👠 SATAR FITA💃🏼
mayafinta ta zara da jakarta tai gaba sai a waje ma sannan ta samu ta dauraye fuskarta dan batai sallah ba.
A bakin titi ta kira Aysha tana tambayarta ko lpy? Kedai bari yanxu gida zanje zumuyi magana idan na samu nutsuwa.
Kada ki kuskura malama!ki zarto gidana direct dan bakisan qurar da kika tadawa kanki ba. Dafe qirji hindatu tai cikeda firgici tana fadin meya faru? Oho miki zakiyi bayani ne ra fada tana kashe wayar.
Saida hindatu ta samu nutsuwa sannan ta fara bawa Aysha labarin abunda ya faru. Gyada kai kawai Aysha takeyi tana jimanta halin hindatu, can kuma tace Hindu dan Allah ki gyara halinki wallahi satar fitar nan batada wani amfani,ina guje miki fadawa matsala.
Ba wata matsala indo kedai kawai ki rabu dani, barin hali sai mutuwa, Indai baza'a daina matseni ba nima bazan daina SATAR FITA ba,haba mutum da girmanshi!
Tsaki Aysha ta saki tana fadin sannu hajiya babbah,ni muje na kaiki gida ki musu bayani acan ta fada tana wucewa gaba.
Kallon Arziqi hindatu bata samu daga gurin umma ba balle baffa,sai nan nan sukeyi da Aysha ganin cikinta ya tsufa,Aysha tanata qoqarin nunawa hindatu ta bada haquri amma taqiya, saida aka kusa 1 wk sannan ta samu sakewa a gidan.
NOTE-
Fans! Inaso nayi anfani da wannan page din nayi explaining wani abu.
Sosae nakejin dadin yadda wannan novel din ya karbu a gurin jama'a har Mutane suketa nemansa haka,ni kaina banyi expecting hakan ba,amma matsalar shine, yawan mutanen dasuke yimin mgn a facebook ko whatsapp akan na dinga turo musu SATAR FITA ta private,gaskiya abune mai kamar wuya,bawai typing novel kawai nakeyi a social media ba,inada abubuwa da dama da nakeyi shiyasa hakan bazai yiwu ba,ku qaramin haquri dan Allah ni bana ajje novel a wayana,idan na sakeshi shikenan saidai na nema nima kaina Idan inaso,banda blog,page kokuma whatsapp grp dazan riqa tara novel, sai kuma masu cewa I'm very slow kuma pages din danake yi sunyi kadan,nima da kaina nasan hakan kuma ina
[21/04, 22:26] Hassan India: Miss collapse
(75)
👠 SATAR FITA💃🏼
Gaskiya da zafi wlh,hindatu ta fada tana dan shafa jelar kitson da Aysha tai mata, amma ae yayi kyau koh, dubi yadda kikai kyau kamar bake ba, mace dake amma sai qyuiyar kitso.
Bugun qofar da sukaji ne yasa hindatu miqewa taje ta bude qofar, da wani dan saurayi sukai kicibis ya gaidata, Amsawa tai tana masa kallon rashin sani yace hajiya sa'ad ne ya aikoni yace ta kawo miki wannan ya fada tareda janyo trolley a bayansa. Tsaidashi hindatu tae ta qwalawa Aysha kira.
A gajiye Ayshan ta tako bakin qofar, gaisawa suka sakeyi da saurayin ya maimata mata saqon, godiya tayi masa tace ya tsaya, kudi taje ta dauko masu kauri ta bashi ya tafi yana godiya.
Bubbude kayan suka farayi,tsadaddun kayane unisex na jarirai masu baleen kyau kala2, rasa bakin mgn Aysha tai, sae ta sungumi wayarta ta bugawa sa'ad din kira, godiya ta fara zuba masa kamar bazata daina ba cikeda qosawa yace plx banason yawan godiya just take care of yourself ya qarashe tareda katse wayar.
Tabe baki Aysha tayi ta zauna tana fadin mutum a rayuwarsa ba'a masa gwaninta,hindatu dake maida kayan tace lpy?
Uhm nida ya sa'ad ne wlh,waifa dan na kirashi na masa godiya shine ya gwaleni,ni ina mamakin rayuwarsa wlhy, shiyasa har yanzu ya kasa yin aure.
Kwabe fuska hindatu tai tace me kike nufi?
Uhm kinga fa babu irin fadan da ummy bata masa akan y samu mata yayi aure amma yaqi,mutum shekara 30 da dauriya yanxu idan akae masa mgnr aure sae yace bashida tym ko baiga wadda tai masa ba.
Babu mamaki hakan ne, hindatu ta fada tana gyara mayafinta ta qara da cewa nifa wlh har yanxu ban sanshi ba dukda zuwan x nky gurin ummy.
An dai ji kunya, aysha ta fada tana gyara kwanciyarta ita kuma hindatu ta fice.
*** *** ***
Baffa na zaune a falonsa shida babban aminin nasa daya kawo masa ziyarar bazata,sosae baffa yaji dadin ganinsa umma nata hidimar hada musu abun tabawa tunda hindatu bata nan sukaji qarar bude qofa, fitowa umma tae tana kallon matashiyar
[21/04, 22:27] Hassan India: Miss collapse
(76)
👠 SATAR FITA💃🏽
matashiyar data shigo gidan, fuskarta a matuqar daure take kallon umma dasu baffa tana harare2, Sannu baiwar Allah,saedai bamu ganeki ba cewar umma dake tsaye a gefe.
Eh nasan baki ganeni ba daman,amma ae karuwar erki ta sanni.
Bude baki sukayi gaba1 suna kallonta cikin mamaki,Abba yace keh yarinya koh babu tarbiyya a gidanku ne da zakizo kina fadawa Mutane zancen banxa a gida!
Tsaki jamila taja sannan ta tabe baki tace wannan kuma kai ta shafa! Ko da yake ba'a yaron banxa sai anyi dattijon banza da Alama Kaine ubanta!
Cikin fusatuwa Alh.sadauki ya miqe baffa yai saurin dafe masa kafada yace keh baiwar Allah meke tafe dake kuma keh wacece da zakizo har gida ki nemi ki tayarwa da mutane hankali!
Gyara tsayuwa jamila tae tace sunana jamila mijina kuma Ibrahim,naxo nan Saboda inaso na baku shawara akan diyarku hindatu ta fita a harkar mijina dan mijina ba lalatacce bane itace ta lalatashi,tana daukansa suna yawo hotel2 a fadin garin nan,kwanaki dana kamasu nai mata gargadi amma da Alama bataji ba,to wlh idan na qara ganinta da mijina saena illata ta idanma ban kasheta ba.
Taya zamu tabbatar da cewa wannan ba labari ne kika shirya ba Saboda ki bata mata suna!
Hannu tasa cikin Jakarta ta zaro wani dogon envelope ta miqawa umma dake gefenta ta fice kamar zata tashi sama.
