Bakinshi d'auke da kalmar انا لله وانا اليه راجعون
abinda yayi ta maimaitawa kenan,
kafin yaje gidan Khulud yaji zuciyarshi tayi mishi mugun sanyi,
ya samu sassauci gami da nutsuwa da salama,
a k'ofar gidan yayi parking had'i da runtse idanshi while yana cigaba da maimaita kalmar,
take yaji gaba d'aya bak'in cikinshi ya gushe nutsuwa ta saukar mishi,
shiyasa Annabi yace " الدعاء سيف المؤمنين
ya dad'e zaune cikin motarshi idanshi rufe kana ya bud'e idanshi,
had'i da zubawa mai gadin gidan Khulud dake zaune waje kan farar kujera ta roba ido,
had'i da kanrantar yanayinshi,
ganinshi yayi yaro k'arami wanda a k'alla bazai wuce 20yrs zuwa 22yrs ba,
ya tabbatar tunda har yaga matashin saurayi yaro yana aikin gadi,
akwai dalili mai k'arfi, imma dai matsalar family, yana aikin ne danya taimaki iyayenshi da 'yan uwanshi,
wata k'ila ma mahaifinshi ya mutu kuma shine babba nauyi ya hau kanshi,
ko kuma ciwo wato rashin lafiya,
may be wani daga cikin danginshi ko iyayenshi ne babu lafiya,
yake neman kud'in magani....!,
ko kuma kud'in karatu domin karatun Nigeria yanzu nema yake yafi k'arfin d'an talaka,
sai 'ya'yan masu kud'i ko masu hanya,
dan yanzu k'asar ta zama waka sani, waya sanka, waya aiko ka,
dame kazo, ame kazo, nawa zaka bayar....!
abin dai sai dai muce Allah ya kyauta.......!,
ya tabbatar cikin wad'annan abubuwan daya lissafa dole akwai d'aya,
dan haka yasan me zayyi,
guntun murmushi yayi had'i da yiwa motarshi key yayi tafiyarshi.
Bayan Sanah ta kammala kwana biyunta Khulud ta amshi girki,
suna zaune a parlor Khulud ta kalli Sanah tace " yau ko kin kira su Abbu...!?
"A'a jiya dai munyi waya har da Dide da Juju, Mamu da Aunty Halan,
kin san na shiga wata na biyu dan yau ina da 6 week da barin gida,
da aure kuma 4 week kenan,
naji Abbu ya fara maganar k'arshen wani watan zanje gida weekend,
ido Khulud ta zaro a tsorace tace " haba....! haushe yayi miki maganar....!?
" Tun last week yake cewa idan nayi 3 months zanje gida,
shiru Khulud tayi tana tunani kafin tace " to yaya kenan....!,me kike ganin zamuyi....!?
"Ina ganin mu fara tambayar Papu,
bai kamata muyi komai kai tsaye ba,
kamata yayi duk halin da ake ciki ya sani,
da kuma mutsunmu tunda he's our master ko...! amma ke ya kika gani....!?
" Eh..!, gaskiya ne dole a sanar dashi,
saboda koba komai ai zai san an girmamashi,
kuma ya fad'awa su Abbu har da Zohal aka tafi service d'in,
so kar azo ayi baki biyu ko....!?
"Gaskiya dai hakan ne ya kamata kam,
" ok badamuwa idan lokacin yayi sai a sanar dashi,
shi yasan yadda za'ayi zai kuma sanar damu abinda ya kamata ayi,
hira sukayi sosai kafin suka tashi suka shiga kitchen d'ora abinci,
kallan Khulud tayi tace " me zamu dafa ne....!?
D'an shiru tayi kafin tace " mu dafa jollop rice with vegetables da coslow ko...!?
"Eh ..! yayi d'ora to,
" tab! waye zayyi girkin...!?
"Ke mana, Sanah ta fad'a mata,
" a'a kiyi please baki ji yadda mijinki yayi santin sakwarar nan ba,
" hmmm wannan miskilin mijinki naki uban iyaye da felek'e,
wai bayan ya gama ci yana santi shine harda kakarin amai,
cikin dariya Khulud tace " kun dai fi kuwa..! ni dai dan Allah kiyi mana,
ni kuma bari naje na gyara gidan da bedrooms d'in mu da nashi,
batayi mata magana ba, ta soma aikin ita kuma ta fita,
kasancewar su biyu ke aikin yasa basu dad'e sosai ba,
suka gama komai akan lokacin,
Khulud ta shiga bedroom d'inta had'i da fad'awa wanka,
ta fito ta shirya cikin riga da zani na shadda,
bata jima da fitowa parlor ba, ya shigo,
cikin nutsuwa ta mik'e ta amshi jakar hannunshi had'i da rumeshi,
yayi mata murmushi gami da shafo gefen fuskarta,
yace " nayi sa'ar jaruman mata,
gaskiya a cikin month d'in nan kin sani cikin zallar farin ciki da annashuwa,
kina yi min abinda na dad'e ina mafarkin samu daga gare ki,
abinda na jima da ciwonshi cikin raina,
yana cimin zuciya had'i da k'untata rayuwata,
murmushin yak'e Khulud tayi,
had'i rik'e hannunshi taja shi bedroom d'inshi,
yabi bayanta still yana cigaba da fad'a mata yadda yake jin dad'in sex sosai fiye da da,
yake kuma samun gamsuwa da nutsuwa,
bayan ta kaishi bedroom d'in fitowa tayi parlor ta zauna saman sofa,
gami da yin tagumi hannu bibbiyu ta fad'a tunani,
ta jima a haka babu abinda take saukewa sai ajiyar zuciya,
kwata-kwata ya manta da Sanah cikin gidan,
dan haka ya fito daga shi sai towel d'aure a k'ugunshi,
har ya iso gefenta ya zauna bata sani ba,
kallanta yayi cike da tausayawa dan yayi tsammanin tunanin rashin haihuwarta takeyi,
cikin sanyin jiki ya sanya hannu ya zame mata tagumin datayi,
kallanshi tayi a d'an tsorace tace " laaah har ka fito...!?
"Eh...! tunanin me kike haka ....!?
" Naka mana..!, ta fad'a tana murmushi,
shima murmushin yayi mata gami da cewa " ni ai naki ne kin same ni kin gama,
dan gani gare ki sai yadda kikayi dani,
ido ta k'ura mishi tana kallan cikin kwayar idanshi,
tace " dan Allah kayi min alk'awarin har abada baka tab'a san wata mace bayan ni...!
baka tab'a bawa wata mace gurbi a zuciyarka bayan ni...!
ta fad'a cikin sanyi hawaye na k'ok'arin zubo mata,
idan shima ya k'ura mata batare daya ce komai ba,
hannunshi ta rik'e gamm-gamm cikin nata,
tace " please mana dan Allah promise me...!
murmushi yayi had'i da mik'ewa yace " ai an riga an gama soyayya,
dan soyayyar farko itace soyayya duk wanda yayi missing first love d'inshi ya rigada yayi asarar soyayya ta har abada,
mik'ewa tayi tana kallanshi tace " ban gane ba Hanash, me kake nufi....!?
Murmushi yayi had'i da shafa furkarta yace " ana a hubbik, (ina sanki)
badan soyayyar gaskiya ba, da tuni bamu tare, badan mahaukaciya kuma makauniyyar soyayya ba da ban aure ki ba,
wallahi Allah badan so da zallar k'auna had'i azababbiyar soyayya ba bazan aure ki ba,
kuma in badan san kasancewa cikin farin ciki, walwala, annusha da jin dad'i,
da tuni bamu tare so kisa a aranki soyayyar gaskiya ce tasa na aure ki nake kuma zaune dake,
murmushin jin dad'i tayi had'i da yin hugging d'inshi,
tace " I really love you,
kanta ya shafa had'i da cewa "ni ma haka my....!
jin uban tsokin da akaja bayansu ne yasa dukkansu kallan gefen da suka jiyo tsakin,
Sanah suka gani tana nufar dinning table,
daga ita sai boom short wannan wandon mai kama da pant,
da half best iya k'irjinta cibiyarta da santala-santalan cinyoyinta a waje,
sororo Hanash yayi yana kallanta,
yama rasa mezayyi mamaki, takaici, bak'in ciki, jin haushinta ko me....!?
Baki ya saki yana kallanta while Khulud na rungume a jikinshi,
sakinshi Khulud tayi ta nufi Sanah,
tana murmushi tace " my Sanah kin fito...!?
"Eh..! yunwa nake ji, zauna muci abinci,
ta fad'a batare data kula shi ba,
kafe ta yayi da idanshi yana kallan tantagayyar rashin kunya,
shi abinda ma yafi d'aure mishi kai shine ko a kanta balle a jikinta ko ta damu,
a hankali ya taka inda suke ya tsaya kanta while idanshi na kanta,
" hey..! you! ya fad'a yana kallanta,
bata ko d'aga kai ba ba balle ta kallshe,
"keee! dake nake, ya fad'a a tsawace,
kallan Khulud tayi tace " please idan dake yake kitashi ki bishi can ku k'arata,
kar yasa min ciwon kai,
idanshi ya runtse yana jin kamar ya shak'eta,
" wallahi zanci ubanki yanzu,
" please kiyiwa mijinki magana ya dameni fa,
yana yi min haushi aka...!,
a fusace ya dank'o hannunta had'i da fizgota ya dawo da ita gabanshi,
cikin tsiwa tace " meye haka Malam akan me zaka tab'a ni...!?
Ta fad'a tana fizge hannunta,
" meyasa baki da kamun kai, nutsuwa, aji ,tarbiyya, kunya, kara da kawaici irin na mata ne...!?
"Meyasa ke tantagayyar 'yar iska karuwa ce....!?
" Meyasa baki suturta jikinki kamar yadda Allah da Manzonshi sukayi koyi da muyi....!?
"Mai yasa ke ballagar mace ce, mara sanin daraja, k'ima da ciwon kanta....!?
Kallanshi tayi tun daga sama har k'asa had'i da tab'e baki tace " kai yanzu muharramin nawa ne, ko dacewa, k'ima, sanin daraja da ciwon kanka ne yasa ka zo gaba na haka.....!?
Ta fad'a idanta cikin nashi,
kwata-kwata Hanash ya manta daga shi sai towel d'aure a k'ugunshi,
da sauri ya kalli kanshi kana ya mayar da kallanshi kanta,
"ok saboda na fito haka ni da gida kuma ina namiji shiyasa kema kika fito haka...!?
" Nop..! ko d'aya akan me zanyi gasa dakai?,
hakan kawai tsari na ne, so I don't care wai kana nan ko baka nan,
ruwanka ka kalle ni ko ka zauna inda nake haka ruwanka kayi sab'anin haka....!
ta fad'a tana d'age kafad'afa da gira,
kallanshi ya mayar kan Khulud yaga tana dariya sosai,
bayyi mata magana ba ya wuce bedroom d'inshi fuuuu.
Washe gari da safe Sir Moli ya dawo k'ofar gidan Khulud,
zaune inda ya iske mai gadin jiya yauma nan ya iske shi,
a hankali Sir Aryan Moli ya bud'e motar ya fito,
ya taka cikin nutsuwa yaje wajen mai gadin,
mai gadin na ganinshi ya mik'e da sauri yace " Allah Malam ka taimaka min kabar nan wajen,
dan Hajiya tace kar na sake barinka ka shiga,
dan Allah ka bar k'ofar gidan nan kar kayi min sanadin barin aiki na,
shiru Sir Moli yayi yana tunanin statement d'in mai gadin,
" idan har Khulud nada gaskiya bazata tab'a hana mai gadinta ya hanani shiga ba,
idan babu wata k'ullalliya bazata tab'a yin hakan ba,
matuk'ar babu wani abun da suke shiryawa a k'asa bazata hana shi,
shiga cikin gidanta ba,
wannan ma ya k'ara tabbatar mishi akawai wata kitimurmura a k'asa,
ya fad'a cikin ranshi yana murmushi,
takawa yayi ya koma cikin motarshi ya d'auko bandir d'in 100k gida 20 na 2 millions ya dawo ya mik'awa mai gadin,
hannun mai gadin na rawa ya amsa bakinshi bud'e,
Sir Moli yayi murmushi yace " idan ka zama yaro na kuma d'an lek'en asiri na,
zan baka wad'an da suka ninka wad'annan kud'in yawa da komai,
jikinshi yana kerrrrma yace " mezanyi maka yallab'ai..!?
" Tambayarka zanyi amma ban san k'arya duk d'acin gaskiya ka fad'a min,
muddin na gane kayi min k'arya ko sau d'aya ne sai na d'aure ka,
jikinshi na tsuma yace " in sha Allah zan fad'a maka gaskiya iyakar sani na,
murmushi Sir Moli yayi yace " mata nawa ne a cikin gidan nan...!?
" Biyu, da matar gidan da Yayarta,
Sir Moli ji yayi gabanshi yayi muguwar fad'uwa haka nan,
a hankali yace " wacece Yayarta ta...!?
Cikin girmamawa mai gadin yace " wannan wacce kuka tab'a zuwa nan tace ita Yayar matar gidan ce,
take duk ilahirin jikinshi ya d'auki tsuma da kerrrrma,
tabbas ya tuna ranar daya kawo Sanah gidan tace ita Yayar Khulud ce,
har yake tsokarta , tace ai ita da safe aka haifeta Khulud kuma da yamma,
jikinshi na rawa ya zaro wayarshi cikin aljihu ya nuna mishi hotan Sanah yace " duba ka gani wannan ce...!?
Kallan hotan Sanah mai gadin yayi kana yace " eh itace,
" ta tabbata...!?
Sir Moli ya fad'a muryarshi na creaking,
"Eh....! Yallab'ai, dan ranar nan ma sun fita tare, itace ma ta tuk'a motar,
kuma ranar daka zo ita na samu a parlor dana fad'a mata kai ne kazo,
naga ta lek'o ta kanga ta window,
sai kuma lokaci d'aya ta canja jikinta ya soma rawa, ta zama kamar mahaukaciya ta rink'a kuka sosai,
baya yayi kamar zai fad'i yayi saurin tare kanshi da kanshi,
had'i da dafe k'irjinshi saitin zuciyarshi dake barazar tarwatsewa,
bai k'ara yiwa mai gadin magana ba ya shiga motarshi,
ya fige ta yayi gida, da wani irin mugun gudu ya shiga yayi parking,
baiko tsaya rufe motar ba, ya fito yana tangad'i ya shiga cikin gidan,
a parlor ya zube had'i da fasa kuka wiwi tamkar wanda aka cewa mahaifiyarshi ta mutu,
cikin matsanancin kuka yace " why Sanah...!?
"Meyasa zakiyi min haka..!?
" Idan so na ne bakiyi is better ki fito ki fad'a man gaskiya,
bawai kiyi wasa da hankali na ba,
dama shiyasa nayi-nayi dake muyi aure kina k'i...!?
"Bayan kuma kin yarda kin amince kince na turo iyaye na shine kika gudu kika b'oye,
ashe dama baki so na duk wannan tsayin lokacin dama yaudara ta kike yi...!?
" Dama bata zuciya d'aya kike tare dani ba....!?
"Kika yi min rik'on talala, rik'on sakainar kashi, kika azabtar da zuciyata,
kika gudu saboda bazaki aure ni ba,
shine kika ce na turo iyaye na zamuyi aure, ashe dama bada gaske kike ba...!?
" Ba aure na zakiyi ba, yaudara ta kike yi,
kin cuce ni Sanah, kin azabtar da zuciyata, min wahalar da ruhi na,
ALLAH YA ISA TSAKANI NA DAKE SANAH BAN TAB'E YAFE MIKI HAR ABADA,
saboda kinyi wasa da zuciyata,
kin mayar da zuciyata tamkar ball kika rink'a garata kina buga ta,
I can't forgive you, I will never ever forgive you,
Allah yayi min sakayya kin cuce ni kin wahalar dani,
I hate you Sanah, I really hate you mote & more for ever,
macuciya ,azzaluma, mayaudariya, kin cuce ni
ya fad'a cikin matsanancin kuka wiwi tamkar ranshi zai fita.
"Mtswwwwww....! wai Khulud meye haka ne...!?
" Tun d'azu muyi ta abu d'aya,
da kin fara abun arziki rumi-rumi amma yanzu zaki koma halin asararanci da lalancin naki ko...!?
" To wallahi Allah bazan d'auki wannan dabbacin da sakarcin ba,
dama danayi hak'uri na d'auka baki sani bane,
baki kuma iya ba, amma yanzu wallahi ban d'aukar lusaranci,
dan sai yanzu na gane kin dad'e kina cutar dani, kin dad'e kina shiga hakk'i na,
amma yanzu ban iya hak'ura na kuma kawar da kai kina cutata,
tunda na d'and'ani zuma da zak'i na gane da mad'aci kike bani,
na kuma bambamce tsakanin zuma da mad'aci,
so imma zaki zage ki zage dan yanzu na gane dawar garin,
ban kuma k'ara yarda ana ban abu kamar ana bani dusa,
ana yin sex lami salaf babu komai,
Hanash ya fad'a cikin fad'a da fushi,
yana kuma rarumo ta, ya dad'e bakinsu,
still baiji yadda yake samu ba,
hannunshi ya had'e alamar ruk'o yace please kiban yadda kike soma,
dan Allah karki canja dan Allah muyi sex kamar na shekaran jiya,
ya fad'a cikin rarrashi muryarshi na creaking,
" kanta ta dafe cikin zallar bak'in ciki tace " me kake san nayi maka Hanash .....!?
"Yadda kike please dan Allah ki taimake ni,
ya fad'a yana k'ara manne mata had'i da soma romancing d'inta,
jin tayi sororo tayi dud'um-d'um yasa shi sakinta yana jan uban tsoki,
yace " wallahi ban d'auka, I can't take it anymore,
ya fad'a yana juya mata baya had'i da jan blanket,
bayanshi ta kalla hawaye na zubo mata tace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
karfa _*RASHIN SANI....!*_ ya sani jefa kaina da rayuwa ta cikin halaka, da matsala
anya kuwa banyi ganganci ba, na jawowa kai na ba, anya banyiwa kaina babbar illah ba.....!?
Ta fad'a hannunta a kanta kana hawaye,
while duk bayan minti biyu sai Hanash yaja tsoki,
cikin sanyin jiki ta mik'e ta fita daga cikin bedroom d'in ta koma nata,
ta fad'a saman bed had'i da sanya kuka,
yadda Khulud ke kwance tana kuka,
haka Sanah ke kwance cikin d'akinta tana rusgar kuka wiwi,
dan sana'arta ce kuka kullum babu fashi,
tana b'oye damuwarta ne saboda bata san Khulud ta fahimci tana cikin bak'in ciki da damuwa,
take danne bak'in cikin ta da halin datake ciki ne saboda kar Khulud ta shiga damuwa ko taji babu dad'i,
ga kuma abinda nurse ta fad'a mata akan Khulud d'in,
dole kuwa matuk'ar tana san Khulud da gaskiya tayi taka tsan-tsan da lafiyarta,
amma kullum babu fashi sai Sanah tayi kuka sosai,
wani lokacin ma tana kukan bacci ke d'auke ta,
haka kullum babu fashi sai ta kira Sir Moli da sabuwar number ta,
wanda dama dan haka ta siya,
wani lokacin yayi picking wani lokacin kuma bayyi wani lokacin ma rejecting yake yi,
idan ta kira shi bata magana, kasancewar ita matar aure ce,
muryarta al'aura ce a gareshi yanzu,
sai dai taji shi tana sauraron shi yana ta faman cewa " hello..! hello....!,
idan ya gaji kuma yayi dropping,
a ranar dai duk gidan kwanan bak'in ciki sukayi,
wanda da Sanah ce kad'ai ke kwanan bak'in ciki.
