Wai wannan wane irin iskanci ne Lubna kitson ma kice bakiso?haka za abarki dakai kamar mahaukaciya?,
Ni bance banason kitso ba Na mamana nakeso wannan bata iyaba kuma da zafi,tafada tana kara sautin kukan Ta,
Wane irin zafi zaki zauna ne kosena jibgeki yadda muka saba?,nikam banaso zanje gun mamana tayimin nata babu zafi,
Haushi ya kamashi yasa takalmi yaimata duka safara'u ta matseta cikeda mugunta ta taimata kitson kuma batama iyaba (kunsan kitson Dan koyo yafi komai zafi haka maman nu'aym taimin lkcn datakeso ta iya kitso ina gudu tana kamoni sun rankwashi ba abinda banshaba😂),
Badee Na zaune korido tana jiyo kukan Lubna babu yadda zatayi mamaki take yadda tanaji tana gani ana so arabata da yarta,
Uban waye yashafamin maiko ajikin fenti? Ko kallonsa batayi ba yadda yazo yana mata ihu akai,wai bakwa jinane? Nace uban waye acikin Ku yashafamin maiko ajikin fenti?,
Miqewa tai tafita daga cikin yaran takoma gefe,wani mugun kallo daya bita dashi tai kamar batasan me yakeba,
Ke kuma meye nakomawa gefe?,cikeda rashin kula tace, naji kace ubanwaye shiyasa nadawo gefe kazagesu su kadai Dan ni bazaka zagi ubana ba,
Sosae yaji haushi shiyasa Yakoma kan yaran kafin yadawo kanta,
Bazaku fadaba kuka zubomin ido kamar Na uwarku? Shiru yaran sukayi dama gasu ba magana sukeyiba,haushi yaturnuqeshi,
Takan abdulrahim yafara yaimasa duka sosae kafin yajanyo abduljabbar badai sokuke Ku lalatamin fentiba kunkwaso mungun halin uwarku ko? Itadai tana tsaye tana kallon ikon Allah yana zuwa kan abdulazeez yaruga ya kankame uwarsa,mama kibashi hakuri bani bane karya dake ni don Allah,
Tayi mamaki sosae ganin yadda majid yayo kansa ze dake shi,
Dakata malam badai dukansa za kayi ba yazo jikin uwarsa? Toko mutuwa na kunyar idon mahaifi Dan haka bazaka dake shi agabana ba seka kara gaba idan ka hadu dashi awaje koyankashi zakayi gaka gashi,
Ke har kinada bakin magana matar databar iyayenta tabi namiji mezata yi taburge mijin kuma mace kamar akuya se haihuwa aure ko shekara Tara beyiba haihuwa bakwai Dan ma Allah yataimake ni daya ya rasu,
Sosae zancensa yataba kahon zuciyar ta amma tadake tagano majid danyaga tana masa shiru ne,majid bansan ka zama Dan dauduba seyau seka bari waccen uwar daka tafadi wannan bakaiba,kuma zancen haihuwa dakake fada da nice kai tun dakaga ina kwasar cikin seka daina raba ta kaga basena kwashi cikin ba,jabir kuma ina rokon Allah yasa me cetona ne tunba yauba nasan bakayi bakin cikin mutuwarsa babu abinda yake bata min rai irin nabude idona naganka agabana waikaine uban yayana,
Batajira yabata amsaba tai shigewarta daki jitake inama tanada wurin zuwa daba abinda ze hanata barin gidan majid,
Bangaren Lubna kuwa taci kuka harta gode Allah,
Tana zaune agefe tana kallon safara'u dake kallo tace,
Anty don Allah ki bude min kofa naje inyi wasa,
Wasar uwarki?kice wurin iyayi da Gulma zaki tunda anriga ankoya miki shegen iyayi kamar ba er shekara biyar ba,
Mamana tace Gulma bakyau kuma bata koyamin ba Dan Wanda yake Gulma dashida me zalunci duk wuta za a saka su kuma wutar Allah zafi gareta,
Cike da yarinta take maganar kuma iya gaskiyarta take fada,
Dallah daga can babu inda zaki dauko tsintsiya kisharemin palonnan tun shekaranjiya kikejin kasa da datti idan kintaka amma dayake kinyo gadon kazanta bakisan koda wasa kice zaki share ba,
Mamana tace zata koyamin shara amma sena kara girma idan nakai girman abdulkadir,
To ni bazan jiraba maza jekidauko tsintsiya tunban jibgekiba wallahi,
Ganin dagaske take yasata shiga kitchen tadauko,kwata kwata batasan me takeyiba idanma taga abin wasa seta ajiye sharar se taji safara'u ta yimata tsawa kafin tacigaba,
Anty nagama inje inyi wasan?tafada tana leqen fuskar safara'u,
Kitchen zamu shiga har girki zaki koya,tafada tana jan hannun ta suka shiga kitchen,
Anty mamana tace zata koyamin girki amma sena kara girma don Allah kibarni inga mamana,takarasa maganar tana kuka,
Babu inda zaki,tunkafin tarufe bakin ta Lubna tafara ihun kuka tayi juyin duniya taki yin shiru, karshe dai ta kyaleta tace zamu hadu dake,
Washe gari Lubna tana bacci dukan da majid ya sabayi mata yatasheta ga baccin yamata dadi Dan kwana tai kuka ita se wurin mamanta zata kwana,
A firgice tamiqe zaune tafara kuka,indai bazaki daina mana fitsari akwance ba wallahi na dinga jibgarki kenan,
Dagudu tafito daga dakin taci Sa'a kofar abude se part din mamanta ta sameta tana shara kafin ta ankara majid ya damqota yahau dukanta tun tana iya kuka har ta kasa itadai badee se kallon ikon Allah take yadda yahaukace yana dukan Lubna kamar yasamu wata babba koda ace babba ce mace bata cancanci irin wannan dukan ba balle Lubna dabatasan komai ba,
Ganin daya yi tazube akasa ko numfashi batayi yasa yadaina dukanta yafara Dane tabarmar kunya da hauka,
Zoki kama yarki gatanan tasuma kinkoya mata munafurci komai setace ke tahanamu bacci ta hanamu hutawa wallahi wata rana sena illata ta kuma tana farfadowa kidawo da ita gun safara'u,
Idonta dasuka chanja kala ta dago tana kallonsa dasu,
Wallahi majid indai kaga Lubna takoma gun waccen algungumar matar taka to bana doron duniya kadaina wannan tunanin kuma kacigaba dadukansu haka ranar daka kashe daya sekayi sunan ka kashe danka na tabbata zakayi bugun gaba dahakan,
Harta juya zata shiga daki bayan ta dauki Lubna tajuyo,
Kacewa safara'u ta hado min kayan diyata Dan bazan bari takoma ba.
Don Allah kuyi hakuri darashin jina kwana biyu nima badason raina hakan yafaruba,ina fata zakuyimin uzuri?🤗😍❤
[7/17, 8:23 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Wannan shafin nakune matan gidan homel&SophieG novel group nagode Allah yabar kauna ameen.
