Duk unguwar kowa zai shedeta mutuniyar kirki ce ....mamanta kadae ta san irin rayuwar da take ...shima don tana kawo mata tsabar kudine ....ko da rana Daya liman bai taba fahimtar abunda ke faruwa ba a gidan ...!!
Bayan da ubanshi ya dawo hajiya ta mashi magana aka fara nemawa Barister shehu auren Maryam ...
Wata Biyar aka saka bikin ...ko da yaje gidansu Maryama bai samu matsala da Ita ba ...ta amsheshi hannu bibiyu ...
Lokaci na zuwa aka daura auren ...an kashe kudi sossae ...don ko lefenta set biyar ne ..Gidansu Huda Barister Shehu ya saka a rushe suka hade da nasu ...aka dibarwa Amarya nata part din !!! ...
•• •°°•• •
"Huda kira man Auntynki "...ya fada tare fa sauketa daga jikinshi ...
Uncle ...
Hannunshi ya saka saman lebenta tare da nuna mata kofa ...
Ta lumshe ido kamar yarda yayi sannan ta tafi da gudu ...Hanne na kwance tana waya tana fadin ...
"Wallahi kawata na gaji da wannan shegiyar yarinya ...Ni kawae zance ya sawake man na tafi gidan iyayenshi idan ta tafi ya maidoni"
tayi shiru tana saurarenta ..
kafin tayi dariya tana fadin ..."Haba kawata ya za'ai yanzu na iya zama kauye ...ai sae dae gidan iyayenshi " ...don ni da kauye hai hata hai hata ....Ke nifa tunda nazo ba abunda ya shiga tsakanin mu .....abun har ya fara damuna kawata "
"Aunty idan kin gama wayar Uncle na kiranki ...amma dan Allah kicewa shegiyar kawarki ina da baba ...itane shegiya bani ba ..!! ..idan kuma ke kika ce man shegiya to ...Allah ya isana !!!
Bata jira amsarta ba ta kwasa da gudu ....
Tarota yayi yana fadin "Bara ki bar gudu ba ko Huda ? ...baran sake goyaki ba !!...
"Sorry Uncle na rantse maka da Allah na daina ..kaji ...!!!tayi rau rau da ido ..
Hannunsa ta kamo ...Uncle wae idan Aunty Hanne ta tafi kauye tana da tsayayyene? ...
Dariya yayi kasa kasa ..." Ban gane ba Huda !!!
"Yauwa ...Ina nufin tana da wanda zai aureta ...?..
zaunar da ita yayi saman hannun kujeran .."Me ya faru Hudah ?..
"Kawae Uncle ka saketa mu zauna mu kadae ,,!! ..Kaji ? ...ta fada tare da langwabe kai ..
Murmushi yayi kasa kasa ...kafin ya dago fuskarta yace .."Idan na saketa ke zaki aureni "..?
"Eh mana ...ko yanzu ma ai ina aurenka Uncle ...tunda ni da aunty muke tsare maka gida ...kai kuma idan ka dawo ka dafa man abinci ko ..?
Hanne ta shigo tana fadin
"Wallahi munafuncin wannan Huda kullun k'ara yawa yake ...banda muguwar fata ni kike fadar a saka ?...Idan an sakeni Uwarki zaa aura?,..
Look Hanne !! ...ya daka mata tsawa ...wallahi kar na kuma jin kin zagi wannan yarinyar ..."
Bata ce komae ba ta zauna tana hararan Huda ....
"Ki shirya gobe ..ko kinki ko kinso ..da safe zamuje kauye a gano kawu ..!!
" To dan Allah yaya ka sawo man wanan safar ta leda mai kama da takalmi ... "
Cikin Mamaki yace "me zakiyi da ita ?
Dan dukar da kai tayi tana fadin.."Wallahi yaya baran iya taka dattin gidan mu ba yanzu ...bana son kazanta ...!!!
Dariya sossae yayi ...ba tare da yace mata komae ba yaja hannun Huda ...Kin tafiya tayi ta tsaya gurin ..
Muje mana !!
" Uncle ba kace zaka goyani ba ?...ta fada a hankali ...
Murmushi yayi ...ai ba yanzu nace ba ko? ...ya dage gira ....
Kafada ta make .."Yanzu mana " ..
