"Sauri sauri ta fice daga gidan cikin canza kamanni bayan ta saci idon mutanen gidan...
"Saida ta sauk'a k'asa da layinsu kafin ta tari tasi ta shige....
************
"Alh Tahir yayi signing petition d'in kafin ya mik'e yana watsa wa Alh Kasim mugun kallo yake fad'in" It's over, we are done, one thing da ya rage mun daga gareka shine takardan sakin d'iyata, make sure your dear son Ya sakar mun d'iyata, she's not meant to be with a criminal like him.... To make it clear, From now on babu business tsakanin Dasuki Holding da Marafah Construction.... PA d'in Alh Tahir ne ya shiga tattara documents d'in har lokacin Daddy bai iya cewa komai ba sai kallon saman table da yake yi yana karkad'a pen.
"Gaba d'aya sauran shear holders suka sha jinin jikinsu, dama bayan Alh Kasim da yake da 50% Alh Tahir shike da kusan 30% which means the company is at risk of going bankrupt....
"Mik'ewa yayi yana huci ya fice daga conference hall d'in. Barr ya dubi sauran mutanen yana fad'in " Excuse us....
"Barr na masa magana ya daka masa wata uwar tsawa... Just shut the hell up, that damn man really crossed the line, I'm gonna make his life a living hell.
"Danna intercom yayi kana yace " Jade tell Cimon to get my car ready.... Daga haka ya katse ya k'arasa ya d'auki babbar rigarsa dake jikin hanger yana k"ok'arin ficewa, Barr na biye dashi yana fad'in" Mr President you need to calm down, ka tsaya a bi komai a sannu...
.
"Bai kulasa ba sai k'arasa lift da yayi ya danna down floor,.....
"A parking Space suka hangi motar Umar, yana ganinsu ya fito yana murmushi...
"Fuzar da iska Daddy yayi kafin ya furta " Oh damn it, nasan kaima kud'i kazo nema, Brr take care of him bazan iya magana ba I'm completely pissed...
"K'arasowa gabansa Umar yayi yana murmushi kafin yace " Alh Kasim seems you're in a rush, anyway I'm not gonna take much of your time,...
"Kallonsa Daddy yayi yana huci kafin yace " What is it again, me kuma kake so, kowa maganan kud'i I can't loose my company....
"Wata murmushi Umar ya Saki yana shafa sumansa da yasha low-cut kafin yace " Relax Mr Dasuki, you ain't gonna loose your company, but what if you lose your only Son,....Ya kuma yin wata murmushi kafin yace I know you never want that to happen..
"Karkata babbar rigarsa yayi yana duban Barr, da sauri Barr ya k'arasa ya dafa Umar yana fad'in" Me kuma kake nema bayan kud'in da muka k'ara maka.
"Da gefen bakinsa Umar yayi murmushi kafin yace " It's not enough, besides wancan kud'in nawa ne, what about the girl that is gonna testify against Zubaidah ita kuma ina nata kason, ....
"Fuzar da iska Barr yayi yana jawosa yake fad'in " Let's not talk about this here.... Cak Umar Ya tsaya yana girgiza kai kafin yace " No it has to be here, a gaban Alh Kasim coz ni zan yanke amount d'in da zaku bada, to prove to you inada abunda zaku defeating case d'inku in court let me present to you .... Juyawa yayi yana kallon motarsa gamida latsa wayarsa kafin yace " Fito nan ki same mu...
"Da mamaki suke kallon motar saiga Zulaihta ta fito sanye da bak'ar sunshade a idanunta....
"Kallonsu Zulaihat keyi kafin tace " Gentle Men Im gonna testify that Zubaidah is a prostitute ta zauna dani a lokacin da suka saka ma raguwarta takunkumi suka hanata fita yawon karuwanci.....
"Ai basu san sanda suka soma wage baki ba suna dariya, Alh Kasim harda shek'ewa kafin yace " Kai abokin aiki ne, tafiyar saida Kai, ....
"Umar Ya kuma yin wata murmushi yana rik'o hannun Zulaihat suka kalli juna suka sakar ma juna murmushi...
"A take suka yanke kud'in da za'a basu Alh Kasim yace Faisal should take care of them... Faisal ne ya rubuta masu check d'in huge amount of money da suka demanding. Alh Kasim ya nufi gida hankali kwance dukda had'arin kariyar arziki dake barazanar samun kampaninsu, yayinda Barr ya nufi gidan Barr Ansar dake Apo.
***********
*Maitama crescent , Dasuki Mansion*
"Tana hango motocinsu tayi saurin fitowa a tasi d'in ta nufo su da sauri tana jan mayafi tana rurrufe fuskarta.... Kan mai gadi ya hangame masu Gate tayi saurin isa jikin motar tana bubbuga glass...
"Securities suka nufota da sauri zasu kamata Alh Kasim ya dakatar dasu snn ya fito daga motar yana kallonta, tsaf ya ganeta... Bud'e murya ya d'anyi kafin yace " Me kuma kuke nema, ko kun janye k'aran da kuka shigar ne, ina mai tabbatar maku kabarinku kuke tonewa...
"Ba tareda ta amsa sa ba, sai maganarsa yake, hannu tasa ta warware bakin zaninta ta ciro engagement ring d'in Salim sai Shek'i take kafin ta Saki wata murmushi...
"Ai cak Daddy ya saka aya wa maganganunsa ya shiga binta da kallo yana k'ok'arin kai hannu jikin zoben don tsaf ya gane zoben a Dubai yasa aka k'era guda biyu kacal iri d'aya exactly don Salim da Kausar......
"Matsar da hannunta baya tayi tana wata murmushi kafin tace " A'a bazan baka ba, nasan sarai kasan me zoben, na tsinceta ne a daren bikin baikon d'anka Salim da Kausar yanda suka yi fyad'e ma Zubaidah, nasan Zoben zatayi kud'i sosai snn zata taka rawar gani a kotu, shiyasa banyi k'asa a gwiwa ba na kawo maka ka sake saya, snn kar kayi tunanin bansan kud'in kaya ba ka bani k'aramar kud'i...
"Murmushi Daddy yayi yana duban gefe da gefe kafin ya Bud'e mata bayan mota yace shige muyi magana, babu musu ta shige... Wayarsa ya danna ya kira Faisal ya kawo masa kud'i in cash right away....
*****************
"Ya jima yana jiran Barr Ansar a parpajiyan gidansa, can jimawa ya fito fuskan nan babu walwala don haka kawai yaji Mutumin bai kwanta masa ba.
"Barr Munir na murmushi ya mik'a ma Barr Kumo hannu yace " Sunana Barr Munir Anka lawyer me Kare wa'enda client d'inka take k'ara...... Fuzge hannunsa Barr Ansar yayi take fuskarsa ta canza ya soma nuna masa gate yana fad'in" Get.... Out... Of....here.
"Barr Munir ya d'an shafi kansa kafin yace " Attorney you and I really need to talk for your own good...
"Matsowa daf dashi Barr Ansar yayi kafin yace " You and I have nothing to discuss, idan hakan ta zama dole zamu had'u a kotu gobe, so why don't you leave it till tomorrow...
"Attorney listen to me, We can offer a huge amount of money, abu guda muke so daga gareka shine kar ka bayyana a kotu....
"Tsalle Barr Ansar yayi ya shak'e wuyan Barr Munir yana fad'in" How dare you, you imbecile, you are despicable, baka San aikin ka ba, snn ka wulak'anta kwalin karatunka, get out of here and don't ever show up again, idan na sake ganin fuskar ka a nan, I'll file a case of harassing against you.... Now leeeeave.......! Ya k'arashe yana nuna masa k'ofa....
"Sosa wuyarsa Barr Munir yake yanda Barr Ansar ya mak'uresa yana tafiya yake fad'in" You'll regret this Attorney, Mark my word....
"Get out you shameless coward... Ansar ya fad'i sanda yake raka Barr Munir da kallon k'yama.....
**************
"Barr Munir ya kuma kurb'an ruwa yana kallon Alh Kasim kafin yace " That Jerk is really an Imbecile,.....
"Murmushi Daddy yayi kafin yace " He have no idea who he's really messing with. Bamuda sauran damuwa tunda mun had'a abubuwa da dama, Yanzu abunda ya rage mana mu tafi asibiti mu sami yaron nan kafin Police suyi interrogating nasa, na fad'a wa Alh Maina kar ya kuskura ya bar Tariq yayi magana ba tareda lawyernsa yazo ba...
"D'an jim Barr yayi kafin yace " Gaskiya ina tsoron ganin wad'an nan mutanen, ... Dafa sa Daddy yayi kafin yace " Let's get going bamu da sauran lokaci the cops will arrive by 8:00pm yanzu kuma already k'arfe bakwai tayi...
"They have no choice dole kaine lawyansu , badon d'ana ba bazan tsaya ma d'an kowa ba.... Mik'ewa Barr yayi suka fice....
Daga parlor Mummy taji k'aran fitar motocin su, goge hawayen idanunta taci gaba da yi, Jane ta kawo mata coffee, tana fad'in" Ma'am your coffee.....
***************
"Daddy ya dafa kafad'an Alh Maina kana yace " Ya jikin Tariq,... Sauk'e ajiyan zuciya Alh Maina yayi kafin yace " Jikin sai ya d'an lafa sai kuma ya kuma rikicewa musamman idan yaga mahaifiyarsa,.
"Daddy ya d'an shafi gishinsa kafin yace " Yeah is not easy, I know both of you are suffering, I feel sorry for your family...
"D'an gyad'a kansa Dad d'in Tariq yayi kafin yace " 'yansanda suna jiran lawyer d'in they gonna Interrogate him now.
"Yeah sure Daddy yace kafin yayi alama ma Barr ya shigo,.... Ai babu shiri Dad d'in Tariq ya mik'e yana nuna Barr da yatsa yake fad'in" This Man, you even have guts to show your face.... Juyowa yayi yana kallon Alh Kasim in a furious way yake fad'in" This Man could be my son's lawyer after my dead body....
"Kafad'unsa Alh Kasim ya kama ya zaunar kafin yace " Calm down, don't be such an idiot, don't forget we are in this together, is left to you ka shawo kan d'anka to cooperate, abunda ya riga ya faru ya faru, we are talking about our childrens freedom here, ka ajiye duk wani grudges aside daga baya ayi dealing wann, and remember arzikinka na k'ark'ashin company d'ina, I can ruin you if I want.... Kallonsa kawai Dad d'in Tariq keyi hawaye na ciko idanunsa.
"Barr Munir bai samu ganin Tariq ba haka police basu samu daman interrogating nasa ba sabida rikicewa da jikinsa ya sake yi......
*On the Day Of the Trial*
_National High court, Abuja_
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:24] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
56
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Annah ta Kalli Barr Ansar wanda gefensa wani lawyer ne abokin aikinsa kafin tace " Ansar wann shine lawyer d'in daka d'aukar ma Jalal, gyad'a kansa yayi yana murmushi kafin yace " Annah meet Barr Hafiz he's a best friend of mine, and he's willing to help, sunyi magana da Jalal already...
"I hope kin gane dalilin da yasa muka d'au ma Jalal lawyer, sabida Confession d'insa, Zubaidah didn't file a complaint against him but kafin ya wanke kansa daga confession d'in da yayi dole saida lawyer tunda this is a court case..
"Annah ta goge k'wallan daya zubo mata sanda Barr Hafiz yake gaidata, ashe akwai mutane irin haka, tama rasa da wani irin kalma zata soma masu godiya sai hawaye... Ansar ya d'an rage murya kafin yace " Let's be getting ready Annah, ki sanar dasu Zubaidah yanzu zamu shiga, gyad'a kanta kawai tayi ta nufi yanda su Zubaidah dasu Hamma suke..
"Su Mommy dasu Daddy sai kallon mamaki suke bin su Kausar da Mum d'inta Hajiya Raliya basu tsammace zasu zo shari'ar ba...
"Kotu tayi tsit kowa ya zauna, Alk'ali yana shigowa suka mik'e gaba d'aya....
"Bayan Ya zauna me karanto laifi ya karanto, Alk'ali ya buk'aci a shigo da wa'enda ake k'ara...
"K'irjinta sai bugawa yake da sauri da sauri, abubuwan da suka faru a wancan daren suka shiga dawo mata sanda aka shigo da Labib da Salim, gaba d'aya bata kula da Jalal ba sai jiyo sautin ihun su da dariyarsu da take Yi a kunnuwanta...... Idonta ya sauk'a kan Jalal dake faman kallonta yana girgiza kai alamum don't panic remain strong....
"Saman kanta tayi da gyad'a masa kai hawaye na k'ok'arin ciko idanunta..
"Bayan an gama karanto confession d'in Jalal, Alk'ali yayi gyaran murya ya soma kirawo sunayensu kaman haka
"Depending Labib Dasuki, depending Salim Dasuki, depending Tariq Maina and Depending Jalal Ibrahim.... Gaba d'ya suka mimmik'e a akurkin tuhumar da suke zaune ciki...
"Alk'ali ya tambaya ina Tariq Maina, Barr Munir ya mik'e yana fad'in" Your honor I'm Barr Munir Anka his lawyer, my client is in the hospital right now receiving treatments sabida had'arin mota da yayi, he couldn't show up...
"Alk'ali yayi rubutu kafin ya d'ago ya ambaci wanda yayi confession d'in wato Jalal.
"Alk'ali ya dubesa bayan ya amsa kafin ya d'ago takardan hannunsa kafin yace " You made this confession ranar ishirin da d'aya ga watar Augusta a ofishin 'yan sanda dake Wuse, shin ka tabbata kun aikata wann laifi.
"Jalal ya kalli Zubaidah itama shi take kallo kafin ya soma fad'in" Your Honor ban aikata ba amma abokaina sun aikata...... Cakumosa Labib yayi da k'arfin gaske yana fad'in" You Trader..... Alk'ali ya buga benchi cikeda b'acin rai.. Barr Hafiz ya tare Labib yana fad'in" Don't touch my client... Barr Munir kuwa rik'e Labib ya soma yi yana bawa Alk'ali hak'uri.
"Alk'ali yace " Barr Anka tell your client to behave himself this is a court...
"Fusfuzgewa Labib yake yana fad'in" He's lying your Honor... Silent...... Alk'ali ya kuma fad'i kafin ya dubi Jalal yace " Go ahead.
"Jalal yaci gaba da fad'in" I was drunk your Honor that I couldn't stop them, Labib started it then Salim then Tariq.... Hawaye ya ciko idanunsa sanda yaci gaba da fad'in" Na koma wajen da safe ban sameta ba, saidaga baya na sameta a asibiti tareda Mahaifiyata da kuma matar yayanta, The Dasuki's threaten her that they will kill her family muddin tayi magana, snn nima sunyi threatening d'ina cewa zasu kashe Mahaifiyata muddin na bari maganar ta fito fili, All I wanted your Honor is to protect Zubaidah sabida tana cikin damuwar da takai tana yunk'urin kashe kanta I thought of marrying her to keep her safe from harming her self and also from the Dasukis, a zatona na aureta ne out of pity but I realized it wasn't out of pity it was out of love, ...... I love her.... Ya fad'i yana dubanta wanda itama shi d'in take duba...
Saida ya d'an d'au lokaci kafin yaci gaba da fad'in, "Su da kansu suka so na aureta sabida asirin 'ya'yansu ya rufu.But they never leave us alone as they promised to.... Ya d'anja fasli kafin yaci gaba da fad'in It wasn't a happy marriage from the beginning although we started to get to know each other all of a recent , amma rad'ad'in abun na tare da ita, na gane pain d'in bazai rabu da ita ba har sai an karb'a mata hakkinta, that's why I went straight to the police and confessed cos that is the only way for her to let go of her agony, ya k'arashe maganar yana kallonta...
"Alk'ali yayi rubutu mai d'aukan rahoto ma na kanyi.
"D'agowa yayi yana duban Jalal kafin yace " According to your statement, kace " Ka sameta a asibiti tareda Mahaifiyarka da matar yayanta idan suna cikin kotun nan, kotu na buk'atar ganinsu a gabanta..
"Babu musu suka mimmik'e, Hadiza sai rarraba ido take kana ganinta kaga maras gaskiya.
"Da Annah aka soma, Alk'ali yace Kinyi rantsuwa zaki gaya wa kotu iyakar gaskiyan ki...
"Annah ta gyad'a Kai tace " Eh Ya Mai Shari'a
"Mai Shari'a yayi rubutu kafin ya soma jefo mata tambaya kaman haka.
" Relationship to the Victim?
"Annah tace " She's my in-law, my Son's wife..
"Alk'ali yayi rubutu kafin ya kuma cewa " Matar d'anki, D'anki kamar yaya, Adopted Son, ko kuwa guide son ko real biological Son d'inki ne...????
"Gaban Annah ya yanke ya fad'i tunda take babu wanda ya tab'a mata irin wann tambayar, Kotu yayi tsit ita ake saurare yayinda k'irjinta yaci gaba da lugude tunowa da tayi tayi ranstuwa idan an tambayeta gaskiya zata fad'i, shin ta shirya fad'a wa Jalal gaskiya...... Muryan Alkali ne ya katseta sanda yake fad'in" Ke muke sauraro Malama Maryam...
"Juyowa tayi tana kallon Jalal wanda shima ita yake kallo fuskar sa cike da shakku da tarin mamaki... Annah tana kallonsa hawaye na gangaro mata tace " D'ana ne dana rainesa amma bani na haifesa ba....
"Gaba d'aya mutanen dake wajen Sun zama shocked harta Zubaidah da take cikin tashin hankalin ganin fuskokin mak'yanta... Jalal kam tamkar dutse haka ya koma a wajen ya kasa fahimtar komai...
"Annah taci gaba da bada labarin yanda ta tsinci Zubaidah har zuwa aurensu da Jalal...
"Mai Shari'a ya gama rubuce shaidar ta kafin ya buk'aci witness na gaba wato Hadiza, itama irin tambayoyin da akayi ma Annah aka mata ta amsa komai saidai bata fad'a alak'arsu ta makirci dake tsakaninta da Dasukis ba, harta Hamma saida tambayoyi ta k'araso kansa.
"Witness na k'arshe Kausar ce yanda ta bada nata shaidan iyakacin abunda ta sani da kuma b'acewar engagement ring d'in Salim a daren bikin baikonsu, ta k'arashe bada testimony d'inta tana watsa wa Salim mugun kallo.
"Rubutu ya kumayi kafin ya jefo wa Labib tambaya.
"Labib Dasuki kaji acquisition d'in da Malama Zubaidah take akan ka, shin ka amsa laifinka...??
"Girgiza kai Labib yayi kana yace " No your Honor ban amsa ba, I'm not guilty.....
