Sanin ta dade ne ya sakata bude kofar falon a hankali ...Tana sanda ....Mahmoud din ta gani zaune bisa doguwar kujera idonshi a lumshe ...san sadawa tayi a hankali zata shigr daki ...
"Hudah ....ya kira sunan can kasan makoshi ...
Juyowa tayi tana murmushin rashin gaskia tare da fadan ..."Uncle Allah mamansu lubna ta tsayar dani ..."
"Su waye suka fita a motar lubna yanzu ? ...ya jeho mata tambaya..
"Uncle aikenmu tayi central market muka sawo mata salad...Allah kuwa" ...
Bai kuma ce mata komae ba ...ya maida idonshi ya rufe ...ta dade a tsaye kafin ta shige dakinta ta canza kaya sannan ta fito ta wuce dakin Hanne ...isketa tayi tana gyaran gado ...
"Aunty Hanne na dawo "....
"Ina kika je ne " ....
Sae da ta kalli kofa sannan ta matsa kusa da ita tare da rada mata a kunne !!
Dariya hanne tayi sannan ta daga mata hannu alamun jinjina tana fadin ..."Ki dae kular mana da kanki " ..
Hararan wasa Hudah ta mata kafin tace .."Me zaa dafa yanzu ",..
"Ki dafa komae ...bara na ida gyaran dakin sae na fito nima "...
Kitchen ta shiga ....ta bude fridge ta fito da kaza ta aje ..sannan ta dauko markadaddun kaya miya da sukayi kankara ta aje gefe guda ....electric gas ta kunna tare da a daura tukunya ta zuba man gyada tare da albasa sannan ta juye kayan miyan ...garlic ta bare ta saka tare da dakakkiyar citta da kanunfari .....ta rufe tukunyar ...
Wata tukunyar ta daura ta saka kazan ciki da dan ruwa kadan tare da albasa da citta da spices ta rufe ....cabbage ta dauko ta yanka da carrot ....tukunyar da kayan miyan suke ta koma ...lokacin ruwan cikin kayan miyan sun tsane ..ta kara mai kadan tare da spices ...bata zuba gishiri ba don yana da site effect bare ma na buhu ...bayan mintina kadan kitchen din ya dauki kamshi ....stv fish ta dauko ta gyara sannan ta zuba cikin miyar tare da cabbage da carrot din da ta yanka...ta rage wutan ta koma gurin kazanta ...tana zuwa taga ta dahu sossae ...da yake kazan yana da mai ...ta zuba kuli kulinta a kai tana motsawa a hankali tare da albasa ...sae da kuli kulin ya bi kazar sossae sanna ta sauke ta juye a foodflask ....ruwa ta zuba ta dafa spaghetti tare da peas zallah ....komawa gurin miyar tayi ta sauketa tare da juyewa a flask ...
Carrots ta wanke sossae tare da gurje bayanshi ..sannan ta yankashi kanana ta zuba a blender ta markadata ta tace sannan ta zuba sugar kadan tare da madara peak ta ruwa ...ta zuba vanilla ginger ...ta hada ...ta saka a fridge ta rufe ...
Daki ta koma still Hanne na wanka ....Itama wankan ta yi ta shirya cikin pakistan riga da wando red ta fito ... Ganin Uncle Mahmoud baya falon ya sakata jera komae a dining sannan ta shiga ta ma hanne magana suka fito ...
Hannen ta shiga dakin Mahmoud din ta iske ya fito daga wanka yana shiryawa ...
"Looking good yaya"...ta fada tana murmushi ...
Shima murmushin yayi kafin su fito falon tare ...lokacin Huda na zaune tana jiransu ...kujeran kusa sa Huda yaja ya zauna ba tare da ya kalleta ba ....
Serving Huda ta masu sannan suka fara ci ....shi kanshi so yake ya kalleta amma baya so ta fahimci wani abu ...ga kamshin turarenta ya gama cika mashi hanci ....Kadan kadan Hanne da Hudah suke taba fira ...
Abinci yaci sossae kafin ya mike ya barsu gurin ...site din da Hudah take ya juya lokacin da yake kokarin tashi ....itama shi take kallo ....Murmushi suka saki lokaci guda kafin tayi saurin dauke idonta a kanshi ....kadan ya dan taka kafarta ..sannan ya juya yacigaba da tafiyar ...
••°°••
twenty missed call ....ta fada tare da waro ido ...
New Number ne ...ko baa fada mata ba tasan me ita ...tana kokarin aje wayan aka sake kira ....
Sae da ta kusa katsewa sannan ta dauka tare da langwashe murya tayi sallama ...
Tana jin lokacin da ya sake ajiyar zuciya sannan yace .."Haba damsel kin san yarda Hankalina yayi masifar tashi tun dazu nake kira bakya dauka ...dan Darajar Allah ki taimaka man ki bani lokacinki ...wallahi tun bayan tafiyarki na kasa samun natsuwa ..harta matata wallahi kallonta nake maki " ...
"Ayya bana kusa da wayan ne.. sorry baby " ...ta fada cikin Husky voice dinta....
"Ya zanyi Damsel ? .. .lokaci guda kin tafi da tunani ...gaskia ke me sa'a ce *_SA'ADAH_*...Lokaci guda kin tafi da zuciyar barister shehu ...baki sanni bane da kin tabbata da you're luckiest person a duniyar nan ..
Murmushi tayi ..a ranta tace "na sanka shehu sanin da kai kanka wawan baka yiwa kanka ba " ..
Amma azahiri shiru ta masa ..cigaba yayi da amayo mata *_Sirrin zuci_* ...yake ba tare da wani shamaki ba ...Sun kusa 1hour suna wayar har sae da tace zata kwanta ..sannan ya mata sallama ba don yaso ba !! ...
Tun da uwar asubaha ya kirata ....dan karamin tsoki ta ja kafin ta dauki Awayar ...
"Good morning my damsel ",...ya fada ahankali ...
"Babyna ka tashi lafiya " ...ta fada kamar mai rada ...
"Ina fa lafiya na kasa bacci Sa'adah!! ..please ki taimaka man ki bani address din gidanku na zo yanzu na ganki dan Allah " ....
Maryam taji tana bala'in wae ya raina mata hankali suna kwance yana waya da wata banza ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_53 to 54_*
Tana jin lokacin da ya wanka mata mari tare da fadin uwarta ce banza ...
Cikin Shagwaba Hudah tace .."Wae baby hayaniyar me nake ji haka ...bye ...anjima munyi magana bana son hayaniya please " ..
"Yi hakuri Sa'adah .. .bara na bar gurin ...kinga wallahi nama tashi ...karki katse wayar dan Allah ...." ya fada cikin sauri ....
