Rayuwa tayi musu dadi a gidan hajiya domin basuda wata damuwa sosae su Abdul ke kula da gidan dakyar ne zasu wuni su kwana dayunwa tun safe suke fita idan babu makaranta inbasu bar abinda za aciba Dayansu ke dawowa yakawo sana'ar su gyaran waya ne kuma suna siyan wacce ba sabuwa ba su kuma siyar Dan haka basuda matsala sosae suke fahimtar juna koda sun samu sabani,yanzu hakama sun siyawa lubna keken Dinki datafara koyo kuma tana Dan kokari dukda bata kware sosae ba kuma en unguwar basu sansuba sosae sedai ma mutanen hajiya ne dake kusa sosae suna mutunci shiyasa suke kawo dinkin,lubna ma daga ankawo style taga me wahala ne take cewa ki chanja me sauki kokuma ki kai wani gurin karna bata miki,dinkin yara idan tayi seyafi kyau doguwar Riga kamar akanti kika siyo,zaman banza ya kare,
Bangaren majid kuwa sati daya da tafiyar su badee abubuwa suka soma sauyawa kwata kwata hankalinsa ba akwance yakeba duk tunaninsa yakoma kan badee da yayanta ya kama hanyar gidan hajiya har besan iyakaba amma seya kasa zuwa daya matsa dabi hanyar sedai yaga tarin traffic dabesan daga inda yafito ba harseyagaji ya sauya hanya damuwar tai masa dawa har rama yayi,
Safara'u tazama gagarumar me mulkar gida se yadda takeso za ayi kwata kwata yanzu bata zama gidan en aiki tadebo ta zuba tafita lokacin da takeso tadawo lkcn dataga dama idan yayi magana seta balbaleshi da masifar kamar uwarsa karshema shine zebata hakuri,
Mamana ta kaina kinga abinda nace yana shirin tabbata ko?sannu sannu bata hana zuwa....
Sedai adade ba akaiba er gaban goshi,
Kusan shekara goma shabiyar muna fama seyanzu hakarmu ke shirin cimma ruwa,kai amma fa munsha jira,
Safara'u da mahaifiyarta ke magana Dan har kware taje sbd yanzu da motarta da driver intafara yawo se indai mai yakare mata,
Yaya asama'u yau takudura aranta duk yadda za ayi seta shiga gidannan tagano kanwar ta seyanzu take hango kalar da girman kuskuren dasuka yi ido a rufe,tashafe sati biyu tana yawon hanyar gidan kowani daga cikin su badee da yayanta ne tagani kozataji sassauci aranta,
Mamaki sosae yakamata ganin bangaren badee'a arufe sedai hankalinta yadan kwanta dan taga sabon apartment daya sha gyara kila kuwa badeen ce aciki dasauri takarasa tana buga kofar,
Kallon mamaki takewa matar data fito tana wani yauki ga kiba duk ta hade ta zama shapeless,
Lafiya dai kika bugamin kofa na bude kuma kin kuramin ido?
Hmm...tasauke ajiyar zuciya,Dan Allah nanne gidan Abdulmajid me mata badi'a?
Ita safara'u se yanzuma ta lura da matar tana kama da badee'a sedai da matar da lubna kamar an tsaga kara ko ince tamkar yaya asama'u tayi kaki,
Eh nanne amma yanxu nice matar sa badee'a bata gidan yau kimanin wata biyu data gudu itada yayanta annemesu an rasa danhaka seki kara gaba kuje zuwa nemanta,takarashe maganar tana yatsina fuska,
Idon yaya asama'u yacika da hawaye,daga ganin Wannan matar ta majid er bariki ce ta karshe kokuma tantiriyar Mara kunya duk yadda akayi masifartace ta ishi badee'a yasa tabar gidan,
Muryarta araunane tace sakinta majid din yayi?,
Bakiji nace guduwa tayiba?be saketaba mugun halinta de yasa tagudu wayasanima ko yawon barbada ta tafi?,
Ran yaya asama'u yabaci sosae danhaka juyowa kawai tayi tana goge kwallar fuskarta basuga ta zamaba dole su tashi tsaye Neman er uwarsu tabar gidan miji karta fada mugun hannu kokuma mummunan yanayi itada yayanta,
Zama tayi a mota tayi kuka harta gode Allah tana Dora duka laifin akanta ma koda su baba sunyi fushi da ita yakamata ace sun saurareta ita macece kuma tasan kalar abubuwan da ita badee take facing kuma ma akan gaskiyarta take me raba da da uwa irin haka se Allah balle ace tabar su gdn da agaban idonta ma basuda wata daraja kuma ace tabar su to hannunwa?Waze mata tarbiyarsu?soyayya ta shafe komai dukda zata iya hakuri amma yakamata ace sun mata uzuri,
Ganin babu sarki se Allah yasa ta share hawayenta tan tunanin gunwa ma zata fara zuwa?yaya mukhtar kam baze saurareta ba,
Gidan farida tayanke zataje dukda faridan batada mutunci amma dole zuwa yanzu tanemi er uwarta Dan koba komai tana sonta,
Bangaren badee kuwa hankalinta kwance sedai jin kusancinta da iyayenta yasa taji duk hankalinta yakoma can dan unguwarsu daya da hajiya sedai layi ne ba daya ba sedai kuma babu wani nisa a tsakaninsu,tafara tuno moment dinsu da en uwanta,
Afili tace koyaya su ummu suke nasan dai sunanan araye, inaso naga farida nasan itama zuwa yanzu yayanta sun girma,
Allah kadawo da hankalin en uwana da iyayena Agareni, ameen inji lubna dake tsaye tana kallonta.
Kuyi hakuri da wannan don Allah banida lafiya kuma dakyar nayi typing sena samu ya goge,Tnx😍
[7/31, 9:11 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to you my everlasting momma Zainab inuwa #aka Anty sis👌🏻,may Allah's noor be wit u now and forever😍.