"To naji ...zoki hau muje ..." ..duk abunki iyakarki toilet zan direki !!!
Shegiya ...hanne ta fada a hankali ...
Gwalo ta mata tana hura hanci ..tare da zaro ido ...
a harzuke Hanne tace .."Zanci Ubanki Hudah "...
Mahmoud ya juyo tare zabga mata harara ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_Yaseen mutane ma sun maidani yarinya ...to wallahi am not a kid ..kyas nake kallonki ...wae na bata un edited copy taza duba man ..yo Fathern ki ya man typing😂😂😂😂😂_*
*_43 to 44_*
Karfe biyun rana suka isa kauyen ..lokacin anata haramar shiga masallaci ....Mahmoud alwala yayi ya shige masallaci ya barsu Hanne zasu shiga cikin gidan ..
Hanne ta tattare Zaninta sama tana yatsina fuska ...ta shiga gidan ...da gudu kaninta ya taho yana fadin ...
"Ga Hanne Ga Hanne ....."
Da sauri taja baya tana fadin ..."tsaya tsaya boy ...dontu touchi mai wallahi _dont touch me_ "
Sakin baki yayi yana kallonta tare da tsayawa jiki a sanye ....Hudah ta kura mata ido tana dariya kasa kasa ....Hanne na lura da Hudah ta zabga mata harara tare da jan karamin tsoki ....
Inno ta fito tana washe baki tare da lale marhabun ...a dakile hanne ta amsa sannan ta isa tabarmar da inno ta shinfida ...dank'walin kanta ta cire ta shinfida saman tabarmar sannan ta zauna....ko da inno ta kawo masu ruwa a kwano ...cewa tayi Hudah ta tashi ta dauko mata swan water a mota don bara ta iya shan ruwan randa ba!!....
Hudah bata amsa mata ba haka kuma bata tashi daga inda take ba ..!!
Basu dade ba Hanne ta azalzalesu suka fito ...a mota banda Dariya ba abunda Hudah ke yi ...Hanne kuwa ta gama k'uluwa don sae Hudah ta kalleta ta madubi sannan ta tuntsire da dariya ....Shi kanshi Mahmoud ya fara gajiya da dariyar Huda ...ta madubi ya kalleta yace ..
"Dariyan me kike Haka ne ?
"Ba komae Uncle " ...ta fada tana toshe bakinta ...
ganin ba daina dariyar zatayi ba ya sakashi daure fuska tare da juyowa ya dan kalleta ...
"ko ki daina dariyan nan ko na bata maki rai Hudah!!!
Sorry Uncle na daina kaji .!!..Benen gidansu aunty na gani yake ban dariya don yana bukatar Faci ...gudun zuwan kawayenta !! ...Uncle Na rantse maka da Allah aunty ba karamar makaryaciya bace ...kasan me take fadawa kawayenta !!
.
"Bana son ji Hudah " ...ya fada tare da daure fuska
"To uncle baran fada ba ...amma kasan ko ..? Cewa kawayenta take idan sunzo wae babanta mai kudine kuma gidansu ya ma fi naka kyau ...kuma kasan?
Kallon da ya mata ne ya sakata natsuwa ....Hanne kuwa rufe ido tayi kamar mai bacci !!
•••°°••
Rayuwa kenan ..Barister Mahmoud na zaune da Amarya maryam lafiya kalau ...sae dae kwata kwata maryam bata ma hajiya magana ...ko gaisuwa bata hadasu ...kullum tana part dinta ...Idan hajiya ma ta aika maryam din tazo ...sae dae tace "aje a fada mata ba zamanta take ba ...don haka bara tazo ba .!!....
Barister Shehu na zuwa zata fada mashi ..
sae dae yace mata. " ai laifin ki ne hajiya ...ta yaya yarinya na zaune dakinta zaki aika ta zo? ...
Sae dae hajiya ta yi shiru don bata da abun cewa .....
Shekaransu daya dae dae suka haifi diya mace kyakykyawar gaske mai suna safina....daga barister shehu har maryam suka dauki son duniya suka daurawa yarinyar ..haka hajiya ma da dad duka suna kaunar yarinyar sossae....kullun sae Hajiya ta aiki yaron dake mata hidima ya dauki Safina ya kai mata ....Tun maryam na badawa har ta fara fadan bara ta dinga bada yarinyarta ba ana zuwa a wahalar da ita .....
