Jamal ne ya bude idonshi tare da fadin momy daman bata da lfy ne?
Kunyan idon usman yasa momy ta amsa amman zuciyarta cike yake da bacin rai"
Daker ta iya cewa eh duk da bata fada ba Amman nakula kwana biyu batajin dadi"
Ido ya sake rufewa"
Momy juya tayi zata fita tare da fadin Asma'u zo"
Abaya tabi momy har cikin dakinta, nafisa ce zaune aciki tana nuke kaya, juyawa momy tayi ta kalleta tace....
Nafisa bamu guri"
Ajiye kayan take hannunta tayi ta fice"
Wani kallo momy tama ma'u sannan tace... .
Asma'u wannan watan kinyi al'ada?
Idonta tasa akasa sannan tace momy ai lokaci beyi ba"
Shiru momy tayi zuwa can tace....
Amman wancan watan daya wuce kinyi?
Eh"
Gaban ma'u banda faduwa babu abinda yake"
Sallaman doctor ne yasa momi mikewa ta fice"
Zuwa can momy ta dawo tace zo asma'u
Suna zuwa momy tace Dr gata"
Kallo kawai tabi momy dashi har aka debi jininta bata daina kallon momy ba"
Itama momyn kauda kai take tare da cin magani, cikin daure fuska tace doctor kaje ka gwada min yanzun dan Allah hankalina bazai kwanta ba har sai naga saka makon"
Hankalin ma'u Kara tashi yayi, kafa fowanta babu kwari"
Dakin Jamal suka koma yayin da momy ta zauna ta hakince ko fara'a bata yi"
Itama ma'u ta kurewa tayi saboda ganin fuskan momy babu annuri"
Saida Dr ya kwashe kusan awa 2 ya dawo"
Hannu ya mikawa usman suka gaisa sannan ya mikawa Jamal, tare da tambayan ya kafa?
Sannan ya juya gurin momy ya mika mata farar takarda tare da fadin Congratulation tana dauke da ciki na sati 2"
Yake Momy tayi sannan ta mike tare da fadin nawane kudin ka?
Adadin kudin ya gaya mata ta biya sannan ya juya ya tafi"
Shiko usman tunda yaji abinda likita yace ya kurama Jamal ido, so yake yasan me zaice amman Jamal yaki bude ido"
Itama ma'u kasa tayi da idonta tare da zallar tashin hankali"
Takardan momy ta jefawa ma'u tare da fadin Asma'u ina kika samo ciki?, bayan mijin ki na kwance ko bayi zashi saida dibara, yau satin shi 5 agidan nan, aina aka samu cikin sati 2?
Cikin sauri Jamal ya bude idonshi tare da kallon ma'u"
Kokarin tashi yake ya zauna dan haka usman ya taimaka mishi"
Hankalin usman tashe yake, ya rasama me zaice"
Momy ta sake cewa ba dake nake mgn ba"
Kuka ma'u ta fara harda shashsheka, domin ita yanzun batasan me zatace ba, domin ko a film bata taba ganin inda uwar miji ta tare matar danta da wannan tambayan ba"
Zaune Jamal yayi yana neman ta ina zai fara mgn mezaice? Ince cikina ne? Kai gaskiya inajin kunyan momy sosai bazan iyaba, acikin zuciyarshi yace Allah yasa husna tace cikina ne, nikuma idan antabaye ni nace eh kawai"
Daidai lokacin usman ya matsa kusa da ma'u yace dan ubanki badake ake mgn ba?
Idonta ta daga ta kalli jamal alma ya mata da hannu tace shine, kyauda idonta tayi tare da tsananin jin zafinshi aranta"
Gadan kadan usman ya nufi ma'u harya kai mata duka ta guce, ta nufi bayan Momy"
Cikin sauri momy ta matsa tabawa usman hanya"
Usman karka daketa, nawane cewar jamal
Cikin sauri momy ta matsa bakin gadon tace naka? Kana hauka ko? A yadda kake dinnan inakai ina kula mace, mezaka iya kafafuwa a daure kana tafiya daker, daidai da bayi sai an raka ka"
Shiru yayi yana sosa kai yazama dole ya bude baki yai mgn idan bahaka ba momy zata sheganta masa ciki"
Sosakai yayi tare da kauda kai gefe yace momy nidai kibar mgnn nan nawane wlh"
Tsakanin Jamal da momy kallon juna suyi inda momy take ganin ko ganin usman ne yasa yace nasa ne"
Jamal karka maidani mahaukaciya bawasa nake dakai ba,
Kara sunkuyar dakai yayi"
Karemai kallo momy tayi, sannan ta juya ta fita cikin tsananin tashin hankali, ma'u ma bayanta tabi"
Usman ne ya karasa bakin gadon yace jamal kaina ya kulle, tayaya asma'u zata samu cikin sati 2, dana Wata 5 akace zan yadda, kaida ke kwance tare fah muke kwana, har Bayi ni nake karaka ka"
Kanshi akasa yace.....
Wlh usman kuna bani mamaki kuntaba ganin inda ake tare matar aure da mijinta ace waye ya mata ciki?
Cikin ido usman ya kalli Jamal yace....
Me kake nufi da wannan mgnr?, kafito fili kamin dallah dallah"
Tsaki Jamal yaja sannan yace, dallah mlm karka dame ni, inace fa'iza tsohon ciki gareta, na taba tirkeka nace maka wayayi mata?
Cike da mamaki usman ya kalli Jamal sannan yace....
Kana nufin kaikayi kenan?
Dagowa Jamal yayi ya kalli usman sannan yace eh ninayi"
Kaika yi?
Eh, ya fada tare da jawo bargo ya rufe kansa"
Girgiza kai yayi tare da fadin gaskiya Jamal basan baka da hankaliba saiyau, banga amfanin zamana agidan nan ba wlh, yau yau zanbar garin nan, nakashe komai nawa nabaro aikina da iyalina dan nayi jinyanka amman kun maidani hoto, ni dan iskane haka kawai zakasa yariya ta rainani, Ashe shiyasa kwanaki da doctor yace ansawa kafa ruwa, dagewa kayi kai baka saba har kanacewa wai nina zuba maka, narantse da Allah dakai karamin yaro ne saina maka matsiyacin duka zanbar garin nan"
Bude fuska Jamal yayi sannan ya kalli usman yace....
Haba usman yazaka tasani agaba kaitamin fada, Husna fa matata ce, ba zina nayi ba"
Ai bance ba matarka mace amman ai anabarin halas kodan kunya sannan ga ciyon dake jikin ka, baka tunanin gurin ya samu matsala ko fah taka kafar ance karkayi"
Nifah usman bantaba karanta aya ko hadisi daya fadi haka ba, kuma ni wannan ciwon be isa ya kashemin rayuwa ba"
OK toh shikenan, azuciye usman ya fita"
Daddare ma'u na zaune momy ta shiko tace biyoni"
Hijjabinta tasa tabita abaya, dakin da Jamal yake ta nufa dan haka tabi bayan Sa"
Ma'u na shiga taga daddy adakin dan haka hankalinta ya kara tashi"
Tunkafin momy ta zauna daddy yace....
Asma'u taho nan Ki zauna"
Inda ya nuna mata ta zauna tare da matso hawaye"
Ahankali daddy yace.....
Jamal ance matarka nada cikin sati 2, shine nake son sanin ko naka ne?
Muyar kasa kasa yace eh"
Shiru daddy yayi sannan yace toh nakane dai kace ko?
Eh yasake fada ahankali"
Shiru daddy yayi zuwa can yace....
Toh Alhamdulillah Allah ya rabasu lfy, daman bawani abu bane yasa na tambaya saidan naga baka lfy, kuma matsalar acinya take, shiru ya sake yi sannan ya sake cewa toh shikenan babu koma, jiya usman yace ka kwana kafa na damun ka, dan haka yanzun likita zaizo ya dubaka"
Momy ko babu abunda take banda hararan Jamal ammam saiyaki kallonta"
Karfe 8:00pm likita ya shigo kwance kafar yayi yana mamakin yadda akayi gurin ya rarike haka"
Ganin inda doctor yake kallon gurin yasa daddy da momy lekawa, sosai gurin ya zurma, juwa yayi ya kalli Jamal yace kafannan anasa mata ruwa meyasa bazaka taimaki kanka ba, kaifa ba karamin yaro bane, meyasa zakana mayar mana da aiki baya"
Haka Dr yaita fada daga karshe ya wanke wajen sannan ya kara ja musu kunne"
Likitan na fita momy ta rufe Jamal da fada, ta inda take shiga ba tanan take fitaba"
Daidai lokacin usman ya shigo nan momy ta kwashe yadda sukayi da dr ta gayamai, sannan ta kara da cewa ashe Jamal da kanshi yake shekawa kansa ruwa saboda rashin hakuri irin nashi, wai ahaka dinnan ya danne yariya ya dirka mata ciki"
Daddy ne ya fara dakawa momy tsawa tare da fadin wai menene haka?
Itama cikin takaici tace barni alhaji abin ne yake bani takaici wlh, ji inda usman ya kashe komai nasa ya zauna dan yaga kasamu lfy"
Jamal ji yayi kamar ya nutse saboda tsabar kunya"
muyar usman game yana cewa.....
Aini momy gobe da sassafe zanbar garin nan, Asma'un tayi jinyar shi"
Kwama cala kenan, usman babu inda zaka, dan wlh idan akabar Jamal da asma'u adakin nan kafar Jamal rubewa zatayi"
Daddy kallo yabi Momy dashi sannan ya girgizakai ya fice domin kalamanta kunya take bashi agaban yara"
Momy naganin fitan dadddy tace....
Gobe idan Allah ya kaimo dakaina zankai Asma'u Kano taje taji da abinda ke cikinta, badan bazan iya jinyarta ba, saidan dan wannnan me wutan cikin....
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
Dedicated
*Sadnaf*👍🏻💋
9⃣6⃣to9⃣8⃣
Jamal be sake kallon inda suke ba, itako ma'u tana takure agefe"
Tattaunawa suka cigaba tsakanin momy da usman daga karshe momy taja ma'u suka wuce"
Adakinta ma'u ta kwana motsi kadan momy taji ma'u tayi zatace me kike so?
Washegari da safe momy da kanta ta hadawa ma'u kayanta sannan tace tayi wanka su tafi"
Wankan taje tayi saidai jikinta babu dadi hakama zuciyarta, azahiri batason Tafiyan tafison ta zauna gurin mijinta"
Bayan ta gama shiryawa ta zauna momy kadai take jira, tsintan kanta tayi da rafka uban tagumi"
Ahaka Momy ta sameta, dan haka ta tsaya cak tanabin ta da kallo sannan ta karasa kusa da ita tare da kiran sunan ta"
Ma'asawa tayi tare da kallon momy"
Ahankali momy tace.....
Asma'u anya kuwa kinason tafiyan nan?, kodai za'abar tafiyan ne?
Cikin sauri ta girgizakai tare da fadin inaso"
A'a asma'u bayan gashi naga duk kin shiga damuwa, ni asma'u bawai inason na rabaki da Jamal bane, wlh ciwon shine yake tayar min da hankali, kuma shi duk abinda likita yafada beji, idan wani abu ya faru Mu zai bari da wahala"
Nisawa tayi sannnan taci gaba da cewa kiyi hakuri nasani daga ke har Jamal bazakuji dadin hukunci na ba amman nan gaba zaku gane gata ake muku"
Tashi sukayi da nafisa kadai sukai sallama suka dauki hanya"
Karfe 2:38pm suka isa Kano suna isa gidan ma'u taga komai ya canja, kamar bata taba rayuwa agidan ba"
Mehadin ne yafara shiga da akwatin ma'u anan ne mama tagane sunyi baki"
Har sukashi falon momy na rike da hannun ma'u"
Da fara'a mama ta tarbe su, nan tashiga hidima dasu, bayan sun natsa ma'u tashi ta basu guri"
Dakinta na da ta shiga nan abubuwa da dama suka dawo mata, kwallace tacika mata ido, rayuwan su da deeni ne ya fara fado mata, dan haka batasan sanda ta fara hawaye ba"
Anan bacci ya kwasheta batare da tasan lokacin ba"
Ta dauki dogon lokaci tana bacci sai can kusan yamma ta farka"
Tana tashi taga wayarta tare da kudin masu yawa agefenta, kwasan kudin tayi ta nufi falo"
Babu kowa afalon dan haka ta nufi kitchen acan ta samu mama tana aikace2"
Mama na kallonta tayi murmushi tare da fadin Asma'u kin tashi?
Cikinjin kunya tace natashi mama ina momy"
Ai tuni ta wuce"
Mun shigo kina bacci tace abarki kar atashe Ki"
Wani iri taji azuciyarta, amman taki bari mama ta gane"
Tare da ma'u suka karasa aikin, bayan sungama tacewa mama zata gidan yaya usman"
Shiru mama tayi zuwa can tace......
Kin ganki, daga zuwanki zaki fara yawace yawace"
Turbune fuska ma'u tayi sannan tace.....
Mama gidan yaya usman din ne yawo? ni idan na tafima sai gobe zan dawo"
Tabe baki mama tayi sannan tace toh ai saiki bugawa mijinki waya idan ya amince drive ya sauke ki"
Da saurinta ta juya daki gyalenta ta dauka ta saka sannan ta fito ta samu mama zaune agefen kujera"
Kallonta tayi tace kinmai wayan ko?
Eh kawai tace tare da gyara gyalenta"
Sosai fa'iza tayi murnan ganin ma'u suna rungume da juna, zuwa can ta kalli ma'u ta sheke da dariya"
Dariya taitayi harda rike ciki, ma'u ta tsaya sororo tana kallonta"
Zuwa can fa'iza ta sarara da dariyan sannan ta kalli ma'u tace.....
Asma'u kenan, jiya keda mijin ki kuncikawa yayan ki ciki, ashe Jamal dan duniya ne ban sani ba?