Page 28
Sosae badee takejin batada lafiya zuciyarta ke mata ciwo tafi 2weeks ahaka sedai bata fadawa kowa ba,
Batasan tana kaunar mijinta ba seyanzu, yanzu dayai mata nisa,badan faricikin y'ay'ana ta ba bazata baro gidanba kodan giftawarsa datake gani yana rage mata damuwa dayawa duk wayannan abubuwan dayayi daga auren safara'u zuwa yanzu bata Dora laifin akansa sedai akan safara'u aganinta duk ba acikin hankalinsa yake aikata hakan ba,
Sosae take jin tanason ta kusantu da mijinta amma yayi mata nisa irin nisanda batasan lokacin da zasu sake haduwa ba tadade bata ji irin wannan yanayin ba ga ciwon da zuciyarta yana dad'uwa batason fada ne kada hankalinsu yatashi,
Addu'a take Allah yakawo mata saukin wannan ciwon kodan taga iyayenta taji sanyi kuma tanaso taga farin cikin y'ay'anta,kuma dole idan tanaso taji sauki a zuciyarta to seta cire Abdulmajid aranta Wanda take hango dinbin aiki agabanta,
Washe gari tunda sassafe takejin babu dadi jikinta har rawa yakeyi har gurin sha biyu tana kwance hajiya batanan ta tafi kware da Abdul'aziz zata karbo amfanin gonarsu lubna ce kadai a gidan itama yau aiki take tun asuba take wanki kayanta na badee Dana hajiya se 11:30 tagama se kawai tayi wanka ta Dora abincin rana dakin tashiga tadan kwanta tahuta kafin ruwan shinkafar data Dora yatafasa,saukar numfashin mamanta taji yana fita ba daidai ba dasauri takarasa kusa da ita,
Mama menene?bakida lpy ne?amsa ko daya badee bata bataba illa hannunta data riqo tana dumtseshi sosae saboda ciwon datakeji a zuciyarta,
Dasauri badee ta fito waje a daburce,dakinsu Abdul tanufa sekuma ta tuno bakodayansu a gidan ga hadari har anfara yayyafi hijab dinta kawai ta dauka ta kwaso uwar tata dakyar take tafiya,
Babu kowa akan hanyar balle tayi tunanin zasu samu abin hawa,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai take maimaitawa a lokacin kuma aka tsuge da ruwa,
Afili tace shine amfanin waya dayanzu nakira yaya Abdulrahim,
Tsayuwa ta gagari badee Dan haka tasulale akasa ta kwanta bata damu da yanda ruwa ke dukanta ba ko magana takasayi lubna take tunani Dan tasan mura bata mata da kyau,
Wata bakar mota ta hango kirar Benz baka tana tafiya slow saboda ruwan da ake,
Mus'ab dake tafiya yana danna wayarsa soyake yaji ya lafiyar matar sa dukda yasan koya kira rashin mutunci zatayi masa amma a condition dinta yakamata ace yasan yadda take dukda bejima da baro gidan ba dago kansa yayi yaga er yarinya budurwa tana tsaidashi ga mutun yana gani yashe akasa Dan haka yai saurin yin parking daga gefe yafito da sauri,
Ke lafiya meyake faruwa?
Dakyar take magana numfashinta nayin sama sama tace,
Mama na kataimakeni zata mutu don Allah,
Hanzarin kwasar badee yayi yasakata abayan mota dasauri lubna tashiga bayan tana rungumo mamanta dake ta juyi ajikinta,
Baze iyayin gudu da motar ba sbd ruwan da ake ga asibitin dayakeso yakaisu dadan nisa domin a can yake aiki yanaso yadubata Dan ga alama tanajin jiki kuma yagansu lyk they are helpless,
Bayan sun isa asibtin yafito dasauri yadauki badee ya nufi emergency lubna na biye dashi abaya tana sharar kwalla, yakai kofar da ze shiga wayarsa ta fara Neman agaji,
Gado yasamu a gefe ya Dora ta kafin yadaga wayar ganin sunan mahaifiyar matarsa,
Sannu isashshe yanzu kabar matar ka a gd naquda ta kamata munzo asibiti baka nan danhaka duk inda kake kazo muna labour room,
Wani Dr yahadasu dashi Dan duk yarikice yanufi gun matarsa,
Bayan mintuna goma da shiga da badee Sega Dr din yafito yamiqawa lubna wata paper yai mata kwatancen chemist,kiyi sauri kikawo muna bukatarsu yanzu,
Kallon paper take taga tarin abubuwan bukata batada ko kobo take hawaye suka fara zubowa da idonta kusa da chemist din taje tazauna akasa,
Mus'ab kuwa kafin yakarasa labour room har matar sa ta sauka, shiga yai yasamu ana gyara su sedai babyn kamar tazo da mura Dan haka dasauri yasauka siyan magani,
Dasaurinsa yakarasa kusa da lubna shiya manta ma dayazo dawata saboda murnan babyn sa da tazo atake kuma yatuno da fuskar lubna aransa yace itace wacce naketa burin Allah yasa ke hadani da ita Alhmdllh,
Baiwar Allah ya akayi?mekike yi anan?,
Cikin Muryarta data soma dashewa tace,abubuwan buqata zan siya kuma ban fito da kudi ba don Allah kataimaka ka aramin kudin,
Amsar takardar yayi yasiya abubuwan dasauri har ya juya ya hango matar sa da mahaifiyarta suna zuwa yanayin fuskarsu yasa jikinsa yayi sanyi,
Karbi inji matar sa me suna jameela tana miqa masa babyn,
Kasa amsa yayi yatsaya yana kallonta yana marairaice fuska,
Kasani nafada maka daga ranar Dana haife maka danka ko yarka zamana dakai yakare kuma bazan taba shayar ma da itaba danhaka gatanan tafada tana ajiye babyn a kasa,
Lubna dake kallon ikon Allah tayi saurin zuwa ta dauke babyn daga kasa,
Don Allah jameela ki taimaka kishayar da ita konawa kikeso zan baki,
Batareda ta amsashiba tajuya itada uwarta dake zugata suka fice,
Kallon lubna kawai yayi yace mutafi aduba jikin mama,
Yadda yayi duk setaji tausayinsa,
Ki tsaya anan zan dubata sedai karki bari ta kwashi sanyi,
Gyada masa kai kawai tayi tana kallon babyn datayi bacci a hannunta,
Bangaren jameela kuwa a zuciyarta tana jin soyayyar yarta sosae sedai abinda mahaifiyarta tafada mata bazesa ta iya kula da yarinyar ba.
😂😂wasu Na cewa wahalar tayiwa badee yawa yakamata tafara jin dadi yanzu Dan Allah kuyi hakuri kubari yatafi yadda na tsarashi I promise u a very happy ending insha Allah har Dan luv za a tabo ammafa niban iyaba saboda banayi😜
[8/1, 11:09 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfahari na)
By sophieG
A very heart touching story 2017
Masu karatu sekunyi hakuri dani Dan sosae nake mistake agurin sunayen yarannan danasan zasu rikitar dani haka daban saka suba amma zanyi kokarin ganin Na kiyaye nagode.
