Wai ke wace irin jarababbiyar mace ce? Abunda Rasheed ya fara furtawa kenan ,Ilham tayi murmushi tace ” captain nifa bazan bar gurin nan ba in har am not convinced kayi accepting apology na ba! I told you am d one who made d mistake,kuma na gyara kum………. Kafin ta k’arasa yayi murmushi yace “Fine!! Apology accepted little miss you may now take your leave(zaki iya tafiya) tayi murmushi tace ” thanks for that,ta juya ta nufi hanyar gida ,yana tsaye yana kallonta ,yadda take tafiya ma kad’ai abun kallo ne ,ya rasa gane yadda akayi tsanarta tabar zuciyar shi, yayi giving up so easily,yarinyar tana neman shiga zuciyar shi ne tabbas kuma duk yadda yayi ya kawar da tunanin ta a wannan dare sai ya kasa.
Bangaren Ilham ma dai hakan take domin kuwa ya dad’e da samun mafaka a zuciyarta ,wannan kuma shine karo na farko da hakan ta faru da ita.
A kwana a tashi yau kwanan su biyar da zama friends ,tunanin Rasheed duk ya gushe gaba d’aya tym d’in da ya saba bawa Imtihaal ya koma kan Ilham, shi a iya sanin shi Imtihaal friend nashi ce bai san ita a zuciyarta ya fi hakan ba ,Sadiq da Al’amin kad’ai suka san hakan ,suma ba don ta sanar da su ba sai don wani takardanta da suka gani ta manta a motan su ,duk wani feelings nata akan Rasheed ta rubuta. Sadiq tun da yaga yanda suka fara shakuwa da Ilham yasan akwai matsala babba ba kad’an ba.
Rasheed na zaune a office nashi shi da Ilham suna hirarsu Imtihaal ta shigo da murmushin ta ,amma tana ganin Ilham ta turnuk’e fuska ta k’arasa ciki rai a dagule duk ta rasa abun da ke mata dad’i. ” precious! Tun d’azu nake so in k’ira ki muka tsaya hira!” Cewar Rasheed kenan. Ba tare da ta saurare shi ba ta d’auki wasu files da ta ke saman table nashi ta fice, ya bita da kallo cike da mamaki, bud’ar bakin Ilham tace ” k’anwar ka kamar bata sona! Yayi murmushi yace ” she’s my best friend” Ilham ta d’an juya ido tace ” oh I see, am sorry! ” ya ce no it’s ok she’s more like a sister to me,kuma ba bata sonki bane ,hala an 6ata mata rai ne, kinga its almost lunch time ,muje mu ci abinci mana” Ilham tayi murmushi ta mik’e suka fita tare.
Tun fitar Imtihaal ta ke kuka har takai office nata ,Sadiq yaga wucewar ta har zai tsokane ta yaga halin da take ciki sai ya fasa ya nufi office din Rasheed ,ganin shi da Ilham ya bashi haushi ,ya juya ya tafi ,Rasheed zai k’ira shi yaga ya juya shiyasa ya kyale shi. Imtihaal ta gama aikace aikacen da zata yi a office ta fice,tana fita a motarta su kuma suna dawowa suka yi ido hud’u da Rasheed amma ta d’auke kai ,abunda bata saba ba. Though abun ya d’aure mashi kai amma ya wuce itama ta wuce. Daidai inda zaiyi parking Sadiq kuma yana mota shima zai fita ,duk da sun had’a ido ,ya ja motarshi ya fice da ya lura cewa Rasheed gurin shi zai zo……………
Wutar d’akin dim light ne kalar blue hakan ya k’ara kyau a d’akin ,Kwance take tana danna laptop nata ,ta kifa ciki a kan pillow ta rungume teddy bear da hannun ta na hagu ,gashin kanta kuwa a kitse yake ya biyo ta wuyanta ,duk da ma ba wani tsayi ne da shi na sosai ba ,saidai ya kusa kirjin ta, hawayen idonta ne ya gangaro ya d’iga a kan wata takarda da ke gaban ta kusa da system din. Tana cikin wannan halin wayarta tayi k’ara, sunan Rasheed da ta gani ne yasa ta ajiye wayar ya kira har kusan sau shida yaji shiru ,kuma tabbas ya san ba bacci take yi ba sai ya hak’ura. Kira na bakwai ta d’aga wayar zata wurga gefe sai ta lura ba Rasheed bane ,K’awarta ne Rukayyah kaxs tana zama Kaduna ,ita kuma ta karanci cosmetology (karatun duk wani abun da ya shafi kwalliya)a London bata ma dad’e da dawowa ba. Imtihaal ta share hawayen fuskarta sannan ta d’aga wayar ,suka sha hirar su Ruky tace mata zata zo Abuja next week, Imtihaal cikin murna sukayi sallama da Ruky kaxs sannan ta kwanta. Rasheed kuwa bayan nan ma yayi ta trying number busy har ya gaji ya bari ,shi Sam ya kasa gane matsalar Imtihaal dat day…….