Ranar da girkin Sanah ya zagayo,
sai da Khulud tayi tatab'urza da ita sosai kafin ta yarda zata je,
ga Hanash, da Khulud ta fuskanci Sanah ta fad'a ne kawai sai ta fakaici idanta ta jefa mata maganin
cikin tea ta bata tasha,
kana ta shiryata ta raka ta har bakin k'ofar bedroom d'inshi,
kana ta juyo ta koma bedroom d'inta,
ita kuma ta shiga, batare daya kalle ta ba yace " yau ma zuwa kika yi kiyi min kwance kamar ruwan kina jira na sarrafa ki....!?
Batayi mishi magana ba, ta zame rigar baccin jikinta,
ta haye saman bed had'i da jan blanket,
rigar baccin ta dake yashe k'asa yabi da kallo kana ya mayar da kallanshi gare ta,
kwance kawai tayi luf saboda sosai maganin ke d'aukarta,
yana dusgarta zuwa gare shi, kuka ta saka sosai saboda bala'in maganin,
kana ta tashi zambur kamar ana caka mata k'arfe haka take ji,
batayi mishi magan ba ta had'e bakin su,
a gaggauce ta soma yi mishi deep & hot kiss,
tana tsotsar lips d'inshi da harshenshi,
sororo yayi cike da tsantsar mamaki,
yaga jiya akan tayi mishi hakan har kuka tayi suka yi fad'a,
amma yau baga da kanta tana yi mishi batare daya nema ba,
sai ya barshi kawai akan idan ita ke da buk'ata ne take zagewa tayi,
amma idan bata buk'ata take yi mishi kwance,
cikin wani irin mugun rawar jiki,
ta sanya hannu tana shafa k'irjinshi had'i da murza nipple'e d'inshi,
d'aya hannun yana kan joy stick d'inshi tana yi mishi massaging nata,
wani irin nishi ya shiga fitarwa,
take duk ilahirin jikinshi ya soma rawa yana kerrrrma,
bai san lokacin daya soma maida mata da martani ba,
yadda take massaging d'in joy stick d'inshi ne ya k'ara gigitashi,
ya mantar dashi a duniyar da yake,
dan tunda yake ba'a tab'a mishi joy stick d'inshi ba,
balle har a rink'a shafa ta cikin salo haka,
yayinda d'ayan hannunta yake murza nipples d'inshi,
a hankali ta cire bakinta daga cikin nashi ta mayar kan nipples d'inshi ta soma tsotsa had'i da d'an ciza kan,
while d'ayan hannunta yana murza d'aya,
d'ayan hannun kuma yana kan joy stick d'inshi,
cikin salo Sanah ke romancing d'inshi tana gigita duniyarshi,
gantsarewa Hanash ya rink'a yi yana ihuuuu da kwararato,
sosai ya d'aga murya yana ihuuu yadda kasan rai ake zare mishi,
in banda sambatu da saka mata albarka babu abinda yake yake yi,
ear face Khulud ta saka had'i da k'ure volume saboda yadda take jiyo ihuuun Hanash,
yana wasu irin maganganu,
a kid'ime ya tura ta baya had'i da gyara mata kwanciya ya soma raya sunna yana kwasar gara,
ai da Hanash yaji cikin gogin dad'in bai san sanda ya soma gurnani yana haniniya da bambami ba,
" please karki barni nima nayi miki alk'awari ban tab'a barinki ban tab'a rabuwa dake please Khulud,
cikin wata irin murya mai wuyar fassara Sanah tace " tabbas rayuwa ta zama dole a tsakanin mu, ko kana so ko baka so,
saboda k'addara ta riga fata Hanash,
ni matafiya ce ba madauwaniya ba ce, dole akwai ranar rabuwa ta har abada,
yana cigaba da pumping yace " no way babu rabuwa ni dake har abada,
koda bak'ar k'addara ta ganmu ta barmu tare,
sai da ta d'an tsotsi lips d'inshi kana tace " a kullum ina fad'a maka k'addara mace ce mara tabbas da a koyaushe tana iya canjawa,
we shall become what we wish to become, do what we wish to do,
when our habitual thought corresponds with our desire,
bai k'ara cewa komai ba ya cigaba da kashe arna,
a ranar Hanash yasan shi cikekken namiji ne mai ingantacciyar lafiya,
dan sai da ya samu kyakkyawar awa biyu akanta kafin ya samu nutsuwa,
ya sarara mata, gamm-gamm ya rungume ta cikin k'irjinshi,
yana sauke ajiyar zuciya da mayar da numfashi,
sai da ya dawo cikin hayyacinshi kana ya sungume ta sukayi bathroom,
camma sun b'ata lokaci sosai suna TBT (tab'e tab'e) kana sukayi wanka suka fito.
A week letter
Hanash da Khulud zaune a parlor ya kalle ta,
yace " Khulud kin san me..!?
"A'a tace tana kallanshi,
" yanzu nasan nayi aure, amma da wallahi hak'uri kawai nake yi,
na kasa gaya miki, na rasa ta inda zan b'ullo na sanar dake ki gyara,
gabanta yayi muguwar fad'uwa,
amma ta dake tace " meye a bayan...!?
"Tab..! a da hak'uri kawai nake,
dan Allah babu labari kwata-kwata,
lokacin baki iya komai ba, babu abinda kika iya at all fa..!,
ke even romance, balle aje ga shi kanshi sex d'in,
wallahi yadda kika san mad'aci haka kike da,
amma yanzu kin koma zam-zam kamar zuma,
murmushin yak'e tayi tace " oh....! karatu naje na d'auko،
gaskiya na goge sosai dan yanzu Alhamdulillah sai godiyar Allah,
amma da yadda kika san a dafa kaza babu magi da gishi,
sai farin ruwa kawai ace ki ci ya kiji ta....!?
" Hmmm kace haka kake ji na kenan a baya...!?
"Ai wallahi har ya fi haka ma, wannan ai k'aramin kwatance nayi miki amma a baya ai ba labari,
yak'e ta kuma yi had'i da cewa " yanzu an canja,
zayyi magana ya jiyo wayarshi na ringing cikin bedroom,
da sauri ya tashi ya nufi bedroom d'in,
bayanshi tabi da kallo hawayen bak'in ciki da takaici na zubo mata,
wai saboda tsabar cin mutunci da fuska ita Hanash yake cewa " kamar mad'aci, kamar kazar da aka dafa da farin ruwa kawai,
innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
tab...! lalle hummmm sauk'in tama bai san da ita ba...!,
koma dai yaya ita ni ce a wajenshi,
hmmmm ta kuma sauke ajiyar zuciya had'i da cewa " gashi ba abin na tambayi my Sanah yadda take mishi ba,
ace 3yrs da aure amma ban san kome ba, sai na tambaye ta sex ita da bak'uwar abun ce,
any way koma dai mezaice mai kuma zaiji ita nice a wajen shi,
kuma har abadan abidina babu kishi, bak'in ciki ko mugunta a tsakani da Sanah,
koda ace zan iya cutar da kowa a duniya kona ha'inci kowa banda my Sanah in sha Allah,
tana k'ok'arin tashi taji an banko k'ofar parlor'n an shigo,
cikin tsoro Khulud ta kalli wanda ya shigo,
Jaddah ta gani tsaye kanta tayi k'ik'am,
" uhmmm hamshak'iya mandiya,
ashe ana nan har yanzu, Allah dai yasa kina sane da lissafin kwanakin dana baki ko...!?
Cikin tsoro Khulud ta mik'e gabanta yana dukan uku-uku,
tace " sannu da zuwa Jaddah ina yini....!?
"Ke dalla can bak'ar munafuka rik'e ina yininki ni tambayarki nake nace kina rik'e da lissafin ko kuwa....!?
" Idan kuma bata rik'e dashi fa akwai yadda zaki yi da ita ne...!?
Sanah ta fad'a tana fitowa daga cikin bedroom d'inta,
daga ita sai rigar bacci iya cinya,
sosai tsoro k'arara ya bayyana a fuskar Jaddah,
amma ta dake tace " sai ta tafi gidan ubanta akawo wata mai haihuwa,
takowa Sanah tayi tazo gaban Jaddah,
gaf da gaf ta yadda har suna iya jiyo numfashin juna,
" ko kuma ke ki tafi gidan naki ba,
dan nan ita gidan mijin ta ne, gidan da take da gado dashi halak malak,
" idan ita gidan mijinta ne ke gidan ubanki ne...!?
"Hmmmm _*RASHIN SANI...!*_ yafi dare hudu,
ba gidan ubana bane amma nafiki iko da gidan,
Jaddah zatayi magana Sanah ta daga mata tsawa tace " fita daga cikin nan...!,
cikin masifa Jaddah tace " ke kin isa ki kore ni daga gidan nan...!?
"Oh..! tak'marki dai gidan jikanki ne ko..!?
" To bari kiji ko shi kanshi mai gidan idan ya nuna rawar kai da fitsara,
ko yayi abinda ba dai-dai ba ana iya korarshi kuma ya koru wallahi bare ki,
" to shikenan yayi kyau Jaddah ta fad'a tana juyawa,
karta juya ta kuma juyowa ta kalli Sanah tun daga sama har k'asa,
tace " au dama tsirara kika fito zindik'i dake haka....!?
" Idan san ganin tsiraicin nawa kike yi fad'i zan iya bud'e miki ki gani,
cikin masifa Jaddah ta bud'e baki zatayi magana,
Sanah tace " ke..! kina san kici na jaki yanzu ne ko zaki fita...!?
Baki Jaddah ta bud'e cikin mamaki tace " ni...!?
"Eh..! wallahi Allah idan baki fita ba,
zan zage iya k'arfi na nayi miki bugun hukuma,
nayi miki tsinannan duka da zaki kasa tashi,
kinga yanzu dai babu kowa gidan,
jikan naki bai nan bare ya kwace ki,
idan kinje kin fad'i kuma Khulud tana iyayin rantsuwa bata tab'a ki ba,
dan haka ki fita ko na nad'a miki na jaki,
yanzu nan jikinki ya fad'a miki,
Sanah ta fad'a tana nufar Jaddah gadan-gadan,
take jikin Jaddah ya soma rawa yana kerrrrma,
gabanta ya shiga fad'uwa, yana dukan uku-uku,
tsoro k'arara ya fito ya bayya a jikinta da fuskarta,
ganin Sanah na nufarta yasa ta saurin fita har tana tuntub'e,
tace " wallahi zaki san ni kikayiwa haka sai nayi maganinki 'yar iska mara mutunci fitsararriya,
Sanah ta d'aga murya sosai yadda Jaddah zata jiyo ta tace " wallahi kika kuma dawowa gidan nan sai dai motar asibiti ta kwashe ki rab'e-rab'e,
dan sai nayi miki bugun hukuma,
Sanah ta fad'a tana dariya sosai dan tana ganin yadda Jaddah ke sauri harda tuntub'e,
fuskarta d'auke da dariya ta jiyo karaf idanta ya sauka kanshi tsaye a corridor ya hard'e hannuwanshi a k'irjinshi had'i da kafe ta da ido,
ganin yadda idanshi ya canja launi daga fari zuwa ja,
da yadda jikinshi ke kerrrrma yana tsuma,
yasa gaban Sanah muguwar fad'uwa,
cikin ruwan bala'i da tsagwaron masifa Hanash yayiyo kanta...................!
MOMYN ZARAH ('YAR BAIWA)
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
_DEDICATED TO_
*MAMUH GEE*
```THANK YOU SO MUCH FOR LOVING ME MY BE LOVED```
4⃣8⃣
Gabanta ya shiga fad'uwa yana dukan uku-uku,
amma dayake jaruma ce ta dake bata bari tsoron ya fito fili ba,
tsaiwarta ta gyara had'i da hard'e hannuwanta a k'irji tana jiran k'arasowarshi,
idanta cikin nashi tana kallan kwayar idanshi tarrr,
gabanta ya tsaya had'i da kallanta tun daga sama har k'asa,
yace " nan gidan ubanki ne...!?
Baki ta tab'e had'i da cewa " a'a...!
" kina da gadon gidan nan...!?
" A'a ko d'aya,
"akan me zaki korar min Kakata...!?
" Saboda ba alkhairi ke kawo ta ba,
" ke alkhairin ke kawo ki...!?
" Allah masani...!
ta fad'a tana kallanshi,
" akan wanne dalili zaki koreta dan ubanki kina 'yar karere dake...!?
"Eh..! naji ni 'yar kareren ce amma nasan na fita iko da gidan,
" tunda gidan ubanki ne dole ki fita iko dashi ai,
"no..! ba gidan ubana bane, amma nafi ta iko da gidan dan ni ina da gadon gidan,
" saboda gidan tsohon ki ne ko...!?
"Nafi iko da nan fiye da gidan tsoho na,
dan gidan tsoho na Mamu da Juju ke iko dashi,
nan kuma mu ke da iko dashi kuma ina da gadon gidan ko a wajen Allah,
cikin b'acin rai Hanash yace " ke wacce irin jahila da dabba ce...!?
"Jahilai dai....!
a matuk'ar fusace ya d'aga hannunshi da niyyar kifa mata mari,
cikin zafin nama ta rik'e hannunshi,
tana kallanshi ido cikin ido fuskarta d'auke da murmushi,
tace " a'a karka soma wallahi dan yanzu ban d'auka,
dama can arziki da mutuncin masu mutunci kake ci,
amma yanzu ka kuskura kace zakayi gangancin mari na,
wallahi zaka sha mamaki ta fad'a tana sakin hannunshi cikin kyama,
"ke iskancin naki da karuwancin naki har ya kai haka....!?
Ya fad'a idanshi kanta,
murmushin gefen baki tayi had'i da cewa,
" hmmm *_RASHIN SANI...!_* dai yafi dare duhu,
dan in banda _*RASHIN SANI...!*_ da baka furta wannan kalmar ba,
dan idan kowa zai kira ni da karuwa,
'yar iska, fasik'a, mazinaciya kai zakayi tsalle ka bugi k'irji kace a'a,
amma dayake kana cikin _*RASHIN SANI...!*_ babu abinda bazaka iya fad'a ba,
amma duk da haka ka godewa Allah daka kasance kai mai sa'a ne a rayuwa,
idanshi ya rufe had'i da girgiza kanshi yana kallanta,
kana ya bud'e idan ya sauke su kanta,
a hankali ya kuma rufe idon da k'arfi,
ya kuma bud'e su ya sauke kanta,
yace " karki k'ara fitowa haka,
baya ta juya mishi, had'i da sanya hannu ta maida gashin kanta gefe,
cikin salon jan hankali da yaudara,
ta sanya hannu ta ware hannun guntuwar rigar baccin,
ta zame ta fad'i k'asa, ya rage daga ita sai pant, bayanta babu komai dan ko bra babu jikinta,
bayanta ya kallanta cike da tsantsar mamaki,
batare data juyo ba, tace " ko kana da buk'atar ganin gaban ma na juyo....!?
Ta fad'a fuskarta d'auke da munafukin murmushi,
jin yayi shiru yasata takawa tana kad'a duk ilahirin jikinta,
ta tsallake rigar baccin ta shige cikin bedroom,
kanshi ya d'aga sama gami da runtse idanshi da k'arfi had'i da girgiza kanshi da k'arfi,
ya dad'e a haka kafin ya bud'e idon,
k'ofar bedroom d'inta ya sake kalla,
had'i da girgiza kanshi, ya kwalawa Khulud kira da k'arfi,
"Khulud...!?
" gani nan fa a kusa dakai kake faman d'aga murya,
" amma kina tsaye kina kallan iskanci da fitsarar da 'yar uwarki ke yi....!?
" To yanzu Hanash me kake san nayi mata....!?
" Sanah dai ba yarinya bace balle kace in kamata in daka...!,
itama ai tasan dai-dai ta kuma san abinda ba dai-dai ba...!
" amma ke a ganinki abinda tayi yanzu ya dace fisabilillahi....!?
"May be ita a ganinta hakan datayi tayi dai-dai,
" ok yayi kyau ni zan d'auki mataki da kai na,
tunda ke bazaki iya yi mata magana ba,
a d'an tsorace tace " me zakayi Hanash....!?
"Oho..! ban sani ba ya fad'a yana shigewa bedroom d'inshi,
had'i da banko k'ofar bammmm,
kamar zai b'allata, murmushi Khulud tayi had'i da girgiza kai,
tace " ai Sanahr ce ma dai-dai da kai,
Sanah tana shigewa bedroom d'inta ta fad'a saman bed,
tana dariya yau ranta kwal ta k'unsawa Hanash,
wayarta ta d'auko had'i da dialing number shi,
as usual kamar yadda ta saba,
muryarshi na rawa yace " hello...!,
cikin tashin hankali ta mik'e zaune,
jin yadda muryarshi ke rawa da alama bashi da lafiya،
dan muryarshi kad'ai ta isa ta bayyanawa mutum halin da Sir Moli yake ciki,
jin anyi shiru yasa shi yin dropping wayar,
durk'ushewa tayi a k'asa had'i da fasa kuka wiwi tamkar ranta zai fita,
sai da tayi mai isarta kana ta mik'e ta shiga bathroom,
Hanash kwance yayi saman bed d'inshi yana dariya,
dan shi abimma dariya ya bashi sosai,
musamman yadda yaga Jaddah ta tsorata jikinta yana kerrrrma,
cikin dariya yace " dama akwai abinda Jaddah ke tsoro...!?
" Lalle gaba da gabanta aljani ya taka wuta, wato ko baba da babanshi,
kuma ko kaka da kakanshi,
duk abin Jaddah yau taga wanda yafita,
lalle Sanah Oga ce, ya fad'a yana dariya.
BAYAN WATA UKU
Duk yadda kake tunanin mutum zai shiga cikin damuwa,
bala'i da tashin hankali to Sir Aryan Moli ya shiga,
yayi-yayi ya cireta daga cikin ranshi amma abu ya gagara,
abun ya ci tura, duk ya rame ya lalace,
ya wani yargwale, ya zama tamkar ba Aryan Rayyan Moli ba,
ya zama wani kalar tausayi, duk k'iyayyarka dashi idan ka gashi sai ka tausaya mishi,
iyayenshi sunyi har sun gaji sun zubawa sarautar Allah ido,
dan babu rarrashi da hak'uri da Nailah, Hilwa da yayyanshi basu yi mishi ba,
amma a banza yadda kasan ma k'ara zuga shi suke yi,
saboda yadda yaga iyayenshi da ahalinshi cikin tashin hankali sun kuma shiga cikin matsananciyar damuwa a dalilinshi yasa,
kwata-kwata ma ya daina zuwa weekend Maiduguri,
dai-dai da students d'in makaranta sun fahimci baya cikin kwanciyar hankali.