Page 29
Komai jiki asanyaye yake yinsa haryagama duba badee tayi bacci yasa akai kaita daki annex Shiga dakin yasamu lubna azaune ta Goya babyn dake bacci da alama yarinyar batada rigima,
Kawo ta nakai ta gida idan da wata matsala seki kirani,yafada yana tsaya wa bayanta Dan ta kwance zanin goyon,
Banida waya itama mama batada waya shiyasa kaga ina Neman taimako kasancewar duk yayyena basa kusa,mun gode sosae Allah yasaka da mafificin alkhairi kudin ka kaga gidan mu adaidai inda kadaukomu zuwa next week insha Allah zanyi kokarin hada maka kazo ka karba,
Kallonta kawai yake yadda take magana cike da manyance seduk yaji ta burgeshi dama tun lokacin yake rokon Allah yasa ke hada su, murmushi yai mata kafin yace zandawo zuwa anjima idan ma dasauki sosae za asallame ku,
A hanya tunani yake Waze bawa yarinyar nan reno mahaifiyar sa bata gani ga kanwarsa akwance komai se an mata ba magana sedai ido kawai larai ke kula dasu duka ayyuka sun mata yawa amma bashida yadda zeyi yanzu dole ze gwada zuwa lallashin jameela kokuma yasamu wata wacce zata kula masa da ita ,amma zeyi matukar bakin ciki idan er ta girma a hannun me Reno zefi kyau ta girma a hannun mamanta,
Huci yafitar daga bakin sa me zafi yana shafa fuskarsa da duka hannayensa bayason hayaniya kokadan segashi rayuwar sa tazo da kaddara me tarin yawa damuwa Na nema tayi masa yawa,
Bayan la'asar su hajiya suka dawo sunsamu babu kowa agidan kuma ga gidan abude basu yi tunanin komai ba suka zauna zaman jiran dawowarsu kila basu yi nisa ba,
Wasa wasa har kusan magrib basu dawoba Dan haka suka fito kofar gidan Abdul'aziz yakira abdulrahim yafada masa su lubna basa gidan a rikice yadawo,
Hajiya tashishshiga makota nakusa dasu amma sunce basu shigo ba hankalinsu yakara tashi sunanan tsaye akakira sallah danhaka suka shiga gidan suyi sallah,
Bangaren badee kuwa kusan magrib dinnan ta farka garau taji jikinta danhaka tace a sallamesu dakyar lubna ta rarrasheta tabari suyi sallah,
Mus'ab yadawo asibitin Dan yaduba jikin wayannan mutanen dabesan kosuwayeba soyake hankalinsa yakoma gu daya irin yadda hankalinnasa ya karkasu bayaso yanaso yai focusing akan damuwa daya,
Azaune yasamesu har kasa ya durkusa yagaisheda badee yamata yajiki ta amsa tana cewa, naji sauki don Allah a taimaka asallamemu mukoma gida bawanda yasan inda muke kar hankalin su yatashi,
Mama bakyajin komai ne yanzu?
Babu abinda nakeji mungode sosae Allah yabiyaka yaimaka albarka,
Ameen ya amsa yana murmushi, fita yayi babu jimawa yadawo da paper hannunta da ledar magani ahannunsa,
A kofar gidan suka sami su Abdul cirko cirko suna jimami fitowa sukayi nan lubna tai musu bayanin shine yataimake su sosae suka masa godiya daga baya sukabi badee Lubna kuma yake mata bayanin yadda badee zatasha maganin,
Har yajuya ze tafi yajiyo muryar lubna tana magana,
Yanada kyau muyi hakuri dakomai da ze riskemu a rayuwar duniya dolene ajarabcemu Dan dolene a gwada imaninmu wannan jarrabawace ta duniya idan muka cinyeta zamu ga daidai idan kaddara tazo mana semu karbeta da hannu bibbiyu mekyauce kokuma sabanin haka nalura kamar kanada damuwa kuma yau naga daya da idona ina rokon Allah daya raya babyn nan akan tafarkin addinin musulunci yakuma albarkaci rayuwar ta,duk yadda rayuwa tazo maka sekayi godiya ga Allah domin idan kaji ta wasu sekaga taka bama komai bace, idan ka koma gida ka shafa min kanta don Allah,
Takarashe maganar muryarta na rawa da alamun kuka takeso tayi,
Duk abinda hakuri be bayarba rashinsa baze bayarba,dabana hakuri dabansan iya cutukan dazasu sameni ba damuwa taimin yawa inaso tarage min kozansamu sassauci,
Ina rokon Allah daya kawo maka mafita,baka fadamin sunanka ba,
Sunana Mus'ab Muhammad Sharif, nikuma sunana lubna Abdulmajid tafada tana murmushi shima murmushin yayi kafin yai mata sallama yawuce,
Yarinyar tashiga zuciyarsa sosae dole yanemi kusanci da ita amma tayaya?
Bari nasan yadda zanyi damatsalolin gabana kafin nakama wannan tunda nasan gidansu kuma bamuda nisa sosae hankalina akwance yake kusan unguwar mu daya ma,
Bangaren majid kuwa komai ya gagareshi albashinsa se yadda tayi dashi idan anyo cinikin kasuwa da kasonta aciki ita kanta batasan iya adadin dukiyar data Tara ba,
Hajiya nifa plan dina yanzu bewuce asakomai ciwo ba ahankali Wanda zegagara yin komai se yakai stage dinda shikanshi yagaji da duniyar sena kwashi dukiyoyina nabarshi banida matsala,
Eh kuma shawarar ki tayi Dan haka kibari wani satin kizo muje dakanki ayi maganar kuma kizo dakudi sosae domin aikin yayi saurin ci,
To shikenan hajiya sekin jini,(wa'iyazubillah Allah ka kallemu da idon Rahama ameen),
Yaya asama'u ta fadawa farida yadda sukayi da safara'u yaya asama'u bamuga zamaba tashi mutafi dole munemeta muje gida a fadawa su alhaji don Allah,
Sun samu ummansu da alhaji suka zayyane musu komai atake ummansu tafashe da kuka,
Dama irin wannan ranar nake so tazo....
Masoya littafin matsayina anty billy tace nabaku hakuri dajinta shiru kwana biyu insha Allah gobe ko jibi zakuji ta,mun gode ❤
[8/2, 5:05 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
Na
SophieG
A very heart touching story 2017
Idan nabaku wannan shafin banyi laifi ba haka kawai na tuna da abubuwa dayawa nasan kuma zaku tuna kuma zaku gane me nake nufi,Ummeejay,Ummeekay,zeenasir,bellzahra,husaena ubandiya(in-law),ummi rilwan(matar big bro),Sha'awa,dizuwa and fatima (matar nu'aym)pls let's reunite😍😭.