Tsaki ma'u taja sannan ta daure fuska tare da fadin anty dan duniya fa kika ce?, kina nufin dan iska ne?
Cikin sauri fa'iza tasa hannunta abaki tare da fadin alallai, ni karkimin fassara bahaka nake nufi ba, kallon ma'u ta karayi har yanzun ranta abace yake, cikin ido ta kalli ma'u tace sai yau na yadda kiyayya tana komawa soyayya, kuma na yadda duk abinda babba ya hango yaro ko yahau rimi bazai gano shiba"
Saboda me kika ce haka?
Murmushi fa'iza tayi sannan tace.......
Na tuna lokacin da kike cewa ke bakison jamal kin tsane sa, ke har cewa kikayi idan aka aura miki shi saikin kasheshi, sai gashi yanzun kin fada kyaunar Jamal dumu dumu, lokacin da Jamal ya bace kika zama kamar zararriya, da ace har yanzun ba'aga Jamal ba wata kila dakin zare"
Shiru ma'u tayi tana nazari, zuwa can tace Anty?, wlh da kwata kwata bani da hankali, idan na zauna ina tunani sainace da wani hauka ne ya shigeni, dan rashin hankali na zauna naita musu dasu Abba, yana cewa ga abinda zanyi inacewa ga wadda nake so, sai yanzun naki ganin illar sarashin jin maganar iyaye, ba dama nayiwa yaya jamal wani dan abu nan danan saiya hassala yaita fada, dan haka yanzun duk abinda yace banamai musu inba haka ba saiyace ai lokacin deeni kaza, akwai wata mgn da mukayi nida deeni bakaramin mamaki nayi da naji abakin yaya Jamal ba, nan ta kwashe komai tagayawa fa'iza"
Jinjina kai fa'iza tayi tare da fadin gsky kuruciyar ki kinyi hauka da yawa, to yanzun gayamin matsayin deeni azuciyar Ki"
Cikin sauri tace....
Deeni?, wlh bana son ganin deeni domin idan naganshi tausayin shi yana kamani, Anty bazan boye miki ba, ayanzun inajin son Jamal kuma bana neman abun da zai rabani dashi, zama na dashi yasa na fahimci halin shi, halayen shi masu kyaune, dabi,un shi suna burgeni, anty yaya Jamal be faye son mgn ba duk abin da zai fito bakinsa me mahimmanci ne, sannan nakula yana tsananin sona dukda yana boyewa bayason nagane ko wani ya gane haka"
Nisawa tayi sannan taci gaba da cewa anty yaya jamal ya dade yana sona amman be bari kowa ya saniba yaita dannewa, kuma koda naje gidansu amatsayin matar sa ko kallo na bayayi, yana nuna bana gaban shi, Amman bayan bacewan shi da aka gano jakarshi nagono sirrikan shi da dama, hutonane bila adadin awayar yaya Jamal wadda bansan sanda ya dauke su ba, sannan hutonane akan wayar Sa, tun alokacin naji sonshi ya ratsa ko ina ajikina"
Dariya fa'iza tayi sannan tace Jamal dai yaci gari kenan?, ya ture gwamnatin deeni"
Girgiza kai tayi tare da fadin to anty idan ma inasonshi yaya zanyi?, da dai ammana umarni da auren maza 2 to wlh dana kara da deeni dan wlh tausayin deeni ya hanani nayi walwala, ina tananin tausayin sa, kuma inaso rayuwar sa ta inganta, wani lokacin inaganin laifin zuciyata data fada son jamal"
Hirar tasu bata kare bace, dan haka sukayi shirin zuwa gidan dada"
Tafe suke suna cigaba da hirarsu, acikin su babu wadda ta tambayi mijinta"
Sun kusa isa gidan ma'u ta tsaya tana waige"
Kallonta fa'iza tayi tare da fadin menene?
Ma'u na wage2 take fadin akwai abinda dada tamin kwanaki dan haka wlh yau saina tsoratata"
Tsaki fa'iza taja sannan taja hannun ma'u suka nufi gidan"
*****
*Abuja*
Momy zaune ita da deeni jefi2 suna hira"
Zuwa can deeni ya kalli momy yace momy yau ke kadaice agidan naji shiru ne?
Murmushi tayi sanna tace wlh dagani sai jamal Nafisa sun fita ita da usman, Asma'u kuma tana Kano"
Kano? Kano kuma? Meyasa zata tafi gano bayan mijinta bashi da lafiya"
Cikin takaici Momy tace, to ai ita ba jinyarshi zata iya ba, itama yanzun tana neman me kula da itane tunda karamin jiki gareta"
Cikin sauri ya runtse ido tare da fadin.......
Ciki? Ciki kuma? Haba wannan ma ai ba mgnr dazata sabo bane"
Kallonshi momy tayi da sauri, tare da fadin meka ce?
Mikewa yayi tare da fadin babu komai' ina zuwa"
Wucewa yayi cikin sauri yana shiga dakinsa ya dungule hannun ya Saki wani kara, jikin bango ya manne sannan ya zame kasa tare da fashewa da kuka, kuka yake kaman karamin yaro, hawaye ne shame2 a idonshi, yanzun asma'un shi tabari Jamal kusanceta anya kuwa zai iya rayuwa, fashewa yasa keyi da kura tare da gwara kansa da bango, wani irin tsananin kishine ya taso masa wadda yakeji bashi iya sarrafa kansa wani irin hawaye ne masu danko suke zubo masa, tare dajin kirjin shi kamar ana sukamai kibiya.......
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
Dedicated
*Meelat Musa*
9⃣9⃣to 1⃣0⃣0⃣
Kwanciya yayi akasa banda numfarfashi babu abin da yake"
Haka ya kwana cikin tsananin damuwa da bacin rai, wadda tunda yazo duniya be taba jin irinsa ba"
Kwace kawai yake hawaye na malalowa ta gefen idon shi"
Babu wadda yasan halin da yake ciki, acikin zuciyar shi yake addu'an Allah ya dauki ranshi, domin yana bakin cikin yaga ma'u da cikin wani bashi ba"
****
Itako ma'u azauren gidan dada ta tsaida anty fa'iza daker ta yadda ta tsaya, cikin gidan ta leka ta hango dada na wanke kayan miya"
Kara lekawa tayi sannan ta gyara murya tare da magewa tace......
Wai ana sallama da Dada"
Batare da dada ta waigo ba tace....
Kaji wata fitina da yamman nan, koma wanene ce mishi ya shigo"
Murmushi ma'u tayi sannan ta kara make murya tace......
Tsohuwa shamsun duna ne fah, kuma tare yake da gayyan kar......
Ai dada bata bari taji karshen zancen ba ta tuntsurar da kayan miyar, ya watse akasa sannan tabi takai a guje"
Dakinta ta shige ta maida sakata"
Fitowa ma'u tayi tana tuntsira dariya, fa'izama dariyar take, tare da nuna ma'u da yatsa tana fadin ke ko?
Abakin kofar suka tsaya fa'iza ce taita kwalawa dada kira tare da fadin kibude dada nice Fa'iza"
Ta fadi haka,yakai so uku dada bata amsa ba"
Zuwacan fa'iza ta sake cewa dada?
Na'am ta fada ahankali"
Nace ki bude"
Ahankali tace bakiga wani dan daba anan gidan ba?
Babu kowa dada Asma'u ce fah take tsorata ki"
Ahankali ta sake cewa ina asma'un take?
Gatanan muna tare"
Bude kofar dada tayi ahankali ta leko da idonta guda daya, ganin su tsaye yasa ta karasa bude kofar tare da fadin......
Kinci jakar ubanki, kinga min fitsararriyar yarinya, shikenan kuma na zama matoni"
Wuceta ma'u tayi ta shige dakin ta haye gadon dada me runfa ta kwanta"
Suma shigowa sukayi dada nacigaba da fada"
Baza ma'u tayi da ita hartayi ta gama sannan ta leko da kanta ta kalli dada tace.......
Ai ni munsa kafar wando daya dake dada tunda kikace wai idan kikazo gurina zamu hada baki dame kare mu kashe ki"
Murmushi dada tayi kadan, sannan ta nemi guri ta zauna tare da fadin"
Aini zolayarki nake takwara mutuwa ai ita muke jira, ina me gidan naki tare kuke?
Me kare?, ma'u ta tambaya idonta kan dada"
Kai, kai, asma'u
wai meyasa kike fadar min da gaba ne?,
Sanin kankine bana sonjin sunan wannan ibilishin yaron, wlh kika sake zan kira ubanki nagaya mai"
Daga ma'u har fa'iza dariya suka Saka, ganin inda idon dada yayi wuki2
Tare da fa'iza suka karasa aikin gidan yayin da ma'u ke kwance tana kwasan bacci"
Sai kusan sallar mangariba ta tashi lokaci sungama hada abincin dare"
Tuwon shin kafa ne miyar ganye, kallon miyar kawai ma'u tayi ta fara sheka amai"
Bayan ya lafa mata Anty fa'iza ta dawo da ita dakin dada, ma'u rike hancinta tayi da hannunta guda 2
kukarin kuka ta fara tare da fadin anty ni kizo muje gida wlh gidan wani iri wari yake yi mara dadi"
Wani irin kallo dada tawa ma'u sannan ta kalli fa'iza tace......
Wannan yariyar ko ita kadai ce?
Cikin sauri asma'u ta mike ta figi gyalenta tayi waje"
Dadama tashi tayi tana fadin ke takwara dawo kici tuwo"
Ina lokacin ma'u harta bar kofar gidan"
Gidan abbanta ta nufa tana tafe tana hada hanya"
Afalo ta samu daddy sunacin abinci shida mama"
Zama tayi fuskarta dauke da fara'a, nan ta shiga gaida abba"
Wani irin fara'a tagani kwace afuskan abba rabon da taga irinsa afuskar abba ta dade"
Amsawa yayi sannan ya tambayeta jikinta tare da jikin yaya jamal"
Cikin jin kunya ta amsa sannan yashiga samata albarka"
Dadi taji sosai ganin abba yabar fushi da ita"
Zuwa can taji yace matso muci abinci"
Karasawa tayi ta dauki cukali ta faraci, badan ranta nasoba saidan tayin da abba ya mata"
Sosai taci abincin jifi jefi abba najanta da hira, zuwa can taji amai na taso mata daurewa taso yi saidai hakan ya gagara, ji tayi zai kwace mata dan haka ta tashi aguje ta nufi toilet"
Kallonta abba yayi itama mama cikin sauri ta aje cukalin dake hannunta tare dabin bayan ma'u"
Sousai ma'u tabawa mama tausayi, wani irin wunkuri take kamar hanjinta zai fita"
Daker aman ya tsaya sannan mama ta wanke mata jiki ta fito da ita"
Daki taso wucewa da ita amman abba yace abarta afalo tasha iska"
Wani irin kunya ma'u takeji, takasa hada ido da abba, sun sunne kai take taki yadda su hada ido da abba"
Tana cikin wannan halin taji muryan abba yana cewa.....
Mamana me kike son ci?
Bakomai abba banjin yinwa"
Mikewa Abba yayi tare da fadin a'a mamana kiyi tunani bazaki rasa abinda kike so ba"
Shiru tayi tana dad'a boye fuska"
Ganin haka Abba yayi murmushi ya juya ya fita"
Bayan fitan abba ma'u ta mike ta shige daki ta kwanta, ba dadewa bacci ya dauketa"
Cikin baccinta taji wani irin kamshi na addabarta, jitayi koma menene tana sonci, dan haka ta tashi da sauri tana baza hanci taji ta ina kamshin ke tasowa"
Daga can gefe ta hango wasu manyan ledoji sunkai 4, saukowa tayi ta fara budewa"
Kayan kwalama ne cike adayan ledan, dayan ko kajine manya manya guda 2, nan ma'u ta shaida sune suke wannan kamshin, bata tsaya duba sauran ba tahau ci"
Ci tayi tai kat, nan bacci ya sureta"
Misalin 11:00pm mama tashigo, bakaramin dadi tajiba dataga ma'u taci naman sosai"
Kwashe sauran kayan tayi ko wanne ta ajeshi a inda ya dace sannan ta tashi asma'u tace tashi Ki koma gado"
*****
Jamal ne kwance agado sai juyi yake ma'u yake son agani, raboshi da ita tun shekaran jiya da suka fita tare da momy"
Yana cikin wannan tunani usman ya shigo, cikin fara ya zauna akusa da Jamal tare da fadin.....
Yazun muka rabo da bello, yashigo gari jiya da daddare"
Tsaki Jamal yaja, sannan yace, wai yaushe zaka wuce ne?, nifa ka takuramin wlh"
Wata yar karamar dariya usman yayi tare da daukan wayarsa yana dannawa"
Tsaki Jamal ya sake ja sannan yace.....
Haka kurum mutum da matar sa ahanashi ganinta"
Eh kuma dole mutum ya hakura ko yaki ko yaso nima matata nabaro da tsohon ciki"
Gyara kwanciya Jamal yayi sannan yace.....
Nina kiraka?, kaikaga zaka iya, ni da karfina babu abin da bazan iyaba wlh, dan Allah ka tafi wajen matar ka, banason jiyar na warke"
Wani irin kallo usman yayiwa Jamal sannan yace waikai wani irin mutum ne?, nifa sirikin ka ne amman kake gayamin irin wannan mgnr"
Jan jiki Jamal yayi ya zauna sannan ya kalli usman yace......
.
Nufin ka naji kunyan ka?, aini bansan kai sirikina bane, da kanayin sirikuta dani da bakazo jinyata ba, har yanzun kai abokina ne"
Mikewa usman yayi tare da fadin shikenan zantafi, tunda kace na takura maka"
Kauda kai yayi usman na daf da fita jamal yace.....
Ka rokar min momy dan Allah ta turomin Husna mugaisa amman dan Allah karka ce injini, cewa zaka yi ya kamata ne"
Waigowa usman yayi yamai wani irin kallo sannan yace......
