Shiru parlorn yayi suna sauraren Barr Munir, banda bugun k'irajensu baka jin komai, ...
"Saida ya kuma goge k'wallan idonsa kafin ya soma fad'in" Salim.... Salim was trying to commit suicide, he shot himself...... Ai baikai aya ba Mummy ta saki wani irin k'ara....
"Kausar ma toshe bakinta tayi tana k'unshe kukanta ta fad'a jikin Asmah wacce itama tashin hankalin ne ya ziyarce ta...
"Cikin tsananin kuka Mummy ta rik'o yayanta Barr Munir take fad'in" No.. No Munir this is ridiculous, tell me ba gaskiya bane, Oh my baby boy me yake nema a duniyar nan bai samu ba har yake yunk'urin kashe kansa... Mik'ewa ta kuma yi tana fad'in" Take me to him Munir, I really want to see my boy, ...
"Mik'ewa Kausar ma tayi idanunta sharkaf da hawaye take fad'in" I'll go with you mummy...
"Barr ya d'an dubeta kafin yace " Inaganin Kausar ki zauna a gida, don zuwan naki ka iya haifar da wani abin, sabida magana ta gaskiya A DALILIN KI ne yake yunk'urin kashe kansa.... Gaba d'aya suka zaro ido harda Mummy, Asmah tasa hannu a k'irji ta dafe..
"Barr yaci gaba da fad'in" Salim was trying to kill himself because of you Kausar, That filthy girl called you and told you k'aryar data saba, wanda DAGA TAIMAKO abin nasu ya koma sharri, a dalilin yunk'urin raba aurenku da kike k'ok'arin yi shi yasa Salim yanke shawaran kashe kansa Don bazai iya rayuwa babu ke ba, yana sonki yanda baki tsammani, don haka inaga ki zauna a gida kawai shi yafi... Hannunsa Mummy ta shiga janyo hannun Barr duk da jin zancen nasa yayi matuk'ar girgiza ta bai hanata watsa wa Kausar mugun kallo ba don tasan komai ka iya faruwa tunda an jima ana b'oyewa Kausar da iyayenta, ficewa sukayi itada Munir cikin sauri....
"Bud'e baki tayi zatayi wa Asmah magana sai kuka, Asmah ta rungumota tana lallashi, jin dirin motar Barr yasata d'ago kai a zabure tana fad'in" Asmau mu bisu kar su b'ace mana, I really want to see Salim, take me to him pls... Ta k'arashe maganar cikin fashewa da kuka....
"Gyad'a kanta kawai Asmah tayi kafin ta rik'o hannunta suka fice suka nufi mota....
"Mai taxi yana ajiyesu tasa kai zata shige, saurin rik'o hannunta yayi kafin yace " I'll be waiting for you here har ki gama classes d'in naki..
"Da mugun mamaki take duban yanda ya rik'e mata hannu ga mutane nata faman kai komo, gaba d'aya jinta a tsarge take, gani take kaman kowa su yake kallo, ..
"A hankali tace " Give me back back my hand.. Tana maganar tana kallon mutane a tsarge, d'an matsowa kusanta yayi yana murmushi kafin yace " Sai kin min alk'awarin zaki amince nazo d'aukanki snn zaki soma Therapy class d'inki as well...
"Jin hannunsa cikin nata yana haifar mata da wani irin yanayi don haka da sauri ta gyad'a kanta kana tace " Eh naji na amince but that doesn't mean you'll be fetching me up everyday.... "
"Murmushi ya kumayi wanda ya jima baiyi irinsa ba har saida fararen hak'waransa suka bayyana he couldn't believe wai yau Zubaidah ke masa magana haka cikin sanyin murya har tana cewa ta amince da buk'atarsa...
"D'an sakin hannunta yayi kafin yace " I'll get you later, take care....
"Ba tare da tace komai ba cike da k'osawa tayi shigewarta, k'irjinta na bugawa da sauri da sauri, sai faman dunk'ule hannunta da ya rik'e take, don ji take kaman har yanzu hannayensu na cikin na juna....
*Dasuki Hospital*
"Daddy yana hango Mummy ya tafi ya rungumeta, kuka mai k'arfi ya kuma b'ark'e mata tana fad'in" Kasim our son, our only son, tell me he can go through this.... Zaunar da ita Daddy yayi yana calming d'inta, Labib dake tsaye tare da Tariq yayi saurin taro ruwa a dispense ya mik'awa Mummy yana fad'in "Have some water Aunt,
"Karb'a tayi tana kallon Labib d'in kafin tace " Tell me your brother will get out of here soon...
"Durk'usawa yayi gaban kujeran da take zaune ya rik'e hannayenta kana yace " Insha Allah Aunt, very soon, I know my cousin is a fighter he can get through this, ki kwantar da hankalinki pls Aunt, Yasa hannu ya amshi ruwan ya Kai bakinta kafin yace " Drink your water..
"Gyad'a masa kai tayi ta shiga kwankwad'an ruwan...
"Nurses ne suka Bud'e k'ofar kana suka soma turo sa kan gado mai tayu.... Ai tuni sukayi kansa gaba d'aya hakan yayi daidai da isowar su Kausar.
"Da sauri ta k'arasa jikin gadon tana kiran sunansa, Nurses kuwa sai faman tattaresu suke don har lokacin bai farfad'o ba snn ga oxygen saman hancinsa...
"Intensive care aka saka sa snn aka hana kowa shiga, saidai suna hangensa ta glass..
"Mummy tamkar baud'eddiya haka ta koma, saida Mum d'in Tariq ta iso kafin ta d'an sami nutsuwa...
"Suna zazzaune gaba d'aya a reception, gaba d'aya Kausar jinta take a tsarge ganin kowa da kalan kallon da yake mata, she felt guilty for what happened, Asmah ta lura da haka taja 'yar uwarta ta kwantar bisa kafad'a coz she knows exactly how she feels.
"Asmah bani wayarki ban fito da tawa ba, Kausar ta fad'i cikin rawar murya ,
"Mik'a mata Asmah tayi ba tareda tace komai ba..
"Mumsy da Pappy suna bisa dinning table suna breakfast lokaci guda suna firan d'iyar tasu da sukayi kewarta wayar Mumsy ya soma ringing, d'agawa tayi tana murmushi take duban mijin nata kana tace "Kaga muna zancenta ga wayar Asmah, k'ila tana can gidan nata..
"Murmushi kawai pappy yayi gamida sipping coffee d'insa sanda Mumsy ke amsa wayar...
"Jin muryar Kausar ce ba Asmah gashi cikin wani irin ta yanayi yasa hankalin Hajiya Raliya tashi wanda yasa Alh Tahir ajiye mug d'in hannunsa babu shiri...
"Wani asibiti kuke, okay gamu nan zuwa, Mumsy ta fad'i kafin ta kashe wayar tana duban mijin nata wanda shima ita yake duba..
"Meke faruwa, waye a asibiti, Pappy ya tambaya sounding curious...
"A daburce ta soma fad'in" Wai Salim ne babu lafiya yana intensive care, Pappy our daughter need us tashi muje pls, oh my poor baby kuka take sanda take min magana...
"Subhanallah d'auko min wayata a sama barince Lawan ya fito da mota, cikin sauri Mumsy ta amsa kafin ta nufi upstairs.....
***********
"Wani farinciki maras misaltuwa yake ji haka kurum wanda shi kansa baisan dalili ba, ni kuwa Sameena nace (Jalal keep on saying taimakonta kake..... you are into the girl irin totally d'in nan..... 😜)
"Shiryawa yayi tsaf cikin k'anan kaya, Ash shirt da brown chinos, yayi kyau sosai dukda raunin dake jikinsa bai hana kyaun halittarsa fitowa ba. A gurguje yayi sallama wa Annah ya sanar da ita zai d'auko Zubaidah snn daga chan zasu wuce gidan Dr Khaleesat therapist wacce zasu na therapy classes da Zubaidah, sosai Annah taji dad'i ganin abubuwa sun soma canzawa tsakanin Jalal da Zubaidah...
"Tana fitowa daga gate d'in makarantar ta hangesa tsaye kasan wata bishiya, haka kurum taji mugun fad'uwar gaba, d'an saita kanta tayi kafin ta soma tafiya cikin tsanaki...
"Tun daga nesa yake murmushi kumatunsa saielotsawa suke, har ta k'araso yanda yake ta tsaya daga can gefe, fuskar nan tana tamau babu alamun fari'a...
"Yasan bazata masa magana d'an kallonta yayi kafin yace " Shall we..
"Ba tareda ta kallesa ba ta soma tafiya.
"So how's your first day at school, ya tambaya sanda suka k'arasa bakin hanya..
"Shiru kaman bazata amsa ba sai kuma tace "Lafia a tak'aice...
" Har suka shige tasi d'in bata kuma cewa komai bar, shima shirun yayi har suka isa gidan Dr Khaleesat....
"Bayan sun sauk'a a tasi d'in ne ta bisa da kallo alamun tambaya.
"Yasan hakan zata kansance kai tsaye yace " D'aya class d'in zakiyi a nan...
"Tab'e baki tayi gamida kauda kai gefe kafin tace " Niba mahaukaciya bane babu therapy d'in da zanyi...
"D'an shiru yayi yana kallonta kafin yace " You promised me.
"Kallonsa tayi yanda yayi maganar cikin sigan tausayi, d'an jimm tayi kafin tace " Eh ai sabida ka amince min zaka tafi shiyasa nima na amince " Gyad'a kansa yayi dukda fad'uwar gaban da yaji, yasan ya mata alk'awarin barin rayuwarta amma baijin zai iya cikawa, he leave her all alone.
"D'an ware madaidaitan idanunsa yayi wanda basu faye girma sosai ba sai tsawo da shape me kyau kafin yace " Fine naji na amince mu k'arasa, bata kuma cewa komai ba ta soma binsa a baya..
"Bayan sunyi knocking mai gadi ya bud m'e masu ya tambayesu ko Dr tasan da zuwansu, Jalal ya shaida masa ta sani snn ya buk'aci ya sake masu iso, ba tareda b'ata lokaci ba aka masu izinin shigowa...
"Masuk'i aka masu a parlour, mintoci kad'an wata mata 'yar gayu ta fito at her early 40's, da murmushinta ta k'araso tana masu sannu da zuwa, Da gani tanada barkwanci.
"Bayan sun gaisa ne Jalal yace shine wanda ya tura mata sak'o ta mail d'inta tace suzo gida su sameta....
"Murmushi Dr Khaleesat tayi kafin tace " Ai tun daga ganinku na ganeku Jalal, ta kalli Zubaidah lokaci guda tana karantar ta yanda ta zauna can gefe Jalal na wani kujera na daban.
"Kan kace me an cika gabansu da drinks, Dr Khaleesat ta kalli Zubaidah ta kalli Jalal kafin tayi murmushi tace " Mr Mrs Jalal ya kuka zauna kujera daban, kallon juna sukayi a tare babu wanda ya iya cewa komai, Dr tayi murmushi sanda take mik'awa Zubaidah cup na drink kafin tace " Kina tsoronsa ko??
"Kallon mamaki Zubaidah ta mata, Dr ta kuma yin murmushi kafin ta dubi Jalal tace " Mr Jay ka d'an jira mu a wancan waiting parlour d'in, ba tarda b'ata lokaci ba Jalal yayi yanda tace.
"Kafe Zubaidah dake faman juya Cup d'in hannunta da ido tayi kafin tace "Feel at home kinji, gidan nan be'azuwa ba'aci komai ba, so ina jinki, tsoron mijin naki kike...
"Sai snn Zubaidah ta dubeta kafin tace " Ni ba tsoronsa nake ji ba, tsanarsa nayi , snn ba mijina bane don ya kusa tafiya ya bar min rayuwata, ...
"Dr ta murmusa kafin tace "Nasan bashi kad'ai ba duk wani namiji ma kin tsana, Zubaidah ta gyad'a kanta kafin tace " Hamma na ne kawai ban tsana ba,
"Jinjina Kai Dr tayi kafin tace " But what makes you hate them, kallonta tayi kaman bazatayi magana ba sai kuma tasa hannau tana share idonta alamun hawaye sun zubo mata, Dr ta d'auko tissue paper kana ta goge mata hawayen kafin tace "I know it hurts, it's very hard to start again, but you have to fight your Devastation, don't let it get into you, only then you'll live again... Ta d'an ja fasali kafin taci gaba da fad'in" First kiyi k'ok'ari kisami soyayyar kanki, ki k'aunaci kanki snn kisa a ranki Allah ba yak'i ki bane ya baki irin wann jarabawan, no it's a trial, it could happen to anyone, second be happy with the people around you, people that shows you love and compassion, don't ever push them away, don't let them go, such people are blessing from Allah. Snn duk mutanen da kika Allah Ya ciresu daga rayuwarki you are not meant to be with them, because sometimes absence of some people makes us something in life...
"Tunda ta fara magana Zubaidah ta nutsu ta bata hankali sosai, maganganun Dr Khaleesat ya haifar mata da tunanin da bata tab'a yin irinsa ba.
"Hira Dr ta ringa jan Zubaidah dashi tana mata tambayoyi gameda rayuwarta, d'an lokaci k'ank'ani taji ta sake da Dr Khaleesat, daga bisani Dr tacee" Toh Zubaidah ni a yanzu k'awarki ce kuma aminiyar shawarin ki, snn pls I need you to be honest with me, no hiding things okay......
"Murmushi Zubaidah tayi gamida gyad'a mata kai don shakka babu taji relief a d'an wann hiran da sukayi da Dr Khaleesat.
"Bayan sun gama da Zubaidah ta nemi ganin Jalal shi kad'ai shima, nan ta d'anyi briefing nasa yanda sukayi snn ta basu Time d'in da zasu na zuwa, sosai Jalal yayi godiya wa Dr ya tambayeta yanayin biyan kud'in.
"D'an murmushi tayi kafin tace " Ta jima tana wann taimaka wa mata 'yan uwan ta da mummunar k'addara ta fyad'e ta auka masu, she's not doing it for money, snn labarin Zubaidah ya banbanta da wanda taci karo dasu a baya, don haka she really wants be part of her Story....
"Godiya sosai ya mata gamida jinjina mata, tabbas da za'a sami mutane irin Dr Khaleesat da Al'ummah taci gaba sosai,... Allah ka yawaita mana irinsu ameen...
"Ana kiraye kirayen sallan la'asar mai taxi d'in ya ajiyesu a k'ofar gida....
***********
"Zaune suke a joint d'in da suka had'u kwanakin baya, Zulaihat ta rausayar da idanu kafin tace " Your highness har na cire ran bazan sake ganinka ba tunda k'anwarka me kishin nan ta d'au wayarka sanda na kira..
"Murmushi Shattima yayi kafin yace " Ai na fad'a maki Abuja gida ne a wajena, you can see me any moment, mayaudarin murmushi ta kuma yi sanda wayarsa tayi k'ara, Usman ne me kira, d'aya wayan yayi suka gaisa suna tsiya ma juna kaman yanda suka saba...
"Zan shigo garejin ku anjima ka fad'awa Jalal pls kar ya tashi da wuri ina nan zuwa, cewar Shattima
"Speaking of Jalal, halan baka san ya d'an yi accident ba ko, jiya da yau baizo gareji ba... Usman ya fad'i...
"Subhanallah wllhi banida labari pls ina zuwa anjima sai ka kaini gidan nasa na gaishesa, ai na ce maka pls, ban son iskanci wllhi zanzo.. Yauwa see you soon... Daga haka yayi hanging up...
"Jin anyi maganar Jalal gaba d'aya hankalin Zulaihat ya karkata kan tunaninta, this is the only chance da zata samu su had'u da Zubaidah.......
Sameena ce 👌🏾👌🏾
[1/23, 22:20] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
42
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Pls let me accompany you, I insist.... Ta k'arashe maganar cikin siga na Salon yaudara.
"D'an tab'e baki yayi kafin yace " Baki tunanin za'a nemeki a gida, this is totally wrong...
"Pls Shattima don't say no, besides we are not doing anything wrong, Dan Allah ka bari nayi maka rakiya, my Aunt would understand me,...
"D'an jim yayi kafin ya gyad'a kansa yace " Okay fine amma daga can direct gida zan ajiyeki sai mu gaisa da Aunt d'inki....
"Cikin Zulaihat ya bada quu, don kuwa k"arya ta shera wa Shattima cewa karatu tazoyi Abj snn a gidan Aunt d'inta take zaune, amma ko kad'an bata so tayi loosing wnn Chance d'in musamman yanzu da Tariq ya bata labarin abunda ya faru....
"Tura masa address Usman yayi don yace bazai sami zuwa ba aiki ya cab'e masa a garejinsu musamman yanzu da babu Jalal....
"Hakan sai yafi ma Zulaihat Dad'i....
"Ana kiraye kirayen sallahn magrib suka isa gidansu Jalal dake suleja, waya ya masa ya sanar dashi gashi a k'ofar gidansu, unbelievably ya fice daidai lokacin da ya ida alwalan sa.
"Jalal yayi mamakin ganin Shattima a gidansu, nan ya fad'a masa Usman ne ya sanar dashi baiji dad'i ba, gaisawa sukayi, snn suka gaisa da Zulaihat ma,
"Jalal ya masu iso cikin gida wajen Annah...
"Da hannu bibbiyu Annah ta karb'esu, suka gaisa cike da karamci,
"Bayan Annah ta mik'e kawo masu ruwa Shattima ya dubi Jalal yace "Ina Madam,??
"Saida gabansa ya fad'i kafin ya d'an murmusa yace " Tana ciki, let me call her..
"A'ah kaji ma an shiga sallah, mu k'arasa masallaci dai first,... A baranda had'u da Annah suka sanar da ita zasu mosque, parlorn ta wuce yanda Zulaihat ke zaune sai k'are ma gidan kallo take, tana ganin Annah ta mik'e ta amshi tray d'in da fari'ar ta, haka kurum Annah taji Zulaihat bata kwanta mata ba,..
"Zulaihat kuwa sai k'ok'arin jan Annah da hira take, Duk ta gundura da ita, saida Annah tace mata bari taje sallah snn itama ta shiga ciki wajen Zubaidah tayi, kafin ta sami sauk'in surutun Zulaihat, sam yarinyar bata mata kama da mai kamun kai ba, shi kuwa Shattima daga ganinsa kaga yaron arziki.. Da wnn tunani ta isa bakin randa yanda butocinta ke jere tayi alwala, a baranda ta shimfida abin sallan ta...
"Zubaidah na zaune tana duba books d'inta don hutun sallah take, Zulaihat ta shigo d'akin da sallama, amsa mata tayi gamida juyowa gaba d'aya...
"Gaban Zulaihat yayi mugun fad'i da ganin Zubaidah, tabbas dole Umar ya haukace akanta. Murmushi ta sakar mata gamida k'arasawa tayi hugging nata without any hesitation, Hello Zubaidah it's a pleasure to meet you, na jima ina son had'uwa dake, ni matar da abokin mijinki Shattima zai Aura ne, inajin yanda Jalal ke fad'in irin soyayyar da yake maki, so I've been dreaming of meeting you in person..
"Cike da mamaki kawai Zubaidah ke dubanta, d'an murmushi yak'e tayi kafin tace " Pleased to meet you too.
"Kallon juna sukai na d'an mintoci kafin Zulaihat ta kuma rik'o hannunta tace" oh by the way sunana Zulaihat nd ina karatu a nan jami'ar Abuja snn a gidan Aunty na nake zaune,.. Hira take kan jan Zubaidah dashi, daga bisani Zubaidah tace " Zakiyi sallah ne??
"Girgiza kai Zulaihat tayi dukda ba hutun sallan take ba kafin tace " No I'm off. Muje parlor gasu sun dawo daga sallahn, ba don Zubaidah taso ba haka tabi bayan Zulaihat suka fito parlorn, gaisawa da Shattima Zubaidah tayi sai janta da hira yake yanama Jalal tsiya, um da um um sai smile, iyakacin abunda Zubaidah ke fad'i knn a hiran nasu..
"Tsaf Zulaihat tana lura daeyanayin Jalal da Zubaidah, tabbas tsakaninsu babu jituwa,...
"Sun d'an jima suna hira kafin suka mik'e don tafiya, Zulaihay harda rik'o hannun Zubaidah alamun itama tai masu rakiya...
"Zaune suka tadda Annah saman darduma tana lazimi sukai mata sallama, tai masu godiya da fatan Allah kiyaye hanya...
"Jalal da Shattima suka nufi mota sanda Shattima ya juyo yayi sallama ma Zubaidah..
"Zulaihat ta rik'o hannun Zubaidah kana tace "Toh Zubaidah naji Dad'in kasancewa dake sosai, Allah sa k'awancenmu ya d'aure, d'an murmushi nan dai kawai ta kuma yi kafin tace " Na gode nima, sai anjima Allah ya tsare hanya...
"Da sauri ta juya zata shige gida, muryar Zulaihat ta tsinkaya tana fad'in" Kinga zamu rabu bamuyi exchanging phone no ba..
"D'an murmushi yak'e Zubaidah tayi kafin tace " Ban haddace no d'ina ba, kar ki damu zamu sake had'uwa ai...
