A can kano kuwa har gobe neman Abuturrab Abba yake, har imagining irin hukuncin da xae masa yake, Sosai Mami ta damu ganin har kusan sati bbu labari, to ina Aliyu xae kai yar mutane, kullum Hajiya Mariya sai ta xo gidan yayar tata tana kwantar mata da hankali amma ko kadan bata nuna tasan idan Aliyu yake ba duk da ta lura xargin ta yayarta take, Mahaifiyar Samantha kuwa ba don mai gidanta da ya hanata ba kotu dama tayi niyar kai karan, bata da aiki sae kuka da tsine ma Abuturrab ta kuma dau kudirin ko da ya dawo da Samantha kasheta kawai xata yi kowa ya huta don bata san mugun abinda yaje yyi mata, da dai ace ta xama musulma gwara ta kasheta a cewarta, bbu bata lkci ta shiga shirin tafiya Jerusalem don yin addu'an Allah ya dawo da Samantha tayi masa sacrifice dinta, mahaifin Samantha kam mutum ne mai saukin kai da boye damuwa baxa ka taba cewa abun na damunsa ba. Ranar Asabar Samha na kitchen tana kkrin daura girki da yamma shi kuma Abuturrab na xaune balcony rike da sabon system din da ya siya don bai iya rayuwa bbu shi, d'aga kai yyi ganin shadow din mutum, ya ga fatima tsaye daga bakin balcony din tace "Mum tace matar ka ta xo" daga haka ta juya ya bi ta da ido, haushin ta ya ji har cikin ransa, ko kadan yarinyar bata yi masa ba, ya ga alamar bata dau hali irin na mahaifiyarta ba sai girman kai, ya tabe baki ya mike ya shiga ciki, kallonsa Samha tayi jin abinda yace, can tace "Toh girkin fa!" Yace "Don't worry ki sa hijab ki tafi" ba musu tayi yanda yace ta fita xuwa part din Hajiya, tana parlor da duk 'yan matan nata uku sai wata dake xaune tare da fatima alamar kawarta ce, Samha ta risina ta gaisheta ta amsa da fara'a tace "Kadaici bai damun ki Samha, ki dinga shigowa nan ku saba da su fatima mana" murmushi Samha tayi tana wasa da fingers dinta tace "Toh" Hajiya tace "yauwa ko ke fa, xama ke dayan nn bbu dadi, ki dinga shigowa cikin mutane" kai samha ta gyada mata, Hajiya tace "Kar fa ki daura girki xa a kai maku idan an gama a nan kin ji" murmushi Samha tayi bata ce komai ba, Mami tace "Gobe su fatima xa su saloon sai ki bi su ki ga gari idan mijin ki ya amince, ke ma sai kiyi gyaran gashin daga can" Samha tace "Uhm to Mami" Fatima ta mike ta dalilin wayarta da yayi kara ta kalli kawarta Bilkisu tace "Gashi sun kira Billy" daga haka suka fita balcony, a waje Billy tace "Teemah new tenant din gidan nan ne yarinyar nn?" Fatima ta kalleta sae ta fasa d'aga wayar tace "Ehh" Billy tace "Kai amma yarinyar is pretty... Amarya ce koh?" Fatima tayi wani murmushi tace "Sai ma kin ga mijin xa ki san she is nt pretty...." Billy ta wara ido tace "Haba dai??" Fatima tace "Uhn He is more than cute, kin san Allah gabana faduwa yake idan muka hada ido da shi, but sai in wani daure fuska ko gaishesa bana yi" Billy tace "Waoww xan so in gansa kuwa" Fatima xata yi magana sai ga Samha ta fito ta sa takalmanta ganin yanda suke kallonta tace "Sannun ku" Billy tace "Yauwa!" Daga haka tayi wucewarta xuwa part dinsu duk suka bi ta da ido. Abuturrab yace "Har kin dawo?" Kai ta gyada masa tace "Tace xa mu je saloon gobe da yaranta" Shiru yyi yana kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Allah ya kai mu" ciki ta shiga tayi kwanciyarta tun da tace kar tayi girki, fatima ce ta kawo masu abinci kusan Magrib bbu sallama ta shigo parlon, Abuturrab na xaune yana kallo a system Samha na gefensa ta jinginar da kanta jikin shoulder dinsa idonta a kan system din ita ma, a tare suka daga kai suna kallonta, ko kunya taji sai kuma ta sunkuyar da kai tace "Assalamu alaikum" Samha ce kawai ta amsa ta karaso ta ajiye abincin tace "Mum tace a kawo" Samha tace "Mun gode" daga haka ta juya ta fice. D'an tsaki Abuturrab ya ja can ciki, Samha ta kallesa tayi murmushi bata ce komai ba. Washegari khadija ce ta taho Balcony tana kallon Abuturrab dake duba newspaper da ya siya daxu da ya fita karo masu kaya a boutique, gaishesa tayi ya amsa tace "Wae Ummin mu in kira Anty Samha idan ta shirya" Abuturrab yace "Toh ga ta nan xuwa, ya sunan ki?" Tayi murmushi tace "Sunana khadija" yace "Alryt xan fadi mata Khadija" juyawa tayi ta wuce ya bi ta da kallo ganin banbancinta da yayarta, baxa ta wuce shekaru sha bakwai ba amma tafi yayar hankali, yana xaune parlor samha ta fito da hijab har kasa tana kallonsa, murmushi yyi yace "Cute" murmushin ita ma tayi, yace "Sae kun dawo but kar ki bari a dinga kalle min ke fa" dariya tayi yace "Yeah nikab ma xan siyo maki" kofa ta nufa ya bi ta da ido har ta fita, jiranta ta samu su Fatima na yi, Hajiya Hajarah tace "Toh sae kun dawo, Allah ya tsare hanya" driver ne xae kai su saloon din, fatima ta shiga gaban mota, Khadija da Rabi'ah suka xauna baya tare da Samha, su kadae suke mata hira har suka iso saloon din, fatima ta bude mota ta fita su ma suka fita suka bi bayanta xuwa cikin babban saloon din, khadija na kallon fatima tace "Big sis a fara yi ma Anty Samha koh?" Fatima ta kalli Samha ganin kallonsu take bbu yabo bbu fallasa tace "Alryt" daga haka taje tayi xamanta kan daya daga kujerun Saloon din sae dae can kasar xuciyarta ji take kamar ta shake yar uwar tata, Samha da Rabia aka fara ma gyaran gashin don akwae mutane saloon din, tun da aka bude kan Samha Fatima da duk yan saloon din ke kallo, matar mai gyara mata gashin sae cewa take "Maa sha Allah you've got a very fine long hair" Samha ta kirkiri murmushi bata ce komai ba sai dai duk a takure take ganin yanda ake kallonta, cikin minti ashirin aka gama mata ta mayar da hijab dinta da sauri, aka kama kan fatima sae dai ita kitso tace xata yi, ita din ma ba baya ba gun gashi, mai saloon din na kallonta tace "Baxa kuyi lalle ba Madam?" Khadija tace "Xa muyi" wani kallo Fatima ta watsa mata tace "ke da wa, waye xae jira kuyi lalle?" Khadija tace "Ae na tambayi Ummi tace mu yi" dauke kai fatima tayi bata ce komai ba, khadija aka fara yi ma snn Samha da taki yarda da farko har sae da Khadija da Rabi'a suka tilastata, suna saloon din har aka kira azahar, Khadija ta kalli Samha tace "Mu shiga daga ciki mu yi sllh Anty Samha" shiru Samha tayi sai kuma ta mike kamar mara laka ta bi bayanta, Khadija ce ta fara alwala a toilet ta fito snn Samha ta shiga, tsura ma tap din ruwan ido tayi, lkci daya xamanta gidan kanwar Abbanta ya fado mata, a hankali ta bude ruwan ta shiga alwalan kamar yanda take yi a kaduna da yaran Aunt dinta, tana gamawa ta fito ta ga Khadija ta shimfida mata wani darduma ta saka hijab dinta ta hau kan darduman babu abinda ta mance a ynda ake sllhn sae d'an abinda baka rasa ba, har hakan ya bata mamaki, tana idarwa Khadija tace "Me xa a karbo maki?" Murmushi Samha tayi tace "Bana jin yunwa..." Khadija bata ce komai ba ta fita, samha ta mike ta bi bayanta, snacks da drinks Khadija ta sa driver ya karbo masu, bbu yanda samha ta iya haka ta karba, ba su suka bar saloon din ba sai kusan karfe uku, part din su suka tafi gaba daya, Hajiya ta yi masu sannu da xuwa tana kallon Samha tace "Har kun dawo?" Samha ta gyada mata kai, tace "Toh sannun ku daughter, bari a xubo maku abinci" Samha tace "Ae mun ci" Hajiya bata saurareta ba tasa mai aiki ta xubo masu abinci gaba daya, har aka yi la'asar tana parlon, Hajiya tace "Khadija ku shiga ciki ku yi sllh" Khadija ta kalli Samha tace "Muje daki muyi sllh" ba musu Samha ta mike ta bi bayanta xuwa bedroom dinsu, kamar daxu haka tayi sllhn suka fito bayan sun idar, nan Hajiya tasa mai aiki ta xuba mata abinci ta kai ma Abuturrab, ta karbi abincin tayi godiya ta fita, Kwance ta samesa parlor yana bacci, ta ajiye abincin hannunta ta durkusa kusa da shi tana kallonsa tace "Doctor!" Bude ido yayi a hankali, ta langwabar da kai tace "Anyi sllh fa" ya mike xaune yana shafa fuskarsa, tace "Are you okay?" Girgixa mata kai yayi yace "Am having headache..." Tace "Toh kayi sllh sai kaci abinci then you take drugs" tana magana amma ido da hankalinsa na kan kunshin hannunta, ta bata rai tace "Ina maka magana" kamo hannunta yayi murya can kasa yace "Waow, baby kunshin yayi kyau sosai, i like it" ta kwace hannunta tace "Thanks" ya d'an marairaice mata yace "Toh baxan ga gyaran gashin ba?" Murmushi tayi ta cire Hijab din jikinta tana kallonsa, ya lumshe ido underneath his breathe yace "I have always loved you from the very first day i saw you Samha!" Kallonsa kawae take, ya bude ido a hankali yace "Tell me daga ina kike that very Night?" Murmushi tayi xata mike ya jawota jikinsa yace "Noo, talk to me baby" murmushin ita ma tayi tace "I don't want to talk about that now!" Yace "Noo plss baby..." Ganin yanda ya zuba mata manyan idanuwansa ta sauke kanta kasa a hankali tace "My frnd forced me to her birthday party, ni ban san it's an indecent party ba, shine na gudu na bar wajen..." Bude kofar parlon aka yi ta xame jikinta da sauri dai dai lkcn da fatima ta shigo, ta sunkuyar da kai ta karaso parlon, Samha ta xamo kasa a hankali ta xauna, takardun hannunta ta mika ma Abuturrab tana kallonsa tace "Ummi tace in baka wannan..." Mikewa yyi bbu yabo bbu fallasa yace "Drop it!" Daga haka ya shiga bedroom, ta bi sa da ido, Samha ta kirkiri murmushi da kyar ta karba tace "Bari in ajiye" sake mata fatima tayi ta juya ta fice daga parlon. Samha ta mike a sanyaye rike da takardun ta shiga dakin da ya shiga, xaune ta gansa gefen gado ta durkusa kusa da shi tace "Me yasa kayi mata haka?"
