*bismillahir rahamanir rahim*
_ina rokon ubangiji Allah dayabani ikon farawa lafiya da kammalawa lafiya yasa mu amfana da darussan dake tattare acikin littafin_
_sadaukarwa ga dukan masoyana_
Page 1
Gidan Majid acike yake da yan barka kowa se kallon babyn yake ana Allah yaraya amma me jego tayi shiru daga gefen gado take zaune dakaganta kaga me damuwa da alama ma kuka tayi ga dan karamin akwati agabanta kayan baby kala hudu nata kuma kala biyu,
Jitayi an riko hannunta datayi tagumin dashi,yayartace asama'u janta tayi har dakin yaranta kafin tafara magana,
Haba badi'a duk abinda zakiyi kibari se an watse kiyi abinki sekin nunawa mutane kina cikin wani hali,
Cikin muryar kuka tace Yaya dole inyi kuka abin yafara isata majid fa ba talaka bane amma kiga wulakancin dayai mana nibama kaina nake jiyewa ba dan jinjirinnan dabesan komai ba haka zetaso yabi layin yayyensa dasuke cikin ukubar rayuwa kamar ba gidan ubansu ba kinsani bantaba magana ba bantaba nuna damuwata akan duk abinda yakemin shida mahaifiyar saba da kuruciyata zasusa hawan jini yakamani,
Dukda dahaka badi'a hakurinnan shi zakici gaba dayi kodan yaranki suyi koyi dake kuma komai na rayuwa me wucewa ne kiga kala biyunnan dayai miki wallahi sedan wane da wane hakama na yaron wasu kalar designers ne dabantaba ganin suba kuma daga gani masu tsada ne kicigaba da rungumar kaddarar ki kinji,
Shikenan Yaya inaga bawata walima da zamuyi kawai dai ayi snaks dakayan rabo nasiyo bucket dozen takwas masu marfi anyi sticker da hoton yaron sukadai gareni kudin zobo ne danaketarawa,
Allah yasa musu albarka zamuyi snacks din nida Yaya muktar farida kuma tayi memo tace zatayi fried rice da kunun aya su Hajiya kuma zamu Tara wani Abu mubasu suhada gara,
Yaya na gode sosae Allah yabar zumunci kuma su Hajiya subar zancen gara ai wayanda za ayiwa ba kirki garesuba,
Kedai babu ruwanki susukace zasu iya,
Shikenan Allah yataimaka,
Dakyar tayi bacci ranar saboda masifar mijinta ga yaronta da azabar kuka tarasa inda zata sa kanta,
Ranar suna yaro yaci suna jabir dakyar ta riqe kukan datakeji har en biki suka watse wani yankwanannen rago ya yanka kamar ma jaririne befi wata huduba da iyayenta sunsan kalr wulakancin da ake mata dasun kashe auren batason mijinta yasaketa saboda tanason sa matsalarsa kawai rashin son haihuwa ne,
Washe gari tagama gyaran gidan yaran su uku sunyi makaranta biyune kusa da ita se jaririnta jabir biyun basu isa akaisu makaranta ba kuma tasan babansu baze kaisuba shiyasa takeso kafin su isa zuwa makarantar ta tanadi wani Abu dantasakasu makaranta medan kudi kodan rayuwarsu ta inganta,
Sallamr mahaifiyarsa taji Hajiya rabi azahiri ta tsorata sanin duk zuwan Hajiya rabi to da cin mutunci take zuwa,
Gaisheta tayi ta amsa ciki ciki mama kizauna mana,
Bazama nazo yiba inabanda nuna isa dankun rainani yaushe zaku aikamin danama kamar abinda na roka toga tsiyarku nan nakawo muku banaso wannan abin zanraba nida en uwana,
Hajiya kiyi hakuri ragon ne bayida girma,
Ohh sannu munafuka wato duk abinda Dana yake miki bakya gani harkin raina girman ragon to wallahi bari yadawo kicenasa ina nemansa senaji idan shine yake daure miki gindi kina wannan iskancin kuma ga namanan idan ba akarominba kuriqe tsiyarku,
Dama badi'a bame magana ceba hakan yasata shiga kitchen ta kawso sauran naman tahada mata tamiqa mata tana bata hakuri,
Babu godiya ta karbe sema kara raina naman datayi tatafi tana fadin bafi'a duk ta kwashe tabawa en uwanta dan munafurci,
Komawa tayi tazauna tamakasa yin kuka kallon jabir take dayketa tsotson mamanta amma bakomai aciki sbd bakinciki tunjiya takasa cin komai ga yaron bashida madara tana tsoron taba abincin data ajiyewa yaranta suzo suci basu koshiba dan tasan ubansu baze bada kudin cefane dasu ba,
Ahaka jabir yagaji yayi bacci sauran yaranma duk sunyi bacci shnifidesu tayi tafito daniyyar wanke wanke Sega majid yashigo,
Binta yayi damugun kallo ko amsa sannu dazuwan datake masa beyiba,
Ledar data gani ahannunsa taje zata karba Dakatar Da ita yayi yabude ledar yanuna mata,
Kinganusu nan kayan miya ne kuma wallahi nakwana biyu ne daga seke se abdulrahim karki sake kibawa wayannan Yayan naki jeka inbiki haihuwar rurrutsa,
Muryarta na rawa tace...,
Allah kabamu hakuri da juriya azaman duniya
Ameen.
