Da marece Mahmoud yazo kofar gidansu Huda ya aje motarshi ...jingina yayi yana jiran ko Huda zata fito ...don so yake yau yayi magana da mamanta ....
Cikin saa ta fito idanunta jawur tayi kuka har ta gaji ....bisa dakalin gidan ta zauna tare da hade kanta da guiwa ....
A hankali ya tako ya iso gurin ya zauna gefenta ..yana kallonta..
" Hudallah"....
dagowa tayi tana kallonshi kafin ta kalli motarshi ta sake maida kanta gurinshi ba tare da ta amsa ba ...
a hankali yace "Me aka maki Huda? ....wani abu kike so ? ..
Kai ta girgiza mashi a hankali tana goge idonta ....
"To fada man mana ' ...ko mamanki ta dukeki? ...
nan ma kan ta girgiza mashi tare da kura mashi ido ...
"To Yaya sa'arki aka batawa rai? ...yauwa Hudallah goge hawayen kinji ki fada man ...oya Yaya Sa'a ce? ..ya fada cikin sigar lallashi ..
Daga kai tayi tana fadin ..." Ba lauya bane ya cuci Yaya Sa'a yayi mata hard'e ...kuma sae da nace kar yayi mata ...amma yaki jina!! ..gashi yanzu ya saka mamanmu sae dukanta take ...tana kuka ..."
Hard'e ? ...mene haka Huda?....!
Harara ta balla mashi tana fadin " karka maidani yarinya mana ...kato da kai baka san Hard'e ba ....wanda idan akayiwa mutanen gidansu suyita kuka??? ..ko baa taba maka bane?..
Shiru yayi yana tunanin me take nufi ...zuwa can yayi saurin kallonta yana fadin ko dae Raping kike nufi ?
Ba tare da tace mashi komae ba ta mike zata shige gida ...yayi saurin riko hannunta yana fadin ..." Tsaya man Huda kinji ....please idan kin shiga gidan kice ina son magana da mama ...!!
" amma kai mugune ...!! ..baka ga irin marin da ta man ba yau" kake aikeni na mata magana ...so kake ta sake marina kenan. ?
kamar yana tsoronta yace " Please Huda ki taimaka kinji ko "...
"Idan ta dakeni ' kanka zan rama wallahi "
Da sauri yace " Na yarda Hudallah "
Shiga tayi ciki zuwa can ta fito tace mashi Idon mamar a rufe yake ....ta mata ...magana taki budewa .....ce mata yayi taje tacewa Yaya Sa'a dan Allah yana son magana da ita ..
Kafin ta bashi amsa yaya sa'a ta fito daga gidan da gudu tana kuka ...tare suka shiga gidan har da Mahmoud din...
Mama na kwance bata motsi daukarta yayi da sauri ya sakata mota sannan yaya saa da huda suka shiga ciki suna kuka sannan yaja da gudu suka fita daga lungun ...
Direct asibiti ya nufa da ita ...cikin gaggawa aka amsheta ....bayan an dubata ne aka tabbatar masu da tana raye ..hawan jini yayi attacking dinta sossae ... Bp dinta 210 ...
Daga Hudar har Yaha Saa kuka suke ...Barister Mahmoud kuwa tsaye yayi yana kallonsu ..shi ya biya kudin komae ...aka hada mata magunguna ..
Har isha'i yana asibitin ...sae da ta daeo normal sannan likita yace zaa sallameta su tafi gida .....
Barister Mahmoud ya dauko su ya kawo su gida ...da zaya tafine ya fitk da 20k ya bawa mama yace su sayi abinci kafin ya dawo ..
Sam Mama taki karba ...tace wanda ya mata bata sani ba ta gode amma wannan bara ta karba ba don yanzu bata bukatar taimakon duk wani mutun Taimakon Allah kawae take so ...Babu irin rantsuwar da bai mata ba ...amma taki karba ...
Ganin yafi damuwa da Huda ne ya saka Yaya Sa'a saurin janyo huda jikinta tana hawaye ...don bata kaunar wani namiji ya kula Huda yanzu .....a iya saninta zata iya kashe duk wanda yayi kokarin batawa Huda rayuwa ...
ganin kamar basu bukatar shi ya sakashi tashi ya tafi ...zuciyarshi cike da tunanin maganar huda ..."wae Hard'e"...what does she means? ...haka yayi ta sake sake har ya isa gida ...
Yana Shiga Mama tace ya dauki matarshi ya tafi da ita ...don wallahi ta gaji da Hanne ....!!!...
Ba dan yaso ba ya shiga dakin Hanne tana kwance sae barcinta take hankali kwance ....pillown da ta daura kanta ya dan buga kadan
ta mike ba salati tana fadin ..."wane banzane mutun na bacci yake tadashi ?
Ba tare da yace mata komae ba ya juya zai fita ..."sam hanne ba da'a" ...abunda ya fada kenan a ranshi ...
hannunshi ta riko "Ohhhh ...Yaya ne ....Yi hakuri bansan kai bane yasin" ....ta fada tana dariya
ba tare da ya juyo ba yace " ki iskeni falo zamu tafi gidan yau" ...
Ihun dadi ta sake tana fadin " Haba yanzu naji magana amma an kunshe mutun cikin gidan sirikai ba damar ya sake sae shegen sa ido "...
Ko nuna alamun yaji me take fada baiyi ba ...ya fice daga dakin ...kafin ya zauna har ta fito janye da uwar jikkar ...
Mamanshi yayi wa bankwana tare da Abba ...sannan suka tafi ..da yake bai ci komae ba ..ya tsaya wani karamun restaurant zai sayi abinci ...
