Abba yace ...Allah ne bai baka saar karesu bane Mahmud ...karka damu kayi ta addua wata rana zaka zama jigon marayu ......tashi muje kayi breakfast kaji ko .....
Bayan sun gama breakfast din ya fita unguwarsu Huda ya je ....ya aje motarshi cikin inuwa ya haye saman motar yana kallon mutanen dake zirga zirga .....
Yaya Saa tazo wucewa janye da hannun Huda ....ganin yana kallonsu ya sakasu tsayawa ta gaisheshi sannan suka wuce ....shigarsu gida da yan mintuna kadan yaga Huda fito dauke da markade ....
Mekake kallo tun dazu .....ta katse mashi tunani tare da kura mashi ido ...
Murmushin yake ya sakar mata yana fadin ...zo nan ina zaki ...
Harara ta watsa mashi ...inda ka aikeni .....
Zo dan Allah Hudallah ....kinji ko ...wani abu zan tambayeki ....ya mika mata hannu
Kaini yanzu an bar hadani da Allah na yarda ....nima jiya ina ta hada wasu da Allah amma sukaki bar mana kudinmu ....kaje kayiwa Mamana jaje kuwa ....ko baka sani ba ....
Yaya Saa ta leko tana nemanta ....tayi sauri boyewa bayan motarshi tana fadin ....Dan Allah kace mata ka ganni nayi nan da gudu tun dazu ....
Dan murmushi yayi sannan yace ....ki fito ta koma ....sae da ta dan leko sannan ta fito .....da gudu ta tafi ....kafin ta bar layin bokitin markaden ya kife kasa ......
Da Sauri ya isa gurin ya dagota yana kakkabe mata jiki tare da sannu ....sannan ya tsince mata wanda bai taba kasa ba sossae yace ta koma gida a wanke mata....
Ido ta waro tana fadin ...ka dauka banda hankali ...so kake mamana ta daman dukan tsiya....baka gani tun dazu na fito ka tsayar dani da surutu ...
Ta dauke bokitin ta sake kwasawa da gudu ....gidan markaden aka wanke mata sannan aka markada .....
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Malan Ibrahim Headmaster ne na primary ta gwamnati ...mutun ne da yake da kyakyawar dangantaka da mutanen da yake muaamula dasu ....tun yana yaro bai cika kwarabniya ba ....su biyu ne gurin mahaifiyarsu sae daga shi sae Yayarshi hanne ...yana da yan uwa wadanda suke uba daya su shidda hudu mata sae biyu maza ....tun da suka taso basa kaunarsu Ibrahim har suka girma suka zama ware ...wadancan kuma suka hada kansu tare ....Hanne nada ya'ya biyu ciwon daji ya kamata ....bata dade tana jinya ba Allah ya dauki ranta ....ta bar Malan ibrahim shi kadae cikinsu ...yaso yaga sun hada kansu amma sam suka nuna basa kaunar dangantaka da su ...daga karshe ma suka ce sun yanke zumunci da shi gaba daya ....haka ya barsu ba dan yaso ba ....ya dawo cikin garin katsina da zama unguwar kofar marusa inda yake aiki a matsayin headmaster tare da matarshi guda daya ...Fatima da ya yansu biyu ...Saadatu sae Huda ......
Suna zaune cikin rufin asirin Allah ...duk da Huda bata jin magana hakan bai dameshi ba kullun addu ar da yake Allah ya shiryata .....Yaya Saadatu kuwa bata cika magana ba ...sannan ba ruwanta da kowa bata da abokin fada duk unguwar shi yasa mutane ke mugun ganin girmanta ....Sae ta dauki son duniya ta daurawa Huda ...bata kaunar taga koda digon hawaye a idon Huda .....don lokacin da Hudar ke karama ....kullun tana makale da yaya saa duk abunda ta samu to zata bawa huda shi ...idan kudib tara aka bata naira biyar to bara ta kashe ko naira ba sae dae tayowa Huda tsaraba da su ....tana dawowa zakaga Hudar tana tsalle ko hannun wa take tare da washe baki tana mikawa Yaya Saar hannu ....to har dare bara ta kara yarda da kowa ba sae yaya Saar ......idan kaga Yaya saa na kuka ta Huda ce take kuka ...sannan idan har tana dariya ta Huda ce ke dariya....Har mamakin Soyayyarsu ake ...zaa iya cewa Yaya Saa tafi son Huda Akan iyayenta ....
Lokacin da suka fara girma ...aka saka Huda makaranta ....idan suka makara to yaya saa zata tara hannu ayi mata dukanta dana Hudar sannan ta raka hudar Aji itama ta tashiga nata ...da yake Lokacin Huda na Aji Daya ...ita kuma yaya Saa na aji shiddah ......
Barister Shehu makwabtan gidansu Malan Ibrahim ne ...ya yarda dashi matuka ..duk wani abunda ya shafi gidan Malan ibrahim Barister Shehu yake fada mawa ...da yake ya daukeshi kamar kaninshi tunda baya da wasu yan uwa da zaya nuna yace nashine ...
