A gaskiya ta matukar bashi tausayi musamman dayaga tana kuka sosae kuma yasan tanada hakuri fiye da tunanin sa tabar iyayenta da en uwanta ta zabeshi yana fatan kada wannan yazama babban kuskure da zatayi arayuwar ta sedai fa yarannan nata idan yagansu jiyake kamar ya sheqesu sunyi masa yawa dayaso kada yayan su suwuce biyu haka amma ummansa takawo matsala na rashin son tsarin haihuwa.....
Jin an riqo masa kafa yasashi dagowa yana kallon yadda take kuka kafin tfara magna,
Abdulmajid don Allah katausaya min da yaranmu kar rayuwar mu tashiga garari kasani auren soyayya mukayi abinda kake mana be dace ba koba don komai ba haqqinmu ne daya rataya awuyanka ka kula mu,
Wannan haqin data ambata shiyasa shi jin haushi Dan haka tausayinta daya faraji yasoma gushewa,
Abdul nasan bakason yarannan sbd bakaso haihuwarsu ba ammakasani yayanka ne kataimake ni koda da abincin dazasuci ne don Allah ba....
Numfashinta sama sama yake har idonta yafara kafewa kafin yayi wani yunkuri tazube agurin,
A rikice ya sungumeta yana zuwa kofar fita da korido yaga su Abdul awajen take karamin cikinsu yasa kuka ya rasa yadda zeyi dasu dole yasa ka su agaba sukaje asibiti,
Takaici ya isheshi ganin yadda suka cika masa mota kamar wata nursery skul bus,bayan sun isa ya cewa abdulrahim ya kakula karyabari sufita daga motar kuma karsu taba komai aciki,
Bayan awa biyu likita yagama dubata harta farfado tana kwance yana gefenta se Harar ta yake,
Muryarta harta soma dashewa tace abdulmajid,
Cikin jin haushi yace menene?
Talura da yanayinsa batasan meyasa yakehakaba yanzu, a hankali tace kataimake ni da yayana don Allah hawayene masu zafi suka zubo mata,
Naji zanyi tunani Kuma menene harda suma? Nace zan sakeki ne kokuma nayi sakin ?
Bakasan yanakeji ba shiyasa iyayena fa suka gujeni,
To ba ganiba ai inakusa yanzu gashi kinjamin nakashe kudi dayawa kuma ga kudin wankin mota wayannan yayan naki duk sun batamin mota ke kin cika rigima wallahi kinjmin hasara yau kudinnan wani Abu daze kawo kudi nasoyi dasu,
Idan tanabiyewa majid seciwon zuciya ya kasheta,
Majid a sallamemu mukoma gida banason asibitinnan,
Fita yayi yadawo da Dr aka dubuta yabata magunguna kafin ya sallamesu,
Bayan kwana biyu bata chanja zaniba dn majid baya wuni a gidan Sam balle Taji inada maganarsu ta kwana se ranar data ristashi tun asuba take tambayarsa kan maganar babu yadda zeyi koba komai tbar iyayenta sbd shi,
Kiringa dafa abinci dasu ama wallahi kar naga abinci anraga ko an zubar ina ganin haka za asamu matsala bani key din store,
Damamaki take kallonsa mezakayi dashi? Ina ruwanki ki bani key nizan ringa dibar kayan abincin dakaina yawan danakeso,
Bataso tayi gardama yace yafasa ta samu ya yarda Dan haka ta miqa masa yayi yadda yakeso fatnta dai Allah yasa yabasu Wanda ze ishesu zata ragewa kanta damuwa sbd batada kowa kusa yanzu Dan jiyama takira kanwarta farida awaya taimata rashin kunya kamar ba kanwarta ba,
A can gidansuma Hajiya Taji kwana biyu ba lbrn yasukayi da badee'a Dan haka seta tambayi abbansu yadda ya amsa mata yasa takama kanta Dan cewa yayi intanason knta da arxiki karta kuma yimasa zancen badee kuma bebata izinin nemanta ba,
Dahaka rayuwarsu tacigaba da tafiya duk ranar da yaga dama seya basu kadan koyaki dawowa dawuri balle yabasu na rana wahala suke itada yaran Dan yanzu makaranta me kawai be chanjawa Abdul rahim ba amma bakin jinin yayanta a idonsa yajawa abdulrahim haushi baya samun abinci sesanda baban yadawo yadebo musu daga store kafin tagama girkawa itada yaran sun tagayyara musamman ita datakeda ciki gashi yakai wata takwas yayi girma naban mamaki kana ganin ta kaga damuwa cikin kadai ke girma kodan kumburin damasu tsohon ciki sukeyi ita batayi komai yinsa kawai take bata wanidamu da sana'ar taba sbd duk ranar datayi wani abinci kafin yadawo dakudin ze haukacemata yace yadaina ciar dasu shagonsa yayi kasa ma sbd ciyarda yaranta dayake shiyasa duk yadda tatara kudin sedai tayi tanadinsu tayiwa yyanta lalurar makaranta, kona asibiti,
Tana zaune a korido itada yaranta Dan yau babu islamiya yunwa natacinsu har karfe hudu da rabi be dawoba Sega sallamarsa yashigo ta amsa masa tana hamdalan dawowarsa,
Hada ido sukayi Taji gabanta yafadi kwata kwata batason abin yanzu ga yunwa tanaji su abdul bame iya kwakkwaran motsi sbd yunwa,
Majid don Allah kabari nabawa yarannan abinci tukunna,ohhh yaranki sunfini kenan inace nine me bada abincin? Tona fasa sekinzo muntafi inbazakiba seki nemi abinda yayanki zasuci,semi zauna da tsinuwar Allah data mala'iku (besan Allah ba se anan)
Dakyar tamiqe tana dafa bango ta cewa abdulrahim kaje da kannenka palona kucigaba da kallon cartoon yanzu zan dawo damurnarsu suka wuce itaam taigaba gogan yabi bayan ta,
Dakyar tayi sallah magriba sbd tsananin gajiya,yana kwance tace Abdul muje kabani abincin na dafa mana,kibari nahuta mana Nagaji baccima nakeji,daga haka yagyara kwanciyarsa,
Ranar dai se 9 sukaci abinci yaranma har sun fara bacci ta tashesu tabasu kafin taci nata ta kwnta,
Ranar alhamis dasafe bayan tadwo daga awo tace bari ta leqa gidan su kafin taje gdnsu majid daukar yaranta ta tsaida adaidaita tashiga gdn gabanta ne yafadi ganin baban su zaune tunkan taaraso yasamata stop,
Kifitar min daga gida kuma kar kafarki tayi tunanin sake dawo min gida bude baki tayi zatayi magana yace bana bukatar jin komai daga gareki kikoma gun yayanki da mijinki masoyanki kuma kifita da Sauri,
Tana kuka tabar gidan ga ciki dakyar take takawa tayi danasanin abinda tayi dma tayarda ta bisu a ranar daga baya ta lallabasu ta dawo gdn mijinta,
Har ta isa gidan su majid kuka take kafin tasamu kakarsu ta lakadawa Abdul'aziz duka yamata banna,
To muna fuka.....
Nagaji😳anty badee🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀
[7/5, 8:06 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfaharina)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
This page goes to u my sister,my frnd anty shukra(Zainab yakasai)ILY.
