Tun kafin ta karasa takejin muryoyin su daddy, amman suna ganinta sukai shiru"
Cikinta babu kwari ta mikawa momy tare da cewa yaya usman zaiyi mgn dake"
Bayan momy ta amsa wayar ma'u gefe ta tsaya kirjinta na dakan uku uku"
Da ido taga daddy ya kalli momy cikin sauri ta mike ta shiga part din daddy"
Bayan momy tabi da kallo sannan sannan ta juya ta kalli daddy idonta kwalkwal kamar zatai kuka"
Daddy yi yayi kamar be ganta ba, ta dadde tsaye momy bata fito ba dan haka ta juya ta koma daki"
Nafisa na zaune ta tallabe kumatunta da duk hannuwanta biyu, ga wayarta agefe tanata tsuwa"
Karasa tayi ta dauki wayar ta mika mata tare da fadin idan kin gama tunanin ana kiranki awaya"
Azabure nafisa ta dauki wayar, harara ma'u ta bita dashi sannan ta koma gefe tayi tagumi"
Tundaga ranar gidan ya zama kowa babu walwala, bama kamar momy da take wuni dakin daddy, tsakanin nafisa da ma'u ko zaman jigun suke"
Usman be sake kiran ma'u ba amman tana yawan jin suna waya da momy"
Ahaka har aka kwashe wata hudu da tafiyan Jamal"
Zuwa wannan lokacin hakali Momy yafi na barawo tashi, harta fara tunani danme za'a boyewa ma'u daddy ne me karfin halin cewa kar agaya mata bari insha Allahu zai dawo"
Deeni ko besan biken da ake ba duk da cewa yanzun yana yawan ganin babanshi na zuwa gidan amma besan meke kawoshi ba"
Burin shi be wuce yaga samu damar da yake jira ba, yasan daga ranan da yasamu damar shikenan ma'u ta zama mallakin sa, Dan haka ya barta ta gama guje gujenta, ko Jamal dawowa yayi baxai hanashi abin da yayi niyya ba"
Duk da dabi'un shi sun fara canzawa amman sonta na nan makale azuciyan shi, kuma yasa ma'u ma tana kyaunar sa so take kawai ta tursasa kanta wajen yiwa mahaifinta biyayya, amma bawai son Jamal take ba"
Itako ma'u abin duniya ya isheta, tarasa dalilin damuwan ta
Hakanan takejin ta kosa tasan wani hali Jamal ke ciki, tare da tsananin son ganin sa, meyasa nakejin haka ?ma'u ta tambayi kanta, meyasa na damu da rashin jinsa?, haka na nufin inason Jamal kenan?
Girgiza kai tayi tare da fadin ba sonshi nakeba, jimamin sa kawai nake amatsayin sa na dan uwa musulmi kuma aminin yaya usman"
Amman meyasa yanzun nabar tunanin deeni, ko haduwa dashi bana fata, ayanzun Jamal kawai idona keson gani"
Tana cikin wannan halin taji hayaniyan mutane afalon cikin sauri ta fito"
Wata dattijuwar mata ce tare da wata yariya budurwa zatakai sa'ar nafisa, daidai lokacin data shigo falon taji matar na fadin Allah ya bayyana shi"
Runtse idonta tayi tare da fadin nashiga uku"
Ganin inda ma'u ta runtse ido yasa momy ta washe fuska tare da fadin"
Wannan itace Asma'u matar Jamal tunda akayi biki baku haduba shikuma be kawo miki itaba"
Wani irin kallo matar tawa ma'u, muryan momy taji tana fadin asma'u wannan itace abokiyar zamana, sannan ta sake nuna budurwan dake kusa da ita tace wannan kuma kanwar Jamal ce"
Hakanan ma'u taji kwata kwata basu mata ba, tunda tazo gidan bata taba ganin suba saiyau"
Gefe ta nufi zama cikin sauri momy ta mike ta jata daki, dan batason ta fahimci halin da ake ciki"
Kallon momy kawai take amman tasan dole akwai abin da ya faru, ta kula ita kadai ne abason ta sani, hawaye ne suka zubo mata tasa hannunta ta share sannan ta kalli hawayenta dake hannunta tace"
Sai yaushe zan daina kuka? Sai yashe hankali na zai kwanta?
Wata zuciyar ce tace sai ranan da Jamal ya dawo, idan kuma mutuwa yayi fah?
Cikin sauri ta girgirza kai tare da fashewa da kuka, tana kukan take fadin Allah karka nufeni da ganin wannan ranan, inason nasake ganin Jamal a idona, inason nasakejin muryan sa tare da kamshin turaren sa"
Daidai momy tayi ma hajiya asabe rakiya tana shigowa taji sautin kukan Asma'u"
Aguje ta karasa ta kalli asma'u tare da fadin meye kuma?
Cikin kuka tace momy idan wani abu ya sameshi ne ki gayamin dan Allah"
Shiru momy tayi na wani lokaci zuwa can tace"
Kinga ki kwantar da hankalin ki idan Allah ya yarda lfy kyalau zai dawo"
Kallon Momy kawai tayi acikin zuciyarta tunani kala2"
Cikin dare kwata kwata ta kasa bacci burinta kawai tasan wani hali yake ciki, tashi tayi ta zauna, sai lokacin ta kula momy ma bata dakin, mikewa tayi ta nufi falo, wannan lokacin babu tsoro ko fargaba azuciyanta"
Momy tagani ita da nafisa sai sallah suke, cikin sauri ta juya daki agogo takallah karfe 2:08am, jitayi bazata iya hakuri ba dole ta kira yaya usman adaren nan wata kila bazai boye mata ba"
Tana dannan no aka dauka kamar daman jira ake Asma'u? Taji yaya usman ya fada"
Cikin dakushshayar muyar ta amsa"
Shiru yayi kaman ruwa yacishi, zuwa can yace Asma'u me kikeyi har yanzun bakiyi bacci ba?
Kuka ne ya kubuce mata cikin kukan tace bakomai"
Shiru ya sakeyi sarai ya gane kuka take dan haka ya rasa mezaice mata"
Itama rasa ta ina zata fara tayi, zuwa can yaya usman yace"
Duba asma'u ki kwanta kiyi bacci da safe zan kiraki"
Haka ta hakura badan ranta yasoba, alwala taje tayi sannan tazo ta tada sallah, tanayi kwalla nasauka idonta"
Har aka kira sallahn asuba tana azaune bayan ta ida sallah tasake kiran no yaya usman, tare da alwashin zata cire kunya ta tambaye shi Jamal"
Yana dauka yace Asma'u kinyi bacci kuwa?
Rasa abincewa tayi tare da rikecewa"
Shiru na wani lokaci sannan yaya usman yace"
Menene ke damunki ?
Tsintan kanta tayi da fadin babu komai inason ne nayi mgn da anty fa'iza"
Toh ina zuwa, ya fada sannan ya kashe wayar"
Ba adaukin lokaci ba kiran yaya ya shigo cikin sauri ta dauka"
Gaisawa sukayi a gajarce sannan ma'u ta fara kuka"
Shiru fa,iza tayi tana sauraranta domin kota bude baki batasan me zatace ba"
Zuwa can ma'u ta tsagaita da kukan sanan tace"
Anty fa'iza meye nufin ku na boyemin halin da ake ciki, sabo dame za'a boye min, idan wani abu ne ya sameshi ku gayamin, kara tsananta kukanta yayi amman a haka tace anty ko ya mutu ne?