"No ai yafi muke gaisawa Zulaihat ta fad'i sanda take zura hannu cikin jakarta, paper da Biro ta ciro kafin ta rubutawa Zubaidah No d'inta tace " Gashi contact d'ina idan kin shiga sai kiyi saving, karb'a Zubaidah tayi tana murmushi, Zulaihat ta kuma hugging d'inta kafin sukayi sallama.....
" Ganin Jalal na nufowa yasata saurin soma tafiya cikin sauri...
***************
"Mumsy ta kuma jefawa Kausar dake kan zuban hawaye wani mugun kallo kafin tace " How could you be so stupid, Da iliminki da hankalinki zakyi abu makamancin haka, ta juyo ga Asmah itama mugun kallon ta watsa mata kafin tace " And you know about it, from the very start baki fad'a mun ba, you all are stupid,..
"Mumsy I never thought it would turn out to be serious, shiyasa ban fad'a maku ba, Asmah ta fad'i a hankali...
"Gajeren tsaki Mumsy tayi kafin taci gaba da fad'in" I don't know what's wrong with you Kausar, ta yaya zaki yarda da zancen wata ki ajiye na mijinki, for Allah's sake....
"Mumsy I didn't mean it, believe me so nake na tsira da mutunci na shiyasa, I know you won't want me to end up with a rapist, a criminal....
"Jawota Mumsy tayi ta rungume kafin tace " Of course my baby amma ba haka ake yi, kinyi bincike kinga gaskiya, shi kansa mai laifin ya fad'a maki gaskiya, meyasa daga baya zata maki waya ranar aurenki ki amince, da tanada gaskiya data fada maki tun da wuri... Oya tashi muje ki shiga kiga mijinki ya farka...
"Rik'o hannunta tayi suka nufo d'akin da Salim yake, a k'ofar d'akin suka had'u da Mummy, Kausar ta sadda Kai k'asa cike da kunyar abinda tayi was Mommy, a hankali ta soma fad'in
"Mummy I'm sorry...... Rungumota mummy tayi kafin tace " It's okay daughter, we all understand you, if there's anyone who's responsible to wnn munafukar yarinyar ce marassa godiyar Allah.... Ki kwantar da hankalinki kinji your husband will soon get well ku tattara ku koma gidanku..... Murmushi sukayi gaba d'aya suka nufi cikin d'akin yanda suka tadda Pappy da Daddy har lokacin fad'a suke wa Salim he shouldn't be stupid, abinda yayi hauka ne ba soyayya ba cewan Pappy, ransa b'ace ya nufi k'ofa, mugun kallo ya watsa wa Kausar kafin ya wuce...
"Daddy kuwa kai kace iyakar gaskiyarsa knn sai sababi yake yana nuna rashin jin Dad'insa har saida Mumsy tasa baki yayi considering situation d'in Salim kafin yayi shiru.
"Ficewa yayi yabi bayan Alh Tahir, jinjina lamarin suka kuma yi a wajen ma kafin Mumsy ta fito suka wuce.
"Suna wucewa Alh Kasim drebansa ya kira yace Company suka nufa..
"Wayarsa ya ciro ya shiga neman layin Barr Munir, bugu biyu ya d'aga kana yace " Me ake ciki, ya amince ya amshi kud'in ko kuwa??
"Daga d'aya b'angaren Barr yace " He's strong head iina gaya maka, he refused to cooperate,.
"Fuzar da iska Daddy yayi yana fad'in" Damn it Damn it, ka gane he must negotiate with us for his own good, yayi wata murmushi kafin yace " No one messes with the Dasuki's, idan bai amince da buk"atarmu zanmu b'atar dashi kaman yanda muka b'adda sauran...... Munir do what ever you can to make him cooperate, If Alh Tahir learn the truth we are done, so ka fad'a masa kud'in da ko a mafarki bai tab'a jin irinsu ba, gani nan am on my way there, ...
"Murmushi Barr yayi kafin yace " Kafi gaban haka how's my nephew, is he out of the comer?
"He's much better, Ya fad'i a taik'ace kana ya katse wayar....
"Barr ya shiga store d'in da aka d'aure Umar, Faisal dasu James suna tsaitsaye da bindigogi, ya dubi Umar dake faman huci ya durk'usa gabansa kafin yace " Ka gode wa Allah my nephew is still alive, da ya mutu daka bak'unci lahira .....
"Yana huci yake fad'in" it's what he deserves, jerk like him Ya cancamci mutuwar wulak'anci....
"Barr yayi murmushi kafin yace da Faisal ya mik'o masa briefcase d'in,
"right away sir, Faisal ya fad'i gamida mik'a masa,
"Bud'e jakar Barr yayi, kud'i in dollars suka bayyana, ya mik'asu gaban Umar kafin yace " Idan kana mafarkin zama mai arziki dama ta sameka, remember they say opportunity comes but once, think about it idan baka karb'a ba you will be the great looser, coz you'll never be free, rayuwarka na cikin had'ari coz you are now involved in the mess, and lastly remember you lost the girl alresdy, so think wisely, bara na baka 5mins kayi tunani, daga haka ya fice yana mayaudarin murmushi.....
Sameena 👌🏾
[1/23, 22:20] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
43
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum... 📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
" Shiru yayi gamida k'ura ma kud'in gabansa idanu, zuciuarsa na masa sogi, he wants to be rich, he wants to take his revenge, but ta yaya zai iya ja da wad'an nan mutanen, they are powerful and loaded,
"Zan karb'a kud'insu idanyaso daga baya sai na yak'e su, by that time na k'wato Zubaidah daga hannun wancan Jerk d'in...
"A hankali yasa bayan hannunsa ya share hawayen da ya fito masa....
"Driver d'insa na gama parking ya shige cikin company d'in, daidai lokacin da Labib da Tariq suka iso...
"Kai tsaye ya nufi yanda suke, Barr ya soma hangowa sai mayaudarin murmushin da ya saba yake..
"Murmushi Daddy ma ya soma kafin yace " I guess everything went perfect...
"Barr ya mik'a wa Daddy hannu sukayi handshake kafin yace " Haba rankashidade wa ya isa yayi rejecting offer d'inka, wama ya isa yaja da kai, we're done with the boy....
"Murmushi Daddy ya kuma yi daidai sanda Umar ya fito rik'e da jakar kud'in...
"Banda mugun kallon da yake watsa masu babu abinda yake.
"Daddy ya murmusa kafin ya k'arasa yana bubbuga kafad'un Umar yake fad'in " Kayi tunani yaro, now you may leave, and get lost completely. .
"Cikin zuciyarsa yake furta I'm not done with you, I'll surely come back to you, all of you must pay, a fili kuwa baice komai ba .... Daga haka ya nufi k'ofa, caraf suka kusa yin karo da Labib da Tariq...
"Wani mugun kallo yabisu dashi su duka biyu wanda yasa su shan jinin jikinsu kafin yayi ficewarsa cikin sauri kaman mai shirin kifawa k"asa...
"Labib na jin k'aran tada mota ya lek'a ta window da sauri ya furta "What!!!! No way he's going with my car, juyowa yayi da sauri alamun zai sauk'a k"asa, Daddy yayi saurin rik"o arms d'insa yana girgiza kai yake fad'in" Um'um don't be stupid, let him go with it, it's just a car, ...
"Rai b'ace Labib ke fad'in " But Uncle this is my Fav Ride for crying out loud,...
"Meye mota, kaje Dasuki Motors ka zab'i irinta, amma wann kam ka barsa as far as babu wani important stuff d'inka a ciki, besides we finally got rid of him....
"Shiru kawai Labib yayi yana hangen window, yanaji yana gani Umar ya fincike Motar da k'arfin gaske ya fice daga company d'in.....
"Tana zaune tana tunaninsa, tabbas yau taga Zubaidahn Umar, kai dole ma ya d'imaice da rashinta,...
"Runtse idanu tayi tana rungume da pillow d'in da ya kwana akai sanda yazo, soyayyarsa na cika zuciuarta, tunanin Shattima ya fad'o mata, she's only using him to get close to Zubaidah, if he knows her real intention on him, he will hate her for good..
"A hankali ta sauk'e ajiyan zuciya gamida furta " I'm sorry,....!!!!
"Kaman daga sama taji ana knocking da k'arfin gaske kaman za'a cire mata k'ofa, tsuka tayi kafin ta soma fad'in" Ina zuwa dalla, ita kadai take zancen zuci sanda ta nufi d'aki d'auko riga don daga ita sai pant da bra take zaune... "Yanzu haka Imam ne, ko wann shegiyar matar me gidan hayan, ni bansan meyasa Tariq bai biyata kud'inta ba har yanzu..... Da haka ta isa k'ofa... "Sandarewa tayi sanda ta gansa, idanunsa jazur, daga ganinsa kasan ba lafiya ba...
"A hankali ta matsa gefe kafin ta sakar masa murmushi tana mai binsa da kallon mamaki tace " Bismillah.... A maimakon ya shige sai rungumeta yayi tsam cikin jikinsa,
"Zulaihat ta razana da lamarin nasa, bata gama shan mamaki ba saida taji d'umin hawayensa a kafad'unta...
"Cikin muryar kuka yake fad'in" I lost her, na rasata har abada, she's with him right now, her so called husband, sun rabani da ita, sun rabani da farin cikin raguwata....
"Dukda kishin da ya tokari Zulaihat bai hanata rungemsa very tied cikin jikinta ba, lallashinsa take kanyi at the same time tana seducing d'insa with her ways, ...
"Zuciyarsa sai Dad'a tunzurasa take kan aiwatar da abinda Zulaihat ke masa, duk ajiye kansa da killace kansa da yayiwa Zubaidah ta watsar tana chan tare da waninsa, da wann mummumanar tunani da shed'an ya haifar masa ya soma biye mata... a haka ya ringa biyeta har basu sanda suka raba jikkunansu da suturunsu ba, da jan hankali da k'issa tai masu masauk"i cikin d'akinta... "Wa iyyazu billah.... "
*********
"Fuskarsa take kan shafawa hawaye tab idanunta, a hankali ta yunk'ura zata mik'e taji ya rik'o hannunta, ...
"Da sauri tasa hannu ta share hawayen kafin tace " I woke you up ko, ...
"Girgiza kai yayi yana murmushi kafin ya rik'o hannunta yayi kissing...
"Cikin muryar kuka Kausar ke fad'in" You're so stupid, How could you came up with that, what if ka mutu, Me zaka ce kace wa mahallicin mu, you know you're so freaking crazy.. Ta k'arashe maganar tana share hawayenta...
"Murmushi ya kuma sakar mata kafin ya d'aura hannu maras canola a Face d'inta kana yace " Yeah I'm crazy about you sweetheart, banga amfanin rayuwa without you at my side ba, I did it out of love Sweetheart, I couldn't believe you don't trust me. Kinfi yarda da zancen wata mak'aryaciya akaina... Yana maganar in a furious tune,.....
"Da sauri tasa hannu ta rufe masa baki kafin tace " Dr yace banda yawan surutu zaka fama ciwonka, ...
"Murmushi ya sakar mata kafin yace " I love you....
"Murmushin itama ta masa a hanakali ta furta "I'm sorry....
"Turo baki yayi yace " Ban yarda ba, sai kin min kiss..
"D'an zaro ido tayi tace " A asibitin, gyad'a mata kai yayi without any hesitation, d'an rausayar da idanu tayi sanda ya mik'e ya jinginu da pillow, kan tayi wani aune taji ya pulling d'inta ya soma kissing d'inta ba tareda la'akari da ciwon dakejikinsa ba, knocking d'in da akayi ne yasa sa sassauta mata rik'on, ta d'an ja baya tana bada izinin a shigo,
"Labib da Tariq ne, Labib yabi bakin Salim da kallo sanda Tariq ke gaisawa da Kausar, murmushi yayi ya k'arasa yana kashe masa idanu...
"Take Salim yaji baiji Dad'in shigowarsu ba, don kuwa duk yanda matarsa take baison ganin Labib a wajen, don yasan waye Labib....
**********
"Zulaihat ranan ta kwana cikin farin ciki, burinta ya cika, ta sami abunda ta jima tana kwad'ayi, shafa bayansa ta ringa yi yana bacci, idanunta ya sauk'a kan d'an makullin mota, da mamaki take bin keys d'in da kallo, a iya saninta bashida mota toh a ina ya samo mota, kai bari dai ta mik'e ta lek'a waje, ai kuwa nan ta hangi hancin mota, " Bak'ar Mercedes Benz GLK 350, asalin new grand, mamaki ya cika Zulaihat, wann ba motan k'anan mutane bane toh a ina ya samu.???....
"Kallonsa ta kuma yi yanda yake baccinsa hankali kwance, sauk'e ajiyan zuciya tayi kafin ta mik'e ta nufi bathroom, tana shigewa ya mik'e don dama idanunsa biyu, kayansa ya saka cikin sauri...
"Zulaihat na cikin wanka taji k'aran tada mota... A guje ta fito daga bayin saidai kafin ta fito waje sai k'uran motarsa ta gani, durk'usawa tayi a wajen gamida fashewa da wani irin kuka.....
"Takaicin kansa ya ishesa, duk yama rasa wanne zaiyi, Hotel ya wuce ya nemi d'aki ya kama, haka kurum yaji zuciyarsa ta cika da k'unci.....
************
"Satin Salim guda a asibiti aka sallamesa, yanzu kam sun d'inke sosai da Kausar d'insa, ita take jinyarsa cike da kulawa, Mummy kaman ta zuba ruwa a k'asa tasha sabida farin ciki, ranar da ya cika kwana uku da sallama ya nace saidai su tare gidansu, a gaban kowa yake nuna tsananin buk'atar sa ga matar sa, Kausar kuwa duk a cikin so ta d'auki haka..
"Mummy da kanta ta taya Kausar suka shirya kayan Salim, da daddare ta kaisu har gidansu dake asokoro, gida da ya amsa sunansa gida, tsayuwa fad'in tsarin gidan b'ata lokaci ne, a wann dare Salim Ya gurza amaryarsa, suka ci soyayyarsu,... Yayinda Labib yayi kusan kwana zaune yana bak'in cikin hakan.....
"A b'angaren Zubaidah fah, makaranta ya zmar da ita busy, snn her therapy classes is going well with Dr Khaleesat, wani lokacin tare da Jalal suke therapy d'in, wani lokaci ita kad'ai wani lokaci Jalal shi kad'ai, rayuwa ta soma tafiya masu normal, a halin yanzu Zubaidah ta soma sakin jiki da Jalal, basu wani hiran soyayya saidai tana jin she can trust him even though bata yafe masa ba har rana mai kaman ta yau, tana son watarana ta yafe masa, amma bata jin zata iya yau class d'in da tayi da Dr Khaleesat tambayar data mata knn shin yaushe ne take jin zata iya yafewa Jalal, amsar da ta kasa bata knn wanda hakan yasa Dr ta maida mata shi Assignment.
"Shi kuwa Jalal assignment d'in da Dr ta bashi shine "Shin yana son Zubaidah" shima ya kawo mata amsar tambayar ta in their next class....
*Manage this habibaties, kwana biyu zakuna jina ba kullum ba due to some wasu 'yan lalura, but as far as komai ya zama normal zakuna jina as in kullum kamar yanda aka saba, love you all..... Stay tuned guys..... 😜😻💋❤*
[1/23, 22:21] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
44
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Zaune yake bisa coach ya k'ure Kid'a sai ka rantse club ne, hannunsa rik'e da kwalban whiskey, lokaci zuwa lokaci yake sauk'e ajiyan zuciya.... Mom taci gaba da buga k'ofar da iya k'arfinta...
"Da sauri ya mik'e yayi saurin b'oye whiskey d'in kafin ya nufi k'ofa yana k'ok'arin kintsa kansa...
"Kallo ta bisa dashi a dak'ile kafin tace " Would you turn that thing down, ta fad'i tana nuni da kayan kallonsa,..
"Ko kad'an baiso su had'a ido don baiso ta gane halin da yake ciki...
"D'an murmushi yayi gamida bud'e duka hannayensa biyu kafin yace " Okay... Okay... Fine.
"Kallo ta bisa dashi tana karantar sa , a hankali ta shigo cikin parlon nasa, nan taji warin barasa ya cika parlorn, toshe hancinta tayi da hannu tana binsa da kallo, kafad'unsa ta dafa kafin tace " Are you drinking again...?
"D'an buge hannunta yayi kafin ya zauna gijif saman sofa...
"A tsawace ta kuma cewa "Tambayarka nake Tariq uwar me kake sha???
"D'ago rinanun idanunsa yayi yana kllon Mom kafin yace " Would you please give me break, for crying out loud Mom I'm dying if depression, Mom nayi nadaman laifin da muka aikata, nayi danasanin zuwa engagement d'in Salim, Mom babu hali na kwanta sai nayi mafarkin yarinyar nan either Tana chasing d'ina or tana wani irin yanayi, .. Ya d'anja fasali idanunsa suka kad'a sukayi ja kafin yaci gaba da fad'in" Mom I couldn't have peace of mind ever since we raped that girl, Mom I don't know but I'm not my self anymore.... Ya k'arashe maganar yana cusa duka hannayensa biyu cikin gashinsa...
"Jiki a sanyaye Mom ta zauna gefensa, rungumosa tayi kan k'irjinta kafin ta soma fad'in" It's okay Tariq, that girl is already married now, she's living a new life, ka cire komai a ranka kaci gaba da rayuwarka kaman normal...
"D'agowa yayi yana dubanta kafin yace " But how mom, how would I suppose to do that, you know what kills me the most, Jalal is completely innocent mom, yet we put the blame on him, Mom we're so selfish... Ta yaya zamuyi ma abokinmu haka, among all of us he's different, he's not a coward like us... Ya k'arashe maganar yana mik'ewa tsaye...
"Kallo mom ta bisa dashi kafin tace " Ina zaka je..?
"Ba tare da Ya kalleta ba yace " I'm sorry mom but..... But I think I'm gonna confess, I'll confess everything.....
"Ai baika aya ba mom ta fizgosa ta zaunar tana huci ta mik'e tsaye tana binsa da mugun kallo kafin tace " Are you going insane, meke damunka Tariq, so kake ka k'arashe rayuwarka a gidan kasu, kar na k'ara jin maganar nan a bakinka idan ba haka ba sai na maka baki kaga sai kayi zaman gidan kasu da dalili....
"D'an kallonta yayi kafin yace " Mom I can't go on like this, I ruined my life since that night, snn mom nayi rashin aboki kaman Jalal, I wish zamu koma kaman yanda muke da, I wish things would turn out the way it was before.... Ya k'arashe maganar yana rik'e da pic d'insu mai su hud'u fuskokinsu cike da Annuri...
"Sauk'e ajiyan zuciya tayi kafin ta rik'o hannunsa cikin nata tace " Son always remember that we're here for you, me and your Dad, Tariq bazai yuyu ka fad'i gaskiya ba, you will endup in jell, and we can't let you do that, coz you're our only child, kai kad'aine d'anmu, pls Son don't do something stupid, you need to remain steady, don't let that get over you okay....
"Kallon Mom yayi idanunta tab k'walla a hankali ya rungumeta shima hawayen ne suka zuba masa....
**********
"Usman Ya dubesa a karo na biyu gaba d'aya ba sai ance maka duniyar tunani ya tafi ba, d'an bubbuga kafad'unsa Usman yayi kafin yace " What's up with you, tunda kazo yau gaba d'aya cikin tunani kake..
"D'an murmushi Jalal yayi kafin yace" I'm that obvious?...
"Zama Usman yayi gefensa kana yace " Clearly, da gani wani abu na damunka...
"Murmushi yayi a karo na biyu kafin ya kira yaron gefensu ya basa wasu kayan aiki yace Ya kai ma Emeka... Daga haka ya soma k'ok'arin cire kayan aikinsa...
"Kallonsa Usman yayi kafin yace " Kai wllhi baka barin wajen nan sai ka fad'a mun meke damunka ya k'arashe maganar yana rik'o rigar Jalal..
"D'an dariya Jalal yayi kafin yace " You so stubborn you know.. Okay fine let go of my shirt zan fad'a maka...
"Sake masa riga Usman yayi yana murmushi kafin yace " Ai maganin miskilai irinku sai mu.. Oya go ahead and tell me, ina saurarenka..
"Tab'e baki Jalal yayi kafin yace " Tambayarka zanyi idan ka sani ka bani amsa.
"Ina dai saurarenka, cewar Usman da Ya kafe sa da idanu...
"Pls yaya ne idan mutum na son wani zai gane, okay yaya ake so, Oh my.. Kai I don't know how to put it, may be you get me...?
"Baki sake Usman ke dubansa, dariya ya fashe dashi harda kama ciki.
"Mugun kallo kawai Jalal ke watsa masa kafin yace " You such a jerk, gajeren tsaki yayi gamida mik'ewa tsaye snn yace idan ka gama dariyar ni na tafi na fad'a maka dama yau da wuri zan tashi sabida inada wajen zuwa...