Page 11
Daga bakin kofar ta tsaya tana sauraren kalar cin zarafin da Hajiya ke yimata yau tasaba zuwa gidan Hajiya tayimata wulakancin da bata zato amma nayau yafi kona mata rai,
Ki karaso mana kiga kalar bannar da danki yaimin Nagano dalilinki nakawo minsu duk lkcn dazakije asibiti sbd kawai ki takurawa rayuwata Dan kinga bana hanasu abinci bakyaso kiga cigabana dani kike kishi Dan Dana yana kula dani to wallahi daga zan dau mataki zo ki kwashi yayanki kubarmin gida tun bankaraa daukar zafiba na illata daya daga cikinsu,
Batareda ta musa ba cikin karfin hali ta dauki abduljabbar daketa kuka yasha duka ta gargada sauran tayiamata se anjima memakon ta amsa se cewa tayi,
Aikam dai dole atafi mace ba control daga antaba ta seciki ke bakya gajiya da haihuwa ne kiketa zubo Yaya haka kamar wata akuya?,
Idan ta tsaya sauraren wannan zancen tsaf naquda zata kamata Wanda ze iyasakata haihuwa akan hanya kirjinta taji yayi nauyi sosae,
Adaidaita ta Tara duka kudin hannunta dasuka saura 90 naira ne da bata biyo gdnsu bane kudin ze isa akaita gd me adaidaitan dayaji kudin data ambata se kallonta yayi sheqeqe, amma malama ina ganin bakida hankali ko? Yoke konace kikawo kudin nakaiki zaki shiga? Ga Yaya rututu? Nikam ba bakin uwa gareniba,shiru tayi tana kallonsa kafin daga baya yaitafiyarsa hakan yasa taja hannun sauran suka fara tafiya akafa seda sukayi nisa sosae ta tari wani adaidaitan dayake sunci Rabin tsfiyar yasa yadaukesu,
Wai Hajiya haryanzu bamu iso bane? Eh seka wuce wannan sabon masallacin kadan, ashar ya lailayo bejira tayi magana ba yace kibani kudina malama ki sauka irinkune basason ganin cigaban mu kinsan har nan zan kawo ki baki tsaya yimin bayani ba,kudinsa tamiqa masa dn tasan yau in batayi ahankaliba zuciyarta fashewa zatayi,
Dakyar taga sun isa gida da zuwanta tasamu abdulmajid yana gida batabi ta kansaba tashige dakinta wanka tayi tayiwa yaranta suka kwanta,
Yaran duk sunyi bacci sbd gajiya itakam takasa baccin ma tunani take EDD dinta saura kwana biyar sotake ta sauke cikin nan sbd ya isheta sosae ba kadan ba bata taba yin ciki me kwatankwacin rigima irin wannan ba fatanta dai Allah yasauketa lpy dole tfara shan magani tsarin haihuwa aboye sbd tagaji sosae ga yayan bawani gata garesuba ita kanta tarasa nata gatan,murmushin dyaafi kuka ciwo tayi tace a fili yaushe rayuwata zata dawo daidai kamar ta sauran mutane?nasani abune me wahala asamu wata me irin matsalata arayuwa uwar miji da miji sun sakani a tsakiya sun dauran laifin dabanawa ba sunkasa gano laifin daga garesu ne shi mijin bayason haihuwa yanaso nayi family planning uwar mijin tana son jikokai tahana ayi family planning gashi yanzu tasoma goyan bayan danta bayan dakomai yagama lalacemin, hawayeni suka zubo daga idonta amma abin mamaki hawayene masu sanyi kuma daidai lkcn babyn dake cikin ta yayi kicking ahankali tashafa cikin tasa hannu daya tana goge hawayen fuskarta,
Sallamar majid yasa tadawo daga tunanin datake se cewa yayi badee zokiga wani Abu yana gama fadar yafita rigarta tadauko tasaka tabi bayan sa A gefen gado tasameshi dasaurinta takarasa yazauna gefensa sbd kafafuwanta dasu kayi tsami sbd tafiyar kasa,
Gani me Zan gani Abu abdulrahim? Bata ga komaiba illa jin bakinsa kan nata😳,
Bayan lafawar komai tashiga sheqa amai batasan dalili ba, gefen gadon ta kwanta tanajin mararta nadan ciwo shiru tayi kafin tafarajin abin yana Neman yafi karfin ta,
Batayi zaton abin zekai haka ba segata adurqushe dakyar ta ke numfashi,ganinta awannan yana yin yasashi rikicewa yafara tambayarta menene?
Abdul muje asibiti inaga haihuwace,
Haihuwa ya maimaita,kuma a asibiti? Nibazan iya Da wannan kashe kudinba ki kira Yaya asama'u mana,
Batasan me zataceba kada tayi magana ya tunzura,a wahale tace don Allah majid kakaini asibiti kasani Yaya bazata zo ba don Allah karna mutu bakasan me nakeji ba,
Dakyar suka isa asibiti bayan ankarbeta yawuceda yaran yakaisu Inda Hajiya seda ya lallabata ta karbesu,
Kusan awa uku tana fama kafin tahaihu tasamu baby girl yarinyar wata kalar katuwa Dan seda akai mata sbd girman babyn,
Wallahi badi'a Nagano babu abinda yake burgeki irin kiga tattalin arzikina ya dakushe kalli bill dinda akayomin fa? Sekisann yadda zakiyi dashi yafada yana jifanta da papern,
Binbayansa tayi dakallo seda tadaina ganinsa kafin tadawo da kallonta kan nurse dinda ke dakin tazo cire mata cannula juyawa tayi tana ajiye babyn agefe tafara kuka,
Matar zatayi sa'an Yaya asama'u durqusawa tayi ta dauki papern tafita,
Batasan iya adadin lkcn data dauka tana kukaba seji tayi andafata ta dago tana kallon matar,
Matar ta sakar mata murmushi,
Hajiya badi'a ansallameku sbd keda babynki kunanan lpy Dan haka seki tashi kitafi gida ana bukatar gadonnan,
Shiru tayi tana tunanin bata fito dawayanta ba Waze kaita gida ga babyn ko kayan sawa batada su adankwalinta aka nado ta,
Kitashi mutafi zan saukeki gida tundazu dutyna yakare ganin kina wahala yasa ban tafiba najira har naga me Allah zeyi kiyarda dani bazan cutar dakeba sunana Zainab Muhammad,
Godiya sosae tayi mata har zata fita daga motar Zainab tace, dafa tan kinada me kula dake naga tafiyama dakyar kikeyi,
Babu kowa nikadaice se yayana kuma duk mazane kanana,
Batareda ta amsataab tajanyo waya da alama mijinta takira tana Neman izinin zata taimakawa wata baiwar Allah a gidan ta kuma be hanataba,
Turus tayi tana kallon....
Nayi kokari yau tun asuba nake typing😜🙈
[7/5, 8:07 PM] Babee Feeya: *Y'AY'ANA (Abin alfaharina)*
_by SophieG_
_A very heart touching story 2017_
Abinda duk ka tsarawa rayuwarka ba shine tsarinka ba domin tunkan kazo duniya Allah yagama tsara yadda rayuwarka zata kasance tun ranar da aka haifeka har zuwa ranar dazaka koma garesa, duk abinda kaga Allah yayimaka shine daidai dakai semuyi imani da kaddara me kyau ko Mara kyau wanda yayi haka shine cikakken musulmi kuma me imani,ina rokon Allah da ya tabbatar mana da alkhairi arayuwar mu ameen.
Anty badee wannan shafin nakine kekadai kaunar dake tsakanin mu ta dabance ina rokon Allah yabarmu tare yakuma bawa ustaz lafiya ameen.❤
Page 12
Turus tayi tana kallon su Abdulrahim su kadai awaje ga kofar korido abude da alama babansu yananan dasaurinta cikin karfin hali takarasa kuSadasu,
Abdulrahim mekukeyi anan?