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By Khaleesat Haiydar📚✍🏻
_Tohm ya na iya tunda Ummu Ilham na da 'yan adawa irinsu Chamo, Zaarah, Teemahluv, Deezoh... Gasu nn dai🙄 su ma kuma sun ce sai fa an masu baxa su yarda ba, toh ina ku ke gashi nan sai ku kacalcala shi bbu ruwana naku ne_ 😆
37
Dagota yayi ya xaunar da ita gefensa yace "Kinsan me Baby?" Ta girgixa kai yace "Hajiya ta ban aiki...." Samha tace "Aiki kuma?" Yyi murmushi yace "Yeah she's also a medical doc...." Tace "Uhm hw did she know you re a doc?" Yar dariya yyi yace "Taga bana xuwa aiki shine ta tambaya nd i told her nayi ma Abbana laifi shi yasa na bar kano..." Xaro ido tayi tace "You told her everything??" Kamo hannunta yayi yace "No i didn't love!" Sunkuyar da kanta tayi, ya daura hannunsa kan dogon gashinta murya can kasa yace "Haka xa ki haifa min yara masu irin gashin nn kin ji" da sauri ta fara kkrin sauka daga kan gadon yaki saketa, kmr xata yi kuka tace "Doctor baka yi sllh ba fa..." Dariya yayi yace "Sai in tare xa mu yi bby" ta kallesa tace "Uhm ae yau na yi!" Yace "Dagaske?" Tayi murmushi tace "Yeah nayi Zuhur a saloon, nayi Asr a gun su Ummi" ya wara ido yace "Don Allah da gaske Baby, toh me da me kika ce a sllhn" wara ido tayi tace "Na fa ce maka ina yi a kaduna, rayuwar da nayi a kd a da yafi wanda nayi a kano da parent dina, am still missing my aunt, amma Mum dita ta rabamu wai she's putting me in the islamic way..." Abuturrab da ke ta kallonta yace "Toh me Abba yace?" Ta wara ido tace "Toh me xai ce? He said nothing, for the past 3yrs aunt dina bata xo gun mu ba..." Abuturrab yyi murmushi yace "Za mu kai mata ziyara knn" da sauri tace "Da gaske?" Yace "Yeah sweety, amma ba yanxu ba" daga haka ya mike yace "let me Ablute..." Washegari kamar yanda Hajiya tace da wuri Abuturrab ya shirya yana 'yan dube dube a laptop, aka danna bell, Samha dake goge gogen parlon ta mike ta isa gun kofar ta bude, khadija ce tsaye tayi murmushi ganinta khadija tace "Ina kwana Anty Samha" Samha tayi murmushi tace "Lafiya lau khadija" khadija tace "Ki ce ma Uncle Ummi tace tana jiransa fa" Samha tace "To" snn ta juya ta koma parlon tana kallonsa tace "Wae Ummi na jiran ka" mikewa yayi ya rufe laptop din ya langwabar da kai yace "Ko mu je tare ne baby, ke fa kadai zaki xauna gida" murmushi tayi tace "It's nothing ai na saba..." Yace "Alryt da wuri xan dawo kin ji?" Kai ta gyada masa ta rakasa har bakin kofa yayi peck din goshinta, ta juya da sauri ta koma parlon ya wuce yana murmushi, A parking space ya tadda ta tana jiransa, ya gaisheta ta mika masa car key din ya karba a xuciyarsa yace to da bai iya tukin ba fa, yana gama warming motar ta zaga ta shiga, duk wnn abun fatima na kallonsu ta window a daki, Ummi tace "Samhar fa?" Yace "Tana ciki Mami..." Tace "Duk xata ji bbu dadi ita kadae ga su fatima duk makaranta za su..." Murmushi yyi yace "Ae ta saba Mami" Sae da suka fita compound din tace "Ina matakin karatun ta ya tsaya?" Yace "Waec ta gama recently, but na kai ta tayi jamb registration nn garin" Mami tace "Good..." Daga haka ta dinga nuna masa inda xai bi har suka iso Clinic din, babba ne sosai asibitin, yana gama parking a space din da aka tanada don haka ta fito snn shi ma ya fita, ya bi bayanta xuwa reception, gaisheta nurses din dake gun suka dinga yi ta amsa ta nufi stairs xuwa office dinta, shi dai yana biye da ita har suka iso, Hadadden office ta shiga da shi, ta kunna Ac, ta yaye curtain snn ta xauna ta nuna masa kujera shi ma ya xauna, wayarta ta dauka ta kira wani likita, ba a dau lkci ba wani da baxae wuce Abuturrab ya shigo, ya gaisheta da ladabi ta amsa tace "A new doctor here, xa ayi employing dinsa a nn" Likitan me suna Shareef yace "Alryt, his qualificatios...." Ta girgixa kai tace "Forget that" ya gyada kai, snn ya juya ga Abuturrab ya basa hannu yace "Am Dr Shareef" Abuturrab ya karba hade da murmushi yace "Dr Aliyu" Dr shareef yace "Welcome to our clinic" Ummi tace "Office din kusa da naka xa ka bashi, idan Bashir ya dawo sai ya koma second flour" Dr Shareef yace "Alryt" daga haka ya kalli Abuturrab yace "Mu je Doctor" mikewa Abuturrab yayi yana kallon Ummi, ta dau makullin mota ta basa tace "Ba da dadewa ba xan fita meeting, when it's four sai kayi wucewar ka gida" yace "Toh ke fa Mami" tace "Akwai wani mota a nan xan fita da shi" yace "To nagode Mami" daga haka ya bi bayan Dr shareef suka fita, office din nasa madaidaici ne me dauke da table da office chair, snn da kujeru, sai show glass mai dauke da magunguna da injections a ciki sae gadon Anti Natal, da dai abubuwan da office din likita ke bukata, Dr Shareef yace "Hope you will like it here" Abuturrab yyi murmushi yace "In shaa Allah" Dr Shareef yace "Toh na bar ka lafiya" daga haka ya fita Abuturrab ya xauna kan kujera hade da lumshe ido. Kafin karfe daya patient din da yyi attending ma sun kusa goma, ana bude kofa ya hade rai, nurse din dai ce ta shigo da wani file kafin ta karaso yace "Ke doctors nawa ne a asibitin nn" kallonsa take bata ce komai ba, ya lura she derives pleasure looking at him, ya wani mugun hade rai yace "r you Daft?" Da sauri tace "Sir?" Kin cewa komai yyi yana kallonta fuskar nn tasa kamar hadari, tace "Amm, amm Doctors shidda ne sir...." Yace "Toh kar ki sake shigo min da file.... Fita" juyawa tayi ta fita, ya ja tsaki shi haushin irin kallon da take masa ma yake kawai. Kamar yanda Mami tace ana Asr yyi ma Dr shareef sallama, har ya kai bakin kofa ganin kallon da nurses din ke masa gaba daya ya juyo ya dawo, yace "I am Dr Aliyu, am gonna work here with you all for the mean time, yeah am very free nd friendly amma bana son kallo don Allah..." Daga haka ya juya yayi ficewarsa, wasu suka bi sa da harara, wasu kuma kamar idanuwansu xa su rakasu har gun motar. kusan a tare suka shiga compound da fatima a tata motar, yana gama parking a space dinsu ya kashe motar ya fito, ita ma ta fito da kawayenta biyu, ko kallon inda suke bai yi ba ya juya ya nufi part dinsa, duk suka bi sa da ido, Salima tace "Kaddai ku ce min shi ne" Fatima bata ce komai ba ta dau hanyar balcony dinsu, Billy ta sauke ajiyar xuciya tace "Shine mana" daga haka suka bi bayan fatima Salima na ta waigan Abuturrab da har ya isa part dinsa. Khadija dake parlor da Samha ta mike da sauri ganinsa tace "Sannu da dawowa Uncle" yayi murmushi yace "Yauwa khadija, how you?" Tace "Fine," Daga haka ta nufi kofa yace "Ina xa ki kuma" tace "Dama xan wuce ne" yace "A'a xo kiyi xaman ki" Shiru tayi bata ce komai ba ya kalli Samha yace "Ina yini Ma" murmushi tayi tace "Sannu da dawowa" yace "Thanks dear" daga haka ya shiga Bedroom, khadija ta dawo tayi xamanta parlon tana ci gaba da ba Samha lbrin da take bata. Kwance Abuturrab yyi Maminsa a ransa, haka kawai ya tashi da ita yau yaji ganinta kawai yake son yi, can ya mike xaune ya dau wayarsa, yyi jim kmr me nazari kafin yayi dialing numberta, yana fara ring gabansa ya shiga faduwa, Mami dake parlor ta rungume hannaye tana sauraren tijaran yakumbo, ba ayi ranan da xae wuce bata xo ta xaxxaga mata tsiyar ta fito da Aliyu ba, a da tana addu'ar Allah ya karkato hankalinsa ya dawo gida ko don xarginta da ake a kan tasan inda yake, amma yanxu kam addu'a ma take kar ya dawo don tasan duk inda yake he is fine don ya saba irin haka, matsalar daya ynxu da yar mutane da ya tafi banda haka ya shekara ma bai dawo ba in dai yana lfya ko a jikinta, dai dai nn wayarta ya shiga ring ta jawo da yake neman hanyar da xata bar parlon take duk da bakuwar number ne hakan bai hanata dauka ba upon maganar da yakumbo take cikin dag'a murya, Abba dai sai operating laptop yake, sallama Mami tayi Aliyu yyi shiru jin muryarta, har sai da ta sake maimaita sallaman, da kyar yyi gathering courage yace "Mami..." Sosai gabanta ya fadi jin muryarsa, ta mike ta kuma yin sallama kamar bata ji sa ba ta nufi stairs, a fusace yakumbo tace "Ahmad dubi ni ta tsallake ta wuce ina mata magana...." Abba ya kalli Mami da har ta kai stairs yace "Hajarah!" Ba tare da ta kallesu ba tace "Ina xuwa, Gwaggo na ce ke kira" daga haka ta wuce sama, Abba ya d'an kalli Yakumbo yace "Tana xuwa yaya..." Tabe baki tayi tace "Ta matse mata can, wato Ahmad ynxu shknn haka xa mu xuba ido an kasa sanin inda Aliyu yake, ni tsorona daya fa kar yaje masallaci a aura masa kafura mu shiga uku..." Sai ta fashe da kuka tace "Wllh Ahmad kaf xuri'ar mu kai ma kasan bbu tubabbe, wnn wace irin kaddara ce haka, mu Aliyu xae xuba ma duwatsu a ido, mu xae kunyata, mu xai toxarta?? toh wllh yyi kadan ko da ya auri yarinyar nn ko bayan raina sai an raba auren, mu xai haifa ma jikokin jaraba? Matsawar ina numfashi wllh wllh bbu aure tsakaninsa da tsinanniyar, ko ya aureta kuwa sae ya saketa, bare kullum axumi nake ina roko kada Allah ya basa ikon aurenta...."