Duk da sanyin da ake ...can cikin garden ya je ga rakube gurin flowers yana k'yarman sanyi gudun kar wani ma yazo ya masa magana ta kashe wayan ....
••°°••
A rana barister Shehu sae ya kirata yafi sau 50 ...duk ta gama rikita mashi kwakwala ...kullun nacin ta bashi address din gidansu yake amma sam taki yarda ta bashi ...duk da itama tana so su hadun ...don akwae plan din da ta
Tana Zaune barister shehu ya kirata ..sae uwar waya take tana dariya ....Uncle Mahmoud dake tsaye kusan 30mints ya saurarenta bata sani ba ....
Yar dariya ta sake mai daukar hankalu tare da fadin "Everything nawa naka ne babyna ...just fell free wit me ...ni kaina yanzu ji nake kamar ace muna da aure ...da sae kace baka taba aure ba a rayuwarka ...zan jiyar da kai soyayyar da matarka bata baka ba before ...
Shiru tayi kafin ta saki dariya tana fadin ...
"just ka sa time ...zan turo maka address dina babyna ...you know how much i love you kuwa ???...
"Jikina da duk wani abunda na mallaka is for you baby ...i reall...
Ji tayi an fizge wayar da karfi tare da jefar da ita kasa ...a firgice ta juyo tana kallonshi ...hatta jijiyar dake kanshi ta fito sossae ...
" Uncle "...ta fada a firgice ..
Tsawa ya daka mata "Da uban wa kike waya " ..
Dukar da kanta tayi kasa ..bara ta iya jin zata fada mashi gaskia ba yanzu koda zaya daketa ne kuwa ...
Wani uban mari ya bata yana fadi "For how long kika mallaka mishi komae naki ...Uban wa yace ke ta shi ke ..?
"Uncle ...!!
"Shut up !!! ...ashe abunda yasa kike nacin ki ci gaba da karatu kenan ...soyayya Hudah as your age 18 years fa .!!....girgiza kanshi yayi idanunshi suka ciko da kwallah ...first time kenan da ya taba kai hannunshi jikin hmHudah ba da niyar ya lallasheta ba sae don duka ...juyawa yayi da sauri zaya shige dakinshi...
Hannunsa ta riko tare da dukawa saman guiwarta
Cikin kuka tace .."Na tuba uncle ..baran sake ba wallahi ...i promise baran yi soyayyar gaskia da kowa ba wallahi ..please Uncle for morethan 6 years kana tare dani ba ...baka taba sakani kuka ba ...sae ni uncle ?sae nice Hudah zan saka fitar hawaye a idon mutumin da yafi kaunata a duniya ...please uncle ka yafe man dan Allah ..!!!
...
Juyowa yayi a hankali yana kallonta kafin ya saka hannu ya dagota tare da share mata hawayen da suka bata mata fuska ...sannan ya hade ta da jikinshi ....
"Bana so Hudah it really hurts ...."...ya fada a hankali
Daga mashi kai tayi...tare da lafewa jikinshi ...
••°°••
Barister Shehu na zaune maryam ta fito rike da keys din mota .. ta matse cikin riga da wando ...binta yayi da kallo ...ta gabanshi ta wuce zata fita ...
"ina zaki haka ? ...bakya da hankaline baki ga yarda kike ba ? ...ya tambayeta tare da mikewa tsaye ...
Wani kallon ta watsa mashi ..."In da nafi wayau zan koma ..don na lura angulu ma ta koma gidanta na gaskia !!!
" Me kike nufi?...kina nufin a haka zaki fita wae ? .
"Kana mamakine? ...Shehu kenan ...to zan fita sana 'ane ...oh na manta baka san me nake ba kafin ka aureni ko ...?
Kallon mamaki ya jefa mata !!
"Haba meye na wannan kallon ...karfa ka manta akan karuwarka ka mareni da safe ....nima kuma naga nawa karuwan suka can suna jirana ..shine naga ya kamata na kai masu ziyara ....!!!
Ficewa tayi ta barsa tsaye sake da baki ...ga uwar sha'awarta da ta taso mashi ....safina ta fito daga daki da gudu tana kiran ...
"Mah!! ..Mah ....zan bi ki "....itama fita tayi waje ta barshi ..... ganin ta saba fitane ta shiga part din hajiya ya sashi kyaleta tare da komawa daki ya hade kai da guiwa ..
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_55 to 56_*
Maganganun Maryam suka fara mashi yawo ....wae karuwanta ...tabbas ba tun yau ya kamata ya gane maryam yar iska bace ...tunawa yayi da first night dinsu ....ba cikakkiyar mace ya sameta ba ...amma salon da ta dinga mashi shi ya hanashi mata magana ....sae yanzu yake tuno wasu abubuwa wanda bariki irinta maryam ta hanashi gane komae ...
Wayar Hudah ya fara nema ....Switch off ...yayi kira yafi dari a take amma bata shiga ...kanshi ya fara mashi ciwo ya rasa inda zai saka kanshi yaji dadi ...bama maryam tafi damunshi ba yanxu ...aa Damsel dinshi ...gashi bata turo mashi address din ta ba bare ya je gidansu
Zazzabi yake neman rufeshi ...amma sae kokarin kiran Hudah yake ya kasa samunta ...jin ihun hajiya ne ya sashi tashi ya fita yana dafa bango .....ko iya bude idonshi baya yi ...
A bakin gate ya ga Safina a hannun dad ..hajiya kuwa sae ihu take kamar tababba ...a hankali ya matsa gurin
"Lafiya hajiya me ke...."Chak ya tsaya ganin jini a jikin Safinar ...
Saurin karbarta yayi a hannun dad din a firgice "Dad me ya faru ...me ya sami safinar ..ku fada man meke faruwa ya naga jini a jikinta ..?...take idonshi ya ciko da kwallah jikinshi sae k'yarma yake ..
Dad yace "Fyad'e aka mata Shehu ....an cucemu Allah ya Isa!!!...ya dafe kanshi tare da tokare hannunshi da bango ...
Zaman dirshan shehu yayi tare da sakin kuka ...ji yake da zaiga wanda ya lalata mashi diya ba abunda zai hana ya kasheshi ....
••°°••
Hudah na zaune Uncle Mahmoud ya shigo rike da leda ....
"Uncle sannu da zuwa" ...ta fada a hankali ..
Dan kallonta yayi tare da sakin murmushi sannan ya mika mata ledar ...sabuwar wayace Iphone6 ...tare da mtn sim da recharge card din 5k ...
Wanni uban tsalle ta saki tare da rungumeshi tana sake mashi kiss ba tare da ta sani ba ....tureta yayi da karfi ya shige daki yana mayar da numfashi .....Jingina yayi da kofar tare da lumshe ido ...