[7/5, 8:05 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari na)*
_labari da rubutawa_ _sophieG_
_A very heart touching story 2017_
*bismillahir rahamanir rahim*
_ina rokon ubangiji Allah dayabani ikon farawa lafiya da kammalawa lafiya yasa mu amfana da darussan dake tattare acikin littafin_
_sadaukarwa ga dukan masoyana_
Page 1
Gidan Majid acike yake da yan barka kowa se kallon babyn yake ana Allah yaraya amma me jego tayi shiru daga gefen gado take zaune dakaganta kaga me damuwa da alama ma kuka tayi ga dan karamin akwati agabanta kayan baby kala hudu nata kuma kala biyu,
Jitayi an riko hannunta datayi tagumin dashi,yayartace asama'u janta tayi har dakin yaranta kafin tafara magana,
Haba badi'a duk abinda zakiyi kibari se an watse kiyi abinki sekin nunawa mutane kina cikin wani hali,
Cikin muryar kuka tace Yaya dole inyi kuka abin yafara isata majid fa ba talaka bane amma kiga wulakancin dayai mana nibama kaina nake jiyewa ba dan jinjirinnan dabesan komai ba haka zetaso yabi layin yayyensa dasuke cikin ukubar rayuwa kamar ba gidan ubansu ba kinsani bantaba magana ba bantaba nuna damuwata akan duk abinda yakemin shida mahaifiyar saba da kuruciyata zasusa hawan jini yakamani,
Dukda dahaka badi'a hakurinnan shi zakici gaba dayi kodan yaranki suyi koyi dake kuma komai na rayuwa me wucewa ne kiga kala biyunnan dayai miki wallahi sedan wane da wane hakama na yaron wasu kalar designers ne dabantaba ganin suba kuma daga gani masu tsada ne kicigaba da rungumar kaddarar ki kinji,
Shikenan Yaya inaga bawata walima da zamuyi kawai dai ayi snaks dakayan rabo nasiyo bucket dozen takwas masu marfi anyi sticker da hoton yaron sukadai gareni kudin zobo ne danaketarawa,
Allah yasa musu albarka zamuyi snacks din nida Yaya muktar farida kuma tayi memo tace zatayi fried rice da kunun aya su Hajiya kuma zamu Tara wani Abu mubasu suhada gara,
Yaya na gode sosae Allah yabar zumunci kuma su Hajiya subar zancen gara ai wayanda za ayiwa ba kirki garesuba,
Kedai babu ruwanki susukace zasu iya,
Shikenan Allah yataimaka,
Dakyar tayi bacci ranar saboda masifar mijinta ga yaronta da azabar kuka tarasa inda zata sa kanta,
Ranar suna yaro yaci suna jabir dakyar ta riqe kukan datakeji har en biki suka watse wani yankwanannen rago ya yanka kamar ma jaririne befi wata huduba da iyayenta sunsan kalr wulakancin da ake mata dasun kashe auren batason mijinta yasaketa saboda tanason sa matsalarsa kawai rashin son haihuwa ne,
Washe gari tagama gyaran gidan yaran su uku sunyi makaranta biyune kusa da ita se jaririnta jabir biyun basu isa akaisu makaranta ba kuma tasan babansu baze kaisuba shiyasa takeso kafin su isa zuwa makarantar ta tanadi wani Abu dantasakasu makaranta medan kudi kodan rayuwarsu ta inganta,
Sallamr mahaifiyarsa taji Hajiya rabi azahiri ta tsorata sanin duk zuwan Hajiya rabi to da cin mutunci take zuwa,
Gaisheta tayi ta amsa ciki ciki mama kizauna mana,
Bazama nazo yiba inabanda nuna isa dankun rainani yaushe zaku aikamin danama kamar abinda na roka toga tsiyarku nan nakawo muku banaso wannan abin zanraba nida en uwana,
Hajiya kiyi hakuri ragon ne bayida girma,
Ohh sannu munafuka wato duk abinda Dana yake miki bakya gani harkin raina girman ragon to wallahi bari yadawo kicenasa ina nemansa senaji idan shine yake daure miki gindi kina wannan iskancin kuma ga namanan idan ba akarominba kuriqe tsiyarku,
Dama badi'a bame magana ceba hakan yasata shiga kitchen ta kawso sauran naman tahada mata tamiqa mata tana bata hakuri,
Babu godiya ta karbe sema kara raina naman datayi tatafi tana fadin bafi'a duk ta kwashe tabawa en uwanta dan munafurci,
Komawa tayi tazauna tamakasa yin kuka kallon jabir take dayketa tsotson mamanta amma bakomai aciki sbd bakinciki tunjiya takasa cin komai ga yaron bashida madara tana tsoron taba abincin data ajiyewa yaranta suzo suci basu koshiba dan tasan ubansu baze bada kudin cefane dasu ba,
Ahaka jabir yagaji yayi bacci sauran yaranma duk sunyi bacci shnifidesu tayi tafito daniyyar wanke wanke Sega majid yashigo,
Binta yayi damugun kallo ko amsa sannu dazuwan datake masa beyiba,
Ledar data gani ahannunsa taje zata karba Dakatar Da ita yayi yabude ledar yanuna mata,
Kinganusu nan kayan miya ne kuma wallahi nakwana biyu ne daga seke se abdulrahim karki sake kibawa wayannan Yayan naki jeka inbiki haihuwar rurrutsa,
Muryarta na rawa tace...,
Allah kabamu hakuri da juriya azaman duniya
Ameen.
Feeyah😍
[7/5, 8:05 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari na)*
*N!$@ online writers*
_written by sophieG_
_A very heart touching story 2017_
_wannan shafin nakune ummeejay,ummeekhaleel,zeenaseer,husaina ubandiya,Sha'awa ibrahim,jidda(dota),shukrah,adama maifata,bilkisu,meera Dan fodio,ddss. Nagode sosae da addu'arku agareni Allah yabar zumunci ameen_
Page 2
Yanzu don Allah majid haka zamu cigaba da rayuwa Yayan cikinka nefa amma ace abincin dazasuci yana musu wuya agidan ubansu,
Magana take kamar zatayi kuka,
To naji malama bazan basu abinciba se randa naga dama kintashi kin haifo yaya jeka inbika saboda kawai ki karyemin tattalin arziki don kinga Allah yasamin hannu to babu ruwana dacinsuko shansu ai seda nanuna miki banida muradin ki haife cikin dukansu bayan abdurrahim kika ki Dan haka dole kece zakiyi dawainiya dasu babu ruwana,
Bata cika sonyin maganaba balle wannan maganar Mara dadi datakejinta
Daga bakin mutumin daba jahiliba Dan boko me tarin dukiya amma se bala'i da makon masifa,
Kije ki hadamin ruwan wanka munada meeting yau akasuwa,
Batace dashi komaiba tabi hanyar dakinsa bayan tahada mai ruwan wankan tazauna zaman jiranshi yafito,
Kallonta yayi bayan yafito yace,
Lafiya dai badee'a?