Da sauri umman ta miqa hannunta ta zari envelope din ta fara budewa! Innalillahi wa inna ilaihi rajiuun kawai ta fara maimatawa,cikin azama Allah sadauki yasa hannu ya amshi pictures din,A fili yake fadin wa'iyazubillah! Kafin ya sake magana sukaji qarar faduwar umma luuuuu a qasa.
Shigowar hindatu layinsu taga motar mai tinted glasses tayo kanta a guje,da sauri ta matsa gudun kada mai motar ya illata ta tabi motar da kallon Rashin sani harta qule. Tsaki taja ta wucewarta, hankali kwance ta tura qofar gidansu ta shiga.....
[21/04, 22:27] Hassan India: Miss collapse
(76)
👠 SATAR FITA💃🏽
Bin motar dake ajje s parking space tae,ta tabbata bata gidansu bace,babu mamaki baqi akayi ta fada tana wucewa har ta kusa bakin qofa abba ya fito daga gani hankalinsa a tashe yake ya fara yiwa drivern sa magana y fito da mota,Hakan kurin gaban hindatu ya Yanke ya fadi, xataiwa abban magana taga baffa ya fito dauke da umma a kafadarsa,a kidime ta fara tambayar kanta meya Sami umma amma,kafin ta dawo daga duniyar tunanin data tafi taji qara ficewar motar a guje daga compound din gidansu,itama a guje ta fita,a sa'arta ta samu mai adaidaita tace yabi motar Abba.
Ita kanta batasan nawa ta bawa mai keke nepep din ba ta fada asibitin tabi bayansu, emergency ward ne suka karbi umma,suna shiga ciki da ita hindatu na qarasowa, hankali a tashe take duban iyayen nata 2, Abba ta tsaye,kokuma nace yana safa d marwa a bakin dakin shikuma baffa na zauna ya hada kai da gwiwa,ya rasa abunda yake damunsa, baffah meya samu ummanahh... Maganar hindatu ta katsesu duka, dagowa baffa yayi ya sauke jajayen idanuwansa a kanta, wani irin baqinciki ya tokare masa zuciya har baisan sanda ya kifeta da wani gigitaccen Mari ba. A tsorace ta dafe gefen fuskarta har xuwa lokaci batajin magana sosae, rai a bace baffa yace wallahi hindatu duk abunda ya sami Amina kiyi kuka da kanki,nayi danasanin haifar ya' irinki,kin lalata rayuwarki kin cucemu kin kuma cuci kanki, ashe har akwai ranar da zatazo da zakiyi fatali da tarbiyyar da muka bakii,ash..... Alh Bashir ya isa haka,Abba ya katseshi da sauri,kome zaka fada k bari idan mun koma gida amma anan zaka karkato hankulan mutane kuma ka tonawa kanka asiri.
Wani asiri ya rage bai tonuba sadauki!ae hindatu ta gama kwancemin xani a kasuwa kuma saeta gane kuskurenta.
Gajeran tsaki Alh. Sadauki yayi sannan yace kinga hindatu maxa jeki gida,ki taya mamanki d adduah Allah ya bata Lpy.
Hindatu dake tsaye kamar dutse ta bishi da ido,har izuwa yanxu ta kasa fahimtar abunda suke nufi, to me nayi da baffa xae
[21/04, 22:27] Hassan India: Miss collapse
(78)
👠 SATAR FITA💃🏽
to me nayi da baffa xae dinga fadamin maganganu kamar wani zararre...
Muryar baffan ce ta katseta dayace wani gidan zata tafi sadauki! Badai gidana ba dan wlh gidana yafi qarfinta,ba mafakar en iska bace,taje can gidan shi dan iskan yaron data saba xuwa.
Habaa Bashir! Wai meyasa kake abune kamar yaro, ka bari aji ta bakinta mana idan yaso sai a yanke hukunci.
Sai kayi sadauki,wlh idan yarinyar nan ta taka qafarta a gidana saina tsine mata Albarka.
Subhanallah.... Allah Bashir kodai ka zare ne? Wannan kuma kai ta shafa baffa ya amsa yana gallawa hindatu wata harara data kada mata hanjin ciki.
Janta Alh. Sadauki yayi har bakin motarsa yace drivern shi ya kaita gidansa. Hindatu ta jikinta yayi sanyi ta kalli Alh.sadaukin tace Abba wai meya samu umma da baffa ne,dazu na fita na barsu Lpy lau yanxu kuma na dawo naji konace naga abu daban.
Murmushin qarfin hali abban yayi yace karki damu hindatu kije gida ki huta, ummanki faduwa tai amma ni kaina bansan meya samu baffanki ba,ki kwanta da hankalinki everything will b alright! Ya fada yana dan dafa mata kafada.
Jiki a sanyaye ta shiga motar, duk irin sanyi da qamshin dake tattare da motar bai hana hankalin hindatu tashi ba, to meya faru? Shine tambayar datake ta maimaitawa kanta har drivern yayi parking batasan sun qaraso ba saida drivern ya fito ya bude mata motar sannan ta dawo hayyacinta, jiki a sanyaye ta fito. Ummi dake shirin fita ma turus tai ta tsaya dan ganin hindatu ta fito daga motar mijinta, bugawa kawai zuciyarta takeyi ta gaza samun nutsuwa tana jiran fitowar mijin nata amma maimakon hakama sai gani tai drivern ya finciki mota ya sake ficewa.
Adan gigice ummin ta dire Jakarta a saman booth din mota ta qaraso kusa da hindatun tana fadin lafiya dai hinduuu na ganki a yanayin daban saba ganinki ba.... Maimakon amsa kuwa sai hindatu ta fashe da kuka mai sauti ta rungume ummyn, wannan ya tayar da duk wani abu mai suna hankali dake jikin ummyn ta fara
[21/04, 22:28] Hassan India: Miss collapse
(79)
👠 SATAR FITA💃🏽
rungume ummyn, wannan ya tayar da duk wani abu mai suna hankali dake jikin ummyn ta fara girgiza hindatun tana fadin hindatu meya faru... Waya rasu ki fadamin dan Allah ki daina kukah.. kimin bayani hindatu Aysha ce ta rasu... Daqyar hindatu ta girgiza kanta tace ummace.....
Hajiya Aminan ce ta rasu? Ummy ta tambayeta a matuqar razane,nan ma girgiza kanta tayi wannan yadan kwantar da hankalin ummyn tace to meya faru hindatu kimin bayani mana. Hawaye ta share da bayan hannunta tareda Jan majina tace umma ce batada lpy kuma bansan meya sami baffa ba sae zagina yakeyi harda cewa zai tsinemin.. cikin rashin fahimta ummy tace meya samu umman?
Wlh ummy ban saniba,dawowata kenan daga gidan Aysha, inaxuwa na tarar da tashin hankalin.
Dan dafa kafadarta ummyn tayi tace kidan kwantar da hankalinki hindatu,ae wannan ba wani babban abu bane,babu mamaki baffan naki Yana cikin shock ne,yanxu ki shiga ki huta ni bari naje na samesu, kikace suna asibitin nassarawa koh? Gyada kai hindatu tai tareda cewa zan biki ummy... Aah hindatu ki shiga ki huta dai,nida kaina zanje naji matsalar.