Page 19
Tsaya wa yai agurin kamar andasa shi Zuciyarsa namasa zafi jiya ke kamar yaje yaita dukanta seta daina numfashi,wato shi zata gayawa magana irin haka?Ashe garada datake kyaleshi akan yanzu datake maida masa da magana?lallai dole yasan yadda zeyi da ita inbahakaba renin zewuce wuri idan takama ko korarta ne yai itada yayanta dole yayi sbd yanzu babu abinda ya tsana irin ganin su,gajiya yai da tsayuwa yawuce yana hura hanci,(daga baya kenan),
Dakyar tasamo kan Lubna ta farfado tun lkcn kuma take kuka tana rarrashinta har tagaji tadaina ta zubawa sarautar Allah ido,
Nidai kaje kadawo da Lubna ta,tafada tana tunzuro baki,ki kyalesu nifa koson ganin yarinyar banayi wallahi wani Abu nakeji inasonta sosae azuciyata amma banaso naganta kodan tanada taurin kaine,
Bakaramin dadi tajiba Dan dama haka takeso,shikenan tunda uwarta tanunamin ita tahaifeta,
Kiyi hakuri kinji en matan baby,zomu kwanta kardamuwa tahnaki bacci,
Washe gari Sunday bayan fitan majid yatafi kasuwa safara'u tafito Neman fada, badee nawanke uniform din yaran bayan sun tafi islamiya Lubna CE kadai a gdn ganin har yanzu tana wasu en firgice firgice yasa bata turata islamiyan ba,
Sannu bakar munafuka to kin karbo yarki sae me?,
Nakarbo yata sekuma shikenan babu yadda za ayi Dan bakukukamin naqudarta ba dazan zauna inakallo ana jibgarta kamar jaka sekijira idan kinhaifi naki kibashi yadaka yadda yakeso badai nawaba,
Angaya miki kowa irinki ne?kamar wata dabba kikesta sako yaya,Toni ba jahila bace senagama gurje amarcina koda zan haihu balle ni wannan baya cikin tsarin rayuwata, haihuwa bakwai ashekarun dabasukai gomaba gida yakoma kamar gidan Reno,
Babu jahili dayawuce Wanda yake tsarawa kansa abinda ba Allah ne yatsara masa ba kuma haihuwa baiwace ki jira ranar dazakiso ganin yayanki amma lkcn yakure miki Niba shashasha bce inada aikin yi idan kin gama surutunki sekin kara gaba,
Allah yawadaran naka ya lalace ni ina zaune da iyayena lpy Nafi wacce tazabi tabi namiji akan iyayenta kuma Na mijin ma batada daraja a idonsa amma dai wallahi anji kunya,takarashe maganar tana karkade kugu,
Kekika damu da wani miji ninan zaman yayana nake bazan yadda nabarwa ballagaza irinki suba Dan bazafin haihuwa kika saniba kuma banso kikoya musu muguwar tarbiyar da tsohuwarki takoya miki tunda har tsohonki bata bariba yanaji yana gani ana abinda ba daidaiba amma be iya magana nikuwa iyayena zaunensu suke qlw,
Sallamar majid suka jiyo yadawo kila koyai mantuwa ne,
Take safara'u tafara birgima,wayyo ni Allah Na shiga uku na lalace,
Aidasauri yazo yarungumeta yana jin Ku kanta har zuciyarsa,
Lollipop dina ya akayi ne?,
Matarka kemin gorin haihuwa kuma harda marina tayi kilama kunnena yadaina ji,
Babu wani bincike yahau dukan badee,ai gara ita akanki inaga sena illataki zaki gane kuskurenki abin naki yawuceni haryakai kan baby na to wallahi kindebo da yawa,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Abdul dukan babbar mace Ashe lalacin naka yakai haka kuma agaban yarta?
Hajiyarsa ce tazo dubasu sbd majid yafi karfin wata beleqa gidan ta ba,
Shiru yayi yana kallonta azahiri ya tsorata daganinta amma akan enmatan baby babu abinda baze iyayi ba,
Kalleni dakyau munafuki sekazo muzauna naji dalilinka nadukan matar ka sannan katanadai hujjoji kwarara dazaka fadamin narashin zuwa kaduba lpyta na stawon wannan lokacin,
Haryabi baynta seyaji muryar safara'u tace,
Baby kazo kamin tausa kuma kasan kace idan kadawo zamuyi magana fa,ta fada cikeda shagwaba tana rausayar dakai kamar karamar yarinya,ai kawai sebinbayanta yayi yama manta da kiran uwarsa,
Bema damu da Kiran datake masa ba yacigaba datafiyarsa,
Hajiya da abinya girgizata kawai tashige part din badee itama tabi bayanta dalubna ahannunta taana goge hawayenta,
Tana kuka ta labartawa Hajiya komai damarsu daya baya hanasu abinci sedai ba isashshe ba,
Yanzu badee kina wannan halin baki taba fadamin ba?Hajiya naga yai nisane bayajin kira,
Aiseki fadamin yanzu wayake biyan kudin makarantarsu?abdulrahim kadai yake biyawa shima yacireshi daga makarantar kudi sauran ninake kukutawa,
Sosae tajinjina al'amarin tabawa badee hakuri tace gobe zata dawo dantasan ba abar majid hakaba amma dalaifinsa,
Dasauri Lubna tace,Hajiya inaganin wani bakin Abu mekamada mage a dakin Anty safara'u akasan gadonta,
Take gaban badee yafadi sbd sosae take tsoron al'amarin Lubna yanzu.
🤗🤗🤗🤗
[7/18, 10:32 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
*ban taba tunanin rubutu ze zama sanadiyar hadu wata da masu kaunata ba burina be wuce na Isar dasaqon danake son isarwa ba kuma ya amfanar,
*Bawannan ne Na farko dana farajin hakaba amma wannan karon senaji ni daban kamar ba safiyya ba,natsinci kaina cikin tsananin nishadi dajindadi,
*wani lokacin kusancinka damutun bashine zesa kushaku ba,
*A rayuwa sewanda baka taba saniba kuma baka taba ganiba seyai maka rana irin wacce baka zato,
*base mutun yafada maka yana kaunarka ba azaman tare kaida kanka zaka fahimci hakan,akace kukan kurciya gamai hankali bayanine,
*ina rokon Allah yabar kaunar dake tsakaninmu Fatima(baby nurse)Allah yasa munada rabon ganin juna Ameen,
Kiyarda dani wani lokacin senayi kamar nahaukace idan natuna yadda kike min banaso nadaina tuna wasu abubuwan sosae nakejin dadi😍,
Daga karshedai wannan shafin nakine ke kadai fatima (baby nurse).
Page 20
Lubna na hanaki irin wannan surutun kosokike muyi fada?,
A'a banaso muyi fada,fada babu kyau kamar yadda kuke da babyn Anty safara'u har yana dukan ki,yarinta afili take maganar,
Badee ta runtse idonta batason yarinyar nan tacika surutu irin haka gashi tagano Sam Lubna batayo halin ta ba batasan taboye abinda keranta ba kuma bata shakkar fada ko agaban waye, sanin idan takara kwabarta wata kwabar zata kumayi yasa taimata shiru,
Hajiya ma kallon lubanr take aranta tace,majid yayi gudun haihuwa gashi be tsallaketaba,be tsallake zuwan Lubna dunaniyaba kuma be tsallake tonuwar asirinsa ba,idan batayi tantamaba yarinyar nan bazata rasa mutanen boyeba,ta tuna lokacin da margayi megidanta yake bata labari tun bayan aurensu lokackn bata jima datarewa ba,duk inda mugun Abu yake mugayen iskokai ne,wani mugun sammu ne,ko kuma maye hankalinsa baya taba kwanciya da wurin, takuma tabbatar dahakan saboda abubuwan dasukayita faruwa kafin rasuwarsa,
Badee bari natafi segoben idansu Abdul sun dawo kigaishemin dasu(daga baya kenan),
Tou Allah yakaimu Hajiya Allah yakara girma, ta amsa da ameen,
Lubna gashi asiyamiki bobon zuwa makaranta,
Tana murna taakrbi kudin harda godiya,badee kam mamaki ne yakamata ganin yadda Hajiya keson jansu ajiki yanzu kometake nufi da hakan?Allah masani sedai yayi kokarin kawarda mamakinta har gate taraka hajiyar taleqa titi abinda tajima batayi ba taga mutane dadama suna harkokinsu ajiyar zuciya tasauke kafin tace kowa da bukin zuciyarsa Allah kaimana sassauci,ameen inji Lubna dake biye da ita,
Hajiya kam kwana tayi tunani Sam bata zaton er uwarta tayi mata haka sedai idan safara'u ce me mugun hali idan hakaneko zatakai karar safara'u gun mahaifiyarta domin ataka mata birki sbd bazata yadda tanaji tana gani arabata da danta ba,wani gefe na zuciyarta kuma mamakin kalar hakurin da badee take,arayuwarta bata tunanin akwai mace irin badee haka kamar ma uwarta ta gado sbd itama batada magana sosae ba kuma haka kawai ake gano damuwarta ba,
Allah sarki badi'a kusan shekaru fiye dagoma kina kwasar takaaici nakasa gano kina son dana tsakani da Allah ammani dafarko baniyyata na tagayyara rayuwarkiba,
Toshi wancan shashasahn batasan ma ta Ina zata soma da lamarinsaba,
Asubar fari ta shirya tayiwa gidan majid tsinke,
Sauri Sauri yake tafiya kamar wanda aka aiko masa uwarsa batada lpy,
Kai Abdulmajid INA zaka?,
Hajiya wani guri nayi yanzu zan dawo,
Kazo nima sauri nake kware zaniyau idan mungama magana seka tafi koda birnin sin ne,
Wayyo Hajiya kijirani safara'u ce ta aikeni tace inyi sauri, yafada yana kara speed,
Lahaula walaquwati illah billah tafada tana tafa hannayenta,majid haka aka shanyeka?mace kakewa wannan azarbabin?nashiga uku ni jikar mallam🤔,(uhm kya gama sallallaminki kikarasa ciki majid ai bashida duwawun zama tunda en Matan baby ta aikeshi),
Hakuri sosae tabawa badee kamar ba hajiyar da badee tasaniba har seda badee tace,don Allah Hajiya kidaina bani wannan hakurin kuma aike uwace sedai muyi fatan Allah yasa mugama da iyayenmu lpy,
Ameen ta amsa,badi'a ya maganar iyayenki kuma,
Ai Hajiya kidaina batunsu idan har suna sona zasu nemeni nayita zuwa basu hakuri basu saurareniba Dan haka nabarwa Allah komai inajira ne yayi ikonsa,
Sosae Hajiya taji tausayin badee taquduri niyyar taimaka mata da yayannnan nata datake bugun gaba dasu kuma tana fatan suzama ABIN ALFAHARINTA,
Abinda hajiyar zata iya nataimako tayi ciki harda yiwa mazan dinkin sallah dake tafe sekuma harkar karatunsu insha Allah zata taimaka Dan itama bawani abin kirki garetaba sbd mugun maqo irin na majid,
Tafito rakiyarta hajiyar tace bari naje dakin waccen isashshiyar nagaisheta tunda ni bazatazo tagaisheniba,
Nikam wai yakumbo meye haka?safara'u tafada dayake haka suke kiranta Dan haka taji en gidansu nakiranta,
Ai dole zaki tambayeni kuma kisani kin bani kunya Wallahi,
A'a toni menai miki tunda sanyin safiyarnan zaki bugamin kofa inabacci kintasheni kuma ki tsiramin masifa,kujimin fitinanniyar tsohuwa,
Tabdi jam ni Hajiya rabi diyar muhammadu jikar maryama da mallan,
Wai menene haka aketa hayaniya en matan baby,majid ya tambaya yana leqo kansa ta kasan hannun safara'u,
Hajiyace kemin fada babu gaira babu dalili,tafada tana hararan badee da hajiyar,
Ko uwarki baztamin haaka ba kuma yanzu can nayi naji ko ita tasaki kiyi min haka karamar Mara kunya kawai,
Aiko safara'u tasa kuka Yakoma ciki tana diddira kafafuwanta daqasa,
Hajiya meye haka kinga kimsaka min ita kuka ko yanzu dakyar zansamu kanta,kekuma munafuka kike kallona ko?zamu had...