Wacce Husnar?
Guda nawa ka sani?
Murmushi usman yayi sannan yace ai tunjiya tana Kano"
Azabure yace kano?, mgnr momy ne ya fadomai, jawo kafafuwan shi yayi ya ajiye akasa sannan yace......
Taya momy zatamin haka sabo da Allah?, harta tura Husna Kano batare da amincewata ba"
Jim usman yayi zuwa can yace, to ai laifin ka ne Jamal"
Tayaya ya zama laifina usman? Me nayi? Da sanda naki auren surutu akaita min, yanzun kuma dayin ba'a kyaleni ba, sai surutu akemin salon kananan yara su raina mutum"
Yazun da aka turata kano, can ma yayatani za'yi kenan"
Kalaman jamal basuwa usman dadi ba, cikin bacin rai yace......
Wai meyasa idan ranka ya baci baka tauna lafazin bakin kane?, waye kake cewa wai ana yayata ka, kadai san bani bace na turata ko?
Jamal kasa mgn yayi bayan wasu mintina ya sake cewa......
Toh naji, yanzun abin da za'ayi kaje ka samu momy kawai atura drive ya dawo da ita"
Usman be juyo ba, yace ai kana da kafa kuma kana da baki, ko ba yanzun ka gama cewa babu abin da baza ka iya ba?
Eh amman kasa mgnr da nauyi, bazan iya taren idon momy na fada mata haka ba"
Mikewa usman yayi ya fice abinshi yayin da Jamal yaita sauke ajiyan zuciyan bacin rai"
****
Sai dare momy ta fito falo, zaune tayi tana jiran shigowan Usman tare da deeni, tun safe yau bataji motsin su ba, garama usman dasafe kan ya fita ya shigo har daki sun gaisa"
Amman deeni rabon da ta ganshi tun taren da ta dawo raka ma'u kano"
Shirun taji yayi yawa dan haka ta mike ta nufi dakin Jamal"
Yana zaune ya hada kai da guiwa"
Kai Jamal yau Usman lfy kuwa har yanzun be dawo ba?
Dago jajayen idon sa yayi ya sauke akan momy, tare da fadin nima shinake jira kuma nakira no dinshi kusan so 10 amman be daga ba"
Atsorace momy tafara dannan wayarta tare da fadin to lfy kuwa?
Bata rufe baki ba taji andauki wayar dan haka ta fara fadin usman ina ka shige gashi har dare yayi?
Momy wlh tafiya ce ta taso min dan haka na wuce, yanzun haka ina kano, gobe zamu wuce Sokwato"
Cikin baccin rai momy tace wanni irin tafiya ne zai taso dahar zaka kasa mana sallama haba usman gaskiya baka kyauta ba"
Hakuri yaitaba momy sannan ta mikawa jamal tana fadin ga Jamal"
Saidai usman najin Muryan Jamal ya kashe wayyar"
Juyawa momy tayi hankalinta atashe tana fadin saura deeni barinje na duba ko shima garin ya bari beyi sallama ba"
Wani Irin abu Jamal yaji yana mai yawo akai, wani mummunan tunan tunanni ya ziyarci zuciyar shi, Husna na kano, Deeni ma yabi bayanta......
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
Dedicated
*Rukayya Hassan Osman*😘
1⃣0⃣1⃣
💝💝💝 Cikin tsananin fargaba momy ta tura dakin deeni"
Abude yake saidai babu kowa afalon, cikin dakin ta nufa tana Raba ido"
Akasa ta hango deeni yana numfashi daker, da gudunta ta karasa tace shamsundeeni meya sameka?, baka da lfy ne"
Be iya amsawa ba, kokarin dagashi ta fara amman ta kasa juyawa tayi waje tana kururuwa"
Daddy ne ya fara fitowa sannan nafisa, ganin inda momy tabi yasa sukabi bayanta"
Shima daddy ganin jikin deeni hankalin daddy ya tashi sosai, me gadi yahau kira, juyawa yayi yakalli nafisa da tunda taga deeni ta fara kuka yace"
Kiramin me gadi"
Nafisa ta juya zata fita sukaci karo da Jamal yana dingisa kafa"
Kaikuma meka fito yi ? Ina zaka?
Kallon deeni yayi tare da fadin bakomai"
Toh maza ka koma daki"
Daidai lokacin me gadin ya shigo, acikin kankanin lokaci suka isa asibiti"
Kan gado suka daura deeni sannan suka fara duba shi"
Daga momy har daddy hankalin su atashe yake"
Ba'a dauki lokaci ba likitan ya fito ya nufi office dinshi"
Daddy ne yabi bayan shi
Cikin natsuwa likitan ya gayawa daddy deeni yana dauke da mummunan ciyon zuciya, wadda yayi karfi ajikin shi sosai"
Sannan ya shiga bashi shawaran cewa adaina bata masa rai, ayi kokarin duk abinda ya nuna yana so anemar mai"
Sannan ya kara da cewa zaman shi cikin damuwa na sati biyu zuciyar shi na iya bugawa"
Bayan daddy ya fito ya samu Momy da nafisa tsaye akan deeni, nafisa kuka kawai take"
Cikin tausayawa daddy ya kalli deeni bacci yake daman likitan yace sai safe zai tashi"
Washegari daddy yayiwa alhaji bashir waya ya sanar mai suna asibiti deeni babu lfy"
Cikin kankanin lokaci alhaji bashir ya iso tare da ummi"
Sosai hankalin ummi ya tashi domin ita tasan ciwon deeni be rasa nasaba da asma'u"
Har yanzun bacci yake be tashi ba, dan haka daddy ya kalli alhaji bashir yace.....
Muje gida akwai mgnr da zamuyi"
Nafisa kawai akabari agurin deeni"
****
Bayan sun isa gida afalon daddy suka zauna yayin da Jamal yake daya daga cikin dakunan dan haka duk abin da suke cewa yana jin su"
Daddy ne ya shiga gaya musu abun da likitan yace, sannan ya kara da cewa ya zamar mana dole mu nema mai lfy be kamata mubarshi ya kare rayuwa awahala ba, ina tsananin tausayawa rayuwar Shamsudeen inason ya zama mutum managarci banaso rayuwar shi ta kare ahaka, kuma insha Allahu zanyi korin nema masa abin da ransa ke so"
Cikin kuka ummi tace ninasan abinda yake damun auta, ya dauki son duniya ya daura akan wata yariya, nayi nayi yai hakuri yabar musu Amman yakiji, ubata yai mata aure tuntuni yakuma ce tirrr yaba shi aureta'
Bantaba ganin auta yaso wani Abu aduniya ba kamar yadda yaso asma'u"
Bacin raine kwance akan fuskan alhaji bashir daddy da momy ko hankalin su tashi yayi domin Susan cewa asma'un deeni itace matar jamal
Mikewa alhaji bashir yayi tare da fadin waye uban yariyar"
Shima daddy mikewa yayi tare da goya hannun shi abaya yace zancen waye mahaifin yariyar ai be taso ba, dafa alhaji bashir daddy yayi sannan yaci gaba da cewa....
Bashir kabarmin komai ahannuna nima ai shamsudeen d'ana ne dashi da Jamal duk daya ne, insha Allahu zan nemo mafita"
Duk waddan magan ganun Jamal naji Dan haka hankalin shi ya tashi, kasa zama yayi ya mike tsaye zufa yaji yana karyo mai, tunanin shi yaya zaiyi yaga Husna kusa dashi beso Husna tayi nisa dashi"
Yana cikin wannan tunanin yaji alhaji nashir na fadi"
Inda ace akwai yadda za'ayi musame ita yariyar asma'u ta zauna kusa dashi kona sati 1 ne wata kila ya dawo cikin haiyacin shi"
Cikin sauri momy ta mike tsaye fuskokin su ta kallah sannan ta fita afalon"
Shiko Jamal jiyayi kirjin shi ya buga daramm afili yace matar tawa?
Bazan yadda da wannan shawarar ba, bazata taba yuwuba"
Daha suka tashi kowa zuciyar shi da abinda yake sakawa"
Daddy da alhaji bashir ne suka koma asibiti amman tare da ummi, momy ko cewa tayi anjima zata zo"
Daker momy ta iyayin abinci akakai asibitin, Sanan ta zauna ta rafka tagumi"
Jamal ko ya kasa zaune ya kasa tsaye kano yake son zuwa amman yadda yakejin jikin shi bazai iya fitaba ji yake kamar yana tsami domin rabon shi da wanka tun ana gobe usman zai tafi"
Mikewa yayi ya nufi toilet cikin dibara yayi wankan ya fito"
Gyara jikin shi yaye tare da fesa turare sannan ya dauko manyan kaya ya saka tare da daura hula"
Tafe yake yana dingishi har ya isa dakin momy, ahankali ya tura kofar tare da sallama"
Cire tagumin momy tayi, sannan ta dago ta kalli Jamal"
Kyau taga yayi sosai, mikewa tayi tare da fadi Jamal wanka kayi ne?, meyasa bakajin mgn?
Momy jinayi ina tsami, dama usman ne kemin tun tafiyan shi kwana 2 kenan banyi wanka ba"
Ai da ka kirani namaka, Jamal ka daina wasa da lfyr ka, yanzun kuma da ka kaso kafa ka taho ina zaka"
Kai ya sosa sannan yace, fita zanyi momy, akwai wani aiki ne zan duba ko yana tafiya daidai, yau zan dawo insha Allahu"
Hmmm Jamal wanne aikine? Inace manyan ku sunsan halin da kake ciki?
Eh sun sani momy, wannan aikin idan ban duba ba za'a iya samun matsala ne"
Shiru momy tayi kamar baxatayi mgn ba zuwa can tace.......
Toh shi kenan Allah ya tsare ya dawo dakai lfy"
Ameen yace sannan ya mike ya fara tafiya, harya kai tsakiyan falon Momy tace......
Jamal wanne garine zaka?
Jam yayi kamar bazai yi mgn ba zuwa can yace Kano"
Kano momy ta tambaya sannan tace zonan Jamal"
Cikin sanyin jiki ya dawo ya zauna tare da sauke kansa kasa"
Saida momy ta gama kare mai kallo sannan tace.....
Jamal kace min kawai zaka wajen matar ka, ai bawai rabaku nayi ba, amman tunda hakane ka koma daki zansa dawo da ita"
Jikin shi sanyi yayi bazai iya musawa momy ba, amman hankalin shi nagun husna"
Har daki momy ta raka shi sannan tamai gargadi karya ya sake fitowa"
Momy bata koma asibitiba har dare, tunanin mgnr bashir take, tayaya matar da tai aure za'ace ta zauna gurin balagaggen namiji, hakika tana taya Jamal kishin matar Sa, kuma tana tausawa deeni"
Daddre ma kasa bacci tayi damuwa yayi mata yawa"
10:30pm daddy ya shigo har cikin dakin Momy, nafisa na biye dashi"
Guri ya samu ya zauna nafisa ko gaida Momy tayi sannan ta wuce dakin ta, tare da fadin bari naje nayi wanka"
Amsa mata momy tayi sannan ta maida hankalinta kan daddy"
Hularshi yacire ya aje agefe, sannan ya kalli Momy"
Kauda idonta tayi tare da fadin ya me jikin?
Yaji sauki, ya farka tunda rana, sai dai har yanzun kuka yake yi, kuma ya fada ma abinda ke damun sa yaki fada"
Shiru daddy yayi momy ma mikewa tayi tafara hada kayanta"
Muryan daddy taji yace......
Zauna mana akwai mgnr da zamuyi"
Cikin sauri momy ta aje kayan ta koma ta zauna"
Gyaran murya daddy yayi sannan yace......
Inason ki saurareni da kyau kuma ki fahimceni"
Wani irin kallo momy tamai sannan tace inajin ka"
Akan mgnr shamsudeen ne, nasani kin san cewa asma'u itace yariyar da shamsudeeni ke matukar so"
Cikin ido momy takalli daddy tace....
Ina jinka"
Cigaba daddy yayi da fadin dan haka nake ganin mezai hana shi Jamal ya hakura ya saketa.......
Mikewa momy tayi da sauri tare da fadin Alhaji kasan abin da kake fada kuwa, Asma'u fah matar Jamal ce, kuma ciki gareta, tayaya za'ace ya saketa shamsu ya aura, antaba haka"
Dakewa daddy yayi tare da fadin idan ma ba'ataba za'a fara akan su, dan hakan ne kadai mafita idan ba hakaba za'a iya rasa shamsundeen"
Alhaji wannan mgnr bazai yiwuba sam, dan Jamal nason matar shi, tunda nake da Jamal banta tunanin zaiso wani abuba kamar yadda yake son matar shi"
Gutun murmushi yayi sannan yace nidai abinda nake so dake kiyi addu'a Allah yasa hakan shine mafi alheri"
Nifah alhaji sam ban amince ba, kama aje wanan zancen wlh bazai taba yiyuwa ba"
Daure fuska daddy yayi sannan yace....
Karki nemi yin jayayya dani, daga ke har Jamal akarkashina kuke, babu wadda ya isa nace ga abinda zaiyi yacemin ba haka ba, Jamal dana ne be isa yayi jayayya dani ba"
Mikewa momy tayi tare da ficewa tana fadin wannan ai zalinci ne"
Girgiza kai daddy yayi sannan ya mike ya nufi dakin Jamal"
Gaisar dashi Jamal yayi sannan ya tambaye shi jikin shi"
Shiru dakin yayi zuwa can daddy yace......
Jamal nazo ne muyi wata mgn, kasan cewa dan uwanka yana asibiti ko?
Eh Jamal ya fada ahankali"
Toh abinda nake so dakai, akoda yaushe mutum ya zama me karban kaddara yadda tazo mai, wani alfarma nakeson kamin"
Tashi jamal yayi ya zauna tare da jingina bayanshi da bango"
Daddy yaciga da cewa nasan kana son dan uwanka, dan haka inason ka tausaya masa ka duba halin da yake ciki, ka sakar masa asma'u bayan ta haihu shi ya aureta"
Wani irin firgita Jamal yayi tare da sauke ida nuwan shi akan daddy hannu Yasa ya mustsuke ido sannan yace daddy kaine ko mafarki nake"?
