"Mamaki ya hana Zulaihat furta koda kalma guda.... Kallonsa take yanda yake driving basai ance maka da zuci yake ba.. Badon glass suna d'age ba sabida Ac da aka kunna da su kansu sun tsorata da gudun da yake falfalawa.....
"Girgiza masa kai ta shiga yi ta soma basa hak'uri ganin fad'a da masifa ba nata bane.... "Banza yayi da ita yaci gaba da driving idon nan nasa jazir, ba komai yake tunowa ba illa Zubaidah....
"Shiru Zulaihat tayi ta zuba wa sarautar Allah idanu.... Amma kam tasan dole suyi isan tsululun dare dukda gudun da yake zubawa, coz Abuja da Yola ba nan kusa ba...
***************
*Bauchi. ATBUTH*
"Har izuwa wann lokaci dai Baba Ciroma baisan duniyar da yake ciki ba, sosai suka masa illa... Maaman Khalifa da k'annenn sa haka suka ringa sharb'an kuka.... "
"Yan sanda suka amshi statement d'in Shattima.... For second Shattima bai bar side d'insu Maama ba, sai k'ok'arin calming nasu yake...
"Sun fito masallaci gabatar da sallahn Magrib Khalifa ya tsare Shattima yana fad'in" You better tell me the exact truth Shattima.... Me ya faru a hanyar ku..
"Shattima ya ajiye butar dake hanunsa cike da mamaki yake duban Khalifa kafin yace " Sorry ban gane me kake nufi ba, just what are you implying...
"Tambayar nake ka fad'a min me ya faru, idan 'yan fashi ne suka tare ku meyasa basu nemi kud'i ba snn meyasa kai basu maka komai ba sai mahaifi na, ... Huh???
"D'an girgiza kai Shattima yayi kafin yace " Khalifa you've already heard my statement what else kake so kaji... So kake nayi k'arya, iyakacin gaskiyata na fad'i nothing more nothing less, so dan Allah ka bar maganar nan haka kafin rayukan mu su b'aci... Daga haka ya ninke hannun rigar sa ya soma alwala...
"Hararan sa kurum Khalifa keyi don ko kad'an bai yarda da Shattima ba...
*************
"Mr President ya kamata ka tsaya let's sort this issue out... Duk wani shirin mu ya rushe, I'm.... I'm just completely pissed right now.... Barr ya k'arashe yana shafe malu d'insa da duka hannaye biyu...
"Ko kulasa Alh Kasim beyi ba sai sorting wasu documents yake... "D'agowa yayi ya kalli Barr kafin yace " Barr let's talk business... I'm stuck of that issue..... Ya mik'a masa wasu takardu kafin yace We've to attend to some clients suna company suna jiran mu....
"Barr ya kalli Alh Kasim shek'ek'e kafin yace " Ban gane ba, already kayi approving project d'in ne..??
"Gajeren tsaki Alh Kasim yayi gamida maida hulan sa baya kafin yace " What else do you want me to do.... I can do anything in my powers to prevent this company from going down.... Mutanen nan zasu saya 10, 10 percent, each of them so me kake so nayi Barr..
"Shiru Barr ya d'anyi kafin yace " Don't say ban gaya maka kasan da su waye kake dealing... Wasu zasu iya raba k'afa su saye majority shears of your company, before you know it Company ta zama nasu, and you must have to step down from your position of being the president..... Kasan dai mai Majority shears shine gaba....
"Murmushi Alh Kasim yayi kafin yace " Kaman bakasanni ba Barr, ni ne fa Alh Kasim Dasuki, mai taka kowa akan abinda yake so, ai bazan tab'a wann gangancin ba, nasan abinda nake yi..... Da zaran Company d'ina ta farfad'o.... I've my ways to get rid of them, don kasan bana deal da carukuce Business Disasters... Ya k'arashe yana wata murmushi.... Dariya Suka fashe dashi gabaki d'ayan su lokaci guda......
"Shiru yaji parlorn tamkar babu kowa, kai tsaye cikin parlorn ya nufa babu ko sallama, zauna ya hangi Salim Ya had'a tagumi da duka hannayen sa biyu, su Mummy da Mamy babu yanda basuyi ba ya fad'a masu meke damun sa yak'i..
"Zama Labib yayi yana jefa crackers d'in dake zube cikin bowl a center table lokaci guda yake canza tashan TV, idonsa naga TV yake tambayar Salim
. "Hey what's up with you, daidai lokacin da ya kai tashan k'wallo..
"Bai ansa ba sai mik'ewa yayi ya nufi can bayan parlour d'in yanda table na snooker ke ajiye, ya d'au cue d'in ya soma zungurin k'wallayen...
"Baki sake Labib ke binsa da kallo... "Mik'ewa yayi ya k'arasa jikin snooker d'in kafin yace " Salim magana nake maka meke damunka..
"A zuciye Salim Ya juyo yana watsa masa kallo kafin yace " It's all your fault, kai kaja duk muka tsinci kanmu a halin da muke ciki yanzu, banma san yaya akai muka biye ka, murmushi ya soma still idanunsa jazir kafin ya soma fad'in" You loved her right, you damn love Kausar and you did it to ruin our engagement night, you did it to tear us apart.... Ya shak'o wuyan Labib yana fad'in everything is your fault Labib Dasuki, Jalal is in jell Tariq yana asibiti and me....
"Fincikewa Labib yayi yana fad'in" Let go of my shirt you coward... In the first place banyi niyyan zuwa engagement d'inka ba, ka tak'urani sai naje... Naji.. Naji Salim I was the one who first came up with that idea, but tell me did I force you to rape her..?? Did I...???? Ya k'arashe cikin d'aga murya wanda yasa Mummy da Mamy dake zaune parlorn sama sauk'owa babu shiri....
"Hannu Salim Ya dunk'ule ya shiga kai ma Labib Naushi a hanci....
_Get to Fuck_ How dare you " Labib ya fad'i had'i da dunk'ule hannu shima ya shiga kai ma Salim duka ta ko ina.....
"A tamanin su Mummy sukayi kansu suna salati, duk iya k'ok'arinsu na ganin sun rabasu sun kasa, Jane ta fita da gudu ta nufi sashen Alh Kasim don kiransa.
"A k'ofa ta iske sa shida Munir zasu fice " Ganinta a rikice yasa su gane babu lafiya...
"Cike da tashin hankali jiki na karkarwa take fad" Sir,... Sir you need to come before they kill them selves.....
"Munir yace " What me kike nufi, just compose your self and spell it out....
"Nuna sashen Mummy ta shiga yi daidai nan suka hangi Mummy ta balcony tana k'walla wa Daddy kira cikin kuka...
"A tamanin suka nufi sashen nata Alh Kasim na fad'in" Those boys won't stop sai sun kashe ni.....
"Jini duk ya b'ata fuskokin su haka wajen kaman an yanka kaza....... Alh Kasim ya shiga jan Labib Barr Munir na janye Salim.... "Salim fad'i yake I'll kill you Labib Dasuki... Labib ma fad'i yake ko kuma ni na kashe ka... You good for nothing....
"Tsakiyan su Alh Kasim ya tsaya gamida daka masu tsawa kafin yace " what sort of nonsense is this... What the hell is wrong with the both of you.... Huuuuhh ku min magana....
"Labib na huci jini na d'iga a hancinsa yake fad'in" You ask this coward ya k'arashe yana watsa ma Salim dake goge jinin bakin sa mugun kallo......
"Salim yana huci yaci gaba da fad'in" I swear kaman yanda na rasa d'ana I'll kill you....
"Da mamaki suke kallon Salim ba tareda sun gane me yake nufi ba.... Juyawa yayi zai fice Alh ya rik'o hannunsa yace " What did you just say.. Wani d'a kake magana..
"Kai tsaye ya soma fad'in" I went to see Kausar and..... Shiru yayi hawaye na bin k'uncinsa.... Fuzar da iska yayi kafin yace " I don't wanna talk about it... Daga haka ficewa yayi yana huci....
"Labib ma k'ofa ya nufa yana huci, rigar Real Madrid dake jikinsa ya cire yayi jifa dashi don duk jini ya b'ata dashike fari ne, ya nufi parking lot wajen motar sa...
"Alh Kasim har hular kansa zamewa tayi bai sani ba, da sauri yabi bayansu yana fad'in " Ku tsaya ku saurare ni, I don't finish talking with you..... Barr ya rik'o Salim yayinda Alh Kasim ya k'arasa gaban Ford d'in Labib yana fad'in" Fito nan Labib...
"Key yayi ma mota kafin ya danna horn da iya k'arfinsa.... Mamaki ya hana Alh Kasim motsawa...
"Lek'owa Labib yayi ta glass yana fad'in" You stay out of my way or I'll run over you.....
"A saba'in ya matsa ganin da gaske kansa Labib zai bi... Yana fad'i ma securities " Don't open that gate...
"Mamy ce ta k'araso tasha gabansa sanda yake danna horn da iyaka k'arfin sa take fad"in " Kabi kaina Labib nace ka markad'e ni..... Cikin tsananin kuka take maganar...
"Bud'e motar yayi gamida barin ta a bud'e sai faman diri take ya nufi cikin gida cikin sarsarfa sai faman huci yake kaman tafasshen kunu....
***********
"Imam ya kuma duban goggo a karo na biyu kafin yace " Goggo zan tafi ofishin 'yan sanda ko Allah zaisa a dace...
"Goggo tayi shiru tana kallon sa tausayin jikan nata ya cika ta..
"Hannayen sa ta rik'e kafin tace " Kayi gaskiya Imamu nima duk a tunani na ko gidan wasu k'awayen nata ta tafi zata kira mu ta sanar damu daga baya, shiyasa ban ce ka tafi ka kai rahoto wa jami'an tsaro ba..
"Imam yayi shiru don haka kurum yaji zuciyar sa tafi aminta da Zulaihat wajen Zubaidah ta tafi tunda ta kasa samun peace of mind gaba d'aya dukda tace zata fad'i shaidar ta.... Sauk'e ajiyan zuciya yayi daidai lokacin da wayar sa dake pantpocket d'insa ta soma ringing... A zabure ya mik'e yana k'ok'arin ciro wayar....
"Ganin Zulaihat ce yasa gaban sa mugun fad'uwa da sauri ya shiga nuna ma Goggo wayar yana fad'in" Goggo gata tana kira.. Goggo ma ta mik'e tsaye sanda yake k'ok'arin amsa kiran....
"Hello Zulaihat ina kika shiga... Nida goggo mun damu, me ya faru, ina kika je....
"Murmushi Zulaihat ta sakar masa kafin tace " Relax bro, I'm okay..... Lafiya lou nake, ina 'yar tsohouwa hope baka rud'ata ba....
"Dafe kansa yayi gamida zama saman kujera kafin yace " Amma dai kinsan kin d'auki hakkin mu koh..
"Kayi hak'uri d'an k'anina zan dawo kwanan nan, ina lafiya, and pls tell goggo not to worry kaji.. Sai mun sake magana.... Bata jira cewar sa ba ta kashe wayar.... Tana watsa wa Umar mugun harara...
"Imam shiru yayi yana duban Goggo kafin yace " Tace tana lafiya she'll be back soon, kar mu damu..... Daga haka bai jira cewar Goggo ba ya mik'e gaba d'aya ya fice....
************
"Dubanta Umar yayi yanda ta had'e rai tamau babu alamun fari'a a tattare da ita..
"Hannu ya mik'a backseat ya d'auko ledar d'azu ya saya masu snacks da drinks a wani restaurant kafin su fice daga garin Jos kafin ya mik'a mata yace " Oya eat before you fall sick....
"Banza ta masa sai kallon glass d'in window take lokaci guda tana share hawayen da suke zubo mata.... "Har cikin ransa yake jin takaicin abunda take masa, but ba yanda ya iya, he just have to put up with her shits for the mean time idan dai yana so ya Mallaki Zubaidah. He has to win Zulaihat back...
"A hankali cikin wani salo na murya ya furta " When did you hate me that much.... "Shiru bata kulasa ba... Hannun sa guda ya Saki steering wheel dashi ya d'aura saman hannunta.....
"Da sauri ta janye hannunta tana watsa masa harara kafin tace " Kar ka kuskura ka sake tab'a ni, na fad'a maka wann ba Zulaihat d'in da ka sani da bane...
"Had'iyan kalamanta yayi yace a ransa "Duk kiyitayi tunda weak point naki shine so na da kike yi over...
"Bai kuma ce mata komai ba, sai maida hankalin sa da yayi ga tuk'in mota.....
*************
"Basu suke shiga garin yola ba sai wajajen k'arfe biyu na dare...
"Kai tsaye Hotel ya nufa zai kama masu masauk'i kafin safiya fir fir Zulaihat tak'i yarda.... Hararansa take tana fad'in" Wllhi kaji na rantse idan baka maidani Abuja kafin ranar shiga kotun Jalal ba wllhi zaka sha mamaki ne ... Zaka san cewa ban mance bariki a kwanyata ba...Zaka san cewa mace nake.
"Fuzar da iska yayi kafin yace a hankali "Enough of this Zulaihat....
"Ta kuma hararan sa kafin tace " Ko kuma mi.. Mi zaka mun, ko nima kashe ni zakayi kaman yanda ka saba.... "Bata kai aya ba ya rik'e arms d'inta sosai cikin daka tsawa yace " Nace ya isheki haka, naji I'm taking you back to Abuja and I won't stop you from testifying.... The only thing you need to do is to change your testimony..... Dole kibi umarni na coz from this very moment you are mine, ke tawace...
"Fizge jikinta tayi tace " Let go of me... Ni ba taka bace get this to your damn head... Daga haka tasa kai ta Bud'e marfin motar zata fice...
"Saurin fitowa shima yayi ya k'araso ya sha gabanta... Lallashinta ya shiga yi yana shan gabanta tana canza hanya.....
"A haka 'yan sanda masu patrol suka k'araso yanda suke suna fad'in" Su waye ku, me kuke yi a waje a wann lokaci....
" Umar yayi saurin rik'o hannunta kafin ya dubi 'yan sandan cikeda confidence yace " Officer barkanku da aiki d'an misunderstanding muka samu she's my wife........ "Hararansa take kafin tace " Hey don't be too fool of yourself ni ba matar ka bace... Umar Ya kuma rik'o hannunta yace " Com'on wifey.... It doesn't have to reach that point....
"D'an sanda tamkar TV suka zame masa, ya kalli wann ya kalli wancan "Da sauri yace " Kai kai just hold it right there.... Ku min bayani k'wara d'aya gamshesshiya ko mu wuce station...
"Umar na shafa baki ya k'araso jikin officer yasa hannu a pantpocket d'insa ya zaro 'yan d'ari biyar biyar kusan guda biyar ya shafa ma officer a hannu kafin yace " Mun gode officer aci gaba da aiki ...Daga haka yaja Zulaihat suka wuce mota, officer sai washe baki yake uwa gonar auduga....
"Suna shiga mota ta fizge hannun ta.... D'an kallonta yayi kafin yace " We spending the night at a hotel... Final say, na gama magana...
"Bata ce masa komai ba har ya isa wani hamshak'in hotel... Koda ya kama masu d'aki ma k'in shiga tayi dole ya fice ya kwana a mota don lallab'a ta yake ya cimma burin sa...
"Washe gari suka nufi gidan su Zulaihat.....
Sameena ce
[1/23, 22:30] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
81
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Tun daga kwanar anguwar jama'a ke kallon hamshak'iyar GLK d'in data karyo kwana,.. Matasa masu zaman bakin titi banda wow basu fad'in komai.. Kai Alla Alla suke suga wanda zai fito daga motar nan....
"Ganin wani had'add'en saurayi da Zulaihat sun fito yasa su sakin baki... "D'aya yace " Kai mutumi na gaskiya daduro ya kai ma yarinyar can... D'aya yace wann daga gani irin 'ya'yan b'arayin nan ta samu zasu kwasheta...
"Kai Baaba ashe akwai kashe k'wark'wata a unguwar nan..... Ire iren chats d'in da wad'an nan matasa masu zaman banza suka rink'a yi kenan.. ( Allah ka shiryar mana da matasan mu ka saka masu kishin kawunansu da zafin nema ameen)...
"Daga wajen gate wajen flowers ya tsaya... Zulaihat ta sa kai ta shige ciki don tasan Dad d'inta bai tafi office ba...
"K'irjinta sai faman lugude yake yana dukan tara tara, ga hawaye da ya ciko mata idanu....
"Gaba d'aya family d'in suna zaune saman dinning table probably having their breakfast.... Ba sai ance maka cikin farin ciki suke ba... Ta kai duban ta ga mahaifin ta wanda keta faman saka abinci a bakin wata yarinya wanda da gani kasan k'anwar ta ce, yarinyar bazata gaza shekaru biyu ba... Murmushi da hawaye ya kufce mata..
"Kaman daga sama taji ance Aunty Zulaihat..????
"Gaba d'aya suka juya suna kallon Imtihal wacce tayi maganar..
"Zulaihta ta d'ago kai hawaye na bin k'uncinta... Da gudu Imtihal ta tafi ta rungume ta tana fad'in Anty Zulaihat kin dawo knn koh, bazaki sake tafiya ki barmu ba koh...
"Zulaihat ta d'ago fuskar k'anwarta tana ganin yanda ta girma sosai... Kan ta sami zarafin magana sai sauk'an mari taji a fuskar ta..
"Ta d'ago tana duban mahaifin ta dake faman huci kaman zaki....
"Wani iskancin kika zo min gida watsettsiya kawai...
"Dafe fuskar ta tayi tana duban mahaifinta hawaye na zuba... " Aunty ta k'araso rik'e da k'aramar d'iyar ta tana tafe hannuwa...
"Dad ka yafe ni pls.... Bata kai aya ba, ya shiga figan hannuwanta suka nufo waje... Kkcib'us sukayi da Umar dake tsaye cikin shirt d'insa mai layi layi long sleeves yayi folding hannayen rigan zuwa elbows d'insa.... Jifa da ita Dad yayi ya nufi Umar a zuciye yana fad'in" Wanene kai dan Uban ka... Who are you..??
"Har ransa yaji zafin zagin da Baban Zulaihat ya masa, ba don yana neman kota wani hanya Zulaihat ta yarda dashi ba, da ya cirewa mutumin nan rashin kunyar sa...
"Umar Ya durk'usa har k'asa yana gaida Dad...
"Ba wann na tambaye ka ba, me kukazo yi gidana..
"Umar Ya d'an sauk'e ajiyan zuciya kafin yace " Baba pls kar ka mana mummunar fahimta, ni nan masoyin Zulaihat ne, ya d'an juya ya kalli Zulaihat dake zuban hawaye... Kafin ya dawo ga dubansa ga Dad sann yaci gaba da fad'in" Dama dama Baba mun zo ne Zulaihat ta nemi yafiyar ka snn.... Ya d'anyi shiru.. "Dad ya katse sa da fad'in" Snn me..?
"Umar yace "Snn na na.. Ni manemin aurenta ne...
"Kwab'e babbar rigar sa Dad yayi yayiyo kan Umar Ya jawosa ya shiga lakkad'a yana fad'in" No zaku nuna wa Bariki, 'Yan k'wal uba, tun kafin a aifi uban ka nayi nawa barikin... Shege maras kunya ka kwaso k'afa uwa mutumin arziki... Wann fuska taka da k'yar idan tana sallah..... Da anganka fulb'e sak amma wann ido naka da gani kaci uwar duniyan ci....
"Zulaihat har k'asa ta tsuguna tana kuka sosai take bawa Dad hak'uri.... Ya juyo kanta yana runtumo mata wasu manya manyan ashariya yana fad'in sai kin gane kuren ki yau... Tiyo d'in bayi ma flowers ya d'auka yayi kanta.... A tamanin Umar Ya k'aras ya kare ta Dad yayita lapta masa....
"Dad yana fad'in" Ka matsa min ko na kar ka.... "Da k'arfin gaske Umar Ya finciki tiyo d'in daidai sanda mak'ota suka soma shigowa don dama sun san gidan Alh Saleh Bushasha haka ne take faruwa idan matarsa ta sami rahoton an gansa a hotel, yaran sa kam ai ya zame masu jiki.... Wnn bak'in dalili na d'aya daga cikin abinda yasa Zulaihat ta shiga duniya....
"Umar yaci gaba da fad'in" Ina son Zulaihat ina sonta kuma dole ka aura min ita ko kak'i ko kaso ko mu tafi wani wajan daban muyi aure.... She's here to repent her mistakes, why is it so hard for you to forgive her... What kind of parent are you... Shin bazaka gode ma Allah ba, ya shiryar maka da d'iyar ka.... Ya sassauta murya kafin yaci gaba da fad'in" Haba Baba alot people suna neman nasu yaran su shiriya basu shiriya ba, pls don't be so selfish, give your a chance to start again... She's only human, she made mistakes.... Don Allah ka yafe mata ka aura mana juna....
"Duk rashin kunyar Alh Bushasha da rashin ganin girman mutane, yau saida Ya kasa tanka wa Umar, mutane kuwa sai jin dad'i suke suna jinjina wa wann saurayi, ga wa'enda suka san Zulaihat cewa suke tayi sa'an miji ta huta da fitanan gidan.....
"Aunty kuwa tab'e baki tayi tace " Mijina idan ka cika d'an halas ka aura wa Zulai wann saurayin.... Ba ita ta iya samo miji a bariki ba, ka duba yanda rankatatap anguwar nan aka fito akai mana chaa, suka baka kunya... Wllhi ka aura mata shi kowa ya huta... Jarabebbiya mai halin uwar ta.....
"Alh Bushasha ya kad'a kai kafin yace " Kinyi gaskiya, dama bansan wani munafuncin da iyayi bane ya dawo da ita muna zaman zaman mu....
"Ya juyo ya kalli Umar yace bata sadaki, mik'a mata a hannunta.... "D'ago kai tayi cike da al'ajabi tana duban Mahaifinta.... "Umar Ya gyad'a mata kai alamun kar taji tsoro...