Cikin mintuna qalilan ummy ta isa harabar asibitin,Abba ne yae mata kwatancen dakin ta qarasa, izuwa lokacin an samu jinin umma yadan sauka tunda dama doctors sunce jininta ne yahau sanadin tashin hankalin data shiga,saedai har lokacin bata farfado ba. A gefen gadon ummy ta zauna tana tambayar baffa ya jiki, daqyar ya iya amsa mata, wai yaya meya faru ne, dazun nan mukai waya da Aminan kuma garau najita,yanxu kuma sai naji sabon labari gurin hindatu.
Bayan hannu baffa yasa yana share hawayensa,cikin mamaki ummy ta miqe ta qarasa kusa dashi tareda dafa kafadunsa tace yaya meya faru kuma kake kuka?
Ruma kinga, dan Allah kibar mana wadannan tambayoyin naki,zamuyi maganar amma ba yanxu ba sai a gida, nan asibiti ne.
Ajiyar zuciya ummyn ta saki cike dason jin abunda ya faru sannan ta koma mazauninta.
Qarfe 11:14 umma ta farka daga dogon baccin
[21/04, 22:28] Hassan India: Miss collapse
(80)
👠 SATAR FITA💃🏽
Qarfe 11:14 umma ta farka daga dogon baccin datasha, wannan karon ummy ce da baffa zaune a kusa da ita dan Alh. Sadauki ya tafi, gwaje2 baffa ya kira doctor yayi mata ya tabbatar da cewa jinin ya sauka, xuwa gobe za'a iya sallamarta amma yace ta tabbata ta nisantar da kanta daga duk wata damuwa.
Kuka sosae umman ta fashe dashi mai tsuma zuciya, ummy ce ta rungumeta tana dan bubbuga bayanta dukda batasan abunda ya faru ba amma ta tausayawa haj. Amina, daqyar ta lallashe tai shiru, itace ta kwanar mata dan baffa ma tafiya yayi bayan ya gargadi ummyn akan ta rufe zancen rashin lafiyar umman karta fadawa kowa.
Daren ranar babu wanda ya samu baccin kirki tsakanin hindatu da iyayen nata, kowa da abunda yake saqawa har garin Allah ya waye. A tunanin hindatun ya dace tayiwa mahaifiyarta abinci takai mata asibiti,dukda kuwa batada tabbacin ko an sallameta ko ba'a,sallameta ba. Breakfast mai rai da lpy ta hada tazuba a kula, drivern ummy ne ya kaita asibitin, da kwatance ta gane dakin ta qarasa a sanyaye ta bude qofa.
Ido hudu sukayi da umma tanashan tea, qwarewa mai qarfi tayi, tana tari nan danan idanuwanta suka sauya colour xuwa red, da sauri ta qarasa cikin dakin bayan ta ajje kular hannunta da niyyar riqe umma amma kafin ta qarasa baffa ya daka mata wata muguwar tsawa.
Birki taja tana kallon baffa,haka kuma hankalin ummy ya dawo kansa,fita daga nan dakin hindatu banaso na sake ganinki a gaban idona. Cikin rawar murya ummy tace wai yaya meyake faruwa ne? Ba ruwanki Ruma,ki rabu da wannan yarinyar,tafi kowa sanin abunda ta aikata,itace maqasudin shigar Amina halinda take ciki, Allah kadai yayi da nisan shan ruwanta.
Hawaye masu zafine suka shiga zarya akan kumatun umma, kallonta ummy tai zatai magana taji umman tace hindatu ki tafi ki bani guri,banida buqatar ganinki wlh, a halin yanxu tantamar kasancewa mahaifiyarki nakeyi.
Amina da Allah kibar wannan zancen,idan rai ya baci mai kamata hankali ya gushe ba.
[21/04, 22:28] Hassan India: Miss collapse
(81)
👠 SATAR FITA💃
Amina da Allah kibar wannan zancen,idan rai ya baci mai kamata hankali ya gushe ba.
Zatai magana kenan doctor ya shigo, bata rai yayi yace Amma kunsan saida nace muku ciwonta baison damuwa koh? Yanxu kuma tun ba'aje ko ina b harta fara koke2.
Harara baffa ya gallawa hindatu ta miqe kamar kaxar da qwai ya fashewa ta fice, ran ummy a bace tabi bayanta suka shige mota, kuka hindatu takeyi a hankali amma mai tsuma rai,harga Allah batasan abunda ta aikata ba,amma tasan lallai abun mai girma ne tunda har baffa d ummanta suka nisanceta haka, daqyar ummy ta lallasheta tayi shiru, a harabar gidan sukaci karo da motar Adams ya kawo Aysha.
Hindatu ki saita kanki banaso en uwanki su fahimci abunda kike ciki. Gyada kai hindatun tayi har sukai parking. Fitowa sukai su biyun,Aysha da Adam suka bisu da kallon mamakin ganin hindatu da sassafen nan, qarasawa sukai suna gaisa umma,amma a zahiri hankulansu yana kan hindatu dake qwawulo murmushin yaqe,fahimtar hakan ummy tai tadan gimtse fuska tace: meya kawoku nan da sassafe kuma?
Dukkansu tambayar tamusu bambarakwai amma dukda haka sae Adam ya dake yace ummy dama Aysha na kawo saboda yau zan dade a office,akwai ayyuka dayawa da zanyi kuma kinga ba'aso abar mace ta tsohon ciki ita kadai.
Hakane Adam,amma yanxu muma fita zamuyi,zamuje can katsina muga er uwarka, gara ka kaita gurin yayanka ishaq.
Aa ummy bari na kaita gurin umma kawai. Da sauri ummyn ta katseshi ta hanyar cewa a'ah ae harda aminan zamu tafi,yanxuma ita muke jira, maxa kai matarka gidan ishaq ta fada tareda jan hannun hindatu sukai ciki.
Kallon2 sukabi juna dashi sannan suka koma motar,zuciyoyinsu sun kasa yadda da abunda ummyn ta fada musu musamman Aysha data karancesu gaba1.
A babban falon abba suka yada xango, yana zaune yana Karanta jarida amma tv a kunne take,kuma ga dukkan Alamu hankalinsa baya kan duk abubuwa biyun. Remote umma tasa ta kashe tv sannan ta fara yiwa abban magana, adan firgice ya kalleta
[21/04, 22:29] Hassan India: Miss collapse
(82)
👠 SATAR FITA💃
Remote umma tasa ta kashe tv sannan ta fara yiwa abban magana, adan firgice ya kalleta,hakan ya qara tabbatar mata da cewa shi kansa yana dauke da damuwa. Gaisawa sukai dashi suka kuma gaisa da hindatu, ya amsa ba yabo ba fallasa. Yallabai a kawo maka breakfast ne? Ummy ta tambaya tana kallonsa. No dear,ba yanxu ba nasha coffee ya fada yana nuna mata cup din dake gefen qafarsa.