"Mik'ewa Zubaidah tayi tana kuka take fad'in" Ka fad'a ma kotu gaskiya you liar.... Order....... Alk'ali ya fad'i gamida buga benchi..... Bata bar kuka tana fad'in Labib ya fad'i gaskiya ba.... Gaba d'aya ta zama out of control, Jalal kam gaba d'aya bai ma gane me ake ciki ba, Alk'ali ya buk'aci a fitar da Zubaidah kafin shari'a taci gaba, Annah ce ta kamata ta fice da ita har lokacin bata daina kuka ba tana fad'in k'arya suke, da sauri Barr Ansar ya d'au excuse yabi bayansu..
"Barr Ansar yace da Annah is better idan suka zauna a wani parlor he can take care of everything, daga haka ya koma cikin zauren gudunar da shari'a..
"Shari'a taci gaba.....
"Alk'ali yaci gaba da fad'in" Kotu tana saurarenka Malam Labib kayi bayanin abunda ka sani game da zargin da ake maka, iyaka gaskiyanka..
"Labib yayi gyaran murya ya soma karanto k'aryar da Barr Munir ya karanta masu su fad'i a kotu kamar haka.
"Ya mai Shari'a Jalal ya kasance abokinmu wanda ba'a rabamu gaba d'ayanmu mu duka hud'u, A ranar da muka isa garin Dukku don gudanar da bikin sakun ranar d'an uwana kuma abokinmu Salim, Jalal ya fad'a mana yaga wata yarinyar da ta tafi da tunaninsa ma'ana yaga yarinyar da yake so, mukayita jan kunnensa kar ya yaudareta kaman yanda ya saba yaudaran 'yammata wayayyu a nan Abuja, a daren engagement d'in Salim Ya nuna mana yarinyar sabida mu bamusanta ba sai ranar, Ashe tana d'aya daga cikin ma'aikatan da akayi hiring nasu, so bamusan yaya akayi ba don dukanmu bamu kwana a gida ba, mun kwana ne a gidansu abokinmu Tariq Maina, babu yanda bamuyi ba Jalal yazo mu tafi gidansu Tariq yaqi zuwa yace " He needs to take care of something tonight, we didn't force him to come with us, muka k'yalesa mukayi tafiyarmu, da safe Jalal yazo mana crying yana fad'in" I forced her slept with me, this is all I know your honor, daga baya family d'inta suka k'i amincewa sabida akwai baikon wani akanta, Jalal ya roki uncle d'ina ya nema masa auren yarinyar don asirinsu ya rufu kar su zama abin kwatance a gari. My uncle did as they wanted, all of a sudden mugaji wann sharri da suka k'ulla mana babu gaira babu dalili.....
"Barr Ansar girgiza kai kawai yake sanda ya buk'aci kotu ta basa dama yayi ma Labib wasu tambayoyi, kotu ta basa dama, haka ya ringa jefo tambayoyi masu rikitarwa wa Labib Barr Munir na karesa, ... Bayan an gama da Labib ne Alk'ali yayi ma Salim same tambayan da yayi wa Labib.
"Shima yayi denying ya bada irin statement d'in da d'an uwansa Labib ya bada....
"Barr Munir ya k'arasa gaban kotu kana yace " Ya mai shari'a ina buk'atan kotu ta bani daman gudanar da shaidun da zasu tabbatar cewa lallai k'age da sharri akayi wa Clients d'ina,.. Kotu ta baka dama Barr Anka..
"Na gode ya mai sharia ya fad'i sanda ya gabatar da Umar a gaban kotu...
"Kotu tana son sanin sunan Malamin ya fadi yana duban Umar, Umar yace sunan Umar Sanda, Barr Munir ya gyad'a kai kafin yace " Ko menene alak'arka da wacce take k'ara.
"Ni Ex Fiancee d'inta ne wanda akwai baikona akanta kafin ta auri Jalal,..
"Barr ya gyad'a kai kafin yace " Ko meyasa baka aureta ba.
"Dalilin da yasa ban aureta ba shine labari ya gama yad'a gari cewa ta bada kanta ma wani d'an me kud'i snn ta bisu sun tafi tare, don lokacin da na dawo ban taarar da familynta ba gaba d'aya sun tafi...
"Barr ya gyad'a Kai kana yace " Mun gode Malam Umar, Ya juyo yana dyvan Mai Shari'a kafin yace " Ya Mai sharia wann bawan Allah tsohon saurayin Zubaidah ne wanda ada yake shirin aurenta kafin taci amanarsa ta bada kanta ma wani ta gudu ta k'yalesa, da wann hujja nake son wann Kotu Mai Alfarma ta dubi irin cin zarafin da akayi ma Babban Family responsible mutane a k'asar nan irin Dasuki Family tayi watsi da wann sharia Mara's asali balle tushe, Na gode ya Mai shari'a...
"Rubutu Mai sharia yayi kafin yace " Ko lawyern wanda take k'ara yanada tambayan da zzaiyi ma tsohon saurayin wacce take k'ara.
"Barr Ansar ya mik'e yace k'warai Ya mai sharia inaso kotu ta bani dama,
"Kotu ta baka dama Barr Kumo. Alkali yace..
"Na gode Ya Mai sharia Barr Kumo yace kafin ya k'arasa gaban Umar yace " Malam Umar ko meyasa da ka dawo daga tafiyarka baka bincike asalin abunda ya faru da Zubaidah ba ka bi maganganun mutanen gari, shin anya kasan hukuncin kafa hujja da zargi a Sharia....
"Zare ido Umar Ya farayi ya rasa me zaice ya soma 'yan kame kame... " Eh Ba zargi nake ba iyayena dasuke mak'ota dasu sun tabbatar da haka.
"Toh meyasa da kace kaji a bakin mutanen gari...... OBJECTION MY LORD... Barr Munir yace kafin ya k'arada, Ya kamata Lawyern wanda take k'ara ya gane cewa Umar yazo nan ne bada shaidan iyakan abunda ya sani ba yazo ne don a tuhumesa ba...
"Alk'ali yace korafi ya karbu Barr Kumo ka gyara Kalman ka..
"Gyada kansa yayi kafin yace " Na gode your Honor... Tambayoyi yaci gaba dayi ma Umar wanda harta Alh Kasim saida zufa ta karyo masa, shakka babu suna da aiki ja a gabansu..
"Bayan Shaidan Umar Barr Munir ya kuma gabatar da shaida na gaba Zulaihat,Yanda itama t bada nata statement d'in lokacin da Zubaidah ta gudu gidanta....
"Daga k'arshe Barr Munir ya kuma nuna engagement ring d'in Salim Alk'ali ya buk'aci ganin na Kausar tabbas iri guda ne babu aunda ya banbanta....
"Alk'ali ya bukaci ganin Likitan da yayi treating nata a asibiti in the forthcoming trial snn aka d'aga k'ara har zuwa nan da 2 ga watar October a lokacin Tariq Maina ya sami lafiya snn za'a ci gaba da tsare wa'enda ake k'ara a gida tasku har na tsawon watanni biyu lokacin da za'a gudanar da sharia na gaba...
"Snn Kotu tabada belin Jalal for he is only trying to save and protect the Victim amma hakan ba yana nufin ya wanku daga confession d'in da yayi bane....
"Barr Ansar da Barr Hafiz suka rungume juna...
" Salim fad'i yake Daddy uncle pls do something I can't stay there for two months, Labib kuwa sai huci yake yana hararan Jalal dake Zaune a wajen kaman wanda aka dasa, har saida Ansar ya kamasa suka fito, tsaye ya hangi Annah da Zubaidah.. Annah kanta a k'asa don bata san ta yaya zata soma fuskantar sa ba...
Kallonsu kawai yake babu ko kyafta idanu sai jijiyoyinsa da gashin jikinsa da suka mimmik'e.....
....Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:24] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
57
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Kaman k'yaftawan ido haka suka nemesa suka rasa ga journalist da sukayi chaa ma Zubaidah, Ansar ne keta faman ansa tambayoyin Journalist d'in yayi nuni masu Zubaidah kan su wuce motar sa.
"Hankalinta duk baya jikinta damuwarta kawai taga Jalal, why did he suddenly disappeared, ta tambayi kanta a hankali, sauk'e ajiyan zuciya tayi don kuwa tasan tabbas hakan nada alak'a da abunda ya faru a kotu, statement d'in Annah, ita kanta ta kasa gane komai snn bata sami zarafin tambayarta ba...
"Ansar ke driving yayinda Hafiz ya dannne masa mazaunin me zaman banza, tattaunawa suke kanyi akan trial d'in da yanda zasu reaching Doc d'in da yayi treating Zubaidah a wancan lokacin...
"Gaba d'aya Zubaidah sai taji babu dad'i yanzu kowa yasan abunda ya faru da ita, kowa na kallonta da abun, ... Jawo mayafinta tayi tana rufe fuskarta, har gida su Ansar suka kaisu, nan suka tarar su Hadiza sun riga sun iso gida, a tunaninta Jalal ya iso gida amma shiru bata gansa ba, kasa daurewa tayi ta nufi d'akin Annah don tunda suka dawo Annah ta k'ule a d'aki...
"Zaune ta sami Annah ta k'ura ma wani hoto idanu, k'arasowa tayi jiki a sanyaye ta zauna gefen Annah, pic d'in hannunta ta kalla, itace da Jalal lokacin bai wuce d'an shekaru goma ba.
"Hannu tasa ta d'an dafa kafad'un Annah.... D'agowa Annah tayi tana dubanta, bata san sanda ta rungume Zubaidah ba, duk k'ok'arinta kar kuka ya kufce mata saida ya kufce mata..
"Cikin kuka take fad'in" He's my son, he's little boy, Jalal d'ana ne Zubaidah.... How am I going to tell him, how how Zubaidah.... Rungumeta sosai Zubaidah tayi hawaye na neman kufce mata itama, but she knows she need to be strong now sabida both Annah and Jalal needs her now, they were there for her a lokacin k'uncinta dole yanzu ta tsaya masu har sai abubuwa sun lafa....
******************
"Zaune yake k'ark'ashin bishiyan hannunsa dunk'ule ya d'aura hab'arsa akai, siraran hawaye suka shiga gangaro masa...
"Ni wanene?? Who am I????? Tambayar da ya ringa nanata ma kansa kenan.
"A hankali yaci gaba da furta why, why this had to happen, why me....???
"Dafe kansa da ya masa nauyi yayi snn yaci gaba da kuka da iya k'arfinsa bashida wani zab'i da ya wuce ya fitar da k'uncin dake cikin k'irjinsa ta hanyar kuka....
"Ya jima yana abu guda tamkar k'aramin yaro, he just couldn't help.....
******************
"Rai b'ace ta ahigo d'akin yanda ta tarar Asmah na kwance saman gado tana chatting da wayarta...
"Kallon Kausar dake faman rage kayan jikinta kafin tace " So how was the trial..? How did it go??
"D'an tsaki Kausar tayi kafin tace " They denied it, sunyi k'aryarsu da suka saba, ganin Salim yau ya kuma fama gyanbon dake cina, wllhi Asmah ji nake kaman na shak'esa kowa ya huta, you should have seen his face sanda akace baza'a bada belin su ba har sai Tariq ya warke, he was screaming calling his Dad and that incompetent Lawyer Munir....
"D'an mik'ewa Asmah tayi ta zauna sanda taga pictures an soma spreading nasu kana tace " Here, gashi sun soma watsa news d'in, Dasuki Holding tana gab da rugujewa Majority shear holders suna gab da cire dukiyansu a company d'in....
"I hope they do so, Kausar tace....
"Shiru Asmah ta d'anyi gaba d'aya jikinta yayi sanyi kafin tace " I'm afraid Ansar life might be in danger, what if something bad happens to him, I'll hold my self responsible..... Ta k'arashe maganar tana kwantar da kanta bisa gwiwoyinta....
"Kausar ta ajiye rigar hannunta kafin ta k'araso ta dafa Asmah tace " Sis pls don't worry, nothing bad will happen to him okay... Insha Allah, Allah yaga niyyanmu na alkhairi ki zama mai kyautata zato.... Kallonta Asmah tayi kafin ta gyad'a kai a hankali still damuwa ne fal a Face d'inta.....
*******************
"Faisal I want you to do a clean job, Alh Kasim yace kafin ya mik'e daga kujeran da yake ya k'araso gaban Faisal yaci gaba da fad'in" I trust you among all my boys, Faisal bana so a sami failure make sure babu wani suspicious da zaiyi linking d'inmu da aikin da zakayi, ...
"Faisal ya gyad'a kai kana yace " Yes Boss you can always count on me, You've my word....
"Murmushi Alh Kasim yayi yana bubbuga kafad'un Faisal kafin yace " Good,..... Saida ya d'anja fasali kafin yaci gaba da fad'in" Apparently gobe za'a shigo da kaya *Marafa Construction Of Company* I want you and your boys to set the company on fire... Make sure komai ya k'one....
"Murmushi Faisal yayi kafin yace " Boss considered it done,....
"Daddy ya murmusa yana bubbuga kafad'un Faisal kafin yace " Maza ka tafi ka soma shiri don aikin ba mai sauk'i bane....
"Gyad'a Kai yayi yana fad'in" Yes Boss kafin ya fice...
"Alh Kasim shi kad'ai ya fashe da wata dariya kafin yace " Alh Tahir kayi kuskure mafi girma a rayuwarka, I'll surely bring you down. . . Ya kuma fashewa da wata dariya.....
******************
*Gombe*
" Meyasa wann tunani ya kasa b'ace masa, meyasa ya kasa barinsa ya huta, ko yaje kai tsaye ya fad'a wa Mai Martaba ne, toh yace masa me, snn ta yaya ma zai soma,..... Kaman daga sama yaji ana k'onk'wasa mai k'ofa da k'arfin gaske... Tsaki yaja a hankali don yasan wann iskanci ba kowa bane illa Ameera , baisan yaushe zatayi hankali ba tasan ta soma girma... A fusace ya mik'e ya nufi k'ofar yana fad'in" Kinsan Allah idan baki daina zuwa kina buga min k'ofa uwa kina bashi ba wataran sai na karyaki a gid....... Aya yasa ma maganganun nasa ganin Ameera ba ita kad'ai bane gashi daga shi sai singlet ne da gajeren wando..... Saurin komawa baya yayi lokaci guda Zahida ta sadda nata kan k'asa....
"Baki a ture Ameera tace toh ba na rako Aunty Zahida bane tunda yanzu ko parlorn Umma baka fitowa...
"Harara kawai ya galla mata gamida komawa cikin d'aki ya zura jallabiya......
"Parlour ya fito yanda take zaune, tana sanye cikin jan leshi da yayi mugun karb'anta kanta yane da Farar alkyabba....
"Saida yayi still a wajen kafin ya k'araso yana fad'in " Meyasa kika shigo mun d'aki kanki d'aya kuwa.... Ki tashi ki fice tun wuri...... In a furious tune yayi maganar...
"Mik'ewa tayi cikin rawar murya take fad'in" I'm sorry Ya Shattima nasan a kwanakin nan ina avoiding d'inka coz bana so rashinka a gaba yayi affecting d'ina sosai, but I realized that I can't bear it, bazan iya jure rashin ganin ka ba Ya Shattima pls don't neglect me....
"Take zuciyarsa ta soma masa zogi, meyasa Zahida take neman zautar dashi bayan yayi alk'awari ma zuciyarsa cewa zai mance da ita for good...
"Dakewa Ya kumayi kafin yace " Get out Zahida, I don't want to have problem with your Father, He trust me I don't wanna break that trust, just get out.....
"Kallonsa take tana hawaye kafin tace " No bazan fita ba until we talk Shattima I can't survive without you...... For the first time da ta tab'a ambatan sunan sa kai tsaye....
"A zuciye ya kuma d'agowa yana fad'in " Then you should learn, kaman yanda nima nake koyon rayuwa babu ke....Are you out of your sense, what if... What if someone sees us and implies something, especially Khalifa da akwai baikonsa akanki yana iya shigowa any moment and you quite know how he is.... kinsan irin had'arin da kike k'ok'arin jefan........ Burki yayi ganin hawaye sharkaf a idanunta, take yaji babu Dad'i, d'an matsowa yayi daf da ita gamida yin k'asa da murya kafin yace " Hey I'm sorry, kiyi shiru kinji sis, pls sorry, I don't wanna see those tears it hurts....
"D'ago idanunta da suka jik'e da hawaye tayi ta sauk'esu kan Face d'insa da tsantsan damuwa ya nuna a face d'insa a hankali ta furta pls don't leave me...
"Kauda kai gefe yayi numfashinsa na fita one after the other kafin yake furta " Zahida don't make it more difficult, ki tashi ki tafi don Allah.....
"Mik'ewa tayi tana goge hawayenta kafin ta fice cikin sauri,... Ameera dake lab'e tana jinsu kallo tabi Zahida dashi cike da tausaywa har ta fice, dukda k'arancin shekarunta kafin ta turo k'ofar d'akin yayan nata ta shigo.... Yanda Zahidah ta barsa haka nan yake zaune a wajen tamkar gunki.... Kai tsaye dispense Ameera ta wuce ta tsiyayo masa Ruqaya glass cup ta mik'a made, d'ago kai yayi yana kallonta kafin yasa hannu ya karb'a gamida rik'o hannunta ta zauna gefensa, a hankali ya furta " Umma should not no about this kinji little...
"Gyad'a masa kai tayi a hankali cike da tausayawa yayan nata......
*********************
"Wayarsa ta ringa nema baya shiga, i zuwa lokacin damuwa ya nuna sosai a fuskar Zubaidah, a jima ba'a jima ba sai ta lek'a k'ofarsa amma shiru, Annah kan tasan halin d'an nata ba lallai ne su gansa yau ba, don haka gaba d'aya duk'ufa addu'ar kariya ta shiga masa.
"Har wajajen k'arfe 12:00am na dare bai dawo gidan ba, Zubaidah kuwa har Barr Ansar ta kira amma ya sanar da ita basa tare, hankalinta Ya tashi sosai, tunaninsa ya hanata sukuni.... What if ya tafi kenan bazai dawo gareta ba, .... Da sauri ta soma girgiza kai ita kad'anta take furta " No... No I know he will come back for me, nasan bazai tafi Ya barni ba.....
"Annah dake kwance kamar mai bacci a hankali ta juya mata baya cike da tausayin halin dasuke ciki....
"Wajajen shabiyu da d'auriya taji k'aran tab'a k'ofarsa zumbur ta mik'e ta rufa hijabi saman rigar baccinta ta nufi waje....
"Tsaye ta hangosa k'ofar d'akinsa shima ita yake kallo, a hankali ta soma takwa har ta isa garesa..... Wasu k'wallan ta hango cikin idanunsa..... Gaba d'aya ta daburce ta rasa da wanne zata soma masa, hak'uri ne ko Me..... Bata ankara ba saiji tayi ya rungumeta very tied yana kuka da iya k'arfinsa.......