Ba mafarki bane Jamal zahiri ne, inason shamsu yaji daddi rayuwa bana so rayuwar shi ta kare ahaka, rayuwar shi abaibai take"
Jim, Jamal yayi sannan yace daddy ai wannan ba kaddarata bace tashi ce, shiya kamata ya karbeta bani ba"
Cikin ido daddy ya kalli Jamal sannan yace nasan haka Jamal amman ai lalurace ta kawo haka"
Shiru dakin yayi Jamal ji yake kaman anamai daka akirji, daddy ne yagaji da shirun yace.....
Jamal inasauraron ka"
Murya kasa kasa yace banzan iyaba daddy, dan Allah kayi hakuri"
Cikin fusata daddy yace nina rokeka alfarma kace min bazaka iyaba, to bari kaji wannan karon umarni zan baka, kafin nan da wayewar gari ka rubuta ma Asma'u sake"
Afusace ya Mike ya fita, wani irin zugi zuciyar jamal kemai tare da tukukin baccin rai wacce irin rayuwa ce wannan yaushe daddy ya sauya hali da zai zabi deeni akaina"
Inason asma'u banga dalilin dazan saketaba, zanyi koma menene dan nakare martaban aurena, shi wanene dabazaiyi hakuri da kandara ba
Irin tunanin da Jamal ya kwana yi kenan washegari dasafe daddy ya sake duruwa dakin"
Jamal naganin shi gabashi ya fadi, hannu ya mika mishi tare da fadin bani"
Sunkuyar dakai yayi batare dayace komai ba"
Cikin fada daddy yace karka maidani dan iska kanaji ko?
Wani irin mummunan tashin hankali Jamal yaji, tunda yake betaba jayayya da iyayenshi ba, kuma baya so ya fara, aman bazai iya aiwatar da abin da daddy yake soba"
Ahankali Jamal yace daddy dan Allah kayi hakuri wlh baxan iyaba, ba nason jayayya dakai, dan gaskiya inason asma'u bazan iya rabuwa da itaba......
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
1⃣0⃣2⃣
Jamal bana wasa dakai, karkace zakayi jayaya dani, kuma wannan mgnr bana son wani yajita tsakanina ne ni dakai"
Daddy dan Allah ka jayen wannan mgnr, wlh daddy bazan iyaba, bazan iya rabuwa da Husna ba, daddy idan nabarta zan shiga wani hali"
Jamal koma waning hali zaka shiga baxai kai wadda shamsu yake ciki ayanzun ba, bana son nakarajin komai daga gare ka, takarda na nema kuma ita nake son kabani"
Kara dukar dakai Jamal yayi, sun dauki lokaci ahaka sannan daddy yace......
Jamal wlh zan bata maka ranka"
Cikin zuciyar shi yace.....
Raina ya dade da bacci daddy"
Cigaba daddy yayi da cewa, zakai abin da nagaya maka ko kuwa?
Murya kasa kasa yace daddy kayi hakuri🙏🏻
Wlh Jamal zan iya tsine maka"
Kallon daddy yayi da sauri sannan ya maida kanshi kasa yace......
A'a daddy kar kamin haka, dole ce tasa na maka musu daddy ba'a son raina bane, daddy idan na saketa rayuwata zata zama cikin hadari, dan gaskiya inasonta sosai babu rabuwa atsari na, kuma itama tana sona"
Cikin daure fuska daddy yace bantabaye ka wannan ba, kaida shamsu nasan kuna da babbanci kai mutum ne me tawakali da kaddara mekyau ko mara kyau, shamsu bayi dashi, ba'a daura shi akan wannan tarbiyan ba, banaso ya mutu, inaso yayi rayuwa kamar kowa"
Kunya ce ta fita a idon Jamal kwata kwata, tsintan kanshi yayi yana fadin daddy wannan ba kaddarata bace, bazan iya kashe kaina na raya wani ba, Allah ne ya bani Husna, batare da naje neman aurenta ba, duk da cewa na dade ina sonta bantaba nunawa kowaba har usman, kuma ni na sani deeni bawani sonta yake ba, wlh nafishi sonta, yana ikirarin yana sonta ne saboda besan menene so ba"
Itama kanta taso deeni ne cikin yarinta alokacin da batasan me take ba, na tabbata ayanzun Husna bazata so deeni ba"
Daddy idan kace lallai saina saketa bakamin adalci ba, Allah ne ya bani ita batare da yayi shawara da kowa ba, haka kuma Allah ne ya kaddara asma'u ba matar sa bace, dame bazai yi hakuri da hukuncin Allah ba, lallai ne abin da yake so saiya samu?, daddy karku shiga hurumin daba nakuba, deeni ba mutuwa zaiyi ba, darasi ne Allah yake nuna mishi, daddy idan ma muwa zaiyi sakin husnan dakace nayi zai kara mai kwanaki ne? Dan Allah daddy munar Allah yayi hukuncin shi, munemin zabin alheri agurin shi kawai"
Jikin daddy sanyi yayi sosai, shiru yayi na dan wani lokaci zuwa can ya sake cewa.....
Jamal nasani duk abin da ka fada haka ne, shiyasa ako ina nake alfahari dakai, amman kayi yadda nace d'in"
Wani irin yar fa hannun Jamal yayi, sannan ya rungumi hannuwan shi akirji"
Ganin haka daddy yace nakara ma lokaci nanda zuwa gobe ka yanke shawaran, zakamin biyayya ko kuma bijirewa umarni na"
Juyawa daddy yayi da sauri yabar dakin"
Yana fita momy ta fito daga dakin ta bayan daddy tabi da harara sannan taja tsaki ta nufi dakin Jamal"
Tana tura kofar ta hango fuskan Jamal hawaye shabe shabe"
Yana ganinta ya fara sharewa tare da boye idon shi"
Kusa dashi ta zauna sannan ta dago kanshi tace......
Jamal karka tada hankalin ka, bare har ka biyewa zancen mahaifin ka, idan har ka saketa bazan taba yafe maka ba, karka manta, nima ina da hakki akan ka"
Cikin rawar murya yace toh momy ni yanzun yaya zanyi?
Ka dage mishi akan kana son matar ka, ni bantajin inda akayi haka ba, alhaji yana da wani irin son 'yan uwan shi, wadda ya wuce misali"
Jamal be sake cewa komai ba, idonshi ya dauke daga gurin momy ya juyar dashi can gefe, cikin tsananin damuwa"
Momy kokarin kwantar mai da hankali take, amman ta kula hankalinta baya gurin ta, yayi nisa cikin tunani"
Mikewa tayi tai waje tare da fadin Allah ya kyauta"
Jamal naganin fitan ta ya kira wayar ma'u, yauma kashe take kamar kullum, tsaki yaja gashi bashi da no mama"
Wata zuciyar ce tace, ka kira usman, wannan tunani yasashi ya kira layin usman
Zuwa can aka daga usman ne yace gauro ya gari?
Cikin rashin kwarin jiki Jamal yace babban yaya ka huce kenan?
Dariya usman yayi tare da fadin aini daman ba zafi nayi ba"
Kayi fushi mana tinda ka tafi babu sallama, ya gida ya iyali?
Lfy lau suke, karkace min asma'u bata gaya maka fa'iza ta haihu ba"
Yake Jamal yayi kamar yana gaban usman yace da gaske?, me muka samu?
Nana Firdausi, usman ya fada cike da murna"
Allah ubangiji ya albarkanceta acikin addinin musulinci, kace inanan nasake baki nayi 'ya ban sani ba"
Dariya usman yayi tare da fadin wlh jiya da dare ta sauka, na dauka Asma'u zata gayama ne"
Karka karamin haka, ko Husna zata fadamin yana da kyau kaima naji daga gareka, amman bakomai tunda Husna taganta kamar nine"
Hmmm wlh Jamal kana min rashin kunya fah, ya jikinka najika wani iri ne"
Eh wlh bana jin dadi ne, dan hadani da husna mana"
Tsaki usman yaja sannan yace batanan gidan kuma basu dade da tafiya ba ita da mama"
Shiru Jamal yayi zuwacan yace toh sai an jima"
Kashe wayar yayi tare da binta da kallo, lallai yanason suyi waya da husna ayau, dan haka ya yanke shawaran kiran daddy"
Bayan sun gaisa da abba yamai barka samun karuwar da akayi"
Dariya abba yayi tare da fadin toh ai Jamal ku za'aiwa barka, kunji kunya tika tika daku sai yanxun kuka aje daya, daker"
Guntuwar dariya Jamal yayi tare da shafu keyarshi kamar yana gaban abba, acikin zuciyar shi fadi yake abba me kakeci nabaka na zuba"
Jim, sukayi zuwa can Jamal yace.........
Amm abba nakira wayan ta ne akashe, ban saniba ko wayar ta samu matsala ne"
Wai asma'u ?
Eh Jamal ya fada ahankali"
Toh, toh, ina zuwa"
Kashe wayar yaji anyi zuwa can yaji wayar na kara"
No Abba yagani, jikin shi har rawa yakeyi wajen daukan wayan"
Muryan ma'u yaji cikin murna da dauki tana rangada sallama"
Tsintan kanshi yayi da lumshe ido sannan ya amsa mata tare da fadin Husna shine kika yadda kika tafi ko sallama babu ko?
Toh ai momy ce tace haka"
Hmmm Husna toh ya kwana 2?
Lfy lau, ya jiki?
Yayi sauki Husna, yasu mama?
Suna lfy"
Yayi kyau"
Cikin siririyar murya asma'u tace....
Yaya Jamal albishirin ka"
Goro ya fada cike da zumudi dan tunda yake da ma'u bata taba sakar mai jiki kamar yauba"
Yar dariya tayi sannan tace.....
Fari ko jah?
Dariricewa yayi domin bazai ce ga takameme abin da ake cewa ba, tsintan kanshi yayi yana cewa jah"
Kukan shagwaba tasa kamar tana gaban shi, tare da fadin fari fa zakace"
OK toh ya isa kisan ban iya irin wad'an nan abubuwan ba, inajiki toh nace fari"
Cikin murna tace....
Na samu d'iya anty fa'iza ta haihu jiya da dare"
Yi yayi kamar be sani ba, ya lankwasa murya yace......
Dan Allah?
Wlh, yaya bakaga yariyar ba, kamarmu daya"
Har cikin jinin jikin shi yake jin muryanta dan haka ya kara kashe murya yace....
Da gaske?
Hmmm kai dai sai ganta da idon ka, wlh har giran mu iri daya ne"
Zanso inganta kuwa, kishafa min kanta, kice wani babanta na mata barka da zuwa"
Shiru sukayi nadan wani lokaci, zuwa can Jamal yace.....
Husna kina inane yanzun ?
Ina dakina"
Ke dawa?
Ni daya"
OK akwai mgnr da zan gaya miki, akwai wata babban matsala da ta tunkaro mu, daddy ya gindaya min umarni, wadda bazan iya biba, kinsan menene?
Girgiza kai tayi tare da fadin a'a
Ahankali ya fara warware mata abin da ke faruwa"
Kafin ya gama hawaye ya gama wanke mata fuska, cikin kukan tace........
Yaya Jamal nagaji fah, wlh nagaji tunanina bazai iya dauka ba, waini sai yaushe zanji dad'i inama na mutu tun ina kar.......
Wani tsawa Jamal ya buga mata wadda yasata yin shiru batare da ta shirya ba"
Kina hauka ne? Karna sakejin kin fadin irin wannan mgnr, duk inda kika samu kanki ki godewa Allah
Kuka take ahankali"
Shima hawaye ya share tare da ajiyan zuciya yace.....
Husna dan Allah karki yadda arabamu, deeni ba sonki yake ba, sha'awarki kawai yake yi, natabajin shi yana miki karyan banza da wofi, har yana kiran Ki da Furan sa, idan natuna inajin takaici, agidan ubanwa kika zama furan sa? Darajan Ki ta wuce ta fura, babu abinda da za'a kwatantaki dashi, yaudaran ki yaki yake, kuma ni tundaga ranan natsani fura
ko ganinta bana so yi"
Kosawa tayi yabar mgnr, dan tasan yana iya birkice mata, yanzu nan, dan haka tace....
Yaya Jamal kabar wannan mgnr"
Dif, yayi xuwa can yace.....
Husna daddy ya bani daganan zuwa gobe, nakawo mishi sakin ki, dan haka adaren nan zabar garin bazan dawoba sai daddy ya janye kudurin shi akaina, zabar wayata agida dan kada anemeni ke kuma Ki ringa barin wayarki akunne dan zan nemeki, idan na isa inda zan tsaya, sannan aurena nakan ki karki yadda da sako arubuce, ban rubutaba, kuma bazan rubuta ba"
Ban aiko kowa ba, kuma bazan aiko ba, karki yadda da kowa, idan bani kika gani idona da nakiba"
Kuka ta fasa, cikin kukan tace......
Yaya Jamal karka tafi ka barni dan Allah"
Husna nima ba'a son raina zantafi ba"
Cikin matsanan cin kuka tace toh ka tafi dani wlh zan bika.....