"Alh Bushasha ya kalli Almajiran dake lek'owa ta gate yace " Kai kira mini Sallau Mai goro da Mal Tanimu Allah yasa basu tafi kasuwa ba..... Yaran suka tafi a guje...
"Alh Sallau da Mal Tanimu sun sha mamakin kiran da Mak'ocin nasu ya masu don ko ba zaman mutunci suke ba......
"Bayan sun hallara Alh Bushasha yace "Toh kune shaidu, dama a musulnce bayan sadaki alwali sai shaidu shknn aure ya d'auru.... Sun sha mamakin jin wann furuci nasa, don basu san da dawowar Zulaihat ba..... Take aka d'aura auren Zulaihat da Umar kan sadaki Naira 1000 don kuwa iyakacinta knn a jikinsa sai wasu 'yan canji da ba'a rasawa....
"Zulaihat bata tab'a tunanin abin na mahaifinta ya kai haka ba, tabbas she should just stop deceiving her self thinking ko asiri akai wa mahaifinta Zunzurutun halin sa ne... "Ubangiji ka bamu iyaye na gari, da 'ya'yaye na gari ameen....
"Kai ita ko a film bata tab'a karo da irin wann aure nata ba.... Abu kaman almara gashi ta zamo matar Umar wai....
"Bayan d'aura aure zata shiga cikin gidan yace " Ina zakije... Ta d'ago tana kallon mahaifin ta... Girgiza kai yayi kafin yace " Ai barikiji na fad'a maki kwabo kwabo wann nawa bakya gani, me zaki shigar min gida kiyi.... Maza wuce ki bisa can maki, kuma baki gama ganin rayuwa ba... Zatayi magana ya nufota yana neman abun raruma yace " Fita fice min daga gida annoba kawai.... Wnn yarinya farin k"afa ne dake da uwarki tunda na rabu daku nake samun nasara,... Hankad'ata yayi Umar yayi saurin tareta ta fad'o jikinsa... Alh Bushasha harda karkad'e hannu alamun an zubar da datti kafin ya maida sakatar gidan sa ya kulle....
"D'ago ido mai zuban hawaye tayi tana duban Umar, da sauri ya rungume ta yana fad'in" It's okay, you have me kinji, i'll never leave your side... I'll always be here kinji... Kasa ce masa komai tayi sai kuka da take yi da iya k'arfin ta... A haka ya Bud'e Mota ya saka ta.... Ya dawo driver seat ya zauna ya soma tuk'i suka fice daga layin.... Kai tsaye Hotel d'in suka koma....
"Bai bari tayi tafiya da k'afafunta ba, cak ya d'auke ta Ya nufi building d'in da ita,.... He's just acting like an Angel, duk wanda ya gansu dole ya rantse Zulaihat tayi dacen mai sonta...
"Ya kwantar da ita a d'aki ya masu placing order snn ya dawo ya shiga riritata tamkar k'wai... Gaba d'aya ya dad'a dulmiyar da k'wak'walwar Zulaihat, sabuwar soyayyar sa ya ringa gina mata a zuciyar ta.... Har ta kawo point d'in da tabbas Zulaihat ta yarda Umar nadama yayi tunda duk ya mata wad'an nan abubuwan... K'arshe sakewa dashi tayi suka wuni suna zallan soyayya a d'akin hotel d'in nan.... Sallah ne kurum yake raba su....
"Kanta na kwance bisa k'irjinsa yana shafa gashin kanta lokaci guda yana hango fuskar masoyiyar sa Zubaidah wacce he's doing all this ne to get her.... Jiyo muryar Zulaihat yayi tana fad'in" Mine toh yanzu baka tsoron Tariq ya mutu, Allah fa zai kama ka...
"Murmushi Umar yayi ya dago ta zaune ya manna mata kiss a kumatu kafin yace " Bazai mutu ba insha Allah sweet, ki daina saka damuwa ma ranki, you'll testify and Jalal would be out of jell, nima na tausaya masu shida Zubaidah they've been through alot, they deserves to be happy just like us.... In spite of everything we went through daga k'arshe mun kasance tare... So suma zasu kasnce tare...
"Murmushi tayi ta rungume sa kafin tace " I love you mine... Bai amsa ta ba sai squeezing nata da ya soma yi, zuciyar sa na raya masa tamkar Zubaidah ce a tare dashi....
"Haka suka kwana suka wuni suna faranta ran juna... Kwanan su biyu a garin Yola kafin suka kamo hanyar Abuja da sassafe....
******************
"Inaso naje Abuja da kaina Abdullah, na kasa samun sukuni har sai na gansa..
"Inaso satin da zamu shiga komai ya zama Ready, snn banaso kowa yasan wann batu, kama daga mutanen cikin gida har na waje... Ga dukkan alamu mugun mu yana tare damu, snn baya fata Modibbo ya dawo gare mu...
"Abdullahi wann magana daga ni ne sai kai babu third party saiko Uban gijin mu.....
"Shattima ya gyad'a kai kafin yace " Insha Allah komai zai zama ready Abbah, I'll have everything under control, albarkanku da addu'o'in ku bazasu fad'i k'asa ba Albarkacin fiyayyen halitta Abbah...
"Mai Martaba ya gyad'a kai kana yace " Tashi kaje Allah Ya maka albarka...
"Shattima ya kuma rusunar da kai kafin yace " Ameen Abbah snn ya mik'e a ladabce ya fice....
***************
"Suna zazzaune a parlor suna kallon labaru a tashar Aljazira malam Liti yayi sallam... Mumsy ta amsa masa gamida masa izini...
"Mal Liti ya rusuna kafin ya gaida Mummy Kausar da Asmah suka gaidas kafin yace " Hajiya dama wasu bak'in turawa ne kukayi....
"Mumsy tace bak'in turawa Mal Liti...
"Mal liti ya gyad'a kai yace k'warai kuwa Haj ba bak'ak"en faata bane..
"Mumsy tace "Toh Mal liti, bismillah a shigo dasu... Da sauri Mal Liti ya wuce masu iso...
"Ga mamakin su ba kowa bane illa Mr Felix Delecolina abokin kasuwancin Pappy na k'asar Holland kafin su dawo Nigeria da kuma Attorney Hamood, tsohon lauyan kampanin Pappy shima tun suna k'asar Holland.....
"Innah ta dubesu Shek'ek'e kafin tace "Aure Ummaru.. " Bata tab'a kiransa da sunar sa ba sai yau...
"Zulaihat ta durk'usa tana gaida Innah, bata amsa ba sai ci gaba da tafe hannaye da take tana fad'in" Na shiga uku ni Fulera, shiknn Baba Wuro kace na aifo ka ma kadangarun bariki.....
"Umar Ya fuzar da iska kafin ya kamo Zulaihat dake durk'ushe k'irjinta na bugawa yace " Muje sweet I'll take care of this.... TTad'ago ido zatayi magana yace " kiyi shiru ki shiga d'aki ki kwanta ki huta, Sai na shigo.... Da kansa ya kwantar da ita kafin Ya dawo wajen Innah suka soma toya tasu wainar...
"Firfir Innah tak'i amsar Zulaihat, fad'i take "Yanzu Baba Wuro duk 'yan mata masu mutunci da suke k'aunar ka ka rasa wacce zaka d'auko ka kawo min a matsayin surkuwa sai wann mai daujejjen fuskar wann daga gani ma idan bata tsere maka ba tayi sa'a da kai....
"A kufule yace " Toh wai Inna haramun ne, hak'uri fah zaki coz you just have to accept her.... Ya mik'e yana duba agogon hannun sa yace " Innah nayi tuk'i na gaji, da safe zamuyi magana.... Kallo kurum Innah ta bisa dashi had'i da rapka uban tagumi....
************
"Yau tun safe ta farka tayi komai ta shirya, kana ganinta basai ance maka tana cikin farin ciki ba, ofishin 'yan sanda suka soma zuwa yanda aka fito da Jalal kafin suka d'unguma suka bi motar 'yan sanda aka nufi kotu....
"Babu mutane da shike ba sananniyar shari'ar da aka saba bane na Zubaidah...
"A bakin kotun suka hangi Zulaihat da fitowar su knn daga cikin mota ita da Umar hannayen su rik'e cikin na juna....
"Jalal ya wani zabura yana fad'in" What are you doing here you Bastard, if you dare come near my wife I'll kill you....
"Zubaidah kuwa sai kallon mamaki take Bin Umar da Zulaihat dashi yanda hannayen su ke sakale cikin na juna... Tunaninta ya katse sanda ta jiyo muryar Umar yana fad'in"
"On the contrary Jalal, I'm not here to cause any trouble, na rako matata ce bada shaida, she's your witness....
"Ba Zubaidah bane kawai ta tsinci abun banbarak'wai gaba d'aya saida suka sha mamaki.. Amma ita ba wann ne a gabanta yanzu ba, mijinta ya zama free shine damuwar ta, ko Umar d'in ne ma yace zai bada shaida bazai dameta ba, idan dai Ya Jay zai fice daga wann k'angi....
"Jalal na huci yake fad'in" You ratchet imbecile... Da sauri Ansar ya shiga janye Jalal baya dukda handcuffs dake hannunsa, Zubaidah kuwa kasa cewa komai tayi don ta zama shock gaba d'aya....
"Alk"ali yana shigowa aka bud'e d'akin shari'a... Ba tareda b'ata lokaci ba Attorney Hafiz ya gabatar da Witness d'insa bayan an soma gudanar da Shari'a Zulaihat ta bada labari a kotu yanda Umar Ya karanta mata cewa Tariq da kansa ya ringa buga kansa a dutse don yayita rok'on Jalal ya kashe sa Jalal kuma yak'i... Dama kuma Jalal ya fad'i haka a statement d'insa.... Akai anfani da hotunan da jami'an tsaro suka d'auka don tabbatar da shaidan Zulaihat.... Ba tareda b'ata lokaci ba Alk'ali ya wanke Jalal daga zargin da ake made.... Masha Allah Alhamdulillah... Wann shine kalaman da suke iya fita daga bakin su...
"Zubaidah ta k'arasa ta rungume Zulaihat tana mata godiya... Umar sai kallonta yake tamkar ya had'iye ta, ta d'an d'ago tana dubansa lokacin Jalal na tareda su Annah su Ansar...
"Umar Ya sakar mata wata murmushi kafin yace " Aren't you going to congratulate Us, ko bakiji munyi aure bane..... Ya k'arashe yana rungumo kafad'un Zulaihat... "Daidai nan gogan ya maida hankalin sa wajen su,.. Cikin sauri ya nufi yanda suke had'i da rik'e hannun Zubaidah guda d'aya don gaba d'aya baiyi trusting Umar ba... "Kafin yayi ma Zulaihat godiya suna masu aika ma juna kallo shida Umar..
"Umar Ya sauk'o da idanunsa k'asa yanda Jalal ya sakale hannun Zubaidah cikin nasa, Zuciyar sa tamkar ta fito waje ta fashe... Huci kawai ya fara kafin ya sunkuyo yayi ma Zulaihat magana cikin rad'a "Let's get out of this place sweet... Kallonsa Zulaihat tayi cike da murmushi ganin yanda ya nuna mata so a gaban kowa kafin sika masu sallama suka nufo waje...
"Suna fitowa haraban kotun ya rungumeta tsam cikin jikinsa yana fad'in" It's over, nothing will tear us apart again insha Allah Baby... I'm now here, your Ya Jay is here... Bata san sanda ta kwanta cikin k'irjinsa hawaye na fita mata ba....
"Umar Ya karyi kwana knn ya hange su suna rungume da juna a farfajiyan kotun... Wani irin bak'in ciki ya tokare masa mak'oshi... "A ransa ya furta, it's not yet over Jalal.... This is just the start I'll take her back... Daga haka ya shiga palpala gudu dasu uwa masu shirin barin gari....
Sameena ce
[1/23, 22:30] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
82
*©Sameena Aeeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Kifa kansa yayi saman steering zuciyar sa na masa zafi.... Why why all this... Meyasa Zulaihat zata yaudare sa haka, she's never going to change, she manipulated him... She made a fool out of him. Goge k'wallan da ya zubo masa yayi kafin yayi key ma mota ya soma tafiya zuciyar sa cike da son sanin meyasa Zulaihat da Umar sukayi aure all of the sudden.. Wait waima when did all this happen, bayan yasan irin rabuwar da sukayi da kuma irin abunda Umar Ya mata, kai kalan grudges d'in dake tsakanin su bazai bari ace sunyi aure haka kurum ba.... She can't just easily fall for his trap again, after what she went through duk a dalilin sa... "B'angare na zuciyar sa ta shiga gaya masa " But she loves him.. So much... Very much... Zata iya fad'a ma tricks d'insa.. Girgiza kai Imam ya shiga yi shi kad'ai yake fad'in" No..no I won't let that happen, bazan tab'a bari ya cutar da Zulaihat with his lies again ba... Gudu ya shiga sulalawa a titi....
"Gaba d'aya Jalal ya kasa sakin hannun ta, tsam ya matse 'yan yatsun hannunta cikin nasa.. Farin ciki da murna a fuskar wad'an nan bayi ba'a bayani..
"Hadiza har wuya ta iso, sai wurga masu harara k'asa k'asa take tana cika tana batsewa ita ala dole ga hajiya hamshak'iya... Karkad'a k'afafu kawai take tana ganin tafi k'arfin wann gidan Ansar d'in nan da wasu 'yan kwanaki...
"Annah ta mik'e ta nufi kitchen tana fad'in bari a soma preparing for the dinner... Su Ansar dasu Hafiz ma suka mik'e suka nufi parpajiyan gidan wajen fararen kujeru suna tattaunawa nasu na laiyoyi da ba'a rasawa...
"Gogan fah ya kasa sakin soft hand d'in matar tasa... K'ok'arin b'anb'are hannunta ta shiga yi cikin k'asa da murya take fad'in" Ya Jay my hand, let go.. Zan jeni kitchen Annah needs me there...
"Matso da ita yayi had'i da kwantar da kansa kan wuyar ta cikin aigan rad'a yake fad'in" But I need you more here baby, even Annah would understand... Let's go to my bedroom and help me take shower....
"Zaro ido tayi tana dubansa.. Ya d'an ja hancinta yace "Hey relax, just kidding... Ta sakar masa murmushi mai kashe sa.. Wayyo Allah guguwar k'aunar ta ne ke kwasan sa...
"Sun jima suna kallon juna babu ko k'yafta idanu.. Tsantsan soyayyar juna kawai suke hangowa a idanun juna.... "A hankali ya soma matso da fuskar sa dap da nata fuskar cikin salo na soyayya.... Har saida tsinin hancin su ya mannu da juna, d'umin numfashin juna suke jiyowa.. ..
"Hadiza dake sauk'owa daga stirs tsaye tayi tana kallon ikon Allah... "Gyaran muryar da tayi ya dawo dasu daga duniyar da suka tafi....
"Kunya ya mamaye Zubaidah baki d'aya, duk saita daburce...
"Jalal ya sakar mata murmushi kafin yace " I'll take shower... "Gyad'a masa kai tayi kafin ya fara wucewa k'ala baice ma Hadiza ba, don a wuya yake da ita...
"Zubaidah tasa kai zata wuce kitchen Hadiza tasha gabanta tana k'are mata kallo da wani munafukin murmushi saman labb'an ta.... "Iyye kaga su fullo an fito birni an waye an iya soyayyar 'yan Habuja... Yanzu ke koh kunya bakiji ba sabida masifa irinta zamani kike biyewa namiji a bainar Jama'a....
"Ko kad'an Zubaidah bata son wani abu ya ruining mata wann rana mai tarin farin ciki..
"Girgiza kai tayi kafin tace " Wato dai idan mutum ba mai fahimta bane toh bazai tab'a fahimta ba... Snn idan aka ce mutum ya jahilci addini toh fah bazaisan lokacin da zai juya halal ya zama haram ba.... _Too bad my dear sister In-law I don't give a damn_... Daga haka ta sakar mata murmushi kafin ta rab'a ta gefen ta ta wuce...
"Kan uban can....!! Wai yau ita Zubaidah ke yab'a ma magana.... Ta shiga muzurai tana wawware idanu tana huci, tunowa da tayi da kud'ad'en ta a banki yasata sakin wani murmushi tana jijjiga tana d'alewa bene uwa wata basarakiya.....
*************
"Umar Ya fito daga motar hannayen sa rik'e da ledojin Amigo shak'e da kayan mak'ulashe, zagayawa yayi ya Bud'e ma Zulaihat.. Ta fito tana mai sakar masa murmushi kafin tace " Thanks Mine...
"Murmushi ya sakar mata kafin yace " At your service your majesty... Kan Zulaihat ya kuma yin girma, rayuwar da take mafarkin samu yau ta same sa Allah Ya cika mata burin ta....
"A tare suka tako k'ofar apartment d'in suna hira cikin jin dad'i... " Cak suka tsaya ganin Imam tsaye jikin taxi d'insa yana jira su k'araso....
"Gaban Zulaihat ya yanke ya fad'i, kana ganinta kasan she's in guilty conscious...
"Umar Ya juyo ya kalleta ya kalli Imam yaga irin kallon da suke ma juna, Imam na mata kallon tuhum ita kuwa kallon tsoro take masa...
"Mik'a mata ledojin yayi kafin yace " Get inside... "Ta d'ago tana duban sa.. "Gyad'a mata kai ya kuma ba tareda ya furta komai ba.... Zatayi magana yace " Now..!!!
"Tune d'in da yayi maganar da ita yasata wucewa sad'af sad'af tana satan kallon Imam.. Har ta kai k'ofa taji muryar sa ya kira sunan ta cak ta tsaya ba tareda ta furta komai ba...
"Umar Ya k'araso gabansa hannaye cikin aljihu kafin yace " Idan zaka mata magana kayi dani don bazan bar mata ta tana magana da irin ku ba...
"Imam ya d'an murmusa kafin yace " I won't take much of her time, on the contrary banzo nan don na mata magana ba, zuwa nayi na bata sak'on ta.... Ya k'arasa trunk ya ciro luggage d'inta kafin ya ajiye gaban Umar yace " Here ka shigar mata daga haka ya juya ya nufi motar sa....
"Umar Ya juya ya kalleta kafin ya bud'e murya yace " Nace ki shige gida... Da sauri ta bud'e k'ofa ta shige tana k'ok'arin maida hawayen ta....
"Umar Ya k'araso gaban Imam yana wata munafukar murmushi kafin yace " You shouldn't have bordered... Bata buk'atan duka wad'an nan.. Why not ka tara 'yan anguwar ku ka raba masu... Opss sorry ko kuma kayi gwanjan su ka sami na kashewa... Don nasan tuk'in motar nan a rana kayita yawo kana neman passenger is not easy.... Imam bai tanka sa ba har ya gama surkullen sa...
"D'an girgiza kai yayi kafin yace " Na gode ma Allah... Tunda nasan bazan tab'a saida mutunci na ba.... Snn nasan baka aureta sabida Allah ba, sai sabida wani biyan buk'ata naka... What ever your plans might be I'm gonna find out.....And you won't get away with it...
"Kayi amfani da soyayyar da take maka kana cutar da ita.... Don zan iya rantsewa you're only using her just like before ne., Why, meyasa zakayi haka ... Because she's in love, because she's Naive, because she's so easy to manipulate, Because you can easily outsmart her....
"Matse sa jikin mota Umar yayi yana fad'in" Shut your trap you idiot.... Don't engage your self into something you've no clue of... It's just a piece of advice.. Kayi nesa dani tun abubuwa suna yanda suke, idan kunne yaji jiki ya tsira... Daga haka ya sake masa wuya yana yarfe hannunsa kafin ya shige gida....
**************
"Alhmdulillah Habibities, everything will go back to normal da izinin Allah... We would rebuild your Pappy's Company, *Marafa Construction* zata dawo da izinin Allah... Zamu nemo best Architecture and Engrs wa'enda zasu kula da company d'in right sweethearts Mumsy ta k'arashe tana duban Asmah da Kausar...
"Murmushi kawai suke suna kallonta kafin suka tafi suka rungumeta suna fad'in" Mumsy ganin kicikin farin ciki shine namu farin cikin... We love you Momma.. Tayi hugging nasu sosai tana murmushi kafin itama tace " I love you both.. Wayar Kausar ne tayi k'ara alamun shigowar sak'o... Ganin Detective Amir ne ya sakata murmushi tana mai karanta sak'on...
"Gaba d'aya Mumsy da Asmah suka tsare ta da idanu suma suna murmushi.... Mumsy ta d'anyi alamu ma Asmah tana tambayar ta a hankali
"Asmah ta tank'wafo ta rad'a ma Mumsy magana a kunne.... Murmushi suka Saki lokaci guda a tare....
"Kausar ta d'ago tana dubansu kafin tace " Mumsy someone wants to ask for your permission..... Em em Mumsy yana waje, can he come in...
"Mumsy da Asmah suka kalli juna sukai murmushi... Don dama Kausar d'ince bata sani ba, already Ansar ya sanar da Mumsy da Asmah cewa zasuyi dinner a gidan sa na murnan cin nasaran Case d'in da abokin sa kuma aminin sa Hafiz yayi.... Snn shi kuma Amir yana neman a bashi dama ya gabatar da kansa officially a gaban Mumsy....
"Kausar ta jefa ma Asmah pillow tana fad'in ke koh.... Zaki sani ai.... Shiryawa sukayi cikin Arabian gowns masu kyan gaske, Na Kausar ja na Asmah Ash color sosai 'yammatan Mumsy sukayi kyau.... Ta saka masu albarka tareda fatan Alkhairi snn ta gargad'i Amir he should drive carefully ..... Amir ko sai murmushi yake yana sunne kai gaban Mumsy....
