Washe gari da safe da wuri su Sanah suka tashi,
suka gyara gidan ko'ina yayi fesss,
koda Mamu ta fito k'anshin bonar turaren wuta ne ya daki hancinta,
da sauri ta k'araso parlor'n dan ganin meke wakana,
ganin ko'ina tsaf ya sata tsayawa cak,
cike da mamaki take bin ko'ina da kallo,
"good morning Mamu, suka fad'a tare suna dariya,
juyowa bayanta tayi inda taji yo muryarsu,
fesss suma ta gansu sunyi wanka,
cike tsantsar mamaki Mamu tace " wa yayi duk wannan aikin?
Suna dariya suka amsa da mune Mamu,
" ku ne?
Tace, cikin mamakin,
"yes Mamu, mu mukayi komai,
dan ma bamu iya had'a breakfast ba,
da sai dai ki tashi ki ganshi jere a dinning table,
cikin mamaki Mamu tace "ikon Allah,
ku ce yanzu dai kun girma kunyi hankali, kun san meya kamata?
" Sosai ma Mamu, cewar Khulud,
"waya koya muku duk wannan aikin?
"Aunty Halan, cewar Sanah,
shiru Mamu tayi na wani lokaci kafin tace " wacece kuma Aunty Halan?
"Wacce muke wajenta ce a makaranta,
ita keyi mana komai, bata barin kowa ya tab'a mu,
"kai amma baku da kirki, amma shine da muka je visiting baku kirata mun gaisa ba?
Sanah tace " murnar ganin ku tasa muka manta,
itama sai da tace meyasa bamu kirata ta gaida ku ba,
Mamu tace " gaskiya dai bamu kyauta ba kam,
"masha Allah cewar Abbu yana saukowa daga samansa,
da gudu Khulud da Sanah suka fad'a jikinsa,
"good morning Abbu,
shafa kansu yayi yana murmushi yace " Alhamdulalillah,
how was your night?
Ya tambaye su, "Alhamdulalillah suka bashi amsa,
Mamu dake tsaye tace " ka ganni nan cike da mamakin yarana,
Abbu yace " mamakin me?
"Mamakin canzawar su mana,
kalli gidan fa gaka yadda suka gyara ko'ina yayi fesss,
parlor'n yabi da kallo yana mamaki shima yace " wai su suka yi duk wannan?
"Eh Mamu tace, kansu ya kuma shafawa yace " Alhamdulalillah yara na sun girma ko?
Sanah tace "eh Abbu, damma bamu iya girki ba da har breakfast sai dai ku tashi ku iske mun gama,
"wannan aikin Mamunku ne ta koyar da hazik'an yaranta girki,
Abbu yayi maganar yana kallan Mamu,
dariya tayi tace " ai dole ma na fara koya musu girki daga yau,
dan nan gaba kad'an duk masu aikin gidan nan sallamar su za'ayi,
Abbu yace " idan aka sallame su suwaye zasu aikin?
"Ina fatan dai ba yara na za'a d'orawa hidimar kula da gidan ba?
Mamu tace " to in ba su ba suwa?
Abbu yace " aiko tun wuri ma ki nemi masu yi miki aiki dan baza'a mayar min da yara bayi ba,
yayi maganar yana dariya,
Mamu tace " gani da 'yan mata har biyu zan tsaya ina d'aukar masu aiki,
suna samin ciwon kai?
"Duk abinda nake so nasan 'yan mata na zasuyi min ko?
Ta k'arasa maganar tana kallan su,
da sauri suka ce " yes Mamummu,
dariya Abbu yayi yace " wato kun gwale ni, kun bi bayan Mamun ki ko?
Khulud tace " haba wane mu, mu gwale Abbun mu guda,
kawai dai muma muna san mu taimaka muku ne,
dai-dai gwargwadon k'arfin, Aunty Halan tasha ce mana duk d'an dabaya tausayi da taimakon iyayensa,
bazai tab'a cin nasara a rayuwarsa ba,
kullum yana cikin wulak'anta da tab'ewa,
ajiyar zuciya Abbu ya sauke yana kallan Mumu yace " gaskiya ya kamata muga Halan d'in nan,
Mamu tace " gaskiya kam,
hanyar fita Abbu yayi Mamu tabi bayan tana cewa " bazaka tsaya kayi breakfast ba?
"Inda anyi niyyar bani da antashi anyi da wuri,
kin dai ga hazik'an yara na, na neman koya miki yadda akeyi idan ke baki iya ba,
yayi maganar yana murmushi cike da wasa,
dariya tayi tace " oh! abin gori ya samu fa yanzu,
har bakin motarsa ta raka shi kana ta dawo gida,
tare dasu Sanah suka shiga kitchen suka had'a breakfast,
ta nunnuna musu duk abinda ya kamata,
da rana ma daza'a girka abincin rana,
tare suka shiga kitchen tana koya musu,
bayan sallar la'asur suka tafi islamiyya.
A islamiyya sosai k'awayen su sukayi murnar ganin su,
dan duk cikin su babu wad'anda aka kai boarding school sai su,
yara suka zagaye Oga Sanah tana basu labarin boarding,
sai zuba take, yayinda Khulud tayi shiru kawai ta zuba mata ido,
dan ita bamai san yawan magana bace,
ranar dai kam haka suka taso babu wani karatu da sukayi sai labarin boarding school kawai da Sanah tayi ta basu,
suna komawa gida suka iske Mamu a parlor,
da murna ta tare su, suka fad'a jikinta,
tace " maza aje a cire uniform,
a huta, kuje ku gaida Jujunku kuzo mu d'ora abincin dare,
Khulud tace " ba wani hutu da zamuyi, bari kawai mu cire uniform mu gaido Juju sai muzo muyi girkin,
"to maza yaran kirki cewar Mumu,
bedroom d'in su suka shiga suka shire uniform d'in,
"Mamu mun cire bari mu gaido Juju mu dawo yanzu,
"sai kun dawo, tace.
A kitchen suka iske Juju na aikin abincin dare,
da sallama suka shiga, fuskarta d'auke da fara'a ta amsa musu,
tana cewa " 'yan boarding sai yanzu aka tashi?
"A'a Juju mun tashi tun safe, munje islamiyya ne,
tayi murmushi tace " masha Allah,
ana dai karatun sosai ko?
"Eh, Juju muna yi sosai, cewar Sanah,
kana ta cigaba da cewa " Juju bari mu tayaki girkin,
"a'a na yafe kuje ku taya Mamu,
Khulud tace " ai tare muke yin girki da ita, yauma tare mukayi breakfast & lunch,
dariya Juju tayi tace " oh su Mamu manya, wato harta fara mayar da yaran ta 'yan mata?
Didi dake zaune a parlor yana karatun jarida yace " ai gwamma hakan kinga sai tayi musu aure da wuri,
dayake basu kula dashi ba,
suka juya da sauri suna cewa " lah Didi dama kana zaune a parlor,
muka wuce bamu kula da kai ba?
"Ina fa zaku kula dani hankalin ku nakan Jujunku,
dariya sukayi suna fad'awa jikinsa,
suka ce " ina yini Didi?
Kansu ya shafa, kana yace lafiya lau, yaran Abbu,
ya Abbun naku da Mamu?
"Duk muna lafiya, Khulud tace " bari mu tafi gida,
Mamu nacan na jiran mu, girki zamuyi,
tunda nan baza'a barmu muyi ba,
tayi maganar tana kallan Juju tana dariya,
Juju tace " ita da taga zata iya cin jagwalgwalanku sai taci,
amma ni da mijina bamu iyawa,
dariya sukayi Khulud ta rik'o hannun Sanah tana cewa " zo mu tafi kinji my Sanah,
tunda basu iya cin girkin mu,
dariya Didi da Juju sukayi suna bin bayansu da kallo.
Da daddare bayan sun gama girki sun jere a dinning table,
Idrak da Aarib,
Ziyad da Zafran suka shigo tare duk su hud'un,
zama sukayi akan sofa, Sanah da Khulud suka fad'a jikin su,
cike da shagwab'a Sanah tace " Yaya kace fa zaka kai mu yawo ni da my Ulud,
murmushi yayi yana k'ara kwantar da kanta ajikinsa yace " sorry Auta na manta ne,
amma ku shirya gobe zan kai ku in sha Allah,
tsalle suka farayi cike da murna,
Abbu da Mamu suka fito tare fukarsu d'auke da murmushi,
gaba d'ayan samarin suka zube suna gaida iyayen nasu,
suka amsa cikin walwala,
Abbu ya kalli Sanah da Khulud yace " murnar me 'yan matan naki suke yi haka?
Yayi maganar yana kallan Mamu,
tace " ina zan sani ne, tayi maganar cikin sanyi tana kallan su,
cike da tsantsar so da k'auna,
kana ta kalle su tace " 'yan matan Mamu murnar me akeyi haka?
Khulud tace " Yaya Aarib da Idrak ne zasu kai mu yawo gobe,
Abbu yace " uhnmmm 'yan gatan Yayyan su,
zama sukayi suka duka akan dinning table,
suna cin abincin cikin farin ciki,
Abbu ya kai spoon d'aya bakin sa yace " uh uhn uhn carkwad'i wayayi girkin nan?
Da sauri Sanah da Khulud suka ce mune Abbu,
Abbu yace " wai badai dad'i ba, tunda nake ban tab'a cin abincin mai dad'in na yau da Yara na suka girka ba,
Mamu ta kalle su tace " oh! kuji k'arfin hali,
daga koyo kuma sai ku zak'e kuce ku kukuyi?
Sanah ta kalli Khulud tace " my Ulud, waya gyara kayan miya?
Khulud tace " mu ne mana,
Sanah ta kuma cewa " waya yanka albasa, ya wanke shinkafa, ya zuba maggi da gishiri?
Khulud tace " mu ne, tana dariya,
" waya rink'a kula da girkin?
"Mu me,
" waya kwashe ya zuba food flask,
ya kuma shirya dinning table?
Khulud tace " duk mune my Sanah,
Khulud ta kalli Abbu da Mamu da Yayyansu tace " to yayi girki?
Duk sukayi kana suka ce " Sanah da Uludinta,
bayan sun gama cin abincin Sanah ta kama hannun Khulud zasu fita,
Mamu tace " ina kuma zaku?
Sanah tace " wajen wad'ancan tsofaffin da suka k'i mutuwa har yanzu,
Abbu ya zaro ido had'i da cewa " uwaku! yana yi musu dak'uwa,
" iyayen namu ne tsofaffin da suka k'i mutuwa?
Khulud tace " Abbu ko sun mutunne bamu sani ba?
"Uwaku cewar Mamu tana dariya,
Sanah tace " ina fa zasu mutu my Ulud, bayan suna jin dad'in duniyar dan na lura ma jin kansu suke yi kamar samari sa'annin su Yaya,
Abbu yayi kwafa yana dariya yace " Ziyad muk'o min yaran can,
da gudu suka fita suna dariya,
washe gari sosai yakai su Sanah yawo, har da su shopride ya kai su kallo,
daga nan ya wuce dasu gidan zoo da rockzy,
da zasu dawo ya kai su cin shawarma da bugger da ice cream,
sosai suka ji dad'in fitar su,
haka hutun su Sanah ya k'are, Mamu tana koya musu abubuwa da dama,
musamman a b'angaren girki,
da kwalliya,
kasancewar Didi d'an k'aida yasa dole sai da aka mayar da su Khulud ranar Sunday da aka koma school,
Sanah manne a jikin Aarib tana ta kuka had'i da zuba masa shagwab'a,
dayake duk cikin mazan sunfi d'asawa dashi sosai,
Khulud ko babu ruwanta, sai Zafran daya rik'e hannunta.
Sir Moli nakan staffroom step zaune,
ya hango su Sanah, yaga yadda ta mannewa Yayanta tana kukan shagwab'a,
shi kuma sai wani lallab'ata yake yi,
yaga Khulud ba ruwanta babu abinda ya dame ta ma,,
aiko Sir Moli ya k'ulu, yazo har wuya,
tsoki yaja ya mik'e ya shige cikin staff yana mita,
"ashe dole yarinyar tayi fitsara da rashin kunya,
tunda an riga an gama sangartata a gida,
shiyasa take rawar kai,
shegiya! ya fad'a yana kuma jan tsoki mtswwwww,
Zafran ya kalli Khulud yace " ina Auntyn taku take?
"Saboda Abbu yace mu tabbatar mun ganta,
" Allah yasa dai ta dawo, amma bari naje na kira ta cewar Khulud,
ta juya zata tafi taji muryar Halan na kwala kira dai-dai lokacin dasu ma motar su take shigowa cikin makarantar,
da hanzari Halan ta bud'e motar ta fito,
da gudu Khulud ta nufe ta had'i da fad'awa jikinta,
cikin murna Halan ta rungume ta,
a hankali ta zame jikinta had'i da cewa " ina our Sanah?
Khulud tace " gata can tana ta kuka,
"kuka kuma cewar Halan?
Tana bin inda Khulud ta nuna mada kallo,
mik'ewa tayi had'i da rik'e hannun Khulud ta nufi inda Sanah take,
suna k'arasawa Khulud tace " Aunty Halan ga Yayyanmu ku gaisa,
sai lokacin Halan ta kula da su,
dan kwata-kwata hankakinta baika kansu ba,
tana murnar ganin su Sanah,
cikin nutsuwa da sanyin murya tace,
" please kuyi hak'uri ban kula daku ba, sun d'auke min hankali,
ina yinin ku?
Tayi maganar tana murmushi,
duk suka amsa banda Ziyad daya kafeta da ido tun ganinta,
ta kalle shi tace " ina wuni?
Gaba d'aya hankalinsa ya tafi dan haka baiji ta ba,
ta kuma cewa " ina wuni?
Had'i da sunkuyar da kanta saboda kallan da yake mata,
ganin ana nema aji kunya yasa Zafran saurin tab'a shi,,,
da sauri yayi firgit, had'i da cewa " kun kira ta ne?
Gaba d'aya suka saka dariya, amma banda shi daya kula da abinda yayi,
a hankali ya shafa kansa yana murmushi,
ta kuma gaida shi ya amsa fuska a sake,
Yayan Halan ya k'araso wajen fuskarsa d'auke da murmushi,
yace " ganin su Sanah yasa kin manta da ni?
"Lah ba haka bane, "to yaya ne?
Cewarsa yana dariya, fuska Ziyad ya had'e danshi a tsammaninsa ko saurayinta,
Halan tace " ga Brother na ku gaisa,
da sauri Ziyad ya saki fuska yana murmushi, ya mik'a masa hannu suka gaisa,
su Khulud ma suka gaidashi, ganin har lokacin Sanah na jikin Aarib yasa Halan cewa " Oga rigima sauko,
Zafran yace " ashe kuma ana d'an tab'a muku halin?
Murmushi tayi batare datace komai ba,
Sir Moli ya lek'o ta window ganin har lokacin Sanah na mak'ale a jikin Aarib,
yasa shi jan tsoki had'i da cewa " shegiya,
exchanging phone numbers sukayi tsakanin Yayan Halan dasu Ziyad,
Ziyad ya ciro bandir d'in 2 hundred naira na 20k,
ya mik'awa Halan,
kai ta girgiza tace " ka barshi na gode,
yace " meyasa?
Tace " haka nan bakomai,
yace "ba kyau mayar da hannun kyauta baya ba fa,
murmushi tayi kana tace " ai nima ba mayarwa nayi ba,
tayi maganar kanta a k'asa,
yace " to me kikayi idan ba mayarwa kikayi ba?
Murmushi kawai tayi batare datayi magana ba,
yace " wannan kyautar ba daga ni bane,
balle kik'i k'arb'a daga Abbu ne,
murmushi tace " to na karb'a tunda daga Abbu ne,
amma gashi nan ka je min,
zan karb'a wata rana,
babu yadda basuyi da ita ba amma tak'i amsa fur,
hakan ya k'ara tabbatar musu daga gidan mutunci da tarbiyya take,
suka kuma k'ara ganin k'imarta,
kana suka taf, bayan sunyi sallama.
Bayan sun koma gida Abbu ya tambaye su sunga Halan,
Ziyad yayi saurin cewa " eh Abbu yarinyar nada hankali da tarbiyya,
Zafran yace "ai kayi saurin bada amsa mana,
Abbu yace " ya aka yi ne?
Aarib yace " ai inaga dai Abbu surukar ku ma zata zama,
Ziyad yayi saurin kai masa duka,
ya goce yana dariya, Didi yace " kai karku damar man d'a,
Juju tace " kai masha Allah, amma gaskiya naji dad'in hakan,
dan daga jin yarinyar 'yar mutunci ce,
duba da yadda ta canja su Sanah a term d'aya kawai,
"ai damma baku ganta ba, wallahi ta had'u sosai gata da nutsuwa,
cewar Aarib,
hannun Zafran Ziyad ya rik'o suka fita,
iyayen nayi mishi dariya, bayan sum fita Ziyad yace " wallahi ina san yarinyar nan,
dan haka ma duk week sai naje visiting,
Zafran yace "kai mutuna irin wannan rik'e wuta haka,
Ziyad yace " ai dole.