Page 30
Na dade inajiran wannan ranar,ranar dazaku zo kuna kukan rashin er uwarku nayi tunanin kunada hankali sena iske sabanin haka,
Tajuya kallonta gun alhaji,
Alhaji badee'a er kace kanada damar yanke mata hukunci akan kowane laifi amma wannan yayi tsauri,kayan ke mata hukuncin rabata da duka en uwanta batareda kayi tunanin wane hali ni uwarta zan shiga ba fiye da shekara ashirin bansata a idona ba kuma nayi shiru ban maka zancen ba kaima ka yimin shiru,
Asama'u kekikafi kowa shaquwa da Badee amma wannan karon kika rufe idonki kika watsar da ita kukan me kikeyi yanzu?,
Farida kekika yiwa badee rashin mutunci harkikeda bakin zuwa kina fada to yanzu bakin cikin me kike?,
Dukanku kunada aure kuma kunason mazajenku meyasa kuke so ita tabaro mijinta awaccen lokacin anya kuwa kunsan darajar soyayya?kukasan metake angowa idan tarabuda mijinta? Babu wani yanayi na rayuwar duniya dayaze dawwama farinciki ne kokuma sabanin haka,kunsan zafin haihuwa kunsan zafin rabuwa da yayaye to akan me zakuga laifinta Dan taki baro yayanta tabiyo ku?gunwa kukeso tabaro su hajiyar Abdul wacce batabawa dancikinta tarbiya mekyauba balle Dan wani?,
To daga yau kar Wanda yasake kulani acikin Ku harse kunganomin yata kuma Ku tabbatar da tana cikin yanayi me kyau harkai alhaji domin Kaine silar komai dakaida mukhtar da tsoron cikin ta tazo amma ya kwada mata mari yakoreta itada gidan ubanta,
Daki tashige tabar su jiki amace Shiru sukayi suna hango girman laifinsu gashi uwarsu tayi fushi dasu ahaka suka bar gidan,alhaji ma yadade jikinsa asanyaye matar sa bata taba daga muryarta akansa ba segashi yau tana fada masa magana kanta a tsaye dole yatafi Neman yarsa me cike da hakuri da kawaici,
mukhtar ma dayaji labarin abinda ummansu tace hankalinsa yatashi yayi yawon gidan majid har yagaji amma bayasamunsa a gida,a haka suka shafe sati biyu babu wani labari,
Bayan sallah la'asar lubna tafito domin siyan kayan Dinki sedai me shagon dake layinsu baya nan danhaka ta karasa layin dake gaba dasu kadan kamar ranar dazasuzo taga shagon da ake siyarda kayan dinki,
Tundaga nesa alhaji ya hango ta yana tsaye a kofar gidan abin duniya ya isheshi sosae yake kallonta wallahi wannan yarinyar kamarta da asama'u ta shahara badan asama'u tazama babbar maceba babu abinda zehana shi cewa itace kuma yayan asama'u babu wacce takamo hanyar haskefatar wannan yarinyar, koda yawo daga tunani beganta ba,to kodai aljanace?
A a wannan mutunce yaba kanshi amsa, tabar ma yashimfida ko Allah zesa tasake biyowa,
Lubna data siyo abinda zata siyo takamo hanyar komawa gida seji tayi an rungumeta tabaya,dasauri tajuya cikeda tsoro waye Wannan,
Ramla kawarta tagani batasan lokacin datace,wayyo dadi kashe ni ramla yaushe kuka dawo?
Aimunjima da dawowa naje gidanku akace kuntashi daga nan ina kuka koma ne?
Wancen Layin nasama,
Gidan hajiyarku kenan?kicema muna kusa muma nan muka dawo sedai mu daga farkon layin muke,
Dadi yakama lubna bakinta yaki ruhuwa se ganin sukayi mota ta tsaya gefen su,
Ahh yaya Mus'ab daga ina haka?,
Daga gida mana ga gidanmu can,yaimata nuni dawani gida mekyau irin gidan masuji da naira,
Allah sarki,
Mekikazo yi anan?,
Kayan Dinki nazo siya sekuma na hadu da kawata muka bige da hira,
OK muje nasaukeki gida dama inaso naga jikin mama,
Aitaji sauki sosae,Baku gaisa da kwataba sunanta ramla,
Gaisawa sukayi kafin su shiga motar ramla suka fara kaiwa gida kafin sukarasa gidansu lubna,
Har cikin gidan takaishi yagaisa da sumama da hajiya yadan zauna kafin yai musu sallama lubna tarako shi dama tanaso ta tambayeshi,
Ina fatan mahaifiyar baby ta dawo?,
Bata dawoba na buga dambu taliya taki dawowa so nakarbi wannan kaddarar ahaka akayi suna bawani taro yanzu ina fafutukar Neman me reno nakasa samu,
Subhuhanallahi tace sekuma tayi shiru kafin tayi saurin juyawa cikin gida tana fadin ina zuwa,
Paper ta samu da Biro takawomai,
Samun numbernka anjima zan kiraka yanzu inada aiki akaina kuma gobe nakeso nagama idan yaya yadawo zan ari wayarsa nakiraka,
Murmushin jin dadi yayi asaukake yasamu yadda zekusanto kansa da ita, rubuta mata yayi kafin yamata sallama,
Tana Dinki tanabawa mamanta da abdulrahim labarin Mus'ab seda takai gun datake son fada musu buqatarta ta ajiye dinkin ta fuskance su,
Mama na fada miki duk Wanda yakeso yaga bacin raina yatabaki zannunamasa halina koshi wanene haka kuma duk Wanda ya farantamiki nikuma da izinin Allah sena taimakeshi sedai in abin yafi karfina,sosae nake tausayawa bawan Allahn nan matar sa tabar mai jin jira kutaima kubani izinin zuwa tun safe zuwa yamma nai masa renon yarinyar nan don Allah,
Ajiyar zuciya abdulrahim yasauke yace,lubna bawai naki ta taki bane domin yana bukatar taimakon sedai kisani ke macece bekamata abarki asakeba kullum kina hanya and haka kawai bakomai a tsakaninku bazamu barki kije gidansa ki zauna ba dama dai ace zeringa kawo yarinyar ne da bazamuki ba,
Yaya mahaifiyarsa da kanwarsa nanan fa kuma sunada me aiki sedai abubuwa sun mata yawa kuma idan kalura shikanshi damuwa ta lullubeshi,
Akwai haka kuma seki tambayeshi idan ya yadda,
Yawwa yaya nagode sosae Allah yataimake mu,
Ameen kawai yace yana fita daga dakin,
Wai mutuminnan kodai sonki yake lubna?inji badee,
Lahhh mama rufani kisayani,kedaganin wannan mutumin kinsan yafi karfi na kawai dai yanada kirki ne,
Badeee kallonta kawai take tana murmushi.
Banan yakamata na tsaya ba amma wallahi nagaji😩❤.
[8/5, 2:52 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Anty Sophie yauba y'ay'ana?
Anty Sophie y'ay'ana shiru kwana biyu,
Anty Sophie munajira fa😀
Baby Sophie ina badee?
Baby Sophie muna missing lubna fa
Anty Sophie nifa inajira naga yadda safara'u zatayi da majid.
Duk wacce tasan tace haka to su suka sakani typing yau sbd haka wannan shafin nasune sukadai😍 anty Sophie, baby Sophie nagodiya😘.