K’arfe takwas na safe ta fito daga chan nesa ta hango Rasheed da murnan ta ta nufi wajen shi don ta fara surprising nashi saboda yau ne birthday nashi da gudun ta takarasa tana d’aga masa hannu. Rasheed ma ya mik’e yana murmushi ,ya daga hannu yana waving sai da ta k’arasa gurin da yake tsaye kawai taga ashe ba ma ita yake gani ba ,da Ilham yake jiki a sanyaye ta juya da gift din hannun ta ta nufi hanyar gida ,sai Lokacin da ta juya kawai ya ganta ,kafin ya tsayar da ita Ilham ta shiga gaban shi tace ” Happy birthday captain!!! Gami da mik’a masa wani box an yi wrapping. Yayi murmushi yace ” thank you ” Ilham ta kauda kai tana wata murmushi wanda na kasa ganewa munafurci ne ko kuma me????………
Har aka kusa gama celebration na birthday party nashi Imtihaal bata zo ba ,yayi k’iran har ya gaji, tun da Imtihaal ta taso bata tab’a fashin zuwa wani occasion da ya shafe shi ba tun ma bata san ciwon kanta ba ,amma yau kad’ai tayi breaking record. A gajiye suka koma gida shi da Sadiq da Al’amin don shi ma ya zo , Rasheed ya zauna bakin gado yana Kallonsu suna ta hidimomin gaban su, guys ko wani zai fad’a min abun da ke damun My precious!!!? Sai da yayi tambayar har kusan sau uku sannan suka dubi inda yake ma ,Sadiq yayi k’arfin hali yace ” banda abunka Rasheed ina zamu sani tunda duk a tare muke da kai? Al’amin yayi murmushi yace ai se Kaje ka tambayeta lover boy !! Ko ba haka bane??” Duk suka yi kwanciyar su suka kyaleshi a gurin. Yaji zuciyar shi ta kasa danne wa kawai ya sa riganshi ya fice yasan inda zai sameta a wannan lokacin saboda haka ya wuce kai tsaye zuwa wajen da suka saba shan iska ta bayan wani lalataccen motar yak’i ,tun suna yara a nan suka saba zama lokacin zafi ko lokacin wasannin su ,gurin ya zame musu tamkar gida don wataran Imtihaal har bacci take yi a gurin.
Zama Yayi a gefen ta yace” Haba my precious!! Can’t you tell me what wrong I have done to you da zan yi deserving such a punishment? ” wani mahaukacin kallo ta watsa masa ta mike tsaye,ba shiri shima ta mik’e.” Haba don Allah! Yanzu saboda Allah ni nake punishing naka ko kuma kai kake azabtar da zuciya ta ? Tun da ka samu Ilham na zama kamar kashi a gurin ka ,ka yada friendship namu, ka manta da ni , you don’t even come over to say sorry !! Now tell me ,ka fad’a min tsakanina da kai wa yake wahalar da wani ? In da kasan akwai wata wanda matsayin ta zai fi nawa da baka sa ni a ranka yadda zan kasa daurewa ba!!!” Rasheed cikin mamaki ya ce ” Ban fahimce ki ba Imtihaal, what are you trying to say?!!me kuma ya kawo wannan maganar? Imtihaal na zaci mu best friends ne kawai?!!” Cikin hawaye Imtihaal tace ” Best friends kawai!!? Did you know how much I go tru when I see you roaming about with that bloody bitch you call Ilham??!! Did you know how much pain it got me into ??” Rasheed ya daka mata tsawa yace WHY!!WHY DID YOU FEEL THIS WAY IF I ONLY SEE YOU AS MY BEST FRIEND??!!!! cikin razana da k’arfin hali tace “Because I LUV YOU RASHEED!! DATS WHY!!!” Rasheed yayi k’asa ‘kasa da murya ya ce ” am sorry Imtihaal ,ban san yaushe hakan ta faru da ke ba ,koma yaushe ne I can’t lie to you ban d’auke ki a matsayin wata abar ba sai a matsayin abokiya ta wanda muka taso tun yarinta , I am in luv with Ilham na zaci kece ta farko da zaki nuna farin cikin ki akan hakan but sai na samu akasin haka, am sorry Imtihaal bana ganin hakan zai d’aure a tsakanin mu ,pls ki tsaya a limit naki as my best friend. Ko kin manta cewa kikayi kin min alk’awari in dai abu zai sa ni farin ciki toh kece kan gaba a nema min shi? My precious Ilham na d’aya daga cikin su ,I loved her so much am sorry my precious. Yana kai Wannan bata saurari me zai fad’a a gaba ba ta ruga a guje ta yi cikin gida yayinda shi kuma ya bi bayanta da kallo har ta 6ace ,ya juya shima zai koma gida ya ci karo da su Al’amin suma cikin k’walla. Ya wuce su ba tare da ya furta ko kalma d’aya ba ya shige gida. Hannun Sadiq rik’e da wannan takardan da Imtihaal ta dad’e tana bayyana soyayyar ta ga Rasheed a ciki…
Daren nan babu wanda ya runtsa a cikin su, ba ita Imtihaal ba har Rasheed, Sadiq, da kuma Al’amin! Da sassafe Imtihaal ta fita aiki yau, shirin ta de yadda ta saba ne yau kam ko d’an kwallin ma da ta saba sawa bata saka ba ,idon a kod’e ta fito.
Ya kai kusan minti talatin yana tsaye a bakin office nata yana ganin halin da ta ke ciki ,jiya kad’ai amma yau bazaka d’auketa a sisi ba ,k’arasawa ya kasa yi don ya fi so tayi kukan ko zata d’an samu relief, a hankali Sadiq ya fice ya rufo mata k’ofar,shi kanshi ya mugun tausaya wa baiwar Allah, kuma da yana da hali ko ikon sa Rasheed yayi da ya saka ya aureta ko baya so.