Ranar hajiya har part dinsu ta shiga tana fada ...ta iske Maryam zaune bisa cinyar Shehu ...maimakon ta tashi daga jikinshi sae ma kara shige mashin da tayi ...
Nan Hajiyar ta dinga balai...idan kujeran dake falon ya amsa to Maryam ta amsawa hajiya ....
Barister Shehu yace "haba hajiya taya zaki zo ki sa yarinyar mutane gaba kina zagi ....bayan ita ta haifi yarinyar nan ...gaskia bana son abunda zai bata wa Honey rai ...don haka kawae ki fita ...ni zan mata magana duk sati sae a dinga zuwa ana daukar maki ita ...!!!
A fusace ta fita daga part din ...Haka rayuwa taci gaba duk sati zaa dinga kai safina Part din Hajiya ta wuni a dawo da ita ..wani sa'in ma hajyar daki take shigewa ta barwa yaronta yana mata wasa ....
Yarinya bata cika shekara Daya ba cikinta ya fara kumbura ....tun suna daukar abun da sauki har suka lura kullun kara hawa cikin yake ...gashi duk abunda diyar taci sae ta amayar dashi ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_Na Feedohm_*💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_45 to 46_*
Asibiti suka kaita ...duk wani abu daya kamata amata ana mata ...daga karshe doctor din ya gane cewa ruwan sperm _maniyi_ ne ya taru a cikinta ....
Daga Maryam har Barister shehu sae da hankalinsu ya tashi ...
Taya zaa ce ruwan sperm sun taro a cikin yarinyar da bata kai 1yr ba ...haba doctor bara ta yiyu ba ...ka dae sake dubawa ...!! barister shehu ya fada a firgice ..
Doctor yace ..."abunda muka gani kenan ..
amma idan baku yarda ba kuna iya sake wani asibitin sir"..
Kusan asibiti uku suna zuwa amma abunda aka fada bai canza ba ....kansu ya shiga duhu ...to ina safina ta samu ruwan sperm ? ...tambayar da kuke ta wa kansu kenan ...!!
Gida suka dawo a firgice ...part din hajiya suka nufa ...a iya saninsu babu inda ake kai safina sae gurin hajiya ...Barister shehu yayi wa Hajiya bayani ...itama cewa tayi bata yarda ba , ba yarda za'ace yarinya karama sperm ya taru a cikinta. ..to ina ta samesu? ...amma a kira yaron da ke dauko safina din ...don wata sa'in gurinshi take barinta idan bacci ya dauketa ....
Yaron aka kira ....tambayarshi suka fara yi ...yarda ya rude ya saka suka gane baida gaskia ...da yaga barister Shehu ya dauko wuka yace zai kasheshi idan bai fadi gaskia ba ..
Sae cewa yayi wae ..Stick dinshi yake saka mata a baki tana tsotsar mashi !!! ...
Kukan kura barister shehu yayi ya makari yaron ..yana duka tare da fadin Allah ya isa lalata mashi d'iya ...sae ya kasheta ...da dae yaron ya samu ya kwace daga hannunshi sae ya ruga da gudu ...dama ba garin yake ba ...zuwa yayi almajiranta hajiyar ta daukeshi ya dinga mata hidima ....
Babu irin neman da barister shehu bai mashi ba amma duk a banza ...ko wanda ya sanshi bai gani ....Sae dae aka cigaba da bata magunguna har Allah yasa cikin ya koma dae dae ...
••°°••
"Hudah bara ki canza ba "...
" Uncle zan canza wallahi ...kaga nama canza ai .."...
Hanne ta fito zata raka bakuwarta ...Huda ta fara kukan akuya ...take jikin hanne ya fara kyarma ...don dama Hudah ta saba mata wannan tozarcin gaban kawayenta ...
Allah Allah take kar Mahmoud yama Hudah magana ...abunda taji yana fada ne ya sa cikinta murdawa ...
Hudah meye Haka ? ..
Sae dae Hudah ta kalli Hanne sannan tace " Uncle kukan akuyar gidansu Aunty hanne nake tunawa.. wannan wadda aka daure kusa da bangon toilet dinsu? da katangar ta kusa ruftawa ? ...ka tuna Uncle? ...