Don Allah jabir zaka siyowa madara naringa hada mishi da ita,
Saboda? Yatambaye ta yana shafamai a hannunsa,
Shiru tayi tana nazari kafin tace,
Saboda ni banasamun isasshen abincin dazanci har ruwan nonon sukawo su isheshi wuni daya,
Bari kiji babu ruwna da jabir nabaki abinci kici banason tsegumi don kisani tunyanxu yashiga layin su abduljabbar,
Takasa cewa komai Dan takaici idan tayarda taci abincin saboda jabir to sukuma su abduljabbar mezasu CI dama abincinta take basu itakuma idan anyi cinikin zobo setasan yadda zatayi taci takara musu,
Dakinta tashi ga tazauna bakin gado tana kallon yayanta tana kuka,
Kuyi hakuri *y'ay'ana*nasani wantarana zanyi *alfahari*daku zancigaba da Neman nakaina don na inganta rayuwarku saboda babanku bashida niyyar sakamin hannu a lamarinku,
Dahaka rayuwarsu taci gaba yau dadi gobe wuya ga yaran duk halinta suka gado basu cika magana ba haka suketa Jan hanji ga ramarsu tarashin wadata tafara bayyana badi'a ma duk tayi zuru zuru damuwa tayi mata yawa takasa sanar da mahaifanta ko babban yayansu besan Halin datake cikiba Yaya asama'u kadai tasani itama kusan halin su daya da badee'a zurfin ciki yayi musu yawa,
Suna zaune jugum ta kammala abincin rana ta hada da nata Dana abdurrahim kallon abincin take abdurrahim,abduljabbar,abdulkadir,abdul'aziz, abincin baze ishesu ba ga jabir yafara cin abinci gashi duk yarame kwanaki yai rashin lafiya amma ko kudin adaidaita sahun zuwa asibiti bebasu ba,
Tazaunar dasu duka harsun faraci Sega majid yashigo,
Sallallamin dayakene yasata dago tana kallonsa,
Yanzu badee'a cin amanata kike kisatar min abinci kiba yayanki sannan kuma ki hadasu da dana salon kar yakoshi?
Nikam bansatar maka abinciba nawa dana abdurrahim na hada musu,
Ina ruwana dayaranki kibasu naki daban mana suci karki sake kikara hadamin su da yarona inaso yaci yakoshi maza zoki raba musu,
Majid don Allah karmu raba kan yayanmu,
Nace kixo kiraba musu abincinan tun raina be baci ba,
Kamar zatayi kuka haka taraba musu abincin nasu abduljabbar befi suyi loma shida shida ba yakare,
Ta dago tana kallonsa da fuska a maraice hannunta kawai yaja yana fadin,
Abdurrahim kaci abinci sosae kaji,
Yaran suka bisu da kallo har suka bacema ganinsu,
Abdurrahim yakoma kusada en uwansa sunaci atare har aka cinye nasu yadauko nasa sukaci atare har jabir ma dayake rarrafe,
Bangaren su badi'a kuwa a Palo ya tsaya yacire rigarsa dagashi se singlet da dogon wandon shadda akan kafafuwansa yazaunar da ita yada kallon bakaken lips d'inta dasuka sha lipstick sunata kyalli ga sky blue din jallabiya takama jikinta tayi mata kyau,
Kinyi kyau badee'a,
Batama jinshi hankalinta yatafi tunanin yayanta ko sun koshi,
Dan kwalin kanta taji yazame yana kara rungumeta ajikinsa,
Watoshi bashida damuwa ko ga yayansu can yunwa zata halaka su batasan lokacin da kuka ya kwace mata ba kamar wata jaririya,
Majid kuwa dama ya kwaso jarabarsa bema saurari kukan datakeba seda ya sauketa,
Taso tahanashi sekuma tayi tunani hukuncinta agurin Allah gakuma tsoron karta kwashi wani cikin dan jiya tafara sallah kuma tasan yanayinta,
Dakinta takoma tasamu yaran a apalo dikansu sunyi bacci gyara musu kwanciyarsu tayi tashi ga uwar dakin,
Bayan kwana biyu tashirya zuwa gidansu tagaida su Hajiya ta kwana biyu batajeba,
Yace ta shirya yakaita taji dadi sosae,
Ke dawayannann yaran orututu da otonyo zaki,
Eh ta amsa tana kallonsa,
Bazasu shigarmin motaba dama da abdurrahim kadai zaki se wannan jabir din dasena dan matse nakaiki,
Dasu duka zani danbansan wazan barwa suba kasan kuma sunyi kankanta abarsu sukadai agida kabarshi kawai zan hau napep,
Kallonta yake cikeda masifa,
Ke kinma fasa tafiyar senagani inkece kike iko dakanki nizaki gaywa wannan banzar maga.......,
Bata jira yakarasa maganarba tana yaranta suka shiga gida,
Shirunta yana masa ciwo danhaka yabita yana balbaleta da fada amma har yakaraci surutunsa batacemasa uffan ba cikida takaicin abinda taimasa yabar gidan.