Tun daga wannan ranar Rasheed ya daina sa Imtihaal a ido ,duk guraren da yasan zai ganta ma baya samun ta, ta 6angarenshi komai yana tafiya yadda yake so soyayyar su sai ‘kara girma take shida Ilham. Sadiq kuwa baya wani shiga harkarshi sosai balle kuma Al’amin da baya ma gida ya koma aiki……
Tana Kwance a Falo ta k’urawa TV ido duk da ma bata san me suke yi ba don hankalin ta baya jikinta Sam,ta shiga wata duniyar tunanin ta daban, knocking d’in k’ofa da akayi ne ya sa ta dawo hayyacin ta wannan ma har me bugawan ya gaji da bugun, da sauri ta tashi ta bud’e k’ofar tana share d’an hawayen da ke fuskar ta.
Rukey kaxs ce tsaye da y’ar jakar ta a hannu an sha kyau, abunka cosmetologist ta shigo sai azalzalar Imtihaal take yi da masifa Wai ta barta tana ta knocking sai yatsun ta sunyi ciwo. Imtihaal tayi murmushin dole tace my ‘kawas kenan yi hak’uri ban ji ki bane shiyasa ” a take Ruky ta gane Imtihaal is off mood ,Tace “k’awata me ke damun ki ne haka gaba d’aya kin rame kin chanza ,ke matsalata da ke ko dan powder baki san ki shafa ba , bama wannan ba pls tell me me ke damun ki ne??
Imtihaal ta rungume Ruky tana ta kuka sai da tayi mai isarta sannan ta kwashe labarin komai ta fad’a mata ,Ruky ta tausaya mata sosai domin itama shaida ce yadda Imtihaal ke matuk’ar k’aunar Rasheed ,a iya sanin ta kusan shekaru goma yanzu kenan. Ruky tayi murmushi na takaici tace kar ki damu k’awata!! If it is your destiny to Marry Rasheed ko ta wane hali ne zai aureki in kuma ba haka bane babu yadda zakuyi ko da kuwa yana son ki ,amma kafin nan ,ina so ki nuna min wannan Ilham d’in in gani ,zan ga me ya gani tattare da ita da har zai ‘ki ki duk yadda kukai matuk’ar shak’uwa!! Imtihaal ta share hawayen fuskar ta tace yanzu dai my dear tashi Kije kiyi freshening up ,gacan abinci a dining sai kici ki huta kafin magariba tayi. Ruky ta mik’e ta shiga ciki itama duk ranta a dagule don haka kawai jinin su ya had’u da Imtihaal jin ta takeyi kamar yar uwarta na Jini…….
[3/13, 8:52 AM] 🅰 " 🅰 " D🅱⭕Y: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[3/13, 6:56 PM] 🅰 " 🅰 " D🅱⭕Y: 👨✈ *CAPTAIN RASHED* 👨✈
*PART 61~~80*
.
Tafiya suke suna shek’a hirarsu irin ta yaushe gamo ita da Ruky kaxs, suka hango Rasheed tsaye yana waya da ta fuskanci ya hango su har ma ya fara tahowa kawai suka koma suka shige mota, duk ranshi a dagule ya bi motar tasu da kallo cike da mamakin precious d’in shi ,bai yi zaton akwai abunda zai rabasu cikin sauk’i haka ba ,saidai kash!!! Bai san halin da zuciyar ta ta shiga ba dalilin shi ,shi a ganin shi zata yi supporting soyayyar shi da Ilham ta mance da soyayyar ta a gareshi wanda hakan ba mai yiwu wa bane Sam, Rasheed bai san me so yake nufi ba bai kuma iya babanta tsakanin so da kuma k’auna ba!!”
Rukey kaxs tace , Haba ‘kawas ban ga abunda wannan Ilham din ta fiki da shi ba, kyau? Matsayi? Ko kuma me? In ma akwai bai wuce na wanka da take d’auka ba kuma nasan hakan ne zai ja hankalinshi zuwa gareta in ba haka ba menene? Gaskiya dole ki bar irin wannan shigar hauka da kike yi ,ki duba fa ki gani kwata kwata ko d’an gyaran gashin nan ma bakya yi kema ki fita a matsayin ki na mace me class! Ni na tabbata Rasheed na k’aunar ki ,bai iya banbance tsakanin kauna da kuma so ba , da wani ne bazai ma damu ya dinga kiranki duk da bakya d’aga wa kuma in ya ganki ya nufi inda kike ba! Ina tabbatar miki kawai saita mishi zama zamuyi sai ya dawo hankalin shi. Imtihaal tayi murmushi kawai ta shiga d’aki.
Satin Imtihaal d’aya tare da Ruky suka yi shirin tafiya India don attending auren wata friend nasu RASIKA CHANDRA wanda sukayi schl tare a Malaysia da imtihaal duk da ma Ruky bata Santa ba don a London tayi nata karatun amma zata rakata. Suka yi sallama da mutanen gida driver ya kaisu har airport basu wani dad’e ba jirgin Yayi take off sai
Rasheed ya gaji da trying numbern Imtihaal shiru tun yana zaune ya mik’e tsaye daga bisani ya wurgar da wayar ya dafe kanshi, hakan yayi daidai da shigowar Ilham yau itace d’auke da files din da Imtihaal ta saba kawowa,ya dubeta sama da kasa yace ” ina my precious na ganki da files haka?” Tayi murmushi tace En… Bata nan ne ,sun jj eee India dazu suka shine Major yayi assigning d’ina kafin ta dawo don zata kai at least three weeks a can.