"Shiryawa tayi cikin wata Royal blue gown mai bak'ak'en duwatsu wanda ya amsa sunar sa wajen kyau musamman Annah ta saya mata sabida zuwan wann rana, ranar da za'a fito da Jalal.... Ba wani kwalliya tayi ba amma tayi kyau har ta gaji....
"Tana sauk'owa daga bene Annah ta saki baki tana kallon ta, a hankali ta furta, wow Masha Allah, my daughter is looking so gorgeous... Zubaidah ta k'araso tayi hugging Annah tana murmushi...
"Murmushi Annah ma tayi kafin tace kinyi kyau Zubaidah, Masha Allah...
"Zubaidah ta murmusa kafin tace " Na gode Annah...
"Annah ta shafi fuskar ta tana murmushi kafin ta mik'a mata wani shopping bag tace oya take this to Jalal...
"Zubaidah ta amsa lokaci guda ta tsinci kanta da fad'uwar gaba sanda Annah ta wuce tana fad'in" Yana d'akinsa maza ki kai masa ya samu ya shirya... Da k'yar ta iya amsawa da toh Annah kafin ta nufi d'akim.... Saida ta d'an d'au lokaci kafin ta murd'a handle d'in da sallama....
"Yana tsaye gaban dressing mirror yana goge jikinsa da towel d'an k'arami snn d'aure yake da wani towel d'in ta shigo..... Innalillahi wayyo Allahn ta this is her first time seeing him naked like this.... Gaba d'aya daburcewa tayi tama rasa ina zata saka ledar hannun ta....
"Shi kuwa totally speechless yake kallonta, ta masa kyau har ta gaji....
"Kanta a k'asa take fad'in " Dama dama Annah ce ta aiko ni... Tace I should bring this, amm am sorry bansan shiryawa kake ba.... I should have knocked before........ Bata kai aya ba taji sanyin sauran ruwan jikinsa manne da jikinta, sosai ya rungume ta ta baya gamida lumshe idanunsa...
"A hankali yake furta... " I was so scared, I tot I might lose you.... I tot I won't be able to hold you in my arms again..... Cikin sassanyar murya yaci gaba da fad'in" It feels so good to hold you like this.... Pls stay and don't let go......
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:30] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
83
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"K'ara matse ta yayi sosai cikin jikin sa yana sakin numfashi a hankali...
"Gaba d'aya Zubaidah ta daburce, wani irin yanayi maras fasltuwa ta tsinci kanta a ciki... "Bugun zuciyar ta yaci gaba da harbawa da sauri da sauri...
"Juyo da ita yayi suna facing juna... "Still idanunta a lumshe ta kasa d'ago kai su had'a idanu... "Jalal ya d'an sassauta rik'on da ya mata kafin yayi magana can k'asan mak'oshi.. " Babbyy... Shiru bata bud'e idanuta ba bata d'ago kanta ba... "D'an murmushi yayi da gefen bakin sa don yasan dalilinta na k'in bud'e idanu..
"Baby look up.. Ya fad'i yana d'ago hab'arta... Ganin tak'i bud'e idanun yasa sa kuma matsota jikinsa yanai mata wani salo yake fad'in" Idan baki bud'e idanun ki ba you'll be the one to dress me up.... Da sauri ta shiga girgiza masa kai tana fad'in" No zan bud'e ya Jay.
"Ya murmusa dimples dinsa suka lotsa kafin yace "Oya Bud'e idanun ki I've a surprise for you...
"Da k'yar ta iya bud'e idanun tana duban face d'insa... Shima d'in ita yake kallo.. "Hannu Jalal yasa ya rik'e face d'inta kafin yace " Ina Sonki Zubaidah, ina sonki da duka zuciyata da ruhina, I can't imagine how life would be without you.... Pls ki barni na nuna maki irin k'aunar da nake maki...
"Jikinta yayi sanyi haka kurum... "Sadda idanunta tayi ta kuma d'ago su da sauri don bazata iya jure ma kallon suffar sa ba...
"Jalal ya ware wata 'yar sark'a me kyaun gaske cikin wata 'yar takarda kafin ya shiga d'aura mata a wuya yana fad'in" Sweetheart this is a key to my heart.... Na mallaka maki ajiyarta sabida kece kika cancanci ki adana ta.... My heart is yours Zubaidah, Jalal is all yours, I'm deeply in love with you.... Daidai lokacin da ya k'arasa saka mata sark'ar ya kwanto da kansa zuwa kunnenta da wuyar ta, k'anshinta ya ringa shak'a yana lumshe dogayen idanun sa, lokaci guda ya soma zame mayafin data rufa a kanta....
"Zubaidah fah ta soma shiga miss call gaba d'aya Ya Jay d'inta seems different yau..... So take ta hanasa but ta kasa, gaba d'aya ma batada wann strength d'in, she became very weak all of the sudden....
"Gaba d'aya ya mance wata duniya suke ciki yayi nisa a wata duniyar..... Har saida ya masu masauk'i saman couch dake gefe a cikin room d'in, dab'as ya d'aura ta bisa laps d'insa... Kissing d'inta yake gently and passionately, his style is just super awesome.....
"Kasa jure masa tayi duk iya cijewa da daurewa da tayi... A hankali ta soma k'ok'arin zame jikinta murya can k'asa take fad'in" Ya Jay not now... Pls...
"Jalal da ya gama susucewa manne ta yayi cikin jikinsa kansa kwance a k'irjinta , cikin wani irin yanayi yake fad'in" Why not now Baby... Understand my situation pls Zubeee hak'urina gab yake da kaiwa 0.00 I'm dying to be with you Zubaidah.... Ya k'arashe yana murza 'yan yatsun hannunta....
"This is very awkward, kai bata ma san me take ji bane, all she wants kawai ya k'yaleta ta tafi.... Kaman yasan tunanin da take ya d'au Vail d'inta ya shiga rufa mata akan ta still tana saman cinyar sa kafin ya dube ta with that smile of his yace " I feel like I'm the most luckiest Man on Earth you know.... Batare da ta kalle sa ba ta d'an yi murmushi....
"Ya murmusa shima ya ja hancinta kafin yace " Kinyi kyau, yanzu haka zaki fita su Ansar su gane min ke yanda kikayi kyau d'in nan, gaskiya inaga bazaki fita wajen nan ba, stay right here in my room kafin na shigo mu biya karatu, don naga alama duk karatun da Dr Khaleesat tai maki sun zube, ya kamata a sake tasa su... Ya k'arashe yana shafa cikin tafin hannunta....
"D'an juya idanunta tayi gamida d'an turo baki kafin tace " Kai Ya Jay ,ni dai please..
"Kwaikwayan muryar ta yayi yana maimaita abinda tace..... "Gaba d'aya suka sa murmushi daidai lokacin da wayar salulan sa ta soma ringing, Ansar ne me kiran sa...
"D'aukar wayar yayi da hannu guda still d'aya hannun na cikin na Zubaidah kafin ya soma ansa wayar...
"Okay okay gata nan zuwa su jirata a parlour, she will be down in some minutes.... Daga d'aya b'angaren Ansar yace " Ah toh better ka matse 'yar mutane a d'aki ka hanata fitowa haka kurum...
"Jalal ya d'anyi dariya kafin yace " Toh kayan wani na d'auka... Sukayi dariya daga shi har Ansar d'in kafin suka hanging up...
"Kallon Zubaidah yayi had'i da shagwab'e fuska kana yace " Baby nifa da zasu taimake ni da sun d'auke mana fita wajen dinner d'in nan, let's have our own dinner a nan, daga ni sai ke... Ya k'arashe yana kashe mata ido guda.....
"Mik'ewa tayi tana murmushi had'i da rufe fuska ta nufi k'ofa ba tareda ta furta komai ba..... Taku kad'an yayi ya capkota ta fad'o jikinsa.... Suka jima suna aika ma juna kallo kafin ya sauk'o da fuskar sa ya sakar mata light kiss a lips d'inta yace " Su Kausar suna jiran ki a parlour, ki kula da kanki make sure su Ansar basu kalle min ke ba kafin na sauk'o.. "D'an hararan wasa ta masa kafin tace " Suma duka da nasu companies d'in suke so just calm down babu wanda zai lura da property d'inka. Ta k'arashe tana murmushi me kashe sa....
"Jalal kuwa cike da mamakin yaushe Zubaidah ta iya magana haka yake k'ok'arin kuma rik'ota ta zille tana fad'in " Late comers za'a punishing nasu.... Cak ya tsaya yana kallonta yanda komai nata ke burgesa..... Ita kuwa sai murmushi take ta kai k'ofa ya kira sunan ta da wani irin siga.... Juyowa tayi tana duban Face d'insa ba tareda ta kalle jikinsa ba.... "A hankali ya furta " I Love You..... " Murmushi ta sakar masa wanda ya kuma narkar dashi kafin ta fice ya bita da fitanannen kallo....
"D'an ware dogayen idanun sa yayi bayan ta fice yana murmushi kafin ya soma shiryawa......
"Hugging juna sukayi suna ma juna barka sanda ta sauk'o k'asa, gaba d'aya 'yammatan sunyi kyau har sun gaji, nan da nan su Kausar da Asmah suka sake gaba d'aya tunda dama Sun riga sun san juna..
"Kitchen suka wuce gaba d'aya suka shiga taya Annah fito da delicious abincin suna kaiwa saman table d'in da aka k'awata sa da kujeru na shak'atawa a larpajiyan gidan gefen grass carpet, ga hasken manya manyan wutar lantarki ya gauraye gidan, dukda gidan bai faye girma ba amma yana da kyau very cute..... "Daga can gefe kuwa Ansar ne dasu Amir da Hafiz suke gasa Barbeque a saman d'an k'arfen gashin..... "Wow Masha Allah sai son barka,
_Me karatu idan ka gansu dole ne su burge ka_
..
"Har saida suka zazzauna saman table gogan ya fito cikin wani lallausar yadi dark ash wanda ya fito da asalin farin fatar sa da kyaun sa, askin nan nasa ta masa kyau d'an gashi da suka soma fitowa sunyi filla filla tamkar ka sure ka gudu sabida yanda yayi kyau.. "Gaba d'aya saida Zubaidah taji kishin mijin ta a zuciyar ta, bata tab'a sanin tana kishin Jalal ba sai yau.....
"Ya k'araso da murmushi yana gaisawa da kowa, Annah kanta saida bakin ta Ya gaza rufuwa ganin yanda D'an nata ya fito tamkar wani balarabe.... SSeat d'insa na gefen na Zubaidah yake k'ok'arin Zara.
"Ansar yayi karaf yace " Mutum ka k'ume a d'aki sai sarauta kai ba basarake ba... Ka barmu sai gashi muke yi.... Ai sai kaje ka k'arasa gasa sauran naman kar ya k'one...
"Jalal ya sakar masa harara kafin yace " Kaga na maka kama da mai gashi ne, ya fad'i yana zama bisa kujera.... Idonsa nakan princess d'insa babu kunya ya rik'o hannunta ya karb'i spoon d'inta ya soma cakalan abincin..... "Ansar yayi saurin janyewa yana fad'in"Ai wllhi baka isa ba sai ka k'arasa gashin nan... Ya ture plate d'in abincin gefe.....
"Gaba d'aya me zasuyi banda dariya... Jalal ya watsa masa mugun kallo kafin yace " Toh daka janye plate d'in nawa ne , aidai kaga me cin abincin koh... "Annah kingansa koh ki masa magana kafin yayi provoking d'ina.... "Annah ma murmushi tayi kafin tace "Ni wann fad'a naku ai yafi k'arfi na, kunfi kusa.... Su Amir da Hafiz sai dariya suke, su Kausar na taya su....
"Zubaidah ma k'unshe dariyar ta take kafin tayi rad'a ma Jalal a kunne, babu musu suka ga ya mik'e sai murmushi yake ya rik'eta suka nufi stand d'in gashin....
"Ansar ya dara yace " AI duk taurin kan nan naka da miskilan ci zata sauk'e maka su.... Gaba d'aya suka kuma yin dariya, daidai lokacin da su Hadiza dasu Hamma suka sauk'o....
"Hankalin Hadiza gaba d'aya naga su Zubaidah yanda suke gudanar da gashin nan cikin kwanciyar hankali tareda so da k'auna, da ka gansu basai ance maka they are having a good time ba...
*************
"I've to accomplish this mission, it's now or never, Zubaidah tawa ce ni kad'ai, bata cancanci kowa ba sai ni.... Ya k'arashe zancen zucin yana hura bakin bindiga.... Mik'ewa yayi ya nufi motar had'i da saka mask a face d'insa ya d'auki hanyar unguwar ta APO ....
"Faisal make sure you get the job done, bana so a sami failure, that jerk must die, Kamar yanda iyayen sa suka mutu shima zaibi sahun su tunda na bisa a lallama yak'i yarda.....
"Faisal ya murmusa kafin yace " Consider it accomplished Boss... Daga haka ya zura bindigar sa cikin belt d'in wandonsa kafin ya kunna motar sa ya d'au titin Apo....
****************
"Ah ah Detective a waje ne kayi parking, Ansar yace sanda suka nufo waje, ...Amir ya gyad'a kai kurum ba tareda ya furta komai ba yana me zak'ulo wayar sa cikin aljihu.... Daidai lokacin da su Kausar suka turo gate suka fito, Zubaidah ta rako su har waje...
"Daga yanda yake tsaye yayi wata murmushi ya furta fad'uwa tazo daidai da Zama,...
"Sallama suke zasu shige mota ta hangi bakin bindiga anyi pointing Ansar dashi.... "Cikin wani irin k'ara mai firgitar wa ta furta Ansaaaar daidai lokacin da ya juyo ita kuma ta k'arasa ta hankad'asa... Tauuu kake ji harsashi ya same ta a gefen k'irjinta..... Innalillahi wa inna'ilaihirraj'iun gaba d'aya hankulan su ya dawo wajen...Amir ya fito da bindiga yana kai masa harbi inaa bai same sa ba.... Kausar ta daburce tayi kan Asmah tana k'walla kira ma Amir inaa yabi bayan Mai harbin, abinka da ga duhu na dare, harbin da Amir zaiyi ya samesa a k'afa, a take ya mida ma Amir martanin harbinsa yanda ya same sa a cikin sa.....
"Ganin hankulan su yayi wajan yasa Umar k'arasawa ya capko Zubaidah gamida toshe bakinta tana ihu, yana nuna masu Ansar bindiga alamun kar kowa yazo.....
"Ansar mutuwar tsaye yayi don baisan meke faruwa ba....... A take Kausar ta fad'i k'asa sumammiya.... Hafiz yayi k'ok'arin bin Umar da Zubaidah ina ya tsere da ita.... "K'aran harsashai yasa Jalal fitowa da wani irin mahaukacin gudu.... Abinda ya gani yasa sa daskarewa a wajen ba tareda ya iya mosta koda d'an yatsa ba.... Daidai lokacin dasu Annah suka fito a rikice....
😰😰😰😰😰😰😰
[1/23, 22:31] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
84
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Wani ihun da Hadiza ta kurma ma iya cewa ya janyo hankulan mutan anguwa.. "
"Annah hannu har na b'ari take neman lambar ambulance.....
"Cike da tashin hankali Hafiz yake duban Jalal yana fad'in" Jalal your wife m, they took her.. Sun d'auke ta....
"Kausar ta mik'e zunbur tayi kan Asmah da Ansar ke zaune gabanta dirshan ya rik'e hannunta gam yana kuka yana sunbatu tamkar zautacecce.... "Girgiza kai take tana fad'in" Sistu pls don't..... Don't leave me.... Kuka yaci k'arfinta.... "Asmah ta kasa fad'in komai sai jini dake fitowa daga bakinta da hancin ta.. Ansar kuwa yasa hannu ya toshe yanda bullet ya sameta don jini ne keta fita....
"Bazata jure kallon 'yar uwarta a wann yanayi ba.... Da sauri ta k'arasa da rarrafe gaban Amir yanda Hafiz ya rik'esa ya toshe shima yanda jini ke kwarara, da intercom d'insa Hafiz yayi amfani ya kira jami'an tsaro....
"Kuka take tana girgiza ma Amir kai take fad'in" Dan Allah kar ka tafi ka barni, pls hang in there kaji.. You'll be fine I knw you will.....
"Kallonta kawai Amir keyi kafin da k'yar cikin tsananin pain yake furta " I....I lo...love you Kausar... "Gyad'a kai kawai take tana tsananin kuka take fad'in " I know... Nasani and... And.... I love you too......
"Da k'arfi Ansar ya kuma fad'in " Get an ambulanceee...! Cikin tsananin kuka da tashin hankali yake girgiza mata kai yana fad'in" You'll be fine my Attorney, kinji kinji zaki sami lafia,..... Kuka yaci k'arfinsa sanda Asmah take fad'in" J... Just promise me... Zaka kula min da family d'ina, you'll be by their side.... You'll protect them... From..... "Muryar ta Ya sark'e.... Ansar yaci gaba da kuka yana girgiza mata kai kurum....
"Me Hafiz yake fad'i Zubaidah kuma, ina take, no bai lura bane Zubaidah tana cikin gida, babu wanda zai rabasu.... Ya k'arashe tunanin yana k'arasawa kan Amir da Asmah wanda ake k'ok'arin saka su a bayan ambulance daidai lokacin da Cops suka iso....
"Jalal sunata faman saka Amir da Asmah a ambulance suna taimaka wa ma'aikatan jinyar yana dad'a k'arfafa masu gwiwa cewa they'll be fine.... ya jiyo Hafiz na bada statement d'insa ma 'yan sanda cewa lallai an d'auki Zubaidah....
"Dam! Dam.! Dam!!! Sautin bugun da k'irjinsa keyi knn kafin ya dawo gaban Hafiz sanda ambulance ta soma tafiya yace " Me kace... Daidai nan Hafiz ya hango Ansar yana k'ok'arin driving mota.. Whatt!! A halin da yake ciki he can't drive da sauri ya dubi Jalal yace " Police zasu binciko yanda take Jalal I hope she will be fine... I'm sorry but I really need to drive Ansar.... Daga haka ya wuce ....Annah ma cike da tashin hankali take duban Jalal....
"Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana..... Zabura yayi yana girgiza kai shi kad'ai kafin ya soma gudu bisa kwalta tamkar zararre.... Annah ta bisa tana kiransa tana kuka inaa ya wuce...
"Gaba d'aya cirko cirko sukayi a wajen Annah da Hamma na kuka yayinda Hadiza take ta binsu da kallo, k'arshe ta soma lallashin su tana nuna masu abubuwa zasu daidaita, don ita kanta lamarin abubuwan sun soma bata tsoro yanzu kam....
"Fincika ta ringa yi tana neman hanyar tsira tana bud'e mota.... Ya fizgo hannunta yana k'ok'arin saita kan mota yana fad'in" Don't Zubaidah.... Ta kuma fincika ta bud'e marfin.... Ya fizgota had'i da kwad'a mata mari ga wani irin ihun da take yi..... Saida bakinta ya fashe., Hanki ya manne bakinta da hancinta dashi tuni ta sulale cikin kujera.... Hankalinsa ya tashi ya soma fad'in" Kinga kinsa ina hurting d'inki, pls kar ki bari na maki wani abu, just stay with me everything will be alright, na tsara mana rayuwar mu.., Ya k'ura ma fuskar ta idanu kafin a hankali ya furta " I love you Zubaidah, very much.....
"Gudu yake ba tareda yasan yanda yake jefa k'afafun sa ba, all he knows kawai shine Maitama crescent ya nufa... Wani irin huci da yake yi zai tabbatar maka ba'a hayyacin sa yake ba.....
"Na'uran computer da suke nuna harbawan numfashi da bugun zuciyar Tariq ya soma ceasing.... "Mum dake zaune gefen sa a kujera ta mik'e a zabure tana jijjiga gadon tana ambato sunan sa... Mik'ewa kawai Tariq yake idanunsa a rufe.... "Danna alarm tayi na kiran Dr ta kuma fita a birkice ta iske Dad na shigowa.... Ganin yanayin ta Ya tabbatar masa babu lafiya.... Daidai sanda take kuka take masa bayani Drs har biyu suka shigo cikin sauri....
"Dakatar dasu Mum sukayi kafin suka shige cikin d'akin... "Ganin irin kukan da Mum keyi yasa Dad tausaya mata ya k'arasa ya rik'ota gamida zaunar da ita duka shima bai sami zarafin iya lallashin ta ba....
"1 2 3 sai su danna wani abu Wanda yake d'ago numfashin mutum idan yayi k'asa haka likitocin suka ringa yi amma abu yaci tura.... Lokaci guda computers d'in suka nuno dogon layi sai k'ara kawai kake jiyowa tsiiiii......
"Ba tareda b'ata lokaci ba suka soma sunce na'uran babban Dr d'in yana bawa Ass d'in nasa time of death na Tariq Maina.... Allahu Akbar bawa bai isa hana abinda Allah Ya k'addara ba....
"Mum da Dad suna hangosu ta glass wani irin k'ara ta Saki ta fad'i k'asa sumammiya ganin yanda aka rufe fuskar tilon d'anta da farin bedcover d'in..... "Alh Maina durk'ushewa yayi yana kukan da baisan sa'ilin da ya kufce masa ba...
"Nurses suka zo da sauri suka d'aga Mum had'i da admitting d'in ta....
*************
"Da iyaka k'arfinsa yake dukan gate d'in yana fad'in " Kasim Dasuki come out here you ratchet imbecile... Kasiiiim ka fito nan... "Securities sai k'ok'arin rik'e Jalal suke sun kasa... Basu Salim kurum ba harta su Mummy saida suka fito a rikice...
"Fincika yake daga rik'on securities d'in yana fad'in" Duk Wanda ya Sake gigin zuwa kusa na, sai na kashe sa.... "Daidai nan Alh Kasim ya sauk'o daga sashen sa ya nufi gate su Labib suka bi bayan sa...
"Jalal na ci gaba da dokan gate d'in Cops suka iso....