Huda kuwa Dakin Aunty Hanne ta nufa da gudu ta nuna mata .....
"Aunty Uncle ".....ta fada tare da rungumeta ....
"Uncle na sonki Hudah!!!! ...hanne ta fada da ma'ana biyu ....
Ba tare da ta fahimce ta ba tace ..."Na sani Aunty Hanne ....Ban san dame zan saka mashi ba ...?
"Da kanki Hudah 'Zuciyarki ya dace ki bashi Hudah...!!Hanne ta fada tare da iko Hannun Hudah ..
Da sauri ta kalli Hannen ..."Aunty amma da wasa kike ko ? ...ta tambaya a hankali
"Ba wasa nake ba Hudah ....!!!..ta bata amsa kai tsaya
" Aunty ki daina wannan maganar please ...Uncle bara ya iya sona ba ..kawae yana tausayina "...ta mike tare da fita daga daki ...
Tana komawa dakinta ...ta hada wayar ...Number barister shehu tayi dialing ...har ta kusa yankewa sannan ya dauka ...yana jin maganarta duk ya rude yana tambayarta lafiya ....Ce mashi tayi bata garin ne taje maiguri grandynta bata lafiya .....
Bai yarda ta kashe wayar ba sae da ta bashi full adress dinta sannan .....ce mata yayi da marece zaya shigo yau ...
Tun wajen karfe 3 ta fara nacin uncle Mahmoud ya barta taje gidansu lubna ....hanata yayi daga farko ..sae da ta fara mashi kuka sannan ya barta ta fita da zunbuleliyar Hijab dinta .....
Karfe 4 ya kirata yace yazo kofar gidan ...suna zaune da lubna alokacin ...ta dan kalleta kafin tace .."ya jira zata aiko yaro ya shigo dashi ...".
" Lubna yazo !! ...ta fada hade da sauke ajiyar zuciya..
Fahad Lubna ta kwalawa kira tace "yaje ya shigo da bako yana bakin gate ...sannan ya kaishi falon baki "....yaron ya amsa da "to" ya fita da sauri
Mintina kadan yaron ya dawo yace ya kaishi ...Huda tayi murmushi sannan ta ciro 1k tace yaje ya sawo chocolate ...kin karba yayi ya koma ciki da gudu
Lubna ta sake mata harara ..."Damsel karki fita da wadannan kayan daukar Alhakin zaiyi yawa ...ko fa rana baa sa maku ba !!
"Da waye ...? ..Hudah ta fada tana kallon cikin idonta
"Barister mana ...sae ki rikitashi wallahi ..."
Yar dariya ta sake mai sauti tace "Kina tunanin aurenshi zanyi ke !!!
Da sauri Lubna ta kalleta ...
Amma kafin ta bata amsa ta fice daga dakin da sauri ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & Perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_57 to 58_*
Cikin takun jan hankali ta shiga falon dauke da murmushi a kyakykyawar fuskarta ....duka jikinta juyawa yake ...da yake riga da siket ne na atampha holland kuma dinki ya amsheta sossae da yake atamphar ash ce da orange a jiki...
Zumbur Barister Shehu ya mike ...ji yake kamar ya je ya rungumeta amma sam ba da shashanci yake son Sa'adah ba ...so yake ya aureta ya adanata gidanshi ...don yanzu sam shida maryam sae kallo gashi ya kasa tabuka abun kirki a kanta ....
Katse mashi tunani tayi ta hanyar hure mashi ido ...kamshin mint din bakinta ya sashi lumshe ido ..ya koma ya zauna kamar wani sakarai...
"Damsel" ...ya kira sunanta tare da zuba mata ido ...
"Why ? ...me yasa kike wahalar dani ...2weeks bama waya wallahi kamar nayi hauka ....bak'ya tausayina Sa'adah....!!
.
Kallonshi tayi ...a zahiri ya rame ...amma wannan ba shine matsalarta ba
"Ayyah sorry baby ..na fada maka naje maiduguri gurin grandy ta da bata lafiya ..amma ai yanzu gani na dawo kuma ina gabanka ..meye na bata rai ...kaga bani phone dinka dear na tura maka pic dina kaima na tura naka yarda ko bama kusa da ka gansu zaka ji dadi ko .....ta karashe maganar tare da langwabe kai ...
Cikin sauri ya bata wayar yana murmushi tare da fada mata pin din.. ...
Janshi ta dinga yi da fira ba tare da ya lura da abunda take ba ...har sae da ta dauki abunda take so sannan ta tura mashi pic dinta guda biyu ....
.
Suna firan tana duba agogo .....
••°°••
Ihun da ta saki ne yasa daga Hanne har Uncle Mahmoud din shiga kitchen da sauri ....
Tana rike da hannu sae hawaye ke zuba a idonta ....da sauri ya rike hannun yana kallonta ....yar yankar da tayi karamace amma duk ta cika gidan da ihu..
Dan karamin tsoki Hanne tayi ta juya tana fadin "Kin daiji kunya wallahi ..kamar ba mace ba ".... _Su hanne mata!!!_
Uncle Mahmoud din ta kalla da idonta da har yanzu ke fitar da hawaye ...shima ita yake kallo ...sun fi minti 10 suna kallon juna wanda ke cike da sako kala kala ....ganin baya da niyar daina kalllonta ga jinin da ke kara tada mata hankali ya sata fara bugun kirjin shi a hankali alamun ya mata wani abu ...
.
"Uncle please do som...!!!.bata karasa ba ya saka hannun a bakinshi yana tsotse hannun ido a lumshe ....
Bude ido tayi tana kallon kyakykyawar fuskarshi ...zata iya rantsuwar tun da take bata taba ganin mutun mai kyau kamar Uncle dinta ba ....
A hankali ta janye hannunta a bakinshi ba tare da ta daina kallonshi ba .......
Idonshi na lumshe ya janyota jikinshi tare da zagayeta da hannu ...!!
Idan har hakan zai saka uncle dinta jin dadi zata iya tsayuwa a hakan har Allah ya karbi Rayuwarta.....ta fada aranta bata san ya fito fili ba...
Ji ta yi ya sake da sauri tare da girgiza kai ...." Bana fatan Allah ya karbi rayuwarki a haka ba Hudah In Sha Allahu .....!!
Binshi tayi da kallo har ya bar kitchen din..sannan ta jingina da drawers din tare da lumshe ido ...
••°°••
Sae da ta kwanta sannan ta bude wayarta ...text din Barister Shehu ta gani kusa 6 ...ko daya bata bude ba sae ma tabe baki da tayi sannan ta bude Imo dinta ....
Hannunta da dungule tare da dagashi sama cikin jin dadi ...