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:24] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
58
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum...📖📚_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Ya jima yana rungume da ita gam gam cikin jikinsa yana kuka kaman k'aramin yaro, rik'on da ya mata ya hanata motsa koda hannayenta ne, very tied ya rungumeta hawayensa gaba d'aya sun jik'a kafad'unta....
"Jikinta yayi sanyi sosai, k'irjinta yaci gaba da harbawa da sauri da sauri, bata tab'a jin yanayin data tsinci kanta ciki a yanzu ba her whole life. Tausayin Jalal yana fizgarta a hankali ta soma yunk'urin d'aga hannunta amma saiji tayi Ya kuma matseta yana fad'in" Pls let me hug you, don't let me go pls....
"Ji tayi k'afaduwanta suna barazanar kasa d'aukarta zuciyarta Ya karaya bata tab'a ganin sa cikin irin wann yanayi ba, she needs to be strong, she needs to remain steady.....
"Cikin rawar murya take fad'in" I'm here... I'm here for you kaji, pls ka daina kukan nan it hurts...... Ta k'arashe maganar cikin tsananin rawar murya..... Jin yayi shiru kaman an d'auke ruwa sai bugun zuciyarsa datake jiyowa daga k'irjinsa dake manne mat da nata yasata sauk'e ajiyan zuciya.... Sun jima a haka kafin tayi anfani da hannunta guda ta bud'e k'ofar d'akinsa suka shige ciki, Kan katifarsa ta zaunar dashi har lokacin bai iya cewa komai ba,..
"D'an kallonsa tayi taga ya k'urama waje guda rinanun idanunsa, a hankali ta furta " Barin d'aura maka ruwan zafi a kitchen then you take shower... Bai amsata ba har ta fice....
"Tana shiga kitchen flask d'in abincin data ajiye masa ta d'auko ta kunna risho tayi warming abincin kafin ta d'aura ruwan wanka wadatacce a tukunya ta nufi d'akinsa da tray a hannun ta...
"Annah tabi Zubaidah da kallo har ta shige d'akin Jalal, sauk'e ajiyan zuciya tayi gamida zama zama gijif cikin sofa.....
"Yanda ta fita ta barsa yana nan a wajen saidai yana looking sick, ajiye tray d'in tayi bisa darduman dake gaban katifar sa kafin ta soma serving nasa tana fad'in" Kaci abinci kafin ruwan yayi zafi yanzu zan juyo maka, but make sure you eat.... Har lokacin bai iya ce mata komai ba sai kallon da yake binta dashi....
"Gaba d'aya saitaji she's not comfortable, d'an mik'ewa tayi tana fad'in" I... I zan duba ruwan pls eat something.... Ta fad'i sanda take k'ok'arin mik'ewa, .... Ji tayi Ya rik'o hannunta gam cikin nasa... K'irjinta yaci gaba da lugude, hakan yake mata a duk sanda jikinsu ya had'u...
"A hankali ta zauna a gefensa gamida kallonsa a fizge.... "Kasa cewa komai tayi har lokacin hannunsa na rik'e da nata... "Jiyo muryarsa tayi yana fad'in" I'm not hungry....
"Ta d'ago ta dubesa da sauri kafin tace " No you must be, nasan bakaci komai ba tun safe, pls you need to have something in your system, if not you'll fall sick...
"Kallonta yake yanda duk ta wani daburce kafin yace " If only I could.... Bazan iya cin komai ba Zubaidah I lost my appetite....
"Sauk'e deep breath tayi tana kallon yanda yake murza 'yan yatsun hannunta, wani yanayi maras fasaltuwa ta tsinci kanta a ciki.... Muryarsa ta jiyo yana fad'in" Ta gaya maki..? Ta gaya maki who are really my real parents.. Pls tell me did she tell you..... "Cikin rawar murya yayi maganar...
"Dabara tayi ta cire hannunta daga cikin nasa kafin ta shiga k'irga 'yan yatsunta tana girgiza kai alamun a'a. A fili tace " But .... Saurin katseta yayi da fad'in" Don't cover up for her.... I can't believe she kept the truth from me all this while... Why did she do that.. Why why... Wanene ni, menene asalina, su waye iyayena suna raye ko sun mutu, idan sun mutu suwaye danginsu, idan suna raye a ina suke.... I need her to explain all these.....
"D'an shiru Zubaidah tayi kafin tace " She must have her reason,...... Da sauri yace " And what is the reason, who knows maybe.... Maybe I'm only a street child or maybe I'm a Bastard..... Da sauri Zubaidah ta katse sa da fad'in" Ka daina fad'in haka pls, ..... "Girgiza mata kai yake kana ya d'agi face d'inta suna kallon juna kafin yaci gaba da fad'in" Idan kinji ana b'oye maka asalinka tabbas bashida kyau ne ko tushe,..... I'm sorry Zubaidah but I really need to leave, bazan iya ci gaba da zama ba, ... I'm sorry I failed you, I couldn't make it up to you.... Ko bana nan ki sani cewa Jalal me k'aunarki ne.... Muryarsa yaci gaba da rawa sanda yake fad'in" promise me ko na tafi You'll keep fighting, I know you're strong, don't back down until they all get what they deserves, kici gaba da magana da muryan matan duniya, kar ki gaza har sai kin karb'a wa mata 'yancinsu na cin zarafin da gurb'atattu daga cikinmu ke masu...... "Girgiza kai kawai take tana hawaye take fad'in " No... No... No pls don't, don't leave me, I can't do it all alone, Don Allah kar ka tafi ka barni nima tafiya zanyi.....
"Manna goshinsu yayi su duka suna hawaye yake fad'in" You don't deserve me Zubaidah, baki cancanceni ba, you deserved someone who has good family background, you suffered alot, kin cancanci ki kasance cikin farin ciki....Ni kaina bansan kaina ba a halin yanzu I don't wanna add more pressure for you bayan wanda kike ciki..... Da d'an k'arfi ta furta "No ni bana son kasancewa da kowa sai kai, you and you alone, I don't care who your parents might be, all I want is to be with you..... Ta rage murya sosai tana girgiza kai take fad'in" Pls don't leave me... Please..... Please...... Rungumeta yayi sosai cikin jikinsa bata san sanda itama ta k'ank'amesa sosai ba.....
"Hadiza dake mak'ale jikin window taja dogon tsaki a hankali kafin tace " Insha Allah sai ka tafi, sai muga uban da zaici gaba da tsaya mata, munafukan banza munafukan wofi... Ji yanda suke kuka suke rungume juna kaman zasu cinye juna.... Ta kuma tab'e fuska ta matsa gefe tana rayawa a ranta inama itane ta sami miji haka mai k'aunarta gangariya kaman yanda Zubaidah ta samu, ta tuna yanzu zataje ta tarar da wann sullutun mijin nata wani k'unci ya kuma tokare mata mak'oshi a fili ta furta dole ma bayan komai Ya lafa na d'auki d'ana mu gudu, naje na sami gangariyan miji irin Jalal na aura... Haka ta wuce d'aki zuciyarta cike da Kishi da takaicin duk k'ok'arinta ganin ta k'ask'antar da rayuwar Zubaidah bata cimma burinta ba saima d'aukaka da soyayyan mutane da take dad's samu.......
"Sun jima suna rungume da juna yaci gaba da lallashinta yana fad'in" It's okay please, ki daina kukan haka, I won't leave you, kinji I'll stay no matter what, we will finish this together I promise you kinji Baby, I'll give Annah chance to explain, and no matter what she's still my Mother ....
"Lamo kawai tayi cikin k'irjinsa sai shan zuciya da sauk'e ajiyan zuciya da take yi akai akai....... A kunnenta yake rad'a mata "Baby could you pls stay here for a while, let me feel your presence pls..... Kasa ce masa komai tayi sai lugude da k'irjinta keyi.... Runtse idanunta tayi sanda taji numfashinsa dabb da fuskarta, shima lumshe idanunsa yayi sanda fuskarsu tayi daf dana juna suna jiyo d'umin numfashin juna..... A hankali ya sauk'ar mata light kiss kan lips d'inta.... Wani shokin ne Ya mamaye illahirin joking.....
.
Runtse idanunta ta kuma Yi sanda taji na k'ok'arin rabata da hijabinta, ..... "Memory d'in abunda Ya faru da ita ya shiga dawo mata, ta shiga jiyo sautin ihun su Salim a kunnuwarta ta tuna yanda suka keta mata rigarta har k'asa, ta tuna Jalal ne ya soma rik'ota Ya mik'ata ma Labib cikin Maye... Runtse idanunta ta kuma yi da k'arfin gaske ta shiga daddamk'e hannayenta....." Da sauri Ya saketa daga rungumar da ya mata..... Ganin yanda ta soma loosing control ta basa tausayi sosai.....
"Hijabinta Ya rufa mata kafin ya soma fad'in" I'm sorry.... I'm sorry baby I didn't mean it. Kiyi hak'uri kinji, bazan sake ba kinji har sai ranar da kika amince mun...... D'agota yayi still tana hawaye, Ya rakota har k'ofan parlorn Annah kafin yace " Goodnight baby..... Kanta a k'asa ta shige da sauri gamida turo k'ofan ta maida ta rufe....
"Tsayuwa tayi jikin k'ofar ta kuma runtse idanunta tana sauk'e ajiyan zuciya a hankali... Ta jima a wajen kafin ta samu ta d'an saita kanta snn ta shige d'aki cikin sand'a....
"Kaman b'arauniya haka ta wuce cikin sand'a ta kwanta.... Duk a zatonta Annah bacci take amma sai taji tace " How is he...???
"Gaban Zubaidah Ya yanke Ya fad'i wayyo Allahnta ji tayi tamkar Annah ta ga duk abunda sukayi da Jalal... Saida ta sauk'e ajiyan zuciya snn cikin d'an daburcewa tace " Eh... Eh lafiansa Lou Annah.... Bata kuma iya k'arawa da komai ba saiyi ma Annah saida safe da tayi.....
"Sauken ajiyan zuciya Annah tayi zuciyarta cike da jin Dad'in samun Zubaidah cikin rayuwarsu......
"Moment d'in da suka kasance da Zubaidah lately ya d'an gusar masa da bak'in cikin da yake ciki, ko babu komai akwai improvement sosai a tsakaninsu, he's hopping one day zata mance komai ta koma normal a hankali....
*****************
"Washe gari haka Zubaidah ta ringa jin kunya, tana son ta shiga ta dubasa amma tana jin kunyan ta yaya zasu soma had'a ido after what happened yesterday...
"Annah ta gama had'a kari snn tace ta kaima Jalal..... Kaman ta mata musu amma ta kasa d'aukan tray d'in tayi ta nufi d'akinsa.... Karaf suka kusa cin karo da Hadiza Hamma na biye da ita a baya yana tambayan ina Jalal d'in" Shakka babu Hadiza ne ta tasosa a gaba,.
"Kallon Zubaidah dataci magani take kafin ta soma murmushi tana wani kalle kalle, dariya ta soma a hankali take fad'in" Hiyye kice kin waye kin soma had'a shimfid'i da Miji..... Harara kawai Zubaidah ta galla mata kafin tayi wucewarta.....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:24] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
59
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Kallo Hadiza ta rakata dashi gamida tab'e baki, k'wafa tayi gamida fuzgo hannun Hamma tace " Toh wuce mu tafi me k'anwa kana gani bamu isheta kallo ba balle gaisuwa.... Bata jira cewarsa ba ta shiga turasa da iya k'arfinta.....
"Da sallama Zubaidah ta shiga d'akin nasa kanta a k'asa, d'aura agogo yake a hannunsa da alama shiryawa yake....
"Da murmushi saman face d'insa ya amsa sallaman nata, Kallo yake kan binta dashi, she looks different yau, bai tab'a ganin kwalliya saman fuskarta ba dukda yau d'inma powder kawai da lip gloss ta shafa tayi looking different, ta k'ara kyau sosai kuma har ransa yaji dad'i this shows she's moving on,...
"Ohh why is he giving me that look, is awkward,.... Ta fad'i cikin zuciyarta, gaba d'aya sai taji dama bata shafa powdern ba,..... " Cikin d'an daburcewa ta soma gaidasa...
"In...ina kwana.
"Karb'an tray d'in yayi ya ajjiye bisa darduma kafin yace" Lafia Lou "Miss Beauriful.
"Miss Beauriful" ta maimaita a zuciyarta, jiya ya kirata Baby yau kuma Miss Beauriful.... Kaman yasan tunanin da take yace " You look gorgeous Miss Beauriful, so how Was your night, did you sleep well... Ya tambaya yana kallon face d'inta.
"Wasa take kanyi da 'yan yatsun hannunta , a hankali ta gyad'a kanta tana fad'in" Lafia, yaya jiki.?
"Still kallonta yake kafin yace " Naji sauk'i yanzu..... Zo ki zauna ya fad'i yana nuna mata gefe dashi... Babu musu ta k'arasa ta zauna...
"A hankali ya furta Serve me Miss Beauriful...
"Oh I'm sorry ta fad'i sanda ta soma d'aukan plate da spoon.
"Um um Miss Beauriful I can't eat any solid, tea kawai is okay....
"Are you sure..? Ta fad'i tana d'an kallonsa sai snn taga yanayin shigarsa yayi matuk'ar kyau, cikin Red Armani shirt da Faded Blue Jeans, bata iya jure kallonsa da sauri ta sadda kanta k'asa...
"Zubaidah ya kira sunanta sounding serious.
"D'agowa tayi ta kuma dubansa " Hannunta ya rik'o kafin yace " Thank you for been here....
"With a smile on her lips tace " Haka ne ya kamata, you've always been there for me..... Sun jima suna kallon juna kafin sukaji sallaman Annah...
"Zubaidah ce ta iya amsa sallaman ta nufi k'ofa ta bud'ewa Annah. Suka sakar ma juna murmushi kafin Annah tace " Daughter ya tashi kuwa..?
"Gyad'a mata kai tayi kana tace " Eh ya tashi Annah ki shiga ni barinje nayi sharan nan, ta k'arashe maganar tana bawa Annah hanya...
"Hannunta Annah ta rik'o snn tace " Muje Daughter kema ya kamata kisan komai, besides he's your husband..... Kaman rak'umi da akala haka Annah tajata suka koma ciki....
"Yana nan tsaye yanda Zubaidah ta barsa idanunsa tabb k'walla yake duban Annah, itama k'wallan ne cikin idanunta.....
"A hankali ta soma furta " I'm so sorry son...... Bai jira ta k'arasa ba ya k'araso da sauri gamida hugging d'inta yana fad'in" Pls don't Annah, you've nothing to apologize, on the contrary I should be the one to apologize, I'm nothing but an ungrateful.... Meyasa zanyi fushi dake after all the sacrifices you did for me. Kiyi hak'uri pls, I shouldn't have reacted that way...... " Girgiza kai ta soma gamida rik'e face dinsa tace " No Son this is all my fault, da ace na fad'a maka gaskiya tuntuni da ba haka ba... But believe me I kept it from you because I don't wanna lose you, and all I wanted back then is to keep you safe...
"Kamo hannunta yayi ya zaunar bakin katifarsa hannunsu rik'e cikin na juna yake fad'in" A iya zamana dake ban tab'a tunanin bake kika haifeni ba, sabida you've always been a good mother to me, ko a baya lokacin da na kasance the mysterious child , you never neglect me, nasan koma su waye iyaye na iyakacin kulan da zasu bani kenan, you raised me all alone, you my Mum and My Dad at the same time, na gode Annah I can't ever repay you for that,....
"Murmushi tayi gamida d'an jawo kunnensa tace " But you still owe me an explanation, things are different now, you've Your Own Family... What I meant kana da aure yanzu and batu na aure batu ne da ya kamata ya zama pure and transparent. .. Juyowa yayi ya d'an kalli Zubaidah itama shi take kallo, saurin kawar da nata idanun tayi...
"Annah tayi murmushi ta rik'o hannun Zubaidah dana Jalal kafin tace " 'ya'ya na yau zan gaya maku wanene d'ana Jalaluddeen....
"Shekarun baya, iyayena sun kasance fulani makiyaya masu yawo gari gari, a garin Dukku ta jihar gombe a nan ne iyayena suka zauna suka jima har suka haifemu nida yaya na guda d'aya tol, Lado, ina matashiyar budurwa Allah yayi masu rasuwa su duka biyu a jere a Jere, Haka muka ci gaba da kiwonmu nida Lado, watarana Lado ya auro wata mata Lantana, wann mata bata da mutunci sam, haka ta ringa gallaza mun har saida na gwammace nayi aure koda mahaukaci ne, don na huta da azabar Lantana.
"Inada wani saurayi Malam Ibrahim saidai shi yaren mu ba d'aya bane, Lado ya k'ek'ashe bazan auri had'e ba, nace masa musulmi ne shima amma Lado ya k"ek'ashe wai had'e ne, k'arshe Lantana tace a badani amma bani da gadon shanun mahaifa na , nidai nace naji na aminta..... A haka aka Aura min Ibrahim badason ran Lado ba... Kunsan bafulatanin mutum da rik'o.... Na d'au shekaru Allah bai bani haihuwa ba, kwatsam watarana saiga ciki, na haifi yarona namiji kyakyawa mijina ya zab'i a saka masa Jalaluddeen, har akayi suna Lado da Lantana babu idonsu, bayan suna da kad'an mijina ya fita gona sai gawarsa aka kawo mun, naci kuka sosai, kuma nasan tunda Lado yace baya son auren nan tofah sai yanda k'arfinsa ya k'are... Ina nan ina takaba, watarana Lado yazo gidan maimakon ya min ta'aziya sai masifan da ya ringa surfa mun k'arshe yace " Saura wann had'en da kika haifa mana a uzuriya shima sai na kashesa, nan na gane Lado ne ya kashe mun miji, asubahin fari na had'a kayana na bar gari, nabi Daji, abunka da bafulatana sam tafiyar bata dameni tunda dama mun gada, Jaririn yarona ya kasa jure tafiyar a hanya Jalaluddeen Allah yayi masa cikawa, naci kuka har na gode Allah, daga baya naci gaba da tafiya tunda banida wani zab'i.... Bayan kaman kwana guda ina zaune k'ark'ashin wata bishiya na hange abu an duk'ulk'ulesa, koda na k'arass sai jin kukan jariri nayi, cike da firgici na tsuguna na duba dun tabbatarwa, ai kuwa jariri ne aka yasar sa wajen, d'aukosa nayi ina jijjiga shi ina mamakin wani mahaluk'i ne zai yasar da d'ansa haka ni gashi ina kukan rashin nawa da na yi..... Saida na duba jaririn sosai naga yanayin suturan dake jikinsa na tabbata ba iyayensa bane suka jefar dashi, wani mugu ne me neman ganin jaririn a mace. Koda na d'auki Jaririn nan na rasa me zan kirasa, zuciyata lokaci guda ta fad'a mun Jalal ne ya tafi Allah Ya kawo maki wani. Take na ambaceka da Jalaluddeen....