Washe gari Monday, bayan anyi assembly kowacce students ta koma class,
bayan an tashi daga class Sir Moli ya koma office d'insa,
yana k'ok'arin kwanciya idansa ya sauka akan voice recorder d'insa,
wacce shi yama manta da ita,
da sauri ya mik'e ya d'auko had'i da kunnawa yana saurara,
ai tun kan Sir Moli ya gama saurara duk ilahrinsa jikinsa ya d'auki kerrrma da b'ari,
idansa suka koma pure red,
sai da ya gama ji kaf,
jikinsa na b'ari saboda tsananin b'acin rai,
zuciya ta kawo shi har wuya,
ransa ya kai k'ololuwar b'aci,
zuciyarsa na tafasa gami da azalzala.........
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
🔟
Da sauri ya fito daga office d'insa,
har yana tuntub'e, akan step ya tsaya yana hanga yarinyar da zai samu ya aika kiran su Sanah,
daga can nesa ya hango wata yarinyar tana k'ok'arin shiga Hostel get,
da k'arfi ya d'aga murya yace " hey,
yarinyar ta juyo a d'an tsorace,
ganin Sir Moli tsaye yasa jikinta d'aukar kerrrrma,
da sauri ta k'araso ta tsuguna a gabansa,
gaidashi take amma bai iya amsawa ba,
saboda yadda zuciyarsa ta gama jagulewa,
yace " ke ajinki nawa?
Jikinta na tsuma tace " JSS2,
yace " kin san Sanah Hamraz?
Ya tambaye ta idanshi na kanta,
cikin kerrrmar jiki tace " eh,
mamaki ne ya kama shi sosai jin ta santa,
kamar zai share sai kuma yace " ya akayi kika san su,
bayan ba class mate d'inki bane?
Jikinta na rawa tace " kowa ai ya san su a makarantar nan,
" saboda me?
Ya kuma tambayar ta a tak'aice,
yana yi mata tambayar ne dan yana san samun k'arin hujjar cin uban Sanah,
"tun ranar da suka daki Aunty Era suka zama popular's,
"Ok, maza jeki kira min su yanzu,
yayi maganar yana komawa cikin office d'insa,
da sauri yarinyar ta mik'e jiki na rawa tayi hanyar hostel,
a zaune ta iske su suna hira da Halan,
yarinyar tayi sallama, kana ta kalli su Sanah tace " Sir Moli na kiranku,
k'irjinta ta dafe had'i da zaro idanuwa waje,
tace " mu kuma?
Yarinyar tace " eh ku yace,
Halan ta kalli yarinyar tace " waya ce ku kira masa?
"Sanah Hamraz ta bata amsa,
ido Sanah ta kuma zarowa tace " na shiga uku me kuma nayi masa?
Ta tambayi yarinyar, tace " ban sani ba, ya dai ce kawai na kira masa ku,
Halan tace " ya kika ga yanayinsa?
Yarinyar tace " ban kula da fuskarsa ba dan kai na duk'e yake har ya gama yi man magana,
Yarinyar ta fad'i haka ne saboda gudun abinda zai je ya dawo,
dan tasan halin Sir Moli sarai,
Halan tagai dubanta ga Khulud ,
da jikinta ya fara rawa tun jin kiran da Sir Moli yake yi musu,
tace " me kuma kuka kuma yi masa?
A tsorace Khulud tace " wacce ni, mai kai ba gashi,
ai sai dai ki tambayi Oga,
Halan ta kalli Sanah tace " yau kuma mai kika tarowa kanki?
Kamar zatayi kuka tace " wallahi Aunty Halan tunda muka dawo ban sashi a ido na ba,
balle nayi masa wani laifin,
idon Halan na kanta tace " kin tabbatar?
Kai Sanah ta gyad'a mata, cikin sanyin jiki suka mik'e had'i da zarar hijabansu,
Halan tace " Allah dai yasa alkhairi ne,
Sanah tace " kayya Aunty Halan kema kin san a kira mutumin nan babu alkhairi,
Halan tayi murmushi, tace " ku irink'a maimaita " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
ku kuma d'auke numfashinku,
ku karanta, Qulhuwallahu Ahad,
sannan ku maido da numfashinku ku karanta Nasi da Falak'i,
da لا حول ولا قوه الا بالله العلي العظيم,
har ku isa gare shi, in sha Allah duk girman laifin da kuka yi masa Allah zai d'ora ku a kansa,
cikin sanyin murya Khulud tace " to Aunty Halan mun gode,
kamar zata fasa ihu Sanah tace " wai ni meye dalilin kiran dayake mana?
Halan tace " o! o! ni da nake nan tare daku ina zan sani?
" Idan kinje can sai ki tambaye shi,
ko idanki ya gane miki,
batare dasun kuma cewa komai ba suka fita,
addu'o'in da Halan ta gaya musu suke ta maimaktawa,
Moli nacan zaune kamar zai fashe saboda tsananin zugin da zuciyarsa keyi masa,
minta d'aya minti biyu sai da duba agogo had'i da jan tsoki,
kishingid'a yayi ya rufe idanta,
yana sauraren yadda zuciya ke azalzalarsa gami da bugawa da sauri,
a k'ofar office d'in suka ci burgi,
kowa yana kallan kowa still they're praying,
Sanah tace " kiyi sallama,
Khulud tace " inyi sallama kamar yaya?
Tayi maganar cikin rad'a gudun kar ya ji,
Sanah tace " amma dai kin san idan ni nayi bazai amsa ba ko?
"Sanin kanki ne shanya mu zayyi,
batare datace komai ba ta matsa kusa da k'ofar tayi sallama,
batare daya amsa sallamar ba yace " in,
a tak'aice, Sanah ta tab'e baki had'i da cewa " sai kace karifi ayi maka sallama kak'i amsawa,
mstwwwwww taja tsoki can k'asan ranta,
durk'usawa sukayi a gabansa,
Khulud tace " Sir ina wuni?
Batare daya bud'e ido ba yace " Alhamdulalillah,
Oga Sanah ko kwata-kwata bata da niyyar gaidashi,
Khulud ta d'an tab'a ta da hannunta tace " ki gaida shi,
baki ta turo ta kau da kanta gefe,
hakan ya tabbatarwa Khulud bata gaida shi,
sun kai 7 minutes batare daya,
motsa ba balle ya bud'e idansa ko yayi musu magana,
Sanah na k'ok'arin yin magana taga ya mik'a hannunsa ya d'auko voice recorder,
yayi playing, still idansa na rufe,
suna fara saurara Sanah tayi baya zata fad'i tana daga tsugunnan,
dab'assss ta zauna a k'asa jiki ba kwari,
tun kafin su gama sauraran voice d'in suka fara gurzar kuka,
kamar ransu zai fita, while duk ilahirin jikin su na kerrrrma,
da tsuma yake, tsoro da firgici ya gama kama su, dan sun san babu mai kwatar su yau a hannun Sir Moli sai Allah,
har record d'in ya k'are Moli bai motsa ba,
yana yadda yake, idanshi rufe,
yana daga hakan yace " that's good,
"hmmmmmm yace yana sauke ajiyar zuciya,
"ashe ni k'aramin d'an iska ne kice babbar?
Yayi maganar still his eyes closed,
"shege d'an iska mai girman kan tsiya, miskilin banza,
ya maimaita under his breath,
"please ina san nasan girman kai da muskilnaci, iskanci da ja'iranci, kwartancin danayi Malama Sanah?
"Ina san sani kiyi man bayani in briefly,
yayi maganar still bai bud'e idan shi ba,
batayi magana ba sai sautin kukan su dake tashi,
"ashe ni munafuki ne, kuma shege, marar aikin yi sai kwanciya?
Ya kuma tambayarta,
mai lab'ewa a uncompleted building,
yana kurb'e-kurb'e da zuk'e-zuk'e ko?
" Mugu azzalumi still ko?
"wallahi idan har kina san na kyale ki sai kin yi man bayanin wad'annan halayen da kika danganta ni dasu,
bayan na tabbatar bani da alak'a da ko d'aya daga cikin su,
ina saurarenki yi min bayanin,
kwartanci, iskanci, ja'iranci, muskilnaci, munafurci, girman kai da zaluncin nadayi miki,
kafin mu zo kan shege, shaye-shaye, zuk'e-zuk'e da kurb'e-kurb'e,
shiru duk suka yi, babu abinda suke yi sai kuka,
jin shiru yasa shi bud'e idansa a hasale ya zabura ya daka musu gigitacciyar tsawa,
" ke dan kan uwarku bada ku nake ba?
Idonsu duk suka d'ago suka kalle shi,
cikin matsanancin tashin hankali da tsoro,
suna had'a ido da yaran yaji tausayin su ya saukar mishi a rai,
musamman dayaga yadda suke kukan mutuwa,
ji yayi zuciyarsa da ransa sunyi masa sanyi,
duk wannan zafi da k'unar ran dayake ji sun gushe,
sai ma matsanancin tausayin su daya mamaye ruhi da gangar jikinsa,
ajiyar zuciya ya sauke yace " shut up!,
duk sukayi shiru saboda tsoro,
ido ya k'ura musu na tsayin lokaci kafin yace "ku tashi kuje,
cike da mamaki suka d'ago suna kallansa,
yace " badaku nake ba?
Da hanzari suka mik'e jiki na rawa zasu fita har sun kai bakin k'ofar fita yace " don't be a greedy girls,
you know greedy pupils will pay for their sins,
jiki na rawa suka amsa da " to!,
bai k'ara bi ta kansu ba ya koma ya kwanta,
yana mamakin abinda yaji yanzu,
ya kuma kasa koda yi musu kallan banza.
_K'ARFI DA TASIRIN ADDU'A KENAN, DUK MAI YINTA BAI TAB'EWA KO WULAK'ANTA,_ _MUSAMMAN DAGA BAKIN YARAN DA BASU BALAGA BA, SABODA ALLAH YACE " DAN YARA K'ANANA DA DABBOBI AKE YI MANA RUWAN SAMA,_
_SANNAN ADDU'AR YARA BATA DA HIJABI GA UBANGIJI, SHIYASA WASU SUKE TARA YARA SUNA YI MUSU ADDU'A_
A bakin hotel get suka iske Halan tana jiransu,
suna ganinta suka fad'a jikinta suna sakin kuka,
a kid'ime ta d'ago su tace " lafiya,
dukan ku yayi?
Kai suka gyad'a mata a tare, tace " me kuka yi masa?
Cikin kuka Khulud ta zayyane mata duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,
ajiyar zuciya ta sauke jin bai dake su ba,
ta mayar dasu jikinta ta rungume,
Sir Moli sai juyi yake cikin dare ya kasa bacci,
babu abinda yake tunani sai irin words d'in da Sanah ta jefe shi da su,
shi abinda yafi d'aure mishi kai k'arfin halin yarinyar da dakewar zuciyarta,
murmushi yayi lokacin daya tuno,
wai irin su ne masu lab'ewa a uncompleted building suna kurb'e-kurb'e,
da zuk'e-zuk'e, murmushi ya kuma yi had'i da girgiza kansa.
A week later Ziyad ya dawo visiting,
Sir Moli ya tarar akan staff zaune,
Ziyad ya mik'a masa hannu suka gaisa suna yiwa juna murmushi,
a nutse Moli ya tambayi Ziyad wad'anda ya zo gani,
Ziyad yace " Sanah Hamraz da Khulud Rawan,
& Halan
murmushi Sir Moli yayi yace " Bother su ne?
Ziyad yace " same Mom & Dad,
ka san su ko?
Cewar Ziyad,
"sosai, Moli ya bashi amsa yana murmushi,
Ziyad yace " ah Sanah ana tab'a halin anan ma kenan?
Ya fad'a yana murmushi, Moli ya zuba mishi ido,
"hmmm wato haka take kenan har a gida, shegiya 'yar iska,
ya fad'a cikin ranshi,
Ziyad yace " nasan dama za'a rina ai dama mai hali baya tab'a fasa halinsa,
murmushi Moli kawai yayi batare dayace komai ba,
head girl ya aika ta kira su,
shi kuma ya shige cikin staff yana mamakin nutsuwa da kamalar Ziyad.
Da gudu Sanah da Khulud suka k'araso, suka fad'a jikinsa,
a nutse Halan ta k'araso, tana murmushi,
sai da ya gama magana da wasa dasu Khulud kana yace " maza ku d'auki kayan kukai hostel,
kuma idan kun tafi karku dawo,
sai da aka sha daru da Sanah kana ta tafi tana kuka,
shima sai da yace mata idan bata daina rigima ba bai k'ara zuwa,
kana ta tafi,
bayan sun tafi ya karkata gaba d'aya hankalinsa ga Halan,
har k'asa ta duk'a ta gaidashi,
ya amsa cike da fara'a da tsantsar farin cikin tarbiyyarta,
a hankali ya kira sunanta " Halan!,
cikin nutsuwa ta amsa "na'am,
yace " zan tambaye amma please ki sanar da ni gaskiya,
tace " in sha Allah,
sai da ya nisa kafin yace " anyi miki miji?
Kanta ta duk'ar kanta k'asa kana tace "a'a,
yace " kina da wanda kike so?
Ta kuma cewa "a'a,
da k'arfi ya sauke ajiyar zuciya,
"Alhamdulillah yace,
kana yaci gaba " magana ta gaskiya Halan,
tunda na d'ora ido na kanki naji kin kwanta min,
na kuma samu nutsuwa dake,
abinda yasa ban zurfafa sosai ba,
sai dan gudun ko kina da wanda kike so,
ko wanda zaki aura, kuma nasan nema cikin nema haramun ne,
magana ta gaskiya ina sanki ya fad'a kan shi tsaye,
tunda ya fara magana ta duk'ar da kanta k'asa bata d'ago ba,
har ya dasa aya, shiru yayi had'i da kafe ta da idonsa dan ganin reaction d'inta,
ganin tana murmushi ne yasa shi fahimtar ya samu karb'uwa,
hira yayi ta zuba mata, ita sai dai ta bishi da eh ko a'a,
kud'i ya bata amma tak'i karb'a,
babu yadda bayyi ba, dole ya hak'ura.
A kwana a tashi ba wuya wajen Allah,
kamar yaune su Sanah suka dawo hutun first term gashi yanzu har sun kusa gama second term exam,
while Ziyad ya zo a term d'in waje 10 tyms,
sosai soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Halan da Ziyad,
har maganar takai ga iyaye, an tsaida magana akan data gama secondary school za'ayi bikin su,
ranar hutu Sanah da Khulud da Halan sun sha kuka sosai,
kasancewar zasu bar Halan a makaranta,
zaman vocation,
koda suka koma gida hutu Mamu d'orawa tayi daga inda ta tsaya wajen koyar dasu girki da sauran abubuwa,
ranar da hutu ya k'are sosai Sanah tayi ta mak'alewa Aarib,
sai da kyar aka raba su, tana risgar kuka,
washe Monday first week na third term,
akayi assembly kamar yadda aka saba,
kowacce students ta kama hanyar class d'in su,
class d'in su Sanah yayi shiru dan basu da yawa wad'anda suka dawo,
dukkan su sunyi shiru cike da tsantsar kewar gida,
ganin haka yasa Sanah tashi ta cire hijab d'inta taci d'an mara dashi a k'ugunta,
ta hau saman seat ta fara kid'a,
abinka da wad'anda ke cikin kewa,
ga kuma k'uruciya na damunsu,
ai ko suka zage suka shiga tik'ar rawa da wak'a, while Sanah naci gaba da kid'an tana rawa daga zaune saman seat,
Khulud na zaune bata ko motsa ba, tana ta dariya,
Sir Moli na SS2 yana teaching,
yaji kid'a na tashi, his face with surprise,
saboda yaune first time daya soma jin maka makamancin haka a school d'in,
a hankali tako ya biyo inda yake jin sautin na tashi,
jin sautin na fitowa daga JSS side,
yasa mamkinsa k'aruwa sosai,
bai tsinke ba sai da ya ganshi a k'ofar JSS1 class,
a hankali ya shiga, ganin Sanah ta tara yara tana yi musu kid'a da wak'a,
yasa shi tsayawa cike da tsantsar mamaki yana kallan ikon Allah,
a ransa kuma yana mamakin wannan wacce irin yarinya ce?
Sosai kid'a da wak'a ya d'auki zafi,
kwata-kwata hankakin su Sanah bai kai gare shi ba,
ya kai a k'alla wajen 15 minutes a tsaye yana kallan yadda Sanah ke zazzaga fitsara,
while Khulud na zaune a nutse tana bin su da kallo tana murmushi,
juyowar da Sanah zata yi idanta ya sauka akan Sir Moli dake tsaye hard'e da hannuwasa a k'irji,
cikin wani irin mugun zafin nama ta yunk'ura da niyyar guduwa,
yayi wuf ya rik'e ta, sai lokacin hankakin sauran ya kai ga Sir Moli,
kowacce ta koma seat d'inta ta zaune a matuk'ar tsorace jikinsu sai kerrrrma yake,
ajin yayi tsit,
tsawa ya daka musu " ku dan kan uwarku tun da kuka zo makarantar nan kun tab'a ganin anyi kid'a?
Duk suka ce " a'a,
" wa yasa ku kid'a da rawa yanzu dan ubanku?
Jikinsu na kerrrrma suka ce SANAH HAMRAZ,
"Idan tace ku shiga wuta zaku shiga?