Muryan usman taji yana fadin"
Ke, be mutuba yanan da ransa, menene kikeyi haka? tun dare kike faman koke koke, Ku daman mata haka Kuke duk kubi ku dama mutum lissafi, yanzun ki bari yau zanshigo Abuja"
Babu laifi ta dan samu natsuwa, saidai yau ta lura gidan yafi kullum rikecewa dan yau ko abun kare ba'adaura ba domin babu masuci"
Da misalin karfe 2 Usman ya iso"
Asma'u na zaune idonta duk sun kode sunyi suntum nafisa ta shigo tace tazo daddy na kira"
Afalon ta same yaya usman da alhaji bashir, momy ma na zaune agefe"
Karasawa tayi ta zauna akasa, acikin dashshiyar muryanta ta gaida su"
Fuskan daddy atunkushe ya kira sunanta, sannan yaci gaba dacewa"
Akwai abun da banso ki sani ba, Amman ba yadda zanyi, ya zama dole kisani, domin abun ya wuce tunanina, tunda jamal ya tafi yau wata uku kenan babu lbr, tun bayan ta fiyanshi da wata daya be sake kiran kowaba kuma ko ankira ba'a samunshi"
Wannan dalili yasa muka fara tsorata kuma tundaga lokaci muke zuwa ofishin su, saidai suma Kansu basu da wani lbr akansu, kullum hakuri suke bamu, tare da nuna mana sunakan meman inda suke ne, amman yanzun mun yanke shawara Usman da shamsudeen zasubi bayan sa"
Tukafin daddy ya karasa ma'u ta fashe da kuka, sai yanzo ne takeji son Jamal me tsanani azuciyarta, fuskan shi ta hango a idonta tare da dogon hancin sa, baya murmushi amman duk sanda yayi abin sha'wa ne, cikin kuka tare da jan majina tace daddy zan bisu"
Kafin daddy yayi mgn deeni ya shigo cikin shirin tafiya tare da wata jaka rataye abayan sa....
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
[22:52, 1/2/2018] +234 806 744 6138: 💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
8⃣1⃣to8⃣3⃣
Wani kallo deeni ya watsa mata sannan ya dauke kanshi"
Cikin tausayawa daddy ya kalli ma'u sannan yace,....
Ki kwantar da hankalin ki asma'u ke macece babu abin da zaki iya illa ki kara musu aiki"
Zaman ki agida shi yafi ki zauna kiyiwa mijin ki addu'a"
Kuka ta kara fashewa dashi, Usman ne yacire tagumin sa yace....
Ke karki kawo mana hauka, yaza tasa mutane agaba keta mana kuka, meye amfanin kukan?
Tsagaitawa tayi da kukan tare da to she bakinta"
Ciga usman yayi da fada har sai da daddy yace ya isa haka usman ka mata ahankali, kasan mata da miji sai Allah
Wani haushi ne ya sake kama deeni, cikin shi yaji yayi sanyi aranshi yace wannan kukan da asma'u keyi na meye, anya ba babu soyayyar Jamal azuciyarta, dan yaga ko kallon inda yake batayi"
Ji yayi kamar yace bazashi ba ya zauna yaga iya gudun ruwanta amman bazai iya ba soboda ayanzun yana Ganin Momy ne tamkar ummin Sa dan haka bazai zauna ba agidaba bayan yana Ganin hankalin ta atashe"
Shiko usma sosai asma'u take bashi mamaki wai ita da take ikirarin zata kashe jamal saigata wujuga wujuga tana kukan rashin sa, kara kallonta yayi yaga idonta duk sun kunbura"
Juyawa Usman yayi ya kalli daddy yace"
Daddy ni zan wuce basai natafi da wani ba, nikadai ma zan iya"
A'a usman zanfi son ku tafi ku biyu zaifi"
Ba yadda usman ya iya dole tasa zai tafi da deeni badan ransa yaso ba"
Koda suka mike suna sallama ma'u kuka kawai take"
Bayan fitan su momy taita lallashim ma'u, tare da nuna mata ta rage damuwa karya jawo mata ciyo"
Bayan tafiyan su da kwana biyu usman yayiwa daddy waya amman batasan abinda suka tattauna ba, dan haka da daddare tacewa momy abata no da yaya usman ya kira dashi"
Momy bata mata musuba dakanta tasa mata no din"
Acikin daren ma'u takira no saidai usman naji muryanta ya kashe"
Washegari duk suna zaune afalo, kowa babu bakin mgn, zuwa wannan lokacin kuka ya daina zuwa ma'u saidai kunan zuciya wani irin zafi takeji akirjinta ji take kamar tayi tsuntsu ta ganta agaban Jamal, idan ma mutuwan ne ta daukesu tare"
Mikewa tayi ta fita daga falon"
Momy da nafisa ne suka bita da kallo"
Ankwashi kusan minti 15 ma'u bata dawoba dan haka Momy ta kalli kofar tace"
Nafisa dobumin Asma'u kigani waje ta zauna?
Dasauri nafisa ta fita zuwa can ta dawo tace momy bafata waje"
Bata waje ? Amman nan naga tayi, kota dawo ne ta wuce ne bamu kulaba, duba ciki"
Dawowa nafisa tayi tace momy saidai ko toilet ta Shiga amman bata daki"
Zama sukayi suna jiran fitowanta, har aka kwashe minti 30 dan haka momy ta mike gaba daya part din saida ta duba toilet din amman babu ma'u dan haka ta fito afirgice tana fadin nafisa asma'u fa bata gidan nan"
Gaba dayan su waje suka nufu, suna isa gurin me gadin suka hada baki wajen fadi"
Asma'u ta fita ne?
Gargiza kai megadin yayi tare da aje radion shi agefe sannan yace tun fitan Alhaji nake zaune gurin nan banga fitan kowa ba"
Shiru momy tayi zuwa can tace anya baba kodai bacci ya debeka ta wuce baka gantaba"
Girgiza kai yayi tare da fadin idona biyu hajiya babu wadda ya wuce"
Cikin sauri momy ta nufi part din Jamal nafisa nabinta abaya, tun kafin ta karasa tahango alamar kofar abude take"
Da saurinta tashiga cikin falan babu kowa dan haka kai tsaye ta nufi dakin ma'u, saidai abinda ya bata mamaki ma'u bata dakin, dan haka arude momy ta fito tana fadin nagaya muku asma'u bata gidan nan, har momy ta kama kofa zata fita Wata zuciyar tace baki duba dakin Jamal ba"
Cikin sauri ta juya hartana hadawa da gudu nafisa ma ba'abarta abaya ba"
Suna shiga dakin suka hango ma'u kwance akan gadon Jamal"
Bacci take idon ta duk shedan hawaye ya bushe, hannunta daya dauke da glass din Jamal yayin da dayan yake rike da jaridan Sa"
Kara matsawa momy tayi har bakin gadon ta kurawa ma'u ido, bacci take sosai, hannuwan ma'u tasake kallo take taji kwallah tacika mata ido, domin ita kanta hango Jamal tayi zaune sanye da gilashin sa, hannun shi dauke da jarida kamar yadda ya saba"
Kuka ne ya kubuce mata cikin sauri tasa hannunta ta toshe bakinta dan karta tashi ma'u
Nafisa ma kuka take tare dabin dakin da kallo"
Ahankali momy tace Allah ina rokonka dan tsarkin mulkin ka Kadawo da jamalumdeen gurin iyalan sa, muna tsananin bukatar sa"
Haka momy taita addu'oi me kama da sambatu, daga karshe ta jawowa ma'u kofar suka fita"
Sai yamma likis ma'u ta shigo, babu wadda yace mata kalla harta nemi guri ta zauna"
Zuwa can momy ta kalleta tace kinyi sallah?