*kwanaki a wani group wata takawo topic akan cikin biyunnan wanne ne zaka zaba*
*1 uwar miji bata sonkine*
*2 mijin ki baya sonkine*
*kowa yafadi albarkacin bakinsa but ni awurina banason kodaya acikin biyunnan sbd in uwar miji batasonki to maganar jin dadi bata tasoba karshema sekun rabu hakama idan mijin bayasonki karma kikawo maganar kwanciyar hankali a gidan sedai idan Allah ne yayi ikonsa*
*Allah ya dubemu da idon rahma*ameen
[7/5, 8:05 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari na)*
_by sophieG_
*N!$@ onlin€ writ€rs*
_A very heart touching story 2017_
_this page goes to you Sha'awa Ibrahim_
Page 3
Abdulmajid kasim asalinsu en garin sokoto ne akaramar hukumar kware duka en uwansu suna kware mahaifinsa ne kadai yke zama a sokoto shikadaine gun mahaifiyarsa shiyasa yake sheke ayarsa yadda yakeso,
Badi'a kintabbatar ba matsala banaso adawo ana dana sanin wannan auren naku,
Babanta ne yasata agaba yana tambayarta don yasan Halin uwar majid batada kirki kokadan,
Abba babu matsala insha Allah,
Banaso kibari sonda kike masa yasa kikasa ganin laifinsa kije kikara tunani nabaki kwana biyu,
Tashi tayi cike da kunya tashi ga daki,
Bayan kwana biyu abba yasake tambayarta ta shaidamasa da babu matsala,
Tana tsananin son sa hakane shima agurinsa yahanata sauraren kowane saurayi inko yaga abu basetace tanaso ba komai aka kawo musu a kasuwa indai namata ne dazasu siyar seya kawo mata amma abbansu betaba bari ta karba ba sedai yakoma dasu ya ajiye,
Yayyenta zama sukayi akayi maganar auren muktar yace abarta tunda tana sonsa shima yanasonta,
Bayan kwana biyu iyayen majid suka turo an saka ranar bikin wata me shigowa,
Lokacin bikin yaxo akayishi cikin kwanciyar hankali gidan amarya yayi kyau komai daidai irin na mutane masu wadata,
Bayan wata biyu da auren badee'a tafara laulayi sunje asibiti aka tabbatar musu datana dauke da ciki wata biyu sunyi murna sosae kamar su fadawa duniya,
Gata da kulawa ba amagana har mahaifiyarsa ttanaji da cikin tun daga gidanta take zuwa takaimata kayan kwadayi,
Shikansa majid idan yafita aiki ko kasuwa seyazo saubiyar kafin lokacin tashinsu office ko kuma kasuwa yayi,
Asibitin da yayarta take aiki acan take zuwa awo,
Tayi masa zancen komawa makaranta yanuna mata bashida ra'ayin komawarta makaranta be rage tada komaiba kuma yafiso kullum yana tareda ita,
Ba ayi yarjejeniyar cewa zebarta tayi karatuba kafin auren dan haka besamu matsala daga gunta ko iyayenta ba se aka share batun,
Cikinta yashiga watan haihuwa zuwa lokacin komai ashirye yake kayan babyn dasuka Tara sukansu basusan adadinsu ba siya kawai suke suna ajiyewa,
Ranar da badee'a ta tashi da naquda da safe a gigice sukayi asibiti hankalin majid duk atashe yakasa kiran kowa yafada suna asibiti,
Ko awa daya ba ayi dazuwan suba Allah yasauki badi'a lafiya tasamu da namiji murna gurin abdulmajid ba amagana anan yakira mamansa yafada mata kafin asallamesu asibiti tacika da dangi,
Ranar suna kuwa anyi barin kudi abinci a ko'ina yaro yaci suna abdurrahim sedai ace Allah yaraya abdurrahim,
Mahaifiyarsa ta umarcesa daya dawo gidanta har badi'a tayi arba'in tadawo dan babu kyau mutun yana kwana shikadai agida,
Bemusa mata ba yayi yadda tace sedai kwana kadai ke kaishi gidan kullum yana gurin badi'a da babynsu,
Ganin haka abbansu yace ranar data cika kwana arba'in takoma gidanta bayason wannan zaryan da mijinta keyi masa agida,
Ana gobe zata koma majid yafito da safe yashiga dakin mamansa,
Umma nafita zamuje asibiti da badi'a,
Batada lafiyane tatambayesa,
A a za adorata kan maganin family planning ne,
Family me?ta tambayesa tana miqewa tsaye,
Planning umma,
Bakuda hankali wallahi kunyi kadan kaikadai na Haifa inaso naga gida yacika da yara babu wani planning banyarda daga haihuwar da daya zaku wani ce planning kusake tunani bada yawun bakinaba,
Umma ai ba wani abubane kuma bawai munce abdulrahim kadai ne zamu Haifa ba,
Banason iskanci kanajina kodan kaga duk abinda kake ina daure ma gindi?tobanda wannan zancen sena Daura zanina naje har gidansu badi'a nayi rashin mutunci,
A a umma base anyi hakaba kiyi hakuri,
Dayafi dai tafada tana zama tacigaba da mita,
Fita yayi yana tunanin yadda zeyi da wannan zencen.
*duk kalar jin dadin dakake arayuwar duniya dazarar katuna da mutuwa zakaji jindadin yaragu amma masu imani ne kadai ke tuna mutuwa maras a imani kuwa harkarsu tqduniya kadai sukasa Agaba wannan babban kuskurene duk yadda kayi niyyar aikata mummunan aiki katunada mutuwa hakan zesa katuna haduwarka da ubangijinka mezakacemasa ranar tonon asiri? Zakaji tsoron wannan ranar dataimakon Allah sekaga kakasa aikata wannan aikin Allah kasa mudace ameen*
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari na)*
_by SophieG_
*N!$@ onlin€ writ€rs*
_A very heart touching story 2017_
_this page goes to you Anty badee social_
Page 5
Baby meyake damun badee'a ne naga ta rame kuma fuskarta da alamun akwai damuwa kuma gasu Abdul kamar yayan riqo suma duk sun rame,
Mijin yaya asma'u ne ke tambayar ta Dan lokacin daze fita ya hadu da badee'a zata shigo anan yalura da ramewarta yadda idonta sukayi zuruzuru,
Shiru tayi nadan lokaci tana tunanin tafada masa koze taimakawa kanwar ta ta,
Kiran sunanta yayi kafintadawo daga duniyar tunanin data shiga,
Mahmoud badee'a nacikin damuwa uwar miji da mijin sunsata atsakiya suna gasa mata gyada a tafin hannu,haihuwa take babu tsari uwar mijin tayi rantsuwa bazatayi family planning ba shikuma mijin bayason wannan haihuwar datake babu kai babu gindi duk cikin yayannan babu shekara biyu a tsakaninsu yanzu halin da ake ciki tundaga kan abduljabbar har jabir itake cida su yace wallahi tunda take haifarsu kamar awaki baze dauki nauyin komai nasuba danshi baze yadda tacinye masa tattalin arziki itada yayanta ba,
Shiru yayi yana jinjina jahilci dakauyanci irin Na abdulmajid,
Baby yanxu su Hajiya basu dauki wani mataki ba aka zuba masa ido yana wahalar da yar mutane?
A'a itace bataso afada musu basusan halindatake ciki ba Dan tunfarko basuso aurenba saboda sunsan uwarsa batada kirki batasan girman kowa ba,ganin badee'a tadage shitakeso yasa suka barta ta aureshi dakunya kuma yanxo daje kai kararsa gurinsu, ga yahanata komawa makaranta kuma babu wata sana'a mekyau dazata kawo kudi zobo takeyi lokacin sanyi ba asiya sosai sbd babu k'ishi tausayinta nake konamiji ya yakara da ciyadda mutun uku bare mace, kuma har yanzu tace tanason abinta,
Dariya yayi yace so hana ganin laifi ai
Uhmm narasa abinda take tsinta agurinsa wallahi,
Allah ya sauwaqe gobe sekishirya dasafe kafin kitafi gurin aiki zanbaki sako ki kaimata,
Ameen tace murna fall aranta datasan mijinta ze taimaka wa yar uwarta batareda wani tunaniba aida tuni tasanar dashi, godiya tayi masa dukda batasan mezaiyiwa badee'ar ba,
Washe gari motarsa yabata yace sakon yana ciki se kuma kudi yabata kuma tacigaba da hakuri insha Allah zata ga ribar yinsa,
A palonta tasamesu abdulrahim kadai yaje makaranta,
Bayan sungaisa Yaya tace
Yanaga yaran basuje makaranta ba?
