◀3⃣1⃣
_wannan page sadaukarwa ne ga mutanena Asmeenat fan's 1 masu feshin sharfi da tattaunawa dafatar kowa yayi haquri da qaddararsa domin ko bakomai tana cikkn rukunnan imani🥂..._
⬅
shi kuwa munauwar tsafff ya shirya duhun dare kawai yake jira ya wanke ya danno hanya...haka kuwa Akayi...kiran farko na safiya, ya d'auki qaramar motarsa qirar 206 ruwan toka mai duhuwa an yane ta da leda me baqi ga glass wanda sedai naciki ya hango nawaje d'od'ar yakama hanya ba wani fargabar dawowa lafiya ko Akasin hakan!... yunwarsa d'aya ya walaqanta jaleelah... ko rayuwar sa na manta
*BAQAR RANAR* da hannunta yayi tsautsayin dallah masa mari har guda biyu...gudu yake amma gani yake tafiyar bata sauri, cikin Abunda be kasa awa biyu ba ya isa qauyen su jaleelah...duk da gidan ya rushe be hanashi saka kai ba, dan yasan baxa tawuce nan ba... cikin sa'a tana lab'e cikin wata dangar kara...yashiga bako sallama innalillahi wa inna ilahim rajiu'n shine bakinta ke Ambato dataga mugun miji A gabanta! taqara qanqame yaranta! sedai yashayar da ita mamaki dan cikin taushi yace d'aukar ku nazooo kishirya! Arazane ta had'a ido dashi zuciyarta na nanata Abunda harshen sa yakaranto! Azahiri kuma kai take girgizawa Alamar bagaskiya bane...cikin murya irrin ta mazan da basu san Allah ba yace bazuwa nayi nace iyi ke kuma kice a'aba tashi mutafi...hanjin cikinta ne suka doka qara sbd firgici tayi narai nara da idoooo tana son furta wata kalma! kallon ta yasakeyi yace tashi muje ko se natara maki jama'a suxo sukalli yaran da U'wa takawo su duniya ta hanyar fasiqanci! rass gabanta yafad'i qwallah ta sirnano mata kasancewar qaramin aikin munauwar ne yimata wannan sharri ga mutanen qauye da saurin imani da qarya...bakinta na karkarwa tace meyasa ka matsa da se nabika...? zakisani idan munje! banyi sallama da kowa ba munauwar... ketashafa...duban shi tayi ido cikin ido karo nabiyu tace dan Allah" hannu yad'aga Alamar tayi shiru, tausayin kanta ya kamata ta dubi yaranta se dariya suke qyalqyalawa basu san me ake cikiba! tashare qwallah tace shikenan muje...zuciyar ta dam dam kamar tafad'o qasa sedai tana shaida mata Abba yaturo shi d'aukar su... hakan yasa tabi bayansa but duk da zuciyarta dake cewa munauwar bazaizo d'aukar kiba tilastawar Abba ce bata shaida wane yanayi tashiga motar sbd sanin waye munawar! tana shiga yafisga suka tafi,,,, tunda suka fito Asako yafara gudu irrin na nashirya zuwa lafira,,se sunyi sama suyi qasa tun tana had'a shi da Allah har ta qyaleshi ta qanqame yaranta anata tunani A mutu tare...bayan doguwar tafiya se yafad'a dasu wani zabgegen daji da bashida iyakar fili baka hango komai, se manyan duwatsu masu ban Al'ajabi da tsoro...dai dai gurin wani kogon dutse me nisan tsayi da zurfi ya tsaya kana yace jaleelah tafitoooo A tsorace taziro qafafuwanta qasa... ya dubeta yace cikin wata murya kin mari rayuwata ko? nikuma zan mari duniyarki dan se na lalata duk Abunda zaki kallah kiyi dariya...yana kallon yaran da takeji tamkar tamaida su cikin cikinta...yawun bakinta ta kalatoooo da kyar ta had'iye busashin yawu tace dan Allah kafara kasheni kafun ka kashe yarana...seda ya qyal qyala dariya kana yace kinyi bahagon tunani domin bazantab'a baki mutuwa me sauqi ba jaleelah... sannan yaranki da kikeso kina kallo kura zatazo tacinye su... hawaye taji sun sirnano mata bashiri taqara sa su jikinta zahiri kuma tace Arnan da ma suna qyamatar macce ne sbd Abun kunya... kaj meyasa kake qyamata? tajah majina tace munauwar narasa gane laifina...?wace irrin qiyayyace haka? da har shaid'an kemaka kuwa karaba u'wa da yaranta! kasan kuwa yadda U'wa kejin xafi da rad'ad'i kukan yaranta bare har kayi iqrarin rabawa? murmushi yayi yace ko yanxu na mutu buqata ta biya dan nahango tashin hankali da baqin ciki tare dake...kana yajawo hanunta yafisgo ta fad'i qasa warwas yara sukayi d'ai d'ai, yazaro igiya a Aljihunsa ya d'aureta ga wani qaton bishiya yadda bazata iya kwancewa ba...ya d'auki yara yayi tafiya me nisa dasu amma tana jiyo qararsu! kana yadawoo yashiga motarsa hankali kwance...be tafiba rana nadad'a fallewa jaleeh gumi take, kuka take, idanuwanta basa san bud'ewa sbd qishi da yunwa hannayenta se d'igar jini suke coxxx of d'aurin da Akamasu! can wuraren ukku yafito da robar faro yayi dariya yace har yanxu yaranki na numfashi kicece su inkuma kedasu se A lahira nikam natafi yajefa mata robar a goshi ya wuce... numfashi kawai take saki takasa furta komai da kyar tace kabani yarana su ci Abuncin su dake Ajikina se kamaida su kafun ni ko su mukoma ga Allah......