Hanne tace " haba yaya me zaka saya a wannan karamin gurin dan Allah? wallahi ba girmanka bane ...!!
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITER'S..._
*_27 to 28_*
Dan juyo yayi kadan yana kallonta cike da mamaki kafin yace " banda wani girma Hanne ..sae dae ke nake tunanin girmanki yakai diyar sarki a babban kauyenku !!!
tasan magana ya fada mata sae ta kulle bakinta tayi gum ....har suka isa gida bata kara magana ba ..bareshi da ba kowa yake kulawa ba ...
Gidan ya dan nunnuna mata sannan ya shige dakinshi ya barta hangame da baki ...
••°°••
Da kyar Yaya Sa'a tayiwa Mama bayani ta yarda ...ranar tace su tashi suje gidansu Barister Shehu ta fada ubanshi wata kila shi ya sauresu a bi masu Hakkinsu ....
Da Mama da Yaya Sa'a sae Huda suka tafi ...cikin saa a harabar gidan suka iske su duka ukun tsaye da alama wani guri zasu ....sae sojojin dake tsaye cirko cirko
Hajiyar na ganinsu ta daure fuska tare da kallon Shehu ....Mama ta iso ta gaida Alhajin ...tun yarda ya amsa mata gaisuwar jikinta yayi sanyi ...
Tace " Alhaji nazo na sanar dakai abunda ya faru ." ..
A wulakance yace "ina saurarenki" .
tace " Alhaji mu talakawa bamu da komae sae Allah ...ni da diyata muna zuwa aiki anan gidan ...sae Shehu ya haye mata har ya mata fyad'e ...shine nazo na fada maka ko akwae matakin da zaka sauka "
"Bullshit kauyawan banza da wofi!! ....matsayita!! sae uban me dan yayi Raping dinta ....kanta aka fara raping koko kanta aka kare ....? ..Kai Shehu ko yanzu kake bukatar Yarinyar nan ...na yarje maka kayi abunda kake so da ita ....gidan ubanka suka shigo .,
..basu isa su wulakanta me ba har gida...!!!
"Dat my dady "....ya fada yana aika masu wani irin matsiyacin kallo ...!!
Dad din yace ..".Guard !!....ku fitar man da wadannan matsiyatan ku bar waccen ...!!! ya nuna yaya Sa'a ...
Da saurin Mama ta rugumeta tare da janta da gudu zasu fita daga gidan ...amma kafin su fita wani daga cikinsu ya fizge yaya Saa tare da tura mama da karfi waje ....haka ya dauki Hudar ya wurgota waje tana ihu tare da turje turje .....
Mama kuwa kwanciya tayi kasa tana birgima lokaci guda numfashinta ya fara sarke mata ....sam Huda bata lura da halin da mama take ciki ba ...tana jikin Gate din tana kuka tare da buga kanta jikin karfen kamar ranta zai fita ...
Yaya Saa kuwa ba shehu kadae ba harda guard din dake sae da yace duk mai bukata idan shehu ya gama ...ya bashi dama ....kadan daga cikinsu ne basu taba yaya Saa ba .....numfashinta har daukewa yake don azaba ...
sae da suka gama wulakanta ta sannan aka bude gate din aka jeho da ita kamar kayan wanki ....Huda tayi kanta ganin jikinta duk jini ..tana kuka tare da jijjigata ......
ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Huda ....fuskarta kamas babu alamun hawaye sae dae kurawa Huda ido da take tana kuka .....Inda mama take yashe ta kalla ....kafin ta ja jikinta ta isa gurin tana kallon fuskarta ...
Ba tare da tace komae ba ta koma ta zauna kar ba mutun ba ....
Huda ta cakumo Yaya Saa tana fadin .." Yaya saa me suka maki ? ....me suka yanka jikinki duk jini?....Me yasa bakya kuka ? ...
Ba tare da tace mata komae ta nuna mata mama dake kwance a kasa ......gurinta ta nufa tana kiran sunanta ...
Mama !!!...ga Yaya Sa'ar sun maido mana. ...ki tashi ki ganta mama duk jini jikinta ban San me suka yanka ba a jikinta......ki tashi dan Allah ta dawo fa Mama ....!!! girgiza take tana kuka ...amma mama ko motsi bata yi ...
Liman din unguwar yazo wucewa ta gurin ya gansu haka ....yace " Subhanallah Huda Me ya sami mamar kwance a kasa ..."
"ban sani ba ...taki tashine ...kazo ka mata magana ...yaya saa ki taso don Allah ...!!!
Da sauri ya iso gurin ...ya leka fuskarta tare da ja da baya ....."inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un "...yake nanatawa ...sannan ya tafi da sauri...
Jimawa kadan sae gashi da mutane ....ina suka dauki Mamar suna fadin wae ta rasu ....duk abunnan da ake Yaya Sa'a na zaune idonta na kallonsu ...har sae da aka dauki mamar sannan Huda ta jata tana kuka suka tafi ...
Kafin me ...gidan ya cika tab da yan gaisuwa ....huda ke ta uban ihu amma yaya saa kukan ma yaki fitowa ....ita kanta so take tayi kukan amma ba dama
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_*
( _Home of Expert and perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_Main mera dil aurtum ho yana phir kyun ho palken ..👌🏻..jhuka yein wahan ..😘 Haske writers ..Ummy Aisha ..Hajja ..Asmy ..Ayusher ..Fatee ..Khaleesalat hydar ..Billy ..Nana diso ..Asy ..HOENPW😘_*
*_29 to 30_*
Bayan sati daya ne barister Mahmoud yazo ganin jikin mamar ....Yana zuwa yaga ana addu'ar bakwae kofar gidan .. ...tambaya yayi me akeyi ...wani ya ce mashi Maman su Huda ce Allah yayiwa rasuwa sati daya kenan...
turus yayi ya kasa koda daga Kafa da k'yar ya samu ya dafa bango ya zauna a dakalin tare da tallabe kanshi da hannu biyu...