Babu abincin dazan basu sutafi dashi kuma lesson suke se 3:00 suke tashi kinga ko bazan turasu haka ba da idan banida abinda zan basu nakan Debi nashi idan nasamu nabiya to yan zuma koshinkafa yadaina kawo buhu awo yake duk bayan kwana biyu,
Hmmm shikenan Mahmoud ne yabani sako nakawo miki mijinki dai bayanan ko?
Bayanan ta amsa tana kallonta,
Hanyar fita tadosa tana cewa kizo mu kwaso kayan,
Abu biyu take ji axuciyarta murna kuma da takaici yadda mijin yayarta ytaimaketa haka amma mijinta abin kaunarta yakasa taimakonta,
Kayan abinci ne masu Dan yawa balaifi sekuma kudi dabansan konawa bane,
Yaya asma'u tace sekuma nawa taimakon duk abinda ake so amakarantarsu kifada min insha Allah zan taimaka kafin muga yadda za ayi achanja musu makaranta,
Cikeda murna tayi godiya kuma zatazo har gida tayiwa mahmoud godiya,
Tundaga wannan lokacin mijin asma'u yake taimakonta dukda watarana takan tashi cikin rashi mijinta kuwa besan meke gudana ba yana ganinta dai tarage damuwa da al'amuransa amma acikin zuciyarta itakadai tasan damuwar datakeda game da abdulmajid,
Kwana biyunnan bata jin kanta daidai fargaba take Allah yasa ba abinda take zargi bane,jiya batayi bacci ba zazzabi takeji ajikinta yadda gabanta ke faduwa yahanata bacci,
Yau kusan sati daya kenan tana fama duk abinda zataci baya zama tayanke shawarar kiran Yaya asama'u,
Kinga bari idan nataso daga aiki Zanbiyo da abin awon ciki mugani kibar kuka,
Yaya asma'u tace bayan tagama sauraren badi'a data kirata awaya,
Karfe uku agidan tayimata,
Karbi badee shiga kiyo fitsari anan inkin gama ki kirani nazo,
Wani kalar dokawa da zuciyarta tayi lokacin da Asmau tafada mata ciki ne da ita,
Yaya muxubar dashi wallahi bazan iya ba wahalar tayimin yawa,
Kice kintuba badeea wasu sunacan suna Neman haihuwar kamar zasuyi hauka amma basu samuba kigodewa Allah tunda rabon wannan yazo zaki haifeshi sedai idan kin haihu zamu dauki mataki kuma kifadawa mijinki kinadauke da cikinsa karki boye masa komai,
Shikenan Yaya nagode Allah yabar zumunci tafada hawaye nabin kuncinta,
Bayan tafiyar asma'u tazauna tayi koka har bata gajiba ba abinda ke daga mata hankali irin....
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
*Abu nabiyu dayake janyowa mutun bakin jini shine wulakanci sekaga wani ba abinda yake burge shi irin yawulakanta dan adam,ko dabba kake wulakantawa zata nisance ka balle kuma mutun me hankali,idan kana wulakantarwa sekowa yaguje ka bawanda yakeson kusantarka*.
*kutuna ita zuciya tanason Wanda yake kyautata mata kuma tanakin Wanda yake musguna mata saboda haka mukiyaye*
Page 7
11:36pm abinci take bawa jabir dukda yadda yake nuna baya so amma dole zatabashi yaci koda ze Harar ne magani takeso tabashi inyai bacci se taje gun jarababben ubansa,
Yadanci kadan paracetamol tasake bashi ko zazzabin ze sauka tasamu yayi bacci,
Babu jimawa kuwa bacci ya dauke shi,doguwar rigar bacci tasaka ta zauna yiwa yaranta addua, muryarsa taji yana cewa,
Kinyi rantsuwa senayi miki kira nabiyu zakizo ko?,
Batace dashi kokaiba seda tagama yimusu addua,hannunsa takama sukabar dakin dan bataso yadaga murya yatashi jabir,
Shikadai yai kidansa kuma shikadai yai rawarsa,
Kallonta yayi ta lumshe idonta tana hutawa,
Wannan wani sabon salone badee?
Tagano sarai meyake nufi amma bata tankasa ba sema shigewa bayi tayi tabarshi dabaki asake,
Rigarta tamayar jikinta takwanta dan jiri ma takeji,
Shima wankan yayo yahawo gadon cike da masifa azuciyarta tace bari kayi masiifa me dalili,
Yabude bakinsa zeyi magana tace,
Inada ciki!
Ci me?
Yatambaya yana miqewa zaune,
Ciki bansan wata nawa bane amma zekai wata uku,
Waike bakida hankali ne bakya gajiya da haihuwa ne?
Dani da kai se aga Mara hankali,
Yasan gaskiya tafada dan haka yayi kasa da murya,
Wai badee babu yadda zakiyi ki abinnan ko dole seda family planning ake wannan din?