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By Khaleesat Haiydar📚✍🏻
Tohm where r u my Fertymerh Zahrah and Ummi Aysha.... ku ma ga naku shuwagabannin Haske, Allah ya kara mana basira baki daya😍
38.....
Tun da ta fara Abba ya tsaida abinda yake yana saurarenta, tana kai wa aya kuwa tace "Ko ya ka ga?" Ya gyada kai yace "Haka ne!" Mami na shiga dakinta ta rufe kofar tace "Aliyu!!" Ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Forgive me plss Mami, i know i disappointed you, ki yafe min don Allah..." Tace "Kana ina yanxu?" Shiru yyi, a fusace tace "Baka ji na ne?" Yace "Mami don Allah kiyi hakuri, ina... Ina kaduna..." Tace "Karya kake Abuu, ina yar mutane?" A hankali yace "Tana nan Mami..." Mami ta girgixa kai tace "Yanxu rayuwar da ka xabar ma kanka kaga shi xae fishsheka Abuturrab, warce ba muharramar ka ba kake rayuwa da ka ajiye koyarwar addinin ka aside?" Shiru yyi bai ce komai ba, tace "Aliyu..." Nan ma dai bai ce komai ba, ta kuma san yana jin ta baxae dai yi maganan bane, tace "Toh yanxu meye amfanin haka Abuu, me yasa har gobe baxa ka dawo gentleman ba?" Xaunawa tayi gefen gado ta dafe kanta, can tace "Look kayi min magana ynxu bana son wlknci, tell me what's the meaning of what you did?" Ya bude idonsa dake rufe da kyar yace "I want to convert her...." Mami tayi tagumi tace "Ta haka ake converting din mutum Aliyu, ka dauketa ku gudu kamar wani Indian film kace min you want to convert her?" Murmushi yyi cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri Mami, ke ma kinsan ynxu idan na dawo da matsala, mami you've got to trust me, kinsan abinda xanyi da wanda baxan yi ba, ni bana fasikanci kin sani, just that this the only way out, xan dawo gida in shaa Allah amma har sai naga hankalinta gaba daya ya karkata ga islam, nasan duk abinda nayi ma 'yar wani surely xa ayi ma nawa kidz din kuma har kannina xai iya shafa sbda haka am very cautious of what i do...." Mami tace "A ina ku ke ynxu?" Yace "Muna Gombe Mami" ta xaro ido tace "Wa ka sani a can Abuu?" Yace "Bbu kowa gashi kuma har nasan mutane ynxu har na fara aiki" tace "Da wani CV din??" Yayi murmushi yace "Da na brain dina Mami" Mami tace "Aliyu ka rufa min asiri ka mayar da yar mutane, Aliyu ni wnn abinda kke son yi ko kadan bai gamshe ni ba, yanxu rayuwar nn wa kaga xae yrda xuri'arsa a samu irin haka, ba fa ce maka tayi tana sha'awar addinin ka ba, kai ke cusa mata kawai, gaba nake jiye maka wllh, shawarata kawai ka dawo in taga tana son musulunci xata yi ne ba sbda kai ba... Ka dawo kayi auren da iyayen ka ke son kayi Abuu, ka ajiye shashancin nn da kake yi son" da damuwa yace "Mami ni wllh ita kadai naji xan iya aure... Pls ki bani go a head ko yanxu xan iya aurenta nasan zata amince kuma dawowa addinina baxae mata wahala ba in har na aureta" Mami tace "Toh ba da yawuna ba wllh, in kuma shakiyancin naka har ya kai ka fara tsallake magana ta to bismillah, na fada na sake fada ba da yawu na xaka je a daura maka aure da Christian ba...." Daga haka ta katse wayarta, ya rike kansa. Can ya mike da kyar ya cire shirt din jikinsa ya kwanta kan gado hade da lumshe ido, ya fara bacci samha ta shigo dakin, durkusawa tayi kusa da shi tana kallonsa a hankali tace "Doctor..." Bude ido yyi don baccin nasa bai yi nisa ba, tace "Abinci fa?" Ya mike xaune yace "I've eaten sai anjima" tace "Toh..." Mikewa tayi xata fita yace "Samha!" Ta koma ta durkusa tace "Na'am..." Ganin kallonta kawai yake tace "Doctor i prayed today also..." Yace "Really?" Tace "Yea, tare da khadija, she came back from islamiyya around 1, shine ta xo nan... Tace min ita ma recently tayi waec" Yace "Waow, shknn kin samu frnd knn... Which means you weren't lonely today!" Tace "Yeah, tare muka yi girki da ita, i like her she's very nice" yace "Uhnn! Ai naga alama" ta langwabar da kai tace "Toh ko nima in dinga bin ta islamiyyan i don't want to be staying at home all alone kafin ta dawo" ya sauko da kafafuwansa yana kallonta yace "If that's what you want love sai in sa ki..." Tace "Ehh ina so!" Yyi murmushi yana kallonta yace "Alryt gobe sae ki fara koh?" Ta gyada masa kai, mikewa tayi tace "Let me go back tana parlor, nayi xaton xaka ci abinci ne" yace "Am ohkay dear, ltr xan ci" tace "Tohm" snn ta fice daga dakin ya bi ta da ido murmushi dauke fuskarsa, sosai yaji ddin islamiyyar da tace xata, and he was happy she brought the idea her self. Washegari yana dawowa daga masallaci ya shiga dakin da take ya tada ta, ta mike xaune tana mitsike ido yace "Yau baxa kiyi sllhn ba knn?" Ta kallesa tace "Sllh kuma?" Ya wara ido yace "Alryt dear, yi kwanciyar ki nayi xaton xa kiyi sllhn ne" bata ce komai ba hakan yasa ya juya ya nufi kofa, mikewa tayi ta bude kofar bayi ya juya ya kalleta bai dai ce komai ba ya fita ya shiga wani dakin don shiryawa tunda yyi wanka kafin ya je masallaci yana buttoning din shirt dinsa ta shigo da hijab jikinta, ta karasa dakin tana kallonsa tace "Nayi sllhn" yace "That's very nyc of you love... Allah ya karba" murmushi tayi tace "Me xan yi maka for brkfst?" Yace "Just lipton xa ki dafa dear, akwao bread" tace "Kwai fa?" Yace "Noo, ni baxan ci ba sai dai ke" juyawa tayi ta fita, ko kafin ya fito har ta dafa ruwan Lipton din ta ajiye a parlor da kayan beverage, ya karaso parlon ya xauna ta hada masa tea'n yana kallonta, ganin irin kallon ta sunkuyar da kanta, murmushi yyi ya jawo cup din tea din, tace "Baxan je islamiyyan ba yau?" Yace "Xa ki mana baby" mikewa tayi tace "Tohm bari in shirya" daga haka ta shiga daki, yana gamawa ya fita xuwa part din Hajiya, karo ya kusa ci da fatima da ta fito daga parlon hannunta rike da makullin mota tana sakale da jaka alamar boko xata, Bai ko kalleta ba ya bi ta gefenta ya isa kofar ya danna bell, kin tafiya tayi ta xuge jakar hannunta tayi pretending kmr neman abu take, Khadija ce ta bude kofar ta gaishesa da fara'a ganin shi ne, yace "Mami fa?" Tace "Tana ciki bari in mata magana" daga haka ta juya ta koma parlor, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Wai ka shigo" Bin bayanta yyi suka shiga parlon, dai dai lkcn da Mami ma ta shigo parlon, xauna yyi kan sa a kasa ya gaisheta ta amsa tana murmushi tace "Kun tashi lfya Boy?" Yace "Alhmdllh Mami" tace "Har ka shirya knn, in dai ka gama abinda kke tun da akwai makullin mota gun ka sai ka dinga wucewa kawai boy" yace "Toh Mami, dama samha ce ke son shiga islamiyyar su khadija, ina son in fara xuwa can da ita ne...." Mami tace "Maa sha Allah, kace mata in dai ta shirya ta xo sai in kai ta.... Kai kayi wucewar ka kawai" A hankali yace "Toh nagode Mami" daga haka ya mike ya fita duk da hakan bai gamshe sa ba don bai son Mami tasan bata san komai ba. Fatima dai na nn tsaye fa har lkcn, wnn karan tare masa hanya ma tayi duk don yyi mata magana, ga mamakinta sai gani tayi ya tsallake karfen dake xagaye balcony din yyi wucewarsa.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
Hmm where are you blood!😍 Ke ma ga naki, Allah ya kara hada kawunanmu sweet sis Iqram Mujaheed (Maryam M Bello) proud to have a sister like u.
39.....