"Rirrik'e Jalal suka soma yi sanda Alh Kasim ya fito Jalal ya yunk'ura ya kai mai naushi mai lafiya a hanci yana fad'in" You worthless imbecile sai na kashe ka.... Fad'i yake ma Cops let go.... Let me kill this Animal....
"Alh Kasim ya tofar da jini sanda Salim yayi wata tsalle ya kai ma Jalal maushi a hanci yana fad'in" How dare zaka zo har k'ofan gidan mahaifi na ka ci masa mutunci, i'll kill you Jalal.... Daddy Ya rik'o Salim yana finfincikewa....
"Jalal yana huci yake watsa masu mugun kallo yake fad'in"Shut your trap you idiot,... All of you must pay, you must pay for all the damages you've caused, non of you is gonna getaway with it......
"Alh Kasim ya murmusa kafin yace " Be careful with your language boy.... Inspector Gusau yace " Calm down dukan ku, we are here to investigate.... "Jalal yayi saurin fad'in" You tell me ina ka kai min mata ta, tell me Kasim...
"What... Labib da Salim suka fad'i lokaci guda suna masu kallon juna.... "Officer yaci gaba da fad'in " Alh munzo nan ne don gudanar da bincike sabida abunda ya faru bada jimawa ba.... Officer ya karanto masu abunda ya faru kafin ya k'ara da Zamu shiga gidan ka muyi bincike saboda the Dasuki's are the only suspect.... Mummy da Mamy kuka suka fashe dashi suka koma cikin gida....
"Alh Kasim yayi wata murmushi kafin yace " You can't just barge in to my house kan iyalai na kuce zakuyi bincike, wata doka ce ta baku wann damar snn maganar mune suspects kunyi kuskure sabida bana da lokacin su balle har na saka ma rayuwar su takunkumi, matsalan da nake fuskan ta da Dasuki Holding ma ta ishe ni, amma sabida guje ma zargi kuna iya shiga ku gudanar da binciken ku.....
"Jalal yana finfincikewa yake fad'in" Ko ka fito min da mata ta ko na kashe ka....
"Kallonsa kawai Alh Kasim keyi don shima ya shiga rud'ani jin Barr Kumo bai mutu ba snn an harbi Asmah da Detective Amir, mutuwar d'an sanda kaman Detective Amir ba k'aramin tashin hankali zai haifar ba, dole a tsanan ta bincike, gashi an d'auke Zubaidah, shi a iya sanin sa basuyi haka da Faisal ba, chance yake nema kurum ya kira Faisal ko Munir yaji wacce uwar ne ya faru.....
"'Yan sanda biyu ne suka shige cikin gidan yayinda sauran suka tsaya a waje dasu Alh Kasim....
"Jalal ji yake kaman ya shak'esu gaba d'aya kowa ya huta, k'iris yake da yin collapsing ya zube a wajen sabida abubuwa da suka taru suka cunkushe masa kwanya, a can su Ansar na buk'atar sa, a nan ma dole ya tsaya yasan halin da matar sa ke ciki tareda 'yan sanda....
"Da jan k'afa Faisal ya samu ya rakub'e cikin wani tsohon warehouse wanda aka jima da daina amfani dashi ya b'oye ciki yana jinyar wajen da harsashe ya same sa....
"A saba'in Barr ya gama parking motar sa yana mai tunanin ta ina zai soma breaking masu news d'in mutuwar Tariq.... Gaba d'aya jikin sa a mace yake GA Hon. Gali yayi demanding a basa duk wani investment d'insa da yayi a company d'in, gaba d'aya Barr baima san a yanda yake jefa k'afafun sa ba...
"Suna isa asibiti Kausar ta kuma collapsing sai gado aka bata itama... Kan kace me Ansar ma ya zube a k'asa sumamme..
"Annah da Hafiz gaba d'aya daburcewa sukayi sai ambaton Allah da suke ne ya cece su...
"Mumsy hankalin ta yakai mak'ura wajen tashi ganin har yanzu bataji from them ba, ta kira wayoyin su daga wanda ba'a d'agawa sai wanda baya shiga.... Zuciyar ta Ya yanke ya fad'i lokaci guda tana mai zafa saman sofa gijif. Tana karanto innalillahi wa inna ilaihirra ji'un.....
"Yana gama parking ya juyo yana kallonta yanda take kwance sumammiya, murmushi ya saki kafin ya soma fad'in" Finally my love, finally....... Zamu kuma kasancewa tare and now is forever....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:31] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
85
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERSA ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
*A Spectacular Chapter For you Sholingaye 😍😘 sak'on gaisuwa ya iso min Allah Ya bar so da k'auna.... Love you from the bottom of my heart, ga k'arin hearts dukda na aika maki da wasu 😅❤❤❤*
"Alh Kasim yana hangosa ya k'arasa da sauri cikin zuciyar sa yake fad'in" Gwara da Allah yasa ka k'araso....
"Hannun Barr guda ya rik'e can k'asa yake fad'in" What the hell took you so long..?
"Barr ya fuzar da iska kafin yace " Things are getting out of hand Alh Kasim... "Da sauri Alh Kasim yace " Kai rik'e abunka not now, I'm stressed out already. Fad'a min what really happenes there..
"Barr ya d'ago ya kalli Cops da fitowar su knn daga Dasuki Mansion ga Jalal a gefe sai huci yake wasu Cops d'in sun rik'esa yace " Alh Kasim let's not talk about it here idan kuma baso kake asirin ka ya tonu ba....
"Asiri na ko asirin mu, Alh Kasim, ya fad'i.
"Barr ya shafi kansa kafin yace " Ai idan na fad'a maka wani abinda ya faru hankalin ka sai yafi haka tashi...
"Zai sa kai Alh Kasim yayi saurin rik'osa kafin yace " Don't tell me they got him caught already... I mean that useless Faisal..
"Barr ya fuzar da iska yace " Ba wann ba, It's about Tariq... "Alh Kasim ya d'ago ido yana kallon sa... "Lafiya ya samu, zaiyi testifying koh,....
"He's no more.... He just.. Passed away..... "Daidai lokacin da Cops suka k'araso sukayi interrupting nasu.... "Alh Kasim ya murmusa kafin yace " Officers ai na fad'a maku you won't find any evidence regarding this very issue a gida na, cuz I have nothing to do with it.... "Jalal yayo kansa a zuciye yana fad'in.. " You liar ka fad'a min yanda matata take, ka tura a kashe Ansar snn kace a taho maka da Zubaidah, admit, just admit Kasim Dasuki..... Ganin yanda ya zama out of control yasa 'yan sanda rik'osa suna fad'in" Jalal this is a very serious matter... Ina mai tabbatar maka bazamu huta ba har sai mun sami wanda yayi wann aika aikan, ka kwantar da hankalin ka ka koma gida, zamu ci gaba da bincike babu hutu....
"Kallon su kawai Jalal keyi yama rasa me zaice kafin ya soma girgiza kai yana fad'in " You all are insane , matar nawa tana hannun wann azzalumin mutumin kuce na tafi gida, ai idan kunga na bar k'ofar gidan nan Kasim Dasuki ya fito min da matata ce....
"Munir yayi saurin katse Jalal da fad'in kayi hankali da kalaman ka, kasan hausawa na cewa baki shike yanka wuya....
"Salulan Inspector ne ta katse su, ya d'aga yana amsawa 'yan uwansa 'yan sanda ne daga can yanda incidence d'in ya faru, sun gama aune aunen da zasuyi da duk wani abinda ya kamata su d'auka... Inspector yace su had'u a station don a samu komai ya tafi in order.. .. "Snn wasu cops d'in asibiti suka wuce don sanin halin da su Detective Amir suke ciki....
"Jalal ya k'araso har gaban Kasim Dasuki lokacin da Cops suke k'ok'arin barin gidan da sharad'in" They'll definitely get back to them...
"Cak ya tsaya gaban Alh Kasim kafin ya soma fad'in" Ka sani bazaka tabbata kanayi ba... Kasan ance *, Allah Ya karya fir'auna balle kai.... Hakkin duniya bazai barka ba, akwai ranar da zaka kwashi duk abinda ka aikata a tsakar kanka kayi bayanin su dalla dalla .... And to remind you this... "No one messes with my wife..... Daga haka ya juya ya shige motar police suka soma k'ok'arin barin wajen....
"Har sun soma tafiya Barr yayi saurin tsayar dasu kafin yace " Officers, regarding this matter, I think someone's hiding behind our shadows...
"Inspector ya fito yana duban sa da murmushi... Daidai nan ma Jalal ya fito a tamanin..
"Inspector ya dubi Alh Kasim kana yace"And what makes you say that Barr.... Kana zargin wani ne..
"Bai kai aya ba Jalal ya soma tunani.... Dukan tayan mota yayi kafin yace " I'm such an idiot, yeah it's him, shine shine ya d'auke ta, meyasa wann tunanin baiyi crossing mind d'ina ba sam, Girgiza kai ya soma idanunsa suka yi jazir ya soma fad'in..... "That damn bastard I'll kill him, ya fad'i yana mai soma tafiya, Inspector ya taro sa , Kan Barr Munir ya nufa ya shak'e yana fad'in" I know you working hand in hand with him... Nasan tare kuke shirya komai... Just tell me where did you take my wife to.. Ka fad'a min....
"Inspector ya rik'o Jalal yana tare sa kafin ya dubi Barr yace " Meyasa kace haka, yaya akayi kasan it could be him.
"Barr ya fuzar da iska kafin yace " Well yayi haka ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, he's been taking advantage of the situation yayi laifi aga kaman mu ne, sabida mune muke Court case da Zubaidah, while on the other hand shi Umar tsohon saurayin ta wanda aurene kurum ya rage basuyi ba....
"Jalal ya shiga janye Inspector yana fad'in" We need to go after that jerk inspector, he's insane zai iya yin komai wa mata ta....
"Suna wucewa Alh Kasim ya kalli Barr kafin yace " Tariq ya mutu bamuda sauran damuwa babu mai fallasa mana sirrin mu...
"Barr ya kalli Alh Kasim tsegege kafin yace " Yanzu ne lokacin da hankula zasu tashi don wllhi na tabbata iyayen sa zasu fad'i gaskiya ba tareda tsoron me ka iya zuwa yazo ba tunda they've got nothing to lose, wanda suke tsoron rasawan sun rasa, shiyasa yanzu shawarin da zan baka don't leave their side a wann lokaci da suke ciki, in fact kaida family d'inka gaba d'aya, they need you now, before they start thinking otherwise,
"Alh Kasim ya gyad'a kai kurun suka nufi cikin gida lokaci guda suna neman layin Faisal bata shiga.....
****************
"Kallonsa Zulaihat ta d'anyi don tunda ya shigo gidan bata gane kansa ba, he's acting wired and strange, shi kad'ai zakaji kaman yana magana idan ta tambaya yace babu komai....
"Yanzu haka ma zaune suke a parlour tayi matashi da cinyar sa suna kallan shirin Americans got talent sai jiyo k'aran motar police sukayi ya gauraye unguwar...
"Gabansa ya yanke ya fad'i sanda ya jiyo muryar Jalal yana fad'in" Umar ka fito nan kafin na kashe ka....
"Inspector ya dubi Jalal yace " Jalal kayi k'ok'arin calming kan ka kalaman da suke fita a bakin ka ka iya jawo maka matsala, I know how you feeling but just try to remain calm ka gane.....
" Inspector me kake fad'a ne Mamata my own wife is with that Animal and you expecting me to calm down.... Ya k'arashe jijiyoyin wuyar sa a tashe haka idanunsa tayi jazir...
"Inspector ya dafa kafad'unsa without saying a word.... Tsaye yayi da Jalal a wajen yana rik'e da hannunsa don baiso a kwab'a wani aikin kuma....
"Wasu police officers suka k'arasa suna danna bell...
"Ba Zulaihat kurum ba harta Innah dake d'aki saida ta fito a birkice tana tambayan lafiya su waye wad'an nan....
"Umar Ya dubi Innah yace " Babu komai Inna ki koma d'aki kawai....
"Zulaihat ta bisa da mugun kallo mai cike da alaman tambaya, bai tankata ba ya zura takalmi ya nufi k'ofa.... Da sauri ta biyo bayan sa....
"Aiko yana fitowa Jalal ya fincika yayi kansa yana fad'in" Where is she, ina take, ina ka kaimin mata, you rachet imbecile... "Inspector ya kuma rik'o Jalal.... Kai k'arshe dai Inspector d'aure hannunsa tareda na Jalal yayi waje guda sabida gaba d'aya ya kasa controlling Jalal....
"K'arasawa sukayi suka soma interrogating Umar, ko gizau yake basu amsa ba tareda wani tsoro ba...
"Ya kalli officers yace " You can ask my wife officers babu yanda na fita naje, ina gida tuntuni, Mata ta ma tana ciki zaku iya tambayar ta.....
"Zulaihat ta bisa da wani irin kallo zuciyar ta na bugawa.
"Officers suka rubuta komai kafin suka kalle sa suka ce zamu shiga ciki muyi bincike, babu musu ya basu hanya yana rik'o hannun Zulaihat....
"Wata kallo kurum suke watsa ma juna shida Jalal wanda da za'a barsu tabbas da an buga Third World War....
"Officers suka gama binciken su kafin suka fito suka same sa suka ce " Kaida Dasuki's kune suspects so zamu iya dawowa ko wani lokaci don ci gaba da gudanar da bincike.... And for now muna buk'atan Epassport d'inka dana iyalan ka sabida binciken mu bai k'are ba....
"Umar Ya soma girgiza kai yana fad'in " Me zakuyi da international passport dina... I thought I made it clear to you bansan yanda matar sa take ba, ban jima da yin aure ba officer me zanyi da matar sa snn kun shiga kun gani da idanun ku.... Officer idan kunada tunani The Dasuki's ya kamata ku bincika don sune suke court case dasu ba ni ba, ni me Barr. Ansar ya min da zan nemi rayuwar sa..... This is very clear aikin Dasuki's ne......
"Officer ya murmusa kafin yace " Hilarious, da kai da Dasuki's are blaming each other, dole akwai wani abu a k'asa, nasan bazan yi arresting naku ba tareda samun k'wakk'waran hujja ko dalili ba, amma ina da right na toshe duk wata hanya da zaisa kuyi tunani ko yunk'urin barin k'asar nan lokacin komai zai fito fili..... So I'm waiting shiga ka kawo min....
"Umar Ya fuzar da iska kafin ya shiga cikin gida lokaci kad'an ya fito da dank'a wa officer passport d'in, saida ya bubbud'e ya gani ya tabbatar kafin ya kallesa yace " We will get back to you.... Daga haka ya nufi mota yanda su Jalal suke....
"Jalal ya dubesa yace ina mata ta.... Inspector ya kalli Jalal da hannun su ke d'aure waje guda yayi murmushi ba tareda yace komai ba....
"Officer ya bawa inspector statement d'in Umar Ya kuma dank'a masa international passport d'insa..
"Inspector ya jinjina kai kafin yace " They both are hiding something suspicious..... Amma for now zamu amshe gaba d'aya passports d'in Dasuki's, no one should leave the country snn wann zai taimaka wajen binciken case d'in Zubaidah.
"Jalal ya soma k'ok'arin k'watan hannun sa daga cikin cuff d'in yana fad'in" Officer let me go, mata ta, tana tareda shi.... Kar ya mata wani abu, pls let go.....
"Officers suka kallesa cike da tausayawa sun ma rasa ta yaya zasu soma calming nasa, gaba d'aya station suka nufa a tare.....
"Cikin tsananin d'aga murya take fad'in "Ka fad'a min, ka fad'a min Umar ina ka kai Zubaidah, ina ka kaita.. Ta k'arashe tana huci...
"You shut up, ya daka mata tsawa yana wani irin huci kafin yaci gaba da rage kayan jikin sa....
"Zulaihat ta kuma shan gaban sa cikin tsananin kuka take fad'in" Ka fad'a min, just tell me why are you like this, meyasa meyasa, I thought you did change, why am I so stupid, you still love her, you will never stop loving her, even if she's not meant for you .... Ka fad'a min da bakin ka....
"I said Enough..!! Ya fad'i had'i da kwashe ta da mari Me kyau... Dafe k'uncin ta tayi ta shiga ja da baya tana hawaye....
"Gajeren tsaki yayi gamida fuzar da iska yayi jifa da rigar hannun sa ya nufota yana k'ok'arin lallashi...
"Ja da baya take tana fad'in" Kar kazo kusa dani, don't come near me... Bai kulata ba ya rungumo ta cikin jikin sa da iya k'arfin sa, duk wani kokawan da take ganin ta k'wace kanta ta kasa.... "Kuka mai tsuma zuciya ta fashe dashi.....
"Inna kuwa tunda taga 'yan sanda hankalin ta Ya tashi, gashi tun lokacin ciwon marigayi mijin ta Baffah ta had'u da hawan jini, shi kansa Umar d'in bai sani ba, gashi bata shan magani ba'a kuma aunawa a san sauk'a yake ko hawa, a kwanakin nan tunda Ummaru ya kawo mata matar sa ya sanar da ita yayi aure take jin jikinta babu dad'i, wani sa'in ma ko toilet ta shiga tofah sai ta kwanta a k'asa, tau yauma tunda taga 'yan sanda taji dalilin zuwan su hankalin ta Ya kuma tashi, tasan yanda Baba wuro yake son Zubaidah, tabbas zai iya yin komai a kanta, Inna ta shige d'aki ta kule kanta ta shiga aikin kukan takaici da bak'in ciki...
******************
"Hankali tashe suka fito zasu nufi gidan Alh Maina suka kuma yin kicib'is da motan 'yan sanda....
"Oh Allah.. Salim Ya fad'i gamida dafe kai, Labib kuwa tsaki ya buga zuciyar sa naci gaba da tafarfasa ...
"Dammit...?!!! What again, Alh Kasim yace sanda ya bud'e motar ya fito...
"Inspector ya sakar masa murmushi kafin yace " Eh dawowa mu kayi...
"Alh Kasim rai b'ace yace " Me kuma kuke nema, bamu son b'ata lokaci don gidan rasuwa muka nufa....
"Inspector yace " We won't take long ka kwantar da hanakalin ka.... Ba tareda b'ata lokaci ba inspector ya fad'a masa abinda ya dawo dasu.... .
"Haba nan Alh Kasim ya soma banbami yana fad'in" Wai ko sun mance wanene shi, shine fah Alh Kasim Dasuki president Dasuki Holding, the famous business man in west Africa...
"Inspector yace " Na sani you don't have to remind me of that..... Aikina nake gudanarwa, kar ka mance it involves police officer aside from that statement d'inku dashi Umar sounds suspicious, yana buk'atan k'kk'waran bincike.....
"Alh Kasim fah tamkar zautacce ya koma, nan ya shiga masifa yana surkulle, yana fad'in" Ko IG bai isa ya masa haka ba.... Saida Barr ya fito ya jasa suka shige cikin gida...
"Su Salim kuwa mita suke kan yi don sunyi niyyan ficewa daga k'asar kwanan nan sai an gansu, gashi yanzu an karb'e passports d'insu....
"Mummy kam kuka ta ringa yi tana fad'in itakam ta gaji da wad'an nan abubuwa sun k'i ci sunk'i cinyewa..... Haka Haj Nurah Mamyn Labib tayita bata baki..
**************
"Kukan nata baya ma fitowa... Innalillahi wa Inna'ilaihirraji'un kurum zuciyar ta ke ambata, ita kad'ai take shaking jikinta hawaye na bin k'uncin ta, Annah na gefen ta itama babu strength d'in a tare da ita, ga tunanin su Zubaidah ko wani hali suke ciki sai Allah..
"Dr suka soma fitowa daga d'akin theater d'in jikin su babu wani k'wari. Annah Mumsy da Hafiz suka nufe su cikin sauri..
"Kallon su sukayi babu wanda ya iya tankasu... " Dr Yusuf ya dafe kafad'an Hafiz yace " Em ku sani idan Allah Ya turo ma bawa k'addara toh fah dole ya karb'i wann k'addaran hannu bibbiyu, me kyau ne ko kuwa akasin sa...... Daidai nan Ansar ya k'araso yana gani bibbiyu
.... Mumsy ta girgiza kai tace " Dr don Allah ka fad'a min sun sami lafia, ka fad'a mun zamu iya shiga mu gansu....
"Police biyu suka k'araso wajen sabida Detective Amir kowa yayi cirko cirko yana duban likitocin... Dr Yusuf ya sunkuyo yayi ma d'an uwansa magana kafin ya wuce ya barsa dasu....
"Dr Frank ya kalle su kafin ya soma fad'in" I'm sorry, we tried but we just. ...couldn't........ "Ai bai kai aya ba... Mumsy ta zube a k'asa.. "Annah dake faman jero salati da innalillahi tayo kanta.....
"Ansar girgiza kai kawai yake ya cakumo wuyan Dr Frank yana fad'in" No... No this is not true, Dr tell me it is not true.... Hafiz yayi saurin k'arasawa yana rik'esa daidai sanda aka soma turosu bisa gado me tayu lullub'e da farin k'ylle..
"K'arasawa yayi ya yaye rufin fuskar ta yana kallo hawaye na kwaranya a idanun sa..... Fuskar nan nata tamkar tana bacci kaman ka kirata ta amsa.. Sosai yake kuka yana fad'in" Hey get up,.... ki tashi, nasan bazaki tafi ki barni ba, Daddy momma Hanif da Haifa and Grandma duk sun tafi sun barni, kin mance kince min you'll never leave me we would live and die together.... Why why did you have to leave me....... Nine Ansar d'inki your Attorney, your Stalker, your super glue.... Asmah kar ki tafi ki barni, Asma'u ki tashi nasan bazaki tafi ki barni ba...... Kuka yaci k'arfin Ansar...... Hafiz ya k'araso yana k'ok'arin janye sa.... "Kallon Hafiz yake yana hawaye yake fad'in" She gave her life for me Hafiz, she sacrificed for me.... "She was the great love if my life.... Hafiz ya rungume sa da sauri sanda aka ci gaba da tura gadon domin kuwa shima juriya ne da k'arfin hali kurum yake yi, da k'yar yake iya fad'in" I'm here bro I'm here, together we will overcome this . Kayi hak'uri Allah yana son masu hak'uri.