Dariya yayi kasa kasa ba tare da yace komae ba ya cigaba da karanta newspapper dake hannunshi ..
Kawar ta kalli Hanne tare da tabe baki ...sannan tayi gaba abunta .....
"Allah Ya Isa Hudah "...ta fada kamar zatayi kuka ...
Mahmoud na dariya ya riko hannun Hanne yana fadin ..."Waya sakaki masu karya?
Hudah ta juyo tana dariya tare da dubarsu ...lokaci guda ta daina dariyar tana watsawa Mahmoud din harara dashi kanshi ya rasa ko ta mecece ....
Juyawa tayi ta shige dakinshi ta barsu yanawa Hanne dariyar Hudah ta karyata Maganin Mai karya kenan ....Zama hanne tayi suka dan taba fira ....dakin ya shiga zai watsa ruwa ya fita...
Hudah ya gani zaune ta kurawa Window ido ...Duk tunaninshi bacci ta shigo zata yi ...bai ce mata komae ba ya shiga toilet yayi wanka sannan ya fito yana goge kanshi da towel ...
"Hudah !!! ya kira sunanta tare da zaunawa bisa kujeran dake kallon gadon ..
Bata amsa ba haka bata juyo ba ...kanta ya tallabo yana fadin "Menene "...?
Da sauri ta buge hannunshi dake saman fuskarta tana hararanshi ...
"Me naki Hudahta ...fada man kinji ko ..? ...ya fada cikin lallashi ..
"Kaine ka rikewa Aunty Hanne Hannu mana !! ...tayi rau rau da ido ..
Ido ya fito cike da mamaki yana kallonta ...kafin yace ..
"Hudah Dan na rike hannun Auntynki shine kike fushi ..matata face ?..
"Nima din ai matarka ce !!! ...ta bashi amsa tare da kura mashi ido ..
Murmushi yayi kasa kasa ..."Huda ke ba matata ce ...ke rayuwata ce kinji ko!!..
"Ba wani ! ...ni din matarkace ...tunda tare da aunty hanne muke tsare maka gida idan ka fita" ....ta fada tana hararanshi..
Feedohm💞.
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_Na Feedohm💞_*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_47 to 48_*
To wayace maki tsare gida shine aure!!
Bata ce mashi komae ba ta mike ta fita daga dakin ....kitchen ta nufa ..insa yake aje mata dabino da biscuit tare da sweet ...ta debo sannan ta dawo lokacin yana shafawa kanshi mai ..
" Karba kaci Uncle "...ta fada a hankali tare da mika mashi dabino daya ..
Babu musu ya karba ya cinye ..sannan ta bare sweet ta mika mashi ..itama karba yayi ya shanye yana kallonta ...sae da ta bashi biscuit sannan ta duba aljihun rigarshi ta fito sa naira dubu ta hankade pillownshi ta aje ...sannan ta dawo kusa dashi tana dariya ...
"Hudallah na me..
Hannunta ta daura saman bakinshi ...
"Yi shiru Uncle ..dama nasan dan ban baka dabino da sweet ba shi yasa kace ni ba matarka bace ...to yanzu na baka ..har kudin da ake bawa amare kaga na dauko ko ...To dan Allah Uncle yanzu ban zama cikakkiyar matar Uncle dina ba ? ...ta langwabe kai tana kyafta idanu ...ita ala dole fari zata mashi yarda taga hanne nayi idan suna zaune a falo ..
Dariya sossae yakeyi ...har sae da yaga ta fara bata rai sannan ya dan rage dariyar ..rasa abunda zai ce mata yayi ...
Ya juya ya shiga distrnt dinshi ya canza kaya ...still yana dariyar ...fesa turare yayi sannan ya fesa mata tare da jan hannunta suka fita...
Ko hanne bai ma bankwana ba ya fita da ita .
Wani katon Moll suka je ya saya mata kaya sossae sannan suka fito yana janye da hannunta...sae da ya bude mata motar ya rufe sannan ya zagaya zaya shiga ...
Har ta zauna sossae ..kafin ya kai ga shiga, ta fito da sauri tana fadin ...
"Uncle yaya Sa'ata !!!..idanuwanta suka ciko da kwallah ..
Barister Shehu ya gani dauke da safina zasu shiga moll din sae dariya yake yana gaisawa da wasu ...