Parlor ya tadda Samha yace "Dear ki shirya Mami xata ajiye ki a islamiyyan...." Shiru tayi tana kallonsa, ya kamo hannunta yace "Yea, i wanted taking u there by my self but she insisted...." Ta langwabar da kai a hankali tace "Toh" mikewa yyi yace "Yauwa baby, sai ja dawo" tace "Allah ya tsare...." Har ya kai bakin kofa ya juyo yace "Bbu rakiya dear" murmushi tayi ta mike ta bi bayansa suka fita a tare, hada ido suka yi da fatima dake tsaye tsakar compound din ta kasa tafiya, Samha ta kirkiri murmushi tana kallonta tace "Good morning sis fatima" Fatima ta mayar mata da yake tace "Same" daga haka ta nufi gun motar ta da take xuwa makaranta da, Shi dai Abuturrab bai ko kalli inda suke ba har ya isa gun motar da Hajiya ta basa ya juyo yana kallon Samha da ta bi bayansa, jawota yyi gabansa yana kallonta yace "Tohm sweet sai na dawo" murmushi tayi ta gyada masa kai, har xai kai bakinsa nata ko me ya tuna kuma ya bude mota kawai ya shiga tana tsaye ya gama bata wuta snn ya kalleta ya kashe mata ido ya ja motar hade da horn mai gadi ya bude masa gate, Kallon motar fatima kawai Samha take har ita ma ta fita da gidan, ta kusa minti uku tsaye tana kallon gate din gidan snn ta juya da kyar ta koma ciki. Cikin d'an lkci Abuturrab ya saba da doctors din clinic din bayan sun fito daga theatre a ranan, barin da suka ga shima kwararre ne, few nurses da yaga alaman suna da hankali kadai ya sake ma, sai dai fa throughout ranan duk da uban aikin da yyi hankalinsa gaba daya na kan maganganun Maminsa da ya tuna sai gabansa ya fadi, shi dai yasan he can't do without Samha, gashi dai duk rashin jin sa baya tsallake maganan Mahaifiyarsa sai dai by mistake, tunanin yanda xai shawo kanta kawai yake amma bai san taya ba, karfe biyar ya bar clinic bayan ya gama abinda yake, hadari ne sosai garin me hade da iska ya shiga mota ya dau hanyar gida, tsaye yyi da motar bakin gate yana jiran motar da ya tarar gate din ya shiga, cije yatsa yyi cike da takaicin clashing din da suke yawan yi da fitsararriyar nn a cewarsa, gani yyi ta ki tafiya bayan gashi ta danna kan motar compound din, mai gadi dai ya koma yyi xamansa, can kuma dai ta ja motar ta shiga, ya yyi tsaki ya bi bayanta yyi part dinsa, yana gama parking ya fito yana satan kallon motarta ganin irin parking din da tayi, har lkcn iska ake yi sosai ga yayyafin da aka fara, har ya nufi part dinsa ya juyo da sauri jin sound din da yyi kama da na faduwa, kallon mamaki ya shiga yi mata ganinta a kasa, ganin she's gasping for breathe ae bai san lkcn da ya nufeta da sauri ba, yana isa gabanta ya durkusa ya dagota, a dai dai lkcn da Samha da Khadija suka fito daga parlor jin tsayuwar mota, daukarta Abuturrab yyi ya nufi cikin parlor da ita da sauri don an fara ruwan sosai, Khadija ta xaro ido tace "Innalillahi, Her inhaler....." Daga haka ta yi part dinsu da sauri ita ma, ita dai Samha bin su da ido tayi, Abuturrab ya kwantar da ita nan tsakiyar parlon yana kallon khadija da ta shigo yace "Me ake bata?" Khadija ta nufi daki da sauri tace "Inhaler dinta..." Yana rike da ita Khadija ta fito kamar xata yi kuka tace "Ni ban san inda ta ajiye shi ba, ina ta dubawa...." Abuturrab na kallonta yace "Ina inhaler din ki?" Bai ga alamar ta ma san yana yi ba don she is fighting seriously to get her breathe, Abuturrab yace "Inhaler kadai take amfani da, ba a mata allura ne?" Khadija ta girgixa kai tace "A'a ba ayi, sai magani da inhaler...." Da gudu ta koma daki dubo maganin sai ga ta ta dawo a rikice tace "Ni ban gani ba wllh" Abuturrab ya ciro waya ya mika mata yace "Kira Mami yanxu" daga haka ya daga ta ya xaunar da ita ya cire mata veil din da tayi roll a kai, Ummi na daukar wayar Khadija tace "Ummi Asthman Sister ne ya tashi ban ga inhaler ba" Ummi tace "Subhanallah, where did she keep d inhaler kin duba motar ta, where is she now?" Khadija tace "Uncle ne ya shigo da ita yace in kira ki, let me check d car" Ummi tace "Alryt yi sauri ki duba ba shi wayar" Mika ma Abuturrab wayar tayi, ta fice da sauri duk da ruwan da ake xuwa gun motar yayar tata, Ummi tace "Hello Doctor, wai ba a ga inhalern ta ba koh?" Abuturrab yace "Eh Mami, ba ayi mata allura ne?" Tace "Ban fiye son alluran bane son, but idan ba a ga inhalern ba bari in kira clinic yanxun nn a kawo mata alluran..." Daga haka ta katse wayar, ya ajiye ya jinginar da ita jikin kujera yana kallonta yace "Where is ur inhaler?" Dawowa khadija ta kuma yi tace "Ni dai bn gani ba ka kara kiran Ummi plss" daukar wayar yyi ya kira mum din tasu kuma, tana dagawa tace "Na sa Dr Usman ya taho da allura ynxu, he is on his way, kafin ya xo you tell khadija to check my room gun da nake ajiye drugs ta kawo maka magungunan sai ka cire wanda xa ka bata..." Abuturrab yace "Alryt" ya kalli khadija ya bata sakon ta nufi dakin, tana fitowa da drugs din ya dudduba ya dau wanda ya kamata, ya karbi ruwan da khadija ke mika masa, maganin ya kai ma fatima baki snn ya bata ruwan yana kallonta, daga haka ya jinginar da ita jikin kujera, yana nn durkushe gabanta Khadija kuma na tsayr kansu Dr Usman ya kwankwasa kofar parlor, khadija ta karasa da sauri ta bude kofar ya shigo yana kallon Abuturrab da ya karbi ledan hannunsa yace "Har ynxu ba a ga inhalern ba?" Abuturrab na kokarin hada alluran yace "Yeah!" Yana gama hadawa ya kalli fatima da har lkcn numfashinta bai dawo dai dai ba, mika ma Usman Alluran hannunsa yayi yace "Ga shi kayi mata" Usman yace "Noo kai mata kawai mana" mikewa tsaye Abuturrab yyi ya kama hannun Usman ya saka alluran a ciki yace "Kayi mata doctor, ina xuwa yanxu" daga haka ya nufi kofa, Usman ya durkusa don yi mata alluran, part dinsa ya nufa cikin ruwan, har lkcn Samha na tsaye balcony, Murmushi ya sakar mata ya isa gabanta yace "What r u doing here baby?" Juyawa tayi bata ce komai ba tayi shigewarta ciki, ya d'an yi jim, sai kuma ya bi bayanta, kwance ya sameta parlor ya xauna daga gefenta yace "Abun yar shariya ce kuma dear" ba tare da ta kallesa ba tace "Welcome" ya d'an yi murmushi ya mike yace "Thank you" daga haka ya shiga bedroom, sauya kayan jikinsa yyi xuwa jallabiya ya fito parlor, tana ganinsa ta rufe ido kamar mai bacci ta juya baya, ya nufi inda laptop dinsa ke ajiye a parlon ya dauka ya xauna kan kujera ya bude, bai yi minti goma parlon ba aka danna bell ya mike ya isa kofar ya bude, Dr Usman ne tsaye yace "Doctor nayi mata alluran, da sauki jikin nata yanxu, i want to leave now" Abuturrab yace "Alryt Doctor, let me check on her again, sai gobe" daga haka suka yi sallama Dr Usman ya wuce, tsaye Abuturrab yyi bakin kofar, can ya juya ya kalli Samha da har lkcn bata juyo ba bare ta bude ido, fita yyi parlon ya ja kofar, Cikin ruwan ya shiga xuwa part din Hajiya, Khadija na xaune gefenta ta lullube ta ita kuma tana kwance kan kujera, karasawa yyi parlon yana kallonta, ba karamin tilasta kansa yyi wajen ganin ya bude baki yace mata "How you feeling?" Sae a snn fatima ta kallesa, sai kuma ta dauke kai ta gyada masa kai kawai alamar fyn, shiru yyi kmr me tunanin abinda xai ce kuma, can dai ya kalleta suka hada ido, kasa cewa komai yyi, yyi saurin dauke nasa idon ya kalli Khadija yace "Yaushe Mami xata dawo?" Khadija tace "Tace tana hanya ynxu" yace "Alryt," daga haka ya kuma satan kallon Fatima nn ma suka hada ido ya juya xai fita daga parlon yaji tace "Thank you..." Ya kalleta bai ce komai ba yyi ficewarsa. Part dinsa ya koma, wnn karan Samha bata parlor, ya shiga daki ya ganta kwance idonta rufe, juyawa yyi ya koma parlor, yyi ta xamansa yana operating laptop har aka kira Magrib, alwala yyi ya fita xuwa masallaci don ruwan ba sosai ake yi ba, ko da ya dawo ci gaba da abinda yake yi yayi, karfe takwas saura aka danna bell ya mike ya bude kofar ya ga Ummi tsaye tace "Son nagode kwarai fah" yace "Mami ae da kin kirani in xo cikin ruwan nn kika fito" tace "It's not heavy ae, ina Samha" yace "Tayi bacci Mami..." Tace "Alryt, Allah bar xumunci, I don't just knw what's wrong with fatima da xata dinga yasar da Inhaler dinta anyhow..." Murmushi yyi yace "Allah ya tsare gaba Mami" tace "Ameen, Allah ya tashe mu lfya" daga haka yyi mata sallama ta juya ta wuce ya koma ciki. Karfe goma ya shiga kitchen bai damu da abincin dake ajiye kitchen din ba kuma yasan na shi ne,ya hada tea kawai ya fito parlor, yana gama sha ya shiga second room, ruwan wanka ya hada a bathroom yyi ya fito yyi shirin bacci yyi kwanciyarsa.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
Kawayen Asali Maman Shakur and Fiddausi s Dangi Jiddoh na gaisuwa, ku sani ku na raina a ko da yaushe😘
40.....