Kafin yakarasa yaji safara'u na kara sautin kukan ta air arikice yabibayanta yaran rufo kofar,
Hajiya kam baki ya mutu se kawai taakama hanyar fita,bata wani jimaba ta is a kware,
Yo ke yakumbo aikinsan kahaifi da ne baka haifi halinsaba sedai muyi ta hakuri da addua,
Maman safara'u tafada bayan tagama sauraren korafin Hajiya,(korafi bekarbu ba hajiya😜)
Hajiya taji haushi ganin er uwarta bata basa zancen muhimmanciba hakan yasata baro garin babu shiri,
Bari mu leqa bangaren yaya asama'u,
A palonta takee zaune ta tasa hoton Lubna agaba tana kallo zuwa yanzu tanaso taji halinda er uwarta take ciki amma shiru ba labari,mamansu har kuka tayi wa asama'u kan tashawo kan mukhtar badee tadawo gida amma abin yafaskara baban suko shima yanaso yaji halinda take ciki amma besan yazeyiba seyanzu yagano yayi katobara daya yarda yahakura lkcn datazo nakarshe segashi yanzu ko labarinta yadaina ji,
Mijin yaya asama'u ma yayi fushi d ita akan maganar badee danyaita binta suhakura tamai kafiya yanzu tayi lallashin duniya yake gun mukhtar yaki harta tadaina masa zancen sedai taita kallon hoton Lubna datakai akacira daga wayarta akayomata na kati akayo enlarging dinsa takafa a palonta.
Safara'u kinji wai yakumbo tazomin nan dashirme,
Maman safara'u ke maganan awaya,
Mama kyaleta ni sonake har ita agamamin da ita kawai Dan naga tanaso takawowa shirin mu cikas,
Murmushi naga tayi tana sauke wayar daga kunnenta.
Luv u oll❤
[7/20, 8:45 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
happy birthday Anty billy Allah yakaro shekaru masu albarka ameen.
Masu Neman yayana daga farko suna biyoni private suyi hakuri don Allah idan sunji shiru u know I'm lazy wahalar marking nakeji🙈.
Page 21
A'a mama ni banason asakashi yahanasu abinci sonake asakashi yadasa musu bakin cikinda suna kallon abincin ma amma cinsa yagagaresu daga uwarta sa har badee da yayanta sonake rayuwarsu ta tagayyara harsesun gudu da kafafunsu kinga idan anyi haka semufara da uban gayyar,
Safara'u ke waya da mahaifiyarta,
Toke safara'u bakyaganin abin zedau lokaci?
Babu wani daukar lokaci ai ance idan masara taji wuta ita dakanta zata fada,
Nida sonayi ko muce yasako musu ciwo nadan wani lokaci harse ransu yabar jikin su wallahi jinake kamar sumutu yanzu wannan uwar dukiyar tadawo hannun mu,
A'a baza ayi hakaba aise ayi saurin ganomu,idan wuya tai wuya tsaf zaki nemesu kirasa,yadda kikeji haka nakeji wallahi Dan majid din maqon masifa ne dashi koyanzu senayi dagaske nake samun wani Abu hannun sa Wanda na aiko miki satowa nayi yatambata nace kila ya zubar ne yaita mita, yanzu dai kije kicemasa akara sako masa tsanarsu har uwar yaji bayason ganinta,
To shikenan sekin jini,
Dahaka sukai sallama nikaina seda na tsorata (anya wai badee bazata mutu ba🤔abin yaimata yawa),
BAYAN WASU SHEKARU
Tundaga Wannan lokacin babu abinda Abdulmajid yasawa gaba irin Neman kudi, yatara dukiyar da shikansa besan adadin taba,
Yayansa,uwarsa da matar sa badee bemasan da zaman suba sesuyi satidaya basu ganshi ba,
Abincin dasuke ci yadamqawa safara'u se abinda taga dama take basu ,
Uwarsa tayi yawo harta gaji dole tahakura addua kawai take masa yanzu sosae take wahala,
Duka kuma sedai idan majid be hadu da daya daga cikin yaran ba har abdulrahim daya zama saurayi yanzu bewuce duka awurinsaba yo ko uwarsa ta tunzurashi se yaimata duka,
Lubna ce kadai matsalarsu yanzu,tazama budurwa wani kalar kyau ne da ita har tafi wacce tayo kyau,bata tsoron sa shida matar sa kokadan indai tana kusa bawan da ya isa yataba uwarta yanzu zaunenta take gida batada matsala dan tagama secondary skul tace kozataci gaba bayanzu se islamiya datake zuwa,kuma tana koyon dinki awurin wata makociyarsu amma da Dan tafiya tsakaninnan,
Yauma kamar kullum tafito zataje gidan datake koyon Dinki ta iso kusada wata qatuwar bishiya abinda takeji yafara tasomata wani kalar tashi gashin jikinta yake kullum tana so takarasa Dan tasan bakaramin abubane wannan koma menene amma setaji abin yana kara yawa,
Afili tace nakusa fara avoiding hanyar nan,
Lokacin da ta dawo tasamu safara'u na surfawa badee rashin mutunci ita kuma tatsaya kallonta kamar hoto,
Wai mama meyasa kike kyale matarnan tana surfa miki ruwan rashin mutunci kina kallon wallahi ki jibgeta seta fita hayyacinta,
Lubna kinsan na hanaki irin wannan ko idan baki dainaba nizan jibgeki bakyajin manya na magana sekin sako bakinki,
Kiyi hakuri mama manyan naga girma ya Riga hankalinsu zuwa,kuma wallahi dabadan duk abinda kayi se anmaka ba babu abinda ze hanani gurzar bakin wata yau,
Shiru badee tayi Dan tasan yanzu idan ta takurata da fada zata hau bori tajiwa kanta ciwo,shine abinda yake damun Lubna idan ranta yabaci shikenan seta fara nose bleeding daga an tabata seta ringa buga kanta duk inda tasamu se anmata ruqiyya kuma dakyar take dawowa daidai,
Safara'u ta buga tsaki, mayun banza ke bakida daraja awurin miji kuma kinkafe kinki tafiya shekara da shekaru kokwana dakin ki bayayi amma kin nace saboda kwadayin abin duniya kinga babu cigaba kinki tafiya ko ina kikai jarrabar ki oho, kodayake ma inkin tafi babu gidan zuwa iyaye sun yafeki sbd anzabi abin duniya akansu shiyasa aka cika gida da yaya sedai Haryanzu babu alamun fidda uwa balle akaiga riba mtswwwwww(ai dasauri najanye fuskar badee nace wannn tsinin baki haka duk wurin tsaki ne karki tsokanewa baby badee ido😂),
Safara'u kenan Aiduk Wanda yayi zagi akasuwa yasan da Wanda yake, tana gama fadar haka tashige daki Dan jin ana kiran sallahr magrib,
Lubna dake tsaye tace, maye dai yasan inda yake kuma kema daknki nan gaba zaki tantance maye acikin mu,kuma wallahi kurwan mu our sedai shi zakiyi wa megidan mu munriqe Allah dankinsani wallahi har hanjinki inagani sedai ina jiran naga ranar da reshe ze juye da mujiyane kuma kaikayi zekoman kan masheqiya, itama binbayan mamanta tayi,
Cike da takaici takoma gefenta lallai yakamata tadau mataki akan Lubna, amma tayaya?ga Hajiya ma itake rage musu wani zafin shiyasa sukeyin kamar basuda damuwa gashi tafara ganin alamun nasara arayuwa Dan abdulrahim da abduljabbar suna kusada kammala degree dinsu ga Abdul'aziz ma yana 100level,abdulqadir da lubna kadaine basu samu admission ba, kuma duka mazan ba azaune sukeba kowannensu yanada sana'arsa ta hannu,