Heart beat
*Mmn Yazeed*
h💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
*Masoya BUGUN ZUCIYA kuyi hakuri pls🙏🏻🙈 abubuwa ne sukamin yawa, naso yau nabaku mamaki amman nakasa, gobe insha Allahu page 2 ko 3 zan turo, nagama typing editing ne ya rage, wadan da sukamin mgn ban amsa ba kuyi hakuri pls🙏🏻 sakon ne yamin yawa*
1⃣0⃣3⃣
Indan katafi ka barni zan shiga wani hali bansan inda Zanyi ba"
Husna kiyi hakuri, nima bansan inda zani ba, kinga bekamata na dauki da karamin ciki inkaiki inda xaki wahala ba"
Cikin kuka tace nidai wlh xan bika, duk Inda ka zauna nima zan iya zama, wlh yaya karka tafi ka barni"
OK toh shikenan daina kuka, maza Ki share hawayen ki kuma ki saki ranki"
Make kafada tayi kamar tana gaban Sa, sannan tace a'a saika min alkawarin bazaka gudu ka barni ba"
Namiki husna, ki shirya yau dinnan inanan tafe, amman karki gayawa kowa"
Dahaka sukayi sallama, jikin ma'u sanyi ya kara haka ta takure guri daya taita kuka"
Jamal ko yana gama waya da ma'u ya tashi ya dingisa, mahimman abubuwan shi ya hada guri daya sannan ya sauya kaya"
Awaya ya kira drive bayan ya shigo yace ya dauki jakar yasa amota gashi nan zuwa"
Drive ya fita babu dadewa Jamal ya fito, babu kowa afalon dan haka har ya fita babu wadda ya ganshi"
Hanya suka dauka acikin su babu me cewa kala, yamma likis suka isa Kano"
Sauka Jamal yayi ya nufi cikin gidan cike da zumudin son ganin ma'u
Salama yayi abakin falon, daga ciki mama ta amsa"
Ma'u tunda taji muryan Jamal ta mike tare da ajiyan zuciya"
Cikin ladabi ya shiga falon yana dingisawa tare da sunkuyar da kanahi kasa"
Mama naganin Jamal tace ah'ah Jamal kai da kanka ka kwaso hanya kana fama da kafar ka"
Shafo keyarsa yayi tare da satan kallon ma'u yana murmushi"
Itako ma'u tsaye tai ta kasa cewa komai, kallon Jamal kawai take tare sonjinta jikin shi"
Bayan sun gaisa mama ta shiga kitchen sannan ta kira ma'u"
Bin bayanta yayi da kallo tare da hadiye miyau"
Zuwa can ta dawo dauke da kayan marmari ta aje gaban shi"
Tana kokarin ajewa ya rike hannunta tare da kokarin dagota"
Kan cinyar shi yaso zaunar da ita ta cije tare da fadin ciyon ka fah?
Gefe ya nuna mata tare da fadin daga nan zaki zauna"
Zama tayi sannan ya hada hancin shi da tana tare da fadin kince zaki bini ko?
Kai kawai ta daga almar eh"
Cikin sauri ya wawuro bakinta, nisa yayi sannan ya fara shafa jikinta"
Ummi ce ta sawo kai bakinta dauke da sallama, cikin sauri ta juya tun batakai ga karasawa ba"
Hakan yayi daidai lokacin da suke kokarin rabuwa da juna"
Ganin mama tajuya ya tabbatar musu ta gansu dan haka takaici yasa ma'u ta fara kuka"
Jamal ma kunya ta kamashi, amman fuskan sa na dauke da murmushi yake kallon ma'u, zuwa can yace......
Ke dai kuka be miki wuya, yanzun dan Allah meye abin kuka?
Cikin kukan tace mama fa ta ganmu"
Toh menene husna?, nifa mijin Ki ne bare kice za'amiki fada, dallah ni tashi ki dauko gyalen ki, sai kice ma mama zaki rakani naganu Firdausi"
Wlh yaya bazan iya ba, ni yanzun kunyan hada ido da mama zanji"
Mikewa jamal yayi tare da fadin toh shike nan, ni bari na wuce, dan bani da lokaci'
Rikeshi tayi da sauri, tare da fadin to yaya ai kai ya kamata ka gaya mata"
Shiru yayi yana kallon ta zuwa can yace....
Ok toh yanzun abin da za'yi, kije ki Debi kayan ki kadan kisa amota"
Yana tsaye harta dawo sannan ya matsa kofar mama yace.....
Mama zantafi"
Fuskarta dauki da fara'a tace yau yau din nan ai na dauka kwana zakayi"
Cikin jin kunya yace a'a yau zantafi nazo ganin Firdausi ne"
Murmushi kawai mama tayi dan haka jamal ya sake cewa......
Zamuje da Husna ne ta raka ne"
Adawo lfy Jamal kaida matar ka"
Dan sosa keya yayi sannan yajuya ya kalli ma'u yace dauko gyale"
Basu wani zauna agidan usman ba suka fito bayan Jamal ya gama tofawa yariyar addu'oi"
Tasha Jamal yasa drive yakai su sannan suka sauka tare da kayan su"
Gargadi yawa drive sosai cewa duk wadda ya taban baye shi yace kano ya kawo shi, daganan karya kara komai"
Saida drive ya wuce sannan suka hau motan sokwato"
Drop suka dauka dan haka karfe 10 da wasu mintoci suka shiga cikin garin sokwato, lokacin har Bacci ya kwashe ma'u tana manne ajikin Jamal"
Har suka isa kofar gidan da Jamal yama drive izinin shiga, ma'u bata tashi ba, kallonta Jamal yayi, bacci take kuma dagani tanajin dadin macci"
Kallonta yake vabu kyaukyautawa muryan drive yaje yace oga nagama sauke kayan"
Azabure jamal ya kalleshi sannan yace......
Toh kashi kuma madam tana bacci ni kuma inada matsalan kafa bazan iya daukanta ba"
Cikin sauri drive yace oga tashinta zakayi ai"
A'a bazan tasheta ba, hukuri zakayi har ta tashi ko wani abu ne saina kara maka, dan babu kyau mutum yana bacci atasheshi"
Shiru drive ban yayi acikin zuciyar yace......
Lallai wannan ba karamin so yakewa matar nan tashe ba, ni ina ruwana indai za'abani kudi, Allah yasa ma karka tashi sai gobe"
Jamal babu abinda yake banda kallon ma'u, tun da yake betaba tsayawa ya kallita hankalin shi kwance kamar yau ba"
Tayaya daddy zaice saina sakeki, bayan na farajin dadin aurena, tayaya hakan zai kasan ce, Addu'a yayi azuciyar shi Allah yasa abba ya fahimci gaskiya"
Ma'u ce ta bude idonta tare da fadin nifa nagaji har yanzun bamu kawo ba"
Munkawo husna cewa nayi bazan tasheki ba sai kin gama baccin"
Wani irin kallo tamai tare da mamakin jamal, kwallah taji ya cika mata ido, Ashe Jamal zaisota haka?, lallai ta yadda kiyayya na komawa soyya"
Waigawa tayi ta kalli gidan tare da zare ido, barikine irin na sojuji, ko ina sojujin ne ke zurga zurga, suna fitowa daga cikin motar wani ya taho ya sarawa Jamal sannan ya mika masa key"
Ma'u na manne jikin shi ya bude kofar suka shiga"
Falo ne madaidaici me dauke da daki daya tak da bayi aciki, daga can gefe kuma akwai madaidaicin kitchen"
Bayan ya zaunar da ma'u yace ina zuwa bari nayi sallah ke kuma kibari ki huta"
Kallon shi kawai tayi yana fitowa toilet din ta shege, dan haka tare suka yi sallah"
Bayan sun idar yace bari naje na samo mana abinci"
Be dadeba ya dawo bayan sunci sunsha, ma'u ta fara hamma "
Kallonta Jamal yayi tare da fadin tashi kije Ki kwanta"
Hawa gadon tayi sannan ta kalli shi yana zaune akasa ya mike kafafuwan shi tace......
Yaya gidan nan fah ya mana kadan, yazun kai a inazaka kwanta?
Ban gane a ina zan kwanta ba?
Jan bargo tayi ta rufe idobta sannan tace naga gado daya ne, kai kuma mace bata hawa gadon ka"
Take sanda ya fada mgr ya dawo mai, dan haka yayi dariya sannan yace.....
Ke bakya mantuwa ne?
Bata sake cewa kalla ba ta rufe idotan tai shiru"
Tanajin shi ya mike ya sauya kaya, sannan yahau gadon tare da yaye bargon ya shiga, zuwa can ya mika hannun sa ya rungumota jikin shi"
*Abuja*
Bayan tafiyan jamal, zuwan momy dakin uku bata ganshi ba, lekawa waje tayi nanna megadin yake shaida mata Jamal ya fita tare da drive"
Momy bata tsorata ba, saida taga drive ya dawo babu Jamal"
Tambayan shi tayi ina jamal, kamar yadda Jamal ya fada mai haka ya fada"
Acikin zuciyarta tace wai meyasa Jamal bejin mgn, wannan kafar tashi so yake ta rube, idan ba hakaba me zai kaishi kano"
Da daddare daddy suka dawo tare da deeni da alhaji bashir harda ummi"
Rike daddy yake da deeni yana mai sannu"
Bayan sun zauna momy ta kawo musu abinci"
Daker deeni yaci kadan kallon shi momy tayi taga ya rame"
Shima daddy kallon Sa yayi sannan ya mike cikin sauri ya nufi dakin da Jamal yake"
Alhaji Momy ta kirashi, sannan tace......
Jamal baya nan"
Bayanan?, ina yaje?
Kwashe yadda sukayi da drive tayi ta gayamai"
Shiru daddy yayi na wani lokaci, sannan yace"
Ni Jamal zai watsawa kasa a ido?, shi kenan nasan abin da yake nufi, wayar sa ya dauka ya kira abba"
Bayan sungaisa yace Jamal yazo"
Daga can Abba yace........
Eh haka na samu lbr ance yazo amman ni bangansa ba"
Asma'u fah ?, tananan agida, koya dauketa ne?
Eh mamanta tace sun fita tare, kasan yaran zamani, ita maman tasu dai yace mata gidan usman zasu"
Wani zancen daddy ya dauko sannan sukayi sallama"
Koda ya kashe Wayar alhaji bashir ya kallah cikin tsananin bacin rai yace......
Wlh zan nunawa Jamal nina haifeshi be isa yaja dani ba"
Meyayi ne haka da zafi?, cewar alhaji bashir"
Umarni nabashi shine bazaibiba, yaje ya dauki asma'u ya tafi da ita"
Cikin rashin fahimta alhaji bashir yace.....
Ban game umarni ba?, kuma inda yake kwance beda lfy kamata yayi atausaya masa"
Cikin ido daddy ya kalli alhaji bashir sannan yace.....
Yanzun kaman Jamal bazaiji tausayin d'an uwansa ba, ni dashi nagaya mai halin da shamsu yake ciki, yau zan gaya muku abin da nake ganin shamsu be gaya mukuba, Asma'u yariyar da deeni ke tsananin so itace asma'u matar da Jamal ke aure"
Alhaji bashir da ummi mikewa sukayi ummi harda gutun hawayenta"
Daddy yaci gaba da cewa ganin inda shamsu ke tsananin sonta yasa nace ma Jamal ya saketa bayan ta haihu shamsu ya aura, bantaba ba Jamal Umar yaki biba sai akan mace?
Komawa alhaji bashir yayi ya zauna sannan yace sai kamai uzuri, kaida kanka ka fada wannan ne na farko, kuma aikai ka nemi yama tawaye, tayaya mutum na zaune lfy da matarsa acemai ya saka wani ya aura"
Shiko deeni wani irin kallo yakewa daddy mekama dana Allah ya kiyaye"
Fada daddy yaita yi tare da yin fushi me tsanani da Jamal"
Itama momy hankalinta tashi yayi, ina Jamal zaikai ma'u tana cikin yanayi irin na laulayi, shikuma yana faman dingisa kafa, yaya za'ayi wannan zaman gashi ta kula jamal yacika fitana, baya duba yanayin jikin shi"
Kuka take sosai deeni na kallonta juyawa yayi ya kalli daddy yaga shi sai fada yake, har zuciyan shi so yake d'an shi yasaki mata shi ya aura"
Tunawa yayi da lokacin da alhaji vashir yace idan ansami mutumin daya aura asma'u zai kashe konawa ne dan ya saketa"
Wannan nanufin baba bashir besan kowaba sai ni kenan, daman haka sukemin tun ina Karami abin da nake so shi suke min"
Sun kuyar dakai yayi sannan yace....
Toh shi daddy be kyaunar jamal ne? Nasha jin daddy nawa Jamal fada kota waya ne, niko basu min fada har gara ummi takanyi wani lokaci"
Ahankali deeni yaketa babbacewa tsakanin shi da jamal akwai babbaci, dakanshi ya hango ashe ma idan ka samu wadda zai tsaya ya maka fada kai dan gata ne"
Lallai idan mutum ya rasa me masa fada ya shiga uku, tabbas Jamal bashi da makusa yana yin abubuwan shi kamar daddyn sa"
Duk cikin zuciyar shi yake wannan tunani tare da daukan alwashi insha Allahu zaiyi aure ko bana soyayya ba, dan yaga ya mallaki yara ya basu tarbiya ba irin wacce aka bashiba"
Kallon daddy yayi yace daddy dan Allah kabar fadan nan, ni tun tuni na hakura da asma'u nacireta azuciyata, ba tun yauba, daddy ya zan yi na aure asma'u, bayan d'an uwana na auren ta, daddy kayi kuskuren cewa Jamal yabar min mata, wlh na barta har abada, dan Allah abani no Jamal nakirashi ya dawo gida, zama awani waje be dace dasuba"
Kowa afalon kuka yake yi ba mazan ba ba matan ba"
Daddy ne ya share hawaye sannan yace......
Ai be tafi da waya ba, dan dana kira naji karanta adaki"
Shiru deeni yayi zuwa can yace........ .
