Wlh ko ni nayi naqudarki se naci ubanki...... shegiya dangin matsiyata,,,kai kawai tasadda qasa tana jiran hukuncin Amma,,,,wuyanta ta jawooo tare da jefata ga wani center table na gilas gefen girarta ya datse sedai beyi wani jini sosai ba,,,, tasake janta tayi hanyar tsakar gidan tadinga jibgarta kad'an take kiran Allah! Allah! Allah,,,,seda amma taga ta nuna da duka sannan tace maza kitashi ki goge mun d'akina marar Albarka! jikin ta ba qwari ta miqe tana tangad'i tafara aikin da Ammah tasanyata,, bayan ta kammala ne tazo bakin famfo tazauna wata Azabtacciyar yunwa takeji kamar taci babu,, idanuwanta sunyi jajir sabida nau'ukan Azabar Rayuwa! kukan dayake rahama gareta yau tanema tarasa hakan yasata tasbihi ga ubangijin muh'd! dan yau da ana aman rayuwa Ahuta da ta amayar da tata rayuwar koxata samu sa'ida,,,,,,tana cikin wannan yanayi Amma dan rashin imani tace taje ga kaya can toilet ta wanke mata,,,,,jaleelah dakanta ta tausayawa kanta,, ta d'ago ta dubi ammah qwallah mai wuyar bayyana ta ziraro "A" idaniyar ta tahagu, sannan tace thom! wani ukku ukku take gani ta miqe tayi inda amma tace! kan taqarasa qarnin jinin haila ya ziyarci ilahirin sassan jikinta baya tayo da sauri,,,amma tace shiga wandunannan xaki wanke kuma ki tabbatar sun fita,,,,,jaleelah duqawa tayi tana wankawa kan kace kwabo amai mai cin xuciya ya qwace mata tun tana durqushe har takai kwance kasancewar ba komai cikin hanjinta wahala kawai take,,,,duk gumi ya wanketa da jigattaciyar shed'a sama sama,,,,,Amma na tsaye kan bakarta se jaleelah tawanke kayan,,,,bayan wani gajeren hutu tace tashi kisoma bakiga komai ba,,,! haka tasake jinginawa jikin bango tana wankewa seda sukayi yadda Amma keso sannan tasamu sa'idahh!...Adaddafe tabaro toilet d'in tazube mazaunar ta tad'azuuu tana haka har magrib ta doso! qarfin hali tayi tayi alwalah tajah jikinta zuwa d'akin da akace tashiga,,,da zaune tayi salloli da kyar! kana tafito waje busashen biredi ta hango har jikinta ke b'ari tasoma ba hanjinta,,,tass ta cinyeshi tareda ba famfo amana ruwa tadinga sha har sai da gefen cikinta ya tamke! daga bisani tabar gurin da kyar takai d'akin tasake xubewa tana saqa rayuwa da tsakiyar da bawanda yasan yaxatakaya Se Allah,, tana shafa mararta da tahad'iye da cikinta A fili tace ko meye duniya zata d'auki Abunda zaifito cikina? sarrrr taji qwallah batadamu da sharewa ba tasake cigaba da tunaninta har gwanin iya sata yasaceta wato bacci,, bayan sallar Assuba bata kwanta ba,, d'auki daneman haquri mai kyawo take nema ga ubangijin da yayimata ni'imar rayuwa mai cike da qalubale,, dan tariga tasan cewa Abunda tagani wata tafita ganinshi,,,,tana haka Abba yashigo yace jiya ammanku tace kina jin jiki ko? kai tad'aga Alamar eh! nisa yayi yace ga alama kinajin yunwa kinci Abunci kuwa!a'a tafad'a,,yad'ora dacewa kinsha maganin da nabta tabaki,,,,?shiru tayi Alamar da magana! seda yadubeta yace bata baki ba ko? kai tagirgixa Alamar eh! miqewa yayi da alamar fushi yafita cikin tsawa yace na lura bakida imani rabi,,,!banida imani? eh bakidashi yanxu yarinya ba lafiya ankawo maganinta kin riqe kuma harda dawowa kice kinbata gwanin tausayi? kin hanata Abunci wace hujja kika tanada Aranar da babu qarya acikinta? ko kinmanta Allah yanakallonki? tsakki tajah mai sauti tare da cewa Ni nazata wani xancen kirkine wlh,,tayi gaba,,,Abun karyawa ya d'iba ya kaimata kana yace jaleelah kidaina kuka nayi imani wannan qaddara ce,, bana cikin iyayen da ke hantarar y'ay'ansu akan qaddarasu,,sedai na tayasu kuka da baqincikin Abunda zaizo yadawo nasani duniya akwai mutane da yawa masu son canza mummunanr qaddarar su amma wannan zanannen rubutu ne daga Alqalmin alqalin kowa zanso ki manta da Abubuwan da suka faru kinji,,,,,! cikin rishin kuka tace nayi tawakkli kuma ba qaddara ta nakewa kuka ba! lumshe idon sa yayi kana yace Allah ya sassauta mana yafita,,,,,,bayan kwana ukku munauwar ne xaune gaban Abbah yayi lamooo kamar mutumin kirki daga bisani yace Abba har yanxu bawani labari akan daudane? kuma binciken da naqara samu ance tun tana shekara goma ya kauda budurcinta! d'agowa yayi tare da cewa munauwar na tsaida binciken kowa,, yarage naka tawakkalin zama da itah ko rabuwa bazan shiga haqqinka awannan karon ba! se nake gani kamar tirsasawar danayi ne Allah yayimun wa'axi dan yazama ixina gareni,,,,shiru yayi sannan yace zanyi shawarar Abunda yadace Abba kuma karage damuwa kasanya aranka haka Alla yaso,,,,,, gaskiya ne munauwar Allah yayimuku Albarka! ameen yafad'a tare da fita,,,,,jaleelah kam kullum gwara jiya da yau ta feqe tayi fari marar ma'ana qassan jikinta duk sun bayyana tana duqe tana shara munauwar yashigo,,bataji motsinsa ba bare ta tsaida ji kawai tayi an dannah mata dum dum abaya seda taga wani duhu ta dunqule gefe d'aya mararta ta wani juyawa da Azababben ciwoooo kan kace mi jini ya sauko zuwa qafafunta,,,,, wurgi yaqarayi da itah ya wuce Abunsa! tsawon awa ukku tana jin tamkar bayanta da mararta da farjinta zasu cire batare da kowa yasan tana gurin ba can Allah yakad'o Abba arikice ya qwallawa rabi kira tare da rungumata jikinsa......
fafan khairi ga kowa naqara maku ai ko?