taku har kullum Asmeenat xeeyan nake cewa kutare ni gaba dan jin yaya zata kaya
[13/02, 20:52] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀3⃣2⃣
_Alhmdullah kaseeran Habiba Idrees hubby ina tayaki murna bisa arziki da Allah yayi muna na bayyanar mama ina roqon Allah yabata lfy 💞_
⬅
da kyar tace kabani yarana suci Abuncin su dake "A" jikina se ka maidasu kafun ni ko su mukoma ga Allah... dariya yasaki me sauti kana yace jaleelah wannan yanayin kad'ai zanganki hankali na ya kwanta, na yadda da kaina cewa saqon da nake aikawa yana isa inda yadace...dakyar ta motsa gashin idonta dayayi jagaf da ruwa ta dubeshi tasake maidawa qasa batare da tace komai ba A zuciyar ta kuma cewa tayi inama Ace yaune za'abusa qahon tashin duniya...! jin takasa magana yakai hannu ya matsi kunnenta da yagashe da zafin rana yace ko gaban Abada bana maki fatan nasara... so nake qaddarar ki tayi nasarar turaki jahannama, yaranki kuma kinada ikon cetarsu idan kin kwance kanki yanxu yarage naki neman mafita! kana ya juya yafad'a mota yayi juyi mai tada qura ya wuce... bayan tafiyar sa Azabar zafin rana da qishi sun kaimata karooo ji take kamar harshenta ya zazzago sbd Axaba da matsin rayuwa...gashi kukan yaranta da take jiyowa ya d'auke...hankalin ta yaqara tashii hawaye cak sun tsaya basa zuba,,, Anan seda tayi gasgata kuka na d'aya daga jerin manya ni'imomin ubangij domin ta nema ta rasahhh... Azahiri kuma cikin jigatattar murya me wuyar fassara da misali tace wata qilah su usaina sun koma ga ubangijin da yabani su...can se tasake jin kukan hasana da kyar tajuya tana duban inda take jiyo sautin kukanta...tayi wani murmushi da tarasa sanin dalilinsa tasake lumshe idanuwanta tana sauraren kuka har tasake jin shiruuuuuu! lokaci yacigaba da tafiya jinin hannayenta da d'a d'iga yake fuskarta tayi jajir jikinta ya d'au mutuwar ta kawai take jirahhhhh... gefen munauwar kuwa tafiya yake mai cike da farinciki da sauke wajibin da yayi rantsuwa se yacika Alqawarin sa! ji yake ko yanxu numfashin sa yatsaya baya wata nadama domin yacika burinsa...! cikin yanayin nan ya isa birnin shehu (sokoto) kai tsaye gidansa ya nufa khairat na zaune tana kallon wani fitinannen fim na y'an less ji take kamar tayi hauka sbd fitina..haka yasameta cikin sauri yakashe tare da rungumota jikinsa! gam yamatseta yace haba khairat meye haka? ko kinmanta kina yawan gayamun kin daina? jin muryarsa ba yadda takeso ba yasa ta turoshi tare da d'aga masa yatsa Alamar ya qyaleta! ze matso kusa da itah taqara d'aga hannu cikin ta danna screen d'in wayarta dama kunne take tafara magana da zully cikin sex voice da Abun yagirma se suka koma group wanda Akayiwa taken less dad'i, kasancewar akwai yara qanana masu qananan shekaru da bazasu fi 12,13,14,15, ba kuma suna wartsake damuwar su musamman yadda suke haskawa da nuna bajintar su domin sunajin dad'i da kyautukan da Akebasu kuma basu gane ina duniya ta dosaba dan haka suna sarrafa farji yadda yakamata
_(nan kam ina kira ga iyaye suji tsoron Allah su daina ba yara qanana waya domin y'an taAddar Allah irrin su khairat na nan zagaye da media)_ munauwar da yaga tayi nisa dole yatashi tare da kitsawa aransa da sannu xai canxa khairat suyi rayuwa me ma'ana...haka daren yau yafara shigewa... jaleelah tarasa mai cetonta domin har yau bawani d'an Adam da yagifta gashi har yau babu manzon ranta bezo gareta ba... sule salin dare yakama babu komai se kukan nau'in dabbobi da macixai dake shawagi ta gabanta suna wucewa bata iya motsa ko farcenta cannn sai tayi shiruuu komai ya daina motsiiiii wata qil rai yayi halinsa! su usaina kuwa ba Abunda yasame su Allah nagadin Abunsa da ni'imominsa cikin wannan yanayj se ga wani mafarauci yasanyo karnukan sa gaba suna tafiya...tunda suka kawo gurin da su usaina suke ko wane yajah ya tsaya suna haushiii me nuni da cewa sunga nama...
takuce dai Asmeenat zeeyan🥂
[13/02, 20:52] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀3⃣3⃣
_Ina qara miqa jaje ga zulaihat bashirrrrr da tarasa wayarta da muhimman Abubuwanta da b'arawo yayi gaba dasu ALLAH yamaida maki alkhairi...na tausaya maki sosai_
⬅
suna haushiiii me nuni da cewa sunga nama...... da Azama ya isooo gurin cikin jimami yarafka salati yayo kansu...duban su yasakeyi ya tambayi kansa wa yaraba su damaman su? jin beda amsah yayi azamar d'aukar su...se saka yatsa suke Abakinsu! ya runguma qam A jikinsa yaduba gabas yaduba yamma ba motsin komai se tsuntsaye...cikin sanyin jiki ya juya d'auke dasu Akafad'arsa yana ta juye juye ko zaiga iyayensu..! amma shiru gashi sanyin dare da d'a sauka yake!! cikin tilastawar rayuwa yabar jejin... gefen jaleelah kuwa tana nan d'aure, ba wani motsi tamkar gawa bata san yanayin da take cikiba...Haka har mafaraucin ya isa gidansa cikin mutuwar jiki rungume da yaran! iyalan sa sunyi bacci yatura d'akin matarsa da yakamata Ace yau darenta ne! cikin kad'uwa da tashin hankali tace mlm lafiya naganka da yara? zaunawa yayi bakin gado yace huraira ba lafiya ba...yaran nan A jeji nasamesu...buga qirji tayi tace mlm bangane Ajeji kasama ba...gwaron numfashi yasaki shima yace Abunda kikaji shine nagaya maki...ta karb'a ta duba tace wayyo Allah! yanxu iyayen yaran nan Allah kad'ai yasan wane hali sukeciki domin gwara mutuwar mutum da b'atansa...wannan hakane huraira tada hajaru kisanar mata halin da muka tsinci kanmu...cikin jajinta lamarin tamiqe takirawo hajara, itama dai salatin ne da tausayin yaran ya d'arsu Azuciyarta kana yadube su yace me kuke gani yakamata? huraira tace mlm. Abari harda safe Asan Abunyi domin dare yayi ...hakane Abarshi harda safen... hajaru ta karb'a da cewa yanxu kuma A d'auko madarar shanu Abasu dan Alamu yanuna sunajin yunwa...haka kuwa Akayi ana azawa suka dinga sha kamar sun saba se bacci yayi gaba dasu harda minshariiii...sukuma sukaje suka kwanta bayan daren da suka raba suna jajinta lamarin yaran nan... gari ya waye labari yakarad'e qauye se zuwa ganin