"A'a,
" wallahi daga yau kuka kuma yi mana kid'a school sai naci kan uwarku,
yayi maganar while yana rik'e da Sanah gam a hannunsa,
tuni Sanah ta soma kuka, jikinta sai kerrrrma yake,
gaba d'aya tsoro ya gama cika mata ciki,
ji take kamar ta saki fitsari,
Khulud na zaune inda take cikin matsanancin tashin hankali da matsananciyar fargaba,
kuka kawai take dan tasan yau Sanah ta shiga ukku,
a fisace ya fita da Sanah, Khulud tayi saurin mik'ewa tabi bayan su,
jin taku a bayansa yashi juyowa,
tsayawa yayi cak ya zubawa Khulud ido,
" ke koma, yayi commanding nata,
shiru tayi tana kuka batare data motsa ba,
ya daka mata tsawa "ke dan uw.....
kasa k'arasawa gazin ta yayi, idansa ya runtse da k'arfi, kana ya bud'e yace " ki koma,
cikin kuka Khulud tace " please Sir kayi hak'uri, tare mukayi laifin ni da ita,
ba ita kad'ai ce tayi ba,
Sanah tayi saurin cewa " no Sir banda ita, ni kad'ai ce nayi laifin,
kafewa Khulud tayi akan harda ita,
while itama Sanah ta kafe banda ita,
kallan Khulud yayi yace " this is the last time da zance ki koma class,
Sanah tace " my Ulud idan baki san nayi fushi dake to ki koma,
tsawa ya daka mata "ke dan ubanki ubanwa yasa bakin ki,
shegiya 'yar iska fitsararriya,
yayi maganar yana matse hannunta dake cikin nashi,
kamar zai karyata,
tsananin azaba ne yasa Sanah sakin gigitaccen kuka,,
tana tsallen wuya,
cigaba da tafiya Sir Moli yayi rik'e da Sanah a hannunshi,
Khulud ta tsaya a inda suka barta tana kuka,
dan yadda taga idanshi, da yadda yake jan Sanah kamar zai b'alla ta,
yana tafiya a zafafe kamar mahaukaci tasan yau sai buzun Sanahrta..................... .
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣1⃣
Har cikin office d'insa ya shigar da ita,
"kneeling down, ya fad'a a tak'aice,
jikinta na rawa ta d'urk'usa bisa gwiwowinta,
zama yayi akan sofa, had'i da k'ura mata ido kusa 10 minutes batare dayace komai ba,
a hankali ya sauke ajiyar zuciya,
yace " ke wacce irin yarinya ce, mai taurin kai?
Shiru tayi bata ce komai ba,
"na dad'e ina tunanin halayya da d'abi'unki,
me yasa baki jin magana?
"Dan ubanki ke 'yar bidi'a ce?
Kai ta girgiza masa, yace " ida kika kuma girgiza man kai sai na kifa miki mari,
shegiya bakin magana nafiki?
Da sauri tace " a'a,
"ah gidan ku akwai club, ko kuna zuwa yawan club?
"A'a tace, tana cigaba da kuka,
"to shaid'aniya ce ke, ko shad'aici yasa ki yin kid'a?
"A'a ta bashi amsa tana kuka,
ganin yadda take kuka yasa shi cewa " dukanki nayi?
"A'a,
" to uban me kike yi ma kuka?
"Bakomai ta fad'a tana goge hawayenta,
"yanzu dan ubanki bidi'a kika san kawo mana makarantar, ko so kike ki lalata mana yara,
ki kangarar dasu kamar yadda kike kangarariya,
ko irin taki fitsarar kike san koya musu?
"A'a, dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa,
"shegiya kullum maganar ki kenan,
"Allah da gaske nake, ban k'arawa,
" 'a'a ai dole kema ki d'and'ana dukan Moli,
ya fad'a yana mik'ewa, direct kan table ya nufa ya d'auki dorinar da yake duka da ita,
(bulala),
Sanah na ganin ya d'auki bulala ta mik'e tsaye a kid'eme tana yarfa hannunta,
kuka ta fasa masa sosai,
"please kayi hak'uri Allah ban k'arawa,
tayi maganar still tana kuka.
Nufo ta yayi gadan-gadan rik'e da zafgegeyar bular a hannunsa,
baya tayi tana yarfa hannu, dan gani take idan ya dake da bulalar hannunsa,
mutuwa zatayi,,
cikin kuka tace " Allah ban san duka, idan ka dokeni mutuwa zanyi,
"baki san bugu amma kike iskanci da fitsara?
Yayi maganar while yana takowa gare ta,
"Allah na daina ban k'arawa,
"k'arya kike,
"Allah da gaske ban kumawa,
dan Allah karka dokeni, tayi maganar tana shaking head d'inta,
"ke kima yi min shiru dan wallahi sai na dake ki,
gwara ma ki motsu na dake ki huta,
jin ya rantse yasata increasing cry volume d'inta,
cikin sanyin murya tace " yanzu duka na zakayi?
Yace " kwarai kuwa ko zaki hana ne?
"A'a, amma dan Allah kayi min a hankali ba mai zafi ba,
"tab yau nake ganin zunzurutun rainin wayo,
wato sai ma kin ban instruction d'in yadda zan dake ki?
A'a, zata kuma yin magana taji saukar bulala ajikinta,
da k'arfi ta saka gigitaccen kuka,
lokaci d'aya ta rud'e ta kid'ime ta fita fita daga hayyacinta,
ta zama kamar mahaukaciya sabon kamu,
saboda tsabar tud'ewa ta cire hijabin jikinta tayi cilli dashi gefe,
bata gama hucewa ba, ya k'ara zuba mata d'aya,
zillo ta fara yi tana tsalle,
ya kuma zuba mata biyu a jere,
durk'ushewa tayi a k'arasa tana murk'usu da juye-juye,
dan kwata-kwata Sanah bata k'aunar abinda zai tab'a lafiyar jikinta koyaya ne,
bata san duka,
duk abinda tasan muddin tayi za'a dake taba yi,
idan ko taji ciwo kota yanke, duk k'ank'antar ciwon an shiga uku ranar a gidan,
dan ta rink'a tsalle da ihuun kuka kenan,
gata da shegen san jiki kamar mage,
yanzu zata lafe a jikin mutum,
a gida shiyasa tafi shiri da Aarib dan kullum tana jikinsa,
idan kaga Sanah ta zauna ita kad'ai to babu mutum ne a kusa da ita,
amma muddin akwai mutum duk k'ank'antarsa koda ta girmeshi sai ta lafe a jikinsa,
Sanah kam akwai san jiki da shegiyar shagwab'a,
tasan darajar jiki da lafiyarta sosai,
sai dai akwai bakin tsiwa da fitsara,
gata masifaffiya dan mafad'aciya sosai,
uwa uba kuma bak'ar zuciya,,
jikinta tabi da kallo taga duk inda bulalar ta sauka yayi ja,
wajen duk yayi rud'u-rud'u,
yayi jajir kamar garwashin wuta,
shima jikin nata ya kalla, yaga wajen yayi mugun yin jajir,
ganin ya d'aga hannunsa zai k'ara zuba mata,
yasa ta mik'ewa da sauri ta rik'e hannunsa da k'arfi,
tana tsalle "dan Allah kayi hak'uri Allah ban k'arawa, tayi maganar cikin gigitaccen kuka,
bin jikinsa da ta rirrik'e shi yayi da kallo,
hannunta d'aya na rik'e da hannunsa wanda ya rik'e bulalar,
d'aya hannun nata kuma ta cukuikuye shi ta rik'e shi gam,
ta shige jikinta ta rungume shi yadda bazai iya dukan ta ba.
K'ok'arin kwace kansa ya fara yi,
amma ina Sanah tayi mishi mugun rik'o,
jin zai kwace kansa yasa Sanah zubewa k'asa had'i dayin ihuuuu,
da k'arfi kamar yadda taga masu aljanu nayi,
ta zub'e k'asa wanwar,
tana k'ifk'ifta idanu, kamar gaske,
idan ka ganta saika rantse da Allah aljannun gaske ta tayar,
da sauri Sir Moli ya ja baya, amma babu alamar tsoro ko firgice a tattare dashi,
ganin yadda take harba k'afa tana yarfa hannu kamar mai farfard'iya ya sashi fita da sauri yayi waje,
Sanah na ganin ya fita ta mik'e da sauri ta dira ta window tayi hostel,
anan ma tabar hijabinta,
yarinya Sir Moli ya aika kira masa Halan da Khulud,
sannan yayi alwala ya shiga Masjid ya d'auko Qur'an,
at the same time Halan da Khulud suka k'arso,
"ku biyo ni, yace a tak'aice,
jikin su kerrrrma suka bi bayansa,
office d'insa ya shiga kai tsaye rik'e da Qur'an,
ganin babu Sanah babu dalilinta,
yashi yin tsaye sororo,
kan sofa ya zaune gami da dafe kansa,
cikin ransa yana mamakin yadda tayi yanzu kamar gaske,
dan shi tsakanin sa da Allah ya yarda da gaske ta,
a hankali suka shigo, suka tsuguna gefe jikinsu na rawa,
zaton su ko Sanah ta jawo musu wani abun kuma,
kallan su yayi kana,
yace " zan tambaye ku tabbatar kun gaya man gaskiya,
dan idan na bincika naga k'arya kuka gaya man,
wallahi sai naci ubanku,
"to suka ce cikin fad'uwar gaba,
" Sanah nada aljanu?
Ya tambaye su gami da kafe su da ido dan yaga reaction d'in su,
kallan juna Halan da Khulud sukayi cike da mamaki,
baki suka had'a wajen cewa "aljanu kuma wanne iri?
" Tambayar ku nayi, ku ban amsa bawai ku maido min tambaya akan tambaya ba,
Halan data gane abinda ya faru,
tayi k'asa fakai tana b'oye dariyarta,
Khulud zatayi magana Halan tayi saurin cewa " a'a, gaskiya tunda muke da ita bata tab'a tada aljanu ba,
amma bamu sani ba ko tana da su ko kum.......
" Ba doguwar magana na tambaye ku ba,
abinda na tambaye ku Sanah tana da aljanu eh ko a'a?
K'asa Khulud tayi da kanta tace " a'a gaskiya bata dasu,
duk wanda ya gaya kama k'arya yake ba gaskiya ya fad'a maka ba,
"good yace, yana mik'ewa ya fita batare daya ce komai ba,
yana fita Halan ta kalli Khulud tace " me kuma ya faru?
Tass Khulud ta fad'awa Halan duk abinda ya faru tun daga farko har k'arshe,
ajiyar zuciya Halan tayi tana kallan Khulud tace,
"inaga fa k'aryar aljanu tayi masa danta kwaci kanta,
ido Khulud ta zaro tace " what! aljanun k'arya ta tayar mishi?
Halan tace " bani da tabbas amma ina tunanin hakan,
dan nasan halin kayana,
ajiyar zuciya Khulud ta sauke cike da tsoro,
Sir Moli na fita direct Hostel get yaje da kansa ya tsaya k'ofar shiga,
ya tura wata yarinyar kiran head girl,
bata jima ba suka dawo tare, a tak'aice yace " duk inda Sanah Hamraz take ki nemo min ita yanzu,
yayi maganar yana gyara tsaiwar shi,
"Ok Sir, ta amsa, tana mik'ewa ta koma cikin hostel,
Sanah na dirawa ta window tayi hostel dan tasan ba damar Sir Moli ya shigo hostel kai tsaye,
tun daga k'ofar room ta fara kwalawa Halan da Khulud kira,
taji shiru, tana k'ok'arin jiyawa head girl ta isa,
batayi mata magana ba ta rik'e hannunta,
Sanah tace " Malama lafiya, zaki zo ki rik'e ni kina ja ba wani bayani?
"Kallanta Head Girl tayi cike da mamakin irin maganar da Sanah ta fad'a mata,
amma sai ta dake tace " in munje can kya gani,
tana jin haka ta gane sak'on Sir Moli ne,
dan haka ta fara k'ok'arin turjewa,
juyowa Head Girl tayi tace " wallahi zansa a d'aukar man ke aka kaiki idan baki tsaya ba,
baki ta turo had'i tana cewa " sai kace wata dabba ko wani kaya,
bata kula ta ba ta cigaba da janta,
HG na mamakin irin halin Sanah,
na rashin jin magana da taurin kai,
a ranta tace " hmmmm tun tana yarinya kafin ta balaga ta zama cikekkiyar mace ma kenan,
ina ga kuma idan ta girma, zan so ganin 'yan matancin yarinyar nan,
dan nasa akwai ganin ikon Allah,
suna isa Sir Moli ya damk'i hannunta yayi office da ita,
kwata-kwata babu alamar tsoro ko firgice a tattare da ita,
sai ma baki da taka buro tana harare-harare,
gami da gunguni, k'asa-k'asa,,
suna shiga office d'in ya saki hannunta ya zauna kan sofa,,
ganin Halan da Khulud a office d'in,
yasa ta runtse idanta da k'arfi,
ya kalle ta yace " sakin aljanun ne ya zo?
Ta bud'e ido tarr cikin nashi, ya mik'e yana d'aukar bulalar shi,
dan ya fahinci tana mugun tsoron duka,
tana ganin ya d'auki bulala ta zub'e k'asa tana tab'a baki zatayi kuka,
hannun ya d'ora akan lips d'insa,
yace " shhhhhhhhhhhh,
da sauri ta had'iye kukanta,
yace " kin san Allah idan baki san na doke ki toki kiran aljanunki suzo,
kuka ta soma tana cewa " Allah bani da aljanu dama k'arya nayi maka danna kwaci kai na,
dan Allah kayi hak'uri ban k'arawa,
"shegiya ga tsoro ga iskanci da fitsara,
ai 'yan iska fitsararru masu taurin kai da zafin zuciya basu saurin saduda,
ban hak'uri wuya yake yi musu,
"ni dai dan Allah kayi man hak'ura, Allah na daina,
"ba yanzu kika gama bada wani hak'urin ba?
"Amma few minutes tsakani kika kuma yin wani laifin,
cikin kuka tace " please kaban last chance yanzu,
idan na kuma yin laifi kayi man koma miye,
wallahi I promise ban k'ara yin laifi harna ban makarantar nan,
" are you sure you promise?
"Yes Sir, Allah idan na kuma kayi min komai kaga dama,
na yarda na d'auka, duk abinda kaga damanyi man kayi man,
murmushi yayi had'i da cewa " good, and keep it in your mind,,
I know one day you will pay for your promise,
kai ta gyad'a masa,
k'ura mata ido yayi wajen 10 minutes yana kallanta,
kana yace " tashi kije while idansa na kanta,
har ta kai bakin k'ofa, yace "Sanah cikin sanyin murya ya kira sunnan nata,
cak ta tsaya jin karo na farko a rayuwarta ya kira ta da real name d'inta,
a hankali ta juyo tana kallanshi ido cikin ido,
yace " kada ki tab'a raina matsayin tsoro,
lalle ki martaba matsayin tsoro,
wad'anda basa jin tsoro rashin tsoron su yakan jawo musu walaha da masifa, a rayuwa,
murmushi tayi tace " ya zaka ce bana jin tsoro Sir?
" Bayan yanzu ma ka gani da idanta,
yace " ni dai na fad'a maki, shawara ce na baki, nasan kuma ko gaba zata yi maki amfani,
murmushi ta kumayi tace " thank you Sir,
ido kawai ya zuba mata har suka fita,
while Halan na kallan su, deep down kuma tana cike tsantsar mamaki,
tana sak'e-sak'e kala-kala a ranta,
komawa kan sofa yayi ya kwanta had'i da lumshe idansa,
Bayan sun koma hostel sosai Halan tayi musu fad'a akan shiga case d'in teachers,
ta k'ara da basu shawarwari,,,
sosai jikin su yayi sanyi, Khulud ta kalli Sanah tace " please ki dai na kinji?
"Allah kwata-kwata ban san yadda yake yi miki,
tayi maganar wahaye na gangaro mata,
da sauri Sanah ta tashi daga inda take zaune ta koma kusa da Khulud,
tasa hannu tana goge mata tears d'inta,
itama kwalla na taruwa a idanta,
Khulud tace " please my Sanah karkiyi kuka,,
kukanta ta had'iye kana tace " to please kema karkiyi kukan kinji my Ulud,
wallahi bana san kukanki, bana k'aunar na ganki cikin damuwa,
ido Khulud ta zuba mata tana kallan yadda duk ta marairaice saboda tana kuka kawai,
cikin sanyin jiki da murya Khulud tace " my Sanah idan na mutu ya zakiyi?
Sosai Sanah ta zazzaro ido waje kamar zasu fad'o k'asa,,
tace " please ki bar wannan maganar,
inba so kike ki tada min hankali ba,
cikin sanyi Khulud tace " my Sanah kin san dukkan mai rai mamaci ne,
dole dukkan mu sai mun mutu,
sai mun d'and'ani zafin da rad'ad'in mutuwa,
ni dai abinda nake so idan na mutu ki rink'a yi man addu'a koyaushe,
ki zama mai sanyin hali, mai hak'uri da kawar da kai please,
a d'an zafafe Sanah tace " kina san tada min hankali ne?
Khulud tayi nodding kanta,
Sanah tace " ki na san na kafa miki kuka tun daga yanzu har safe?
Khulud tayi dariya tace " a'a Oga rigama,
tace " to kibar maganar nan please,
Khulud na dariya tace " na bari,
kasancewar wannan shine 3rth term, a wannan term d'in ana mugun repeating,
dan daga shi sai 1st term JSS2,
yasa Sanah da Khulud dagewa da karatu sosai baji ba gani,
Sanah da Khulud na tafiya, zasu koma hostel,
daga area class's,
Khulud ta kalli Sanah tana zaro ido had'i da ja baya,
Sanah ta kalle ta tace " lafiya?