"Ta d'an ja fasali tana dubansu gaba d'aya hawayene ya wanke fuskokinsu kafin taci gaba da fad'in" Kasancewad a lokacin d'ana bai jima da mutuwa ba sai naci gaba da shayar da kai, na yanke shawarin dawowa gida da kai tsoron kada kaima ka galabaita..... Koda na koma Lado frightens me again, cewa wllhi sai ya rabani da wann had'en.... Jin haka ya haifar min da firgici, don lakaci guda Allah Ya saka mun soyayyar ka fiye da d'ana dana rasa. Da wann dalili ya sanya ni sayar da wasu 'yan kadarana dukda Lantana ta kwashe kusan duka kayana. Na shiga mota nazo garin Gombe, a nan ne na had'u da iyalan Dasuki family na soma masu aiki har na shiga makarantar yak'i da jahilci don na samu na gudanar masu da aiki yanda suke so, bafulatani da saurin fahimta tuni na fahimci abubuwa.... Na soma rainon yaransu wa'enda suke tsara da Kai wato Labib da Salim, jin dadin aikin da suke yi tare dani yasa su aminta dani sosai dukda k'arancin shekaru na a wancan lokacin... Hajiya Farha mahaifiyar Salim tayita kawo mun zancen aure a wancan lokacin nak'i aminta na nuna mata ni babban buri na shine nayi raising d'inka well, banyi aure ba balle 'ya'yan mijin ko shi mijin ko matarsa su tsangwame ka... A haka har muka dawo Abuja tareda su, wanda hakan ma yafi mun ko babu komai nayi nesa dasu lado..... Wann shine labarinmu Jalal,..... Ta k'arashe tana goge hawaye.....
"Cikin kuka Zubaidah ta rungumeta tana fad'in" Ashe ba ni kad'ai bace na had'u da iftil'ai na MATAN YAYA ba, you also suffered from some of my experiences.....
"Annah tace haka ne Zubaidah shiyasa duk me nemanka da sharri ka tura masa aniyarsa, har a gurun Allah kaine ka fishi....
"Basu ankara ba sai ganin Jalal sukayi durk'ushe gaban Annah yana kuka sosai..... K'arshema d'aura kansa yayi saman cinyoyinta yayi mai isarsa " He's out of words, but all he knows is that he owes Annah his life... She's a Heroin to him, she's his savour his everything,... He wasn't mistaken she sacrifices her life for him to survive, what on earth would he do to repay her all she's done for him, amsar shine babu wanda ya wuce ya k'aunaceta a matsayin mahaifiyarsa ya kuma ci gaba da yi mata addu'a har k'arshsn rayuwarsa......
"Fita wajen aikin da baiyi ba kenan sai wajajen LA'asar ya fice ya nufi garejinsu, cike da mamakin rashin jin Usman, shirun nasa yayi yawa....
"Yana isowa abokan aikinsa suka soma gaidasa suna masa jajen abinda ya faru, don labarin is everywhere now, chan jikin wata Tanka ya hangi Baban Usman wanda dama shine mai garejin, tunda ya hangi Jalal ya b'ata fuska...
"Da sallama Jalal ya k'arasa yana fad'in" Barka da maraice Baba, mun sameku lafiya...
"A ciki ciki Baba ya amsa ba tareda ya k'ara da komai ba, Jalal ya d'anyi Jim kafin yace " Baba a min afuwan rashin zuwa aiki kwana biyu, hakan ta kasanc...... Dakatar dashi Baba yayi kafin yace " Jalal a gaskiya bazan b'oye maka ba, bazaka iya ci gaba da aiki a wann garejin ba, nasan kanada k'wazo amma gaskiya dole ka ajiye aikin nan....... "Zaro sogayen idanunsa yayi baki har na rawa yake fad'in" Baba kayi hak'uri, inada iyalai kuma da wann aikin kawai na dogara, Baba idan fashin da nayi ne I promise to make it up to you, i'll work harder na kuma k'ara extra working hours in fact zan iya zuwa har a ranakun hutu, but pls don't fire me....
"Jalalu saidai fah kayi hak'uri don a gaskiya banyi shirin rasa wann gareji ba, yau kwana hud'u knn wasu mutane majiya k'arfi suna zuwa suna nemanka, snn sunce duk randa sukaga k'afarka a nan sai sun kashe.. Ni kuwa inaji ina gani bazan bari tashin hankali ya samemu ba, shiyasa ma nace masu ka bar aiki, yau shekaru kusan ashirin kenan da Bud'e wann gareji ba'a tab'a samun matsala ba saida kazo, snn ban tab'a samun sab'ani da d'ana Usman ba saida kazo, akan nace bazan k'ara aiki dakai ba, Usman yayi zuciya yayi tafiyarsa can Katsina garin mahaifiyarsa... Kaga kuwa ajiye aikinka shi yafi alkhairi Malam Jalal....
"Ya jima yana tsaye a wajen kaman an dasa kafin yace " Haka ne Baba, I'm surrounded with alot of troubles, and the last thing I want is to drag you in, na gode Baba, ttaimakon da kayi Allah Ya biyaka. pls idan kanada layin da zan sami Usman ka taimaka min dashi.....
"Yaro don Allah ka tafi kafin mutanen nan su riskeka a nan, kayiwa Allah ka tafi....
"Hak'uri Jalal ya basa kafin ya soma tafiya, gaba d'aya 'yan garejin basuji dad'i ba har suna murna Jalal ya dawo....
"Koda ya dawo gida a baranda ya zauna saman dakali gamida yin tagumi yana tunanin rayuwa, wann shine kad'ai aikin da yake yi gashi ya rasa, how would he support his family, how, a hankali ya soma anbaton Allah... Daidai nan yaji hannun Zubaidah a kafad'unsa.
"D'agowa yayi ya dubeta gamida sakar mata murmushi k'arfin hali...
"Har yanzu tunani lake ta tambaya tana mma zama d'an gefe dashi...
"Fuzar da iska yayi kafin yace " Tunani nake yanda zan rik'eku na ci daku da halal and to give you the life that you deserves.
"Pls ka daina sa ma ranka damuwa we are living a good life haka ma Alhamdulillah.... Gyad'a kansa yayi a hankali kafin yace " that was then Zubaidah, ina tsoron rayuwar da zamu fiskanta a yanzu, cos I'm.. I'm jobless, I lost my Job, I was fired, those Imbeciles will never leave us alone ...
"A tak'aice ya labarta mata komai...
"Idonta ya kawo ruwa, a hankali ta soma furta, Why life has to be so selfish..... Da sauri ya rufe mata baki kafin yace " Kar kiyi butulci wa rahaman ubangiji, this is all part of the trials in life, dole ubangijinmu ya jarabce mu ta yanda bamuyi tsammani ba, Allah Ya bamu ikon cin jarabawarmu.. I know we can survive this, we can go through it okay, Allah bazai barsu ba da sannu zai kamasu lokaci guda kaman yanda yayi wa pir'auna..... Rungume juna sukayi yana lallashinta.....
"Daga chan Hadiza ta hangosu rungume da juna ta saka shewa tana tafe hannu tana fad'in" Ah fillo an waye, Zubaidah kece mak"ale a k'irjin namiji.... A fusace ya d'ago zaiyi magana Zubaidah ta girgiza masa kai alamun a'a, a hankali ta furta " Let her be, this is all she knows.... Haba nan fah Hadiza ta k'ule ta soma surfa masifa wai Zubaidah zaginta take da harshen nasara, yaushe ta waye tazo birni, waya koya mata wanka har ta zama mutum, ... Fuuu ta wuce kirawo Hamma...
"Hayaniyarta ya d'aga Annah, Zubaidah kam tagumi kawai ta rapka tana tunanin yaushene zata rabu da masifar Hadiza... Jalal ya dubeta cike da damuwa, kai kodon Jarabar Hadiza zai karkad'e takardunsa ya nemi ko wani irin aiki ne ya d'auke matarsa ya rabata da wann Lunatic Woman d'in... Gaba d'aya bai iya hayaniya ba, amma sabida jarabar Hadiza yanajin zai koya......
**********************
*Marafah Construction Company*
"Har wajajen 11:00pm Alh Tahir bai fito daga company d'inba kasancewar kaya mai yawa ake sauk'ewa a store d'insa mai d'iban containers sama da d'ari.... Suna nan cikin store d'in shida muk'arrabansa suna tantance kayan nan suka soma him smoke ya gauraye ko ina, nan suka soma tari, securities suka shiga k'ok'arn danna abin kawo d'auki, the worse part d'in shine gaba d'aya exit na company d'in an gargark'amesu, babu hanyan tsira.....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:25] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
60
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Kausar zaune saman gado tana kuma bin takardan sakin da yau Pappy ya karb'o mata daga wajen Salim a prison, goge hawayen idanunta ta kumayi zuciyarta na mata zafi, ta tuna satuttuka k'alilan baya tana cikin farin ciki sai gashi yau ta tsinci kanta da akasin haka, lallai ubangiji abin tsoro ne.... Shigowar Asmah cikin wani irin kuka yasa Kausar mik'ewa tsaye zunbur tana tambayarta lafiya...?
"Cikin shesshekar kuka Asmah take fad'in" Kausar Pappy.... Pappy ne, ...
"Rik'eta sosai Kausar tayi kafin tace " Asmah me ya sami Pappy na ina yake..... Bata iya amsata ba sai mik'a mata wayarta datayi nan taga yanda company d'in keci da wuta fire service sai k'ok'arin dakatar da wutan suke amma sun kasa.... Cikin sauri Kausar ta nufi downstairs tana fad'in" Pappy must be home ai, no My Pappy is at home, nothing bad will happen to him,.... Sandarewa tayi jikin staircase ganin Mumsy durk'ushe gaban mutum an rufesa da farin k'yalle....
"Wani fincika Kausar tayi gamida k'walla uban k'ara nan ta zube a k'asa sumammiya..... Mutanen dake parlon suka bi takanta Mumsy kam ita kanta hankalinta baya jikinta....
"Wasu securities biyu ne suka kuma shigowa parlon suka dubi Mumsy suka ce " Hajiya we are sorry we couldn't stop the fire...... Basu kai aya ba Mumsy tace " Ku fice mun a gida don Allah, na rasa abin da yafi dukiyar da take kan k'onewa, ku fice mun kafin nasa a fitar daku..... Ta k'arashe maganar tana kwantar da kai saman k'irjin Pappy....
"A hankali take fad'in" Meyasa ka tafi ka barmu Tahir, bazan iya rayuwa babu kai ba, why why Pappy.... K'arasowa Kausar tayi ta zube akan Mumsy tana wani irin kuka mai ban tausayi.... Wann dare gabaki d'aya Iyalan Alh Tahir Marafa haka sukayisa yanda sukaga rana haka sukaga dare.... Kan kace Me gida ya cika da jama'a abunka da Mutum mai yawan hidima da jama'a......
********************
"Washe gari da sassafe Ansar yazo d'aukansa maganar tafiyarsu Dukku sabida bincike da 'yansanda zasu aiwatar a yanda incidence ya faru, snn sunaso suyi reaching Dr d'in as soon as possible, ..
"Har k'ofar gida suka rakosu, idanun Zubaidah yayi rau rau Jalal ya gane hakan,... A hankali ya matso yanda take sanda su Annah suke kan magana da Ansar dashike shima gwani ne wajen zuba surutu....ya d"an rage tsawonsa saitin kunnenta yake rad'a mata...
"Hey don't cry, I won't stay long there, just a couple of days kinji Miss Beauriful, and Hamma zai ringa rakaki sch... Take care I love you..
"A hankali ta furta " You too take care......
"Wayan Ansar ne ya soma ringing a zatonsa su Detective Amir ne don tare zasuyi tafiyar, ga mamakinsa Lambar Asmah ya gani...
"Murmushi ya d'anyi data dace da kyakywar face d'insa wanda yake wankan tarwad'a kafin ya d'an ja gefe ya d'aga yana fad'in" Hello my Annoying Attorney kin tashi lafi....... Bai kai aya ba jin yanayinta.... " Cike da tashin hankali Ansar yace " Asmau Lafiya... Make faruwa..??
"Cikin kuka take fad'in" Ansar Pappy ne, My uncle has gone...... Bata gama yin shiru ba ya shiga jero salati da addu'o'i.... Kuka ta fashe mashi dashi sosai, Ansar ya shiga lallashinta hankali tashe... Cike da jimami suka k'arashe wayar, Ya maida dubansu gasu Jalal Wanda kwacaukwan hankulansu kega fuskar wayar Jalal... Jiki a mace ya k'araso garesu, Annah ta d'an subesa kafin ta k'arasa don kuwa suma news d'in da yanzu suke ganinta a wayar Jalal ta matuk'ar girgizasu.....
"Ansar kaji labarin ko, ta tambaya tana dubansa...
"Idonsa jazir yace " Kuma kunji koh, Alh Tahir Allah Ya masa rasuwa a sakamakon gobara da companynsa tayi... Annah ta gyad'a Kai tace gacan labarin da yanda wuta taci company d'in a wayar Jalal, ..
"Da sauri Ansar ya k'arasa ya amshi wayar Jalal yana gani...
"Ko menene yayi causing wutar sai Allah. Cewar Annah...
"Jalal ya d'an shafe gishinsa kafin yace " Wutar tafi kama da kunnata akayi, don daga waje ta soma ci kafin ta shige ciki...
"Ansar har lokacin kallon video d'in yake kafin yace " Definitely wann kunnata akayi...
"Annah tace " Toh wa zai masa wann aiki na zalunci haka....
"A hankali Ansar ya furta ALH KASIM.... Sunji abunda yace gaba d'aya suka juyo suna dubansa..
"Meyasa zai masa haka, after all he was his business partner...cewar Jalal fuska cike da damuwa...
" Fuzar da iska Ansar yayi kafin yace " Kafin Alh Tahir ya rasu sunyi baran baran da juna, The Marafah's and the Dasukis are now against each other.... Annah ta danyi jimm kafin tace " Exactly na tuna lokacin da d'yarsa Kausar tazo nan don taimaka mana tabbas basa good terms...
"Ansar yace " So sun zo nan before su sameni..?
"Da mamaki suke duban Ansar, ..... Dafe kai ya d'anyi kafin yace " Banso kuka sani bar, but ya kamata ku sani coz mun zama d'aya yanzu...
"Kausar da cousin d'inta Ansar su suka had'ani da case d'in Zubaidah, at first nak'i yarda masu sabida nasan halin Kasim Dasuki, nasan shi waye, he's the reason why I lost everything... A d'an tak'aice ya basu labarin grudges d'insa da Alh Kasim....
"Mamaki ya cika su....
. "Zubaidah na hawaye ta soma fad'in" If that's the case the Dasukis must be watching us, precisely sun gane we are somehow allied with the Marafah's, and nayi imani duk wanda suka san munyi alak'a dasu wajen karyasu toh sai sun gama dasu...... Kuka sosai ya kufce mata sanda taci gaba da fad'in" It's because of me, ni ZUBAIDAH everyone has to suffer saboda ni, maybe da ban yi magana ba things will different.... why me..why....
"Da sauri Jalal ya k'arasa ya rik 'e hannayenta kana yace " This is non of your fault, the Dasukis are to blame, sune sila, and they must all pay for each and single crimes they had committed.... Share hawayen nan I don't wanna see them.... Gyad'a masa kai kawai tayi tana share hawayen....
"Jalal ya k'arasa wajen Ansar yana fad'in" So what would we do now Attorney, kanaga tafiyar nan namu zata yuwu kuwa, Asmah needs you now, ya kamata ayi zaman nan har kwana uku dakai, snn now I'm afraid to leave my family all alone, ina jin tsoron kar wani abu ya samesu, looks like Alh Kasim is desperate, he's willing to do anything to take his out of prison, he's capable of anything.....
"Ansar ya dafasa yace " You're quite right Jalal, but that doesn't mean zamu k'yalesa yaci gaba da ta'addanci da kashe innocent souls.... Snn kasan Prosecution office ne suka tura Detectives d'in don gudanar da bincike, bazai yuwu a d'aga masu rana ba, snn you the only one that knows the place, so you really have to go, don't worry about your family, nida Hafiz muna nan we would look after them insha Allah. You have my word...
"Gyad'a kansa Jalal yayi kafin yace " I trust you Attorney, Allah Ya bamu sa'a ya d'aura mu kan azzalumai...
"Ansar ya amsa da Ameen thumma ameen, wayarsa ya latsa lambar Detective Amir kana yace " Detective bamu ganku ba...
"Daga d'aya b'angaren Detective yace " Mun riga mun wuce Attorney, you also should be on your way, coz we want to do this as soon as possible...
"Ansar ya amsa da okay Detective, yeah right, sure... Bayan ya katse wayar ya dubi Jalal yace " Jalal you need to get going sun riga Sun d'auki hanya, and the prosecutor yana expecting report d'in before our up coming trail, kar ka mance maganan Dr d'in, do anything you can reach him, we will be on touch....
"Gyad'a kansa kawai Jalal yayi amma har cikin ransa tunani yake Allah yasa kud'in jikinsa su ishesa.....
"Sallama suka kumayi da Annah da Zubaidah Ansar ya kaisa har tasha....
***********************
"Isowarsa garin kenan sai wani cincin magani yake, tsaki ya kuma ja a karo na babu adadi ganin jikin mahaifin nasa ba har yanda Balele yake fad'i masa bane a waya, .
"Inna ta ajiye masa damun fura a gabansa tana fad'in" Kashi abunci ka kwaso hanya....
"Kauda kai gefe yayi ya kuma jan tsaki a hankali gamida watsa wa Baffah dake kwance kan tabarman azara wata uwar harara.... Inna ta kuma nanata masa a karo na uku....
"A hasale ya katseta da fad'in" Inna nace maki bansha bansha ko dole ne...
"Jiki har na b'ari Inna ta d'aga k'waryan tana fad'in kayi hak'uri Baba Wuro, aradu bansan ka daina chi bane.... Yayi gajeren tsaki kafin yace " Tashi tashi ki kamasa mu kaisa asibiti....
"Babu musu Inna ta soma cicciban mijinta, ko kallo basu ishe Umar ba yayi ficewarsa waje yana karkad'a key d'in mota...
"Bayan sun isa garin da location d'in da incidence d'in ya faru suka soma kasancewar gari ya soma duhu.... Nan da nan Detectives suka soma aune aunensu harda tape suna d'aukan wajen a hotuna.....
"Ganin wajen ya tuno masa komai, yasa sa tuna wancan bak'in daren, d'ya bayan d'aya haka abubuwan suka ringa dawo masa kwanyarsa....