Ajiyar zuciya ummyn ta sauke sannan tace yallabai tambaya mukazo da ita,har yanxu hankulanmu sun gaza kwanciya, mun kasa gane laifin mai Hindu tayi da iyayenta da suka haifeta zasu wofantar da ita.
Girgixa qafa abban yayi a hankali sannan yace hindatu tashi ki bamu guri zamuyi magana da mamanki.
Aa yallabai,kome zaka fada ka fadeshi kawai a gabanta,gara tasan laifinta tunda wuri,dubi yadda yarinya ta kode a cikin Kwana 1.
Gyara zama abban yayi ya dago yana kallon hindatu datai qasa da kanta yace hindatu wacece jamilah matar Ibrahim??
A razane hindatu ta dago tana kallon Abban daya kafeta da idanuwa,so take ta tambayeshi meye alaqar jamila da matsalar datake ciki amma bataga fuska ba, to a ina ma Abban yasan jamila?
Dake nake hindatu,Abba y fada yana qara gyara zamansa.
Eh nasanta Abba,amma meye alaqarta da matsalata.
Meye alaqarki da ita hindatu? Meye dangantakarku?
Shiru hindatu tai tana tunanin ta yadda zata amsawa abba wannan tambayar tashi taji umma tace, hindatu ki saki ranki kimana bayana please.
Qasa tayi da kanta sannan tace Abba banida wata alaqa da ita,amma muna mutunci sosae da mijinta,a tunaninta soyayya mukeyi shine taketa nemana da fada.
Iya dangantakar kenan? Abban y tambaya cikeda shakka.
Eh Abba, iya alaqarmu kenan.
Gyada kai Abba yai ya kalli ummy yace, ruma tashi kije dakina ki duba qasan pillow na zakiga wani envelope ki daukomin.
Ba bata lokaci ummy ta kawo,alamu yae mata ta miqawa Hindu envelope din yace ta bude. Ta rasa dalilin dayasa zuciyarta ke bugawa, a hankali ta bude,zaro pic din farko tayi
[21/04, 22:29] Hassan India: Miss collapse
(83)
👠 SATAR FITA💃
A matuqar razane ta miqe tsaye, pic enta ne tsirara da ita da Ibrahim suna kwance akan gado. Gumi ne y fara karyo mata tako ina, salati kawai takeyi da hirji. Ummy da batasan meyake faruwa ba itama hannu tasa ta fara duba picx en, Sam kasa magana tayi ta kuma kasa motsi.... bata tsammaci haka daga gun hindatu ba.
Muryar Abba ce ta katseta dayace kimin bayani akan wannan pic en, su waye a jiki?
Daqyar hindatu ta iya duqawa qasa hannunta riqe da pic din tace Abba! Wallahi bansan komae akan pic dinnan ba, wlh bani bace.
Karki yimin qarya hindatu, bazaki rainamin hankali ba, waye a jiki idan bake b?
Abba wlh ka yarda dani,bansan komae akan pic dinnan b, wlh bani bace....
A fusace Abba ya miqe dan a ganinsa ya gaji da rainin hankalin da hindatu keyi masa.
Juyowa tayi tana kallon ummy sannan tace ummy ki yadda dani wlhy bani bace.
Bazan iya yadda dakeba hindatu,saedai idan kika fito da wata qwaqwqwarar hujja da zata tabbatar da hakan. Bata qara cewa komai ba tabar falon.
Kafin yamma idanuwan hindatu sunyi suntum tsabar kuka, a haka Aysha tazo ta sameta, ita kanta Aysha ta gigita dataga picx din, amma ko kusa bata zargi hindatu ba,ta tabbatar da cewa sharrin jamila ne.
Lallai jamila takae maqura wajen hada makirci, dahar ta iya hado picx din nan, amma kiyi haquri hindatu da kaina zanje har gida na sameta,ya zama wajibi gareta tazo ta warware mana wannan qullalliyar domin samun kwanciyar hankalinmu gaba1.
Amma tayaya kike tunanin hakan zai faru? Hindu ta tambaya tana jan majina.
Ki kwantar da hankalinki,ko tayaya zanyi saena samo mn solution, lallashin hindatu ta dingayi har dare sannan ta koma gida.
Juye2 kawai Aysha keyi, duk tunaninta bai wuce yadda zatae ta tona asirin jamila ba amma brain dinta ya cushe,a haka Adam y farka y ganta. Dan janyota yayi jikinsa yace honey kinsan fa babu kyau mai ciki ta dinga yawan tunani,hatsarina ga lafiyarta da kuma danta. Ki fadamun meye damuwarki.
[21/04, 22:29] Hassan India: Miss collapse
(84)
👠 SATAR FITA💃
A fusace Abba ya miqe dan a ganinsa ya gaji da rainin hankalin da hindatu keyi m
Lumshe idonta tayi ta qara gyara kwanciyarta a saman qirjinsa tace ya Adam hindatu cee, tana cikin babbar matsalaa.
Wata matsalace zata hanaki bacci haka?
A kasalance ta miqe daga jikinsa ta gyara zamanta akan gadon ta fara bashi labari.
Kallon picz din Adam yayi yace amma ke kin tabbata wannan ba hindatu bace?
Na tabbata honey,wannan ba jikin hindatu bane fuskarta ce amma, wannan qulalliyar jamila ce.Honey nasan hindatu fiye da kowa ni aminiyarta ce, samm hindatu batada irin wannan mummunan halin, duk abunda zata fada wlh a baki ne amma bazata aikata haka b.
To yanzu ya za'ai? Adam y tambayi Aysha cikin rashin madafa.
Tunani nky naje n samu jamilar har gidanta na roqeta taje ta kwance wannan chakwakiyar tareda alqawarin babu Hindu ba mijinta.
Kina ganin zata yadda kuwa?
Idan taqi yadda zan hadata da mijinta yayi mata magana domin wannan wasa ne da qima da darajar hindatu nikuma bazan lamunta ba.
Murmushi Adam yae har haqoransa suka bayyana yana sake godewa Allah bisa kyautar aysha daya bashi a matsayin mata.
Next day-washegari....
Daidai qofar gidan Ibrahim Adam ya parking motarsa,tare suka fito da Aysha, jikin gate din gidan ta qarasa fara qoqarin bugawa, wasu samari dake zauna a gefen gidan nan sukace haj. Masu gidan nan fa basa nan.
Basanan? Aysha ta tambaya cikin takaici.
Eh,hajiya kusan kwana 2 kenan.
A sanyaye aysha ta kalli Adam sannan suka kalli bangaren d samarin suke,Adam yace ina sukaje?
Wani daga cikinsu yace, eh,shi Alh.Ibrahim din ne y tafi qaro karatu saeya tafi da matarsa amma gaskiya na manta sunan qasar d sukaje.
Cikin karaya Aysha tace innanillahi yanxu ya kenan?
Godiya Adam yayi musu yaja hannu Aysha suka koma mota. Gaba1 hankalin Aysha bai kwanta ba ta rasa yadda xatayi,can tace honey ko muje office dinsu Ibrahim din kokuma gidansu jamilah ni wlh bansan ya zanyi b.