Kasa bacci yayi ya rasa dalili, har karfe sha biyu da rabi idonsa biyu, mikewa xaune yayi daga karshe ya jima a xaunen kafin ya tashi ya nufi kofa ya fita, dakin da take ya karasa, ya kusa minti uku tsaye kafin ya tura kofar a hankali ya shiga, kwance ya sameta cikin bargo, ya karasa gefen gadon ya xauna yana kallonta, can ya sa hannu a hankali ya cire bargon, bai kai ga gama cirewa ba ta rike, kallonta ya tsaya yi can ya fixge gaba daya yace "Are you okay?" Mikewa tayi xata sauka daga kan gadon ya rikota yace "You re going no where har sai kin gaya min d reason for ur sudden change of behavior today, what's wrong with you?" Wani kallo ta watsa masa da yasa shi buda ido, ta kwace hannunta tace "That's because i want to be left alone...." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Look Aliyu, you take me back to my parent immediately, i don't want any of this anymore...." Fixgota yyi yana mata wani irin kallo yace "Amma dai bni nasa ki taho gidana ki same ni ba that very night ryt?" Tsayawa tayi tana kallonsa ko kiftawa bbu, ya sake ta ya mike ya fice daga dakin ta bi sa da ido, har karfe daya tana nn xaune yanda ya bar ta ko motsi ta kasa, da kyar tayi karfin halin mikewa daga karshe, ta dau Hijab ta saka ta nufi kofa ta bude ta fita xuwa parlor, bata yi xaton ganinsa a parlorn ba, kuma suka yi ido hudu don kwance yake kan 3 sitter, ta dauke kai ta nufi kofar parlorn da sauri, mikewa yyi tana ganin haka ta ja kofar taji sa a rufe tana kkrin budewa da makullin jiki ya karaso ya fixgota, wani ihun da ya ji har tsakiyar kan shi ta saki tana son kwace kanta, ya rungumeta ya rufe bakinta da hannunsa yace "Meye hakan kike yi? Are you on ur right senses" Kokuwa ta dinga yi da shi tana son freeing kanta da bakinta a hannunsa amma ta kasa don wani irin rikon da yasa ko motsin kirki bata iya yi yayi mata, gajiya tayi tayi give up, sai a snn wasu hawaye masu xafi suka dinga xubo mata, duk jikinsa yayi sanyi a hankali ya saketa ta sulale nan gabansa ta fashe da wani matsanancin kuka, xubewa yyi gabanta kan gwiwowinsa shi ma, da kyar yayi karfin halin cewa "I didn't mean it Samha, forgive me plss i don't know what came over me...." Mikewa tayi da sauri ta kuma nufar kofar shi ma ya mike tsaye tun kan ta isa ya rikota, duka ta dinga kai masa cikin kuka tana cewa "Ka bude min pls i am going back to my parent, let me out immediately, xan maka ihu idan baka bude min ba" toshe bakinta yayi ganin da gaske ihun xata kuma yi, ya d'aga ta kamar yar shekara biyar yayi bedroom da ita ya direta kan gado yace "Pls you stop all this Samha and listen to me, am vey sorry don Allah kiyi hakuri i mean none of what i said to you....." Bbu irin lallashin da bai yi mata ba amma kamar yana d'a d'a tunxurata, sosai yake jin kukan da take har cikin ransa, wanda hakan yasa bai yi wani tunani ba ya kai bakinsa nata, nan ma dai ba karamin kokuwa tayi da shi ba amma lkci daya yasa ta nutsu, Tun yana yi don lallashi har abun ya fara wuce gona da iri, lkci daya ta fara kokarin kwatar kanta amma ta kasa don Abuturrab yayi nisa, xaro ido tayi da duk karfinta ta kwace bakinta cikin rawan murya tace "Don Allah kayi hakuri doctor ka sake ni, what's all this" doctor kam bai san tana yi ba, lkci daya ta fashe da kuka cikin rawan murya tace "Na shiga uku, Aliyu pls stop this am begging you, pls stop...." Da kyar murya can kasa taji yace "Pls Samha, you know... You know i... i love you..." Gigicewa tayi tace "Wayyo Mumy na shiga uku, don't Aliyu, i followed you because i trust you. Don't betray my trust for you.... Na yarda da kai...." Sama sama ya dinga jin abinda take cewa wanda hakan yasa jikinsa yayi sanyi amma ya kasa hana kansa, ji yake kamar his life depend on this, he just can't let go of her, cikin wata iriyar murya da ba tasa ba yace "Trust me Samha, auren ki fa xan yi..." Tana kuka sosai tace "Baka aure ni ba tukun doctor, don Allah ka tausaya min ka bari, ka daina plsss" Doctor fa yayi nisa bai jin kira, ba din daukewa da numfashinta ke kkrin yi ba tsabar tsoratar da tayi a lkcn da Samha fa an fita daga lane din da ake, ba shiri ya dawo Abuturrab dinsa sai dai duk jikinsa ya mutu, lallashin nata ma ya kasa, yana kallo ta mike ta fada bathroom, bayan kusan minti goma yaji karfi ya xo masa yayi karfin halin mikewa ya nufi bathroom din, murda kofar yyi yaji a rufe, ya jingina jiki ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Open pls Samha, kiyi hakuri don Allah, i never meant that too..." K'in budewa tayi kuma bata ce masa komai ba sai dai yana jin sheshshekar kukanta, ya durkushe wajen ya dafe kansa da yayi masa nauyi da ya sani kawai yake a lkcn, what came over him ma yayi haka duk daurewa da shan pills da yake ga yawan tsayuwar dare, ji yayi ya tsani kansa lkci daya, bai ma san me xai kuma ce mata ba, ya fi awa biyu bakin kofar amma taki budewa daga karshe ya mike gwiwa a sake ya karasa kan gado ya xauna, yanda bai yi bacci ba daren nn haka ita ma bata yi ba, ana kiran sallah ya fita ya koma daya bedroom din, wanka yyi ya dauro alwala ya fito yayi raka'atainul fajr sannan ya fita xuwa masallaci har ya dawo Samha bata bude bayin ba, gashi duk keys din har da spare a gu daya suke, ganin gari ya fara haske ya sake komawa dakin nn ma bbu lallashin da bai yi ba amma ta ki cewa komai kuma ta ki bude masa, xaunawa yyi gefen gado yana tunanin abun yi kuma, bakwai da kusan rabi ya mike da kyar jiki a sanyaye ya fita, part din Hajiya ya tafi, ya danna bell mai aiki ta bude, ya amsa gaisuwarsa yace "Hajiya na ciki?" Tace "Ehh tana nn" yace "Kiyi min sallama da ita" juyawa tayi ta koma, bayan kusan minti biyar ya ji muryar Hajiya na cewa "Boy ka shigo mana" ya shafa kai yace "Ba jimawa xan yi bane Mami..." Mami ta karaso bakin kofar ya gaida ta da ladabi ta amsa yace "Ya mai jiki?" Tace "Alhmdllh ga ta cab tana breakfast ne ma" yace "Toh Allah ya sauwake..." Tace "Ameen boy" ya na ci gaba da shafa kansa yace "Mami dama wata yar magana xa mu yi dake if you re free pls" tace "Toh shigo daga ciki mana" Yace "A'a Mami idan ba takura i wanted mu yi shi a can ne" ya nuna balcony dinsa, Mami tace "Alryt... Mu je" daga haka suka nufi balconyn a tare, ta ja kujera ta xauna tace "Toh ya aka yi son?" Xaunawa yyi, ya d'an yi shiru sai kuma yyi kasa da kai yace "A kan Samha ne Mami" Mami ta tattara hankalinta gaba daya tace "What about her boy, laifi tayi maka ne?" Ya girgixa kai yace "Mami ba dauke ki matsayin mahaifiyata da na baro a kano, don haka baxan boye maki komai ba, amma Mami this is a secret between us...." Mami ta gyada kai tace "Ina jin ka?" Ba karamin karfin hali yyi wajen cewa "Mami Samha fa ba matata bace!" Wani kallo Hajiya ta shiga yi masa daga sama har kasa kamar bata fahimce abinda yace ba, ya dafe kansa yace "Yea Mami sai dai kuma ba xaman fasikanci nake yi da ita ba Allah ma ya shaida..." Ita dai Hajiya har lkcj kasa cewa komai tayi da ganinta kasan ba wai mamaki kadan tayi ba, ya girgixa kai da kyar yace "It's a long story Mami... And Samha ba musulma bace Mami, hasali sunanta Samantha ni ne na mayar Samha..." Buda baki Hajiya tayi tana kallonsa da mugun mamaki, ya gyada kai a hankali yace "Ehh Mami" Hajiya tayi karfin halin cewa "Aliyu???" Bai dago ya kalleta ba ya ci gaba a sanyaye yace "Gidan iyayena is just few houses away from her parent's... That is layi daya muke, My father is a soldier My mum a lecture then, Samantha was born nd brought up in a strong Christian home, mahaifiyarta Pastor ce, her dad a politician...."
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
41......