_"Allah sarki, Allahu Akbar... "Kullu man alaiha faan"... Fad'in Allah ne "Duk abunda ke doron k'asa zai shafe".. Allah kasa mu cika da imani.. Ameen.._
"Haka Allah yake gudanar da lamran sa ba tareda shawarin kowa ba, Azza wa Jalla, yakan jarabci bayin sa ta ko wani hanya mai kyau ko maras kyau ba wai don yak'i ka ko ya soka ba... Saidai sabida Buyan sa, Sarkin da babu kaman sa..
************
"Bud'e idanunta da suka mata nauyi tayi sann ta soma gani duru duru.... "Ta yunk'ura zata tashi taji ta a d'aure, bakinta an d'aure shima babu halin ihu.... Kallo ta shiga k'are ma wajen cike da tsoro hawaye na gangaro mata, wani sakwarkwaceccen d'aki ne wanda duk ruma ya cinye, babu komai a d'akin sai wann yagalgalalliyar gadon da take bisa... Hannayen ta da k'afafun ta gaba d'aya a d'aure suke....
"Take ta soma tunanin " Where am I, ina ne nan, me ya faru...?? Take komai ya soma dawo mata kwanyar ta.... Girgiza kai ta soma tana hawaye murya baya fita dashike an d'aure bakin... Kifa kanta tayi saman gwiwoyinta tana wani irin kuka da duka zuciyar ta..
"Ga tsoro da son sanin halin dasu Asmah ke ciki ya cika ta...
"Tsanar Umar take ji har cikin jinin jikinta...
"Tab'a k'ofan da akayi yasata firgita tana k'ok'arin ja da baya...
"Tsaye yayi yana k'are mata kallo yanda take kuka da duka zuciyar ta, tana yunk'urin ihu da tashi...... " Karasowa cikin d'akin yayi ta kuma fincika saidai babu halin tashi...
"Ganin bazata daina azabtar da kanta ba, yasa sa ficewa cikin sauri don bazai juri ganinta tana shan wahala ba..
**********
"Zama Zulaihat tayi can k'arshen gado sanda ta farka taga baya nan... Tasan wajenta ya tafi, ta sani.... "Why why, meyasa rayuwa ta kasance haka.... Ta matse kanta waje guda tana ci gaba da kuka mai tsuma zuciya...
*************
"Misalin k'arfe 7:00am tsaye suke k'ofar ofishin 'yan sandan, daga nesa ya hangi Annah ta sauk'a daga tasi, jikinta kaman Kazan da aka tsoma a ruwan zafi... "Da sauri ya k'arasa gareta... Ganin hawaye kwance saman idanun ta yasa jikin Jalal ya kuma yin sanyi..... Bai iya cewa komai ba sai rungume ta da yayi yana kuka mai tsuma zuciya...
"Annah murya na rawa take fad'in" Stay strong Jalal pls, kaji.... Kaji.... Son.... Be a man
"Cikin wani irin murya mai had'e da kuka yake fad'in" But I couldn't Annah, I just can't..... Why life has to be so unfair, why all this,..... Annah why am I feeling this way.... Kaman Allah hukunta ni yake for my past.... "Annah nasan na sab'e ki na sab'i Allah.... But wllhi na tuna tuntuni.... Na gyara halayya na tuntuni.... "Annah kodai Allah fushi yake dani, ko akwai wani sab'on da nake ma Allah ban sani ba... "Annah ki yafe min duk saka ki damuwa ta hanyar bin abokan banza da nayi a baya ki yafe min, .... Yana mai ci gaba da kuka ya durk'usa saman gwiwoyinsa yana ci gaba da fad'in" Annah don Allah kice kin yafe min ko sami sauk'i a lamrana.....
"Annah wacce itama kukan take, tasa hannu ta d'ago Jalal tana girgiza kai take fad'in" Jalal ka daina fad'in haka, " Ko kusa kar kayi fushi lamarin uban giji, ka tuba tuntuni, Allah Gafurun ne Raheem, Allah baya tab'a kama bawan sa don yayi laifin da baisan laifi bane, shine mafi adalci, yana jin k'an bayin sa, duk abubuwan da suke faruwa tuni a rubuce suke, mu Karb'e su hannu bibbiyu muyi tawakalli sai muga nasara, Allah yana datar da masu hak'uri..... "Rungume juna suka kuma yi suna kuka mai cike da ban tausayi da tab'a zuciyar mai sauraro...
"Saman wasu kujeru suka k'arasa suka zauna, har lokacin Annah bata fad'a masa rasuwar Amir Tariq da kuma Asma'u ba.... Tana son sanar dashi don gwara ya sani tunda tasan dole ya sani mutuwar da ya k'unsa harda jami'in tsaro... Tana cikin wann Thought d'in Jalal ya jefo mata tambayar yaya su Amir....... Gaban ta na fad'uwa ta Bud'e baki zatayi magana knn wayar Jalal ta soma ringing.... Ganin lamba ce babu suna yasa sa saurin d'agawa hankali tashe...
"Daga d'aya b'angaren Umar Ya fashe da dariya kafin yace " Does it hurt, a rabaka da masoyiyar ka, of course it does, I know it does...... "A zuciye Jalal ya mik'e yana huci yake fad'in" You really are a scumbag, you imbecile, I'll kill you with my very own hands....
"Shut your trap you coward, Umar Ya katse sa kafin yaci gaba da fad'in" I only called ne to let you know that you will never see her again, I took her back, she's mine, ni kid'ai sai 'ya'yan mu da zata haifa mana, zamuyi rayuwar da muke mafarkin yi kafin ku shigo rayuwar mu.......
"K'iris ya rage zuciyar sa bata fashe ba.... " Jifa da wayar yayi ya nufi motar inspector wanda isowar sa knn k'iris Ya rage basu kad'e Jalal ba, Annah ta d'au wayan tabi bayan sa tana kira...
"Inspector yayi saurin rik'esa yana fad'in" Ka tsai da hankalin ka waje guda Jalal... "Girgiza masa kai kurum Jalal yake kafin yace " No no inspector ya d'auke ta, who knows me zai mata, I really need to go, .... "
"Ba tareda ya gane maganganun Jalal ba ya Bud'e mota suka shige, Sargent guda ya amshi wayar Jalal daga hannun Annah, gefe ta koma tana kallon motar har suka shige, tana karanto addu o'i, cikin zuciyar ta....
"Shiryawa ta gama yi tsaf, ta d'auki 'yar jakar ta na jido kud'i a banki ta mak'ale a hammata, saida tayi lek'e lek'e ta tabbatar babu kowa gidan kafin ta fito, Hamma yana can paranda sai zuba salloli yake, yayinda Kamal ke bacci a d'aki, kai ai gwara tayi ta amso kud'inta kafin hankula su dawo jikkunan su, yanzu daidai lokacin amsar kud'in ta ta gudu da yaron ta...
"Tana fita ta fito bakin babban titi, sai waige waige take kana ganinta kaga maras gaskiya, Tasi ta samu ta d'ale ta basa sunan bankin jikin Check d'in ya karanta mata, kai tsaye ya wuce da ita Bankin....
Sameena ce
[1/23, 22:31] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
86
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Desiccated To All Victims Of Rape...*
_Assalamu'alaikum Beautiful People, da fatan duk kuna cikin k'oshin lafia.. Ameen. Okay na sani previous chapter was brokenhearted... 😰 Sai k'orafi kuke min na Kashe Asmah da Amir kaman kun mance ba laifi na bane, duk aikin Alh Kasim ne, Kuma dae harda k'addara..... 😭 Tau da masu k'orafi dama wa'enda basuyi ba, duk kuyi hak'uri Sameena will make it up to you insha Allah... Kwanan zakuyi dariya har ku gode Allah 😜... I love you all 😍😘_
*Anty Batool Jatko and Mom Hanan wann shafi naku ne.... Sameena na yinku sosai 😍😘*
"Shuttt Up...!!! Ya daka mata wani uban tsawa yana huci.... Wanda ya sata sunkuyar da kai tana ci gaba da kuka..
"Umar Ya tsuguna gaban ta yana kallon ta Ya shiga d'ago fuskar ta da bakin bindiga yake fad'in" Zubaidah ki kalle ni, pls ki kalleni, why did you choose that idiot over me... Why, kin mance ne, kin mance mafarkan mu da kalan soyayyar mu, Zubaidah kin san duk abinda nakeyi ba hali na bane, I'm only doing this out of love.... "Snn ko kad'an banso ganin ki kina wahala haka, mu tafi wani waje yanda babu mai matsa wa rayuwar mu muyi rayuwar mu, I love you Zubaidah, I does... So much... Ya k'arashe yana k'ok'arin kai hannu zai shafi fuskar ta.....
"Da k'arfin gaske take k'walla wani irin ihu tana fad'in" No.. Don't touch me.... Na tsane ka, na tsane ka Umar..
"Mik'ewa yayi yana huci kafin ya soma fad'in" Why why.. Meyasa kika tsane ni, k'arya kike kina sona, na sani kina yi.... You never stopped loving me.... Admit... Oya admit you still love me.... Ya k'arashe yana fizgo gashin kanta, yana huci a saman face d'inta....
"Kuka take tana mai jin rad'ad'in damk'e mata gashi da yayi....Da k'yar take fad'in"Pls let go, ...kaji tausayi na, don't hurt me please....
"Sake mata sumar ta yayi yana huci jijiyoyin jikinsa gaba d'aya sun tashi yake fad'in" Zubaidah muna son juna kafin su shigo rayuwar mu, pls ki rabu da rachet Jalal d'in nan, if he loves you, bazai bar wad'ancan Bastards d'in suyi raping d'inki ba, ba mutum d'aya ba 3....3 men Zubaidah raped you lokaci guda, a gaban sa bai yi komai ba because he's nothing but a coward... Just imagine da ace ni ne a wajen wllhi nayi imani duk da sun bak'unci lahira a lokacin..... Zubaidah kar ki rabu dani pls.....
"Zuciyar ta yayi zafi, ya kuma d'ago mata mik'in da ya soma bushewa a zuciye ta soma fad'in" Yes I love Jalal... What I felt for you ba love bane, yanzu ne na gane Jalal shine masoyi na, ban damu ba koda yana d'aya daga cikin su..... If you really do love me kaman yanda kake cewa, then why can't you leave me alone, leave us alone.. Please na rok'e ka, ka daina cutar da Jalal yanada good heart..... Kana buk'atan Dr kaje kaga likita pls Umar, you are sick.
"Dammit... Ya fad'i gamida buga k'afar sa jikin kujeran da ya d'aure ta..... " Sunkuyowa yayi yana huci yake kallon ta yana fad'in" Why is it so hard for you... Why why Zubaidah, Okay yes banida lafiya, amma kece silan ciwo na .... " Me Jalal yake dashi wanda bani dashi..... Farin fata ne? Tsayi ne... Ko kuma kyaun halitta.... Ya shiga b'alle buttons d'in rigar sa yana fad'in " Kalle ni, d'ago ki Kalle ni babu wani abinda yake dashi da bani dashi......
"Cikin wani irin kuka take girgiza kai idonta a rufe tana basa hak'uri hawaye na kwaranya, tsoro da firgici suka cika ta, ya shiga tuno mata da wancan Daren 🌘.
"Ganin ta soma shid'ewa yasa sa daka mata wani tsawan kafin ya soma fad'in" Zubaidah bazan iya barin ki ma wani d'an iska ba..... You are so selfish, I chose you but you chose him.... Na rantse maki yau Jalal zai bak'unci lahira...
"Zan kirasa nan na kashe sa a gaban ki, kuma sanda zai iso nan, kwance zai ganni tareda ke, kinga ko ban kashe sa ba zuciyar sa zata buga, banida alhakin mutuwar sa....
"Kaman sauk'an aradu haka taji maganar... Ta shiga jijjiga kujeran tana fad'in" Ka min rai don Allah... Kar ka kuma kashe mun rayuwa..... Ko sauraren ta beyi ba... Ya Bud'e k'ofa ya fice...
"Kai tsaye apartment d'insa suka nufa, Jalal yace Inspector na tabbata bazamu same sa a nan ba, ka bari mu d'auki hanyar Akwanga...
"Inspector yayi murmushi kafin yace " Jalal this is my job ko baka yarda da profession d'ina bane....
"Jalal ya d'an ji babu dad'i kafin ya girgiza kai yace " A'a ko d'aya Inspector, ina dai fad'a maka ne abinda nake da tabbaci akai...
"Inspector ya gyad'a kai kafin yace mu fara zuwa nan...
"Zulaihat na zaune a d'aki taci kukan ta har ta gaji, taji ana bubbuga k'ofa, da sauri ta fito da niyyan yima Umar rashin mituncin da bai tab'a zato ba... "Ganin Jalal da polisawa yasa ta soma ja da baya...
"Jalal a zuciye yace " Ina mahaukacin mijin nan naki... Ina yakeee..!!
"Inspector ya rik'o Jalal yanai masa nuni da cuffs d'in hannun sa yace " Jalal idan bazaka nitsa hankalin ka ba, zan kuma d'aure hannayen mu...
"Jalal ya fuzar da iska kurum yana huci....
"Inspector ya dubi Zulaihat dake faman shaking yace ina yake.??
"Murya na rawa tace " Yayya baya nan , ya fita aiki...
"Inspector ya murmusa kafin yace " Ke kuwa ko kishi bakiji ne, idan kina kishin kanki ya kamata ki fad'a mana gaskiya, don mijin ki Ya kira mu Ya sanar damu Zubaidah na hannun shi, and that means he's also responsible for the death of DT Amir Kaita and Barr Asm'u Marafa.....
"Kaman sauk'an aradu haka Zulaihat taji zancen... Cikin wani irin murya take fad'in" Yanzu kuna so kuce min rashin imanin Umar har ya kai ya kashe mutane har biyu, .... Innah da fitowar ta knn ta soma ganin k'asa na juya mata, bata iya k'arasa fitowa ba, ta sulale a k'asa.
"Zulaihat ta fashe da kuka kafin tace " Officer wllhi bansan yanda yake ba, ban sani ba tun daren jiya ya fice... Ta k'arashe tana durk'ushewa a wajen tana wani irin kuka.....
"Jalal ya kalli Inspector yace " Kaji koh, pls ka k'yaleni na tafi ni nasan yanda wann Jerk d'in zai kaita, who knows me zai mata Inspector, he's insane he's capable of anything .... Ya k'arashe yana mai soma tafiya cikin sauri...
"Inspector ya rik'o hannun sa kafin yace " Bazaka d'auki doka a hannun ka ba, snn zuwa nan da ka ga muyi zamu k'ara report d'in a cikin case d'in ne... Wanted ake neman sa yanzu, ...... Inspector baikai aya ba, Sargent ya k'araso ya sara ma inspector cike da rusunawa ya dank'a ma Jalal wayar sa da ake kira....
"Jalal ya kalli screen d'in ya d'ago ya kalli Inspector kafin yace " Speaking of the Devil.... Saurin d'agawa yayi ya soma fad'in" You Animal ina ka kaimin mata, ina matata....
"Inspector ya masa alama kan yyasaa handsfree, Jalal yayi yanda Inspector yace "
"Umar yaci gaba da fad'in" You coward idan kana son matar ka be a man for once and stop being coward... Let's see how much you love her.... I'll send you location, kazo kai kad'ai and don't bring cops with you.... Let's see idan da gaske kana sonta and you can protect her.... D'iff ya kashe wayar....
"Jalal ya wani fincika yana dafe kansa yake fad'in" That imbecile I'll destroy him... Daidai lokacin da k'aran text ya shigo.... A tare suka karanta, Inspector ya kalli Sargent yace ya kira mota guda na police....
"Jalal ya shiga girgiza kai yana fad'in" No no inspector, rayuwar matata na cikin had'ari... Who knows what that Bastard could have done to her.... Zanje ni kad'ai kaman yanda ya buk'ata na dawo da ita.... Ya k'arashe yana mai soma tafiya...
"Inspector yayi saurin rik'esa kafin yace " Already hukuma na neman sa, Trap ya had'a maka sabida kaje kai kad'ai, amma a bisa a haka, ga motata ka tafi da ita mu kuma zamu biyo ka da wata motar daban..
"Jalal ya gyad'a kai ya amshi motar inspector ya kwashe ta a tamanin ya bar wajen...
"Inspector ya masa fatan tsarin Allah, snn ya gargad'esa sosai, he should be careful, kar ya d'auki doka a hannun sa....
"Daga nan Inspector ya danna intercom d'insa ya sanar suna buk'atar hilox ASAP.....
"Zulaihat tana shiga gida taci karo da Innah zube a k'asa tamkar bata numfashi, rud'ewa tayi tama rasa wanne zatayi gaba d'aya sai kuka,.. No d'in Ambulance ta shiga dialing hannayen ta suna rawa.
************
"Tsayuwa tayi k'ofar Bankin don ba wai ta iya bud'ewa bane.... Sai kalle Kalle take tana raba idanu, mutane kuwa sai kai komon su suke.
"Fuskar nan nata sai k'yallin Vaseline take.... "Hadiza fah abu ya dameta taga mutane sai shige da fice suke, babu wanda yabi takan ta... "K'arshe dai security d'aya ne da tun shigowar ta yake lura da ita ya k'araso yanda take yace " Lafiya hajiya..???
"Jin yayi mata hausa ba kaman masu tsaron gate d'in nan da suka ta shek'o mata turanci ba yasata washe baki ta soma gaidasa harda rusunawar ta... Ba tareda b'ata lokaci ba ta ciro checks d'inta har kusan guda uku tana nuna masa kan cewa kud'ad'en ta tazo amsa...
"Security ya k'are ma checks d'in kallo cike da mamakin yawan kud'ad'en dake jiki kafin ya soma tafiya yace ta biyo sa...
"Hadiza ta kuma washe baki ta rusuna tanai masa godiya suka nufi cikin Banki....
"Yana huci yayi saitin ta da bakin bindiga yana fad'in " Take off I said, take off those clothes, kar ki bari na cire maki da kaina don wllhi you'll regret....
"Kuka take tana girgiza masa kai take fad'in " Dan Allah kar ka min haka, kar ka zama d'aya daga cikin su, kar ka bari bak'in tarihin ya maimaita kansa...... " Kaji tausayi na don Allah.....
"Zaki min shiru ko sai na fasa kanki, munafuka kawai, wasu 'yan iska ma wa'enda basu sha wuya akan ki ba sun same ki a bulus balle ni.... Ki cire kayan ki nace, snn ki fad'a min yaya kike so abun ya kasance" Fast and furious ko kuma Slow and Gentle..... Talk ya k'arashe yana dad'a pointing nata da bakin bindiga.....
"Girgiza masa kai kawai take, ta duk'unk'une wuyar rigar ta gaba d'aya sai faman rawa da jikinta keyi....
"Yana hararan ta Ya shiga b'abb'alle boturan rigar sa yana fad'in " Wllhi yau sai Jalal ya ganki kwance cikin jikina idan yaso ya mutu.....
"Girgiza kai kawai take tana fad'in" No... No pls.. Don't do this, I beg of you, have mercy......
" Kallon wajen yayi tabbas this is the location, a tamanin ko k'arasa parking motar beyi ba ya fice ya nufi tsohuwar ginin mai tarin d'akuna yana tunanin ta ina zai dosa.... Kaman daga sama ya jiyo ihun ta sanda Umar ke k'ok'arin fincikar rigar ta......
"Wani irin wawan tsalle Jalal yayi ya nufi yanda ya jiyo sautin ta.... Da wata irin gudu.....
"K'afar sa yasa ya daki k'ofar saida ta b'alle.... Innalillahi Umar Ya hanga na kokawa da Zubaidah yana neman rabata da suturan ta.... Wani irin kukan kura yayi fatar sa ta koma jazir haka idanun saw... Take wani irin zufa ya karyo made.... " Dunk'ule hannayen sa yayi har kanajin k'aran Lank'washewar k'ashi da wata irin tsalle ya isa ya kwantar dashi da naushi yana masa wata iirin duka ko ta ina ba tareda ya iya furta komai ba......
"Kuka Zubaidah taci gaba da yi tana k'ank'ame jikinta tana kallon yanda Jalal ke dukan Umar, bata tab'a ganin sa cikin irin wann yanayi ba... Yana yi hawaye na fita idanun sa....
"Jefar da Umar da zaiyi ya jefa sa saman bindiga....
"D'aukar bindigan yayi da sauri yana dafe gefen cikin sa ga jini na bin bakinsa da hancin sa ya shiga pointing bindigar a kan Zubaidah yana kallon Jalal yake fad'in " I'll kill her........
*******
"Tun daga costumers care, kowa ya kalli check d'in sai ya mik'a ma d'an uwansa.... Maganganu suke kanyi ta harshen turanci suna kallon Hadiza...
"Sai faman cika take tana wani batsewa Acn Banki na ratsa ta, tana jin ta tayi kud'i, idan ta kalle su saidai ta tab'e baki tace " Ku gama turancin munafuncin ku kud'ina ne dai dole ku fito mun dasu... Gashi har alk'awari tayi ma security d'in da ya rakota cewa zata sammasa wani abu da zaran ta fito... _Nasan su o'o ma sun sa rai a kud'in Hadiza... 🤣_...
"D'aya ya mik'e ya bada check d'in a counter... Suma kalla sukayi cike da mamaki kafin suka kira accountant d'in Dasuki Holding suka sanar dashi right away....
