari, dan babu makarinta, itakuma tana sakar da jijiyoyin jikine su daina aiki gaba d'aya, wannan yasaka jikin Sarki Saifudden ya sandare?.
Wani amintaccen likitanmune yabada shawarar mu maidashi India dansu sunada kwararrun likitoci, kuma zaifi samun kulawa da tsaro a can.
Wannan shine silar dawowarmu wannan k'asa, da cuku-cukun mahaifina Sarki Abdul'fatah, dan komai namu mukam ya k'are, duk abinda Sarki Saifudden kedashi yagama k'arewa a neman Magani.
Tunda muka dawo India kuwa Sarki Saifudden yafara samun kulawa ta musamman, saidaifa maganar ta kud'ine. Wasu sarakuna da yawa sun bamu gudunmawa, wasuma suna akan bamu.
Sanin Zara bata barin dami, gashi kullum cikin buk'atar kud'i muke sai mahaifina yakafa wasu sana'oi da sauran kud'enmu, tanan muke samun kud'in shiga. Karatun Muh'd da Haneefa kuma Mahaifiana ke d'aukar nauyi..
Tundaga primary har jami'a anan Sameer yayi karatunsa.
Kiyayyar Saifudden kuma ga mama Fulani saita dawo jlkan Muh'd gaba d'aya, kokad'an bata k'aunar ganinsa, kullum tsakaninta dashi sai aibantawa da jifansa da kalamai masu had'ari ga yaro.
Tunda Muh'd yafara sanin Kansa, yaga halin da mahaifinsa yake saiya fara canjawa daga mai hakuri zuwa mai zafi.
Ga ciwonsa kuma, duk yabi yayta kuntata zuciyarsa akan ciwon mahaifinsa da burin d'aukar fansa.
Muh'd mai fara'a da barkwanci yakoma mutum marason magana da azabar rashin d'aukar raini, duk da hakurinsa nanan bai dainaba, dan zakata masa Abu ya shareka kamar bai ganiba, sai randa yazo k'arshene zaka gane kurenka a wajensa.
Mahaifina Sarki Abdul'fatah shine yamatsa tun Muh'd na secondary school dole idan akayi Hutu yazo najeria, dan acewarsa tahakane kawai zai fahimci sarautar gidansu.
Muh'd ya karanci Engineering ne, dama tun yana yaro kingansa kullum cikin son had'a Abu yake, shine tsinka wayar fitila tsinka ta redio ya had'a wani abun, tunma ina masa fad'a harna bari kawai. Ashe abincinsa awajen yake. Yanzu haka sunada Company na had'a wayoyi? da Computers??, da sauran kayayyaki dai. Sannan yana wasu business domin dai muke samun kud'ad'en kulawa da mahaifisa da sauran matsalolinmu, dan babu mai kulawa damu a masarautar gagara badau sai Sarki Jalaludden.
Wani zuwa da Muh'd yayi Nigeria shine aka bashi sarautar *Galadima*, galadima Sarautace mai k'arfin gaske, dan sai d'a mafi soyuwa ga Sarki ko k'ani ake bamawa. Kuma akance batada banbanci da sarautar waziri, dan duk abinda waziri zaiyi Galadima ma zai iyayinsa. Akwai ma wasu abubuwan da daga Sarki sai Galadima kan yisu a fada.
Da da farko nace ya mayar musu amma sai mahaifina yace a'a, ai hakan da sukayi dai-daine.
Sharrin kuwa dakika sun masa, har tsautsayi ya jefaki a ciki, sunyine dan hankalinsa ya tashi, har takai zuciyarsa ta buga ya mutu sun huta.
Dan ayanzu ne suke ganin sunfa *kashe macijine basu sare kansaba* Galadima yazamar musu *RAINA KAMA.....*, basuyi tunanin zaikai tsawon rai hakaba, saboda Ciwo mai had'ari dake a tare dashi.
Shikuma Muh'd yafi karkata hankalinsa ga jama'ar wajene sukama mahaifisa haka, koda akwai jama'ar masarautar gagara badau to kalilanne, kuma mama Fulani kawai yake zargi.
Nikuma ba ita kad'ai nake zargiba, amma yakasa fahimtata gaba d'aya har kawo yanzun kuwa. Dagashi har Haneefa sunfi zargin jama'ar waje, don mutananen masarautar suna 6oye musu ainahin fuskarsu ta zalunci, mama Fulani ce kawai tata take a bayyane.
Wannan yasaka tun sharrin da akai muku nasaka amin bincike a kanki, Alhmdllh ban samu wata matsalaba a tarihinki,, daga nan na dukufa addu'a da neman za6in ALLAH.
bamma kai ga furtama kowa matsalata ba sai mahaifina Sarki Abdul'fatah (papi) yace Muh'd saiya aureki.
Nasan ba sonsa kikeba, amma ina rok'on ubangiji da yasa wataran kuso junanku, kinada tarbiyya da wayon da zaki iya canjamin Muh'd, dan banason hallayarsa ta yanzu, nafi son nake ganin walwala atare dashi a ko yaushe, ki taimakeni ki shiga rayuwarsa sosai, dan ke macece, sai kin fishi zama cikin jama'ar masarautarsu, zakuma ki fishi fahimtar halayyarsu, sannan kidinga bashi shawara akan abinda yadace dashi. Inaji a jikina zaki iya canjamin Muh'd, saboda kinada hankali. gudun kar wani yasakama zuciyarki tunani daban yasaka nace yakawoki da wuri, domin kisan yanda zaki rayu a masarautar, kafin kutafi insha ALLAH komai Na zamantakewar masarauta za'a koyar dake kinji”.
Kaina Na gyad'a mata, sannan a sanyaye nace “Momma namiki alk'awarin zai taimakesa akan matsalarnan, kuma zan bama rayuwarsa gudun mawa insha ALLAH, Sai dai Abu d'aya ne ban ganeba”.