Kingane koh Aysha....
[21/04, 22:29] Hassan India: Miss collapse
(85)
👠 SATAR FITA💃
Kingane koh Aysha,ki rabu da zuwa wasu gurare ku kuma godewa Allah tunda jamila bata zabi watsa picz en nan a social media ba,kinsan yanxu mutane qiris suke jira,a ganina wannan zancen na cikin gidane,kuma a gidan zaa warwareshi.
Amma tayaya? Aysha ta tambaya.
Zuwa zaki ki lallabi ummi kimata bayani yadda zata gane cewa ba hindatu bace, idan yaso ita saeta tambaya ayi solving case din.
Gyada kai Aysha tai cikeda gamsuwa daidae lokacin daya sauketa a qofar gidansu.
A falo ta tadda ummy zaheeda er gidan ruqayya na hannunta tanata kuka,qarasawa tayi ta karbi yarinyar tana mata wasa har tayi shiru sannan ta juyo ga umma bayan sun gaisa take tambayarta hindatu.
Dan jimm ummy tai sannan tace ai hindatu batajin dadi, zazzabine ya rufeta jiya da daddare saeda doctor yazo ya dubata,yanxu dae bacci takeyi.
Ajiyar zuciya aysha ta sauke sannan tace yanxu ummy kema kin yadda wadannan picz din hindatu ne?
To me zance ne Aysha,ga abu qiri2 muna gani.
Ummy kenan, wlh wannan ba pic din hindatu bane,yanxu duniya ta waye ba kamar daa ba,kina zaune da wayarki zaki iya hada irin wannan abun,ummy takun saqa sosae akeyi tsakanin Hindu da jamila shiyasa ta qulla mata wannan qullalliyar saboda tasan batada fita, daganan ita kuma tabi mijinta suka bar qasar.
Kallonta ummy tai cikin gamsuwa tace yanxu Aysha idan na yadda wanene zai sake yadda da hakan, kowa yadau zafi da hindatu a wannan lokacin kuma kinga dama can hindatu mai laifi ne shiyasa kowa ya kasa yadda da ita.
Shigowar Abba ne ya katse aysha daga magana, a kujera ya zauna fuskarsa a sake suka gaisa da Aysha yana tambayarta yaushe tazo dakuma jikin nata, a kunyace ta amsa sannan y sake tambayarsu hirar me sukeyi.
Ummy ce tai masa bayanin abunda Aysha ke cewa itakuma Ayshan ta qara da cewa Abba kaima fa dan siyasa ne, duk kasan irin wannan yarfen da akeyi dan kawai a batawa mutum suna, labarin matsalar hindatu da jamila ta kwashe ta fada musu amma batace hindatu taje
[21/04, 22:30] Hassan India: Miss collapse
(86)
👠 SATAR FITA💃
labarin matsalar hindatu da jamila ta kwashe ta fada musu amma batace hindatu taje ta kwana a hotel ba.
Gyara zama Abba yai cikin cikakkiyar gamsuwa yace idan hakane dole Bashir yaji zancen nan kuma ya sauko daga tudun fushin daya hau, tunda yau Hindu batada lpy ku shirya gobe muje gaba1 ayi musu bayani.
Cikin tsananin farinciki Aysha da ummy suka fara rafkawa abba godiya.
Hindatu ma ba qaramin dadi tajiba da aysha ta fada mata sanda ta farka,har kukan dadi saeda tayi.
Washegari-
Cike falon yake da mutane, Abba,baffa,ummy da umma suna zazzaune akan kujera,hindatu na rakube gefen ummy sae aysha dake zaune a gefen umma kowa yayi shiru yana sauraran abunda Abba zaece
Dan gyaran murya Abba yayi sannan y fara cewa, bisa ga abunda y faru kwanaki Alh.bashir,haqiqa dani dakai mun tafka babban kuskure bisa zargin hindatu kawai saboda wata mata tazo ta fadi wata magana,munyi saurin fushi da gaggawar yanke hukunci wanda ya rage qiris mu shiga halaka,Alh bashir nayi bincike nayi kuma nazari na tabbatar da cewa wannan b hindatu bace, watace can aka dauko jikinta aka hada da fuskar hindatu dan kawai a haifar mana da matsala,ita kuma shedaniyar matar datasan ga abunda ta aikata saita gudu tabar qasar tareda mijinta saboda tasan komai dadewa sai wani yazo yin bincike akanta. Allah ne ya tarfawa garinmu nono bamuyi abunda zamuzo muna danasani b.
Shiru baffa yae kamar mai nazari sai can yace amma Senator tayaya zan tabbatar da zancen nan?
Murmushi Abba yai yasa hannu cikin aljihun babban rigarsa ya fito da wasu pic guda 3
Na farkon ya nunawa baffa yae yace wannan shine pic din da matar ta kawo,ya janyo na farkon yana fadin wannan kuma shine asalin pic din,wadannan porn stars ne, ma'ana masu hada fina finan batsa,wannan kuma itace fuskar hindatun da suka samo suka daura. Nasan zaka tambayi tayaya suka samu pic din hindatun,wannan b abune mai wahala ba tunda nasan tana saka picz dinta a social media wanda yawancin mata
[21/04, 22:30] Hassan India: Miss collapse
(87)
👠 SATAR FITA💃
Nasan zaka tambayi tayaya suka samu pic din hindatun,wannan b abune mai wahala ba tunda nasan tana saka picz dinta a social media wanda yawancin mata sukeyi yanxu,shiyasa mafi yawancin lokuta rashin saka photon yafi saka photon kwanciyar hankali. Jiya Sam ban runtsa ba saida nasa akaimun bincike akan picx din
Ajiyar zuciya baffa ya sauke tareda cewa haqiqa naso na tafka babban kuskure,amma sadauki ya nusar dani da wuri,na gode maka,godiya mara iyaka sadauki. Yiwa Kaine bashir, hindatu diyata ce kamar rukayyah, bazan bari wani abu y sameta b.
Ta iya yiwuwa wadannan picz din da jamila ta kawo na qarya ne, na yadda da cewa ta shiryasu ne saboda ta hadowa hindatu mummunar guguwar datafi qarfinta,ban musa hakan ba,na yadda da hakan dari bisa dari.
Wata ajiyar zuciya hindatu da aysha suka sauke tareda sakarwa juna murmushi.
Amma kuma.....umma ta cigaba
Har yanxu ina tantama akan hindatu,dan haka inaso na tambayeta abu guda, inaso taimun alqawarin fadamun gskia komai dacinta,amsar tambayar eh ko aa ne babu buqatar dogon bayani akai.
Juyowa umma tai tana kallon hindatu,fuskarta babu alamun wasa tace hindatu kin yadda xaki fadamun gskia?
Cikin sanyin jiki hindatu ta gyada kai tare da cewa qwarai umma nayi alqawarin fada miki gaskiya ta komai muninta kuwa.
Taku 2 umma ta qara,ta juya musu baya gaba1 tace hindatu inaso ki fadamun shin baki taba bin Ibrahim wani gurin kun kwana ba,har matarsa ta kamaku???