Daddy ina son nayi aure, nabaka zabi ka zabar min mata ko ya take indai ka amince da tarbiyan ta, inaso na haifi yara na musu tar biya ba irin wacce akamin ba
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
1⃣0⃣4⃣
Takaici ne ya kama alhaji bashir, tare dajin bakin cikin abin da ya aikata abaya, ga dukkan alma deeni baya al'fahari da zaman su iyaye agare shi"
Itama ummi kuka take tasani tuna baya garesu abin kunya ne, suna da mummunan fenti"
Daddy ne ya share hawaye sannan yace"
Allah ya maka albarka shamsu, naji dadi daka fahimci haka, kuma nima nasan banma Jamal adallaci ba, gani nake kamar bazaka rayuba, rayuwarka taban tausayi, inason nan gaba rayuwar ka tai kyau, atunanina sai ka same asma'u ne zaka tsaya ka gane me rayuwa take ciki, duniya ba wani abubane shamsu inda kasan wasan kwaikwayo haka take, idan ka biyewa son zuciya saikakai kanka ka baro"
Nisawa yayi sannan yaci gaba da cewa.....
Shiyasa Jamal yaban mama ki daya zabi barin gida, hakan dayayi ya nunamin yana son matar shi, matsowa daddy yayi sannan ya dafa kan deeni yace....
Shamsu insha Allah matar da zan zabo maka saikayi mamaki, fatana ka kwantar da hankalin ka, kuma kaci gaba da daukan karatun ka agun malam"
Ana cikin haka momy ta mike ta shige daki bakomai ke damunta ba illah barin Jamal daga gida, ba laifin kowa bane illah na alhaji, idan kafar Jamal ta samu matsala dashi xatayi kuka, inama shika dai ya tafi, da hankalinta bazai tashi sosai ba"
Akacin wannan tunanin ummi ta sameta, dago ido momy tayi ta kalleta ta sake maida kanta"
Saida ummi ta share hawaye sannan tace zamu tafi"
Toh kugaida gida Momy ta fada fukarta daure"
***
Bayan fitan suma momy zama tai taishiru kamar wadda akawa mutuwa"
da dare daddy
ya samu momy adakinta, acikin dibara ya fara sako mata zancen shawaran daya yanke, akan cewa mezai hana ahada shamsu da nafisa"
Cikin sauri momy ta mike tare da fadin Sam alhaji, dan me zakace nafisa ta auri shamsu?, kodan kaga bakai ka haifeta ba?
Wani irin kallo daddy ya mata sannan yace....
Yanzun ne dai zaki nunamin bani na haifeta ba, dan inda ace nina haifi nafisa bazan yi shawara dake ba, tun agurin zance nabashi nafisa, ni yanzun roko nazo dan Allah kicire tunanin komai insha allahu alheri ne"
Nifa alhaji bakin shamsu nake ba, dabi,un shi neke tsoro"
Ai yanzun ya shiryu ke dajin kalaman shi na dazon kisan kura tayi lfy"
Eh tabbas ya gyara abubuwa da dama amman alhaji shamsu fah ko mgnr arziki yake sai karkace baki abin ya riga ya zamar masa jiki, sannan har yanzun inajin kyankyanin rayuwar da iyayen shi sukayi, ina musu kallon tsofaffin banza"
Kul daddy ya fada sannan yaci gaba da cewa.....
Karki zama me roko, komai me wucewa ne"
Hmmm Alhaji idan na yadda aka hada wannan aure na cuci nafisa, kuma ma ai dangin babanta bazasu yaddda ba"
Murmushi daddy yayi kadan sannan yace......
Ai bayan fitana dazon naje wajen wan babanta, mun gama mgn dashi yakuma ce sun bani wuka da nama, na yi komai idan nasa rana na sanar masu"
Shiru momy tayi zuwa can tace kuma ka gaya musu waye shamsu??
Cikin fada daddy yace.....
Nace mishi dan kanina ne, kuma ban amince kije ki gaya musu wata mgn ba, na lura so kike ki tuzarta ni, kamata yayi kiyi addu'a Allah yasa alheri muke shirin kullawa"
Mikewa momy tayi
tana share hawaye tare da fadin shikenan alhaji idan kaga dama ma kayi gunduwa gunduwa da nafisa, amman kafin kayi abinda kaga dama ka nemomin dana ya dawo gida dan baza ahada min zafi 2 ba"
Dariya daddy yayi tare da fadin wannan kicire shi azuciyar Ki, ai shiba mahaukaci bane"
Cikin kuka momy tace nifa idan Jamal be dawo gidaba hankalina bazai kwanta ba"
Tsaki kawai addy yaja sannan ya fice abinshi
Bayan kwana biyu daddy ya shiga har dakin nafisa, kwace take tana latsa wayarta ganin daddy yasata saurin mikewa"
Murmushi daddy yayi sannan yaje bakin gadon ya zauna, sannan ya kira sunanta
Ahankali ta amsa daddy yaci gaba da cewa, nasan zaki mamakin ganina adskin ki ba komai bane ya kawani illah wani alhri da muke shirin kullawa, mum yake shawaran hadaku aure keda shamsu"
Nasani ke yariya ce me biyayya, kuma nasan zaki amince da bukatata, karki yadda momyn ki ta zugaki insha Allahu zamuce gara da akayi"
Kan nafisa akasa wasa take da hannun ta, hakan nan ta tsinci kanta cikin farin ciki saidai fauskan Jamal tana firgitata lamarin shi yana bata tsoro, Allah yasani tun ranan dataga deeni ya kwanta mata arai tsoron fasifar shi yasa tayi nesa dashi"
Mikewa daddy yayi tare da fadin umarni na baki bana neman zabinki, ina fata bazaki ki jin umarnina ba"
Kai da daga ahankali, sosai daddy yaji daddy har yabar dakin yana samata albarka"
Shirye shiryen baki daddy ya hauyi gadan2 komai da ake zubawa yar gata daddy yasa anzuba agidan da yabawa deeni"
Shiko deeni bawani shiri yake ba, domin kokari yake yaga rayuwar sa ta gyaro, bema san wacece amaryar ba, kuma be damu ya sani ba, burinshi kawai yaga ya aje iyali"
Abangaren momy kuwa, kullun fuskarta daure take tam, taki gayawa kowa zancen auren nafisa, dan haka daddy da kanshi ya sanarwa dangita"
Koda yayyata sukazo lallashinta suka yi, akan tayi hakuri insha Allahu auren zai bata mamaki"
Haka shirye shiye ya dada kankama nafisa sai rawar kai take, tare da kawayenta, sosai takebawa momy haushi, saidai batace mata kala, har biki ya rage sati, kuma aranan ne Jamal yacika sati uku da barin gida"
****
Jamal da ma'u nagani agaban doctor, sai ya mutsa fuska take Jamal na tarota"
Bayan Dr ya gama rubuce rubucen sa ya dago ya kalli jamal yace"
Ranka ya dade inaganin abin da yafi kawai, ku raba makwanci har cikin yayi kwari, domin idan har zaku dinga haduwa za'a samu matsala gaskiya"
Shiru Jamal yayi zuwa can ya daure fuska tare da fadin.....
Bakomai insha allahu zan kiyaye, sai mgnr kafata?
A kafar ka Alhamdulillah ta cike saidai ansamu matsala inaganin daga Dr dake wanke maka ciwon ne tun da farko, dan gashi bata warke yadda ya kamata ba, amman bawata matsala"
Godiya Jamal yawa dr sannan ya daga ma'u suka fito"
Biyosu Dr yayi tare da fadin Oga akiyaye fah"
Bayan sun koma gida tarairayan ma'u Jamal keyi sosai baya yadda ta dauki ko kofi abinci ma abaki yake bata, cak yake daukanta ya kaita toilet yai mata wanka, cikin dare ko haka yake rungumeta tsam ajikin shi, kamar dai wani zai kwace masa ita"
Har mamakin Jamal ma'u take wai ayanzun ita Jamal yakewa bauta, duk girman kannan ya ajeshi agefe"
Bayan sati 1
Yau jamal ya tashi da tunanin gida sosai axuciyar shi dan haka yadau waya yasa no momy"
Bugu biyu ta dauka, hayaniyan mutane yaji tare da dallaman Momy"
Ahankali ya amsa"
Arikece momy tace......
Jamal?
Na'am momy kuna lfy?
Kaniyarka Jamal, kai kana da hankali kuwa?, kana inane yanzun?
Momy nakirane naji lfyr ku kuma kusan muna lfy"
Jamal ina Asma'u?
Tana toilet"
Kafarka fah?
Karamar dariya Jamal yayi tare da fadin ta warke mom......
Karya kake Jamal be isa ta warke ba"
Wlh Momy ta warke bari zan turo miki pic dinta kikani"
A'a karka turomin kadawo gida kawai Jamal, hankalina bazai taba kwanciya ba, sainaga ka dawo idan ma kai bazaka dawoba toh katuro Asma'u gida"
Kawar da zancen Jamal yayi tare da fadin momy wai baki gida ne naji hayaniyan mutane ne"
Ina gida Jamal, bikin Nafisa ake yanzun aka daura mata Aure"
Aure kuma Momy?
Fashewa momy tayi da kuka tare da fadin eh Jamal daddy ka ya matsa saiya aurar da ita"
Da sauri Jamal yace dawa?
Da shamsudeeni"
Deeni ?, momy ta yaya zaki bari adaura wa Nafisa aure da deeni?
Jamal kasan halin daddyn ka da kafiya da naso hanawa ma cewa yayi dan naga bashine ya haifeta ba, dan haka nabarshi yayi abin da yaga dama da ita"
Hakuri Jamal ya karabawa momy sannan ya mata alkawarin sunanan dawowa"
Bayan ya aje wayar ya tashi ya shiga dakin baccin su, ma'u na kwance akan gado, hawa yayi ya kwanta, sannan ya jawota jikinshi ya rungume tare da sun batanta ta, acikin kunnenta ya rada mata yau kawarki na Aure"
Zainab ? Ma'u ta tambaya"
A'a Nafisa"
Tashi tayi ta zauna tare da fadin nafisa?, naga yau satin mu 4 anan kuma banji ana mgr aurenta ba"
Eh daga baya ne"
Tabe baki tayi tare da fadin aiko banji dadiba naso ina gida za'ayi, to wa ta aura?
Kauda kai yayi sannan yace deeni"
Deeni? Yaya da gaske???
Zan miki karya ne?, yanzu nakira momy awaya take fadamin"
Guri daya ma'u ta kurawa ido, tare da kokarin danne abinda ke shirin bijuro mata"
Kallonta kawai jamal yayi sannan ya mike ya fita adakin"
Hawaye taji yana zubo mata ahankali ta fara tuno irin rayuwar da sukayi da deeni abaya"
Acikkn xuciyanta take cewa...
Haka Allah ya nufa deeni ba mijina bane bazamu zauna tare ba, duk irin soyayya da mukayi tazama abanxa abubiwan da sukaitayi ne yaita fado mata, zama tayi kamar mahaukaciya wani tai murmushi wani tai hawaye, acan karkashin zuciyanta ko bataso nafisa ta aure deeni ba taso yasamu watacan ya aura"
Tun daga ranan yanayin ma'u ya dan canza haka ma Jamal dayake lora da ita"
***
Deeni ko Sai a Wajen daurin auren yasan nafisa ce amaryan, fuskan shi babu yabo babu fallasa, abokan shi na kano duk sunzo cikin manyan kaya kamar basuba, bayan andaura aure duka suka wace caka ne kawai ya tsaya"
Lokacin da caka zai raka deeni gidan shi saida suka fara biyawa gidan alhaji bashir sosai sukamai fada harsaida abin ya bashi mamaki, bayan sun mike ummi ta kalli caka tace wlh bakuga inda kukayi kyauba, kamar baku ba, wai ya sunanka ne?
Cikin murmushi caka yace ummi sunana *Faisal*
Hannu ummi ta tafa tare da fadin sunanka me dadi ake cemaka wani wai caka, dan ALLAH auta daga yau ka rinka kiranshi da sunan shi"
Addi'oi tayimai sosai sannan suka wuce gidan deeni"
Gidane nagani nafada daddy ya mallakawa deeni tare da mota me zafi, har cikin falon suka shiga har sun nufi cikin dakin deeni ya tuna da karatun malam acikin zuciyan shi yace bazan shiga dawani har cikin dakin mamata ba"
Waigawa yayi ya kalli caka yace faisal zauna anan ina zuwa"
Bakin gado ya samu Nafisa yafe da gyalenta me tsananin shiki, hannu yasa ya yaye gyalen, cikin sauri ta sukuyar da kanta kasa, yana daga tsaye yasa hannu ya dago habarta suna hada ido ta maza ta rufe ido"
Murmushi yayi kadan sannan ya ninke gyalen ya aje agefe sannan yace kisa hijjabi ki sameni falo akwai abokina dazaku gaisa"
Kamar yadda yace haka tayi bayan sungaisa ta koma daki"
Aranan deeni be runtsaba adaren ya dama furanshi kuma yashanye ta tas"
Nafisa ta jigata sosai tayi kuka tayi magiya dan haka dasafe idonta yayi jawur bata san haka haka aure yake ba da bazata taba yadda ba"
Shima deeni tausayinta ya kamashi tsam yasata akirjinshi dare da lalabo duk Wata kallama ta lallashi yana gaya mata"
Ahankali yafarajin sonta na shigarshi, farin cikin yaji ya kamashi sosai tare da godewa Allah daya amsa addu'anshi daman ya shanye furan ne ayau Dan ya yakice burbushin son ma'u azuciyan shi"
Haka suka kwashe tsayon sati uku suna cin soyayyar su, zuwa wannan lokacin sun saki jiki da juna kuma ahankali suna kara shakuwa"
Zuwan su gidan momy 3 amman da daddare suke zuwa itama momy ta fara sakkowa domin ayanxun duk lokacin dazakaga deeni cikin farar jallabiya yake tare da carbi ahannun shi"
Har kasa yake tsugunawa ya gaisheta betaba yadda su hada ido, Nafisa ko cikin manyan hijabai take"
Tayi wani irin kiba naban mamaki"
****
Jamal ko jinyan ma'u yake, tare da kokarin cire mata kowanne irin tunani sosai takejin dadin zama da jamal, dan yi yake tamkar ya maidata ciki"
Dakanshi yake girka mata abincin da zataci, baya barinta tayi ko cangal, anacikin haka ne ya koma aiki dan haka dole yasa ya nemo me aiki"
Bayan sati 2 ma'u tana kwace afalo cikin duguwar riga, sosai cikinta ya turo kaikace cakin wata 7 ne, kyau cikin ya mata tare da Kara fari da sheki"
Daya daga cikin. yaran Jamal taga ya shigo da wusu manyan ledoji guda biyu, cikin sauri ta miki tare da mamakin meyakawo Jamal da rana"
Muryan yaya usman taji yana sallama tare da anty fa'iza"
Batasan sanda ta mike taje gaban fa'iza tana fara'a ba, amsan yariyar tayi sannan ta jawo hannun fa'iza suka zauna yaya usman ta fara gaidawa amman ke madagas yaki amsawa, ganin haka jikinta yayi sanyi gaisawa suka da anty Sannan sukaciga da hira sama sama"
Hannun anty fa'iza ma'u ta dada dagowa tare da fadin zo muje daki"
Bazataba, usman ya fada fukan shi cike da haushinta, cigaba yayi da cewa mara kunya kawai ke me miji ko ?