Number da tayi saving da Kwad'o tayi dialing thrgh video call...
*Feedohm💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITER'S..._
*_59 to 60_*
Cikin Saa yana online ya dauka ...Rufe idonta tayi tana fadin
"Uncle nayi fushi kuma baran bude idona ba sae kace man sorry ...na canza phone da kyar na yi recalling numberka amma kai ko ka tuna dani haba uncle na .....oya kace man sorry sannan na kalleka ."..
Ta fada cikin wata irin murya tare da murmushi a fuskarta ...wanda ya dada fitowa da ainahin kyawunta ...
" double sorry pretty"..
Ya fada cikin sanyin murya ..duk da yana tunanin mistaken number tayi ba shi bane ...amma da yake ido ga mata sae yaga bara ya iya barin wannan pretty din ba ta wuceshi ...
Ta bude idon da sauri tare da waro ido _wanda ta tabbata ko uncle tayi wa irinshi sae yafi minti talatin kafin yabude idonshi ya kura mata ido ..barewa wannan karen ...wanda take tunanin ko jakka aka daurawa zani sae ya bita !!!!_
Haka kuwa ya faru ..don baisan lokacin da ya rungume wayar ba ..sae alamun zanen shaddah da ta gani ...
Dariya tayi mara sauti sannan ta datse kiran tare da aje wayar gefe guda ...
Kasa hakura yayi ya kirata ..Tana jin alamun ana kiranta amma ta share wayar ...sae da yayi mata missed call kusa 5 bata dauka ba ...
Imo din ta koma ta tura mashi text
_"am sorry mistake din number nayi..a digit din karshe instead nasa 6 sae nasa 9 "_
kafin ta fira har ya fara typing ...
" _Nasan prety ...amma babu ta inda Allah baya hada mutane_ !!!
"Ashe kunsa Allah ? ...ta fada a fili sannan ta maida mashi da "
" _Ok"..._
Kiranta yayi a video call ...har sae da ta kusa tsinkewa sannan ta dauka
ba kunya ya tasa karamar yarinyar cikinshi gaba yana mata sabbatu . ....
Kallonshi kawae take tana murmushi kafin tace ..
"kayi hakuri na fada mata mistaken number nayi please...!!
At long last ma cewa yayi ta bashi adress din garin da take da gidansu ...
" ba bukata "...ta fada a hankali .."domin gaskia kai saan ubana ne kaga bara ya yiyu nayi soyayya da kai ba !!!
"So baya tsufa pretty" ....ya fada cikin sauri ...
.
Datse wayarta tayi gaba daya sannan ta kashe .....
Dad din shehu kuwa cigaba yayi da kiranta amma yaji ta rufe ...daran ranar kasa bacci yayi ...bai taba haduwa da yarinyar da ta tafi da imanin shi ba irin yau ....
tana bude wayarta kamar rige kiran dad din Shehu na shigowa ..yana katsewa na shehun na shigowa ...bata dauki ko daya ba ta shige tayo wanka ...dama tun da daddare mama ta ce da safe Mahmoud ya kawota zata tayata zama saboda Abba zaiyi tafiya ....
Bayan ta shirya suka shiga mota ita da Uncle Mahmoud ..
Sun dauki hanya sossae ba wanda ya tankawa wani tsakani ...sae dae lokaci lokaci suna kallon juna ...shiru ya mata yawa gani take kamar baya lafiyane ...tana so ta tambayeshi meke damunshi amma ta kasa ...da ky'ar ta bude baki tace ..
"Uncle baka lafiyane ? ...tana kallonshi ...
juyowa yayi a wahale yana kallonta ..wani murmushi ta sake mashi da ya sashi ta taka birki da sauri ya kauce hanya ...
tsoranta da tayi yasa ta fada jikinshi tare da zagaye hannunta jikinshi ...sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya zagaya da hannunshi bayanshi ya riko hannuwanta tare da zameta jikinshi yana kallon idonta ...
Bata fuska yayi .."Kin san me kikayi kuwa? ..
*Feedohm💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_61 to 62_*
"Uncle me nayi "...ta fada hade da fito ido waje ....yarda tayi tunani haka ta faru ..domin lumshe ido yayi na tsawon mintina ...
"Da kin kashemu da kin huta",....ya fada still idonshi a rufe ...
Rufe bakinta tayi tana fadin ."Uncle daga murmushi ...
Harara ya sake mata ...ta kwashe da dariya ...ita kanta yarda take dariyan so yake ya zame mashi matsala ...
Tada motar yayi yana fadin "please Hudallah".. ...sauran maganar ya makale a makoshi ....
Dariyan ta cigaba dayi cikin salo tana kallonshi tare da fadin ..."Uncle ...!!! Tare da Jan sunan
Motar ya kashe ba tare da ya kalleta ba ya fita ...napep ya tsayar ya zagayo ya bude mata kofar ...
1k ya daura mata saman cinyarta yana fadin ..."zo ki wuce Hudah mun hadu acan please " ...
"Uncle .."..ta fada a shagwabe ...
"Please Hudah .!!..ya hade hannayenshi guri guda yana Nuna mata napep
Ba haushi ya bata ba ...sae dariyar da ta masa ta hau napep din tana waigeshi ...sae da sukayi nisa sannan ya tada motar ya tafi gidan shima
Sae da ya rigasu zuwa gidansu...yana zaune falo ta shigo tana kwalawa Maman kira ...
Harara ta sake mashi sannan ta zauna still tana kwalawa mamanshi kira ...
mama ta fito tana fadin. ""Wannan kira haka Huda sae ko fasawa mutun kunne "
"Mama na gajine mai napep din da ya kawoni zagaye yayi Dani" ..ta fada tana kallon Uncle din Wanda shima tunda ta zauna ita yake kallo ..
"Yo garin ya ? ...ba tare dakuka taho dashi ba ...!!
"Mama tambayarshi dae... har fa mun taho daga na mashi dariya shine ya saukeni ya tare man napep yace na taho ...!!
Mikewa yayi ya shige ciki ba tare da yace komae ba ...mama kuwa dariya ta masu ..sannan Hudah ta mike suka shige ciki ...
••°°••
Kwanaki na kara ja....soyayya sossae ake tsakanin Hudah da Shehu da kuma dad dinshi ...
duk sun dauki son duniya sun daura mata ...Dad address din gidansu wata kawarta ta bashi ...duk lokacin da yace zaya to sae ta shirya ta tafi ....
Lokaci guda ta gama rikitasu ....Barister Shehu yace mata yana so suyi aure a wannan shekaran ...
Ce mashi tayi "bara ta iya auren mai mata ba Wallahi sae dae idan zai saki matanshi sannan zata yarda ta aureshi ..!!.