Cikeda tsananin tashin hankali hindatu ta kalli Aysha,itama Ayshan kallonta tayi cikin qololuwar tashin hankali.
Gumi ne ya fara keto musu duk da ac dake aiki a falon, gashi gab1 idanuwa sun dawo kan hindatu,ita kanta batasan abunda zatace ba, to me zance ta tambayi kanta,tasan idan tayi kuskuren cewa eh to lallai kashinta ya gama bushewa,batada sauran fita. Idan kuma tace aa to lallai alqawari da girmansa saiya cita ko badade ko bajima.
Ina sauraronki hindatu
Umma ta fada fuskarta a matuqar daure fiye da da
[21/04, 22:30] Hassan India: Miss collapse
(88)
👠SATAR FITA💃🏼
Tashin hankali kenan! Cikin rawar murya hindatu ta bude baki ta fara cewa umm...umm wlh n.... eh ko aa hindatu bance inada buqatar wani dogon bayaninki ba. Ko kusa hindatu bata dubi inda aysha take b balle ta lura da kifta mata idon da takeyi,rumtse idanuwanta kawai tayi tace Ehh ummah amma.....
Salati daukacin falon ya dauka, umma ma zaman dole tai dan ko kadan bata tsammaci haka daga hindatu b.
Riqe kanta kawai tayi,fatanta kawai duk abunda taji y zamo qarya amma hakan bai yiwu ba.
Abba ne yayi gyaran murya sannan yace kenan hindatu kina nufin abunda matar nan ta fada duka gaskiya ne?
Bazatace komai ba abbansu,ni nasan hindatu ta canza halinta,ta yiwu laifinmu ne da muka Gaza gane hakan mukaqi aurar da ita da wuri, a tunaninmu ta hakan ne zata wuce WULAQANCIN DA NAMIJI ashe ba haka bane,munyi mummunan kuskure da muk....
Wlh umma ban taba qetare iyakokin Allah ba,ki yadda dani ban taba aikata zina ba,wlh ranar ma tsautsayi aka samu kum..... shut up! Baffa ya fada ya tsawace sannan y cigaba d cewa,ashe har yanxu bakinki bai mutu ba!bayan tozarcin da kikai mana harda rainin wayo zaki qara,to wlh baa gidan nan ba. Qwarai kuma Alh. Aurar da ita kawai zamuyi dan wlh bazan iya cigaba da zama da ita ba nasan watarana baqin cikinta ne xai kashenii..... a razane hindatu ta dago, aureee....maganar tai mata qararrawa a kunnenta. Da sauri ta rarrafa gaban baffa cikin kuka take fadin baffa dan Allah kayi haquri wlh bazan sake qin jin maganarku ba,dan Allah karkace zaka aurar dani wlh mutuwa zanyi... a qule baffa y miqe yace, na baki sati 2! Just 2 wks ki fito da miji idan kuma ba haka ba kowa na zaba miki ki kuka da kanki, daga haka yabar falon, hannun umma ta riqe ta fara mata magiya,umma ke uwatace,ki yadda dani ban taba aikata zina b,umma bazan wulaqanta tarbiyyar da kukaimin ba. Itama umma zare hannunta tayi ta miqe tabar falon. Abba!ummy kuji qaina kuyi musu bayani,karsu yimin haka..... a sanyaye suma su
[21/04, 22:32] Hassan India: Miss collapse
(89)
👠SATAR FITA💃🏼
Abba!ummy kuji qaina kuyi musu bayani,karsu yimin haka..... a sanyaye suma suka bar gidan.
Riqe hannunta Aysha tai cikin tausayawa suka rungume juna,sheshsheqar kukan hindatu ce kawai take tashi a falon, kuka takeyi mai tsuma rai,tausayinta sosai aysha takeji, daki suka shige aysha ce ta lallabata daqyar tayi shiru sannan tace hindatu kin gani koh? Shisa kullum nake rabaki da SATAR FITA amma bakyaji,yanxu me gari ya waya, da ace duk sanda zaki fita da amincewar iyayenki na tabbata wannan masifar bazata sameki ba, yanxu ba kuka zakiyi ba solution zamu nema yanzuu.
Aysha kinsan yanxu ban shirya aure ba, inada buqatar yin wasu abubuwa a rayuwana kafin..... matsalarki kenan hindatu, ki fadamin meye idan kinyi aure yanzu, sa'anninki nawa ne suka tara yaya 3 ko fiye da haka, dan Allah hindatu karki batamin raina....
To Aysha ki fadamin WAZAN AURA! Sanin kanki ne bana kula kowa, banda wani tsayayyen saurayi! Aysha ki taimakamin.... ya isa haka hindatu, a cikin sati 2 ISA zaki samu miji wanda ya dace dake, baxan bari kiyi auren jeka nayika ba,nima kin taimakamin a lokacin da nake cikin matsala,kema ya zamemin dole na taimaka miki hindatu wannan aikina ne. Ayshh bansan ta yadda zan miki godiya ba amma.... ya isa hindatu ae a tsakaninmu ba wata godiya. Da irin wannan lallabawar aysha t tafi.
1 wk later-
Zaune yake akan kujerar babban falonsu, laptop dinsa nakan table din dake fuskantarsa,hira sosae sukeyi da aminin nasa Sa'ad ta kafar sadarwar Skype, da alama baya qasar ne dan naji yana zancen jibi zai dawo. Shigowar Aysha ce tadan dauke masa hankali, gefensa tazo ta zauna kamar yadda tace, saida suka gaisa da yayan nata sannan sukai sallama Adam ya rufe laptop din ya dawo da dubansa kanta.
Hannayenta ya riqo yana murzawa a hankali sannan ya dago habarta da hannunsa 1, cikin taushin murya ya fara cewa Aysha at least ki fadamin meyake damunki mana, wlh banason ganinki cikin damuwar nan, what is d problem
[21/04, 22:32] Hassan India: Miss collapse
(90)
👠SATAR FITA💃🏼
Hannayenta ya riqo yana murzawa a hankali sannan ya dago habarta da hannunsa 1, cikin taushin murya ya fara cewa Aysha at least ki fadamin meyake damunki mana, wlh banason ganinki cikin damuwar nan, what is d problem dear....
Fashewa tai da kuka ta rungumeshi tana fadin, na kasa cika alqawarin dana dauka honey! Na kasa cika alqawarina dana daukarwa hindatu..... rungumarta yayi sosae shima yana dan bubbuga mata baya yace kiyi shiru kimin bayanin matsalar taki aysha,wani alqawari ne hk?
Baffa yace zai yiwa hindatu aure,ya bata 2 wks ta fito da miji, wlh honey hindatu bata kula kowa, kaga kuwa samun miji a cikin sati 2 ba qaramin wahala bne, nayi alqawarin taimaka mata amma gashi har sati 1 ya wuce ban samu mafita ba, bansan ya zanyi ba....