y'an biyu ake kowa yaduba se yaji inama shi Allah yayiwa kyautar su haka Abun ke tafiya gefen su usaina...gefen jeelah kuma har yanxu ba kowa can cikin tausayin Allah yajefo wasu mutane biyu maza masu nazari akan geography cak suka tsaya domin yau taimako yayi wuya se suka wuce Abunsu,,,,, harsun yi nisa gudan yace gaskiya sadis hankalina bazai kwanta ba in har ban taimaki yarinyar can ba...kallon sa yayi tare da cewa bawai taimakon ba kar mu jajibowa kanmu balai'n da zai shafi rayukan mu da dangin mu...numfashi yasaki tare da cewa domin Allah nayi niya duk Abunda zaifaru sedai yafaru amma jikina nabani na taimaketa,, guntun murmushi yayi yace naji amma badani ba muhad'u A kaduna...ohk mu had'u yajuya bayan da suka barota... da farko tsaye yayi yana dubanta se kuma yaduqa yana kwancew yana ta kuka jin numfashinta na bugawa ya tambayi kansa itako me tayi aka yanke mata wannan hukuncin? ... da son sanin tushen labari ya d'auketa yasa A mota gabansa nata fad'uwa ya tuqa...tunda yashigo cikin gari yafara tambayar ina babbar hospital take anan...? dayawa gwalo ido suke suna tabbatar mashi se yakoma cikin gusau...beji wani Abuba yakama hanya cikin amuncewar Allah gashi cikin gusau cikin wata unguwa tabarakallah...yasake fitowa yayi tambaya kallo d'aya zaka masa kagane rikice yake, wani daga jama'ar da yake tambaya yayi qarfin hali yimasa kwatance domin yanxu mutum ba Abun yadda bane...cikin hanzari yashiga mota se hospital... but Abun tashin hankali sunqi rabashi da itah wai seda police... ji yayi tamkar yazama likita yadubata amma wani gefen da gaskiyarsu...haka yaje yasamo yakawo kai tsaye case d'in yadawooo hannun su suka fara zargin wanda yakawota kamar yadda aka saba kana akace afara dubata...haka kuwa akayi cikin zafin nama aka d'orata kan gado...A ka d'auko Ambuback aka manna wa hancin ta xuwa bakinta aka d'inga bata iska tsawooon mintuna aka cire
asmeenat xeeyan nake cewa muhad'u A gobe
[13/02, 20:52] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀3⃣4⃣
_yau mun samu sojah maman nannah ubangiji yabaki lafiyar tarbiyarsa da shayar dashi cikin qoshin lafiya yacigaba daraya nannah cikin tarbiya yasanya mahardata qur'an ne💞_
⬅
tsawon mintuna aka cire...suka fara Rx_ yadda ya kamata. daga bisani suka koma gefe jiran yadda Allah zeyi,,, sukuwa police sun riqe wanda yazooo da itah har se sunji gaskiyar zance ga maras lafiyar in ta farka duk da cewa hashen likitocin da suka dubata na nuni dacewa bazata farkaba se bayan 72hours...gefen su Abba kuwa yau da sanyin la'asar yakira Ahamad yace gobe su shirya shida munauwar su d'auko jaleelah da y'an biyunta,,,, fad'ad'a murmushin sa yayi kana yace d'azu ma munauwar ke cewa yaushe zata dawoo? nace baka sanar ba... dariya Abba yayi me ma'anoni idan an fassara...Ahamad yad'ora da cewa insha Allah gobe da sanyin safiya zamuje d'aukan su...Allah yakaimu Abba ya fad'a! da wannan labarin Ahamad yatashi be zame ko ina ba se gidan munauwar cikin rashin sa'a bayanan be shigaba dan jininsu da khairat be had'uba haka kawai yakeji yatsaneta...ya juya hancin motarsa xuwa gidan kajin munauwar dayake kiwooooo, cikin sa'a kuwa yasame shi da Abokan sa sun zagaye sunata shan shisha suna huro hayaqi me qamshi ga hanci, me kuma illata huhun d'an Adam...dakewa yayi yace salamu Alaikum, munauwar yajuyo ya saki murmushi tare da cewa shigo kayi wani tsayawa kamar baqo...yaqe yayi yaqaraso ya had'a hannu da su dass kana yace zo wucewa zanyi muyi magana...dasss ne yace wai kai Ahamad yaushe zakaci lokacin ka? kullum rayuwa kake kamar bagidaje... guntun murmushi yasaki iya leb'e yace kuma ina maku fatan shiriya. yanxu kowa haramar sallah yake ku kuma kuna nan...dariya dass yayi harda qyal qyalawa yace wayagaya maka muna sallah yau? galalala yadube shi yace dama kuna da ranar sallah ne? eh dan munada lalura...kamar ya bangane ba duba da bakwa jinsin mata bare nayi amannah da hakan? dubansa dass yayi yace kasan idan mutum yasha barasa kwanaki arba'in yake Allah baya amsar sallar shi, shine mukayi group muka d'aukewa kanmu duqin banza...shiru yayi mai rikicewa dan sun nuna ga fili basa tsoron Allah kana yace cikin muryar tausayi dass ku koma ga Allah tun kunada sauran hankali..cigaba da zuqa sukayi suna masa dariya basu saurarsa,,, yace munauwar zooo konatafi...? aa tsaya mana yabiyo shi sukayi nesa da mutane yace gobe zamuje qauye d'aukar jaleelah...tsalle yayi me nuna kaji mugun dad'i yace har naqagu gari yawaye...murmushi yasaki tare da kauda zancen dacewa munauwar meye acikin barasa da har kukeji zaku bar sallah? wlh bakomai Ahamad jaraba ce kawai idan bakasha bakajin nutsuwa! ciza bakinsa yayi yace munauwar katuba domin Allah karabu dasu dass yanxu kai magidanci ne ko wane lokaci kana iya mallakar y'ay'a yaya zakaji idan suka gane kai d'angiya ne? kana gani zasu kalle ka matsayin uban kirki? dariya yayi yace yana iya da qaddarata Adai sanya mu cikin Addu'a...da wannan suka rabu...haka dai lokaci nadad'a tafiya har gari yawaye munauwar tsafff yashirya ya d'auko hanya Ahamad beyi mamaki ba dan yasan in munauwar nason Abu ko zaikashe shi se ya aikata, kai tsaye ya kimtsa suka hau hanya fafiya suke cikin kwanciyar hankali da tab'a firar duniya...Ahamad na duba gari da kuma banbancin Al'adu yace gaskiya munauwar tafiyar mota qarin ilmi ne da sanin sunaye garuruwa...hakane Ahamad ya tsuke bakinsa, da haka har buwayi gagara misali yasauke su qauyen lafiya. zaune yayi kamar wanda ya manta garin yana cewa Ahamad ina gidan nasu...nuni yayi da hannunsa yace gashi can! ware idanu yayi yace kardai jalee na naciki? murmushi Ahamad yayi yace tana ciki kuma ai batada inda yafi mata nan domin shine gidan ubanta...hakane muje naqagu na wanke idanuwana da d'anyar yarinya da ta Azabceni cikin sati d'aya...dariya Ahamad yayi yace Allah kasa ta amsheka dan...bebari yafurta ba yace karka mun baki domin jaleelata daban ce da sauran mata suka fito suka rankaya cikin gidan...