"Jim kad'an ya iso wajen ya karb'i checks d'in yana gani, wann ba signing d'in Alh Kasim bane, this is fake, irin masu satan check ne suje a kwaikwayi signature d'in mutum a maka a jiki... Da sauri ya dubesu yace " Call securities right away, don't let her escape.. Daga haka ya nufi ofishin Manager...
"Waya akayi Dasuki Holding, Alh Kasim yace atafau baisan zancen ba suyi arresting d'inta.... Accountant yace an gama...
"Alh Kasim ya kalli Barr suka fashe da dariya kafin yace " We got rid of her. Ba ita mayyan kud'i ba, ina zamu iya kyautan wad'an nan kud'ad'e in spite of halin da muke ciki na had'arin kariyan arziki, taje can su k'are da 'yan sanda pressing charges zanyi nasan bazata tab'a yarda 'yan uwanta su sani ba, asirin ta zai tonu.... Suka kuma fashewa da dariya....
"Put that gun down you idiot.... Jalal ya fad'i yana ware hannayen sa yana wani irin huci.... Daidai lokacin da motar 'yan sanda suka k'araso... "
"You coward police ka kira... Cewar Umar lokaci guda hankalin sa yayi kan k'aran takalman cops... Jalal yayi anfani da d'an damar yayi tsalle ya janye Zubaidah, Tasss..!!! Umar Ya kai harbi sai a kafad'ar Jalal... Zubaidah ta k'walla uban k'ara, gamgam Jalal ya rik'eta da hannu guda...
"Umar Ya dira ta window 'yan sanda suka bisa a guje, suna masu dakatar dashi ko suyi harbi, ina gudu yake yana juyowa suna musayen wuta da cops, nan suka same sa a gefen bayar sa ta k'asa, gudu yaci gaba da yi yana cijewa ya shige ciyayi....
"Sosai Jalal ya rungume Zubaidah dake kuka da duka zuciyar ta yana fad'in" its over baby insha Allah, I'm here, I'm here baby... Police zasu kama sa and he will pay for everything he's done.... "Kuka kawai take tana dad'a kwanciya cikin jikinsa, shi kuwa sai cijewa yake yana matse idanun sa sabida rad'ad'i da bullet d'in take masa a cikin jikin sa....
"Nan da nan aka kawo ambulance aka d'auke su, journalist kuwa kaman anyi ruwan su, bama kasan wa ya gayyace su ba...
"Hadiza ta were idanu sanda 'yar sanda guda d'aya ta shiga janta tana fad'in" Get up, tashi nace b'arauniya kawai...
"Hadiza ta had'e giran sama da k'asa tana fad'in" Me na maki, kud'i na nazo karb'a.. Ta fad'i tana karkad'e Ghana most go d'inta na jdan kud'i,.
"D'ayar ta kuma jawo ta tana fad'in tashi kafin na sauk'e maki kulkin nan saman k'afarki, munafuka inama kikayi kalan amsar wad'an nan kud'ad'e ta fad'i tana d'aura wa Hadiza handcuffs...
"Hadiza ta soma kuruwa tana fad'in" Wllh ita ba b'arauniya bace, inaa ko kulata basuyi ba, suka wuce da ita bayan motar 'yansanda......
"Jet d'insu tayi landing a babban filin jirgin saman Abuja, kai tsaye Mansion d'in sa suka wuce dake Aso Rock, idan kaga Mai Martaba bazaka shaida shi cewa sarki bane, don kuwa gaba d'aya ya b'adda kamanni, jampa yasa da hula, k'uruciyar sa da kamannin su da Jalal sai ya fito sosai....
"Hon. Gali ya buga table kafin yace " Don't take me for a fool Alh Kasim, kowa yasan halin da company d'inka ke ciki, irin zaluncin da kayi Allah bazai barka ba, nayi danasanin zuba dukiyata a wann k'azancecciyar company d'in naka... I won't allow you to ruin me, zan cire dukiya ta, I mean everything that I invested here, single scent bazan bari ba.... Yayi Wata murmushi kafin yace " If I were you zan fara tunanin ta yanda zan fito da kud'ad'en nan kafin wata mai kamawa... Ya kuma yin murmushi kafin yace " Hon Gali nake, ko a house ka tambaya kaji wanene Gali.... Daga haka ya gyara babbar rigar sa ya fice...
"Barr da Alh Kasim suka kalli Juna....
"Tsaki ya buga kafin ya danna wayar gaban sa ya kira sakatariyar sa yace " Jade get me all pending matters right away... Daga haka ya katse wayar yana huci...
"Barr ya kafe sa da ido kafin yace " What do we do now...
"Tsaki Alh Kasim ya kuma danna wayar yace " Jade check my skedule with the CEO Modibbo Cooperation.... Daga haka ya kuma katse wayar....
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:31] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
87
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Kasa samun layin Ambulance tayi gaba d'aya hankalin ta Ya kai mak'ura wajen tashi, ta rasa waye zata kira ya taimaka mata ga Innah dai kwance take lifeless a k'asa..
"Tsoron ta guda kar Innah ta mace mata a nan...
"Kuka take sosai tana nadaman auren Umar wanda bata tab'a yin irin sa ba... Tunanin Imam ya fad'o mata, kai anya zata iya kiran sa, toh waye zata kira idan bata kirasa ba, batada kowa a garin nan bayan shi...
"Hannun ta na rawa ta shiga neman layin Imam tana mai Allah wadai da hali irin nata...
"Suna zaune a Caf shida abokin sa wayar Zulaihat ya shigo wayar sa, mik'ewa tsaye yayi yana kallon wayar shaye da mamaki...
"Anas ya kalle sa yace " Lafiya ko sarkin nacin nan ne har ya shiga...
"Imam ya girgiza kai ba tareda yace komai ba ya d'aga wayar k'irjinsa na bugawa da sauri...
"Cikin wani irin murya mai cike da kuka ya niyo Zulaihat tana fad'in" Imam ka taimaka min pls kar ta mace min a nan, don Allah kazo bro... I need you pls.... Daga haka yaji ta katse wayar tana ci gaba da kuka...
"Cak yayi tsaye yana bin wayar da kallo ba tareda ya fahimce ta ba..
"Anas ya tsare sa da idanu yana karantar sa...
"Imam yayi saurin d'aukan car keys d'insa ya tattari folder d'insa da wayar sa yana shirin tafiya..
"Anas ya rik'osa yace " Guy wai meke faruwa ne, ina zaka je..
"Imam ya zaro kud'i a aljihun sa ya ajiye saman table kafin yace " Friend zamuyi waya, I really need to go, Zulaihat ta kirani tana kuka ban gane kanta ba, but koma meye nasan babu lafiya...
"Uban tsaki Anas ya buga kafin yace " Amma you are very stupid wllhi, dama kan wann yarinyar ne kake wann rawar jikin, wllhi na ma zaci Goggo ne zaka ce babu lafiya... Ya kuma yin tsaki kafin yace " Babu yanda zakaje wllhi, Kadai san Dr Habu d'aukan attendance yake ...
"Imam ya d'an dafe kansa kafin yace " Anas zamuyi maganar idan na dawo, Ka bani hanya pls...
"Anas ya saki baki yana kallon Imam yanda ya ture sa gefe ya wuce cikin sauri....
"Tab'e baki yayi yace " Kaje Allah sa ta tsinka ruhin ka gaba d'aya bama zuciya ba, maras zuciya kawai....
**************
"Har aka isa station Hadiza bata daina kuruwa tana rantse rantse cewa ita ba b'arauniya bace.
"Ko sauraren ta basuyi ba suka tura k'eyar ta cikin cell.
"Wata gabjejiyar mata dake zaune a gefe tace " Idan baki mana shiru ba zaki gane kuren ki...
"Hadiza dake cike fam da haushi batasan sanda ta soma surfa wa matar nan zagi ba...
"Mata ta kad'a kai ta mik'e tsaye, take ta ga gaba d'aya sauran 'yan d'akin sun mik'e, idon Hadiza ya raina fata... Bata ankara ba taji sauk'an duka tako ina harda toshe bakinta sukayi don kar tayi k'ara aji..
"Haka d'ika d'ikan matan nan suka zaune Hadiza sukayita jibga tamkar an kawo masu jaka...
************
"Tana zaune gefensa cikin jikin sa aka gama dressing wajen da bullet d'in ya shige masa, aka nannad'e hannun cikin bandage..
"Zubaidah taci gaba da kuka tana fad'in" It's all because of me, babu Asmah da Amir saboda ni, kowa yana shan wahala saboda ni,.. Why all this, why this had to happen,....
"Hannu d'aya yasa ya rungumota cikin jikin sa gamida lumshe idanu... "Yana jin sauk'an aniyar zuciyar ta... Kafin ya soma furta " Babu abunda zai faru face yana rubuce tuntuni Zubaidah, Allah yafi mu sanin meyasa Al'amra suke faruwa haka. Never doubt what the Almighty can do, the Lord of the worlds Knows how to suddenly change things, He can suddenly Open the doors we never dreamed would open... He is the best Planner.... Ya k'arashe yana sakar mata sassanyar murmushi cikin k'arfin hali
" Gyad'a masa kai ta shiga yi da sauri tana goge hawayen idanun ta... Cikin wani irin murya mai rawa sosai take fad'in" I was so.... Scared, I thought I was going die,,... "It reminds me of that nigh 🌘..
" Shiiihhh" Jalal ya katse ta da fad'in haka kafin yace " Don't speak Baby,, Ina tareda ke babu abunda zai sake samun ki da izinin Allah, Duk tsananin bazan tab'a rabuwa dake ba, It's a promise .!!! Cikin zuciyar sa kuwa tsannin k'una da zogi yake masa wanda har yafi wanda yake ji a wajen ciwon sa.. " Ji yake da zai kama Umar tabbas da yayi masa kisan gilla...
"Dad'a matse ta yayi tana mai ci gaba da koke bak'in cikin ta... " A hankali ta iya furta " Duk sanda nake tareda kai Ya Jay I feel secured pls don't leave me kaji....
"Murmushi yayi gamida sumbatar kanta kafin yace " I love you Zubaidah bazan tab'a barinki ba till my very last breath, so ki daina tunanin akwai abinda zai sa ni Jalal na rabu dake, babu shi.. ...
"Ta kuma rungume sa tana mai tuno kalan ibtila'in dake kan faruwa dasu wanda daga wann sai wancan.
"A haka Dr ya shigo ya tadda su, ya masu prescribing magani su duka biyun kafin ya sallame su.
"Suna fitowa sukayi kicib'is da polisawa suna son d'aukan statement d'in Zubaidah, ga Journalist sunyi chaa tun daga waje...
"Ta kalli Jalal tana girgiza masa kai alamun bazata iya ba...
"Matse yatsun hannunta yayi sosai cikin nasa yana gyad'a mata kai kafin yace " You can do it, Ina tare da ke...
"Ta d'an sakar masa murmushi kafin suka k'arasa can wani rumfa 'yan sanda suka d'auki statement d'inta...
"Suna fitowa suka hangi Annah da Shattima.. Cike da mamaki suke binsu da kallo don basuyi tsammanin Shattima yazo ba...
"A tare Annah da Shattima suka k'araso yanda suke, Idanun su cike da tsantsan tausayi...
"Shi kuwa Jalal murmushin k'arfin hali kawai yake yi...
"Zubaidah ta k'arasa da sauri ta rungume Annah, hawaye na kwararo mata, Annah kuwa fad'i take" Ya isa Zubaidah, mu gode ma Allah... Allah kuma ya tsayar haka, Allah Ya bamu ikon cin jarabawar mu...
"Shattima ma k'arasawa yayi ya d'anyi hugging Jalal ta gefen sa maras ciwon kafin suka soma gaisawa, Shattima yai masa yaya jiki had'i da jaje da kuma addu'ar Allah ya tsayar haka..
"Jalal ya amsa da ameen had'i da tambayar sa su Ummah, Shattima yace " Duk suna lafiya sunce a gaida ku..
"Jalal ya murmusa kafin yace " Muna amsawa kuwa, mun gode sosai,
"Zubaidah da Shattima suka soma gaisawa sanda Annah ta tafi ta rungume Jalal d'inta....
"Jalal ya tambaye su yaya jikin su Kausar da Ansar, Annah tace " Ah Alhamdulillah, duk sunyi tawakkali, dukda pain d'in na cikin jikkkunansu, Yanzu haka ma daga can gidan Haj Raliyan muke, 'yan uwan Amir sun iso daga can Katsinan, Hafiz ma yana taredasu a can...
"Jalal ya d'an girgiza kai sanda tunanin Tariq ya fad'o masa, A hankali ya furta, Allah Ya maka rahama friend, Allah yasa kwanciyar hankalin ka knn...
"Ameen" ya jiyo muryoyin su suna amsawa...
"Gaba d'aya motar Shattima dake pake a parking space suka nufa..
"'Yan Jarida kuwa sukai masu chaa suna so suji ta bakin su, musamman Jalal da Zubaidah...
"A mota Shattima sai jansu da hira yake yana so ya d'an mantar dasu damuwa..
"A haka har ya d'auki hanyar Asorock ba tareda sun lura ba..
"Jalal ya d'an dubesa yace " Kasan dai bai kamata mu wuce gidan rasuwa a haka ba, ka kaimu gida first mu d'an kintsa..
"Shattima dai bai ansa ba sai d'an slow da yayi yace " Annah wai dama da inaso ku d'an gaisa da Abbah na ne don gobe zai wuce ba jimawa zaiyi a garin ba...
"Annah ta murmusa tace " A haba Baba na ai babu komai, mu k'arasa tunda ka biyo damu hanya...
"Shattima ya amsa da yauwa godiya nake Annah, kafin yaci gaba da driving da confidence..
"Jalal kuwa wata duniyar tunani ya tafi, wani Abbah Shattima yake nufi, yadai san Mahaifin sa Baba yake fad'i masa, snn Yakan kira Mai Martaba da Abbah, toh shin Mai Martaban ne yazo ko kuwa.... Haka kurum yaji ya tsinci kansa da fad'uwar gaba mai tsanani.. Daidai lokacin da Shattima yayi horn a wani wagegen Mansion wanda gate d'inma kawai abin kalla ne...
"Wow inji Sameena sanda Shattima ya saka hancin BMW dinsa a cikin a wagegen gidan. Tsayuwa fad'in tsarin gidan b'ata lokaci ne, guards ne tako ta ina suna tsaron gidan... Daga waje baka hango gidan dukda ginin bene ne dashike kaman yayi gidan kaman yayi slope, kwalta kuwa ya ratsa ko ta ina a cikin gidan, wasu tankama tankaman Parking lots ne har guda biyu suna facing juna wanda ko wani guda d'aya zai d'auki motoci ak'alla goma. Saida na soma hangan moticin ciki ne nace Masha Allah, idan bakayi bani waje inji hausawa, shak'e parking lots d'in suke da Luxurious Cars, Kama daga kan Mercedes da dai sauran su.. Kai Masha Allah dai kawai....
"Shattima na gama parking suka soma fitowa saida Shattima ya taimaka ma Jalal da Bud'e k'ofa sabida hannun sa..
"Gaban Jalal kuwa sai fad'uwa yake ya rasa dalili.. Harta Annah saida taji wani irin yanyi sanda suka iso gidan...
"Securities masu tsaron k'ofa suka shiga bubbud'e masu k'ofofin alfarman suna masu kwasan gaisuwa....
"Abbah na zaune a parlorn nasa wanda yasha ado da furniture na alfarma daga center.... A hankali ya mik'e tsaye Sanda Shattima ya shigo ya baro su a waiting parlor...
"Kallon Shattima yake yana mai k'arasowa tsakiyar parlorn yake fad'in" Abdullah ina Modibbo, kar kace min wani abu ya kuma gifta tsakanin mu, kace min zan sake ganin sa...
"Shattima kai a k'asa yake murmusawa don gaba d'aya bai saba da wann canzawan na Mai Martaba ba... A hankali yace " Allah Ya taimake ka Abbah, tare muke da Modibbo da family d'insa, idan ka min izini zan masu iso...
"Mai Martaba na murmushi da bai tab'a irin ta ba, siriryar hawaye tana sauk'o masa a idanun sa guda, kumatun sa suka lotsa kaman yanda na Jalal yake kafin ya shiga gyad'a kai yana fad'in" Bismillah bismillah Abdullah...
"Shattima ya rusuna yayi godiya kafin ya mik'e ya k'arasa ya masu iso....
"K'iraje suka shiga bugawa, jikkuna suka shiga samun sauyin yanayi, zuciyoyi suka shiga girgizawa, Idaniya suka shiga kallon Al'ajabi..
"Takowa ya ringa yi yayinda Jalal ma ke takawa cikin parlorn yanajin wani babban Al'amri a tareda shi, harta k'afafuwan sa da k'yar yake iya d'agasu.
"Gaba d'aya su Annah kallon ikon Allah suka tsaya yi....
"Saida suka k'araso daidai tsakiyar parlorn k'asar k'wan wuta mai geza Kafin suka tsaya cak su duka biyun... Bugun zukatan su ya k'aru..
"Tun daga d'an yatsar k'afar sa Mai Martaba ya soma kallon sa har ya d'ago zuwa fuskar sa, k'walla tab idanun sa, Tabbas shine, wann d'ansa ne Lamid'o..... Jalal dai sai kallon buwayar Ubangiji yake ba tareda ya iya furta koda kalma guda ba, yanayin da ya tsinca kansa maras misaltuwa ne, ganin wann mutumi ya jefasa cikin wani yanayi...
"A hankali Mai Martaba yakai hannunsa dake kan faman rawa ya d'an janye bandage d'in da aka d'aure hannun Jalal dashi....
"TAMBARIN ya gani, Tambarin masarautar su.... Kukan da yake rik'ewa shi ya kufce masa.... Ya shiga shafa fuskar Jalal dake tsaye babu alamun kuzari a jikin sa yana fad'in" Lamid'o dama kana raye, dama zan sake saka ka a k'wayan idanu na... Modibbo meyasa ka tafi ka barni nake rayuwa cikin k'unci na rashin ka da Mahaifiyar ka a tare dani.... Ya k'arashe yana mai Rungumar Jalal idaniya naci gaba da zubar da ruwa....
"Kuka ne ya b'alle masu gaba d'aya ba Jalal kawai ba....
"Cikin wani irin murya mai cike da shauk'i da tausayi had'i da kuka Jalal yake fad'in" Abbah, kaine Abbah na, Abbah ka jefar dani, Abbah meyasa... Meyasa kuka jefar dani....... Kuka yaci k'arfin Jalal...
"Shattima ya k'unshe bakin sa ya fice wani k'ofa yana mai fitar da kukan sa wanda yasan shakka babu na farin ciki ne....
"Annah da Zubaidah suma suka rungume juna suna nasu kukan..
"Mai Martaba ya shiga shafa fuskar Jalal yana fad'in " Ko kad'an, ko kad'an Masoyi na, duk iya tsawon rayuwar da nayi nayisa ne cikin k'aunar ka da sake son ganin ka, nasan watarana Allah zai kuma had'ani da kai.... Ina sonka muna sonka Lamid'o, bamu tab'a dainawa ba... Ya k'arashe daidai sanda suka rungume juna a tare shida Jalal...
RANAR ALKHAIRI, RANAR DATA GOGE BAK'IN CIKIN, RANAR DA ZUKATA SUKA CIKA DA FARIN CIKI.
***************
"Barr ya dubi Alh Kasim dake kan bincikan wasu files don ko zarafin yima employees d'insu salary basu samu ba., yace Ka saurare ni Alh Kasim ko kasan har yanzu ba'a sami Faisal ba, thank Goodness mun b'uya a inuwar Umar don yanzu gaba d'aya hankalin police na kansa. Amma ka sani duk randa suka kama sa toh fah za'a zak'ulo mu tunda Faisal za'a soma nema...
"Alh Kasim yaja wata doguwar tsaki yana rik'e da k'irjinsa dake masa zafi kad'an kad'an kafin yace " Barr wai kashe kaina ne kake so nayi, how many times do I have to tell you kasan yanda za'ayi a zak'ulo that imbecile Faisal wanda baisan aikin sa ba, that jerk deserve nothing but to die... I want him dead, idan ya mutu thing might be easier for us...
"Babban damuwa na yanzu shine na samu na rabu da wann d'an iskan Honorable d'in don naga alama bashida ta ido, bazan bashi k'ofa yayi destroying d'ina ba, da zaran munyi had'akar kasuwancin nan da Modibbo Cooperation kaga ahiknn, zan samu na watsar da d'an iska..
"Barr ya fuzar da iska kurum ba tareda ya furta komai ba, Don yasan akwai k'ura a gaban su, tun daga yanda PA d'in president na Modibbo cooperation yake masu yawo da hankali, don har rana mai kaman ta yau da PA kawai suke communicating basu daman magana da Mr President ba....
*********
"Da k'yar saida wata 'yar sanda ta shigo ta kwaci Hadiza a hannun matan nan wa'enda suka saba da shiga rikici iri da kala...
"Ko d'aga hannun ta ta kasa balle ta iya tashi, idanunta kuwa haka ya kumbura suntum, bakinta kuwa uwa shantu haka ya koma sabida yanda ya kumbura yayi tsayi suntum..
"Can gida kuwa a tunanin su Hamma Hadiza na tare dasu Annah ne....
Sameena ce 👌🏾
🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
88
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Desiccated To All Victims Of Rape...*
*Maryam Ahmad Paki dearest Inlaw... the chapter is yours sweetheart😍 Allah Ya bar k'auna, Alkhairin Allah Ya Kai maki🤝.... ❤*
"Kallo take ta faman bin Imam dashi yanda yake ta kaikomo a asibitin nan sabida Innah, K'walla mazu zafi suka kuma ciko idanun ta, Kai her whole life bata tab'a ganin mutum irin Imam ba, his generosity is extra ordinary, despite duk abinda ta masa he didn't turn his back on her, he's still here for her..... "
"Har Imam ya k'araso kujeran gefen ta Ya zauna Zulaihat bata san ya iso wajen ba, tayi nisa duniyar tunani da kaico na rayuwa, lokaci guda hawaye na bin pale face d'inta, ... " Hannun sa ta hango yana mai mik'a mata hanki...