Kamar ta mashi asiri yace ya yarda zai saki maryam din yau ....Ita dae bata ce mashi komae ba sae murmushin da ta mashi ...
Ranar da ya saki maryam din ranar yazo gidansu lubna gurinta ....
Da kyar dama uncle Mahmoud ya barta ....bayan sun gama firansu ne ta rakoshi ....ko a wajen janta yake da fira sam idan yana tare da Sa'adah baya so ya rabu da ita ....murmushi kawae take mai cike da ma'anoni daban daban ....Karar motar Uncle Mahmoud taji ta juya da sauri tana kallonshi ...Ji tayi numfashinta na Neman barin jikinta ..da kyar ta tsaida natsuwarta guri guda.....
Kallon kallo suke su duka ukun ....wanda barister shehu yafi maida hankalinshi ga Barister Mahmoud ...Hudah kuwa dukar da kai tayi kasa
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm*💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_63 to 64_*
Ba tare da yace komae ba ya figi motar ya koma cikin gida kamar zaya tashi sama
Barister shehu ya saki ajiyar zuciya yana fadin ...
"Kin san wancan ne Sa'adah ? ...
Girgiza mashi kai tayi tana murmushin yake .. "
"kai ka sanshi ne ? ...ta tambaya tare da kura mashi ido
" Yeah ...da gurin aikin mu daya ..Don shine ma babban mu ..but yanzu ya bar gurin aikin for morethan 5years ban san inda ya koma ba ...amma naga yana maki wani kallo ...ko ya kyasa ne ...?
Murmushi tayi ba tare da tace komae ba ...
" Kwalelenshi ...Sa'adah sae Shehu,! ...Ya fada yana murmushi ...
"Jiya munyi magana da dad ...yace zaa turo gidanku ...!!
Ba tare da tace mashi komae ba sae juyawa da tayi tana daga mashi hannu ....
Dakin Lubna ta fada tare da fashewa da kuka ...
"Damsel menene ? ...wani abu ya maki ...ko cewa yayi baya sonki ....please kiyi magana mana !!! ..ta fada a rude tare da rike kafadarta ...
"Uncle Lubna ...Uncle ya ganni da mutumin da ya fi tsana a duniya ....!!! ..ta fada cikin kuka ...
" Ina ya sanshi Damsel ? ...ya akai kika san baya kaunarshi ...? ..shin uncle din ya maki magana ne ? ...
"I know everything a tsakaninsu lubna ...wanda shi kanshi uncle din bai san na sani ba ...!!!
"Kinga damsel kije kiyi magana da Uncle din mana ...may be ma shi bai dauka da wata manufa ba ....!!
Ba tare da tace komae ba ta dauki zunbulelen Hijab dinta ta saka sannan ta fita cikin sanyin jiki ...yarda taga yayi parking din motar sae da gabanta ya fadi ....
Tana shiga falon ta iskeni tsaye hanne na tsugunne sae uban bala'i yake mata .....fuskarnan tashi jawur kamar an saka mashi ruwan zafi . ...
bai bari ta shigo sossae ba ya shakareta tare da wurga ta saman kujera ...kafarshi yasa ya take mata ciki ...Uban ihu ta sake tana hawaye ...
"Kinsan Uban waye kike tare dashi !!! ...ya fada cikin tsawa ...
ihu ta sake ta kasa magana saboda wuyanta da ya shake ...hanne ta taho tana rikeshi tare da kuka ..
"Dan Allah ka barta " ...kar ka kashe masu yarinya " ...haba ya....Wani uban mari ya sake mata tare da hankadata gefe guda ...!!
"Bansan baki da hankali ba sae Yau Hudah ...kin san da uban wakike tare ...fada man tun yaushe kike soyayya da wannan banzan ....!!
Batace komae ba sae uban kukan ta take mashi .....dukanta ya fara yi yana tambayarta ...amma bata masa magana ba ...
Ganin kamar kara haukacewa yake yana sabbatu ya sata kokarin kwatar kanka ....fa kyar ta mike daga inda take ....da gudu ta ruga zata shige daki ...kafa ya saka ya tadiyeta ta fadi kasa da karfi ...bakinta ya fara fitar da jini ...still fizgarta yayi da karfi ta mike tsaye ya hadeta da karfi ...Hanne kuwa Kuka take iya ranta ...gani take kamar yazauce ....
"Wane irin so kake mata Yaya ...wanda yasa zaka iya kasheta don ta tsaya da wani namiji ? ...Hanne ta fada tare da rike mashi hannu tana kuka ...
ita da Hudah ya hade guri Guda ....Kamar garwashi haka Hudah ke ji a ranta ...barata iya daukar wannan dukan ba anymore ....bata san tana da karfi ba sae yau ....Hannun Uncle Mahmoud din ta rike tana kallonshi tare da angazashi baya da karfi ...
"ka daina Uncle !!! ....ta fada cikin tsawa ...tuni idonta ya bar zubar da kwalla ya bushe tare da sauya kala ...
Yarda tayi tsawar ya sakashi kallonta shima ...
"Ka dauka ban san Waye Barister Shehu ba ? ...to na sanshi ...sanin da shi kanshi wawan bai wa kanshi ba ...ko ka dauka soyayya nake dashi ...!!! ...ta kareshe maganar cikin tsawa ...
Daga Uncle Mahmoud din har Hanne tsayawa sukayi suna kallonta ...
"Mutumin da yayi sanadiyar rabani da Mahaifiyata ya rabani da yaya sa'ata ...a tunaninka shi zan so uncle ? ...Juyar da kanta tayi ga barin kallonshi . ..."ya ma yayata Fyad'e ..mukaje gidan Ubanshi yace ya sake mata idan yaso....a gaba suka wulakanta ta ...Anan Mamarmu ta rasu tsakar titi Uncle ...yaya Sa'a ta samu cutar HIV..shin kasan wacece yaya sa'atah? ..sannan kake tunanin ya ci bulus Kenan ? .. *_A DALILIN YAYATA_* na ke tare dashi ...hakan yasa na rasa Mamata ...Uncle shine ya kawo mana dukiyarmu ta gado sannan ya biyo dare da yan fashi suka sace *Harda kai ciki Uncle*!! .....ta fada tare da nunoshi da karfi....
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_65 to 66_*
Baya yayi tare da fadawa saman kujera yana kallonta ...
"Hudah ...!!... ya fada a firgice ..
"Quite Uncle !!! .....ko zan manta idon kowa baran mata idon mutumin da na fada jikinshi ba lokacin da Shehu ke kokarin dauki jikkar kudin ... .Da zoben dake hannunka na kara tabbatarwa lokacin da kazo gidanmu da safe Uncle ..idan har zaka lura har zoben na taba lokacin da ka daura hannunka saman jikina..!!! ...