Asmeenat zeeyan nake cewa muhad'u da yamma danjin yaya zata kaya💋
[13/02, 20:52] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀3⃣5⃣
_nazari da qwaqwalwa shine aikin marubuci, duk Abunda kashuka wataran shi zakayi girba,maras gaskiya shi zaiyi gumi ko yashiga kogi... na tabbatar ba mai canxa maganata saqo na aiko ga maqota tunda kukaso baxanyi shiruba brilliant gidan zaman Amunci muka shirya in natuno su har kuka nake...ko babu brilliant wata qungiya baxan shiga ba! na roqe sarki Allah yayimana garkuwa domin lokacin mune tarkon mu yayi kamu ko ba'aso ajimu tilass media aganmu tunda gamu ga masoya cigaban wasun mu shine muke taburi jameela musa(mrs) surayyahms...haleematu sadeeya (leema) real me dambu ,meemah,ummuhany! ummu farhana,,fateema A first, haleema yahaya twenty! umman sayeed,khaleesi, saleehat (beuty) leema sabo and real bello_🥂
⬅
suka rankaya cikin gidan... sukayi sallama sau ukku babu motsi, munawar yace mushiga mana duk yanda naganta ai matatace...shiru Ahamad yayi yace kadai shiga kai in yaso daga bisani ni nashigo haram ne naganta babu hijabi...cikin zumud'i yasanya kai yana kiran sunanta amma shiru, yace Ahamad jikina nabani ba kowa cikin gidannan bani number ta mukira muji inatake...? dariya Ahamad yayi tare da cewa sarkin rawar jikk bata da waya, bara mubincika maqota se akira mana itah... haka kuwa Akayi wani matashin saurayi sukayiwa sallama tare da cewa dan Allah ina jalee ke zama? d'agowa yayi yadubesu yace gaskiya labarin dana samu shine jalee takoma birni bata mayi sallama da mutanen gariba se zaginta akeyi...A tare suka fidda ido bakunan su nafurta takoma birni? eh takoma yabasu amsa...Ahamad ne yayi qarfin halin cewa tun yaushe? yace koda dai akawayi garin jiya babu labarinta...innalillahi wa inna ilaihim raji'un, inna lillahi wa inna ilaihim raji'un Ahamad ke fad'a yayinda gigicewa da tashin hankali suka bayyana A fuskar munauwar...duk kuma sunkasa motsin kirki da kyar Ahamad yace kaji munauwar meyakamata muyi? cikin muryar kuka yace bansani ba Ahamad, kaina ya kwance bansan cewa Akan
*BAQAR RANA* ne nake saqa burina ba...dafa shi Ahamad yayi yana cewa karkayi saurin yanke hukunci? why Ahamad? yafad'a muryarsa narawa! yawu yahad'e tare da cewa babu tabbacin cewa ta tafi muqara bincike...haka suka fara binciken sedai labarin irri d'ayane ta tafi birni batayi sallama da kowaba...jiki Amace Ahamad yazaro waya yasanar wa Abba... haqiqa hankalin dattijon yayi qololuwar tashi dan seda gumi yaketo A goshinsa cikin sarqewar murya yace Ahamad ka tabbata ance ta dawo? ita dawa? yaushe ta taho? tare yajero tambayoyin... Ahamad yakasa furta komai dan bashida wad'annan Amsoshin da kyar ya kalato yawuun bakinsa dake neman hijira yace Abba bansan komai ba kawai duk wanda muka tambaya cewa yake ta tafi birni...gwaron numfashi ya sauke tare da cire gilashin idonsa yace inashi mijin nata? gashinan se kuka yake tamkar macce Abba...innalillahi wa inna ilaihim raji'un, Ahamad ba lokacin kuka bane kuyi hanxari kuje tashar mota kuyi tambaya in babu haske kumiqa report wa police sannan kudawooo gida musan Abunyi kajii... lumshe ido kawai yayi yakashe waya, yadubi munauwar yace haba kadaina kuka mana zamuganta da ixinin Allah...duban Ahamad yayi tamkar soko yace karka tsaida kukana bazan iyaba Ahamad kanemomin jaleelata kar zuciyata ta fashe dan Allah...bece komai ba dan yayi imani duk furucin da zaifito bakinsa dai dai wannan lokacin tabbas kukane yasa hannu yajawo munauwar suka tafi...tafiya suke kawai batare da hayyaciba Azahiri, bad'ini kuwa munauwar tamkar yafashe da dariya yakeji haka harsuka isah tashar gusau...da Azama suka fara bayani ga masu tsaron qofofin Aka tambayi suna suka bayar aka duba daga jiya zuwa yau ba Ad'auki macce me J ba gabad'aya hankalin Ahamad ya linka tashi yatambayi kansa wai ina jaleela tashiga? meyasa ma zata masu haka? ko tamanta zasu shiga tashin hankali me girma ?idan ta tsere masu... da wannan saqe saqe masu d'aci ga zuciya yajuya hancin motarsa ixuwa maru police station......