Yaya Saa kuwa ta bar magana da kowa ....Sannan duk wani namiji da yazo masu gaisuwa bata karba ...sae ma ta janyo Huda jikinta ta hanata koda motsawa ....!!
••°°•••
Barister Mahmoud yana kokarin kawo masu taimako amma sam yaya Saa bata karba ....da taga yana kallon Huda zata fara kuka tare da rokanshi ya fitar masu daga gida dan Allah ...!!!
Cikin dan lokaci abunda zasu ci ma ya fara gagaransu ....ganin basu da madafa yasa yaya saa fara wanki da guga da kuma dakau idan ta samu ...duk kokarinta na nemawa Huda kudin makaranta da abinci ...zata iya kwana biyu bata ci abinci ba ...amma bata barin Huda da yunwa ko ta mintu Biyu....duk wani aikin wahala da zatayi bata kashe ko sisi a jikinta sae dae ta kashewa Huda .....duk wani gurinta na duniya yana ga Huda !!.....ta dauki son duniya ta kara daura mata ...
Lokacin da cikinta ya fara girma sae ta fara fuskantar wulakanci gurin yaran Unguwa ..da Huda ta fita sae yaran su dinga tsokanarta wae yayarya tayi cikin shege ...!!
Haka itama yaya saa da ta fita an dinga zind'enta ana gulmarta ....sae ma ta daina fita kwata kwata ....duk tayi bak'i ta rame ...don Ma Huda ba kanwar lasa bace ...duk wanda ya taba yaya saa bata kyaleshi sae ta bishi har bayan uwarshi ta duka ...idan matar aurece bata kyaleta .. kan yaranta kanana take fanshewa don da sun fito waje zata kamasu ta doka ..yaran basu kara sukuni har sae matar ta zo har gida ta bawa yaya Sa'a hakuri.....
Ranar da Huda akayi masu hutu ta dawo daga makaranta ta iske yaya saa kwance bata lafiya ...
" Yaya Sa 'a ki tashi muje asibiti kinji ko ...sannu ..ki ta masu Allah ya isa har su mutu ....!!!
Ganin ciwon ya dameta ne ya sakata tashi ta shirya suka tafi asibiti ...
Bayan sunje ne aka mata aune aune sannan aka ce su jira result ...suna zaune sae uban surutu Huda keyi ..nurse ta fito da result din tare da kiran yaya Saa office din ...
banda "Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un" babu abunda yaya Saa ke furtawa ...wae HIV ni Sa'a .... ....Juyar da kanta take ta rasa inda zata sakashi ...
tun likitan na kokarin mata bayani har ya fuskanci sam bata cikin hayyacinta ...Huda ta fado office din da gudu ...tana fadin ..
"Yaya Sa'a ki fito mu tafi mana ....kin zauna sae surutu suke maki wae Har da fadin kina da HIV ..dan Allah ba sae ki godewa Allah ba ...ni da ko ABC ban dashi ya to zanyi ...ki tashi mutafi ...dan Allah" ..
Zuba mata ido doctor din yayi tare da fadin "Sister baraka ...ki fita da wannan yarinyar mu karasa maganar tukun"...
Yaya Sa'a tace " kubarta ...itace rayuwa duk abunda ya sameni tare muke bakinciki ...na sani ko batayi yanzu ba gaba sae tayi bakincikin da yafi wanda nayi yanzu...ku kyale ta ...ku kyale man Hudata ...!! ...idonta ya ciko da kwallah ..
Da sauri Huda ta kalli doctor din tare da zabga mashi harara tana fadin .." ku mazan nan mugayene ..me yayata ta maku da duk lokacin da ta ganku sae tayi kuka ...ba ku sonta ne? ....tashi muje Yaya sa'a ki bar kuka kinji ko .. Ni kadae ke sonki yayata kuma duk wanda ya cuceki baran taba kyaleshi idan na girma ...!!! ..hannu ta saka ta share mata hawayen tana kallon likitan ...
Hannu Yaya Sa'a ta fizga da karfi suka bar office din ...yarda take jan Yaya Sa'a sae ka dauka itace yayarta ....
Yaya Sa'a in tsaida mana Okoda mu hau ?...
Cikin Kuka tace ..Huda banda kudi okoda.. ....kin gaji da tafiyar ne ? ...
Daga kafarta tayi tare da nunawa Yaya sa'a tana fadin..
" lokacin da kika shiga gurin likita na taka kwalba ...ban iya tafiya Sossae Yaya Sa'ata ...
kanta ta dafa tana fadin ..."Sannu kinji Huda ....".
kafin Huda ta amsa Yaya Sa'a ta sab'eta ...duk da uban nauyin Huda ga kuma ciki sannan bata lafiya haka ta kaita gida ...sannan ta shinfideta saman katifarsu ...
Nan da nan ta hada wuta ta zuba ruwan zafi ta dafa...ta gasawa Huda Kafa ....Duk irin rakin Huda Shiru tayi ganin Hankalin Yaya Sa'a ya tashi sossae .....