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀2⃣2⃣
_Saqon fatan Alkhair nake aikewa ga mutanen Brilliant writer's masu dattako da riqon amana Allah yayimaku jagora Abadan bazan manta dakubu! kullum taken ku goda ne masoyanku na ranku,maqiyanku basa gabanku tasalima fatan shiriya kukeyi garesu! gaskiya inason brilliant me matasan kirki💋_
⬅
Arikice ya qwallawa rabi kira tareda rungumeta jikinsa.....be jira fitowar ta ba yasanya jaleelah mota da kansa ya tuqa zuwa Assibitin qwararru dake jahar sokoto,,,,,cikin gaggawa suka amsheta akafara bata taimakon gaggawa! cikin tausayin Allah anceto cikin jikinta dake barazanar zubewa ta hanyar amfani da hanyoyi daban daban! kana suka nemi ganin Abba,,,suka shaida masa gaskiya yarinyar nan nada buqatar hutu da Abunci mai kyau kuma inbahaka ba za'a iya rasata daga ita har Abunda ke cikinta,,,,,hawaye yaji bashiri yashare tare da cewa insha Allah zanyi bakin qoqqrina...ya miqe yatafi,,, kwanan ta ukku hospital Abba da Ahamad kejinyarta Amma ko leqe batazo ba, Abunci ma nasiyarwa sukeci,,,,jaleelah kuma se anyi da kyar take kurb'a madara... bata son motsin mutane tafison shiru,,,,bayan wasu kwanaki aka bata sallamah suka koma gida,,,, amma batasan da zancen cikin jaleelah ba se yanxu da Abba ke koro mata bayanin dole jaleela ta huta,,,,hankalinta yayi mugun tashi yayinda tarinqa zargin kanta da sakaci? kana tamiqe tace Allah yasauwaqa,,,,Abba maganin jaleelah ya nunamata tare da cewa duk Abunda take buqata tasanar mashi! ita kuma amma nashiga takira d'anta tace yasan da zancen cikin jaleelah? murya d'ashe yace nasani amma bugun da namata na tabbatar yazube,,,, be zubeba munauwar! Amma kamarya bezube ba? bayan naga jini na shawagi aqafafuwanta! nisa tayi tace kwantar da hankalinka in sunsan wata basu san wata ba zanyi komai dan ganin na juya hankulan mutane koda ko kai da d'an bakuda banbanci,,,,, yehhh ammana shiyasa nake bala'in son ki! suka katse line. haka rayuwa tacigaba,, kwanaki goma shatakwas kenan babu wata hantara tsakanin amma da jaleelah sedai jaleelah takanji ajikinta akwai wani Al'amari da amma ke shiryawa,,wani lokacin takawar da zancen da isti'azah haka rayuwa taci gaba,,,, cikin jaleelah yakai wata hud'u kenan! tasamu tafara cika irrin namasu juna biyu, duk Abunda tasooo shi abba da Ahamad kemata, sedai amma da munauwar kallon kar tasan kar suke masu,,,,yau takasance lahadi kowa yashiga bacci dan sule salin dare yatsala jaleelah na kwance da kayan baccinta bata yane jikinta ba saboda ni'imar zafi da Allah yasaukar cikin yanayin bacci tadinga jin kamar ana soka mata wani Abu daga bayanta! firgigit ta miqe zaune setaga Nasine mai gadin Abbah wasu ruwa natafitar masa ga penis runtse ido tayi tare da qwallah ihuu cikin azama yadafe mata baki yana neman yimata rumfa daga sama muryar amma tadinga tashi tana wayyo kwarto wayyo kwaro! Abba da gudu yazooo yana inah? tana nuna d'akin jaleelah,,, dattijo jikinsa narawa ya Afka kawai nasi ya qwallah ihuuu yana cewa wlh Abba itake gayyato ni bani nake kawooo kaina ba! baqin ciki da tashin hankali sunfi qarfin barin Abba da numfashi zuuuu ya rafke qasa somamme! aka kira su Ahamad da munauwar cikin daren jaleelah ta had'e da bango kuka kawai take rerawa tarasa da wanne zataji,, shikuwa Ahamad jibgar nasi yake yana neman tasge penis d'inshi can kuma Abba yafarka yarasa mezaice sbd baqinciki,,,,, Amma kuma kuka take meban tausayi kowa yakasa me zaicewa jaleela dan yau Allah ya toni Asirinta,,,Ahamad cikin rishin kuka yace jaleelah kin ban mamaki da bangani da idona ba bazan yarda ba! muryar ta rawa take sosai tace wlh Ahamad bantab'a aikata zinaba,,bansan dad'in namiji ba bare nayi,marmari had'uwa dashi! qarya kikeyi fasiqa munauwar yajefo maganar! Abba kuma bazai juri kalamanta ba dan yanda yakeji kamar yasoketa tamutu kowa yahuta,,,ahmad shiru yayi kana cikin muryar kuka yace jaleelah kinyaudari kanki,, tace cikin wata murya Ahamad kaima,kayarda na aikata zina? bayan jinake inna rasa shaidar kowa bazan rasa taka ba!? Ahamad kar ka zargeni dan Allah se kuka ya qwace mata .....
[13/02, 20:46] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀2⃣3⃣
_Uhum uhum Agaskiya bansan yadda zance maku ba masoya littafina,Abun yayiwa nabi kowane sharhi nayi godiya sedai kusani ina tare da ku inajin dad'i kuma hakan kullum qara qarfafa mun guiwa yakeyi,,,sedai kumun Afuwa wlh ko read more 1 daddafe nakeyin sa,,sbd rashin lokaci mai kyau Asmeenat takuce! nasan dayawa sun sani in ina free x3 nake sakin page's kowace rana_
WANNAN NA BESTY NA NE! SURAYYAMS FATAN ALKHAIRI NAKE MATA KOWACE SAFIYA😊
⬅
Ahamad kaima ka yarda na aikata zina? bayan jinake inna rasa shaidar kowa baxan rasa takaba!? Ahamad kar ka zargeni dan Allah se kuka ya qwace mata.... d'agowa yayi yace jaleelah yakike kallon kowa bagidaje? ko kina so kice idanuwan mu qarya suka nuna muna!? seda tajah majina tace cikin shashhsheka Ahamad gaskiya suka nuna maku Amma Allah shaida ne ban aikata Abunda zuciyoyinku sukayi ammana ba! tasalima jinsa kawai nayi Abayana! d'agowa yayi suka had'a ido jijiyoyin kansa sun fito rad'a rad'a yace meyasa baki qaryata shiba? lokacin da yake iqirarin ke kika gayyato shi,,sai yanxu da bayanan? sadda kanta qasa taqarayi hawaye na d'iga kna tyels tace duka hankalina yabar gangar jikina lokacin dayake maganar! cikin rashin yadda yace yanxu kinaso kice dani hankalin yadawo? d'agowa tayi suka had'a ido tace Ahamad Allah zai bayyanah gaskiya, bansan me zance kayarda dani ba! dan banida qwarin guiwa ko hajja da zan killace kaina! sedai nasani wannnan guntun zamane, watarana zamu had'u gaban Allah lokacin da baki baya magana, dan nayi imani wata shari'a se lafirah! hawaye yaji sun kub'uce masa jikinsa yayi sanyi lau, yace hakane wata shari'a se gaban Alqalin dake zartar da hukunci kan gaskiya,,,kuma namaki alqawari xanbi sawun nasi dan ganin an goge maki wannan baqin fenti,,,,hawaye cike da idonta tana riritawa kar suxubu tace Ahamad kayarda ban aikata ba ko haryanxu kana kan bakarka? hannu yasa yashare hawayen sa yace na yadda baki aikata ba jaleelah! yamiqe yafita,,,,haka dare me baqi da gumurzun d'aci yashigewa mutane ukku! jaleela, Ahamad,da Abba!!! bawanda yasake komawa bacci,,,yayinda buqatar Amma da munauwar tabiya!! bayan wayewar gari jaleelah kwance kawai take batasan meke mata dad'i ba zahiri bata iya ban banta fari da baqi! Abba kuma yakasa kai ko ruwa bakinsa se hawaye da ke zubo mashi akai, akai yana sharewa tare da maimaita