Eh kawai tace sannan tasa kanta akasa"
Abinci nafisa ta dauko ta aje agaban ma'u sannan ta zauna tace muci"
Wani haushi ne ya kama ma'u dan haka tasa hannu ta ture abinci tare da fadin banci "
Momy ce ta kalle su sannan tace wanni irin bakici ina kula dake yau kusan kwana nawa? bakicin abinci, kina nufin rayuwa zata yiwo ahaka?
Kamar me shirin kuka tace momy konaci awuya yake tsayamin wlh baya wucewa"
Haka nan zaki daure Asma'u nikaina idan inacin abinci ji nake kamar inacin magani"
Momy wlh bazan iya ba yanzun ma kirjina zafi yake min ji nake kamar nufashina zai dauke"
🙆🏼Kinga?, Asma'u ki rage tunani karki jawowa kanki ciyo"
Washegari da safe ma'u taji wayarta na kara, tana dubawa taga Abba ne, duk da tana cikin wani hali saida taji farinci, dan ta dade tanason kiran Abba da mama tsoro ne yake hanata"
Cikin siriyar muryarta tayi sallama, Abba ya amsa sannan ta gaida shi"
Ya amsa babu yabo babu fallasa, nasiha ya shiga mata tare da nuna mata komai mukkadari ne daga Allah kuma babu wadda ya isa ya canja yin Allah"
Wanna mgn ta Abba ya kara tayarwa ma'u hankali saitake ganin kamar Jamal ya mutu ne, dan haka ta kara rikicewa da kuka tare da fadin abba ya mutu ne?
A'a waye yace miki ya mutu?
Toh abba naji kana min nasiha ne"
Jim, yayi zuwa can yace yanzun asma'u sai jamal ya mutune zanmiki nasiha?, toh yanzun wannan kuka da kikeyi meye amfanin sa?, kinfi iyayensa son sa ne?
ance baki cin abinci, rashin cin abincin shine zai dawo dashi?, ki natsu kimai addu'a shi yafi bukata ayanzun, kuka da rashin cin abinci bazaiyi magani ba, irin wannan nasiha daddy yaita mata harta sarara da kukan sannan yaba momy wayar, itama nasiha taita mata daga karshe sukayi sallama"
Ma'u bata daina zuwa dakin Jamal ba, kulum can take bacci rana, domin da dare bata iya bacci adakin nasa ma, wani abunsa take dauka ta rungume, bacci ne yake daukanta batare da sanin lokacin ba"
****
*Somalia*
Tunda Usman da deeni suka taho magana bata hada suba ko kallon juna basu yi"
Yau kwanan su biyo agarin, gida daya suke kwana kowa da barayin shi"
Hakanan usman yaji be yadda da deeni ba dan haka yake kulle dakin daya yake"
Shiko deeni yarasa wacce hanya zaibi dan yaga jamal dan yana son ya ganshi kafin kowa ya ganshi"
Ranan da suka cika kwana uku agarin deeni zaune wani soja ya shigo yace Oga yace ka fiti idan kashirya idan baka shirya ba xai wuce"
Tashi yayi cikin sauri domin aganin shi yafi kowa son ganin Jamal dan haka duk wulakancin da usman zai mai zai jure"
Amota daya suka tafi, wani katon waje yaga anshiga wadda yayi ma deeni kama da gidan sojoji"
Suna tsayawa Uman ya fita ya fara tafiya cikin hanzari irin naso na sojoji"
Ko ina ka kallah sojoji ne ke shawagi"
Gadan gadan usman ya nufi shiga cikin sauri sojojin dake wajen suka dakatar dashi"
Hannun Yasa yaciro idcard dinshi ya nuna musu, cikin sauri suka saramai tare da bashi hanya"
Ko waiwaye usman beyi ba ya shige, deeni ko basu barshi wucewa ba dan haka yacika kamar zai fashe
Heat beat
*Mmn Yazeed*
[22:52, 1/2/2018] +234 806 744 6138: 💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
*SADAUKARWA GA*
*Masoya BUGUN ZUCIYA*👍🏻👍🏻👍🏻💋💘💘
8⃣4⃣to8⃣6⃣
Wani guri deeni ya nufa ya zauna, abin duniya ya dameshi, yana kallon yadda sojojin ke kaiwa suna dawowa, dan zaman shi gurin ya fahimci suna girmama manyan su, koda kuwa sun wuce su ashekaru"
Dan ko usman da suka sara masa, da yawa daga ciki sun girmeshi, wani tunani ne ya fadon masa acikin rana waishi yana ina ne lokacin da wadannan yan fici ficin yaran sukai karatu?, me nakeyi agida? Har waddan da aka haifesu abayana suka zama wani abu ni ina zaune?
Yanzun gashi ina kallo akabar waccen me kama da lagwanin ya wuce, ni aka hanami, duk su ummi ne suka jamin, gaskiyan momy ne su ummi basu daurani hanya mekyau ba"
Tunawa yayi da malamin da ummi ta turo masa shima dukka bazai wuce 22 ba, amma gashi har na kiranshi malam, karatu abakin shi kamar me, shiru yayi na dan wani lokaci zuwa can yace"
Yanzun idan nace zanyi karatu ta ina zan fara?, ko secondary ban gama ba taya zan zama kaman wadancen"
Hawaye yaji yana zubomai hakika su ummi basumai adalci ba, kusan ma su suka kashemai rayuwa, ayanzun ya fahimci ilmi shine gaba yanzun gashi yana da lfy yana da karfi amman ya zama dan kallo"
Share hawaye yake yanayi yana basarwa dan kar wani ya fahimci halin da yake ciki"
Saida usman ya kwashe kusan awa biyu sannan suka fito, su da yawa ya gani, yayin da wani ya taho da gudu ya bude musu mota suka shiga"
Itakanta motar daka ganta saika tsorata domin fentinta kallar kakin su"
Yana kallo motar ta tashi yayin da wasu motocin suka rufa musu baya"
Shiko deeni yanan zaune agurin babu wadda ya sake bin ta kansa"
Misalin karfe 9:38 sanyin gurin ya fara damun sa, zucigarshi babu dadi wani irin radadin yake ji azuciyan shi, nisawa yayi, zuwa can yaji wayarsa tayi kara daddy ne"
Bayan sun gaisa ya tambayeshi halin da ake ciki"
Beji kunyan cewa babu abinda ya sani ba, kwashe duk halin da ake ciki yayi ya gayawa daddy"
Jamm, daddy yayi sanan yace toh bari nakira usman din yasa akaika masauki, idan babu dama ma kai ka dawo gida"
Basufi Monti 5 da aje wayaba wani yazo yacewa deeni ya taso yakaisa gida"
Tunda ga ranan be sake Saka usman a idonshi ba har tsayon sati biyu, amman idan sunyi waya da daddy yana ce masa yanzon suka gama waya da usman kuma babu wani lbr"
Ranan da suka cika sati 2, da rana deeni na zaune yana tunanin ma'u aharabar gidan"
Ganinta yayi acikin idonsa ranan da ya fara sakata a idonshi"
Tsugunawa tayi har kasa tace ina wuni yaya shamsudeen, tun lokacin yaji ta shiga ransa"
Dan kaha yake mata bakam ta gama budurinta aka shi, kuma lokacin ne ta gama shiga zuciyan shi, murmushi ya sakeyi tare da fadin Asma'u yariya ce me shiga zuciya, inama farincikin da muka samu afarkon haduwan mu ya daure har yanzun" duk da naga asma'u na kokarin tura son Jamal acikin zuciyanta kamar yadda nima nekeyi ayanzu, amman azahiri banason Jamal natsane Sa, bantabajin na tsani wani ba kamar yadda na tsane sa, nasani Malam ya gayamin ciwa babu kyau gaba, amman nakasa cire kiyayyan Jamal acikin zuciyata, cire kiyayyan sa ko nanufin nabar basa Asma'u, nikuma bazan iyaba, *Na dad'e ina dama furata bazan yadda haka nan wani ya shanye min ba*