Rasheed ya mik’e a fusace yace why won’t my precious even inform me about that?? ” yayi maganar cikin 6acin rai ya karb’i files d’in daga hannun Ilham yace ” pls zaki iya tafiyah gami da nuna mata k’ofa ” cike da mamaki da takaici ta juya ta fita ba musu ta rufo mishi k’ofa . a cikin ranta tace “wato har yanzu bai cire ranshi a kan yarinyan nan ba ko? Amma ba komai na lashi takobi bazan sake na koma ruwa ba har da me tafini da zai wani damu da ita haka ? Kazama da ita!!!:roll:”
Satin su uku a India su Imtihaal suka yi haramar dawowa Nigeria , cikin wadannan satikai kuwa haukacewa ne kad’ai Rasheed bai yi ba ya rasa gane meyasa ya kasa fitar da Imtihaal a zuciyar shi, duk da dai yana son Ilham ne kad’ai,Sadiq de ya zuba mishi ido ne don ya tabbata Rasheed bai san me ake nufi da asalin k’auna ba!!
Taku take irin na k’asaita d’aya bayan d’aya take sauk’owa daga benen takalmin k’afarta blue mai tsini (high heels) designer na Manolo, doguwar rigarta fitted ce na wani hadadden material shima turquoise blue designed by Jimmy choo ,sai purse nata shima design na Manolo, sark’a dankunne, bangles kuma design na Megna ne (wata indian designer) sannan tayi rolling da gyale kalan stones d’in rigar wato dark blue, tana tafe tana y’ar hirarta ita da Kawarta….. Wani kyakkyawan mutum sanye da suite bak’i da rigar ciki kuma fara ce ya d’aura black and white polka dot necktie, hannun shi rik’e da briefcase ya fito daga cikin jirgin shima sai uban sauri yake dokawa ya kara wayar shi a kunne , daidai exit na airport d’in ya ci karo da ita wayar hannun nashi ta fad’i, IMTIHAAL ta juyo da sauri tana cewa “oops!!! Am very sorry sir! Actually I didn’t notice you coming this way ” ta durkusa ta d’auko mishi wayar ta mik’a masa. Ya karb’a cike da murmushi yace ” it’s alright thanks ” Muryar shi ma kad’ai abun sauraro ne. Suka fice daga airport kowa yayi nasa waje.
Abun mamaki shine waje d’aya suka nufa, Ruky kaxs tace “My Frnd kiga wancan mutumin kamar fa biyo mu yayi ,Imtihaal tayi dariya tace ba biyomu yayi ba ga dukkan alamu wani babba ne a nan don naga tag d’in a jikin suit nashi” Ruky tace *Better!!!.
K’afarta ta fara jefowa daga motar, fuskarta ta saka sunglasses saboda rana da ake yi saidai brown colour ne ba bak’i ba, tana fitowa duk kallo ya koma kansu basuyi tsammanin an taru haka ba is like General yana expecting bak’i, kowa neat cikin uniforms tsaro ta ko ina an sa tsaro shi yasa ma bata wani damu ta k’arasa ciki da motan ba suka sauk’a don k’arasawa ciki. Kaf cikin wad’anda suka Santa babu wanda ya gane cewa Imtihaal ne duk kowa ya sake baki don basu tab’a ganin kyau irin Wannan ba. Babban abun mamakin shine even Captain Rasheed doesn’t seem to recognize Imtihaal!!!:oops:.
Ana wata ga wata!!!! Shin waye mutumin da suka yi clash a airport? Is captain Rasheed really captain Rasheed?? And if he is me yasa ya kasa nuna k’auna ga Imtihaal?? This really change the story my dear readers coz this is where the truth unveils!!!!!
Mutumin da suka ci karo a airport da shi bai zame ko ina ba sai inda General (Abbah )yake tsaye suka yi wata maganar su k’asa k’asa sannan mutumin ya yi cikin gidan General d’in wato gidan su Rasheed, yayin da captain Rasheed ma ya bi bayanshi. Major Ahmad Suraj (baban Imtihaal)ya hau stage ga press a gaba ya gama speech nashi ,haka dai suka gama aka watse daga taron kowa yayi nasa guri.