A b'angaren su Khulud kuwa ana nan yadda ake,
kullum Hanash da Sanah cikin fad'a da 'yar tsama suke,
tun wannan zuwan da Jaddah tayi har yau bata k'ara zuwa ba,
Sanah na kwance saman bed taji wayarta ta soma ringing,
kwata-kwata yanzu bata san yawan magana,
bata san hayaniya, bata san a rink'a yi mata magana ma,
abu kad'an ne ke tunzura ta ya hayayyak'a ta,
tayi sama taita ruwan bala'i kuma ba wai iya Hanash d'in take yiwa hakan ba,
har ita kanta Khulud Sanah bata kyale ta ba cikin kwanakin nan,
ita kanta duk abin duniya ya dameta,
ga kwata-kwata bakinta babu dad'i,
ga wani irin mugun cin abincin datake yi, dan a rana sai taci abinci yakai sau bakwai ko fiye da haka,
dan har cikin dare yunwa farkar da ita takeyi,
ga zazzab'in dare kullum dashi take kwana dashi take tashi,
ita babban matsalarta ma yanzu mugun son sex dan kwata-kwata bata jin gajiya,
idan za'a kwana ana sex a kuma kwana bata jin ta gaji...!,
wani lokacin ji take tamkar tayi hauka saboda tsabar sha'awa,
ta kasa zaune ko tsaye idan Hanash bai gidan,
wani lokacin tun kan ya dawo zata shirya ta sanya fuska ta fita parlor tana zaman jiranshi,
yana dawowa bata wani b'ata lokaci take soma romancing d'inshi tun a parlor,
daga Khulud har Sanah suna matuk'ar mamakin wannan bak'ar jarabar datake damunta,
kiran wayar ne ya k'ara shigowa ta motso a hankali takai hannu ta d'auko had'i da kallan screen d'in wayar,
ganin Abbu ne yasata zaro ido had'i da mik'ewa da sauri ta fita,
a parlor ta iske Khulud zaune tana kallan shirin kwana cas'in a tashar Arewa24,
da gudu Sanah ta k'arasa kusa da ita ta zauna,
had'i da zaro ido tace " Abbu ne ke kira,
itama ido ta zaro had'i dayi mata alamar tayi picking,
" a'a my Ulud kar mu d'aga kema fa kin san maganar mu fara kiran Papu muji mai zaice kafin mu d'aga wayar Abbu ko....!?
"Eh..! kema kinyi magana mai kyau bari na kira shi,
ta fad'a tana d'aukar wayarta,
had'i da yin dialing number Papu,
sai da ta kusa tsinkewa kana yayi picking,
cikin girmamawa Khulud ta gaida shi ya amsa a mutunce,
kana tace " kan maganar Abbu ne yanzu ma sai kira yake kuma kasan maganar zuwan Sanah hutu ne..!
"eh..! na sani, mantawa nayi ban k'ara kiranku ba,
ta amsa mishi zata zo ranar Friday,
in yaso Friday d'in sai tace zata biyo k'awayenta suma zasu zo hutu,
"Papu nan da kwana biyu fa kenan...!?
" Eh..! taje idan tayi sati d'aya ya ganta hankalinshi ya kwanta sai tace mishi k'awayen nata suma zasu koma,
dan haka zata bisu su koma tare,
"ok to bari na fad'a mata ta kira shi yanzu,
" yauwa hakan ma yayi, ya fad'a had'i da kashe wayar,
kallanta ta mayar ga Sanah kana tace " ki kira Abbu kice mishi jibi zaki biyo k'awayenki kizo,
bata yi mata magana ba, tayi dialing number Abbu,
bayan sun gaisa ta fad'a mishi kamar yadda suka tsara,
sosai Abbu yaji dad'i yayi farin ciki,
kana sukayi sallama ta kashe wayar,
ta kalli Khulud tace " to za'ayi yanzu.....!?
"Na me fa....!?
Khulud ta tambaye ta idanta kanta,
" kan maganar tafiyar mana,
"eh..! normal ne ai, kawai jibin zaki je, ni kuma after kamar 2days sai nazo ko.....!?
" A'a ba haka ya kamata ayi ba,
kamata yayi naje can na same ki, kina jira na, da sunan kinzo tarbata,
in yaso shi kuma Hanash ki fad'a mishi hutun mu ya k'are zan koma ko ya kika gani....!?
"Eh....!, hakan ma yayi in yaso idan muka fita, sai dareba yafara kaiki tasha daga can ke kuma sai ki hau adai-daita sahu,
" no my Ulud ba haka ya kamata ayi ba,
kamata yayi ke zuwa wajen gobe ki kira Mamu kice mata Sanah tace miki Friday zata zo hutu..!,
so daga nan sai ki fad'a mata zaki zo da wuri kuyi aikin tarbata,
in yaso ke sai ki fara tafiya, bayan kin tafi da kamar awa d'aya nima sai na biyo ki,
"Ok ba damuwa hakan ma yayi,
a yanzu babu abinda Sanah tafi so kamar markad'add'un fruits,
a had'a da dabino, kwakwa, zuma da madara, tana mugun son wannan had'in sosai,
dan haka kullum da dare sai Khulud ta had'a mata tasha....!
yanzu ma kallan Khulud tayi cikin shagwab'a tace " my food please murmushi Khulud tayi had'i da k'ura mata ido,
tace " anya Sanah ba ciki ne dake ba....!?
Ido ta zaro a tsorace tace " what...! ciki fa kika ce....!?
"Eh..! Allah ni dai kamar haka nake gani,
kalli boobs d'inki fa, sun cicciko sunyi tantsan-tantsan dasu,
kuma wannan cin abincin naki har mamaki yake bani, ga shegen son miji kullum idan yana gida kina nanik'e dashi,
bayan da sai dakyar sai an had'a da rok'o da magiya kike zuwa gare shi
amma yanzu har zaman jiran dawowarshi kike yi, ga kwad'ayi da ciye-ciye komai kika gani kina so zaki ci,
kuma ni sai naga kinyi bak'i wallahi,
rigarta ta d'aga tana dariya tace " Allah babu wani ciki, baki ganin yadda su Aunty Halan ke shan wuya,
suna laulayi idan suna da ciki,
may be saboda zazzab'in dare danake yi kullum ne,
ido Khulud ta zaro tace " au har zazzab'in dare ma kike yi....!?
"Eh.. Allah kullum dashi nake kwana,
ido Khulud ta tsura mata tana kallanta,
d'an turo baki tayi tace " Allah ni yunwa nake ji, abani abinci ko asamu matsala...!
cikin dariya Khulud tace " ah rufaman asiri kar a haifar d'a mai rowa bari na tashi nayi himmar bawa d'an Baba abinci,
ta fad'a cikin dariya sosai da tsokana..!,
zama tayi nan tana jiran Khulud,
tana jin kamar tayi 24hrs bata dawo ba, saboda zak'uwa,
"kiyi sauri please ta fad'a tana lellek'a hanyar kitchen,
cikin murmushi Khulud ta fito kusa da ita taje ta zauna,
ai tun kafin ta mik'a mata Sanah ta fizga takai bakinta,
kasancewar had'in datake sha yasa kullum Sanah cikin zubar da ruwan ni'ima take wani lokacin ma har pad take sawa,
ko tayi ta canja pant, sai da shanye tasss kana tace " thank you so much my Ulud,
cikin dariya Khulud tace " sai ki tashi kije ki shirya dan d'aya abincin naki ya kusa dawowa,
shima sai ki shirya cinshi ta fad'a cikin zolaya,
d'an duka Sanah ta kai mata tana mik'ewa,
ta koma cikin bedroom d'inta ta fad'a wanka, dan harga Allah a hannu take, ita gani take yi saboda wannan had'in datake sha ne.
A parlor Hanash ya iske Khulud zaune,
tayi tagumi tana tunnin maganar daya fad'a mata jiya,
iska ya hura mata a fuska had'i da cewa " tunanin me ake yi ne...!?
Mik'ewa tayi tsaye tana murmushi tace " you're well come dear...!,
" dear..! ko?
Ya fad'a yana jan hancinta,
"to me..!?
" Kin manta kenan..!?
"Sweetheart..!?
" no..!
" My life..!
" no..!
"My hope, My soul, my love...!?
" A'a basu bane duk kin fad'i ..!
d'an shiru tayi tana tunani kana tace " please tunamin..!
" humm wayo, a'a ban tuna miki ki bari ki tuna da kanki..!
ya fad'a yana shigewa bedroom d'inshi,
murmushi tayi had'i da bin bayanshi da kallo,
bedroom d'inta ta shige ta kwanta saman bed idanta kan ceiling ta fad'a tunani,
Sanah na gama shiryawa ta d'auki abincinshi a tray ta nufi bedroom d'inshi,
tsaye ta iske shi a gaban mirror ya fito daga wanka,
cikin nutsuwa ta aje abincin akan center table d'in dake tsakiyar kujerun dake cikin bedroom d'in,
kana ta nufi shi, ta baya ta rungume shi had'i da lumshe idanta tana shak'ar k'amshin jikinshi dan duk duniya babu abinda Sanah tafi so a yanzu,
sama da k'amshin jikin Hanash,
tace " sannu da zuwa *MAN...!* _(sunan da take fad'a mishi wanda yake san Khulud ta tuna d'azu)_
murmushi yayi yace " kin tuna sunan kenan....!?
A hankali ta d'ora kanta saman kafad'arshi idanta lumshe,
tasa hannunta tana shafa kwantaccen gashin dake k'irjinshi,
"tom acici na lura dai idan banyi da gaske ba, tsotse min ruwan jikina zakiyi tasss,
ya fad'a yana zagayo da ita gaban shi,
idanta rufe ta kuma nakik'e mishi,
" to za'a barni naci abinci ko a'a...!?
Cikin shagwab'a tace " ni dai please ta fad'a tana lasar wuyanshi,
idanshi shima ya lumshe yana shak'ar iska,
cikin salo tasa harshenta tana lasar kunnenshi zuwa wuyanshi,
sai da ta gama tsotse wuyan tassss kana ta gangaro k'asa a hankali ta soma lasar k'irjinshin da nipple's d'inshi had'i da cibiyarshi,
sannu a hankali ta rink'a yin k'asa harta zo mararshi,
ai Hanash kasa tsayawa yayi ya d'auketa cak ya nufi kan bed,
cikin kunnenshi ta rad'a mishi " sofa please,
ta fad'a cikin wata irin murya data k'ara zautar da Hanash,
jikinshi na rawa ya zauna saman sofa,
ita kuma tana kanshi, cikin salo ta cigaba da tsatsa had'i da lasar duk sassan jikinshi,
ta yiyo k'asa zuwa mararshi take duk ilahirin jikin Hanash ya d'auki tsuma da kerrrrma,
a hankali ta zame towel d'in dake jikinshi ya fad'i k'asa,
sai da ta kalli fuskarshi kana ta runtse idanta da k'arfi,
dan yaune karo na farko da zatayi mishi sucking،
shima jiya taji ana maganar a group d'in Hauwa A Usman Jiddarh na matan aure mai suna......!
taji yadda ake koya sucking da abubuwa da dama,
ba zato ba tsammani Hanash yaji joy stick d'inshi cikin bakinta,
abinda ba'a tab'a yi mishi ba tunda yake a duniya,
wani irin abu ya caki kwakwalwarshi zuwa tafin k'afarshi,
a hankali ta soma tsotsarta tana lasa,
cikin salo while hannayenta nakan kowanne kan nipple's d'inshi,
tana murzawa, jin abinda bai tab'a jiba yasa Hanash bud'e murya iya k'arfinshi yana kwarara uban ihuuuuu,
cikin tashin hankali Khulud ta mik'e ta fita da gudu ta shiga d'akin Sanah,
ganin bata nan yasata nufar bedroom d'inshi,
daga bakin k'ofa ta jiyo sambatun Hanash a d'imauce yake magana " wallahi ko zan mutu bazan rabu dake ba,
ko zan rabu da kowa da komai,
wallahi koda kowa zai k'i ni zai kuma juya min baya,
ke ta dabance acikin mata, daban Allah ya halicce ki, wayyyyyyo zan mutu....!
wayyyyyyo dad'i zai kashe ni,
mutuwa zanyi yau, wayyyyo Allah na dad'ii,
I really really really love you so much,
sosai Hanash ya bud'e baki yana kwarara uban ihuuuu da sambatu,
wanda Khulud ta tabbatar da har mai gadi da mak'otansu suna jiyo ihunshi da maganganun da yake yi,
duk da idan da sabo Khulud ta sabo jiyo ihuuuun Hanash,
dan matuk'ar zasuyi sex da Sanah babu fashi sai yayi ihuuu,
amma nayau daban ne dan ya fita daban,
ita da farko abin mamaki yake bata,
amma na yau kamm yasa abin ya fara bata tsoro yana fad'ar mata da gabanta,
kuka ta saka sosai had'i da sanya hannu ta toshe bakinta,
ta koma bedroom d'inta da gudu ta fad'a saman bed,
cikin matsanancin kuka tace " me Sanah keyi mishi haka....!?
"Wanne irin abu take yi mishi wanda ni ban sanshi ba, ban kuma iya ba....!?
" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
ita abin tsoro yake bata sosai dan yanzu k'iri-k'iri tana san yin sex da Hanash amma tana jin tsoro da fargabar abinda ka iya zuwa ya dawo,
wani lokacin sha'awa na cinta kamar ta mutu amma take dannewa ta hak'ura,
_(Ni ko nace ki shiga group d'in Hauwa A Usman Jiddarh na matan aure mai suna.....)_
sai da Sanah ta gama gigitashi kana ta zame bakinta daga kan joy stick d'inshi,
ta kalleshi tace " Man...! aje aci abincin ko...!?
Bayyi mata magana ba dan bai jin zai iya furta koda kalma d'aya ce,
a rikice ya burkitata ya soma kashe arna,
yakai awa d'aya da rabi kanta kafin ya samu nutsuwa ya dawo cikin hayyacinshi,
saman sofar yayi kwance ya d'ora ta kanshi,
gashin kanta daya zo tasa hannunta ta maidashi baya,
tace " Man...!
bakinta yana rawa, kallanta yayi batare da yayi magana ba yana murmushi,
" dan Allah meyasa kake cewa Sanah karuwa, mazinaciya 'yar iska fasik'a...!?
"Meyasa kwata-kwata baka k'aunar ganinta baka santa metayi maka ne a rayuwa.....!?
"A k'alla nayi maka wannan tambayar yakai wajen sau goma amma baka tab'a bani amsa ba,
please yau ka bani amsa Man..!,
murmushi yayi yana shafa kanta yace " please mubar wannan maganar ban san nayi k'arya,
"please tace a shagwab'e,
" ni dai mubar wannan maganar,
fatana kawai kar ki rabu dani har abada...!,
d'an shiru tayi jimmmm kana tace " hmmmm koda bamu rabu yanzu ba,
tabbas akwai ranar rabuwa ko ba jima koba dad'e,
koda ranar tazo ka d'auki hakan a matsayin k'addara kamar yadda nima na d'auki tawa k'addarar,
murmushi yayi yace " to baki k'arasa ba ai,
murmushi itama tayi tace " k'addara mace ce mara tabbas da a koyaushe tana iya canjawa,
yayi dariya had'i da cewa " ban tab'a kasancewa dake batare dakin fad'i wannan kalmar ba,
"yes..! ina kuma san ka rik'e ta cikin ranka har abada,
" yo wannan ai ko karatu ne tuni na gama haddararshi,
"tom sauran wak'ar yau baki yi ba,
tayi murmushi had'i da gyara murya tace " farin ciki kai ne mai bawa zuciya,
bak'in ciki in tai kasata dariya,
dana gane ka sai inji nazam sarauniya,
aure na dakai ba wanda zai san dashi,
sosai yayi dariya kana yace " koda baki nan kina nan a zuciyaaaa...!,
suka saka dariya,
(duk sanda Sanah da Hanash suka keb'ewa sai sunyi wannan wak'ar koda basuyi sex ba),
cak ya d'auke sukayi bathroom,
camma sun dad'e suna wasan ruwa kafin sukayi wanka suka dawo suka kwanta,
haka batare dasun sanya kaya ba, ya ja musu blanket.
Tsakar dare yunwa ta tashi Sanah,
tana farkawa shima ya farka,
fuska ta marairaice mishi tace " yunwa..!,
yayi dariya yace " bari na d'umamo mana abincin can,
"oh...! haka ne fa kaima baka ci ba ko..!?
" Eh...!, yace yana mik'ewa, wardrobe ya bud'e ya d'auki boxer ya saka kana ya d'auki abincin ya fita,
bayan ya gama d'umama abinci a microwave ya d'auko ya fito,
daga saitin bedroom d'in Khulud ya rink'a jiyo kuka,
a hankali cikin fad'uwar gaba ya nufi bedroom d'in,
cikin sand'a, tana kwance saman bed tana kuka wiwi tamkar ranta zai fita,
"ashe dama ni ba mace ba...!?
" Tunda nake da Hanash bai tab'a yi min ihuuuu ko sau d'aya ba,
bai tab'a yi min sambatu ba, I hope zan iya tambayar Sanah abinda take yi mishi,
naji wanne irin abu ne wannan dake saka Hanash rud'ewa ya fita daga cikin hayyacinshi,
yana kwarara uban ihuuuu haka,
na shiga uku innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
ni Khulud na shiga uku,
a hankali cikin sand'a ya bud'e k'ofar ya shigo wufffff da sauri,
dama taji motsin ana doso k'ofar dan haka tayi saurin durk'ushewa a gefen gadon,
had'i da sanya hannu ta toshe bakinta,
d'akin ya shigo yana duddubawa,
cikin sand'a ya taka ya nufi inda datake b'oye ,
yana gaf da isa wajen yaji Sanah tana kiranshi,
da sauri ya fita hannunshi rik'e da tray d'in,
a parlor suka zauna suka ci abincin suka k'oshi,
nan ma sai da suka kuma raya sunna kana ya kwasheta sukayi bedroom,
washe gari da Khulud ta fito Sanah taga idanta sun kumbura sosai suntum,
babu irin tambayar dabatayi mata ba,
amma tak'i fad'a mata sai cewa tayi kanta ke ciwo,
kamar yadda suka tsara haka sukayi Khulud ta kira Mamu ta fad'a mata abinda suka tsara,
da daddare bayan Hanash ya dawo Khulud ta sanar dashi Sanah zata koma gida hutunsu ya k'are,
bisa mamaki Khulud sai taga ya mik'e ya fita parlor wajen Sanah,
ya zauna akan sofa ya kalle yace " da abinda kike buk'ata ne...!?
"A'a tace, idanta kanshi,
yace " idan kina buk'atar zakiyi siyayya ki shirya na kaini idan kuma baki buk'ata gashi,
ya fad'a yana aje mata 500k a kusa ita,
kamar bazata karb'a sai kuma tace " nagode sosai Allah yasaka da alkhairi Ubangiji ya k'ara bud'i da arziki,
Allah ya biya maka buk'atu na alkhairi,
dummmm Hanash yayi cike da tsantsar mamaki,
dan tunda yake da Khulud bata tab'a yi mishi makamciyar wannan addu'ar ba,
cikin sanyin murya ya juyo ya kalle ta had'i dayi mata murmushi yace " nagode Sanah...!,
take note dears yiwa miji godiya yana k'ara miki k'ima, mutunci, daraja, ya kuma rink'a yi miki abubuwa,
ranar Friday a round 12:00pm Khulud ta shirya ta tafi gida,
kasancewar Hanash bai sani ba yasa Sanah yin shiga tamkar Khulud,
taje ta amshi hakk'inta sun dad'e suna raya sunna,
bai fita ba sai wajen 4:30pm kana Sanah ta shirya da trolley d'inta tsaf ta fita,
yayinda Khulud ke can tana faman kiran wayarta,
jin bata d'aga ba, yasa Khulud yin dariya tace " jarababbiya acan ana amsar gara,
dan ta tabbatar sex suke yi shiya bata yi picking ba,
k'arfe biyar na yamma dai-dai Sanah ta k'arasa gidansu,
tun daga harabar gidan yara 'ya'yan yayyansu suka soma ihuuu suna ga Aunty Sanah...! ga Aunty Sanah.