Ajiyar zuciya Adam ya sauke sannan yace to aysha ai ba ruwanki a cikin zancen nan, duk tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan doka, babu irin nasiha da fadan da ba'a yiwa hindatu akan ta gyara halinta amma Iraqi ji, yanxu ae saiki zuba mata idoo.
Taya zan zuba ido ina kallon hindatu a cikin tashin hankali bayan ni a nawa lokacin matsalar bata rabu dani ba,itace ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta ingantamin rayuwana harna sami MIJIN NUNAWA SA'A, aa yaya Adam ya zamemin tilas na fidda hindatu daga cikin matsalar nan..
Ta wani hanyar kenan? Adam ya tambaya yana kallon Aysha. Taimakonka nake buqata honey,so nake kaimun alqawarin duk abunda na buqata zaka yimin.
Zanyi miki Aysha,kin wuce neman alfarma a gurina,ke matata ce.
Runtse idanuwanta tai saboda nauyin abunda zata fada sannan ta budesu ta qara riqo hannun Adam tsam sannan tace
So nake ka auri hindatu,ka ajjeta a matsayin matarka kamar niiii
Battery low
[21/04, 22:33] Hassan India: Miss collapse
(91)
👠SATAR FITA💃🏽
WHAT! shine kalma ta farko data fara fitowa daga bakin Adam, qararrawa kawai maganar take masa a brain dinsa.
Ya Adam plx,nasan kaji abunda nace maka.
Tsalam Adam ya miqe tareda cewa Aysha da alama yau kin samu matsala,y kamata kije kiyi bacci.
Garau nake jina,kuma sarai nasan abun nake fada, honey k fahimceni plx.
Babu abunda zan fahimta,I don't think kinsan abunda kike cewa.
Qarasawa kusa dashi tayi ta ruqo hannayensa tace ya Adam plx kaimun wannan taimakon,kayimun wannan alfarmar,bayan wannan bazan qara tambayarka wata alfarma b.
Daure fuskarsa yayi sannan yace Aysha kinsan abunda kike fada kuwa? Taya zakice n auri hindatu?kinsan me auren Hindu yake nufi kuwa?
Nasani ya Adam,kuma saeda nayi dogon naxari kafin na yanke wannan hukuncin.
Aysha bazan iya ba,ki nemi wata alfarmar a gurina amma b wannan b ya fada yana zare hannuwanta daga nasa.
Duk yadda kaso bazaka kauce ba ya Adam,nasan kanason hindatu tun kafin ka aureni! Mesa yanxu da kakeda dama bazaka cika burinka na aurenta ba! Bazaka tallafawa zuciyarka ka hadata da abunda ta dade tana muradi ba,mesa kake kokarin kaucewa akan wani abu wanda a ganina baikai dalili b? Nasan kana qaunar hindatu a yadda nake ganin kishinta baro baro a idanuwanka amma ka kasa bayyana mata A DALILI NA, mesa zaka cigaba d azabtar da kanka Saboda niii
Tsam Adam ya tsaya a inda yake ya kasa motsawa,tabbas yasan abunda Aysha ta fada gskia ne,amma yanxu hindatu ta zama haramiyarsa tunda har y auri Aysha.
Gabansa Aysha ta qaraso tace zaka iya boyewa duk wanda kaga dama amma ni hakan bazai boyu a gurina ba,kai mijina ne,nasan matsalarka,nasan abunda kakeso da wanda bakaso, kuma inada yaqinin zuciyarka na qaunar hindatu, ya kamat......
Duk abunda kika fada hakane Aysha, na dade ina qaunar hindatu tun tana qaramarta,a lokacin da batasan kanta bama,na rayu ta qaunarta har xuwa lokacin da bana tareda ita,koda yaushe burina na dawo gida na ganta,na girma da muradin aurenta
[21/04, 22:33] Hassan India: Miss collapse
(92)
👠SATAR FITA💃🏽
na girma da muradin aurenta,a lokacin dana dawo naso na fada mata ina sonta,amma.... Amma ya maimaita cikin raunin murya, sae umma ta kawomin zancen aurenki, ta nunamin sha'awar hakan, nikuma bazan iya watsawa mahaifiyata qasa a ido ba,domin umma tamun soyayyar da ko wacce ta haifeni iya abunda zatai kenan, banida zabi na yadda da aurenki, na aminta dake Saboda kyawawan halaye da dabi'unki, tun daga lokacin nasan cewa hindatu tayimun nisa,ko kusa banaso na bata zumuntar dake tsakanin ku shiyasa ako da yaushe nake fafutukar yaqi da zuciyata wajen rabuwa da qaunar hindatu... Amma Aysha yanxu kinaso ki fama min radadin danaji a baya, dan Allah banason jin wannan maganar daga bakinki dan bazata yiwu ba daga haka ya wuce dakinsa ba tareda y sake dubanta ba.
Hawaye ne ya wakewa Aysha fuska! Ashe hasashenta ba qarya bane mijinta yanason er uwarta kuma aminiyarta, ta shigo tsakani ta rusa musu shirinsu ta rabasu da juna, babu mamaki shine dalilin dayasa Sam hindatu bataso aurensu da Adam ba, ta yiwu Itama tana sonsa amma ta boye Saboda farincikina. Abubuwa barkatai ke yawo a zuciyar Aysha, har dare bata samu ta runtsa ba Saboda tunanin yadda zata bullowa Al'amarin
Next day sukuku tayi gashi tun safe Adam ya fita bai dawo b sae Qarfe 8, duk yanda yaso subar zancen da Aysha bata bari ba, maganar ta dinga maimaita masa har saeda suka samu sabani,daga qarshe a dole ya yadda xaije ya samu baffa da zancen dukda baisan irin kallon da zaiyi masa ba, Ayshan ce ta dinga bashi confidence.
Safiya ce sosae,agogon bangon ya nuna qarfe 8:25, umma na kitchen tana qarasa abun karyawa baffa na zaune a falo yana kallon morning show a NTA news Adam y shigo da sallamarsa, da fara'a baffa ya amsa yana fadin likita bokan turai, murmushi kawai adam yayi sannan ya qaraso falon ya zauna yana gaida baffan ummah ma ta fito suka gaisa tana tambayar ko lafiya ta ganshi da sassafe.
Murmushi ya sakeyi zuciyarsa na bugawa yace lfy lau umma, dama akwai
[21/04, 22:33] Hassan India: Miss collapse
(93)
👠SATAR FITA💃🏽
Murmushi ya sakeyi zuciyarsa na bugawa yace lfy lau umma, dama akwai exams din da zamu rubuta ne, bangaren manyan doctors din da sukai specialising a bangaren qwaqwalwa shine nace bari naxo a samun Albarka a kuma tayani da addua. Sosae umma taji dadi, dukda ba ita ta haifi Adam ba amma ya dauketa uwa ba kamar wasu yayan ba da zakuga duk yadda mariqiyarsu ta riqesu da amana wataran sai sun nuna mata ita ba uwarsu bace.