"Hannunsa Usman Ya rik'o still laughing kafin yace " Yi hak'uri Mr miskilanci, kai ni banma san wani sahu zan saka ka ba, I can't believe you asking me that, toh wai abokiyar zama zakayi ma matarka ne kake tambaya ko kuwa har yau baka yarda kana son matar taka bane...
"D'an kallonsa yayi da gefen idanu kafin yayi murmushi da gefen bakinsa yace " You know me, when it comes to women, a da kasanni womanizer ne I won't deny it, they gave me pleasure but only on bed... Nothing more nothing less, kai in fact ni amfaninsu a wajena ma knn until I met Zubaidah... Shiru ya d'anyi gamida k'ura ma tayan mota idanu kafin yaci gaba da fad'in" But Zubaidah.... she's different,....Snn labarin aurenmu ya banbanta dana kowa, maybe it's not a happy marriage, amma ina son ganinta cikin farin ciki dawamammiya.... our story is quite different, you might not understand what I'm telling you right now, sabida baka san labarin ba, labarinmu akwai sark'ak'iya da tarin jarabawa na rayuwa, everything is complicated,..... So please ka fad'a min abubuwan da mutum keji ya gane he's in love...
"Kallonsa Usman yayi cikeda Al'ajabi da tausayawa, yanayin Jalal yasa jikinsa yin sanyi, d'an murmushi yayi kafin yace " From the looks you got in your face kana sonta, snn daga maganganunka kana sonta, snn daga gani something serious is going on between you two, And destiny brought you together. Koma dai menene don't ever let her go Jalal, coz she's the love of your life,.....
"Kallonsa Jalal yayi kafin yace " What if she's in love with someone else, what if she hates me for good, kana tunanin inada wani ghost of chance...? Ya fad'i yana kallon Usman idonunsa cike da damuwa...
"Dafasa Usman yayi kafin yace " Don't ever give up on her, no matter the hadships and the challenges might come your way...... Kallon juna sukayi gamida sakar ma juna murmushi......
"K'arfe shad'aya da wasu mintoci Ya nufi gida...
"Wanka yayi ya shirya tsaf kafin ya nufi parlorn Annah, sun jima suna fira kafin ya fice.....
"Zaune take k'asar bishiyar data saba jiransa, yauce ranar karb'an assignment d'in Dr Khaleesat gashi bata jin ta samo wann amsar, runtse idanunta tayi tana tuno abubuwan da suka faru a rayuwarta, ko babu komai Jalal yanada matsayi babba a wajenta koda bata yafe masa ba, tunanin Umar ya fad'o mata, tabbas baya sonta yanzu, tabbas ya gogeta a babin rayuwarsa, shin ita kuma fah?? Ta daina sonshi ne ko kuwa.... Bata kai ga samo amsa ba sai jin daddad'an muryarsa tayi yana mata sallama... Da sauri ta d'ago tana dubansa, yana sanye cikin jampa ruwan k'asa harda hula, yayi matuk'ar yin kyau,.... Sosai ta shafa'a da kallonsa.... Har saida ya k'araso gamida karkad'a d'an yatsan sa saman Face d'inta yayi gyaran murya kafin yace " Am I that handsome that some couldn't stop starring at me huh...? Ya k'arashe tensely.....
"Da sauri ta zaro ido gamida furta "What, Allah sawak'eni, na gaji da jira ne, you kept me waiting, while kasan Dr tana jiranmu....
"D'aga giransa yayi kafin yace " I'm sorry, so tell me, have you done your assignment...?
"Hararansa tayi kafin tace " Ba damuwanka bane, ta k'arashe maganar tana mik'ewa tsaye sanda ta soma tafiya.
"Rik'o hannunta yayi gamida k'ura mata ido, itama kallonsa take, a hankali ta sunkuyar da idanunta.
"Murya can k'asa yace " Will you forgive me...?
Kallonsa tayi gamida gano tsantsanr gaskiya a k'wayar idanunsa kafin ta sadda kanta k'asa....
"Har ya cire ran bazatayi magana ba ya tsinkayo muryarta tana fad'in" JALAL.... For the first time data kira sunansa snn taci gaba da fad'in" I really want to forgive you one day, ina son na yafe maka watarana, but I don't know how and when, all I can say now is that I trust you, Na yarda da Kai, snn na yarda bazaka cutar dani ba...... Sandarewa kawai yayi yana saurarenta.
"A hankali ta d'ago kanta tana dubansa snn tace " Ka mun alk'awari ka rabu da wad'ancan abokan naka har abada...
"Matse hannayenta tsam yayi kafin yace " You don't have remind me of that, they are already in the past, Na rabu dasu har abada you have my word.... .... Jin d'igan hawayen ta saman hannunsa yasa sa yin shiru....
"Tausayinta da soyayyarta ya cika zuciyarta, baisan sanda yayi hugging nata very tied ba, a hankali yake furta " I'll never let you down, I'll never leave your side, I'll always be here for you til my very last breath....
"Gaba d'aya ta mance cikin k'irjinsa take, k'aran wucewan motoci ne ya dawo da hankulansu.... Cikin sauri ta turesa daga rik'on da ya mata.. Kasa d'ago kai su had'a idanu tayi ba tareda ta dubesa ba ta soma tafiya...
"D'an murmushi yayi da gefen bakinsa gamida karkad'a kai kafin yabi bayanta......
****************
Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin jin Dad'i a hankali suke sabawa da juna, da taimakon Allah da taimakon Dr Khaleesat, da kuma mutanen da suke tare dasu....
"A b'angaren Tariq abun yayi affecting d'insa sosai, ya koma tamkar bashi ba, wayarsa ya ciro yayi dialing lambar Jalal..
"Da mugun mamaki Jalal ke bin wayarsa da kallo, d'an tsaki yayi gamida yin rejecting don alk'awari yayiwa Zubaidah babu abinda zai kuma had'asa dasu , saida ya kira sau kusan biyar kafin Usman yace " Ka d'aga pls, ka sauraresa kaji me zai fad'a maka...
"D'an fuzar da iska yayi kafin ya d'aga a dak'ile ya soma fad'in" What is it again...
"Daga d'aya b'angaren Tariq yace " Jalal pls let's meet in person, let's talk about it for the last time, I promise I won't bother you again,...
"Hold on,.... Jalal Ya dakatar dashi kafin yaci gaba da fad'in" Bana buk"atan jin komai from either of you, stay out my life pls, and don't you dare call me again.......
"Da sauri Tariq yace " I beg of you don't hang up the phone, for the sake of old times.... Jalal dan Allah kayi hak'uri mu had'u later, it might be our last goodbye, I don't I can continue living here, I'm leaving to abroad, dan Allah Friend let's meet for the last time......
"Sauk'e ajiyan Zuciya Jalal yayi kafin yace " Okay I'll see what I can do, idan na tashi a aiki zan kiraka na fad'a maka location d'ina sai mu had'u..... Daga haka yayi hanging....
"Tana nan zaune yanda ta saba jiransa shiru shiru bai iso ba, d'an duba agogon hannunta tayi taga Time ya tafi sosai, d'an sauk'e ajiyan zuciya tayi kafin tace " K'ila bai tashi a aiki bane.. Maybe he has alot to finish. Mik'ewa tayi ta nufi bakin titi ta tare a daidaita ta shiga, gida ta nufa kasancewar yau babu zuwa gidan Dr Khaleesat....
"Suna tafe cikin adaidaita jefi jefi tana tunaninsa, batasan daga yanda ta tsinto murmushi saman fuskarta ba, haka kurum taji babu Dad'I yau da baizo d'aukanta ba, tunda ta soma zuwa sch bai tab'a fashin kawota ko zuwa d'aukanta ba...... Cak ta daina murmushi gabanta ya shiga lugude sanda ta hangesa da d'aya daga cikin fuskokin datafi tsana, dukansu suna murmushi suna hugging juna....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:21] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
45
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Tariq yayi hugging Jalal kana yace " I'm leaving soon Bro, thanks for everything, na gode da duk karamcin da ka mana, I know I owed you alot...
"Mik'a masa hannu Jalal yayi sukayi handshake kafin yace " Allah Ya kiyaye hanya yasa tafiyarka shine alkhairi...
"Gyad'a kansa yayi kafin yace " Ameen, goodbye Bro.
"Kallonsa Jalal ma yayi kafin yace goodbye, daga haka Jalal ya soma tafiya don dama sauri yake yaje ya fetching Zubaidah daga makaranta.
"K'arasowa gabansa Tariq yayi da motar sa yanda yake tsaye bakin kwalta kafin yace " Let me give you a ride...
"D'an girgiza kai kawai Jalal yayi kafin yace " A'a ka barshi kawai, na gode and don't insist pls..
"Gyad'a kansa Tariq yayi kafin yace " Okay goodbye again... D'aga ma juna hannu sukayi kafin Tariq yaja motarsa ya bar wajen...
"Agogon hannunsa ya kuma dubawa gamida yin gajeren tsaki, yasan ta gaji da jiransa, hannu yasa da sauri ya tari mai mashin d'in da ya iso gabansa, cikin sauri ya d'ale yana mar bayani....
"Malam ajiye ni a nan, ta fad'i cikin rawar murya, Mai adaidaita ya juyo ya dubeta kana yace " Hajiya ai ba nan kikayi zan kawo ki ba ko kin fasa ne...
"Gyad'a kanta tayi tace " Na fasa ajiyeni a nan.
"Mai adaidaita yayi yanda tace...
"K'asar wata bishiya ta samu ta zauna, abunda ta gani ya kasa b'ace mata a idanunta, who would she trust, so all these while Jalal is been lying to her. Meyasa ya bari saida ta aminta dashi, a tunaninta bazai cutar da ita ba ashe duk k'arya yake mata, all men are the same,.... A hankali ta goge hawayen da suka zubo mata, a fili take furta " I was such a daft da har na yarda dashi, idan da na aminta baiyi raping d'ina ba, yanzu kam na Dad'a yarda yayi, harda shi, maybe shine yin k'arshe, dukansu munafukai ne mak'iyana, I shouldn't have believed him. He's also lying.... I won't go back there, bazan koma ba, bazan ci gaba da zama dashi ba,..... Kuka mai k'arfi ya kufce mata saida tayi mai isanta kafin ta d'ago kanta kaman wacce aka zabura, tunani ta soma yi, ina zanje wa na sani a garin nan....
"Take tunanin Zulaihat ya fad'o mata, ita kad'ai ta sani a garin nan, da sauri tasa hannu cikin jakar makarantar ta don dama ciki ta ajiye lambar da Zulaihat ta bata...
"Gefe da ita business center ne nan ta k'arasa ta biya kud'i ta soma kira....
"Zulaihat was very surprised jin Zubaidah ce, jin tana kuka yasa hankalin Zulaihat tashi, cikin sauri ta tambayeta location d'inta. Nan ta mik'a ma masu wayar suka mata kwatance, Zulaihat ta ringa kwantar mata da hankali snn tace gata nan zuwa right away....
"Lambar Imam Zulaihat ta kira Allah yasa yana kusa nan suka wuce d'auko Zubaidah.....
"Neman duniya yayi bai sameta ba, haka kurum yaji gabansa na mugun fad'uwa, what if she get lost tunda ba sanin gari tayi ba, kaman zararre ya soma girgiza kai shi kad'ai yana furta No no ta isa gida safely insha Allah, a sittin ya kuma tare mashin ya nufi gida.....
"Tunda suka shigo layin Zubaidah ta kasa sakewa, bataga alamun mutunci a wajen ba, a iya saninta Zulaihat tace mata she's leaving with her Aunt, bata ga alaman Auntyn Zulaihat ba har suka shige ciki.... Zama tayi dirshan saman sofa a parlor, sai k'are ma yanayin gidan kallo take cike da tsoro.
"Fitowa Zulaihat tayi wajen Imam while Zubaidah na zaune a parlor..
"Kannare idanu Imam yayi kafin yace " Wacece wancan yarinyar gaskiya tayi min, sabuwar shiga hark'a ne, kafin ki had'ata da wani Alh gaskiya nidai tayi min, ke da aure ma ni zan nemeta... " Ya k'arashe maganar yana wani kashe ido...
"Baki a tab'e kurum Zulaihat ke dubansa kafin tace "Kai dalla jacan, kai har wani namiji ne, ni dalla ba wann ba, kaga yarinyar nan babu ruwanka da ita , zan fad'a mata kai k'anina ne sabida yanayin shigarka gidan nan babu control...
"Dariya Imam yayi yana kad'a key din tasi d'insa kafin yace " Ah haba k'ani saidai yaya kema kinsan na fiki...
"Dalla ni yimin shiru ka gane taimaka min zakayi, kaga bani da cash account d'ina ma yayi k'waras bansan meke damun Tariq ba kwana biyu, nasan dai cikin satin nan zai turo min monthly allowance d'ina, so pls idan da kud'i a jikinka ka sayo min dangin su macaroni pls kaji....
"Zaiyi magana ta tura kansa cikin mota tana fad'in" tafi tafi banson complain abeg....
"Dariya kurum yayi ya shige mota kafin yace " Zan had'a cikin balance d'inki..
"Eh dai jeka ta fad'i tana rufe k"ofar parlorn....
"Kallonta Zubaidah tayi sanda ta shigo parlorn, Zulaihat ta sakar mata murmushi kafin tace "Feel at home ki Saki jikinki. Ta mik'e ta kawo mata drink..
"Zubaidah dai bata sake ba, ta d'an kurb'i ruwan kafin tace " Kince min da Aunty d'inki kike zama, where is she..?
"Gaban Zulaihat ya bada dammm, tama mance tayi wann k'aryar.. Murmushi yak'e tayi kafin tace " Oh aww, ai Aunty ba Me yawan zama bane, ta tafi wani seminar a Jos, yanzu haka ma nida wancan k'anin nawa da ya kawo mu ta bari a gidan...... "Zubaidah ta zaro ido waje kana tace "Oh you mean shima a nan gidan yake kwana..?
"Da sauri Zulaihat ta girgiza kai kafin tace " No a campus yake zama, yakan d'an zo mana weekend dai amma yanzu tunda kinzo I'll ask him to leave..
"Jim tayi gamida sakin murmushi a hankali, Zulaihat dai sai karantar ta take, tabbas akwai yaranta tsundum a lamarin Zubaidah amma me zaisa ka baro kowa naka ka taho wajen k"awar da rana guda tak kuka tab'a had'uwa... Mik'ewa tayi ta shige d'aki tana fad'in kisha lemo fah yanzu Imam zai kawo aike na d'aura mana abinci..
"Murmushi kawai Zubaidah tayi gamida gyad'a kai....
"Tunda ta shige d'aki take neman layin Umar bai d'aga ba, k'arshs ta hak'ura tasan ba lallai bane ya d'aga don tunda yasa k'afa ya fice daga gidan bai kuma kiranta ba... Sauk'e ajiyan zuciya tayi ta tsunduma kogin tunanin ko ta masa text ne....
*************
"Annah ya kamata ace ta dawo by now, I can't loose her, what if wani abu ya sameta, I'll never forgive my self sabida laifina ne banje na d'auketa ba, ya k'arashe maganar yana hargitsa gashin kansa........ Cak ya tsaya sakamakon jiyo sautin kukan Hamma Habibu da sukayi... Cikin harshen fillanci yake kan sunbato yana ambaton Zubaidah k'anwarsa....
"Kallo kurum suka bi Hadiza dashi don kuwa ita ta taso sa gaba tana fad'in k'anwarsa ta b'ace, basu ma san wayagaya mata ba cewa Zubaidah bata dawo ba, shakka babu ta masu lab'en data Saba ne...
"A hankali Jalal ya furta " Oh my Allah give me some strength, I need to remain steady, they all rely on me... Annah ce ta k'arasa tana bama Hamma Habibu baki amma kaman cewa take ya k'ara, k'arshe zama masu yayi dirshan a k'asa yana kuka yana jejjefa k'afafu, Kamal ya k'arasi ya rungume baban nasa suna ci gaba da kuka...
"Hadiza kuwa banda tab'e tab'en baki bata furta komai...
"Annah ta juyo ta dubi Jalal wanda damuwa ce k'arara a Face d'insa, tausayin d'an nata ya cika zuciyarta, tasan he's in pain sabida tasan irin son da yake ma Zubaidah, zatayi magana yayi saurin k'arasowa ya rik'e hannayenta cikin rawar murya yace " I'll find her Annah, don't worry she'll be safe, just take care of them okay... Ya k'arashe maganar yana nuni dasu Hamma Habibu wanda shida Kamal bakace wanene k'aramin yaro ba sai kaga girman jiki...
"Har ya isa k'ofa Annah ta kira sunansa, tsayawa yayi yana dubanta idanunsa fal damuwa, k'arasowa Annah tayi gamida shafa fuskar sa tace " Ka kira Dr Khaleesat, gyad'a mata kai yayi tamkar k'aramin yaro da k'yar ya iya furta " Bata je ba Annah, I've bad feelings something bad might happen to her....
"Girgiza kai Annah tayi kafin tace " Babu komai insha Allah, I know she's safe, where ever she is....
"Gyad'a kansa yayi kafin ya fice cikin sauri, lmbar Usman ya shiga nema ya sanar dashi abinda ke faruwa a gurguje, sosai hankalin Usman ma ya tashi ....
"Neman duniyar nan sukayi shiru babu ita babu dalilinta, ga dare yaja sosai wajejen k'arfe 10:pm. Usman yace " Amma kanaga batasan kowa a garin nan ba, share k'wallam da ya zubo masa yayi abunka da farin mutum fatar tayi jazur haka jijiyoyin gishinsa sunyi rud'u rud'u green shar dasu
"Da kakkausan murya yake fad'in" I'm nothing but a coward na kasa tsareta daga sharrinsu, I couldn't protect her"
"Jalal pls ka daina d'aura ma kanka laifi, haka Allah Ya k'addara dole hakan saita faru, nidai inaga maybe akwai wanda ta sani k'ila tana chan, she might probably be mad at you muddin ta ganka da one of your friends, tunda kace a bakin hanya ka had'u da Tariq nidai inaga ta ganku ne.
"Usman batasan kowa a garin nan ba, ina zataje, what if the Dasukis harm her, what if they are responsible , ..... Kaman wanda aka zabura haka ya mik'e yana fad'in" I must go to them, nasan sune, su kad'aine zasuyi haka, Those bastard I'm gonna kill them all.... Cikin sauri Usman ya rik'o hannunsa yana fad'in" Calm down, calm down Jalal, don't be stupid abi abun a sannu, what if bata wajensu, what would you expect huh, what if they file a complaint against you, ka masu sharrin kidnap, if police got involved your little secret is exposed, think about it...
"Da k'arfin gaske ya fizge hannunsa yana huci yake fad'in" Hoe would I suppose to calm down, matata Tana cikin halin da van sani ba and yet kana ce min I should calm down.... They must all pay I don't care.... I don't care anymore Usman, let anyone gets what he deserves, I swear to you if they did any thing to her, I swear I'll kill them with my very own hands....... Wayan Unman ne ya soma ringing "Shattima ne ya bayyan a jikin screen d'in...
"D'an sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin yayi picking, " Mai sarauta ya akayi, cewan Usman bayan yayi sallama.
"Daga d'aya b'angaren Shattima yace " I just arrived at the city ina kake, don idan ban baka kud"in nan ba bazaka barni nayi bacci mai kyauw ba.
"D'an fuzar da iska yayi ya saci kallon Jalal, kafin yaja gefe ya shiga labarta wa Shattima abinda ya faru, sosai hankalkn Shattima ya tashi, cikin sauri yace Usman ya masa texting location he's on his way there...
"Zama sukayi su duka biyu kan madaidaicin darduman dake a parlorn, Zubaidah dai ba wani cin abincin take ba, gaba d'aya a tsarge take jinta, tun sanda taji mak'otan Zulaihat sun shigo suna maye.... Zulaihag sai k'ok'ari take ta kawar mata da tunanin lokaci guda tana shan cikin Zubaidah tana son jin dalilin da ya baro da ita gida.
"Zubaidah bata ja hiran ba, saidai tace wa Zulaihat ta gaji ne kawai da zama sasu she needs some space and bata san wajen wa zata je ba, so that they shouldn't find her...
"Gyad'a Kai Zulaihat tayi gamida d'aurs fake smile saman face d'inta....
"Suna gama ci Zulaihat ta raka ta har d'aki ta bata kaya masu sauk'i sabi fil dasu tace ta shiga ga bayi tayi wanka, murmushi Zubaidah ta sakar mata gamida mata godiya....
"Wyarta ta d'auka sanda Zubajdah ta shige toilet kana ta turawa Umar text
_We need to talk, ASAP, call me when you have time_
Sauk'e ajiyan zuciya tayi ganin sak'on ya tafi...
"Jalal kayi hak'uri mu k'arasa gidan da nake sauka a nan Asorock mu kwana is already late, idan yaso first thing tmrrw morning sai muyi reporting police station da kafafen yad'a labarai....
"Ba don yaso ba saidon tilasta masa da sukayi, baccin da baiyi ba, yanda yaga rana haka yaga dare. K'arshe yanke shawarin fitowa parlour yayi don yin nafilfili..