Da gudu su Halan suka fito Khulud ta rungume ta,
tana cewa " I really missed you my Sanah,
" I missed you too Sanah tace kamar gaske,
Halan ta rik'e hannunta suka shiga ciki,
duk families d'inta ta gani zaune a parlor suna zaman jiranta,
har mazan, ga Abbu, Dide, Juju, Mamu ce kad'ai bata gani ba....!,
tana shiga cikin parlor taji wani irin k'amshi mara dad'i ya bugi hancinta,
k'amshin abincin da aka girka mata,
dana turarurrukan Yayyanta dana su Abbu da Dide,
dana shi kamshi gidan ya had'u ya bada wani irin k'amshi mai wari-wari a hancin Sanah,
take taji muk'uk'in amai ya taso mata,
taji gaba d'aya ta tsani gidan kwata-kwata,
bata ankara ba aman ya kufce mata ta shiga shek'a aman tamkar zata amayar da kayan cikinta,
ji take idan ta k'ara even 1 second cikin gidan tana iya mutuwa,
tunda Sanah ta soma amai Khulud ta shiga cikin tsantsar tashin hankali da firgici,
gabanta ya shiga dukan uku-uku,
yayinda gaba d'aya families d'inta dake zaune cikin parlor'n suka mik'e tsaye, Abbu ko sandarewa yayi a tsaye,
da sauri Khulud ta k'araso inda take ta rik'e ta tana jera mata sannu,
Abbu yace " dama baki da lafiya ne...!?
Khulud ta kalla tayi mata alama data amsa da eh,
"eh...! Abbu malaria ke damuna,
" ok tashi mu kai ki asibiti to,
da sauri Khulud tace " a'a Abbu ba sai anje asibiti ba,
cikin rawar murya Mamu dake tsaye kamar an dasata idanta kafe akan Sanah ta k'ura mata ido tace " Sanah...!,
innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
ai zuwa asibiti yama zama dole............!
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
4⃣9⃣
Cikin matsanancin tashin hankali da firgici Khulud ta d'ago kai ta kalli Mamu,
Mamu ta kuma cewa " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
haka kika koma Sanah...!?
"Ji fa yadda kikayi bak'i kika rame,
meke damunki haka...!?
Da sauri Khulud tace " Mamu kema fa kin san yadda ake lalacewa idan akaje bautar k'asa,
bak'ar wahala fa suke sha kamar ba gobe,
cike da tausayawa Aarib ya k'araso ya d'ago Sanah a hankali,
ya kalli Khulud yace " kai ta bathroom,
ta gyara jikinta sai muje hospital d'in ko...!?
"A'a Yaya ba sai anje wani hospital ba, acan ma fa naje sun bani magani har k'arin ruwa sukayi min,
Khulud tayi karaf tace " yanzu dai a barta tayi wanka tazo taci abinci in yaso letter sai asan abinyi,
ta fad'a tana jan hannunta zuwa bathroom,
suna shiga Khulud ta rufe k'ofar had'i da jingina da jikin k'ofar,
ta d'ora hannunta saman k'irjinta tace " wai hummm Alhamdulillah,
a hankali Sanah ta zauna bakin bed tana mayar da numfashi,
tace " wallahi ban san warin gidan nan kwata-kwata,
ta fad'a kamar zata fasa ihuuuu,
a hankali itama Khulud ta zauna bakin gadon gefen Sanah,
tace " hummmm dole na dawo gidan nan fa inba haka ba kwab'armu tayi ruwa,
"kamar ya...!?
" Eh...! dan wallahi ina ganin kamar ciki ne dake fa,
kuma kin san iyayen mu da kakaninmu kallo d'aya zasu yiwa mutum su gane yana da ciki,
dan haka yanzu ki cewa su Mamu baki sallah ma ke period kike yi,
baki Sanah ta tab'e had'i da cewa " ke kin damu ciki..! ciki,
waya fad'a miki ciki ne dani wai....!?
"Kawai dai change of environment ne,
murmushi Khulud tayi had'i da cewa " tom naji yanzu dai tashi kiyi wanka mu fita parlor,
batare datayi mata magana ba ta tashi ta shiga bathroom,
tayi wankan ta fito, sai da ta shirya tsaf kana suka fita,
har sun kusa parlor Khulud tace " kiyi controlling kanki fa,
kai ta d'aga batare da tayi mata magana ba, zaune suka taradda kowa kamar yadda suka barsu,
cikin su ta zauna suna ta hira ana labarin Damaturu da bautar k'asa,
wanda inza'a kashe ta ko hanyar Damaturun bata sani ba..!,
dakyar Sanah tayi controlling kanta da abinda take ji,
dan kwata-kwata bata san warin wajen,
haka ma abincin dakyar ta daure suka ci,
suna shiga bathroom Sanah ta mayar da k'ofar ta rufe ta kalli Khulud tace " wallahi ban iya zama cikin gidan nan,
warin ba dad'i Allah, please mu bar gidan nan karna mutu..!
ido Khulud ta zaro a tsorace tace " na shiga uku,
rufa mana asiri mana Sanah, ki daure just 1 week ne fa,
ko har nan cikin bedroom d'in ma kina jin warin....!?
Hawaye na zubowa Sanah ta girgizawa Khulud kai tace " a'a banda nan,
"yauwa tunda banda nan da sauk'i da safe mu rink'a tafiya part d'in Juju dasu Aunty Halan,
ko mu rink'a fita joint, sai dare sai mu rink'a dawowa nan d'in ko...!?
Cikin sanyin jiki ta d'aga mata kai alamar eh,
" yauwa my Sanah, then..! ki rink'a rage cin abincin a gabansu,
idan kin ci yanzu anan anjima idan kika kuma jin yunwa sai mu tafi part d'in Aunty Halan,
idan kika k'ara ji sai muje part d'in Juju,
then part d'in Aroos dana Aunty Seema,
yunwar dare kuma shi wanda yayi cikin shi za'a d'orawa kullum zan sashi ya kawo mana abinci take away muna ajiyewa a bedroom,
idan kinji yunwa da dare sai ki tashi ki ci kinji my Sanah,
batare datayi magana ba ta kuma d'aga mata kai,
"yanzu bacci zakiyi ko baby yana buk'atar ganawa da Dadynshi.....!?
Ta fad'a cikin tsokana tana dariya,
itama Sanah dariya tayi had'i da cewa " yanzu kam Alhamdulillah koda za'a buk'ata sai zuwa dare ko gobe,
Khulud tace " ai dama wallahi nasan tunda na kira ki baki d'aga ba nasan kina can duniyar sama,
d'an duka Sanah ta kai mata kana ta kwanta,
wajen k'arfe goma na dare Hanash ya kira waya,
kasancewar Khulud bata nan tana parlor,
yasa Sanah yin picking bayan ta sanya voice maker,
" amincin Allah ya tabbata a gareka,
murmushi yayi had'i da cewa " amin tare dake,
kin shirya ne nazo na d'auke ki...!?
"A'a Man..! anan zan kwana my Sanah ce bata jin dad'i,
" ayya meke damunta....!?
"Ciwon mara,
" Allah sarki please kice ina mata sannu,
"ok zataji in sha Allah,
wai yanzu mesaya naga ka canja akan Sanah ne....!?
Murmushi yayi wanda ya bayyanar da tsantsar kyanshi gami da k'uruciyarshi,
yace " saboda ke mana ai dole na canja yanzu ai bani babu yin musu da gardama,
yadda ake bani gara ina kwasa ai bana yarda nayi sake nayi laifi ba,
"hmmmm Man..! kenan,
" eh mana ko kinga laifi na...!?
"A'a ban gani ba,
dan Allah ka taimaka ka kawo min kazar yahuza da ice cream please,
" oh..! ni wannan ciye-ciye da kwad'ayi naki,
badan-badan ba da sai nace ko dai an gamu ne,
cikin rashin fahimta tace " dame...!?
"A'a nayi shiru,
" please dan Allah ka fad'a min,
" kodai ciki ne dake Khulud..!?
"Kin san fa anyi dashen mahaifa ana iya samun ciki ko yaushe fa,
murmushi tayi had'i da cewa " ba lalle ba,
" no cewa zakiyi Allah yasa,
ni kuma nace amin,
haka nan taji gabanta ya fad'i,
amma gudun kar yayi zargi tace " tom Allah yasa,
yayi murmushi had'i da cewa " Amin ya Allah,
" to dan Allah zaka kawo min kazar da ice cream d'in....!?
"Kinga yanzu ma muna wayar nan har nazo yahuzan,
" yauwa Man..! thanks so much,
"no amma fa da sharad'i idan nazo sai munyi TBT (tab'e-tab'e) ko da bamuyi sex ba kin yarda.....!?
Ido ta zaro tace " anan d'in zamuyi...!?
"Eh..! in kuma baki so shikenan nayi tafiya ta na kwanta,
" gaskiya ni dai a'a idan wani yazo ya gan mu fa muyi yaya kuma....!?
"Sai a bani matata mu tafi gidan mu muk'arata,
" ni dai a'a tsoro nake ji kar a kama mu,
" ok tunda baki so shikenan sai da safe,
ya fad'a yana k'ok'arin kashe wayar,
da sauri tace " na yarda amma a parlor'n bak'i kuma bazamu kunna fitila ba, a cikin duhu zamuyi ko hasken wayarka bazaka kunna ba ka yarda kai ma....!?
Dariya yayi yace " na yarda...!
"kayi alkhairin bazaka kunna fitila ba...!?
" Eh..!,
"to sai kazo,
" karki manta karki fito da komai a jikinki,
ido ta kuma zarowa a tsorace tace " ban gane babu kaya ba...!?
"Eh.. ina nufin naked sai ki zumbula hijab,
dariya tayi had'i da cewa " jarabatu,
shima yayi yace " jarababbu dai,
ki bani nan da 30 minutes yanzu zan k'araso,
"ok Allah ya kawo ka lafiya,
yace " amin had'i da kashe wayar,
tashi tayi ta fita ta yafatu Khulud,
dake zaune parlor suna hira da Mamu,
ba musu Khulud ta mik'e ta nufi Sanah,
"ke..! gafa Hanash nan zuwa d'aukarki,
" yaushe d'in zaizo d'auka ta...!?
"Yanzu mana yama taho yana kan hanya,
" ya akayi kika sani...!?
"Yanzu muka gama waya dashi a matsayin kece,
" ya kukayi dashi...!?
Batare data b'oye mata komai ba ta fad'a duk yadda sukayi dashi,
" kammm! wai kina nufin nan d'in zaizo kuyi sex...!?
Da sauri Sanah ta rufe mata baki had'i da zaro ido tace " relax mana,
kiyi a hankali kar wani yaji, ajiyar zuciya Khulud ta sauke tana d'an waige-waige,
hannunta Sanah taja cikin bedroom,
kana tace " eh ..! wallahi haka yace " dan haka yanzu zaizo sai kije parlor'n k'asa ki same shi,
yauwa kuma yace babu kaya naked yake so,
Sanah ta fad'a tana juyawa "ke..! wai tsaya kina nufin ni zanje ko me...!?
" Da waye zaije...!?
"Kin san dai babu yadda za'ayi na sanya fuska anan koda munzo da ita bare ma tana can gidan,
kin san matuk'ar mukayi wannan ganganci asiri yana iya tunuwa ko...!?
Idon Khulud waje cike da tsantsar tsoro take kallan Sanah,
deep down gabanta na fad'uwa,
dan harga Allah yanzu bata san abinda zai had'a ta sex da Hanash,
dan ta gaji da zagi da cin fuskar da yake yi mata,
muddin zataje gareshi, sai ya kushe ta, ko yasata gaba yayi tayi mata tsaki,
yana surutai , shiyasa kwata-kwata yanzu ko ita keda buk'ata bata kai kanta,
" amma gaskiya baki kyauta min ba,
ta fad'a kamar zatayi kuka,
ido Sanah ta k'ura mata na tsawon lokaci,
kafin tace " wai ke meyasa kwata-kwata yanzu baki san zuwa wajen Hanash...!?
Sai kiyi ta tura ni kodai da akwai wata matsalar ne....!?
Cikin alamun rashin gaskiya Khulud tace " a'a bakomai kawai dai kije dan Allah,
" ni ban zuwa, idan ba zaki je ba ki kira shi kice baki fita,
dan karma yasha wahala yazo,
" dan Allah ki fita ta k'ofar baya,
ni kuma na d'aukewa su Mamu hankali,
tunda kinga ke baki san zaman parlor...!,
" hmmmm naji amma ban zuwa in baki zuwa ki barshi,
Khulud zatayi magana kiran shi ya shigo,
da sauri ta kalli Sanah tace " ki d'aga please,
" itama wayar in baki d'agawa ki barta ta fad'a tana hayewa saman bed..!
gudun kar kiran ya tsinke yasa Khulud saurin d'agawa,
"ina parlor'n bak'in ki fito & karki manta babu kaya naked,
muryarta na rawa tace " tom gani nan,
marairaice fuska sosai Khulud tayi tace " please kije dan girman Allah,
ganin Khulud na niyyar kuka yasa ta jan tsoki had'i da mik'ewa,
tace " sai ki je ki d'aukewa Mamu hankalin,
murmushi tayi had'i da cewa " thank so much my Sanah,
ta fad'a had'i da yi mata kiss a kumatu,
baki Sanah ta turo had'i da goge wajen da Khulud tayi mata kiss tace " ban so,
dariya Khulud tayi tace " tom naji dai nagode,
ta fad'a tana fita wajen Mamu,
deep down kuma tana jin zafi da rad'ad'i ita da mijinta amma k'iriri tana san kasancewa tare dashi amma abu ya gagara,
kaya Sanah ta cire ya rage daga ita sai pant & bra,
kana ta zumbula hijab ta fita tana jan tsoki,
tabi ta k'ofar baya ta shiga parlor,
parlor'n yayi duhu dumd'um ko tafin hannunka baka iya gani,
"kin k'araso..!?
jin maganar shi yasata gane yana cikin parlor'n, sannu a hankali ta bi inda ta jiyo muryar tashi,
bata san ta kai ba, sai ji tayi, tayi tuntub'e da kujera,
cikin zafin nama Hanash ya tare ta,
had'i da cewa " kibi a hankali mana,
"ai ban san na k'araso ba,
zama yayi saman sofa had'i da zaunar da ita saman cinyarshi,
yace " hope dai ba kayan kika fito,
ya fad'a yana cusa hannunshi cikin hijab d'in,
jin jikinta ba kaya yasa shi sauke ajiyar zuciya,
had'i busar da iska yace " I love you,
ya fad'a yana cire mata hijab d'in,
d'an tsotsar lips d'inta yayi ya kuma cewa " I love you..!,
still batayi magana ba,
" wai meyasa sometimes sai nayi ta ce miki I love you,
amma baki ce min you love me too...!?
murmushi tayi had'i da had'e bakinsu,
cikin salo ya gazaya da hannunshi bayanta ya cire mata bra,
kana ya sanya hannunshi yana murza nipples d'inta, while bakinsu yana manne,
itama hannunta tasa tana murza joy stick d'inshi,
had'i da nipples d'inshi,
hannunshi d'aya yasa yana shafa cinyarta,
harya isa ga HQ d'inta, a hankali yasa hannu ya kawar da pant d'inta gefe had'i da sanya yatsanshi,
ya soma fingering d'inta,
while bakinsu manne, d'aya hannun kuma yana kan boobs d'inta,
a hankali ta zame had'i da sanya joy stick d'inshi a baki ta soma sucking,
da k'arfi Hanash ya soma ihuuu,
cikin tsoro Sanah ta zame bakinta had'i da sanya hannu ta rufe mishi baki,
tace " ba fa a gida muke fa,
dakyar ya iya cewa " please cigaba,
mik'ewa tayi had'i da cewa " a'a ka tafi karmu jawa kanmu abin kunya,
kaga fa harka fara ihuuuu,
"please ki cigaba ban k'ara yin ihuuun,
badan taso ba ta maida bakinta kan joy stick d'inshi,
idanta kanshi tana kallanshi,
k'ok'arin sakin ihuuu Hanash ya kuma yi,
Sanah tayi saurin mik'ewa had'i da cewa " sai da safe,
da k'arfi ya fizgo ta, danji yake ko duniya zata taru babu wanda ya isa ya hanashi sex da ita,
danji yake kamar zai mutu gaba d'aya hankali da nutsuwarshi basa jikinshi,
kuka ta saka mishi had'i da cewa " please dan Allah ka bari kaga fa a gida muke,
bai kula ta ba, ya kwantar da ita,
had'i da zame mata pant d'in dake jikinta,
shima ya soma sucking d'inta,
idanuwa ta zazzaro waje, had'i da saurin sanya hannu ta toshe bakinta gudun kar ta saki ihuuuun itama,
tana gangantsarewa, sai da ya tsotse ta tasss kana ya shige ta,
ganin yana k'ok'arin sakin ihuuu yasata saurin toshe mishi bakinshi,
Khulud na zaune a parlor ta kalli agogo taga har 11:00pm na dare,
kuma tun k'arfe 9:00pm na dare Sanah ta fita,
Khulud tana matuk'ar mamakin yadda Hanash yake muguwar dad'ewa akan Sanah,
which is ita bai tab'a yin 20 minutes kanta ba,
amma Sanah har sama da 2hrs yi suke yi,
tana nan zaune har sha biyu na dare tayi،
ganin tana ta kallan agogo yasa Mamu cewa " kije ki kwanta idan bacci kike ji,
nasan ita waccan tayi nisan kiwo yanzu kam,
murmushin yak'e tayiwa Mamu had'i cewa " sai da safe ta fad'a tana mik'ewa,
"Allah ya bamu alkhairi،
" amin tace tana shigewa bedroom d'in Sanah,
tana shiga ta fad'a saman bed had'i da sakin gigitaccen kukan bak'in ciki da takaicin rayuwarta,
" wayyo Allah ni, wayyo Allah rayuwata..!
su Sanah kam basu kammala ba sai k'arfe kusan biyu na dare,
kana suka samu nutsuwa, kwance yayi a gefenta yana shafa kanta,
yace " yau dai munyi abun kunya,
damma Allah ya taimaka ban shigo da motata ciki ba,
dariya tayi had'i da cewa " da sai dai ka gudu ka barta kam,
"ina sanki yace yana kissing goshinta,
tayi murmushi, had'i da cewa " nagode..!,
" ni fa ina mamakin ki wasu lokutan..!,
"meyasa...!?
Tace tana kwantar da kanta saman k'irjinshi,
" sai nayi tace miki ina sanki amma baki bani amsa wasu lokutan,
murmushi kawai tayi mishi had'i da shafa fuskarshi tace " Man...!
"na'am Mrs Man..!, ni dai dan Allah ki kasance dani a kowanne irin hali,
wallahi rashin ki bak'ara min bala'i bane ga rayuwata ba,
dan ina iya mutuwa, murmushi tayi had'i da cewa " a koyaushe ina yawan fad'a maka ni matafiya ce,
kuma akan hanya nake, dan haka bazan tab'a yi maka alk'awarin kasancewa tare dakai har abada ba,
yanzu ma k'addara ce ta had'a mu kuma tana iya raba mu a koyaushe,
murmushi yayi yace " tom yau nima bari na d'ana,
k'addara mace ce mara tabbas da a yaushe tana iya canjawa,
dariya tayi sosai had'i da dukan k'irjinshi tace " saura d'ayan to,
" wanne yace yana kallanta cikin duhu.....!?
"Au kamanta ma kenan...!?
Ta fad'a tana turo baki kamar yana ganinta,
murmushi yayi yace " ayi hak'uri a taimaka a tuna min...!
cikin dariya tace " farin ciki kai ne mai baiwa zuciyaaaa,
bak'in ciki in tai ka saka ta dariya,
dana gane ka sai inji nazam sarauniya,
aure na dakai ba wanda zai san dashi,
cikin dariya yace " na kulle ido na akan so da k'auna su ma bar kira na ni ked'ai na gano,
dake zani zauna in morewa raina,
ko da baki nan kina nan a zuciyaaaa...!,
yace " nayi miki alk'awarin zan kasance dake a kowanne hali,
duk abinda ya tun karo ki a duniya ko meye shi zan tare miki shi,
zan kasance mai haska miki ki hangi gabanki,
duk sukayi dariya, suna cikin hira suka ji an fara kiraye kirayen sallar asuba,
a kid'ime ta mik'e tana cewa " oh..! na shiga uku yau, yana k'ok'arin sake rok'o ta, tayi saurin zura hijab d'in ta,
had'i da d'aukar ledojin ice cream da kazar,
ta zari pant da bra d'inta a hannu tace " sai da safe,
"bazaki raka ni ko jikin motar ba....?