“miye baki ganeba d'iyata?”.
“Abokinsa Muftahu, shima a masarautar yake?”.
Murmushi Momma tayi, tace “daga Muftahu har Harun duk 'yan masarautar ne, Muftahu kakanni suka had'a dasu Muhammad, da kakan Muftahu da Sarki Abubakar kakansu Muh'd uwarsu d'aya ubansu d'aya, shikuma Harun d'an waziri ne na yanzu, kuma shima wazirin haifaffen gidanne, saidai inason sanin ko wani Abu kika gani tareda wani acikinsu?”.
Kaina Na girgiza alamar A'a.
Momma ta sauke ajiyar zuciya, “Munaya saikin dage kinji, domin Na had'aki da aiki mai wahalar gaske, mai kuma sark'akiya, musanman akan halayyar Muh'd, dan bai yarda da kowaba dakike ganinsa nan, koyaya Abu ya had'aku sai yayi zargin turoka akayi garesa, kuma zaka Shiga jerin wad'an da yake tuhuma. amma kekad'aice mafi kusanci da Muh'd yanzu, zakifi kowa sanin matsalarsa da wuri, saikuma kin fimu fuskantar tunaninsa, danni kinga jinyar mahaifinsa tasa banwani zauna dasu irin sosai d'innanba, yanzu haka kafin nasan matsalarsa 'Yar uwata Zaitun (mom) tasani ko Haneefa (aunty Mimi), garama Sauban.
Nace “shikenan Momma ki tayamu da addu'a kawai”.
“insha ALLAH muna kan yimuku kullum, ALLAH yayimuku albarka, ya albarkaci aurenku da dukkan rayuwarku da abinda zaku haifa”.
Ban iya amsawa ba, kaina Na k'asa nikam, ko azuciya ma ban amsaba, dan nayi alk'awarin zai taimakesa kamar yanda ta buk'ata. Amma ina gamawa zan nemi sakina, koda nanda shekaru 2 ne kuwa, amma gaskiya Na tausayama Galadima, dan nakula yana cikin tsakkiyar mak'iyane masu fuska biyu. abinda kuma nalura da Momma bata ganeba shine Galadima bawai bai yarda 'yan gidansu nada saka hannu akan ciwon babansa bane, baya dai nunawane kawai, sai dai bansan dalilinsaba.
CCTV camera d'in dana gani a d'akinsace tadawomin a rai, maybe ya sakatane domin sanin masu shiga da fita koda bayanan.
Haka Na kusan yini cikin damuwa da tausayinsa, dan duk saiya bani tausayi wlhy. shiyyasa zaka gansa kullum shiru-shiru, gaskiya 6angaren hak'uri Na yarda yanada hak'uri kam.
***********
Yau saida yamma mukaje muka duba Abie, mun iske Galadima baya asibitin, dama tun da rana yazo gida yay wanka yakuma fita.
Har dare muna a asibitin, saida Galadima yazo muka taho tare, ina gaba ni da shi da khaleel dake barci a cinyata, yayinda sauban da aunty Mimi da Samha ke baya.
Maganar da samha ta fad'amin d'azun a asibiti ta dawomin a rai, Ashe mahaifinsu ya rasu suma shekara 2 kenan, itace d'iyar Aunty Mimi ta farko, sai Hakim da suka rasu tareda babansu, saikuma khaleel auta. Suma a Nigeria da suke zaune, bayan rasuwar mahaifin nasune suka dawo nan india, duk da dangin mahaifinsu sunso kar6arsu papi yahana, babansu tsohon Governor ne shima, mutuwar tasa kuma akwai lauje cikin nad'i shima, dan ya tsananta akan binciken ciwon surukinsa Abie sosai, shiyyasama ake zargin an kasheshine saboda wani Abu daya gani.
Har muka Isa gida bansan hirar dasukeba a baya, dan shima Galadima baya cewa uffan.
Shine ya kar6i khaleel a hannuna, ya sa6ashi a kafad'a muka shiga ciki, har d'akinsa ya kaisa. ni lokacinma harna haye saman..........??
Barkanku da juma'a.
Zanyi last page gobe idan ALLAH ya kaimu da rai da lafiya???♀???♀.
Network yanata min iskanci tun jiya shiyyasa kuka jini shiru?
*_YA ALLAH ka gafartama iyayenmu_*???
[5/4, 1:09 PM] ? M B A ?: *_Typing?_*
*_HASKE WRITERS ASSO...?_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_?RAINA KAMA......!!?_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce??_*
??3?0?
..................Da sallama ciki-ciki ya shigo, nayi saurin maida zip d'in rigata sama nafasa cirewa, a sace ya kalleni yawuce bakin gadon ya zaune tareda dafe kansa.
Kallonsa nayi Na kauda idona nima, kusan mintuna 3 kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa. d'agowa yayi yakuma kallona, kamar an masa dole yake maganar cikeda k'asaita, “k! Wai bazakima Momma magana ba kikoma d'akinki?”.
Kamar bazanyi maganaba saikuma nayi batare da Na kallesaba, “inaga kaine yakamata kamata maganar ai, dan nima zanfi son haka, duk nabi Na takura zama da Namiji d'aki d'aya”.
Banza yamin bai sake tankawa ba, saima yamik'e yana jan k'aramin tsaki, nikam Na ta6e baki a zuciyata ina fad'in ka iya fad'ar R kafin kamin mazurai.
Baima san ina yiba, yaje wajen wardrobe d'insa ya d'auki kayan barci yanufi bathroom.
Murmushi kawai nayi, danni rayuwar mutuminnan mamaki take bani, ina dad'i kabi ka k'untata kanka irin haka? baka hira da kowa, baka dariya, shifa ko kallo inba labaraiba ban ta6a ganin yanayiba, hakama wak'a banta6a jin yana jiba, koranar dana duba wayarsa karatun Qur'an kawai nagani da Tafseer. nakai dubana gawata 'Yar kanta dakecan gefe a bedroom d'in nasa, mafi yawanci littatafan addini ne awajen, sai English Novels. (To yayi karatun addinine? tunda naji Momma tace anan India ya girma?). Wata zuciya tacemin su India basuda musulmai ne?. “hakane kumafa” nafad'a a fili ina mik'ewa.