Cikin sanyin murya yace "Duk da layi daya muke da Samantha ni bn taba lura da ita ba sai watarana da daddare....." Nan Abuturrab ya shiga ba Hajiya Hajarah labarin tun daga farkon haduwarsu da ita har ixuwa ranan da suka bar garin kano tare, Hajiya bata samu bakin cewa komai ba da ganinta kasan kanta ya gama daurewa haka ta tsaya kallonsa baki bude, ya ci gaba kansa a kasa har xuwa abinda ya faru jiya bai boye mata komai ba sai dalilin fushin da Samha tayi, Sai a snn Hajiya tace "Ya salam! Haba Aliyu duk ilimin ka ynxu kake xaune da warce ba muharramar ka ba, why boy, ynxu ba don Allah ya tsare jiya ba me kke tunanin xae faru, me yasa ka ajiye koyarwar addinin ka sbda son xuciya?At d first place ma meye na guduwa da yar mutane ka xabi toxarta iyayen ka, wato kai ba indiye koh?" Da damuwa yace "Mami ko da ma ban gudu da ita ba nasan baxan ji dadi gun Abbana ba, everything just happened all of a sudden, sannan ni Mami bn jin xan iya rayuwa da ita, i just can't do without her, and i notice tana da interest for islam, musuluntar ta baxai wani dau lkci ba, kuma ni aurenta nake son yi Mami, ni ko ...." Mami ta mike a fusace tace "Rufe min baki malam, is she still inside d bathroom" kai ya gyada mata tace "Wani dakin?" Yace "By the left..." Shiga parlon tayi tana mamakin karfin hali irin na Aliyu ynxu ashe duk wnn abun yarinyar nn ba matarsa bace, wai ba ma musulma bace, sai dai kuma abinda ya burgeta game da shi yanda yyi iya kkrinsa na ganin bai yi sabon Allah ba cos she can see he is very sincere, tunda gashi a dalilin abinda ya faru jiya yasa ya buda mata cikinsa, tausayin Samha ya shigeta sosai, ita kuma sbda soyayya ta yarda ta yasar da iyayenta ta ajiye addininta ta bi namiji bata san duk yanda Namiji yake to fa shi ba d'an goyo bne, sai dai all the same she is happy for her don da alama conversion dinta xuwa addinin gaskiya baxae yi wahala ba, tana isa dakin ta karasa kofar bayin cikin sanyin murya tace "Samha open the door, it's me" Samha da ke xaune bathroom din har bacci ya fara daukarta ta bude ido da sauri ta mike tsaye, Hajiya ta sake cewa "Ki bude Daughter ni ce" wasu sabbin hawaye ne suka cika idonta da ya tashi don kuka, ta fara kalle kallen bayin ta dau towel ta daura, Hajiya tace "Samha..." Cikin sanyin Murya tace "Toh Ummi" daga haka ta bude kofar amma ta kasa kallon Mami, Hajiya tace "Haba samha sai ki kwana a bayi?" Ita dai bata ce komai ba, Hajiyar da tausayinta ya rufeta sosai tace "Dau kayan ki ki sa kin ji" bbu musu Samha ta dau dogon rigar ta ta saka, Mami ta mika mata Hijab shi ma tasa, snn ta kama hannunta suka fita, har lkcn yana xaune balcony, suna fitowa ta yi ido hudu da shi, ta dauke idonta da sauri, shi kam kasa daina kallonta yyi, wani mugun sonta na fizgarsa ga tausayinta, Mami bata ko kallesa ba tana rike da ita suka fita balcony din tayi part dinta da ita. Suna shiga parlorn Hajiya Fatima ta bi su da ido don tana xaune parlon, Ita dai Samha bata dago kai ba har Hajiya ta shiga da ita bedroom dinta, tana kallonta tace "Ki shiga kiyi wanka xaki ga sabon toothbrush a bayin ma kin ji" kai Samha ta gyada mata ta nufi bathroom din, bayan minti sha biyar ta fito taga kayanta ajiye bakin gadon da mai da turare, duk a sanyaye ta gama shiryawa ta xauna nan kasan dakin, hawaye ya shiga sakko mata, ta rasa takamaiman abinda ke ranta a lkcn, she know she's regretting following Aliyu, ta fashe da kuka sosai tana tuna furucin mum dinta always na cewa musulmai ae bbu abinda suka iya sai cin amana, does this mean her mum is right, she never expect such from Aliyu, bude kofar dakin aka yi, ta sunkuyar da kanta tana share hawayen idonta, Ummi ta karaso dakin tana kallonta tace "Kuka kuma Samha?" Tashi ki xauna kan gado, Samha ta kasa dagowa har sai da Ummi ta kuma yi mata magana, ta mike jiki ba kwari ta xauna gefen gadon, Ummi tace "Bana son in kara ganin kina kuka, ko baki dauke ni matsayin uwa ba Samha" girgixa kai kawai tayi, Ummi tace "Toh ki daina kukan nan, kar ki wani damu kanki kuma ki saki jikin ki a nan kamar kina gidan ku kin ji" kai kawai ta gyada bata iya ta bude baki ba, Ummi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo mata da breakfast ta ajiye mata tace "Sakko ki karya" ba musu Samha ta sakko kasa, Ummi ta juya ta fita, da kyar Samha ke shan tea din duk damuwa yyi mata yawa, yanxu ae in ta koma gida kilan sai dai wata kuma ba ita ba tasan Mumy will never take it likely with her, or kawai ta wuce kaduna gun aunt dinta, abinda xuciyarta ke raya mata knn kuma taji ta gamsu da hakan, khadija ce ta shigo dakin ta wara ido tace "Ashe kina nan Sis Samha, Ummi tace baki da lafiya, ya jikin?" Murmushi Samha ta kirkira tace "Da sauki...." Khadija ta xauna dakin tace "Ayya, Allah ya sauwake" khadija na fita Samha ta mike ta shiga gyaran Bedroom din duk da bbu wani gyaran da yake bukata, snn ta kwashe plate da cup din da ta karya ta fita da su, Har lkcn fatima na xaune parlor idonta a kan wayar hannunta, tana dago kai suka hada ido da Samha, Samha ta dauke kai ta nufi kitchen, Fatima ta bi ta da ido, tana ajiye kwanukan hannunta ta fito parlor, Dai dai nn Hajiya ta shigo tana kallon Samha tace "Har kin karya?" Kai kawai Samha ta gyada mata, Hajiya tace "Toh mu je daki" bin bayanta Samha tayi suka koma dakin, Hajiya tace "Kiyi xaman ki a nan...." Har yamma Samha na bedroom tare da Khadija dake ta bata labarai, sae dai idan lkcn sllh yayi su tashi su yi, Ummi kuwa tun Sha daya ta fita gun aiki, Samha tayi iya kokarinta na ganin Khadija bata gano tana da damuwa ba don sae biye mata take, sai dai taji haushin kin barin ta ita kadai da Khadijar tayi don her plan was to leave, ko kara ganin Aliyu bata son yi, Fatima ma na gidan throughout sae dai bata ko leka inda suke ba, karfe biyar Khadija tace "Sis Samha mu je ki raka ni kitchen in daura dinner mai aikinmu bata xo ba yau, Sis fatima kuma is still pretending she is not okay" murmushi Samha tayi ta mike ta bi bayanta suka wuce kitchen, Shinkafa Khadija ta daura, Samha kuma ta dau kayan miya tana wankewa, can ta kalli Khadija tace "Rabi'a bata nan ne?" Khadija tace "Tana gidan wani uncle din Ummi tun jiya" Samha bata kuma cewa komai ba, har ta gama gyara kayan miyan, Khadija tace "Yauwa ya ma name din spice din nn da kika sa ranan a stew mai kamshi?" Yar dariya Samha tayi tace "Xaki sa ne ke ma?" Khadija tace "Ehh mana don Ummi tasan nice nayi girkin yau ba sis Fatima ba" Samha tace "Toh bari in dauko maki" Har ta isa bakin kofa sai kuma tayi jim, ta gefen ido ta lura khadija na kallonta kawai sai ta fita, jiki a sanyaye ta nufi nasu part din, ta shiga kitchen da sauri ta dauko spices din gaba daya ta fito dai dai bakin kofar fita ta kusa cin karo da shi, ta koma baya a tsorace, shi kam kallonta kawai yake can yace "Am, am sorry Samha forgive me pls" hade rai tayi ta bi gefensa xata fita ya rikota ta fasa ihu, muryar Ummi suka ji tana cewa "Are you stupid Aliyu, sake ta immediately..." Saketa yyi ta bi ta gefensa da sauri ta fice, Ummi tace "What brought you here?" Abun hannunta ta nuna mata, Ummi tace "Bana son in sake ganin ki part din nn...." Samha bata ce komai ba ta bar wajen, Ummi na masa wani irin kallo ta jefa masa envelope da makullin motar dake hannunta ta bi bayan Samha, lumshe ido yayi kafin ya bude har sun shiga part din Hajiya, duk jikinsa yyi sanyi wani hukunci knn Ummi ke son dauka? Da kyar ya duka ya dau files din da makullin mota ya juya ya fita daga compound din. Karfe takwas yana kwance parlor kiran Ummi ya shigo wayarsa yana dauka tace "Ka taho ka karbi abinci" toh kawai yace ta kashe wayarta ya mike xaune, can dai ya tashi ya fita, Fatima na xaune balcony textbook gabanta alamar karatu take, bai ko kalleta ba ya isa bakin kofa ya kwankwasa, ajiye pen din hannunta tayi tana naxarin what's d meaning of Samha staying a part dinsu tun sassafe, tana son gano me ke faruwa amma tasan Ummi will never tell her, Khadija ce ta bude kofar ya shiga, Ummi na parlon da Samha da Khadija, Samha ta sauke idonta kasa, shi kam idonsa na kanta ya xauna, Ummi tace "Ga abincin ka a dinning...." Karasawa yyi ya dauka ya dawo yace ya gode, Ummi tace "Godiya kuma, Pls gobe da safe kafin ka fita gun aiki xaka je dauko Yusuf a airport boy, though am nt sure ko goben xae taho, in goben ne i will give you a call" Abuturrab yace "Toh Mami..." Daga haka ya kuma kallon Samha da ta dago ita ma don satan kallonsa, suna hada ido tayi saurin dauke nata idon.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
42.....