Har inda yake ta tako tare da dukawa kasan kujeran hannunta saka ta dago hannunshi ta zare zoben dake jikinshi tare da sakawa cikin dusbin ....sannan ta dago fuskarshi ...
"Uncle aka pictures kadae ? ...ka shiga gidan marayu? ...haba Uncle ...na sani kana son Abbanka amma Uncle bai kamata kaso naka ka tarwatsa wasu ba ...kowa Uncle idan shi aka ma haka na tabbata hakan zai aikata ..Uncle na goge pictures din duka....!! ..Nagode sossae Uncle har yanzu baka canza ba a raina !!!
"Hudallah" ....ya fada ahankali ...
Hannunta ta daura saman lips dinshi tare da mikewa taja Hannun Hanne da tayi mutuwar tsaye tana kallonsu ....
••°°••
Soyayya kuma da mutanen bata fasa ba ...sae dae bata kara yarda wani yazo gurinta ba cikinsu ....
Kusan kwana uku bata ganshi ba .. .. tana so taje taga ko lafiya amma tana kunyarshi. . yarda ta dinga mashi tsawa ranar da abun ya faru sae take ganin kamar bata mashi halacci ba ...
A hankali ta dan kalli Hanne dake cin abincinta hankali kwance.....
"Aunty Hanne wae Uncle baya garin ne ko baya lafiya ? ...ta fada tare da dan goge hawayen da suka zubo mata da bayan hannu...
Ta dade tana kallonta kafin ta girgiza kai tace ..
"amma dae Hudah baki da zuciya mutumin da ya dakeki kamar jaka shine kike tambayarshi ...cab wallahi ni ko magana bana mashi ..."
Aunty baki san waye Uncle ba ko?.. ...ta tambayeta tana kallonta ..."Dan Allah ki yafe mashi kinji!!!
"Ke ai kin sanshi.. sakara mara zuciya anan falon ya gama cin ubanmu amma dan kina banza shine zakice na yafe mashi..." ...ta mike tare da shigewa daki abunta ...
Ita kam bara ta iya fushi da Uncle dinta ba..kwana biyun nan ma da bata ganshi ba Allah kadae yasan yarda take ji ...Uncle dinta ya riga ya zama wani sirri azuciyarta wanda ba kowa ne zai fahimta ba .. ...
mikewa tayi ta nufi dakinshi tare da turawa a hankali dauke da sallama.....
Zaune yake ya hade kai da guiwa ...kneeldown tayi kusa dashi tare da dafa kafarshi da hannunta ...
Ko bai dago ba kamshinta ya sanar dashi wacece ...
"Uncle "...ta kira sunanshi a hankali ..
Dagowa yayi yana kallonta ....da alama kuka yayi yarda idanuwanshi suka canza kala ...itama kukan ke niyar kwace mata ...
"Uncle me ke damunka ? ..ta fada a hankali ..
"Am sorry Hudah ...dan Allah ki yafe m"...
saurin toshe mashi baki tayi da hannunta tana girgiza mashi kai ....
"Dan Allah ka bar fadin haka uncle..wallahi baka da wani bashin yafiya da kake bani ..ni ce nake dauke da bashin alkhairinka a tare dani ...!!!
"Tashi muje Uncle ..please kawae ka biyoni Uncle am assure baka ci komae ba Uncle..!! ...hannunshi taja ba tare da ta jira abunda zai ce ba ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_67 to 68_*
Kitchen ta ja tana fadin "uncle zaune..!!
"Me zan dafa maka uncle ?
Shiru ya mata yana kallonta ..."Zakaci indomie ko, Na dafa maka irish da sauce? ...
Shiru ya mata ...juya idanunta tayi tana turo baki .."Uncle su kadae na iya fa !!
Dan murmushi ya mata ba tare da yace komae ba ...
Attarugu da Albasa ta mika mashi tace yayi mata grinding dinsu ....irish ta dafa sannan ta hada mashi sauce da taji albasa da kifi busasshe sae kwai ....
Lallabashi take tana so ya saki jiki da ita kamar da ...bayan ya gama ci ta hada mashi ruwan wanka sannan ta fita ta barshi ...
••°°••
Tana ganin ya tafi office ta cewa Hanne zata je ta dawo ....general hospital ta nufa ...direct dakin da masu karbar maganin HIV ta nufa ...duk da baa barin marasa cutar su shiga da yake sirri ce ...sae da ta ba masu tsoron gurin 20k suka barta ta shiga ta zauna tana kallon yan matan dake zuwa karbar maganin ...
Da sauri ta bi bayan wata yar kyakykyawa bayan ta fita daga gurin ..sallama ta mata ta amsa tare da juyowa sukayi musayar murmushi ...
"Mu dan samu guri mu zauna please muyi wata magana !!! ...huda ta fada dauke da fara'a..
Cikin asibitin suka koma suka samu wani guri safe da babu koma suka zauna bisa fararen kujeru ...
"Wani aiki nake so kiyi man sister please" ...huda ta fada tare da kamo hannunta ...
"Wane irin aiki yar'uwa? ...itama ta fada dauke da murmushi ...
" Ina so kiyi sex da wani mutumi ...please !!...ta fada a hankali ..
Da sauri budurwa ta kalleta ...zatayi magana hudah tace "please zan biyaki ko nawa ne " ..
Idanuwan budurwa suka kawo ruwa ...tace "me yasa Yar'uwa .. kema sun tabaki ne ? ...
Hudah tace "Sun man babban tabone"....idanuwanta suka ciko da kwalllah ..
Sauke ajiyar zuciya tayi ..."Zan maki ko ba kudi sister ...kin ganni nan wallahi yanzu banki ace duka lalatattun maza suna dauke da cutar da nake tare da ita ba ..kadan cikinsu ne na kirki ...Ina da saurayi har an sa mana rana dashi ..ana gab da bikinmu don har sadaki yakawo ..yace na rakashi unguwa ...wani gida ya kaini yace ai yanzu na riga na zama matarshi tunda har an bada sadaki ...ya yaudareni sossae har yayi amfani dani ...wallahi tundaga lokacin bai kuma zuwa gidanmu ba ...ashe yana dauke da cutar ..shine asalin lika man ita"..
Murmushi Huda tayi tare da fito da wayarta ta fara kiran number dad din shehu ...rejecting yayi ya kirata ...
"Please kana ina ..?
"Ina nan Guest House dina lafiya Prety? ...
"Zamuyi discussing wani serious issue ne yanzu ..."
"To bara bazo gida na sameki yanzu ..just ki bani 5mints ganinan zuwa Pretty" ....ya fada cikin sauri
"No bani adress din nima na fito ina hanya man .."..