"Detective Amir suna gama abunda zasuyi suka dau hanyar Abuja a lokacin, Jalal kuwa baici ta barin gari ba, he really need to find that Doctor....
*******************
"Admitting Baffah akayi Umar sai wani foffozewa yeke irin shi ga shegen nan, Likita na masa bayanin ciwon uban nasa ko kulasa beyiba yayi ficewarsa yana fad'in is non of my business, you can discuss that with his wife, nayi iya abunda zan iya tunda na biya charges d'in.....
... "Danno kan da zaiyi ya hangi fuskar Jalal ya tunk'aro ward d'in" Cikin sauri ya lab'e har saida Jalal ya wuce. .
"A hankali ya furta what is that jerk doing here.... " Shi kad'ansa ya saki wata murmushi a hankali kafin yace " I'm pretty sure ka kawo kanka kabarinka...
*Mannage this guys 😍😘*
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:25] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
61
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Jalal ya dubi likitan dake gabansa cike damuwa yace " Yanzu Dr bakasan yanda zan samesa ba, baka san ina ya koma ba. .
"Dr ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Dr Hashim ya kwana biyu da barin asibitin nan kai garinma entirely, and a iya sanina ba gwamnati bane ta canza masa wajen aiki, wayan gari akayi aka rasa sa, he disappeared just like that.
"Hannu yasa cikin gashin kansa yana cukurkud'asu kafin yace " I knew it, they will do anything in their powers to hide that imbecile so called Dr... Damn it....
"Dr ya dubesa kafin yace " You alright...?
"D'an kallon Dr yayi kafin yace " Oh yeah yeah I'm fine... Anyway na gode k'warai Dr pls idan kaji wani abu gameda wancan Dr d'in pls let me know right away....
"Dr Madi ya gyad'a kansa kafin sukayi exchanging phone number da Jalal... Har bakin asibiti ya rako Jalal kafin ya koma.....
"Tunani ya soma yi where would he stay to spend the night, gashi babu wadateccen kud'i a jikinsa balle ya kama room a hotel, gashi shi ba sanin kowa yayi ba... Agogon hannunsa ya duba kafin ya furta Shattima a hankali...
"Wayan Shattima ya shiga nema.. Saida tayi ringing har kusan sau uku kafin aka d'aga...
"Daga d'aya b'angaren da murna Shattima ya d'aga suka soma gaisawa da hiran yaushe rabo.... A gurguje Jalal ya fad'awa Shattima gashi a yankinsu...
"Shattima harda wani d'an ihu da tsallen murna kafin yace " I'll come and get you bro..
"Murmushi Jalal yayi kafin yace " No.. No no you don't have to that zanzo da kaina, idan na iso sai na kiraka..
"Shattima yayi yayi yazo ya d'aukesa Jalal yak'i amincewa, dole ya hak'ura aka bi ra'ayin Jalal.....
"Daga bayan bishiyar da ya lab'e ya gama jin hiran Jalal snn ya gane ina ya dosa.... Shi kad'ai ya fashe da dariya kafin ya shiga neman layin Balele.
"Balele yana d'agawa ko gaisawa basuyi ba Umar yace " Kana Tasha ne..??
"D'an tsaki Balele yayi kafin yace " Toh idan ina tashan me zan maka, don har yanzu fushi yake da Umar....
"Gajeren tsaki yayi kafin yace " Ka fad'a mun mana bana son wulak'anci...
"A tak'aice yace masa " A'a bana nan...
"Okay su Boris fah kanaga zan samesu....
"Da mamaki Balele yake fad'in" Yau kuma kaine da neman su Boris me zasu maka...
"Cikin sauri yace " A'a no babu komai kawai so nake mu d'an gaisa don yau yau zan wuce kasan bazan iya kwanan garin nan ba...
"Balele ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Ummaru kayi hattara da duniya, itafah wann rayuwa da kake ganinta wllhi ba komai bace " Gaba d'aya ka canza ka koma wani abu daban, kar ka mance a da kaine mai mun nasiha nabi duniya da iyaye a Sannu amma yanz...... Cikin hasala ya katse sa da fad'in" A'a a'a don't you dare scold me, who the heck you think you are to lecture my authority... Ina ragar maka ne for old time sake.. Mtsw useless kawai.... Daga haka ya katse wayar....
"Yasan probably Jalal bai isa bakin tasha ba tunda a acab'a zaijeshi.... Da d'an banzan gudu ya kwashi motar sa ya nufi tasha wajen aikinsa a da...
"Bai jima yana neman su Boris ba ya samesu a lungun da suke zama suna shan kayan maye, basu sha mamakin ganin canzawan sa ba tunda ance ya tafi bulaguro... Haba nan fah su Boris suka shiga masa fadanci, shi kuma sai d'dd'aga kai yake uwa namijin k'adangare.....
"Umar ya ciro kud'ad'e ya mik'a masu kafin yaci gaba da fad'in" Kuna jina zaku gansa wani d'an dogo baida jiki sosai, fari ne sosai mai yalwan suma.... I want you guys to Finish him up....KILL HIM...
"Qazaza na tangad'i yake fad'in" ka mana bayanin yanda zamu gane da yaren da muke fahimta....
"Umar ya d'an tank'wafo yana waige waige kafin yace " Ina nufin ku kashesa har lahira.... Dariya suka tuntsure dashi kafin suka ce an gama, masu gidan rana kawai zaka k'ara mana, babu musu ya k'irgo kud'i ya kuma basu, don idandai akan ya sami Zubaidah ne ta zama MALLAKIN SA babu abinda bazai yi ba...
"Daga nan ko asibiti bai koma ba ya d'auki hanyar Abuja cikin palpala gudu abinka da lafiyayyar mota, zuciyarsa fari k'al ya kusa mallakan Zubaidar sa, the love of his life.....
*******************
"Bai sha wahalan samu motar da zata fitar dashi zuwa cikin garin Gombe ba, saidai matafiyar basu da yawa...
"Sunyi nisa sosai kafin daga nesa suka hango Danger ana dakatar dasu.... Driver ya soma salati yana k'ok'arin sake starry, Jalal dake front seat shima salatin yake yana tambayar driver meke faruwa.
"Bawan Allah ai inaga mazan daji ne.... Daidai sanda suka bugi motar da sanda suna fad'in" Tsaya tsaya ko uwarka ta haifi wata ....
"Mazan Daji Jalal ya nanata a hankali... Finfincike marfin motar sukayi idanunsu a rurrufe ga sanduna da dangin su adda a hannunsu suke fad'in" Ku fito, ku fito akace....
"Tsegege Jalal ke kallonsu yana mamakin wann irin rashin imanin ganin harda mata cikin motar suke fad'in" A kwanta a k'asa.... Ai kaine d'an iska bazaka kwanta ba ko, cewar d'aya daga cikinsu... Jawosa suka shiga yi suka sauk'a jeji dashi yana fad'in" Ina zaku kaini, ku karb'a abunda kuke so, me zaku mun..... Tummm yaji sauk'an murtuk'ek'iyar sanda a gefen kansa take jini ya watsu ya kwanta a k'asa....
"Driver da sauran 'yan motan harda budurwarsu wacce da ita aka had'a plan d'in suka kwashe da dariya suka koma garin Dukku, don dama k'arya suka masa bazai sami motar Gombe a lokacin ba.
"Dukansa suke kaman Allah ne ya aiko su, tun yana 'yan k'ara yana rik'e cikinsa har ya daina, sai ka rantse hatsi suke bugewa yanda suke runtuma masa sanda da iya k'arfinsu.... Tun yana d'an motsa yatsun sa har ya daina.....
"D'an mirginar dashi sukayi tabbas baya numfashi nan suka fashe da dariya suka shiga jawosa a k'asa har k'ark'ashin wata bishiya snn suka k'yalesa.....
********************
"Shattima ya kira wayar Jalal yafi abunda yafi, gashi dai tana ringing amma ba'a d'agawa, hankalinsa ya tashi sosai ganin dare ya soma ja....
"Tsakar gida ya fito yaci gaba da trying layin still shiru, ba'a d'agawa.....
"Ameera ce ta hangosa daga kitchen taje dafa indomie ta k'araso tsakar gidan tana fad'in "Yaya wai Aunty Zahidah kake nema ne haka.....
"Harara ya b'alla mata kafin yace " Ke wai ni sa'anki ne, k'arama dake sai sa ido, yaushe ma na soma wann wasan dake.....
. "Ameera ta turo baki tace " Au gani dai nayi munada little secret d'inmu nida kai ko kana so na fad'awa Umma, ta d'an soma jada baya tana dariya take fad'in" Ranar da Aunty Zahidah tazo kuka sha kukan soyayya...... Tsalle d'aya yayi ya capko ta kafin yace " Haba little deal d'inmu ne wancan ai.... Yasan halin Ameera da shegen zuba uwa kurna yanzu saita yad'a sa har kunnen Khalifa... Umma ce ta fito daga sashen Baba Waziri ta hangesu tasan wata suke k'ullawa tunda ta gansu haka....
"K'arasowa tayi tana tana watsa musu kallo kafin tace " Uban me ku kuma kuke k'ullawa....
. "Ameera ta washe baki tace indomie nake dafa mana ai kema zakici ko Umma...... Rufe mun baki Umma ta katse ta kafin tace " Ni zakuyi ma Boko, yaushe aka haifeki Ameera, wato ya k'ulla maki munafuncin da zaki fad'a ko, ai dai kam idan aka ganku ku biyu cikin shiri da juna wata kuke k'ullawa tunda sam bakwa zama inuwa guda....
"Shattima yace " Umma Ameera fah only sis d'ita ce, idan kinga ina scolding nata so nake ta zama good girl, right little...?? Ya k'arashe yana duban Ameera da har ta soma sakin layi tana fad'in" Eh mana ai Umma ta zaci waya kake da Aunty Zahida tunda tace ka mance..... Jawo Ameera yayi yana faman toshe bakinta....
"Umma ta fizgota tace " Munafuki barta ta fad'a, ta shiga tafe hannaye tana sallalami take fad'in" Auho wato Shattima har kuka ka soma yi sabida mace, Na shiga uku ni Amina, ban haifi lusari ba..... Ta soma k'ok'arin fuzge wayan tana fad'in"Bani naga uban da kake kira....
"Ran Shattima idan yayi dubu ya b'aci, har ransa masifar Umma na damunsa, mik'a mata wayan yayi yana fad'in" Haba Umma ni shikenan bazan girma ba a idanunki, fah yanda kike d'aukan Ameera haka kike d'auka na, toh gashi ki gani abokina da nake baki labari shi nake kira, yace mun yana hanya kuma har yanzu bai iso ba,... Gashi see it your self... Ya k'arashe maganar yana bata wayar fuska a murtuk'e ya wuce d'aki.....
"Baki Umma ta sake kana tace " Kafi shanu d'aurewa...
. "Ameera ma baki a ture ta wuce d'aki tana fad'in" Umma wllhi yanzu shiknn kinsa zai fasa bani kyautar da ya min alk'awari....
"Tab'e baki Umma tayi ta rakasu da kallo ta soma tafiya tana fad'in" Can ta matse maku, kunfi kusa.......
**************************
"Bacci take had'e da wasu irin mafarkai marassa kan gado, idan tayi mafarkin saita farka a firgice, idan tayi addu'a sai ta samu komai ya lafa mata, hankalinta yafi karkata kan son sanin halin da Jalal yake ciki, tunda sukayi waya yace zaije ya nemi Dr d'in basu sake waya ba, haka kurum tunanin sa ya haifar mata da fad'uwan gaba mai tsanani... Mik'ewa tayi ta d'au wayanta ta shiga neman layinsa dukda dare da ya. ja..
"Haka wayar ta ringa ringing babu response, hankalinta taji ya tashi sosai, haka kurum jikinta ya bata something is going on with him, she has a feeling he's in danger....... Tsawa akayi kasancewar hadari da ya had'u sosai..... Kecewan ruwan yayi daidai da kecewar kukanta.........
"Babu shiri Annah ta bud'e ido firgit ta hangi Zubaidah dake k'ank'ame da jikinta tana kuka....
"Mik'ewa Annah tayi ta kunna tocila tana fad'in subhanallahi lafiya Zubaidah, meke faruwa.....
"Cikin kuka take fad'in" Annah bai d'auki wayata ba, what if something bad happens to him, what if he's life is in danger, what if he doesn't come back to me, what if that was the last goodbye what if bazan sake ganinsa ba.......
"Gaba d'aya gwiwoyin Annah taji sun sake sunyi sanyi, but she needs to be strong, d'an rungumo Zubaidah tayi kafin tace " Ki kwantar da hankalinkk Zubaidah Jalal yana lafiya da izinin Allah, and he will surely come back to us, he's doing this for us to live in peace. Nasan probably yanzu bacci yake shiyasa bai d'aga wayarki ba. But first thing tomorrow morning yaga missed calls d'inki zai kira, ki kwantar da hankalinki kinji.. Gyad'a mata kai kawai take har llokacin hankalinta bai kwanta ba.....
"Oya come here, Annah ta fad'i gamida bud'e mata hannayenta, rungumeta tayi ta ringa shafa bayanta a hankali tana mata tausasan kalamai masu kwantar da hankali.....
***************
"Bashi Ya iso garin ba sai wajajen k'arfe biyu na dare, da mamaki yaga takalmin gardi a k'ofar apartment d'insa, kutuman ubancan ya furta a hankali, yayi amfani da makullinsa ya bud'e parlour, jar ubancan, kwalaben whisky ya gani masu d'an karen tsada, gefe ga ATM d'insa na Diamond Bank wanda baisan yaya akayi ya isa hanun Zulaihat ba,
"stirs ya nufa yana karkad'a kai yana lissafin cin uwar Zulaihat da zaiyi a gidan nan...
Sameena ce
[1/23, 22:25] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
62
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Da k'arfin gaske ya tokari k'ofar saida ta bud'e, kwance Ya hangeta saman rug shame shame basai an fad'a maka a shaye take ba...
"Tsaki Ya buga Ya soma toshe hanci yana mai shiga d'akin, quite messy and untidy.... Kai dagaji ma d'akin warin amai na barasa take...
"Da k'afarsa Ya shiga shureta yana fad'in" Ke Ke tashi dalla, ki tashi nace....
"Bata tashi ba sai faman shure shure da take... A fili Ya furta
_"What a f**k"_
"Da k'arfin gaske Ya fincikota gamida d'aura mata lafiyayyar mari wanda yasata bud'e ido firgit babu shiri..
"Tun tana ganinsa duru duru har ta hangesa sosai yana tsaye gabanta sai huci yake kaman wani mayunwacin zaki... Bata tsamman zai dawo yau ba, cikin sauri ta soma fad'in" Dama zaka dawo, bansani ba I should have placed order for you.....
"Da k'arfi yace " Shut your trap you bitch... Bayani zaki min wani d'an iskan kika kawo min gida da bana nan....
"Zulaihat ta Saki murmushi kafin tace " Au Imam ne ba kowa ba....
"Jawota yayi Ya mak'ure yana fad'in" K'arya kike munfuka wancan wines masu d'an karen tsada uban wa Ya saye su, kinsan dai ni ba sha nake ba... Oya fad'a mun gaskiya wa kika kawo apartment d'in nan....
"Cikin k'ak'arin murya take fad'in" He's just a friend, I swear to you....
"I thought we made a deal with you... Ko ba ce min kikayi kin daina bin kowa ba... Witch nasan bazaki iya ba, ... You know I don't tolerate shits , you leaving my apartment right this very moment..... Ya k'arashe yana isa bakin sip Ya shiga watso kayanta...
"Rik'esa take tana fad'in" Haba Umar don't do this to me, haba kar ka mun haka, ina zanje idan ka koreni, remember you said you loved me...
"Fashewa da dariya yayi kafin yace " That was your thoughts babe, coz you're so naive so easy to manipulate.... I love only one girl, .... Well I was only using you... And you've done your part... Dole ki tafi ki bar min gida before you causes hell for me.....
"Rik'e rigarsa tayi tana basa hak'uri tana kuka ina ko kulata beyiba Ya shiga janyota downstairs... Har sun kusa sauk'a Ya tuna Ya ajiye kud'insa a bedside a cikin d'aki...
"Kamota Ya kuma yi kafin yace " Muje na duba kud'ina wllhi kabo yayi ciwon Kai ke zan kama....
"Aiko yana Bud'ewa $700 d'insa suka ce d'auke mu.... Whattt!!!! Ya furta da k'arfi kafin Ya mik'e Ya k'araso gaban Zulaihat yanda take durk'ushe tana kuka kafin yace " Where is my money...
"Bata amsa sa ba sai kuka..
"Shak'eta Ya kumayi yana tambayarta....
"Cikin kuka take fad'in " Wllhi Allah ni banma san da kud'i a ciki ba..
"Dariyar rainin hankali yayi kafin yace " Don't take me for a fool, I'm not in the mood to play such games, bani kud'ina tun muna mu biyu.....
"Kallon mamaki kawai take binsa dashi, how could someone be so ungrateful, after all what she's done to him, is that how he repay her....
"Girgiza kai kawai ta soma tana fad'in you are a monster, I shouldn't have believed you in the first place... You are my worse nightmare... Bayan duk abun da na maka abunda zaka saka min dashi kenan... Yeah you're right I was so naive and stupid, ba laifinka bane laifin soyayyar da nake maka ne.. But I promised you, you'll regret this, you'll come to me begging pleading and asking for my forgiveness.... You've no idea what I'm capable of....... Janyota Ya shiga yi da k'arfi yana fad'in "Get the heck out of my house you garbage.....
"Har waje Ya fitar da ita kafin ya dubeta yace " Babu abunda zaki iya mun, k'ark"arinta kice zakije bada shaida a kotu, fine kije, ni iyaka gaskiyata na fad'i, kefah??? Snn ba'a magana biyu a kotu, idan suka gane k'arya kikayi a baya they will have you locked up in jell..!! Oya fice daga nan.. And kud'ina da kika sata zan san yanda zanyi na amshe su... And remember babe "I'll be watching you..... Ya k'arashe yana nuni daga k'wayar idonsa zuwa Face d'inta...
"Tafiya ta soma yi ga uban dare, gashi har lokacin ana yayyafi kad'an kad"an.... D'an wani gefen kanti ta samu ta rakub'e ta shiga neman layin Imam...
"Sosai Imam Ya razana da ganin kiran Zulaihat at this hours, yana d'agawa ta fashe masa da kuka, cikin kuka tayi briefing nasa,
"Da sauri Ya mik'e Ya zira riga yana fad'in" Kar ki dam stay right there, it might be dangerous... I'll get you soon....
"Har lokacin kuka take tana tuna wulak'anci da cin mutuncin da yau Umar Ya mata, ko shine autan maza ta hak'ura dashi...