Hajiya ce takawomu wai fita zatayi bakowa a gidan bamu gankiba munata kuka babanmu yadawo yabude gida shine yace nazo mukwanta muyi bacci amma karsu Abdul'aziz sushigo zasu damemu shine nace banajin bacci yai fushi yace inmuka shigo seya zanemu kuma munajin tsoro,
Yakarashe maganar yana kuka batasan lkcn data janyosu jikin ta ba tafashe dakuka yaran ganin uwarsu nakuka se hankalinsu yatashi suka biye mata,
Zainab dake kallon su ta lura daga yaran har mamansu sunada damuwa sosae kusa dasu ta matsa tace maman baby kina bukatar wanka ki huta ki ajiye damuwarki gefe yanzu kinga magriba ta kusa inaso in koma gida dawuri tun safe nafito,
Murmushi nadole badee tayi tace kiyi hakuri nabarki a tsaye,
Bakomai ai,
Ruwa tahada mata tai wanka tahada mata tea tasha seyaba kyaun gidan take talura mijin ne bashi da hali amma gdnsa ya tsaru ta tabbata gidan ta baze fi wannan ba duk dukiyar mijinta da baban ta kuma ga alama mijin Dan gayune sbd talura kamar sbd fenti yayi kamar ba yara a gidan,
To maman baby se abawa baby abincin ta tunda ke kin koshi,
Murmushi kawai tayi taakrbi babyn takalleta sosae sekuma ta share hawayen dasuka zubo mata tana cigaba da kallon yarinyar ahankali tace,
Barkarki dashigowa duniya me tattare da abubuwa naban takaici abubuwa naban tausayi abubuwa na jin dadi, kuma ina miki barka dashigowa gidan babanki dabaya kaunarki baya maraba dake barka da zuwa hannun mamanki me cike da kaunarki Barka da zuwa hannun yayyenki masu sonki insha Allah ina adduar Allah yabaki juriya da hakurin zama wannan gidan mecike da bakinciki ina miki Barka......
Zainab ta rufe mata baki da hannunta, haba maman baby kada bacin rai yasaki furta abinda ba shikenan ba ki yadda wannan rayuwar taki d yayanki kaddara ce kuma kiyi imani da ita kikasance me hakuri kuma irin hakurinda baya karewa kinji,
Gyada mata kai kawai tayi tace kitashi anty Zainab kitafi gida dare nayi kilama kin barwa megidanki hidimar yara,
Murmushi me ciwo Zainab tayi tace megidana ba shida matsala koda zan kwana nanne kuma banida yara koda ya,
Ganin yadda badee kekallonta yasa tace kibari gobe zan dawo idan na dawo Zan baki lbari bani numbernki zankiraki kiga tawa sekiyi savin idan da Marsala ki kirani, bayan fitarta badee taga transfer na Dari biyar tayi murna sosae sekuma tayi shiru tunawa da kotakira ba daga wa zatayiba data ta siya tabude watsapp dinta kai tsaye tanemo sunan yaya asama'u tatura mata massage kamar haka...
As salamu alaiki
Yaya Allah yasaukeni lpy yau nasamu baby girl kitaimakemu koda da addua ne kadai na gode.
Tatura mata hoton babyn gatanan dake take kama har bakinku iri dayane.
Kwanciya tagyara musu kafin tashiga tunanin abdulmajid yana gidan amma bezo yadubasu ba hakan yasa tanufi dakin sa dauke da babyn,dasallamarta tashiga dakin zaune ta samesa yana signing wasu takaddu, zaunawa tayi kusa dashi tayi shiru,
Ya akayi? Yatambayeta yana cigaba da aikinsa,
Yarka nakawo maka naga ko daukarta bakayi ba,banida bukatar daukarta naganta ahannunki ai,
Bata karayin magana ba tayi shiru kusan mintuna goma sha Biyar kafinnyadago yakalleta se idonsa suka sauka kan babyn dake ta sharar bacci abinta,
Ka taimakeni Abdul koda hudubane kayi mata kasamata duk sunan dakakeso don Allah tafada cikin rawar murya,
Shiru yayi yafafda kogin nazari,yakamata yashare mata hawayenta kardamuwa taimata yawa ga babyn data Haifa kyakkyawa yaji yarinyar tashiga ransa fiyeda abdulrahim dole yaimata suna da sunan dayafiso aduniya,
Taga kamar ba shida niyyar yin abinda ta roqa seji tayi ya sunkuci yarinyar yana murmushi harda bisimillah,
Bayan yagama abinda yadace yamiqa mata babyn yace sunan ta LUBNA(I'm in love with this name❤),
Murmushi ne ya kwace mata lkn data tuno hirar dasu kayi auren su saura sati biyu,
Baby badee wane suna kikafiso asawa yarki ko danki? Idan nahaifi namiji nafiso asamishi abdulrahim ko abubakar sadeeq inkuma macece nafison Fatima ko safiyya🙈 ,
Murmushi yayi yace nikuma nafison sunan babana Abdul'aziz idan macece nafison Lubna❤,
Kai amma baby bantaba jin sunan ba idan nasamu baby girl zakasamata Fatima tabiyun kuma sekasa Lubna din ko?,
Badee kije ki kwanta kingaji yafda yana mikar da ita,
Wani kalar dadi taji daysa dole seda tayi hugging dinsa sosae irin sosae dinnan 😂😍
Wanna page din Na gobe ne lol. Luv u oll😘
[7/5, 8:07 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Wannan shafin nakine meela adeel(meelolo mekan giginya😂😜).