Ganinaima bara nacire kayana kafin yafito, daya fito saina shiga nima.
Har ga ALLAH banyi tunanin fitowarsa ba yanzun, dan haka hankalina kwance na zuge zip d'in rigar, na cireta gaba d'aya, shima sket d'in nayi k'asa dashi yafad'i k'asa.
Juyowarnan da zanyi da nufin d'aukar towel dana ajiye saman akwatina sai kawai naga mutum tsaye a k'ofar bathroom, hannunsa rik'eda k'aramin towel yayi tsaye yana kallona.
Bansan Na kwalla k'araba wlhy, Na rarumi towel d'in nayi saurin kare jikina, ALLAH ma yaso k'ofar a rufe take, dan dawuya su Aunty Mimi sujini.
K'arata tadawo dashi daga sumar tsayen dayayi, yawani kauda kansa cikeda basarwa yana ta6e baki, saikuma yaja guntun tsaki yaje bakin gadon ya zauna yana cigaba da goge fuskarsa, dan har yayi shirin barcinsa a ciki.
Jinayi tamkar na makesa, d'an rainin hankali yagama kalleni zai wani miskile fuska asfa baiga abin kalloba. hijjabin sallata na janyo Na saka, sannan nawuce bayi ina hararsa.
Ina shiga yamik'e yana wani munafukin murmushi, abin salla ya shinfid'a ya kabbara shafa'i da wutiri.
Nadad'e abayin nak'i fitowa, saida nabar jin motsinsa duka sannan Na fito, dayake nayi shirina a bayin nima, nazata ya kwanta, amma saina iskeshi zaune a kujerar dake gefen kantar littatafan nan ya bud'e laptop yana danne-danne, gefensa kofine yanata turiri, da alama coffee ne aciki.
Yad'an juyamin baya kad'an, dan haka cikin sand'a Na rufe k'ofar, nakuma tako a hankali har zuwa wajen sofa Na kwanta, duk zatona baya ganina, Ashe yana kallon duk abinda nakeyi ta gefen idonsa.
A ransa yace munafunci. cigaba yay da aikinsa hankaki kwance, bai bar wajenba har kusan 1:30pm, maimakon ya kwanta sainaga yashiga bayi ya d'auro alwala.
Nima har time d'in barci yakasa d'aukata, maganar Momma tanata min yawo a zuciyata, tunanin ta inda zan taimaki Galadima kawai nakeyi.
Ina kallonsa ya kabbara salla. saida yay kusan raka'a 6 yanayi yana sallamewa, daganan ya d'auki alku'ani yafara karatu k'asa-k'asa.
Masha ALLAH nafad'a a raina, danjin yanda muryarsa ke fita cikin karatun littafi mai tsarki, gashi yana fidda kowane harafi cikin tsantseni da kwarewa. Tun ina saurarensa har wani barci mai dad'i ya saceni, bansan lokacin daya kammala ba yazo ya kwanta.
Muduka makara mukayi sallar asuba yau, dan haka shima yau a gida yayi.
Bayan ya idar waya ya d'auka naga yayi kira.
Bayan an d'aga daga can sukayi gaisuwa, jin ya tambayi ya Nigeria Na gane da 'yan can yake wayar. yacigaba da fad'in.
“Nuren naga ka turomin hotonsa, shin a inane yake haka?”.
Bansan mi akace masaba daga can, naga dai yayi kwafa, sai yace “ya maganar Minister? dan nagansa wajen d'urin aurena, ban kuma yi zaton zai zoba”.
Canma aka kuma yin wata maganar.
Zamansa yagyara, yakuma jingina da bangon, dayake yana kan abin salla har yanzun. “kayi k'ok'ari Nuren, yanzu abinda nakeso dakai shine, akwai yarinyarsa d'inan datake karatu a nan jami'ar Abuja, inason a sacemin ita k'arshen watannan, yanzu ka saka ana bibiyarmin komai nata, Shikuma Alhaji Balala driver n sa zaku d'aukemin, dan bincikena ya ganomin shekarunsa 30 dawani Abu yana masa aiki, kuma randa su Alhaji balala sukayi zama da Abie shine ya kaisa masarautar mu, inada tabbacin zai San wani Abu koda kad'anne, kuyi aikinku da kulawa Nuren, banason asami matsala kamar wancan time d'in, gobe kashiga birnin gayu plaza kuyi zama Na musamman da Saleem akan maganar CCTV camera data daina aiki randa abinnan ya faru, ni naso Na zauna dashi, amma kaga Momma tamatsa akan dawowata”.
bayan nacan yagama magana.
Yace “ok babu damuwa, zan turo maka number yarinyar, saiku bibiyeta tanan. sai anjima, ka gaidamin Mom d'ina”.
Koda ya ajiye wayar saiya koma gado ya kwanta abinsa, nikam ina zaune sai cud'awa da kwancewa nakeyi, ban fahimci wayar tasaba gaba d'aya, shin wanene kuma NUREN!? shikuma miye alak'arsa da Galadima kuma?.
Tabbas aikina bazai yuwuba saina San wanene NUREN, wane kuma aiki yakema Galadima a sirrence, su waye wad'annan mutanen biyu daya ambata Minister da Alhaji balala? suna cikin wancan case d'in Na Abie ne? kokuwa tasu dabance?.
Kwanciya ta na juya yanda zanji dad'in tunanin da k'yau, saikuma naga ai ba sanin waye Nuren bane matsalata yanzu, kamata yayi nafara sanin shi kansa Galadima d'in da rayuwarsa, na tuna maganar Momma da tece “shi mutumne dabashi da yadda”. Mutum mara yarda kuwa yanada wuyar sha'ani, kad'an na juyo na kallesa, idonsa a rufe yake, amma ban yarda barci yakeba, na janye idona nima na maida lumshe, barcine mai nauyi ya kwasheni, harya fita bamma saniba inata barci, babu kuma Wanda yazo ya tadani.