" Tab..! bayan kayi min wayo mun kwana tare,
ta fad'a tana fita, dariya yayi shima ya mik'e ya sanya kayanshi,
kana ya tafi, Khulud na can kwance saman bed sai juyi take ta kasa runtsuwa,
duk bayan minti biyu sai ta kalli agogo,
tasan muna can suna yin sex,
ita rabonta dashi takai wajen 1 month,
taci kuka har ta gaji,
tana kwance taji Sanah ta turo k'ofar ta shigo,
da sauri Khulud ta rufe idonta kamar tana bacci,
ganin tana bacci yasa Sanah ajeye pant da bra d'inta a gefen bed,
tana jan tsoki tace " kawai ya sani gaba yayi ta surfa shi baima gajiya,
haba ayi ta abu d'aya, tunda yazo bai barni na huta ba,
ta fad'a had'i da shigewa bathroom,
tana shigewa Khulud ta bud'e idanta ta kalli pant da bra d'in,
a hankali taji siraran hawaye na gangarowa kan fuskarta,
cikin sanyin jiki ta goge had'i da gyara kwanciyarta.
Bayan kwana shida
Mamu da Khulud zaune a parlor,
Mamu ta kalli Khulud tace " wai me yake damun 'yar uwaki ne...!?
"Me kika gani Mamu...!?
" Wallahi gani nayi duk ta canja,
kwata-kwata bata san zaman parlor da cin abinci,
kullum tana cikin d'aki ko part d'in Juju da Halan,
"oh..! ni ma nayi mata magana take ce min wai karatu take yi,
kuma bata sallah ,mararta na d'anyi mata ciwo,
" hmmm to Allah ya kyauta ya kuma bada sa'a,
"amin ya Allah Mamunmu ,
gobe ne tafiyarta ko...!?
" Eh ..! wai tana san ma na raka ta kasuwa tayi siyayya,
"ok yaushe yau d'in ko gobe...!?
" A'a yau mana ai gobe ina tunanin da asuba zata tafi kin san fa Damaturu ba nan bace,
"tom sai kun dawo nima na baku sautu,
" tom ai yanzu zata fit.....!
"ai nama fito d'in tashi muje kinga yamma nayi,
kuma gobe da asuba mukayi zamu tafi,
" waye zai kaiku driver ko Aarib...!?
"Yaya Aarib ne inaga ma yana waje dan naga kiranshi,
" wacce kasuwar zaku...!?
"Saban gari ibo road by market,
" yauwa dan Allah ku taho min da agushi, kwanla, crayfish, da oyedu leaf, to sukace kana ta basu 50k tace Abbu ne ya basu,
suna fita Khulud ta kalle ta tace " wai za'ayi da kud'ad'an nan ne...!?
"Wad'anne kud'i kuma....!?
" Sadakinki da ragowar 900k da kuma 5m na lefenki da Papu ya bayar,ga 500k d'in da Hanash ma ya baki suna hannu na,
"idan an had'a duka nawa kenan...!?
Ta fad'a batare data kalle ta ba,
" 6.5m,
"ok, za'a bawa Baba driver 2m a bawa Baba mai gadi shima 2m,
sannan abawa sabon mai gadinki 1m driver'nki shima 1m,
kinga saura 500k kenan,
sai a bawa Dide 100k sadaki na,
sauran 400k d'in kuma kan mai rabo,
" yanzu Sanah ta yaya zamu bawa Dide 100k....!?
"Karki damu zan bashi yanzu ma nace a wajen service aka bamu,
ni kuma da kud'i a hannu na,
" ok tom badamuwa amma mai zai hana sauran abawa Aunty Halan...!?
"Idan kin bata kice waya baki kuma ina kika samu...!?
Sanah ta fad'a tana kallan Khulud,
" haka ne amma kema da zakiji shawara ta karki nawa Dide kud'i gaskiya,
"to naji a had'a a bawa wad'annan tsofaffin da muma tasowa mukayi muka taraddasu suna yiwa ahalinmu bauta,
" gaskiya kam, Khulud tace cikin sanyi,
Sanah tace " yanzu kud'in suna hannunki....!?
"A'a suna banki duka 200k ne kawai a hannuna,
amma karki damu wajen jibi sai na dawo na kawo musu,
daga haka babu wanda ya kuma yin magana,
ganin Aarib d'in baya harabar gidan suka shiga part d'in Halan,
zaune suka iske Ziyad a parlor,
kwata-kwata Sanah bata kula da Ziyad ba,
ta shige kitchen inda ta jiyo motsin Halan,
Khulud na gaf da shigewa ta kula dashi,
har k'asa ta duk'a ta gaidashi, ya amsa cikin fara'a,
tare Halan da Sanah suka fito daga cikin kitchen suna dariya,
yaran Halan na wasa a tsakiya parlor'n,
Sanah na gaf da fita Ziyad yace " wai ke meyasa mara mutunci ce....!?
"Kina gani na zaune amma babu ko sannu, balle gaisuwa,
baki ta turo had'i da cewa " banfa ganka ba,
"ni kike turowa bakin dan ubanki....!?
Kallan yaran Ziyad dake wasa tayi tace " dan ubanku baku ganni bane shine bazaku gaida ni ba...!?
Daga Halan har Khulud abin ya basu dariya sosai,
Ziyad ya mik'e tsaye had'i cewa " ni na zage ki, dan haka rama kai tsaye a kai na,
shegiya mara kunya fitsararriya,
kallanta ta mayar kan yaran tace " shegu 'yan iska fitsararru kuna kallan k'anwar ubanku baku iya gaida ita,
saboda tsabar rashin tarbiyya,
cikin b'acin rai Ziyad ya nufota gadan-gadan,
itama ta nufi yaran gadan-gadan,
tace " Allah idan ka dake ni sai na rama akansu,
naga fad'an gaskiya kayi min nima nayi musu,
tunda gaida kai ne banyi ba suma basu gaida ni ba,
gwara kai Yaya na ne ma, su ko ni k'anwar ubansu ce,
ganin Ziyad yana nufar Sanah kuma idan ya kamata duka zataci,
yasa Khulud saurin shiga tsakiyarsu tana cewa " dan Allah Yaya kayi hak'uri,
matsar da Khulud yayi gefe yana kuma nufar Sanah yace " wallahi yau sai na ci ubanki naga k'arshen rashin kunyarki,
"au yanzu Yaya harka fi san 'ya'yanka akai na, kumaa akan su zaka dake ni....!?
"To tunda abin 'yar san kai ce idan ka dake ni wallahi nima sai na turo maka uba na,
tunda akan 'ya'yanka zaka dake ni,
kana ta mayar da kallanta ga yaran tace " ku daina kallo na shegu masu kama da 'yan ruwa,
ku godewa Allah Aunty Halan ce Mamanku, wallahi da ubanku ja muku mun d'aura daku kenan,
amma kunci arzikin babarku,
"kanshi ya girgiza had'i da nuna kanshi yace " ni kike fad'awa haka...!?
"Tab..! wallahi sai naci ubanki yau,
ganin yana nufo ta yasa ta d'aga murya tana kwalawa Dide kira,
Dide..! Dide..!! Dide ..!!! nima kazo ka cece ni,
Ziyad na gaf da k'arawa ga Sanah Aarib ya shigo,
da sauri ya shiga tsakiyarsu, had'i da tare shi,
Khulud tayi saurin janye Sanah sai da takai bakin k'ofa ta kalli yaran tace " wallahi sai naci uban ku, kuma ku godewa Allah ubanku bai tab'a ni ba,
da akanku zan rama, kana ta mayar da kallanta ga Ziyad tace " ka jira zaka ga ubana nima dan sai na turo maka shi,
ta fad'a tana fita da gudu,
shima Ziyad ya kwace yabi ta da gudu,
tana gudu tana ihuuu yana binta a baya,
Hanash tsaye a harabar gidan hard'e da hannunshi yana kallan ikon Allah,
shi abimma dariya ya bashi,
daga ita sai doguwar rigar material,
kanta babu d'an kwali iska tana d'aukar gashin kanta,
tana ihuuuuuu ta nufo Hanash gadan-gadan tana cewa " ka taimake ni *MAN.....!* Allah duka na zayyi,
MAN...! MAN...!! MAN....!!!
ka taimake ni dan Allah kayi min alk'awarin zaka kasance dani a kowanne hali,
kace zaka kasance mai bani kariya,
MAN...! kace duk abin ya tun karo ni zaka tare min shi,
zaka kasance mai haska min hanya na hangi gaba na MAN...........!
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
5⃣0⃣
Cikin matsanancin tashin hankali Hanash ya d'ago kai yana kallan Sanah,
bisa mamakinshi sai yaga Khulud ma shi ta nufo tana kuka had'i da yarfa hannunta,
kafin Hanash ya gama tantance wacce tayi maganar yaji,
Sanah ta fad'a jikinshi, had'i da ruk'unk'ume shi tana cigaba da ihuuuu,
cike da kunya Hanash ya soma k'ok'arin kwace kanshi,
amma kwata-kwata babu damar yin hakan dan ta rik'e shi gam sosai,
ganin yana niyyar kwacewa yasa Sanah zagayawa bayanshi had'i da rik'e k'ugunshi gam,
while tana cigaba da ihunnnn " please karka barshi ya dake ni,
ta fad'a tana k'ara rirrik'e shi had'i da tsalle,
sosai Sanah ta cukuikuye Hanash tak'i bashi damar kwacewa,
tsayawa Ziyad yayi cak yana kallanta,
cikin fushi yace " dan ubanki sake shi..!,
"idan na sake shi duka na zaka yi,
suna cikin haka su Abbu suka fito,
da sauri suka k'araso wajen Abbu yana cewa " lafiya..! meke faruwa..!?
Da sauri Sanah ta saki Hanash ta nufi Dide had'i da sanya kukan shagwab'a,
tace " Dide wai duka na zayyi akan yaranshi,
murmushi Dide yayi gami da cewa " ban gane zai dake ki akan yaranshi ba d'a dama har yafi d'an uwa...!?
"Tambaye shi Dide ni ma na tambaye shi,
Abbu ya kalle ta yace " tsakanin ki da Allah me kikayi mishi....!?
Ya fad'a yana murmushi,
sai da ta d'an turo baki kana tace " gidanshi na shiga wajen Aunty Halan,
ban kula dashi ba, shine yaji haushi na wai ban gaida shi ba,
shine yayi tayi min fad'a,
" tom daga nan fa kuma...!?
"Ni ma naga yaranshi basu gaida ni ba ina a matsayin k'anwar ubansu,
shine fa nima nayi musu fad'a,
Abbu yace " kika ce musu me...!?
Baki ta kuma turowa tace " abinda ya fad'a min shina fad'a musu,
shi ne yaji haushi, Abbu yayi murmushi had'i da cewa " ni dai nasan hali, ai ruwa baya tsami banza,
ganin ana niyyar d'ora mata lefi yasa ta fara diddira k'ara had'i sanya kukan shagwab'a tace " Allah bayan rayanshi yabi,
har fa cewa yayi wai yafi san su akai na,
kuma wai sai ga ubana, wai yaranshi sun fi ni,
wai baiga wanda ya isa ya hana shi duka na ba,
Ziyad shuru yayi cike da mamkin sharrin da Sanah ke gindaya mishi,
Dide yace " zo mu tafi kinji daughter kyale shi,
kuka ta saka sosai tana cewa " ai dama Yaya Ziyad yace ba mai sona,
ko kashe ni yayi ya kashe banza,
ashe da gaske yake babu mai san nawa...!?
da Aunty Halan ma na bashi hak'uri,
cewa yayi wai Abbu da Dide ma sunce sun gaji dani,
Ido Ziyad da Halan suka zaro suna jin ana yi musu k'arya k'iri-k'iri,
Dide yayi murmushi yace " aiko idan yasake ya tab'a min 'ya akan nashi yaran nima sai na dake shi,
tunda d'a bafin d'a yayi ba, ko kuma na rik'e miki su ki daga san ranki,
" yauwa my Dide dama nasan kafi kowa so na, fad'a mishi dai,
dama yace yana san ganin gata na,
Abbu da Dide sukayi murmushi,
Dide yace " ai dai na fad'a mishi kuma yaji,
idan ya sake ya tab'a min 'ya shima sai na tab'a shi,
"I love you so much my Dide,
Abbu yace " mu da ba'a san mu akai can,
ya fad'a yana nuna mata shara,
tayi murmushi had'i da cewa " I love you our Abbu,
duk sukayi dariya, kana su Abbu suka gaisa da Hanash suka shige cikin gida,
Ziyad ya kalle ta had'i da yin kwafa yace " zan kama ki ne,
tayi mishi kwalo had'i da cewa " oha dai ina da Dide ,
nufo ta ya kuma yi tayi saurin b'oya a bayan Hanash had'i da rik'e shi gam,
yatsa Ziyad ya nuna mata had'i da cewa " shegiya gwara ma kizo ki had'a kayanki ki koma inda kika fito,
ya fad'a suna shigewa cikin part d'in su shida Halan ya rage daga,
Khulud sai Hanash da Sanah a compound d'in،
dariya tayi while bata saki Hanash ba,
Hanash tsaye yayi yana tunanin ashe har yayyanta ma bata kyale su ba,
har yayyanta ma fama suke yi da ita,
idanshi kanta yace " ita wannan babu wanda ta bari ne....!?
Baki ta murgud'a mishi had'i da cewa " eh..! d'in ina runwaka...!?
Kanshi ya d'aga ya kalle ta danya fahimci taji maganar dayayi cikin ranshi,
kannunta dake sak'ale da k'ugunshi ya kalla,
tayi saurin janya hannun had'i da murgud'a mishi baki,
tace " kai a gidanku ba'a iya taimako bane...!?
Ta fad'a tana mayar da fad'an kanshi,
while idanta cikin nashi,
" kai wanne irin mugu ne ana neman taimako,
baka iya kawo taimako ko sai masifa kawai ka iya irinta kakarka...!?
Kallanta yayi kana yace " kin gama...!?
Hararshi tayi had'i da cewa " a'a ban gama ba da saura,
wato saboda ka mayar dani aku sarkin sututu shine kake tambayar na gama...?
"A'a dama cewa zanyi idan kin dama ki d'aga ni,
ki kuma janye hannunki daga kan k'irjina,
ido ta zaro gami da kallan kanta a tsorace,
sai lokacin Sanah ta lura gaba d'ayanta akan shi take,
saurin d'agashi tayi tana kakkab'e jikinta,
kana ta kuma kallanshi ta murgud'a mishi baki had'i da watsa mishi harara tayi gaba,
yabi bayanta da kallo gami da jan tsoki yace " mahaukaciya,
ashe bani kad'ai take yiwa ba har yayyanta ma masu aure da yara,
bata kyale su ba, yi musu rashin kunya take yi,
kwata-kwata Hanash ya manta da maganar kalaman bai ma k'ara bi ta kansu ba,
dan yayi zaton Khulud ce ta fad'e su,
saboda yadda abun yazo akan gab'a,
kallanshi ya mayar kan Khulud yana murmushi yace " ina zuwa....!?
" Hummmm kasuwa zan raka waccan rigimammiyar,
"au ashe kema kin san rigimammiyar ce...!?
" Kun had'u ke da mijinki kuna yi da ni ko...!?
Sanah ta fad'a dai-dai lokacin datake k'arasowa wajen,
cikin dariya Khulud tace " miji na ko mijin mu....!?
Da sauri Hanash ya kalli Khulud idanshi d'auke da tambaya,
ganewa tayi ta kwabsa dan haka tayi saurin cewa " yes komai nawa ai nata ne,
kamar yadda komai nata nawa ne,
danta kawar da maganar ta kalli Sanah tace " ashe har kina tunanin zanyi maganarki ta b'atanci da wani mahaluk'i a duniya....!?
Ido Sanah ta zaro tana kallan Hanash tace " tab..! yanzu Khulud mijin naki ne wani.....!?
Ta fad'a tana kama bakinta,
dariya Khulud tayi tace " to haddasana badai zaki had'a mu ba,
ta kalli Hanash tace " kaji wai kai ne wani, tab..! ka bari matarka tana ce maka wani lalle kayi sake,
yadda take maganar tana zaro ido had'i da karkata bakinta,
yasa shi yin dariya had'i da cewa " to ina ruwanki...!?
"Mun fi kusa ai, ta kira ni da duk sunan da taga dama babu ruwanki,
baki ta tab'e had'i da cewa " oho dai , ta fad'a had'i da bud'e motarshi ta shiga ta zauna,
kallanta yayi cike da tsantsar mamakin baud'add'an halinta,
kanshi kawai ya girgiza kana ya bud'e motar ya shiga,
Khulud ma ta shiga,
sai da suka fara tafiya kana ya mayar da kallanshi ga Khulud yace " wacce kasuwa zan kai ki....!?
"Zaka kai mu dai, tunda ai ba ita kad'ai ka d'auko cikin motar ba,
kallanta Khulud tayi tana dariya tace " my Sanah ko dai kin fara kishi da ni ne ban san ni ba.....!?
Kallanta Hanash yayi yace " kishi kuma...!?
Cikin rashin gaskiya Khulud tace " eh..! mana ta mayar da ni kamar kishiyarta,
har su Mamu, Juju da Aunty Halan ma sun fahimci haka,
duk abinda nace ina so itama sai tace tana so,
"hmmmm yanzu dai wacce kasuwar zaki....!?
" Nace ka rink'a saka harafin munjaye,
murmushi Khulud tayi had'i da cewa " ke karki damar min miji,
ki barshi ya huta, kin saka shi gaba kin dame shi ki sakar mishi mara yayi fitsari,
tab'e baki Sanah tayi had'i da cewa " kuma dai,
Khulud ta kalli Hanash tace " saban gari zamu,
suna cikin tafiya idan Sanah ya sauka akan agwalima,
da sauri tace " dan Allah Ma..! jin tana neman sakin layi yasata saurin gyara kwalarta, tace " dan Allah Hanash zan sha agwalima, ta fad'a idanta kan agwalimar,
bayyi magana ba ya ganganra gefan hanya yayi parking,
ai tun kafin ya gama yin parking ta bud'e motar ta fita,
da yawa ta siya kana ta koma cikin motar,
kallanta kawai Khulud tayi,
ta d'auki agwalimar d'aya ta soma sha,
Khulud tace " bazaki bari a wanke ba....!?
"Wa..! tab..! wallahi ban iya tsayawa,
tana cikin shan agwalimar ta hangi mai tsamiyar biri,
nanma tayi saurin tsaiyar dashi ta fita ta siyo,
tana shan agwalimar tana shan tsamiyar birin,
basuyi nisa ba, ta kuma hangar mai yalo da d'ata, da sauri tace " lah yalo zanci please,
banza Hanash yayi mata dan gani yake rainin hankali ne kawai,
ganin yana k'ok'arin wucewa yasa Sanah zuro hannu tana tab'a shi tace " dan Allah zanci please karka wuce,
" sai dai ki mutu amma ban kuma tsayawa,
sosai Sanah ta sa mishi kuka tana rok'onshi ya tsaya,
Khulud ma nayi mishi magiyar ya tsaya, shi abimma mamaki ya bashi sosai,
cikin masifa yace " sai kace mai ciki kin damu mutane komai kika gani kina so,
to wallahi ko ciki ne dake sai dai ya zube,
cikin kuka Sanah tace " dan Allah ka taimaka min Allah ina iya mutuwa in banci ba,
cike da tsantsar mamaki ya kuma kallanta,
yace " aiko sai dai ki mutun,
"Hanash _*RASHIN SANI...!*_ ke saka yin duk wad'annan abubuwan,
amma inda kasan abinda ke b'oye da kobannce ba kai da kanka zaka tsaya,
karkayi kuskuren da har bada zaka rink'a kuka,
karkayi kuskuren da har bada bazaka tab'a yafewa kanka ba,
d'an jimmmm Hanash yayi yana tunanin kalamanta,
ganin haka yasa Khulud saurin cewa " dan Allah ka tsaya Allah nima ina so,
banza yayi musu ya cigaba da tuk'inshi,
har suka isa Hanash bai kuma yin magana ba,
sai su biyu ke ta faman yin surutunsu
suna fitowa warin cakwalin wajen ya bugi Sanah,
aiko taita kelaya uban amai kamar zata amayar da kayan cikinta gaba d'aya,
cike da tausayawa Hanash da Khulud sukayi ta jera mata sannu,
Hanash ya kalli Khulud yace " dama bata da lafiya ne...!?