Page 13
Shifa ko period take becika son cin abincin data girkaba sbd kyankyami kawai dai ta iya girki ne,
Badee meye haka kisakeni mana bakyajin karninda kike keda babyn😣,shiyasafa banason haihuwar nan karnin nono da jini duk su dame mutun dauki babyn ki kutafi se dasafe,
Tasani sarai bawai don yanason babyn yasa mata sunaba kawai dai yanada wata manufa ne talura da yadda yake kallon yarinyar ko abdulrahim baya kallo haka,
Bayan fitar ta daga dakin yasoma tunani, akwai matsala babba indai ba umma ce ttaadawa en uwansu Na kwareba baze fada musu haihuwarnan ba kauyawa suzo su cika masa gida acinye mai abinci subata mai gida,
A bangaren yaya asama'u kuma tana zaune tana tunanin halin da er uwarta take ciki kila yanzu tanachan da cikinnan yasata agaba ba lpy ga yara,tsaki tayi bayan tuno yadda badee tayi agaban mijin tanuna ta mato akansa dole yaji dadin kara wulakanta ta kuma tawatsa musu kasa a ido amatsayinsu na en uwanta da mahaifanta, wayarta ta janyo tanaso tadaina tunanin badee tashiga WhatsApp da sauri tannufi number ganin anturo hoto kodai hotonsu ne tafada afili har zata wuce se kuma ta dawo,
Sosae take kallon hoton har batason kyafta idonta, masha Allah tafada tana shafa screen din wayarta ga yarinyar kyakkyawa me kamada ita amma babu halin kulawa da ita bazata taba shiryawa d badee ba se lkcn databar gidan Abdul majid sbd jityi ko sunansa batason tunawa balle taji wani yafade shi hartakai ga ganin mesunan,
Amma setayi kokarin ganin zuciyarta tahanata zuwa ganin babyn karta ruguza komai,
Washe gari Zainab tana off nakwana biyu hakan yasa ta kammala komai Na gidanta bayan ta sallami mijinta yatafi aiki ta shirya komai tanufi gidan badee, a korido ta sameta tana bacci tun a tsakar gida take sallama bataji an amsaba, Allah sarki ta fada a fili,gdn angyarashi komai tsaf tayi wanka tayiwa babyn sunata bacci abinsu ga alama ma yaran basa gidan,
Farkawa tayi idonta sekan Zainab da sauri tatashi zaune,lahh Anty yaushe kika shigo? Inata baccin gajiya nasha aiki,
Ainaga alama kam keda kikeda Dinki ajikinki meye naki Na wannan urban aikin,
To idan nabarshi Waze yimin? Banidakowa akusa,
Baganiba inji Zainab tana murmushi, bani babyn a huda mata kunne kafin tagama sanin zafin jikinta,
Bayan angama huda mata kunnen Zainab ta tattara nutsuwarta ta fuskanci badee,
Inaso kibani labrinki kumabawai don inason sanin sirrinki bane sedan inaso Na taimaka miki,
Ahankali tabata labarin rayuwrta Wanda taji zata iya fada,kuka take kamar ranta ze fita Anty Zainab narasa kowa da komai nikadai nasan me nakeji azuciyata idan da soyayyar mijina kadai ta zaunar dani gidanan datuni Na tsufa gidanmu inaso abbana yafahimci abinda nake gudu dayasa ban bishiba kiga yayana gasunan duka mazane babban shekarr shi shida wazan barwa su? Wazemin tarbiyarsu? Kakarsu data hanani yin planning yanzu tabi bayan danta batasonsu kokadan duk lkcn Dana kaimata su dukansu take kamar jakai kiga danta bashida tarbiya kokadan babu abinda yasawa gaba irin Neman kudi abincin dazamuci wuya yake mana inba yanzu daya yadda yake bani komai dakansa ba dukda dagishiri dazansa amiya shine yake debarmin adadin dayakeso kuma idan abincin beyi dadiba ya balbaleni da masifa, Allah yasoni hawan jini bekamaniba kigafa duka en uwana sun gujeni inason ganin mahaifiyata amma banida iko,haihuwa nayi amma bayanke dani bawanda yataba ganin babyn bakuma alamar za azomin barka yayata Dana tura mata hoton babyn ko reply Na Allah yaraya batayimin ba abdulmajid yajanyomin bakin jini agurin en uwana😭,
Dakyar Zainab tasamu ta rarrasheta,ki godewa Allah badee kin samu haihuwar shekarata goma sha uku da aure ko bari bantabayiba dagani har mijina lpyr my qlw babu yadda zanyi inason mijina bazan iya rabuwa dashiba nasan yanason haihuwa amma betaba chanjamin fuska ba ganin idan bansashi yayi aureba awaje abokanansa kokuma mahaifiyarsa zata sashi yayi auren kuma akwai en zuga inagudun su zugashi yajuyamin baya ganin nayi shekara bakwai ba haihuwa nace yakaro aure kila za adace matar ta haihu, yacemin shi bashida ra'ayin mata biyu nikadai yakeso zezauna dani saboda Allah kuma ga yayan yayyensa nan aisun ishemu har kararsa nakai gdnmu babanmu yakirashi amma zancen dayane baze iya karo aureba nikadai yakeso haihuwa ta Allah ce koda yakaro auren idan Allah besa yanada Rabin haihuwa ba bazetaba samun taba,
Badee inason yara sosae shiyasa nace zan koma makaranta nayi skul of nursing bayan nakammala degree Na seban nema aiki dashiba najira har nzama nurse nasan zanyita ganin yara a asibiti,
Yanzu matsalar danake fuskanta itace mamansa tasoma sauyamin bakamar da ba,yaranki sun burgeni sosae kuma Na tausayawa rayuwarki shekarunki sunyiwa damuwarki kadan,
Kema abin atausaya miki ne Anty idan haihuwar alkhairi CE agareki Allah yabaki,nikaina inaganin idan nakara shekaru biyu awannan halin to matsalolina kasheni zasuyi bansan wazan tunkara zuciyata tayi sanyiba damuwa tamin yawa bama kaina nake jiyewa ba yayana rkar rayuwarsu ta gurbace ina iyakar kokarina nagrayuwarsu ta inganta Anty don Allah kitaimakeni da maganin planning bawai nagaji da haihuwar bane inaso ne nadan huta har wayannan yaransu kara girma nasan insha Allah watarana zanyi alfahari dasu,
Amma kekam anyi sakarar mace sauna kuma Allah wadaran wannan mugun halin naki yanzu matar dabaki saniba kika zauna kina zubewa sirrinki?,
Basusan dazuwan hajiyaba sejin muryarta suakyi,gaban badee ba karamin faduwa yayi ba.
Nikaina nafirgita amma nadake sbd jarumta😎
En uwa semun hadu wani lkcn🏃🏻♀
[7/5, 8:08 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to u Anty billy❤
Page 14
Kekuma munafuka kinzo zaki hure mata kunne ko? Tun wuri ki kwashi kafafuwanki kibar gidannan irinkune sarakan zuga kinzo kikashe mata aure,
Zainab batace komai ba tamiqe tana murmushi,badee se anjima kinji nagode sosae,badee kam ba bakin magana se hawaye zuciyarta kuna take sosae anwulakanta mata bakuwa batasan yazatayi ba,
Bayan fitar Zainab hajiya takaaraso ta zauna itada wata fitsararriyar mata da alama daga kware tazo se kallon gidan take tana yatsina fuska irin kallon datakewa badee yayi kamada harara,
Munzo ganin jaririyane tunda ban isa akaimin itaba ninazo ganin ta dakaina,
Kiyi hakuri umma wallahi yau nakeda niyar idan yadawo daga office mukawo miki ita,
Harseda aka kwana? Aitunjiya yakamata akaimin ita amma dayake ban isaba seda ninabiyota dakaina safara'u karbomin ita nagani natofeta da addu'oin tsari tunba asa tabi sahun yayyenta ba yaranann dakike gani basa kaunata insunganni kamar sunga azara'ilu(wayannan mutanen basuda alkibla ko kadan inace ita take hantararsu harda duka?🤔).
Arnyi mata huduba ne?