Page 31
Tundaga sallamarta yagano itace domin sosae muryarta sosae take San yaya zuciyarsa amsawa yayi yana gyara zamansa bayan sun gaisa tace,
Am yaya majid dama nace zancen wacce zatayi renon baby ne shine nace idan ba asamu ba kuma babu damuwa insha Allah zanyi,
Jin zancen yayi daga sama Dan haka yayi saurin miqewa yana cewa gani nan zuwa,
A'a tsaya mana yanzu dare yayi amma idan ka amince gobe ma zan fara zuwa kuma bawai zaka biyani bane kawai zanyi ne saboda Allah sanadin taimakon dakayimin nida mahaifiyata,
Wani dadi yakeji sosae magana ma kasa yi yayi sedai jitayi kawai yace alhmdllh,
Yaya kayi shiru ko akwai Matsala ne?,
Dasauri yace A'a wallahi babu komai na gode sosae gobe dakai na zanzo nadaukeki,
To Allah yakaimu amma baka fadamin sunan y'ar tawaba,
Murmushi me sauti yayi yace sunanta Fatima amma dai ninafi kiranta da baby,
To Allah yaraya mana baby Fatima ameen yace kafin sukayi sallama,
Dagudu takoma dakin su tasamu badee nagoge mata kayan da tadinka dazu dama haka suke sesun goge Dan dinkin zefi kwanta wa yayi kyau,
Mama yaya Mus'ab ya yadda kuma yace dakansa zezo yadauke ni sedai mama zaki bimu kiga gidan?
Meyakaini ni badeeyatu Allah dai ya kiyaye insha Allah baze cutar dake ba,
Mama don Allah kibini muje kiga gdn zakuma gaisa da mamansa kinji,
Ganin ta marairaice fuska yasa badee tace to shikenan amma bazan zauna ba dawowa zanyi, aidama mama bazaki zauna ba,
To Allah yakaimu lubna se kije ki karasawa indo dinkin ta Dan yanzu dinkin zesami gibi tunda bakya zama,
Wallahi kuwa mama ai hannu yarage kawai nasa se zip gara na kashe darennan nadinka mata kayanta naji anacewa batada mutunci kar tazo tayimin RM(inji anty badee) wallahi na gurji bakin yarinya,
Bazama tayi miki ba Dan naga alamar ke Sam bakya gudun fitina,
Shiru tayi tana cigaba da dinkinta,
Washe gari karfe 8:15 am a gidan tayiwa majid sbd zumudi ganinma yayi Daren yai masa tsayi har cikin gidan yashiga shi dai yana jinjina tsaftar su,
Yaya nace zamuje da mamana su gaisa ta hajiyarka kuma zataga gidan,
Babu damuwa yace yana murmushi,
Ta kofar gidan su badee aka bi kasancewar layinsu daya sedai akwai Dan nisa a tsakanin gdnsu Dana su Mus'ab,
Sosae badee ta kurawa kofar gidan ido Sega alhaji yafito yana shimfida tabarma, sosae take kallon sa yananan yadda yake sedai alamun tsufa ya bayyana sosae ajikin sa ai dole ya kwana biyu,
Alhaji kuma zaman cikin gidan baya masa dadi Dan ummansu badee bata wani kula shi iyakacinta da shi gaisuwa se gabatar masa da abinci ko magana yaimata a daqile take amsa shi abin yadameshi yarasa hanyar samun badee se addua yake,
Tunda suka shiga gidan tsikar jikin lubna ke tashi tana jin hankalinta na miqewa daurewa kawai take har suka shiga palon gidan yai musu iso dakin hajiya,
Dasauri lubna tai baya danji tai kanta ya masifar sarawa,badee tayi saurin kallon ta,
Lubna meye haka?
Mama bazan iya shiga dakin nan ba,
Mus'ab yai saurin dawowa da baya yace,
Meyasa?
Yaya Mus'ab kayi hakuri Ku bincika dakinnan ina Palo inajiranku,
Kallon badee yayi yace,
Mama kokingane me take nufi?
Um...tanada matsalar iskane idan kaga tayi haka to taji a jikinta akwai abinda ya shafi asiri,tsibbo,da sihiri nagane haka ne tun tana karama hankalinta baya taba kwanciya a wurin ina baka shawarar kanemo mataimaka aduba dakin nan dagidannan dakyau,
Mutuwar tsaye yayi yana tunani to su Waze musu wani asiri agidn kuma wa suka tsarewa wani abu?shi sema yanzu yake tuno abubuwa da dama,
Mama bari nakira larai tadawo da hajiya Palo zan dauko safna megadi ya tayani muduba hankalina yatashi,
Babu matsala tace tana juyawa,
Sunanan zaune Sega larai riqeda hannun hajiya takuma goyo baby dasauri lubna takarasa ta na karbar baby bayan sun zauna suka shiga gaisawa da hajiya dama tasan da zuwansu,
Kukane ya kwacewa lubna ganin kyakkyawar budurwa akwance komai se an mata babu baki bakafa balle hannu se idanu kawai tana kallon mutane, Allah sarki batasan hawaba batasan sauka ba ankwantar da ita haqiqa duk yadda kake ganin rayuwar ka tayi tsanani ka godewa Allah domin akwai wayanda tasu tafi taka wuya da wahala,
Goya babyn tayi daketa bacci dayake batada rigima kokadan, zuwa tai tana kallon safna taimata murmushi tace sannunki,gyada mata kai kawai safna tayi tana kura mata ido,
Hajiya tace maman lubna mungode sosae Allah yabiyaki da gidan aljanna Mus'ab yamin bayanin komai mungode,
Babu komai hajiya muma godiyar mukazo yi,murmushi kawai hajiyar tayi,
Mus'ab yazo da wasu maza su biyu zasu shiga dakin hajiyar lubna tace,
Kufara binciken tun a bakin kofa idan takama har tile din dakin a bambare baruwanku da gado ko wardrobe naji a jikina wannan abin yajima adakin gadon kuma bazefi shekara biyu ko ukuba,
Ya jinjina wahalar dazasuyi Dan tile din bana yanzu bane sesun sha wahalar daga shi,
Katifar suka soma dagawa suka cire komai najikin gadon basuga alamar komai ba secan idon Mus'ab ya sauka kan wani tile dabe zauna sosae kamar sauran ba seya tuna lokacin da za adaura gadon,
Ranka yadade ga wani tile mun gani be zauna sosae ba kuma munfara Daura gadon,
Musbahu tile din akasan gadon yake?
Eh,
To indai kun fara aikin kubarshi kawai baze zama matsala ba tunda akasan gadone,
Dasauri yakarasa ya daga tile din wani kalar Abu yagani kamar randar ruwa er karama bakikirin ga takarda a jikinta andaura da zare bismillah yayi yadauko tafito palon yana cewa mazn suci gaba da dubawa,
Kuga abinda naciro yace yana nunawa badee dasauri tamiqe takarba sukayi waje Dan tasan idan lubna ta gani birkicewa zatayi.