Tayi maganar tana matsawa jikin Khulud,
da sauri Khulud ta ja baya tana kallan Sanah a tsoroce tana nuna mata kanta,
cikin tsoro Sanah tace " me?
Khulud tace "k'adangare, a razane Sanah ta saki k'ara tana cire hijabin jikinta,
tayi cilli dashi,
sosai Sanah ke tsalle tana ihuuuuuu,
Khulud ta kalle tana dariya while tana ja baya,
tace " wasa nake yi,
da gudu Sanah ta bita, tana dariya,
itama ta kwasa da gudu tana dariya,
suka shiga zage wajen, cikin matsanancin farin ciki,
sai da suka gaji da zagaye wajen kana Sanah ta rik'e Khulud,
rungume juna sukayi suna dariya cire da so da k'aunar junansu,
abin sha'awa.
_MAFARIN K'ADDARA_
Ranar Saturday dukkan su sanye cikin game were,
suka nufi filin game suna tafe suna wasa da dariya,
Sanah ta kalli Khulud tace " haka nan naji gaba na, na fad'uwa,
Halan tace " kiyi ta maimaita innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
cikin sanyin jiki Sanah tace " to, amma wallahi sosai gaba na ke fad'uwa fa,
Khulud ta dafa ta had'i cewa " karki damu kinji my Sanah?
"In sha Allah babu abinda zai faru,
kuma ma baga ni ba, tayi maganar tana dariya,
kai Sanah ta d'aga mata cikin sanyin jiki batare datace komai ba,
suna isa clubs d'in su Sanah ta koma gefe ta zauna tare da rafka tagumi hannu bibbiyu,
hango ta Khulud tayi, a zaune a hankali ta nufe ta had'i da durk'usawa a gabanta tasa hannunta ta zame tagumin da Sanah tayi,
tace " my Sanah meke damunki ne?
"Nima ban sani ba haka nan nake ji na wani iri,
tayi maganar kamar zatayi kuka,
Khulud tace " in Allah ya yarda babu abinda zai faru sai alkhairi,
karki damu kinji my Sanah?
"To Sanah tace, Khulud ta rik'o hannunta tace " to taso muje muyi fara wasan ko,
Sanah tace " a'a ban jin zan iya buga ball d'innan,
ido Khulud ta zaro had'i cewa " tab! kema kin san baki isa ba,
Allah sai kinyi kinji ma na rantse,
salan a cinye mu yau, Sanah ta d'aga kai ta kalli Khulud tace " kiyi hak'uri amma yau banyin ball,
baki Khulud ta zumb'uro had'i da zama a gefen Sanah tana tab'a baki zatayi kuka,
Sanah tace " ke meye kuma na kuka?
Khulud tace " Allah idan baki san nayi kuka to ki taso muje muyi ball,
idan ba haka ba yau na kwana ina kuka,
Sanah tayi dariya tana kamo hannun Khulud tace " shikenan tashi muje mu fara,
dariya Khulud tayi tace " thank you so much my Sanah,
sosai wasa ya d'auki zafi, sai buga ball suke yi,
har lokacin babu 'yan b'angaren da suka ci,
ganin haka ya zuciya Sanah dan haka ball d'in na shigowa hannunta, ta bugata da k'arfi,
da hannu 'yar d'aya b'angaren ta tare ball d'in dan haka akayi musu fanaret,
duk suka tsaya cak aka saka Sanah ta sake buga ball d'in.
_Wayyo tsautsayi da k'addara_
*RASHIN SANI* yasa Sanah buga ball d'in da iyakacin k'arfinta,
bisa tsautsayi sai ball d'in ta daki Khulud sosai a ciki,
garin Sanah ta juya ta kuma yiwa Khulud k'afa a cikin ta,
Khulud ta k'urawa Sanah ido tana daga tsaye tace " my Sana....
Bata k'arasa ba ta zube k'asa,
a kid'ime Sanah ta nufi Khulud da gudu tana kiran sunanta da k'arfi Khulud!!!!
saboda tsabar rud'ewa yasa Sanah mantawa ta kuma taka cikin Khulud da takalmin 'yan ball akan ruwan cikin ta,
tsananin azaba ne yasa Khulud sakin mahaukaciyar k'ara,
kana idanuwanta suka kakkafe numfashinta ya d'auke cak,
da k'arfi Sanah ta shiga jijigata tana kiran sunanta da k'arfi cikin matsanannacin kuka,
ganin bata motsi yasa Halan tafiya staffroom da gudu ta kira Malamai,
da gudu su Sir Moli suka k'araso a kid'ime Moli ya kalli Khulud,
yaga kwata-kwata bata numfashi,
da sauri ya sunkuya kusa da ita yana tab'a k'irjinta, gami da kunnensa a hancinta,
jin yayi shiru yasa Sanah sakin mahaukacin kuka ta rirrik'e shi kamar zararariya tace " meya same ta?
Rik'e hannunta yayi yana kallan Sir Jeeb tare da girgiza masa kai yace " bata numfashi ina ganin kamar fa ta mut..........
Bai k'arasa ba yaji Sanah ta fad'o jikinsa,
bata numfashi idanuwanta sun kakkafe............
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣2⃣
A gigitacce Sir Moli ya mik'e rik'e da Sanah a hannunsa,
yana jijjiga ta had'i da kiran sunanta da k'arfi,
Sanah! Sanah!! Sanah!!!,
duk ya rud'e ya fita hayyacinsa,
jikinsa sai kerrrrma yake, yana rungume da ita, ya nufi fanfo da gudu,
duk Malamai da students dake wajen tsayawa sukayi kallan ikon Allah,
kanta ya tara a bakin fanfon yana jijjigata,
while yana cigaba da kiran sunnata da k'arfi,
ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi ta bud'e idanta a hankali,
shima ajiyar zuciyar ya sauke had'i da runtse idansa,
da sauri Sanah ta mik'e daga jikin Sir Moli,
dakyar tace " ina my Ulud?
Sai lokacin hankalin Sir Moli ya koma ga Khulud,
da sauri ya mik'e daga durk'ushen dayake,
ya nufi inda Khulud ke kwance ya sungume ta yayi sick bay da ita,
Sanah da Halan suka bi bayansa suna cigaba da kuka,
da sauri aka kwantar da ita akan patient bed,
school doctor d'in su ya fara dubata,
Sir Jeeb da sauri ya fita yayi dialing number Abbu,
dayake kowacce students akwai number parent ko guardians d'inta,
bugu d'aya Abbu yayi picking ganin VP Roni ke kiransa,
hankalin Sir Jeeb a tashe yace " Assalamu Alaikum,,,
"Amin wa'alaikassalam Abbu ya amsa,
bayan sun gama gaisawa, Sir Jeeb yace " Sir please kuzo makarantar yanzu,
gaban Abbu yayi muguwar fad'uwa,
a hankali yace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
lafiya dai ko?
Abbu ya tambaya a k'agauce, VP yace " lafiya, amma ba lau ba,
a kid'eme Abbu yace " meya faru?
"Khulud Rawan ce ba lafiya,
da sauri Abbu ya mik'e yana cewa " meke damunta?
"Wallahi bamu sani ba amma doctor yana duba ta,
"ok to gamu nan, Abbu ya fad'a yana fita,
hankali tashe ya kira Didi,
" hello Dide yace,
cikin rawar murya Abbu yace " ka shirya yanzu zamu je Roni,
a firgice Didi yace " lafiya, meke faruwa?
Abbu yace " wallahi nima ban sani ba,
yanzu Vice Principal d'in su ya kira ni,
yace Khulud bata da lafiya, tsaki Didi yayi yana komawa kan sofa ya zauna,
" yanzu dan Khulud bata da lafiya sai mun kwasa rid'i-rid'i har mu biyu munje?
Yayi maganar cikin dauriya yana danne abinda yake ji,
Abbu yace " please karka yi min irin halin naka nako in kula,
ya za'ayi akira daga makaranta a sanar damu 'yar mu bata da lafiya amma ko a jikinka,
Didi yace " to ai kai ne da wata magana,
saboda bamu da aikin yi sai mu tafi Roni har mu biyu dan Khulud bata da lafiya,
kai ma da zaka ji tani da bazaka je ba,
Abbu yace " idan ban je ba waye zaije?
Didi yayi shiru, Abbu yace " ai bama ni kad'ai zani ba,
" kai da wa zaka je?
" Ina ruwanka tunda kai dai baka zuwa shikenan,
Abbu ya kashe wayarsa yana mamakin kara da kawaici irinna Rawan,
Didi ko yana jin Hamraz ya kashe waya,
ya kwantar da kansa akan sofa had'i da runtse idansa,
dan Allah ya sani yana mugun san Khulud,
duk cikin yaransa babu kamarta,
yafi santa fiye da kowa, kawai dai yana kara da kawaici ne saboda tsakaninsu da Hamraz, kuma Hamraz yana iyakar bakin k'ok'arin sa wajen tsayawa iyalin su akan komai,
ko kayan abinci da school fees kafin shi ya biya sau d'aya,
Hamraz ya biya sau goma, haka ma a b'angaren cefane, da kula da iyayen su komai Hamraz keyi bai jiransa,
saboda akwai so, k'auna, sabo da matsananciyar shak'uwa a tsakanin su,
tun suna yara suka taso da san junun su,
kamar yadda suka ga Ganez da Danish na san junan su har yau har gobe.
Juju dake kitchen tana girkin abinci,
ta fito da sauri,yadda taga yanayin Didi ya canja ne ya tabbatar mata ba lafiya,
a hankali tace " lafiya Dide?
Shiru yayi bayyi magana ba,
komawa tayi kitchen ta rage wutar girkinta sosai,
kana ta dawo, ta zauna a kusa dashi,
cikin sanyin jiki ta dafa kafad'arshi,
tace " lafiya, meke faruwa?
Ta kuma tambayarshi a karo na biyu,
ganin bashi da niyyar yin magana ne,
yasa ta tausasa muryata k'asa-k'asa tace,
koma me ke damunka kayi addu'a,
sai Allah ya sausauta maka shi,
ya kuma yi maka maganin matsala da damuwarka,
ko kayi ta maimaita,
innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
tana kaiwa nan ta mik'e cikin sanyin jiki zata bar wajen,
tausayinta ne ya kama shi, dan haka yayi saurin rik'o hannunta,
yace " Khulud ce bata da lafiya,
yanzu Abbu ke sanar dani Vice Principal d'in su ya kira shi,
" meke damunta?
Ta tambaye shi,
" ban sani ba, dan ni ko tambayar Abbun ma ban tsaya yi ba,
shiru tayi had'i da k'ura masa ido,
kana tace " Allah ya sauke, Ubangiji ya bata lafiya,
"Amin yace yana kallan kwayar idanta,
murmushi tayi masa kana tace " kasan dai yanzu ba 'yar mu bace,
sai dai muyiwa Abbu da Mamu jaje,
dan nasan yanzu haka ma suna cikin tension,
tayi maganar tana dariya,
danta kwantarwa da Didi hankalinsa,
dariya yayi shima kana yace " kamar ko kin sani,
ke kinji yadda Abbun ya kira ni a kid'ime wai in shirya zamu Roni,
dariya tayi, zatayi magana sai kuma tayi shiru,
cikin alamun jimami tace " Sanah fa?
Dide yace " me?
Tace " Allah sarki 'yata Sanah,
Allah kad'ai yasan cikin mawuyacin halin datake ciki yanzu,
cikin jimamin shima Dide yace " wallahi kuwa,
nasan yanzu tana can cikin tashin hankali da kuka,
ni nama fi jin tausayin Sanar akan Khulud,
murmushi Juju tayi ta mik'e tace " bari na dubo abinci,
Mamu dake tsaye bakin k'ofa,
ta share hawayenta, ta juya ta koma part d'in su.
Abbu na kashe waya ya kira Ziyad, Zafran ya sanar da su,
batare da wani b'ata lokaci ba,
suka d'au hanyan Roni, Ziyad na driving,
Zafran na gefensa, Abbu yana baya,
sai da suka hau hanya sannan Abbu ya kira Mamu ya sanar da ita,
sosai hankalinta yayi masifar tashi,
ta nuna masa kamar bata sani ba.
A makaranta ana ta faman k'ok'arin maido da numfashin Khulud,
amma kwata-kwata babu alamar dawowarsa,
wata irin gigitacciyar k'ara Sanah ta saka,
had'i da fasa kuka ta fad'a jikin Khulud ta rungume ta tana ihuuun kuka,
" please my Ulud ki tashi, kinyi man alk'awarin duk abinda nasaki zakiyi,
idan kuma na hana ki zaki bari,
dan Allah ki tashi, wallahi idan kika mutu nima mutuwa zanyi,
bazan tab'a rayuwa cikin farin ciki da walwala ba,
matuk'ar baki tare dani,
a hankali tasa hannu tana marin kuncin Khulud a hankali,
tana cewa " ki tashi kince bazaki ta tab'a rabuwa dani ba,
kince tare zamu girma muyi aure,
dan Allah ki tashi my Ulud,
nayi miki alk'awarin bazan tab'a barinki cikin k'unci da matsalar rayuwa ba,
nayi miki alk'awarin bazan tab'a barinki cikin damuwa da masifa ba,
nayi miki alk'awarin zan zame miki garkuwa daga dukkan matsalolinki,
zan zame miki maganin dukkan damuwa da k'uncinki,
dan Allah ki tashi ta k'arasa maganar cikin rikitaccen kuka tana d'ora kanta akan k'irjin Khulud,
duk wanda yaga yadda Sanah ke kuka tana magana tana jijjiga Khulud abin sai ya bashi tausayi komai rashin imanin mutum,
sai yaji zuciyarsa ta karyae,
Halan na gefe na aikin kuka,
Sir Jeeb zaune kan sofa ya zuba musu ido cike da tausayin Sanah.
A hankali Sir Moli ya d'ago pure red eyes d'insa ya kalli Doctor yace " wai ya ake ciki ne har yanzu shiru?
Doctor yace " hmmm gaskiya ciwon babba ne dan ko numfashi batayi,
Sanah ta k'ara sakin rikitaccen kuka,
Sir Moli yace " kamar ya?
" gaskiya koma me ke damun yarinyar babban ciwo ne,
Sir Jeeb yace " wai har yanzu baka gano ciwon ba?
" Eh, ban san takaimaiman abinda ke damunta ba,
ni fa ina ganin mutuwa zatay........
gigitacciyar k'arar da Sanah ta kwalla ce ta hana Doctor k'arasa abin da yayi niyyar fad'a,
a gigice ta mik'e tsaye had'i da d'ora hannu aka tana rikitaccen kuka mai ban tausayi,
" a'a wallahi na tabbatar Khulud bazata tab'a mutuwa ta barni ba,
ko ita kanta mutuwar zataji kunyar d'aukar Khulud a gaban ido na,
kuma koda mutuwar ce da gaske tazo nasan Khulud zatayi iya k'ok'arin ta na ganin bata tafi na barni ni kad'ai ba,
tayi maganar a matuk'ar rud'e,
gaba d'aya ta fita hayyacinta, ta kid'ime ta fita fit daga hayyaci da nutsuwarta,
jikinta sai rawa da kerrrrma yake,
ganin yadda ta rud'e ne yasa Sir Moli dakawa Doctor tsawa " kai baka da hankali ne, baka san aikin ba ne?
Yayi maganar a tsawace, da sauri Doctor da Sir Jeeb suka kalle shi cike da mamaki,
da saurinsa ya rik'e Sanah ya sunya hannu a hankali yana goge mata hawayenta,
cikin sanyin murya yace " kiyi hak'uri Khulud bazata mutu ta barki ba kinji?
Kai ta d'aga masa, " ki rink'a yi mata add'u, ki dai na kuka, tunda kinga bata san kukan ko?
Ta kuma d'aga masa kanta a hankali,
" magana zakiyi kinji ban san nodding kai,
da sauri tace " na dai na, ban k'arawa,
ya shafa kanta yace " yawwa good girl,
cikin sanyin murya ta kuma cewa " bazata mutu ba ko?
Tayi maganar hawaye na gangaro mata,
cike da tausayinta ya d'aga kai,
" ka tabbatar zata tashi?
Ta kuma tambayarsa,
" in sha Allah, ya bata amsa,
bazato yaji ta fad'a jikinsa tana cewa " thank you so much Sir,
tayi maganar tana k'ara shegewa jikinsa,
murmushi yayi yana k'ok'arin zame jikinsa daga nata,
da sauri ta k'ara matseshi, tana cewa " I will never forget you in my life,
yayi murmushi kana yace " are sure?
" Yes , tace tana cigaba da kukanta,
a hankali ya zame jikinsa, duk da tana k'ok'arin k'ara shigewa jikin nasa,
ya mik'e yana kallan Sir Jeeb,,
da mamaki ya gama kashe shi a tsaye,
ba Sir Jeeb kad'ai ba, duk wanda ke wajen yana cike da tsantsar mamaki da al'ajabi,
ya lura sarai da reactions d'in su amma ya basar, ya tamke face yace,
" ka kira gidan nasu kuwa?
"Eh na kira su tun d'azu ma,
Sir Moli ya kuma cewa " tun yaushe ka kira su?
" Tun wajen 2 hours back, yaci ace sun iso ma,
yayi maganar yana duba agogon hannunsa,
" ka k'ara kiran su please, asan abinyi tun da wuri,
"ok yace yana ciro wayarsa daga aljihu,
yana k'ok'arin kiran su, kiran Abbu ya shigo,
da sauri Sir Jeeb ya d'aga,
Abbu yace " gamu mun k'araso muna bakin get,
kana ina?