Kanta akasa tace eh yayi mata jiya dadaddare yace sunanta Lubna,
Yadda hajiya ta zaro ido seka zata cewa akayi sunan babyn shegiya,
Yanzu sabon salo aka samu baza anemi shawarataba akasawa yarinyar suna? Lallai akwai abinda kikayiwa Abdul wannan karon dole Na tashi tsaye karki rabani dashi, da alaamr mamaki take kallon umman (metake nufi?),
Eh kikalleni dakyau bakar munafuka wacce tazabi namiji akan iyayenta aiba abinda bazata iyayiba,
Safara'u dake gefe tace wai dama mama wannance matar yaya Abdul? Eh itacefa kingantanan kamar diyar roko wannn aise zaman hakri tashi mutafi Allah yaraya tunda kinyi son ranki,
Nan wurin ta zauna ta hsarbi kukanta harta koshi kafin ta janyo wayarta tayi Kiran Zainab kalar hakurin databaa harseda yaso kular da Zainab din Anty kiyi hakuri kuma ban fasason maganin ba inda yadda zaki taimakeni kikawo min don Allah,
Babu komai kibari se jininki yadauke zansan yadda zanyi kuma akulamin da Lubna sosae kinji,
Insha Allah nagode sosae se anjima,
Har ranar suna babu wani chanji agurin majid danshi yace bayason taron suna dakyar yana share gumi yayanka rago daya ranar sunan bawani abin azo agani sukayiba sukadaine agidan daga yaranta se en uwansa daga kware basu wuce su shida suma banda habaici ba abinda suke mata agidan itadai iyakacinta dasu ido da aka shigo da naman kadan ta diba tamiqa musu sauran sukaiwa hajiyarsa batason fitina,
Daga haka rayuwarsu take babu wani ci gaba jiya iyau kalar ramar datayi kadai ya isa yanuna tana cikin damuwa gun Zainab kadai take samun taimako shima Zainab ta daina zuwa gidan sbd haukar da majid yai musu wai be yadda da itaba,
Yanzu lubna tana wata bakwai kome take taji muryar babanta zata rufe ido kota fara kuka lokuta dayawa yakeson daukarta amma bata taba yadda dashiba inkaga dariyarta to gun yayyenta ne ko mamanta,
Ba ita kadaiba har manyan tsoron babansu suke abdulrahim ne kadai yakedan jin sanyi tagefensa kuma har yanzu sunanan da yunwarsu abinci ba lallaine yake basu Wanda ze ishesu ba maganar aci nama batamazo kusaba sedai shi yasiyo yashige daki yaci abinsa badee batada halin Tara kudin sana'arta tasiyamusu abin marmari idan tayi ranar setayi regretting ga uban jaraba musamman yanzu dayaga andau lkci bataace ciki gareta ba se abin nasa yaakra kaimi,
Kuka kuwa yazama abincinta babban bakincikinta bewuce rasa en uwanta datayi ba har gidan yaya muktar ta tafi amma ko kallonta beyiba gashi tanason ganin mahaifiyarta amma abin yafaskara,
Tura abincin kawai take badon tanajin dadinsa ba sedon ganin Lubna tana rama sbd rashin samun isashen abinci damuwarta ta tashafi diyar bayan ta kammala dura abincin tasawa Lubna nono abaki harta kama sekuma ta gantsara mata cizo dasauri ya yakiceta tace,
Yaushe kika zama muguwa harda cizo haka kallon uwar tayi tabingire da dariya su abdulrahim suka kama mata sunata dariya batasan lkcn da dariyar ta kwacemata b tace Amma yarannan sedai nace Allah yashirya minku 😂😂.
[7/8, 2:15 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
A rayuwata ta duniya babu abinda Na tsana irin wulakanci wallahi ko wanda muka fito ciki daya yaimin wulakanci yanzunnan senayi sahur dashi nadau azumin shiga harkarsa Na tabbata babu writer dinda take yin yadda nakeyi wata sekiyi mata magana setai kwana biyu ta amsa shima se idan taga damar amsaki ne amma ni kowa yazo jikin nabari nake kulashi dankar ace nai wulakanci amma dukda haka ban tsallake ba seyanzu nagano abinda yasa ake cewa writers Nada jijjidakai🤔.
Akace shiru shiru......?😕.
Page 15
BAYAN SHEKARA 5
Tun lokacin da safara'u ta zo gidan bayan anhaifi Lubna tamaida gidan digan zuwa ba'a wata daya batazo sokoto ba kuma tana zuwa se gidan Abdulmajid take sauka intazo kwarkwasa da iyayi bawanda badee bata gani ga yaran tayita hantarar su duk lkcn da tazo basa sakewa,
Kusan sau uku ana kawo kudin aurenta setace ta fasa kuma hajiyar majid ke daure mata gindi acewarta da ayi taki zama gwanda kar ayi tunda tace yanzu tfasa dole akyaleta babanta kuma Na kamar hoto haka yake,
A haka har Lubna tai shekara biyar babu wani chanji duk yadda badee tayi Dan ta shirya d en uwanta da mahaifanta Abu yakiya amma dukda haka batayi kasa a gwiwa ba haka ta shirya taje gidan kasancewar yaran duk suntafi makaranta,
Mukhtar tasamu akofar gidan yafito tunkafin takaraso yafara magana,
Kin tabbatar kinbaro gidan mijin nakine Dan wallahi matsaawar bakin baro gidansa bane karki kara zuwa nemanmu,
Don Allah yaya kasaurareni kutausayamin kodan yaya na bazan iya barinsu ba don....saukar Marin da taji ne ya katse ta,
Tun wuri ki kama kanki kibar kofar gidannan wallahi,
Ko abinda majid ke mata betaba bata mata rai irin haka ba ita da gidan ubanta idan shine bayason ganin ta bazataje gidansa ba amma sbd me ze hanata sasantawa da iyayenta suma da laifinsu kusan shekara nawa basu taba nemanta ba amma daga yau tadau Alukawarin bazata kara nemansuba sedai idan sune suka nemeta,
Tfiya take dakafa harta isa gida sbd yadda zuciyarta kekuna bazata iya magana ba ko sallama batayiba ta shiga gidan wunin ranar akwance tayishi dakyar tasamu ta daidaita kkanta,
Kwata kwata abinda yake damun majid be wuce yadda Lubna ke kin yadda dashi ga besan ya akayiba yakesonta sosae ba tun tana karama sosae yakesn daukarta amma yana zuwa kusa da ita zata kwalla ihu yanzu kuma datake tafiya kowasa take daga tagansa take guduwa ko yadda take ganin yayyenta nayi idan yadawo baba sannu da zuwa ita idan yadawo kokallonsa batayi guduwa ma take,
Ikon Allah kawai take kallo yadda majid ya Dora tsararren gini daga gefe tanamamaki sosae,
Yauma kamar kullum yagama sauke mata jarabarsa take tambayarsa ko en haya zesaka asabon ginin,
Babu ruwanki banason tambayoyi ki zubamin ido kiga yadda zanyi komai sekin sanine,
Shiru tayi batace komaiba,
Shima bangarensa mamaki make shekara biyar bawani mataki bawani ciki amma dai shiyafison haka Dan wani haushi yakeji idan yashigo gidan yagansu gasunan bi da bi,
Tunda ta tashi yau takejin gabanta na faduwa addua kawai take hartadan samu sassauci bayan isha karfe tarada hartadan gota taji shigowar motoci bata kawo komai arantaba tana zaune seji tayi anata rangada guda sekawai ganin mutane tayi a palonta da mace agaba tarufe fuska da mayafi,
Shiru kawai tayi tana saurarensu badan tana fahimtar me suke fada ba,
Wata tsohuwa er kili bibi tace to badee'a ga amarya nan munkawo bawai munbaki amanarta bane sedan mufada miki kikama kanki sannan tafi karfin asiri yadda kikaso kiyiwa majidu manta uwa Allah be yadda ba yakubutar dashi to wannan ma tamiki yawa sedai kiyiwa wasu bakar muna fuka,wata mata dake gefe ta takalleta sheqeqe tace,uhm kuga mace har mace amma se mugun hali ko kula damiji ba a iyaba duk Wanda yasan majid da baze yadda shine yanzu ba ga haihuwar kamar tunkiya keko er soyayyar nan da miji damata ke kwasa bakyayi sbd kincika gida da yaya kamar gidan reno gasunan jeka inbika to yanzu dai ga wacce zata kula dashi nan munkawo se kibi ahankali,
Kukan ma kin zuwa yayi har suka gama cin zarafin su suka fita bata Ankara ba,
Batun majid yashigo bema tasoba yadda taga dare haka taga rana, ita kanta batasan metake tunaniba, washe gari ta shirya yara taturasu islamiya tun karfe takwas tana nan zaune a apalo Sega majid,
Rana ta farko dataji bata kaunar abinda zesa ta kalli fuskar majid batason ganinsa gaba data,
Nace ki hada mana abinkari kinsan amarya ga gajiyar biki ga gajiyar jiya,har yakaraci surutunsa ko kallonsa batayi ba,
Seda yazo saubiyu kafin tasamu bakin magana,
Majid menai maka Dana cancanci wulakanci irin wannan?koda ace mata uku zaka auro baynni yakamata kafadamin bazan taba hanakaba balle nace zan tashi hankalina akanka dan nasani yanzu banida wani gurbi azuciyarka bawai kawai INA zaune azomin da amaryarkaba ko musulunci be lamunci hakaba anya majid zaka iya da haqqina kuwa?zancen nagirka muku breakfast bema taso ba inace bauta tazoyi? Tunda tayi ta jiya dadare aitafara kenan Dan haka seta fito da kanta tayi girkin ninayi nawa tundazu kuma nagaji duk abinda zakayi bazan hanaka ba akwai ranar kin dillanci,
Tabarshi tsaye agurin tunda yake bata taba gayamai magana ba seyau dole yadauki mataki.