"Imam yace " Kiyi hak'uri kinga wann shine irin abunda nake ji maki, I've told you time without numbers ki daina wann low life d'in da kika d'auka ma kanki, be happy for who you are, ki koma gaban iyayenki ask for their forgiveness, kiyi aurenki, You are still young and beautiful son kowa kin wanda Ya rasa...
"Harara ta b'alla masa kafin tace " Yimin shiru as if I asked for your opinion... Wllhi bana barin garin nan until I take my revenge, I'll make him pay, na gode da nasihar ka da shawarinka kuma insha Allah I'm a changed person now... Happy..!! Ta k'areshe tana murmushi...
"Murmushi shima yayi kafin yace " Yeah happy.. Kiyi baccinki ni barinje d'akina, and feel at home, although gidan nawa babu komai, ba irin gidan da kika saba bane, kinsan ni d'in student ne kuma taxi driver....but kar ki damu akwai wata tsohuwa cikin d'akin nan zata baki breakfast...
"Kallon mamaki ta masa kafin tace " I thought you living alone...
"Murmushi yayi kafin yace " Yeah my grandma bata jima da zuwa ba,.... So have a goodnight.. Ya fadi yana murmushi kafin ya fice...
"Murmushi Zulaihat ma tayi gamida kwanciya bisa couch, tana mai mamakin wadatan zuci da godiyan Allah da saurayi mai k'aramin shekaru kaman Imam yakeda.......
*********************
"Har wajajen k'arfe bakwai na safe wayar Jalal ba'a d'agawa, k'arshe yama daina shiga gaba d'aya, I zuwa lokacin ba Zubaidah kawai ba, harta Annah ma hankalinta ya soma tashi, wayar Ansar suka kira suka sanar dashi halin da ake ciki..
"Ansar ne yazo ya ringa kwantar masu daehankula yana nuna masu akwai possibility na abubuwa, maybe wayar babu charge ko kuma wani abu makamancin haka, but yasan Jalal is very strong , su bari zuwa nan da 24hrs idan basuji sa ba sai suyi reporting to police station...
"Kallonsu kawai Zubaidah keyi amma bata tunanin zata iya kaiwa har nan da awanni ashirin da hud'u ba tareda tasan halin da Jalal ke ciki ba.....
********************
*Gombe*
"Shattima zaune gaban DPO yaci gaba da fad'in" Sir babu wani report na accident ko robbery da kuka samu, don ya tabbatar mun Ya fito a jiyan snn wayarsa tana shiga har da safen nan daga baya ta daina gaba d'aya....
"Dpo yace " Ranka shi dad'e bamu samu wani report da yayi kama da abunda ka lissafo ba daga jiya zuwa yau, snn tashan motoci ai an daina barin motoci suna tashi da dare sabida guje ma faruwan hadd'ura da kuma tabbatar da tsaro.... Amma we are going now, barin shirya yarana zamu bi hanyar snn zan kira station d'inmu na can su soma gudanar da bincike... Shattima Ya mik'e yana fad'in " I"ll go with you sir....
"Dpo ya kad'a Kai yace babu matsala.....
**********************
"Koda suka isa garin Dukku sun samu tuni polisawa sun soma gudanar da bincike, shugaban tashar motoci ya tabbatar babu motan da tayi tafiya daga Dukku zuwa Gombe a jiya, haka nan tashan motar garin Gombe Sun tabbatar babu motar Dukku datazo Gombe a jiya entirely.....
"Hanya suka soma bi jeji jeji suna nemansa, wani bend da suka gangara suka kalli k'afafuwan mutane dashike garin akwai damshi, k'afar suka ringa bi dukda basu san ko na masu noma bane.....
"Nan dpo ya tura yaransa ta ko ta ina suka soma hudanar da bincike.....
"Har sun firfito suna shirin tafiya don basu ga kowa ba, .... Can k'arkashin wata bishiya wani police officer ya danna intercom d'insa yana fad'in" Sir there is a body here, Direction bla bla bla.... Ya fad'i daidai wajen.....
"A sittin suka shige dajin yanda yayi directing nasu...
. "K'arasawa kansa Shattima yayi gwiwoyinsa duk a mace ganin irin dukan da kayi ma Jalal, jini duk Ya bushe a jikinsa, Shattima zai tab'asa Dpo Ya hanasa..... Intercom d'in hannunsa ya danna kafin ya soma magana, Nigerian Police station, we need an ambulance Direction bla bla bla... Yeah ASAP, ASAP... Okay.
"Gwaje gwaje suka soma yi yayinda Shattima Ya koma gefe ya durk'ushe baisan sanda hawaye suka shiga zubo masa ba.... Mintoci kad'an Ambulance ta iso likitoci suka shiga nasu aiki....
"Da sauri suka saka masa oxygen snn suka ciccib'esa suka sa a bayan ambulance bayan sun rufe hannayensu da gloves suna fad'in" He's breathing, let's go let's go....
"Jin ance na numfashi yasa Shattima saurin mik'ewa ya nufi nasa motar, su dpo ma suka haye nasu motan.......
" Babban asibitin garin Gombe aka nufa dashi yanda likitoci suka shiga k'ok'arin ceto rayuwarsa don kuwa dukan da aka masa ba Wanda hankali zai d'auka bane, da ba don Allah yasa nada sauran numfashi ba tabbas da ya jima da mutuwa....
"Gida Shattima Ya koma don sanar da iyayensa abunda Ya faru. Umma da Baba Waziri sosai hankulansu Ya tashi, oh wann duniya abin tsoro, har wani yayi yunk'urin kashe hallita irinsa wanda baisan yaya aka k'era ba,... Haka Umma ta ringa sunbatu idan Shattima yaji zata Saki layi sai ya d'an kalleta...
**********************
*Abuja*
*Dasuki Mansion*
" Cheers...!! Cewar Alh Kasim dake zaune a center gefe dashi Faisal ne da kuma Barr Munir... D'aga cups d'insu sama sukayi su duka suna amsa masa fuskokin su Ya cika da farin ciki..
"Barr Munir yace" Wnn alamu ne dake nuna mana nasara tana garemu....
"Dariya Alh Kasim yayi kafin ya mik'e Ya k'arasa gaban Faisal yana bubbuga kafad'unsa yake fad'in" Without you non of this would had happened, you did a great job boy..... You deserve the reward.....
"Faisal yayi murmushi kafin yace " I'm always at your service Boss...
"Suka kuma fashewa da dariya Alh Kasim yace " Ku tashi muje mu masu ta'aziya so that no one should suspect us.....
"Fitowar da zasu yi sukayi ido hud'u da Mummy hawaye tabb idanunta....
"Daddy ya d'an fuzar da iska kafin yace " Farha make faruwa wa Ya tab'a mun ke,.... D'aga masa hannu tayi sanda yake k'ok'arin k"arasowa gareta tana fad'in" I knew it, nasan you are behind all this.... Kuka ya kufce mata ta shiga dukan k'irjinsa tana fad'in" I hate you, you are nothing but a disaster to my life..... Da sauri Munir Ya k'arsa ya rik'eta yana fad'in" Calm down Farah, put your self together......
"Fuzgewa tayi tana fad'in let go of me, you are a snake Munir, I can't believe you are my flesh and blood. Kai kake saka sa duk abubua marassa kyau.. I hate you all... Kuma barin gidan zanyi bazan zauna da murderer ba..... Fizgota Alh Kasim yayi ya nufi upstairs da ita yae kulle kafin yace " Mujenku I'll deal with that idan mun dawo....
"Babu kunya babu tsoron Allah suka shiga har parlor yima Hajiya Raliya Ta'aziyya.
"Kausar dake duk'unk'une cikin bargo don tunda akayi rasuwar batada lafiya, jin ana cewa gasu Alh Kasim Dasuki sunzo ta'aziya yasata buga wani uban tsalle daga saman gadon ta duro k'asa, Asmah dake zaune saman rug rik'e da k'aramin Alqur'ani ta dubi Kausar dake zura hijabi tace " lafiya Sis ina zaki ...... Kausar bata amsata ba, sai zura slippers datayi ta nufi downstairs tana fad'in" I can't believe that Scumbag got some nerve to show his face here......
"Jin haka yasa Asmah saurin mikewa tabi bayanta....
.Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:25] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
63
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*Ehen this spectacular chapter goes to you my dearest Sis Rally, thanks for the love and care 😍❤*
"Har gaban Alh Kasim Kausar ta k'arasa idanunta na fidda hawaye sai faman huci take..
"Da mamaki ya d'ago yana dubanta kafin ya sakar mata murmushi yace " Kausar yaya mukaji da hak'uri.....
"Murya a dake take fad'in" Don't act innocent....Get out of here you killer......
"Gaba d'aya mutanen dake parlorn kallo ya dawo kan Kausar, Mumsy ma kanta kallonta take cike da mamaki....
"Asmah ta d'an matso tana k'ok'arin janye Kausar a hankali take fad'in" Kausy let's go, don't make a sin here... Fizge hannunta tayi da k'arfin gaske ta k'arasa gaban Daddy sosai tana nuna masa k'ofa take fad'in" Ka fice nace kafin na kira maka police... I can't believe you have some guts to show your face here bayan duk abunda kayi...... "Barr Munir ne ya mik'e da sauri yana fad'in" Be careful with what you saying now.... Lafiyanki kuwa kinsan abunda kike fad'i.....
"Juyowa tayi tana duban Barr still tana hawaye kafin tayi magana saiji tayi Mumsy ta fizgota cikin tsananin fushi sun nufi stirs... Juyowa Kausar ta kuma yi dukda janta da Mumsy take bata fasa magana ba cikin kuka take fad'in" You murderer, you'll pay for what you did to my family, sai mun had'u a kotu coz I'll press charges against you.... Daidai sanda Mumsy ta jefata cikin d'aki had'i do d'auketa da lafiyayyar mari.....
"Wai tabarmar kunya da bori ake nad'e ta, ko minti biyu mai kyau basu k'ara a gidan ba suka kwashin manyan rigunansu suka fice, Alh Kasim sai faman muzurai kawai yake yana huci shi a dole Kausar taci mutuncinsa babban mutum kaman shi, wani b'angare na zuciyarsa kuma ta cika da shakku da mamakin k'arfin hali irin na Kausar.....
"Dafe k'uncinta tayi ta d'ago idanunta masu zuban hawaye tana kallon Mumsy wacce itama hawayen ne keta faman kwaranya a idanunta fuskarta cike da b'acin rai da takaici.....
"Baki na rawa Kausar ta soma fad'in" Mumsy zan iya rantsewa he's behind all this.... Yi mun shiru...!!!! Mumsy ta katseta cikin daka tsawa kafin taci gaba da fad'in" Kinyi hauka koh? Nace kinyi hauka koh..?? Ta k'ara fad'a cikin tsananin fushi.....
"A hankali Kausar take girgiza kanta har lokacin tana hawaye idanunta suna kallon k'asa, cikin rawan murya ta soma fad'in" Mumsy I just can't stand Man wllhi nasan wann duk aikinsa ne, but pls kiyi hak'uri.... I.... I just couldn't help it ne, I still can't believe my Pappy is gone...... Ta k'arashe cikin sheshshek'an kuka.....
"Rungumota Mumsy tayi kafin itama tayi bursting cikin kuka saida sukayi mai isansu kafin suka zauna bakin gado.....
"Mumsy ta rik'o hannayen Kausar kafin ta soma fad'in" Dear I know exactly how you feeling, but what you did lately was wrong, it doesn't suite you at all... Yau da Pappyn ki zai tashi yaga irin abunda kikayi bazaiji dad'i ba, snn nima banji dad'i coz I'm also suffering... Your Father was the great love of my life..... But I had to accept the fact that he's gone.... Ki kasance mai tawakkali Allah yana son masu hak'uri, snn duk wanda ya zalunceka a duniyar nan kaine a saman sa... Ki bari hukuma tayi aikinta wann ba field d'inki bane tunda they are already investigating the matter....
"Kiyi hak'uri kiyi hak'uri kinji Kausar kiyi ma mahaifinki addu'a shi kid'aine abinda yake buk'ata daga gareki a yanzu kinji daughter...... Gyad'a kanta tayi tana share hawayen idanunta da bayan hannunta kafin ta rungume Mumsy very tied kana tace " Mumsy pls stay here with me for a while.... Murmushin k'arfin hali Mumsy tayi tana shafa kanta kafin tace " I'll always be here for you sweetheart, together we will overcome this horrible tragedy.., Asmah dake tsaye bakin k'ofa ta goge hawayen da suka zubo mata, tausayin family d'inta yana ratsa ta b'argo da tsoka, she needs to be very strong, her family needs her now more than ever.....😪
*****************
"Sai faman masifa yake shi d'aya yana huci, lek'owa ta d'an tsakiyar mota yayi ya dubi Faisal dake front seat kafin yace " Faisal are you sure you did a clean job, na fad'a maka bana so wani suspicious yayi linking d'ina da abinda ya faru, coz I've had enough already, dealing with the issue of those kids ma ya isheni, bana so na sake fad'awa wani court case coz a halin da ake ciki yanzu our company is not financially stable....
"Faisal ya d'an karkato yana kallon baya kafin yace " Boss you don't have to worry about that, let them go ahead and press the charges, sune a rana, coz basu da wani evidence against you..... Dariyar da Barr yayi ne ya katse su.... Daddy ya karkato yana dubansa alamun yana jiran amsa yaji dariyar me yake.....
"Barr yaci gaba da fad'in" Ai a halin yanzu ba shigar da k'ara bane a gabansu, su samu su wanye da masu hannun jari a company d'insu, sabida idan wasu sunyi hak'uri wasu bazasu yi hak'uri ba, Alh Tahir was a very wealthy man, yanada hannayen jari a k'asashe daban daban snn yana banking da bankuna a k'asashe daban daban a duniya, a lokacin da mukayi Business partnership with his company Attorney na Company d'insu ya bani wasu documents duk wani breakdown na business dinshi was written on that document..... So I suggest mu ringa bin k'afafun Employees d'insa da kuma shear holders na company d'insa a hankali muna nuna masu muna influencing nasu muna persuading nasu muna nuna masu cewa lallai lallai kar su yarda, Hajiya Raliya sai ta fito masu da kud'insu da sukayi asara, daga nan mujasu a jiki su zuba kud'ad'ensu a company d'inmu tunda dama we are at risk of going bankrupt, so kunga basu da wani lokacin shigar da k'ara koda ace zasu san gaskiya ma, wancan issue d'in zaiyi distracting nasu.....
"Tunda ya soma magana Alh Kasim ke binsa da kallo lallai ya yarda Barr abokin tafiya ne.... Dariya ya fashe dashi harda cire hula kafin yace " You are just an incredible Attorney , wann yayi , you should start working on that right away, kayi copying document d'in a computer ka fara spreading nashi to their Emails....
"Wata silent murmushi Barr yayi kafin yace " You don't need to tell me what I should do, You can trust me on that.... Shigar da k'ara shine babban kuskuren da Haj Raliya da d'iyarta zasuyi....
"Ganin motocin police a k'ofar company d'insu ya basu shock dukda sun san hakan ka iya faruwa.....
"Motarsu tana gama parking securities suka shiga bud'e masu.... D'aya daga cikin securities d'in na company d'insu ya soma fad'in" Sir we got some police men here, they said they are here to interrogate you Sir.. Gyad'a kai yayi kafin yace let them in....
"Tambayoyi Police suka masa gameda k'onewar company d'in abokinsa da kuma mutuwarsa, snn suka ce zasu iya dawowa any moment, Daddy yace " You are always welcome, Im willing to cooperate with you duk lokacin da kuka dawo, what I can't take shine wann ridiculous acquisition d'in da 'yar marigayi take mun, I should hve press charges against her amma sabida zaman mutunci da kuma alkhairin da ya faru tsakani na da mahaifinta shiyasa nake d'aga mata k'afa.... But next time I won't tolerate such scandal...
****************
*Police station*
" Sunyi jigum suna jiran feedback,Ansar sai faman kai komo yake yayinda Zubaidah da Annah suketa faman bin mutanen dake shige da fice da kallo...
"DPO ne ya fito tareda Ansar, suna tafe suna magana, Detective Amir shine cikon na ukun su,..
"Zubaidah kam tunda ta hango fuskar Ansar ta cika da damuwa tasan tabbas something is definitely wrong, mik'ewa tayi zata nufesu Annah tayi saurin rik'o hannunta tace " Mu jirasu a nan Daughter...
"Kallon Annah ta d'an yi fuska cike da damuwa kafin ta koma ta zauna tana mai bin umarninta, Zuciyarta bai daina bugawa da sauri da sauri ba, ita kad'ai take dunk'ule 'yan yatsunta tana bud'e su tunani kalan daban daban suka shiga zayartan kwanyarta... Har Ansar ya k'araso wajen bata sani ba saida taji salatin Annah kafin tayi saurin d'ago kanta a zabure tana dubansu.... Ganin hawaye na fita daga idanun Annah ya kuma firgita Zubaidah...
"Kuka ta fashe dashi tana fad'in" Sun kashe shi koh, nasan bazasu k'yalemu ba.... Annah ina yake I want to see him, pls take me to him....... Sosai Annah ta rik'eta tana girgiza kai itama tana hawayen take fad'in" Basu kashesa ba Zubaidah, Jalal na nan a raye.... amma sunyi masa illa sunji masa rauni.....
"D'agowa tayi tana duban Ansar wanda ke nan tasye jugum snn tace "Where is he? ...
" K'ak'aro kalamai yayi ya d"aura saman harshensa ya soma basu labarin duk abunda ya faru according to yanda ya sami labarin, snn ne yake tambayar su ko sun san Shattima, nan Annah ta fad'a masa alak'arsu da Shattima.
"Ansar ya sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Gobe da safe insha Allah zamu wuce gomben, a halin yanzu police are investigating the issue, na fad'a masu main suspect d'inmu Alh Kasim Dasuki ne sabida shika da grudges against Jalal, zasu tafi suyi interrogating nashi right away.... "Ya d'an ja fasali kafin ya shafi sumar sa yace " Annah to be honest with you zamanku a Suleja is risky considering the situation, kunga irin abubuwan da suketa faruwa a kwana biyun nan, Alh Kasim is capable of anything. He's a a monster, he do not have a heart, who knows what he's up to, especially yanzu da idon duniya ta masa cha, mutane sun soma gane wanene shi...
"Annah ta sauk'e ajiyan zuciya takai dubanta ga Zubaidah wacce har lokacin hawaye take da alama bata tare dasu tayi nisa wani duniyan...
"D'agowa tayi ta dubi Ansar kafin tace " Barr ina zamuje wa muke dashi cikin Abuja....