lahaula wala quwata illah billah! haka ma Ahamad neman mafita da sassauci yake nema mata ga mai juyar da Qunci ixuwa farinciki! Amma kuma tabada maqudan kud'i ga nasi dan yabiya mata buqatarta taqara jaddadawa munauwar lallai akaishi hospital dan jiya yasha duka,,,,haka rayuwa tacigaba ba wani sassauci sega Allah,,,jaleelah komai yajagole bata samun wanda zata gayawa magana se zuciyarta Ahamad ma Abba yatsaida huld'arsa da jaleelah shi aganinsa horon ta yake dan yayi imani in yakoreta duniya zata zargeshi da rashin Adalci duk da cewa basu san baqin tambo da tayiwa zuciyarsa ba? lokaci yajah kwanci tashi Asarar me Begen Duniya, cikin jaleelah yakai watanni shidda... bata fita Awon ciki bare Agane cikin na cikin qoshin lafiya ko a'a!? halayen da takeyi se godiyar Allah dan kamar tafara zauceawa!!!! yau jumu'a tana zaune ta had'iye kai da guiwa kamar yadda tasaba,, cikin ga yayi tsini gwanin ban tausayi! sega Ahamad yashigo kallonsa kawai tayi tasaki murmushi amma batayi masa magana ba! ransa ya sosu matuqa da yaga yadda jaleelah ta canxa hlitta! da kyar ya kalato murmushi ya azawa fuskarsa yace yau jaleelah ba gaisuwa? shiru batace komai ba se idooo da ta gwale mashi!, nisa yayi yakawar da zancen da cewa kina zuwa ANC kuwa! nan ma dai kam shiru! idanuwa yazuba mata cikin tsantsar kulawa yace jaleelah fushi kikeyi da Amininki yaqarashe kamar me farautar kuka! nan madai babu motsi,,,,,,,da yagaji da magiya se yatashi yayi tafiyarsa da saqa Abubuwa biyu aransa fushi takeyi kodai tafara tab'uwa? dahaka ya kai gurin da Abba ke zaune! fuskarsa babu haske yace wai Abba jaleela nazuwa ANC? kai yagirgixa Alamar a'a? Ahamad kamar zaiyi ihuuu yace Abba yakamata taje bamusan ya Abun zaizoo ba?! cike da kulawa yace Ahamad in nakauce karinqa tunasar dani qwaqwalwata bata gane komai ni har namanta dawani Awon ciki! se kazoo kaje da ita gobe,,, cikin girmamawa da jin tausayin Abba yace thom allah yaqara gabaci kana yatafi...haka kuwa akayi bayan wayewar gari da sassafe yazoo yatafi da jaleelah,,,,tafe suke yana ta zabga tambayoyi amma iyakarta ido ko kuma murmushi babu dai magana har suka isa hospital! sunyi fad'a sosai kafun suka amsheta kuma da yawa sun tausaya mata ga qarancin shekaru ga jaza'in duniya daka dubeta kasan sun zauna,,,,, photon cikin Aka d'auka wanda result da aka samu yabada y'an biyu ne Acikinta kuma qafafuwan su ne qasa maimakon kanunsu,,,,,,,,
[13/02, 20:46] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀2⃣4⃣
⬅
result da akasamu yabada y'an biyu ne A cikinta,, kuma qafafuwan sune qasa maimakon kanunsu,,,,,,sannan infection yamata yawa, dole Akwai buqatar saka mata hannu arage wannan qazantar,,, haka kuwa akayi Dr. Ruqayya ce ta umrce ta da shiga wani sirrantaccen d'aki bamusu tashiga, bayan tashiga tace ta hau gado nan ma dai bamusu! kana tajanye zanenta tare da shaida mata zata sa mata hannu ta d'an ware qafafuwanta! haka kuwa jaleela tayi ruqayya seda taji ciwo aranta ganin inda take son sa hannunta yayi siranta da yawa amma yata iya wani ciwoo ke fidda wani! ta tosa hannunta! amma jaleela ko uhumm saboda tawakkali seda taji azabar ciwooo sannan tacije leb'e tace washhh! haka ruqayya tayi qoqarin rage mata qazantar daga bisani tace ta tashi anqare! tare ta taimaka mata tasauko qasa,, idanuwanta sun canxa Alamar taji zafi, cikin tausayawa rayuwa tace sannu kinji jaleelah? kai tad'aga Alamar amsawa! harsuka fito waje! magunguna qarin jini da kuzari da cin Abunci aka rubuta mata da wasu shawarwari... kana suka kira Ahamad suka bashi shawara sukace bayan sati biyu Adawo da itah.....tun cikin hospital ya tsaya yasiya mata magani suka d'au hanya zuwa gida,,, har sun kusa kaiwa yayi parking gefen titi ya tsareta da idoooo, yace jaleelah shirun nan naki d'agan hankali yake! me yasa kike qyamar yimun magana? ko kuma kina ganin ina cikin masu bada gudummuwa wurin... be isa fad'a ba yaga hawaye sun wanke mata fuska bakinta narawa tace Ahamad ban tab'a zargin kowaba akan rayuwata se dai tsoron kaina nake da kaina dan gani nake babu alkhakri tare dani,,,, qaddarata shafar duk wanda na rab'a take! tana sa masu yawan shekaru zubda hawayesu,,, seda tanisa taciga dacewa kaima da zakabi nawa kayi nesa dani har lokacin da Abu biyar da nakewa kaina wasu zasumin se kayo kusa dani domin kullum lokacin nakejira nasan zaixo labarina yazama tarihi ga masu yawaita ma qaddarar su kuka!!! shiru yayi yana sauraren ta hartaqare kana yace ke Alkhairice jaleelah, kar kiyi magana akan gaibu, kar tsananin rayuwa yasanya kicire rai ga rahamar ubangiji ki fauwllawa masa lamarinki watarana zakiyi murmushi mai sautiiii! hawayewa tashare tare da cewa uhumm Ahamad ninasan me nake gani! kadai tayani da Addu'a ubangiji yatsare imanina, na mutu kan musulunci! ina kanyi jaleela Allah yakawo d'auki,,,,,ya tada mota suka isah gida, kana yabata maganinta tare da yimata fatan samun sauqi! tunda tashiga ta killace kanta kamar yadda tasaba,, gefen munauwar kuma soyayya shida khairat ba Acewa komai sun shagalta fiye da yadda d'an Adam ke tsammani, sedai Wata badaqala da zully ke shiryawa sbd tad'au Alwashi Aranta bazata bari kowa ya mallaki khairat ba se ita, taqara nanata d'aukar Alqawarin shidawa duniya cewa su y'an ta'addar Allah ne tahanyar Auren kahirat! duk da cewa Auren macce da macce yaxama ruwan dare dama duniya!!! haka dai b'angarorin suka cigaba da tafiya! yau laraba jaleelah ta tashi da zubar wani farin ruwa A farjinta da ciwooon baya me tsanani batasan waza tashidawa ya tallafeta ba,,Abu wasa wasa har takai bata iya motsin kirki,,,ciwooo takeji babu sauqi gumi dukkk inda take da gashi fita yake tayi jagaffff,, idanuwanta sunfito sosai har dare ya tsala takwana haka taqara wuni haka baci ba sha gazafin naquda! can gurin magrib Allah yabiyo da Abba sama sama yajiyo nishinta,,da Azama yafad'a! tausayi da wahala da take fama dashi tana sa hannu tana buga bango yasashi zubda hawaye ba shiri! sannnan yakirawo Ahamad da amma yace suxooo akaita hospital,,but qarfin hali irrin na Amma tace ai subari agani zuwa Ajima dan haihuwar tayo kusa da farko Abba be amunce ba se tasa kisisina irrin ta mata wai,,,,,,,,
kuyi haquri da wannan pls
[13/02, 20:46] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀2⃣5⃣
_Alhmdullah bini'imaty! maman nana godiya ba Adadi Allah yasaka da Alkhairi yaraya mana nannah akan hanyar musulunci! ummu hydar fatan Ana shagalin biki lafiya,,,💞_
⬅