Dole na riqe takuna Lubna nashirin ruguzamin komai,
Kamar wani zaki haka yashigo dakin badee daya fi wata be leqoba yaka yaringa ihun kiranta dasauri tafito gabantanafaduwa dan tasan ba alkairi ke kawo shiba,
Ban hanaki yiwa enmatan baby gorin haihuwa ba,
Shiru tayi tana sauke idonta kasa,
Hakan yatunzurashi bazata daina yimasa shiru ba kenan shifayarasa abinda yahana shi sakinta ko kuma korarta itada yayanta ya tsani ganin su,
Kyakkyawan mari yadauketa dashi,dasauri Lubna tafito tanajanta gefe,
Metai maka? Tafada muryarta da alamun kuka,
Zaki kaucene kosena jimiki ciwo,badee tace, Lubna banason irin haka kije kicigaba da aikinki,
Mama kidaina bata yawun bakin ki babu Wanda ya isa ya wulakantaki ina kusa,
Saukar mari taji hakan yasata tsaya wa tana kallon majid sekuma jini yafara fita daga hancinta.
Ku yarda dani idan aka kirani Anty wani dadi nakeji senaji nazama wata babba,irin anty Sophie ina wuni ya typing😎 wayyo dadi sanaji kamar nabawa wacce takirani Anty sweet🍬,
Inkinaso kiga yadda murna ke lullubeni kicemin baby Sophie 🤔 ranar sekin goyani kuma da zani😂.
LUV U ALL❤
[7/21, 5:49 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
*Wani Abu se rayuwa lokacin dakake dariya lokacin wani ke kuka,lokacin dakake ta kamar kanada lpy lokacin waninacan yana shan wahalar ciwo,haka a kullum aka haihuwa haka kuma kullum ake mutuwa😭,
*yayinda kake takama da tarin dukiya wani yana can yana tunanin ina ze samu abinda zeci yanzu anjima bema San ya zeyi ba, don Allah kada mu jira se munsamu dayawa zamu bayar, Dari biyun daka fi karfin ta koda a kullum irinsu zasu fadi daga jikinka bazakama lura ba itace zata saka rayuwar wani cikin nishadi da jin dadi na wuni daya,
*nera goman dazaka bawa wani bawan Allah baka saniba ranar gobe kiyama kilama itace zata zama cikon mizaninka Na shiga aljanna,
Ya Allah kabamu badon murama ba sedan mukasance masu jinkai da taimakon en uwanmu Allah ka kara rufamana asiri duniya da lahira ameen thumma ameen,
Page 22
Daga hannun sa yai ze mareta badee ta janyeta,
Haba majid yanzunnan idan ta birkice ni zaka bari da ita kuma kasan yadda take don Allah kai tafiyarka karka tadomin rigima,
Wallahi ban haifi danda ze fifita uwarsa akainaba ni zaki nunawa soyayyar uwa har za kice bazan yimata hukunci ba,gorin haihuwa za tayiwa matata wayasanima ko duk cikin datake samu yana zubewa kece sila,ni nafara zarginki ma wallahi bakar munafuka dole nai bincike akan ki Dan nafara gano take takenki kuma wallahi duk nakara jin anmata gorin haihuwa sena illataki mutanen banza mutanen wofi,
Majid kadai San inda mutanen banza suke Dan kana tareda su,ni wallahi nafi karfin nayiwa kishiya wani mugun Abu wai dan karta haihu,ta haihu mana gatanan ga gidan da mijin,inda saniyar gaba tasha ruwa wallahi anan ta bayan ta zata sha,ba dai kabawa Neman kudi muhimmaci ba akan bautar Allah da kiyaye dokokinsa badai kayi watsi da tarin tulin haqqoqin mu dake kanka ba?to wallahi ka shirya ranar da Allah ze damqeka ranar da zakayi kidanka kuma kayi rawarka,
Haryayi niyar fita yaji ta ambaci haqqi se yadawo ya kama hannunta, dama Riga da zanin jikin sunmata kyau Dan haka yakauda idonsa daga cikin nata dama haka kesa yaji ya tsaneta,
Sekicemin haqqinki kikeso abaki jarrabar ta motsa kenan to ai ba kiyi magana da wuriba,
Nidai bahaka nake nufi ba kasakemin hannuna inada aikin yi,
Taji tsoro sbd tajima batasha maganiba Dan ganin yana Neman share shekara be nemeta ba to ita yanzu yama zatayi?Lubna dake kan Ku jira zaune ta kalla da alama ma bata hayyacinta,
Janta dayayi dakarfine yasa tadago tana kallonsa dasauri yadauke kansa danbayaso abinda yai niyya yaruguje, dakin sa dabaya tuna rabonsa dayashiga ba ya tura kofar, yayi mamaki sosae ganin dakin agyare da alama anadan kula dashi sedai yadanyi kura,
Waike wane irin wulakanci ne wannan?se kibarni inata.....sekuma yai shiru yana kyacci hadida girgiza kansa,
Seda ta Daura zaninta tace,inaso ne nanuna maka yanzu bakina ya bude kuma kasani niba zaman ka nakeba zaman yayana nake zancen jaraba kuma kaika koyamin kuma nadaina yi Na barka da abinka banida damuwa dakai,ka kiyayi ranar dazaka nememo karasa kuma daga yau in ka kwaso yayan jarabarka ga en matan baby can always available karka kara zuwa gurina balle katadamin hankali Dana yayana,
Baki asake yake kallonta, gsky zata kwafsamai domin tafi safara'u akomai amma besan meyasa yake jin kamar yakasheta ba inya ganta dukda inya tuna yadda tacika mai gida ransa yana baci, to wai duk ina soyayyar danake mata?(yadda naji kamar nabuge bakin dan air),
Miqewa yai yashiga bayi yayo wanka badee kuma dakinta takoma,
Tasami Lubna adaki tana jera kayansu a wardrobe batako kalli inda takeba tawuce toilet gani take kamar duk Lubna ta fahimci komai,
Ita kuma bin maman tayi da kallo hartashige toilet,murmushi kawai tayi afili tace inama waccen matar zata barku kuzauna lpy?,
Safara'u taga shigarsa bangaren badee amma tayi jiran fitowarsa har tagaji be fito ba,
Meya tsaya yi ohh ni safara'u, daga karshe dai tahakura tazauna tunanin yadda zatayi da lubna,
Lubna ta dawo daga islamiya da safe around 12:15 a gate tasami wani manna'u daya manne mata yasan lkcn datake dawowa daga islamiya Dan haka anan take samun sa tayi kora harta gaji,
Yi tayi kamar batasan da zaman sa awurinba Dan haka yai saurin shan gabanta, haba lubna ta kisaurareni koda minti biyarne,
Malam banida lokacin ka Inada abinyi kabani hanya,
Tana gama fadar haka tabi gefensa zata wuce seya riqo hijabinta daqarfi ta kwace tana masa mugun kallo Dan haka Yakama kansa,
Tana shiga tai wanka ta Dora musu abincin rana fara damai har sun saba kullum shinkafa ba miya sedai mai da gishiri sharrin safara'u ne wannan,
Tafito tsakar gida dibar ruwa taga safara'u da majid sun gito da alama seyanzu zefita ko kallonsa batayi ba tacigaba da aikinta,
Ke lubna baki iya gaisuwa bane?majid yatambayeta ganin da koba komai tana gaisheshi,
Batako dago ta kallesu ba,
Yaushe zata gaishemu kuwa yarinya ta girma taga kirjinta ya cika takai daidai dakowa aure takeso,
Ita tafada miki tana son aure?