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA馃崄馃崄_*
馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*馃挕
Na Feedohm馃挒
_*DEDICATED TO*_
_EXCLUSIVE WRITERS.._
13 to 14
Huda na aji Uku Malan Ibrahim sunje wani taro da suke na oldboys daura mai adu'a...sukayi hadari motar ta kama da wuta ...su shidda cikin motar babu wanda ya fita cikinsu ....a ranar sunga tashin hankali unguwar don ba karamin rashi sukayi ba ......Sam Huda bata san me ake ba ...ana zaman gaisuwa ita kuma ta tara yara suna carafke .....kowa kallonta yake ...
Bayan kwana goma ne da taga ta rabu da ganin babanta sae ta fara tambayar Yaya Saa ...ina babanmu
Sae dae tace mata ...Huda bayana nan ...zaya dawo kinji ko ...
Daga bayane ta fahimta sosaae ....shima batayi kuka ba sossae ...ta danyi yan hawaye da akace mata bara ya dawo ba ...daga baya kuma ta share hawayen tacigaba da wasanta ....
Barister Shehu sae ya koma shi ke kula da duk dan abinda malan Ibrahim ya bar masu ...mutane sun dan tara masu taimako...sannan duk abunda ta samu sae ta sanarwa da Barister Shehun ...Daga baya sae komae ya tsaya masu abincin da zasuci ma sae ya fara gagarar su daga baya ma Sae mamarsu Huda ta koma tana zuwa ta dan taya mamarsu Barister Shehun aiki duk wata ta dan bata abunda zasuci abinci ...Da yake masu kudine ...
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Wae lafiya barister two weeks baka zo office ba .....
Dariya ya sake da rafu kuka ciwo sannan yace ....Normal Shehu kawae har yanzu ban sake da lamarin munafikin mutun kamarka bane ....ya karashe maganar yana dafa kafadarshi .....
Munafukan mutane dae guda biyu ....ya bashi amsa tare da fashewa da dariya .....
Meye Ribarka ciki Shehu ka cutar da marayu wadanda kae ya dace ka taimaka masu .karamar yarinya tana rokonku amma ka kasa tausaya mata....Ya tambayeshi a sanyaye ...
*_DALILIN YAYARTA_* nake komae shi yasa na tsani yarinyar don na lura duk abunda bata so to yayarta ma bata so ....saboda yarinyar yayarta take kina duk da bata fada man ba .....Barister Mahmoud ina tsananin son Saa ...amma Huda bata sona .saboda hakan Saar ma bata kaunata ...har gida naje na kaiwa saadatu kudi ta bar awarar amma taki karba tace suna da abunda zasu rufawa kansu asiri ....idan suka talauce ba ...ita da kanta zata zo ta rokeni ni kuma lokacin zanyi amfani da damata .......
Ba tare da ya bashi amsa ba ya bar office din don baya bukatar zama tare dashi .........
Gidansu Huda ya nufa cikin saa ya ganta ta fito tana cin goriba ......kwala mata kira yayi ....
Daga bakin kofar gidansu ta tsaya tana watsa mashi harara tare da fadin....wallahi yaro ka mayyar garinnan ta yayeka bara ka ci goribar nan ba .....
Lumshe ido yayi ya matsa kusa da ita yana fadin ...baci zanyi ba Huda ....ki shiga kicewa Mamanki ina son magana da ita kinji ko ...
Lah bata nan ....tana gidansu lauya tana aiki sae da marece zata dawo ....ta bashi amsa tana kallonshi ...
five thousand ya ciro ya mika mata yana fadin ...ki kaiwa Yayarki ...kice tayi maku cefane kinji ko ...
Tsaye tayi tana kallonshi kafin ta juya ta shige gida ba tare da ta karbi kudin ba ....ya dade tsaye yana tunanin ko zata sake fitowa amma sam babu dalilinta ......
Ko da ta shiga cikin gida ta iske yaya saa tana wanki ...da yake yanzu ita kewa yan gidansu barister shehu wanki suna biyansu ....
Yaya Saa kawo na dauraye maki ....ta janyo bucket din da kayan wankin ke ciki ta fara daurayewadaurayewa
Da sauri ta rike hannunta tana dariya ...barshi Huda karki jika jikinki ....
Baran jika ba Yaya Saa ki bari na tayaki ....ke kullun mutun zaya maki abun kirki sae kice bakya so ....ta karashe maganar kamar zatayi kuka .....
Bana so ki wahala ne Huda kinji ko ....zan maki komae a rayuwarki in Allah ya yarda ba zaki wahala kamar ni ba ....karba ....ta fito da naira goma dake daure a zaninta ta mika mata ....
Jiya kince kina so ki sayi dankalin gidan Lado ko ....ga kudin na samu kije ki sayo sae kici kinji ko ....karki toni kuwa saman hanya ba ruwanki da kowa ....kinji ko ...