Abba be Amunce ba tasa kisisina irrin ta mata.....wai da can da nan duka d'ayane tana ma jin qamshin haihuwa Ajira dai agani har inbata haihu ba,,jin Abba bece komai ba Ahamad yace hakane Ammah, Abba mujira muga hukuncin Allah kuma ko bakomai tafi mu sanin me ake nufi!! duban Ahamad kawai Abba yayi cikin tsanaki kana yace bawai naqi bin shawararta bane ko kuma rashin jiran hukuncin Allah, yarinyar nan qaramace kuma ita kad'ai tasan me takeji muje gun masana tunda buqatar hakan ta taso!! nisa yayi yace thom Abba bara na d'auko mota, sam Abun beyiwa Amma dad'iba dan takitsa ma ranta kisan Abunda yaso zuwa duniya muddin rayayye ne dan Alwashine da ta d'auka tsakaninta da Allah bazata had'a jini da talakka ba...ranta b'ace ta juya tayi tafiyarta! Abba ko Ajikinsa har Ahamad yad'auko mota,,,, sannan suka kama aka saka ta mota tana ta yarfa hannu tana rintsa ido,,,,,kana Ahamad yaja Ahankali har suka isa hospital, cikin gaggawa suka Amsheta aka d'ora kan gadon haihuwa! hannu aka fara sanya mata Abu yazoo kusa dan 8cm haiuwar take, suka d'ora mata N/S tsayin mintuna shabiyar! ga naquda kamar ahaihu babu haihuwar Oxtc Inject,,aka bata 2ml dan taqarawa mahaifar qarfi nan take Abun yaqara hauhawa da qarfi take nisawa amma gurin yayi kad'an, se kan yazoo yakoma nan take aka d'auko rezoor aka yankata J-shape Akace tayi pushing sosai, tayi amma bawani mai qarfiba dan baya iya fitar da yarooo! baby oil aka shafa mata tare da riqe mata perineal area wanda yaraba Anus da vaginal orifice ganin suna qoqqrin had'ewa... akasake cewa tayi nisa nan ma dai takasa gashi ji take kamar ranta zaifita Sbd zafin naquda,,,da Abun yaqici yaqi cinyewa dole aka d'auko wasu kuyafu guda biyu dan jawo yaron! haka aka ware qafafuwanta ba can ba! Aka tosa kuyafun gefe gefe na cikin farjinta aka d'an juyasu yadda bazasu tab'a lafiyar baby ba! hawaye kam ba'acewa komai "A" fuskar jaleelah Sbd bala'i da zogi irrin nafitar wani rai cikin wani! cikin nasara akasamu jawo d'aya babyn, bayan wasu mintuna aka sake jawoo wani jini ya goce kamar an kunnah famfooo ta someee! gyara babys aka farayi y'an mata biyu da ko Afarce basu baro jaleelah ba, suna cikin qoshin lafiya se kuka suke rerawa gwanin sha'awa aka basu vitamin K injection Akashirya su cikin fararen kaya da Ahamad yasiyo cikin kayan da aka buqata yakawo,,,,,kana suka koma kan u'war suka share mata jikinta da wurin da ta b'ata can ta farfad'o suka tosa wasu qwayoyin magani ukku cikin farjinta d'aya qasan harshenta dan su tsaida jinin dake fita! sannan sukabi da d'inki! daganan aka had'a tea mai kauri da zafi akace tasha ba laifi tasha kana suka bata yaranta! karb'a tayi tagani se hawaye suka wanke mata ganin basuda wata kama da zata d'aga yatsa tace munauwar babansu ne! hankalinta yayi mugun tashi dan da wannan shaidar tayi niyar d'aukar fansa ga munawar! ganin jikinta na rawa yasanya wadda ta amsar mata haihuwa amsar jariran kana tace meye ke damunki jaleelah!? shiru batace komai ba! juwa kike gani? shiru se ma jikinta da ke ta rawa kamar me Epilepcy (farfad'iya) kan tayi wani Abu se yawuuuuu da birkicewar idanu ya Afku! da gudu takirawo Dr. hamza dan ya taimaka mata ganin tana gudu haukace Ahamad yafad'a d'akin haihuwar dan yasan dagani ba lafiya qam yaqame ganin halin da jaleelah keciki shikuwa Dr.hamza dagudu yashigo cakkk yatsaya be masan me zeyiba dan jijjigar ta tsaya ta wani miqewa kamar gawa, cikin sanyin guiwa ya tab'a gefen nonota na hagu ya tabbatar tana da sauran numfashi! nan take sukayi amfani da Ambuback wurin ceto numfashinta! da aka samu ta farfad'o se ta qwallah wata qara mai gigitar da jin d'an Adam, tasake komawa gurinta! likitan jariran ya damqawa su Ahamad tare dq jansu gefe yace su bar kuka dan Allah be kamata ba matsayin su namaza, ana samun irrin haka dayawa, mata sushiga wannan yanayi becouse of phobia (tsoro) kamar suyi kuka sukace Dr. meye mafitar wannan matsalar...seda yanisa yace gaskiya ba aikin mu bane...
[13/02, 20:46] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀2⃣6⃣
_Fan's ina baku haquri akan alqawarin da nayi nacewa yau zankawo KUKANA63 thom wlh banasamun damar kawowa sakamakon baquwa danayi kuma kunsan yadda baqo yake da nauyi dafatr zakuyi mun Afuwa💞_
⬅
seda ya nisa yace gaskiya ba aikin mu bane..... but zamu turaku psychiatric hospital suyi maku Abunda yadace! cikin kad'uwa sukace psychiatric? lasa leb'ensa nasama yayi kana yace eh kuma bawani Abun motsin rai bane! kuyi haquri xata dawo normally in kunje,,,,,, Abba ne yace thom Dr. Allah yakawo mana d'auki! suka miqe tareda fita fuskokin su bawalwala, recovery room suka nufa jaleelah na kwance Alamar bacci, kana suka ma kanunsu mazauni gefen gadon! Abba qwafa yayi yanata jajinta lamarin Allah, yayinda Ahamad yatsura ma yaran idanuwan sa dake ta motsa baki da hannayen su alamar Abunci suke nema! hawaye suka ziraro masa ganin hardasu jarrbawar ta shafesu daga zuwansu duniya! muryar sa narawa yace Abba yakamata ayi masu hud'uba kan jaleelah ta farka ko zata iya basu Abuncin su! shima cikin d'arsuwar yanayi yace I masu hud'uba da hassana da usaina! bejirqa komaiba yatada kabbara ga kunnayen su yarad'a masu sunan kamar yadda Abba yaso! sannan ya Ajiyesu!har ukkun rana yaran basuci komai ba dan jaleelah bata farkaba! dole aka rubuta masu madara mai sinadaran vitamin's daban daban aka siyo, kana aka dama aka basu! sunsha gwanin tausayi kana Abba yariqe d'aya Ahamad yariqe d'aya,,,,can wuraren magrib ta farfad'o idanunta kamar su fad'o qasa kallo d'aya zakamata ka tabbatar ba lafiyaba! cikin sanyin jiki da jajinta Al'amarin zuci sukace sannnu jaleelah! kallonsu kawai tayi se kuma tabushe da dariya harda qyal qyalawa! daga Ahamad har Abba seda sukayi qwallar baqin ciki,suka qara imani d'an Adam bashida wata garkuwa da tawuce lfy, sannan suka kira Dr. yazo yaduba yabasu takarda da sa hannu... yace but karsu tafi da ita se ansamu wa anda zasu riqeta kasancewar tana iya cousing Road accident kafun sukai dan yanxu komai tana iya yi taga daidaine! da shawarar doctotrn sukayi amfani gurin samun ward server's guda biyu mata aka sanya ta mota kana suka d'au hanya,,,,,mintuna talatin suka kwashe kan sukai hospital! suna shiga suka yanka mata file na ganin likitah! kamar karsu zauna Abun jaleelah yabore da kuwace kuwace harta na nema tafi qarfin Abba da Ahamad so take kawai Abata dama tayi guduuuu,,,,ganin tana shiga haqqin dan dazon maras lafiya da ma aikata,, aka matseta ta qarfi akayimata valium injection ga jijiya! cikin mintuna da basu fiye biyu ba bacci yayi gaba da