Babu yadda zasuyi dole amarya tafito tayi girki a gefanta dakyar ya lallasheta tafito wai ita tagaji,
Badee bata gane wacce amaryaba Seda takwana biyu tafito rakiyar miji badee taganta wato safara'u aka San yadda akayi aka Liqa mai.
Kuyi hakuri da wannan yau dakyar Anty bily tabarni nayi wannan😏
[7/10, 2:02 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Wannan shafin nakine Sha'awa Ibrahim(wai yaushe zaki cigaba mana da safiyyah ne? Wasu harsun manta dashi🤔).
Abin duniya ya ishi badee tarasa inda zata saka kanta majid seda yai sati biyu dakin amarya ko raba musu kwana beyiba tun tana zuwa dakinsa takwnta zaman jiran zuwansa harta dena Dan yatattara yakoma dakin amarya yanzu amaryar tafi wata a gidan amma kokallon gefen ta bayayi sedai ta hango fitarshi shikadai kokuma da amarya babu yadda zatayi sedai tasha kukanta ta koshi,
Yau abdulrahim ya tashi ta ciwon kai ko makaranta bejeba, kaje gun babanku kila ya saurareka danni konaje ba kulani zeyiba, jiki a sanyaye ya yafara tafiya yana tunanin yadda zeyi ko jiya dayaje korosa suka yi wai yashigo da kazaman takalminsa alhali babu komai a palon se wasu kalar kujeru da ba mahadi ma Dana mamansa kuma palon ko shara babu amarya an iya gyaran jiki amma ba a iya gyaran muhalli ba,
Tun kafin ya kwankwasa kofar aka bude babansa yagani cikin shirin zuwa office,
Baba ina kwana?,lpy lau ya akayine? Kudin magani nazo kabani kaina keciwo,waikai yaushe zakuyi lpy kuda uwarku?kullum cikin matsala?Kodai ita ta turoka da gangan baakayi kamada Mara lpy ba,hannunsa yasa yazaro nera goma gashi kasiya paracetamol kasha,karba kawai yayi yana mamakin yadda yabashi nera goma kokunya babu, yakasa tafiya se kallon kudin yake maganar safara tadawo dashi daga tunanin dya tfi,
Strong ya maganar kudin damukayi bakace komai bafa se shirin fitarka kake kuma nafada ma yau ankeso natura mata,irin yadda take maganar kamar zatayi kuka tana kara shigewa jikinsa shikam Dan yaro kallonsu kawai yake,
Sweety kinsan bazan hanaki ba kibari bazan dadeba zandawo sena Ciro daga banki,Na wane kudin ma kikace?
Dubu hamsin dabiyar ne, OK sena dawo maza kikoma daki wannan kyau haka ina kishin yadda bishiyar nan yazo take kallonki, Seda taimasa bye bye sannan tashige ciki baban ma gaba yayi sukabar abdulrahim tsaye agurin,
Koda yaje yakaimata kudin bakin ciki yahanata magana, sekaje kasiya maganin yafi kaita zama daciwon kai gashi kun kusa fara exam (yana jss1),
Shigowarsa gida kenan yasami Lubna tana wasarta tunda ga nesa yatsaya yana kallonta sosae take burgeshi bayason taganshi tagudu Dan baya tuna ranar da suka hada ido ta tsaya kokuma taimasa magana,
Jikawai tayi an dagata sama Seda tatsorata ta kwalla kara,
Lubnatyn baba ninefa yafada yana juyo da Ita,
Cikin hausarta dabata gama fita tace nika sauke ni kaiba babana bane kuma ni sunana Lubna,
Meyasa kikace niba babanki bane? Yadda take ihu seya sauketa yasa shi ajiyeta agabansa,
Kawata ramla kullum ina ganin babanta yakawota da mashin dinsa kuma yazo daukarta amma ni sedai mamana ta rakani da kafa ita tana sona,
Yadda take maganar babu alamun tsoro kokuma shakka atareda ita cikin idonsa take kallonsa tana fadamai abinda ke ranta,yajima tsaye yana kallonta wasanta tacigaba tana jira yazo ze tabata tabballa dagudu sbd tga yadda ko takalmansa su Abdul suka taba yana jibgarsu abdulrahim kadai yake dagawa kafa,
Tana zaune a palo tana goge kayan yaran gasunan dayawa da alama tajima tana gugar,
Kalli tarin tulin kayan yara nan amma duk sun soma kodewa abdulrahim kayan ma sunsoma yimasa kadan bansan yazanyiba ubansu bashida kula kalli yadda yaimasa wulakanci kwanaki maganin nera goma haryaushe yaro zefadama bashida lpy kabashi kudi awulakance? Nidai Allah yataimkeni da yarannan dole nasan....
Matsalarki kenan rashin godiyar Allah duk abinda nake miki keda yayanki bakya gani dankinga nadan sassauta miki ko?,
Azahiri yakona mata rai sosae hakan yasa taso gasa masa magana se wata zuciyar tace ta kyaleshi,
To Allah dai yakawomin me sharemin hawayena kwata kwata banida damuwa safara'u ta kiyaye komai akaina amma ke duk ranar Dana rabeki sekin bata min rai seki zauna dakeda yayanki kukarata kuma daga yau karki kara turamana yaranki suna damunmu dannasan da gayya kikeyi,
Wannan karon idan tayi shiru ya shammace ta shiyasa ta shirya fadamai magana amma kuka yazo mata ga bakin cikin kishiya miji yawulakanta ta agabanta,
Abdul ni inada damuwa sosae nakeda Ita,harkanada bakin budewa kace ina samaka damuwa kasani kalar damuwar danake ciki babu adadinta kuma kaida mahaifiyarka ne sila,
Mahaifiyata tafita abaknki,yaushe zata fita majid kaima se idan kaki gaskiyane Hajiya itace silar komai sonkai yamuku yawa kanku kadai kuka sani bakwa tunanin halin dazan shiga ko yarannan shiyasa kukayi wasa da rayuwata yadda kuke so kun rabani dakowa nayi mamaki dahar yanzu bakin cikin dakukasamin kaida Hajiya....