Washhh anty Sophie tagaji😰
[8/5, 3:45 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Page 32
Mus'ab menene Ku fadamin kuna ina tana kokarin tashi larai tayi saurin maidata zaune hajiya ki zauna suna zuwa kinji babu komai, wannan larai tamusu halacci batada matsala kuma tana tausaya musu,
Suna zuwa waje badee tai bisimilla hadi da adduar neman tsari daga muggayen aljanu da mutane,
Papern jiki tasoma cirewa ta bude rubutu ne na Hausa anyishi kasa sama dakyar ta iya hada kalmomin makaranta
Sunan wata tagani arubuce da manyan haruffa ankuma bada yadda za akarya asirin ta hanyar kona wayannan abubuwan idan wacce akayi wa ta chanja ra'ayinta na kar yawa,
Tana gama karantawa Mus'ab yai saurin zuwa yadauki fetur da ashana suka kona abin seda yazama toka kafin suka koma cikin gidan,
Muryan Hajiya sukaji Tana cewa innalillahi wa inna ilaihirraji'un larai haske nake gani suna shiga tana faduwa asume,
Dasauri sukayi kanta badee tace mus'abu kakira wani malamin idan akwai shi nan kusa atake ya kirashi kasancewar basuda nisa segashi yazo cikin mintuna a shirin,
Addua yai mata sosae sekuma bacci yadauketa yace abarta tahuta kafin yatafi suka bashi lbrn yadda akayi yajinjina al'amarin sunanan en mazannan biyu suka fito megadi yace,
Alhaji mun matso wardrobe gaba sedai munga alamar anfasa gini dasauri ya dauki hammer suka shiga dakin daidai wurin yafasa Sega laya guda biyu sun fado,
Dauka yayi da bismillah yafito palo yanuna musu atake malam yace akona a palon yadora kan tile yasa kero da ashana yakona,
Seji sukayi safna tace maaama😳,
Kuka kawai Mus'ab yasa wato duk wannan wahalar da mahaifiyarsa da kanwarsa keyi fiyeda shekaru goma Ashe wanine yakunsa musu Ashe haduwarsa da lubna alkhairi ce atake yaji wani sonta yakaru azuciyarsa,
Juyawa yayi yana kallonta daniyyar yimata murmushi seya ganta a dunkule ko motsi batayi, dasauri yayi gunta hakan yajanyo hankalin su malam yakoma gunsu,
Badee takarasa tadaga zaune se ganin jini tayi yana fita ta hancinta innalillahi wa'inna ilaihirraji'un tafurta, batason ganin nose bleeding dinnan Dan yanzu setajiyawa kanta ciwo,
Bayani taiwa malam ganin alamun kansa yakulle ruwa yace abashi a Kofi yai Addis aciki dakansa ya matse bakin yadura mata ahankali jikinta yafara saki se sauke ajiyar zuciya take,
Alhmdllh bayan kwana biyu lubna na zuwa gidan yanzuma ita kewa baby wanka larai takoya mata kuma hajiya tadan soma gani ba sosae ba safna ma tafara zama sedai bata jimawa azaunen kuma bata magana sosae amma duk malam ya basu magani suna sha dakuma addu'o'i majid yarasa inda ze Dora lubna sbd shukin sonta daya kamashi ga son babyn sa datake sosae take kula da ita yauma yaji dadi sosae yaga ta dinkawa baby riguna guda biyu sunyi kyau ta gwada mata se surutu take mata kamar Tana gane me take cewa yarinyar ko se dariya take kwasa,
Adakin hajiya suke zaune suna hira hajiya tana jinjina wannan lamarin,
Lubna tai murmushi tace nifa Momy Sam bana mamakin wannan abin naga abubuwa da dama arayuwata masu kamada wannan babana yakasance mutum Wanda bayason haihuwa dukda wadatarda Allah yaimasa ya watsar damu bamusan meye kulawa daga bangaren uba ba muntaso cikin tagayyarar rayuwa mamanmu itace komai namu se mahaifiyar babanmu dake taimaka mata daga baya kuma ya auro wata er uwarsa daganan komai yakara lalacewa bin malamai dabokaye take tanaso ta hallakamu muda babanmu mudai Allah ykaremu sbd munriqeshi kuma mundogara dashi sedai babanmu tasamu sa'arshi be riqe ibada kamar yadda yariqe Neman kudiba yanada dukiyar dabesan adadin ta ba akowace kasuwa dake garin nan yanada shaguna akalla biyar ko shida ana haka yakawomin miji mugun miji Wanda yakasance shedani Na karshe munyi kokarin ganin hakan bata kasanceba amma abin yacitura se kawai muka hada kayanmu mukabar gidan yanzu haka muna gidan hajiyarsa kuma har yau betaba zuwa nemanmu ba muma bamu koma Neman sa ba,
Sosae Momy ta tausaya musu tace yanzu haka kuka baroshi da muguwar mata idan ta kassarashi fa?
Komai tayimai Momy shiyaso yawulakanta mu fiye da zato bezo nemnanmu ba muna bazamu nemeshi ba,
Kiyi shiru kawai lubna ke yarinya ce,safna dake gefe tana saurarensu tayi dariya da muryarta slow slow tace Momy kibarta su sukasan rayuwar dasuka yi dashi, kiyi shiru kema safna bakisan komai na rayuwa ba,murmushi kawai tayi bata saba magana me tsayiba wannan datayi setaji duk ta gaji,
Ke nifa Momy Allah kadai yasan iya adadin bala'in da matar nan ke kullawa dayanzu kila ta kassaramu,
Tafada tan dariya suma dariyar sukayi,
Yauma suna zaune a Palo suna hutawa Dan lubna Goya baby tayi sukaje motsa jiki da safna dan tafara tafiya,
Mus'ab yashigo yabasu wayoyi masu kyau kirar Gioni A1 safna se murna take lubna kam sake baki tayi ina ita INA Wannan zankadediyar wayar daurewa tayi taimasa godiya tace to aini yaya bansan yadda zanyi dawayar ba ko kira ban iyayiba,
Zama yai yadan koya mata masu sauki yace takoyawa safna fita zeyi,aiko tasamu abinyi baby tasha pics ba adadi,
Bari mu leqa majid,
Kwance nasameshi yana ko bayida lpy ne oho,
Safara'u kinsan dai ina bukatarki ko dakinacewa sena baki kudi yanzu kuma kona baki kudin bakya karba kitaimakeni karna mutu kinsabamun da abinnan karki gujeni yanzu pls,
Kallon uku saura kwata taimasa tace kaikam ka boni da jaraba namiji kullum cikin buqata sekace doki?kaibaka gajiyane?nikam wallahi nagaji bakada lpynma sekayi jaraba?tobari kaji inada abinyi yau basussukan danake bi zanje karbowa kuma kila bazan dawo yauba Dan daganan har kebbi da zamfara zani ban kuma CE ga ranar dazan dawoba sedai kawai kaganni,
Shiru yayi yana kallonta taja mayafinta taita tafiya,
Ahankali hawaye ke zubo masa kila wani bala'i ne ke shirin samun sa sbd jiyake kafafuwnsa duk sun soma sakewa ga wani nayi da qirjinsa yaimasa,badee ce tazo masa arai dasauri yatashi zaune sauri sauri yashirya yazari key din mota,
Hanyar gdn hajiya yakama amma ga mamkinsa akasuwa ya gakansa se kawai yasamu wuri yai parking yadafe kansa da yai masa nauyi da hannayensa.