Zaune ta tashi sbd abin yamatukar bata mamaki,
Kadaina jarabar nan shine family planning bayan na asibiti kabari se sanda kaji kanason asake haifama da ko ya nabiyu Wanda zakaciyar kakaisu makaranta dakanka kadauko su sukuma sauran shegu ne,
Fuska yahade,
Badee ni kike gaywa magana?,
Banason damuwa Abdul kasan condition dina yanzu ina bukatar Hutu,
Kwata kwata yakasa bacci duk laifin hajiyata ne wallahi,
Washe gari har yaran suka tafi makaranta jabir yana bacci se karfe goma yatashi da zazzabi ga kansa ya dan kumbura,hankalinta yatashi Sosae addu'a take Allah yabashi lafiya, (nace ameen)
Wasa wasa karamin Abu ya zama babba dan ciwon jabir se gaba gaba yake kansa yayi wani irin kumburi mahaifiyarsa duk ta gigice,
Abdul jabir fa balafiya kalli yadda kansa ya kumbura,
Uhm nagani Allah yabashi lafiya,yana gama fadar haka yajuya ze fita dasauri takarasa kusa dashi tana rokonsa yakaisu asibiti dafarko soyai yashare ta sbd yau yanada abubuwan dazeyi kuma kudi zasu shigo amma ganin ta zauna kasa tana kuka yasa yace tazo sutafi,
Dole aka kwantar dasu amma bill kodaya babu Wanda abdulmajid yabiya acewarsa yarontane intaga dama tabiya,
Dan Allah abdulmajid kayi hakuri kaceci rayuwar danka kaji ance ma se anmasa aiki,
Karki kara cewa dana danki dai tunfarko seda nafada miki kiyarda azubar dashi kika ki kuma seda nafada miki duk dan dakika Haifa bayan abdulrahim toki shiryawa dawaiyarsa,
Dagowa tayi tana kallonsa kafin tamaida dubanta ga mutanen gurin kusan dukansu suke kallo cigaba yayi da surutansa cikin daga murya,
Yaya gasunan jeka inbika ko shekara takwas ba ayi da aurenmu ba amma Yaya biyar gana shida nan kan hanya mace babu control kana tabata se ciki gida Yakoma kamar makarantar naziri (tik'ek'en jahili),
Juyawa kawai tayi tanufi dakin da aka kwantar da jabir kukanma yaki zuwa seyau take danasanin auren abdul bata taba tunanin jahilcinsa yakai hakaba,
A gida kuwa yaran sundawo se kuka suke basuga mamansu ba abdul nacikin daki yafito yadaka musu tsawa atake suka hadiye kukan,
Anacikin haka Sega mahaifiyarsa tazo unguwar barka shine tabiyo gidan,
Bataga uwar yaran ba ta tambaye sa yafada mata suna asibiti tattara kan yaran tayi tace dasu zata tafi har kaninsu yaji sauki sudawo gida,
Har bayan kwana biyu gidan su ba asaniba seda Yaya asam'u takirata take fada mata suna asibiti da jabir,
Yaya tayi mata fada sosae dan bata fada ba har ankwana biyu,
Alokacin kuwa badee zaune kawai take tana jira taga abinda Allah zeyi.
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
_this page goes to you baby nurse(fatima zarah)_ ILYSM
*Abu na uku dayake janyowa mutun bakin jini shine munafurci*
*munafiki betaba farin jini ba, munafiki annobane idan ana zaune dashi babu abinda yakeso irin yaga ya tarwatse zaman*
*munafurci yana kunshe da abubuwa ne guda uku*
*abubuwannan guda uku idan mutun yakasance acikin daya dagacikinsu to yatabbata munafikine*
*na daya shine duk yadda zefada magana to baze fadi gaskiya ba cikin kaso Dari bazaka samu kaso daya dayakasance gaskiya ba acikin maganarsa wannan shine makaryaci zakuga daga yazo za afara sulalewa saboda ansan indai yazauna ya ringa zuba karya kenan and the worst part of zama makaryaci shine duk yadda yazo da gaskiya baza'a taba yarda ba koda kuwa ze hadiye Qur'an yana kashin ayoyi ne baza'a yarda ba saboda kasaba zama kana sharara karya watarana zaka iya zuwa kayi magana akan abinda kai ko waninka yake bukatar taimako alokacin amma kowa seyai buris dakai saboda bakada gaskiya kunga kuma tun anan ansamu matsala kenan*
*munafurci babbar cutace don Allah mukiyaye*
Page 8
Yaya asma'u ta firgita sosae dan ganin yadda kan jabir yakumbura sosae se kuka yake batun atada shi zaune bema tasoba ga uwarsa ma akwance wani kalar jiri take gani idan ta miqe gani take dama takoma hagu (abin tausayi),
Dasauri anty asma'u takira yayansu mukhtar tafada masa halin da ake ciki ba bata lokaci ya iso asibitin,
Yayi mata fada sosae ganin yadda jikin yaron yayi tsanani amma ace har kwana biyu bata fada ba,
Hakuri tabasu wallahi ita batasan mema zatayiba abubuwa sunmata yawa itama batada lafiya,
Yanzu ina baban sa? Ya mukhtar yatambaya,
Tun ranar damukazo ko awaya bekara kiran mu ba kuma yace kar akara tambayarsa koda kudin maganine aranar ma bebiya kudin komai ba yayi tafiyarsa,
Magana take tana kuka da alama ma batasan maganar nafita ba ganin yadda idonta suke a rufe,
Bari kuga naje naga Dr daga baya mayi maganar yaronnan yanajin jiki idan aiki za aimasa senakira babansa muji yadda za ayai yana gama fadar haka yafita daga dakin,
Shiru tayi tana kallon yadda jabir yakura mata ido ko k'iftawa bayayi ahankali ta riko hannunsa kara riqe hannun yayi yana lumshe idonsa bayan dan lokaci taji yasauke ajiyar zuciya kuma ya dan saki riqon dayayiwa hannunta, gyara masa kwanciyarsa tayi dan yaji dadin baccin,
Asma'u nagefe tana kallonta atake taji zufa nakaryo mata,
Mukhtar ne da Dr suka shigo dakin ze duba jikin jabir susaka lokacin da za aimasa aiki,
Yaya asama'u tana gefe tanajira taga yadda Dr zeyi bayan yagama bincikensa,
Dagowa yayi yna kallon badee dan yasan itace uwarsa besan taya zefara fada mata jabir ya rasu ba se kawai yaja hannun mukhtar suka fito,
Se hakuri yace yana kallon mukhtar,
Allah yajikan sa yasa me ceto ne wannan yaron yafi 30mnt darasuwa kuyi hakuri yana gama fadar haka yajuya dan ganin yadda mukhtar ya qame,
Dake wayayi yashiga dakin kokallonsu bebiye ba yashiga nado jabir acikin zani yamaida kallonsa ga badee,
Ku tattaro kayannann mutafi gida,
Dasauri tadago tana kallonsa atake tagano jabir mutuwa yayi ganin yadda mukhtar yarufesa ruf har fuska da zani,
Batasan lokacinda takai jikin bangoba dakarfi ta rufe idonta kafin tabudesu atake idonta sukayi ja kuka takeso tayi amma yaki zuwa,
Asmau ce tashi ga hada kayan cikin karfin hali tanason yaron sosae amma yakamata ace akwai Wanda ze karfafawa badee gwiwa kodan lafiyarta da abinda ke cikinta,
Har yanzu tana gurin takurawa kofar da mukhtar yabi yafita da gawar jabir ido,
Hannunta Asmau taja suka fita binta kawai take batama ganin gabanta,
Yaron ya kwanta mata sosae azuciya tanasonsa yanada sanyin hali tasaba dashi shine Abokin hirarta,
Yasan yasaka hannunsa yana share mata hawayen fuskarta duk lokacin dayaga tana kuka se lokacin taji hawaye masu zafi sun zubo mata batayi kokarin hanasu zubowa ba,
Tanaso sucigaba dazubowa kozataji sanyi azuciyarta.