Kallonta tayi tare da kura mata ido ba tare da ta amshi kudin ba ...ita tama manta ta tayi maganar jiya ...amma yaya saa tana rike da abun bata manta ba .....
Karba kanwata ...ta katse mata tunani tare da janyo hannunta ta aza mata kudin ta turata waje tana murmushi .....
Har lokacin Motar mahmoud na kofar gidan .....ta kalleshi da idanuwanta da suka ciko da kwallah sannan ta kauda kai taci gaba da tafiyarta .....
Feedohm馃挒
鈥⑩€⒙奥�
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA馃崄馃崄_*
馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_*
Na Feedohm馃挒
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_Gaisuwa mai yawa ga haske writers Allah ya kara basira da daukaka.._*
15 to 16
Saadatu bakya wankewa su hajiya kaya suna fitane sossae ....Mama ta fada lokacin da ta kai lomar tuwo a bakinta ...
Da Sauri Yaya saa tace ...wallahi mama ina wankewa sossae ...cewa sukeyi basa fitane
Aa cewa sukayi wae sae dae kije can ki dinga wankewa zasu fi fita acan .....amma gaskia ni bana son wannan yawon Saadatu ...ni ina fita aikatau kema ace kina wankau ...Sae dae suyi hakuri
Aa mama zanje ....don Allah ki bari naje ....idan har na bar wankinnan ban san inda zaa sami kudin da zaa kai huda secondary ba ...dan Allah karki hanani ...bana so Huda ta wahala kamarni ..ina son ta samu ilmin mai yawa ...dan Allah ki bari na nemawa Huda kudin makaranta da karfina ...dan Allah mama .....hawayen dake cike da idonta suka samu damar gangarowa saman kumatunta .....
Huda ta matso kusa da ita saka hannu tana goge mata ....Dan Allah yaya saa kar kiyi kuka kinji ...ta tabe baki hawaye na sauka saman fuskarta ...
Nan da nan yaya Saa ta maida hawayenta tana lallashin Huda ...Mama na zaune ta zuba masu ido .....
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Table din dake gaban Barister Mahmoud ya buga da karfi yana fadin ....Meye dalinlinka na bincikar shaguna na
Idan table din ya amsa to barister mahmoud ya amsa masa ....
Wallahi Mahmoud ka kuskura maganar nan ta fasu na rantse maka da girman Allah sae na watsa ka a duniya ...sai na saka ubanka da kake takama dashi ya tsaneka da ka shi zai koreka ka fitar mashi da gida ...Don wallahi bani kadae zan dauki laifinka har da kai ...sannan ka sani inda kyakykyawar hujjar da kai akayi fashin .......
Then So what idan ka fadawa duniya har dani akayi fashin ....kai duniya ta dama amma ina tabbatar maka wallahi asirinka yana gab da tonuwa..
掳掳鈥⑩€⒙奥�
Dady wani abokin aikinmu ne ke cikin matsala wallahi ..
Dady ya kalleshi tare da fadin ..
Subhannallah meke faruwa dashi ....
Lumshe ido yayi sannan yace ...Wae wasu sukayi forcing dinshi yayi fashi a wani gida ....
Ya so ne Mahmoud ....sam bai kyautawa aikinshi ba da iyayenshi ...
Dady dole ba aka mashi ....
Mahmoud na san idan kaine ko zaa daura maka bindiga bara kayi ba ....kabar wannan maganar ....Allah ya kyauta ..
Ameen amma dady ...
hannu ya daga mashi ....akul Mahmoud ....gobe ka shirya zamu je kauye akwae diyar Kawu Nalado da yace ya baka ka aura ....
Aure dady ....ya fada a firgice ....
Nima umarni aka bada Mahmoud Allah yasa Alkhairi ce .....
Ba tare da yace komae ba ya sadda kai ...kirjinsa ke dakan uku uku ....addua yake karantuwa har ya samu natsuwa sannan ya mike ya fice falon....
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Kamar yarda Yaya saa ta fadawa mama haka take zuwa kullun gidansu barister shehu tana wanki sannan ta dawo ta baro mama gidan .....A lokacinne Huda tayi jarabawar fita daga primary school .....bayan jarabawar ta fito ta samu Government day dake kusa dasu .....
Yaya saa tace bara tayi government ta tara kudin da zata kaita makarantar kudi ....ita da kanta ta kaita makarantar ta mata registration da kudin da take tarawa......
Ranar da ta kaita makarantar ta juya zata tafi taga discipline dinsu ya daga bulala zaya daki Huda ....tayi saurin dawowa ta rungumeta tana rokanshi kar ya daketa sabuwar zuwa ce .....
Huda kuwa girgije girgije take tana fadin ...yaya saa barshi ya tabani bai san Hudalliya bace ...yaro kaje unguwarmu ka tambayi yarda nake kada katti kasa ina duka ...
Yaya Saa tacewa malamin ...dan girman Allah kayi hakuri ka barta tana da matsalar aljanu ne shiyasa bata ji..