"Ok pretty ...Sardauna estate No 6 dandume road ....'"
katse wayar tayi tana kallon budurwar ...
"Hudallah Ibrahim" ..ke fa ?
" Shafa'atu kabir" ....ta fada dauke da fara'a ...
"Please kinsan maganin da zaiyi raising fellings din mutun lokaci guda ?
Shafa'atun ta bude jikarta ta fito da wani abu ta mika mata .."Kinga wani nan nima banishi akayi na kaiwa hajiyarmu ..gashi " ...ta mikawa Hudahn ..
Dae dae kofar gidan suka tsaya ta kirashi tare da fadin Sun iso ...
Fitowa yayi da babbar riga da alamun ko dogon wando babu ciki ...
Suna Shiga suka zazzauna ya bude fridge tare da fito masu da fresh milk ya zuba masu a cup ya mika masu ..
"Prety wannan special visit haka ? ...bakuwa barka da zuwa . .!!.
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_69 to 70_*
Lumshe ido Huda tayi ..."sweetheart bakuwata bata shan fresh milk a bata coke ..'" ..j
Mikewa yayi yana fadin.."to to pretty " ...da sauri ta zuba abun cikin cup din dake hannunta tare da girgizawa ahankali ...har ya narke ...
Yana zama ta koma bisa hannun kujeranshi tare da kanga mashi cup din a baki tana murmushi ...yana kallonta har ya gama kwankwadewa sannan ta koma kusa da Shafa tana kallonshi ...
Mika yayi ...yana kallonsu ...kadan kadan take dan janshi da fira ...tun yana bata amsa har ya fara gyada kai yana mika ....cire babban rigar yayi ..da sauri ta kauda kai gefe ...ganin pant ne a jikinshi ...ga stick dinshi ta mike ...
K'yarma ta fara ganin ya nufo gurinta ....nannade siket dinta tayi ta kwasa da gudu tana fadin ..."Shafa'atu please kiji dashi ..!!..
A bakin kofar gidan ta zauna har lokacin gabanta bai bar faduwa ba ....
Kusan minti talatin tana jiranta sae uban tsaki take zabgawa bata ga abun dadewa a ciki ba ...
Cikin gidan ta koma ga mamakinta sae taga Shafa'atu tana soka mashi allura a hannun .da jini a ciki ...
Ido ta waro "Ke shafa'atu ya haka karfa ki kashe mutun gaskia" ...
Dan juyowa tayi tare da jefa mashi rigarshi saman jikinshi sannan ta dauki gyalenta ...suka barshi sae uban nishi yake taja hannun Hudah suka fita ...
Hudah ta kasa hakuri ..."Alluran me kika mashi wae ? ...
"Jinina ne na zuba mashi a ciki ...ko bata shigeshi da sex ba ta shigeshi yanzu ...sai nan da six month zata yi mugun kamashi ...karki damu ..dama muna haka .mafi yawancin abunda zaki saya gurin masu cutar suna zuba jininsu aciki wallahi ...!!!
••°°••
Suna zaune da Hanne tace ..."Hudah Yaya na nemanki ...!!
Ji tayi gabanta ya fadi ...bata san dalili ba ...ta mike ta zata tafi ji tayi hanne na mata dariya tare da fadin ..."bara ki shafa powder ba da lip gloss .?..
bata san dalili ba sae ta sami kanta da hararan Hannen ....
Har zata shiga dakin sae kuma ta shige dakinta ...samun kanta tayi da shafa powder har da janbaki sannan ta fito ...
Bata shiga can cikin master din ba sae tsayawa tayi daga dan falon inda kujeru suke tana fadin ...
"Uncle gani....!!!
Bai ce komae ba har sae da yaga ma sa shaddarshi light blue da akawa aiki da zare baki ....ya daura agogo sannan ya fito ...
Suna hada ido ta sakar mashi murmushi don ba karamin kyau kayan suka mashi ba ...
"Eyeh Uncle daurin aure zaka je ne" ...ta fada tana murmushi ...
Shima murmushin yayi tare da zama kujeran dake kallon tata ....
"Hudallah ."...Ya kira sunanta ...
" Na'am Uncle kayi kyau sossae kamar a saceka ..."....ta langwabe kai ..
"Ko"
"Huh ,baka duba mirrow bane ?...ta fada yana murmushi ..
" Sanin nayi kyau dinne yasa na kiraki na tambayeki .. Zaki auri Uncle din kin? ...ya tambayeta kai tsaye ..ba tare da tunanin komae ba ...
Da sauri ta rufe idonta da hannayenta tare da mikewa zata gudu ...carab ya cafke hannuta guda .. tsaye tayi ba tare da ta juyo ba ...mikewa yayi shima ya rike kafadunta ya juyo da ita ....
A kunnenta ya rada mata ..."Answer me please "....tsigar jikinta ta tashi tayi saurin matse jikinta gam tana kallon kafafuwanshi...
"Please uncle ka sakeni ..." ...ta fada a hankali ...
"Sae kin amsa man.. .this time biscuit din da kaina zan sawo maki yarda zaki ji dadin zama cikakkiyar matar Uncle dinki ..."...ya karashe maganar cikin zolaya ...
Fizge hannunta tayi ta ruga da gudu tana rufe bakinta .....
Daki ta shiga tare da fadawa saman gado tana mirgina ......pillow ta janyo tare da kankamewa ...murmushi ya sake yana kallonta ...farincikin da ya gani a idon Hudah shiya tabbatar mashi da tsantsar soyayyar da take mashi ...
"Ki daina Hugging pillow haka mana ' dani kika yi hugging may be da kinfi jin dadin sossae" ....ya fada cike da zolaya ....
Pillown ta wurgo mashi tare da lullube fuskarta da zanin gadon tana dariya ....yafi minti 10 yana kallonta sannan ya shiga gurin hanne ya mata bankwana tare da kissing dinta a baki ...for the first time kenan a rayuwarta ....sae yanzu ta gane Hudah haskene ga dukkanin gidan...
dakin Hudah ta fada tana zolayarta wae "amaryar Uncle" ...kallon mamaki Ta bita hannen da shi a tunaninta zatayi kishi sae ma taga kamar tana cikin farin ciki da abun .
Mahmoud kuwa gidan liman ya wuce...da yake duk wani abun Huda sae ya gaya mashi ....magana suka je Sukayi .. liman yayi farinciki sossae da jin Mahmoud din zai auri Hudah ...ce mashi yayi duk lokacin da ya shirya yazo a saka rana ....