Sai around 11:30 na tashi, wani masifar ciwo kaina yakemin, haka dai na tak'ark'ara nayi wanka, nagyara d'akin sannan na sako k'asa, gidan shiru tamkar babu kowa, sai television daketa aiki, zama nayi bisa kujera dafe da kaina.
“ranki ya dad'e lafiya dai?”.
Bud'e idona nayi a hankali, sai naga jakadiya ce, namata murmushi tareda yunk'urin tashi zaune, “wlhy kaina ke ciwo jakadiya, halanma ke kad'aice ma a gidan?”.
“subahanalla, sannu ranki ya dad'e, bara na samo miki abinci saikisha magani, eh ni kad'aice ranki ya dad'e su Sauban sun tafi makaranta. Gimbiya Mimi kuma tana asibiti itama, taga kina barcine shiyyasa tahana a tadaki”.
Nace “ALLAH sarki”.
Wucewa tayi zuwa kitchen, babu dad'ewa saigata tadawo da tire, a gabana ta ajiye tana fad'in “gashi ranki ya dad'e, kici saikisha magani kafin Magajin gari yadawo saikuje asibiti”.
Kallonta nayi da mamaki, “jakadiya waye magajin gari kuma?”.
Tayi 'Yar dariya, “ranki ya dad'e ina nufin mai gidanki, ai magajin gari nake cemasa”.
Murmushi nayi ina girgiza kai kawai, na had'a tea nasha, sannan nasha maganin, anan falon na kuma kwantawa, barci yakuma kwasheni.
Jakadiya na zaune tana gadina.
Da sallama ya shigo, jakadiya ta amsa tareda mik'ewa da sauri ta kar6i kayan hannunsa tana masa sannu da zuwa, yad'an saki fuska yana amsawa. d'aya acikin kujerun ya zauna, sai lokacin idonsa ya sauka kaina.....
maganar da jakadiya take masa ce yasakashi janye ido daga kaina ya maida kanta.
“ranka ya dad'e akai kayan samane?”.
“no jakadiya kibari zan hau dasu, ai sunmiki nauyi, ita wannan mike damunta tayi barci anan?”. ‘yay maganar yana maido idonsa kaina’.
“kanta ke ciwo ranka ya dad'e, amma tasha magani ma, shine barcin ya kwashe a wajen”.
Ido yad'an tsuramin, kafin ya cije lips d'insa kad'an.
Jakadiya tajuya zuwa kitchen, babu dad'ewa tadawo da ruwa ta ajiye masa.
Sannu yamata sannan yad'auka yana sha, itakuma tabar wajen.
Kofin da yasha ruwan ya ajiye, ya maida kansa jikin kujerar ya jingina kansa, tareda maida k'afarsa d'aya kan d'aya, lumshe idonsa yayi, ta k'asan ido yake kallona, tsawon lokaci yana a haka, yayinda nikuma nake barci bansan yana yibama.
Kamar an tasheni saina bud'e idona a hankali, dashi na fara tozali, dan haka namik'e zaune da sauri, tareda warware d'an kwalina na yafa, dan gown d'in material ce a jikina, gashi irin mai santsinan, kuma rigar takamani sosai, a raina nace dukma yagama kalleni, wama yasan tun yaushe yake anan?.
Duk abinda nakeyi yana kallona, sometimes yarinyar nan takan bashi dariya, a d'an zaman dayayi da ita yalura tanada kunya, saidai batason raini, bakuma tada tsoro ko kad'an, ganin ina Neman mik'ewa saiya bud'e idonsa.
Harna fara tafiya saina juyo, danjin kamar ana kallona. idonsa a kaina, amma saiya wani basar tareda janyewa.
Kaina kawai na girgiza, harzan cigaba da tafiya saina tuna nemanfa kusanci nake dashi domin cika alk'awarin Momma da zanyi, baya na dawo nakoma na zauna, muryata a sanyaye nace, “sannu da dawowa”.
Sosai na bashi mamaki, dan haka ya kalleni da k'yau, kamar zaiyi magana saikuma ya fasa, kusan minti 1 dawasu Second's sannan yace “mike damunki kika kwanta anan?”.
“kainane ke ciwo amma yama daina”. maganar dayayice tabani mamaki.
Mik'ewa yayi yana fad'in “ba gulma tasaki k'inyin barci jiyaba, dole ai kitashi da ciwon kai”.
Galala nabishi da kallo, kai wannan guy d'in yafara bani tsoro, dama yasan banyi barciba jiya kenan? Anya guy d'innan baya gani har hanji?? nabishi da kallo yayinda yake taka step d'in benen cikeda izza, hanunsa d'aukeda ledojin daya kwashe a falon, saida ya 6acema ganina sannan na sauke ajiyar zuciya.
★*★*★*★*★*★*★
*_Nigeria_*
Tun bayan zuwanmu sallama da tafiyarmu 'yan gidanmu sai suka dainama innarmu magana, musamman yanda sukaga anata fita da abubuwan dana bari a baiwa mutane, innarmu ko'a kwalar rigarta itakam, bata damu da rashin mata maganar dasukeba, harkokin gabanta kawai takeyi hankali kwance.
Innaro kam kud'in da Galadima yabata suka sakata d'agama innarmu k'afa, ko gaidata tayi cikin salama take amsa mata, a jiya harda siyoma su Aryaan sllifas, wai taganine a hanya sun mata k'yau ta siya musu, murmushi kawai innarmu tayi damata godiya ta kar6a.
Wannan k'yauta tasaka mamansu yaa Hameed kasa hak'uri taita sakin habaici, daga nan sauran matan gidanmu suka d'auka suma, innarmu saita saka karatun alkur'ani ma a waya tashige d'aki tarufe kanta.