Tunda akace Yaya Sa'a nada HIV sauran farincikinta da ya rage mata ya tafi ....bata da aiki sae kuka ....sannan bata gaza ba gurin neman kudin da zata biyawa Huda Makaranta ba ....
Barister Mahmoud kuwa kullun kokarinshi na yarda zai taimaka masu amma duk a banza ...don da Yaya saa ta ganshi zata tura Huda daki ta rufo ta dawo tana hadashi da Allah ya tafi ya barsu ....bama shi kadae ba duk wani namiji bata kaunar taga ko kallon Huda yanayi ...
••°°••
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_Assalamu Alaikum ...wadanda suka man magana da dadewa akan na bude masu GRP nace masu banda ra'ayin haka ...to Alhmd na bude maku saboda wasu dalilai ...idan har yanzu you're interested sae Ku sake man magana👌🏻👌🏻_*
*_Jaane kahan Keene pehesr zyada ..QUEEN MERMUE..NAFEE ANKER ...AMNOOR ...FEEDOH CLASSIC...AUNTY SIS ..MUM FATEEY ..SALAMATUN INNA ...AOH😘_*
*_31 to 32_*
Huda ..!!! Ya Kwala mata kira dae dae lokacin da yayi parking a bakin gidansu ...
Ta juyo tana kallonshi kafin ta koma da gudu ta janyo kofar gidansu ta saka dankwalinta ta kulle kofar ta dawo gurinshi tana hararanshi ..
"Wae kai ina zuciyarka take ?
Kirjinshi ya dafa yana murmushi ..."Tana nan Huda !!
baki ta tabe tana fadin .."ni na dauka baka da ita ...banda k'wak'wa kullun yaya Saa na fada maka ka daina zuwa gidanmu amma sae ka janyo wata motarka kazo kana washe baki ..."
Murmushi yayi ba tare da yace mata komae ba ...
"bara kayi magana ba ...to Na rantse maka da Allah duk ranar da ka kara zuwa ka saka Yayata kuka sae naje har gidanku na saka Yayarka kuka itama ....
Zagayowa tayi tare da bude Marfin motar tana fadin..."Zo ka shige ka tafi ko na maka rashin mutunci ....!!
zuwa yayi kamar zaya shiga sae kuma ya hade hannayenta guri guda ya dagata ya daurata saman motar tare da dungure mata kai yana fadin ...
"Bakya da kunya ko Huda ..? ..ni zakiwa rashin mutunci ? ...ya hade fuska
Daga kasan kafafuwanshi ta fara kallo har zuwa kanshi ..saman ta hadiyi miyau da kyar tana kallonshi ...ganin tsoro ya bayyana a fuskarta ya sashi sake daure fuska yana kallonta ...
"Ni zaki wa rashin mutunci nace maki ?
"Allahu" ...ta juyar da kai kamar saliha ...dariya taso bashi yarda take zare idanu ga fuskar bayin Allah da ta koma ..amma ya dake yana kallonta
.
"Oya ...yiman rashin Mutuncin nace !!
"To dan Allah idan nace kayi Hakuri fa ? ...ba sae ka saukeni ba na tafi gida ...sannan kullun kazo ni kuma na dinga gaidaka ....saukeni ka gani yarda zan dinga maka ..."
Sake mata hannu Yaya tare da ja da baya ...tsalle tayi ta dira kasa tana washe baki ...sannan ta hade hannayenta guri guda ..
"Kafana ma k'aikayi take man ....bara na sosa kaji ? ...ta fada tana kalloshi tare da murmushi ..
Dukawa tayi tana sosa kafar tata ...ta dago a hankali ta kalleshi taga hannusa a harde kamar ba ita yake kallo ba ...da sauri ta rarumi kafarshi da niyar ta kadashi kasa ...amma sae ji tayi kamar icce ko alamun yasan abunda take baiyi ba ....
Ta dago tana hararenshi suna hada ido ta washe baki tana kakkabe hannu ."Har ga Allah ni bama niyar kadaka nayi ba " ...
kafin ya bata amsa ta ...ta bar gurin da gudu ....dariya yayi ya bude boot din motarshi ya fito da kayan abincin da ya zo dasu ...sannan yayi waya ...wasu mutane guda Uku sukazo mata...ya basu kayan abincin sannan ya shiga motarshi ya tafi ...
Matan suka saka yara tare da daukar masu kayan abincin suka kai cikin Gidansu Huda ...yaya Saa na zaune tsakar gida taga yaran suna ta shigowa da buhunna ...bude baki tayi tana mamaki ...kafin tayi magana taji Huda na fadin ..
"Wallahi yaya Sa'a ko kayan waye wannan bara mu bashi ba ...tashi mu kaisu Daki mu boye tun kafin maisu ya shigo nema ...Dan Allah Yaya Sa'a tunda muma an taba yi mana fashi ba sae mu rama ba mu dauke kayan ....
Kafin ta rufe baki Matan sun shigo ..tsalle daya Huda tayi tare da tara hannu tana kange kayan tana fadin ..
"ba Wanda ya isa ya daukesu tunda bamu mukace a shigo mana dasu gida ba ..."
Wata daga cikinsu tayi murmushi tana fadin ...dama ai naku ne Diyata ...daga gidan marayu muke aka baku Taimakon da ake yiwa Marayu ...
Murna kamar me gurin Yaya Sa'a ...godiya ta dinga masu har da kuka ...bayan sun tafine Huda ke cewa ...
"Yaya Sa'a mu dafashi duka idan mun ci sai mu aje sauran ...yarda ko wadannan barayin sun zo bara su iya dauka ba ...kinji .."