Duk da bata da kowa ..amma duk wani abun alada sae da Mahmoud ya kawo aka saka rana wata 8 ...ba yarda Mahmoud din baiyi ba akan a barshi wata biyu ...amma liman yace " So yake yama Hudah duk wani abunda Uba kewa diyarshi ...nan da wata takwas yake tunanin kudinshi zata su fito don Haka yayi hakuri ya jira.". ....
Ba yarda Uncle Mahmoud din ya iya haka aka barshi ...Hanne ya gaya mawa..Sae a gurinta ma Hudah ke ji ...
••°°••
Barister Shehu na gida aka bugo mashi waya wae shagonshi na zinarai wuta ta kama ...ba'a samu aka fitar da komae ba duk sun narke ....
Sae da ya kwanta asibiti kwana 8 sannan aka sallamoshi ....Hajiya tayi ta wahala dashi don dad yanzu hankalinshi yana ga Hudah ....ko ya kirata waya bata dauka sae ta ga dama ...sannan yayi nacin yazo gidansu ta hanashi .....
Bayan an sallamo shi da gardadin a guji abunda zai bata mashi rai saboda yana da ciwon zuciya ga kuma hawan jini ...Part din hajiya ya koma ...dama safina na can tunda ya saki maryam ....
Da marece ya shirya yaje gurin Hudah ...satar hanya tayi ta iskeshi gidan su lubna ...
Yana zaune saman kujera duk ya rame ....ta dan kalleshi tare da kau da kai ...
Yana ganinta ya mike har kyarma yake ..don kwana biyun nan da baya ganinta sae yaga ta kara wani bala'in kyau ....
B'ata fuska tayi kamar zatayi kuka
....Tana gaidashi ....
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
_Na rigaya na sadaukar da wannan book din ga exclusive da babu abunda zai hanani sadaukar maki da wannan page din Sweet Farida ... Amma duk da haka ina maki fatan alkhairi tare da addu'ar samun zuri'a ta gari ...._😘
*_70 to 71_*
"Bakomae ."...ta fada tare da kawar da kai gefe guda tana matse hawaye ....
"Ya zaki ce ba komae damsel ....Allah ki fada man meke faruwa ne ...indae ba so kike nima nayi kukan ba ..!!..
A hankali tace ..."ina yaron da na aiko farkon zuwanka nan gidan ya shigo da kai....?
"Eh na tunashi ..wani abu ya sameshi .?...
"Eh ..ya samu neotrophy ne _ita kanta bata san abunda kalmar take nufi ba ..jikin kwalin sabulu taga neotrophy din_ ...shine muke so mu fitar dashi india a masa aiki ...ga dad baya nan ...bama so mu fada mashi saboda yana da hawan jini ...to kudin ne sun tsaya cak ...ban san yarda zaayi ba!! ....ta fada tare da goge kwallah da suka zubo mata ...
"Haba damsel akan kudu kike kuka ...duk da shagona ya kone bayan na gama zuba dukiyata hakan bara ya hana na samo maki kudi ba duk inda suke ....nawa ne kike bukata ? ..
"ka barsa sweetheart" ...ta fada a hankali ...
"No dan darajar Allah ki fada man nawa kike bukata ...."
"Kudin na da yawa fa ...ka barshi kawae nagode!!! ....
"Aa dan Allah wallahi ko nawa ne zan baki !!....
"ok 20m "....ta fada tare da kura mashi ido tana karantarshi ...
Cikin sauri yace ..."ba matsala damsel insha Allah zan kawo maki zuwa jibi .....
"Ina zaka samesu bayan kace shagonka ya kone " ....
"Takardun gidan da muke ciki yana hannuna ...zan sayar dashi ba da sanin dad ba ...na tabbata nan da one year na tara kudin sae na mayar masu da kudinsu na karbi gidan ....ba tare da kowa ya sani ba !!!!
tasowa tayi tare da kissing nashi a goshi sannan ta koma suka cigaba da fira ....
Bayan ya tafine ta kira dad dinshi tace tana bukatar 20M ...tana so ta sayi mota da dan karamin gida ..saboda friends dinta sun fara mata gori cikinsu itace batta da mota da gida ....suna gama wayar ya mata transfer kudin da yake akwae su ...
••°°°••
So take ta tashi tayi inserting farin pure miskin da lubna ta bata tun da aka samata rana tace duk one month da ta dinga inserting...satar kallon Uncle din tayi taga ya maida hankalinshi ga news yana kallo ....Hanne dama ba gwanar fira bace ...ya shige daki abunta..
Mikewa tayi da sauri tare da fadawa daki ta shige toilet ta dauki cotton kadan ta dangwalo .....wani uban ihu ta sake tana dire dire ...
Da sauri ya shigo dakin yana kiranta ...ganin tana toilet ne ya sashi tsayawa bakin toilet din ..
"Hudah .....menene ?
Kokarin kunna heater take ta kasa sae uban ihu take tana tsalle ...
"Na shigo Hudah? ....ya fada a hankali ...jin ihun nata yayi yawa ...
bata bashi amsa ba ta cigaba da ihunta ....tura toilet din yayi ya shiga da sauri ....kwalbar miskin ya gani da cotton din da ta dangwalo ...ita kuma tana gefe sae uban ihu take ...
Ko baa fada mashi ba ya san abunda takewa ihun ....duk da ta bashi tausayi amma dariya yake mata ....bai ga wanda ya sakata ba kilbibi ne irin nata .....
Cikin kuluwa da dariyar da yake mata ta juyo tana hararanshi tare da watsa mashi ruwan sanyin da ke cikin bucket ....
"Ba komae kije da zafinki .....see ..naga wani abu irin wannan a gurin wata mata idan na fita zan sayo maki sae ki kara sakawa ..tunda naga kin girma da yawa ....!!! ...ya fada yana dariya ...
Da sauri ta juya ta hade kanta da bango cike da kunya ...ga azabar take ji ...Allah ya isa kuwa ta jawa Lubna yafi cikin kwando .....
Kamar yarda barister shehu ya fada ...haka ta faru ...gidan da suke ciki ya sayar a tunaninshi nan da shekara daya idan ya samu ya maida masu gidansu ...da marece ya kawo mata kudin ....ba tare da sanin kowa ba ta rabasu uku ...kashi daya ta kai gidan marayu akan Allah ya kai ladar kabarin Yaya Saa ....sannan gudan ne ta kaiwa Aunty hanne tace ta boye mata ....sauran gudan kuwa ...babban masallacin garin ta kai tace a gyara shi sannan a sayi duk abunda zaa bukata ....ta sadaukarwa Yaya sa'a da mamanta sae babanta .
..
••°°••
Barister Shehu ne ke fada mata dad dinshi baya lafiya ...45%t fever ...ga diarrhea sossae ......"Allah ya sawake ta fada ."...!!
°°••°°
0 comments:
Post a Comment