Adam ae ako da yaushe albarkarmu tana tare dakae kuma kaima kana tareda nasara insha Allah, Allah ya baka sa'a dana. Murmushi yayi yace baffa kaif.... Fitowar hindatu ce ta dauke masa hankali, Riga d skirt ne a jikinta na atamfa,tadan yafa dankwali a kanta tayi hanyar kitchen, a yadda ya gani har tadan rame dan yadda yaga skirt din na mata rawa b kamar daa ba.
Keh hindatu! Baffa ya kirata adan tsawace, tsayawa tayi bata juyoba zuciyarta ba bugawa,tasan yanxu kullum babu wata maganar arziqi dake fitowa daga bakin iyayenta a kanta sae fada da tsangwama.
Ba magana ake miki ba,zaki tsayawa mutane kamar itace! Kanta a qasa ta qaraso da durqusa, bakya ganin yayanki bazaki gaidashi ba,har yanxu wannan mummunar dabi'ar tana tareda ke koh? A hakan za'ai miki auren?
Siririn hawaye ne ya kwaranyo mata tae saurin saka hannu ta share, ita harga Allah batasan cewa anyi baqi ba, saeda ta dago kanta sannan ta taga Adam, ya Adam ina Kwana. Ta fada cikin sanyin muryarta, cikeda tausayawa ya amsa da Lpy lau hindatu xae qara mgn umma tace hado masa breakfast maxa2.
Aa umma,a qoshe nake wlh saeda n cika cikina kafin na fito, gyada kai umma tai sannan tayiwa hindatu alamar tafiya. Duk tayi sanyi babu wannan tsiwar dake qara mata kyau, gskia bazai iya barin hindatu cikin wannan halin ba....
Nace meyasa bakazo da Aysha ba....firgigit ya juyo yana Sosa kai dan bawai yaji abunda umma ta fada bane. Shiru umma tai tana kallonsa sannan tace Adam Anya kuwa ba,wata magana a bakinka? Kansa ya sosa a hankali tareda cewa uhmm....
[21/04, 22:34] Hassan India: Miss collapse
(94)
👠SATAR FITA💃🏽
Qasa yai da Kansa zuciyarsa na bugawa da qarfi2 saboda baisan yadda iyayensa zasu dauki maganar ba yace uhmmmm dama umma uhmm yadan kalli gefen baffa dake kallon tv amma hankalinsa yana kansu yace dama maganar hindatu ce ta kawoni ya fada tare da kallon gefen baffa.
Juyowa baffa yayi tareda ajje remote din hannunsa yace Ehn,ta fito da mijin kenan koh?
Eh itace kalmar data fito daga bakinsa
Daga baffan har umma washe baki sukayi,baffa yace to masha Allah shi yaron dan ina ne?
Qasa ya sakeyi da kansa yana dan murxa yatsun hannayensa sannan yace dama baffa nine..
Kaine wa? Umma ta tambaya cikin rashin fahimta.
Dakewa ya sakeyi yace umma dama nine nakeson auren hindatun...
A zabure ummah tace what? Kasan abunda kake fada kuwa Adam?
Na sani umma,kuma wlh da gsk nake inason hindatu.
Kai adamu banason zancen banza dana hofi,wani shashanci kake fada haka kana auren er uwarta kuma kaxo kace kana sonta?
Baffa ba haramun bane ba,kuma da amincewar Ayshan nazo.
Haba Adam,da hankalinka?shin bakasan ana barin halak dan kunya bane, kai kanka bakaji nauyin abun a bakinka ba, taya kake tunanin zamu amince da wannan shashancin naka, ai koda hindatu ba diyata bace bazan bari ka aureta ba umma ta fada cikin fada fada.
Umma ya kamata ki fahimceni, manzan Allah ma ya auri matar sayyadina zaid,kuma kinsan cewa shi.....dakata min Adam,ba wa'azi nakeson ji ba, maganar nan banason na sake jinta kuma inaso ta mutu anan, dan munan ba qananan Mutane bane daga haka suka tashi suka bar masa falon.
Kusan 5 mins ya dauka a zaune sannan ya shiga dakin hindatu, tea n bread ne a gabanta sae kuma plate din egg n chips ta sakasu a gaba amma ta kasaci, guntayen hawaye ne suke sauko mata a hankali na baqin ciki da takaici,kusan sallama 3 yayi sannan ta dago, da bayan hannunta take share hawayen har ya qaraso dakin, a bakin gado ya zauna yana fuskantarta.
Har yanxu kukan kikeyi hindatu? A'ah ba kuka nake ba,yajin albasar dana yanka dazu ne
[21/04, 22:34] Hassan India: Miss collapse
(95)
👠SATAR FITA💃🏽
Har yanxu kukan kikeyi hindatu? A'ah ba kuka nake ba,yajin albasar dana yanka dazu ne. Murmushi ya danyi dan yasan qarya take yace hindatu mesa zakimun qarya kuma ki dinga boye hawayenki a gabana, ko saboda baki daukeni a matsayin yayanki bane,aminu kawai kika mayar yayanki?
Da sauri ta girgiza kanta tace ya Adam bansan yanda zanyi ba,jinake kamar na mutu na huta,yaya za'ace iyayen da suka haifeni sun kasa yadda dani kuma suke qoqarin fatali da martabata ta mace har suke tunanin yin talla na ga duk namijin da sukaga dama,wani namijin ne zai daraja macen da ake tallanta, kenan hakan na nufin banda wata qima kenan?
Hannunsa ya dora akan fuskarta yana share mata hawaye yana cewa ko kadan hindatu,ke mace ce mai cikakkiyar qima da martaba,macen da kowani namiji zaiyi fatan samu, ki daina yiwa kanki fatan mutuwa kuma ki daina saka kanki a sahun ballagazazzun mata,karki manta kinada yayanki a tare dake cikin kowani runtsi,bazan bari ki wahala ba,bakuma zaki wulakanta ba nayi miki wannan alqawarin.
Amma taya hakan zai faru? Ki kwantar da hankalinli kawai hindatu kici abincin ki sai anjima ya fada tareda ficewa.
Da saqe saqen yadda xae bullowa lamarin yabar gidan, bai koma gida ba sae wajen 7:15. A zaune ya tadda Aysha a falon tana kallon wani shiri a arewa 24, murmushin yaqe kawai ta sakar masa zuciyarta na bugawa,addua kawai takeyi akan Allah ya sassauta mata kishin da takeji a ranta sannan ta fara qoqarin miqewa. Yi zamanki baby kar kisha wahala yanxun nan zan fito ya fada sannan ya shige cikin daki. Da kansa ya dauko dinner din sukaci Saboda ya fahimci cikin na wahalar da Aysha sosai.
Ya maganar hindatun? Ta tambaya fuskarta a sake. Yanda sukai da dasu baffa yai mata bayani.
Ashsha! Ni wlh ban dauka da zafi ba dear,ai hindatu er uwata ce ba zaman kishi zamuyi ba, ni daman ban taba sakawa a raina ni kadai zan zauna a gidan mijina ba, da'a daukomin wata bare ae gara hindatun tunda munsan halin juna.
[21/04, 22:34] Hassan India: Miss collapse
0 comments:
Post a Comment