Dazu naganta dawani harda riqe mata hijab aiko nace sena fada maka kaga inbaka yardaba ga shaida,
Tanuna masa hoto awayarta, sbd tasan wannan saura yin wata rana tanaganinsa yana tare Lubna sedai bata taba kula shiba Allah yasa burinta yacika a aurar da Lubna auren dole Wanda bazata taba jin dadiba yadda uwarta take ayanxu (safara'u kin manta dadi da wuya babu Wanda ze dawwama),
Nikam da lubna ta lalace ai gara ka aurar da ita nikam inason ta kuma ai da nakowane, yadda take maganar dukse yaji ya yadda da ita amma wannn hoton ya harzuqashi,
Kusa da lubnar yatafi,yanzu kinzabi kizubarmin da girma da mutunci akan ki fadamin kina son aure namiki?,
Ni bancewa kowa inason aureba kuma bantaba yin iskanci ba kaima kasani banaboye abinda ke raina matukar inada gaskiya,
Karya kikeyi kinkoyo munafurci gun uwarki Dan haaka dole nadauki mataki dole na aurar dake akan kijanyomin abin fada kihanani shiga mutane,
Itakam cigaba tayi da aikin ta tana tabe baki Dan bata bawa zancen muhimmanci ba,
Safara'u dake gefe tayi wani murmushi alamun jin dadi aranta tace, dole akarawa malam kudi Aikinsa nakyau(kuji Dan Allah majid ba bincike hujjar dabata hujjaba yahau kai yazauna),
Anty Sophie
Baby Sophie luv u buhu buhu❤
[7/22, 7:42 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Bance dole se kowa ta karanta littafina ba,babu abinda ze bakanta min rai irin mutun fiye da dari su karanta littafina amma basu wa'azantu da abinda ke cikiba, su karanta littafina batareda sundauki darrussan dake ciki ba,koda mutun daya yakaranta littafin kuma yadauki wa'azi da darasin dake ciki to zanfi alfahari da hakan kuma nayi bugun gaba dashi ako'ina,ba don in burge kokuma in Tara tarin masoya nakeyi ba inayine saboda Allah.
23
Mama Wannan gashin naki dani nakeda shi dole mane na saka mai relaxer kigafa yadda yakeda uban yawa gashi seyaita nannadewa,
Lubna dakewa badee kalaba take fadar haka,
Kuma ahaka dakika ganshi bantaba saka masa relaxer ba ko bayan aurena ba yadda babanku beyiba nace bazan saba karyazo ya lalace min irin na Fareeda Dan gashinmu iri daya da ita wai ita batason shi ahaka taje tana saka relaxer aiko duk ya kakkarye,tafada tana dariya,
Itama lubna murmushi tayi tace inaso naga kanwar nan taki amma nafiso nafara ganin yaya asama'u Dan yadda kike ban labarin ta,
Hmmm,Ashe kinada jira lubna adadin shekarunki aduniya shine adadin shekarun da suka guje ni, inaso naga mahaifiyata amma banida hali nasan ita tanaso taganni idan su basa sona fatana dai Allah yasa suna cikin koshin lafiya,
Ni fa mama nayi mamakin yadda kika ki binsu kika tsaya gun Wannan mutumin nifa ina danasanin shine mahaifina wallahi Sam Sam banso yakasance u....
Lubna yakamata zuwa yanzu kifahimci abinda nake kokarin nuna miki a kullum, eh naji ke yarinya ce amma duk yarinyar data kusa shekaru a shirin a duniya yakamata tagano abinda ake kokarin nuna mata,
Yau inaso ki tsaya ki saurareni dakyau idan da a can baya ina fada miki magana atakaice to yanzu Zn miki bayani sbd kina bukatar sani Dan ke macece watarana kina gidan aurenki,
Lubna idan akace miki aure to magana ce da babu wasa acikin ta magana CE me girma kuma aruyuwar duniya wuya ko dadi babu Wanda ze dauwama kamar yadda rayuwar mu bazata dauwama a duniya ba,
Eh Allah ya hallatta saki amma koshi bayasonsa beside inason babanku sosae lokacin dough yanada laifi babba ma dan bekamata yabarni da dawainiyar yayansaba Dan bayason haihuwa, kuma tarbiyar yaya yakamata ace sunsameta ne daga gurin mahaifiyarsu,
Lubna kinsan duk abinda babanku yake yi ada dasa hannun mahaifyarsa?idan natafi nabarku Waze kula min daku dukda lkcn ba ahaifekiba nasan abune me wahala idan narabuda babanku subarminke sanin kanki ne banason hayaniya Allah ne kadai yakawoni gidannan, lubna inason kusamu tarbiya mekyau idan nabarku wahala kawai zakuyi kiga yanzu da ace bananan ya auro safara'u duk tarbiyr data doraku akai ita zakubi which bana tunani zaku samu tarbiya ta gari,
Yadda kikejin anacewa uwa uwace to haka ma uba ,iyaye dakika gani ba'acanza su duk yadda sukakai ga lalacewa dole ne abasu girman su na iyaye Dan haka inaso ki kiyaye harshen ki akansa kodan yadda kike ganin su Abdul sunayi kinji,(yanada kyau muringa nusar da yayan mu irin wannan),
Bayan haka lubna akwai hakuri a rayuwar duniya bakitabajin Wanda yakeda hakuri ya wulakanta ba Dan haka idan baki dashi tun yanzu kikoya ina fatan wannan rayuwar damuke ciki mu gaggauta barinta Allah yatabbatar mana da alkhairi yakuma baki miji nagari,
Ameen ta amsa tana rufe fuskarta dadukan tafin hannayenta,
Murmushi kawai badee tayi tanajin son yayanta fiye datunanin me karatu,
Babuko sallama yafado dakin yana kiran sunan lubna fitowa tayi tana kokarin rufe zip din rigar ta,
Gani ta fada bayan tafito,yawwa sako hijab Dinki ga bako kinyi awaje sunansa Mubarak Dan gidan wani abokin kasuwanci nane Dan naga kinfara kula maza yanuna kina son aurene dan haka gara na aurar dake akan kizubarmin da mutunci,
To baba ni banfa cemaka inason aure ba,takarashe maganar tana turo baki,
Koma dai menene kije yana waje,fita yayi daga dakin,
Hmm wallahi se yatafi da kafafunsa haka kawai,
A tsaye ta same shi yajingina da motarsa taimasa sallama shiru be amsa ba,
Seji tai yace wooo wannan mezafin ce,dasauri takalleshi da alama besan maganar a fili yaiba,
Tab....wannan ko gaisawa bazata bari yayiba taga alamar riqaqqen Dan iska ne wato yama gano me zafi ce hmm,
Ban baka damar yin magana ba inaso kasaurareni dakyau kaji,
Dafarko dai tundaga ganin ka danayi baka kwantamin ba in fact u'r not my type karkabari abata ma lokaci idan aure kakeso kaje kanemi daidai kai, ina fatan zaka fadawa Wanda yaturo ka baka dace dani ba? Nagode,
Baki asake yake kallonta harta bacema ganin sa,lallaima yarinyar nan dama haka take batada mutunci to wallahi dole nasan yadda zanyi tazo hannuna nazata mesaukin kaice na wawusheta nabar kasar gaba daya🤔,
Yaukam dukansu yaran suna gida Dan haka suka zauna palon mamansu sunata hira Sega majid yashigo dukansu suka gaidashi be amsaba segun lubna ya tsaya beyi wata wataba ya kifa mata mari afirgice ta miqe,
Ni zaki maida karamin mutun,naturo yaro gurinki ki walakanta shi dankina takama da rashin mutunci?,
Nifa nagansa ne beminba shiyasa nafada mai gaskiya dankar na wahalar dashi,
Ni nace miki se Wanda kikeso zaki aura?Wanda nakeso naturo miki kuma dole kiyi yadda nakeso,
Wallahi ni banason sa nagwammace na mutu akan na auri wannan Dan iskan,
Chajan dake gefe ya zaro yahau dukanta, ko uwarki ba ta isa ina magana tana magana ba balle ke kuma gidannan idan ana kaunar zaman lafiya dole ayi yadda nakeso,
Sunso su kyaleshi amma abdulrahim yaga hankalin baban baya jikinsa da haka dasauri ya kwaceta yana boyeta bayansa dama yana cike da haushin baban,
Ya'isa haka baba tadaku sosae kalla har jini ya soma fita,inace kuma kasan yanayinda take ciki?kuma ajirata takawo Wanda takeso bawai akakaba mata Dan iska ba,
Abdulrahim har dakai kakoyi rashin kunyar?inace kaima kasan halina Dan haka miqomin itanan,
Basuyi auneba suka soma jin ihun safara'u, labe take musu Dan taga yadda zasuyi,Ashe lubna taganta kuma dama majid ya tabo abubuwan,
Dakyar da bala'i aka kwaci safara'u a jaka tabar part din badee sbd ta daku,majid kuwa kokarin dukan lubna ya soma yi sedai abinda yagani ya matukar firgitashi duk yadda suke fada beyizaton abin yakai hakaba,
Ka gani ko majid?yanzu a tsaye zamu kwana wallahi jiwa kanta ciwo zatayi abdulrahim kukama min ita karta kashe kanta.