Yaya Sa'a tace ...Huda ba yarda za'ai mu dafa shi duk kinji ko ...idan ma sun zo sun dauka Allah da ya bamu wannan zai sake bamu wani !!!!
••°°••
Huda na JS2 ..cikin Yaya Sa'a ya cika wata tara ...ranar kasa bacci sukayi ...Tun cikin dare take nakuda ..Huda ke ta mata fita tare da Sannu ....ana kiran asuba ta fita da gudu ta kira liman tace yayanta bata lafiya ...
Tare suka dawo cikin gidan ..lokacin Yata Sa'a ta wahala sossae ko Bude ido bata yi ....Banda Kuka babu abunda Huda ke yi ...har aka dauketa aka tafi da ita asibiti ...
Basu isa asibitin ba Yaya Sa'a ta rasu saboda deep labour din da tayi sannan jininta duk ya fita sossae ...
Tana ganin an juyo zaa dawo ta rike hannun liman din tana fadin
"Dan Allah karmu koma ...bata lafiya sossae ko magana bata iya man ...duba liman yayata idonta ya rufe ...dan Allah mu tafi asibiti ...ina sonta ...karmu koma liman ..wallahi da munje asibiti zan fita nayi bara na samo kudin sae na bayar da kudin ...ni bana so tasha wahala .!!!...ta fada jikin yaya saa tare da fashewa da kuka ...
Duk wanda ke motar sae da yayi mata kuka ...ko da suka isa zaa fitar da yaya saa daga mota kin sauka tayi daga jikinta sae dae aka daukesu tare ...
Bayan an aje ta ne Zaa Mata wanka liman ya rugumota jikinsa ...ya ma rasa me zai ce mata ...ya tabbata duk wanda ya hana Huda kuka ya cuceta !!!
Tana jin wani na fadin Ta Rasu ne ...tayi sauri fizge kanta daga jikin liman tana fadin ...Ta rasu kamar Mamata????..Barata dawo ba?.
Da Sauri Liman din yace ...bata rasu ba Huda !!! ..
Hannushi ta kama tare da daurawa jikin Yaya Saa tana fadin ...
"Yauwa Liman ...to tadata ...kace mata Hudanta na kuka..bata son kukana fa ...nasan zata tashi .liman ka tadata Dan Alllah !!...yaya Sa'a tace fa ...kace ta tashi' ko kukan ta ma naji zanji dadi ...Dan Allah ki tashi ...!!
Da kyar liman din ya fita da ita daga dakin yana kuka .....babban tashin Hankalinsu yarda zasu fitar da gawar daga gidan ba tare da Huda ta gani ba ...!!! ...
NO WAY OUT ...Haka suka dauko gawar Yaya sa'a ..lokacin Huda na jikin Liman a waje tana kuka...kowa ya tabbata da tayi rashi ...RASHI BABBA !! ...wanda babu wani mahalukin da zai maye mata gurbin Yaya Sa'arta !!!!
Ganin tana kokarin tashi ya saka liman din riketa gam a jikinshi ....
Kamar mai bacci take fadin.. "kace kar su tafi man da yayata!!...ina sonta ita kadae gareni ...Liman kaga ko Lauya shine ya ma Yaya Sa'ata Hard'e! ...mukaje gurinsu suka kara yankar naman jikinta ...sannan suka wullota ...Mamana ta rasu saboda Hard'e ...yaya Sa'ata ma ta rasu sabodashi ...Liman nima din ina so in masu Hard'e ...da lauya da babanshi da hajiyarshi ..zaka rakani ?
Ganin ba cikin Hankalinta take ba ...sannan idonta a rufe yake ! ya sashi ..cewa "Zan rakaki kinji Huda !! .."Yaushe zamuje ..?
Yanzu !!!...ta bashi amsa tare da rufe idonta ..bai kara ce mata komae ba sae addu'a da ya dinga tofa mata...
*_JUST THE BEGINNING....😘_*
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO ...💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
_*33 to 34*_
Tun daga lokacin Huda bata kuma magana ba ...kukan da takeyi ma ya tsaya cak ...sae ajiyar zuciya da take saki lokaci zuwa lokaci ...da marece Liman ya tafi da ita gidansu bayan kowa ya watse ....
Bata iya bacci ba .. ta riga ta saba a jikin yaya Sa'a take bacci kulun amma yau ita kadae bisa katifa ...juyi ta dinga yi ...da ta rufe idonta barister Shehu take gani yana kallonta ...sae ta kai hannu zata kamashi sae ya sille mata ...
Ranar ta Hudu ce bayan an dawo daga masallacin juma'a aka tsaya za'ayi addu'ar bakwae ...
Lokacin Barister Mahmoud shima daga masallacin ya biyo ta gidansu Huda yaga yarda suke ....mutane sun taro sae addu'a ake ..
Huda kuwa na zaune gefe guda ta daura kanta saman guiwarta ...yana gama parking ko fitowa baiyi ba ya kura mata ido tare da kiran sunanta ..
Hudallah!!!!!
Hankalinta baya duniyar gaba daya bata man san da zuwanshi ba bare ta san yana kiranta .....ganin bata da niyar kallonshi yada shi fitowa daga motar . ..
Har yazo gabanta ya tsugunna bata sani ba ...sae da ya tallabo kanta sannan takalleshi da idanuwanta da sukayi jawur ...
" Hudah ....menene ? ..idonki ke ciwo?...ya tambayeta a hankali ..
Kamar jira take ta fada jikinshi tare da sakin kuka ....duk ya rude yana tambayarta ...