"Eh..! ai na fad'a maka bata jin dad'i,
" to ko muje hospital....!?
Ya fad'a cikin tausayawa,
Khulud tayi saurin cewa " a'a , kullum sai family Doctor yazo gida ya duba ta,
sannu ya k'ara yi mata, kana ya bata ruwa ta wanke bakinta,
karaf idanta ya kuma sauka akan sabon goro yalo sharrr dashi,
d'an langwab'ar da kai tayi gefe tace " zan ci please,
Khulud batayi magana ba ta kira mai goron,
mai goron na zuwa ta sanya hannu ta d'auka ta soma ci, batare data tsaya an siya ba,
shi dai Hanash tsaye yayi cikin tsantsar mamaki,
yana kallan iko da hukuncin Allah,
cikin ranshi yana tunanin anya yarinyar nan ba cikine da ita ba,
dan yadda take yin abun kamar zalamammiya ko mayya,
yana d'aure mishi kai, Khulud ta siyi goron mai yawa,
babu yadda Hanash bayyi kan su koma gida ba,
amma Sanah tace babu komai zata iya yin siyayyar haka nan,
basu koma gida ba, sai magrib,
shine ya mayar dasu har gida,
bayan sun biya yahuza sun siyi kaza da fura.
Washe gari Sanah sai kukan rabuwa da gida take yi,
tana manne da jikin Dide while Khulud da Halan na gefenta,
an fito mata da kayan tafiyarta gaba d'aya kaf,
Dide ya kalleta yace " yaushe abokanan tafiyar taki zasu k'araso...!?
Kafin Sanah yayi magana Abbu yace " ai ba su zata bi ba,
Aarib ne zai kai ta har Damaturun,
kafin ya gama rufe baki Aarib ya fito cikin shirin tafiya tsaf,
wata irin muguwar razananniyar fad'uwa gaban Khulud da Sanah yayi,
a lokaci d'aya suka kalli juna,
cikin rawar murya Khulud tace " meyasa Abbu.....!?
"Eh...! dole sai wani ya bita yaga inda take dan bai yiyuwa ace babu wanda yasan inda take ba,
cikin tashin hankali Sanah tace " amma Abbu inyi yaya da k'awaye na wad'anda muka zo tare dasu....!?
"Kasan bazasu ji dad'i ba idan nayi musu haka, da niyyar kwana uku-uku suka zo amma saboda ni suka k'ara,
idan suka ji na tafi haushi zasu ji,
" babu abinda ya shafe ni da wasu k'wayenki,
idan kin damu dole sai kun tafi tare sai kiyi musu waya suzo nan Aarib ya kaiku tare,
ai hauka ma kenan ace kawai na turaki ke kad'ai sakaka har Damaturu,
ke kad'ai kina mace, da har dani da Dide da su Ziyad ma za'aje dan a gano inda kike,
to sai akayi rashin sa'a nida Dide kayan mu yau zasu k'araso,
Ziyad, da Zafran da kuma Idrak suma yau suna busy,
amma da gaba d'ayanmu zamu tafi,
fuska Sanah ta kwab'e kamar zatayi kuka tace " but Abbu a......!
"ke..! wallahi Allah ko zaki mutu sai Aarib ya kaiki,
kinji ma na rantse,
Khulud dake tsaye gabanta nata fad'uwa,
k'irjinta yana dukan uku-uku,
tayi shiru ga lokaci ya k'ure bare su kira Papu su sanar dashi halin da ake ciki,
shiru kawai tayi ta rasa abinyi,
murmushi Aarib yayi had'i da bud'e mota ya sanya kayanshi dana Sanah,
ganin suna k'ok'arin shiga mota yasa Khulud cewa " tunda kai ne zaka kaita nima bari na d'auko kaya na ka mik'a ni gida,
dan Hanash yace min bazai samu damar zuwa ba,
saboda bai jin dad'in jikinshi,
Abbu yace " ayya meke damunshi....!?
"Wai cikin shi ke ciwo,
" idan kinje kice kina gaida shi da jiki,
Allah ya sauk'e, ta amsa da amin,
komawa tayi ta d'auko kayanta,
suka shiga mota suna k'ok'arin tafiya,
Abbu yace " Aarib idan kunje gidan Khulud ka tabbatar ka shiga ka duba Hanash fa,
ya amsa da " to in sha Allah,
jugum-jugum suka yi a cikin motar kowa da abinda yake sak'awa cikin ranshi,
wayarta ta zaro daga cikin jaka ta turawa Khulud text,
_" ya zamuyi yanzu ne...!?_
Jin shiru Khulud bata duba ba, yasa Sanah juyawa ta kalli Khulud dake zaune tamkar mutum mutumi,
tace " wai ba wayarki ce ke k'arar notification ba...!?
Ta fad'a idanta kan Khulud ajiyar zuciya ta sauke had'i da kallan Sanah,
suna had'a ido Sanah tayi mata alama data duba wayarta,
cikin sanyin jiki Khulud ta duba,
reply tayi mata _" hummmm ni ai na rasa abinyi ma, dan gaba d'aya kai na ya gama kullewa,_
Sanah ta k'ara turo mata _" ki kira Papu ki sanar dashi halin da ake ci mana,_
Khulud ta rubuta mata amsa _" tab..! yana cikin motar zan kira Papu...!?_
Sanah ta tura mata _" tom yanzu meye mafita....!?_
_"Yanzu dai bari mu turawa Leenah text, (k'awarsu ce amma ta islamiyya ta kuma rigasu gama secondary school)_
_yanzu suke service,_
_" me zaki ce mata...!?_
_"Ce mata zanyi ta saka kayan service d'inta a jikinta please yanzu zamu zo gidansu,_
_" to daga nan fa....!?_
Cewar Sanah,
Khulud tace _" sai mu had'a baki muyiwa Aarib wayo muja ra'ayinshi,_
"ok to tura mata text d'in, Khulud na turawa Leenah text bata jima ba ta dawo mata da amsa " ok badamuwa sai kunzo,
turawa Sanah abinda Leenah ta turo Khulud tayi,
had'i da cewa " to yanzu saura musan yadda zamuyi da Aarib,
Sanah tace _" yanzu kiyi ta kira na ta waya, amma karki bari Aarib ya gane kece ke kira,_
Khulud batace komai ba, ta soma kiran layin Sanah,
Sanah ta kalli screen d'in wayar had'i da basarwa,
Khulud ta kuma kira, sai da Khulud ta kira sau biyar kana Aarib ya kalli Sanah yace " ki d'aga mana,
d'an tsoki taja tace " wad'anda da zamuyi tafiyar da su ne,
wallahi Yaya Aarib ban san me zance musu ba,
"to ki d'aga kiyi musu bayani mana,
" a'a yaya haushi na zasu ji, gwara kawai ma had'e acan,
Khulud tayi karaf tace " kai gaskiya ba dad'i, to amma mai zai hana Yaya Aarib yayi miki alfarmar binsu,
duk duniya kowa yasan tsakanin Bros & sis akwai taimakekeniya,
" wa wai ni kuke san na karya umarnin Abbu, na koma nace mishi me....!?
" Sai kak'i komawa gidan sai gobe ko jibi dan Allah Yaya Aarib,
ka taimaka kar mutuncin Sanah ya zube a wajensu,
"wai ku baku da hankali ne,
idan wata rana ya sani gaba yace in kaishi wajenta fa, in yi yaya.....!?
" Baga waya ba, sai nayi maka kwatance ta waya,
kuma ai kai zaka kaini wajen su mu tafi akan idanka,
daga Khulud har Sanah suka marairaice fuska had'i da sanya kuka suka shiga rok'onshi suna yi mishi magiyar kan ya taimaka yakaita wajen k'awayenta su tafi tare,
while Khulud tana cigaba da kiran wayar Sanah,
d'an jimmm yayi yana saurarensu,
kafin ya fuszar da iska yace " tom naji, ina ne gidansu friends d'in naki....!?
Ihuuuun jin dad'i sukayi a tare,
Sanah bata san sanda ta rungume shi ba,
Khulud ma dake baya ta rungume shi,
kad'i dayi mishi kiss a kanshi suka ce " thank you Yaya,
yayi murmushi,
har k'ofar gidansu Leenah ya kaisu, suna isa Khulud ta kira ta a waya,
ta fito sanye da kayan bautar k'asa,
sosai sukayi hira harda Aarib kana Aarib ya kalli Sanah yayi mata nasiha da fad'a sosai,
kan ta rik'e mutuncinta da kuma addininta, da al'adarta,
kana ya mayar da kallanshi ga Khulud yace " muje na kaiki gida ko...!?
"A'a Yaya kaje kawai zan tsaya naga tafiyarsu dan bai kamata ace babu wanda yaga tafiyarsu ba,
" ok badamuwa hakan ma yayi,
ya fad'a had'i da shiga motarshi,
Leenah na tsaye tana binsu da kallo dan kwata-kwata bata gane abinda ake yi ba,
Allah bai kuma bata ikon tambaya ba,
Leenah tace " to ku shigo mu shiga ciki ,
Khulud tace " ina ai bazamu shiga ba,
daga gida nan mukayi dama wayo mukayi mishi wai sai mun bishi gidanshi a Kaduna ,
mu kuma bamu san zuwa,
"wallahi baku isa kuzo har k'ofar gidanmu batare dakun shiga kun gaido Maman mu ba,
sama-sama suka shiga gidan su Leenah suka gaida 'yan gidansu,
kana suka fito suka tari adai-daita sahu sukayi gida,
a parlor suka zube gaba d'ayansu,
Khulud tace " washhhh yau kam mun tsallake rijiya da baya,
"hmmmm kedai bari kawai, amma fa kin ban dariya dan yadda kika rink'ayi da idanki,
wallahi saura kad'an dariya ta kufce min,
ta fad'a tana dariya, Khulud ma ta saka dariyar.
Tun dare Sanah keta faman kelaya uban amai kamar zata mutu,
kafin safe tayi muguwar jigata sosai,
ga zazzab'i ya rufe ta ruf sai faman rawar sanyi take yi,
gari na wayewa suka tafi hospital bayan Hanash ya tafi office,
dan bai san Sanah ta dawo gidan ba,
direct wajen Doctor d'in da suke shirya komai dashi suka je,
batare da wani b'ata lokaci ba aka shiga duba ta,
gwajin farko aka gano Sanah nada shigar ciki na wata wata hud'u da sati biyu,
(4 months 2 weeks), cikin tsantsar murna da farin ciki Doctor ya kalli Sanah da Khulud yace " congratulation,
abin nema ya samu dan Sanah tana da ciki na wata hud'u da sati biyu,
saboda tsabar murna da farin ciki Khulud bata san sanda ta sanya kuka wiwi ba,
Sanah kammm shiru tayi tana magana cikin ranta,
" wato rabo abu ne mai matuk'ar k'arfi,
shiyasa akace idan kana da rabo waje kona shak'awar iskar wajen ne kad'ai sai kaje,
balle rabon haihuwa wanda yafi kowanne rabo k'arfi,
dan idan rabo ya rantse har kashe mutum yana yi,
hmmmm duk abinda Allah ya tsarawa mutum sai dai yayi godiya kawai,
duk fafutuka da had'amar da mutum yake a rayuwa Allah ya riga ya gama tsara mishi komai,
sai dai ka jira lokacin wanzuwar hakan kawai,
in bada al'amarin Ubangiji yama zatayi ta auri mijin Khulud har ta haihu dashi,
in banda k'addara ace wai yau itace d'auke da cikin Hanash mijin Uludinta,
lalle _*RASHIN SANI...!*_ yafi dare duhu,
k'addara kuma ta riga fata,
sujjada Khulud tayi tana godiya ga Allah,
Doctor yayi murmushi yace " ni zan fad'awa Papu ko ku.....!?
Cikin kuka Khulud tace " ni, kana dialing number Papu,
yayi picking, kasa magana Khulud tayi sai kuka datake ta faman yi,
a rud'e Papu yace " lafiya Khulud...!?
Jin yadda hankalinshi ya tashi sosai yasata cewa " Sanah na da ciki Papu harba wata hud'u da sati biyu,
sandarewa Papu yayi a zaune ya kasa furta koda kalma d'aya,
saboda tsananin farin ciki da mamaki,
while Khulud na rik'e da wayar tana cigaba da kuka,
sun dad'e a haka kana Papu yace " ku jira ni a hospital d'in, ya fad'a had'i da kashe wayar,
dan bai jin zai iyayin magana,
kwanciya Papu yayi had'i da rufe idanshi yana tunanin lalle rabo sai a barshi,
a ma godewa Allah da rabon bai kashe Khulud ba,
ba'a kuma same shi ta mummunan hanya ba, dan tunda Allah ya riga ya tsara akwai rabon haihuwa a tsakanin Hanash da Sanah,
da ko shege ne sai an haife shi,
ya kuma k'ara godewa Allah daya yarda da maganar dan yasan dabai yarda ba, dole cikin biyu ayi d'aya ko Khulud ta mutu suyi aure a haifi rabon,
ko kuma wani akasin yazo ayi cikin a waje a haife shi shege,
kwanciyarshi ya gyara had'i da cewa " to wai tayaya ake yi Hanash d'in yana kusantarta,
kuma har bai gane ba Khulud bace ba,
hmmmm mata dai sai a barsu dan shu'umai ne idan suka so yin abu Allah kad'ai ke hana su,
a hankali ya mik'e ya zari key d'in motarshi yayi hospital d'in,
Sosai Khulud ke kukan farin ciki dana bak'in cikin, yadai tabbata kenan bata haihuwar,
sai dakyar Doctor da Sanah suka rarrashe ta,
ana cikin rarrashin Khulud Papu ya shigo,
direct wajen Sanah ya nufa ya rik'e hannunta had'i da cewa " thank you so much daughter,
you make me proud, lokacin da kuka zo min da maganar gani nayi sharme ne,
ashe Allah kad'ai yasan meya b'oye,
nagode sosai nima na kusa ganin jika na,
cike da mamaki Khulud take kallan Papu ganin ko inda take ma bai kalla ba,
gaba d'aya hankalinshi nakan Sanah sai faman yi mata godiya yake, yana sanya mata albarka,
taga kota kanta ma bai bi ba,
ganin godiyar tak'i k'arewa yasata yin gyaran murya had'i da cewa " sannu da zuwa Papu,
"oh!... I'm sorry ban kula dake ba Khulud,
Papu ya fad'a while idanshi kan Sanah,
mamaki ne ya k'ara cika Khulud sosai,
" ok badamuwa tace tana danne abinda take ji,
"to yanzu za'ayi Papu....!?
Sai lokacin Papu ya juyo ya kalli Khulud,
hawaye ta gani a idanshi,
amma sai ta basar tayi kamar bata gani ba,
Papu yace " our next plan is yau ki kwana kina shek'a amai,
in fact kawai kiyi pretending baki da lafiya,
nasan gobe shi da kanshi zai kawo ki hospital,
wajen Doctor, & kai kuma Doctor ka canja sunan result d'in cikin da sunan Khulud,
sai ka bawa Hanash ka kuma tabbatar mishi Khulud tana da ciki na wata hud'u da sati biyu,
duk suka amsa da to.
Sir Aryan Moli kwance a saman sofa a parlor'n shi,
Leem na gefenshi yana ta faman had'a shi da Allah yana yi mishi magiyar ya fad'a mishi meya faru tsakanin shi da Sanah,
" Aryan ka ganka kuwa, kaga yadda ka koma ka lalace...!?
"Gaba d'aya ka fita daga hayyacinka da nutsuwarka,
ka rame ka koje ka zama wani iri,
dan girman Allah ka taimaka ka sanar da ni meke faruwa,
murmushi takaici Sir Aryan yayi while hawaye na gangaro mishi,
yace " Sanah bata so na, taci amana ta,
ta yaudare ni, ya fad'a yana fashewa da rikitaccen kuka,
cike da tausayawa Leem yace " yanzu akan mace ka koma haka Aryan....!?
"Kana neman lalata rayuwarka,
ka kashe kanka a banza kaga yadda ka koma kuwa.....!?
" Wallahi in banda nayi mika farin sani da ban iya gane ka,
duk wannan kyau, gayu, tsafta kwalisar duk babu, ka koma wani iri dakai,
haba Aryan ko ita kad'ai ce mace ai sai haka,
ka rabu da ita mana, sai kace itace autar mata, bayan ga matan nan kamar jamfa a jos saika zab'a ka dirje,
murmushi yayi while yana kukan,
yace " ita kad'ai nake so Leem,
wallahi ko duk matan duniya za'a hab'a min ban san su Sanah kawai nake so,
Leem baka san hak'ik'anin zallar tsagwaran soyayyar gaskiya bane,
wallahi in da za'ace min idan na auri yau gobe zan mutu zan amsa da na yarda,
ina matuk'ar santa fiye da komai da kowa,
I really love her so much, me nayiwa Allah daya jarrabeni da wahalalliyar soyayya?
"Wallahi na gwammaci mutuwa ta akan mawuyacin halin danake ciki,
abu d'aya tak Sanah zatayi min a duniya na tsane ta na kuma hak'ura da ita duk girman son danake yi mata,
shine taci AMANA TA...!!! , wallahi muddin taci amana ta, na rabu da ita har abada,
ajiyar zuciya Leem ya sauke cike tsantsar tausayawa abokin nashi,
yace " haka ne, na gane na kuma fahimce ka, amma dan Allah ka daure ka fad'an abinda ya faru,
kamar bazai fad'a mishi ba, sai kuma ya tsinci kanshi da fad'awa Leem komai,
tun daga farkon lokacin daya fara yi mata maganar aure,
tace sai bayan 1yr,
har zuwa lokacin data amince da abinda ya faru ya fad'a mishi komai,
d'an shiru Leem yayi yana tunanin,
kana ya sauke ajiyar zuciya yace " to amma kai kana ganin dan karta aure ka ne tabar gidan su....!?
"Eh...! mana saboda waye in ba danni ba,...!?
" Bata so na ne, tayi min muguwar sakayya, _*RASHIN SANI...!*_ ne yasani amincewa da ita,
iska Leem ya kuma fitarwa yace " to amma kana ganin idan har dan kai ne zatayi k'arya wa iyayenta, batar 'yan uwanta, gidansu, ahalinta da mahaifanta da kowa nata kai kana ganin idan dan kai kad'ai ne zata yi haka...!?
Wata irin razananniyar fad'uwa gaban Sir Moli yayi had'i da mik'ewa zaune ya zubawa Leem ido,
dan shi bai tab'a yin irin wannan tunnin ba,
Leem ya cigaba da cewa " sannan kana ganin in dan kai ne zata yiwa iyayenta k'aryar bautar k'asa ta tafi ta barsu.....!?