Anty Sophie ta gode😎
[7/23, 8:34 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to u Jidda (dota) & umzeey Allah yanunamin aurenku in kwashi Shoki ameen❤.
To kardai kuyi min fada yadda kuka saba Dan nahade Ku a page daya😏.
Page 24
Wani kalar faduwa tayi da seda hankalinsu yatashi sun tsaya suna kallonta kowa yakasa isa inda take, daganan kuma bata kara motsiba,
Ko mutuwa zakiyi sedai ki mutu akaiwa Mubarak gawarki aljanin jikin ki ma yaci ubansa,dakici gaba da borin kiga inban saka muciya ko tabarya na bugeki ba bakar munafuka,
Fuuu yafita kamar ze tashi sama (kadai tafi zuwa gashin jikin enmatan baby😡),
Abdulrahim ya kwashe ta ya kaita dakin mamansu abduljabbar yai mata addua ajiyar zuciya tasauke sekuma ta gyara kwanciyarta se bacci,
Zama sukayi adakin suna maida zancen,
Abdulrahim yace,mama waime baba yake nufi damu ne kusan shekara goma bamuda maraba da babu a gidannan sedai idan yana Neman amfani damune musamman lubna,
Numfashi badee tasauke,Abdul nima bansaniba amma nasan duk kalar hakurin danake yakusa kaini maqura,sundauki karan tsana sundorawa lubna karkaji mamakin safara'u ce tazugo shi in kuma ba hakaba to yanada wata manufa,
Abduljabbar yace ,lallai kam dole dabiyu yabijiro da Wannan zancen haka kawai ya dauko mata zancen aure ba batareda wata manufa ba,
Abdul'aziz yamiqe yana cewa karfa kuji mamakin saboda kudi ne zebada ita Dan babu abinda baba yasawa gaba irin Neman kudi,
Abdulqadir yayi murmushi yace, idan dagaske auren yakeson yimata bayaso tazubarmai da mutunci meyasa bazece ta kawo mijin dakanta ba?wallahi idan ya takurata bataso wannan Mubarak din zamuyi wa duka seya fita hayyacinsa,
Bance kudaki Dan mutane ba amma dai kome zakuyi indai zakukarbowa kanwar Ku yancinta ne kuyi amma karku illata yaran mutane,
Abdulrahim yatashi tsaye yana fadin Hajiya zamu fadawa kawai,
Yome hajiyar ta isa tayi banda tsufa daya tasomata ma,ga baba bayajin maganarta ko kadan, inji aabduljabbar,
Aiko wallahi barmasa gidan zamuyi Dan baze kashemu daranmu ba, fadar abdulqadir,
Abdul'aziz yace wallahi kuwa dama bamuda wani amfani a gidannan sedai kawai yana amsa sunan ubanmu ne,
Kuyi tunani dai dukanku bayara bane koba komai ubankune kuma shiyake cidamu,
Mama kidaina zancen abinci,muntaba ci mun koshi ne? Ana ganin mu anga yunwa kullum cikin cin fara damai kekanki kina marmarin cinnama amma kinfi sati ko takardarsa baki ganiba, duk abinda muke samu a sana'ar damuke tabawa aharkar makaranta yake karewa,inji abdulrahim yadda yake maganar abin yakai shi maqura kenan,
Kusani dai duk lalacewar gidan uba gara ace kunadashi kuma inaso kudan masa uzuri dukda wasu abubuwan dason ransa yake yi amma bayinkansa bane, kuma idan munbar gidan ina kukeso mutafi?kunsandai banida inda zan kaiku ko?
Abdul'aziz yace mu babu ruwan mu dashi danki zamuyi danhaka mujira muga mezeyi ,in zancen gidane ai akwai gidan Hajiya daki semun zaba danhaka ki kwantar da hankalinki,
Shiru kawai tamusu Dan taga alamar ba abinda yashafesu da mahaifin nasu,
Kukan lubna ne yasa duka suka maida hankalinsu gareta,
Yaya kubani ruwa don Allah karku dauko a cup nafison nacikin bucket Jinake kamar Na shekara bansha ruwa ba,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, yaukuma da shan ruwa abubuwan suka zo?
Abdulrahim yadebo ruwa a cup ya tofa adduo'i aciki yabata ko sauke hannun sa beyiba yaga ta ajiye kofin yaleqa yaga bakomai aciki kallonta yai yaga ta lumshe idonta,
Dariya Abdul'aziz yai yace wannan mutanen na lubna inaga daga birnin sin suke kuma da alama kasa suke zuwa wannan shan ruwa haka sekace garin kwaki😂
Dariya sukayi dukansu kafin suyiwa maman sallama suka nufi dakin su,
Washe gari koda suka tashi hannun lubna ya kumbura sosae da alama taji ciwo ne lkcn data fadi, dakyar suka ga gari yayi haske danse kuka take,
Dole tace su Abdul sukaita gidan me gyara targade a duba hannun Dan babansu baya nan bazata fita ba izinin sa ba,
Mama kikamamin nasa Riga,inji lubna,
Meye kuma sekin canja kaya kayanma na bacci?
Mama sababbi ne fa kuma kinga Wando ne banaso naje anajan hannun ina tsalle Allah tsaf zan hankade zanennan, amma kinga inwando ne nayi wulli yadda raina yakeso,
Sosae badee tai dariya tace Allah ya shirye ki lubna
Ameen tace bayan sun gama saka rigar,
Da shigarsu zauren gidan taga wani hadadden saurayi da wata matashiyar mata agefe da alamamatarsa ce Dan ga cikinan jikinta zekai wata biyar se matsar kwalla take tana kallon kafarta data kumbura,se sannu matashin ke mata,
Lokacin da akazo Jan kafar ihu take tana lailayo ashar, shi kuma se sannu yake mata kiyi ahankali karkiji wa baby ciwo,
Seda akazo daure kafar tayi shiru tana kallon mijin nata daya shagala wurin kallon cute face din lubna,
Hawaye take ahankali ganin yadda wannan matar ke ihu kila da zafi sosae,
Me dorin yacewa su Abdul bisimillah,bayani sukai masa faduwa tayi kan hannun kafin safe yakumbura yana mata zafi,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un tafada lkcnda akafara Jan hannun, Dan matashin saurayinnan se kallon yadda take damqe hannun nakusa da ita take tana kuka ahankali dukseyaji ta burgeshi,
Wani uban tsalle tayi lkcn da akasa abin daurewar ya tsuke sosae, dukansu seda sukayi dariya,kekuma ki tsaya mana karki batamin aiki,
Bayan angama haryanzu mata damijinna zaune da alama wani Abu suke jira,
Tunda suka shigo talura yana kallonta har suka fice, jyuowa tai taga haryanzu ita yake kallo suna hada ido se yasakar mata murmushi Dan kallon matar sa tayi se taga ta ware mata yatsunta guda biyar ta motsa labbanta alamar Uwar ki?
Zaro ido tai sosae sekuma tayi saurin dauke idonta tacigaba da tafiya da sauri sauri Dan su Abdul sunyi gaba.