"Ansar ya d'an Saki murmushi kafin yace " Haba Annah don't talk like that zaki sa naji kaman har yanzu nida ku bamu zama d'aya ba,
"Gidana wadacecce ne, zan iya komawa chan sashen baki sai na bar maku cikin gidan kuyi zamanku har zuwa lokacin da zamu kammala Shari'an mu.... Yanzu bari na kira Hafiz ya taho da mota idan yaso sai ya d'auko su Hamma, kuma sai muje ku d'auki duk wasu kayan amfanin ku for the meantime.....
"Wayarsa ya ciro ya shiga neman layin Hafiz gamida matsawa d'an gefe kad'an...
"Annah kam kallo ta bisa dashi cike da mamakin mutunci da karamci irin na Ansar, Allah sarki tausayinsa na rashin iyayensa da 'yan uwansa ya cika zuciyarta, tabbas yau da iyayensa na raye zasuyi alfahari da samun d'a kaman Ansar, Allah yaci gaba da karesa daga sharrin masu nemansa da sharri, Tabbas addu'an Alkhairi shine kurum zasuyi ma Ansar dun ko kusa bazasu iya biyansa abubuwan da yayi masu ba....
******************
"Tunda suka shigo gidan su Hadiza sai washe baki ake ana d'add'ana kujeru, Kamal ma ya tab'a wann flower vase d'in ya tab'a wancen, sai kalle kalle da d'an k'uyanci suke, Ansar ya nunnuna masu d'akuna da komai da komai, harta su kitchen su Store kayan buk'ata na abinci da sauransu, gidan nasa babu laifi ya wadace su ba tareda tak'ura ba.. Zubaidah kam kallonsu kawai take burinta bai wuce gari ya waye ta ganta a garin Gombe ba...
"Bayan ya gama nuna masu ko ina ya sauk'o downstairs ya nufi d'akin bak'i ya karkad'e ko ina ya shiga jera kayansa a wardrobe, yana cikin shirya kayan wayan Asmah ya shigo masa, " Bayan sun gaisuwa irin ta masoya ta cika sa da shagwab'a shiko sai biyeta yake yana lallashinta snn ne ya soma fad'a mata abubuwan da suke faruwa har kwaso familyn Jalal da yayi ya dawo dasu gidansa, da kuma maganar tafiyarsa Gombe a gobe idan Allah ya kai rai...
"Sosai hankalin Asmah ya tashi da jin abinda ya sami Jalal, oh when will all these end, ta furta a hankali....
"Cikin sanyin muryarsa taji yace "Soon insha Allah my Love, zamuyi auren mu cikin sabuwar duniya maras rikici da fargaba da izinin Allah......
"Haka kurum taji jikinta yayi sanyi, cikin sanyin murya tace " Allah yasa my Attorney, murmushi yayi gaimda lumshe idanu kafin yace " Ameen my Attorney, kiyi bacci I'll call da safe kafin mu wuce kinji.. ..
"Sallama sukayi kafin suka katse wayar.... ..
"Kwance take saman gado rungume da rigarsa, tunaninsa ya ringa yawo a k'irjinta, ko wani hali yake ciki...... Ta goge hawayen da ya zubo mata gamida k'ank'ame rigarsa, tayita tuno abubuwan da tayi masa a baya, ta tuna irin hak'urin da yi da ita, ta tuna irin fad'i tashin da yake don ganin rayuwarta ta inganta, ta tuna irin sadaukarwa yake kanyi duk a saboda ita.... Kai anya ta cancanci Jalal, anya bai cancanci sabuwar mace ba wacce babu wani Mahaluk'i da ya lalata mata rayuwa,.... Take taji gaba d'aya she's feeling ashamed tabbas ta yarda tana son Jalal, amma tana tunanin ranar da za'ace ta soma rayuwar aure da Jalal,...... Girgiza kai ta soma da sauri tana mai dad'a k'ank'ame hannayenta had'i da runtse idanu, don kuwa wann tunani ba komai ya haifar mata ba, sai gano fuskokin su Labib da take cikin idanunta.... A haka Annah ta shigo ta sameta, ta zauna gefe da ita ta shiga lallashinta tana nuna mata addu'a shi zaiyi masu maganin damuwarsu ba kuka ba.... Mik'ewa Zubaidah tayi ta nufi bathroom don yin alwala tabbas Allah shine maganin komai.....
"Washe gari Annah har ta tashi ta had'a masu breakfast. Ansar ya shigo cikin shiri yana fad'in" Wow daga ina wann aroma d'in ke fitowa, Murmushi Annah ta sakar masa kafin tace " Good morning, oya have a seat....
"Zama yayi d'aya daga cikin kujerun Annah ta shiga serving nasa tana jansa da hira....... "Jin yayi shiru baya amsawa yasata d'ago kai tana dubansa, k'walla ta gani tab idonsa ya k'ura ma abincin idanu....
"Kujera ta d'an jawo ta zauna chan gefe dashi kafin tace " Ansar are you alright....?
"D'an goge k'wallan idonsa yayi ya k'a'karo murmushi kafin yace " I'm fine Annah, it just that you remind me of my Mum,.... You sounds like her, and she cooks delicious food, I missed her so much, inama tana nan a yanzu nayi devoting entier life d'ina wajen kyautata mata, even though nasan bazan mata kwatankwacin sadaukarwar da ta min ba sanda nake yaro,..... I couldn't have chance to be with her, all of them ....
"Tausayinsa ya cika zuciyar Annah, wani sabon tsana Alh Kasim ya kuma wanzuwa a zuciyarta, a hankali ta soma fad'in" Ansar kai d'a na gari ne wanda ko wata mahaifiya zatayi alfahari da kai, nasan addu'an alkhairi da kake masu yana isa garesu, snn shi wanda yayi sanadinsu bazai tabbata a doron k'asa yana zalunci ba, da sannu Allah zai kawo k'arshensa....
"D'ago Kai yayi yana gyad'awa kafin yace " Hakane Annah insha Allah k'arshen Kasim Dasuki yazo snn zai girbe duk wani abinda ya shuka.......
"Hadiza dake lab'e a k'ofa jinjina kai ta soma cikin zuciyarta take fad'in" Kenan duk yanda akayi Alh Kasim nada sa hannu a mutuwar iyayen Ansar..... Murmushi ta soma a hankali cikin ranta taci gaba da fad'in" Kai haba ai biri yayi kama da mutum, shiyasa ya tsaya kai da fata ganin Zubaidah taci wann shari'a bayan ba biyansa ko tasi ake ba, idan kuwa hakane lallai zatayi amfani da wann damar,.... Ta k'arashe zancen zucin nata tana mai kai duvanta ga family pic d'in Ansar dake ajiye saman console a corridor d'in..... Jin k'aran tafiya alamun ana sauk'owa daga stirs yasata saurin saita kanta ta k'arasa cikin parlorn suka soma gaisawa da Ansar da kuma Annah, sai faman fari'a take uwa gonar auduga....
"Zubaidah ce ta sauk'o parlorn ciki shiri itama, tana sanye cikin red atampa mai touches d'in sea blue, ta d'aura sea blue hijab wanda yake daidai gwiwarta, tayi matuk'ar kyau duka she's looking pale, da gani kasan she had a sleepless night.... Annah ta sakar mata murmushi suna masu amsa sallamarta itada Ansar yayinda Hadiza ta bita da wani mugun kallo k'asa k'asa.... Bayan sun gaisa Ansar kam d'aukan abincinsa yayi ya koma cikin parlorn ya zauna yana ci, nan Hamma ma ya fito ya zauna tareda Ansar suka ci abinsu tare, sosai Ansar kejin dad'in hira da Hamma...
"K'arfe tara da wasu 'yan dak'ik'ai na safiya suka d'auki hanyan Gombe, har waje Hamma da Hadiza suka raka su gamida masu fatan alkhairi snn suka bada sak'on gaisuwarsu a isar ma Jalal...
"Ansar kuwa saida yaja kunnen danga security dake masa gadi sosai da sosai, yace ya kula da Al'amarin tsaro sosai...
. "Suna tafiya Hadiza tayi shirinta tsaf ta had'a Hamma da Kamal da kallon tashan gwaigwai na yara (cartoon) tace bari taje kasuwa ta sayo masu kayan miya na fridge ya k'are...
"D'aukan k'aramin hoton dake ajjiye saman console tayi ta b'oye cikin jakarta kafin tayi ficewarta......
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:26] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
64
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*A Big Shout Out To All The Readers 😻*
"Zaune yake gaban Mai Martaba, Ya tattaro nutsuwarsa gaba d'aya ya had'e waje guda, kan nan nasa duk'e a k'asa, kallo guda zaka masa ka gane ramar da yayi.....
"A hankali Mai Martaba ke karantar canzawan da Shattima yayi a 'yan kwanakin nan, yana son Shattima yana jinsa tamkar d'an da ya haifa, ko kusa baison ganinsa cikin wann yanyi... Ajiye takardun hannunsa yayi saman makeken darduman Alfarma dake malale a parlorn kafin yayi gyaran murya ya kirawo sunan Shattima da ainihin sunansa had'i da jefo masa tambayar da yasa gaban Shattima mugun fad'uwa...
"Abdullah...... Shin akwai abunda ke damunka ne.???
"Shattima ya d'an daburce yama rasa me zaice, don kuwa magana ta gaskiya bazai iya fad'awa Mai Martaba son tilon d'iyarsa yake ba, toh ma ta ina hakan zata kasance bayan har an bayar da Zahidah..... Muryar Mai Martaba ya kuma jiyowa yana fad'in" Abdullah kai d'ana ne , ka fad'a mun idan akwai abunda ke damun ka, ko tafiya Kanon ne baka shirya ba...... Ai Mai Martaba bai kai aya ba Shattima ya soma girgiza kai yana fad'in" A'a Abba dama... Ya d'an ja aya.... K'irjinsa yaci gaba da bugawa sabida k'warjinin Mai Martaba ya wuce gaban ka masa k'arya. Take dabara ta fad'o masa ya tuna kan Ya shigo an masa waya ana nemansa a asibiti patient d'insa ya farka.... Nan Ya soma fad'in"
"Abba dama...emm dama akwai wani abokina da 'yan fashi suka taresa a hanyarsa ta zuwa garin nan suka masa duka to the point of death, yanzu haka yana asibiti yana receiving treatments..... snn bashida kowa a garin nan sai ni, toooh sun min waya daga asibitin sun sanar dani ya farfad'o.... Toh Abba dama inaso na biya na dubasa idan akwai wani abu sai nayi settling kafin nayi tafiyar......
"Subhanallahi.... Mai Martaba ya fad'i fuskar sa cike da nuna damuwa. Snn ya d'aura da " Haba Abdullah yaya baka sanar damu ba, bayan kasan duk ranar juma'a mukan shiga asibiti duba marassa lafiya....
"Kai a k'asa Shattima yace " Ayimin afuwa Abba, amma jiya ne ma abin ya faru shiyasa ban sami zarafin sanar da kai ba. ....
"Shiru Mai Martaba yayi haka kurum Ya rasa dalilin samun faduwar gaba da yayi a dalilin wann labari da Shattima ya basa... D'agowa yayi bayan wucewar wasu 'yan dak'ik'ai kafin yace " Kaje Abdullah snn maganar tafiya Kano mun janyeta cikin satin nan har sai Allah Ya bawa bak'on ka lafiya.... Snn a kula dashi k'ark'ashin kulawar mu har Allah Ya basa lafiya.....
_(Tabbas ba k'aramin Al'amari bane zaisa gaban Sarki fad'uwa)_
"Kai a k'asa Shattima ya ringa jero godiya had'i da addu'ar girma da arziki wa Mai Martaba kafin yayi masa sallama ya fice......
"A daidai hanyar sashen Mai Babban D'aki ya hange Zahida alamun sashen Mai Martaba ta nufa.... Cikin sauri kaman me shirin kifawa haka ya fice ya nufi motar sa......
****************
"Damn it.... Damn it, cewar Alh Kasim had'i da buga table d'in dake gabansa kafin yaci gaba da fad'in" Sun mayar min da company kaman ofishin 'yan sanda.... It's all because of that stupid girl... If only I could kill her with my own hands......
"Mik'ewa Barr yayi yana shafa kansa da hannaye biyu kafin yace " Calm down Mr President.....
"No.. Don't ask me to calm down, I'm sick and tired of everyone accusing me just like that, da abunda nayi da abunda banyi ba..... Cewar Alh Kasim cikin tsananin fushi
"Barr yace Alh Kasim, first we need to think of who could have possibly do that, muddin aka ce anyi attacking Jalal toh fah mune za'a soma zargi, duk wanda yayi attacking Jalal fansa yake nema akanmu tunda mune dole za'a soma zargi....
"Alh Kasim yayi shiru yana muzurai kafin yace " That must be Hajiya Raliya and her daughter, sune kurum suke neman revenge akaina, sune zasuyi haka don ace ni nake yunk'urin kashe Jalal....
"Barr ya fashe da dariya kafin yace " This is ridiculous Alh Kasim.... Ta yaya zakayi tunanin Hajiya Raliya would do something terrible like this, .... That woman and her daughter are not capable of murder..... It's clearly someone's wants to see Jalal dead.....
"Toh waye kenan.. Alh Kasim ya tambaya yana mai tsare Barr da idanu....
"Tafe hannu Barr ya soma yana wata muguwar murmushi kafin yace " It's Umar.... That jerk is really insane, I'm quite sure he won't stop har sai yaga babu me numfashi cikin su hud'un, Jalal, Labib Salim da kuma Tariq... Kar ka mance he shot Salim a wajen nan, kar ka mance yanda yayi reacting ranan he's eyes full of seeking for revenge. Zaiyi komai just to be with that girl.... "
"Gyad'a kai Alh Kasim yayi yana huci kafin yace " I won't let him drag me into his mess.....
"Murmushi kawai Barr keyi kafin yace " Come to think of it....... Alh Kasim you are already in the mess ko ince we.... Don't forget mu muka jawo shi cikin wann mess d'in from the very beginning, we can't get rid of him just like that, ni dai a gani na what we should do kawai mu kirasa mu sanar dashi mun san komai he's behind of what happened to Jalal, yayi laifi ya b'uya a inuwar mu tunda mune main suspect na police... " He should just obey us ko meye muka saka shi yi tunda shid'in abokin aiki ne, if not we would expose his little secret.. Ko yaya kace..???
"Dariya Alh Kasim ya fashe dashi kafin yace " Shiyasa nake sonka Barr wann moleliyar kan naka ba a banza ba, now just call the idiot right away don karma yayi tunani zai b'ace mana, we have eyes everywhere..
************
"Tun daga nesa Mum ke rakub'e rakub'e tana tunanin shiga d'akin.
"Dad ta hanga ta cikin glass yana zaune kujera Me kallon na Tariq. A hankali tasa hannu ta tura k'ofar d'akin....
"Me kike yi a nan Dad ya tambaya yana watsa mata mugun kallo....
"Dan Allah ka barni nagan d'ana na rok'i arzikin ka kar ka koreni pls....
"Get out of here, you've no right over my son. Bakiji kunyan zuwa nan ba, you should be ashamed of your self.... I hate you I hate you Karima...... Ya k'arashe yana zama bisa kujeran had'i da goge hawayen idanunsa..... Kaman wanda aka mintsili Tariq haka ya bud'e ido.... Da sauri Mum ta k'arasa wajensa tana fad'in" Son Tairq my So....... Bata kai aya ba ya shiga k'ok'arin tashi dukda bandage d'in dake d'aure a kansa da wuyarsa kasancewar ya sami internal injury anyi masa aiki..... "Cikin zafin nama yake fad'in" Me kike yi a nan,.... Get out I don't need you in my life, just go back to your lover or what ever you call him.... You are despicable Mum I hate you for good, just get outta..... Muryarsa ya sark'e sakamakon tari da yaci k'arfin sa..... Hankalinsu gaba d'aya Ya tashi ganin yanda Tariq ke tari kaman zai amai da kayan cikinsa.... " Mum tayi kansa a rud'e tana kiran sunan sa yayinda Dad ya fice kiran likita a guje, nan d'aya daga cikin polisawa masu tsaron Tariq yabi bayan Dad........
****************
"Fitowarsu kenan daga cikin company d'in sakamakon wayar da Jane ta masa ta sanar dashi Hajiya Farha babu lafiya...
"Daga can bakin company d'in ya hangi Hadiza..... Wata murmushi ya sake don yasan ba'a ganin Hadiza haka nan... Da sauri yace da driver d'insa su koma cikin company, nan yasa security guda d'aya ya shigo da Hadiza....
"Suna zaune a wani meeting room madaidaici shida Barr security ya turo k'ofar yace da Hadiza " You can enter Miss.... Kallonsa kawai Hadiza tayi gamida tab'e baki tayi shigewarta don bawai ta gane me yace bane...
"Tun daga nesa Barr yake sud'e baki don kullum yayi tozali Hadiza haka yake yi, ....
"Alh Kasim ya mik'e yana murmushi kafin yace mata bissmillah ya k'arashe yana nuna mata kujera.
"Zama tayi tana watsa wa Barr kallo ganin idanunsa k'yam akanta, ba tare da b'ata lokaci ba ta gabatar masu da abinda ya kawota....
"K'uri Alh Kasim yayi ma hoton data mik'a masa yanason gano fuskar mutumin jikin hoton...... Marigayi Alh Ma'aruf Kumo ya ambata cikin zuciyarsa tabbas shine ko shakka babu wann Alh Ma'aruf ne snn wann matarsa ce wanda sukayi dabi a kotu..
"Murya har na rawa Alh Kasim yake nuna ma Hadiza hoton kafin yace " In.... Ina kika san wad'an nan.... ??
"Hadiza ta juya idanu kafin tace kai zan tambaya ina ka sansu, koda shike nasan kai kayi ajalinsu da zalunci irin naka......
"Alh Kasim ya kafeta da ido kafin yace " Be careful with your language lady......
"Tab'e baki tayi kafin tasa hannu ta fizge hoton tayi masu nuni da d'an matashin yaron dake jikin hoton tace hala kun gane wann fuskar...??
"Barr ya matso sosai yana kallon fuskar yaron, it's looks quite familiar, a ina yasansa??
"A fili Barr ya furta " ANSAR KUMO....... Shitttt.... Ansar Kumo. Ma'aruf Kumo, shakka babu d'ansa ne.....
"Daddy Ya mik'e gamida cire hulan kansa yayi jifa dashi yana fad'in" Make shirin faruwa dani, bayan na gama da Ma'aruf Kumo da iyalansa ashe na kashe maciji ne ban sare kansa ba..... No wonder that imbecile is doing all his best to defeat us in court, but I won't let that happen, I'll finish him just like I did to his family..... He has no clue what he's getting him self into..... Kallon Barr yayi kafin yace " Get me Faisal right now... Daga haka yasa kai Ya fice sai huci yake tamkar kububuwa, gaba d'aya ji yake duniyar na neman juya masa.....