Da sauri Sir Jeeb yace " gani nan zuwa,
ya kashe wayar yana kallan Sir Moli,
yace " sun k'araso fa, Sanah dake zaune bakin gadon da Khulud ke kwance ta d'ora kanta saman chest d'inta,
ta k'ara runtse idanta hawaye na zubowa.
Da sauri Sir Jeeb ya fita ya tari su Abbu,
hannu Sir Jeeb ya mik'awa Abbu had'i da d'an risinawa,
"Assalamu Alaikum, sir Jeeb yace,
fuskar Abbu d'auke da murmushi ya amsa,
Sir Jeeb yace " muje office,
"Ok cewar Abbu yayi gaba,
Ziyad da Zafran na bin su a baya,
zama Abbu yayi a kan kujerar dake fuskantar Sir Jeeb,
ajiyar zuciyar ya sauke kana yace " please Sir kuyi hak'uri bamu san meya faru ba,
muna staffroom Halan ta zo ta kira mu,
saboda yadda hankalin mu yake a tashe bamu tsaya tambayar abinda ya faru ba,
Abbu yace meya same ta?
" Har yanzu Doctor yana kanta,
ba'a gano takaimaiman abinda ke damunta ba,
"tana ina yanzu?
Mik'ewa Sir Jeeb yayi yace " muje,
duk suka mik'e suka bi bayansa,
da sallama Abbu ya shiga cikin sick bay,
duk Malaman dake wajen suka amsa,
ganin yadda idanuwan Khulud yayi fari fat,
babu alamar bak'in kwayar ido,
ga idan ya kakkafe
yayi masifar d'agawa su Abbu hankali,
da sauri suka nife ta, Abbu na cewa " Subhanallah,
hannun sa na rawa ya d'ago Khulud yana jijjiga ta had'i da kiran sunanta,
Ziyad da Zafran kasa motasawa suka yi daga inda suke tsaye,
zuciyar su ta karye sosai,
sun shiga rud'u da tashin hankali,
Abbu ya d'ago ya kalli Doctor da idanuwansa da suka gama zama yin jajir,
muryarsa na creaking yace " please Doctor meke damunta?
"Nayi iyakar bakin k'ok'arina wajen gano abinda ke damunta amma na kasa,
Doctor ya fad'a cikin sanyin murya,
a hankali Abbu yasa hannu ya d'ago kan Sanah dake ta kuka kamar ranta zai fita,
d'agowa tayi ta kalle shi had'i da k'ara fashewa da rikitaccen kuka,
tace " Abbu na kashe my Ulud da kai na,
ni da kai na buga ball, na kuma naushe ta a cikinta, sannan na taka ta da takarmin 'yan ball a cikinta,
dan Allah ka bata hak'uri kace mata tashi ban k'arawa,,
*_RASHIN SANI_* ne yasa ni yin hakan,
wallahi Allah Abbu ban sani ba na buge ta na kuma taka ta,
ni da kai na yiwa kai ma illa,
ni da kai na, na kashe my Ulud,
ni da kai na, na illata rayuwa ta da zuciya ta,
bazan tab'a yafewa kai na ba,
bazan tab'a sake tsintar kai na cikin farin ciki da walwala ba,
bazan tab'a sake dariya da murmushi ba, har na mutu,
duk wani abu na jin dad'in duniya da walwala na haramtawa kai na har abada,
ko aure bazan tab'a yi ba Abbu,
ta d'ago hannunta da k'afarta tana yi musu wani irin kallo,
kana tace " bazan tab'a yafe muku ba,
mutuk'ar my Ulud ta mutu sai na azabtar daku,
sai na azabtar da kai na rayuwa ta,
azabtarwa mai rad'ad'i, ta k'arasa maganar cikin matsanancin kuka,
mai cin rai.
Kanta Abbu ya shafa, kwalla na taruwa a idansa,
kana yace " ba laifinki bane Sanah,
da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi,
tace " Abbu laifin waye idan ba laifi ba?
"Wallahi Abbu ni da kai na, na buge ta na kuma taka ta, a kan ruwan cikinta,
tayi maganar kamar zararriya,
" k'addara ce tasa faruwar hakan,
karki d'orawa kanki laifiin kinji Sanah?
Zata yi magana Abbu yayi saurin mik'ewa had'i da sungumar Khulud,
da sauri su Ziyad da sukayi mutuwar tsaye suka tare shi,
jikin Zafran na rawa ya karb'i Khulud daga hannun Abbu,
jikin Sanah na rawa ta mik'e tabi bayan su,
saboda sauri har tana tuntub'e,
cike da tsantsar tausayinta Sir Moli ya bita da kallo har suka fita,
kishingid'a yayi akan sofa had'i da lumshe idanuwansa,,
kafin su fito har Halan tasa Juniors sun fito musu da kayan su kaf,
babu abinda ta bari, ko tsinke,
Ziyad ya bud'e bayan boot ya saka gaba d'aya kayan.
A baya Sanah ta ke bin su Abbu tana sauri harda tuntub'e,
Sanah na zuwa dai-dai flowers,
dake zagaye da staffroom taji wani abu ya fad'o mata a jikinta,
d'aga idan da zatayi taga............
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣3⃣
D'aga idan da zatayi taga k'aton k'adangare (jangwali gwada),
ai kota tayi muguwar tsorata,
a rud'e ta nufi Zafran tana tsalle had'i da ihuuu,
ganin katon koren k'adangaren dake jikinta yasa shi yin baya,
shima a rud'e, saboda shima yana mugun tsoron k'adangare,
a kid'ime take binsa yana yin baya shima,
ga k'adangaren ya mak'ale mata,
da rud'e ta cire hijabinta tayi wurgi dashi,
tana cigaba da kukanta da tsalle,
ganin Zafran na ja da baya ga k'adangaren na neman shigewa cikin rigarta,
ya sata d'aga murya da k'arfi a matuk'ar rud'e tace " SIR MOLI! SIR MOLI!! SIR MOLI!!!,
dan girman Allah ka taimakeni zan mutu,
Sir Moli na kishingid'e lumshe da ido akan sofa cikin office d'inta,
ya jiyo muryarta tana kwala mishi kira,
da sauri ya bud'e idannasa, had'i da kasa kunne dan jin da gaske ko gizo muryarta ta keyi masa,
da k'arfi ya kuma jin Sanah tace " please Sir Moli zai shiga cikin riga ta kazo da sauri,
a mugun kid'ime ya mik'e ya fita ko takalmi bai sanya ba,,,,
lokacin daya isa tana gaf da cire rigar jikinta,
wani irin wawan tsalle Sir Moli yayi,
wanda shi kansa bai tab'a tsammanin zai iya yin irinsa ba,
bisa gwiwowinsa ya isa gabansa a durk'ushe ita kuma tana tsaye,
tana kuka da tsalle,
tana yarfa hannuwanta idanta sunyi jajir duk ilahirin jikinta kerrrrma yake,
gami da tsuma,
a zabure yasa hannu yayi saurin gyara mata rigar jikinta,
gudun karta k'arasa cireta a gaban mutane,
sannan ya fusge k'adangaren yayi jifa dashi,
kai da ganin yadda yayi jefa dashi kasan yana mutuk'ar jin haushin shi,
yana daga durk'ushen a gabanta ya d'auko d'ankwallinta,
ya d'aura mata, ya maida mata hijabinta jikinta,
kumatunta ya d'an tab'a a hankali yana murmushi yace " karki k'ara k'ok'arin cire kaya a gaban mutane kinji ko?
Ta d'aga kai a hankali hawaye faca-faca a fuskarta,,,
tunowa da tayi baya san d'aga kai yasa cewa " to ai tsoro nake ji tayi maganar a hankali,
idansa na kanta, while yana murmushi yace " ki zama d'aya daga cikin matan da ko kashe su za'ayi bazasu tab'a bayyanar da tsiraicin su ba,
bazasu tab'a zubar da k'ima da mutuncin su ba,
idansu sark'e cikin na juna tace " meye k'ima?
Murmushi yayi yana shafa kanta yace " k'ima da mutunci duk abu d'aya ne,
kuma abu ne daya fi komai mahimmanci a rayuwar d'an Adam,
muddin akace mutum bashi da k'ima da mutunci dashi da dabba duk d'aya suke ba zai tab'a zama cikekken mutum ba,
cikin sanyin murya tace " to ya za'ayi ni ma na zama mai mutunci?
"Kina san ki zama mai mutunci?
Ya tambaye ta idansa na kanta,
"Eh tace,
yace " meyasa?
"Saboda naji kace duk wanda bai da su,
dashi da dabba duk d'aya,
murmushi yayi kana yace " ki zama mace mai kunya, daraja,
tausayi da jin k'ai, mai jin magana da d'aukar gyara,
ki zama mai k'an-k'an da kai,
mai karrama mutane, mai gaskiya da amana,
mai tsoran Allah, mai addini, mai suturta jikinta wacce tasan darajar kanta da jikinta,
ki zama salihar mace, wacce iyaye, ahalinta da 'yan uwanta zasu yi alfahari da ita,
su kuma samu kwanciyar hankali da nutsuwa a duk inda take,
ido kawai ta zuba masa bata ko k'iftawa,
har ya kai aya sannan tace " ya za'ayi na iya duk wad'annan?
" Kiyi yak'ini a zuciyarki cewar zaki iya,
karki tab'a zama mutum marar kwarin gwiwa,
ki sawa ranki da zuciyarki, zaki iya cimma duka burikanki,
duk abinda kikaga mutum bai yi ko ya iya ba,
bashi da yak'ini ne,
a hankali tace " yak'ini?
"Meye kuma yak'ini?
Murmushi ya kuma yi kana yace " gaskatawa, yarda da tabbatarwa duk suna cikin yak'ini,
shiru tayi tana kallansa kana tace " duk wad'annan abubuwan d'aya suke nufi?
"Eh yace yana kallan kwayar idonta,
Abbu, Ziyad da Zafran suna tsaye cike da tsantsar mamaki suna kallan ikon Allah,
shi Abbu mamaki d'aya yake yi,
yadda duk jama'a da Malaman su dake wajen bata nemi taimakon kowa ba,
sai na wanda baya wajen,
bayan a wajen har da shi kansa mahaifinta, ga Ziyad, da Sir Jeeb,
amma babu sunan wanda ta kira sai na MOLI,
kanta Sir Moli ya shafa yace " bye,
juyawa tayi ta nufi mota, har ta d'ora k'afarta zata shiga motar,
ta juyo bisa mamakin kowa sai akaga tayi murmushi akaro na farko tun bayan faruwar abun tayi murmushi,,
cikin sanyin murya tace " nagode sosai,
bazan tab'a mantawa da alkhairin daka yi min ba,
thank you so much,
tayi maganar tana murmushi,
murmushi kawai yayi mata batare dayace komai ba,
motar ta shiga ta zauna, ta d'auki kan Khulud ta d'ora akan cinyarta,
Abbu na gaba Zafran na driving,
Ziyad na baya yana rik'e da hannun Sanah,
Halan bata bar wajen ba har sai da motar su tabar harajar makarantar,
shima Sir Moli yana nan durk'ushe bai motsa ba har suka fita daga get,
a hankali ya d'aga kansa sama had'i da lumshe ido,
duk Malaman suka yi jugum-jugum suna kallan ikon Rabbi.
A mota babu wanda yake cewa komai,
kowa da abinda yake sak'awa a ransa,
shi dai Abbu Sir Moli ne ya tsaya masa a ransa,
musamman yadda ya lura akwai sabo tsakaninsa da Khulud da Sanah,
dan yadda Sanah ta kira sunanshi ta nemi taimakonsa shi kad'ai bayan tarin mutanen dake wajen ya tabbatar masa da hakan, kuma tunda suka je baiga yayi magana da kowa ba sai Sanah,
kuma kallo d'aya zaka yi masa kasan yana cikin tension,
saboda ya hango wani abu a cikin kwayar idansa,
a hankali Abbu yace " Sanah waye wannan?
Cikin muryar kuka tace " wa Abbu?
Yace " Sir Moli,
hawayen dake zubo mata ta goge kana tace,
"Malami ne a makarantar amma mu baya d'aukar mu,,
ba permanent teacher bane service yazo,
Abbu yace " daga gani yana da sauk'in kai da tausayi,
gashi nutsatstse,
shiru Sanah tayi bata kuma cewa komai ba,
dan ita kad'ai tasan me take ji a ranta,
ita kad'ai tasan irin zafi da k'unar da zuciyar ta keyi mata.
A harabar Aminu Kano Teaching Hospital suka yi parking,
dan Abbu yace wannan babban case ne yafi k'arfin private Hospital,
dole sai babban asibiti inda manyan Doctors zasu duba ta,
sai dai idan matsalar ta wuce nan su tafi Germany 🇩🇪,
suna yin parking Abbu ya fito da sauri ya shiga ciki,
bai shima ba ya fito tare da Doctors biyu da Nurse's hud'u,
d'auke da gadon d'aukar marasa lafiya,
da sauri aka d'auki Khulud, Sanah tayi saurin fitowa tabi bayansu hannunta cikin na Khulud tana cigaba da kukanta,
suna isa k'ofar Emergency room,
Doctor ya kalli Sanah yana dariya yace " Mrs Cry sake ta zamu shiga ciki,
jin abinda Doctor d'in yace ya sata sakin gigitaccen kuka,
" ni Allah ban rabuwa da Khulud sai dai mu shiga tare,
Doctor ya kalle yana murmushi yace " ina ai ba zai yiyu ba,
tana kukan ta fara buga k'afa " Allah ba mai raba ni da Khulud,
salan a fito ace man ta mutu,
Doctor yace " a'a ba wanda zai ce miki ta mutu in sha Allah,
sai dai ayi miki albishirin ta warke,
" ni dai a'a tace kana cigaba da kuka,
dai-dai lokacin su Abbu suka k'araso,
jin yadda ake ta fama da Sanah ya sashi hasala ya daka mata tsawa " ke badake ake ba?
Sosai Sanah ta rikice jin tsawar Abbu ta saka rikitaccen kuku,
kallan Abbu Doctor yayi yana girgiza masa kai yace " no Alhaji,
ba haka ake yiwa yaran dake cikin matsala da damuwa ba,
a hankali Doctor ya durk'usa a gabanta kana yace " kina san Khulud d'inki ta samu lafiya?
Da sauri ta d'aga kanta,
yace " kin tabbatar?
Ya kuma tambayar ta, ta d'aga masa kanta a karo na biyu,
yace " to matuk'ar kina san ta samu lafiya ku cigaba da wasa tare ki bari a duba ta,
cikin rawar murya tace " to na bari,
murmushi Doctor yayi had'i da goge mata hawayenta yace " ki dai na kuka kiyi mata addu'a kinji?
" To tace, mik'ewa yayi yana k'ok'arin shiga emergency room,
da sauri Sanah ta rik'o hannunsa tace " ka tabbatar My Ulud zata tashi bazata mutu ba?
Tayi maganar cikin wani irin yanayi mai ban tausayi hawaye na zubo mata,
wanda hakan yayi masifar saukarwa da duk jama'ar dake wajen tsananin tausayinta,
a hankali Abbu ya goge hawayen dake k'ok'arin zubo masa,
ido kawai Doctor ya zuba mata batare daya iya furta koda kalma d'aya ba,
ta kuma cewa " dan Allah kayi k'ok'arin ceto min rayuwarta idan ba haka ba nima mutuwa zanyi,
kai ya jinjina yana shafa kanta yace,
"da yardar Allah nayi miki alk'awarin zanyi iyakar bakin k'ok'arina,
murmushi tayi masa hawaye na zubo mata tace " nagode.
Gefe ta koma ta rakub'e a k'asa tana cigaba da kuka,
abin gwanin ban tausayi,
Abbu ya ciro waya ya kira Mamu bugu d'aya tayi picking,
bayan sun gama gaisawa Abbu yace " muna Aminu Kano b'angaren accident and Emergency,
kuma nasan kwantar da mu za'ayi,
da sauri tace " ok ganin zuwa yanzu,
me za'a kawo muku?
A tak'aice Abbu yace " duk abinda ya kamata,
"ok tace tana mik'ewa da sauri,
Abbu yana kashe wayar Mamu ya kira Didi,
bugu d'aya yayi picking yana dariya yace " Abbun patient,
fuska Abbu ya b'ata kana yace " muna Aminu Kano b'angaren accident and emergency idan kana iya zuwa,
Abbu na fad'ar haka ya kashe wayar,
murmushi Didi yayi yabi phone d'in da kallo,
kana ya kira wayar Juju,
yace ta shirya yanzu zasu je Hospital,
tace " aiko yanzu Mamu ta kira ni tace na shirya zamu tafi,
yace " ok to mu had'u acan.
Da sauri Didi ya k'araso inda Abbu yake,
duk fushin da Abbu yake yi da Didi yana ganin shi yaji zuciyarsa tayi sanyi,
yaji duk zafin ransa ya gushe,
yaji bai iya yi masa komai,
Abbu ya kalli Didi yace " wato dan kaga bana iya yin dogon fushi dakai shiyasa kake man san ranka ko?