itah,,,suka zauna jiran akira sunanta..... misalin qarfe goma sha d'aya aka kira sunan jaleelah dikko Also dai dai wannan lokacin ta farka, but babu wani kuzari tare da itah! haka akajata har counsulting room kana suka zauna! d'akin cike yake da qwararrun likitoci kamar su psychology, psychiatric, sociology da duk wasu manyan masana akan sha'anin qwaqwalwa da halayyar d'an Adam,,, shiru d'akin yayi kowa na rubuta observation d'inshi akanta daga bisani aka tattare aka bama wani siririn likita dake tsakiyar su! gyaran murya yayi yace jaleelah yayajikin naki? tsaki kawai tayi masa,,,,yayi murmushi yace kin kyauta yanxu gaya mun ina na kike nan? hankalinta ta juyar gefe bata masan yanayi ba! natsuwa yayi yamaida akalar tambayarsa ga wanda sukazo da itah! cikin taushi yace Alh. bisa dube dube da mukayi tare da had'a bayanan mu guri d'aya mungane yarinyar ku tasami tab'in hankali tun wata 5 da suka wuce! mene? Abba da Ahamad sukafad'a suna qoqarin miqewa tsaye! gyara murya yayi yace ku zauna zamuyi maku bayani! silale suka zauna yace observe na likitan mu nafarko yagane cewa tanada depression, nabiyu yace tanada mania but ba sukai modrate ba da tazooo gurin aihuwa se phobia yashiga wad'an can suka qara tashi! shiru sukayi duka biyun sannan yacigaba da cewa tana kuma cikin had'arin jego, dan hallitunta bazasu koma dai daiba se bayan sati biyu da haihuwa! in sun koma za'a fara bata chemical theraphy (drug treatment) na mania and depression inkuma akayi rashin saa se anfara magance phospartum sannan ayi na matsalar! duka subiyun gwaron numfashi suka saki tare da cewa yanxu meye mafita! nisa yayi shima kana yace nan zakubarta sati hud'u se musan ta ina zamufara! d'an fito da ido sukayi cikin jimami tare da cewa tanada yara kuma jarirai be yuyuwa abata magani se tasha can gida!? be yiyuwa sbd matsalarta na iya haddasawa takashe wanda takeso takashe kanta dan kar yashiga matsalar da tashiga sbd juyewar neuro na qwaqwalwar ta! sannan batada inside kuma yanxu ba komai zamuyi mataba da yawuce tayi surutai mu rubuta tanan se mugane meya haddasa wannan matsalar daga bisani mod'orata akan Electric convaltion treatment dan yayi girgixar qwaqwalwarta! jefo tambaya suka qarayi da cewa yarafa? karku damu akwai mata dayawa masu yara jarirai da masu cikkuna kuma munada ma aikata masu kula dasu!!! ciza leb'e Ahamad yayi, kana Abba yace ba damuwa nawane kud'in zama? 150,000 ne! kai tsaye yabiya aka kira ma aikata akace sushiga da jaleelaa female ward, wasu akabasu riqon yaran! bayan antafi da ita ne Ahamad yace wai Dr. me ke kawo wa mata haukar nan? naji kace akwai mata dayawa masu cikkuna da jarirai!? seda yajuya kujira yace gaskiya Abubuwan nada yawa...wasu sanadiyar rasa wani nasu, wasu kuma yawan shaye shaye, wasu talauci, wasu tunanin ya zasu haihu! wasu kuma maza ne! amm zahirin gaskiya 99% damuka qididdige baqin cikin da NAMIJI keyiwa macce ne kesa suna haukacewa!! cikin kad'uwa Ahamad yace 99% kace NAMIJI fa Doctor? eh hakane dan dayawa suna amfani da qarfinsu suna zalintar mata! basa basu hakkin su! sun maidasu tamkar kayan qawata gidajen su! adake su ahansu kuka... ire iren wad'annan se su sanya masu damuwa daga qarshe se Abun yazooo su samu hauka in akayi rashin sa'a macce nada kishiya se A zargeta alhalin mijin nanne yasa ta haukacewa! shiru Ahamad yayi daga bisani yace Allah ya kyauta sukayi sallama suka tafi Abunsu! jaleelah nashiga aka sauya mata kaya blue irrin na masu tab'in hankali,,,,,,,,,,,,,,,,,
da fatar saqona ya isa ga d'umbin mazan dake amfani da igiyoyin aure suna walaqanta mata suji tsoron Allah watarana dukk zamu had'u gurin Allah yayi hisabi akan gaskiya😢 dagaske kuna bada guddumuwa gurin samin tab'in hankalin macce😴 kudaina mantuwa da duk tsayin shekarunku watarana zaku isko ubangiji🙌🏻
[13/02, 20:46] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀2⃣7⃣
_Alhmdullah bini'imaty💞_
⬅
jaleelah nashiga aka sauya mata kaya blue irrin na masu tab'in hankali......kana aka jawota aka Ajiye cikin sauran y'an u'wanta, dube duben bqaon guri ta hau but dai bata shaida ina take! se kallon kalolin hauka take wasu kuka babu dalili,wasu dariya, wasu rawa, wasu gurzar jiki aqasa Abun dai ba'acewa komai! tana zaune Ahaka kawai wata daga cikin masu tab'in hankali tasamu zabgegen dutsi ba ankara ba ta jefa ga gushin jaleelah sha jini ya wanke tana d'aga murya wai taga take takenta se ta halakata! da Azama ma aikatan suka shiga tsakani wasu sukaja jaleelah, wasu sukaja d'ayar da kyar aka rufe cikin d'aki jaleela kuwa aka hau yimata dressing, itako waccan tahau zage zagen u'wayen ma aikata, ba wanda yakula dan sun saba da shan maruka da cizooo da zage zage daban daban ga maras lafiyoyin nasu! haka dai har akasamu gurin yayi shiru... can wuraren magrib Akaba jaleelah yaranta akace tabasu nono ana qoqarin nuna mata yadda zatayi ba laifi tabasu kuma sunsha aka goya su tun da ganan aka fara observe na halayyarta! gefen su Abba sun sauka gida lafiya ran kowanne badad'i sedai basu labartawa Amma komai ba akan hallin da jaleelah keciki ita kuma bata tambaya ba"" rayuwa dai haka tafara takon saqa! bayan kwana shidda munauwar ne zaune gaban mahaifinsa yana neman Alfarmar a nema masa Auren khairat...seda yayi shiru irrin nasu na manya yace munauwar meyasa kanace se khairat? yarinyar da bata mallaki tarbiya ba! yaya kake tunanin bayanka duba da zab'in da Annabi yayimana? seda ya marairaice murya yace Abba khairat nada kirki, wlh nayi imani xakayi Alfahari da ita cikin danginka...murmushi yayi mai wuyar fassara,, yace zan Amunce da zab'inka but Akwai sharad'i,,,,cikin zumud'i yace Abba ko menene zanyi wlh yana wasar baki! seda yabari d'an yanatsu yace kace cikin jaleelah ba naka bane na yadda! sedai kasani har yanxu matarkace dan ba da ciki tazooo gidanka ba! Abinka da wanda bashida gaskiya seda gumi ya wankemasa baki nab'ari yace Abba ni har yanxu bangane inaka dosa ba...nisa yayi tare da cewa sharad'in shine zaka cigaba da riqe Auren jaleelah kuma zaka riqe Abunda tahaifa amatsayin y'ay'anka...dam, dam, dam zuciyarsa ke harba jini, cikin kad'uwa da zaucewar hankali yace sharad'inka yamun tsauri Abba se yasa kuka yacigaba da cewa bazan iya kallon d'an wani A matsayin nawaba, bazan juri kallon mazinaciya ama tsayin matata ba, ina roqonka karka nace Akan buqatarka domin zaman zargi da takaicin rayuwa zanyi da itah Abbah yaqara d'inkewa da kuka! shima Abban hawaye suka zuba akan kuncensa yace munauwar naso ka amshi buqatata domin