asmeenat zeeyan💋🥂😍
[13/02, 20:52] +234 703 252 2872: *🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀3⃣6⃣
_saqon gaisuwa ta musamman gareku...!maman nannah,ummu hydar mmn Abba KD, sumayya yareema,teema cool,faeema zhara,mammy,ramlat, maryam umar,nusaiba zauro,hassana hasan,beuty,jameela (aunty) marayam,zee,zainab Aliyu,Aisha Abbakar, muh'd, mr rabi'u,zahara, ramla tukur,mrs jameela,fateema Abbakar umar,ruqayya hameedu, mamy harbau Aliya said,rabi sani,rabi mukhtar,rabiata jameela umar hammah, nafeesa umar, deeja, sajiyo, ralleya Abba, cervecer, bride umar, da wasu dai masoya da bansaka suna ina jone daku kar mucanye page in_
⬅
yajuya hancin motarsa ixuwa maruu police station... ba wani b'ata lokaci suka ga D.P.O bayan sun zauna Ahamad yafara koro bayani dallah dallah.. seda D.P.O ya gyara murya yace gaskiya yanxu bamuda case na Accident ko b'ata ko makamancin hakan...but kobamu photonta idan munji labari se musanar maku... sannan zamufara bincike daga yanxu insha Allah...yawu Ahamad yahad'a kana yace bamuda pix nata sedai na jariran nata kuma koshi tawaya...ohk badamuwa bamu haka sukayi had'in xender aka tura kana sukabada contact's d'insu suka tafi cike da b'acin rai...gudu suke sosai babu kwanciyar hankali har suka isah gidah da Azama dattijo yatare su yace ba Aganta ba ko? rud'ewar dake tare da Abba ne yasa su b'uyar da tasu damuwar, cikin sanyi da taushi Ahamad yace Abba ba Aganta ba ka kwantar da hankalin ka...cikin d'aga murya yace maganar banxa kenan...na kwantar da hankalina nasan wane hali takene? dan sale baya raye se nayi biriss da Al'amarinsa yau narasa kaina zaifi min kwanciyar hankali da rasa jaleelah...shiru kowanen su yayi dan yau Abba yarikice sannan daga bisani munauwar yayi qarfin halincewa kamata yayi Abba munemi mafita bamuda lokacin b'atawa...kamar yayi kuka yamaidawa munauwar martani dacewa kusan Abinyi qwaqwalwata bata sarrafa Abubuwa masu amfani ji nake kamar zuciyata ta tsage na huta Da Azabar duniya...sosai Ahamad ya tausayawa Abba dan kalaman sa kad'ai zasu tabbatar ma zauce yake cikin rad'ad'i da disashewar murya yace Abba zamu kai sadaka masallatai da kuma kai report wa police na sokoto sannan zamu watsa labarin kafafen sada zumunta na yanar gixoo ko Allah zaisa aganta...kallo Ahamad kawai yayi me nuni da cewa ya amunce...haka suka fita sukabar Abba da zariya yana duban hanya,,,,suna fita Ahamad yace munauwar mu raba kai kaje masallatai ni naje police...cikin zuciyarsa murna yayi da zancen Ahamad Afili kuma cewa yayi thom muyi hakan Allah yadatar damu...suka rabu Ahamad police yayi shikuma gidansa yazame...yana shiga ya qyal qyala dariya sannan yafad'a ban d'aki yayo wanka yasa wata jalabiya baqa mai taken inada damuwa...yafito ransa fall da farinciki...ya d'auko wayarsa yaddana numbar Amma cikin zumud'i tace d'an halak kundawoooo... yace Amma naso dake mukayi tafiyar nan dakin rantse da ubangijin ki bansan komaiba akan b'atan jakar nan ...kai munauwar bara dai naxoooo inaga labarim zaifi armashi...dariya yayi har haqoransa suka bayyana yace ohk kiyi sauri dan d'an nacin can na iya zuwa daga yanxu zuwa kowane lokaci thom ganinan zuwa...bayan mintuna 30 amma ta iso gidan Ana tafiya irrin wannan me nuni da nikad'ai keda darajjah...har ta iso tsararren room d'in khairat tana kwance kan kujera tayi d'aya d'aya da wasu fitinannun kayan bacci ga Alama dai ma dakayan takwana..cikin jin dad'i da sanyin rai ammah ta iso ga khairat kad'an ta tab'ata Alamar tadata ne take...Ahanki tabud'a wutsiyar idonta tana ganin Amma tasaki wani mugun tsaki mai ciwoooo da nadama... cikin haushi tace ke ba'a gaya maki dokata bane in ina bacci ba A tadani...Ammah da Azama tacire madubin da yasamu arzikin zama fuskarta cikin qunar rai tace khairat kingane ni kuwa? tashi tayi zaune rabin nononta Afili ta tsaida idonta kan na Ammah tace nikuwa naganeki ba RABI CE MATAR DIKKO BA?