"Fitowar Shattima knn daga balcony ya gama amsa wayan Mai Martaba ya hangi Jalal ya kwab'e riga daga shi sai singlet alamun zai shiga bayi alwala......
"Sandarewa Shattima yayi yana kallon shatin tambarin dake a gefen kafad'ar Jalal ta hannun dama, wanda bashida maraba da tambarin masarautar su....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:21] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
46
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Hannun Shattima yaji bisa kafad'unsa, da sauri ya juya yana dubansa, dubansa Shattima ma yayi har lokacin hannunsa naga kafad'ar Jalal,.
"Murya cike da Al'ajabi Shattima yace " Ina ka sami wann mark d'in..
"D'an murmushi Jalal yayi kafin yace " I was born with it...
"Shiru Shattima yayi sai k'ura masa idanu da yayi, don kuwa ya tuna akwai lokacin da coincidence yaga irin wann tabo exactly a kafad'ar mai Marta wani rana yana sanye da 'yar shara suna hira da Shattima irin na d'a da mahaifi dukda bashi ya haifesa ba, ya tuna Mai Martaba ya basa labarin wann tabo da ya gani a gefen kafad'arsa cewa, babu wani sarki a masarautarsu Face yanada wann shaida, ..... Sosai ya k'ura ido yana k'are wa shaidar kallo batada maraba dana Mai Martaba.... Muryar Jalal ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi...
"D'an dafa kafad'ar Shattima Jalal yayi kafin yace " Don't get wrong idea nasan zakayi tunanin k'ila tatu ne nayi ko, to ba haka bane, I'm a good Muslim nasan babu kyau yin tattoo, Believe me I was born with it, yanda ka gansan nan..
"D'an murmushi k'arfin hali Shattima yayi kafin yace " Kayi alwalan ka I'll make some coffee, it will help you...
"Gyad'a kansa kawai Jalal yayi kafin ya shige bathroom...
"Gaba d'aya jikin Shattima yayi sanyi, kai wani babban Al'amari na shirin faruwa dashi,...
*************
"Washe gari tun ida sallahan asuba suka nufo suleja, to their greatest surprise Dr Khaleesat is there too, tana ganin Jalal ta sakar masa murmushi tace " You can go through this, don't worry kaji, we would find her...
"Murmushin k'arfin hali kurum ya sakar mata ba tare da yace komai ba..
"Annah ta rungumesa tana maida hawayen da ya kufce mata, Murya na rawa Jalal ke fad'in" Annah I couldn't find her, what if something bad happens to her, I'll never forgive my self...... Shigowan Hamma Habibu da Hadiza ne ya katse su don dama sunji tsayuwar mota...
"Kai tsaye hannun Jalal ya k'arasa ya rik'e yana fad'in" Jalal ka samo mun k'anwata, ka samota koh, nasan kai kad'aine zaka iya kular min da ita, ka fad'a min ka samota tana cikin k'oshin lafiya, idan wani abu ya sameta Inna da Baffah zasu gani daga makwancin su koh, zasu ce ban kula da ita ba ko,........
"Tausayi ya cika illahirin zukatan mutanen dake wajen.
"Hannayensa Jalal ya rik'e gamida zaunar dashi saman dakalin dake a veranda d'in kafin yace " Ka kwantar da hankalinka Hamma, I promise I'll find Zubaidah where ever she's, nayi alk'awarin zan samota duk yanda take da izinin Allah koda hakan zai zama sanadin rasa rayuwata, ka kwantar da hankalinka Zubaidah bazata so ganin hankalinka a tashe ba, kayi mata addu'a kaji...
"Haka Hamma ya ringa gyad'a kansa yana goge hawayensa da riga tamkar k'aramin yaro.....
"Kaman daga sama sukaji wayar Annah na ringing, Hadiza tayi saurin shigewa d'aukar wayan don Annah kam bataci ta kula waya ba.
"Jin muryar Zubaidah cikin wayar yasata fitowa da sauri tana fad'in itace Zubaidah ce.....
"Daga d'aya b'angaren kuwa Zubaidah cewa take " Ki bani Annah da Hamma na,..... Daidai sanda Annah ta fizgi wayar, Jalal kam mutuwar tsaye yayi yana binsu da Kallo.
"Daughter where have you been, we were all worried about you, Annah tace cike da nuna damuwa...
"D'an jim Zubaidah tayi duk sai taji babu Dad'i, Annah bazataji dad'in abunda tayi ba, despite all her efforts on her. A hankali take fad'in" Annah ina nan lafiya shiyasa ma na kira na sanar daku don kar ku damu, I just want some space ne, I'll come back to you soon, ina Hamma na.... Ta k'arashe a hankali.
"Annah bata iya furta komai bar, sai manna wayar a kunnen Hamma Habibu da tayi....
"Shida baya tareda su ya tafi duniyar kuka jin muryar Zubaidah a waya yasa sa mik'ewa zunbur yana murmushi,
"Zubaidah, Zubaidah na, Zubaidahn Baffa da Inna, ina kikaje.... "Jalal ya damu dake..... Gaba d'aya suka dubesa jin statement d'insa...
"Hamma yaci gaba da fad'in" Nima na damu dake, Don Allah ki dawo garemu kinji k'anwata, duka muna sonki, muna sonki....
"Share hawayen da ya zubo mata tayi kafin tace " Nima ina sonku Hamma, zan dawo kwanan nan kaji, kar ka d'aga hankalinka idan ba haka ba kuma bazan dawo ba, ka kwantar da hankalinka kaji.....
"Muryar Jalal taji cikin wayar yana fad'in" pls come back, if you want I'll leave the house, but pls don't put your self in danger, Hamma is worried so much about you, ki dawo don Allah ko kuma ki fad'a mun yanda kike, I'll get you right a way....
"Cike da masifa take fad'in" I won't listen to your lies again, I hate you even more, snn kar kayi tunanin zan dawo nan kusa, and lastly don't you dare involved police idan ba haka ba, wllhi kaji na rantse I'll leave you all for good, snn bazan dawo ba...
"Yanajin sanda tayi tsuka ta kashe wayar.....
"A hankali yana mai lumshe ido ya k'arashe da " I love you.... Be safe dear.......
"Gaba d'aya suka k'ura masa idanu cike da tausayawa.
"Dr Khaeelsat tace yi mun dialing number d'in, babu musu ya sake dialing amma sai jinta yayi a kashe, a sanyaye yace " is switch off..!!
"Gyada kanta tayi kafin tace let's talk private, babu musu yabi bayanta...
*************
"Mik'a ma Zulaihat wayar tayi tana mai zama bisa sofa ta shiga share hawaye, Zulaihat ta dafa ta kafin tace " Meyasa bazaki koma ba, suna sonki, you're so lucky da kika sami family haka masu sonki da yawa ta k'arashe zancen sanda take cire sim d'in da zubaidah tayi amfani dashi don dama extra sim d'inta ne wanda take solo ma Alhazawanta dashi, ..
"Girgiza kai Zubaidah tayi kana tace " No bazan koma ba, snn ko zan koma sabida mutane biyu ne, Annah da Hamma na, su kad'aine basa min k'arya...
"Zulaihat ta sauk'e ajiyan zuciya kafin ta mik'e tana gyara mayafinta tace " Okay ni zan fita breakfast na kitchen, ki shiga kici duk abinda kike so, zaki iya kulle gidan gaba d'aya.
"Gyad'a Kai Zubaidah tayi kafin ta dubi Zulaihat tace " Na gode, thank you for your kindness.
"Gajeren murmushi kawai Zulaihat tayi kafin ta suri jakarta tace " See you soon.
"Window Zubaidah ta k'araso tana lek'en Zulaihat da Imam, Imam harda mata murmushi da waving, bata kulasa ba sai sauk'e labulen da tayi ta k'arasa ta rufe k'ofar parlorn....
*************
"Annah dasu Jalal harma da Dr Khaleesat suka ja gefe suna tattauna lamarin bayan Dr sun gama ganawarsu da Jalal, ,
"Shattima yace " Nifa ina ganin we should report that to the polic, the earlier the better...
"Girgiza kai Jalal yayi kafin yace " Tace muddin mukayi reporting bazata dawo ba,.
"Are you sure babu wanda ta sani ko a cikin Abuja ne, Dr Khaleesat ta tambaya.
"Da sauri Annah ta kuma d'ago kai ta dubi Shattima, ta tuna kwanaki ya kawo masu budurwarsa, cikin sauri ta k'arasa gabansa tace " Kai kuwa ina yarinyar da kazo da ita kwanaki gidan nan, matar da zaka aura don ban mace ba haka ta fad'i mana, ita kad'ai Zubaidah ta sani me yuwa gidansu taje...
"Jalal yayi saurin mik'ewa yana recalling tabbas anyi haka...
"D'an jim Shattima yayi harga Allah Ya mance tare suka zo da Zulaihat amma ta ya ta zama matar da zai Aura, rabonsu da waya ma yana ganin tun wancan lokacin ne, k'ila ita tace masu haka knn...
"Da sauri ya furta "Zulaihat, Annah ta gyada kai tace k'warai...
"Kan kace Me Jalal ya fuzgo hannun Shattima yana fad'in" Muje pls take me to their house....
"Wait Jalal wllhi bansan gidansu Zulaihat ba, ban tab'a zuwa ba...
"Wani mugun kallo Jalal ya watsa masa kafin yace " Matar da zaka aura d'in ne baka san gidansu ba,
"Matar da zan Aura..? Shattima ya maimaita.
"Annah ta gyad'a kai tace "K'warai haka tace mana,.
"D'an girgiza kai kawai Shattima yayi kafin yace " Wllhi ko gidansu ni bansani ba........ Baikai aya ba Jalal ya shak'ure masa wuya yana fad'in" K'arya kake, then why did you bring her here, meyasa ka kawota nan.... Usman yayi tsalle yana k'ok'arin ceton Shattima...... Annah ta tafi da sauri tana Janye Jalal....
"Da k'yar aka k'waci Shattima daga mak'uran da Jalal ya masa....
"Janye hannun Jalal Annah tayi suka wuce d'aki rai b'ace...
"Ni bansan yanda zaka kai wann zuciyar taka ba, haba haba Jalal, idan kayi haka me kake tunanin Habibu zaiyi, You always let your temper get the best of you, kamata yayi ka nustu musan abin yi, idan neman Zulaihat d'in za'ayi sai ayi, and wnn yaro da ka masa haka bai deserving haka ba, he's here to help he cares about you, me kake tunanin Usman zaiji .
"D'an shiru yayi amma har lokacin huci yake a hankali ya furta " I'm sorry Annah....
"D'an dafa kafad'arsa tayi ta sassauta murya kafin tace " Son I know this is difficult for you, it hurts me ganinka a wann condition d'in, but we all need to remain steady, akwai mutanen da suka fimu rauni cikinmu, think about her brother abin yayi affecting d'insa sosai, pls kayi composing kanka kaji Son, and Dr Khaleesat bazataji dad'i ba regarding what you did earlier, tashi muje and apologize to them...
"Gyad'a kansa yayi kafin ya mik'e jiki a sanyaye..
"Gaba d'aya basuji zafin abinda yayi ba, saima tausaya masa da suka yi, Shattima ya dafa sa kafin yace " I know exactly how you feeling, and I'm willing to help Jalal, na kira wayan Zulaihat munyi magana tace " Zubaidah bata wajenta, but she sounds very wired like something is wrong with her, batayi rawan kan nata data saba ba, she was quite strange , the best abu shine mu fita mu nemi resident d'inta...
"Gaba d'aya sunji Dad'in shawarin Shattima, Jalal ya d'an dafa kafad'arsa yace " I'm sorry again Shattima, murmushi kawai yayi yace " That's what bothers are for, let's get going the earlier the better...
"Gaba d'aya suka gyad'a kai, Dr Khaleesat ma Office tace zata wuce ganin k'arfe takwas tayi snn tace " suyi keeping nata update duk abinda ake ciki, a tare suka fice, Dr Khaleesat ta nufi motar ta yayinda Su Jalal suka wuce Ride d'in Shattima...
***********
*Sheraton Hotel, Abuja*
"Kallon d'akin da yake kwance a ciki yayi, ya dubi suturun dake jikinsa masu d'an karen tsada, his life is different now, komai ya canza, he's rich handsome and educated, abu guda da ya rasa shine ZUBAIDAH She suppose to be here with him enjoying the luxury, this is the life he's been dreaming of, finally ya samu, what next now???? Ya tambayi kansa. Zuciyarsa ne ta basa amsa kai tsaye
"GET HER BACK, Get your girl back, she's yours, she's meant to be with you no one else, get back what's rightfully yours...
"Mik'ewa yayi ya soma shiryawa, cikin drawer ya hangi tsohuwar phone d'insa wanda tunda yayi kud'i ya jefarta ya sai iPhone8, sauk'e ajiyan zuciya yayi sanda ya tuna irin baran baran d'in da sukayi da iyayensa sanda ya koma masu yayi kud'i dare d'aya, gaba d'aya basu yarda da arzikin nasa ba, d'an tab'e baki yayi kafin ya d'au wayan halama sun kirasa, duba wayar ya soma yi yaga sakk'wanni da kira masu yawa, yyawanci na abokinsa Balele ne da Zulaihat, na Zulaihat ya soma dubawa, ya shiga kiran wayarta yaji a kashe, ita kuwa masu amsan kud'in gidan haya ne da Shattima suka sakata kashe wayarta, ya kira ya kira a kashe, karanta sak'on data tura masa yayi,
"D'an jimm yayi kafin ya furta " I shouldn't have abandoned you anyway, you help me sanda na zo, fita yayi ya wuce Mall ya soma mata shopping, kaya sosai ya saya mata kafin ya nufi gidanta......
Sameena ce
[1/23, 22:21] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
47
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*"Salam. Ina rok'on Allah yayi maki albarka fiye da k'ok'arinki, Ya shirya maki iyalanki fiye da tarbiyarki, Yayi maki Rahama fiye da tubanki, Yaji k'anki fiye da tunaninki, Ya k'ara azurtaki fiye da nemanki, Ya karb'i ibadunki fiye da k'wazonki.... Allah yayi ma Mahaifanki gafara ba tareda binciken ayyukansu ba, Allah Ya rufa maki asiri duniya da lahira.... Ina maki barka da Jumma'ah*
*"Sak'onki a gareni 💅🏼Maman Sadiq💅🏼......👆🏽*
*Na gode na gode k'warai da gaske da kyawawan addu'o'inki da nuna k'aunarki a gareni, Ubangiji ya saka maki da khairan, Sameena na k'aunarki, Alkhairin Allah Ya kai maki duk yanda kike... 🤝🤝the whole chapter is yours dear😍😘*
"Imam don Allah ka bar duk abinda kake kazo muje, wann mutumin ba mutunci ne dashi ba, wai Ya kira Tariq ma bai d'aga wayarsa, he's talking nonsense, wai saidai ya kwana dani tukunna zai d'aga min k'afa, kasanni bakina baya shiru nan na gaggaya masa magana son raina, probably nasan yana hanyan zuwa gidan ya min watsi da kaya ga Zubaidah tana can pls kayi sauri.... Ta k'arashe maganar tana yarfe hannu...
"Daga d'aya b'angaren Imam yace " Gani nan zuwa, just send me your location, cikin sauri ta amsa gamida tura masa....
*******
"Tana zaune gaban kayan kallo tana kan duba plates d'in da suke jere a cikin drawer d'in dake mak'ale jikin TV stand, yawanci Americans films ne saiko Nigerian films, bangon d'aya kaset d'in ne yayi mugun d'aga mata hankali don kuwa abin babu kyaun gani basai ance maka bluefilm bane, k'irjinta ya shiga bugawa da sauri da sauri, tayi saurin jifa da kaset d'in ta shiga k'ank'ame jikinta ita kad'ai tana matsawa jikin garu.... Hakan yayi daidai da soma knocking, Zubaidah ta kuma firgita, toshe bakinta tayi da iyaka k'arfinta da duka hannayenta biyu, tsoro da firgici ya mamaye ta baki d'aya.... Da alama mai knocking gajjiya yayi kokuwa ya tafi.
"Cikin sand'a ta isa jikin labulen window tana lek'awa, kasa gasgata abinda idanunta suka gane mata tayi, is that really him, ba don ta masa faran sani ba tabbas zata ce bashibane k'ila an canza sa, this one's different from the Umar she knows, sanye yake cikin kaya na alfarma hannunsa rik'e da d'an makullin mota, fuskarsa sunkuye yana rubutu jikin takarda, gama rubutun da zaiyi ya k'arasa jikin wata da ba sai ance maka taji kud'i ba, Zubaidah tana gani ya shiga lodo kaya yana ajiyesu bakin k'ofar had'i da d'aura note d'in saman shopping bags d'in....
"Sulalewa tayi a wajen k'irjinta na barazanar tarwatsewa, ta nemi kukan da take ta rasa, tana jin tafiyar motar tayi saurin fitowa ta d"auki note d'in.... Abinda ta gani a ciki yafi komai girgizata.
_Hello, I've been calling your number wasn't going, I wanted to thank you for your kindness and for accommodating me, snn to be honest with you, akanki na soma sanin Wata mace so bazan mance ki a rayuwata ba, when ever you've time pls phone up me.. ... UMAR_
"Durk'ushewa tayi a wajen kaman zararriya ta soma fad'in" No bashi bane, it wasn't him, Umar bazai tab'a yin haka ba,....... Kuka mai k'arfi ya kufce mata, tana tsaka da kukan taji an daki windown dake gefenta da sauri ta mik'e tsaye tana tattare hijabinta.
"Wani murtuk'ek'en mutum bak'ik'irin ta gani idanunsa tamkar garwashi sai muzurai yake, tsawa ya daka mata tuni ta yarda takardan dake hannunta, ta shiga ja da baya.
"Da kakkausar murya mutumin ya soma fad"in" Ina zaki gudu munafukai kawai, tsayawa zakiyi ki fad'a mun yanda shegiyar k'awar taki ta tafi, don nasan plan kuka had'a tunda na gaya mata zanzo amsar kud'ina tunda daduro ba k'anwar uwarta bane balle na ubanta, shegu kawai kunsan bazaku iya biyan kud'in haya ba kuka baro gidajen iyayenku kuka fito daduro, toh wllhi akanki zan amshe kud'ina, munafuka harda wani hijabin munafunci saikace sallahn kuke, .......
"Jiki na kararwa Zubaidah ke ja da baya tana fad'in "Wllhi bansan kom...... Bata kai aya ba ya kai mata sura tayi wani tsalle had'i da ihu, daidai nan Zulaihat da Imam suka shigo,....
"Zulaihat baki na rawa take fad'in" Duguja wani irin bura'uba ne wann yaya zaka tsorata min k'awa.... Wawan naushi ya kai mata a baki saida jini ya fettsesu... Zubaidah ta kuma sakin wani k'ara cike da firgici, Imam kuwa kukan kura yayi ya cakume Duguja da duka, Ai Zubaidah na ganin haka, ta zura hannu bakin k'ofa ta suri jakarta ta soma gudu tamkar zararriya... Zulaihat dake kwance shame shame a k'asa da k'yar take iya k'walla kira wa Zubaidah amma inaa, ko juyowa batayi ba, tamkar mahaukaciya haka take gudu bisa layin, mutane 'yan layin kuwa wanda akasarinsu karuwai ne suka fito bama ido abinci sai shewa ake memakon ayi yunk'urin rabasu, babu tarbiya sam... Allah ka tsare Al'umman musulmi ameen...
"Da k'yar da mak'ek'yata suka sami wanda yasan gidan Zulaihat, har layin aka kaisu, tundaga nesa gabansu ke fad'uwa ganin yanayin mutanen dake wajen da yanayin layin mmusamman sabida fad'an da akayi.. tabbas wann waje babu danshin tarbiya.
"Murya na rawa Jalal ke fad'in" I can't believe my wife is here, Shattima this is a Barracks bana tunanin matar aure me mutunci could leave in this place, Shattima ya paka motar kafin yace " Nima dai abinda zance knn, but she says she's leaving with her Aunt muje dai muga... Usman cewa yayi I'm speechless, that bitch lied to you...
"Tunda suka soma tafiya matayen wajen ke admiring d'insu, duk macen da suka wuce saita Bank'are masu k'irji ko kuma tayi wani salon wasu harda fad'in" Wow cuties.... gaba d'aya suka sha jinin jikinsu..
"Suna isa suka tarar k"ofa a Bud'e har lokacin bala'i ake Duguja yana fad'in sai ya amshi kud'in hayarsa a jikin Zulaihat Imam ya kasa ya tsare yace bai isa ba.....
"Da mugun mamaki suke kallon wann sure d'in, Ganinsu yasa Duguja guduwa don ya d'auka kiransu sukayi su kamasa. Yana gudu yana juyowa yana fad'in" Shegiya kariya nasan kiransu kikayi ban gama dake ba ina nan dawowa wllhi sai na amshi kud'ina, idan suna sonki su biya maki ko ki biya da jikinki agwagwa kawai...
"Kallonta kawai Shattima keyi cike da k'yama yana girgiza kai, unbelievably. Jalal kam tuni ya shige cikin gidan sai bankad'e banked'e yake yana neman Zubaidah.