Har sukaci suka tsire dan kansu sukayi shiru.
Kusan k'arfe hud'u na gamma saiga Zarah wujiga-wujiga tashigo gidan, ga ciki yafito masha ALLAH, Innarmu dake tsakar gida tana wankin kwanuka tayi saurin cewa “zarah lafiya?”.
Jikin innamu tafad'a ta fashe da kuka, “innarsu 2 ki taimakeni zai kasheni, wlhy bani na d'auka masa kud'iba, narantse da ALLAH........”
Tuni 'yan gidanmu duk sun fito, danjin kururuwar Zarah, mamansu yaa hameed tazo ta janyeta daga jikin innarmu, “k mahaukaciyar inace dabazaki nutsu kisan wazaki fad'ama matsalarki bane?”..
Oho ita Zarah ba wannan bane matsalarta a yanzun, takuma fad'awa jikin mamansun tana kuka da rantsuwar ba ita ta d'auki kud'iba.
Ganin tana neman yage musu zani a kasuwa sai mamansu tajata suka shige d'aki.
Wata dariyar gatsatsa maman Safara'u tayi, tareda ta6e baki tana kallon Gwaggon Haleematu dake k'usa da ita “to anfara da bismillah kenan? Wata 6 an koro yarinya da duka?......
Caraf Momy Hadiza ta k'ar6e “yo mai kashi a gindi ai baya toshe hanci yace makwafcinsa na wari, kidai iya bakinki tunda kema kinkai gidan wani”.
“can a bakinki, nakai kuwa, kuma tawa zama daram babu yaji balle nik'a gari, tunda ba auren hange-hange da tauye hak'in wasu namata ba, ai bama saikin zak'eba, munsan mai kaza a aljihu dama baya jimirin Asss!, indai nice kinga tafiyata, kiyi da wani ba niba”.
Tamkar Momy Hadiza zata daki maman Safara'u haka ta hayayyak'o mata, wannan hayaniya ce tafara jawo kunnen makwafta gidanmu, saiga innaro tamkar an jehota, ta shiga tambayar ba'asin hayaniyar, dansu Abbanmu duk suna wajen aiki.
Duk shiru sukai mata, sai innarmu Ce da maman Fauziyya suke fad'a mata abinda yafaru.
d'akin mamansu yaa hameed tashige domin jiyo ba'asin dawowar Zarah n.
Itadai innarmu jikinta duk yayi sanyi, wannan zamanin ko aurar da yaranka mata kayi tsugunne bata k'are makaba, dan sai ALLAH yabasu mazaje na garin dazasu iya hak'urin zama da juna, aurene tunkan ayisa zakaga angama kwashe masa albarka wajen buruka da bidi'oin biki, ga iyaye yanzu gaba d'aya hankalinsu Yakoma ga d'irkama 'ya'yansu kayan mata kawai ba koya musu dabarun zaman aurenba, sun manta kayan mata basu kad'ai bane ma'aurata ke buk'ata a zaman aure, sudai sukan kawo wata nutsuwane da kuma dank'o cikin rayuwar auren, gaba d'aya yanzu zakiga gidajen auren Malam bahaushe sun canja, wuyarta dai akai yarinya miji ya kauda mata budurcine, wata biyu yayi yawa kwarnafinsa ya kwanta saiya fara Neman makusarta, gakuma yaran basuda wata dabara dazatasa su taka tsantsan ga zamantakewar, har yakai an sami sassaucin cin zarafi daga mazajen nasu, to an nuna musu kayan mata sune kawai jigon aure da hangar mallakar mijin kansa, to ALLAH ka zaunar mana dasu lafiya dai agidajensu.
Nace amin innarmu???
★★★★
Kusan minti 10 da shigarsa saina tashi nabi bayansa, waya nakeson ya aramin nayi kiran su innarmu Susan mun sauka lafiya.
Saida nai sallama yabani izinin shiga sannan, saman sofa na iskeshi zaune yana latsa waya, da alama waya yagama ko zaiyi.
Zama nayi a kujerar da yake karatu takusa da kanta, na kwantar da murya cikin sigar ladab nace “yalla6ai ka aramin waya dan ALLAH nayi kiran innarmu da Munubiya”.
Biris yay dani, sai zuwa can yad'ago ido ya kalleni, ya motsa baki zaiyi magana amma jin kai ya hanashi, saiyay shiru kuma yacigaba da latsa wayar, saida yamula dan kansa sannan yajawo ledar daya shigo da ita, wata k'aramar pink d'in souvenirs bag yamik'o min batareda yace uffanba.
Tasowa nayi zuwa gabansa zan kar6a, hanun bag d'in k'aramine, dan haka hanunmu ya had'u waje d'aya, ni da shi kowa saida yaji shock, yay saurin janye hannunsa, yayinda bag d'in tayi k'asa zata fad'i yay saurin kuma k'ok'arin tarewa kamar yanda nima nakawo hannun hagguna da sauri. Sai kawai na damk'e hannunsa kanmu ya gwaru waje d'aya.
Kowanne dafe kansa yayi da sauri, yayinda hanun damarsa dana hagguna suke tallafe da juna mun tare bag d'in karta fad'i.
Na kallesa tamkar zanyi kuka, dan wlhy naji zafi, kansa kamar kwakwa?.
Hararata yayi yana fad'in “k wane irin kaine dake haka?”.
Haushi saiya kamani, shi baiga nasaba sai nawa, na matso kwallar dasuka cikamin idona, cikin turo baki nace “kana niyyar fasan kai, shine zaka maida abun kaina?”.
Hanunsa daya dafe kai yasaka ya d'an bugi bakina, “k kinma rainani wlhy”.
K'asa na durk'ushe kawai nasaki masa kuka. ya waro ido da mamaki yana kallona, wannan d'an abin dayamin shine na kuka? yarinyar nan akwai rainin hankali fa”.