Ido ta waro tana karkade kunne ....zuki ....Kai yaya saa dan dae kece da sae ince ...Mamanki ta saka man su ....amma kiyi hakuri kinji ko ...
Bata ce mata komae ba taci gaba da bawa malamin hakuri wanda yace ...idan duk duniyace gatanta sae ya daketa tunda bata da kunya.....
Ganin yaya saa na kuka ya saka malamin kyale Hudar ....
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 _*A DALILIN YAYATA馃崄馃崄*_
馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_*
Na Feedohm馃挒
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
_*Thank you so much sweet HAJJA....YAS鉂�..komae naki daban yake da na saura .....!..I Hhp am the first to wish you Happy birthday ASMY馃憚 ....WULLNP.....!..Best wishes UMMI A'YSHA..Kdeey ..Ayusher..Kubrieh CIE...billy galadanchi..Maman Khadija ...Asy darling ...khadeeja chafe ...Khadija candy ...jeedah Aliyu ..Billy BB...Nafee Anker.. Amnoor ... Queen Mermue ...IRSY馃槝*_
*17 to 18*
Zaman Yaya saa gidansu barister Shehu ...Sae ya fara kawo mata salo daban daban ..
Idan tana zaune inda take wanki sae barister shehu ya dinga zuwar mata da zancen banza ....tun bata kula shi har ta fara jin tsoronshi ...don tana zaune sae taji mutun ya shafa bayanta ......
bata taba fadawa kowa ba sae dae tayi ta kuka ....don kwata kwata bata jin dadin aikin yanzu ...Sae tana zaune sae Shehu ya dinga kokarin taba mata kirji ....Sae tayi niyar Barin aikin sae ta tuna da Huda dake makaranta ....
Yau ma bayan ta gama wankin tana tsaye tana shanya kayan ...Shehu yazo ta bayanta ya rungumeta ....ta fara kokarin kwace kanta tana kuka ...yaki sakinta sae ma kokarin sakamata hannu yayi a cikin riga ....hajiyarshi ta leko tana fadin ...
"Shehu wane irin shashanci ne wannan"...!
ya juyo a firgice yana kallonta ....Yaya saa kuwa wani sanyi taji a ranta ta saka bayan hannunta zata goge hawayen ....cak ! ta tsaya lokacin da hajiyar ke fadin ...!
"Idan sha'awarta kake bara ka jata daki ba sae ka tsaya waje salan uwarta ta fito ta ganka kuma ka ja mana tsegumi ".....!
Bai jira komae ba ya fizgeta da karfi ya shiga da ita dakin dake kusa dashi ...wani ihu ta saki tana turje turje tare da hadashi da Allah ya barta amma sam yaki barinta ...sae da ya rabata da darajarta ta ya mace ....sannan ya janyota kamar kayan wanki ya wurgota waje inda take wankin ya koma daki.....
Hajiyarshi kuwa tana shiga ta iske mamarsu Huda na goge goge ....tace mata.." ta tafi gida zata fita unguwa".....
Mama tace mata ...."To bara na kira Saadatu tana baya tana wanki "....
Hajiya tace ..."aa ki barta na aiketa nan makwabta ta karbo man sako" ...
Mama tace ..."to Na tafi hajiya Allah ya kiyaye ".....!
Yaya Saa lokacin da hankalinta ya dawo ta hade kai da guiwa tana kuka kamar ranta zai fita ....ga uban radadin da ke damunta ....haka ta ja jikinta ta fice daga gidan tana kuka ......
Zata shiga gida ta ga Huda ta dawo daga makaranta rataye da jikka .....baya ta koma ta lafe jikin bango gudun kada Hudar ta ganta tana kuka hankalinta ya tashi ...har sae da hudar ta shige gida sannan itama ta share hawayenta ta shiga gidan ...
Bata bari Mama ta gane halin da take ciki ba ...sae dae Huda da ta kamata tana kuka bayan ta gama sallah isha'i ...!
" Yaya Saa me aka maki ."...ta tabe baki ...nan da nan idonta ya kawo ruwa ...
Jikin Hudar ta fada tare da sakin kuka ....Hudar ke girgizata tana kuka ...."Yaya Saa dan Allah kiyu shiru ...me aka maki dan Allah ....waya tabaki Yaya ...Yaya Saa dan Allah ki fada man ".
Girgiza mata kai take tana kokarin tsaida kukan amma sam ta kasa ....ita da Hudar ke kuka kamar ransu zai fita ....Yaya Saa ta kasa fadawa Hudar asalin damuwarta ....tama rasa bakin da zata mata magana ...bata so Hudar taji abunda ya faru da ita saboda tasan Huda sarae zata iya rike abun a ranta har abada ...
Mama ta shigo ta iskesu haka ...tambayarsu take meke faruwa amma babu wanda ya bata amsa ...da taga abun bana karewa bane ta zauna ta zagesu tsaf tace su mata shiru ko su fitar mata daga daki ...idan bara su fada mata damuwarsu ba ......Yaya Saa ta fara shiru sannan ta lallashi Huda da kyar ta samu tayi shiru ...