Da sauri yaja hannunta ya suka shiga motar tare ...gurin driver suka zauna su duka biyun ...tana lafe jikinshi tana hawaye ....baiyi kokarin tursasata tabar kukan ba ...sae dae hannunshi dake jikinta yana bubbugata a hankali ...
••°°••
Hanne me kike so maki dan Allah ? ...ya fada a fusace ...
Haba yaya...me yasaka baka kulani ne ...ko hugging dinka nayi ka fara ja da baya kenan ...3yrs da aurenmu amma ko so daya baka taba sauke hakkin dake kanka ba !!
Murmushin takaici ya sake kafin yace ." Me zan maki bayan halittar dake jikina ita ke tattare dake ..?
Amma Yaya duk da nake maza mata ai akwae abunda ya dace kaman naji dadi nima "
"Mace ya kamata ki nema ! ...ya bata amsa tare da barin daki ...!!
°°••°°
Shekaru nata tafiya ...sam Huda bata da matsala gidan Mahmoud ...idan tafiyar nesa ta kamashi zai dauketa ya kaiWa mamanshi har sae ya dawo sannan ya daukota ...wani sa'in ma cewa take gurin maman zata zauna don tafi jin dadin zama nan ...amma baya iya barinta ko kadan bai kaunar yin nesa da ita ko na second biyu ...ji yake kamar yayi loosing Something very important a jikinshi .....haka zaita lallabata har ya samu ta biyoshi ...
Cikin ikon Allah Huda ta gama secondary school dinta ...lokacin duk wanda ya ganta bara ya taba tunanin Hudalliyar da bace ...Fatarta tayi fresh da ita ...cikar yan mata tayi ...kamar ita tayi kanta ...a lokacin shi kanshi Mahmoud tsoron zama da ita yake su biyu ....yayi baya sossae da ita ...haka itama ta shiga taitayinta ...!!
••°°••
"Uncle please dan Allah ,yanzu zan dawo wallahi ...please ka ji ? ...ta fada cike da shagwaba ...
Kallonta yayi tun daga sama har kasa ...tana sanye da gown black ...sannan ta yane kanta da black gyale ...kaf jikinta ba inda ake gani ...kamar wata balarabiya ...kafarta sanye da plat shoes black ...sae yar jikkar dake hannuta black itama ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_49 to 50_*
Ganin ya tsaya yana kalllonta ya sakata hade hannuwata guri guda tare da dan dukawa kadan
"please uncle " ...na tafi ?,...
Da kai ya bata amsa tare da lumshe ido ...wani tsalle ta daka. tana dariya sannan ta fice da gudu ....ya bita da kallo..
Gidansu kawarta Lubna dake makwabtansu ta shiga ....ganin ba kowa a falon ya sakata shigewa part din su lubna ...lubna na kwance tana karanta wani book na Ummy A'isha *_WANI HASKE_* ...Awayanta ...taji kamshin turaren Hudah baki kofa...
Da sauri ta juyo tana dariya ..."Zuwa ba alert "...ta fada cike da zolaya
"Duba phone dinki daga CBN na turo maki shi tun daxu ..."
Uhm ...ta Uncle Mahmoud ina zuwa wannan irin kwalliya nasan dai hakanan bara ki man irin wannan kyaun ba ...
Baki Huda ta tabe tana kokarin cire gown din dake jikinta ...tare da jefawa saman gadon ...
Lubna ta bude baki tana kalllonta kafin tace ...
"amma wallahi Damsel kin cuci Uncle ...don munafunci shine kika sanyo wata gown a saman wannan shedanun kayan .." ina zaki ?
Riga da wandone matsatstsu ...rigar iya karta guiwa mai gajeran hannu pink ...sae wando pencil black ....
Tabe baki tayi tana fadin ... "dallah ban san gulma ni ki taso ki rakani ..".
XIna ? ..lubna ta tambayi Hudah cike da mamakinta ..
"Bana son wulakanci ..zan sayar dakene? ...ki taso mana ...bawae dan kina da mota ba ki tsaya ja man aji ...nasan mama batta nan har mun dawo bata dawo ba ...taso please ..!!! ...ta karashe maganar tare da yin gaba abunta ...