Ganin abin nawa azimunne saiya mik'e tsaye, tareda d'iremin wayarsa bisa cinyata ya shige bathroom.
Yana shiga nama bayansa gwalo, dama duk cikin takune, sonake kawai nagano lagwansa. goshina nad'an shafa dan gaskiya naji zafi, saima naji wajen kamar yafara kumbura.
Ban tashi a wajen ba nashiga loda numbar innarmu, amma tak'i shiga, saina saka ta Munubiya, itama tak'i tafiya, nad'an ja tsuka, ina kuma shafa goshin, kamar wasa wajen sai rad'ad'i yakemin, ina cikin mulmulawa da matse baki yafito, kallona yad'anyi kamar zai basar saikuma ya kasa, ya k'arasa jikin wardrobe d'insa yana bud'ewa, “har yanzu goshin zafi yake?”.
Kamar zanyi kuka nace, “eh wlhy ”.
Daina abinda yakeyi yayi yajuyo yana kallona, saikuma ya maida drowan yarufe yanufe inda nake zaune. A gabana ya d'urk'usa, k'amshin sabulun wankan ya daki hancina, hannunsa na haggu ya d'aura bisa kaina, ya d'aura na damar akan goshina, sanyin damshin ruwan da taushin hannunsa suka ratsa goshina, a hankali yafara mulmula goshin, nafara matse baki ina rik'e hannunsa, dan wlhy akwai zafi, “please kabarsa dan ALLAH, wlhy akwai zafi fa”, bai saurareniba, duk rik'e masa hannun danake saida ya mulmulamin sosai sannan yamik'e yana hararata da ta6e baki, “halan kekam kina jaririya ba'a miki wankan jegoba?”.
Baki na tunzuro masa, nace “ka kira innarmu ka tambayeta mana, ni ina zan sani”.
Batareda ya shiryaba ya murmusa yana barin wajen. Kayansa ya d'auka yakoma bayi danya sanya.
Nikuma saina mik'e nakoma kan sofa d'in ina bud'e bag d'in d'azun. kwalin wayane mai k'yau, wani dad'i ya kamani, amma saboda jan aji saina maida na ajiye gefena, nacigaba da danna kiran su innarmu.
A haka yafito ya sameni, yana sanye cikin Brown d'in wando da Navy blue t-shirts mai gajeren hannu, ya tsuke k'ugunsa, bai kalleniba yawuce wajen wani kwando mai k'yau da aka zuba sandunan wasan Golf a ciki?, guda biyu ya ciro, sannan ya tako inda nake yana fad'in “bani wayata idan kin gama”.
Fuska na marairaice nace “ALLAH kagani bamma yiba, tak'i shigama”.
Wayar ya kar6a ya duma number, bakinsa ya d'an ta6e “k bak'auyar inace dazaki kira number a haka? ko nan k'asarkice?”.
Tunawa nai da saina saka + ashe, nace “oh namanta saina saka + wlhy”.
Aljihu ya saka wayar, “saiki bari sai wani time d'in kuma, yanzu sauri nake ana jirana”.
Da sauri nace “zan bika please, wlhy gidan shiru babu dad'i”.
Yana fesa turare yace, “ba yauba, baga jakadiya nan a gidanba, yanzu kuma Khumar zai d'akko khaleel a school ai”.
Shiru nayi bance komaiba, saiya juyo ya kalleni, ganin na kwa6e fuska cikin damuwa saikuma yaji wani iri, juyawa yayi yagara kwalar rigarsa, kafin yaje drowan gefen gadonsa ya d'akko wasu album na pictures har hud'u, saman cinyata ya ajiye batareda yace uffanba, yakwashi sandunansa yakama hanyar fita, batareda ya juyoba yace “wad'annan kayan nakine ki duba”.
Kafin nabasa amsa harya fice abinsa.
Kaina na girgiza ina ta6e baki, a fili nace, “Alaramma mara R ALLAH ya gyarakama Momma kai dai”. (Kifad'a a gabansa mana yarinya. ??).
_______________,,___________,,,______
Da sauri mamansu yaa Hameed ta kwa6e bakin Zarah alamar tayi shiru, saboda shigowar innaro, innaro bata kulaba, dan haka ta zauna a kujerar falon idonta akan Zarah, ganin yanda duk jikinta shatin duka, “kekauwa zara'u miya sameki haka? Ga ciki?”.
Harara mamansu yaa hameed taketa zubama Zarah, amma ina bata kulaba, ta share kwallar fuskarta tana fad'in “innaro wai kud'i ya ajiye a gidan jiya, shinefa yaduba yau bai ganiba, ina kitchen yashigo yana tambayata wai kona canja musu wajene? shine nace bammasan yashigo da kud'i gidan ba bare harna canja musu waje, ko rufe baki bai bari nayiba ya fallamin mari, nikuma naji zafi namasa ALLAH ya Isa, shinefa kawai yacire belt d'in jikinsa yahau buguna, wlhy da k'yar nagudo na fito, nasan idan nashiga gidan Siyama zai iya bina har can, tunda gidan d'an uwansane, dak'yar nasamu napep a anguwar nataho gida”.
Innaro tarik'e ha6a tana fad'in “oh ni marwanatu jikar Falalu, yanzu shi Sa'eedunne yamiki haka da hankalinsa? toke kin tabbata baki d'aukar masa kud'iba?”.
“wlhy innaro ban d'auka ba, kinji na rantse miki, shi dama halinsane haka?, indai ransa ya6aci ko kika masa kuskure sai dai kawai kiji mari, wlhy zuwana gidannan tun bankai satiba yake marina idan namasa Abu, yaune harda duka, gashi ko kad'an bashida hak'uri, Abu kad'an yagani saiyayi tsogumi, idan kuma kin masa na kirki bazai yaba mikiba, dawuya kimabasa Abu sau 10 bai kushe 8 a cikiba, 2 kuma bawai zai nuna yaji dad'i baneba?”.