"Kuma idan dan kai ne ai kai zatayiwa k'aryar ba iyayenta ba,
kuma ai idan dan kai ne to kai meye had'inka da iyayenta,
kuma idan har san rabuwa take yi da kai iya kaci ta daina picking call d'inka,
ta daina kula ka, ta daina yarda kuna had'uwa,
kuma gashi kace ko makaranta ta daina zuwa wajen 5 months kenan rabonta da makaranta,
kuma ni ina ganin saboda kai bazata bar karatunta tana level 3 going to level 4 ba,
bazata lalata wahalarta ta shekara da shekaru ba,
ni dai ina ganin kamar akwai wani abu a k'asa,
akwai zarge cikin nad'i, akwai wata k'ullalliyar gaskiya,
amma kaje dai kayi tunnani,
kuma kace min mai gadin gidan su yace ita da Khulud da Hanash d'in ne kad'ai suka fita a motar lokacin daza'a kaita Damaturun,
then kace mai gadin yace tun daga ranar Khulud bata kuma zuwa gidan ba,
then mai gadin gidan Khulud shima ya fad'a maka tana gidan,
har ma ga abubuwan da tayi, kai a ganinka bata san naka ne zatayi hakan...!?
" Har tayi abu kamar hauka ta rink'a kuka daga kawai ta ganka,
then kace idan ka kira number ta baka samu,
amma da Yayanta ya kira the same number ta shiga,
so ina san ka kuma kiran number yanzu,
jikin Sir Moli na rawa ya d'auki wayarshi,
yayi dialing number Sanah, still not reachable,
idon Leem na kanshi
yace " bani number, ba musu Sir Moli ya fad'a mishi number,
yayi dialing a wayarshi, jim kad'an wayar ta soma ringing,
sai da ta kusa tsinkewa kana tayi picking,
" hello..!, Sir Moli najin muryarta yayi zambur ya mik'e tsaye,
murmushi Leem yayi had'i da kashe wayar,
yace " an saka number ka a black list,
koda zaka shekara kana kira bazata tab'a shiga ba,
saboda tana cikin block list (rejecting call),
ido kawai Sir Moli ya zubawa Leem gumi yana keto mishi ta ko'ina,
d'an shiru Leem yayi kana yace " yanzu mafita d'aya gare mu kawai,
da sauri Sir Aryan yace " me...!?
"Gidansu zamuje mu tambaya,
idan tana gidan to ya tabbata dan kai ta gudu,
idan ko har yanzu bata sannan sai mu tsananta bincike dan tabbas akwai wani a abu b'oye,
ai tun kan Leem ya k'arasa magana Sir Moli ya zari key d'in motarshi ya fita,
da sauri Leem yabi shi, had'i da zama mazaunin driver,
yace " bani key d'in ni zanyi driven dan ban yarda ka kashe mu a banza kai romio ne,
ya fad'a yana dariya, had'i dayiwa motar key, suka fita, Leem na driven Sir Moli yana zaune a gaba dafe da kanshi idanshi a lumshe.
Khulud ta kalli Doctor had'i da cewa " to amma idan akace ni ke da cikin ai Hanash zai gane daga baya,
tunda dole ciki ya rink'a girma,
murmushi Doctor d'in yayi yace " karki damu akwai wani tablet na fake pregnancy da aka fito da ita a USA,
wanda idan mace tana sha cikinta zai rink'a girma kamar na mai ciki,
kuma kwayar bata da side effects,
dan duniya ta yarda da ita, duk wata zaki rink'a shan kwaya d'aya tak,
cikinki zai rink'a girma ya fito kamar na me cikin gaske,
amma kwayar tana da tsada sosai dan duk guda d'aya takai 3k dollars,
kuma duk wata d'aya tak ake sha,
Papu yace " karka damu indai matsalar kud'i ce, dan me aka neme su aka tara su,
ai saboda magance damuwa da matsalar,
zan baka kud'in kayi mata oder,
"Ok badamuwa,
" zan turo maka kud'in ta account d'inka,
sai a siyo gaba d'aya, ya kama guda biyar kenan tunda zata sha wannan watan ma,
"a'a guda hud'u dai, ai banda wannan watan,
sai cikin ya cika wata biyar zata fara, kaga 5,6,7,8,
Khulud tace " to ya za'ayi cikin ya dawo normal kuma....!?
"Ai shiyasa bance 9 ba, dan bazaki sha a wata na tara ba,
da zarar kinyi tsallaken wata d'aya baki sha ba,
cikinki zai dawo normal,
k'ara tattaunawa sukayi kafin dukkansu suka fito,
Papu ya shiga motarshi ya tafi,
su Sanah ma suka shiga motar,
Khulud taja kasancewar Sanah ta dad'e da koya mata motar itama,
kwance Sanah tayi a gaban motar had'i da lumshe idanta,
dan tunda akace mata tana da ciki gaba d'aya jikinta yayi mugun yin sanyi,
a dai-dai government house danja ta tsayarda su,
kasancewar dama ce motar, yasa Sanah ke zaune a b'angaren da driver ke zama a sauran motoci,
a hankali motar su Sir Moli tazo dai-dai motarsu ta tsaya suna jiran danja ta basu hannu,
Sir Moli kwance gaban mota idanshi rufe,
haka ma Sanah,
Khulud tace my Sanah....!
a hankali Sanah ta bud'e idanta ta kalli Khulud,
" my Sanah daga yanzu fa Hanash bazai k'ara sanin kina cikin gidan ba,
d'an tsoki Sanah taja had'i kawar fuskarta ta kalli waje,
karfa idonta ya sauka akan Sir Moli,
idonta ta zaro waje kamar zasu fad'o had'i da tab'a Khulud ta nuna mata shi,
duk ilahirin jikinta na kerrrrma da tsuma,
dai-dai lokacin Sir Moli ya bud'e idanshi,
ba zato idanshi ya sauka cikin na Sanah,
a matuk'ar razane Sir Moli ya kuma bud'e idanshi tarrr yana kallanta,
take duk ilahirin jikinshi ya soma rawa yana b'ari,
cikin tashin hankali ya bud'e motar..................!!!!!!
MOMYN ZARAH
_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
```Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh```
_DEDICATED TO_
*MARYAM HASSAN D'AN IYA*
```(MARYAM OBAM)```
~K'awar arziki abokiyar shawara, Allah ya bamu tare~
5⃣1⃣
Cikin matsanancin zafin nama Leem ya rik'o shi had'i da mayar dashi,
cikin motar ya danna key,
" mai yasa baka iya control kanka akanta ne....!?
" Please dan Allah ka barni naje,
gata can fa na ganta please let me go,
" relax mana..! ya kamata ka rink'a dannewa zuciyarka wani abun,
kayi hak'uri mu fara zuwa gidansu muyi bincike mu tabbatar kafin kayi duk abinda kake san yi,
ajiyar zuciya ya sauke while idanshi na kanta,
itama tana k'ok'arin fita Khulud tayi saurin sanyawa motar key,
"shin kin manta ke matar aure ce.....!?
" Ko kin manta akwai igiyoyin auren wani akanki....!?
"So da zafin soyayya yana neman kai ki ga hakala,
ya halakar dake, ya kai ki wuta,
danna lura kin manta hukunce-hukunce dake kanki,
na addini da shari'a da kuma hakk'ok'in aure,
kin manta abubuwan da Allah yace akan matar aure da kuma mijinta,
duk abinda zakiyi ya kamata ki rink'a yin tunani kafin ki aiwatar,
cikin masifa da zafin zuciya Sanah ta kalli Khulud idanta jajir tana zubar da hawaye,
tace " eh..! na manta wacece ni,
na manta komai da kowa, kuma so da soyayya tabbas su suka makantar dani,
amma so da soyayya bana wani ba,
face ke Khulud, akanki na watsar da komai nawa,
na lalata rayuwa da duniya ta, na tarwatsa gobe na da farin ciki na,
amma har kike tambaya ta hakk'in aure...!?
"Abubuwa nawa ne ba dai-dai ba,
amma na rufe ido nayi su akanki,
kafin hakk'in aure ya hau kaina ai hakk'in iyayena ne a kai na,
sannan da kike cewa kina ga na manta abubuwan da Allah yace,
eh..! tabbas suma na manta, kamar yadda na manta iyayena,
farin ciki na, *ZAB'IN RAI NA* (Sis Nerja'art)
ARYAN RAYYAN MOLI, na watsar da ahalina, tushe na duk akanki ke d'aya,
ta fad'a d'an kwalinta na zamewa daga kanta,
Leem yace " kaga ni ko...!?
"Da alama kamar fad'a suke, dan naga Sanah zata fito d'ayar ta rufe motar,
Aryan bayyi magana ba, idanshi k'uri na kanta,
murmushi Khulud tayi tace " naji muma nagode,
and nasan its not you, saboda I know you modern anybody Sanah,
nasan ko da zakiyiwa kowa tijara a duniya bazaki tab'a yiwa Uludinki ba,
I knew cikin dake jikinki shike saki yin abubuwa da dama,
a fusace Sanah tace " then..! unlock the car an let me go,
ta fad'a a tsawace,
while bata bar kukan ba,
"idan kin manta bari na tuna miki wacece ke,
MATAR AURE CE KE, yanzu MATAR HANASH WASEEF kike ,
akwai igiyoyin aurenshi har guda uku a kanki,
instead of da da kike budurwar MOLI,
" so fucking what....!?
"To hell with auren da shi kanshi mijin,
kana ta juya ta shiga dukan k'ofar tana kiran sunanshi, while hawayen baibar zuba ba,
" HUB...! HUB...!! HUB....!!!!,
ta fad'a tana dukan k'ofar da k'arfi,
ai Sir Moli yana ganin yadda take yi ya zabura ya soma k'ok'arin bud'e motar shima,
ganin haka yasa Khulud keyiwa motar key,
ta figeta da gudu batare da danja ta basu hannu ba,
sitiyarin motar Sir Moli ya daka had'i da dakawa Leem tsawa,
yace " follow them...!
"please Aryan ka.........!
" I said follow them....! ya fad'a cikin matsanancin b'acin rai,
tamkar mahaukaci sabon kamu,
shima Leem a d'an fad'ace yace " wai are you mad Aryan...!?
"Yes..! I'm mad..! nace ka bisu kou...!?
Banza Leem yayi dashi har aka basu hannu,
yayi gidansu Sanah, saboda ya garida yasa gidan,
tun lokacin da sukayiwa Sanah left,
cikin nutsuwa yayi parking ya fito,
kana ya zagaya b'angaren Aryan ya bud'e had'i da rik'o hannunshi,
tamkar d'an k'aramin yaro Sir Moli yabi bayanshi,
har suka k'arasa jikin get d'in,
knocking Leem yayi mai gadin ya lek'o,
ganin Sir Moli ya sashi washe baki,
had'i da fitowa gaba d'ayanshi,
yace " a'a ranka ya dad'e kai ne yau a gidan namu....!?
Sororo Sir Moli yayi yana kallan mai gadin dan yanzu bakomai yake ganewa ba,
"amma sai yau...., ai nayi zaton da mutuniyar ta dawo hutu zaka zo amma sai naji ka shiru....!?
Murmushi Leem yayi dan gudun kar mai gadin ya zari wani abu,
yace " oh..! yauwa kira mana ita,
" a'a badai baku san ta koma ba...!?
" Ta koma kuma...! ina kenan ta koma...!?
Leem ya fad'a dan ya tabbatar,
" bautar k'asa Damaturu mana,
ai tazo hutu dan ina ganin kamar ma satinta d'aya ko fiye da haka,
"yaushe tazo, kuma yaushe ta koma....!?
" Jiya Aarib ya maida ita makaranta Damaturun,
" to amma..........!
Leem zayyi magana yaji Sir Moli ya fizge hannunshi ya nufi matar a fusace,
da sauri Leem yayi tsalle ya shiga cikin motar ya zauna maunin driver,
ya kalli Aryan cike tsantsar tausayawa,
yace " abokina kaga abinda nake fad'a maka ko....!?
"Ni dama wallahi nayi zargin akwai wani abun,
kaga dai har yanzu bata dawo gidan ba...!?
"Tayiwa iyayenta k'arya, and yau mun gansu,
idan ka kalli cikin kwayar idon Sanah zakaga she's still love you,
ji fa yadda take hauka kan saita fito ta ganka,
wallahi there's something behind,
" zaka ja motar ko kuma surutun banza zaka tsaya yi....!?
Aryan ya fad'a da k'arfi,
"Tom..! yanzu ina zamu je...!?
" Gidan Khulud,
"ai ban san gidan ba, ina ne gidan...!?
" Kanshi ya kwantar had'i da lumshe idanshi,
ya d'an dad'e haka kana ya bud'e idon,
ya kalli Leem yace " bani na tuk'a,
"bura uba....! in baka ka kashe mu kenan,
wallahi ban bayarwa in baka bani address d'in gidan sai dai mu kwana nan,
idanshi rufe ya fad'awa Leem kwatancen gidan Khulud,
kana Leem yaja motar suka nufi gida,
shiru kawai Aryan yayi yana tunanin why Sanah zatayi mishi haka,
while gaba d'aya jikinshi kerrrrma da tsuma yake,
deep down kammm ba'a magana danji yake tamkar ya tsaga k'irjinshi ya tsigo zuciyarshi ya jefar.
Da gudu Khulud ta shiga compound d'in gidan tayi parking,
ta bud'e ta fito, had'i da zagayawa ta bud'e b'angaren Sanah,
ta rik'o hannunta, suka shiga cikin gidan,
sosai Sanah ke kuka tayi zaman dirshen a parlor'n had'i da sanya hannunta cikin gashin kanta,
tana yamutsawa while tana kukan tamkar mahaukaciya,
ta saka ta gaba tana ta faman rarrashinta had'i da bata hak'uri amma a banza,
dan Sanah ta riga tayi sama,
gaba d'aya so da tsumin soyyayar Aryan ya motsa mata,
soyayarshi ta dawo mata sabuwa fil,
" I hate my self na cuci wanda yake mutuwar sona,
ji yadda Aryan ya koma, duk ya lalace,
ya zama kamar ba Aryan d'ina ba,
kamar ba shine wannan kyakkyawan santalelen saurayin nan son kowa k'in wanda ya rasa ba,
ji yadda ya koma ya rame, Khulud na tsani kaina da rayuwata,
nasan tabbas nima Allah bazai tab'a kyale ni ba,
dan Ubangiji ba azzalumin sarki bane,
baya zaluntar bawanshi, sai dai shi bawan ya zalunci kanshi,
Allah bai tab'a yafe laifin wani akan wani,
nasan na cuci Aryan nasan sai Allah ya hukunta ni,
a hankali Khulud ta sanya hannunta tana gogewa Sanah hawaye,
while itama tana kukan,
" I'm so sorry, wallahi nayi regretting abinda nayi,
please kiyi hak'uri, dan bakin alk'alami ya riga da ya bushe,
lokaci bai tab'a dawowa baya,
kamar yadda hannun agogo bai dawowa baya,
nadasani k'eya ce a baya take,
dan Allah kiyi hak'uri my Sanah,
ta fad'a tana fashewa da rikitaccen kuka.
Kasancewar mai gadin gidan Khulud sabo ne,
dan wancan tunda Sir Moli ya bashi 2m yabar aikin gadi,
yaje yayi registration d'inshi,
, sauran kud'in kuma yayi jari ya soma business,
yasa wannan mai gadin lek'owa had'i da cewa " waye kuma daga ina....!?
Da sauri Leem yace " tare muke da Hajiyarka da suka shigo yanzu,
itace tace mu zo, ganin manyan mutane ne,
kuma daga ganinsu kud'i sun zauna da gindinsu,
yasa shi bud'e musu get d'in batare da wani kokwanto ko b'ata lokaci ba,
tun kafin Leem ya gama yin parking Sir Moli ya bud'e motar ya fito,
cikin zafin rai ya nufi cikin gidan gadan-gadan,
da sauri Leem ya rik'e had'i da cewa " baka da hankali ne....!?
"Ya za'ayi ka shiga gidan mutane kuma matar aure kai tsaye...!?
" Please ka barni in shiga,
inba haka ba, idan ta fito cemin zatayi Sanah bata nan,
please allow me to get in, dan Allah,
ya fad'a cikin muryar kuka,
gamm sosai Leem ya rik'e shi,
ganin haka yasa Sir Moli d'aga murya yace " K'ALBI.....!
tamkar mahaukaciya ta mik'e tsaye zambur had'i da cewa " HUB...!,
ta fad'a da k'arfi daga Leem har Aryan sunji,tana k'ok'arin fita,
Khulud tayi saurin rik'e ta tace " no Sanah, we are too late,
yanzu kina da ciki, imma kin fita ya ganki, kin koma gida,
kin san dai ba'a yin aure da ciki,
dole sai kin jira 5 months kin haihuwa kuma Hanash ya sake ki kana,
kinga an b'ata goma d'aya bata gyaru ba,
cikin matsanancin kuka Khulud ta durk'usa k'asa bisa gwiwoyinta a gaban Sanah,
tana kuka tamkar ranta zai fita tace " dan Allah ki rufa min asiri,
munzo gaf, muna gab'a yanzu idan kika daure kika hak'ura saura 4 to 5 month kawai,
dan Allah my Sanah karki yi min haka,
karki juya min baya, ta fad'a tana dafe k'irjinta had'i da soma tari,
baya Sanah tayi ta fad'a saman sofa tana cigaba da kuka,
har lokacin Sir Moli yana kwala mata kira kamar mahaukaci,
ganin haka yasa Khulud kiran Hanash yana yin picking tace " kazo gida babu lafiya,
tana fad'ar haka ta kashe wayar ta batare data jira amsarshi ba,
ta kira Hanash ne dan tasan bata iyawa da Sir Moli,
Hanash ko jikinshi na rawa ya zari key yayi gida,
Sir Moli na harabar gidan yana ta faman ihuuun kuka had'i da kiran sunan Sanah,
"K'albi please don't do this to me,
wallahi idan kika barni mutuwa zanyi,
karki barni ina sanki, zan iyayin komai akanki,
dan Allah Sanah, karki yi min haka please,
I beg you in the name of almighty God,
please come to me, I will die Sanah,
I will die,
duk haukan da yake yi tana jikin window tana kallanshi,
ta sanya hannu ta rufe bakinta tana ta faman kuka,
a hankali ya zame ya zube k'asa had'i da d'aga kanshi yana cewa " please...! please...!! please....!!!,
cikin mutuwar jiki Leem ya d'ago Sir Moli,
da k'arfi Sir Moli ya kwace jikinshi yayi cikin gidan da gudu,
Leem yabi shi ya rik'e suka shiga kokawa,
dai-dai lokacin Hanash ya shigo cikin gidan,
ganin abinda ke faruwa yasa shi yin parking da sauri ya fito,
Sir Moli na kokawar kwacewa yana cewa " sai na shiga na fito da Sanah,
tana ciki, wallahi tana ciki tana jina,
Allah ko duniya zata taru saina shiga wajen Sanah,
ko duniya za tashi sai na shiga,
"hey..! hey..! you don't dare you enter my home,
if not wallahi duk uban daya tsaya maka,
koya d'aure maka gindi sai na d'aureka,
wancan ma darajar wasu kace,
amma idan ka kuskura ka k'ara yin wannan gagancin da kuma gigin shigar min cikin gida,
wallahi sai na d'aureka, Hanash ya fad'a yana k'arasowa wajen,
cikin matsanancin kuka Sir Moli yace " ko da zaka d'aure ni d'aurin rai da rai,
na yarda amma dan Allah ka barni naga Sanah even once,
please..! please...!
ido Hanash ya k'ura mishi yana tsantsar mamakinshi,
mamaki na farko da Hanash yake yi,
duk wannan izzar, tak'amar, da isa, jijji dakan duk babu su sun tafi,
mamaki na biyu kuma yadda ya rame ya k'ek'ashi, ya lalace,
ya koje, gaba d'aya ya zama wani iri kamar bashi ba,
in banda yasan face d'inshi sosai da bai tab'a gane shi,
bisa mamakin Hanash, da Leem da kuma Sanah dake tsaye tana kallansu ta window,
suka ga Aryan Rayyan Moli ya zube k'asa gaban Hanash,
ya durk'usa k'asa bisa gwiwowinshi ya riga rok'onshi had'i dayi mishi magiyar yabarshi yaga Sanah,
ya taimaka yasa Sanah ta fito,
wani irin haukacin, gigitaccen, razanannan kuka Sanah ta saka,
yau Sir Moli ne durk'ushe gaban wani,
bisa gwiwowinsa yana rok'o da neman alfarmar a barshi ya ganta sau d'aya tak,
da gudu ta shige bedroom d'inta had'i da fad'awa saman bed,
take duk ilahirin jikin Hanash yayi sanyi,
lokaci d'aya tausaya Sir Moli ya mamayen duk ilahirin jikinshi,
a hankali ya durk'usa ya d'ago shi,
cike da tausayawa dan yasan meye so, meye wahala, zafi da k'unar so,
yace " kayi hak'uri please nasan bata nan, dama hutu tazo,
kuma hutunsu ya k'are ta koma gida,
cikin kuka Aryan yace " wallahi tana cikin gidanka, da ido na naganta na kuma ji muryarta yanzu,
shiru Hanash yayi kana yace " Khulud...! Khulud...!
ya kwala mata kira da k'arfi,
jikin Khulud na rawa ta sanya hijab ta fita,
ido ya k'ura mata yana karantar yanayinta,
kafin yace " Khulud ina Sanah...!?