"Imam ne yabi bayan Jalal yana fad'in malam lafiya, yaya zaku shigo gidan mutum ku hau masa bincike...
"Wani mugun kallo kawai Jalal ya watsa masa jijiyoyin jikinsa sunyi rud'u rud'u yake fad'in" Where... Is..... She.... Word by word yayi maganar,
"Imam kuwa Ba tareda ya fahimci me Jalal ke nufi ba yake dubansa , wani uban tsawa Jalal ya kuma daka masa " Where's My wiiifeee! I know she's here, just tell me ina takeee,.. Ya k'arashe maganar yana mank'uran Imam, da sauri cikin kakari Imam yake masa nuni da waje kafin yace " She left, she left...... Sake sa yayi ya fito waje a guje yanda su Shattima suke. Gaban Zulaihat ya k'arasa yana bata wani irin look wanda da an maka sunanka sorry kawai, ...
"Ina take??? Ya tambaya yana daka tsawa, baki na rawa Zulaihat take fad'in" Wllhi ta... ta tafi tun sanda aka soma fad'an nan...
"Idanunsa sun kad'a sunyi jazir, kana iya jin hucin da yake kaman kububuwar maciji, shak'eta yayi da iyaka k'arfinsa ya had'a da jikin garu yana fad'in" I'll kill you Garbage, .... "Da k'yar su Shattima suka k'waceta ganin zaiyi kisa...
"Sumkuyawa tayi tana tari tana sosa wuyarta ga jinin da ya kuma b'allewa a bakinta ciwon da Duguja yaji mata,..
"Yana fiffizgewa yake fad'in" If something bad happens to her I swear you'll kill you, tell me are you working for them, you're working for them right, you are working for the Dasukis, admit, just admit you bitch...
"Da k'yar ta d'agi kai tana fad'in" I've no idea what you talking about, Zubaidah ita ta kawo kanta nan, I didn't drag her here,.....
"A zuciye Shattima yace " Then why did you lie to Us, meyasa kika min k'arya, why did you even show up in my life, idan ba kinada wani bad intentions dinki akan Zubaidah ba, . First you lied to me cewa da Aunt d'inki kike zaune, while ba haka bane you're just a prostitute, second kinma Zubaidah k'arya cewa ke fiancee d'ina ne, tell us what do you have in mind, what ate your intentions...
"A zuciye ta mik'e cike da jin zafin maganganun Shattima kafin taci gaba da fad'in" Yes I lied to you I admit, I was only using you to get close to Zubaidah sabida na gane mutumin do nake so gangar jikinsa da ruhinsa na gareta, mutumin nan ba kowa bane illa Umar her Xfiancee, he loves her very much wanda har takai bazai iya kallon wata mace ba face ita, wann shine dalilina, snn zaman da Zubaidah tayi a wajena ban cutar da ita ba Allah shine shaida na.... Ta k'arashe maganar tana hawaye .....
"FFuskar nan tasa tayi jajazur gashin jikinsa sun mimmik'e haka idanunsa sunyi jazur, kaman mutun mutumi haka ya tsaya a wajen, sai dunk'ule duka hannayensa biyu da yayi...
"Shattima ma ya zama shocked sosai, a hankali ya soma jan hannun Jalal yana fad'in" Let's get out of here, babu musu ya soma binsa tamkar rak'umi da akala, har sun isa jikin mota Shattima ya juyo ya dubeta kafin yace " I'll never forgive you.. Daga haka ya soma k'ok'arin bud'e mota, Usman ne ya karb'i keys d'in yana fad'in" Let me drive, babu musu Shattima ya mik'a masa ya koma seat d'in baya .....
"Kifa kansa yayi gaban mota sanda yaji wani irin hawaye mai k'una ya ciko idanunsa. Why all this, why why, why life has to like this,... Jin zuciyarsa na neman kaucewa rahamar ubangiji yasa soma karanto innalillahi wa Inna ilahirraji'un, Allahuma ajirni fi musibati wa aklifli khairan minha....
Sameena ce
[1/23, 22:22] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
48
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Tafi minti biyar tana durk'ushe a wajen tana kuka, for the first time data soma jin takaicin irin rayuwar data jefa kanta ciki, rarrsshin duniya Imam yayi tak'i kulasa, sai snn ya kula da shopping bags d'in da akayi patali dasu a gefe, k'arasawa yayi ya tattaro su, komai na cikin jakar are sealed, daga can gefe ya hangi 'yar k'aramar takarda, d'aukowa yayi ya ajiye gabanta kafin yace " Kiyi hak'uri ga sak'o nan I'm sure is yours..
"D'ago rinanun idanunta tayi tana bin kayan da kallo wanda ita kanta batasan dasu ba sai yanzu, goge hawayen idanunta tayi ta amshi takardar ta soma dubawa, tana gama karancewa ta kuma fashewa da wani matsanancin kuka.... Tunowa da tayi tabbas Zibaidah ta karance takardan nan koma tayi arba da Umar yasata sakin wani murmushi, ko babu komai yanzu Zubaidah zata fahimci Umar ya barta for good snn da har yanzu yana sonta da bai tafi ya k'yaleta ba, da ya tafi da ita...
"Wani murmushi Zulaihat ta kuma Saki kafin ta shiga bubbud'e kayan, kaya ne masu d'an karen tsada haka ta ringa fitfito dasu Imam na tayata, fad'i yake, ai gwara ki kira mutumin da ya kawo kayan nan ya biya maki kud'in hayar ki, don daga gani he's loaded, ..
"Zulaihat dai bata kulasa ba sai firfito da kaya take, wayarta ta d'auka ta shiga dialing lambar Umar sand take umurtan Imam ya shigar da kayan ciki....
"Bugu biyu ya d'aga wayan, ba tare da ta iya furta komai ba sai kukan data fashe dashi.... "Cike da damuwa yake tambayarta lafiya..
"Cikin salo Zulaihat ke shesshek'an kuka tana fad'in " Pls come to my place, dan Allah kazo yanzu, come before he kill me... Daga haka ta katse wayar...
"Hankali Tashe ya bar breakfast d'in da yake ya fito ya nufo gidanta...
"Mintoci kad'an ya kawosa apartment d'in Zulaihat, tana ganinsa ta fad'a jikinsa tana shesshek'ar kuka, sosai ya razana da ganin yanayinta, fuska a daddauje gashi Tana kuka,..
"Rungumeta yayi cike da tausayawa, murya cike da mamaki yake fad'in" What happened to you, who did this to you...
"Cikin kuka Zulaihat ta labarta masa komai na maganan gidan haya,...
"Rai b'ace yake fad'in" If I see that jerk I'll make him pay, ta yaya zai bugeki, you should have called me right away,....
"Goge hawayen tayi ta kuma matsewa cikin jikinsa kafin tace " Banyi tunanin haka ba, I thought you will never come back to me, ...
"D'ago ido tayi tana dubansa sanda ya k'ura mata idanu, hannayensa ta rik'e kafin tace " Me ka fad'a wa Zubaidah, I thought idan ka ganta you won't let her go, now I believed you feel something for me, ka zab'eni ko..?? Ta k'arashe maganar tana sakar masa murmushi....
"Jin maganganun nata yayi kaman almara,..
"Wait you mean to say Zubaidah's here with you..? Ya tambaya yana zaro bold eyes d'insa...
"D'an jim tayi tana tunanin toh kodai basu had'u bane kafin ta d'an girgiza kai tace " but not anymore, she left awhile ago...
"Mik'ewa yayi yana fad'in" Ina kike tunanin ta tafi, ina zan sameta, ... Wait how did you know her...???
"Ganin gaba d'aya ya rikice yasa jikin Zulaihat yin sanyi...
"Mik'ewa tayi ta shiga tattaro kayayyakin da ya saya mata ta shiga jibgawa a gabansa tana fad'in" You'll never stop loving her, will you,... Just get out of here, I don't wanna see you ever again..... Turasa ta shiga yi da iya k'arfinta tana dukan k'irjinsa har suka isa k'ofa kafin ta rufe k'ofar ta durk'ushe wajen tana kuka...
"Hannu yasa ya shafi askinsa wanda yake low-cut kafin fuzar da iska, cikin ransa yake fad'in" No Zulaihat I can't leave you, zaki min amfani wajen cimma burina, I need to work with you, I must know ta yaya kika san Zubaidah har tazo gidanki while halayyan ku ya banbanta.. you must be an important person to her....
"Jingunuwa yayi jikin k'ofar gamida k'ank'an da murya kafin ya soma fad'in" Pls Zulaihat let's talk, don't shut me out pls, I'm sorry I mean it....
"Cikin kuka take fad'in" Ka tafi don Allah bana son ganinka and don't show up ever again...
"Bai tafi ba sai ma magiya da ya ringa mata,... A haka Imam ya iso ya iske a bakin k'ofa ga sautin kukan Zulaihat da yake jiyowa,.. A sittin Imam yayi kansa ya cakume masa wuya yana fad'in" What's it again, who are you.. Me ka mata...
"Jin Imam ya kaure Umar da fad'a yasata saurin bud'e k'ofar tsakaninsu ta shiga ta rabasu gamida daka wa Imam tsawa tana fad'in" Just go Imam I can handle this,.. Cikin tsawa shima yake fad'in"No I won't let any jerk lay a finger on you again..
"Then nace ka tafi ka tafi pls, is not what you thinking.... Mugun kallo ya watsa wa Umar kafin ya k'araso gareta ya rik'e kafad'unta yace " Always remember that you can count on me, I'll be here when ever you needs me, kin wuce k'anwa a wajena...
"Murmushi ta sakar masa gamida gyad'a masa kai, daga haka Imam ya fice yayi tafiyarsa.
"K'arasow Umar yayi gamida bata light hug cikin k'ank'an da murya yace " I'm sorry, gaba d'aya sai ya tafi da Zulaihat, tuni ta mak'ale cikin jikinsa tana sauk'e ajiyan zuciya..
"A hankali ya soma fad'in" I didn't mean to hurt you Zulaihat, ki min uziri, what I went through babu sauki, I was to marry her, dakawai baikona a kanta kafin wann Jerk d'in Jalal ya aureta, Zubaidah betrays me, my whole life nayisa ne bisa sohayayyarta but still she chooses to be with that imbecile, ba komai yasa nake son sanin yanda take ba a yanzu illa to take my revenge on her and her so called husband, I want to make them pay I wanna see them suffering,... Ya d'an Dad'a matseta cikin jikinsa kafin yace " Believe me I'll never leave you again, you have me completely.... Da sauri ta d'ago idanu tana dubansa gyad'a mata kai yayi kafin yace " Yeah I promise, all I want from you is to tell me everything every single thing you know about Zubaidah kinji my luv...
"My luv ta maimaita a hankali batasan sanda murmushi ya kufce mata ba... Da sauri ta kuma rungumarsa very tied....
"Murmushi shima yayi gamida k'urama waje guda ido, cikin zuciyarsa yake fad'in" You'll help take Zubaidah back, she's mine.....
**************
"Neman duniyar nan basu sameta ba, ga dare ya soma yi, ga ruwan da ake kan zabgawa kaman da bakin k'warya, gaba d'aya ya fita hayyacinsa, duk tausayinsa ya rufe su,..
"Usman ya dafa sa yace " Bro mu mik'a cigiya kafafen watsa labarai ko Allah zaisa a sameta, kaga dare yayi ga ruwan da ake kan zabgawa, kaga yanda ruwa ke d'iga a jikinka zakayi ciwo.....
"Kallon Usman yayi da rinannun idanunsa kafin ya soma fad'in" I don't care Usman ban damu nayi ciwo ba, All I want is to see her again, what if she couldn't take care of her self, what if something bad happens to her, me kake tunani.... Yasa hannunsa gamida kwantar da sumansa da ruwa ya jik'a had'i da fuzar da iskan bakinsa, ga wani sanyi da ya soma kad'asa...
"Juyawa yayi ya kalli Shattima wanda har yanzu cikin damuwar abinda Zulaihat tayi yake kafin ya k'arasa k'asar bishiyan da yake.... Bud'e bakin da zaiyi da niyyan magana wa Shattuma ya hangi mutum kwance bayan katakon shagon dake k'ark'ashin bishiyar, hijabin makarantar ta ne a jikinta, kwance take tamkar maras numfashi da alama ruwan ya jima yana bugunta..... bai iya ce masu komai ba sai k'arasawa wajen da yayi, cikin sauri suma suka k'araso wajen gaba d'aya....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:22] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
49
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"D'agota yayi ya rungume cikin jikinsa hannayensa na rawan sanyi, murya na rawa yake fad'in" I'm sorry, you'll be I got you.... Zafin jikinta da nasa suka gauraya waje guda yana jin fitar turirin numfashinta a hankali , haka ya ringa sumbatu still tana rungume cikin jikinsa, Shattima ne ya dubi Usman kana yace " Get the car buddy,
"Yeah sure, Usman ya fad'i ya nufi yanda suka faka motar ya k'araso da ita yanda suke, ...
"Dafe shoulder d'in Jalal Shattima yayi kafin yace " Muje Jalal... Babu musu ya mik'e gamida d'aukanta a hannu tamkar baby... Shattima ya bud'e masa back seat suka shige yayi saurin wucewa mazaunin Me zaman banza....
"Dr Khaleesat ta d'an ja medicated glass d'inta k'asa kad'an ta duba agogon dake d'aure a hannunta na hagu ya nuna k'arfe 10 da wasu dak'ik'ai sauk'e light breath tayi kafin ta dubi Annah data rapka uban tagumi tace " Ki kwantar da hankalinki Insha Allah everything will be alright, is getting late ni zan wuce gida idan yaso gobe sai muyi reporting to the police snn mu kai cigiya kafafen yad'a labarai...
"Gyad'a mata kai kawai Annah tayi ba tare da ta iya cewa komai ba..... Kaman daga sama suka jiyo muryar Hamma Habibu yana fad'in
"Annah Annah sun sameta, sun samo k'anwata, Jalal ya samo mun ita....
"A tare Annah da Dr Khaleesat suka mik'e, Hadiza ce mai d'aga labule Hamma na gyara mata, Tana nan rik'e a hannunsa ya shigo bai tsaya ko ina ba sai bedroom d'in Annah cikin sauri suka d'unguma suka bi bayansa, ajiyeta yayi saman bed ya shiga rarumo bargo yana rufa mata, sai gaishesa suke faman yi amma bai sami zarafin amsa su ba, she dai kawai yaga Zubaidah ta zama safe, ... "Jin jikinta ya kuma yin zafi yasa sa d'ago kai yana duban Dr kafin yace " Her temperature is burning ko asibiti za'a kaita..
"Let me see, cewar Dr Khaleesat , da sauri Jalal ya matsa gefe ya bata waje sunkuyawa tayi tana tattab'a jikin Zubaidah jafin ta girgiza kai tace " No babu komai tsananin fever ne kawai kuma ruwan da ya jima yana sauk'a jikinta ya saka mata give her paracetamol idan ta tashi and I'll prescribe her medication as soon as I get home idan yaso sai na maka texting, ta d'anyi murmushi tana duban Jalal kafin tace " Mr Jay baka lura kayan jikin matar taka a jik'e suke ba ka ajiyeta haka and still ka rufa mata bargo, take off the clothes ka saka mata wasu snn a matsa mata jikinta da warm water with a towel sabida zafin jikin ya sauk'a.....
"Kaman jira Hadiza take nan tayi karaf tace " Ni Dije zanga yanda za'a canza wann kaya mutanen da ko kwana d'akj guda basu tab'a yi ba shine za'a ce ya sake mata ka...... "Aya ta saka ma zancen nata ganin wani irin muguwar kallon da Jalal ya watsa mata.... "Babu wanda yace k'ala sai Dr Khaleesat data kuma duban Jalal tace " you should change your clothes too before you fall sick, kai nasan kaima baka da lafiya, zan maka prescribing magani kaima, don I'm pretty sure ciwon soyayya kuke.... Gaba d'aya suka murmusa harda Hamma wanda ke durk'ushe yana rik'e da hannun k'anwarsa.
"Toh ni zan wuce and pls a guje duk wani abinda zai b'ata mata rai for now.... Dr Khaleesat bata Kai aya ba Hamma ya dubi Hadiza yace " Kinji koh Hadiza likita tace kar a b'ata mata rai dan Allah kar ki mata masifa kinji.....
"Kallon fuskokin mutanen wajen Hadiza tayi kafin ta kafesa da wani mugun harara tace " Da shike nice uwar 'yan bala"i koh, dan na nuna damuwata akanta ashe nayi laifi.... Banji ba ban gani ba balle kuce nace.... Ta buga wani uban tsaki gamida ficewa fuuuu....
"Gaba d'aya suka bita da kallo, Hamma ya mik'e yana dariya wanda shi a tunaninsa murmushi yake ya dubi Dr yace " Kar ki damu haka take, haka take... Zan je na mata magana, ya k'arashe maganar yana nuni da k'ofa, ...
"D'an murmushi kawai Dr tayi gamida gyad'a kanta... Annah kuwa kaman ta nitse sabida takaicin Hadiza, sallama suka kuma yi da Jalal kafin Annah tayi ma Dr rakiya....
"Tsura mata dogayen idanunsa wanda basu faye girma ba yayi yana tunanin ta yanda zai soma canza mata kaya, .
"Mik'ewa yayi jiki babu laka ya nufi drawer d'in da yake tunani nata ne kafin ya bud'e, kayanta ya gani a shirye tsaf a ciki.... D'an fuzar da iska yayi kafin ya ciro wasu kayan. Ya dawo yanda take...
"Ya jima yana durk'ushe gaban gadon yana dubanta, fuzar da iska ya kumayi kafin yasa hannu ya yaye bargon,... K'irjinsa ya shiga bugawa da sauri da sauri sanda yake k'ok'arin rabata da rigar jikinta.... Abubuwan da suka faru a wancan daren suka shiga dawo masa, fuskokinsu yake hangowa sanda suke keta mata rigarta.... "Da k'arfin gaske ya runtse duka idanunsa biyu... Kasa cire mata rigar yayi sai mik'ewa tsaye da yayi cikin sauri ya nufo parlor, a k"ofa suka had'u da Annah sai rawan sanyi yake.... Kan ta sami zarafin magana yayi saurin mik'a mata kayan Zubaidah dake hannunsa yace "Barin duba su Shattima..... Ya k'areshe maganar cikin rawar murya irin ta maras lafiya....
"Kallonsa Annah tayi kafin tace " Ah sun tafi ai, sunce zakuyi waya.... "Baka da lafiya ne, she added..
"D'an jim yayi kafin yace" I'll be fine Annah just take care of her, I'll be in my room idan kina nema na..
"D'an gyad'a kai kawai tayi ta bisa da kallo cike da tausayawa har ya fice..
"Layin Shattima ya soma kira yajita a kashe, nan ya kira na Usman, .
"Usman ya sanar dashi Shattima ke da journey gobe da sassafe, zaije sa Kaduna and daga chan maybe ya wuce Gombe...
"Jalal ya kuma tak'urewa cikin bargo kafin yace " I feel bad you know, I couldn't have chance to thank you... Zan sake kiransa gobe da safe insha Allah... Na gode na gode sosai Usman " You guys are incredible Allah Ya bar zumunci...
"Haba Jalal ka daina fad'im haka pls, that's what brothers are for.. I'll see you tomorrow Allah k'ara rufa asiri...
"Ameen Jalal ya amsa dashi sukayi sallama kafin yayi hanging up...
"Washe gari tunda ya tashi tun safe bai fita ko k'ofa ba dukda jikin nasa ya masa dama dama breakfast ma har d'aki Annah ta kai masa, lokaci zuwa lokaci yake tambayar ko Zubaidah ta tashi..
"
"Wajajen k'arfe sha biyu da rabi goshin azahar ya fito ya nufi d'akin Annah...
**************
*Dasuki Holding*
"Zaune yake yana juyi saman kujeran nasa waya mak'ale a kunnensa ba sai ance maka da sahibarsa yake wayan ba, banda uwar harara babu abunda Labib ke watsa masa....
"Salim yaci gaba da fad'in" are you serious sweetheart, wait how comes bansan kina shirin had'a mana spectacular dinner ba.
"Murmushi yayi sanda ta basa answer kafin yace " Okay kice k'aramar biki zaki kuma had'a mana, okay zan fad'a wasu Daddy right away tunda duka suna nan har Pappy... Ohh my Baby can't wait to see you, kar dai kiyi aiki sosai ki gaji kinji Baby na... Ya kuma yin want murmushi mai sauti yana juyi bisa kujeran kafin yace " Okay my darling kisses to you.....
"Har ya k'arashe wayar Labib bai daina danna masa harara ba...
"Mik'ewa Salim yayi yana gyara suit d'insa ba tareda ya dubi Labib ba yake fad'in" Kausar is inviting us all for dinner tonight zanje na fad'awa su Daddy right away su Mummy ma will be there,... Bai damu da rashin ansa sa da Labib beyiba idan da sabo ya saba da halin d'an uwan nasa...
"Har ya kai k'ofa ya juyo yace " Pls ka kira Tariq ka fad'a masa though his family is invited too, amma dai pls ka fad'a masa idan yaso sai ya zama kaman farewell party d'insa...