Didi yayi dariya yace " ai ni ban ma iya fushin dakai koda wada ne, bama dogo ko gajere ba,
kuma nasan ai zakayi fiye da abinda ni zanyi,
Abbu zayyi magana Mamu da Juju suka shigo,
da sauri Mamu ta k'arasa tana tambayar ina Khulud,
Abbu yace "tana Emergency room,
shiru Mamu tayi tana safa da marma,
Juju ta kalle Abbu tace " Sanah fa?
Murmushi yayi kana ya nuna mata inda Sanah ke rakub'e a k'asa tana kuka,
har ta fara fita daga hayyacinta,
" Subhanallah Juju ta fad'a tana nufar Sanah,
d'ago Sanah Juju tayi ta rungume had'i da bubbuga bayanta,
Sanah ta saka gigitaccen kuka,
jikinta sai kerrrrma yake yana tsuma,
tace " Juju na kashe my Ulud da kai na,
Juju dan girman Allah kice mata ta tashi karta tafi ta barni,
idan ta tafi ta barni bazan tab'a jin dad'in rayuwar duniya ba,
tayi maganar a matuk'ar firgice,
a hankali Didi ya k'araso wajen,
ya zauna kusa da Sanah, shida Juju suka saka ta a tsakiya,
ta kalle shi bakinta na rawa tace " Did.....
bai bari ta k'arasa ba ya jawo ta jikinsa ya rungumeta,
yana shafa kanta, batare dayace komai ba.
An kai wajen 3grs kana Doctors suka fito,
da sauri Abbu da Mamu suka nufe su,
Sanah ma tayi sauri kwace kanta daga jikin Didi duk da yana k'ok'arin k'ara matseta a jikinsa,
Doctor bai kalli su Abbu ba, gaba d'aya hankalinsa nakan Sanah,
dan koda yana duba Khulud gaba d'aya hankalinsa na wajen Sanah,
dan mugun tausayin ta yaji ya kama shi,
a hankali ya durk'usa kusa da ita yana murmushi,
ido kawai Sanah ta zuba mishi ta kasa cewa komai,
yace " Alhamdulillah babu abinda ya samu Uludin ki, gogon suma ne kawai tayi,
sai numfashinta dayake sneezing,
amma munyi mata allura mun saka mata Oxygen dan numfashinta ya dawo normal,
jikin Doctor d'in Sanah ta fad'a ta lumshe idanta hawaye na zubo mata,
"thank you so much Doctor,
dariya yayi yace " ki godewa Allah,
tace " Alhamdulillah,
a gadon tura marasa lafiya aka fito da Khulud d'aure da k'arin ruwa da Oxygen,
d'aki aka kaita, d'akin mai kyau akwai bed, sofa toilet & bathroom, wardrobe,
da sauri Sanah ta zauna a bakin gadon ta d'ora kanta akan k'irjin Khulud tana cigaba da kuka,
abin tausayi,
Mamu ce ta zauna ta kwana dasu.
Har washe gari Khulud bata farfad'o ba,
al'amarin dayayi masifar d'agawa Sanah hankali kenan,
ta rink'a kuka tana jijjigata Khulud tana kiran sunanta,
"please my Ulud ki tashi, dan Allah ki tashi,
karki mutu dan Allah, tana maganar cikin matsanancin kuka,
Mamu dake gefe zaune akan sofa cike da tausayin 'ya'yan nata,
ta mik'e a hankali ta nufi inda Sanah take kwance akan Khulud tana kuka tana kiran sunanta,
Mamu ta rungume su duka, kana tacewa " Sanah jeki alwala kiyi sallah ki rok'i Allah yabawa Khulud lafiya,
da sauri Sanah ta d'ago fuskarta dake cike da hawaye tace " Mamu idan nayi addu'a zata warke?
Mamu tace " Addu'a ai maganin komai da komai ce Sanah,
duk abinda ya damu musulmi koya shige masa duhu,
ko mutum ya shiga matsala da damuwa idan yayi addu'a ya rok'i Allah,
sai Ubangiji yayi masa maganin matsalarsa,
ya kuma yaye masa damuwarsa,
ya kawo masa mafita,
baki ganin 'yan kowanne addini suna addu'a wa abinda suke bautawa,
dan haka ki rik'e addu'a Sanah aduk halin da kike ciki,
idan kika dage da addu'a sai Allah ya kawo miki d'auki, ya shiga cikin lamuranki,
ki zama mutum mai zafin addu'a da addini, wallahi sai kinfi k'arfin komai da kowa dake duniya,
sai kin zama gagara badau, sai kin zama murucin kan dutse,
ko aljani da mugayen mutane sai kin gagare su,
Annabi (S.A.W) yace " الدعاء سيف المؤمنين,
Allah maji rok'on bayinsa ne,
mai kuma amsa addu'ar su,
musamman addu'a daga bakin yara k'anana wad'anda basu balaga ba,
cikin sanyin jiki Sanah ta mik'e tace " Mamu zanje nayi alwala nayi ta Sallah da addu'a bazan daina ba har sai my Ulud ta farfad'o,
murmushi Mamu tayi mata kana tace " yauwa good girl.
Alwala Sanah tayi ta d'auko prayer mat & Qur'an, hislin muslim a inda Mamu ta aje,
sallah tayi raka goma sallama biyar,
kana ta bud'e hislin muslim tayi addu'a sosai,
ta aje ta d'auki Qur'an ta fara karanwa a fili muryarta na rawa irin ta masu kuka,
Abbu, Didi da Juju suka shigo tare d'auke da food flask na breakfast,
tun daga bakin k'ofar shiga d'akin suka jiyo muryar Sanah tana karatun Qur'an cikin kuka,
akan Sofa Abbu da Didi suka zauna Mamu na zaune a bakin gadon Khulud,
bayan sun gama gaisawa, Didi ya kalli Sanah yace " aje karantun kizo kiyi breakfast,
bata ko kalli inda yake ba taci gaba da karatunta,
babu yadda Didi da Juju basu yi ta aje ta karya ba amma bata ko kalle su ba,
Didi da Abbu suka fita tare suka bar Juju da Mamu,
tun asuba Sanah ke karatu tana addu'a har akayi sallar azhur,
alwala kawai ta tashi tayi,
ta dawo ta cigaba da karatun Qur'an da addu'a,
haka ma da akayi sallar alasur,
sau biyu Doctors na shigowa suna ganinta,
duk wanda yayi mata magana bata kallansa balle ta amsa,
sosai Sanah ta burge Doctors da Nurses d'in dake shigowa ta kuma k'ara basu tausayi.
Da daddare Abbu da Didi suka shigo d'auke da basket na abinci,
lokacin Doctor da Nurses sun shigo duba Khulud,
da sauri Didi ya turje ganin yadda suka bar Sanah tun safe haka suka dawo suka same ta,
Didi yace " Sanah lafiyarki kuwa?
Bata kalle shi ba ta cigaba da karatunta tana kuka,
Doctor ya kalli Dide da Abbu, Juju & Mamu yayi murmushi yace " wallahi duk inda kayi yau a cikin Hospital d'in nan maganar Sanah kawai akeyi,
Abbu yace " ikon Allah,
Juju tace " duk yau fa ko ruwa bata sha ba,
duk suka yi jugum-jugum,
Doctor yayi musu sallama ya fita cike da sha'awar halayyar Sanah,
_Ni ko nace hmmmm Doctor baka san Oga Sanah bane, ruwa ne ya k'arewa d'an kada, kaje ka tambayi Sir Moli wacece Sanah Hamraz_
Allah maji k'oron bayinsa,
wajen 11:00pm na dare,
Doctor ya shigo ya duba Khulud,
bayan ya gama dubata ya kalli inda Sanah ke zaune har lokacin tana addu'a,
yayi murmushi ya bud'e baki zayyi magana,
suka ji muryar Khulud na salati,
sai da tayi salati sau uku a jere,
kana ta kira sunan Allah, sai kuma tad'anyi shiru,
duk d'akin aka rasa wanda zayyi magana balle kwakkwaran motsi,
har shi kanshi Doctor d'in, da k'arfi suka ji Khulud tace...............
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣4⃣
Da k'arfi suka ji Khulud tace " My Sanah!!!!,
Sanah dake ta faman karatu bata san wainar da ake toyawa ba,
sai jin muryar Khulud datayi tana kiranta,
da sauri ta juyo da kanta ta kalli inda Khulud ke kwance,
dan ta tabbatarwa da kanta abinda kunnawanta suka ji ye mata,
ganin da gaske Khulud d'ince yasa ta yin sujdul shukru ,
tana hawaye ta shiga gode ma Allah,
da sauri Mamu ta nufe ta tana kiran sunnata,
"Khulud kin tashi?
Taba ko kalli inda Mamu take ba,
gaba d'aya hankalinta yana wajen Sanah,
Doctor tsaye yayi yana kallan ikon Allah,
yadda suka yi ta faman k'ok'arin ganin Khulud ta farfad'o amma abu ya gagara,
amma sai gashi lokaci d'aya ta farka,
Abbu ya k'arasa inda Khulud ke kwance tana kallan Sanah ,
ya shafa kanta yana murmushin jin dad'i yace " Alhamdulillah Khulud kin tashi?
Kwata-kwata hankalinta baya kan gaba d'aya jama'ar dake wajen,
balle ma tasan abinda suke yi,
gaba d'aya hankalinta yana kan Sanah,
a hankalinta Sanah ta d'ago daga sujdar ,
ta tako inda Khulud take,hawaye na cigaba da zubowa daga idanta,
ta k'urawa Khulud ido,
da k'arfi ta fashe da kuka gami da fad'awa jikinta,
itama Khulud kukan ta saka a hankali tace " my Sanah ki daina kuka,
tayi maganar dakyar,
murmushi Doctor yayi kana ya k'araso bakin gadon,
idansa nakan su,
yace " Mrs Cry zan duba ta,
yayi maganar cikin tsokana,
baki Sanah ta turo kana tace " tafa warke,
cikin dariya yace " to fa Doctor Sanah,
wato ke har kin san ta warke ko?
Bata bashi amsa ba,ta kalli Khulud tace " ai kin warke ko my Ulud ?
Dariya itama tayi tace " eh my Sanah babu abinda ke damuna,
Doctor ya kalli Sanah yace " naga alamar dai baki san ta warke sosai yadda zaku koma gida da wuri ko?
" Ina so mana ta fad'a cike da k'uruciya,
yace " to idan kina so ki bari a duba ta,
batare data ce komai ba,ta matsa ta koma gefe ,
aune-aune da d'an gwaje-gwaje yayi,
kana ya d'ago kai ya kalli Khulud yace " akwai inda ke miki ciwo?
A'a, ta bashi amsa,
"babu inda ke miki ciwo ko zafi,
ya kuma tambayarta idansa na kanta ,
dan ya tabbatar da abinda zata fad'a,
" eh ta fad'a itama tana kallanshi,
yace " kiyi tunani dai kinji our Khulud yayi maganar cikin wasa,
dariya tayi,kana ta d'anyi shiru alamar tunani,
"babu ,ta kuma bashi amsa,
yace " kin tabbatar da gaske babu abinda ke damunta ko inda ke yi miki ciwo?
"Karki fa kiyi amfani da maganar our Sanah datace babu abinda ke damunki,
murmushi tayi kana tace " Allah babu abinda ke damuna,
sai baki na danake jin babu dad'i,
sai kuma jiki na dayake man ciwo,
idan shi na kanta yace " bakin ki rashin apartheid ne,
jikin ki kuma dad'ewar da kikayi a kwance ne yasa shi yin tsami,
da our Sanah tayi miki wanka da ruwan zafi zaki warware,
yayi maganar cikin tsoka na,
dariya duk sukayi batare da sunce komai ba,
yace bayan nan fa?
Tace " babu komai,
juyawa yayi wajen su Abbu dake tsaye suna kallan su fuskokin su d'auke da murmushi,
yace " Alhamdulillah, Allah maji rok'on bayin sa ne,
abinda muka kasa yi acikin 48hrs ,
gashi Sanah tayi a cikin yini d'aya kawai,
Allah ya amsa addu'arta,
gaskiya ko ni anan na k'aru,
k'aramar yarinya ta tunatar dani fahimmanci da amfanin addu'a,
ta nusarshe ni komawa ga Allah,
da kai kuka ga Ubangijin talik'ai mai kowa da komai,
gaskiya ne babu abinda ya gagari addu'a koya fi k'arfin Ubangiji,
wannan kad'ai ya isa ya nunuwa mutum akwai Ubangiji,
ya isa ya nunuwa wad'anda basu yarda akwai Ubangiji ba,,
cewar akwai mak'agin kowa da komai.
Ya k'arasa maganar yana kallan Abbu ido cikin ido,
murmushi Abbu yayi kana yace " Alhamdulillah mun godewa Allah,
Doctor yayi murmushi yace " kuma da gani akwai so da k'auna mai k'arfi a tsakanin yaran,
musamman yadda Sanah ta d'aga hankalinta,
tak'i ci da sha ,
da kuma yadda itama Khulud tana farfad'owa babu sunan wanda ta fara ambata sai na Sanah,
kad'ai ya isa ya tabbatarwa mutum suna mugun san junan su,
yayi maganar idansa na kan Khulud da Sanah,
cike da sha'awar su,
murmushi Didi yayi cikin jin dad'in yabon da Doctor yake yiwa yaran su,
yace " mun gode sosai Doctor,
Allah ya saka da alkhairi Ubangiji yabar zumunci,
Allah ya albarkaci iyali,
" amin ya Allah,ya amsa kana ya d'ora da cewa " ai babu iyalin har yanzu,
muna dai nema ya k'arasa maganar yana shafa kai idansa nakan Sanah,
murmushi Abbu yayi yace " to madalla Allah ya bada nagari,
"Amin, ya kuma cewa idansa nakan Sanah,
har ya juya zai fita Mamu ta kira sunanshi " Doctor,
a hanlaki ya juyo yana kallanta had'i da amsawa "na'am,
cikin murmushi Mamu tace " zuwa yaushe za'a sallame 'yar ta wa?
Dariya yayi kana yace " ko zuwa gobe ma in sha Allah,
dan babu sauran abinda yake damunta,
"Allah ya kai mu,Mamu tace,
ya amsa da "Amin,
ya d'ora hannunsa akan handle d'in k'ofa ,
Sanah tace " thank you so much Doctor,
juyowa yayi yana murmushi yace " don't mention it,
murmushi tayi a tak'aice tace " ai dole nagode ,
"saboda me?
Yace idansa na kanta,
" besouse you fulfilled your promise ,
dariya yayi kana yace " it's my pleasure,
suka yi dariya su duka,batare da sun ce komai ba,
Sanah ta mayar da kallanta ga Khulud tace " hankalina ya tashi sosai,
tayi masa cikin sanyi da karaya,
"karki damu muna tare har rai da mutuwa in sha Allah,
Khulud ta fad'a tana dariya,
Sanah tayi rau-rau da ido alamar tana san yin kuka tace " Allah nayi mugun tsora ta fa,
na gama sawa rai na...,
sai kuma tayi shiru had'i da k'urawa Khulud ido hawaye na zubo mata,
Khulud tayi rolling idonta " please my Sanah ki dai na kukan kinji?
Idan ba so kike na koma jinyar ba,
tayi fad'a tana gogewa Sanah hawayen dake zubo mata,
murmushi Sanah tayi tace " ke kyama so ma komawa,
Khulud tayi dariya,
d'an shiru Khulud tayi na wajen 5 minutes kana tace " my Sanah Sir Moli,
tayi maganar can k'asan mak'ogwaranta,
baki Sanah ta d'an tab'a kana tace " kamar ya Sir Moli?
A hankali Khulud tace " yana ina?
Cikin masifa Sanah tace " bangane yana ina ba?
"Ko an fad'a maki yawo nake dashi ko kuma shi d'an gidan mu ne ,
dazaki tambaye ni inda yake?
Cikin sanyin murya Khulud tace " kawai na tambaye ki ne,
saboda.......
sai kuma tayi shiru had'i da sunkuyar da kanta k'asa,
ido Sanah ta k'ura mata bata ko k'iftawa,
zatayi magana Mamu tace " hala an manta damu ko?
Da sauri Khulud ta d'ago ido tana mik'awa Mamu hannu tace " lah ba haka bane Mamu My Sanah ce ta d'auke man hankali,
Mamu tayi murmushi tana cewa " ai naga alama,
tayi maganar tana zama kusa dasu،
cikin sanyin murya Khulud ta gaida Mamu,Juju,Didi da Abbu duk suka amsa Abbu yana shafa kanta ,
cikin so da k'auna,
Abbu ya tambaye ta abinda take san ci ,
ta kalli Sanah tace " My Sanah me zamu ci?
Sanah da har lokacin idanta yana kan Khulud ta k'ura mata ido,
tun tambayarta Sir Moli datayi,
ta d'anyi guntun murmushi kana tace " anything,
tayi maganar a tak'aice,
Khulud ta kalli Abbu tace " nasan babu abinda my Sanah tafi so kamar shawarma da gashashshan kifi karfasa,
da kuma ice cream,
Abbu ka siyo kana su,
"to yanzu kuwa, Abbu yace ya fita,
Mamu ta mik'e ta had'awa Khulud ruwan wanka mai d'umi,
tayi wanka da brush,ta kuma rama sallolin da ake binta,
tana idarwa Abbu ya shigo ya mik'awa Sanah ledojin su ,
ya mik'awa Mamu nata, kana ya mik'awa Didi da Juju nasu,
suka amsa suna godiya ,Didi yace " wannan sauran ledoji ukun fa ,ko na amaryar ne?