narufa Asirin zuriyar sale, banaso yaran nan da jaleelah tasamu subud'e ido ba uba tare dasu, nasani zasuyi kuka kuka mai yawa! domin uba shine Adon kowane d'a Aduniya koda kuwa gindi yake jah akan titi, dahaka nake roqonka munauwar dan Allah kayi wannan jahadin pisabillilah koda bayan sun mallaki,hankalin kansune se kasanar dasu yayasuke! d'agowa yayi yace idan na amunce zaizamo nadama gareni da kuma su kansu yaran, gwara tun farko su san Asalinsu domin kama da wane bata wane! iska Abba ya hurooo yace Shikenan munauwar sedai kasani ita dama sau d'aya takk mutum ke mallaka Arayuwa da yawa Abunda mutum keso ba Alkhairi bane ina maka fatan nasara! cikin rashin kuxari yamiqe tare da cewa ngd Abbah,,,,tunda ga lokacin zancen Auren munauwar da khairat sanusi d'an boko yasoma qarfi... Ammah kuma guri yacika d'anta zeyi Auren qwarya tabi qwarya! Anfara shirin biki na nuwa duniya akawai...ansanya biki watan gobe idan rai ya kaiiii!...Ahamad kam Abu be masa dad'iba yau fuska ba walwala yaje yasami munauwar zaune da kwalbar barasa gabansa, cikin rashin san magana yace munauwar yanxu khairat kazab'a A matsayin u'war yaranka? yarinyar da tagama watseaa a titi? y'arshaye shaye? cikin tsawa yace dakata Ahamad! kanada iko kafad'an komai but banda sukar khairat domin bazan jure ba! sanyayyar Ajiyar zuciya yasaki yace shikenan amma komai lalacewar yanayi karka nemeni muddin maganar khairat ce! to dama can ai baneman ka zanyiba! babu sallamar arziki suka rabu,,,,kwanci tashi yau kwanakin jaleelah goma sha ta kwas sedai bawani canji illa ma yunqurin kashe kanta da takeyi! yau Accidentlly bacci ya kwashi mutane kasancewar dare ne tasamu hawa kan kujera doguwa ta kara wuyanta ga fanka na Aiki sarr ta yanki wuyanta zafin da tajine yasa tayin ihunnn da yatada mutanen dake tsaron su cikin gaggawa Aka d'auko Ambulance aka fita da ita xuwa A and E dep. d'inkewa akayi tare da Addmiting nata tun safe aka d'auke ta zuwa Electric Convaltion treatment wuri ne da dukkkk haukar mahaukaci yashiga bazayi muradin komawa ba sbd Azaba da rad'ad'i dasukeji,,,,kan gado aka d'orata akasa zane aka rufeta tare da daddannewa kana akasa susu wa hancinta da bakinta kana akayi joing na wuta ga kunnuwanta kan kace wani Abu na u'rar tafara sata jijjiga kamar yadda ake buqata,,,,,,,,,,
[13/02, 20:46] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀2⃣8⃣
_Alhmdullah bini'imaty,,,,innalillahi wa inna ilaihim raji'un ummiey y'ar u'warku da tab'ata ALLAH yabayyana ta darajar muh'd S.A.W💞_
⬅
kan kace wani Abu na u'rar tafara sata jijjiga kamar yadda ake buqata,,,,,,,,,,bayan mintuna aka cire tare da sanya wasu gardawan maza ukku d'aukarta izuwa wani tsafta taccen gado suka Ajiye,,, mintuna goma shabiyar da ajiyeta tafarka cikin yanayin maye Alhali ba giya tasha ba, aka sanya wasu mata riqonta izuwa ward d'insu,,,kwance aka Ajiyeta bacci me qarfi ya sureta bayan isha ta farkka tare da tambayar me yakawota nan? ina cikinta? se tafashe da kuka! wata siririyar mata ce ta tasooo tana tambayar jaleelah me kikewa kuka!? d'agowa tayi batare da tsaida hawaye ba tace me nazoo yi anan baiwar Allah? murmushi tasaki tare da jan hannu jaleelah suka bar d'akin izuwa wani,, tace zauna jaeelah, jin takira sunan ta tazauna cike da son sanin me tazooyi Anan? gyaran murya matar tayi kana tace jaleelah ki kwantar da hankalinki, nan hospital ce ta masu tab'in qwaqwalwa! zare idanuwan ta tayi kana tace to ni meye had'ina da tab'in qwaqwalwa!? dariya tayi marar sauti tace jaleelah ba had'ine ko mu'amalaba...Allah na jarbtar ka ne lokacin da yakeso kuma kema yajarbceki lokacin dayaso ya maida maki hankalinki batare da shawarar kowaba! Allahu Akbar tafad'a tare da shafar mararta dataji ta sauya, hawaye na malala tace na haihu ko? eh kin haihu kinsamu yara mata guda biyu kyawawa? dumm qirjinta ya harba tace y'an mata guda biyu? Eh jaleelah tana murmushi takira d'aya daga masu rainon su tace akawowa jaleelah yaranta...haka aka kawo mata su Aka ajiye jikinta, duban su tayi se hawaye da tausayin rayuwa, kana tayi godiya ga Allah xahiri tare da roqonsa yabata juriya da haquri akan rainon su dazatayi ba Adon duniya,,,,matar seda tayi qwallah itama da tafahimci su usaina basuda uba kana tace jaleelah tarungumi qaddara yara mata rahama ne ga wanda yayi farinciki da basu tarbiya... godiya tayi tare da cewa na karb'i hukuncin Allah domin yanasane dani dakuma irrin kyautukan da yake min,,,,,,cikin jajintawa Aka amshi yaran akace taje ta kwanta dan ba A kwana da yara d'akin cox komai na iya faruwa! haka tabarsu ta tafi sedai dukkk iya satar bacci yau kam yakasa sace jaleelah tunanin baya da Abubuwan da suka shud'e ke zariya A idanuwanta da ilahirin jikinta,,,har gari yawaye tun Assuba sallah tayi tasake komawa gadonta har 9:am, sannan aka kirata tabama yaranta nono tana ba hassana taga bayan kunnenta da wani baqi kamar na munauwar tasake duba na usaina shima haka aranta taji sanyi se tabarwa zuciyarta,, tana riqe dasu har akazoo ganinsu cikin sa'a da jaleelah aka fara tazooo aka d'auki BP ta sannan aka tambayi lafiyar jikinta dakuma Abunda tazooyi nan!...cikin nutsuwa tabada amsa' kana suka gane inside da yafita yadawoo suka bata shawarwari da maida komai gurin Allah S.W kana sukace yau zasu sallameta! cikin kad'uwa tace dan Allah kubarni anan zanfi samun nutsuwa na roqeku,,, d'ifff sukayi dukansu kana wani yace meyasa ba kya san zuwa ga Ahalinki,,,? kallon shi tayi tare da cewa karka matsa da son sanin dalili domin kuwa ita rayuwa sirrice! shiru sukayi kana suka yi amannah tana fuskantar qyama ne dole se an had'u da iyayenta Ayi family treatment...sukace tayi haquri zaa gyara but fa sun sallameta,,,fuska ba walwalah tamiqe tafita dan ba wasu guri, kana aka kira Abba akace suxoooo zuwa 4:pm sutafi da y'arsu...harga Allah yaji dad'i ya kuma kira Ahamad yasanar mashi dan su shirya tafiyar shi kan dad'i har sajjada yayi... munauwar kuma yau saura sati d'aya aurensa da khairat dan haka shagalin gabansa yake shida Ammanshi da qawayenta,,,,,,haka har lokacin d'auko ta yayi sukaje su Amma basuda labari...Alhmdullah sunji dad'in ganinta da kuma yaranta dake cikin qoshin lafiya kan ma suyi, magana ita tafara gaida su cikin taushi da sanyin murya,,,ansawa sukayi tare da yimata barka da Arziki kana sukayi ciki jan kunnen su akayi akan karsu qyamace ta kuma ayimata wankan jego, aka bata tbs cpz tare da cewa bayan wata d'aya su dawo! godiya sukayi kana kowa yad'auki d'aya, d'aya,suka shiga mota...