"Bai amsa sa ba sai faman kad'a biro da yake, yana ficewa yaja tsuka gamida furta " Useless..
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:22] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
50
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*I've received your messages masoyan k'warai wllhi lisaffo sunayenku ma aiki ne sabida yawanku.. Nonetheless ina sonku irin totally d'inan Alkhairin Allah Ya kaimaku duk yanda kuke...😍😘❤*
"Ya jima yana tsaye bakin k'ofa hannunsa a Hard'e kan k'irjinsa, kallon siraran hawayen da suke bin k'uncinta yake...
"Jikinta ne ya bata da kwai mutum a wajen snn wann k'amshin nasa bai barin hancinta da sauri ta d'ago kai tana dubansa,... Fuskan nan nasa a mirtuk'e babu alamun Fari'a, yana sanye cikin inner red Mai V-neck had'i da lallausar wando Wanda da kad'an ya wuce gwiwarsa....
"Cikin sauri ta kauda kai gefe don bata juran kallonsa...
"Taku kad'an yayi ya k'araso cikin parlorn.... Cak ya tsaya a gabanta cikin dakakkiyar murya ya soma fad'in"
"Why... Me yasaki yin haka, .... "K'ara sautin muryar yayi cikin tsananin fad'a yake fad'in" Tell me why, what... What if I couldn't find you, what if I couldn't protect you.... Do you even realize the kind of trouble you almost got your self into huhhh..?? Do you think you the only suffering..?
"D'agota yayi sanda kukanta ya k'aru ya rik'e arms d'inta da k'arfin gaske suna fuskanta juna yaci gaba da fad'in" Look into my eyes and tell me what the heck did I do to you this time around...
"Bud'e jik'akk'un idanunta da suke sharkaf da hawaye tayi ta sauk'esu kan farin fuskarsa da ya turning red, siriryar jijiyar goshinsa ta fito sosai, siraran dogayen idanunsa sun firfito waje, sirirn hancinsa wanda bai faye tsawo ba k'ofofin sun bubbud'e, his cute pink lips keeps blowing kaman ya shafa lipstick....
"Ta tuna yanayin data gansu da Tariq zuciyarta ya shiga mata zogi da rad'ad'i..
"Da k'arfin gaske cikin tsananin kuka take fad'in" Eh gwara na tafi ko ina ne, 'cause you all the same, you... Are... Just... Like... Them... You all raped me... Snn I saw you with him hugging each other probably planning something again ...
"Are you going to deny it, huhh.. Ka fad'a mun Me kuke shiryawa akaina, ka fad'a mun kuna shirya yanda zaku...... ENOUGH.!!!!!! YA daka mata wata tsawan da saida hawaye ya fita daga idanunsa.... Annah dake kitchen saida ta yarda ludayi....
"Ita kanta Zubaidah shaking ta soma tana kallonsa bata tab'a ganinsa cikin irin wann yanayi ba....
"Ido cikin ido yake dubanta in a furious tune yaci gaba da fad'in" I love you.... I love you ultimately more than you might think. And you know I'm not asking you to love me back.. All I want is protect you and to keep you safe koda hakan zai zama ajalina.... I don't care anymore if you don't believe me..... Daga haka ya juya ya fice daga parlorn cikin sauri.......
"A bakin k'ofa suka had'u da Annah, bata sami zarafin masa magana ba ganin yanyain nasa, ta jima bataga irin wnn yanayi a tattare da d'an nata ba, ... "Cikin sauri ya nufi d'akinsa. Kallo Annah ta bisa dashi har ya shige. Sauk'e nannauyan ajiyan zuciya tayi ta shiga parlon tana addu'an Allah Ya kawo k'arshen wann Al'amari.....
"Har lokacin kuka Zubaidah take, lallashi ya zame ma Annah jiki...
"Yana shiga d'akinsa wandosa ya canza zuwa ta jeans kafin ya fice.
"Suna jin ficewarsa ko sallama bai masu ba.
"Zubaidah ta kuma shigewa jikin Annah hawaye na fita idanunta, tausayin kanta ya kuma kamata, for the first time dataji babu Dad'i abinda tayiwa Jalal, Kalman *I love you and I'm not asking you to love me back* ta ringa nanatawa cikin zuciyarta, wani hawayen na kwarara mata musamman idan ta tuno abunda Umar da Zulaihat suka mata....
*******************
*Police Department Headquarter Wuse2 Abuja*
"D'aga idanunsa yayi ya kuma karantawa, zuciyarsa tana Dad'a basa k'arfin gwiwa akan abinda yayi niyya, kai tsaye ya kutsa kai ciki, tuni ya nemi ganin IG, ba'a basa daman ganin sa ba, ya jima yana jiran neman ganinsa bai samu ba har saida IG ya fito daga meeting, haka kurum yaji yana son ganin Jalal, nan aka masa izini.....
"Kai tsaye bayan sun gama gaisawa IG ya tambayesa "How may I help you young man.
"Without any hesitation Jalal yace " Sir I came to confess...
"Kalllonsa yayi da kyau kafin ya kuma tambayarsa, kai tsaye Jalal ya kuma nanata masa... In details Ya fad'i komai bai b'oye ba mai d'aukan rahoto bisa computer Ya rubuce komai.
"Inspector yasha mamakin abun sosai, don kuwa babban mutum a k'asa irin Kasim Dasuki bai zaci zai yi haka ba, koda yake mutane for their children babu abunda bazasuyi ba...
"Kallon Jalal yayi da kyau kafin yace " Mr Jalal I've heard your confession and zamu rik'e Ka a nan, but before muyi arresting sauran sai ita victim d'in tayi magana you understand what I mean say tayi filing complaint..
"Intercom ya danna kafin wani Sargent ya shigo ya fita da Jalal...
"Annah tasan halin d'an nata idan yayi fushi tasan kalan zuciyan Jalal, sai iya shafe sati ba tareda sun gansa ba, lambarsa ta shiga nema,
"Sargent d'in da ya d'auka ne ya sanar da ita Jalal na police station. Ai tuni Annah ta mik'e tsaye tana tambayarsa me ya kai d'anta police station, Kai tsaye Sargent d'in ya mik'a ma Jalal wayan...
"Cikeda tashin hankali ta soma magana, Jalal, me kayi aka kama ka, me ya faru......
"A hankali yace " Annah ki kwantar da hankalinki ni na kai kaina, I confessed everything,
"Annah ta nanata a fili daidai sanda ta juya taga Zubaidah ta mata k'uri alamun tana saurarenta... Da sauri ta k'araso tana fad"im Annah Dan Allah barin masa magana, tana maganan cikin rawan murya zuciyarta cike da takaicin kanta don kuwa ita tayi provoking d'insa.....
"Pls come back home, dan Allah ka dawo I promise bazan sake ba, kaji but pls don't leave me all alone by my self..... Abunda yaji knn cikin kunnuwarsa wanda ya kasa gasgatawa.
"Damk'e wayar yayi sosai kafin ya soma fad'in" I'm doing this for us to live in peace, all I want from you is to talk, don't remain silent, File a complaint against your enemies, don't let them get away with it, kiyi magana kiyi magana, talk kinji babu rufarufa from this very moment, let the whole world know the truth, let us get what we deserve, kinji... Pls talk.
"Kaman na ganinta haka take nodding kanta tana hawaye take fad'in" I'll talk Right away, I'll speak up, kaji, you'll be safe and you'll be free..... Kuka ya kuma kufce mata, Annah ce ta karb'i wayan ta tambayesa station d'in da yake......
****************
"A hankali ta turo k'ofar d'akin har lokacin zuba kaya yake cikin luggage d'insa, dafasa mum tayi kafin tace " Tariq da gaske tafiya zakayi ka barmu, Tariq you are our only son bazan iya jure rashinka ba.....
"D'an jefar da rigar hannunsa yayi ya d'ago yana dubanta kafin yace " Oh com'on Mum do we have to talk about it again, bazan iya ci gaba da rayuwa a nan bar, I need a change of environment Mum, I need to forget everything that happened here, I need to start a fresh....
"D'an goge hawayen idanunta tayi kafin tace " Zan ringa visiting d'in ko yaushe, ..
"Murmushi yayi gamida hugging d'inta da hannu d'aya cikin arms d'insa kafin yace " Bazaki iya visiting d'ina ko yaushe ba, munyi nisa, Moscow da nan akwai nisa sosai Mum, all I can say you'll always remain here.... Ya k'arashe yana nuni da k'irjinsa ma'ana heart d"insa... Murmushi ta sakar masa itama ta rungume sa sosai... Sa hannu yayi ya share mata hawayen idanunta...
"Tayasa arranging kayan taci gaba dayi, sunayi suna hiran sanyin da zai tarar a Moscow, nan ta tambayesa ko zaije dinner d'in da Kausar ta had'a anjima..
"D'an jimm yayi kafin yace " I'm not so sure coz flight d'ina da safe ne so banson nazo ban tashi da wuri ba...
"Shafa kansa tayi tana fad'in" No excuse you are going, at least kayi sallama da kowa.... Zaiyi magana ta d'aura hannu bisa lips d"insa tace" Final you are going na gama magana....
"Murmushi yayi kana yace " Alright Mum just because you insist, that's my boy ta fad'i sanda take zipping jakar....
"Around 7:00pm ya nufo stirs d'in Mum don jin kota shirya su tafi tare, wayan da yake jiyowa daga d'akinta yasa gabansa ya yanke ya fad'i.
"Mum taci gaba da fad'in" Haba Barr Munir na fad'a maka zanzo zanzo , idan Tariq ya tafi ma mun huta had'uwa a hotel coz gobe zai tafi, tayi wani dariya kafin taci gaba da fad'in" Haba kar ka damu alak'armu bazata Tab'a yankewa ba don bazan tab'a bari Alh Maina ya sani ba.....
"Bibbiyu Tariq ya soma gani, ya kasa gasgata abubuwan da ya gama ji, cikin sauri ya juya ya sauk'a k'asa, kai tsaye motar sa ya nufa ya fice a guje, fuskar Barr Munir kawai yake hangowa, shi kad'ai yake huci yake fad'in" I'll kill that Bastard with my very own hands.........
*At the company*
" Salim Ya kuma duban Labib kafin yace " Hey stop being so stubborn, dalla ka tashi mu tafi, kaifa mugun D'angelo iska ne, you wai uwar Me zaka tsaya yi ko anan zaka kwana ne.
"Da wutsiyar Ido Labib ya kallesa kafin yace " Do I always have to explain my self, nace maka bazanje ba fine, ka tafi mana abunka...
"Rufe laptop d'in gaban Labib Salim yayi yana wata murmushi yake fad'in" Hey your crush is gonna be there too, Asmah I'm pretty sure tana chanma probably helping Kausar, com'on don't be stubborn tashi muje.....
"Hararansa kawai Labib yayi kafin ya mik'e yana zungurin k'eyarsa yace " You such a jerk you know....
'Dariya Salim yayi yana fad'in whatever.... Dariya kawai Labib d'inma yayi kafin suka nufi lift suka sauk'o k'asa.
"Dukansu motar Salim suka shige, Labin yayabawa wani security car keys d'insa yace ya kaimasa gida....
"Suna fitowa k"ofar company d'in motocin police , cike da tashin hankali suke bin polisawan da kallo, guda d'aya ne ya fito ya nufi motarsu... Tuni suka bud'e motar..
"Cike da gadara Labib yake fad'in" Lafiyanku wa kuke nema snn bakusan nan company bane, and idan wani kuke nema working hours zakuzo ba yanzu ba... Police biyu Suka fito,
"I'm Detective Amir you need to come with us to the station..
"Sai snn Salim ya fincike marfin mota ya fito yana fad'in" Officer what the heck are you talking about, you can't arrest us just like that, besides meyasa zamu biku station...
"Idan munje chan kwaji bayani ya fad'i sanda ya kalli Sargent biyu yace ARREST THEM , No... No you can't do this to Us, kunsan su waye mu, kunsan mu 'ya'yan waye.. You will all regret this, you doing this to loose your job.... Salim ya fad'i sanda yake kallon securities d'in company d'insu yace" Call my Dad right away.....
"Haka sunaji suna gani aka tasa k'eyarsu.....
*At Salem's House*
"Su Daddy da Pappy suna parlour suna hira, akasarin hiran kan business ne da kuma forthcoming election, Alh Kasim yana bawa Alh Tahir shawarwaei kan garuruwan da ya kamata suje convention su kuma gudanar da Rally....
"Mummy da Mumsy suna k'aramin parlon Kausar suna nasu hiran, yayinda Kausar da Asmah da ma'aikatan ta guda biyu suke zarya daga kitchen zuwa makeken dining area d'inta wanda table d'in ke d'auke da kujeru goma sha bbiyu...
"Barr na waje yana amsa kiran da aka masa cewa anyi arresting su Salim, kaman daga sama yaji sauk'ar naushi a kumatunsa sa saida wayar ta tarwatse a k'asa, cakumosa Tariq ya kumayi yana fad'in" I'll kill you, you Bastard....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:22] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
51
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Kaman Allah ne ya aikosa haka yake dukan Barr Munir da iya k'arfinsa.... "Hankulan securities masu tsaron Gate ya tashi cikin sauri suka nufi cikin gidan suka sanar dasu don sun kasa dakatar da Tariq da irin dukan da yake ma Barrister..
"A sittin suka fito gaba d'ayansu hakan yayi daidai da isowan su Mum d'in Tariq da Dad d'in sa...
"Su Mumsy su Mummy Kausar da Asmah gaba d'aya suka daskare suna kallon wann ikon Allah...
"Alh Tahir da Alh Kasim suka yi kansu suna rirrik'e Tariq..
"Fuzgewa yake yi yana fad'in "Let go of me, let me go.... Let me kill this Animal.... Alh Kasim ya janye Barr yayinda Alh Tahir ke rik'e da Tariq...
"A tamanin Su Mum d'in Tariq suka fito daga mota suka nufo su....
"Da gudu tayi kansa tana fad'in" Tariq my Baby Me ya faru....
"Idonsa na zubda hawaye yake nunata da yatsa yaci gaba da fad'in" Don't you dare come near me, you have no idea how shameful it is being your son.... You are disgusting, I can't believe you're his mistress. Na tsaneki na tsaneki snn ke ba mahaifiyata bace.
"Juyawa yayi ya kalli Barr dake zaune shame shame a k'asa fuska duk jini yace" I'm not done with you, you miserable coward, sai na kashe ka har lahira Worthless imbecile... Mark my word.... Cikin sauri ya nufi motar sa yana haki....
"Kallon k'yama da mamaki Alh Maina ke watsa wa Mum d'in Tariq dake tsaye tana zuban hawaye.... Jin yanda Tariq ya kwashi motar yasan komai ka iya faruwa yasa sa saurin shigewa motarsa yabi bayan d'ansa....
"Gaba d'aya jikkunansu sunyi sanyi babu kaman familyn Kausar, this is a disgrace, ace uncle d'in Inlaw d'insu ne wann, Mum d'in Tariq jiki a sanyaye ta fice daga gidan cike da kunya da nadama...
"Mummy da Daddy suka ja Barr suka nufi guestroom dashi, yanda take shiga bata nan take fita ba, yanda kasan ba yayanta ba haka take tsefe sa,
"Ka rasa wa zaka nema sai k'awata kuma matar aure, matar abokin mijina uwar abokin d'ana haba haba gaskiya nidai baka kyauta min ba ...
"Daddy ne ya shiga lallab'anta yana nuna mata kuskurene da sharrin shed'an Amma he can fix this taje taji da bak'i...
"Mummy ta kuma narka masa harara kan nan nasa a k'asa kaman munafukin k'adangare, bai iya furta komai... Tsaki tayi ta fice fuuu tana tunanin da wani ido zata kalli Haj Raliya Mum d"in Kausar....
"Mummy tana fita Alh Kasim ya matso kusa dashi kafin yace " Kayi kuskure yaya zaka nemi wacce you are somehow closed to her family, ai idan zakayi bariki waje zaka fita ka nema, kaga yanzu ga abinda ya haifar, me kake tunanin Alh Tahir zai d'auke mu, Irresponsible mutane ko me??? ....
"Dafe kansa yayi gamida buga uban tsaki yana goge jinin bakinsa kafin yace " Ai wann Me sauk'i ne kan abinda zan fad'a maka...
"Police arrested Salim and Labib, wayan da aka mun kenn ana gaya mun kafin d'an iskan yaron nan ya iso, nasan shima the cops are after him Allah sa su capke shege.....
"Wait. Wait.. Wait..... Daddy ya dakatar dashi da fad'in haka, kafin yaci gaba da fad'in" Kana nufin kace " An kama only son d'ina....
"Galala Barr ya kallesa kafin yace " Me yasa basu iso ba har yanzu, for your information your precious little boy is spending the night in a jell....
"Mik'ewa Daddy yayi yana girgiza kai yake fad'in" k'arya ne wann, babu wanda ya isa ya kulle mun d'ana, tashi maza ka tafi, you are their lawyer, kar ka bar wani shege ya tab'a mun lafiyan yaro..
"Mik'ewa Barr yayi yana goge hancinsa mai zuban jini yake fad'in" Yarinyar nan ta b'allo ma kanta aikin da bazata iya ba.... Turasa k'ofa Daddy yayi yana fad'in" Just go I'll take care of the situation here....
"Duk sunyi jigum jigum a parlor suna jimamin abinda ya faru, kowa da kalan tagumin da ya rapka, suna hango Daddy Kausar ta mik'e tana fad'in" Daddy ina Salim he should be here by now, me ya hanasu isowa har yanzu.....
"Jim Daddy yayi yana duvansu kafin yace " ..... The girl..... Shiru yayi sakamakon k'irjinsa dake bugawa,... Dakewa yayi yaci gaba da fad'in" The... Girl Filed a charges against them. An tafi dasu police station...... Ai bai gama rufe baki ba Kausar ta Saki wani irin k'ara gamida zubewa k'asa, cikin sauri Mumsy da Asmah suka rik'eta....
"Kuka take tana fad"in" Na sani na san ba k'arya take mun ba, kune mak'aryata macuta mayaudara azzalumai kuka bari na auri criminal son d'inku...... Pappy ne ya dubi Mumsy da Asmah yace su haura da ita sama...
"Fuzgewa Kausar ta kumayi ta k'araso gaban Mummy tana watsa mata mugun kallo take fad'in" Aren't you going to say something Haj Farha, kiyi magana mana Ashe kinsan d'an iskan d'anki rapist n....... Bata kai aya ba Pappy ya d'auketa da wani wawan mari..... D'agowa Kausar tayi tana dubansa cike da mamaki tun tasowarta ko zunguri bai tab'a had'ata da mahaifinta ba sai gashi yau ya mareta... Cikin kuka dafe da k'uncinta take fad'in" Pappy you shaped me because of these worthless people.... Da k'arfin gaske ya kuma fad"in " Raliya I said take her up stirs...
"Mumsy da k'walla ya ciko idanunta da sauri ta shiga jan Kausar Asmah na tayata suka haye sama d'akin Kausar.
"Mummy jiki a mace take kuka ta nufi balcony...
"Wani mugun kallo Alh Tahir ke watsa ma abokin nasa kurum...
"Daddy ya d'an fuzar da iska kafin yace " I guess we need to talk, babu musu Alh Tahir yabi bayansa suka koma cikin parlorn suka zauna....
"Bud'e baki Daddy yayi zaiyi magana Alh Tahir ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu kafin ya soma fad'in" No more lies Alh Kasim, just go straight to the point and tell me the exact truth.... In a furious tune yayi maganar....
"Sauk'e ajiyan zuciya Daddy yayi kafin ya soma 'yan kame kame....
"Ai Mr President kasan halin yaran yau, kwata kwata basa jin magana, duk iya k"ok'arinka na ganin ka wadata su sai Sun sab'a kasan yar..... Da wutsiyar ido kawai Alh Tahir ke kallon Alh Kasim kafin ya d"aga masa hannu alamun dakatarwa yace " Mr President go straight to the point, Did they commit the crime or not..???
"Tura hulansa baya yayi kafin yace " Yes the Did, but...but....
"Period abinda nake son ji kenan, cewar Alh Tahir Marafa kafin yaci gaba da fad'in" Ban tab'a zaton amincin dake tsakaninmu zaisa ka rufa wann babban laifi da d'anka ya aikata ba ka bari na aura masa tilon 'yata, ka bani kunya Alh Kasim.
"Cikin sauri Daddy ya soma fad'in" Yaran nan yara ne, kuma ita yarinyar mun wadatasu da kud'i rashin godiyar Allah ne yasata maka k'ara....
"Jinjina kai Alh Tahir yayi kafin yace " Yanzu na gane cewa kai wani irin mutum ne, na d"auko dukiyata na zubata a company d'inka snn na d'auki only daughter d'ina na Aura ma d'anka.... For your information I'm taking all my money I mean all my shears out of the company, I don't want you to drag me and my family into this mess of yours.....