"Ta d'ago ta dubesa cike da jin nauyi kafin tasa hannu ta karb'i hanki d'in tace " Na gode... D'an jimm yayi kafin yace " Do you need something? Are you hungry...??
"Girgiza masa kai tayi alamun a'a kafin ta soma fad'in cikin muryar kuka " Imam na gode, na gode da duk d'awainiyar ka dani, Allah NE kawai zai iya biyan ka, ...... "Da sauri Imam ya katse ta da fad'in" Ki daina fad'in haka Zulaihat I beg of you kinji, nasha fad'a maki ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, when ever you needs me , I'll be right there.... It's a Promise, snn ko gobe ne ma kike neman wani taimako na don't hesitate to tell me right away kinji......
"Girgiza kai ta soma tana share hawayen ta kafin tace " Imam ya kamata kayi nesa dani don ban cancanci mutane irin ku, ni mayaudariya ce, mai mance Alkhairi wacce zuciyar ta bai cika da komai ba face abinda take so take muradin samu ta ko wani hanya..... "Imam don Allah ka tafi kayi nesa dani, insha Allah wann shine k'arahen taimakon da zan nema daga gare ka....
"Imam ya kafe ta da idanu tausayin ta na ratsa zuciyar sa, so yake yayi hugging nata ko rad'ad'in dake zuciyar ta zai ragu amma babu hali....
"Murya a hankali ya soma fad'in" Zulaihat d'ago ki kalle ni.... Kasa d'agowa tayi sai share hawayen ta da take kan faman yi.... Ya kuma kiran sunan ta a hankali....
"D'agowa tayi tana duban sa with her watery eyes....
"Imam ya d'an muskuta don baison aminta da abinda zuciyar sa ke fad'a masa tunda matar wani ne....
"A hankali ya soma fad'in" Everything is happening for a reason, bamu ke tsara rayuwar mu yanda muke so ba saidai muyi fata, if to say d'an Adam shi zai tsara rayuwar sa yanda yake so ba Allah ba da duniyar ta gagari kowa, amma shike tsara mana rayuwar mu saidai muyi fatan kasancewa daga cikin bayi zab'bb'u kuma na k'warai.... Ki daina blaming kanki for what's happening, Allah Ya fimu sanin meyasa Al'amra suke a yanda suke yanzu ba..... Ki kwantar da hankalin ki kinji, I won't leave your side har mahaifiyar mijin ki ta samu lafia.....
"Zulaihat ta share hawayen idanun ta kafin ta furta a hankali " You are an Angel.... Daidai nan Dr ya fito yace yana son yin magana da Zulaihat in private...
"Zulaihat ta girgiza masa kai kafin tace " Dr zaka iya fad'a min komai a gaban sa he's my brother...
"Dr ya d'anyi jimm kafin yace " Well fine, mu k'arasa office d'ina, suka bi bayansa a tare...
"Dr ya kalli Imam ya kalli Zulaihat kafin yace " Mahaifiyar ku tanada hawan jini sann bata shan magani, rashin shan maganin da batayi ya haifar mata da kidney problem, I mean gaba d'aya two kidneys d'inta sunyi failing, for now zamu ke mata dialysis (Wankin k'oda) a k'alla a sati sau uku, snn wanki d'aya dubu ashirin ne... Pls ku samo kud'in as soon as possible a soma mata don kuwa her life is in danger.....
************
"Hannun Jalal na rik'e cikin nasa ya kasa saki yake jero godiya da addu'o'in girma wa Annah bisa babban gudumawar da ta bada a rayuwar d'an sa....
"Gaba d'aya Annah sai ji tayi she's not comfortable da irin godiyar da Mai Martaba yake mata, musamman da suka fahimci shi d'in sarki ne Mai cike da madafan iko, d'aya daga cikin manyan sarakunan arewa masu tutar daular Shehu Usman...
"Kai a k'asa Annah ta soma fad'in" Allah shi taimake ka, ni ce nafi Cancanta na mik'a godiya ta WA Rabbil Izza wanda ya zab'e ni a matsayin wacce zata raini Yarima d'an Babban sarki ta kuma shayar dashi, hak'ik'a wann ba k'aramin d'aukaka bane, Modibbo yaron arziki ne, Modibbo d'an arziki ne snn mijin arziki ne, Shakka babu jinin dattako na yawo a jijiyoyin jikin sa.... " Ubangiji ya kare ku daga sharrin mahassada da abokan gaba, Allah Ya ja zamanin babban sarki da Yarima, Allah Ya nuna mana d'iyoyin Yarima nan bada jimawa ba.....
"Mai Martaba ya kasa resisting murmushin girman dake kwance saman fuskar sa, tun bayan rasuwar Suhaima mahaifiyar Jalal ya jima baiji kalaman da suka kwantar masa da hankalk suka saka sa nishad'i irin kalaman wann baiwar Allah ba.... " Baisan sanda ya bud'e murya yana fad'in" Ameen ya Rahmanu ba.....
"Mai Martaba ya kai duban sa ga Zubaidah dake zaune gefen Annah kanta a k'asa yana mai bayyana murmushin iko yake fad'in" Yaki taho nan d'iyata....
"Zubaidah ta mik'e cikeda ladabi had'i da kunya ta k'arasa gaban Mai Martaba ya d'an rusuna gefe guda...
"Jalal sai satan kallon ta yake...
"Mai Martaba kuwa karanto masu Albarka ya shiga yi tareda jero masu addu'o'in samun nasara a rayuwa had'i da zama lafia da Juna da kuma fatan samun zuri'a d'ayyiba...
"Gaba d'aya kunya lullub'e Zubaidah yayi tamkar k'asa ta tsage ta shige ciki.... Su Shattim da Annah kuwa sai amsawa da Ameen suke....
"Wayar Shattima ne tayi k'ara yayi saurin sakata a silent gamida sulalewa ya fice zuwa wani k'ofa....
"Saida yayi wata silent murmushi kafin ya d'aga wayar cikin dakewa....
"Daga d'aya b'angaren Jade suka gaisa da Shattima a matsayin sa na PA d'in Modibbo Cooperation, nan Jade ta sanar dashi Boss d'inta na son yin magana dashi... Kai tsaye Shattima yace ta had'a su...
"Cikin k'ank'anin mintoci Jade tayi transferring call d'in to office din Alh Kasim...
"Ya d'aga sai faman washe baki yake suka gaisa da Shattima, nan Alh Kasim ya buk'aci ko zai iya magana da Mr President...
"Saida Shattima ya murmusa kafin yace " I'm sorry Sir my Boss is a very busy Man..... Ba kasafai ake samun sa ba, yanzu haka yana tsaka da meeting da wasu clients d'insa da suka zo daga Singapore.... Gaskiya bazaka iya samun damar magana dashi ba, you know how you business Men are...
"Alh Kasim yaji babu dad'i yau har shine ake wulak'an ta sa akan ganin wani, koda shike tunda shine mai neman abu he just have to put up with the situation...
"Cikin sauri yace " Okay eh.. Eh... Haka ne, amma dae pls this time around mu samu muyi confidential meeting d'in sabida already kayan sun zama ready....
"Shattima ya murmusa kafin yace " I can't promise you that Mr President, coz my Boss is very committed.... Amma dae I'll try my best na saka a schedules d'insa... Shattima yaci gaba da fad'in" I really have to go Mr President ya kammala ganawar sa,... " Ko me ake ciki I'll get back to you....Daga haka Shattima ya katse kiran yana wata murmushi yana karkad'a kai....
"Alh Kasim ya d'ago yana kallon Barr da ya masa k'uri.... Fuzar da iska yayi kafin yace " Barr ina so a samo min details akan owner na Modibbo Cooperation...
"Barr dai kallon sa kurum yayi kafin yace " Ina muka kwana da zancen Faisal...
"Alh Kasim ya murmusa kafin yace " Mutuwa ce ta kamace sa sabida amfanin sa ya k'are mana. Just get your boys ready, a zak'ulosa duk yanda ya shiga... Alh Maina kuma da matar sa zansan abinda zanyi dasu don nasan babu abinda zai hanasu testifying a kotu, what matters alot now shine mu samu kampanin nan ta farfad'o in two weeks time, I really wanna get rid of that imbecile Honorable.... Daga haka ya wuce ya nufi lift yana neman layin Salim da wuni zubur suna gidan su Tariq...
***********
"Ansar ne ya shigo da wasu lauyoyi sukayi ta'aziya wa Mumsy, ya tambaye ta Kausar fah, Mumsy tace tana can parlorn sama ku k'arasa..
"Ansar ya amsa mata kafin yayi jagora ma sauran 'yan uwan sa lauyoyin...
"Zaune ya hange ta fuskar nan nata very pale, watery eyes d'inta na lumshe tana k'udundune cikin ash hijab wanda yake har k'asa, cazbaha ne a hannun ta da alama tazbihi take...
"Ansar ya d'an sa hannu ya k'wank'wasa k'ofar, ta d'ago ido suka kalli juna... "Yayi k'arfin halin sakar mata murmushi kafin yace " May I...
"Tashi tayi ta zauna sosai tana gyara zaman hijabin ta da ya d'an zame kwantantun suman gishin ta suka fito.. "Gyad'a masa kai kurum tayi ba tareda tace komai ba..
"D'an k'arasowa gaban ta yayi cikin parlorn kafin yace " Ina su Mardiyan yaya suka barki ke kad'ai bayan nace masu ke d'in amana na bar masu., gashi sun barki those tears suna sake zuba..
"D'an murmushi kawai tayi na k'arfin hali kafin tace " Sun d'an fita ne amma suna dawowa...
"Ansar ya d'an murmusa, shima kana ganin sa kasan kurum juriya da k'arfin hali yake, he needs to be strong for Kausar and Mumsy.. Sann yace " Okay colleagues d'ina zasu maki ta'aziyya...
"Gyad'a masa kai tayi kafin tace " Bismillah su shigo.. Ta k'arashe tana goge ragowar hawayen ta....
************
"Su Annah da Zubaidah tuni an masu masauk'i a wani tangamemen section yayinda Jalal ke durk'ushe gefen Mai Martaba, Shattima na daga Side...
"Mai Martaba yaci gaba da fad'in" Insha Allah gobe ni zan koma Abdullah zai raka ni sai ya juyo, ya d'an ja fasali kafin yaci gaba da fad'in" Modibbo ka sani daga yanzu ba kai kad'ai bane, kanada Mu kanada gatan ka, babu mahaluk'in da zai kuma tauye maka wani hakkin ka, ko na bari ya muzguna maka, ba kai kad'ai ba, dukda iyalan ka baki d'aya, ina so ka sake dani kaman yanda Abdullah ya sake dani, Allah Ya baka lafiya ya kuma sa zakkan jiki ne....
"Jalal kai a k'asa yace " Na gode Ranka shi dad'e...
"Mai Martaba ya murmusa kafin yace " Ka kirani Abbah...
"Jalal ma d'an murmusawa yayi kafin ya furta ABBBAH "
"Farin ciki maras misaltuwa ya wanzu a zuciyar Mai Martaba, yau gashi ga gudan jinin sa, Allah Ya cika masa burin sa.. Yakai kallon sa ga yatsun k'afafun Jalal wanda babu abinda ya rabasu da nasa, yanda suke a kwance dogaye...
"Shattima kuwa sai murmusawa yake...
"Mai Martaba ya k'arada " Modibbo ka tabbata ciwon nan baya damun ka,..
"Jalal ya d'an murmusa kafin yace A'a Abbah da sauk'i sosai...
"Mai Martaba ya jinjina kai yana murmushi ya kasa d'aga idanun sa daga barin kallon Jalal, ji yake anya zai iya bari har sai nan da sati biyu su iso Fadah...
_Lallai wann rana akwai babban biki inji Sameena, kar ku bari a baku labari.._
"Basu suka bar gidan ba sai bayan sallan isha, a hakan ma da Abbah yaso su zauna a nan gidan sa gaba d'ayan su, Amma da yaji labarin Ansar sai ya amince masu su koma chan saidai zai wadata su da securities, Jalal dai duk ba son irin wad'an nan abubuwan yake ba, amma babu hali ya musa ma Abbah, Charisman sa ya wuce gaban wasa...
"Wani sabon tashin hankalin suka tarar sanda suka isa gida suka tarar babu Hadiza, Kuka Hamma da Kamal suke an rasa me rarrashin wani cikin su..
"Hankalin Zubaidah sosai ya tashi ganin Hamman ta da Kamal a wann yanayi wanda hakan ya tada hankalin Jalal sosai, ko kad'an baison ganin hankalin Zubaidah a tashe ...
🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
89
*©Sameena Aleeyou...✍🏾*
_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝_
*Dedicated To All Victims Of Rape...*
"Jalal Ansar ku zauna a gida kawai ku kula da gida ni zan fice neman ta, zan wuce police stations na sanar da 'yan sanda ko Allah zai sa a dace, don kunsan tunda ba'a kama Umar har yanzu ba komai ka iya faruwa...
"Shattima ya gyad'a kai kafin yace " Haka ne, I'll go with you..
"Jalal da Ansar suka rako su har parking space, suna addu'an Allah yasa a dace.
"Cikin gida kuwa Annah da Zubaidah sai faman lallashin Hamma da Kamal suke...
"Motar Shattima sukayi anfani da suka fice. Bayan fitar su Ansar ya juya ya nufi d'aki dun gaba d'aya baya jin dad'i. Jalal ya take masa baya yana d'an d'ingisawa sabida ciwon sa...
"K'ofar d'akin Ansar ya tura ya shiga da Sallama...
"Zaune ya hange sa yana kallon hoton Asmah a cikin wayar sa, d'aya hannun sa rik'e da hoton family dinsa...
"Da sallama Jalal Ya shiga gamida zama gefen Ansar , har lokacin Ansar bai d'ago kai ba ga dukkan alamu hawaye ke zuba a idanunsa...
"Jalal ya d'anyi still kafin ya dafa Ansar da hannun sa maras ciwo, kasa ce masa komai yayi sabida tausayin sa dake ratsa zuciyar sa....
"Da k'yar ya iya furta " Friend kayi hak'uri......
"Cikin muryar kuka Ansar yake fad'in" No matter how hard I tried bro, but I just couldnt help.... Duk sun tafi sun barni Jalal, meyasa mutanen da nake so the most suke tafiya su barni, why why Jalal.... Ya k'arashe yana mai kifa kansa da gwiwoyin sa.....
"Jalal ya kuma dafa sa kafin yace " Kalan taka k'addaran da jarabawan knn friend, Allah Ya bamu ikon cin jarabawar mu baki d'aya... " Ka sani Ansar, we are all here for you, together we would overcome this horrible tragedy, snn insha Allah Umar bazai tsere ma jami'an tsaro ba, duk iya gudun sa akwai ranar da Allah zai kama sa, and he'll pay for all the crimes he's committed...
"Ansar ya d'ago Face d'insa da jajayen idanun sa had'i da d'aura hab'ar sa saman hannayen sa da ya dunk'ule waje guda...
"Cikin wani irin siga yake fad'in" Ba zallan aikin Umar bane, I'm quite sure the Dasuki's are behind this, na sani wnn aikin Alh Kasim ne, shi kad'ai ne yake farautar rayuwa ta, That imbecile took everything away from Me.... I swear, na ranste I won't rest until he's locked up in jell.... Da shi da 'ya'yan sa duk sai sun tafi prison snn a lokacin zai d'and'ani zafin rashi.... Ya k'arashe siriryar hawaye na gangaro masa....
""Jalal ya d'an basa light hug cike da tausayawa
***********
"Da k'yar ya samu jinin ya tsagaita, sai ciccija leb'e yake, a haka ya hangi wata motar kaya ta yo jidon doya zata shigar k'asashen north east, wato Arewa maso gabashin k'asar nan, yankin da Jihar Gombe take...
"Da dabara ya samu ya d'ale cikin doyan nan ya kwanta abinsa ba tareda kowa ya gansa ba...
"Mai trailer kuwa yana zuwa yaja motar sa ya d'au hanya....
"Da k'yar Faisal ya samu ya fice daga warehouse d'in da ya b'oye, da cizge baki da dabaran gujewa jami'an tsaro ya samu ya iso Dasuki Holding....
"Daga gate d'in baya ya kira wayar Barr ya sanar dashi halin da yake ciki yana buk'atan treatments amma yasan muddin ya tafi asibiti police will arrest him...
"Barr yayi wata murmushi yana kallon Alh Kasim kafin ya katse wayar yace " Ta zo gidan sauk'i abin farautar mu ya kawo kansa gida, ..
"A tamanin Alh Kasim ya mik'e yana fad'in" He shouldn't be here, idon 'yan sanda na kanmu... Babu shiri suka nufo waje suna neman sa ba tare da sanin kowa ba..
"Faisal kuwa daga yanda yake rakub'e ya hange su, ya fito cikin sauri ya nufesu yana jan k'afar da k'yar...
"Yana isowa yanda suke Alh Kasim ya d'auke sa da wani wawan mari... Kafin yace " This is exactly the reward of a Jerk like you.... Daga haka ya zaro k'aramar bindiga a gefen business suit d'insa yayi pointing Faisal dashi...
"Faisal yana girgiza kai cikin rashin yarda da abinda yake gani yake fad'in" Boss no.... No Boss kar ka min haka, ni ne Faisal babban yaron ka...
"Alh Kasim ya tintsire da dariya kafin yace " And also babban idiot, A jerk like you bai kamata yaci gaba da rayuwa ba, rayuwar ka na nufin mutuwa na, kaga idan ka mutu banida sauran damuwa zanci gaba da b'uya a inuwar Umar, baka raye balle idan yabada statement d'insa ayi tunanin zak'ulo ka ni kuma ka zak'ulo ni, snn kayi failing aikin ka tunda har yau Barr Kumo na numfashi.. So I'm sorry but you've to go..... Daga haka ya d'auke kan Faisal da harsashi...
"Shida Barr suka fashe da wata dariya, Barr yana nunsa yana dariya yake fad'in baka da kyau, kayi amfani da mutum ka yar dashi... Alh Kasim ya kuma murmusawa kafin ya hura bakin bindigar yayi ido masu James kafin suka k'araso, ya Kalli James yace " Get rid of this mess... Daga haka suka nufi motocin su shida Barr....
***************
"Saida suka zaga station uku kafin suka ci karo da case d'in Hadiza, 'yan sanda suka fad'a masu yanda abin yake, tun daga zuwan ta banki da kuma dalilin kawota cell...
"Ba Hafiz kawai ba harta Shattima saida yayi mamaki, toh me zai had'ata da Dasuki's... Suka kasa nemo amsar gaba d'ayan su ...
"Babu yanda basuyi ba a basu belin hadiza 'yan sanda sun k'i yarda, suka ce case d'in ba nasu bane, Alh Kasim tuni yayi pressing charges...
"Hafiz yayi shiru yana nazari kafin Shattima yace " Ai sai mu k'arasa can gidan muji ko akwai wani abinda suka sani gameda batun....
********
"Gaba d'aya mamaki ne ya ishe su, Hadiza da Alh Kasim toh ma ina zataga check, kai kurum Zubaidah ta shiga girgizawa tana fad'in" Bazata daina hali ba, ni na tabbata wani abin take k'ullawa tareda su a bayan idanun mu reshe ya juye da mujiya.
"Jalal ya sauk'e ajiyan zuciya yana tunanin toh me matar nan zata k'ulla da Dasuki's..
"Annah kuwa girgiza kai kurum tayi kafin tace " Yanzu abinda ke gaban mu shine muyi k'ok'arin sanin me take k'ullawa dasu ko ta samu ta kub'uta daga hannun 'yan sanda..
"Hafiz ya fuzar da iska kafin yace " Nifa abin ma wllhi ya dame ni ko kad'an na kasa gano me zai had'ata da wad'an nan mutane...
"Zubaidah ta d'an girgiza kai kafin tace " Idan dai Yaya Hadiza ce kunga kad'an, halin ta ne bazata canza ba, ni na tabbata wani abin take k'ulla min tare dasu, ina tausayin Hamma na, da Kamal,.... Ta k'arashe tana goge hawayen idanun ta... "Jalal ya d'an yi amfani da hannun sa guda ya d'aura saman yatsun hannun ba tareda kowa ya lura ba yana mai mata alama da idanu kan she should be strong...
"Annah ta bud'e murya tace " Aiko ko kusa kar ayi Hamma yaji wann zancen.... Kaman daga sama suka jiyo muryar sa yana fad'in"
"Na sani nasan bazata daina tsanar k'anwata ba, na sani wani abin take k'ulla mata tareda wad'ancan azzaluman mutanen. Kuyiww Allah kar ku karb'o ta, ku dubi girman Allah ku k'yaleta a can ta koyi darasin ta... Ta sha fad'i min inada nakasu a hallita na.. Amma ko kad'an ban d'auki hakan nak'asu ba don ban zamto tamkar ko wani namiji ba..
" Allah Ya gani a iya zaman mu ban tab'a tauye mata komai na rayuwa ba, ta zalunci Zubaidah tun tasowar ta, Na sani Allah bazai barta haka kurum ba taita aikata zalunci a bayan k'asa ba.. "Ya k'araso gaban su sosai yake kuka duk ya jik'a hannun rigar sa sabida goge hawaye kafin yaci gaba da fad'in" Zubaidah kin ga yanda Allah ke canza Al'amran sa koh,.... Duk hassadar da take maki kullun ci gaba kike, ki yafe ni k'anwata babu yanda na iya ne tuntuni...... "Bai kai aya ba Zubaidah ta k'arasa ta rungume sa tana fad'in " Hammaaa.... Kuka ya kufce mata, sosai shima yake kuka..