Karan motocin dayaji ne ya tsayar mai da tunanin"
Usman yagani ya dakko daga mota duk yayi furu furu ya fita hankalin sa"
Suna saukeshi suka juya suka fita daga gidan, part dinshi ya shige batare daya kalli inda deeni yake ba"
Tashi deeni yayi yabishi yana daba kofar yajita kulle, dan haka ya koma gefenshi ya zauna zuciyan shi cike da tunani barkatai"
Washegari karfe 7:00am daddy ya kira deeni"
Cikin sanyin jiki suka gaisa da daddy sannan yace"
Shamsundeen ya kamata muhakura haka, dan atunanina Jamal baya raye, duk inda ake tunanin ganin su anje babu shi amman ansame gawan wasu daga cikin su, shima Jamal din ansame jakar sa tare da wayoyin Sa, amman shi babu shi cikin kuka daddy ya karasa mgnr"
Shiko deeni yarasa abin da yakeji yayi, farin cikine ko bakin ciki be sani ba"
Daddy ne yaci gaba da cewa ka hada kayanka yau zaka dawo, usman yace akwai abun da zai yi bayanzun zai dawo ba"
Koda suka aje waya deeni cewa aidaman nasan asma'u tawace"
Deeni besake ganin usman ba sai afilin jirgin sama, gani yayi ya rame idonshi jawur kamar garwashi, jakar dake hannunshi ya mikawa deeni yace kabawa daddy jakar Jamal ce"
Har jirgin ya tashi usman natsaye ya rungume hannun akirji"
*Abuja*
Koda deeni ya isa gida samun kofargidan yayi cike anata zuwa wa daddy jaje, abban ma'u ya hango zaune kusa da daddy dan haka yayi maza yabi ta baya dan bayanson ya ganshi agidan nan"
Daddy ko yaga wucewan deeni dan haka ya tashi yabi bayansa"
Zuwa can ya fito dauke da da jakar Jamal ahannun shi sannan ya kira Abba da alhaji bashir suka shiga cikin gida"
Falon ma cike yake da yan jaje cikin harda da momyn usman, tare da anty fa'iza"
Atsakiyar falon daddy ya tsaya yace inna asma'u?
Tana dakin nafisa"
Kai tasaye suka nufi dakin momy ma bayan su tabi"
Ma'u na zaune tayi tagumi taga abbanta ya shigo dan bata san da zuwan su ba"
Afirgice ta mike tare da dafa bango dan tasan hakanan abba bazaizo ba, idan ma yazo toh bazai shigo har daki ba"
Kamata momy tayi suka koma suka zauna, suma su daddy zama sukayi sannan suka fara mata nasiha daga karshe ya fada musu halin da ake ciki tare da ajiye jakar Jamal atsakiya"
Fashewa Momy tayi da wani irin kuka, me tsuma rai sannan tace ban yadda ba, alhaji be mutuba, idan kuma ya mutu babu abin da na isa nayi amman kubani gawan sa"
Ma'u ko batace kala ba, kuma batai kuka ba, asalima gutun murmushi ne akan idonta"
Wani irin mikewa tayi, cike da karfin guiwa ta tsuguna agaban jakar"
Ahankali ta zage zip din ta zazzage kanyan ciki akasa, Abba ne yayi yinkurin hanata amman daddy yace abarta"
barbaza kayan ta farayi nan taci karo da hotona ahankali ta zaro daya, kara zaro ido tayi ganin pic dinta, akofar gidan su deeni lokacin da taje ana gobe dauri auren su, ajiyewa tayi agefe sannan ta kara dauko wani, shima natane lokaci da yayi zuwa nafarko zai tafi bata manta ba lokacin ne yake ce mata yayi ciwo harya warke batamai sannu ba"
Haka taita fitowa dashi, duk natane alokuta daban daban, mamakine ya kamata dawani lokaci yake daukata hoto batare da ta sani ba, zabura tayi ta watsar da huton sannan ta rarumo wayar sa"
Kunnawa tayi, pic din tane ya bayana akan fuskan wayar tana zaune afalo hannnuta zane da lalle, daga cen gefen pic din an rubuta My Queen"
Tundaga lokacin wuta ya daukewa ma'u, ta kame kam, kwata kwata bata motsi illah hawaye dake diga ta gefe idota"
Momy na kuka tazo ta girgiza ta amman babu motsi kuma hawayen be daina sakkowa ba"
Ihu momy tasa haka ya jawo hankalin mutanen dake falon"
Da taimakon su aka aka daura ma'u agado sannan daddy ya fita domin ya dauko wayar sa ya kira family doctor"
Ta kofar baya ya fita dan haka dan haka yana fita sukaci karo da deeni"
Ganin daddy arude yasashi tambayan daddy fly?
Shima arude yace babu lfy, yariyan nan asma'u ta kwallafa rai akan mijinta, gashi yana nema ya zaman mata matsala, yanzun tana ganin jakarshi ta suma"
Daddy be jira jin abin da deeni zaice ba ya wuce"
Deeni ko jikin bango ya manne tare da fadin suma? da gaske asma'u daman son Jamal take? dagaske ba dan antursasata bane take zaune? Wata zuciyarce tace da gaske ne mana lokacin da ta
rasaka ai bata suma ba, jiyaye kamar numfashin sa zai dauke, wani irin kara yakeji daga kasan zuciyan shi, nan ya manne ajikin bango tare da fitar da wani iron numfashi
Bayan doctor yazu ya gama aune aunen sa, ya tabbatar ma'u ta kamu da ciwon zuciya, wadda yace idan ba ai hankali ba zuciyarta zata bugu"
Lokaci da doctor kewa daddy mabayani, deeni naji dan hanka hakalin sa ya kara tashi, kafuwan sa banda rawa babu abinda suke"
Awannan halin daddy ya fito yasamu deeni dan haka yace kai kuma meke damun ka"
Be iya amsawa ba, kira daddy ya fara kwalawa Dr tare da tafiya yana fadin zo ka dubamin shi"
Deeni najin haka yaja jiki yana matsanancin haki yabi ta wani logu yabar gidan dan ya tabbarar idan aka gwadashi za,ace zuciyar shi ta wargatse"
Koda suka dawo babu kowa gurin dan haka daddy yace yaje zai kawo sa"
****
Tsayon kwana 3 ma'u ta fara motsawa, amman babu baki kuma hawayen nan makale agefen idonta bata rabo dashi"
Haka kuma batacin abinci koda yaushe ruwa, dan haka momy take dama mata koko datace ruwa saita zuba ruwa akai ta mika mata"
Aranan su abba suka tafi gaba daya bayam sun mata nasiha sosai, sunso su tafi da ita amma ta nuna bazata ba"
Deeni ko kokari boye damuwan shi yake amman ji yake zuciyar shi tafi garwashi zafi"
Tsayon sati daya da tafiyan su abba amman bar yanzun ma'u bata magana ta rame ko cikakiyar mikewa bata iyawa, farau faraun ma yanzun sai anyi da gaske takesha wanna wadda tarage shi momy ke kurbewa"
Damisalin 12:31am kowa ya kwanta ammam babu wadda ya runtsa"
Dagacan suka farajin kara motaci tare da hayaniya"
Cikin sauri daddy ya tashi ya zauna yana tunanin anguwar lfy kuwa? yana yinkurin sauka agadon wayar sa tai kara, be duba no ba ya dauka tare da mikewa tsaye"
Muryan usman yaji yana fadin daddy abude mana Get"
Fitowa daddy yayi yana tsakiyar falon ya daga murya yace usman kana nufin kana kofar Gidan nan?