"K'ok'arin mik'ewa ya soma Alh Kasim ya k'arasa ya dafe kafad'arsa kana yace " You already in the mess kar ka mance d'ana na auren 'yarka snn if you are thinking sabida siyasarka zaka yanke alak'a damu then you are mistaken sabida you can't go anywhere without us, Alh Tahir you perfectly well know Me, kasan kalananyan mutanen da nake dasu a k'asar nan, kasan I can ruin you, your carrier in politics and last your Reputation, so ina mai baka shawara just back down, muci gaba tunda kaima ka shigo cikin mess d'in....
"Buge hannunsa Alh Tahir yayi kafin yaci gaba da fad'in" Your criminal son must divorce my daughter don ban haifa mata ma criminal irinsa ba, snn da kake maganan you can ruin me, fine go ahead, abu guda ne nasan bazan bari ka lalata mun ba shine Reputation d'ina, you can go ahead and ruin my carrier in politics but I'll not allow you to ruin my reputation a idanun duniya kaman yanda naka sunan yake gab da b'aci..... Daga haka ya fice cikin sauri yana sab'a babbar riga, gaba d'aya ma ya mance dasu Kausar.....
"Kallo Daddy yabisa dashi har ya fice, da k'arfi ya daki garun parlorn da yasha ado da golden wallpaper yana fad'in" Damn it dammit...... I'll not allow you to bring me down you filthy mere girl....
"Mumsy wllhi sai na bar gidan nan, ko kwana bazan kumayi ciki ba, snn wllhi dole Salim Ya biyo ni da takarda na ko na maka sa a kotu, ..... Ta k'arashe tana jefa kaya cikin trolley d'inta, Asmah dai tama rasa wanne zatayi, haka suka had'u ita da Mumsy suketa faman lallashin Kausar..... Ana haka Mummy ta turo k'ofa tana k'ok'arin shigowa jiki a sanyaye uwa munafuka..... Harara kawai Kausar ke b'alla mata sabida duk sun san gaskiya suka take....
"Mik'ewa tayi tana fad'in" What are you doing here, kin karb'o mun takardan Saki na ne ko me..??
"Cike da b'acin rai Mumsy ta daka mata tsawa gamida zaunar da ita, bana son rashin hankali Kausar, kina shaye shaye ne kike fad'a wa manyan mutane maganganu irin haka, especially uwar mijinki.....
"Cikin kuka Kausar take fad'in" Mumsy wllhi ni ba uwar mijina bane, wllhi sai ya sakeni....
"Kallon Asmah Mumsy tayi tace " Rik'eta ku sauk'a k'asa ina zuwa,.. Gyad'a kai kawai Asmah tayi kana ta rungumo Kausar suka nufi downstairs....
"Mummy ta Kalli Mumsy jiki a mace, da k'yar ta iya bud'e baki da niyyan magana, Mumsy ta dakatar da ita...
. "Haj Farha I know you must be having a hard time, but inaso ki sani dukanmu muna cikin tashin hankali a yanzu, ban zaci zaki iya manipulating d'ina haka ba, claiming to be my friend, ta yaya zaki bari Yata ta auri criminal bayan kinsan mafarkin ko wata uwa 'yarta ta kasance cikin auren soyayya da kwamciyar hankali, my daughter is suffering, tunda muke da Kausar bata tab'a zama maras kunya ba sai yau, ko da yaushe cikin obeying d'inmu take, kema shaida ce, dole ma abin yayi affecting d'inta, ta yaya zakiji ace ga mijinki ana shari'a dashi ya aikata babban laifi irin fyad'e, ko ke da kike mahaifiyarsa abun bazaiyi affecting d'inki kaman matarsa ba, abu guda da zai dameki shine rashinsa da zakiyi muddin aka jefasa gidan yari, So pls kar ki soma tunanin zan lalashi Kausar tayi zaman gaibu da d'anku, snn kema mace ne, ko baki haifi d'iya mace ba, kiyi tunanin irin k'uncin rayuwar da yaranku suka jefa wancan yarinyar a ciki, iyayenta wani hali suke ciki, ni Mace ce kuma mother of Mace, Ni dai abunda zan iya cewa Allah shi karb'a wa mai gaskiya hakkinsa.. Snn maganar auren Salim da Kausar dole a datsesa.. Daga haka Mumsy taja akwatin Kausar ta nufi k'asa rai b'ace...
"Mummy kam kifa kanta tayi bisa gado ta shiga rusa kukan abubuwan takaicin da suka sameta a yau...
"Cikin tsananin tashin hankali Dad d'in Tariq yaci gaba da suka gewaye motan yana fad'in call an ambulance.... Cikin mintoci kankani ambulance ta iso aka saka Tariq da ya kwankwatse a mota aka wuce dashi emergency
***************
*Gombe, Palace*
"Kai tsaye parlorn mai Martaba Babban gwani ya nufa, he's looking tired and exhausted, bisa ga alamu bai jima da shigowa garin ba...
"Tundaga waje fadawa ke masa kirari,
"An gaisheka Shattima, Sallama ya gaisheka, Madawaki ma gaisuwa yake, An gaisheka D'an Wazari badad'in Mai Martaba, ...... Gyad'a masu kai kawai yake yana mai ci gaba da tafiyar sa, yana isowa k'ofa Shamak'i ya basa hanya yana gaishesa yana fad'in" Shiga cikin aminci baka da Shamak'i....
"Zaune ya taddasa da shalelensa Zahidah... Da sallama kai a k"asa cike da ladabi irinta babban gida Shattima ya shiga wargajejen parlorn.... Rusunawa yayi yana mai mik'a gaisuwarsa ga mai Martaba, Ta k'asa k'asa Zahida ke kallonsa tana tunanin yaje yaga sahibarsa Zulaihat... D'an satan kallonta shima yayi sanda ta mik'e tana gyara alkyabbanta ta rusuna tace " Abba na barka lafiya. Murmushi yayi kana yace " Allah Ya sada mu da Alkhairi mamata... Ficewa tayi Shattima ya d'an biebayanta da kallo don baiso Mai Martaba ya Kula kallon Zahida yake, juyowan da zaiyi ya sauk'e idonsa kan makeken hoton babyn nan, gabansa ya yanke ya fad'i sakamakon hango fuskar Jalal da yayi cikin hoton.....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:23] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
52
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Har lokacin ta kasa saka komai a cikinta, hawaye na kan zuba a idanunta, Allah sarki Jalal koda ace yayi raping d'inta Ya cancanci yafiyarta balle ma ta yarda dashi tasan iyakar gaskiyarsa knn beyi ba, sa bayan hannunta tayi ta goge hawayen, Kamal ne ya matso kusa da ita kana yace " Didi wai inji Mama na uncle Jay bazai tab'a dawowa ba wai kullesa za'ayi...
"Wani hawayen ta kuma gogewa kafin tace " Zai dawo zai dawo garemu, idan kayi sallah ka ringa masa addu'a kaji.. Gyad'a kansa yaron yayi fuska fal damuwa kafin yace " Ina sonshi bana so ya tafi ya barmu... Kema kina sonshi ko Didi... Wani sabon kukan ya kufce mata, batasan sanda ta shiga nodding kanta da sauri ba gamida jawo Kamal ta rungumesa...
"Annah dake hangosu daga veranda ta goge k'wallan da suka cika idanunta....
"Cell d'in gefe da Jalal aka jefasu, ... Salim fad'i yake Officer you can't arrest us just like that, you've no clue who you really messing with...
"Labib kuwa hango Jalal yayi, fincikian k'arfen ya shigayi yana fad'in" This is all your fault you Trader, I swear I'm gonna make you pay for this,.... " Da k'arfi Jalal ya mik'e yana fad'in" Shut your Trap you criminal....
"Labib ya kuma watsa masa harara kafin yace " You're nothing but a Trader, how dare you betrayed us, bari kaga na fito daga wajen nan sai na sata ta k'aryata abinda ta fad'i......
"Naushin da Jalal ya kai masa ta cikin k'arafunan Ya hanasa k"arasa maganar,
"You Imbecile ka gama maganganunka akaina but the moment ka sake wani magana akan matata sai na kashe ka. Bas... tard..... Ya fad'i sanda yake komawa wajen zamansa...
"Janyo Labib Salim yayi kafin yace " K'yalesa kasan tsiyan talaka abinda ya gada knn, 'cause bai gaji arziki ba, we are getting out of here soon, and we will take our revenge.
"Zama kawai Labib yayi bisa benchin yana goge jinin bakinsa yana watsa mugun kallo wa Jalal...
***************
"A ranar da suka cika kwana biyu aka fito dasu za'a canza masu cell, gaba d'aya families d'in sun had'u a station harda Mamin Labib data riski labarin gangaratsau....
"Babu yanda Barr beyi ba akan abada belin su IG ya hana yace sai an shiga kotu sati mai zuwa duk abinda alk'ali ya yanke fine.. Coz bashida say a yanzu tunda ta shigar da k'ara..
"Hannayensu cikin handcuffs aka fito dasu, su mummy da Mami Me zasuyi banda kuka,..... Salim girman carpet da Ac jikinsa har wani daddaujewa yayi, jajazur kaman me borin jini a d'an kwana biyun da yayi cikin cell....
"Mummy Daddy pls take me out of this place, I can't stand it, pld Dad do something, don't let them take me away.... Haka Salim ya ringa fad'i polisawa na turasa suna fad'in move..
"Labib kuwa da taurin zuciya sai k'arfafa gwiwa wa Maminsa yake..
"Barr ne ya fito yana fad'in" Kar ku damu zanyi komai wajen tsaya maku... Uncle pls do something.. Salim Ya kuma fad'i...
"Kausar bata bari Asmah ta gama parking ba ta bud'e motar ta isa gaban Salim tana fad'in" You liar this is where you belong, make sure ka rubuta min takardan sakina....
"Kausar my love pls don't believe her, she's just lying... Bai kai aya ba Kausar ta kuma fad'in" Just shut up you imbecile, I'll give her my unconditional support, until I see you locked up in jell... Asmah ta shiga jan Kausar baya ganin Journalist sun cike wajen sai d'aukan rahoto suke, sai faman d'aukan fuskar Kausar suke yanda take zuba masifa ma Salim...
"A kunnenta Asmah take rad'a mata Kausar let's get out of here, kinsan su Pappy basu san mun fito ba, zasu k'ara fushi sosai tunda an hanaki fita... Kan su ankara sai ganin abokan aikinta Journalist wa'enda basa good terms suna d'aukanta suna fad'in" Mrs Salim Dasuki da alama kema baki bayan mijin naki knn da gaske ne kema kin yarda ya aikata laifin da ake zarginsa ko kuma dama wann hali d'abi'Anas....... Jawo mayafinta Kausar tayi ta shiga rufe fuskarta tana tutture Jama'a tana neman hanyan fita daga wajen....
"Daidai sanda aka bud'e masu motar masu laifi adaidaitan su Zubaidah ya paka a wajen itada Annah...
"A guje ta fito gamida k'walla masa kira da k'arfin gaske " JALAAAL, a hankali ya furta Zubaidah, saurin juyowa yayi sukayi ido hud'u gaba d"aya mutanen dake wajen kallo ya koma kanta.... Gefe da ita ya hangi Umar ya paka motarsa ya fito....
"Fincika yayi da k'arfin gaske yana fad'in" Don't come near my wife, don't you dare come near her, I swear I'll kill you.... Gaba d'aya kallo ya kuma komawa kan Umar....
"Gaban Zubaidah yayi wani irin yankewa Annah ta rik'eta sosai tana fad'in" Kar ka damu Jalal, I'll look after her for you, I'll take care of her...
"Just take care of yourself son...
"pls Annah do that for me, ki kular min da ita....
"Cikin kuka Zubaidah take fad'in " Don't worry I'll be safe, promise me you'll come back to me....
"Siriryar hawaye ta fito daga idanunsa sanda ya furta I love you.... Kafin ya shige bayan motar....
"Hanki d'in hannunsa kawai take hangowa har motar ta wuce....
"Annah tayi saurin rik'ota suka nufi adaidaitansu sanda Journalist sukayi chaaa akanta suna jefo mata tambayoyi.....
"Alh Kasim ya kafe Umar da ido kafin ya sunkuya saitin kunnen Barr yace " I thought we made it clear to that idiot that he should get lost, what heck is he doing here??
"Barr kuwa wata murmushi ya Saki kafin yace " Zai mana amfani, bai jira cewar Alh Tahir ba ya saci idon Jam'ma'a ya nufi motar Umar, zama yayi a Front seat yana fad'in " Keep driving...
"Galala Umar ke kallonsa kafin yace " Ban gane ba ina zan kaika,...
"Gajeren tsaki Barr yayi gamida fuzar da iska kafin ya kuma fad'in" Don't be such an idiot just keep moving.
"Karya staring mota yayi kafin suka mik'a titi.....
***************
"Tunda suka soma tafiya hankalin Annah ya karkata kan tunani guda, ina zasu samu lawyer wani lawyer ne zai tsaya masu, kai komai na duniyar yanzu ma saida kud'i yaya zatayi....
"Hannun Zubaidah taji cikin nata, tayi saurin d'agowa tana kallonta,.
"Murya na rawa take fad'in" I'm sorry Annah, believe me nima bana son ganinsa cikin wann halin, da nasan zai tafi police station da banyi provoking d'insa ba.....
"Damk'e hannunta sosai Annah tayi tana girgiza kai kafin tace " None of this is your fault Zubaidah, abinda Jalal yayi yayi daidai, let them all be punished, sun zalunceki, they shouldn't get away with it, Allah yana nan baya bacci da sannu zaibi kadin mai gaskiya...
"Babban abinda ke gabanmu a yanzu shine samun lawyer.... D'an jimm Zubaidah tayi kafin ta d'ago da sauri tana fad'in " Dr Khaleesat,.... We should talk to her right away maybe she can help....
"Shiru Annah tayi tana dubanta tana nazarin maganan nata kafin tace " Dr Khaleesat tana mana k'ok"ari I don't want us to be a burden to her...
"Damuwa ya kuma nunawa a fuskar Zubaidah, shiru tayi ta shiga wani tunanin daidai lokacin da mai tasi ya ajiyesu....
"Da mugun mamaki suke kallon motar dake pake k'ofar gidansu, k'irjinsu ya yanke ya fad'i lab'ewa bayan Annah Zubaidah ta soma tana fad'in" Annah bazasu tab'a k'yalemu ba na sani....
"Annah ta rik'e hannunta sosai cikin nata tana fad'in" Kar ki damu babu abunda suka isa su mana, muje...
"Kausar tana hangosu tayi saurin fitowa a motar, ganin Kausar ya basu mamaki, take Zubaidah ta had'e rai tana fad'in" Me kike nema a nan, me ya kawo ki nan, kinzo ne ki kuma k'aryatani kaman yanda mak'aryacin azzalumin mijinki yayi, idanma kinzo sayan mu da kud'ine kaman yanda kuka saba toh ki sani bakuda arzikin da zaku sayemu... We won't back down. Justice must be served.....
"Annah ta dubi Kausar kafin tace " Kinji da kunnuwanki toh tun wuri ki tafi kafin muyi filing retraining order against you....
"Rik'ota Asmah ta soma tana fad'in" Mu tafi Kausar....
"Kausar ta soma girgiza kai cike da tausayi kafin tace " Kar kuyi tunanin ina tareda su, wllhi bana tareda su, nima babban burina shine na gansu behind bars, hawaye ya soma zuba a idanunta sanda taci gaba da fad'in" Auren Salim shine babban kuskuren da na tapka, ta rik'o hannayen Zubaidah duka biyu taci gaba da fad'in" I'm here for you, I want to help I want them to be punished, pls don't push me away, let's do this together.....
"Girgiza kai Zubaidah ta soma kafin tace " Pls leave we don't want more trouble, idan suka san we are seeing each other, things might get more complicated.
"Annah ta gyad'a kanta tacee" Haka ne Kausar, kinga family d'inku are related Don Allah ku tafi kafin ku b'allo mana wani abun...
"Goge hawayen idanunta tayi kafin tace " They will never find out,... Kun sami lawyer ne..?? Ta tambaya tana dubansu..
"Shiru kaman babu me cewa komai cikinsu Annah tayi murmushi tace " Kar ku damu zamuyi komai cikin talaucinmu Ko bamuda kud'i do mulki munada Allah, da sannu zai kawo mana mafita, snn abu na k'arshe dan Allah kuyi nesa da gidan... Mun gode k'warai da kulawarku.. Daga haka taja hannun Zubaidah suka shige gida...
"Asmah taja hannun Kausar suka shige mota..
"Suna tafe Asmah ta d'an juyo ta dubeta sanda take karya Stairing mota kafin tace " Kausar I think they are right, we shouldn't be creating more problems, the Dasukis have eyes everywhere, they might be watching all our movement especially now that we are against them....
"Harara Kausar ta galla mata da rinanaun idanunta masu zuban ruwa kafin tace " I don't care, they can do their worse but I swear I won't back down har sai na gansu cikin k'unci da damuwa like the way they caused me , I want to see them suffering, I want to see them going down.... Ta k'arashe maganar tana huci ita kad'ai.....
"D'an sauk'e ajiyan zuciya kawai Asmah tayi gamida maida hankalinta ga driving....
"Suna gama parking a haraban gidan suka hango Pappy daga saman balcony hannayensa hard'e a k'irji ya kafesu da ido fuskan nan tamau.. K'irjinsu ya soma dukan uku uku......
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:23] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
53
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*Where are you Bintu Abiha and Habiba love... This one's for you guys, I read your chats jiya and nasha dariya sosai sosai oo 😂😂... 😍😘*
"Sosai Pappy Ya masu fad'a Mumsy ma fad'an tayi masu sosai, Harta car keys d'insu saida ya karb'e yace " No should drive again har sai komai ya lafa....
"Kafin dare an soma yad'a abinda Kausar tayiwa Salim a social media 'yan adawan siyayasan Pappy abu ya masu Dad'i..
"Shiru yayi gamida k'ura ma Video d'in ido, yasan wann kad'an ne da aikin Alh Kasim, he promised to ruin him completely, kan kace me party chairman d'insu ya kira urgent meeting akansa, a halin yanzu ana gab da amshe ticket d'insa na presidential election....
"Zama yayi yana nazarin kalaman Barr.
_We want you to testify against Zubaidah in court_
"Zulaihat ne ta zauna gefe dashi gamida rungumo kansa cikin k'irjinta tana wani mayaudarin murmushi. Gani tayi gaba d'aya hankalinsa baya tare da ita, d'an rik'o kumatunsa tayi kafin tace " Hey what's the matter, meke damunka....
"Sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin yace " Zubaidah Filed a complaint...
"Zama da kyau Zulaihat tayi kafin tace " So, meye naka na damuwa ka kyalesu suci kansu...
"Shafa fuskarta yayi kafin yace " Kin tuna nace maki you'll help me to get my revenge on them ita da mijinta....
"D'an jim Zulaihat tayi kafin tace " We are living a happy life nida kai bana so muyi engaging kanmu cikin wani matsala...
"Mayaudarin murmushi yayi kafin yace " No matter what I'll never leave you alone, just help me do this kinji baby na.
"Ganin tayi jim tana dubansa yasa kamo kugunta sosai snn yaci gaba da fad'in" Pls Baby do this for me ko baki son ganin farin ciki na ne,
"D'an tab'e fuska tayi kafin tace " Toh me zaisa ka damu dasu bayan yanzu haka ma cikin tashin hankali suke...
"Wata murmushi ya kumayi kafin yace " Idan naga ta rabu da Jalal har abada zaifi komai yi mun Dad'i, snn na maki alk"awari bazan koma mata ba, kinsan ina sonki, as they say, if they love you they will come back to you, kinga da na tafi ai na dawo gareki meaning I can't do without you, so iyaka abinda zaki iya mun shine ki taimaka min na d'au fansan abinda aka mun...
"Murmushi Zulaihat tayi kafin tace " Toh how may I help you,
"Shafa low cut askinsa yayi kafin yace " Zubaidah spent a night here with you, meaning ta gudo daga Chan gidansu, I want you to give your testimony in court...
"Da mamaki Zulaihat ke kallonsa kafin tayi magana yace " this is all I'm asking of you my love, I'll explain everything to you later. Yanzu barin mana placing order ina zuwa, daga haka ya mik'e ya fice yana neman layin Barr Munir...
*************
"Tun daga k'ofar abisitin tasha jinin jikinta, kamar wacce k'wai ya fashe ma a ciki haka take tafiya..... Ai tun daga k'ofar ward d'in da ya hangota ya mik'e yana fad"in " Kar ki k'araso nan, kar ki kuskura kiyi gigin zuwa kusa da d'ana kije wajen d'an iskan sairayin naki tunda mun baku space sosai yanzu a gidan, but don't you dare think of coming closer to my son...
"Mum rakub'ewa tayi jikin garu tana kuka.... Daidai nan cops suka iso, Alh Maina ya mik'e da sauri yana fad'in " Lafiya officer..
"Guda d'aya daga cikinsu yace " Lafiya Sir, muna nan ne don tsaron d'akin da d'anka yake
...
"No.. No Officer you can't do this, my son isn't out of comer yet, idan ya ganku hankalinsa zai kuma tashi...