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Karfe 3 na rana su Barister Mahmoud suka isa kauyen ....Kawu ya masu tarba mai kyau aka kawo masu madarar shanu da dambu ....Mahmoud kasa ci yayi sae dae yasha madarar kadae ...
shi kuwa dady zama yayi yaci ya koshi. ...Inno ta shigo suka gaisa sannan ta fita
..Kawu yace "a kira Hanne "...
*_Feedohm馃挒_*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS_
*_Nagode sossae da addu'o'in Ku Allah ya saka da Khairan💞_*
*19 to 20*
Kaninta ya fita da gudu ya kirata dandali.....Ko minti 10 baayi ba sae gata da tawwagar Yara sunzo ga nin mijin da zata aura daga birni ....
Gaban Mahmoud din ta zube tare da kura mashi ido tana dariya ..
sannan ta juya gurin kawayen tana fadin ....Kun ganshi nan irin mutumin nan na jikin Rigar dan mai gari ....!!..Wohoho no Hanne Duk kauyen nan albarka !!
Hanne diyar kawu nalado ...irin mutanan nan ne masu shegiyar karya da iyayi .....bata cin abincin gidansu ta gwammace ta sayi malak'i ....saboda inno bata sanya masu kayan miya kamar yarda gidan maigari suke nasu girkin .!!...Irin yaran nan ne masu hange hange ..baka da gashin wacce kace sae kayi kitson wance ....!!
Doguwace Jawur tana da kugu sossae da tsawon gashi ...amma kirjinta ba wani cikakke bane ....tun lokacin da kawu nalado ya fadawa Hanne cewa zata auri Mahmoud take ta murna don bata kaunar rayuwar kauye duk da acikinta ta tashi .....!!
Sae ma ta daina hudd'a da yaran da take hudd'a dasu ya'yan talakawa kalarta... ta koma sae Ya'yan gidan Maigari da masu kudin kauyen take hudda ...!!
Su Mahmoud basu tafi kauyen ba sae da aka daura aurenshi da Hanne .!!...duk da dama ba da shirin aure suka zo ba ...amma kawu Nalado yace ba abunda zasu jira ayi komae a gama su tafi da ita ....nan take suka bada sadaki aka daura ....su hanne sae murna ake ....Bangaran Mahmous kuwa tunda ya sadda kai bai kuma dagowa ba ...zufa ke biyo mashi ta ko 'ina ..."Innalillahi wa inna illaihir raji'un" kawae yake ..."Allahumma Ajir ni fi musibati "...kuwa ya furta ta tafi dari.!! ...
wannan wace irin masifa ce ..!!!.abunda yake fada a ranshi kenan .....har aka gama daurin auren ....!!
Ko a mota bai iya furta koda kalma daya ba ...sae Hanne dake ta karadi Abbah na biye mata ....!!
Gidansu Mahmoud din ta zauna kafin ya ida gyara nashi ....Momy ba ta iya cewa komae ba sae fatan alkhairi data mashi ....
••°°••
Tunda Shehu ya ma Yaya Saa fyad'e bata kuma zuwa gidan ba ...haka mamanta kuma bata takura mata...sae dae tayi tambayar duniyar nan ta fada mata me ke damunta .....!
Bayan wata daya ne Yaya Saa ta fahimci tana da ciki ...domin har lokacin menstruation din yazo bata ganshi ba ...sannan ga wani canji da take ji a jikinta ....
Hankalinta yayi bala'in tashi sam bata da sukuni duk ta bi ta rame kullun cikin kuka take ...ga bala'in tashin zuciya da take ...abun kadan zaya sakata amai ...
Tana tsugunne a kewaye tana amai gidan ba kowa ....Taji an dafa mata baya ...ta juyo a firgice tana kallonta ...ganin Huda ce ya saka ta sake a jiyar zuciya tare da janyo buta ta wanke bakinta ta mike ...
Daki suka shiga Huda na rike da hannunta ta zauna saman gado tare da kara janyo Hannunta tana fadin ..!
"Me ya sameki Yaya Saa ...sannu kinji" ...cikinki ya kumbura ?....ta fada tare da kura mata ido...
Hawayen dake fuskar yaya saa suka samu damar gangarowa ....tana girgixa kai ...
"Kiyi Shiru mana Yaya Saa ...me kika ci ya kumbura maki ciki...bara naje gidansu Fatse na karbo maki maganin kumburin cikin kinji ko ...sannu" .....ta mike da niyar fita ...!
Yaya Saa tayi saurin kamo hannunta tana fadin ..."Hudallah ! ...
" Na'am Yaya saa" ...menene ko tafasar jiya ta bata maki ciki ...?.
Girgiza mata kai tayi tace ..."Huda maganin da kike kokarin karbowa bara ya iya man magani ba !!...