Wannan mgn ta daddy babu wada bejitaba dan duk Gidan basu runta ba"
Daidai lokacin da daddy ke fadin baba megadi bude get, a guje ma'u ta duro daga gado, tana fitowa falo ta fadi kasa......
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
.💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
8⃣7⃣to8⃣9⃣
Ma'u na kwance akasa taga wucewan momy da nafisa aguje dan haka tafara kokarin mikewa amman jiri sai maita yake"
Daga can ta farajin karan momtoci suna shigowa gidan tare da hayaniyan mutane"
Ai ganinta kawai tayi ta mike, tana daf da isa gurin taji momy na fadin....
Usman ?, ansame Jamal din ne?
Bataji amsan da usman yaba momy ba tasakejin daddy yace yana raye?
Aguje ta kwasa ganinta kawai tayi atsakiyan sojoji, kutsawa taitayi har ta isa gaban motar da taga sunzagaye"
Anan taga suna ciki cikin fito da Jamal daga cikin motar"
Daga momy har abba rigegen kallon Jamal suke, dan haka gaba daya sunkewaye gurin"
Momy fadi take Jamal? Kaine Jamal?
Ahakali yace nine momy"
Ina ka shiga jamal kabarmu cikin wani hali?
Cikin yanayi irin na mejin jiki yace kuyi hakuri"
Itako ma'u har yanzun raba ido take takalli deeni, domin kafarshi kawai take iya gani mutane duk suntare mata ganin sa"
Wani daga cikin sojojin ne yace.....
Alhaji yakamata akaishi ciki domin yana bugatan hutu"
Cak suka daukeshi suka nufi part din daddy, kan gadon daddy suka kwantar dashi, sannan suka juya usman kadai ya zauna"
Duk suna tsaye akan jamal daddy Momy, nafisa ma tana tsaye agefe"
Jamal suke kare ma kallo yadda aka daure cinyan shi duk biyun, gashi yayi wani irin baki ya rame, tare da tarin uban kasunba"
Bayan daddy ya gama karewa Jamal kallo ya kalli usman yace"
Wai karayace har cinya biyu?
Girgiza kai Jamal yayi tare da fadin harbi ne aduk kafa fuwan, kuma ya shiga naman sa sosai, dan haka akace karya taka kafan harsai wajen ya warke"
Jimami sukaitayi akan jamal, shidai yana kwance idonshi rufe shi kadai yasan me yakeji"
Sai lokacin Momy ta juya ta kalli dakin tare da fadin a'a ina asma'u?
Gaba dayansu waigowa sukayi suna kallon dakin arude sukayo waje"
Itako ma'u kunya ce ta kamata tana kutsawa momy da abba suna kutsawa dan haka ta zauna afalo tare da hada kai da guiwa domin ta kusa tasa Jamal a idon ta, amman saidai shi kanshima Jamal din kunyan hada ido take dashi"
Suna fitowa suka ganta zaune tayi tagumi"
Daddy ne yace ke meyasa zaki zauna Anan ?, tashi maza"
Kanta akasa ta fara kokarin mikewa Momy ce ta taimaka mata ta mike sannan ta riketa har suka shiga dakin"
Abakin gadon ta zaunar da ita sannan ta juya ta fita badan tagaji da kallon Jamal ba saidan ta kula kamar kunya ma'u takeji"
Shima Jamal din yanajin fitan momy ya bude ido da sauri ya sauke kan ma'u, cikin sauri ya fara kokarin jawo jikin shi kusa da ita tare da miko hannu"
Usman deke zaune agefe ya dago kai ya kalli ma'u gani yayi har yanzun bata daga kai ta kalli Jamal ba, dan haka ya mike ya fice"
Kaman jira ma'u take ta juya ta kalli Jamal tare da fadawa kan kirjin shi, fashewa tayi da wani irin kuka har su momyn dake falo suna jinta"
Hannun shi yasa guda daya ya kara danna kanta akirjin shi, ji yayi zuciyar shi fari kar domin kukan ma'u ya tabbatar mai tayi missing dinshi"
Dan kwalin dake kanta ya zame sannan ya tura hannun shi cikin gashin kanta, zuwa can ya fara sunbatanta tun daga gashin kanta har zuwa wuyanta"
Kara karfin kukanta tayi tare dasa hannunta tana cakumo mai gaban riga kamadai me shirin fada"
Tsayawa yayi cak yan kallonta zuwa can ya rike hannunta muryan shi can kasa yace husna menene haka?
abin kuma fada ne?
Tsayawa tayi cak tana sauraran muryan shi, jin abin take kamar mafarki Dan haka ta dago kai ta kalleshi, kur sukawa juna, zuwa can ta bude baki cikin kuka tace
Yaya Jamal kai ne???
Nine husna"
Hannun ta kara kaiwa kan kirjin shi tare da fadin, Allah yasa ba gizo idona kemin ba"
Kara shafu gashinta yayi tare da kura mata ido, muyar kasa kasa yace.....
Husna ba gizo idonki ke miki ba nine da kaina"
Kusan minti 5 suna kallon junan su zuwa can ma'u ta cire idonta tare da wasa da yatsanta"
Jamal ko ci gaba yayi da kallonta tundaga fuska har zuwa hannun da take wasa dashi"
Kara jawoyo jiki yayi ya rike hannun"
Cikin sauri tayi yinkurin kwace hannunta tare da matsawa can bakin gadon"
Jamal ma kara jawo jiki yayi ya iso bakin gado yana kokarin mika hannun shi ya kamo na ma'u ta mike da sauri ta fita"
Lebe Jamal ya cija sannan ya fara kwalawa usman kira"
Daman usman naganin wucewan ma'u ya mike tare da bin bayan ta da kallo, acikin zuciyar shi yace munafukar yariya"
Yanajin muyar Jamal ya nufi dakin da sauri"
Samunshi yayi ya dawo bakin gado dan haka yace menene haka Jamal?, yaya akayi ka dawo nan?
Kawar da zancen yayi da fadin wai husna tayi ciwo ne naga duk ta rame?