d'od'ar suka hau titi zuwa cikin garin sokoto suka tsaya A jidda plaza suka siyawa usaina da hassana kayan jarirai da komai na buqatarsu sannan suka wuce gida,,,,,Amma tasha mamaki ganin jaleelah da yaranta biyu sedai kuma tayi farinciki ganin ba wanda zai dubesu yace sun had'a da munauwar! hakan yasanya ma tayiwa jaleelah barka da zuwan marar Ado duniya! jaleelah tashayar da ita mamaki ta hanyar amsa mata da cewa rashin tarbiya ne rashin Ado tawuce Abunta zatayi,magana Abba yakatseta da cewa tayi shiru ita tajawa kanta,,,sosai taji zafi kuma ta qudurce jaleelah zatacigaba da nadama izuwa lokacin da numfashinta zai tsinke A doron qasa... rayuwa mai cike da burin walaqanci, d'aukar fansa, da ta wakkali Aka shirya tafiyarsu...kwanci tashi jaleelah bata fuskantar matsala ko d'aya se habaici da iqirarin shaggu da Amma keyiwa su usaina but Abun baya damunta dan tashirya fuskantar hakan...yau lahadi ranar d'aurin Auren khairat da munauwar ranar da dayawan sakkwatawa kuka sukeyi kasanceaar Antashi da rasuwar me martaba sarkin muslmi, haka dai aka d'aura Auren bawani armashi da yayatawa duniya...har lokacin kawooo amarya yayi ,,,, mutane suka gaji dajira suka wuce gidajensu Amma tasha mamaki ganin har shabiyun dare ba akawo Amarya gidan taba...tatanbayi kanta hakan na nufin batada darajar da za'akawo mata sirikar ta tayimata hud'uba? ko kuma wayewa ce irrin ta wanda suka rayu da boko?
[13/02, 20:46] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀2⃣9⃣
_Alhmdullah bini'imaty💞_
⬅
ko kuma wayewa ce irrin ta wanda suka rayu da boko? da wannan saqe saqe har bacci yasureta,,,gefen gidan Amarya kuma ba wani armashi domin tun Awaje ansan juna su zully ankasa an tsare dasu za 'araya daren Auren! munauwar beyi mamaki ba domin khairat nasanar mashi mahimmanci zully da girmanta A zuciyarta! se ya wuce d'akin sa ya kwanta itakuma zully tafara sarrafa khairat yanda suka saba dama an dad'e ba Ahad'uba...bayan wayewar gari har shad'ayan rana basu farka ba se shi dakansa yashiga yatada su amma yaji tsoron yanda yasamesu sedai yabarwa zuciyar sa komai,,haka dai wunin ranar yasoma tafiya ran Amma jagule munauwar kuma babu dad'in rai irrin na angwayen da suka mallaki sabuwar amarya! zaune yake yaxabga uban tagumi yana tunano daren kawo jaleelah da wayewar gari da kuma ladabinta... jiki silale ya miqe ya watsa ruwa yasa shadda blue mai duhuwa yafito cikin qasaita da jin kaiii ya tosa kansa d'akin Amarya da Azama yafitooo ganin yadda mata ke bad'ala kan gadon sa na sunnah sedai babu khairat a ciki,,,,wayar sa yazarooo ya kirata cikin wata shiga me fisgar hankali tafitooo riqe da hannun zully...ransa yayi mugun sosuwa yace ina son ganinki! seda zully tace taje sannan tabi bayansa...A fusace yace khairat wannan shashanci bazan d'auka ba domin nan fa gidana ne na sunnah shine zaki tara min y'an mad'igo tun Adaren farkona? cikin rashin tsoro da damuwa ta kurb'a barasa ta kwai kwayi muryarsa tasa dariya tace ko bahaka kace ba? baki yasaki galalah yana son fad'ar wani Abu amma yakasa,, da tafahimci hakan ta narke tace sorry my really sati d'aya kacal zasuyi subamu guri mushana tana qoqarin goga nonota A qirjinsa! d'an riqeta yayi yanda zata iya juya jikinta yace shikenan Dharkan but yau dare na ne ko yaqarashe kamar zaiyi kuka murmushi tayi tare da kashe idonta d'aya Alamar wata magana shima dariyar yayi tare da fidda nonota d'aya ya tsotsa kana ta qwace dan tasan gargad'in zully,,,,,shikuma yabi ta qofar qasa yafita kai tsaye gidansu yanufa Amma nazaune ga Alama hankalinta baya tare da itah yashigo murmushi d'auke ga fuskarsa! yagaidata cikin ladabi bawani sakin fuska tace munauwar Ango...dagaji yasan ciki da magana hakan yasashi gyara zamansa yace Amma wayatab'a man ke? kallonsa tayi tace ina khairat ko se naje nagaida ta? sosa kansa yayi sannan yace aa amma ita zatazoo zuwa gobe bata jin jikin ne murmushi tayi me ma'anoni tareda fad'ar inagaidata da jiki,,,,,, yace zataji sukaciga da tab'a firar duniya,, daga bisani yamiqe zuwa sashen Abba shidai Abba be tambayi amarya ba yadai yimasa fatan zama lafiya,,,,yayi gdy yafito zuwa sashen Amma yana tambayar ina suka samu yara masu wannan kuka na cin rai tun sama yake jiyo kukansu...tsaki taja tace d'iyan y'ar iskar can ne mekama da Aljanu haka suke masifashshe mu wlh in wagga ta Ajiye wagga ta d'auka... tsakki yajah yace nikam natafi bana iya sauraro... koda yafito jaleela na takai kawooo tana jijjigasu ji take kamar tayi kuka tarasa waza tabama d'aya kwatsam bata ganiba ta kauri munauwar kamar me jira ya dallah mata maruka har biyu yaqara sa qafa yayi fatali da usaina seda tasha bango,,,,, Aikan usaina tasauke qarar da ta fallah jaleelah takai ga fuskar munauwar tas tas tasauke masa maruka hagunsa da dama masu zafiii da wuyar mantawa kana Afusace tace na dad'e ina sha'awar marinka! kuma kasani yazama qarshe, iskancin ka da rashin imani su tsaya iyani domin zan iya kisa batare da nadama ba muddin kanemi tab'a lafiyar y'ay'ana...diff duniya ta d'auke masa yarasa me zaiyi yarama wannan qasqanci da jaleelah ta kafa masa wanda A tarihi rabo da Amareshi baya iya tuna rana, da kyar yad'ago idanun sa yace jaleelah kifara lissafa yau amatsayin jindad'in ki naqarshe domin nayi rantsuwa se nakafa baqin cikk da kukan zuci A duniyar ki,,,se marina yazame maki qunci dauwamamme! cikin rashin damuwa tace nashirya zuwan hakan dan haka bazanyi nadama ba,, barema me yarage mun Aduniyar wanda bangani ba? kai zance kajira nadama da quncin rayuwa domin na tabbata *BAQAR RANAR* na nan zuwa"A" gareka xata dasa wata magana ya b'allah mata marin da yasa takai qasa sedaai batayi kuka ba tasalima gogewa tayi tare da cewa kayi ta marin fuskata munauwar bazanji haushi ba domin ni rayuwar ka namara