Kasa daurewa Fatima tayi misalin karfe tara Samha na daki tare da Khadija ta shiga bedroom din Ummi, xaune ta tadda Ummi idonta sanye da glass tana aiki gaban computer, ta karasa ta xauna tace "Ummi..." Ummi ta juya tana kallonta tace "Ya aka yi?" Tace "Uhm wai da gaske gobe yaya Yusuf din xai iso?" Ummi ta ci gaba da abinda take tace "Ki kirasa ki ji mana" Shiru tayi bata ce komai ba don ba tambayar da ya kawo ta knn ba, Can dai tayi karfin halin cewa "Ummi me Samha take yi a nn ne wai?" Juyawa Ummi ta kuma yi ta kalleta tace "How is her staying here affecting you?" Yake tayi tace "Noo, Ummi it's surprising ne ta bar mijinta ta xo nan, i tot bata da lafiya ne ma" Ummi tace "Toh ba matsalar ki ba ne..." Daga haka Ummi ta ci gaba da abinda take, Fatima ta mike ta fita daga dakin cike da jin haushin abinda ummi tayi mata. Dakin yayanta ta shige tayi kwanciyarta. Da asuba Ummi ta shigo tada khadija tayi sllh, ga mamakinta sai taga sun ma tashi suna sllhn, tsaye tayi bakin kofa tana kallon Samha, a xuciyarta tace "Ikon Allah, amma wnn ai aikin baban giwa take..." Tausayinta sosai taji a ranta ta kuma dau kudirin xata dau time ta tambayeta her view about islam, is she interested, but ga dukkan alamu ma she is interested tunda har ta iya tashi da asuba tayi sllh, juyawa Ummi tayi ta fita. Abuturrab na idar da sllh part din Ummi ya taho don jin ko xae je airport din kuma, "Na kira wayarsa bai je ba, je kayi abinda xaka yi idan ma ya iso sai ya dau taxi kawai" cewar Ummi kenan bayan ta fito, yace "Toh Mami" daga haka ya juya ya bar wajen. Xama Abuturrab yyi a parlor ya rike kai bayan ya koma part dinsa, he never taught hukuncin da Ummi xata dauka kenan, me yasa take kkrin nisanta shi da Samha, sae yaji duk xaman gomben ma ya ishesa, damuwa yyi masa yawa, what happened the day before yesterday was just a mistake, sharrin shaidan. Ya rasa gane whether he is regretting telling her or not, gaba daya yaji bai jin xai ma iya ci gaba da xama garin. Samha na xaune daki tana kallon khadija dake karatun qur'ani sai dai gaba daya hankalinta bai gun, gaba daya tunaninta na gun Abuturrab is she missing him or what, hawaye taji na neman taruwa idonta, why is all this happening to her in just 2 month, kwanciya tayi a hankali ta juya kanta hawaye na sakko mata. A ranan Abuturrab na xaune office ya jinginar da kansa jikin kujera wayarsa dake gabansa ya fara ring, dauka yayi yaga Hajiya Mariya ce ke kiransa, ya lumshe ido ya daga kiran ya kai kunne, cikin sanyin murya yyi mata sallama ta amsa daga daya bangaren, ya gaisheta tace "Abuu ko kira baxaka dinga yi ba, ya kuke?" Yace "Lafiya lau mum, ya gida?" Tace "Alhmdllh, ina Samhar?" Yace "Tana gida mum" tace "Kai kana ina?" Yace "Ina gun aiki Mum" tace "Aiki kuma, da wani qualification din" yayi murmushi yace "Uhn da na kai na Mumy..." Tace "Toh a ina ka samu aikin..." Bayanin Hajiya Hajarah ya shiga yi mata, Hajiya Mariya tace "Allah sarki, Allah ya mata albarka... Yanxu kuma Abuu haka xaka ci gaba da rayuwa da wacce ba muharramar ka ba..." Yace "Mumy i told Hajiya everything jiya da safe, shine ta dauki Samhar ta komar da ita nata bangaren i really can't tell what she is up to...." Hajiya Mariya tace "Maa sha Allah naji dadin hakan gaskiya, am happy akwai babba tare da ku da xata dinga gaya maku gaskiya tana nuna maku, what she did is the right thing...." Abuturrab yace "But Mum, kar ta raba ni da ita wlh mum baki ji yanda naji da ta mayar da ita bangaren ta ba..." Hajiya Mariya tace "Keep quiet, hakan shine dai dai, ta burge ni wllh... Idan ma conversion din ne gwara ita tayi converting dinta" kasa ce mata komai Abuturrab yayi, tace "Yea, sai mun yi waya" daga haka ta katse wayar ya ajiye ya rike kansa. Samha na kitchen tare da khadija da mai aikinsu misalin karfe biyar saura suka ji fatima dake parlor da wata Billy, wanda da alamar ita ta kirata ta xo tana cewa "Welcome big bro..." Khadija ta ajiye yankan salad din da take yi da sauri ta fice daga kitchen din tana cewa "Oyoyo yayana" tsaye Samha tayi bakin kofa tana kallon yayan nasu dake kkrin cire takalmin kafarsa ganin kanwartasa ya mike ya wara ido ya rungumeta yace "Oyoyo lil sis..." Kankamesa khadija tayi tace "I missed you broo..." Yace "I missed you too, ina Ummina" khadija tace "Bata dawo ba..." Yace "Rabi'a fah?" Tace "Tana gidan Abbu..." Sau daya ya kalli Samha da tayi saurin sunkuyar da kai ya amsa gaisuwar Billy ya wuce bedroom dinsa. Bayan Magrib Samha na kwance daki khadija ta shigo tace "Sis Samha ki fito mu ci abinci..." Samha ta kalleta tace "Ae daxu na ci abinci..." Khadija tace "Dinner fa ba lunch ba" murmushi Samha tayi tace "Toh ni dai na koshi...." Khadija tace "Ummi fa ce tace in kira ki" mikewa Samha tayi ta bi bayanta suka fito parlor, Dai dai lkcn da Abuturrab ya shigo parlorn, kanta a sunkuye ta karaso parlon, shi kam idonsa na kanta har ya shigo, khadija ta gaishesa ya amsa har lkcn idonsa na kan Samha, Fatima kuma idonta na kansa kamar xata cinye sa, ya xauna yace "Ga ni Mami..." Ummi tace "Abinci xaka ci dama, Samha kun gaisa kuwa?" Sai a snn ta dago kai ta kallesa, sai kasa daina kallonsa tayi, can tayi karfin halin cewa "Ina yini..." Ya kasa amsawa, Ummi tace "Ba ku ma gaisa da Yusuf ba Boy" daga haka ta kwalo ma Yusuf kira, Khadija tace "Ae bai shigo daga masallaci ba..." Bata rufe baki ba Yusuf ya shigo parlon da sallama, Abuturrab ya juya ya kallesa, karasowa yyi parlon yace "Ummi am jet hungry...". Ummi tace "Ga abinci can dinning ai, bayan tafiyar ka Allah ya hada ni da wani son wanda ya take ka a rashin ji ma, ka gansa yana nn yana ban wahala shi ma..." Sosai ta ba Abuturrab dariya, khadija ta fashe da dariya ita ma, Samha kam murmushi tayi ta sunkuyar da kai, Yusuf ya wara ido yana kallon Abuturrab yace "Really Ummi..." Daga haka ya mika masa hannu murmushi dauke fuskarsa suka gaisa yace "I am barrister Yusuf Ahmad...." Abuturrab ya mayar masa da murmushin yace "I am Dr Aliyu Ahmad...." Yusuf yace "It's nyc meeting you..." Kai Abuturrab ya gyada masa har lkcn murmushi fuskarsa yace "Same..." Ummi na kallon Samha tace "Kun gaisa da shi dota?" Sai a snn Samha ta kallesa shima ya juya yana kallonta, a hankali tace "Ina yini?"
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
43.....
Yusuf da ke kallonta shi ma yace "Lafiya lau...." Daga haka Ummi ta mike tace "Ga dinner can a dinning, fatima u serve it..." Mikewa Abuturrab ma yyi yace "Mami na taho da abinci fahh" kallonsa Ummi tayi tace "Toh ae bn ce ka taho da abinci ba, ga abinci can nace a dinning" Daga haka ta nufi dinning din ganin Fatima bata da niyyar mikewa, da kanta tayi ma kowa serving abincin ta juya tana kallonsu, Yusuf ne ya fara nufar dinning din fatima ta bi bayansa, ya ja kujera ya xauna, Khadija ta kalli Samha tace "Mu je..." Mikewa Samha tayi ta bi bayanta suka tafi, Khadija ta ja mata kujerar da ke kallon na Yusuf, ta xauna, snn ta xauna gefenta, Ummi na kallon Abuturrab da ya ki tahowa tace "Toh ko sai na dauko ka..." Murmushi yayi ya taho dinning din ba don ya so ba, ya ja kujerar dake gefen na Fatima a hankali ya xauna, can ya kalli Ummi yace "Ke baxa ki ci ba Mami..." Ummi tace "A'a ku dai ku ci My boy..." Daga haka ta wuce daki, Yusuf kam kansa na kasa yana cin abincin gabansa sai dai lkci lkci ya kan dago ya kalli Samha dake opposite dinsa, wanda hakan yasa duk ta takura ta kasa cin abincin, Abuturrab ya dago ya kalleta, ganin ba dagowa xata yi ba yasa ya sunkuyar da kai ya shiga cin abincin gabansa, fatima kuma sai satan kallonsa take, Kamar ance Abuturrab ya kalli Yusuf ya ga idonsa a kan Samha, ji yayi abincin na neman dawo masa ya mike da sauri hade da rufe baki kamar me shirin amai, Fatima ta mike ita ma da sauri tana kallonsa, Yusuf ya tashi shi ma da mamaki yace "What happened...." Abuturrab na girgixa kai yace "Am... Am not okay, i need to throw up...." Daga haka ya juya da sauri ya bar dining din, Samha ta bi sa da ido, ae bata san lkcn da ta mike ta bi bayansa ba, Yusuf ya bi su da ido, can ya kalli Khadija yace "Who's she?" Khadija tace "His wife..." Shiru yyi yana kallonta ko kiftawa bbu, Samha na fita taga har ya kusa balcony, ta bi bayansa da sauri, nan bakin kofa ta gansa durkushe sai kkrin amai yake ya kasa, ji yyi gaba daya cikinsa ya hautsine amma ya kasa amai, ga wani mugun bugu da xuciyarsa ke yi, ta durkusa gabansa ta rikosa hankali tashe tace "Me ya faru doctor, baka son abincin ne, ni da khadija fa muka yi..." Bai iya ya ce komai ba, jin hannunsa a shoulder dinsa yasa shi fara jin saukin abinda yake ji, ganin ya fara nutsuwa yasa tayi shiru tana kallonsa, a hankali ya dago idonsa da yayi jajir yana kallonta, sauke idonta kasa tayi, sai ji tayi ya rungumeta, tayi lamo jikinsa tana jin bugun xuciyarsa, duk yanda ya so bude baki yayi mata magana kasawa yayi, lkci daya hawaye ya kawo idonsa, ta dago a hankali ganin haka