Bazan usman yayi dashi sannan ya gyara mai kwanciya, juyawa yayi yana fadin duk dai abinda zakayi kayi ahankali, kasan dai abinda likita yace"
Shima share zancen yayi bece komai ba"
Washegari gidan cika yayi da baki, cikin harda abba da mama"
Ma'u kasa hada ido tayi dasu abba wani irin kunya takeji idan ta tuna yadda taita kuka akan Jamal"
Tun daren da Jamal ya dawo deeni ya sani Amman yanata kaucewa haduwa dashi"
Kwanan su Abba 1 suka koma, kuma aranan ne alhaji bashir ya kawo ummi deeni"
Bayan tayiwa momy Allah ya kyauta gaba, suka rankaya harda dakin Jamal"
Jamal naganin ummi gaban sa ya fadi domin bazai taba manta wannan fuskar ba"
Saidai abin da ya basa mamaki menene ya kawota gidan su"
Adaddafe suka gaisa, sannan Jamal ya kureta da ido"
Bayan tafiyanta Jamal
yasa usman
ya kira masa momy"
Zama momy tayi kusa da Jamal sannan tace gani yaya akayi?
Idonshi kur awaje daya yace, momy wannan matar da kuka shigo tare wacece?
Kanta tsaye tace matar babanka ce alhaji bashir, itace babar shamsuddeen"
Shamsuddeeni ? Jamal ya maimaita sannan yayi shiru, zuwa can yace Momy kina nufin itace mahaifiyar shamsuddenin da daddy yake gayamin?
Cikin fara'a momy tace itace, ai shamsuddeenin ma yana nan gidan, kasan wani irine shi shiyasa baku haduba, saidai mutaro mumai addu'a Allah ya shirye shi"
Gaban Jamal sake bugawa yayi, Allah Allah yake Momy ta fita ya kira ma'u dan ita kadai take da amsan tambayen shi"
Ji yayi hankalin shi ya tashi idonshi ya rufe mamaki ne yasa ya rasa mezai yi yaji daddi, gashi babu damar tafiya"
Bayan momy ta fita usman ya dawo tun kafin ya zauna jamal yace....
Usman dan Allah kiramin Husna"
Wani irin kollo usman ya masa sannan yace wannan ne kuma baka isa ba wlh, komenene xanyi maka amman ka daina min zancen asma'u bare ma har kace nakira maka ita"
Shiru yayi zuwa can yace toh bani aron wayarka nakira"
Mikamai yayi sannan ya mike ya fita, yana zaune afalo ma'u tazo tashiga dakin da Jamal yake"
Acikin zuciyar shi
Yace wannan ba girmana bane, ya kamata nabar gidan nan"
Ma'u nashiga Jamal ya mata wani irin kallo, tunda take bata taba ganin ya mata irin kallon ba"
Tsayawa tayi tana kallon shi"
Fuskanshi dauke da bacin rai yace"
Husna ke munafuka ce ko? Dake da deeni kuka kulla wannan munafuncin ko, tayaya za,ace deeni dan uwanane? Sai yanzun nasan kunnen kashi gareki, wato kin kawoshi har cikin gidan ubana kuci amanata?
Tuni ma'u fara kuka tare da fadin yaya Jamal bari kaji, dan Allah ka tsaya kaji"
Be saurareta ba daga murya yake cikin fada yana cewa.....
Husna ni kika munafunta ashe duk kukan da akace kinyi na rashina muna funcin ne? shikenan nagaji da halin ki hakurina ya kare, husna inada tsananin kishi akan abin da nake so, zan hakura dake dan nasan yanzun kinbashi kanki"
Cikin kuka take girgiza kai tare da fadin wlh a'a yaya Jamal ka tsaya kaji, wlh bansan komai ba game da zuwan deeni gidan nan, nikaina dana ganshi nayi mamaki, wlh yaya Jamal ban kulashi ba, kuma babu wani abu daya shiga tsakanina dashi"
Cikin tsawa yace karya ne, karya kikeyi, tun kina gidan iyayenki kikai niyar basa kanki, nasan komai"
Dam taji gabanta ya buga take hawaye suka fara zubowa kamar anbude famfo"
Cikin kukan tace yaya Jamal karka yanke hukunci cikin fushi, wlh wlh banci amanarka ba, dan Allah ka natsu karka batamin suna, yaya Jamal karkai sanadin da iyayena zasu tsine min, idan kayi haka ka zalinceni,😭 zanta kuka har karshen rayuta, dan Allah kamin adalci🙏🏻
Wata muguwar tsawa ya daka mata tare da fadin fita kibani guri"
Aguje ta fita tana sheshshekar kuka, cikin mamaki usman ya shiga cikin dakin"
Samun Jamal yayi fuskan shi murtuk idonshi jawur"
Yaya dai ? Usman ya tambaya yana kokarin zama"
Tsaki jamal yaja sannan ya kyauda kai tare da fadin babu komai"
Shima usman tsaki yaja sannan sannan yace wlh kaji kunya akan asma'u zaka dinga bata ranka har kana daga murya tun daga falo nakejin hargagin ka"
Tsaki Jamal yasake ja sannan yace.....
Sanda zaka tafi nemana ance kaida dan gidan baba bashir kuka tafi, amman meyasa baka gayamin deeni bane saurayin husna?
Deeni? Kana nufin shamsundden shine deeni?
Au zakacemin baka gane bane?
Dafashi usman yayi sannan yace yace, aini bawani sanin sa nayiba ina kamar so daya na taba ganinsa, dan bezama dole nagane shiba, amman kai me kake tunani akan hakan?
Kanshi tsaye yace akwai wani abu ban yadda da wannan Al'amarin ba"
Wani iri usman yaji cikin sauri yace jamal zan baka shawara badan asma'u tana kanwata ba, dan Allah ka aje kishinka agefe kayi bincike"
*****
Haka suka kwashe sati tsakanin ma'u da Jamal ba wadda yake runtawa saboda damuwa, hakama usman da tausayin abban sa ya damesa"
Kuma sosai yaji zafin kalaman Jamal amman babu yadda zaiyi dole ya daure"
Yauma kamar kulum jamal na zaune akan gado yana aikin tunani yaga daddy ya turo kofar rike da hannun deeni"
Mantawa yayi da ciwon dake kafarsa daddy be ankaraba yaga Jamal shakure da wuyan deeeni"
Arude daddy ya rike Jamal din tare da fadin yaya haka Jamal? innalilahi wa inna ilaihir raju'un, kasa kwatan deeni yayi"
Shiko deeni beyi yunkurin kwatan kanshiba, gutun murmushi ne akan fuskan shi, tare da tarin wahala"
Salatin Abba ne yajawo hankalin duk mutanen gidan ciki harda ma'u
Daker usman ya kwaci deeni ahannun jamal , Jamal cigaba yayi da fadin wlh koni ko kai, yariya ma tayi aure bazaka barta ba? tana gidan mijinta kana bibiyanta?
Sororo su momy sukayi, har ya gaba bambamin sa ya juya ya kalli ma'u dake tsaye cikin dogowar riga kanta babu dan kwali"
Hannun shi ya kada yana nuna ma'u tare da fadin.....
Eh tunda kin ganshi ai dole ki fito tsirara, juyawa yayi yana dingishi sannan ya koma bakin gado ya zauna"
Ya bude baki zaiyi mgn momy tazo da sauri ta matsamai baki, tare da fadin Jamal? Wasu irin maganganu kakeyi haka? Kwakwalwarka ta samu matsala ne"
Daddy ko tunda yaji kalaman Jamal ya dago kan zancen, dan abban ma'u be rufemai komai ba"
Kallon deeni yayi ya kalli Jamal sannan yace duk kuzauna, Malam Jamal ai abin bekai haka ba"
Kai deeni daman kaine wadda ka taba neman asma'u shine baka taba gayamin ba?