Anty Sophie na fatan yauba korafin yayi kadan? 🤗
[7/28, 3:03 PM] Babee Feeya: [7/26, 12:40 PM] Safiyyah galadanchi❤: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Wannan shafin nakine yar uwa rabin jiki billy galadanchi❤
Page 25
Daganan gidan Hajiya suka wuce dama Abdul'aziz ne kawai se abdulrahim suka kaita suna zuwa suka samu hajiyar azaune tsakar gida ita kadai da kofin koko agabanta da sauri lubna ta karasa gaban hajiyar tana murmushi,
Hajiya barka da hutawa,barka dai kanwar maza yakuke ya mamanku?
Lpy lau suka amsa,
Kokon dake gaban ta lubna tadan kurba tace haji wai anya ba kwakwa a kokon nan jinake ina wani lulawa,
Dariya sukayi dukansu Hajiya tace kikarasa shanyewa naga alamar ko karyawa bakiyiba,
Wlhy kuwa Hajiya kamar kinsani,
Meyasameki a hannu?
Jiya na fadi Ashe naji ciwo seyau dasafe natashi hannun yakumbura shine aka gyara,
Nan abdulrahim ya zazzage mata abin da yafaru,
Tabdijam...idan aure yakeson yimata aiseyace ta fito damiji, towaima yaushe yasan Ku yayansa ne dahar zenuna isa akanku?
Kunga Ku tashi Ku tafi zuwa sabogoginku kubarmin ita nan nayi wanka naje gidan kobayanan zan jira shi Nagano take takensa iskanci ne danhaka wallahi dole na dauki mataki danyaga nazuba masa ido ne shiyasa iskancinsa ke ta'azzara harni zekawowa batun banza,
Shiru sukayi suna saurarenta dasuka masifarta bamekarewa bace suka barmata gidan,
Wanka kawai tayi komai bata shafa ba tasaka kayanta suka nufi gdan majid,
Suna tafiya kafin su samu adaidaita tana faman mita,
Yaushe zanyadda atura yarinya gdn mijin da bataso, daya aka kare ma da auren soyayyar balle Wanda babu ko digonso acikinsa,ga yaron fandararre wallahi dasake,
Har suka samu adaidaitan suka isa gdn surutu take har tsoro tabawa lubna ,wannan mita har ina er tsohuwa?
Batakobi takan lubnar ba ta shiga gidan dakin safara'u tafara zuwa taringa buga kofa amma bata bude ba dole tahakura tayi bangaren badee,
A kwance suka sameta Palo tayi shiru tana tunanin abin duniya,
Gaisawa sukayi da Hajiya ta kawomata Dan waken datayi yau dashi suka karya kuma dashi zasuyi abincin rana,
Kai amma er nan kin kyauta dama inajin yunwa da babu komai acikina tunjiya se ruwan kunu,
Allah sarki Hajiya yakika zauna da yunwa kunu aiba ya rike ciki?,
Badi babu komai gidan se farar shinkafa komai babu, er wannan yarinyar dake gurina shekaranjiya uwarta tazo ta dauke ta wai aure zasu mata banida Dan aika ga su Abdul ma sunkwana biyu basujemin ba,
Zaro ido badee tayi tace, Hajiya zama ke kadai a gida babu dadi ko zaki tafi da lubna ne?,
Bazan je da iyaba kema ai kina bukatarta sedai inkosu Abdul dayansu ze koma can,amma lubna kam kodan Wannan munafukar matar ta majid bazan daga da itaba Dan nasan koba komai tana tare miki wani abin,
Hakane kuma bari abdulrahim yazo muji seya fadi Wanda zekoma candin Allah yakauda bacin rana kar wani Abu yataso bakowa kusa,
Uhm,ke dalilin zuwana gidannan abdulrahim yacemin wai aure majid zewa lubna kuma batason mijin?
Eh haka yazo jiya yana fada Dan ma yaturo yaron nibansan me lubnar tace mai ba shine yaje yahado majid din yazo nan yaimata duka ciwon ta yamutsafa shine kikaga taji ciwo a hannun,
To ana auren dole ne kuma idan aure zemata seya bata damar kawo mijin datake so,
Inji Hajiya,
Hmmm,yaushe zeyi haka tunda zugoshi akayi saboda ba akaunar ganin farin cikin mu,
Kardai kicemin safara'u ce ta zugoshi?,
Itace fa hajiya kuma wallahi nasan dabiyu yayi haka baze rasa wata manufa akan wannan ba tunda baban yaronma abokin kasuwancin sa ne,
Aiko yadebo ruwan bala'i Dan wallahi bazata sabuba baridai yadawo yau inanan inajiransa,mukayi rashin mutuncima ba gaira ba dalili balle antabo mu?(yau antuna da baya kenan hajiya),
Bayan azahar safara'u tatafi part din bade tana zuwa ta tabe baki,
Tsohuwa sarkin jaraba anzo?toyau dai koda mekikazo keda munafukar matar danki dabatada maraba da sharar gidannan awurinsa inada yadda zanyi daku domin Dan naki atafin hannuna yake,
Badee dai shiru tayi Dan ita batason tashin hankali sedai tasani Hajiya ba kyaleta zatayi ba,tunkafin tagama tunanin tajiyo muryar hajiyar,
Yo safara'u akwai munafukin dayakaiki keda uwarki?anyi muku inuwa amma kuna saka Wanda yakaiku inuwa rana?karki manta taimakonki nayifa keda uwarki Dan nazata son Allah da annabi kike wa majid Ashe ba haka bane Dan abin hannunsa ne ya tsokale muku ido,
Tawani gefen bana ganin laifinku sbd shine yabaku dama babu abinda yasawa gaba seneman kudi shiyasa kuka samu damar rufe masa ido yana tunanin kune masoyansa kukasa ya guji uwar data kawo shi duniya,yabar mace guda daya dadaukar dawainiyar yayansa harsu biyar,
Idan kin lura mumunkama Allah shiyasa muka zamemiki kadangaren bakin tulu,danke kina er bakin ciki zakije ki zugoshi ya aurar da yarsa gawani can Dan iska wato haka kikeso kiga rayuwar bayin Allah cikin mugun yanayi bakisan shi Allah ba azzalumin sarki bane danhaka munanan dubunki zata cika,
Kuma wallahi yau koda bala'i da masifa da rashin mutunci babu Wanda ya isa ya aurar da lubna ga wanda bataso kuma inanan inajiran shi majid din dakike ta kamar ke kike juyashi,
Shegiya mekar kama dabakar zuciya,
Duk abinda zakice kice danki dai a hannuna yake kuma yau zakiga yadda miji ke tsallake umurnin uwarsa yabi na matar sa,
Majid yadawo jinhayaniya bangaren badee yasa shi tafiya can yana fadin
Allah yasa ba enmatan baby aka taba ba,(kuji Dan iska),
Aiko safara'u tana hango babbar rigarsa na cika da isaka ta daka tsalle tafadi kasa,
Wayyo Allah wayyo nikaina namutu na lalace Na shiga uku na,
A gigice ya isa yamiqar da ita yana tambayar menene,
Wai Hajiya ce tazo shine nazo ingaisheta sukafara zagina itada badee'a wai nafita karna shafa musu tsiya kuma dannace lubna tazo ta tayani fito dakayan wanki shine sukemin gorin haihuwa wama yasani koni ke zubar da cikin danake samu lubna bazatajeba karna koyamata bin bokaye da malaman tsibbu Dana saba bi Nida uw...