_kuyi hakuri da wannan wallahi yau se a slow nasamu deepcut ne dan yatsata_ILVY oll.
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
_wannan shafin naki ne anty bilkisu (maman nu'aym)_
*kada mudauki rayuwar duniya abakin komai domin ba komai bace*
*Arayuwar duniya mutun uku ne sukafi kowane mutun bakin jini*
*mutun nafarko shine mutun me girman kai yanajin kansa so high idan yashiga mutane seya ringa d'age d'age yanajin yafi kowa,to wannan mutun zakuga kowa bayason haduwa dashi domin zuciya tafison Wanda yake kyautata mata semu kiyaye wannan idan munshiga mutane semu kyautata mu'amalar mudasu saboda mutane Rahama ne*
*Allah yabamu hakuri Ameen*
Page 6
Yaran dukansu suna makaranta daga ita se jabir suna zaune a corridor yana ta wasan sa miqewa tayi tashiga daki dan jin karar wayarta,
Bata fito ba seda tagama wayar dasauri tadaga labule tana fitowa danjin karar wani abu,
Tsayawa tayi tana kallon abdulmajid kafin ta maida dubanta ga jabir dayake kuka haryana shidewa ga gefen fuskarsa yayija harya soma kumbura dauke idonta tayi daga kallonsa takarasa kusada abdulmajid tanayimasa sannu dazuwa cikin karaji yafra magana,
Banason sannu dazuwanki munafuka nahanaki zama dayaranki duk inda nake ajiye kayana amma dan wulakanci shine zakibar wannan yaron yataba min takalmi yau dasafe nabawa me shoeshiner ya gogesu kalli yadda danki yasaka musu kura bayan hakama kinsan ko nawa nasiye su?,
Kallonsa kawai take kafin tamaida dubanta ga takalmin babu alamar kura kokuma antabasu,
Wanine yataboshi awaje shaine yazo yasauke hannunsa kan dan bawan Allah kobadan komaiba kodan yarintarsa ze masa uzuri,
Batace komai ba tasamu guri ta zauna kallon jabir din take da wahala tasakashi bacci gashi balafiya gareshiba yauma da zazzabi yatashi,
Bin bayansa tayi da kallo yadda ya daki kofar dakinsa yashige tabe baki tayi,
Azuciyarta tace yau nayi niyyan fadamaka ina dauke da cikinka Na shida amma naga kanka Na hayaki batason hayaniya yau shiyasa zanbari harka huce komai zakayi sekayi,
Adaki kuwa mamakin hali irin na badee yake ko yaki ake bisa kanta inbataso tankawa ba bazata tanka ba shikuma abinda ya tsana kenan yafiso tabiye mai suyita yi amma betaba samun haka ba,
Fama take da kanta gakuma jabir yatashi da zazzabi me zafi dan ko zama yakasayi se mak'alk'aleta yake dakyar tasamu tashirya yayyensa suka tafi islamiyya,
Paracetamol tabashi na yara Allah yataimaketa akwai shi goyashi tayi tashi ga kitchen dukda tanajin badadi jiri takeji gakuma zafin jikinta yana haduwa da nasa seta ringajin wani iri,
A daddafe tasamu ta kammala abincin takoma daki ta kwnatarda jabir dayayi bacci,
Se bayan isha tasamu kanta yaran duk sunyi bacci saboda wahalar wuni amakaranta,
Kallon fuskqr jabir dake gefenta take shatin yatsun babansa da ya kwandara masa mari dazu gasunan radorado wurin ya kumbura tausayinsa yakamata batasan lokacin da hawaye ya zubo mataba dasauri tasaka hannunta ta goge hawayen fuskarta jin abdulmajid ya kwallah mata kira tashi tayi kafin ta amsa da muryarta can ciki,
Yawwa badee nace abdulrahim yaci abinci kuwa naji shiru kamar yayi bacci,
Gyada masa kai kawai tayi danjitake bazata iya magana ba,
Bakida bakin da zaki amsamin ne?
Eh yaci tayi maganar dan batason hayaniya,
Janyota yayi jikinsa yana tambayarta,inafatan kema kinci?
Eh tace tadora da fadin,
Kayi hakuri yau bazan kwana adakinka ba saboda jabir bayida lafiya tunsafe yake fama da zazzabi,
Nikuma ina bukatar ki,
Yafada yana harde hannayensa akirji yazuba mata idanuwansa,
Kauda kanta tayi gefe dan batason irin wannan kallon kafin tace,
Kasani bazan bar yarana sukadai adakiba kuma daya cikinsu babu lafiya ze iya tashi cikin dare shisa nace kayi hakuri yau kadai,
Banyaddaba inkuma kin yadda ki kwana cikin tsinuwar Allah da mala'iku ne karkizo,(wai kuti ke cewa kaza k'azama)
Kayadda nazo dashi dakinka? Ta tambayesa cikeda gajiya da maganar,
Banyadda ba nafada mini,
Yafada tareda ficewa daga wurin yana barinta atsaye,
Takasa koda motsi dangaskiya bazata iya barin dantaba ga bayida lafiya.
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfahari)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
Assalamu alaikum
Dafatan munyi azumi da sallah lpy? Allah yakarbi ibadunmu ameen.
Inajiran goron sallah na 😎.