Asmeenat zeeyan nake maku fatan jumua lfy🥂
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀3⃣7⃣
_Alhmdullah bini'imaty💞_
⬅
ni kuwa nagane ki ba Rabi ce matar Dikko ba?... galala tacigaba da duban khairart tana d'aga kai da kyar kuma tace ni koce khairat, sedai kisani kinyi da maiyi dan yau ba se gobeba zakisan na iya haihuwa...hhhhh khairat ta qyal qyala dariya tana kwaikwayon muryar amma da inkaji sautin kasan Ab'ace take...sannan ta tsagaita tace dukkkk bura'ubar ki kice yasakeni taqamar ku kenan iyayen miji to bud'a kunnenki biyu kiji bana wata nadama domin inada mijina...tasss amma ta gallawa khairat mari hannuta be gama saukaba khairat tamaida mata martani da biyu masu zafi da rad'ad'i seda amma takife ga tyels ta juya d'uwawu tace bana cikin jerin matan da iyayen miji ke wulaqantawa domin banyadda da so ba, bare ya illatani, nadai yadda da ilmina kyauna da kuma wayewata...Amma rabonta da qwallah tamanta rana takasa motsi ga khairat se dasa mata magana take...suna wannan yanayin munauwar ya sauko da pure milk cikin hanzari da kad'uwa yace wai me ke faruwa...juyowa khairar tayi tadube shi tace mari na tayi na rama...rassss gaban munauwar yafad'i yace kinsan kuwa me kike furtawa khairat...? inaji bakaji da kyau bane marina tayi na rama tana farfarniya da idooo, cixaah leb'e kawai yayi bece komaiba yayi kan Amma, cikin tsawa me sa hanji su motsa tace kana nufin taci BULUS kenan? bazaka nuna mata banbanci tsakuwa da Aya ba? kamar zeyi kuka yace thom ni Amma me zanyi? bansan me yahad'aku ba...hannu takai ta wanka masa lafiyayyen mari tare da cewa yanxu ka fahimta ko yaya...? dafewa yayi tare da cewa ni meye laifina amma? da haka kawai zaki mareni...mekike so nayi ne? d'agowa tayi idont jajir tare da cewa gaskiyane ba Abanxa Allah ya hallici shed'an Ajinsin maza ba... to indai baka gane ba so nake kazab'a ni ko itah! shiru ya ratsa me d'auke numfashi ga munauwar, da amma... yayinda khairat ta tsiyaya barasa tasha sannan tace ni nazata wani Abun kirki zakiyi wallahi kazab'a ni ko itah...tajah tsaki tayi u'war d'aki...cikin rishin kuka Amma tace munauwar yaushe kazama soko? yanxu har kayi auren da zakazama mijin tace? shikenan kazauna da khairat ni dakai har Abada...da azama ya miqe ze d'aga qafa khairat daga ta taga da take kallon su tace my really...ya juyo suka had'a ido, cikin yanga tace kana d'agawa kasanya igiyoyin Aurena da kai sun katse...cak! ya tsaya suka hau kallon kallo da Ammah gumi se keto mata yake, tsayin mintuna sannan tace daga yau kinqare mulki gidan d'ana gwara da nagani tun yanxu...fuuuuuu tafita zuciya kamar ta dirooo qasa...tana fita tace ma drebanta zamau mukayi...cikin ransa cewa yayi Allah kashirya baiwarka dan yasan gurin da take magana suje gurine na had'a Allah dawaninsa...Arayuwar sa kamar yamata wa'axi sedai yasan tamasa gargad'i me muni cikin tilastawa yad'au hanya......munauwar kuma khairat ta fara mantar dashi Abunda yafaru ta hanyar makircin mata...gefen jaleela ta farka taganta inda bata tsammani gidan duniya kenan da bata mararin xama a cikinsa cikin gigitaciyar murya tace ina husaina da hassana? wayyo usaina bazan iya rayuwa babuku ba... wayakawo ni batare daku ba? Allah karka jarbceni da rashin su usaina xan banu in lalace wayyo...kwance take jigace tana kukan da maganar! shiru kowa yayi dan tana cikin ma wuyacin hali, da kyar wata siririyar likata ta qaraso ta riqe hannhta tace haba baiwar Allah komai yayi tsanani maganin sa Allah, matsayin ki na musulma yakamata kituna cewa jarrabawa ce daga ubangijinki wanda yafi kowa sanki da qaunar ki...! seda tajah kuka mai ban tausayi tace to meyasa yake jarbtata da manyan qaddarori bayan ina iya qoqarina dan ganin ban sab'a mashi ba...haba sister kiyi gaggawar tuba zuwa ga ubangijin ki kan yakamaki da laifin maganar ki...tajah kuka tace karkiga laifina y'ar uwa tawa jarrabawar me santsi ce da raba mutum da imanin sa ce...kallon ta tayi cikin rauni zuciya tace yakamata kisan kafun ke anjarbci Annabawa da manxanni da salihan bayi sukayi haquri Allah yasaka masu da mafificin alkhairi meyasa ke bazakiyi kwad'ayin koyi dasuba...kallon matar kawai tayi se tafashe da matsanancin kuka me girgixa zuciya da fassara me bantsoro
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀3⃣8⃣
_ALFAHARI NAKE DA TAWA MRS JAMEELA MUSA (MEELAT) DAN HAKA WANNAN PAGE NAKINE_
⬅
Me girgixa zuciya da fassara me bantsoro...... itama cikin kuka da sigar rarrashi taqara riqe hannun jaleela, kana tasaita tace kiyi shiru ki fauwalawa Allah lamarinki kinji... batare da bud'e idoba tace yaza'ayi nayi shiru..? narasa usaina da hassana sanadin qaddaratah...me yasa na farka duniya...? cikin wannan
*BAQAR RANA* da Abadan tarihin ta bazai goge Axuciyata ba? me yasa? tana rishin kuka take maganar...seda duk dayawa suka koka dan jaleelah na cikin tashin hankali da sanin qirmansa se ubangiji da ya rubuta faruwarsa tun kan tazo duniya...wani magidancin likita yamasto daff da itah yace baiwar Allah kiyi haquri da saqon Allah...kituna lokacin da baki dasu, kituna ba wayo kowani kwalliya kikayiwa Allah ba, tausayinsa da saukar da baiwa inda yakeso yasa yabaki...yanxu dan yayi nasa ikooo se ki butulcewa ni'imarsa ta baya...? bayan dakansa yake cewa ko godemin da kyautukan da nake maku inqara maku... yakamata ki kasance me juya zuciyarki ba wai ita tajuyaki ba!! domin bakida labari watarana zata turaki wuta... seda tadafa kanta da rad'a rad'an jijiyoyi suka bayyana tace wannan gaskiyane...da yarana mutuwa sukayi salon Alun, tabbas bazanyi kukaba... !Amma yanxu yazama wajibi na zubda hawaye domin kisan gillah Akayimasu gabana wanda basujiba basu gani ba, bala'in rayuwata ya wuce dasu...seda kowa ya d'auke na wasu mintuna sannan wani yayi qarfin halin cewa wa yakashe maki yara? jimmm wuri yayi tsit se hawaye dake reto A idon jama'a sannan tace Mugun miji agareni, Mugun uba Agaresu...taja majina da shasheka tad'ora da cewa shi ya