Band’aki ya shiga ya tsaya gaban mirror yana kallon fuskar shi,a hankali yake shafa fuskar yana murmushi domin ya tuna da abun da yafi mishi sauyuwa a zuciyar shi wato Imtihaal, ya gama kallon fuskar shi sannan ya fara yage mask din dake fuskar abun mamaki fuskar babu wanda wanda zai gani yace ba nashi bane ashe na roba ne!!! Dagowan da zaiyi nima Bomboy saida na tsorata domin kuwa babu abunda ya raba shi da captain Rasheed !!! Ya sani cikin zullumi domin masu karatu in baku manta ba captain Rasheed ba yan biyu bane ,sannan bashi da wa balle kani !!!muje zuwa!!………
Imtihaal na zaune a palour tana ganin video na auren da sukaje a India d’in sai dariya take yi,taji an buga k’ofa ,tana lek’a wa taga Captain ne sai ta k’i bud’ewa ta koma tayi zamanta, ya gaji da tsayuwa ya jiya ya tafi duk ranshi a dagule domin kuwa bai san me ya faru ba. Yana tafiya hannun shi rik’e da wani Jan jewelry box mai kyau kawai yaji an ja riganshi ta baya a fusace ya juya yace ” and who the hell are you?!! Cike da mamaki Ilham ta ce “Haba captain!! Yau kuma baka ganeni ba ko? Toh Sannu sarkin zolaya gaskiya Muryar ka ta chanza!!” Rai a 6ace ya daka mata tsawa yace ” look I don’t know who the hell you are ! Just get out of my way!! A firgice ta matsa gefe idanuwan ta suka kad’a sukayi jaa ta bi bayanshi da kallo.
Dakin shi ya shiga ya zauna shiru sai ga Sadiq ya shigo d’akin ba tare da ya kulashi ba ya hau cire kayan jikin shi, Rasheed ya dubeshi yace ” dude Wai nikam my precious bata nan ne? Ko bata dawo daga Malaysia bane?? Sadiq ya juyo cikin sauri ya rungume shi yace ” its you dude!! Ashe kai ne ,yaushe ka dawo ko kira bakayi ba? Duk a lokaci guda yayi maganganun nan. Rasheed yayi wani latest murmushi wanda ya kara fitar masa da kyau yace ” ai numbern ne yak’i shiga kasan Pakistan sai a hankali !! Especially chan Kashmir d’in. Sadiq Yayi darya yace ” abokina am glad you are back don wallahy abubuwa sun kusa dagule wa a nan fa , Duplicate Rasheed din nan yaso ya 6ata rawar shi da tsalle!!!:oops::oops: Rasheed ya mik’e da sauri yace ” me yayi? Imtihaal ta dawo ne?? Ina shi duplicate Rasheed din yake?? Duk a lokaci guda Rasheed yayi tambayoyin. Sadiq ya sauk’e Ajiyar zuciya ya kwashe labarin abunda ya faru tun daga farko har zuwa dawowan Imtihaal da had’uwa duplicate Rasheed da Ilham…………..
Rasheed ya mike a fusace as well very heart broken saboda bai yi tsammanin har duplicate Rasheed din nan zai yi affecting love life nashi ba ,tabbas zuciyarshi tayi bak’i!! Suna cikin haka sai ga duplicate Rasheed ya shigo ,yana faman cire mask na fuskan shi wanda akayi shi mai kama da Rasheed Sak!! Fari ne kam kuma shape na fuskarshi irin na Rasheed ne abunda yasa ma aka za6eshi kenan duk cikin sauran captains domin har tsayin su d’aya ne!! Yana gama cire mask din captain Rasheed ya zuba masa wani uban mari wanda saida yaga wuta a take ya rik’e kuncin shi yana kallon Rasheed. “Am very disappointed in you khaleel!!! Sunan da RASHEED din ainihi ya K’ira duplicate Rasheed da shi kenan. Amana fa na baka ! Just because I trusted you I left you amanar abunda yafi soyuwa a zuciyata ,na zaci zaka nuna mata gata har in dawo sai ka chusa mata tsananin tsanata a zuciyarta! Ka lalata min rayuwa ta!!! Rasheed ya sake chukume kwalar rigar khaleel yace ” kasan Allah in har Imtihaal is not able to forgive the mistakes you have made in my position I am going to teach you a lesson that you will never forget in a hurry!! Ya fadi hakan ne cikin rawar murya idanuwan shi sun ciciko da k’walla jikinshi har rawa yake yi.
Hayaniyar da Inna ta jiyo ne yasa ta hauro sama domin ta duba ko me yake faruwa, a gigice ta k’arasa inda suke ta kama hannun Rasheed wanda da kyar ta iya janye shi daga jikin khaleel tayi waje da shi ,yayin da khaleel ya nemi bakin gado ya zauna sai maida numfashi yake duk jikinshi na rawa ,cikin zuciyar shi yace ” kai Wannan mutumin akwai k’arfin bala’i” yana yi yana shafa gurin da aka shak’e shi……..
“My son! Lafiyar ka kuwa? Yau khaleel d’in kake shak’e wa kamar zaka kashe? Ko kayi hauka ne, mutumin da ya karb’i matsayin ka ya goge duk wani personality nashi don kawai ka je ka gama assignment d’in da ke gaban ka har ma ya kula maka da duk wasu business naka bai yi wa iyayen shi ba shine zaka yi wa haka?? Rasheed bai yi wata wata ba ya kwashe labarin duk abubuwan da khaleel (Duplicate Rasheed)ya aikata ya fad’a mata ,Inna tayi mamaki matuk’a kuma ta san yadda d’anta ya ke k’aunar Imtihaal duk hankalin ta ya tashi domin kuwa tasan akwai matsala babba idan har ya rasa abun da yake k’auna. Tayi shiru jiki a sanyaye shima ya tashi ya mik’e ya fice daga d’akin daidai ana shiga sallar maghrib,tare suka yi sallan da Sadiq suna idarwa bayan sun yi adduoi basu zame ko ina ba sai k’ofar su Imtihaal akayi sa’a house maid d’in ce ta bud’e musu k’ofar ,suka gaisa sannan tace su zauna zata yi magana da Imtihaal d’in. Suna zaune suna jira wajen minti talatin har sun fara cire rai zata ma fito sai gata,saukowa take daga stairs tana danna wayarta, hannun ta yasha henna tattoo (lalle) riga na atamfa dinkin high waist da skirt ne a jikinta tayi dauri irin me step step din nan ,k’afarta slippers ne baki me kyau tabbas sai lokacin yayi recalling cewa da Imtihaal d’in shi suka yi clashing a airport ! Lallai precious d’in shi ta chanja Sam !! She’s so beautiful but yayi missing crazy looks nata:D.