Nidai INA bayan safara'u yadda takecin uban majid yamin daidai😎
[8/7, 5:31 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
This page goes to you anty billy❤
Page 33
Mama kiyimana addua Allah yasa ayi nasar samun aikin nan kinsan Dan tsohon governor din garin nan muna mutunci sosae yanzu da muka gama service yace mukawo takardunmu nida abduljabbar insha Allah babansa zesama mana aiki,abdulrahim yafada yana murmushi,
Tun yaushe Abdul?shine bansaniba seyau?,
Jiyanefa nabashi nazata abduljabbar ya fada miki,
A a nikam,Allah yatabbatar mana da alkhairi,
Ameen ya amsa yana miqewa,
Bari na dubo lubna lafiya har yanzu bata dawo ba akwai mamaki Dan bata saba kaiwa hakan ba,
Daka kyauta kuwa amma kada kayi mamakin tana tareda majnun dinta ne?
Tsayawa yayi yana cewa,wa kenan?,
Mus'ab mana aini tuni naganosu inata so nafada maka kasata agaba ta fada ma gaskiya amma bansamu lokaci ba,
Ummm lallai ma lubnar nan nita maida bi can kenan?,nafa tambayeta Dan kar afara surutu tace min itafa bakomai mutunci kawai suke dashi haka takejinsa kamar ni,
Hmm yanzu kam asiri yatonu seka fadamata ka gano Dan asan abinyi,
Lallai kam yace yana fita,
Dakafa yataka yazo daidai gidansu badee ya hango ta goye da baby da waya akunnenta Mus'ab na gefenta yayinda safna ke tafiya daga gefe ita kadai,
Ke gani nazo gidanku bakya nan,wai ke bakyajin kunya kinje kin tare a gidansu saurayi?,inji ramla da wannan shine zuwanta nabiyu gdnsu lubna amma batanan,
Dariya lubna tayi tana kallon Mus'ab da shima ita yake kallo bakin nan kamar me tallar Maclean,
Eh din ai gidanmu ne,meye kike nemana?,
Hajjaju Dinki nakawo miki kuma express ne,
Wazaki kawowa Dinki express?,
Ke dalla banason iskanci gasunan nabarwa mama anjima zan dawo bikin kanwar mijina za ayi shine seyau yakawomin kayan danya raina ni,
To masifatu naji sekinzo, bata jira ta amsaba ta katse wayar Dan ganin abdulrahim ya iso kusa dasu,
Bayan sun gaisa da Mus'ab yace wannan kanwar tamu nafito dubawa ganin bata saba kaiwa warhaka bata dawowa,
Gaskiya kam,wallahi baby ce batajin dadi taki yadda dakowa sekuka take yanzu ma nace don Allah tatafi da ita har taji sauki,
Aiba komai danan dacan duk dayan....
Juyowa yai jin ana gaidashi safna yagani,
Ahh kanwar mu ansamu sauki kenan harda yawo?,
Murmushi kawai tayi tajuya, shima murmushi yayi yana cewa seku koma ko kar dare yayi tunda gani ma karasa gidan tare,
To shikenan inji Mus'ab yaiwa lubna sallama yanaji kamar karsu rabu itama haka take ji amma bayadda za suyi (bansan yaushe wannan luv ya kullu har yakai wannan stage din ba)
Salamu alaikum
Wa'alaikumussalam abdulrahim ya amsa yana kallon tsohonnan dake tsaye idonsa yayi ja sosae ga hawaye kwance acikin idon sa,
Dan Allah idan babu damuwa zanso kuzo mukarasa gidana inason zanyi magana daku ne don Allah badon halina ba,
Abdulrahim yakalli Mus'ab dabasu Riga sun tafiba,alama yaimasa dakai subi tsohon,
Har tsakar gida yakaisu amma kowa bakinsa dauke da addua akan tabarma suka zauna,
Na Dade ina ganin wannan tana wucewa tanan sosae jikina kebani ita jini nace amma saboda girman laifina yasa banida karfin halin tunkararta naimata magana seyau Dana ganku atare nakasa jure abinda nakeji don Allah Kuyafe min Ku nunamin mahaifiyarku inaso naganta kafin nabar duniya,
Dukansu baki asake suke kallonsa meye hujjarsa idan sudin jininsa ne amma ita lubna tagane meyake nufi sedai tayi shiru tanaso taji yafada da bakinsa,
Nasan kanku ya daureko?,
Insha Allah Ku yayan badee'a ne idan banyi kuskureba Kaine abduljabbar ko kuma abdulrahim saboda kune manya a yayanta wannan kuma naji labari sunanta lubna kece karama acikinsu naganeki ne saboda tsakanin kama dakike yi da yayar mahaifiyarki asama'u,
Arayuwata bantaba ganin mutun me zurfin ciki ba irin maman mu, Ashe muna kusa da iyayenta bata taba nuna mana ba Dan tasan zamu iya zuwa,
Dasauri umma ta fito daga daki tana kallonsu karasawa tai kusada lubna tana shafa fuskarta se hawaye tarasa Na menene na bakincin rasa yarta datayine duk wannan shekarun kokuma na farin cikin ganin jikokanta ne dakuma jiyo kamshin erta dake kokarin kusantota,
Ganin hawaye afuskar umma yasa bade yin murmushi ta juya tana kallon su Abdul,
Yaya kuganemin wannan tsohuwar wai kuka take,tafada tana murmushi kafin tajuya gun alhaji tace,
Dan tsoho angona mekake bawa kishiya ta ne datake da hawaye a idonta har yanzu?
Basusan lokacin da dariya ta subuce musu ba, da alama jikar tasu me barkwanci ce,
Abdulrahim yace kunaso mukawo muku itane kokuma zakuje dakanku Ku ganta,
Eh kuje kukawo mana ita inji umma,
Dasauri lubna tace a'a yaya baza ayi haka ba zamu kasan mama Nada ciwon zuciya so zamu bita a hankaline,
Alhaji mamana ta cemin bazata taba nemankuba indai kuna sonta dolene Ku nemeta dakanku danhaka inaga Ku fara tura yayyen nata da kannenta su gwada lallashinta I'd an ta sauko dakanta zatazo da ganku amma fa kunada aiki ja agabanku kunsan ance wanda baya fushi duk ranar dayayi to saukar sa abune me wahala,
Abdulrahim ya akayi kanwar ka tafika wayo?inji umma,
Tadai fini sanin halin mama ne,
Dariya sukayi suduka kafin suyi musu sallama Dan magriba ta gabato,
Ranar umma kasa bacci tayi saboda murna itada Allah bayan er tsohuwar soyayyar su sukayi nafila domin nuna godiya da jin dadi ga Allah.