Ajiye ma kurasu Ajeji ta cinye su...innalillahi wa inna ilaihim raji'un...shine bakunan mutane ke Ambato da kyar wani yace haqiqa Alamomin duniya sun fara bayyana, mutane sunfara kashe jininsu da kansu...wani yajefo da cewa kinsan inane mijin yake? mu d'aukar miki fansa...wani kuma yace ku sassauta mata da tambaya har tadawo hayyacinta wata qillll tarasa hankalinta ne amma banaji zamaninnan da iyaye keson y'ay'nsu fiye da rayukansu! akwai wanda zaiyi fasadin ba kura yaransa ta cinye...da yaya tayi yawa dole aka fitar da kowa waje aka barta...haka tacigaba da kuka marar sassauci ga rayuwa har dare ya tsala...Night duty sister Asmeenat keyi, taji labarin jaleela da Abunda take fad'a A harshenta wanda takasa yadda da hankalinta take zancen ko zauceawa tayi? da taga Abun yaqi cinyewa ta taso cikin raunin murya tace baiwar Allah...bata Amsaba tadai d'aga idanuwanta dasuka fara zama redish brown ga kala tasake lumshewa hawaye na zariya cikin kunnuwanta...cikin hikima da baiwa sister Asmeenat tace dan Allah kijinkirta kukanki kisanya aranki ko wane tsanani yana tare da sauqi guda biyu...lada mai yawa da kuma sauya tsananin zuwa sauqi, ki tsaida harshenki akan Ambaton lailaha illah anta subuhanaka inni kuntu mina zalimin, domin ubangiji shine Arrahamani rahim, yafi kowa kusa dake kuma yafi kowa tausayin ki, kuma narantse da Allah inkika barmashi zai amasa dukkan kukanki ya sauya maki da Alkhairansa...cikin sassaucin murya tasaki shashsheqa tare da cewa ngd da shawara kuma zan koyawa zuciyata cewa ta amshi wannan qaddarar har lokacin da ijaba zata sauka...yauwa haka yakamata musulmin kirki yakasance da yarda da qaddararsa domin kuwa gwargwadon yadda kake yarda da qaddara haka ne gwargwadon imaninka, da irrin wannan kalaman tayi nasarar tsaida kukan jaleelah suka cigaba da zama shiru sedai shashsheka da ba arasawa ga zuciyarda tasha kuka......gafen Amma ta isa zamau lafiya but kamar kullum matasan mata mushirikai da basu yadda da Allah ba suna nan laye kamar masu amsar gafara...haka ta kutsa tasamu gurfanawa gaban me yankan wuqa...seda yayi ihuuuu sau biyar sannan yasaki dariya yace ya Akayi...? tarissina irrin zakayi sajjada tace wani tashin hankali yasanyoni gaba me yankan wuqa, nakeso ka gaggauta warkar min dashi kafun yazama ciwo Azuciyata......
ASMEENAT ZEEYAN NGD DA SHARHIN DA KUKE MUN MUHAD'U GOBE🥂
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀3⃣9⃣
_ALFAHARI NAKE DA TAWA MRS JAMEELA MUSA (MEELAT) DAN HAKA WANNAN PAGE NAKINE_
⬅
nakeso ka gaggauta warkar min dashi kafun yazamo ciwoo Azuciyata...seda ya qyal qyala dariya irrin ta shaid'annun bil Adama,, kana yace fad'i damuwarki na bada rayuwata dan ganin nabiya maki buqatarki Rabi...sake rissinwa tayi tace meyankan wuqa akan d'ana ne damatarsa nakeso ka taimakeni nacigaba da janragamar zuciyoyin su bawai nazama tamkar Allo se sunjingina ni ba...hhhhhhhh yabuga qasa yace d'anki har yanxu Aljani kwankwan na Ajikinshi...kuma zuciyarsa kangare take baya jin maganar kowa se taki, sannan yana walaqanta matarsa yadda kikace Asanya mashi rashin imani da rashin tausayi...seda ta had'a yawuuu tace kaga farceni me yankan wuqa...munauwar ya auri kalar wadda nakeso, sedai bata bin umurnina. ita nakeso tadawo bayana se nace mata ga gabas...dariya yayi sannan yayi wasu y'an kuwace kuwace yayi tsitttt na daqiqa talatin yace wannan Aikin jane...matar d'anki tabiyu shaid'aniya ce...tanada Aljanu bisa kanta da inmukayi Asiri zasu warwareshi, kuma suna makantar da d'anki intana tare dashi, baya ganin girman kowa se nata...shawara d'ayace kicigaba da mulkin jaleela da d'anki lokacin da baya tare da khairat...Rassss gaban Ammah yafad'i tace A'a meyankan wuqa kayi Abu dan Al...bata iyar ba yace karki kuskura kikira muna Sunan Allah anan...qara gyarwa tayi tace Ayimin aikin gafara me yankan wuqa, bazan komaba adai taimakeni...cikin gumjin murya yace zan taimakeki, sedai kisani akwai sharud'a, tare had'ari me muni qarshen rayuwarki, me kikace? seda ta saita murya tace ko zanyi yawo tsirara ina tallah farji ga titi na Amunce idan harzanbiya buqatata...shewa yasaki yace haka nakeson ji... da farko zaki tsaida sallah ta kwana shad'aya, na biyu zaki yanka baqar mage kiba munauwar namanta, na ukku zai qauracewa matarsa se bayan kwana sha ukku...in kuma yasadu da itahhhh muna cikin Aikinmu toooo har kangarewar da biris da yake da zancen Abbanshi xai warware kinji me nace? idan wannan ne bana haufi duka zanyi fara aiki mai yankan wuqa,, yace shikenan yau jumua" kifara neman baqar mage lahadi nakeso kifara aikin nima lokacin zanfara...da haka sukabaro garin zamau...suka dawo sokoto...Abba na zaune yakasa gane komai ta wuceshi dan fara shirinta...shima be kulata ba dan duniya ta matseshi sauraron inda zai sami labarin jaleela ne damuwarsa...bayan wayewar gari tun da sanyin safiya Ahamad yataso yarame idansa har sunyi zurfi yagaida Abba tare da jajinta lamarin da yadame su...sannan Abba yace Ahamad kasake komawa gusau kaje manyan hospital kaduba ko zamu dace, shikuma munauwar se yaje na nan sokoto mugani tunda nema muke kozamu dace...hakane Abba bari naje...fitar Ahamad da mintuna sega munauwar, yagaida Abba tare da jajinta lamarin sannan yayi cikin d'akin Ammah...kwance yasameta tayi rufff da ciki tana saqa wani Abu, yashiga, da sallama murya d'ashe, kamar komai be faruba ta tareshi tare da tambayar lafiyar khairat? har aransa yaji dad'i kana yasanar mata Abunda Abba yace...murmushi tayi kawai dan tasan wainar datake toyawa...sannan daga bisani tace lahadin nan zan aikeka tanzania kasan yadda zakayi kacewa Abbanka xakayi tafiyane akan binciken jaleelah...karaf ya karb'e dacewa babu damuwa amma zanyi haka sannan yafita...Gefen jaleelah kuwa tana nan dai tagodewa Allah babu Abunda kemata gezau se y'anbiyu da bawa zuciya haquri,tana kwance police suka fara yimata tambayoyin cin rai sedai Amsa d'aya tabasu cewa ba shi yamata komai ba kana.........