Yayi maganar cikin zolaya,
" wacce amarya na iyayen mu ne,
Abbu ya fad'a yana dariya,
Didi yace " kai dai ka fad'i gaskiya ko kana tsoro ne?
Yayi maganar yana kallan Mamu,
murmushi Mamu tayi tace " tsoran wa zaiji?
Duk suka saka dariya,
hankalin Sanah da Khulud nakan Ice cream, shawarma da gashashshen kifin su,
Abbu yace " to ni fa zan tafi naga 12:20 ya fad'a yana kallan agogon hannunsa,
Didi yace " muna ai tafiyar zamu yi,
sukayiwa su Mamu sallah suka fice.
Washe gari da safe k'arfe 8:30am na safe Doctor ya shigo sanye cikin cot ,
fuskarsa d'auke da fara'a ,
ya kalli Sanah yace " good morning Mrs Cry,
"no ka bari na gaida ka,
tunda nice k'arama ,
murmushi yayi yana k'ara jin yaran na burge shi,
saboda hankali da nutsuwar su,
har k'asa Sanah da Khulud suka durk'usa,
had'i da cewa ina kwana?
" Lafiya lau,
ya amsa yana murmushi,
"an tashi lafiya?
" Alhamdulillah ya basu amsa،
duba Khulud yayi sosai yaga she is normal ,
babu abinda yake damunta,
dan haka ya basu sallama,
sosai Khulud da Sanah sukayi mishi godiya,
Mamu ta kira Juju ta sanar da ita an sallame su,
kar ta sha wahalar kawo breakfast,
Juju tace " ok badamuwa zanyi na naje muku idan kun k'araso sai kuyi break d'in a gida,
Mamu ta amsa mata da " to,
tana kashe wayar ta kira Abbu,
yayi picking bayan Mamu ta gaidashi ,
ta sanar da shi an basu sallama ,
yace " ok dama ganin nan na kusa k'arasowa,
"ok Mamu tace ,kana ta kashe wayar,
Abbu na k'arasowa ya nemi Doctor ya kuma yi mishi godiya sosai,
kana ya kwashi su Khulud suka yi gida,
kafin suje gidan har Mamu tasa 'yan aiki sun shirya breakfast akan dinning table ,
sai da suka karya kana suka shiga part d'in kakanin su,
saboda dakyar Abbu ya basu hak'uri suka zauna a gida ,
yayi ta kwantar musu da hankali yana lallashin su,
sannan suka hak'ura,
dan tuburewa sukayi sai an kai su Hospital d'in su duka,
bayan sun dawo suka shiga bedroom yin bacci.
_BAYAN SATI BIYU_
Sosai Khulud ta warke garau ,
dan har sun koma islamiyya,
ganin haka yasa Abbu kiran su parlor,
bayan sun zo ya kalle su yace " to yaushe za'a koma makaranta?
Kafin Khulud tayi magana Sanah tayi saurin cewa " Allah ni dai Abbu ban san boarding school,
a samar mana day school kawai mu koma,
amma ni ban k'ara yin boarding,
na gama yin boarding har abada,
Khulud tayi saurin kallanta dan ba haka taso ba,
dan ita taso su koma Computer Girls Secondary School Roni,
amma dole ta hak'ura tunda My Sanarta bata so,
ita kuma duk abinda Sanah bata so ta barshi har abada,,
saboda bata k'aunar duk abinda zai shiga tsakanin su ko ya raba su,
shiru tayi batare data ce komai ba,
ganin yadda tayi shiru yasa Abbu cewa " Khulud ko kinfi san boarding d'in ne?
Yayi maganar idanshi na kanta,
murmushin yak'e tayi tace " a'a Abbu nima ban san boarding d'in a canja mana kawai,
" wacce kuke so?
Abbu ya tambaye su,
duk suka ce " babu,kawai ka zab'a mana kowacce,
"ok ku tashi kuje,
Abbu ya fad'a,
washe gari Abbu ya aika Aarib da Ziyad suka amso musu transfer,
bayan kwana uku Abbu ya samu musu admission a Momy speed international School,
makarantar private School ce mai shegen kyau,
ranar Monday suka fara zuwa,
Ziyad ne yake shaidawa su Sanah Halan sunyi candy tun last week,
aiko suka addabe shi akan sai ya kai su wajenta sun ganta,
dole tasa ya kai su dan itama ta dame shi da maganar su,
yana yin parking suka fito da gudu suka shiga gidan,
Halan na zaune a parlor tana yankan salad taga su Sanah,
cike da murna da farin ciki ta rungume su,
dan kwata-kwata Ziyad bai sanar da ita zuwansu ba,
Halan ta kalle su tace " I really misses you so much my dears ,
dariya suka yi kana suka ce " we miss you too ,our Aunty ,
Sanah tace " Allah Aunty Halan kullum sai munce Yaya ya kawo sai yak'i,
yau ma dakyar ya kawo mu,
Halan tayi dariya tace " ni ma haka,har cewa nayi ya kai ni na gano ku amma ya k'i,
baki Sanah ta turo tace " aiko bamu komawa sai dai ya tafi shi kad'ai,
"yauwa My Sanah ku zauna anan,
Khulud tace " muna nan har sai randa zaki koma gidan mu sai mu tafi tare,
mahaifiyar Halan dake zaune kan sofa tace " aiko baku isa ba,
idan kuka zo kun zo kenan ban barin ku,
ku koma,tayi maganar cikin fara'a da sakin fuska,
kwata-kwata basu lura da ita ba,
sai da tayi magana,
cikin nutsuwa suka durk'usa har k'asa suka gaida ita,
ta amsa tana d'ago su,
wayar Halan ta fara ringing tayi saurin picking ,
yace " wato anga su Khulud an manta da ni ko?
" Lahhhh yi hak'uri Allah sun d'auke man hankali ne,
tayi maganar cikin shagwab'a,
mahafiyarta ta jefa mata uwar harara wanda tasa ta saurin mik'ewa tana dariya ta nufi bedroom d'inta,
tana shiga tace " ka sani na manta nayi picking gaban Nanan mu,
dariya yayi yace " ni dai ki fito ina waje,
"to tace ,fuskarta ta d'an gyara kana ta fesa perfumes masu sanyin k'amshi,
anan ya bar Sanah da Khulud,
sai dare ya dawo d'aukar su,
koda ya dawo k'in fitowa sukayi,
suka cewa Halan tace masa su sunzo kenan,
da Halan ta fad'a masa cewa yayi taje tazo dasu,
Sanah tace " Allah ko naje haka zan fad'a masa tayi maganar tana murgud'a baki,
daga bakin k'ofar sit room suka tsaya,
ya had'e fuska yace " muje ko?
Ya fad'a batare daya kalle su ba,
Khulud tayi gaba sumi-sumi ganin ya had'e rai,
dan har tsoro ya kamata ,
amma Oga Sanah sai ta shiga bubbuga k'afa tace " please Yaya ka barmu nan,
ido ya zaro yace " exam d'in da zaku fara next week fa?
Sanah tace " daga nan zamu rink'a zuwa ai,
yace " wazai rink'a kai ku?
Sanah tace " Aunty Halan mana,
ya zaro ido sosai ,kana yace " wacce Halan d'in,amma badai tawa ba ko?
Sanah tace " taka kuma Yaya ko ta mu,ko harka kwace mana ita?
Dariya yayi yace " a'a ,dan ya lura Sanah bata tsoran zare ido,
sai dakyar Sanah tabi Ziyad shima sai da yayi musu alk'awarin dasun gama exam zai kawo su,su zauna har ayi biki,
bayan sati uku da fara zuwan su Khulud school ,
aka fara 3thr term exam,
duk da a k'urarran lokaci su Khulud suka shiga school d'in su,
sai da suka yi matuk'ar bada mamaki dan Sanah ta d'auki 1st position Khulud second ,
a islmaiyya kuma Khulud ta d'auki 1st position Sanah second ,
dan dama Khulud tafi Sanah k'ok'ari a ismiyya,
suna dawowa gida suka tarar da duk 'yan gidan a parlor,
da gudu Sanah ta fad'a jikin Aarib ,
Zarfan kuma ya mashi result d'in su,
yana dubawa, Ziyad yace " meye kuma na dubawa kai da ka san na yadda suke zuwa?
" Ai dole a duba saboda sabuwar makaranta ce,
Mamu tace " to yanzu na nawa suka zo?
"Yadda dai suke,tayi murmushin jin dad'i tace " ai har abada ba'a canjawa tuwo suna,
Sanah ta kalli Ziyad tace " Yaya ya alk'awarin mu?
"Na me fa?
Ya tambaye ta,
baki ta turo tana buga k'afa tace " Yaya zaka fara ko?
" To ikon Allah,kin tab'a ganin an kama mutum da laifin dabai sani ba?
Khulud tace " Yaya kai fa kayi mana alk'awarin damun gama exam zaka kai mu gidan su Aunty Halan har a gama biki,
dariya yayi yace " yara ai yanzu an shiga Inconclusive,
dan haka kuma kun shiga inconclusive,
Sanah ta tab'a baki zatayi kuka Khulud tace " no please karki yi kuka ki bari muje idan yace bai kai mu nima sai ma tayaki kukan,
Sanah tayi saurin mai da kukan ,
duk suka zuba mishi ido suna jiran suji abinda zai ce su fara kuka,
"kambuuuu Ziyad yace yana dariya,
" wato tsabar rai nin hankali har mai da kuka ake yi ana jiran mai zance ko?
Duk sukayi shiru babu wanda yace masa k'ala,
ganin yadda duk suka kafe shi da ido,
yasa shi cewa " to ban kai ku,
aiko suka had'a baki suka saki kuka lokaci d'aya,
Aarib yayi saurin cewa " kuyi shiru please ni zan kai ku,
kamar d'aukewar ruwan sama suka yi tsit,
Ziyad ya kuma yin dariya,
Mamu tace " naga nan gidan ma bikin za'ayi,
kuma ai kamata yayi ku tsaya wajen Aroos (yayar Khulud wacce take bi),
Sanah ta zumb'uro baki,
Idrak angon Aroos (dayake auren zumunci za'ayi musu),
yace " au wato baku tsayawa ku taya tawa amaryar hidimar biki ko?
Sanah tace " ita ai bata san mutane,
tafi san komai nata tayi ita kad'ai,
Mamu tace " uwaki,Yayarki kike cewa haka?
Khulud tace " Allah Mamu haka take ,
shiyasa muma muke ja baya,bata da kirki gata da saurin dukan mutane da zagi,
Idrak yace " aiko sai na fad'a mata,
Sanah tace " ai halinta ne,ta juya ta kalli Aarib tace " Yaya kai yaushe zakayi auren?
Ido kawai ya kafe ta da shi batare dayace komai ba,
dole tasa su Khulud hak'ura da zuwa gidan su Halan dan biki uku za'ayi a gidan,
bikin Ziyad & Halan,
sai bikin Aroos & Idrak da bikin Zafran & Seenah,
Seenah 'yar mak'otan su,ce yarinyar mai hankali da nutsuwa kamar Aroos & Halan,
itama iyayenta mutanen kwarai ne,masu mutunci da kamala,
kamar na Halan.
satin biki na zagayowa aka shiga hidimar biki kowa ba zama yayi busy musamman Juju da Mamu,
ba wata bidi'a akayi sosai ba,
anyi yinin biki normal sai walima da wa'azi,
ranar Friday a babban masallacin juma'ar gidan sarkin kano bayan an idar da sallar juma'a millions mutane suka d'aura auren,
Halan & Ziyad
Aroos & Idrak
Seenah & Zafran,
a ranar kowacce ta tare a gidan ta dake Hard'o Family estate,
sosai mugun sabo da shak'uwa ta k'ura shiga tsakanin Halan da su Sanah,
suka kuma mai da hankali sosai akan karatun su.
_BAYAN SHEKARU 5_
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
1⃣5⃣
_BAYAN SHEKARU 5_
Tafiya suke sannu a hankali cikin nutsuwa kamar basu san taka k'asa,
sanye suke da uniform mai kalar peach color ,
da guntun hijab wanda k'irjinsu kawai ya rufe,
'yan mata guda biyu santala'sanatala,
san kowa k'in wanda ya rasa,
gaba d'ayan su kyawawan gaske ne ajin farko,
irin mata nan da zakaji ana kira da full option,
wato komai yaji, babu abinda zai k'ara d'aukar hankalinka a ajikinsu sai kalar fatar jikinsu,
wacce ita ba fara ba ba kuma bak'a ba,
wato chocolate color,kalar su tafi ta fararen mata kyau da tsada,
saboda fatar su tafi laushi da tsantsi,
duba nakai kan k'irjinsu naga na fulanin su tantsan-tantsan,
a hankali ya gangaro da ido na zuwa k'ugun su,
"masha Allah kawai na iya furtawa,
saboda sun wuce iya kar kyau da had'uwa,
matasan 'yan mata masu ji da kyau da k'uciya 'yan 16yrs,
daga bedroom d'in su suka fito,
cikin sauri da alama sauri suke yi,
cornflake naga d'aya daga cikin su ta d'eba takai bakinta ,
tana sauri ta kurb'i ruwan madarar dake gefe ajeye cikin glass cup,
wata dadtijiwar mata naji tace" SANAH bazaku tsaya kuyi breakfast bane?
Wacce aka kira da Sanah ta jiyo a hankali tana murmushin dayasa dimples d'in dake kumatunta lutsawa,
jerarrun fararen hak'uranta masu d'auke da siririyar wushirya suka bayyana,
hakan ne ya bani damar k'arewa faffad'ar fuskarta kallo mai d'auke da dogon hanci ,
da dara-daran idanu farare tass,
kalar kwayar idanta blue color,
badan a Nigeria na ganta ba da sai na rantse Pretty Zinta ce ,
domin babu abinda ya raba su ,
sai kalar fatar jikinta da lulu eyeball d'inta,
sai daga k'ugu tafi Pretty Zinta hip da fad'in k'ugu da cikar booms nesa ba kusa ba,
rolling lulu eyes d'inta tayi masu kamar tana jin bacci tace " no Mamu munyi late ,saura 2hr kawai mu shiga final exam,
Mamu tace " to kuma shine bazaku tsaya ku karya ba?
"Bayan naga kuna da sauran lokaci,
Mamu ta fad'a tana kallan Sanah,
d'an tsukakken bakinta mai d'auke pink lips ta turo tace " Mamu yau ne ranar Graduation's d'in mu,
shiyasa bana san muje a late,
Mamu tayi murmushi kana tace " au to cewa zakiyi duk murnar kammala karatun Secondary ne yau,
Sanah tayi dariya tace " ashe dai kin gane our Mamu,
daga yau bamu da fama da uniform,
Mamu tace " Khulud kema bazaki k'arya ba?
Wacce aka kira da Khulud na kalla ,
can k'asan mak'ogwaro na ,na furta masha Allahu,
Ubangiji yayi halitta anan, dan itama kyakkyawa ce ta gaban kwatance,
siririya dogowa mai doguwar fuska ,
abu d'aya Sanah zata nuna mata shine wushirya da dimples,
sai kuma bam-bamcin halitta,
ita Sanah 'yar duma-duma ce irin jikin Jennifer Lopez,
ita kuma Khulud siririya ce mai irin jikin Thamanna Batia,
Sanah tad'an fi Khulud jiki da k'ira,
ita Sanah dirarriyar mace ce,
Khulud kuma irin matan nan ne da ake kira American Lady,
saboda irin jiki da shape d'in turawa ne da ita,
silent smile tayi tace " no Mamu ba sai mun karya ba,
idan muka je maci abincin,
baki Mamu ta tab'e tace " kwaji dashi dai,
ai dama nasan tunda Sanah tace " a'a kema a'an zaki ce,
Khulud ta kuma yin murmushi tace " eh mana Mamu ai ba'a tab'a raba d'aya biyu,
Mamu tace " ku dai kuka sani, idan zaku wuce ku d'auki Mash su mik'awa Halan d'anta ya dame ni da k'iniya,
baki Sanah ta turo tace " yanzu sai an samu d'aukar yaro Mamu?
Mamu zatayi magana Khulud tace " bakomai Mamu bari sai mu mik'a shi tayi maganar cikin sanyinta,
a hankali Khulud ta d'auki Mash dake ta wasa,
har sun kai bakin k'ofa Mamu tace" Khulud idan kunje kucewa Halan ta turo man da Maheen tazo,
"to Khulud tace kana suka fita,
direct part d'in Halan suka shiga,
a bakin k'ofa suka iske ta rako Ziyad ,
suna tura k'ofa Halan takai bakinta tayi masa kiss,
Sanah ta zumb'uri baki had'i da cewa " 'yan iska kawai,
tayi maganar cikin ranta,
Khulud ko kauda kanta tayi gefe ,
Halan tayi dariya tana cewa " ah ah kaga 'yan candy yau,
Sanah bata kulata ba, sai Khulud ce tace " Allah Aunty Halan yau ji nake kamar anyi man bushara da aljanna,
Halan tayi dariya tana cewa " ai haka ne dama ,
musamman kuna ganin zaku shiga sawon'yan mata,
Sanah tace " au yanzu mu ba 'yan matan bane?
Dariya Halan tayi tace " kwailaye dai,
Sanah ta turo baki " haba Aunty Halan we are 16yrs now and you call us kwailaye?
Halan zatayi magana Ziyad yace " dan ubanku baku iya gaisuwa bane?