“kai amma wannan yaro anyi wulak'antaccen yaro, yoshi dama dukan mata yake akasa nabashi jikata? Bari su Auwalun suzo, koti zansa su kaishi, sai an kwatar miki hak'inki,”.
“nidai babu wani court k innaro, kawai akirasa amasa bayani a sasantamu nakoma d'akina, inason mijina wlhy”.
“enyeee! A lallai zara'u kinkai kuwa, nikike fad'ama kina son mijinki? to dan ubanki auwalu saiku tashi ki koma yanzu, idan yagadama anjima akiramu jana'izar gawarki”. fuuu tafito tana sababi, kayaya tunta da maimaita maganar da Zarah tafad'a mata yasaka 'yan gidanmu fahimta komai, wasu dad'i har tsakar kansu, (yo dama gidanmu kowa bawani son d'an uwansa yakeba, salon munafurcine kawai da bariki na tsoffin mata).
'Daki Momy Hadiza tashige takira Siyama danjin k'arin bayani, anan Siyaman ke sanar mata wai dama ba wannan ne karon farko da Sa'eed d'in yay Complain Zarah na d'auka masa kud'i ba”.
Momy Hadiza ta rabga salati tana fad'in “k 'yarnan da gaske?”.
“wlhy kuwa Momy, yanzu haka ma gashi anan gidanmu suna maganar da Sulaiman”.
“to ALLAH ya k'yauta, ni dama auren ya mutu ki zauna daga ke saike, danni bama na k'aunar wannan had'in gambizar family d'in, komai yaro yamaka ido nakai”.
“yo nifa Momy wlhy yanzu haka bama magana da Zarah, daga ranar mun had'u da ita a gidan sunan Hanan k'anwarsu, toni shine ya kaini da kansa, itakuma Ashe bashi yakawitaba, shine ta tambayeni miyasa ban biya mata mun taho tareba? Nace mata ai shine yakawoni, itama nazata Sa'eed d'inne zai kawota, shinefa taketa faman fushi da gaba dani”.
“eye, kice tafara miki hassada kawai saboda taga mijinki tafi kulawa dake? to wlhy bance ki d'aga mata k'afaba, karma kituna da ubanki da ubanta ciki d'aya suka fito”.
“insha ALLAHU Momy bazan raga mataba”.
“yauwa 'yar albarka. Yanzu yamaganar kud'in damukayi ranar? kinsan fa bikin nata tahowa?”.
“zan aiko miki Momy, wai Momy da gaske Munaya bata Nigeria? ”.
Tsaki Momy Hadiza taja, cikin bak'in ciki tace “haka dai iyayenta sukace, mudai bamuda tabbas tunda ba'a gabanmu jirgin yatashiba, anzo dai mana sallamar munafunci itada wannan miskilallen mijin nata”.
“aikam Momy indai da sunzo d'in to da gaskefa sun tafin, dan Sulaiman yacemin yaga Galadima a airport shekaranjiya da sister d'inan watawa, shikuma yaje raka babansune zaiyi tafiya”.
“suyita tafiyar mana, kema dan sakaraice ai, yo mi mijin nata yafi naki? Amma kod'an Honeymoon d'in nan da ake zuwa ke kin kasa sakashi ya kaiki”.
“lallai momyn nan, shikenan tunda laifina kike gani, nidai zan kiraki anjima, yanzu jirana suke nakai musu abinci”. ‘bata jira cewarta ba ta yanke wayar’.
Takaici yakuma kama Momy Hadiza, saitaja tsaki, amma saboda munafurci saita nufi d'akin mamansu yaa Hameed jiyo abinda ya maido Zarah gida. (Fuska biyu??).
*******************
Hotunan na ajiye nafara bud'e wayar, woow irinfa wayarsa ce komai da komai, saidai tawa pink ce, gakuma extra condom na wayar har kala uku, kai gsky wayar tayi babu k'arya, layin dana gani a ciki na d'auka na saka sannan na jona charge saboda d'oki, sauran ledojin nahau bud'ewa, duk kayan sawane k'ananu marasa nauyi, kuma bamasu fidda tairaiciba, zan iya sakasu gaban kowa, a raina nace Ashe Galadima yanada kirki haka?, saida nagama had'a kayan waje d'aya sannan na haye gadonsa da yaune karon farko zan haushi, nawani 6ararraje ina kallon hotunan, wasu hotunan abin dariya wlhy, dan wasu yana yarone k'arami, wani a makaranta, wani awajen wasan yara, wani a masarautarsu, wani tareda mom, wani da aunty mimi da sauban, duk inda suke da Abie saida nayi kuka, dan abie duk yana kwancene, k'alilanne yakeda lafiya sannan. wasu kam ya zube wayoyi yanata had'e-had'en abubuwa na wasan yara?.
Kallon hotunan ne suka d'aukemin hankali har wani lokaci dasu Sauban suka dawo, bamma san sun dawoba saida Samha tahawo saman.
Zama tayi tanamin bayanin wasu mutanen jikin hotunan muna dariya, bamu sakkoba saida Sauban ya hawo yakiramu.
******
Sai bayan isha'i suka dawo shida aunty mimi.
Ina d'aki zaune har sannan ina kallon pictures d'in ya shigo, d'ago kaina nayi na kalleshi tareda amsa masa sallamar. Namasa sannu da zuwa.
Ciki-ciki ya amsa yana zubewa bakin gadon, d'an kwanciya yayi kusan minti 10 kafin yamik'e yashiga bathroom, kusan 1hour sannan yafito maybe su yalla6ai an sauke nauyine (??).
Yau saida na jirasa harya idar da shafa'i da wutirinsa, dan magana nakeson muyi, ganin ya idar ya zauna latsa wayane nace “dan ALLAH yalla6ai in tambayeka?”.
Batareda ya d'agoba yace “uhmm”.