"Gaba d'aya suka tausaya masu...
"Bayan wasu mintoci Shattima ya masu sallama kan cewa da safe jet d'insu zata d'aga zuwa Gombe..
"Har bakin parking space Jalal ya rako sa suna ci gaba da wata 'yar tattaunawar su..
"Shattima ya dubesa yana murmushi kafin yace " Prince you and I need to have a serious talk...
"Ya kamata a koya maka d'abi'un Babban gida da madafan iko, ..
"Jalal ya d'an Harare sa kafin ya Tab'e baki yace " Kaima kasan nazan iya wann abubuwan hidiman sarauta sarautan nan ba, it sucks, besides I'm only ordinary, I'm not used to all those kind of things...
"Shattima ya murmusa kafin yace " Then you must adopt... Kai fah dole ne ka zama committed don lokacin hutu na nima yazo, zan maka handling abubuwa da dama...
"Jalal bai saurare sa ba ya k'arasa ya bud'e masa marfin mota yace " Oya zo ka wuce you talk too much...
"Shattima ya murmusa ya shige kafin suka kuma yin sallama...
"Tsaye yayi yana kallon su daga bakin k'ofa itada Kamal tana kwance gefen sa tana karanta masa tarihin Annabi Yusuf yanda 'yan uwansa suka masa duka suka jefar dashi but at the end ya taimake su...
"Jalal sai murmushi yake yana hangosu itada ya ransa watarana hakan ne zata kasance da izinin Allah....
"D'an gyaran murya yayi had'i da sallama kafin ya shigo d'akin...
"Zubaidah ta mik'e tana rufe sharab'arta da suka bud'e.. Kamal kuwa da gudu ya tafi wajen Jalal yana fad'in " Uncle Jay kaima ka d'aura irin abinda John Cena ya d'aura a hannun sa ne...
"Jalal yayi murmushi ya durk'usa yana shafa kan yaron kafin yace " Yes Champ amma kasan reason d'ina na sakawa..
"Kamal ya girgiza kai alamun a'a..
"Jalal ya murmusa sai satan kallon Zubaidah yake kafin yace " Ciwo naji amma soon zan cire kaji na ci gaba da d'aga ka sama harma da Didi ..... Ya k'arashe yana kallon ta...
"Kamal tsalle yayi yana murna Jalal ya d'an dunk'ule hannu yana fad'in" Give me punch... Kamal ma yayi yanda Jalal yayi suka d'an buga hannayen su a tare lightly.... Gaba d'aya sukayi dariya kafin Kamal ya fice yana fad'in" Zaije duba Umman sa ko ta dawo.... Cike da tausayi suka bi yaron da kallo....
"Ya rage daga Zubaidah sai Jalal a cikin d'akin. Babu wanda yace ma kowa k'ala sai yunk'urin mik'ewa da take daga saman gadon..
"Kafin ta tashi saiji tayi ya mata runfa... Suka shiga kallon juna cikin ido.... Ga k'irjinta dake faman lugude...
"Gaba d'aya ya sauk'e nauyin sa saman k'irjinta kasancewar bai iya amfani da d'aya hannun sa...
"Yana jin yanda jikinta ya soma shaking.... " Cikin kunnenta yake rad'a mata, Why..? Are you still not ready... Ya k'arashe cikin kashe murya yanai mata wasu salo masu rikita ta...
"Kwiwkicewa tayi kafin ta soma fad'in" Ya Jay this is not the right time neither the right place , kaga Kamal zai iya shigowa any moment.. And.... And... Kuma Baka da lafia....
"Dad'a tura kansa cikin wuyar ta yayi yana rad'a mata " Bakiji addu'an da Abbah da Annah suka mana bane, suna son ganin grandchildren d'insu, basu san ke ce kika hana a samo grandchildren d'in ba...... "Zubaidah dai gaba d'aya ko sauraren sa bata yi, burin ta kawai ya tashi daga kanta.... Shi kuwa Jalal yayi nisa wata duniya....
"Har saida ya zame ya d'an fad'i kan hannun sa mai ciwo..
"D'an k'ara kad'an yayi sabida zogi da ya ji wajen na masa...
"Zubaidah ta tashi a firgice, hankali tashe take rik'e hannun sa tanai masa sannu idanunta duk sun firfito waje sabida tashin hankali..
"Da zafi ko, ka fama ciwon ka koh, oh my Allah barin karb'o first aid a wajen Annah ta K'arashe maganar tana k'ok'arin kintsa kanta zata sauk'a daga gadon ya rik'ota ya rungume cikin jikin sa had'i da lumshe dogayen idanun sa... " A hankali ya furta "I love you Zubaidah...
"Tayi lamo cikin jikin sa tana shak'an k'anshin body spray na AXE ba tareda ta iya furta koda kalma guda ba...
"Sun d'an jima a haka kafin suka jiyo muryar Annah daga downstairs tana kiran Jalal sun san bazai wuce shan maganin dare ba...
"K'ofa ya bud'e ya d'an dafa staircase kafin yace " I'm coming Annah..
"Annah tace ka kira Zubaidah ma itama tasha nata maganin...
"Jalal ya amsa da toh Annah, yana mai kallon Zubaidah yana d'aga mata gira had'i da murmushi irin itama lambar ta Ya fito d'in nan....
"Zaune suka same su gaba d'aya a parlor Ansar yana daga balcony yana amsa wayar inspector akan maganar Case d'in Hadiza...
"K'arasowa parlorn yayi ya same su bayan ya gama wayar kafin yace " That was inspector Bilal, ...Suka kad'a kai gaba d'aya suna kallon sa kafin yaci gaba da fad'in" Har yanzu no news on Umar, snn ita kuma Hadiza tak'i magana, tak'i fad'in dalilin da yasa checks d'in Alh Kasim ya isa hannun ta... Shi kuma Kasim Dasuki yayi blaming namu da cewa muna turota ta masa sata ne don ya sami kariyar arziki, ita kuma tak'i magana kwata kwata balle a k'aryata sa, that Jerk can do anything to frame us, don kawai yayi dividing attention d'inmu for the forthcoming trial, shari'ar da yasan dole ya tafi Jell da izinin Allah...
"Jalal ya d'anyi shiru yana nazari kafin yace " I've feelings that she's hiding something from us, what if she's working with them, the Dasukis..
"Annah ta katse sa da girgiza kai kafin tace " Don't jump to conclusions mu jira har lokacin da zata sadududa ta fad'i gaskiya tunda wajen ba dad'in zama ne dashi ba....
"Gaba d'aya sukayi na'am da batun Annah, k'ok'ari suke suga suna d'an kawar ma Hamma tunanin abin, shi kuwa Kamal ce masa sukayi maman sa ta tafi Dukku ne ba jimawa zatayi ba...
**********
"Washe gari Shattima yayi rakiya wa Mai Martaba zuwa k'asar ta Gwambawa d'iban fari...
"Ba tareda saninsu ba Mai Martaba yayi hiring private investigator wanda aikin sa kawai shine ya nemo likitan da yayi aiki ma Zubaidah lokacin da tsautsayin ya faru..
"Yayinda Shattima keta shirin business da Dasuki's wanda ko Mai Martaba ma baida masaniya akai, iyakaci dai yasan Shattima zai dawo Abuja sabida su Jalal da kuma wani business matter da zaiyi dealing....
**********
"Allah Ya taimake sa motar doyar K'asae Taraba ta nufa, ana wuce Gombe kad'an ya samu ya dire daga motar ya kutsa daji.....
"Da wuya da babu dad'i ya samu ya isa garin Dukku, kai tsaye gidan su abokin sa Balele ya nufa, Balele yayi mmakin ganin Umar cikin wann yanayi na tsananin ciwo, tun kan ya soma jero masa tambayoyi yace " Ka tabbata babu wanda zai ganni, ka taimaka min da d'akin ka da abinci har na gama jinya ta....
"Balele ya kallesa cike da tausayawa gamida girgiza kai, Allah sarki raguwar su a da can yake tunowa kafin Umar Ya dawo something else..
"Babu yanda Balele baiyi ba ya fad'a masa a ina yaji ciwo fir yak'i fad'i, k'arshe ma sai ce masa yayi idan bazai taimaka masa ba zaiyi tafiyar sa.. Balele bai kuma tuntub'ar sa ba sai mik'a masa kwanon tuwon sa da yayi...
"Koda Umar Ya bud'e kwanon ya jima yana kallon abun, rabon sa dashi har ya mance, babu yanda ya iya haka Ya nad'e hannu ya dinga gabzan loma....
******************
"Sauri sauri ta fito daga gidan bayan ta d'an tattaro duk wani savings d'inta, ta dnna security lock d'in motar Umar Ya bud'e, tana k'ok'arin zura key ma k'ofa taji bakin bindiga a k'eyar ta... Cike da firgici ta saki hand bag d'inta a k'asa, jikinta na rawa take karanto innalillahi...
"Danny ya daka mata tsawa da fad'in" Shut up, ina d'an iskan mijin naki, he think he can outsmart us ko, kuna planning barin gari ba tareda ya biya mu kud'in aikin mu ba....
"Zulaihat baki na rawa take fad'in " Wllhi I've no idea.... Ban.. Ban San yanda yake ba, pls don't hurt me I'm innocent....
"Danny ya fizgi car keys d'in dake hannun ta kafin yace " Mun tafi da wann, God save you ba don muna sauri ba da mun had'a ke.....
"Tana jin yanda suka fincike motar suka fice daga layin da gudun gaske...
"Durk'ushewa Zulaihat tayi a wajen had'i da toshe kunnuwan ta tana kuka, gaba d'aya 'yan kud'ad'en nata ma sun kwashe... Tana a haka Imam ya k'araso. Ganin yanyinta yasa sa cakka burki a sittin ya fito yayi kanta yana tambayar ta lafia, cikin kuka ta labarta masa abinda ya faru...
"Taci gaba da fad'in" Imam ta yaya zan had'u dashi ya bani takardan saki na, I can't take this anymore..... Ta k'arshe cikin kuka...
"Cike da tausayawa Imam ke kallon ta Ya shiga lallashin ta da tausasan kalamai... Saida yayi calming nata kafin suka nufi asibiti..
"To her surprise Imam shi yayi settling hospital bills d'in Innah gaba d'aya..
"Wani sabon girman Imam ta shiga gani a idanun ta, lallai kuwa masu iya magana sunyi gaskiya da suke cewa wani babban girma ne kurum ya tara babu hankali yayin da wani yaron ya ninninka wani babban a sani ya kamata, tabbas yau bata ma Imam kallon yaro a idanunta kaman yanda ta saba... Tausayin sa ya cika zuciyar ta, wani babban Al'amari take ji a tareda shi... Ashe kuwa tabbas ba kyaun halitta bane kurum yake sa a so mutum, tabbas kyaun hali na taka babban role a soyayyar d'an Adam....
"Innah ta kalle su su duka biyu bayan ta d'an farfad'o, cikin maganar ta D bai fita sosai ta ringa saka masu albarka, ta tuna yanda tak'i jinin Zulaihat daga farko, Allah sarki ashe duk munin halin mutum yana good side, snn shi mutum magani ne, sai ka haifi d'a baka moresa ba ka mori na wani..
"Haka Inna tayita saka masu albarka da muryar ta da bai fita sosai..... Idan ta tuno Baba Wuro kuwa sai kaga ta soma wani nishi tana shid'ewa...
************
"Kwanci tashi babu wuya wajen mai sama, Jalal ya sami sauk'i sosai har an warware bandage d'in.. Sosai Zubaidah ke kula dashi kai harma da Annah, Ansar ma ya d'an soma dawowa normal, haka Kausar da Mumsy ma...
"Hamma yaje yaga Hadiza yanda halittar ta Ya sauya lokaci guda. Idan ka ganta baka shaida ta ba, fuskar ta duk ya tuttuje ya dauje, matan cikin cell kullin sai sun zaune ta sun lakkad'a mata duka, musammman da sukaji tsugugun yawan kud'in da tayi niyyan sata.
"Babu yanda Hamma Habibu baiyi da Hadiza ta fad'a masa yaya akayi hakan ta kasance ba, fir tak'i, saidai kurum tace duk cikin sharrin su Alh Kasim ne, Alhali cikin zuciyar ta kuwa tsoron fad'in" gaskiya take, tasan zasu tsaneta harta Hamman... Daga bisani ya fad'a mata zasu tafi Gwambe kwanan nan, ya bata labarin duk yanda Al'amran Ubangiji suka kasance...
"Hadiza ta d'aura hannu aka ta kurma ihu tana fad'in" Na shiga uku na lalace ni Hadiza, yanzu Zubaidah ce ta zama matar d'an sarki, lallai hausawa sunyi gaskiya da suka ce hassada GA Mai rabo taki, zakaran da Allah Ya nufa da cara, ko ana muzuru ko ana shaho sai yayi, duk iya hassadan ta datayi ma Zubaidah ganin ta dak'ushe rayuwar ta tun tana yarinya hakan bata kasance ba....
"Tana komawa cikin cell taci gaba da yima oganniya matsa k'afafu, idan batayi daidai ba saidai taji sauk'an mari a kumatun ta, fuskar duk shatin yatsu Ya cika......
****************
*Dasuki Holding*
"Bakin Alh Kasim ya gaza rufuwa sabida farin ciki, finally yau President na Modibbo Cooperation zaizo su sami ganawar su, yau dai zai yarda k'wallan mangoro ya huta da k'uda, wato Hon Gali, gaba d'aya Company har wani sanitation na musamman yasa ayi..
"Daga can kuwa Shattima cewa yayi ya tabbata Companyn sa akwai wadaceccen tsaro sabida Mr President ba ko wani irin waje yake zuwa ba, kasancewar ya yarda da Dasuki Holding ne shiyasa zaizo..
"Alh Kasim baki har kunne, this is a huge honor, musamman da yanzu yasan Modibbo Cooperation MALLAKIN WAYE,.. An gyara hall anyi komai, su Salim da Labib sai kai komo suke, don suma gwara su tsaya ayi introducing nasu ma owner of the great company mai tashen suna da kud'i a yanzu. Tabbas sun san zasu iya samun contracts, tunda yanzu Dasuki Holding nafsy nafsy ake....
"Tafe suke cikin luxurious cars d'insu, in convoy, ko wani plate number na motocin sunan Company d'insu ne akai, ....
"Suna isowa Dasuki Holding kaga yanda ake hangame masu Gate, haba tuni su Barr Munir an rud'e an shiga kai komo ganin komai ya tafi normal.
"Motocin suka pappaka a haraban Companyn, Sai diri kawai suke AC na aikin sa...
"Escort guda ne ya fito Ya bud'e wa Shattima k'ofa suka nufi building d'in, zo kaga yanda ake basa tsaro, su Alh Kasim duk a zaton su Mr President ne da kansa....
"Kai tsaye akayi directing nasa to Hall d'in, su Alh Kasim sai rawan jiki ake, su Labib kuwa mamaki ne ya cikasu ganin President na babban company kamar Modibbo cooperation k'aramin yaro ne bazai wuce tsaran su, ba, su kuwa su Alh Kasim tunani suka soma yi k'ila d'ansa ne ke tsaya masa a hidimar kasuwamcin sa tunda shi bashi da wann lokacin...
"Bayan Sun gaggaisa har an bawa Shattima wajen zama sann ne yake fad'a masu, shi PA ne na Mr President, shigowa yayi ya tabbatar da tsaron wajen kafin Boss d'insa ya shigo, idan sun tabbatar da tsaron dake cikin company d'insu Boss d'insa zai sami damar shigowa...
"Su Alh Kasim baki har na rawa suke jaddada wa Shattima tsaron dake cikin company d'insu.
"Suna gani ya ciro Intercom suit pocket d'insa ya shiga kiran Orderly na Mr President ya sanar dashi everything cleaned zasu iya shigowa...
"Gaba d'aya baza baki da hanci sukayi suka k'ura ma k'ofa idanu suna jiran suga wann bawan Allah da zai shigo....
************
"Ansar ya ajiye documents d'in gaban Mumsy kafin yace " Mumsy komai ya zama intact, I've already talked with one of the best architectures company in Turkey, So probably they are working on the Design now...
"Mumsy ta kad'a kai tana jinjina masa, caraf suka jiyo muryar Kausar tana fad'in" May I interrupt....
"Ansar ya juyo ya dube ta yana murmushi kafin yace " Sure... Kausar ta k'araso tana murmushi.
"Mumsy dae kallon su kawai tayi tana murmushi.
"Kausar ta zauna gefen Mumsy kafin tace " Gina sabon Company yanzu ba namu bane, abinda ya kamata muyi shine mu saya Company..
"Mumsy ta juyo ta dubeta da alaman tambaya.
"Kausar ta gyad'a mata kai tana d'aga gira kafin tace " Mumsy nasan zamu samu.
"Murmushi kawai Ansar yayi don for sure ya gane plan d'in Kausar. Gyad'a kai shima yayi kafin yace " Yes Mumsy I go with her, sayan ginanne bazai kai wanda za'a gina ba, snn already zamu samu employees, saidai kawai mu k'aro k'wararrun Engrs da Architectures kawai tunda Construction Company ne...
"Mumsy ta d'ago tana duban su kafin tayi murmushi tace " Okay my children yanda kuka yi deciding...
"Kausar da Ansar suka kalli juna had'i da sakar ma juna murmushi....
*************
"Mamaki ya hanasu motsawa daga yanda suke gaba d'aya.
"Salim da Labib a tare suka mik'e suna kallon ikon Allah... No is this for real, kai kodai kamanni ne, no this can't be... It can't be him..
"Yayi tsananin kyau cikin business suite d'in sa, guards biyu ne a gefensa all in black sun toshe idanun su da shades...
"Shattima kuwa kallon sa kawai yake yana murmushi kafin ya juyo yana kallon su Alh Kasim wanda suka koma tamkar gumaka...
"Shattima ya soma introducing nasu ma Jalal yana gaisawa dasu, daga bisani aka basa seat dake a center ya zauna...
"Har lokacin su Alh Kasim basu dawo daidai ba..
"Su Salim kuwa sai shafe kai kurum suke suna kallon sa...
"Shattima ya d'an ware hannayen sa kafin yace " Gentle Men let's proceed.... Ya k'arashe yana mik'a wasu takardu gaban Jalal..
"Kallon petition d'in Jalal yayi kafin ya zaro pen a gefen suit d'insa kaman zai yi rubutu sai kuma ya fasa... " Barr sai fad'a masa abubuwan da sukayi ordering yake, kalan kayayyakin da zasu shigo dasu da kuma ingancin su.. Kana jin maganganun nasa kasan da k'yar yake yana yi yana kurb'an ruwa.
"Jalal ya kafesa da idanu kawai yana murmushi kafin yace " Hold on Attorney, you don't have to explain everything, I perfectly well know you... All of you...
"Alh Kasim ya shiga muzurai yana share zufan dake keto masa duk sanyin dake cikin wajen..
"Jalal ya mik'e ya isa gaban Alh Kasim kafin yace " Alh Kasim Dasuki kaji mamaki ne, well wann ba abin mamaki bane a wajen wanda yasan Allah, yasan zai iya juya al'amran sa duk lokacin da yaso...
"Your Company is going bankrupt, and you expecting me to negotiate with you.... Ya d'an murmusa kafin yaci gaba da fad'in" Saving your company is your top priority now, but too bad I don't deal with a scumbags like you...
"Koda yake ni ba mugu irin ka bane, zan maka donating huge amount of Money, nasan it will help... Ya k'arashe yana kallon guard d'insa guda d'aya... Da sauri ya ciro wani kud'i cikin envelope, ya mik'a ma Jalal..
"Jalal ya amsa yana murmushi kafin ya tako har gaban Alh Kasim, ya ajiye envelope d'in yace " Take a look of it Alh Kasim da fatan ba'a canza komai ba. D'auka ka duba ka tabbatar kud'inka na nan intact...
"Gaba d'aya suka bi envelope d'in da kallo, tabbas kud'ad'en da suka basa ne lokacin da suka tursasa masu auren juna shida Zubaidah, don asirin 'ya'yansu ya rufu....
"Wann rashin mutunci har ina, shine Jalal zai zo har companyn mahaifin sa ya ci masa mutunci.. Da sauri Salim Ya k'arasa zai kai cakuma ma Jalal yake fad'in" How dare you, you Trader....
"Guard d'aya ne ya finciko Salim da hannu guda zai kai masa duka, Jalal ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu kafin ya matso fuskar Salim yace " Salim Dasuki kai naka ba'a nan bane sai mun had'u a kotu.... Ya k'arashe yana murmushi kafin ya juyo ya dubesu gaba d'aya yace " Gentle Men if you excuse me, zan wuce coz I have alot of commitments to take care... Daga haka ya sakar masu murmushi yace " See you in Court.... Guards dinsa suka rufa masa baya Shattima kuwa sai mirmusawa yake abin ya masa dad'i bai zaci zai sami had'in kan Jalal haka ba, Jalal ya burgesa, don farko da yazo masa da batun k'i yayi daga baya kuma da kansa ya shirya komai....
"Gaba d'aya suka wuce guards d'insu suka rufa masu baya...
"Salim sai wani fincika yake yana fad'in" You scumbag you won't get away with this... Labib ya jawo sa yana karkad'a masa kai alamun a'a...
"Alh Kasim tuni ya rik'e k'irjinsa dake masa zafi Ya fara durk'usawa jikin table yana k'ak'ari... Kan kace me ya zube a k'asa, nan hankulan su Salim da Barr ya dawo Kansa...
"Salim yayi kansa a tamanin yana jijjiga sa yake fad'in" Daddy daddy... No no daddy... Call an ambulance.... Ya fad'i cikin tsananin d'aga murya yana rungume da Alh Kasim..
"Ko gizau Labib beyi ba, sai Barr da ya fice a tamanin
0 comments:
Post a Comment