Sanah ta kawar da kanta tana turo baki,
Khulud tace " yi hak'uri Yaya bamu lura da kai bane,
ina kwana?
Ta fad'a cikin girmamawa,
lafiya lau ya amsa mata fuskarshi a sake,
kallansa ya maida kan Sanah yace " ke zanci uwarki fa,
shegiya mai fad'in ran tsiya,mai bak'in hali,
Halan tace " a'a Abban Maheen karka kuma ce mata mai bak'in hali ba kyau,
a fusace yace " ai daman ke ke d'aure mata gindi take zubawa mutane iskaci da fitsara san ranta,,,
Khulud tace " please Yaya kayi hak'uri,
Halan ta kalli Sanah taga ko ajikinta yadda kasan bada ita yake magana ba,
idan Halan na kanta tace " Sanah!,
Sanah ta juyo ta kalle ta,
Halan ta nuna mata ta gaida shi da ido,
Sanah tace " oh! wai dama dani ake?
"Ai ban sani ba,
tayi maganar tana mik'ewa tace " sorry Yaya good morning,
ko kallanta bayyi ba yayi tsaki yayi ficewarsa,,
ta bi bayan sa da harara,
Khulud ta kafe ta da ido had'i da cewa " it's not good my Sanah, bai kamata ba,
Sanah tace " to shi abinda yayi yanzu ya kamata?
Halan tace " mai yayi?
"Ai ke dama bazaki ga abinda yayi ba,
Halan tace " oh ni Halan shi yace bana ganin laifinki ko ban san laifinki,
kema kice ban ganin laifin sa ko ban san laifinsa,
ni dai kun sani a tsakiya ,
ta fad'a tana dafe kanta,
Sanah tace " ina Maheen?
"Tana kitchen wai breakfast zata koyi had'awa,
Sanah ta zaro tana cewa " she's 4yrs fa,
Halan tace " a to na sani kotayi gadan rawar kai wajen k'aramar uwarta,
"wajen wacce uwar tata?
Halan tayi dariya tace " ni dai ai ban ambaci sunan kowa ba balle a kama ni da laifi,
"hmmmm kima ji da tsohon cikin ki,
bada tsokanar mutane ba,
" ai dole naji dashi tunda a jiki na yake,
Sanah ta mik'e had'i da dafe bayanta,
tana gwada irin tafiyar Halan tace " to mu zamu tafi,
Halan takai mata duka tana dariya,
itama ta goce tana dariyar,
Halan tace " rai dai ,ni ma zan rama,
wama yasan irin naki cikin ke,
Sanah tace " aiko bazaki rama ba,
dan ni ba anan k'asar zanyi goyan ciki na ba,
balle har ki gami,
Halan tace " ai in dai nan cikin duniyar zakiyi ciki sai na bi ki,
ko'ina ne na gano,
Sanah na shirin fita Halan ta kalli bayanta,
ta zaro ido tace " Sanah bleeding kike ne?
A d'an tsorace Sanah tace " bleeding d'in me?
Halan tace " period mana,
"ina period d'in yake?
Sanah tayi maganar tana zaro ido,
Halan tace " gashi nan ya b'ata ki,
dariya Sanah tayi tace " wai ni zaki ma wayou dan ki kama ni ko?
Halan tace " Allah da gaske nake yi maki,
jin Halan ta rantse yasa Sanah zaro ido tace " please seriously da gaske kike?
Halan ta kuma cewa " Allah da gaske ,
ta kalli Khulud tace " zo ki gani sai ki fad'a mata,
cikin sanyinta Khulud ta mik'e ta zo tana duba bayan Sanah,
kallanta kawai Khulud tayi ,Sanah ta gane da gaske ne,
ta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace " just 2 weeks back ba nayi wanka,
Halan tace " ai tun kuna SS 1 nace miki kije kiga Doctor kika a'a is normal,
amma bleeding d'in yayi yawa ,kuma duk after 2 weeks period ya dawo ai da matsala idan kikayi aure,
a tsorace Sanah ta kalli Halan idanuwanta duk waje tace " wacce irin matsala kuma?
Dan kwata-kwata bata fahimci abinda Halan ke nufi ba,
murmushi Halan tayi kana tace " ke is not so serious issue ,
"are you sure?
Sanah tayi maganar cikin sanyin jiki,
Halan tayi dariya kana tace " yes Ma'am,
Khulud tayi murmushi tace " oh! ni dai na huta da wannan jidalin,
"wanne jidali?
Halan ta tambaye ta,
Khulud tace " na period mana,
Halan tace " kamar ya kin huta bayan kowacce mace bata da hutu akan shi?
Khulud tace " aiko ni Allah ya hutashe ni,
Halan tace " wai kamar ya Allah ya hutashshe ki?
Kai tsaye Khulud tace " ai ni ban fara ba ,
a kid'ime Halan ta zaro ido "what!?
Tace a razane,
murmushi Khulud tayi kana tace " yes mana,
a firgice Halan tace " wai kina nufin baki fara period har yanzu ba?
Ta tambaye ta cikin tension ,
Sanah tace " eh bata fara ba,
akwai damuwa ne?
"Innalillihi wa'inna ilaihirraji'un,
Halan tace ,Sanah da Khulud suka kalli juna cike da tsantsar mamaki,,
cikin tsoro Sanah tace " meye Aunty Halan?
Halan tace " tunda kika fara 2yrs back dama ita bata fara ba?
Cikin sanyin jiki Sanah ta d'aga kanta,
a sanyaye Khulud tace " lafiya Aunty?
Halan tace " amma shine baku fad'a anje hospital ba?
"Hospital kuma?
Khulud tace,
" eh man ai dole aje hospital dan aji meke faruwa,
mace 16yrs bata fara period ba ai akwai damuwa,
ta kalle su tace " uban me ya hana ku fad'a?
Cikin sanyin murya Sanah tace " bakomai ,ai mun d'auka there's no problem ne,
"ubanwa yace muku babu problem?
Halan ta fad'a a tsawace,
tunda suke da Halan bata tab'a yi musu ko kallan banza ba,
balle har ya kai ga tsawa ba yau sai yau,,
gasu yanzu a k'alla sun kai wajen 6yrs da ita,
saboda yadda take nuna musu so da k'auna take kuma jan su ajikinta sosai,
yasa suma suka fi sabawa da sakin jiki da ita sosai akan Seenah da Aroos,
tunda sun fahimci halin Seenah da Aroos kusan d'aya ne,
shiyasa ta su ma tafi zuwa d'aya akan Halan,
duk da babu wani rashin jituwa ko matsala a tsakanin su ,
su duka ukun,suna zaune lafiya babu wata damuwa,
tare suke yin komai,kan su a had'e yake sosai sai dai d'an abinda ba'a rasa na yau da kullum ba,
ko yaran su kan su a had'e yake suma sosai, komai na su iri d'aya ne,
dan Danish da Ganez suna iya bakin k'ok'arin su wajen ganin sun had'e kan zuri'ar su,
ta yadda ko bayan babu su,sun san basu tafi sun bar baya da k'ura ba,
kuma Alhamdulillah family'n su yana zaune lafiya cike da so da k'aunar juna,
basa tare da wata matsala ko rashin jituwa a tsakanin su,
haka ma Rawan da Hamraz suna iya yin su dan ganin sun kafawa zuri'arsu zumunci mai k'arko da dank'o,
shiyasa kullum suke k'ara nusar da yaransu mahimmanci, amfani da k'arfin zumunci,
suna koyar dasu su zama tsintsiya mad'aurin su d'aya ,
kuma cikin ikon Allah sunyi narasar kafa hakan a zukutan ahalinsu,
kowa cike yake da san d'an uwansa babu wani nuna bambamci ko ware-ware,
duk sun d'auki kansu d'aya,babu abinda wani zai zartar batare da sani ko shawarar junansu ba,
dan k'ara k'arfafa zumuncin su yasa every last Saturday ta k'arshen wata suke family meeting,
yaran Halan biyu mace da namji Maheen itace babba sai k'aninta mash,
sai yanzu data ke tsohon ciki haihuwa yau ko gobe,
Aroos kuma yaranta biyu duk mata Aabish ce babba sai Aairah bata kuma da ciki,
dan tace sai ta huta,
Seenah yaranta d'aya namiji Ejaz itama tana da ciki.......
Duk sukayi shiru cikin sanyin jiki ta kalle su tace " saura awa nawa ku shiga last exam?
"1hr 40 minutes Khulud ta bata amsa cikin sanyin jiki,
dan tunda suke da ita basu tab'a ganin b'acin ranta irin na yau ba,
ta kalli Sanah tace " na baki just 10 minutes kije ki gyara jikinki kizo yanzu mu tafi holital,
Hospital ?
Sukace cike da mamaki,
batare data kalle su ba , ta d'auki wayarta tayi hanyar bedroom tana dialing number Ziyad,
duk suka bi bayanta da kallo,
Khulud tace " kiyi sauri ki shirya naga alamar yau ranta yayi masifar b'aci,
"ok kawai Sanah tace tana barin wajen,
a parlor ta tarar da Mamu zaune akan sofa da remote a hannunta tana canja channel,
cikin mamaki Mamu ta kalle ta tace" au dama baku tafi ba?
Sanah tace " eh jiki na zan gyara tayi maganar tana shiga d'aki da sauri,
cikin gaggawa Sanah ta shirya, ta fito da gudu zata fita,
Mamu tace " kin d'ibi pad & pant spare?
Kanta ta dafa alamar mantuwa kana ta juya ta kalli Mamu tace " thank you,
ta koma d'akin da gudu ta d'ebo ta watsa cikin school bag d'inta ,
ta fita da gudu, a harabar gidan ta iske Khulud da Halan tsaye ,
suna ganinta suka shiga bayan mota ,
driver ya ja motar,
a harabar Nasarawa Hospital sukayi parking,
batare data kalli inda suke ba ta fita suka bi bayanta,
bayan ta gama yiwa Doctor bayanin matsalar data kawo su,kana ya kalli Khulud yace " kina jin ciwo ko wani abun ne?
Tace " a'a ,
yace " baki jin wani sigh a mararki ko cikin ki?
Tace " eh ban jin komai,
a hankali ya mik'e yaje bakin gadon dake cikin office d'in,
ya kalle ta yace " Bismillah,
ba musu ta mik'e taje inda yake tsaye,
yace " kwanta,
gyara mata kwaciyar yayi ,
sannan ya d'an d'aga rigarta yayi k'asa da wondon uniform d'in dake jikinta,
yasa hannu a hankali yasa d'an danna mararta,
yace " duk inda na tab'a kikaji zafi ko wani emotions kiyi man magana,
tace "tom,
yakai wajen 10 minutes yana tab'awa amma batayi magana ba,,
ya kalle ta yace " baki ji komai ba?
Tace "eh,
" sakko yace mata,yana barin wajen,
'yan rubuce-rubuce yayi kana ,ya kira nurse yace " kije da ita,
ki kaita Scanning room,
za'ayi mata Scanning kala biyu,
na mara dana mahaifa,
sannan ki kaita lap a d'ebi jininta,
"Ok Sir tace cikin girmamawa,
sai da suka yi wajen 1hr a hospital d'in ana gwaje-gwaje da aune-aune,
sannan Doctor ya dawo , ya karkata gaba d'aya hankalinsa ga Halan,
yace " gaskiya munyi mata duk abinda ya kama,
munyi mata Scanning & tests amma bamu ga komai,
asalima lafiyarta k'alau tana cikin k'oshin lafiya,
babu wata matsala ko damuwa,
kana ya d'ora da cewa " kowanne mutum da kika gani akwai irin nau'in halittarsa,
da kuma kwayayensa,da organs & cell d'in jikinsa,
dama ana iya samun irin haka,
sai kiga wata macen ma takai 22yrs bata fara period ba,
ko kuma kiga mace bata da ciki ,
asalima bata da auren amma sai kiga tayi wajen 5monts batayi period ba,
muna kiran abun a likitance Hormonal imbalances,
kuma abubuwan dake haifar da haka suna da yawa akwai,
Birth Control,
Thyroid irregularity ,Polycystic ovary syndrome (PCOS),
Early peri menopause,
Stress ,weight loss and Breastfeeding,
wad'annan abubuwan suke iya haifar da dad'ewa ba'a fara period ba,
ko mace ta dad'e bata ga yazo ba,
amma ita Khulud lafiyarta k'alau kawai Allah ne yasa bai zo ba,
ajiyar zuciyar Halan ta sauke,kana tayi masa godiya suka fice,
ana saura 15 minutes su shiga exam suka isa makaranta,
d'alibai na ganin Sanah suka saki ihuuu ,
dan Sanah popular student ce,Halan taita dariya had'i dayi musu addu'ar sa'a.
Suna fitowa daga exam hall suka fara sakin ihuuu,
wasu daga cikin students d'in na yayyaga uniform d'in su,
duk d'alibin daka kalla a ranar kasan yana cikin tsananin farin ciki,
assembly principal da teachers sukayi musu as usual sukayi musu nasiha mai ratsa jiki da jijiya,
aka basu shawarwari akan rayuwar duniya,
daga wajen assembly wajen bikin murnar yaye d'alibai suka nufa ,kowa yaci yasha cikin tsantsar farin ciki,
kana aka sallami kowanne students d'auke da kyautar da yasamu,
kasancewar Khulud itace mosque prefect yasa aka bata kyaututtuka masu tarin yawa,
harda Qur'an da litattafan addini,
itama Sanah dayake itace Labour prefect itama tasha kyauta sosai,
dan principal naji da ita sosai,
dama su Sanah sunce kar azo d'aukar su daga gida dan zasu biya wajan saloon da henna,
saboda Abbu ya shirya musu walima a gida saboda tare sukayi Candy da saukar Al Qur'an mai girma,
fita sukayi daga cikin get d'in makarantar suka nufi bakin titi dan shiga napep.
Sanah ta kalli Khulud cikin tsananin farin ciki tace " my Ulud ya kike ji yau?
Khulud tayi murmushi kana tace " wallahi ji nake kamar na zuba ruwa a k'asa nasha dan murna,
muma yau mun girma mun zama 'yan mata Classy & big Beb ,
"ke ya kike ji yau my Sanah?
Tayi maganar tana kallan Sanah,
Sanah tayi gaba had'i da juya bayanta tana tafiya tana fuskantar Khulud,
tace " ni kuma yau ji nake kamar nayi ta burgima a k'asa ina ihuuuun dad'i,
Khulud tace " my Sanah kin juyawa titi baya fa,
kuma kina tafiya da baya-baya bayan kin san ba kyau,
Sanah ta d'aga hannayenta sama cikin farin ciki tana tsalle tace " barni my Ulud yau d'aya nad'an sha iska na wataya,
ta fad'a tana dariya,
d'aga idan da Khulud zatayi taga wata sabuwar mota dalleliya kirar Kia 2019 ,
ta nufo Sanah gadan-gadan,
a kid'ime Khulud ta saki k'ara had'i da d'ora hannu aka,
ganin haka yasa Sanah juyawa a firgice,
shima matuk'in motar kwata-kwata bai lura ba sai da yaji ihuuun Khulud,
a gigice ya taka burki da k'arfi k'uuuuuu,
duk da haka sai da motar ta gogi Sanah,
ta fad'a cikin ruwan dake tare gefen hanya kasancewar kwana akayi ana ruwan sama jiya,
hijab d'inta da d'ankwalinta suka fad'i gefe,
kwantaccen gashin kanta ya zubo ya rufe mata fuskarta,
hannunta ta saka ta kawar da gashin gefe,
bakin bud'e take bin jikinta da kallo ,
taga yadda duk ruwan ya gama b'ata ta,
taga mai motar kwata-kwata bashi da alamar fitowa da alama ma jira yake ta tashi ta bashi hanya ya wuce,
cikin tashin hankali Khulud ta k'araso tasa hannu tana k'ok'arin d'ago Sanah,
tace " my Sanah baki ji ciwo ba dai ko?
Sanah tace " babu abinda ya same ni,
ki koma gefe ga guri can ki zauna yau zanga k'aryar iskanci,
ta fad'a tana kallan motar,
Khulud tayi dariya kana tace " a'a my Sanah ki tashi mu tafi,
zamanta ta gyara sosai a cikin ruwan kana tacewa Khulud " kin san Allah ban tashi,
sai dai mu kwana anan naga k'aryar taurin kai,
d'an gutun tsaki yaja had'i da gyara zansa a cikin motar ya k'ara k'arfin ac,
kana ya kwantar da kujerar motar baya,
ya kishingid'a gami da lumshe idonsa,
sun kai wajen 30 minutes a haka Khulud na tayiwa Sanah magiyar ta tashi su tafi amma tak'i,
idansa ya d'an bud'e gami da kallan agogon hannunsa k'irar Gucci,
ya ja tsaki ganin tana niyyar b'ata masa lokaci,
cikin isa da tak'ama gami da aji ya zuro k'afarsa d'aya k'asan motar ,
sanye da takalmin Gucci sau ciki,
wacce kallo d'aya zakayi mata kasan k'afar d'an hutu da jin dad'in duniya ce,
sai da akayi 2 minutes kafin ya k'ara fito da d'aya k'afar tasa,
nan ma sai da yayi wajen 2 minutes kafin ya fito gaba d'ayansa,
ya taka k'asa kamar baya so,
dai-dai lokacin idan Sanah ya sauka akan.................
0 comments:
Post a Comment