Kara sukuyar da kanta tayi tare da matso hawaye"
Basu dadde da zama ba taji tsayowar motar jamal tasan gayamai akayi yayi baki"
Yana shigowa ma'u ya fara kallo sannan ya koma gurin da usman ke zaune karasawa Jamal yayi tare da fadin babban yaya daman nasan kaikadai ne matsala ta tunda ka bincikoni akurgumin daji babu a inda bazaka binciko ni ba"
Wani irin kallo usman yamai sannan hace....
Yazun saboda Allah abinda kayi kan kyauta kenan?, kabar momy cikin tashin hankali"
Katseshi yayi tare da fadin haba usman ko kaine bazaka zauna ba hukuncin daddy yayi tsauri da yawa gaskiya inason matata yaya za'ayi ba acemin wani nasaketa "
Juyawa Jamal yayi yaga idon ma'u alamar tai kuka, cikin sauri ya tashi tsam, ya nufi gurinta, ganin tahowanshi yasata mikewa ciki sauri dan tasan riketa zaiyi gaban yaya"
Bayanta yabi tare da fadin.....
tsaya mana, ina daki ta shige Jamal nabin bayanta hannu sa yasa ya tarota sannan yasata ajikin shi tare da fadin usman ne ya bata miki raiko?
Guntun hawaye ta share sannan tace yaya yaushe zamu koma gida?, kaga yaya usman na fushi dani nagaida shi yaki amsawa, ina tsoron kar ace abba ma yayi fushi dani"
A'a Husna Abba bazaiyi fushi dake ba, ni mijin ki ne kuma sun san muna tare, dole ce tasa nai haka bayin kaina bane, dan haka ki daina damun kanki da tunani banza, nasan halin usman ciki dabai, zuwa dare zan kira miki abba Ku gaisa, wata kila hankalin ki zaifi kwanciya"
Sakin ranta tayi kadan, nan Jamal ya barota ya dawo falo yana zama anty fa'iza ta miki dakin ta shiga sosai ma'u taji dadi, nan hira ta barke tsakanin su, lbr yadda abba ya shiga damuwa da daddy ya gaya mushi Jamal yabar gida tabata
Cikin ido ma'u ta kalleta tace kila shima yanzun haushina yakeji?
Bawani haushi, ko jiya da mukaje ya fada mishi ya samu inda kuke cewa yayi agaida ku, kuma usman ya roki Jamal idan cikin ki ya tsufa ya dawo dake gida"
Ajiyan zuciya tayi sannan sukahau hira"
Jamal ma da usman hira sukayi sosai acikin hiran ne usman ya isar da sakon abba"
Difff Jamal yayi xuwa can yace kasan abin da yasa na kasa dawowa wlh banson ganin deeni kullum tsanarshi kaaruwa take axuciyata"
Ai kaji irin ta mutumin da yayi auren shi ina ruwanka dashi, kaifah daman kacika kishin jaraba, shiyanxun ma bata Asma'u yake ba bakaga gadda. Nafisa tai kyauba naji kanmar ma ance ciki gareta, shikanshi deeni idan ba Sanin shi sosai kayiba baka iya shaida shi"
Ker Jamal ya yadda idan cikinta ya tsufa zasu taho, anayin la'asar suka kamo hanya"
Jamal yaciga ba da lallashin ma'u harta saki ranta so daya ya taba kira mata Abba, bayan sungama waya ya kira mata momy, tundaga ranan ya kashe waryarsa"
Bayan 4
Cikin ma'u ya tsufa tafiya daker tashi daker, idan ka ganta saika tausaya mata"
Kuma lokacin ne hankalinta ya tashi sosai, cikin dare bata iya bacci tashi take ta tasa jamal agaba da kuka"
Cikin tsananin damuwa yake tashi ya zauna, tare da fadi husna kiyi hakuri mana kidaina dagawa kanki hankali"
Nina gaji yaya, ciki kusan shekara daya ajikina ni gaskiya daga wannan bazan kara ba"
Kauda fuska Jamal yayi yai dariya sannan ya juyo ya kalleta tare da fadin gobe zamu wuce gida, dan naga nema kike hawan jini ya kamaki, haba ace mutum be gajiya da kuka"
Murna ce ta kama ma'u sauka tayi wai xata hada kaya, jamal ne yahanata shida kanshi ya hada musu kaya"
Dasafe ya kira no Momy, tana dauka tace Jamal wai yaushe raini ya shiga tsakanin mu haka?, bazaka dawo da yar mutane ta haihu agida ba?, cikin watan haihuwanta fa take"
Cikin mamaki Jamal yace momy waya gaya miki?
Uwarka ce, akace maka bansani bane?, ai ina lissafi, ko ta haihu ne ma?
Sosa keya yayi tare da fadin a'a munan isowa yau"
Yauwa Jamal Allah ya maku albarka dan Allah kutaho da wuri"
Toh momy amman kafin mu tahu inason zan shiga kasuwa"
Me zaka saya indai kayan haihuwa ne nariga dana hada komai"
Heart Beat
*Mmn Yazeed*
💗💝💝💗
*BUGUN ZUCIYA*
( Heartbeat)
💓💝💗
💗
💓💝💗
By
💗
*Fadeela Lamido*
*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*
*Sadaukarwa ga duk me karata BUGUN ZUCIYA, nagode da irin soyayyar da kuka nuna min tare da wannan lbr BUGUN HEAT, Allah yabar kyauna💋*
*Sakon gaisuwa da fatan alheri ga marubutan mu, wad'an da suka karamin karfin guiwa wajen rubuta wannan lbr, bani da bakin mgn, hakika kun nunamin kyauna, sai dai nace Allah yabar xumunci🙏🏻*
1⃣0⃣5⃣
✋🏻✋🏻✍🏻 Karfe 3:15pm suka shiga gidan momy murna momy take sosai tana rike da hannun ma'u tare da tsareta da ido, nandan lbrin dawowan su ya zaga ko ina, tsilum saika Nafisa aguje ta shigo da cikinta daya fara tasowa manne ajikinta"
Jikin ma'u taso fadawa, momy ta tareta tare da fadin nafisa lfyr ki lau kuwa? Kewai bakijin nauyin jikin ki ?
Komawa tayi kusa da ma'u ta xauna, sannan ta shiga gaida Jamal wani irin amsawa ya mata batare daya kalleta ba,
'Daga ma'u nafisa tayi sannan ta suka nufi daki, kallon nafisa ma'u take tana mamaki wai yanzun cikin deeni ne jikin nafisa?, Ikon Allah kenan"
Hira suka barke dashi daga falo su momy sunajin dariyar su"
Sai dare deeni yazo daukan nafisa be shigo ba, waya ya mata tafito sutafi sannan tace yana gaida momy"
Daddare momy so tayi ma'u ta kwana gurinta amman taga Jamal sai zarya yake yafita yadawo dan haka tace tashi su tafi"
Dukda kwaciya kawai zasuyi tare yafison haka akan ace sunyi nesa da juna,
Washegari da safe sukaje gaida daddy abinda ya bawa Jamal mamaki daddy be nunafushi ba, sosai farin ciki ya bayyana afuskar shi, koda zasu tashi yaga ma'u na kici kicin tashi, cikin fada daddy yace haba Jamal taimaka mata mana, kunya ce ta kamashi daker ya iya mika hannu ya dagata Albarka daddy yaita samusu tare da addu'ar Allah ya sauketa lfy"
Adaren ranan ciwon nakuda ya tayarwa ma'u tunda momy taga inda take cije baki ta kira jamal, daki ta shiga ta dauko kayan haihuwa tace asibiti zamu"
Karfe 10:39pm ma'u ta haifo zarkada zarkadan 'ya'yanta guda biyu dukkan su maza ne masu kama da Jamal"
Bakaramin maki Jamal yayi ba, tunda suke zuwa asbiti babu wadda yataba cewa yan biyune acikin husnan shi"
Momy ko farin ciki ya hata mgn, adaren suka dawo gida domin ma'u lafiya lau take"
Tun asuba momy ta fara gayawa yan uwa da abokan arziki dan haka tunda safe gidan ya fara cika da baki"
Nafisa ma murna ba'a magana tare da deeni sukazo fuskanshi dauke da murmushi nafisace ta kwaso yaran ta mika mishi kallon yaran yayi gwanin ban sha'awa nan danan idonshi yacika da kwallah yasa hannu ya share tare da fadin nafisa yaran nan sun bani sha'wa inason yara sosai sunbatan yaran yayi tare da fadin Allah yayi muku albarka ya karawa mahaifiyar ku lafy shekara me zuwa ta sake haifo mana kalan ku, yakuma bawa mahaifin ku abinda zai ciyar daku"
Amsawa nafisa tayi da ameen, sannan tace ka manta addu'a daya da bakiyi ba"
Dagowa yayi
ya kalleta, idontshi da ragowan hawaye ga kuma murmushi akan bakin shi yace....
Wacce kenan?
Cikin murmushi tace......
Bakace muma Allah ya bamu irinsu ba"
Murmushi yayi tare da cewa a'a nafisa muruke me albarka kawai, ko mace kona miji ke duk abinda Allah yabani zan karba nayi godiya lokuta da dama abinda mukeso ba alheri bane agare mu"
Dahaka ya mikawa nafisa yaran sanan yace ta gaida asma'u"
Aranan momyn usman ta iso tare da dada"
Tunkafin ta shiga gidan take fadin you alkawari ya cika gani agidan takwara"
Koda suka shiga dakin ma'u daure fuska tayi, tare da kyauda kai, itama dada daure fuska tayi tare da fadin nima ba gurinki nazo ba"
Aranar da daddare hajiya asabe tazo ganin jarirai, farin ciki sosai ta nuna"
Acikin zuciyan Momy tace inma bakin ciki kike ke kika sani, ni baki gabana mantawa ma nake inada kishiya idan yana gidan ki gani nake kamar tafiya yayi"
Awaya deeni ya kira Jamal yamai barka, ana gobe suna ya dauki nafisa suka shiga kasuwa kayan yara yaita kwasa kala kala tare da kayan wasa kai harda keke komai iri daya ne kuma bibbiyu, mota sukaita lodawa, Wata sarka nafisa tagani tace ka saiwa asma'u"
Wani kallo ya watsamata tare da fadin awani dalilin zan saimata ?, kinason mijinta yakaini kutu ko?
Turo baki tayi sannan tace wato ka maida yaya mafadaci ko?
A'a nafisa aiko nine sai inda karfina ya kare"
Washegari akwai suna, anci ansha jama'a ba masaka tsinke da sunan su aka barsu *Hassan da Hussain* aciki waddan da sukazo suna harda zainab kawar ma'u"
Lokacin da yan waliman Jamal suka cika gidan da hayani ma'u ta jawo zainab bakin window da hannu ta mata nuni da deeni"
Tabassa deeni yayi kyau babu wadda zaice yayi rin
rayuwar da yayi abaya, Saika ma zaci yafi su Jamal roko da addini domin su dikine na zamani sanye ajikin su, yayin da deeni yake cikin jallabiya fara karrr hannun sa rike da carbi, gefenshi Faisal ne zaune"
Washegshegari duk yan suna suka watse, sai dada kadai ta rage"
Kulum abba ke kiran dada awaya tare da tambayan jikokin shi, wata rana abba ya kira dada suna cikin mgn ma'u ta kwace wayar tasa akunne tare da fadin abba kulum ni baka tambayata"
Dariya yayi sannan yace......
Asma'u ai muna waya da mijin Ki, nasan lfy lau kike, ya mutanen gidan naku?
Lfy lau"
Toh madallah, Allah ya miki albarka, yadda kika min biyya kema Allah yaba ki masu miki, akullum ina miki addu,a zama lfy tare kwanciyar hankali"
Ameen abba, idon ma'u cika yayi da kwallah, sallama sukayi da abba, hawaye kawai ma'u taji suna Zubo mata daman haka iyaye sukeji idan dan su yai masu biyyaya, lallai naso nayi kuskuren nabi son zuciyata, kome nayiwa iyya na bazan biyasu ba, addu'a ta shiga ma iyayenta Allah ya saka musu da alheri"
Haka dada taciga da kula da yaran ma'u Hassan da Hussain har sukayi arba'in aranan Jamal yakaisu Kano, bayan sati 2 ya koma ya dauko su"
Bayan wata 5
Nafisa ta haifi katon danta, murna gurin deeni ba'a mgn, ya dade rungume da yaron, yana kwalla tare da tufa mishi addu'oi"
Ma'u ma bakinta ya kasa rufuwa, shiryawa sukayi ita da momy zasu tafi, momy na rike da hassan, hussaini a hannun ma'u har sun fito harabar gidan, motan Jamal ya shigo"
Tunkafin ya fito ya daure fuska"
Ma'u ko fara'a take tare da zumudin fadamai nafisa ta haihu"
Cikin basarwa yace naji ai, ina zaki?