Guri ta nema ta zauna tana k’are musu kallo d’aya bayan d’aya sannan suka gaisa ,ta amsa musu babu yabo ba fallasa. Abun takaici shine duk yadda Rasheed yaso yayi explaining abubuwan da suka faru ,Imtihaal ko sauraron shi bata yi hasalima cewa tayi dama ba son tsakani da Allah yake mata ba ,ta gane kawai yanzun ma don yaga tayi kyau ne shiyasa ya biyota kamar yadda yake bibiyan Ilham!! Ta mik’e ta fice abunta ta barshi a gurin baki a sake.
Jikin a sanyaye ya ajiye wannan jewelry box d’in da ya kawo mata da yamma ta ‘ki bud’e kofar a kan center table suka fice house maid d’in ta rufo k’ofar…….
.
*NAGA KAMAN BAKWASO DON BAKWA COMMENT YANDA YAKAMATA KO MUCANXA NE❓*
[3/13, 6:56 PM] 🅰 " 🅰 " D🅱⭕Y: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[3/14, 6:34 PM] 🅰 " 🅰 " D🅱⭕Y: 👨✈ *CAPTAIN RASHED* 👨✈
*PART 81~~100*
.
Yana Kwance kan gadon shi daga shi sai 3quater trouser sai faman kirga ceiling yake yi ya yi zurfi sosai a cikin tunanin da yake yi ,har Abbah ya shigo ya zauna kusa da shi bai sani ba ,ya ajiye files din hannun shi sannan ya had’a hannun shi da na d’an nasa duk da haka Rasheed bai ko kifta ido ba ya dauko wani glass cup da ruwa a ciki ya zuba mar a fuska. A d’an firgice Rasheed ya tashi ya zauna sannan ya jingina da gadon yana ajiye numfashi sama sama. Abbah ya fara da cewa ” my dear I know you are having hard times tun da ka iso garinnan d’azu ,kuma nasan game da Imtihaal ne coz Sadiq ya fad’amin komai in fact I have spoken with the Major about issue naka da Imtihaal,soon zamu je nema maka auren ta ” Rasheed na jin haka ya zaro ido ya gyara zama. Kafin yace wani abu Abbah ya ce yanzu dai ga wad’annan files din ka duba su don gobe akwai possibility za’a buk’acesu during the meeting kuma akwai issue na wad’annan Sargent guda biyu Ezekiel da simon make sure an gano wanda yayi laifin!!” Abbah yana kai wannan ya nufi kofar fita ,gami da turo masa k’ofar d’akin ,shi dai Rasheed murna fal ransa Imtihaal ta kusa zama mallakin shi.
Yau da ruwan sama mai k’arfin gaske aka tashi tun bayan sallar asubah ,babu wanda ya shirya fita aiki kowa yana Kwance ,Imtihaal na tsaye a saman balcony tana ta mik’a hannu tana wasa da ruwan sama ,sai dariya take yi a haka har kusan k’arfe tara na safe ruwan ya d’auke, garin yayi matuk’ar sanyi ba kamar jiya ba! Bai ma gama d’auke wa ba ta hango Rasheed ya fito da motarshi yayinda mai gadi ya mayar da gate ya rufe shi kuma ya yi parking motar ya fito waje yana waya ,hannun shi guda kuwa yana buga key d’in motar da ke hannun shi. Duk abun da yake yi tana tsaye tana gani, ta tuna da gift d’in da ya ajiye mata jiya a Falo ta ruga ta nufi gurin ta k’urawa box din kallo kafin ta sa hannu ta bud’e. Wani hadadden silver ring ne me dutsen diamond a saman shi da kuma necklace nashi mai matuk’ar kyau ,designed by Michael korrs. A k’asan zoben akwai wani card mai kyaun gaske an rubuta, ” will you marry me? ”
ta dad’e a gurin tana kallon card d’in ashe Ruky kaxs na bayan ta. Ruky ta wafce card d’in ta gudu tana dariya Imtihaal ta bita da gudu itama suka fara zagaye falon tana cewa ” Oooh my Frnd pls ki bani mana !! Ai kuwa bata bata ba sai da ta gama karantawa duk suka zube a kasa tsabar gajiya suna maida numfashi kamar wanda aka sasu gudun dole. Ruky ta mik’e da wuri tace ” k’awata duk da wannan fa ba cewa nayi kiyi giving up so easily ba!! Ki nuna masa baki ma san da zancen ba kuma by the way plan d’in mu zai fara aiki yau, kin san na yarda da Ahmad sosai ,saurayina ne zai iya yin komai for my sake saboda haka zai zama acting boyfriend naki ,har sai Mun tunzira Rasheed dinki ya gane kuskuren shi !! Duk suka bushe da dariya sannan suka cigaba da hirarsu………
Rasheed na zaune a office nashi sai fama yake da computer yana duba files d’in da Abbah ya bashi,jin karar bud’e k’ofar shi da akayi ne yasa ya d’aga kai don ya gane ma idon shi wanda ta shigo…….,………….