Da hannu ta dingawa Lubna kwatance har suka isa tsohuwar unguwarsu ...ta gaban gidansu suka wuce ...sae da gabanta ya fadi ...inda yaya sa'a ke zama tana awara ta kalla ...yara zaune gurin sae wasa suke ...take idonta ya ciko da kwalla tayi saurin juyawa ta goge ba tare da lubna ta lura ba ..
Gidansu ta kalla an rusheshe an hade da gidansu barister Shehu ..baki ta tabe ta kauda kai tana kallon waje ..
Nesa da gidansu barister Shehu tace suyi parking ...sannan ta duba agogon dake makale a hannunta tare da fita da sauri tana fadin ..
Excuse me please lubna !!!...
Gidan ta fada cikin sauri ...direct part din hajiyar ta nufa ...sae da tayi gyaran murya sannan ta shiga ...hajiya na zaune bisa doguwar kujera..tana amsa waya ..
Sallama tayi a hankali ta harde hannayenta a kirji tana kallon hajiyar ...
Katse wayar tayi tare da amsa sallamar tana murmushi ...hajiya dama irin mutannan ne masu son mutun mai kyau ...
"Bak'owa shigo mana "...ta fada dauke da faraa don ta tabbata da ganin Huda ba diyar karamin mutun bace ..
Dan murmushi ta sake mai burgewa tare da dukawa kusa da hajiyar tana fadin ...
"Mummy ina wuni " ...ta fada kamar tana rada ..
"Lafiya lau ..yarinya ...Tubarakallah ..daga ina haka ?,zauna sossae mana".hajiya ta fada tare da fadada fara'arta ..
Hudah ta dan dukar da kai tana fadin.."Ayyah Mummyn mu baki sanni ba ..ai kawar Zahra ce ...tana ma nan kuwa ?
Zahra. ...?...hajiya ta tambaya tana murmushi .."ae ko nan gidan ba zahra kila dae baa baki adress din dae dae ba ...
Barister Shehu ya shigo tare da sallama...sallamar ta katse mashine ya tsaya cak tare da kurawa Hudah ido yana murmushi ...
Ta gefen ido ta kalleshi ..sannan ta saka hannunta tsakiyar cinyoyinta tare da matsetsu tana bubbuga kafanta a hankali .."Oh Mummy ..wallahi na wahala sossae ,tun dazu fa nake neman gidan duk inda na shiga ba nan bane ..gashi phone dinta a rufe....OMG ..what should i do ? ..ta dan wurga idonta tana bata fuska kamar mai shirin kuka....
Barister Shehu yayi saurin shigowa falon tare da zama kujeran dake kallon ta Hudah yana fadin .."Mom bakuwa mukayine ?
Murmushi Hajiyar tayi tare da fadin .."Wallahi kuwa Shehu gashi sae wahala suke bata har yanzu bata samu gidan ba !!
Mikewa Hudah tayi tare da dage kafada tana fadin "anyway!! ..nagode mummy bara na tafi tunda banan bane .."
Hajiya tace "Ki tsaya ko ruwa na kawo maki mana "
Dan juyowa tayi tana kallonsu tare da lumshe ido ..."thanks ...." ta fada tare da juyawa ta fita da dan gudu gudunta ...
Har tuntube Barister Shehu keyi gurin binta ...gabanta yasha yana fadin.."
"Excuse please"
Tsayawa tayi tare da kura mashi fararen idanuwanta ..
"Please wa kika ce ma kike nema "
Murmushi ta sake mashi tana fadin "Zahra Abdullahi "..
"To ko zaki bani phone numberki idan na nemo maki ita nan unguwar din sae na tura maki housenumber dinsu please !!...ya karashe maganar cikin ky'arma ...
Kura mashi ido tayi ...ba laifi ya dan manyanta ra fada a ranshi ..."thanks ...ka barsa" ...ta fada tare da cigaba da tafiya ...
"Please na rokeki da girman Allah .." ya fada kamar zaiyi kuka ...
Cak ta tsaya tare da sakin murmushi ...takowa yayi har inda take ..ya mika mata phone dinshi ..hannunta da yasha jan lalle ta saka ta karbi wayar ta sa mashi numberta ...
"Thank you so much beauty" ...ya fada cike da murna ....
gaba tayi abunda ..da karfi yace .."please me zan sa " ..
*_DAMSEL SA'ADAH.._* Ta bashi amsa kai tsaye tana tafiyarta ...
0 comments:
Post a Comment