Sanyi jikin ma'u yayi, tare da rasa abincewa"
Momy ce ta kalleshi tace.....
Zamuje gano jariri ne"
Da sauri yace amman bada Husna ba"
Daure fuska Momy tayi tare da fadin da Husna kuwa, Jamal wai me kake nufi ne?, kiri kiri ka hana Asma'u zuwa gidan Nafisa, bata taba zuwaba, watanta 6 da haihuwa amman ka hanasu suyi zumunci, wanne irin bakin kishine wannan?
Shiru Jamal yayi tare dasa idon shi akasa"
Cigaba momy tayi da cewa toh abin ya fara damun nafisa, dan harta fara korafi akai, abinda kake nufi baxai yuwuba gara ka canza tunani, jayawa tayi ta kalli asma'u tace wace mutafi"
Acike suka samu falon, ummi na zaune rungume da d'an deeni ahannunta, bayan gaishe gaishe ma'u ta amsa yaron, dakin nafisa ta nufa, tana kokarin shiga dakin sukai karo da deeni yana fitowa"
Cikin sauri ya matsa gefe tare da fadin Ya subuhananlah"
Dago ido ma'u tayi ta kalkeshi, shima idosa nakanta"
Tafiya ta fara tare da gaidashi bayan ya amsa tamai barka sannan ta shiga dakin jikinta asanyaye"
Saida yamma suka koma gida tundaga ranan Jamal be sake barin ma'u tajeba, har ana gobe suna"
Ran momy ya baci sosai dan haka dayazo sallama zai tafi aiki ta rufeshi da fada"
Fadan momy yasa hankalin jamal ya tashi har ya yanke shawaran zuwa ya gano nafisa tare da jaririn da ta haifa"
***
Yana shiga gidan deeni na kokarin fita amman ganin jamal yasa yai saurin fitowa"
Hannu ya bashi suka gaisa fuskan deeni asake yayin da ta jamal take daure"
Har dakin baccin nafisa ya kai Jamal sannan ya juya ya fita"
Bayan sun gaisa ya rungume jaririn ya koma gefe"
Gunshekan kukan nafisa yaji, cikin sauri ya daga kai ya kalleta, sannan yace.....
Ya da kuka kuma?
Yaya Anty asma'u fah bata taba zuwa ba, gashi yanzun ma tunda tazo so daya bata sake zuwa ba"
Shiru yayi yana kallon yadda take share hawaye, zuwa can yace.....
Au saboda haka kike kuka, lallai shagwaba ta miki yawa dallah zoki amsa yaron Ki"
Juyawayi yai ficewan shi"
Daddare nafisa na zaune taji muryan asma'u kasa jira tayi ta shigo"
Cikin fara suka kalli juna sannan nafisa ta karbi yan biyu ahannun ma'u
Bayan sun zauna nafisa take tambayanta halan keda momy?
A'a yaya ne ya saukeni wlh abin yaban mamaki ina zaune yace wai nashirya yakaini Gidan Ki na kwana tunda gobe suna, wlh na dauka sunan ma bazai barni zuwa ba"
Wani farin ciki ne ya kama nafisa, mara misalantuwa"
Washegari yaro yaci suna Mashkur, aranan sunan Faisal yazo, walima sosai deeni yayi"
Washegarin sunan ne daddy ya hada Jamal da deeni, fada ya musu sosai tare da nasiha me shiga ciki, bayan ya gama ne yayiwa deeni albishirin ya budemai manyan rumfuna dazai yi kasunci aciki"
Godiya yayi sosai, nan danan deeni ya zama shararran dan kasuwa"
Tare da faisal suke gudanar da komai cikin Ikon Allah kasuwa saikara burun kasa take"
****
Jamal da deeni zuwan su baguma 3 tare dakai musu niki2 abun arziki"
Yan biyu nada shekara daya ma'u ta sake samun ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji wadda aka sawa Aliyu, sosai yan biyu sukayi wayau tafiya suke gwanin sha'awa"
Aliyu nada wata 7 Nafisa ta sake haihuwan Jafar"
Zuwa wannan lokacin Jamal da deeni suna mgn sama sama, yadda yaga deeni na nuna soyayyar nafisa ako ina yasa jamal ya saki jikinshi, kullum cikin kara ririta ma'u yake"
Sosai Abba yakejin daddy idan ya tuna Asma'u na dakin mijinta, Jamal betaba kaimai karanta ba, kullum yaje gaida Abba idan xai tafi ya dinga godiya kenan"
Ita ko ma'u akullum suka hadu da Abba albarka yake saka mata"
Bayan ma'u ta yaye aliyu ne Jamal ya maida ma'u makaranta domin ta cigaba da karatunta"
Manyan hijjabai ya saya mata dakan shi yake kaita indai yana gari"
Bayan shekara 3
Ma'u na daf da karasa karatunta, ta fara laulayin ciki, tashin hakali ta nuna sosai, ganin haka Jamal yaita kwantar mata da hankali tare da nuna mata ai ciki bazai hanata karasa karatu ba"
Lallashinta yaita yi tana dada narkewa ajikinshi tare damai shagwaba iri iri, biye mata yai tayi, har ta saki jikinta"
Itako nafisa cikin na hudu ne ajikin ta, kulawa deeni yake sosai wajen basu tarbiya, baya wasa, beciga son kaisu gidan abbashi bashir ba, daya kaisu aranan yake komawa ya dauko su betaba bari sun kwana agidan ba, duk da yasan cewa komai ya zama daidai amman hankalin shi baya kwanciya"
Gidan momy ko aduk sanda suka samu hutu can yake kaisu har hutun ya kare, dan haka mushkur da yan biyu suka kule, wasa suke sosai"
Cikin ma'u ya tsufa dan haka Jamal ya matsa zai koma gidan shi, momy taso ya bari sai ma'u ta haihu amman ya dage"
Acewar shi tunda da tace tsoro take ji yanzun ai ga yara nan ta samu"
Sun koma da sati 2 ma'u ta haifi 'ya mace"
Kowa ya kalli yariyar cewa yake da ma'u tai kama, amman Jamal dagewa yayi wai shi ta dauko, haushi ma'u takeji idan jamal yace shi ta biyo, dan haka ta fara daure fuska"
Nafisa ce taita sintiri zuwa gidan da goyota abaya har akayi suna ayanzun yaran nafisa 4 kuma duk maza ne, yayin da ma'u keda 4 amman haihuwanta 3"
***
Yanzun Hassan da Hussaini suna da shekara 10, girma sukai na ban mamaki farare ne tas idan ba wadda ya sansuba baya iya babbaci su"
Wayon tsiya gare su, idan ka kalli ma'u baka taba cewa ita ta haife su, shi kanshi Jamal idan ya fita dasu cewa ake kannin sa ne, dan sun kusa kafardar shi"
Wata rana jamal ya kwaso duk gidan domin zuwa gidan momy, akan hanyar ne hira ta barke tsakanin Jamal da yaran shi, inda yake tambayan so idan sun gama karatu me suke so su zama?
Hassan ne ya fara cewa nidai daddy SOJA zan yi"
Kai amman ka burgeni kaifa hussaini?
Tura kanshi yayi gaban motar inda Jamal da ma'u ke zaune yace.....
Nidai daddy so nake kawaai na auri Hussaina"
Gaba dayan su dariya sukayi ban da ma'u data zafgawa Hussaini harara"
Itama Fatima wadda suke kira shikuriya zuboro baki tayi tare da matso hawaye"
Bayan jamal ya gama dariya ya waiga ya kalli Hussaini yace amman ai saika gama karatu ka samu aiki zakai auren ko?
Kafin Hussaini ya bashi amsa yaga Shukuriyya na shirin kuka dan haka ya juya ya kalli ma'u yace....
Toh fah, ita kuma wannan rigimanmar waya bata mata rai, nakula duk dabi,unta naki ne"
Juyawa yayi ya sake kallon shukuriya yace gaya min wanene ya bata miki rai?
Cikin shagwaba tace ba hussaini bane yake cewa baxai aureni ba, wai Hussaina zai aura"
Murmushi Jamal yayi kadan sannan yace wace wacece Hussaina?, rabu dashi aina zai samu Husaina ?, karya yake yi"
Hassan ne yayi dariya tare da fadin dolowa kawai, yaya za, ayi ya aureki ?, mamarmu daya babamu daya ai ba'a aure, saidai ki Aure mashkur"
Azuciye ma'u ta waga ta daka musu tsawa tare da fadin wlh duk wadda ya kara mgnr aure cikin ku saina fasamai baki, waigawa Jamal yayi ya kalli ta ya dauke Kai domin ya lura kamar ranta bace yake"
Babu wadda ya sake mgn har suka isa gidan' bayan Jamal ya gaida mikewa yayi zaifita saitin kunnen ma'u yaje yace.....
My Sweet Heart idan nina bata miki rai kiyi hakuri, idan kuma yara ne ki musu uzuri yarinta ce ba wani abuba"
Yana gama fadan haka yajuya ya tafi"
Da daddare ya dawo ya dauke su suka koma gida"
Jamal na kwace agefen gadon ma'u yake tambayan ta wai dazun menene ya bata miki rai ne?
Cikin damuwa tace....
Yaya tsoro Hussaini ke bani bashi da zance saina aure kusan kulum sai yayi mgnr, sai naga kamar babu karatu agaban shi"
Murmushi yayi sannan yace......
Ki daina damun kanki Husna yarinta ce ke damun shi, babu abin da ya sani fada kawai yake"
Washari da safe daddy ya bugawa Jamal waya cewa nafisa ta haifi 'yan biyu duk mata"
Cikin fara'a Jamal ya fadawa ma'u, shiri tahau yi cikin tsan tsan farin ciki"
Tunda Hassan da hussaini sukaji suka kama murna tare da rukon suma zasu"
Lokacin da suka isa gidan cike suka samu falon ciki harda dadddy da momy, alhaji bashir da ummi, deeni har kuka yake saboda farin ciki, kasa amsa barkan da Jamal kemai yayi sai hawaye dake zuba a idon shi, bayan shi Jamal ke bugawa tare da fadin ba kuka yakamata kayiba ka godewa Allah"
Addu'io Jamal yayiwa Hassana da hussaina sanan ya mikawa ma'u"
Kwlla cike da idonta bakinta dauke da murmushi take kallon su"
Damunta yan biyu sukayi dan haka ta mikawa husaini Hasssana girza kai yayi tare da fadin momy Husaina zaki bani"
Hararan shi tayi sannan kowanne ya dauki takwaran sa"
Kinbawa kowa su sukayi, momy ce tace, nifah 'yan biyu ban gane bane, me kuke nufi?
Dariya ummi tayi tare da fadin kika sani ko yar gida za'ayi?
Dariya daddy yayi sannan yace kudai kuce kishi na damun ku"
Tun daga ranan ma'u ke zarya zuwa gidan har akai suna, kulum idan ma'u zata tafi sai 'yan biyu sunce ashafa musu kan jarirai"
Abba da kanshi ya kawo mama suna sannan yaita sawa yaran albarka dayaga deeni be iya shaidashi ba, saida daddy yagaya masa"
Ma'u nakai ziyara kano akai akai, inda lokaci bayan lokaci yaya usman yake kai mata fa'iza da dada"
Wata rana dada ta kawo mata ziyara da gangan tajata gidan nafisa, suna shiga tsakiyan harabar gida ma'u ta juya ta kalli dadda tace......
Dada kinsan Gidan wa na kawoki?
Saikin fada takwara"
Dariya ma'u tayi sannan tace gidan me kare"
Rawan jiki dada ta fara tare da fadin La haula fisha'atillahi azubika, Allahu akkubar Allah da kirma kake, fitsari ne ya fara zubowa ajikinta, banda dariya babu abinda ma'u keyi"
Daida kokacin deeni ya fito daga gida, ganin haka yasa ma'u ta tsaya da dariya tare da kama hannun Dada tana fadin zomuje"
Tirjewa dada take tana cigaba da surutun ta"
Deeni ne
ya matso yana fadin yaya akayi ne dada?
Yauwa bawan Allah zoka tai make ni, ka maida ni Kano ya riyar nan bata kyaunata so take taga bayana, zata kaini inda za'a akashe ni"
Ganin in da dada take arikece yasa ya kama hannun ta, motar shi ya bude ta shiga, ma'u dariya take tayi badan kar dada ta sumaba data kara cewa wani abu, cikin gidan ta shige"
Shiko deeni bayan sunyi nisa yaga jikin Dada ya daina rawa, anan ya fara tambayanta meya hadata da asma'u?
Warware mishi komai tayi, kwashewa yayi da dariya acikin zuciyan shi yace sai yashe asma'u zatai hankali ta daina tsokana, daman har yanzun tana nan da halinta?
Gidan daddy yakai dada sannan ya gaya musu abinda ke faruwa, dariya sosai daddy yayi sannan yace ai ga mekaran nan agaban Ki"
Mamaki ne ya kama dada daman Abba ya gaya mata deeni ya shirru Amman batasan takai haka va"
Hira sukaci gaba tsakanin deeni da dada daddy da Momy na souraran su"
Bayan shekara 10
Soyayya ce me karfi tsakanin Hassan da Hassana, Husaini da Hussaina, tun suna kana suka taso da kyaunar juna, duk da cewa su hassana basu wuce shekara 12 ba"
Jamal da deeni zumuci suke sosai har sun yake shawaran hada inbiyun su aure, da zaran ko wannen su ya kammala karatun shi"
Ma'u tun daga shikuriyya bata sake haihuwa ba, Jamal kara shagwabata ma'u yake idan ka gansu adaki bakace suna da yara 'yan shakara
20 da duriya ba"
ALHAMDULILLAH
Heat Beat
The End🙋🏻
*Mmn Yazeed*
0 comments:
Post a Comment