Page 9
Badee'a tayi lkuka harta gode Allah sotake taga laifin mijinta nakin kulawa da lalurar data sami dansa har yakai ga ajalinsa,
Majid mugune Dabadan se lkcn mutun yayi yake mutuwa ba da ta dauki kaddarar mutuwar jabir rankatakaf ta rataya awuyan majid sekuma wannan yaci karo da abu biyu sonda takeyiwa mijinnata dakuma albarkacin yayan dake tsakaninsu,
Bangaren majid kuwa mutuwar ta dan tabashi sbd betaba kawowa yaron mutuwa ba gashi badi'a ko kallonsa batayi tunjiya bayan dawowarsu daga asibiti dyasani yake dabe kula yaronba lkcn dayake bukatar taimako kobadan kasancewar sa dansa ba kodan mahaifiyar yaron dayake matukar so tawani bangaren kuwa abincin da yan tsirarrun mutane masu zaman amsar gaisuwa en uwansa da nata keci shine yakeji kamar naman jikin sa ake cira gani yake kamar tattalin arzikinsa suke cinyewa gsky akwai matsala baze iya yin wani yunkuri na hana zaman ba amma yana ftan daga Gobe arufe zaman makokin (wannan ko dai Dan iska ne🤔),
Dahaka rayuwa take tafiya har akayyi wata biyu da rasuwar jabir babu abinda ya sauya a al'amarin majid da gidansa badia wahala take ga wannan karon batayi sa'ar cikin ba yana bata wahala sosae sana'ar da take bakullum takeyi ba yaranta duk sun fita hayyacinsu,
Yauma kamar kullum ta tashi se a hankali dakyar ta hadawa mijin breakfast yafita aiki ga yunwa Dan kadan tahada danata bayawa Dan haka yaran kawai sukaci tace zata jira abincin rana lkcn cikinta yana wata shida kenan,
Bayan azahar yadawo gida yasameta kwance a korido zazzabi yahanata sukuni ga jiri,
Yaya asma'u ta taso daga aiki tace zatazo taduba kanwarta tundaga waje take sallama bataji an amsaba,
Maganar majid taji yasa ta tsya awaje,
Zma yayi kusa da ita en mata abani abinci na debo yunwa garinnan rana tayi yawa,
Don Allah kayi hakuri wallahi yau banajin dadi banyi girki ba,
Miqewa kawai yayi ya soma fada,
Dan bakyajin dadi sena zauna da yunwa kullum seki lafe kice ba lpy amma kin iya yin sna'ar ki seni zaki zalunta kibarni da yunwa? To wallahi kinyi kadan yanzunnan kitashi kidafamin abinci inajiranki Dan Nagano nema kike kizama muguwa,
Batason masifar nan shiyasa ta miqe zuwa kitchen tasan idan ba girkamasa tayiba masifa zetayi,
Yaya asma'u wni abune ya tsya mata awuya zuciarta tadau zafi Tajuya tabar gidan dole sudau mataki baze yiyu sunaji suna gani a kashe musu er uwa ba tafiya take tana kwalla sbd tausayin kanwarta mijinta takira tafada masa tana hanyar zuwa gdn ya mukhtar zasuyi magana ne yasan batada yawo Dan haka ya amince,
Tayi Sa'a yayan yana gida yadawo da wuri tazauna ta labarta masa komai datasani tun bayan haihuwar abdulrahim har zuwa yau,
Yayi masifa kamar ze cinyeta danme tayi shiru seyanzu tafada masa yabashi hakuri yace tawuce gida zeyi tunanin me zasuyi,
Washe gari tunda sassafe yaje gidansu yazauna da iyayensa cikin kwamciyar hankali yafadamusu yadda sukayi da Yaya asama'u yakuma cekarsu daga hankalinsu baba yashirya ranar asabar zasuje gidan dole sudau mataki mahaifiyarsu har kuka tayi sbd tausayin erta da halin datake ciki,
Sunyi sa'ar samun majid a gida Dan sammako suka yi idonsa zuru zuru domin be taba ganin alhaji a gidan ba sama sama suka gaisa Yaya mukhtar yanemi akira masu badi'a Gabanta yayi mummunan faduwa dataji lbrn babanta ne da kawunta se Yaya mukhtar harda asama'u aka zo,
Tass suka zube masa sunsan halin da badi'a takeci Wanda sune shida mahaifiyarsa suka sanyata ciki atake ya kidime zufa yafara karyo masa,
Alhaji ne yafara magana
Abdul bana bukatar sulhu Sakar min yata zakayi yanzu base anjimaba sbd itama haifarta akayi ba jaka nakawo maka ba kuma tanada gata gaba da baya kuma inaso kasani Yaya dakake cewa bakaso naka ne kokaki kokaso Dan kasanima yanzu idan zamu tafi iya kadai zan dauka nabar maka yayanka shima wannan cikin wallahi daze yiyu nabar ma ka shi baze taka kafarsa gidana ba sekaje can kasamu wacce batason Yaya irinka ka aura,
Seyanzu yasan yana cikin tashin hankali Dan harya fara hango rayuwarsa babu badeea ya hango rashin kwanciyar hankali tsintsarsa aciki yatafi duniyar tunani kukan badee ne yadawo dashi,
Ta kama kafar alhaji,
Baba don Allah kayi hakuri karka rabani da yayana da mijina wallahi inasonsu kubarni dasu kodan tarbiyar yayana,
Garama kidaina rokona bazan juri ana wulakanta ki ina kallo ba kobana raye bazan yadda ba,
Baba wallahi inkuka rabani da majid zan iya mutuwa wallahi inason uban yayana ,idonta yarufe da soyayyar mijinta bata gani bata hango abinda magabatan ta ke hango mata duk baba har aransa baso yake yarabata damijinta Ba yaso ace tabashi hadinkai ya hora majid amma takawo cikas,
Akaro na uku baba yasa ke umurtarta data tattaro kayanta kuma bayaso tadauko yaro ko daya acikinsu abdul ,
Idonta arufe tana kuka tace baba kayi hakuri bazan iya barin yayana ba nasani wata rana zasu zama ABIN ALFAHARINA don Allah kutausayamin Ku hango abinda nake hangowa,
Zuciyar baba takawo wuya mikewa kawai yayi yace duk abinda yataso koyasameki ko yayanki karki sake kinemeni bejira su kawuba yafi ta,
Yaa mukhtar yamiqe shima idonsa yayi ja sosae zefita tariqo kafarsa tana roqonsa tana kuka kokallonta beyiba sbd tawulkanta su aganinsa yajira tasake masa kafa yasakai yafi ta kawukam yaga kowa yafi ta shimexeyi seyabi bayansu,
Gun asama'u taje zata fara mata magiya ta daga mta hannu tana miqewa tsaye kafin tace ba kinzabi mijinki akanmu ba aiseki zauna gashinan kuma kisa aranki bakida er uwa asama'u aduniya tana gama fdar haka tafita.
Kuka sosae badeea take batasan INA zata sakantaba en uwan datake takama dasu sungujeta harda mahaifinta .
0 comments:
Post a Comment