"Hadiza ta mik'e tana fad'in" Ni kazo ka sallame ni dun wallhi bana aikin banza...... Barr Munir yasha gabanta yana wani tand'e harshe uwa tsohon maye yake fadin " Relax I'll take care of you..... Muje mota na baki kud'in aikin ki..... .
"Babu musu Hadiza tabi bayansa tana narka masa wata uwar harara, don ko babu komai tasan Habibun ta yafi wann fasali, hasali ma ba don kyau da Allah yayi masa ba da bata aure sa ba sabida lalurar da yake fama da ita......
*********************
*Prison*
"Zaune yake yayi jigum akan gadonsa wanda yake tamkar na 'yan makarantar kwana..... Kallon yanayin wajen kurum yake kanyi da mutanen dake wajen, wanda ko a mafarkinsa bai tab'a hango kansa a wajen makamancin haka ba, kai ko karen gidansu d'akinsa yafi nan balle ma'aikata..... Wai yau shi Salim Dasuki ne yake rayuwa a irin wann wajen, it's all because of her, that filthy mere girl, bak'awyiya Me kiwo, wai yau a dalilinta yake experiencing wann horrible experience d'in... This is a nightmare...... K'walla masu zafi suka ciko idanunsa..... Da k'arfin gaske ya daki bunk d'in dake gefe dashi.....
"OgaChuna Ya bud'e ido a hankali kafin ya malmalo wata ashar ya watsa wa duk wanda ya tadashi daga baccinsa gashi yau ranar hutunsa ne....
"Salim kam a maimakon ya basa hak'uri sai zaginsa daya soma, AI wata wawan tsalle ogachuna yayi ya cakumo Salim Ya shiga kilansa uwa Allah ne ya aiko sa...... "'yan d'akim kuwa sai ele suke suna wasa ogachuna..... Shigowar Labib kenan rik'e da bokiti, a tamanin ya yar da bokitin ya shiga k'watan d'an uwansa yana bawa Ogachuba hak'uri..... Ina Ogachuna bayaji baya gani, fad'i yake, let me teach this spoilt brat a lesson, ba kana gadara kai d'an Kasim Dasuki ba ko shi Kasim d'in ne yazo nan da kansa dole yabi ogachuna a sannu, coz this is my palace, I rules here....
"Saida Labib yabawa Ogachuna hak'uri ya tabbatar masa da zaran sun fita daga prison d'in nan zaiyi masa hiring good lawyer wanda zaiyi handling case d'insa shima ya fice snn Ogachuna ya hak'ura ya k'yale Salim, bisa wann yarjejeniya, har wani dad'i ogachuna yake ji snn yabawa Salim hak'uri shi kuwa sai foffozewa yake, ga jikinsa bai saba da wahala ba duk Ya wani tattauje Ya sauya kamanni....
"Labib ya jawo Salim gefe yana fad'in" You're very stupid you know, how could you got Into a fight with that d'an fashi.... Hararansa kawai Salim yake yana goge jinin bakinsa don sai yanzu yake ganin duk laifin Labib ne, idan da ace basu biye nasa ba, da yanzu yana nan tare da Kausar d'insa.. He did that to ruin his marriage with Kausar......
"Labib yaci gaba da fad'in" Guy we need to put up with everything around this place na d'an wani lokaci ne, we will soon get out of here and take our revenge Ya k'arashe maganar yana marking sauran kwanakin da Ya rage masu a shiga kotu jikin wata 'yar kalandar dake manne gefen gadonsa....
"Hararansa kurum Salim yayi gamida kwanciya kan gadonsa zuciyarsa ta cika fam da k'unci......
***********
"Ana kiraye kirayen sallan magrib suke shiga garin ta Gombe.......
Sam sam..... Sameena ce 😍
[1/23, 22:26] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
65
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Bayan ya gama bawa Shattima labarin duk abunda ya faru, Shattima ma ya basa labarin yanda akayi suka samesa, dukda jin jikin da Jalal keyi bai hanashi yima Shattima godiya ba cikin muryarsa da bai fita sosai....
"Shattima ya girgiza kai kana yace ka daina min godiya haka pls Jalal, idan da inada ikon cire maka ciwon nan gaba d'aya da nayi.... This is the least I can bro....
"Murmushi Jalal ya d'anyi kafin yace okay bro, can you plz help me with a phone, I really need to call my family, inason jin halin da suke ciki coz nasan who ever did this to me kasheni yayi niyyan yi..... Snn nasan their lives might also be in danger.... I need to protect ZUBAIDAH... Ya k'arashe cikin rage sauti sabida rad'ad'i na ciwo da yake ciki......
"Tausayin Jalal ya cika zuciyar Shattima, gaskiya irinsu Jalal basuda yawa a duniya, despite his situation but he still thinks of his family, .... Sauk'e ajiyan zuciya Shattima yayi kafin yace " Jalal babu abinda ya sami family d'inka, according to police your family already knew about this.... Snn banida contact d'insu I should have called them.. Amma most important shine ka sami lafiya... Already 'yan sanda suna bincike, sun so suyi interrogating naka amma sabida yanayin jikin naka Dr yace a bari saiko zuwa gobe idan ka dad'a samun k'arfin magana....
"Shiru kawai Jalal yayi yana tunanin for how long zai zauna a nan waye zai kula da Zubaidah like he does, snn wani hali Annah ke ciki yanzu yasan for sure ta shiga tsananin damuwa....
"Muryar Shattima ya tsinkaya yana amsa sallama. Wata mata ce mai kama sosai da Shattima saiko wata 'yar budurwa wacce bazata wuce shekaru sha biyu ba....
"Shattima ya mik'e yana fad'in" Umma sannu da shigowa..... Umma kam bata iya amsa Shattima ba sai kallon data bi Jalal dashi, haka kurum taga tamkar tasan mai irin fuskar....
"K'arasowa sukayi itada Ameera suka zauna a wani coach dake gefe sunai ma Jalal sannu...
"Jalal ya d'an soma k'ok'arin mik'ewa yana son zama, Umma tayi karaf tace haba haba d'ana Don Allah kar ka tashi na yafe ka wllhi, sannu kaji sannu da jiki....
"Jalal na murmushi yake d'an amsawa da k'yar, nan Shattima yayi introducing Umman sa da k'anwarsa ma Jalal....
"Suka soma gaisawa shida Umma, sai faman jansa da surutu take sai ka rantse sun saba tun tuni,.... Abun har ya soma damun Shattima don likita yace Jalal kar yayi surutu sosai sabida aikin da aka masa, Yasan halin Umma idan ta ringa jero ma Jalal tambayoyi sai yasha kunya kafin ta basa kunya gwara ya katse zancen...
"Ya kai dubansa ga Ameera wacce ta sake baki da hanci tana kallon Jalal kafin yace " Little bazaki gaida abokin nawa bane...
"Ameera kam da baki bashida burki koda yake sak Umma ta gado. Bud'an bakinta sai cewa tayi " Mr Handsome yaya jiki...
"Murmushi kawai Jalal yayi kafin ya amsa mata.....
"Takaicin duniyar nan ya cika Shattima, ai tuni ya mik'e kafin a kuma b'anb'aro Wata yace " Umma tashi na rakaku kinga yanzu za'a kira isha kinsan Baba baison tuk'in" Malam Halliru da dare.....
"Harara kurum Umma ta watsa masa don sarai ta d'ago nufin Shattima baiso taji labarin 'yan fashin da suka tare su Jalal ne.... Mik'ewa tayi ba don taso ba ta shiga sallama da Jalal, shi kuwa harga Allah yaji dad'in company d'in Umma, haka yayita masu godiya had suka fice.
"Shattima na jan hannu Ameera ta kuma turo kai ta k'ofar tana d'agawa Jalal hannu tace " Allah k'ara sauk'i Mr Handsome....
"Jalal kam sosai yarinyar ta basa dariya kai family d'in Shattima sun burgesa da gani shida k'anwar nan tasa Tom and Jerry ne dukda ratan dake tsakaninsu a shekaru, ga Umman nasu kanta akwai barkwanci....
"Wata uwar rank'washi Shattima ya zuba wa Ameera bayan sun fito daga ward d'in kafin yace " Wato tsabagen kin rainani iskancin naki har ya tashi akaina ya koma abokai na.....
"Turo baki Ameera tayi kafin tace " Toh ba gaskiya na fad'a ba yaya wllhi yafika kyau..... Gajeren tsaki kawai yayi ya shiga jawota da kunne har jikin mota...
"Umma dake zaune a owners corner tab'e baki tayi kafin tace " Ai idan bakuyi ba baku had'u inuwa guda ba....
"Mal Halliru gaisawa suke da Shattima lokaci guda yana dariyan fad'an Shattima da Ameera.... Har saida yaga ficewar motar su daga haraban asibitin kafin ya sa kai ya koma cikin asibitin.... A daidai hanyar da zai sada ka da ward d'in ya hangesu.... Cike da mamaki yake binsu da kallo don kuwa tabbas ya gane Annah da Zubaidah, sai dai bai shaida namijin da suke tare dashi ba.... Cikin sauri Shattima ya k'arasa garesu...
"Annah ashe kuna tafe barkanku, barkanku da zuwa, sannun ku... Shattima ke fad'i sanda ya k'arasa gamida mik'awa Ansar hannu sukayi masabah... Tuni Annah da Zubaidah sun gane Shattima, gaba d'aya suka shiga gaisawa had'i da jajen abinda ya faru da Jalal. .. Jin Annah ta soma jero masa godiya yasa sa saurin cewa "Mu k'arasanku ciki, Jalal d'inma bai jima da farkawa ba.... Shattima ya soma yin gaba yayinda suka d'unguma gaba d'aya suka bi bayansa ..
"Yana kwance saman gadon idanunsa a rufe, kaman mai bacci, yana sanye cikin wata rigar ash color da ake sanyama duk wani patient a asibitin, jin an tab'a k'ofa had'i da sallaman su yasa shi Bud'e idanunsa a hankali..
"Da mugun mamaki yake binsu da kallo don kuwa bai tsammaci ganinsu ba, two women d'in da yafi so a rayuwarsa, his mum and the love of his life matar sa Zubaidah....
"Tun daga nesa idanuwan su suka cika da k'walla.... Jalal ya d'an soma yunk'urin mik'ewa Annah ta k'araso da sauri ta rik'esa tana girgiza kai alamun kar ya tashi ... Duk iya k'ok'arinta ganin ta maida kukan ta inaa saida kukan ya kufce mata.... Fuskarsa take shafawa tana fad'in" Meyasa suka maka haka bayan baka masu komai ba, why why....... My little boy, my son..... Kuka yaci k'arfin Annah.
"Hannunsa maras cannula ya d'ago snn ya shiga goge mata hawayen yana girgiza kai cikin murya na marras lafiya yake fad'in" Pls don't Annah, ki daina kuka kinji Annah na.. Mu godewa Allah basu cimma burinsu akaina ba....
"Annah ta rik'e hannunsa ta sumbata kafin tace " Allah Ya baka lafiya Jalaluddeen. Allah Ya shiga tsakanin ka da mugu... "Murmushi kawai Jalal yayi kafin yace " Ameen Annah nah.... Ansar ya d'an mik'o masa hannu sukayi musabaha kafin suka soma gaisawa... Jalal zai soma yima Ansar godiyar d'awainiyar da yake da family d'insa Ansar yayi saurin kawar da zancen da fad'in" Don't even start patient if not nasa Annah ta goge ka cikin 'ya'yan ta coz I'm her new son.. kasan anfi son sabon d'a.... Gaba d'aya suka murmusa idan ka d'auke Zubaidah dake rakub'e bayan k'ofa, gaba d'aya she's feeling guilty for what happened to Jalal, she feel responsible.
"Waige waige ya d'an soma yi da kansa, gaba d'aya Sun d'ago nufinsa, neman Zubaidah yake, tabbas idan bai b'ata gani ba, Ya ga wann fuskar da a kullum yake kwana yake tashi da ita....
"Shattima da Ansar suka fice suna hira tamkar sun saba da juna...
"Annah ta juyo ta kalli Zubaidah wacce fuskarta ke duk'e, ba sai ance maka hawaye take ba, juyowa tayi tana duban Jalal wanda ya kafe Zubaidah da idanu kafin tace " barin d'an zauna a reception ta fice tana d'an murmushi tana goge ragowar hawayen dake idanunta.....
"A hankali ta d'ago idanunta da suke jik'e da hawaye ta sauk'esu kan kyakkyawar fuskar sa.... Kallonta kawai yake babu ko kyafta idanu..... Takowa ta ringayi a hankali tana tuno tun farkon had'uwarsu da irin k'alubalen da suka fuskanta ko ince wanda suke kan fuskanta har rana mai kaman ta yau.....
"Cak ta tsaya gaban gadonsa ba tare da ta iya furta koda kalma ba.....
"Hannu Jalal ya mik'a ya rik'o hannunta...... A hankali ta soma fad'in" I'm sorry.... I'm sorry Ya Jay....... Kuka mai k"arfi ya kufce mata..... Kwanciya saman k'irjinsa tayi ta shiga rusa kuka mai tsuma zuciya....
"Dukda rad'ad'in ciwo da yake ji bai hana zuciyarsa yin sanyin dad'i ba..... Hannunsa maras cannula d'in yasa ya dafe bayanta a hankali ya d'an rungumeta ido a lumshe yana shak'ar k'amshinta. A hankali ya soma furta " Please Zubaidah...... Shiru ya d'anyi sabida har cikin b'argo da tsokarsa yake jin zogin kukan nata.... A hankali yaci gaba da fad'in" Pls ki daina kukan nan, it hurts kinji...... Tsit yaji ta daina kukan sai ajiyan zuciya da takeyi, sharkaf ta jik'a masa gaban riga da hawaye..... D'an dafe jikin gadon yayi yana k'ok'arin tashi.... Cikin sauri ta mik'e tana k'ok'arin taimaka masa had'i da goge hawayen idonta.... Kallonta kawai yake yana murmushi had'i da d'an ciccije leb'e sabida wajen aikinsa dake masa zogi....
"Pillow ta saka masa jikin garu ya d'an kishingid'a .... Kallonta yake kanyi yanda taketa faman goge ragowar hawayen... Hannu ya bud'e mata kafin yace " Come here....
"Babu musu ta k'arasa ta haye gadon gamida shigewa jikinsa, a hankali yake shafa kanta yana fad'in" Zubaidah bana so kina blaming kanki bisa duk abubuwan da suke faruwa, non of this is your Fault Miss Beauriful...... D'ago ido tayi tana duban fuskar sa na d'an wasu dak'ik'ai kafin ta sadda kan nata k'asa ta soma fad'in " But I don't wanna see you suffering, you don't deserve all this.... I'm sorry to say, but I already made up my mind..... I'm dropping the charges,....
"D'agota yayi da kyau yana dubanta kafin yace " You what?? No no Zubaidah you ain't going to drop the charges, Ko kin janye k'ara ko baki janye ba Alh Kasim Won't Leave us alone so as his children Labib and Salim.. ... Kallonta yake ido cikin ido kafin yaci gaba da fad'in" I won't allow to do that.... " But Ya Jay..... Bata kai aya ba ya katse ta yana girgiza kai yake fad'in" We can't make peace with those heartless until they all paid for their evil crimes.... Pls Baby don't give up kinji.... You're not doing this for your self alone, you're doing this for the entire ummah, akwai mata da yawa who are suffering from your experience, but they couldn't have chance to talk,..... Kinsan irin dad'in da suke tsintar kansu ciki lokacin da labarinki ya isar masu, I'm quite sure zasuyi farin ciki, and this is not a REVENGE it is your right your freedom, don't back down baby, you are not alone.... You have us all.....
"Kallon Jalal take soyayar sa da tausayin sa na ratsa zuciyarta, he's an Angel fad'awa jikinsa tayi ta rungume.... Ya d'anyi k'ara sabida ciwon sa data d'an fama..... Da sauri ta mik'e tana fad'in" Oh my I'm sorry, I'm sorry kaji, does it hurt.... Kallonta kawai yake da siraran idanunsa yanda duk ta daburce gaba d'aya..... Mak'aleta ya kuma yi da side guda snn ya soma fad'in" Hey relax is nothing serious...
"Ta d'an kallesa tace are you sure..?
"Gira ya d'aga mata dimple d'insa sai lotsewa suke kafin yace " Naji sauk'i tunda nayi tozali dake, oya tell me, what happened kika rame haka, dukda hijab ne jikin ki I can see that you lost weight....
"D'an turo baki tayi kafin tace ba ba kaine ba, I was afraid I might lose you....
"Cike da jin Dad'in kalamanta yake shafa 'yan yatsun hannunta kafin yace " Nothing will tear us apart kinji sweetheart oya give me a kiss ya k'arashe yana turo mata pink lips d'insa wanda suka k'ara jazir kaman fresh tomatoes.... Zaro ido waje tayi tana dubansa .... Kashe mata ido yayi kafin yace " Yeah a speedy recovery wishing kiss...
"Tafukan hannayenta tasa ta rufe fuskanta dasu.... Murmushi Jalal yayi kafin yace " I'm serious miss beautiful......
"Turo baki ta kuma yi kai a langab'e kafin tace " Pls Ya Jay.... Fah zan maka kuka...
"Okay sai na kira Dr Khaleesat ai... Kukan shagwab'a ta soma masa yayi saurin kwantar da kanta saman k'irjinsa kafin yace " Okay okay fine, but you I'm owing you a kiss ko bacci kike zan amshe kiss d'ina....
"Bacci ina zaka ganni bayan anjima kad'an zamu tafi masauk'in mu...
"Hannu yasa yana zame hijabinta yake fad'in " You must be kidding baby, ina kuma zakije after all kinzo jinyar mijinki ne.......Knocking d'in da akayi ne ya katse masu zancen nasu yayi saurin maida mata hijabinta snn yabada izinin shigowa, Zubaidah zata sauk'a daga gadon yayi saurin rik'eta yana rad'a mata stay right here baby....
"A hankali take fad'in" Ya Jay pls mana..... Daidai nan Dr ya shigo rik'e da files..... Murmushi ya sakar masu kafin Ya soma gaida Jalal, Zubaidah ma ta gaidashi cike da jin nauyin yanda Jalal ya hanata sauk'a a gadon.... Su Annah ne harma dasu Shattima suka take wa Dr baya....
"Wayyo wani sabon kunya ya mamaye Zubaidah, kaman gadon Ya tsage ta shige ciki, .Dr yace amma dai wad'an nan sabin aure ne...
"Ansar yayi karaf yace " Newlyweds ne ai Doc,
"Dr yayi murmushi yace I see..... Jalal dai murmushi kawai yake yi yana satar kallon Zubaidah... A hankali ta samu ta zame ta sauk'a daga gadon sanda Dr ya soma bayani wasu Shattima.....
0 comments:
Post a Comment