Ransa yakai kololuwar baci yasan uwarsa bazata dakuba danhaka yaikan badee dake tsaye cike da tsoro tana firfito da ido dama irin haka take gudu shiyasa duk yadda safara'u keson suyi fada bata biye mata saboda duk laifin duniyarnan hukuncinsa duka ne ita da yayanta duk basu wuce hakan ba,
Marin daya gaura matane yasata dawowa daga tunanin datake atake kanta dake ciwo yasara mata dafe kan tayi tana zama ahankali take kuka,
Hajiya takoma gabansa takwada mai mari har yadaga hannunsa sekuma ya sauke hannun,
Wannan abin safara'u taso yakasance tasan daya daki uwarsa lallai daga uwar har badee'a da yayanta barin gidan zasuyi sekuma Allah yadauki mataki akan majid da kansa batareda tasha wahalar kawar dashiba,
Ashe kai karamin Dan iska ne tunda bazaka iya rama marin da uwarka tamakaba?,
Duk ba wannan yakawo ni ba inaso kasani wannan auren dazakiyiwa lubna babu shi banason nasakejin batun yatashi,
Kasan halina sarai Abdulmajid idan tayi nasarar rufemaka ido har kake tsallake bin umurnin uwarka tayi nasarar sawa ka mance da matar ka baiwar Allah uwar yayanka to nasan batayi nasarar kawar ma da memories dinka na daba wallahi tallahi kaji na rantse zandawo Hajiya Rabin daka sani ada kuma ba karamar barna zamu aikata ba kaji na fada maka kuma mu zuba ni dakai shege ka fasa,
Sosae maganganunta suka shigeshi har yadanyi sanyi yana hada ido da safara'u ya birkice,
Yarinya y'atace kuma na bada ita Dan haka koduk duniyarnan zata taru akaina babu Wanda ya is a yasa na chanja maganata danhaka nanda sati daya za ayi komai agama kuma wani acikinku yayi trying something stupid kuga yadda zan tada hankalin kowa agidannan,
Fuuu kamar zetashi sama yafita,
Lubna ta sulale akasa tana kuka sosae harda sheshsheka,
Badee ma haka ta kalli Hajiya,
Yaushe zamuji dadin rayuwarmu ?Hajiya zuciyata nauyi take min abubuwa dayawa marasa dadi take dauke dasu,kikalli yarana koda sundauko jin dadi nawuni daya dole se an wargaza musu shi bansan me safara'u take nufi damuba,
Sosae Hajiya take tausayinsu,seda ta lallashe su sukayi shiru tace zata tafi se dayadaga cikin yaran yazo,kuma duk abinda yataso su aika mata Dan daga yau bazata kuma yin shiru ba dan tagano badee kamar doluwa ce komai akemata bakin nan gum kamar ruwa yaci shirwa,
Seda ta sakata a adaidaita kafin tajuya gida tana tunanin yadda za asaka wa rayuwar erta kunci tun tana yarinya.
(Ashe akwai Dan karamin yaki a gdn majid).
Don Allah fans kuyi hakuri dajina shiru kwana biyunnan banji dadi bane shiyasa nagode❤,
Bansan me mutane sukeso su saniba amma dayawa suke tambaya na wai billy galadanchi yayata ce wasu har private suke bina,to ga amsarku nan,
Anty Bilkisu yayata ce the same father the same mother ita nake bi☺
[7/28, 1:48 PM] Safiyyah galadanchi❤: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Taskar billy galadanchi
Miemiebee novels
Ummeeja'afar novel group
Zauren biebie isa
Billyn Abdul novels
Zarah bukar novels
Shukra novels
Ayusher fans club
Feedo novels,Wannan shafin nakune ina godiya sosae da kwarin gwiwar dakuke bani inajin dadi sosae Allah yabiyaku❤ameen.
Page 26
[7/29, 1:13 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017.
Taskar billy galadanchi
Miemiebee novels
Ummeeja'afar novels
Zauren biebie isa
Billyn Abdul novels
Zarah bukar novels
Shukra novels
Ayusha fans club, nagode sosae da kwarin gwiwar dakuke bani Allah biyaku da mafificin alkhairi ameen.
Page 26
Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba domin majid ya haukace hagaga shirin biki yake dukda ba ayi komaiba yace Daura aure kawai za'ayi,
Sosae suka shiga firgici bakamar lubna Dan dayazo baban yatursasata dole tafita a motarsa ta same shi,
Sauke glass yayi ganin ta tsaya tana kumbura Fuska,
Madam shigo mana kika tsaya awaje,
Shiru ko motsi batayi ba yaita magana ta kyale shi,
Inba zaki shigo ba zan kira baba Wallahi, Dan murguda baki tayi tashiga motar tana jin takaicinsa sosae tasan idan tayi rashin kunya yanzu majid yaji kan mamanta ze sauke kuma batason abinda zetaba badee danma kwanakinnan tana ganin ta se a slow ko baccin kirki batayi,
Zama tayi tabar kafafuwanta awaje tajuya masa baya,kishigo mana kinsa AC yanata bin iska yace yana kallon bayanta,
Babu abinda na tsana irin kallon fuskarka, na tabbata ashekarar nan baza asamu Wanda zeyi kalar danasanin dazakayiba idan kayi gangancin bari aka Daura auren nan,
Hango majid tayi yasa dasauri tasakafafuwanta tana rufo kofar,
Murmushi yayi yajuyo sosae yana kallon fuskar ta dake a tamke kamar an aiko mata Manzon mutuwa,
Dan matsowa yayi ganin majid yashige gida yana Dora hannunsa kan shafaffen cikinta me aka sawa cikinnan?
Dagowa tai dasauri ta kalleshi da idanunta dasuka soma chanja kala zuwa ja,
Kadauke hannunka daga jikina kuma karka kara wannan kuskuren,
Jikinki aina wane kwana nawa yarage?daga nadan Dora hannuna abinda zan mulka son r...
Mari ta wanka mai shine sanadin tsayawar sauran kalamansa,
Dan iska la'ananne wallahi ka gaggauta fadawa mutanen nan kafasa auren nan Dan zakayi danasani fiye da tunanika,
Fitowa tayi tashigewarta gida tana zuwa tabawa badee labari atake badee taji batada lpy,
Addua kawai tasa agaba Allah yakawo musu mafita,
Washe gari koda suka tashi majid yakawo wani shirgegen kato wai gadin lubna zeyi karta fita,
Duk basu tabbatar da abinba seda suka ga lallai fa auren zemata haryaraba invitation card duk masifar Hajiya al'amura sun tsaya,
Kuka lubna take kamar ranta ze fita yanzu gobe za auramata mijin dabataso,
Yayyanta duka suka zauna adakin mamansu suna jajanta all al'amarin ganin kawai sukayi abdulrahim yafita bababu jimawa segashi yadawo,
Wardrobe dinsu ya warware wata katuwar jaka yahau zuba kayan su lubna aciki,
Saboda bacin rai har inner wears seda ya zuba a ciki se kallonsa suke,kusan duka kayan su ya kwashe dama kayan bawani yawa garesuba,
Badee tace abdulrahim mekake shirin yi?
Gidan zamu bari Wallahi bazaku kwana gidannan ba harmuma,
Yajuyo yana kallon kannensa yace,Ku shirya fada zamuyi megadin can ymzamuyiwa dukan tsiya,
Abdul'aziz ya kwashe da dariya kai yaya idan kakaimu can Waze bamu abinci,?
Allah zebamu kamar yadda yasaba bamu,
Kutashi mu tafi,aidasauri lubna ta tashi Dan duk wata hanya dazata sa afasa aauren sonta take,
Suna zuwa gate megadin yataso yana kallon lubna,
Ke koma megida yace kar abarki ko gate ki l....
Kyakkyawan naushi yasamu daga Abdul'aziz sauran suka riqe shi,
Kabarta ta fita inkayi gardama jikinka yayi tsami,inji abduljabbar,
Itadai badee wani dadi takeji ganin yadda yayan ta suka soma zama abin ALFAHARINTA,
Abdul'aziz yaja hannunta Dana lubna suka sasu a adaidaita yakaisu gdn hajiya,
Zuwa yai yace kusakeshi kuzo mubi bayan su gobe zamuzo adebi kayan shimfiida Dan babu makwanci a gidan,
Me gadi kam bakinsa yatoshe daya sha haushi,shima Barin gidan zeyi dama anbashi Rabin kudinsa,
Hajiya har kuka tayi data gansu rayuwar majid nacikin hadari batasan ta ina zata faraba yanzu sunbarmai gidan Siya cinye shida safara'u,
Majid da safara'u dasukaje kware sun dawo suka samu bangaren badee a rufe ga megadi baya nan dakinsa ma bakomai,
Sosae suka firgita ganin har suna shirin kwanciya basu dawo ba, safara'u takafe mai kafafuwa baze iya zuwa gidan hajiyarsa ba seya tuna can kadai su keda mafaka hankalinsa ya Dan kwanta,
Wani kalar nishadi safara'u takeji yanzu tarabashi dakowa saura dukiyar sa dama Dan ita kadai take tare dashi burinta Dana mahaifiyarta yakusa cika,
Danhaka ta zage damtse taiwa majid tarba me kyau yau,
Washe gari yakira baban Mubarak yace amarya tagudu tunjiya yake nemanta babu labari,
Yanzu alhaji kasan yarinarnan bataso zata tursasata?nidai ko anganota yarona yafasa danbanason tashin hankali,
Be jira majid yamasa bayaniba yakashe wayarsa.
Daga nan auren ya lalace,
Saura kuma muji yadda safara'u zatayi da babyn ta.
Kuyi hakuri da Dan Wannan pls.😍
0 comments:
Post a Comment