[13/02, 20:46] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀3⃣0⃣
_ALHMDULLAH BINI'IMATY_
⬅
banji haushi ba domin ni rayuwarka namara,,,,,,,zaiiii cafko ta tayi tsalle ta d'auki yaranta ta guduuuu... hurooo iska yayi tare da fitahhhh farfajiyar gidan baki d'aya ...A wannan baqin yanayi ya isa gidansa ya zube kan kujera yana tunanin yadda zai rama gayyar da jaleela ta masa! haka rayuwa taci gaba munauwar kullum da burin fansa yake kwana dashi yake tashi, ko wace shigar sa gidansu dama yakejira ta had'uwa da jaleelah!!! har kwanaki sukajah, besamu dama ba... kullum marin gezau yake masa, yakasa mance ranar da shacin hannun macce ya kwanta Afarfajiyar fuskarsa,,, yauma da burin walaqanci yashigo coxxx yaji Abba yayi tafiya! ganin yaduba ko ina begantaba, yace ma Ammah ina jaleelah? qasqance ta dubeshi tace me yadame ka da itah? Burin fansa amma... yadda yayi magana yasa ta d'agowa ta dubeshi, kana tace qauyensu suka tafi tunjiya...iska me zafi ya hurooo tare da cewa itada wa sukaje? Abbanku tabashi amsa... cikin wani yanayi ya furta nan ma narasa damata, sedai wajibi na ne namaida Aurena Akanta domin tahaka ne kawai zan iya maida mata martanin tarihin da takafa arayuwata, wanda yahana ni baccin dare da rana! kallonsa tayi yana maganar idanuwansa nadad'a rinewa da jar kala haka yakeji tamkar yanxu ne ta mareshi kuma dan qasqanci harda cewa tadad'e tana sha'awar marinsa! kafad'arsa amma ta dafa tace ina goya ma baya munauwar nikaina na tsaneta, bana son ji ko ganinta, sanadiyarta yanxu haka Aurena bakin mutuwa yake, narasa ya zanyi na kawar da ita A doron qasa domin takai takawo ina zargin mahaifinku na tarayya da itah, soyayyar da yake nuna mata hankali bazai iya d'auka ba"" Nima ina zargin haka Amma tare da miqewa yafita waje karffffff sukayi da Ahamad yace Ango na Amarya...murmushi ya qaqalo yace Ashe kana nan dama gurinka zanje! ohk mushiga ciki thommm...bayan sun zauna yace dama Auren jaleelah nakeso na maida... tass qirjin Ahamad yabuga yace dama ka saketa ne? a'a ban mata saki ko d'aya ba yabashi amasa! seda yahad'eye wani yawuuuu mai ciwooo yace munauwar maganar gaskiya baka dace da cigaba da zama da jaleelah ba! akan me? halayenku sunyi hannun riga...cikin muryar kuka yace nacanxa Ahamad nayi nadama, ina so ne na killace mutuncin Abba akan usaina da hassana da yakeso surayu cikin aminci da walwala batare da wata tsangwamar bakunan mutanen duniya ba! sannan nayi nazari naga wannan kad'ai zanyi martaba ta tadawo A idon Abba, shiru Ahamad yayi kana yace munauwar in domin Allah zakayi ina tare da kai, inkuma da wata manufa zakayi karka zalinci marainiya dan girman Allah yaqarashe yana mai son kuka... seda yanisa yace Ahamad dagaske jahadi zanyi...tundaga ranar yafara shirinsa bayan dawowar Abbane ne Ahamad dashi sukaje da maganar maida jaleela! sosai yayi murna domin Abunda yake Addu'a kenan munauwar yakarb'i kukanshi,,,,,yace yaji dad'i amma se yaji tabakin jaleela in tadawo. munauwar baki har kunne domin yasan seda yashirya tsafff yazo da maganar gurin Abbah... qasan zuciyarsa kuma Azazzalar shi take yacimmata qauyen yayimata tonon silili! da hakan suka rabu sai dai shi zamewa yayi yaje yasanarwa Amma halin da ake ciki, tace yayi kyau! gobe yabi Asubbah yaje qauyen ya b'atar da jaleelah da wannan qodurin yabar gidan... acan qauye kuma jaleelah tafita ziyar dangi,,,tafe take tana kallon garinsu da kuma d'an cigaban da Akasamu ba tsammani tayi karo da dauda cikin mutunci da sakin fuska suka gaisa kana yagyara tsayuwar sa yace jaleee nanemo kud'i, kud'i masu yawa! nasha wahala gurin tarawa amma kinsan me jalee? kai ta girgixa Alamar a'a! yace bana damuwa domin muryarki nakeji tana cewa dauda qara tarawa kadawo zan Aurenka qara tarawa dauda,,,,gashi natara jalee yaushe zaki dawoooo ki aure ni? sadda kanta qasa tayi tace dauda ina tayaka murna, amma banguje ka sbd kud'iba! da zanbud'e ma rayuwata da kayi kuka tare da imani da qaddararka mai sauqi ce! kai macce karasa nikuma A bubuwa da yawa...narasaka dauda, narasa papana, narasa farincikina gabaki d'aya,,,ga Alqawari da bazan iya sab'awa ruhin papana ba... duk da cewa yaxama gawa...zan mutu a qangin bauatar Aure da danasanin Alqwali danayi na cewa ko mijina zai yanka naman jikina bazan gujeshiba, dauda katayani Addu'a har yau ina jiyo sautin papa na qarshe cewa jalee ko saud'aya kikabaro gidan munauwar da sunan tashi banyafe maki ba...domin wannan maganar Amo take Akunne na... tanaabani lasisin zama gidan mijin aurena! ta d'ago sukayi musayar kallo kana tassada kai qasa tacigaba dace dauda naga Abubuwa,,rayuwata darasine ga iyaye da kuma masoya masu zargin anguje su dan anga kud'i... dauda nasan kana sona amma ina roqo ka manta dani domin nikam namanta dakai, najeraka cikin sahun mutanen da qaddara taraba muna son juna, dauda karoqe Allah ya karkare mani yafi jiran tsammani taqarashe cikin rishin kuka...haqiqa jalee tabashi tausayi muryar sa narawa yace shikenan jalee se watarana ina maki fatan samun sauqi dacin jarrabawar rayuwa...sukayi sallama ta cigaba da tafiyarta inda tayyi niyar zuwa da rashin kuzari ta isa bayan sun gaisa tadawo gida kasancewar duhun dare yakama...haka tadawooo gida ta zauna jiki mace tana rayawa ina ma Ana mutuwa Adawoooo da papah yayi kuka da nadama marar Amfani irre irre wannan tunanin kad'ai ke mata shawagi A qwaqwalwa har dare yaraba...shikuwa munauwar tsafff yashirya duhun dare kawai yake jira ya wanke ya danno hanya...
taku har kullum Asmeenat zeeyan nake cewa kutareni gobe dan jin ko munauwar zaici nasara ga jaleelah?
[13/02, 20:52] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
0 comments:
Post a Comment