Cikin alamun rashin gaskiya tace " bata nan,
idon Sir Moli na kanta yace " Khulud yanzu ni zaki kalla kice Sanah bata cikin gidan nan....!?
"Bata nan Sir,
Leem dake tsaye kanshi ya gama kuncewa,
tunda Sir Moli ya d'urk'usa gaban Hanash,
ya gama yankewa da al'amarin,
shiru kawai yayi cike tsantsar mamaki dan yafi kowa sanin waye Aryan ,
yace " Khulud kiji tsoran Allah,
yanzu muka ganku tare, kuma da muka shigo tayi magana,
amma k'iriri kice bata nan,
kuka ta sanya had'i da kallan Hanash tace " Allah bata nan,
shiru Hanash yayi yama rasa waye mai gaskiya tsakaninsu,
dan tunda yake da Khulud bata tab'a yi mishi wani abu na rashin gaskiya ba,
kallan Sir Moli yayi yace " bari na shiga na duba maka ko'ina,
in an out kuma nayi maka alk'awarin zan sanar dakai gaskiya,
Khulud najin haka tayi saurin turawa Sanah text,
"hide,
abinda kawai tace mata kenan,
while gaba d'aya jikinta na kerrrrma da tsuma,
duk gidan babu inda Hanash bai duba ba,
amma baiga Sanah ba, cikin mutuwar jiki ya dawo, gaban Khulud sai dukan uku-uku yake yi,
Hanash yace " I'm sorry wallahi na duba ko'ina amma bata nan,
Aryan zayyi magana Leem yace " shikenan ba damuwa mun gode sosai,
ya fad'a yana rik'e da Sir Moli,
bayansu Hanash yabi da kallo cike da tsantsar tausayawa,
Leem yayiwa motar key suka bar harabar gidan,
Sanah ko Khulud na tura mata text,
ta shige bedroom d'in Hanash,
ta b'oye dan tasan ba lalle ne ya duba nan ba,
amma saboda yayiwa Sir Moli alk'awari sai da ya duba har nan,
Allah ne bai bashi ikon ganinta ba,
Leem na driven babu mai cewa kowa komai shi da Aryan,
yaji yace " park..!
ba musu Leem ya gangara gefen hanya yayi parking,
motar Aryan ya bud'e ya fita,
had'i da jingina da jikin motar,
cikin zafin rai ya naushi motar da k'arfi,
inda ya nausa ya loma, had'i da juyawa motar baya,
hannunshi d'aya cikin sumar kanshi,
d'ayan hannun rik'e da k'ugunshi,
cikin mutuwar jiki Leem ma ya fito,
ya tsaya nesa dashi, yana kallanshi,
gigitaccen kuka Aryan ya saki had'i da durk'ushewa,
Leem bai san sanda hawaye suka soma zubo mishi ba,
bayyi k'ok'arin hana Sir Moli kuka ba,
dan yasan hakan itace kad'ai hanyar samawa kanshi da zuciyarshi salama,
sai da yayi mai isarshi, kana ya bud'e motar ya shiga da kanshi,
Sanah na nan b'oye Hanash ya shigo bedroom d'inshi,
ya zauna bakin gado had'i da yin tagumi hannu bibbiyu,
babu abinda ke damunshi yana yi mishi yawo cikin rai sai Sir Moli,
dan harga Allah ya tausaya mishi sosai,
cikin sanyin jiki ya mik'e yayi naked (zindir) ya shiga bathroom,
Sanah dake tab'e tana kuka, tana ganin naked Hanash jikinta ya soma tsuma,
take taji mood d'inta ya soma canjawa,
da sauri ta mik'e ta fita, a parlor ta iske Khulud zaune itama tayi tagumin,
"please bani number Doctor ta fad'a tana shigewa bedroom,
da sauri Khulud ta bi bayanta,
ta shiga had'i da dannawa k'ofar key,
tace " me zakiyi da number Doctor...!?
"Laifi ne danna tambaya...!?
" A'a, Khulud tace had'i da bata number ta koma ta zauna gefe dan taga Sanah tayi dialing number,
had'i da tsura mata ido tana san jin me zatace mishi,
bugu d'aya Doctor ya d'auka saboda yana da number ta, itace dai bata da shi,
cikin fara'a da wasa yace " me ciki,
murmushi tayi gami da gaidashi,
ya amsa kana ta d'anyi shiru,
" kiyi magana, yace , cikin sanyin murya tace " dama tambayarka nake san yi,
"ba damuyi yi tambayarki kai tsaye ba komai,
" dama cewa nayi ina yawan jin feeling (sha'awa) sosai,
abu kad'an sai anji ina buk'atar namiji,
wani lokacin ma marata har ciwo take yi min,
which is ni kuma ban san hakan gaskiya.
Murmushi Doctor d'in yayi kana yace " eh...! akwai cikin dayake zuwa da haka,
wani lokacin ma zakiji idan baki samu ba,
tamkar ki mutu, akwai kuma wanda kwata-kwata bai san sex d'in koma kiji kin tsani wanda yayi miki cikin gaba d'aya,
kiji baki ko san ganinshi,
kamar yadda idan kina son sex zaki ji kina matuk'ar son wanda yayi cikin ko wani abu daya shafe shi,
kamar k'amshin jikinshi, kuma koda baki sanshi zakiji kina sonshi kina kuma damuwa dashi sosai,
a likitance ana son ciki mai saka yawon sa sex saboda dalilai biyar a likitace,
1. Sex Lowers Blood Pressure,
sex during pregnancy will help you to lower blood pressure,
during intercourse a hormone called oxytocin,
also known as the love hormone is released which is a good stress reliever,
this hormone will help to alleviate the built up tension and stress this in turn,
will help you to keep the blood pressure at a healthy level,
2. Enables Sound Sleep :- it's obvious that during pregnancy women often experience all kind of discomfort,
starting from back pain to frequent urination and the sleeping hours get disrupted and shortened as the fetus grows in the womb,
having an intercourse resulting in organs will make youf feel wonderful,
and you have no problem falling asleep,
this why sex during pregnancy is an excellent way of getting sound sleep,
3. Better Intimacy With your partner,
having sex during pregnancy will increase the intimacy between you an your partner and that bond will remain unbreakable forever,
4. Reduce pain an 5. Organs experience,
so ba saina tsaya yi miki bayanin su dalla-dalla ba,
amma dole zaki so sex sosai saboda cikin jikinki,
ajiyar zuciya ta sauke had'i da yi mishi godiya kana sukayi sallama,
a hankali Sanah ta kwanta saman bed tana tunnin rayuwa,
dan saboda tsabar kukan datayi yanzu hawayenta ma sun k'afe,
kwata-kwata kukan ma ya tafi babu shi babu dalilinshi,
a hankali ta soma jin mararta na kartawa,
anan ta gane yunwa + feeling ke damunta,
fuska ta d'an yamutsa had'i da d'ora hannu saman cikinta,
cikin nutsuwa Khulud ta mik'e tayi kitchen dan ta lura yunwa Sanah keji,
dan haka take yi idan tana jin yunwa,
har saman gadon Khulud ta kawo mata abincin ta rarrashe ta kana taci,
shima badan ranta naso ba, sai dan jin zata mutu.
A ranar Khulud kwana tayi tana amai (pretending),
washe gari tunda sassafe Hanash ya kwashe ta sukayi Hospital wajen family Doctor,
gwajin farko Doctor ya sanarwa Hanash Khulud nada shigar ciki na wata hud'u da sati biyu,
kammmmm! ai tsaye kawai Hanash yayi ya kasa cewa komai,
sai da Doctor ya tab'a shi kana ya dawo cikin hayyacinshi,
kallan Doctor yayi had'i da cewa " please say it again,
cikin murmushi Doctor yace " your wife is pregnant,
kanshi ya girgiza had'i da d'an mari kanshi yace " I know I'm dreaming,
ya fad'a yana cigaba da girgiza kanshi,
a hankali Doctor ya kama hannunshi ya zaunar dashi,
kana ya k'ara maimaita mishi had'i da bashi result d'in,
ai Hanash na gama karantawa ya sanya kukan farin ciki had'i da yiwa Rabbi sujjadul shukru,
ya dad'e duk'e yana yiwa Allah godiya,
cikin matsanancin kuka kana ya d'ago had'i da rungume Khulud gam-gam,
yana kuka, itama kukan tausayin kanta da mijinta, da kuma na sanarta ta sanya,
hummm ranar duk wanda ke hospital d'in nan yasha kud'i,
tun daga kan, labourers, Doctors, Nurse's, an so on,
babu wanda Hanash bayyiwa gigitacciyar kyauta ba,
daga nan gidan marayu ya nufa can ma yaje yayi b'arin naira,
haka Hanash ya rink'a bin hospital da gidajen marayu dana marasa k'arfi yana bada taimako,
tsayawa fad'ar murna, farin ciki, jin dad'in da tsantsar zallar dad'in da Hanash yaji b'ata lokaci ne
Khulud kam shiru kawai tayi cike tsantsar mamaki,
da kuma tausayin kanta,
shi yayi murna a dai-dai,
dan d'anshi ne halak malak, ko a wajen Allah,
kuma shine magajinshi,
amma ita fa, dan tasan kowa rai yayiwa dad'i bai kai yameshi ba,
then...! kayan aro baya rufe katara,
duk da tasan d'an Sanah itama nata ne, amma ai bashi da gadonta,
kuma ita bazata ji murna da farin cikin da ake ji ba lokacin fad'ar ciki da haihuwa ba,,
bazata san zafin nak'uda, shayarwa da rainin ciki ba,
siraran hawaye ta goge, had'i da cewa " thank you God, for helping me, an showing me the right way,
I know no body know what's left behind us,
cikin k'ank'anin lokaci zance yabi dangi da 'yan uwa Khulud is pregnant,
kowa ya d'auki murna da farin ciki,
aka shiga yi mata addu'oi kala-kala,
Mamu da Juju kam har kukan farin ciki sukayi,
Jaddah kam data ji rawa ta taka tana kuka saboda murna da farin ciki,
har gida tazo ta bawa Khulud hak'uri ta kuma nemi yafiyarta.
Bayan kwana biyu komai ya wuce a b'angaren Khulud da Hanash,
amma banda Sanah dan tana cikin matsananciyar damuwa akan Aryan d'inta,
kwance take saman bed tayi nisa cikin duniyar tunani,
wutsil taji abu ya motsa cikin cikinta,
d'an sararawa tayi ta nutsu sosai,
dan taji ta kuma tabbatar, wutsil-wutsil taji an kuma motsawa har sau biyu,
d'a da uwa sai Allah, take Sanah yaji wani irin mugun dad'i da farin ciki sun lullub'e ta lokaci d'aya,
taji ta nemi gaba d'aya bak'in cikin datake ciki ta rasa,
fuskarta d'auke da murmushi ta mik'e zaune,
had'i da sanya hannu ta shafa cikinta,
tace " sannu bacci kake yi ko yunwa kake ji...!?
Ta fad'a kamar tana magana da mutum a zahiri,
jin ya kuma motsawa yasa komawa kwance had'i da d'age rigarta ta sanya hannu saman cikin tana shafa had'i dayi mishi magana,
sosai kamar tana hira da mutum,
tun daga wannan lokacin Sanah ta samu abokin hira,
dan kullum kuma koyaushe cikin yi mishi magana da hira take,
wani lokacin ma rigar take cirewa gaba d'aya tayi kwance tana shafawa tana magana,
duk abinda tayi saita bashi labarin,
har labarin Roni, dana BUK cikin nan nasha,
labarin Sir Moli kam har ya gaji dashi,
wani lokacin haka zata fito harabar gidan ta zauna tana bashi labarin duk abinda ke wajan,
kai ko film Sanah ta gani sai ta bashi labari tas,
haka labarin families d'inta kam ta bashi,
wani lokacin har da dariya ko murmushi, idan ko aka yini bai motsa ba tab ta rink'a yiwa cikin magana kenan har sai Allah ya bashi ikon motsawa,
kullum bata da aiki sai hira da cikin jikinta.
Hanash da Khulud zaune a bedroom suna hira,
" wai ni kin san abinda ke bani mamaki.....!?
"A'a sai ka fad'a,
" kai na yana d'aurewa yadda duk bayan kwana biyu kike canjawa ,
wani lokacin kuma sai naga nafi 2 weeks ina yi amma babu abinda ya canja,
wai ya abin yake ne meye sirrin...!?
Murmushin yak'e tayi tace " eh...! kawai wani lokacin ina gajiye ne,
sai na tab'a halin ta fad'a tana dariya,
shima dariyar yayi had'i jan hancinta,
we are latest parent, an best Dad of year,
cikin shagwab'a Khulud tace " au Dad ma kawai zaka ce banda ni kou...!?
"Sorry harda ke mana ai idan nace ni har ke nake nufi, because we one,
ya fad'a hannunshi kan cikin ta shafawa,
a hankali ya kara kunnenshi sai tin cikinta,
wai zai jiyo motsin baby, kissing cikin yayi had'i da cewa " I love you so much my on born,
hmmmm ikon Allah kenan, wato duk inda jinzikiri yake daga Allah ne,
gaggawa ce daga shaid'an, ki duba fa we are 3yrs da aure amma ko b'ari,
da Allah ya tashi bamu sai ya bamu na 4 months getting to 5mnts,
wallahi randa Doctor ya fad'a min you're pregnant,
kusan zaucewa nayi, dan sai da kwakwalta tayi hook,
naga yau ni ne matata ke d'auke da ciki na,
na kusa ganin d'ana gudan jini na,
gaskiya I'm very happy ever before,
kinga da mukayi hak'uri Allah ya bamu,
duk maganar da Hanash keyi hannunshi da idanshi kan cikin yana shafawa,
deep down yana jin yafi son cikin fiye da komai da kowa,
ciki kuwa harda ranshi da rayuwarshi,
dan harga Allah, Allah yayiwa Hanash mugun son yara,
shi bama nashi ba na wasu ma so yake,
a tak'aice dai duk inda kuke neman mutum mai matuk'ar son yara to Hanash he's the best among the rest.
"I love you ya fad'a yana had'e bakinsu,
d'an dukan k'irjinshi tayi had'i da ture shi,
matse ta ya k'arayi sosai a jikinshi,
gami da k'ok'arin tura hannu cikin rigarta,
murmushi tayi tare da kwace jikinta,
tayi hanyar fita, da sauri ya kuma rik'o ta, ya had'a ta jikin bongo ya matse ta sosai,
k'irjinta na jinkin bangon, cikin salo Hanash ya had'e k'irjinshi da bayanta,
had'i da zura hannunshi kan cikin ta yana shafawa,
had'i da wasa da cibiyarta, ya d'ora hab'arshi saman kafad'arta,
yana goga mata kwantaccen gashin dake fuskarshi, sajenshi (k'asumba),
muryarshi can k'asan mak'ogwaro yace " ina sanki ina matuk'ar sanki,
ya fad'a hannunshi na yawo saman cikinta,
murmushi tayi batare datace komai ba,
cikin salo Hanash ya zame hannun rigar baccin dake jikinta ta fad'i k'asa,
ya rage daga ita sai pant ko bra babu,
yatsanshi ya sanya gadon bayanta,
yana wasa dashi had'i dayi mata dirty talk,
take ta rasa control, cikin zafin nama ta juyo a sukwane,
ta had'e bakinsu, ta shiga tsotsa tana shafa k'irjinshi,
cak Hanansh ya d'auke ya direta saman sofa,
ya juye ya hau samanta suka cigaba da hot romance,
basu sararawa juna ba sai da suka samu nutsuwa,
kwance sukayi dukkansu suna mayar da numfashi,
cikin sanyin jiki Sanah ta d'ora hannunta saman hannun Hanash dake saman cikinta,
tace " ga amanar d'ana nan, zan tafi na barka dashi, ka tabbatar ka bashi ingantacciyar tarbiya, da ilimin addini,
karka bari son da kake yi mishi ya rinjayi zuciyarka ka kasa yi mishi tarbiyya dan Allah,
duk son da wani ko wata zayyiwa d'a bai kai ga uwarshi mahaifiya ba,
dole d'a sai uwarshi, babu wanda zai iya jure masa'uliyar d'a sai iyayenshi na ainahi,
saboda yau da gobe sai Allah,
duk duniya nafi kowa sanin zafinshi, da ciwonshi,
nafi kowa sanshi, da sabawa dashi,
dan d'a tun yana ciki yake sabawa ya shak'u da mahaifiyarshi,
" haba Khulud wai meye haka ne, ya kike yin abu kamar mai mutuwa ko mai bada wasiya....!?
"Ni dai dan Allah ga amanar baby na nan a hannunka,
tunda nasan ni ko ba dad'e ko ba jima dole sai ba tafi,
ni ba mai rayuwa dashi bace, dole sai na rabu dashi, bazan rayu da abinda ke ciki na ba,
dan Allah ka zama garkuwarshi,
ka zama mishi uwa mahaifiya da kuma uba mahaifi,
dan kai ne uwarshi kuma kai ne ubanshi,
dan nasan duk duniya babu wanda zai kai mu so da k'aunarshi,
ni mahaifiyarshi ce amma ta b'oye dan bazan kusance, na kwana dashi a matsayin uwa mahaifiya ba,
ba wai lalle sai mutuwa ce zata raba mu ba,
amma nasan tabbas wata rana babu ni,
dole kai ne gatanshi, dan dole zai rasa uwarshi a kusa dashi,
bazai tab'a sanin dad'in uwa mahaifiya ba,
bazai san dad'in uwa ba, ba zai san dad'in d'umin jikin uwa ba,
ka tallafi rayuwarshi ka cire mishi kewa da maraicin mahaifiyarshi,
ko ina da rai ko bani da rai dole zai rasa ni,
ta k'arasa maganar tana hawaye,
ji yayi gaba d'aya jikinshi yayi sanyi ya d'auki kerrrrma da tsuma,
kasa koda furta kalma d'aya yayi,
batare da yayi magana ba, ya rungume tsam cikin jikinshi,
cikin sanyin jiki ta kwantar da kanta saman k'irjinshi,
hawaye na cigaba da zuba.............!
0 comments:
Post a Comment