Dariya tayi ..."haka zaki ce Yaya saa bawae ki rikeni ba ! .."to bara na kira mama gidansu lauya sae mu kaiko asibiti su baki magani ...sae su rubuta sunana idan na gama makaranta na fara aiki sae na biyasu ko? ....ta mike da sauri ...
"Tsaya Hudallah "....ta fada a hankali ..."karki fadawa Mama hankalinta zai tashi kinji ko ...ki barshi tsakaninmu karki fadawa kowa ina amai" ..
"Sirri Yaya Saa ..!!....ta fada tare da dafe baki tana waro ido ...!
"Sirri Hudallah!! ...ta bata amsa..
""Sirrin Amai !!!...ta kara tambaya cike da mamaki ...!
"Bara ki iya rike sirrin yayarki ba Huda ?...
"Zan iya mana Yaya Saa ...ko mama baran fada mawa ba ..sae ma nacewa mutane Yaya Yar baiwa ce bata amai ....Sannu kinji Yaya saa ..Allah ya baki lafiya ...Allah ya isarmu mai tafasar nan da ta sayar mana ...muguwa shi yasa naga tana kallona ...kila ma ni taso cikin nawa ya kumbura."..!!
Bata ce mata komae ba ta mike ...surfen da aka kawo mata ne ...ta dauka tayi ...sannan ta bawa Huda kudin ta saka Jikkarta ta makaranta gobe tayi kudin Tara...!!
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_21 to 22_*
Hanne!!!...irin matannanne masu shegen kilbibi da karya ....watanta biyu gidansu Mahmoud ta waye ta goge kamar ba ita ba ...kafin kace me tayi kawa makobtan gidan ....mai suna Saly ...haduwarta da Saly sae idonta ya sake budewa ...don kullun saly na gidansu Mahmoud tana kara budewa Hanne Ido ...kadan kadan sae ta fara zabgawa Maman Mahmoud Rashin kunya ....sannan idan an dafa abinci bai mata ba sae ta saka a sake dafa wani a zubar da wancan ...
Abun ya fara damun Momy gashi bata son ta fara kai karar Hanne gurin Abba ...sae yaga kamar bata son zama da ita ....
Momy na zaune ta rabka uban Tagumi ...Abba ya shigo tare da Mahmoud suna fira kadan kadan ....Hanne ta sauko daga upstair ta tsuke da riga da wando three quarter .....tana ganin Mahmoud ta sake fuska tare da tahowa tana murmushi
..
Babu kunya tayi niyar fadawa jikinshi ...wani kallon ya sake mata babu shiri ta sulale kasa tana gaida Abba ....
Abba yace " Hanne ki shirya zamuje kauye an kirani babanki baya jin dadi .."
Ta hade Fuska tana Fadin "ni gaskia Abba baran je ...idan kunje ku gaidashi .."
Akan me? ...Abba ya tambaya cike da Mamaki ...
Gaskia Abba yanzu lokacin damina ne ...nasan gidan duk ya kazance da kashin goat da cow da chickenks ...kuma inno ba iya gyarawa zatayi ba ...ni kuma baran je wari ya isheni ba ...
daga Momy har Mahmoud sakin baki sukayi suna kallonta ...Abba kuwa dariya ta bashi ..wae Goat da cow da chickenks .
..
Hanne Manya...!! ...ya fada lokacin da yake kallonta ...
Mahmoud yace " Abba da yaushe zaa tafi ?...fuska daure
Gobe Mahmoud ....ya bashi amsa ...
Ke !! ...ki shirya gobe da safe zamuje kauyenku!!!,...ya mike ba tare da ha sauri kowa ba ya shige daki ...
Momy kuwa cewa tayi ." Allah ya kyauta .." ..sannan ta mike ta fada kitchen itama ...
••°°••
Maman Huda na tsaye tana goge goge .. Barister Shehu ya fito daga daki fuska daure ....ya zauna bisa kujeran da take kallonta ...
Malama ...daga yau karki kuma zuwa aiki nan gidan an sallameki !!!!...ya fada tare da daukar remote yana latsawa ..
Maman Huda tayi sararo tana kallonshi cike da mamaki kafin ta danyi murmushi tace .,." Lauya wani abu ya faru kuma ?...
Lokacin da nace kizo ki dinga taimakawa Hajiya kin tambayeni dalili? ...ya bata amsa yana kallonta ...
"To ....Me yayi zafi Haka lauya ? ..."bara na samu Hajiyar idan wani abu nayi mata sae na bata Hakuri "...
Ba sai kinzo ba ...!!..gani nan fitowa ....hajiya ta fada lokacin da take fitowa da part dinta ...
Sannan ta ci gaba ..." Da kike son zuwa gurina ...dama ni daukeki aikin ? ...ina jin Shehu ne .. kuma yace ya sallameki to meye na sauran magana ? ...
Maman Huda tayi tsaye rike da tsumma tana kallonsu ...a iya saninta babu wani abun da ta aikata ba dae dae ba ...ta ko don Saadatu ta daina zuwa ne? ...ta tambayi kanta arai...