Shiru yayi tare da sosa kai, ke kuma asma'u meyasa baki nuna kisan shamsudeen ba"
Sukuyar dakai tayi tare da share hawaye"
Cikin sauri Jamal yace ai munafukai ne, bazasu fada ba"
Momy ce ta kara dakatar dashi tare da fadin kul Jamal bari zargin matar ka idan ba hakaba zaka lalata auren ka' kuma nikaina shaida ce, tun ranan haduwan su da shamsudeen asma'u ta rikece tazama firgitattaciya kwanciya dakin nafisa ya gagareta, daga karshema tacemin ita adakina zatana kwana, wlh dataji kara take tsorata, dole tasa nake rufe kofa, ko falo bata fitowa"
Wani sanyi Jamal yaji azuciyan shi, daddy ne yace"
Jamal shamsudeen dan uwanka ne, da wacce ta haifeni da wacce ta haifi baban sa uwa daya uba daya suke, dan haka babu fada, kada nasakejin Wata mgn, wannan ma ai zancen baza ne kakeyi asma'u ai matar Aure ce, wani kishin banza zaka nuna mana?
Shiru Jamal yayi tare dasa hannun shi yasafu fuskan shi"
Shiko deeni kyauda kai yake tare dajin wani iri acikin zuciyar Sa"
Daddy ne ya juya ya kalli deeni sannan yace"
Kai kuma Shamsudeen kayi hakuri, kadauka dama can asma'u ba rabonka bace, Kuma ba laifin mahaifinta bane, kasa azuciyar ka Allah ne me badawa kuma me hanawa karfin mutum da dukiyar sa baza su iya bada abinda Allah be yadda dashi ba, haka kuma inda Allah ya nufa asma'u matar kace Duk kin da mahaifinta yayi saika aureta, dan haka ina dada baka hakuri, Sannan nabaka dama kaje ka nemi yariyar da kakeso ko yar gidan waye zan tsaya maka, amman ka gyara halinka, nasani ka rage wasu abubuwa amman inason cigaban yafi haka, Allah ya muku Albar ka🙏🏻🙏🏻
Deeni bece komai ba kuma be daga kai ya kalli kowaba ya tashi ya fita"
Cikin sauri daddy yabi bayan shi, momy ma mikewa tayi sannan ta mikawa asma'u hannu suka fice"
Daga Jamal sai usman suka rage adakin, Jamal sai kyauda kai yake' sai yanzun yakejin kunyan usman"
. Da daddare Jamal ya dami Momy da waya, saidai daya kira kusan sau 6 kuma data dauka saiyace ya manta ne, ba ita zai kira ba"
No ma'u tun rana yake kira amman ba'a dauka"
Momy yasake kira bayan ta dauka yasake Jan tsaki yace wai no nan rikina ni take"
Gutum murmushi momy tayi sannan tace....
Anya jamal mantuwa ce ? kodai asma'u....
Bejira me momy zatace ba yayi maza ya kashe wayar"
Befi da minti goma ma'u ta shigo, fuskanta turbune, kamar zatai kuka, can nesa dashi ta tsaya sannan ta sunkuyar da kanta tare da fadin gani"
Kallonta yayi sosai sannan ya nuna mata gefen shi tare da fadin zokizauna"
Karasa tayi ta zauna inda ya nuna mata, cikin zafin nama ya jawota jikin shi ya rungume"
Sun dadde ahaka, dumin jikinta ya gama daburta shi, wani tunani ya fara kawowa, zaiso hakan ya kasan ce ayau, amman kuma likita yace karna ataka kafar bare asa masu ruwa, wanka ma da dabara usman ke masa"
Wata zuciyar ce ta tambayeshi bazaka iya bane? Zan iya ya bata amsa, haka zuciyar shi taci gaba da bashi karfin guiwa dan haka yasa hannun shi ya yaye hijjabin dake jikinta ya ajeshi agefe"
Arude ma'u tace dan Allah kabari yaya usman fah yana falo"
Cikin Wata kasalalliyar murya yace bazan iyaba inason Zumata ayau.....
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
9⃣0⃣to9⃣2⃣
eyi yinkurin hanawa ba, cikin sauri ya saketa tare da kauda kansa gefe"
Bakin gadon ta zauna jikinta asanyaye, waigowa Jamal yayi ya kalli ma'u sannan yace.....
Oya tashi ki tafi, tunda nikikewa rowa, ina matsayin mijin ki amman na nemi hakki na aki bani, ni daman nasan ba sona kike ba, ai waccen katon dan isanka kin bashi dama sobo dashi kina son shi"
Da sauri ta waiga ta kalleshi tare da fadin yaya Jamal ni ka dani gayamin irin wannan mgr.....
Bazan bariba baki bashi dama bane? Duk hiranku kedashi inasa ne da ita niba jahili bane da ilmina karkiga kamar bansan abun da nake ba, da kunnena naji bawani bane ya gayamin, na dade ina dama furata bazan bari wani daga sama ya shanye min ba, zaki iya tuna amsan da kika bashi alokacin?
Idan bazaki iyaba barin tuna miki"
Kuka ne yaci karfin ma'u tare da wani irin nadama, fada ta farawa kanta da kanta meyasa bataji mgr Abba ba tun farko gashi abin na neman zama mata matsala agidan aurenta"
Girgiza kai tayi tare da fadin yaya Jamal nace maka kabar irin wannan maganganun, dan Allah ka bari"
Jajayen idonshi ya sauke akanta sannan yace....
Bazan bariba Husna, aduk lokacin dana nemin wani abugurin ki kika hanani abinda nake tunuwa kenan, fita kiban waje"
Mikewa tayi cikin fushi ta fita, usman ne ya kula cikin fushi take dan haka ya tsaidata tare da fadin yaya akayi?
Hawaye ta share tare da saukar da kanta kasa, zuwa can ta bude baki zatai mgn yaya usman ya tsaidata"
Ido ya zuba mata yana kallon yadda take share hawaye zuwa can yace....
Ki koma ki bashi hakuri"
Ido ta daga ta kalli usman da niyar mgn ya sake tsaidata tare da fadin nace miki kibashi hakuri ko?
Juyawa tayi ta koma ta sameshi idon shi kamar me bacci, cikin siririyar muryanta tace....
Yaya Jamal kayi hakuri bazan sake maka musuba"
Saida ta maimaita sannan ya bude ido tare da miko hannun Sa"
Karasawa tayi da saurinta dan gudun karta kara laifi"
Sosai ya shige jikinta, dada jawota yake kamar wadda yayi wanka da ruwan sanyi alokacin sanyi"
Ma'u arude take amman babu yadda zatayi dole tasa ta rufe idonta tanajin yadda hannun Jamal yake Yawo ajikinta"
Jikinta banda rawa babu abunda yake sai yazon ne tasan me aure yake nufi da batasan menene Aure ba, ko lokacin da ta bamawa deeni dama bata kawo ya zataji ajikinta ba, itadai kawai tanason taga deeni yayi farin ciki"
Yanzun ne wannan tunanin ya fado mata, yanzun ne take tuna lallai idan tabar Jamal zai gana mata azaba, amman bata isa tace komai ba idan ba haka ba yanzun nan Jamal zai burkitata"
Haka tanaji tana gani Jamal ya fara rabata da kayan jikinta, yadda yakeyi bazaki ce akwai ciwo ajikin saba ya manta da cewo sha'anin sa kawai yake "
Ganin haka abin ya farabawa ma'u tsoro da mamaki yanzun yaya Jamal ne yakemin haka mutum me jijji dakai tare dashariya"
Abu ya dada kankama ma'u dukta firgita da sallon Jamal, kuka tasa tare da rike hannunsa"
Jaye hannun sa yayi yaci gaba da abin da yakeyi, tare da tushe mata baki da nasa"
Ganin inda Jamal ya rikice ya makale ma'u yasa nayi saurin barin dakin😜
Jikin kofar na makale daga can naji ma'u tayi wata yar kara, shiko Jamal wani irin nishi yake kamar wadda ya shanye robar yaji"
Zuwa can naji yana cewa....