Lafiya Huda? ...menene? fada man kinji ?...wani abu ya sami yayarki ?...Shiii yi shiru mana ki man magana please ..!!..ya fada a rude ...
Ba tare da ta bashi amsa ba tacigaba da kukanta ....shafa bayanta yake a hankali ..yana so ta mashi magana amma ta kasa ..sae uban kukan da take ...
Liman ya taso ya dafa bayanshi tare da yi mashi bayanin komae ...
A tsorace ya kalleta da idanuwanshi da sukayi jawur ...kafin ya sakw rungumeta sossae yana bubbuga bayanta ....
Suna nan tsugunne har aka gama addu'ar sannan aka fara shawarar wanda zai tafi da Huda gidanshi ...don babu wanda yasan dangin babanta bare a kai masu ita...
Liman yace "Har ga Allah ina son daukar Hudallah amma ina tsoron uwar dakina ? ...sam bata kaunar taga wani ya rabeni sae ta dinga azabtar dashi ...kuma rikon Huda ba zai yiyo haka ba ...domin ita marainiya ce ta sha banban da sauran yaran da ake rikewa kara zube ....dole wanda zai dauketa .. ya guji kukanta da bacin ranta ...sannan kuma bazai saketa hakanan ba ....Saboda marainiya Mutun na iya shiga wuta !! ...Na tabbata uwar dakina bazata taimaka man ba mu riketa tsakani da Allah ba tare da cuta ba ..."..Amma dan Allah cikin ku idan akwae wanda ya tabbata zata iya zama gidanshi cikin farinciki ...wallahi nayi alkwarin duk wata zan bashi buhun shinkafa da taliya da jarkar mai da kudun cefane ...dan Allah wani ya taimaka !!!
Mahmoud dake tsugunne yana jin duk abunda suka fada ....ya dago Huda daga jikinshi tare da share mata hawayen da suka wanke mata fuska ..
"In je na dawo ko Huda ? ...zauna kinji ...!!! ..ya zaunar da ita sossae sannan ya tashi ya matsa gurin
Yace "Malan za'a iya bani Hudallah ....na maka alkwarin riketa kamar uwa da diyarta ...sannan in Sha Allah barata taba kuka ba ta sanadiyata ....Dan Allah ku bani ita .."
Liman ya dade yana kallonshi kafin yace "Wane unguwa kake Yaro ? ...kuma dama kasan su ne ? ..
Cikin Sauri yace ..."na sansu wallahi ba tun yau ba ....nan take ya fadawa liman din address din gidansu ..
Liman Yace "Alhamdulillah Mahmoud ai nasan mahaifinka ...duk wata yana kawo mana taimako ...na tabbata zata ji dadi gurinku !!!
Godiya sossae yayi kafin ya koma gurin da Huda ke zaune ....
"Zaki bini ko Huda ..zan baki rayuwa mai cike da jin dadi ..zan maye maki gurbin Yaya Sa'anki ...Muje ko? ..ya fada a hankali tare da tsugunnawa kusa da ita
dagowa tayi a hankali tana kallonshi ...bakinta ya motsa ahankali sae dae bai ji abunda take fada ba ....gurin da su liman yake tsaye ta nuna mashi da hannu.....
Tare da fadin ... .."Lauya"
Feedohm💞
💧💧 _*A DALILIN YAYATA🍁🍁*_
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS....._
_*35 to 36*_
A hankali ya juya yana kallonsu ...Barister Shehu ya gani rike da wata takadda yana nunawa liman din rai a bace ...
Da sauri ya mike ta rike mashi hannu tare da binshi suka isa gurin ...
Cikin fada barister Shehu yake fadin "Dakata malan me ka sani dangane da wannan gida ...in jin nine lauyan ubansu tun kafin ya rasu ....to wannan gidan da kake wani hakilo akan basu sayar dashi ba ....to tun kafin uwarsu ta rasu ta sayar man dashi kuma ga shaidata nan"...ya mikawa Liman Takardar gida
Barister Mahmoud ya karbi takardar ba tare da ya kalleshi ba ...ya budeta yana karantawa ...tabbas takardar gidan ce amma ya tabbata karya yake ba sayar mashi da ita akai ba !!
Dan Murmushi ya saki kafin ya kamo hannun Barister Shehu ya damka mashi takardar yana fadin ..
"Malan ku bar mashi ya tafi ....Barister har kayan dake cikin gidan ya kamata ka yi takarda don babu abunda zatayi da su ....A juri zuwa rafi ".....
Ya juya tare da jan hannun Huda suka tafi ba tare da ya juyo ba ...Huda kuma tafiya take amma Barister Shehu take kallo ta kasa dauke idonta akanshi har suka isa bakin kofar ....
Gaba ya bude mata ya sakata sannan ya koma ya shiga suka tafi !!!
Falo suka iske hakima Hanne kwance saman kujera tana kallo ... Suna shiga ta mike da sauri tana dariya ..ganin Huda ya sakata matsawa da sauri tana fadin ...
"Tsaya tsaya ...karki shigo ....yaya ina ka samo wannan yarinyar duk datti ...!!!...karki shigo bara na miko maki towel kiyi wanka a wancan tap din sannan ki shigo ...yaya yar aiki ce? ..
Bai saurareta ba ya janyo Huda Har tsakiyar falon ...tare da dagata sama yana dariya ya zaunar da ita saman hannun kujera ....
Juyowa yayi gurin Hanne yana fadin "Hudallah .. _Daugter ta ...Best friend dita .... Little sister ta ....Heart cherry ... My Queen _ ......Kin fahimta ? ..