Tace "Kuyi Hakuri Hajiya idan dan saadatu ne wallahi har ga Allah bani na hanata zuwa ba ..!! ...
Wake maganar sakaran yarinyarki yar iska...!!! ...Hajiya ta katseta tare da zabga mata uwar harara ...
Yar iska ....?...ta fada lokacin da idonta ya ciko da kwalla ...
Eh Yar 'iska matsiyata ...barister Shehu ya bata amsa ...
Wallahi diyata ba yar'iska bace sae dae kaine dan iska ...arziki da talauci duk na Allah ne ...!!!ta basu amsa a fusace ...
Bata rufe baki ba Hajiya ta dauketa da Mari tana fadin .."Allah ya mana katanga da talauci ...fice mana daga gida tun kafin na saka a futa dake ...bara kizo har gida ba kina kiran dana dan'iska na zuba maki ido ba ....kama hanyar akurkunki tun kafin na sakashi ya maki shegen duka gurinnan...
Allah ya baku Hakuri ...Abunda ta fada kenan tare da fitowa daga gidan ....ko gabanta bata gani sossae har ta isa gida ...
Ganin yanayinta ya saka Yaya Saa tayi saurin kamota tana tambayarta lafiya..
Lafiya mama ...me ya faru ?..me suka maki..?...ta tambaya a rude ...
bata boye mata komae ba ta fada mata duk irin wulakancin da Barister Shehu da hajiyarshi suka mata ...daga saa har Maman kuka suke kamar ransu zai fita ..
Huda dake tsaye jikin kofa tana jinsu ....ta fita da gudu ..
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_23 to 24_*
Ta fitaa da gudu daga gidan ... ..bata tsaya ko'ina ba sae kofar gidansu Barister Shehu ...Wai dadi taji ganin ba maigadi a kofar gate din.. ...ta kutsa kai ta shige cikin har tsakiyar falon ...babu kowa a cikin ...katuwar Plasma dake falonsu ita ta nufa ta fito da duwatsun dake cikin jikkarta ta makaranta ...ta dinga bugawa da karfi ...kafin me plasmar duk ta farfashe ...sannan duk wani abunda tasan na glass ne sae da ta fasa shi..harta windows din dake cikin falon sae da ta fasa...!
Jin karar Glass yasa Hajiyar fitowa da sauri daga sink din wanka. ..ta daura towel ...don duk tunaninta daga waje karar ke fitowa sae da taji tabbas daga falon take fitowa Sannan ta fito daga toilet ....tana fadin ..
"Waye anan ? ..."nace wane shegene ya shigo yake mana barna...? ...cak ta tsaya ganin karamar yarinya rike da duwatsu duk ta farfasha masu kayan dake falon ...!!
Nice nan Hudalliya ....ta fada tare da runtumawa da gudu ta fita daga falon ...hajiya ta bita da gudu tana fadin ..
Bala rike man wannan shegiyar yarinyar karka bari ta fita ...!!!...ganin babu maigadi ya saka Huda sake juyowa tare da jifar Hajiya da wani dutsin sannan ta fice da gudu ...!!
Da sauri hajiyar ta dafe gefen idonta da dutsin ya sameta ..kafin zafin ya saketa Huda ta bace mata da tunani ...!!
"Wace Shegiyar yarinya ce wannan ? ..take tambayar Kanta ..yar gidan wane shege ce ? ...me muka mata dan ubanta ?..."Hurul ..aa Hudiya...mts ...aa ba haka tace sunan ba" ...ta fada tare da dafe kanta tana son tuno sunan ...Da yake bata san Huda ba ...don duk da suke zuwa Huda bata taba biyo Yaya Saa ko Mama ba ...
Barister Shehu ya shigo rike da friut din da Hajiyar ta aikeshi sawowa tun bayan fitar Maman Huda ....turus yayi yana kallon hajiyar da ta zabga uban tagumi zaune tsakiyar falon ...
"Yan Fashine suka zo Hajiya? ...ya tambaya a rude ...
"Yan fashi ko shegiyar yarinya Shehu ?...ta bashi amsa tare da mikewa tsaye..." wallahi wata shedaniyar yarinya ce ta shigo duk ta mana wannan barna ...ban san ko yar gidan uban wa cece ba ...amma tace ko Hurus ...wallahi sunan ya shige man ...amma zan saka a nemo man ita cikin unguwar nan ..."
da Sauri yace ..."ko Hudallah? ...
"Ba Hudallah ba Shehu ...na manta sunan ...amma wallahi duk randa na kamo ta taja wa ubanta bala'i dan baran kyaleta ba ...har da ni fa tayiwa ruwan duwatsu Shehu ji binan Yar da idona ya kumbura"..to meye hadinmu da ita ..?..
"Hajiya kinga yi man kwatancen yarda yarinyar take ...na tabbata Huda ce wallahi "...
"To wacece ita Huda? ..."na fada maka ba haka sunan yake ba" ..."itama da Hu din sunanta ya fara amma nata sunan ban taba jinshi ba ."..