Tasss taji saukar mari,badee rainin haka yakai tsakanina dake? Zankuwa dauki mummunan mataki akanki wallahi,
Betaba dukantaba seyanzu da yasamu jarababbiya irinsa duk kalar rashin kunyar dayake yiwa hajiyar seyanzu yasan yahana a galaifinta,
Bakin cikin dakuka samin be kasheniba shine harda duka majid?babu komai rayuwa ce kuma Allah yana nan yana kallo danshi ba azzalumin sarki bane akwai ranar kin dillanci ranar da zanyi alfahari da y'ay'ana kuma lokacin nayi maka nisa nisanda gani kusa dakai.....sekuma tai shiru basena karasaba inda rai da lafiya zaka ganewa idonka,
Lubna tashigo tagudunta mama kidaina kuka kema wannan baya sonki ko kamar yadda baya sona nida su yaya abdulrahim ko?dazu Na fada masa ai kuma kice yadaina shigo miki daki tunda baya sonki,
Hawayen idonta tagoge tanajan hannun Lubna,zokiga yadda ake guga domin kikoya ki hutar dani watarana,har lokacin yana tsaye kuma Lubna batabar zancenba sosae tagyara zamanta tace,
Ki kyaleshi mama muma BAMA SONSHI tafada tana kallon cikin idonsa,
Sosae yafirgita dajin kalamanta,wannan kodai aljanu gareta yafada azuciyarshi yalura wannan ba kamar uwarta da yayyenta takeba.
🤔🤔🤔 (akwai matsala kenan),
Kuyi hakuri dajina shiru kwana biyu nima ba ason raina nake hakaba.nagode
[7/12, 10:01 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Wannan shafin nakine maryam Yusuf Ina miki fatan Alkhairi arayuwarki❤
Page 16
Baby nikam wai bazakaje kwana dakin maman Lubna ba? Tunda fa nazo baka taba kwana dakin ta ba,
Zaune ya tashi yana kallonta,bakiga yadda ta Tara yaya ba yaza ayi nakwana dakinta?,
Amma dai kasan babu dadi kar ace nice nahanaka kaje koda yaune kadai ne,
Nifa jarabar nan tata ce bazan iya da itaba kuma dayara zamu kwana adaki?
Ai kanada daki kuje can mana,seda yadan yi shiru kafin yamiqe yana kwasar wayarsa yarufe system dinsa,seda safe yafada fuskarsa a hade,
A zahiri bayason ma kallon fuskar badee amma azuciyarsa yana azabtuwa darashinta besan meyake damunsaba ga wani tsanar yaran maza daya tunkaroshi jiyake kamar yakamasu yaita jibga sekuma tsoron Lubna dayake wani kalar Abu yake hangowa a idonta dabesan komeye ba amma komenene yatabbatar da me girma ne,
Tsaf tayi shirin kwanciya tagyara yaran ta abdulrahim da abdul'azeez sune manya ta bude musu dakin dake cikin palonta daban ta gyara musu dukda bashida wani girma amma baze matsesu ba lkc yayi daza araba musu makwanci,kullum seta saka su sunshare dakin sbd batason kazanta kokadan,
Sauran yaran kanana tayi musu shimfida adakinta bayan takaisu sunyi fitsari,
Ita takwanta da Lubna akan gado suna hiransu Dan Lubna badai surutu ba har bacci yadauke ta tana jikin mamanta,
Ke kisame ni adakina inajiranki,shinen kawai abinda ya iya fada yafice,
Bin bayansa tayi da kallo,wannan mutumen wani show zekara hadawa bari naje naji dame yazo yau,
Daga kofa ta tsaya tace malam gani,kikaraso mana keda za ataimaka kin wani tsaya daga kofa,
Kamar ya?wane irin taimako?,
Dallah malama kikaraso jarrabar bata isheki bane da kika tsaya acan kina iyayi,
Ahankali takaraso cikin dakin,dani dakai waye jarababbe?kai naji ma inada jarabbar amma daga yau nayafe indai ta gefena ne Allah yabani hakuri,
Tnangama fadar haka ta kama hanyar fita daga dakin zuciyarta Na wani irin kuna tayi abinda bata taba yiba Allah ka gafarta min wato ma nizai taimakawa ko ai wallahi yanzu bakina yabude,
Lokacin dayake kallon fuskarta seyaji kamar yaimata mugun bugu seta dauke wuta, amma tana juyawa yaji babu abinda yake muradi kamarta,kardai dagaske matarnan tafiya zatayi be ankaraba yaji ta bude kofar da azama yadamqota yadawo da ita bayaso yaji abinda yakeji idan yakalli fuskarta dasauri ya kaisu gado bayan yakashe wutar dakin duk iya kokarin ta takwace takasa shiyasa tabarwa Allah amma bada son ranta ba,
Kuka take harda sheshsheka rabonta dajin haka tun haduwarsu ta biyu wannan mugunta yai mata kuma se Allah yasaka mata tundai ai daga baya tahakura bata hanashiba shine ze mata wannan aikin,
Malama seki samu damar tashi kike wani kukan munafurci kamar wata amarya nikitashi kifice tun bankasa jurar kukan nan naki ba na doddokeki anan gurin,
Zaninta tadaura tasa hijab dinta kafin tamiqe tsaye dole ta jure wannan zafin tasani baze jimaba ze tafi haihuwa bakwai aiba wasa bane zafin mutuwa kadai yarage taji,
Allah sarki nida nakeda danda yabawa shekara goma baya ni ake duka yanzu kuma akan gaskiyata nake ko abdulrahim yawuce duka akan wasu kanannan laifuka balle nida nahaifeshi Amma zankara fada maka Allah yana gani kuma namiqa dukkan lamurana da damuwata agareshi zeyimin magani kuma seya sakamin nida yayana,
Bata jira jin mezece ba tafita,
Kallonta yake tafiyarta ta chanja dagangan yaimata haka sbd tabarshi shiyake kidansa shiyake rawar sa kokadan beji tausayinta ba amma fa he's more than satisfied badeee capital A ce, lol
Ruwan zafi sosae tayyi wanka dasu kafin yakai yaranta masu fitsari sukayi tagyara musu kwanciya,
Kusan makara sukayi yaran ko wanka basu samuba suka tafi makaranta,
Abangaren safara'u kuwa wani dadi taji domin tasamu yin abinda malam yace ba ita take zuwa mahaifiyarta ke zuwa seta karbo mata mugun abu ,
Wannan karon yace kasan gadonta gefen damijin ke kwanciya anan zata yi rami ta binne laya,
Haka kuwa tayi ta daga katifa tayi yanda yace,murna take seyanda tayi dashi kafin taje kan yayansa,
Dayamma suna zazzauna ita dayaranta tana yiwa Lubna homework se ga Abdul ya shigo bayan safara'u tagama zugo shi,
Baby Dan Allah ka karbomin Lubna mana nasan kanada iko akanta kadaici yamin yawa yadda nakesonka haka nakeson yayanka sedai su ko gaiaheni basayi,
Cikeda kissa take magaanr tana gwadawa ne taga aikinta yayi,
En matan baby kwantar da hankalinki koyanzu kikeson Lubna tadawo gunki zata dawo barikiga ina Zuwa,
Malama hadomin kayan Lubna zata zauna hannun safara'u zaman kadaici yai mata yawa,
Tasani sarai Lubna bazata taba yadda ba setace,gatanan mana idan tayarda nimeye nawa aciki ammafa seka tambayeta idan bataso bazaka takurata ba,
Sosae yaji haushi, ai umurni ne Dan haka baseda yaddar taba,
Lubana najin haka takoma jikin uwarta, mama kice yakyaleni nafison muringa kwana dake bazan bi waccenba tayi nuni da kofar dakin safara'u,
Tana kuka yana janta tana tirjewa dayaga tacika taurinkai seya fara dukanta kamar wata babba ita kanta ta tsorata dole tahakura tabishi itadai maman kallonsa kawai take,
Tananan zaune segashi yashigo yana huci kamar wani zaki,
Zaki hadomin kaynne kokema se kinji bugu,kinmaida yarinya bata jin magana har ubanta yace tayi Abu takiyi wallahi .zakija Na illatata,
Shiru yai ganin tamikomai jakar kayan yakarba yawuce azuciyarta tace lallai maza azzalumai ne betaba sanin shi ubnta bane seyau, nasan dole zata dawo indai Lubna ce,
To ensamari kuzo kubiya karatu kuka tsaya cirko cirko kuna kallona,
Abangaren safara'u kuwa tsalle take tana murna lallai abin indai hakane cikin kankanin lkc zata tarwatsa gidan dama ta tsani lubnar nan me ido kamar an soya wake,
Lubna kuwa akasan tile daya jefar da ita anan ta gama kukanta bacci ya sureta sukayi gabas😂
Kuyi hakuri u know fiyya is always lazy🙈
[7/13, 4:33 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
This page goes to all the active members of taskar billy galadanchi #one love❤ you made my day😂😂.