Ta gurin Mamanka kuka hadu ? ...ta tambaya a dakile
Huda ya kalla yana fadin ... Hudah ta ina muka hadu ? ...ta nan ko ? ...ya taba kirjinshi yana mata murmushi ..
Bakinta ta gumtse kafin ta fara kyafta idanu tana kallonshi .....
Oh Sorry ...Taso muje kiyi wanka kici abinci...mu dawo na baki labarin Abunda Yaya Sa'armu tace na gaya maki ...
Da gaske ? ...ta fada tare da fito da idanu ..
Kai ya daga mata yana fadin ..."Yes ...muje "...... Ya mika mata hannu ta sauko ..
Hanne dake tsaye tana kallon ikon Allah tace .."Wae Wacece wannan ? ...
Kallonta yayi a fizge yana fadin .
".Hanne bara nayi wanka zamuyi magana kinji ko ..."
Binshi tayi da kallon har suka shige part dinshi ....
" Kutmar Uba...ban taba shiga part dinshi ba amma ya shiga da wancan ... " ..ta dafe kai tare da fadin ..."to ko dae kanwar uwarshi ce "
Dae dae zai fito ya baro Huda tana wanka yaji tana fadin Kanwar uwarshi ....
Shigowa yayi Falon yana fadin .."No Hanne ba kanwar Uwata bace ...Marainiya ce ta wuce duk yarda kike tunanin"
Wani Uban tsalle tayi tare da mikewa .."Kuma dan Iskanci anan gidan ?
A fizge ya kalleta yana murmushi yace " Ki rushe in da kika gina man !!!
"Wallahi bata yiyuwa Yaya ...bamu gidan marayu " ...ta fada tare da zama kusa dashi
Look Hanne !! ..kina son zama dani ? ..
Gyad'a kai tayi tana kallonshi ...
"Good ...to ki so wancan yarinyar ...."
"kwana nawa zatayi ?...ta tambaya a hankali ...
"Abadan da'iman".....shima ya fada a hankali ..
"Amma ai nan da shekara 8 idan tayi aure shikenan ko yaya ? ..
Kallon da ya sake mata ne ya sata yin lakwas ...tashi yayi ya shiga dakin ...Hudana Zaune bisa kujera da alama lokacin ta fito daga wanka ...
"Come on ...kin yi alwala ? ....ya fada tare da fito da t shirt daga drawer shi ...red mai dogon hannu ya mika mata ...
"Tashi ki saka kafin anjima mu je Super market a sayo maki naki ko ?....
Karba tayi ta sanya ...tazo mata iya guiwa ta mata kyau sossae ...ya kalleta yana murmushi ..
"Ayehhh Hudata ..kinga yarda kikayi kyau ...come on ...na maki photo ? ...
Uhm Uhm ...ka fada man abunda Yaya Sa'an tace ....tayi rau rau da idanu ...
Hannunta ya kama ...tare da dukar da kanshi saitin fuskarta yana fadin ..."Sae kinci abinci sannan "...yaja hannunta suka fito falon ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS...._
_*37 to 38*_
Still Hanne na zaune inda ya barta ....
" Me kika hada mana lunch ?...ya fada tare da kallon Hanne ...
"Lah Yaya bana fada maka ba tun shekaran jiya kaina ke ciwo .".
..
"Good"...ya fada tare da fadawa kitchen ...yana janye da hannun Huda ..
Zaunar da ita yayi bisa table din dake cikin din.....sannan ya kunna gas ....
"Me kike so ki ci "...ya fada dauke da murmushi tare da kura mata ido ...
Lumshe idonta tayi ba tare da tace komae ba ....Tabbas yasan Har yanzu Yaya Sa'a na ranta ....hannunta ya kamo ...
"Hudallah ...zaki ci Indomie ? ...
Girgiza mashi kai tayi alamar aa .....
"To me kike so ? ... Cous cous ..?
nan ma girgiza kanta tayi ...
Dago kanta yayi yana kallonta ..."Su kadae na iya Huda ...ya fada a hankali ...ko na soya maki Dankali? ...
Bude idonta tayi da ya ciko da kwalla tana kallonshi ...Ganin zatayi kuka ne ya sakashi juya mata baya tare da kurawa Tagar kitchen din ido ...wanda a zahiri hankalinshi na kan yarinyar ...!!
Da sauri ya juyi yana fadin ...Yaya Sa'a tace idan har Hudallah na kuka to barata taba samun sauki ba a ranta ....
Share hawayen tayi da sauri tana fadin .." To idan na daina fa ? ..
Idonshi ya lumshe ...."Allah zai sakata aljanna taji dadi sossae ",..
"To na daina kaji ...kace mata na daina kukan ...taji dadi sossae dan Allah ...kuma kaji kace har yanzu ina sonta ....!!! Idonta ya ciko da kwalla tayi saurin maidasu tana kakaro murmushin dole ...
Rungumeta yayi tare da mata peck a goshi ...sannan ya daura tukunya ya zuba ruwan zafi tare da kayan miyan leda ya bata albasa ta yanka mashi ....cikin mintin kadan ya dafa masu indo mie da kwae ...ya juye masu a plate...
Hanne ya kalla yace ..."Come and enjoy your lunch ...ya aika mata wani mugun kallo ...
Tana son taci amma babu fuska duk da an mata tayin ....!!!
••°°••
Satin Huda Biyu gidan ta fara warwarewa ...Sae dae matsalan idan ya fita hanne ta sakata a gaba ...da zagi ...