Kallon kallo kawai suke ta yi kafin daga bisani ya mik’e tsaye cikin 6acin rai yace ” what the hell did you think you have done!!? Yaya zaki shigo min office ko sallama babu ? Ko kin dauka nan wajene wanda zaki shiga sakaka haka?” Ilham ta gyara murya tana juya manyan idanuwanta ta k’araso gaban table d’in tace ” seriously ka cika zak’ewa d’azu fa muka sha hirarmu da kai a parking lot ,yanzu kuma Kazo kana chanja salo anan nifa gaskiya banason irin Wannan ” Rasheed ya daka mata wani uban tsawa mai tsoratarwa ni kaina saida na girgiza balla ita da take kusa da shi yace ” don’t you dare lie at me!! Yaushe muka hadu da ke?? Kije chan ki nemi sa’an ki kar ki sake sa kafarki a office d’ina in kuma ba haka ba I will definitely ruin your career!! ” Ilham ta bushe da dariya tace ” lallai kuwa zamu ga waye zai yi ruining career na wani a tsakanin ni da kai ta buga table din da hannun ta a fusace ta fice ya bita da kallo yadda take rangwada ya k’ara tabbatar masa cewa y’ar bariki ce wannan ta asali ,shi gashi ko sunanta bai sani ba.
Ya doki table din gabanshi da hannun shi hakan yasa har wasu takardu suka zube, yace ” what kind of life is this!! Shekaran jiya kawai na shigo k’asar amma komai ya cunkushe min, khaleel ya bi son ransa ya rabani da my precious and now all of a sudden ga wata jaka tana son shiga rayuwa ta babu dalili….. ” Duk abunda ya faru a kunnen Imtihaal ne don ta d’auko files zata kawo mishi ne ta hangi Ilham a cikin office din ,taji duk maganganun da yayi, tabbas hakan yayi tallying da maganar da suka so su sanar da ita shida Sadiq!!. Nan ta daskare ta kasa ko motsawa domin yanzu itama tayi believing cewa ba Rasheed bane na farkon ,because of the way he acted towards her!! A ranta tace but wannan ba shi bane zaisa nayi giving up so easily!!! Tayi wata yar murmushi.
Tana cikin wannan yanayi captain ya fito daga office bata ma sani ba saida yayi banging k’ofa sannan ta tsorata ta dawo hayyacin ta ,kamar mai kinkina take magana a lokaci guda tana mik’a masa files din hannun ta, ” gashi wannan shi za’a turawa lieutenant colonel” tana kai wannan ta juya ta barshi a gurin shima da sauri ya bi bayanta ,ta shiga motar ta bai wani damu ba shima ya bud’e ya shiga. Motar ta d’auki silence na wajen mintina biyar ,Rasheed kuwa kawai k’aremata kallo yake yi yadda tayi matuk’ar kyau lallai uniform d’in ya karbeta sosai,ita ma kallon nashi take yi duk sun shagala. Khaleel ya fito kenan yana ta kad’a key d’in motar shi ya hango su ,ranshi a 6ace zuciyan shi na tafarfasa yace ” Oohh!! So this is it !! Ai bana so game din yayi over a nan kusa!! Rasheed ban yi expecting haka da wuri ba amma all the same tunda plan A bai zama accomplished ba lallai plan B zan sako a gaba believe me sai na tarwatsa maka duk wani farin ciki kamar yadda nima na rasa nawa farin cikin!!!! Ya ci gaba da tafiyar shi yana lalumar wayar shi a aljihu………..
Khaleel yana d’aya daga cikin soji masu bincike, aikin shi d’aya da Imtihaal saidai itace babba a gurin sun kuma san amfanin ko wanne irin makami daga k’arfin shi har zuwa weakness nashi da kuma yadda za’a sarrafa shi ,in fact duk wani file na abubuwan gurin yana hannun su ne……
Khaleel yana da k’anwar shi mai suna Husnah ,kuma asalin haifaffun garin Kaduna ne ,transfer akayi mishi aka dawo da shi Abuja saboda kwazon shi kuma da kaifin basira ya karb’i lambobin yabo da dama, shi da imtihaal. A dalilin Imtihaal suka shaqu da Rasheed har suka zama friends. Husnah k’anwar khaleel tana matuk’ar k’aunar Rasheed yayinda shi kuwa Rasheed bai d’auketa a karan komai ba face k’anwa ,khaleel kad’ai ya san haka…
Wani lokaci kimanin shekaru uku da suka wuce khaleel ya umarci Husnah da ta bayyana sonta ga Rasheed kuma ta yarda, ta samesu zaune shida Al’amin suna hirar Imtihaal sai ta ‘boye a bayan wani pillar tana jin su. A nan ne hankalin ta ya tashi domin kuwa Rasheed ya bayyana irin son da yake wa Imtihaal kuma yanda ya bayyana ta tabbatar babu abunda zai iya shiga tsakanin soyayyar shi da ita bai kar shi ba!:oops:ko Al’amin ma kasa cewa komai yayi don yasan yadda zuciyar Rasheed take in har aka tab’a abun da ya riga da ya shiga ranshi!!