Page 17
Ni yarinyar nan bansan halin wa tayo ba shegen taurin kai , haryanzu fadan be gadi karewa ba kenan,
Koda yayi taurinkai bekamata ka doketa irin haka ba kasan raba da da uwa se Allah baby,
Kekikasan wannan ko uwarsu taimin irin haka ba Abu bane me wahala aguna nai mata duka ba,
Naji dai nikam banason duka kalli yadda kasamin yarinya bacci akasan tile haka aise sanyi yakamata,daukar Lubna tayi takaita dakinta har kan gado,
Lubna anji jiki har lkcn kwanciyar su bata farka ba,dayan dakin safara'u takaita Dan bazasu kwana daki daya ba sedai tabar kofa bude koda ta tashi,
Ina Lubna ne?yatambaya lkcn dayake shirin kwanciya,
Tana can dakin amma nabar kofa abude koda ta tashi kasan babukyau kwana da yaro daki daya,
Bece komaiba ya kwanta,
Cikin dare Lubna ta tashi tana kuka tayi kofar Palo kuka take tana dukan kofar,
Mama zoki tafi dani dakin ki banason nan bazan kwana ba mama kizo kidaukeni karya kuma dukana,
Tsawa ya daka mata,ke maza kikoma kikwanta kona kara zaneki wallahi,
Nace maka nafiso nakwana wurin mamana banason nan dakin,sena kuma dukannaki kenan,bata kaunar ataba lpyr jikinta shiyasa tafara tafiya ahankali suna biye da ita takwanta kan gado tana kuka ahankali,safara'u ke shafa bayanta don munafurci hartakoma yin bacci,
Da asuba safara'u taiwa dakin tsinke bayan sun gama sallah,tasamu Lubna akwance idonta arufe ruwa ta debo ta daga Lubna ta zuba kafin tamayar da ita yadda take,
Baby wai dama yarinyar can tana fitsarin kwance ne?,ban taba jin dakin dakin mamanta yana warin fitsari ba gsky batama yi inndai tayi yau iskanci ne kawai kuma sena zaneta,
Sedai kar akuma kam kuma meyawa tayi banmasan yazanyi ba amma duka bashine magani bari natasheta naimata wanka,
Yana tafe tana bin bayansa nidai karka daketa baby banason duka,
Aidole tgane kurenta da gangan tayishi sbd kokadan mamanta bata shiri da fitsarin kwance,
Lubna tana kwance sejin duka tayi afirgice ta tashi tana kuka,wayyo Allah Na menayi ?nibanyi komaiba ake dukana?,mamaki yakama shi yadda kokadan bakinta baya mutuwa,
Dan iskanci shine zakiyi fitsari akwance air bakya yiwa uwarki zaki gane indai haka zakyi muzuba nidake,
Seda yaimata duka da sleepers yakyaleta acikin kukan yaji tanamagana tana kallon safara'u dake gefe tana murmushin jin dadi,
Ai malaminmu a islamiyya yace zalunci babu kyau Wanda yayi kuma se Allah yasa shi cikin wutar jihannama yakonashi,😭
Jan hannun safara'u kawai yayi suka fita daga dakin,
Anan taci Ku kanta ta koshi hartagaji tayi shiru tana tunanin mamanta,
Abangaren badee kuwa dakyar tai bacci lkcn datakejin kukan Lubna kuwa itama seda tayi kukan Tace ,Ya Allah kana ganin abinda bayinka suke mana ya Allah kataimake mu😭,
Lubna tashi ayiwanka lkc atafiya karki letti a a makaranta,
Batareda tayi magana ba ta miqe,bayan tayimata wankan tashiryata cikin uniform tabata tea kadan tasha tace takoshi,
En matan baby naje naga mamana🙄tafada tan kallon safara'u,
Cike da mamaki takalleta kafin tagyara mata ba Anty zaki kirani ba en matan baby ba kinajina kokuma nasa babanki yazaneki,
Ai haka naji ya kiraki dazu,kiyi shiru kije gun mamanki tabaki lunch box Dinki nibanzan iya girki yanzuba kice tasaka miki abincin data girka,
dagudun ta tafita,
Tana zaune seji tai anrungumeta sosae murmushin jin dadi tayi dantasan lubnarta ce,
Mama shine jiya bakizo kin kwaceniba yaudasafe matarnan tasaya zaneni wai nayi fitsari akwance kumafa itace tazuba ruwa agurin,
Kiyi hakuri muje narakaki makaranta,uhm tace kiban abincin dazanje dashi ita bazata iya girkiba wai,ai yananan nahadamiki,
Cike dafarinciki ta rakata ta dawo,
Bayan tadawo daga makaranta ta hadu da babanta a harabar gidan sauri sauri take tafiya Dan bataso ma yai mata magana kuma yau bazata kwana gun wannan antyn ba,
Lubna ta,yfda yana tahowa kusa da ita yakarbi lunchbox dinta yanabudewa Ita dai batayi magana ba,
Iyye Lubna er gayu yau da Irish akaje makaranta lallai sabuwar mamanki naji dake,
Mamana ce tabani ba wannan antynba,nikam bani abina nakara sa cinyewa,
Gani kawai tayi yawuce fuuu bayan yamiqa mata lunchbox dinta,
A tsakar gida yasameta tana wanke wake yau alala take Sha'awa ,kaudin meye naki nabawa Lubna abincin zuwa makaranta iye kobakya jina,ita taturota wai nabata abincin,karya ne bakar munafuka nakara ganin kinmin irin wannan kaudin kiga,
Wai majid yaushe lubnar tazama yarka inace duk kabarni da lalurar su tomeye naka natada jijiyoyin wuya kana nufin zaka fara nunamin iko akan ya....
Marin dayai matane yasa t yinshiru,
Lubna takaraso kusa dasu tace, mama mubar gidannan tunda dukanmu yake mukoma gidan babanki dakike bani labari,
Bata amsata ba tashige dakinta tana kuka me ban tausayi harseda taji kanta ta yafara ciwo kafin tahakura,
Nayi danasanin rashin binka babana gashinan kungujeni dalilin haka rayuwata tana cikin tsaka mewuya nadauki soyayyar miji data yaya gashi tana wahalar dani banida mafaka dole senan gidan majid idan nafita bansan inda zan dosaba waxe karbeni da yaya haka kuma bazan iyabarinsu ba rayuwarasu ta lalace, Allah ka kara bani hakuri da juriya Ameen Lubna dake gefenta tashare mata hawayen fadar ameen dukda bata fahimci komaiba.
Feeyah tayi kokari yau💃🏻💃🏻💃🏻
[7/16, 9:43 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Sadaukarwa ga dukkanin masoyana Allah yabar so dakauna ameen❤
0 comments:
Post a Comment