Tana zaune a falo ita kadae sae game take abunta tana dariya ....Hanne ta shigo tare da fizge game din ta wurga saman kujera ...
Kunnenta ta murde ta zauna kusa da ita tana hararanta ...
Da sauri Huda ta dafe kunnen tana ihu ....
Bakin hanne ta buge tana fadin "wae ke dan ubanki idan Yaya ya shiga dake daki me kike ce mashi da kuke dadewa a ciki kuna dariya"
Cikin jin zafi Huda tace ..."Fada mashi nake ke muguwa ce kullun idan kina zaune kiyi ta man tusa ..sannan bakya wanka !!!
Wani uban rankwashi ta kai mata akae ...ihu ta sake da karfi ..
Dae dae lokacin Mahmoud ya shigo falon ...jin Ihun Huda ya hanashi karasa sallamar ya shigo da gudu yana fadin...
Hudah ...lafiya ....tsaye yayi yana kallon Hanne dake shafa kan Huda tana murmushi tare da fadin "Kai baby don na maki ci uku shine zaki man wannan ihu "..
Kallonshi Huda tayi kafin ta sake murmushi ta ruga da gudu ta fada jikinshi ...dagota yayi yana fadin..
"Hudah Game kuke ? ..
Hanne ta kalla sannan tace "Eh Uncle Game muke irin na aunty muguwa ...Dan Allah Uncle' banda mugunta irin ta Aunty Hanne sae ta murde man kunne da karfi ?
Hanne ya kalla duk tayi fiki fiki ...kafin ya maida idonshi kan Huda ...
"Me kika mata? ..
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO_*💡
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_39 to 40_*
Hanne tayi karaf tace .."Amma Hudah ke munafuka ce ...daga wasa ? ...
Murmushi yayi kasa kasa ....sannan ya mikawa Huda ledar da ya shigo da ita ..."Jeki dauko littafin da na kawo maki jiya ..."
Babu musu ta karba ta shige dakinshi da gudu ...
Bai cema Hannen Komae ba ya koma ya zauna tare da lumshe ido ...ita da kanta tazo tana bashi hakuri ...sae dae yayi murmushi ba tare da ya bude idonshi ba ...
Fad'uwar Hudah jikinshi ya sakashi bude idonshi yana murmushi ...Sossae ta zauna jikinshi ..ya karbi novel din yana karantawa ....
••°°••
Barister Shehu na zaune gida kusa da Hajiyarshi ..phone din shi ta dauki kara ....
Kamar bara ya dauka ba ...ganin babban yaronshi dake kular mashi da kasuwar zinaranshi ce ya sashi dauka wayar ..
"Hello ...Bello ya akai ",..ya fada tare da saka wayar handsfree ya daura saman hannun kujeran ...
daga dayan bangaren akace "Oga wallahi wata mata ce tazo ta sayar mana da gold dinta na 2.6m ...bayan ta tafine muka gane gold din jabu ne ...kuma mun rasa inda ta shiga a kasuwar...!!
What ? ....Uban wa cikinku ya auna zinarin lokacin da zaku saya ? ...ya fada a firgice ...
"Wallahi oga mu duka muna tsaye Bala ya auna ....Amma...
"Shuttt up ...banzaye taya mace zata sayar maku da jabun zinari ku kirani kuna fada man bayan baku kamota ba ....wallahi bazanyi asara ba ...kune zaku dauketa wawaye.!!!
Kashe wayar yayi yana kallon hajiya sae gumi ke keto mashi ....
"Zancen banza ne shehu ...ba yarda za'ae mu dauki asara su zasu dauketa wallahi ..
barsu karka kara kiransu ...!!
Amma Hajiya...
"Karka ce komae ...gobe zan tura Auwalu gurin ...zasu fito da su ne "
Tashi yayi zai shiga daki ...tayi saurin tsaidashi tana fadin ...
"Wae Shehu ya maganar yarinyar nan ta gidan Alhaji Tukur ...Kun dai daita ?
Sosa kanshi yayi yana fadin .."Adama wae Hajiya" ..
"Ita mana "...
"Nifa dama ba aurenta zanyi ba hajiya ..kawae mum hutane ...Yarinyar duk da tana diyar mai kudi sae shegen roko ..!!..So nake Allah ya bani ta kirki sae na aura ..!..Yauwa Hajiya naga wata yarinya gidan liman ko ita za'a neman man ...tana da bala'in kamun kai ga addini ...kuma suma ba talakawa bane !!
Hajiya ta saki dariya tana fadin ...Wae Maryam ...nima kaina yarinyar ta kwanya man ..akwae natsuwa gata yar mutunci..bara idan dad dinka ya dawo sae in masa magana !!!...
*_MARYAM..._* Diyar liman ce wanda yace bara ya dauki Huda ba amma asali bashine ya haifeta ba agolace a gidan ....saboda Mugun Halin Matarshi ya hanashi daukar Huda !!....Hajiya zubaida itace uwar maryam ...su biyune ya'yanta ...daga Maryam sae Abdallah kaninta ....Shi liman Allah bai taba bashi haihuwa ba har yanzu ...kuma bai taba damuwa ba !!,..Kullun tana sanye cikin zunbuleliyar hijab ...a fuskarta kamar sahila amma azuciya sam babu tsoron Allah ...idan ta saka hijab a unguwarsu tana fita daga unguwar zata kira saurayinta yaxo ya dauketa ....duk wani club dake garin babu wanda Maryam bata zuwa ....yar' bariki ce ta k'in k'ari ....
0 comments:
Post a Comment