Husnah ta ruga a guje ta nufi gida ,khaleel na zaune ta wuce shi da gudu tana kuka bata zame ko ina ba sai cikin d’akin ta ,ta rufe , khaleel yayi yayi ta bud’e tak’i bud’ewa hankalin shi ya tashi.
A bakin k’ofar ya kwana har gari ya waye yana tashi kamar zai bud’e kofan kuma sai ya fasa yayi tunanin bacci take yi ma ,sai ya wuce masallaci ,kusan k’arfe bakwai ya shirya zai fita sai ya gwada murd’a door handle din kawai kofar ta bud’e………
Tunda yake bai tab’a shiga tashin hankali irin na ranan ba , a gurin ya durk’usa jikinshi na rawa kamar mazari ,yana hawaye da kuka mai sauti na ban tausayi ,ya d’aga kanshi yana kallon ta Kwance bakinta duk Jini har ta hanci ga kumfa ,wasu kananan magunguna a zube a k’asa hannunta guda ta damk’e wata paper ,ya d’aura kanta a cin yarshi yana hawaye yana karanta abunda ta rubuta.
Mikewa yayi tsaye idanuwan shi duk sun kad’a sun yi jajir ya damk’e paper d’in yana ambaton sunan Rasheed har wajen sau uku sannan ya fice daga d’akin ,dama basuda kowa sai k’anwar baban su itama tana cikin gari don tayi aure ,anan akayi janaiza ,khaleel tun daga wannan ranar ya dauki alkawarin sai ya zubar wa Rasheed hawaye domin dalilin shi kanwarshi ta hallaka kanta kuma ita ce Hasken idanuwan shi a rayuwa bashida abunda ke saka shi farin ciki irin Husnah.. Amma kuma cikin ruwan sanyi ya yi niyyar yi.
Wannan yasa lokacin da Rasheed zai yi tafiya zuwa Pakistan General Abubakar Rasheed ya zabi khaleel yayi shige irin na Rasheed domin kar a yi suspecting wani abu a base ,saboda shima Rasheed da wata fuska zai shiga Pakistan din ,mission din ba karami bane , khaleel ya ji dadi da jin haka yana ga kamar wannan shine step na farko da zai fara amfani da shi don rusa farin cikin Rasheed, kafin ya tafi kuma babu wani day to day activity na Rasheed da khaleel bai sani ba ,domin dole ne yayi acting as Rasheed, harta lokacin da Rasheed ke waya da Imtihaal an sanar da shi ,da duk wasu abubuwan da ya kamata ya sani tunda shi basajan Rasheed ne!!…..
Zuwan Ilham ya ‘kara masa k’arfin guwiwa na tarwatsa soyayyar Rasheed da Imtihaal!!
Wannan kenan
Imtihaal ta murd’a key d’in motar ta fice a d’ari ,shi kuwa Rasheed na zaune yanda yake yana kallonta bata fasa gudun ba kuma ba hanyar da ya kamata subi ta bi da su ba , da yaga abun natan na yi ne sai ya ce ” park d damn car Imtihaal ko so kike ki hallaka mu ne?bata bi ta kanshi ba ,direct wani city Hall ta wuce da shi shi de bai yi magana ba tun daga wancan maganar ta bud’e kofa ta fice shima hakan yayi ya bi bayanta though bata umarce shi da ya yi hakan ba…..
Hall d’in cike yake da sojoji wad’anda ake damawa da su a Army wasu ma bak’i ne daga Niger ,totally Rasheed ya manta da za’a yi taron tuni ya fara Sosa ‘keya Imtihaal ta juyo sai dariya take masa ,da iPad d’in hannun ta ta bugi kafad’ar shi sannan ta wuce ciki ta barshi nan a tsaye ranshi fal farin ciki yau abunda yafi soyuwa a zuciyar shi ta yi managing to forgive him sannan ya wuce ciki.
Major Ali wato mahaifin Imtihaal ya ji dad’in ganin reunion d’in y’arsa da Rasheed domin kuwa babu abunda ke burgeshi irin yaga y’ar shi cikin farin ciki kasancewar ta marainiya , bata samu motherly love ba sai daga gurin mahaifiyar Rasheed abunda ya sake ‘kara musu shakuwa kenan, ta kula da ita ta kuma tarbiyyantar da ita bisa tafarki na addini ,ita dai matsalar Imtihaal dama chan a fannin dressing ne da makeup shine kad’ai Inna ta kasa gyara mata don in tayi kokarin yi to bazasu wanye lafiya ba. General ma ya ji dad’in ganin hakan ba kad’an ba.
Kowa ya ci yasha ana ta murna amma banda khaleel da ke zaune yana kallon su ,yayinda ganin shima yana cikin damuwa kamar yadda take ciki yasa Ilham itama ta yi joining nashi, suka d’an fara hira. “Amma Muryar ka seems familiar ! Kamar na tab’a jin Muryar ka at several occasions gashi kuma sai yau na tab’a ganin ka” abunda Ilham ta Fadawa khaleel kenan. Murmushi kawai yayi ba tare da ya amsa ba ya d’auki glass cup yayi sipping sannan ya maida kallon shi ga su Imtihaal. Cikin ranshi yace ” Celebrate all you want !! Day will come that your laughter will turn to streams of hot tears!!!!
0 comments:
Post a Comment