Naso ganin yadda tsofaffi ke soyayya🤣🤣🤣nikadai Dana fadi abin senaji shi bambarakwai🏃🏻♀🤣
[8/9, 1:30 PM] Babee Feeya: Y'AY'ANA (abin alfaharina)
By
SophieG
A very heart touching story 2017
Sadaukarwa ga daukacin masoyana fatan alkhairi agareku Allah yabar soda kauna❤
Page 34
Alhmdllh abdulrahim yasamu aiki shida abduljabbar, abdulrahim a federal inland revenue shida abokinnasa dayai masa hanya abduljabbar kuwa abangaren health ne,(👃🏻najiyo kamshin yarannan zasu zama young billionaires),
Ranar jumu'a ne da sassafe aka turo masa ta email Abduljabbar se Monday nasa yashigo sunyi murna kamar zasu zuba ruwa akasa susha se hamdala suke,
Aranar kuma 10:00 am tana zaune itada lubna da baby dake zaune tanata wasanta,
Lubna shikenan kin karbe musu yarinya?nifa banason shishshigi Dan kinga sun sake damu haka sosae zaki kwaso musu yarinya kwana da kwanaki kinsanfa halin mutane balle ma babu dangin iya babu na baba,
Mama ki kwantar da hankalinki sunada kirki sosae kuma nifa bani nace zanzo da itaba itace ta maqale min babanta yace nazo da ita kuma tausayinta nakeji karma dai idan natuna yadda uwarta ta ajiye ta akasa cikin asibiti ko sau daya batasan dumin jikin uwarta ba,
Um Allah yakyauta bari intashi yau dambu nakeson ci,
Nikuma drinks zansiyo yau baki zanyi kawayena zasu zo tafada tana murmushi kafin tasaka hijab ta dauki baby,
Ke kam ina kikaga kawayen?,
Sababbi nayi umma idan sunzo zaki gansu,daganan tafice tasiyo su exotic da five alive,
Su mama da hajiya anbaje an zubo dambu dayaji zogale se tururi yake kowa da plate dinsa hajiya se afawa ake ana yabon dan danonsa,
Badee dai se murmushi take batace komaiba, sallama sukajiyo daga waje hajiya ta amsa tanacewa kosuwaye sukaraso gamunan,
Da sauri badee tamiqe hawaye cike da idonta tama kasa magana,da sassarfa suka karasa gabanta sekuma suka zube akasa suna kuka kamar ransu ze fita dakyar asama'u tayi karfin halin riqo hannunta,
Badee'a bamuda bakin rokon ki amma kisani mun gane kuskuren mu don Allah kiyi hakuri kitausaya mana,
Farida ta karbe, yaya badee kikarbi tubanmu Dan Allah da darajar umma munyi ta Neman ki gdnki munje babu adadi amma bakya nan kuma bama ganin mijinki umma tayi fushi samu ko kallon mu batayi dagamu har alhaji,
Shiru tayi tana hawaye to ita me zatayi da kin amin cewa dasu bayan Allah ne amshi adduarta wannan abin farincikine agurin ta en uwanta gatanta sun dawo gareta atake taji 70% na damuwarta yakau,
Jin tayi shiru kusan minti biyar yasa yaya asama'u miqewa tace,nasan abune me wahala kiyafe mana da wuri amma munbaki lkc kiyi tunani kuma bazamu ga laifin ba domin laifin mu me girmane,
Ganin sunjuya yasa tayi azamar janyosu ta rungumesu ta saki wani kuka me sauti tana cewa,
Yaya bakuda laifi nice me babban laifi kunnuna minso kunso kufitar dani acikin wahalar rayuwa Amma so yarufe min ido nayi babban kuskure wahalar Dana sha bansan dame zan kwatantamuku ba bamusan meye dadin rayuwaba har seda takai ga mun gudu daga gidan,yaya Allah ne ya karbi addua ta yadawo min daku yadawo min da gatana yaza ayi na butulce masa,
Lubna dake jikin kofa tana kallon su tasulale kasa tana murmushi hawaye na zuba daga idonta tanajin wani sanyi na ratsata babu abinda yafiye mata ganin farincikin mahaifiyarta,
Badee yaya mukhtar na waje fa tare mukazo,
Ku shigo dashi mana kunbarshi Awaje,
Kai atakaicedai ranar ta shirya da en uwanta suka ringa neman gafararta aka kawo musu abinci da lemu sukaci se santi suke har yaya mukhtar daya zama magidanci dole yasaki jikinsa amma sosae yake kallon badee tarame sedan haske datayi dama ita ba fara bace sosae amma ba baka bace,
Su abdulrahim duk sundawo suka iske abin farinciki, yaya asama'u tace duk kuzo nizan fada muku sunayenku domin kowannenku nasan fuskarsa,
Sosae sukayi mamakin ganin batayi kuskure wurin fadar sunayen suba tazo kan lubna tace kekuma kanwar maza ke photo copy nace sak dukda bantaba ganinkiba amma nasan sunki kece lubna,
Dasauri lubna tafada jikinta tana dariya harda hawayen jin dadi tace dama haka dangi suke?
Ranar da qafa suka taka har gidansu badee,
Ummansu ta rungumeta tana kukan farinciki daganan komai yawuce se kallon gidan badee take komai ya sauya yasha fenti da tile ko ina se kyalli yake kamar gidan wata amarya,
Bari na Dan leqo majid,
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un nafada ina ja dabaya ganin mutum yashe akan gado yarame kamar Wanda tunda aka haifeshi yake asibiti kai kamarma an tonoshi daga rami bayako motsi se ido dake yawo se wari yake ga jikinsa babu alamar yaji ciwo balle nace ciwon ne sanadin warin,
Inanan ina sharar kwalla Sega hajiya safara'u se kamshi take tashigo dakin,
Yabude bakinsa zeyi magana kawai se jini kamar yana amai kusan sau uku yana attempting yai magana amma jini dake fita ya hanashi,
Hehehe,waikai baka gajiya da magana ne sokake jinin ka yakare? To zuwa nai namaka wanka domin warinnan naka yana takurani,
Gani nayi ta saka hand gloves tajanyoshi kasa kafin ta karkatashi ta kwantar dashi kasa tajashi har tsakar gida tacire zanin gadon tabayar akai shara se kuma tajona tiyo jikin famfo takunna kamar me wankin mota haka taringa fesamai ruwa numfashinsa nayin samasama,
Kayan jikinsa tacire tabi jikinsa daruwan kafin ta sakamai jallabiya tamaida shi daki bayan tasa inno me aikin ta tagyara dakin.
Kuka sosae nake majid yazaama abin tausayi kamar bashiba gashinan awulakance😭😭😭
Ya Allah look at us wit idon Rahama ameen.
0 comments:
Post a Comment