"We are sorry but we are only doing our job..You there you over there.... Haka ogan nasu ya jejjefasu kowa da wajen da ya tsaya.....
***************
"Yau ya rage saura kwana uku a shiga kotu gashi basu sami lawyer ba, gashi Dr Khaleesat bata nan ta tafi wani seminar a Lagos, gaba d'aya abu ya rincab'e masu, Gashi tun baya kama su Jalal Usman bai lek'o ba, Annah har garejinsu taje bata sami Usman ba, abokan aikinta na makaranta ma ta baza cikiya neman good lawyer, amma kunsan mutum a yau komai saida abin duniya... Zubaidah kullum cikin kuka take, Ga Hadiza ta sakata gaba da tsangwama tana cewa laifinta ne, datayi hak'uri da Jalal bai kai kansa ma polisawa ba, kuma wllhi ta zama bazaura bazata zauna da ita ba, tayi d'awaiyinyarta tun k'uruciya bazatayi har zauwarci ba....
"K'unci ya taru ya mata yawa, kullum cikin addu'a da neman taimakon Allah suke.....
***************
"Asmah pls, wllhi nasan basu sami lawyer ba, you know how people are nowadays,.....
"Ajiye littafin hannunta Asmah tayi kafin tace " For crying out loud Kausar me kuma kike so nayi, kina ganin irin fad'an da aka mana da irin dokar da aka sa mana a gidan nan, me kike so nayi, na gaji da taro mana damuwa da kike yi....
"Tasowa tayi daga saman gadon kafin tace " Kina zuwa school kina samun Chance na fita, that's why I'm asking you to do this, don Allah ki samar masu lawyer I'll take are no fun his bills all I want is for justice to be served, Asmah kema fa mace ce, kuma kar ki manta ciwon d'iya mace na d'iya mace ne, it could happen to us, zamu iya zama Victims muma, pls Sis let's do this.....
"Shiru Asmah tayi kafin tace " You are absolutely right, but abun da muke niyyan yi yanada matuk'ar had'ari ba garemu kawai ba harda family d'inmu, idan suka sani zasu sa wa pappy harma damu takunkumi, kiga videos d'in da suka watsa suka sa aka dakatar da pappy a jamk'iyarsu, what if they find out we are helping her, things might get worse...
"Kausar ta goge hawayen idanunta kafin tace " Na sani, kar ki damu akwai Allah bazai barsu suyita zalunci ba, let's do it...
"Asmah ta rik'e hannunta sosai kafin tace " Zanyi zanyi Kausar sabida ina son ganin murmushinki randa aka jefa Salim a prison. Rungume juna sukayi suna hawaye....
*************
"Tsaye suke a bargan dawakin Mai Martaba suna zab'an dokin da zasu hau su fita kilisa,
"Khalifa ya dubi Shattima da gaba d'aya 'yan kwanakin nan ya canza, dafasa yayi kafin yace " Wai meke damunka ne, kwana biyun nan kana looking dull,
"Murmushi Shattima yayi Wanda iyakacinsa fatar baki kafin yace " Babu komai kwai banjin Dad'i ne kwana biyun nan...
"Khalifa yayi wata k'asaiteccen murmushi kafin yace " Ko kuma kana tunanin Gimbiya Zahidar ka ta kusa zama Mallaki na a ranar da za'a nad'ani sarautar Yariman masarautar nan...
"Galala Shattima ke kallonsa kana yayi murmushi yace " Zahida ta fah kace.
"KKhalifa ya gyad'a kai yace " K'warai kuwa kowa yasan irin shak'iwar dake tsakaninku tamkar yaya da k'anwa, a ranar data zama matata zan saka maka katangar k'arfe tsakaninku tunda de kai ba muharraminta bane..
"Murmushi kawai Shattima yayi sanda yake d'ale doki had'i da yin gajeren tsaki kafin yace muje da Allah, dan wllhi muka k'ara minti biyu bamu fita ba zan fasa fita kilisan nan....
"D'ale doki Khalifa yayi yana mai ci gaba da fad'in jikina na bani nine sarki mai jiran gado.
"Shattima baice komai ba sai tunanin da yake yawan yi a 'yan kwanakin wanda ya rasa ma waye zai soma fad'i gashi abun ya damesa sosai...
*Manage this 'yan uwa zaku jini later insha Allah... 😘😍*
[1/23, 22:23] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZIBAIDAH*
54
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Kai tsaye gida ya wuce bayan sun sauk'a daga dawakin.
"Parlron Ummansa ya shige ya tarar babu kowa sai TV dake faman aiki.
"Zama yayi gijif cikin sofa gamida turo hulansa gaban goshi ya lumshe idanunsa,
"Umma ce ta fito tana k'wala kira wa Ameera k'anwar Shattima.... A'ah Shattima yaushe ka shigo, Umma tace sanda take zama cikin d'aya Daga cikin kujerun.
"D'an mik'ewa yayi ya zauna sosai kafin yace " Ummah barka da gida.
"Tsaresa tayi da idanu don ta lura da canzawansa kwana biyu.
"Bud'e murya Umma tayi kafin tace " Kai wai lafiyanka kwana biyu kake neman zama lusari, gaba d'aya ka canza kaman bakai ba, idan akan auren yarinyar nan Zahidah da Khalifa ne, na fad'a maka ka cire ta a ranka, Zahidah ba matarka bace sanin kanka Baba Ciroma ba barin wani zaiyi ya auri Zahidah ba tunda ya k'wallafa ma wann d'an nasa mai wuya kaman marken lema....
"Tunda ta soma magana Shattima ke kallonta, Umma dai bazata Tab'a canzawa ba, wnn masifa nata ya rasa taxation da ita...
"D'an jim yayi kafin yace " Umma am I that obvious??
"Wani uwar harara ta kuma watsa Masa kafin tace " Bana son iskanci Karma ka soma min turancin rashin kunya ka bud'e baki ka fad'a min abunda ke damunka baka da wacce ta wuce ni mahaifiyarka...
"Shattima ya kuma sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Ummah ba tunanin Zahidah nake ba, besides na cire Zahidah a raina tuntuni tunda yau wata uku cif ya rage aurenta da Khalifa childhood friend d'ina, abinda ke damuna wani abu ne daban snn tun da akayi maganar aurenta take avoiding d'ina, Umma bazan iya jure rashin maganarta a gareni ba..
"Shek'ek"e ta kallesa kafin tace " Au ka yarda ka bari wani ya aureta, ka yarda ka badakai a aura mata wanda bata so...
"Kllonta kawai Shattima keyi cike da mamakin halin Umma saikace ba itace yanzu take masa fad'an ya cire Zahidah a ransa ba..
"D'an fitowa yayi daga cikin kujeran ya turo gaba kafin yace " Umma ba wann ba, wani tambaya nake so na maki..
"Ina jinka menene?? Ta fad'i tana karyan goro.
"Tab'e fuska yayi yana dubanta kafin yace " Umma wai Don Allah ke ba tsohuwa ba sai cin goro, bakisan illansa ba koh..
"Tab'e baki tayi gamida ci gaba da taunar goronta tana fad'in" Idan ka gama iyayinka da felek'en sai ka sanar dani Likita bokan turai, kai wannan da likitanci ka karanta da kad"ifirin naka da yauk'in yafi haka..
"Shafa kansa yayi gamida bata hak'uri.
"Saida ya cire hular kansa ya ajiye saman hannun kujera kafin yace " Umma kince mun matar Mai Martaba ta fari d'iyar sarkin Zazzau k'awarki ce kafin Allah Ya mata rasuwa...
"Cak ta tsaya da taunar goron da take tana dubansa, k'walla ya ciko idanunta,...
"Shattima yaci gaba da fad'in" Umma wai meye asalin labarin mutuwarsu itada jaririnta Modibbo,..
"Umma ta goge hawayen idanunta kafin ta soma fad'in" Dadda (sunan da ake kiran marigayiya matar mai martaba a masarautar)d'iya ce ga sarkin Zazzau wanda yake sonta sama da sauran 'ya'yansa, zata girme mun a shekare sabida lokacin da aka auro ta masarautan nan ba'a ma soma maganar aurena ba, auren soyayya na saurayi da budurwa sukayi da Mai Martaba, a lokacin da akai masa wankan nad'in sarauta a lokacin aka Aura masa ita..
"Sun d'au lokaci sosai Allah bai basu haihuwa ba, don har akayi aurena da mahaifinka shiru babu labari, Nida Matar Ciroma k'anin Mai Martaba a jere muka haifeku kaida Khalifa amma har lokacin shiru matar Mai Martaba bata haihu ba, kasan babban gida da k'anan maganganu musamman ganin K'aninsa ya haihu shi bai haihu ba, ..
"Mahaifiyar Modibbo da kanta ta rok'i Mai Martaba ya k'ara aure, snn ita da kanta ta zab'awa Mai Martaba yarinyar da zai Aura, ko ya sani a masarautar nan baya son auren amma sabida Mahaifiyar Modibbo da kuma Mahaifiyarsa shi kansa Mai Martaban suna so yasa sa amincewa, nan aka auro mahaifiyar Zahida a lokacin bata fi shekaru goma Sha biyar ba zuwa sha shida, ashe tun lokacin da akayi auren Mai Martaba da Ummin Zahida Dadda nada juna biyu babu wanda ya sani.... Bayan biki da kad'an cikinta ya bayyana, nan fah kulawa ya tattara ya koma kanta gaba d'aya, Mai Martaba har mancewa yayi yayi amarya, Madaki mahaifiyar Mai Martaba nan itama kulawarta ya k'arau sosai akan Dadda, wann dalili ya sanya Ummin Zahida cikin tsananin bak'in ciki ga k'uruciya da yarinta, a lokacin har saida suka sami sab'ani sosai da Mai Martaba, Dadda matar arziki 'yar Babban gida ita ta gyara komai, suka ci gaba da zamansu lafiya, taci gaba da rainon cikinta, wata tara cif ta haihu, haihuwar da ba'a tab'a irinsa ba a masarautar nan, anyi biki na haihuwarsa wanda ba'a tab'a irinsa ba yanda yaro yaci sunan Modibbo Lamid'o....... Kukan Umma ya tsananta.. Shattima ya tashi daga kujeran da yake ya dawo gefenta ya zauna gamida rik'o kafad'unta...
"Goge hawayen tayi kafin taci gaba da fad'in Daren da akayi suna da kwana bakwai daren data zama bak'in dare a wann masarauta daren da ya sauya farin cikin wann masarauta zuwa bak'in ciki, daren da har yau ya kafa tarihi a masarautar nan, daren da aka masa lakabi da BAK'IN DARE, a wann dare aka wayi gari aka tarar da gawan Dadda snn aka nemi Yarima Modibbo aka rasa......
"Kuka sosai Umma keyi har saida Shattima yaji dama bai d'ago maganar ba, da k'yar ya samu ya lallashi Umma tayi shiru. Mik'ewa yayi ya fice ya nufi d'akin sa yana tunanin al"amarin " What if Modibbo is still alive, what if..... K'irjinsa ta shiga bugawa da sauri da sauri, What if Jalal is Yarima Modibbo, But.... How's this be possible....? No way Jalal has his own family , mahaifiyarsa tana nan da rai, ta yaya ma zai soma fad'in wann abu, da Mai Martaba zai soma ko kuwa da Jalal zai soma.... Toh wai ma how did he come up with all this, dafe kansa yayi gamida zama bisa sofa, yana addu'an Allah Ya bayyana Modibbo a duk yanda yake matuk'ar yana raye...
*****************
"Hamma ne ya fita ya amsa sallamar da ake, ganin mutum cikin bak'ak'en kaya black suit yasa sa komawa cikin gida da gudo yana neman abun d'auka, can ya hangi muciya wajen wanke wanke ai nan ya rarumo muciyar nan ya nufo waje a guje...... Zubaidah dake kwasan shanya a sittin ta biyo bayansa tana tambayarsa lafiya...., Annah ma fitowarta kenn daga bayi ta ajiye butar hannunta tabi bayansu cikin sauri.
"Hamma kam fad'i yake " Turoka sukayi koh, wai zaka gane kuranka..... Da iya k'arfinsa ya nufi bawan Allahn nan, Zubaidah tayi ta maza ta k'wace muciyar hannun Hamma tana fad'in" A'a a'a Hamma....
"Barr Ansar Kumo dafe kansa yayi yana jiran ta Allah ta samesa...
"Zubaidah ta shiga jan Hamma yana fizgewa yana fad'in" Ki barni na gama dasu ki barni dasu Zubaidah, sunga babu Jalal suna tunanin zamu bari su ci zarafinki...
"Gida ta shige dashi yayinda Annah ta k'arasa ga Barr Kumo tana fad'in" Lafiya bawan Alla, idan Dasuki ne suka turo ka tun wuri gwara ka tafi kafin mu kira maka 'yansanda...
"Kallonta Barr Kumo yayi kafin ya sauk'e nannauyiyan ajiyan zuciya yace " Sannu Hajiya.... Em by the way sunana Barr Ansar Kumo, ni lauya ne daga k'ungiyar kare rajin hakkin bil adama musamman Mata da k'anan Yara....
"Cike da rashin hamsuwa Annah ke kallonsa don tasan Dasuki's zasu iya turo sa,... Zubaidah ce ta fito Hadiza na biye da ita....
"Barr Kumo ya dubi Zubaidah data masa k'uri yace " Kar ku damu banazo nan bane don cutar daku sai don taimaka maku ......
Katsesa Hadiza tayi da fad'in" Malam ka dubeka kasha bak'in kaya uwa d'an fashi kai ai da ganinka ma babu alheri a tare da kai, .. Hararan da Annah ta narka mata yasata yin shiru....
. "Girgiza kai Zubaidah ta soma kafin tace " Malam ka fad'a mana gaskiyan wanda ya turo ka wajenmu nasan sai ankai k"orafi kungiyarku snn kuke ba wa mutum d'auki, mu kuwa bamu kai ba don bamu da hanya, nasan su suka turo ka don fad'ar damu a kotu, Kayi wa Allah ka tafi ka k'yalemu, ka tuna idan hakan ya faru akan d'yarka yaya zakaji. Don Allah kar ka taimaka masu su ci gaba da zalunci...
"Tausayinta ya cika zuciyar Barr Ansar, sauk'e ajiyan zuciya yayi kafin yace " Kinyi gaskiya Zubaidah snn labarinki ya zama media circus, yasa hannu ya ciro jarida cikin 'yar jakan dake hannunsa ya nuna mata kafin yace " Kin gani, a halin yanzu labarin ki is everywhere a cikin k'asar nan, people are curious to know more about you, Zubaidah ni na kawo kaina nan da ra'ayina ba tareda taimakon wata k'ungiya ba....... Idonsa ya kad'a yayi ja sosai sanda yaci gaba da fad'in" Those Despicable are hiding behind their shadows, they must pay for each and single crimes they had committed....
"Gaba d'aya suka bisa da kallon mamaki sanda yasa bayan hannunsa ya goge hawayen da suka zubo masa.
"Annah jiki a sanyaye tace mu shiga daga ciki.....
"Daga yanda Faisal ya paka motarsa ya danna wayarsa, bugu biyu Alh Kasim ya d'aga " Ina saurarenka Faisal..
"Sir no doubt they've got an attorney.......
"Mik'ewa tsaye yayi yana fad"in what.!!!!!
"No way they can't find a lawyer, abinda nake so da kai follow him and see who's helping them, Faisal bana so a sami failure make sure kayi clean aiki... Yeah I trust you..... Daga haka ya katse wayar yana safa da marwa shi kad'ansa a parlour....
"Yanda Alh Kasim ya umurcesa haka yayi..... Har suka shigo cikin Abuja Barr Kumo baisan ana biye dashi ba. A k'ofar gidansa dake unguwar APO yayi parking ganin Asmah cikin tasi tana jiran isowarsa....
"Fitowa tayi daga tasi d'in sanda shima ya fito daga motarsa suka sakar ma juna murmushi. A hankali tace " My chewing gum how does go.
"Murmushi Barr Ansar yayi kafin yace " My silly girlfriend na fad'a maki ni nafi k'arfin your chewing gum saidai your super glue. D'an hararansa Asmah tayi kafin tace " I'm not your girlfriend you know....
"Murmushi yayi kafin ya kuma cewa we can't talk here mu d'an shiga daga ciki, hararansa ta d'anyi kafin tace " I hope su mommin ka na ciki...
"K'walla ya kuma ciko idanunsa sanda ya soma tafiya ba tare da yace mata komai ba, d'an girgiza kai kawai tayi tabi bayansa tana fad'in" Ansar bazaka daina wann hali naka ba, a da nayi zaton ko wani abu ke damunka amma yanzu kam na gane tsaf halinka ne....
"Gida ne apartment me kyaun gaske, saidai tun daga waje Asmah ta gane kaman shi kad'ai yake rayuwa a gidan, parlorn sa tsaf yasha furnished sai picture wanda ba sai ance maka na family d'insa bane, saidai duk hotunan yana yaro ne Wanda bai wuce shekaru sha biyu ba, harda 'yan k'annensa mace da namiji guda biyu....
"Drinks ya kawo ya ajiye mata ta dubesa da kyau kana tace " Attorney kasan dai bazan sha komai a nan ba tunda da alama 'yan gidanku basa nan.....
"Mik'ewa tsaye yayi in a furious tune yake fad'in " Yeah basa nan kuma bazasu tab'a dawowa ba, I'm all alone, I've no family, ya k'arasa ya d'auko hoto guda d'aya yana nuna mata yake fad'in" Kinsan dalilin da yasa farko nak'i amince wa buk'atarki, kinsan dalilin da yasa nace maki " I didn't want to have anything to do with that Despicable Kasim Dasuki...????
"Zaro ido kawai Asmah take tana girgiza kai, Ansar yaci gaba da fad'in" That Bastard is the reason why I'm all alone now, that imbecile destroyed my Family,
"My Father was an international Business Man, Kasim Dasuki ya yaudaresa ya saka kud'ad'ensa gaba d'aya a company d'insu, back then bana zama a k'asar nan, ina can Qatar da Grandmother d'ina, My Dad my Mum and my two siblings were living here in Nigeria, rana d'aya heart attack ya kama mahaifina sabida karyasa da Kasim Dasuki yayi, Dad d'ina ya shigar da k'ara baiyi nasara ba, sabida Kasim Dasuki is very powerful Man, Mum d'ina tayi jinyarsa ya soma, babu yanda banso naga Mahaifina ba amma babu kud'in da zanzo Nigeria, Grandma d'ina da take jinya itama a can Qatar depression na ciwon mahaifina ya mata yawa, kwana kad'an Allah yayi mata cikawa, ni kad'aina no family no relatives ga k'arancin shekaru haka da taimakon bayin Allah na k'warai aka kai grandma makwancinta, Dad d'ina yana riskan labarin shima Allah Ya masa cikawa, .... Kukansa ya k'aru sanda yaci gaba da fad'in" I couldn't have chance to say goodbye to my Dad, Mum d'ina ta d'aukaka k'ara dare d'aya gidansu tayi gobara k'urumus, da Mamata da k'anne na guda biyu all died a gobaran. Ban tashi sani ba sai lokacin da na saka k"afata a k'asar nan, bayan shekaru masu yawa, bayan all the hardships I gone through ni kad'aina a k'asar Qatar, aikatau babu kalan wanda banyi ba, har na sami kud'in jirgi na dawo, na tarar da wann bak'ar labari wanda nasan ba aikin kowa bane illa aikinsa sabida Mum d'ina ta d'aukaka k'ara shiyasa ya halak'asu. Wann shine dalilina na zama lawyer to bring Justice to the society,...... Zama yayi bisa sofa hawaye na bin k'uncinsa,
"Tausayinsa ya cika zuciyar Asmah batasan sanda hawaye ya shiga gangara mata ba. Hanki ta ciro cikin jakarta ta mik'a masa, ya karb'a ya goge hawayen kana yace " Thank you....
"Har Asmah ta isa layinsu jikinta a mace yake da jin labarin Barr Ansar, ta k'ofar baya ta shige hide....
"Faisal da sai lokacin ya karya kan motarsa ya danna wayar uban gidansa kana yace " Sir the Marafa's are the ones helping them....
"Murmushi Alh Kasim yayi kafin yace " Alh Tahir Marafa dabinmu da kai bata k'are ba, I'll prove to that no one messes with the Dasuki's.......
"Wayan Barr Munir ya kira kafin yace " Ka bincika wanene wann lawyer d'in nasu his profession at work and his family.... Sai naji feeback, do that fast attorney we don't have much time, kwana d'aya jal ya rage mana a shiga kotu....
"K'asar akwatin ta ta bud'e ta ciro zoben tana murmushi, tasan wann ba k'aramin amfani zai masu ba tunda za'a shiga kotu, tasan Alh Kasim Dasuki zai biyata mak'udan kud'i ta gudu ita da d'anta taje ta sami miji mai hankalk tsaranta ba wann susu shashan ba..... Wata dariya Hadiza ta kuma fashewa dashi kafin ta sunce bakin zaninta ta d'aure zoben, mayafin ta ta shiga yafawa.....
0 comments:
Post a Comment