kuyi haquri da wannan pls
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
*🅱AQAR RANA*
*NA*
*ASMEENAT ZEEYAN*
◀4⃣0⃣
MAMAN NANNAH
MARYAMA
MAMY HARBAU
MRS JAMEELA
DOTA FATEEMA ZAHARA
YAKAI INDA KUKE SO YAKAI
⬅
kana.......suka dubeshi sukace yanxu yaza'ayi? yace xai d'auketa yaje da itahh gidansa kan tadawo hayyacin ta yasada ta da magabatan ta,,,,haka sukayi musayar contact da shi sannan aka sallame jaleela dan ciwoonta yana d'aya daga ciwon da keda group non pharmalogical therapy, hospital bazasu shawo kan matsalar ba kenan, zaifi sauqin warkewa ta hanyar indvidual therapy, but duk dahaka seda sukabata health education daga bisani sukayi counselling da wanda zaije da ita gidansa suka nuna dole yariqa reassurance nata da bata kariya, sanna wajibi yanuna mata tayi haquri...da haka suka bar hospita yad'auki hanya dazata sadashi da garin gwbvna kaduna kenan...jin shiru yayi yawa se yasa karatun qur'ani suratul Abas...sura me magana akan wani rikitaccen wuni da babu makawa se kowa ya halarce sa...lahaula walaquwata illah billah, haqiqa sha'anin wunin yagirma mata da miji anyi soyayya ana cewa hony abban wance gidan duniya Alokacin wunin tsaki zakuyi in kun had'u da juna...la ilaha illah lahu... wunin da surar ke magana yagirma,,,,hakan yasa suyin shiru suna tasbihi Ila rabbihim...can ganin man motarsa yayi low yasa shi saka hancin motarsa cikin A.zamson petroleum dan yasha mai...kud'i ya miqa aka bashi har zaitada mota se yafitooo yarabawa wasu gajiyayyu sadaqa bisa tsau tsayi begani ba phon d'inshi ta fad'i qasa kuma ba wanda ya ankara bare ya miqa masa...! har yashige mota yatada yatafi be lura va...Gefen Ahamad kuma yashigo garin gusau lafiya" da Assibitin qwararru yafara inda aka d'auke jaleelah...cikin sa"a yafara d A and E dep. d'akin da takwanta sallama yayi daga bisani yanemi ganin I.C na gurin ba b'ata lokaci aka sadasu cikin girmamawa suka sake gaisawa daga bisani Ahamad yace nema nake nawata qanwata da tab'ata, to se mukaga yadace muxoooo muduba...shiru I.C yayi kana yakira Doctor owalanke...cikin harshen turanci yace ya zagaya da Ahamad d'akunan su yaduba ko zaiga nashi, in babu suje d'akin Ajiye gawawaki yabincika...haka akayi...Ahamad dubawa yake yana kuka yanaqara respecting ma aikacin lafiya, danshi ke saving more million lives batare da duba Albashin saba, yana haka suka shiga d'akin da yatsaida numfashin sa"" ganin mataccin mutane cikin cool planing kamar suyi magana wasu harsunfara qanqara lahaula wala quwata illah billah...haka yafito jiki sab'ule babu qwarin guiwa..har yafito aka tuna an sallami wata patient aka kirashi yazana kamanninta Exectlly patient d'inda suka sallama ga wata hujja husaina da hasana da bakinta ke ambato...seda sukayi gyaran murya sukace bi ixnillah itace...bejira komaiba har bakinsa kerawa wurin cewa dan Allah iina take? yanda yayi maganar seda suka dubeshi kana sukace case nata na police kaje can zaka samu bayani...har jikinsa ke b'ari wurin cewa wace police yallab'ai? maru suka bashi amsa...sajjada yayi kana yafad'a mota yana godiyar Allah tayoyin har barin qasa sukeyi dan yayi sauri yaga jaleela da kuma Abunda yasameta cikin mintuna qalilan ya isah tare da yiwa S.S.P bayanin Abunda yakawo shi...bawani b'ata lokaci aka kira hamisu wada danshi ke kula da case d'in, haka yazo tare da bud'a file aka kira contact d'in wanda yatafi da it,a wani Abun haushi kira bakwai ba d'auka, ga na takwas se aka kashe wayar gabaki d'aya...hankalin Ahamad yatashi sosai, se aka maida Abun ta sadarwa daga ina aka kira line da kuma inda aka kashe shi tanan suka dawooo kai tsaye suka gano bayan A.zamson petroleum ne dake tsafe har zasu tafi Ahamad yakira Abba yasanar mai halin da ake ciki...kamar yaro yajinqa hannu yace wow! Ahamad yanxu zamu d'auko hanya nida munauwar......
comment's reader's nagaida ku kuna daban ne A xuciyata nadaina ganin beuty😢
*🅱RILLIANT WRITERS ASSO...🖊*
( _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_)
🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑🌑
0 comments:
Post a Comment