Zamana na gyara cikin nutsuwa nace, “shin tunda Abie yafara jiyya anta6a masa maganin gargajiya ko amaida hankali ga addu'oi haka?”.
Yanzun kam d'ago ido yayi ya kalleni, dama tunda nafara maganar ya dakata daga latsa wayar.
“lips d'insa yad'an cije, kamar zaiyi magana saikuma yay shiru.
Nace “kayi hak'uri idan nashiga hurumin daba nawaba”.
Nanma shiru yamin, saida yaja wasu mintuna kafin ya ajiye wayar yagyara zamansa, cikin alamun bak'in ciki yace, “duk an gwada masa, saidai gaskiya bakamar yanda aka maida hankali gana asibitinba, saboda anriga da an sanar mana Allurar gubace aka masa, amma muna k'ok'arin sakashi a sallalolinmu na farilla dana nafila. Kullum addu'oinmu akansa yake”.
Ajiyar zuciya na sauke, nace “ALLAH yabashi lafiya, yakawo mana iyaka, yakuma bashi ikon cinye jarabawar nan”.
“amin yafad'a a la66ansa”.
Dagani harshi babu Wanda yasake magana har muka kwanta, saidai yauma banyi isashen barciba, inata cud'awa da kwancewa, har gabannin asubahi kafin barcin ya saceni..................??
_To Alhmddlh my sweet fans, zamu dakata anan kenan, saikuma ALLAH yakaimu bayan salla darai da lafiya, zanbar wannan a matsayin *RAINA KAMA..... PART ONE* yanda zamu tafi a tsare kawai, basai mundawo ba kuma mushiga tunanin inama aka tsaya? Ina kuma za'a tashi, a *RAINA KAMA PART TWO* zamuga yanda Munaya zata taimaki Galadima kamar yanda Momma ta buk'ata, shin zai bata had'in kaima Kuwa? domin kunji Momma dai tace bashida yarda? ya matsayin auren Zarah? Muftahu yaya zata kasance idan Galadima ya cafkoshi? shin Munaya tanada wani fikra ne game da ciwon Abie?. wannan amsoshin duk suna cikin *RAINA KAMA PART TWO* da zaizo bayan sallah insha ALLAHU my guys, one Luv?????????_
_tabbas banida bakin godiya a gareku, saboda addu'oi da mahaifina ke samu agareku, Comments naku suna matuk'ar sakani a farinciki sosai, ngd ALLAH yabar zuminci, duk inda masoyin wannan buk yake yasaka aransa yana can k'ark'ashin zuciyar Bilyn Abdull.???????????????????._
_ga azumi zamu shiga, 'yan uwana dan ALLAH mu maida hankalinmu ga ibada, sadaka da k'autatama marasa k'arfi, marayu,, k'autata mu'amullarmu da jama'a dayin amfani da abinda malamai zasu fad'akar damu, karya zam kullum muna wahalar zuwa tafseer amma bamu d'aukar komai, da bayan salla yawuce munkuma koma kan munanan ayukanmu, karmu manta irin wannan watan saikuma mai rabon gani, sau 1 tak yake zuwa mana akowacce shekara, wani yawuce agaresa kenan har Abadan, zata iya yuwuwa nice ma?, zata iya yuwa kece 'Yar uwa???, zata iya yuwa kaine d'an uwa???. dan ALLAH mu gyara please & please, muyi amfani da damarmu kafin ta kufce mana, (kullu nafsin za'ikatul maut, kowane rai saiya d'and'ani mutuwa, ubangiji bai turo maka date d'in da rundunar mala'iku zasuzo d'aukar rayin nakaba,? mutuwa bata kwankwasa k'ofa, batada wata alamar yanda zatazo ta riskeka, kana tafiya ne, ko kana barci, ko kana salla, ko zaune, ko kana hira, ko kana aikata wani sa6o, ko kana wani abin alkairi?, ya ALLAH ka d'auki ruhinmu muna masu imani agareka da tsoranka, ALLAH ka gafarta mana, kamana maganin abinda muka Sani da wandama bamu saniba._
_ina rok'on dukkan Wanda na 6atamawa a yayin wannan rubutun ko kafin shima dan ALLAH Ya gafarceni, nidai na yafema kowa._???
*_duk masoyina na gaskiya Dan ALLAH inason yasakani a ddu'arsa ta cikin azuminnan koda sau d'ayane, idan munada Rabon haihuwa adunaya nida mijina ALLAH ka azurtamu da samu masu albarka cikin sauk'i da rahamar ubangijin talikai, idan ba alkairi bace agaremu ALLAH kasamana hak'uri da juriyar azuciyata???, ALLAH kayaye mana dukkan damuwarmu baki d'aya._*???
Dan ALLAH ko sau 1 yane kar'a manta dani???
Amin afuwa zan rage groups saboda yawan groups d'in suna cimin data wlhy, idan nayi sub na wata d'aya ko sati bata yimin take k'arewa??.
Ngd sosai, ALLAH yabar zuminci, ALLAH yasa munada rabon sake had'uwa a bayan salla, ALLAH ka kar6i ibadunmu baki d'aya. yabamu juriya da hak'urin ibadar dake tunkaromu nanda kwana 1??.
Happy Ramadan Advance??????????
Binyn Ku Ce dai??
Writer??
*Abdul-maleek bobo!!*
*Auren k'addara ko biyayya!?*
*Ban saketa ba!!*
*Ciki da gaskiya...!!*
*Karayar arzeek'i!!*
*k'anwar uwace ko kishiyar uwa!?*
*Kukan krciya...!!*
*Ni da Aminiyata!!*
*Nawaff!!*
*Rashin Sani!!*
*Raina kama.....!!*
*Sabon Al-amaree!!*
*Sanadin bikin salla!!*
*Siyasa ko k'abilanci!?*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*???
Plss dan allah part 2 Raina kama kaga gayya bai fita bane nayi serch ban samuba
ReplyDelete