"Huda diyar mamansu Saadatu ce wadda aka kora yau ...kuma nasan yarinyar sarai bata da mutunci ...bara yanzu zanje idan ma itace ta sake jawa uwarta bala'i ....!!!
Ya fita da sauri ...ko mota bai dauka ba ya taka kasa ....baiyi Sallama ba ya fada gidan a fusace ...Mama na tsugunne ta rafka uban tagumi ...Yaya Saa tana wanke kwanukan da suka ci abincin safe dasu ...
Su duka suka mike tsaye ganinshi ...
ya Nuna Mama da hannu yana fadin ..."Ina shedaniyar diyarki ? ....
Ran mama idan yayi dubu ya baci ta kalleshi a fusace zata yi magana yaya saa ta rigata ...
"Bamu da Shedaniya a gidannan ....amma akwaita a gidanku mai dattin da kwali sabon shigan arziki ...banza maciya amana jahilai ...!!! ...ta fada tare da rushewa da kuka ...
"Rufe man baki Shedaniya ...akwae shedan irinki mai bin maza ....shegiya karuwa..!!!
Mama ta daukeshi da mari ..."Karya kake Shehu har yanzu ban haifi Karuwa ba Wallahi kuma baran taba haihuwarta ba " ..!!
Ni kika mara ? ...ko da yake ba komae bane tunda har na kwanta da diyarki !!..zafin ba wani bane da zai dameni ....don ko kadan bai kai zafin da zakiji ba alokacin da kika fahimci diyarki karuwar Shehu ce ..!! ..don bana tunanin ban bar maku yaron da zaku raina ba na Shehu ..ko a tunaninku mutuncin da nake maku sonku nake ..? mtsee Jahilai ...to Sha'awar diyarki nake kuma fine ta kawon budurcinta har gadona ....!! ...ba wani shegen da iyasa ya tsaya maku ..matsiyatan banza!!
Wani wawan mari yaya saa ta dauke shi dashi ..tare da sakin kuka ...bata sauke hannunta ba ..Mama ta dauketa da mari itama tana kallonta cike da tuhuma ....!!
Sulalewa Yaya Saar tayi bisa guiwarta tana fitar da wani irin gujin kuka ....!!
Dariya Barister shehu yayi tare da fita daga gidan ya barsu cirko cirko ...yaya Saa na tsugunne Mama na tsaye tana hawaye ...
A zaure yazo fita sukayi karo da Huda ...wani mugun kallo ya aika mata ....itama ta sake mashi nata ...sannan tayi cikin gidan da gudu jin kukan yaya Saa ....
Yaya Sa 'a ....dukanki ki ya kuma ?....ta fada tare da dukawa kusa da ita ...
Mama ta saka hannu a fusace ta janye Hudar Gefe guda tare da dauke yaya Saa da mari ta janyo kwalar rigarta ta dago kanta ....!
"Fada man Sa'adatu' ...fadan man gaskia abunda Lauya ya fada hakane ?..ko karya ya maki Sa'adatu?..ta fada tana kuka ...
"Wallahi karya ya mata Mama!! ...Huda ta fada ba tare da tasan abunda ake magana akai ba kawae ta tsinci maganar ne...
"Yi man shiru Huda dan Ubanki ...!!!..mama ta kwasa mata tsawa ....firgitar da tayi ya sakata fadawa jikin yaya Saa tare da sakin kuka ..."Fada man Saadatu "...shin na haifi karuwar Shehu kamar yarda ya fada?.. koko sharri ne .!!...
Cikin Kuka Yaya Saa tace .."wallahi Mama baki Haifi karuwa ..ba laifina bane Fyad'e yayi man mama ...!!
Wani uban duka ta kai mata tana kuka da karfi ....Huda ta rike mata hannu tana kuka ...
"Wallahi Mama Hard'e yayi mata ".....ta leka fuskar yaya Saa tana tambayarta ...Yaya Saa Hard'e kika ce ko? ...
Fizge Huda tayi daga jikinta tana dukanta ba tare da tasan inda take duka ba ...su duka ukun kuka suke kamar ransu zai fita...
"Dan Allah Mama ki kyaleta na rantse maki da Allah Hard'e yayi mata ..!! .mama wallahi agabana yayi mata ...har cewa nayi karka yi mata Hard'e amma yaki saurarena !!! ...kuma wallahi Yayata bata Amai kullun!!!. ....Mamarmu dan Allah ki bar dukanta ..bana so ..!!.....ta karashe maganar tare da rike hannun mamar tana kuka...
Wani Uban Mari Mamar ta bata ' ..kafin ta hankadata gefe guda ta cigaba da dukan yaya sa'a ...amma Huda dawowa tayi jikin yaya Sa'ar mama ta ci gaba da dukansu a tare ...
Jikin Mama har ky'arma yake ...jin zata fadi kasa ya sakata jingina da bango tana kuka ....sannan taja jikinta ta shige daki ta barsu tsakar gida !!
Feedohm💞
0 comments:
Post a Comment