Tsarki ya tabbata ga ubangijin daya kago wannan halittan, Allah ya miki Albarka, Husna dame zan kwatantaki, idan nace miki zuma ma na maidaki baya, husna barin takaice miki, duk duniya babu wani abu me dadin dazan kwatantaki dashi, shiru naji, zuwa can ya sake cewa Husna dadinki yafi dadi dadi, kin sani farin ciki mara misaltuwa Allah ya miki albarka"
Kuka kawai ma'u ke yi, saboda irin radadin da takeji ta kasan ta, hawaye ya fara share mata, zuwa can ya wawusheta yayi toilet da ita"
Gasata yayi tsaf, duk da cewa bata son haka amman ba yadda zatayi dole ta daure"
A toilet din ya baro ta ya fito ya canza zanin gadon sannan ya boye wadda ya cire"
Daidai lokacin asma,u ta fito, tana kanin Jamal ta rufe ido"
Kamota yayi ya zaunar da ita abakin gadon fuskan sa dauke da farin ciki, yace.....
Bude idonki mana"
Kin budewa yayi dan haka yace....
OK to shikenan amman inason kimin wani abu dan Allah kijirani naje nayi wanka kinga idan usman yaga Zanyi wanka bazai barni ba"
Komai batace ba ya juya fita, taganin shiganshi ta mike ta maida kayanta sannan ta maida hijjabinta ta zauna"
Be Wani dade ba ya fito yana dingishi tare da runtse idonshi guda daya"
Cikin sauri ya maida kayanshi sannan ya hau gadon ya kwanta"
Jawota yaso yi jikinshi cikin sauri ta mike tana dingisawa"
Gani tayi usman be wajen dan haka tawuce batare da wani ya gantaba"
Bayan nafisa ta kwanta idonta be daina zubar da ruwaba kamar yadda jikin ta be daina mata zugiba"
Can cikin dare zazzabi ya rufeta, rawan sanyinta ne ya tashi nafisa"
Ganin halin da take ciki Yasa ta kira momy"
P.c.m momy ta bata sannan ta rufeta da katon barko kafin da same akira likita"
Kusan kwana Jamal yayi yana kiran wayar ma'u amman taki dagawa"
Yau tsayon sati daya kenan ma'u bata daukan kiran Jamal, sannan kullum saiya aiko nafisa kiranta saitaki zuwa"
Momy ma hartayi mgn ta gaji, kirikiri take kin zuwa"
Ranan doctor dayake duba kafar Jamal yazo yana warware ciwon yace kash amman nace muku kar abari ruwa ya taba gurin"
Cikin sauri usman ya eh doctor ai munabin doka"
Girgiza kai yayi tare da fadin wannan kamar ansa musu ruwa sosai ma kuwa"
Usman ne ya kalli deeni yace kasa ruwa ne ?
Kyauda kai Jamal yayayi tare da fadin ni? Idan ma ruwan ne saidai idan kai kazuba"
Tsaki likitan yaja sannan ya fara wanke ciwon tare da kwaso ruwan daya shiga cikin ramin"
Bayan ya kama nadee kafar yayi tare da fadin ku kula sosai dan Allah kuma karya taka kafar koda yaushe ta kasance amike, idan ba hakaba gurin bazai warke yadda ya kamata ba naman wajen zai iya tattatewa"
Doctor na fita momy tacewa usman ko za'abar wankan ne?
Eh momy gara abarshi"
Momy najuyawa zata fita jamal yace usman dan rakani dakin nafisa"
Waigowa momy tayi sannan tace...
Kanajin dai abinda likita yace ko?, usman karka kulashi"
Mikewa yayi tare da fadin aini momy yau fitama zanyi basai ya ganni ba"
Kaitaye momy dakin nafisa ta nufa, hannun ma'u ta kamo bata saketa ba saida ta kaita gaban Jamal, sannan ta juya ta fita"
Murmushi ya sakar mata sannnan yace....
Husna wani irin huro ne wannan? Kodan kinga bani da kafa? Haba husna anya kina tausayamin kuwa ?
Muryanta kasa kasa ta fara gaidashi"
Make kafada yayi tare da fadin bazan amsaba, banason irin wannan gaisuwan"
Ahankali ta sake cewa wacce iri kake so?
Matso in nuna miki"
Saida gaban ta ya fadi, domin yanzun muryan Jamal kadai fadar mata da gaba take"
Ahankali ta karasa hannunsa ya ware, ta shige ciki"
Yauma Jamal be kyale ma'uba abinda ya nema rannan yauma shiyasa ke nema, harma yafi ranan nan zakiwa, tundaga ranan Jamal ya maida abin alada kullum sai yayi, tare da wujjugata sosai"
Ahaka har aka samu sati 2, dataje gaida shi usman yake fita falo, da wannan damar Jamal yake amfani yayi abin dayaso"
Wani fari yayi yai jawur, har usman na tsokanar shi dacewa lallai na iya jinya wannan irin murjewa haka"
Dariya kawai jamal keyi"
Domin shikadai yasan me yakeji"
****
Yau tunda ma'u ta tashi takejin miyau abakinta, ta rasa meke damunta"
Bata kawo tunanin komai azuciyarta ba, itadai kawai tunaninta bakinta ya bacci da kwadayi"
Zama tayi tana tunanin abinda zata saka abakinta domin miyoun ya daina zubowa"
Zuwa can tunaninta ya fada mata kan gwaiba, juyawa tayi tace nafisa nikam inasoncin gwaiba ina zan samu"
Tafff ai yanzun ba lokacinta bace"
Miyau ne cike da bakinta ta mike taje ta zubar tundaga ranan ma'u bata sakejin dadin jikinta ba"
Yauma kamar kullum ma'u taje gaida Jamal ta samu usman sai fifita yakemai, ya hada uban zufah"
Tsaye tayi agefe dan ko gaisuwan data mai ya kasa amsawa"
Zuwa can momy tashigo abincin dake gefe ta bude tare fadin....
Jamal daure katashi kaci abincin kafin likitan yazo"
Kallon abincin kawai ma'u tayi ta fara kakarin amai, da gudu ta nufi toilet, duk abinda ke cikinta saida ta amayar dashi"
Bayan ma'u ta fito wani irin kallo momy ta bita dashi me cike da tuhuma"
Gani tayi ma'u ta dashe tayi fari fat,
Acikin zuciyarta tace bazata sobo ba, dole nasa agwada min yariyar nan kamar ciki gareta daman Jamal ya fada akwai wata alaka tsakanin shamsudeen da asma'u na karyata shi, ga gaskiya na shirin bayyana
0 comments:
Post a Comment