sai ta fashe da kuka, cikin sanyin murya yace "I love you Samha, i will be nothing without you... Kar ki bari son ki ya xama ajalina, don't make me a living dead...." Ta rungumesa cikin kuka tace "Why is all this happening to us... Why did you teach me how to love you deep...." Saketa yyi ya goge fuskarsa jin motsi a balcony ya mike tsaye sai ga Ummi ta shigo, wani kallo take masa daga sama har kasa strictly tace "What happened?" Rasa abinda xai ce mata yyi, tace "Baka ji na ne boy?" Da kyar yace "Mami... Ji nayi i want to throw up...." Kallon Samha da ta tashi tsaye ita ma tayi ta hade rai tace "Me kika xo yi nan?" Kamr xata yi kuka tace "Ummi, naga..." Kofa Ummi ta nuna mata tace "This shud be ur last, kada ko da wasa ki sake shigowa nn, leave now" A hankali tace "Toh Ummi..." Daga haka ta fita, Ummi ta kallesa tace "If you like throw up till tomorrow...." Daga haka ta juya tayi ficewarta, ya jingina jikin bango xuciyarsa na bugawa. Samha na komawa bata yarda ta je dinning ba tayi shigewarta dakinsu Khadija ta kwanta duk jikinta yyi sanyi, har ta fara bacci Khadija ta tada ta wai ta tashi tayi Isha, mikewa tayi ta shiga bayi. Karfe goma Yusuf ya shiga bedroom din Umminsa, as usual tana aiki, ya xauna tace "Ya aka yi Barrister..." Ya shafa kai yace "Gobe Abba xai taho week end ko Ummi?" Ta girgixa kai tace "Sai next week" yace "Okay, Ummi wai Aliyu ashe matarsa ce yarinyar nn" Ummi ta kallesa tace "Wa ya gaya maka?" Yace "Khadija..." Ta girgixa kai tace "Ba matarsa bace...." Lumshe ido yyi na kusan second biyar kafin ya bude a hankali, shiru Ummi tayi kamar bata so fadin hakan ba, duk yusuf na lura da ita, can tace "Amma ba wai nace kaje ka fada masu bane, i mean ur siblings, shi kuma you don't say anything to him about it... Yanxu ka tashi kaje can part din nasa sai ku kwana tare" da sauri yace "Why???" Ta kallesa tace "Sbda ina son ku yi xumunci sosai, he is very good nd brave..." Yace "A ina ma kika samo sa Ummi?" Tace "You leave now, sai da safe... You've interrupted me enough...." Murmushi yayi ya mike yace "Aiit Mother, sai da safe... But in ji dai bai da ji da kai, idan naga haka xan dawo inyi kwanciyata a nan" murmushi tayi tace "No, he is nyc son" sai da safe Yusuf yyi mata ya fita, a parlor ya kusa cin karo da Samha da taje dauko ruwa kitchen ta koma baya da sauri, ya koma gefe yace "Yi wucewar ki..." Gefensa ta bi ta wuce kanta a kasa, shi kuma ya nufi kofa da system dinsa xuwa part din Abuturrab, kwance ya samesa parlor Abuturrab ya mike xaune ganinsa, Yusuf yace "Hi Dr, came to spend d nyt here, hope m welcome..." Murmushin karfin hali Abuturrab yayi yace "Of course you are Brrstr..." Yusuf yace "Ohh tnx..." Daga haka ya xauna gefen Abuturrab yana kkrin kunna system dinsa yace "As I've said before, i am yusuf, born nd brought up in Abuja... I school in Uk, i soo love football" daga haka ya kalli Abuturrab dake kallonsa, Abuturrab yace "Uhn! That's nyc... I was born nd breed in kano, studied Medicine nd Surgery in Uk, amm may be i do love table tennis, and.... Snooker" dariya yusuf yyi ya kai masa Knuckle, Abuturrab ya dunkule hannunsa yana murmushi ya kai kan nasa, Yusuf yace "It's nyc meeting you...."
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By Khaleesat Haiydar📚✍🏻
44.....
Abuturrab ne ya fara mikewa bayan awa daya yana kallon Yusuf yace "If you er done sai ka shigo ni xan kwanta yanxu" Yusuf yace "Aiit...." Daga haka Abuturrab ya shiga daki yayi kwanciyarsa sai dai ya kasa bacci, ya rasa me ke masa dadi a duniyar, har Yusuf ya shigo bayan kusan minti talatin bai yi bacci ba, sae dai idonsa a lumshe suke, Yusuf ya shiga toilet ya dauro alwala snn ya fito yayi kwanciyarsa. Da asuba kusan a tare suka tashi duk suka yi alwala suka fita xuwa masallaci, ko da suka dawo yusuf ya koma yayi kwanciyarsa shi kuma Abuturrab ya shiga bathroom. Kafin karfe bakwai har ya gama shirinsa, bai tada yusuf dake bacci ba ya dau makullin motar dake gun sa ya fita, yana warming motar yaji an kwankwasa masa glass ya daga kai ya ga fatima ce tsaye, ya dauke kai snn ya sauke glass din, ba tare da ya kalleta ba ya shiga jiran jin abinda xata ce, a takaice tace "Good morning" har lkcn bai kalleta ba yace "Morning how you?" Tace "Ummi tace in kira ka" yace "Ohk..." Juyawa tayi ta bar wajen, sai a snn ya daga kai ya bi ta da kallo, can ya bude motar ya fita ya nufi part din Hajiya, yana shiga parlon ya xauna, Ummi ta fito daga kitchen ya sauke kai kasa ya gaida ta ta amsa tace "Baxa kayi break ba boy?" Yace "Xan yi a office..." Tace "A'a ka jira dai kayi kafin ka tafi ka ji... Me ya same ka jiya wai?" Daga kai yayi ya kalleta yace "Ba komai Mami, am ohk now..." Kallonsa kawai take bata ce komai ba, can dai tace "Shknn ka je khadija xata kawo maka kayan karin, naga kamar baka son cin abinci a nn koh?" Murmushi yayi ya mike yace "Toh nagode Mami" daga haka ya mike ya fita, karasawa yayi ya kashe motar snn ya shiga parlonsa ya xauna, bayan kusan minti bakwai aka bude kofar, daga kai yayi yaga fatima ce ta shigo rike da tray na breakfast, ya kauda kai har ta karaso ta durkusa gabansa ta ajiye tray din, ta dau cup xata bude flask ya dakatar da ita yace "No.. No kiyi tafiyar ki...." Bata tanka sa ba ta bude flask din xata xuba ruwan shayi a cup din, yace "Wai ba kya ji ne, i said..." Dago kai tayi tayi masa wani kallo ta xuba ruwan a cup snn ta rufe flask din ta shiga hada tea'n, mamaki ne ya cika sa, tana gama hadawa, ta ajiye gabansa ta bude plate din dake dauke da Irish da kwai sai plantain, snn ta mike tayi ficewarta ya bi ta da ido, can yayi tsaki ya dau tea din. Damuwa bai barsa ya ci break din da yawa ba kawai ya mike daga karshe ya fita ya hau mota ya fice xuwa office. Khadija da Samha na shirin tafiya islamiyya Ummi ta shigo dakin, tana kallon Samha tace "Ki bari gobe ki je Samha... Ita khadija ta yi wucewarta" Samha tace "Toh" Khadija ta turo baki tace "Sbda me Ummi.... Yau fa kika ce xata fara" Ummi bata tanka ta ba ta fita, haka khadija ta gama shirinta ta wuce ita kadai ba don ta so ba, Samha kam tayi kwanciyarta don dama duk sai taji ma xuwa islamiyyan ya fita kanta... Tana kwance ita kadai dakin aka bude kofa ta kalli Kofar, Yusuf ne tsaye wajen ganin ita kadai ce dakin bai karaso ba yana kallonta yace "Good morning" ta mike xaune tace "Ina kwana..." Ya d'an yi murmushi yace "Kin tashi lfya?" Sunkuyar da kai tayi ya juya ya fita ta koma ta kwanta, mai aiki ce ta shigo tace mata Ummi na kiranta, ta dau hijab dinta ta sa ta fita xuwa bedroom din Ummi, xaune ta ganta gaban computer, ta xauna kasa tace "Ga ni Ummi..." Ummi ta kalleta tace "Tashi kiyi xaman ki sama..." Ba musu ta mike ta koma gefen gado, Ummi tace "Samha..." A hankali ta dago tana kallonta tace "Na'am" Ummi tace "Duk tambayar da xan maki ki fada min gaskiya, kar ki ji shakkan komai kin ji daughter...." Samha ta gyada mata kai, Ummi tace "Do you have interest for islam?" Kallonta kawai Samha take bata ce komai ba, Ummi tace "Talk to me dear..." Hawaye ne ya cika idonta, a hankali ta girgixa kanta alamar A'a, shiru Ummi tayi tana kallonta, can tace "Baki da interest knn?" Samha ta gyada mata kai, Ummi tace "Toh me yasa kika yarda kika biyo Aliyu" hawaye sosai take yi, ta kasa cewa komai, cikin sanyayyan murya tace "You take me as ur mother Samha, tell me what's in ur mind kar ki ji komai...." Samha ta shiga goge fuskarta bata ce komai ba, Ummi tace "Tell me why did u follow him bayan baki da ra'ayin addinin islam..." Murya can kasa tace "I don't know... Buh i know i love him shi yasa na biyosa, snn ya taba ce min in yi addinina yayi na sa...." Da mamaki Ummi ke kallonta, can tace "Toh me yasa kike sllh, har kike sha'awar shiga islamiyya, kuma wa ya koya maki sllhn?" Wasu sabbin hawayen suka kawo idonta cikin rawan murya tace "Aunt dina dake kaduna musulma ce ita ta koya min sllh, she is my dad's younger sister...." Ummi tace "Toh islamiyyan da kike son shiga fa?" Shiru tayi bata ce komai.... Ummi tace "Talk daughter" ta share idonta a hankali tace "Kawai dai ina son xuwa ne...." Ummi tace "Toh kince you don't have interest for islam me yasa kika yarda da musulmi kika amince masa har kika biyosa kin san baki son musulinci?" Kuka ta shiga yi a hankali, Ummi tace "Kuka kuma? Ni ban ce ki min kuka ba Samha...." Bude kofar dakin aka yi Yusuf ya shigo da sallama... Kallonsa Ummi take, shi ko idonsa na kan Samha barin da yaga hawaye idonta, Ummi tace "Ya aka yi Yusuf?" Kallon mum din tasa yayi snn ya kalli Samha, da harshen fillanci yace "Ummi kukan me take yi? Me ya faru?" Sharesa Ummi tayi ta kunna computern gabanta, Samha kam bata dago kanta ba, can Ummi ta kallesa da yaren ita ma tace "You leave now...." Da damuwa yace "But Mum she is crying...." Hade rai Ummi tayi hakan yasa ya juya ya fita kawai, Ummi ta kalleta ganin kukan gaba yake karawa cikin sanyin murya tace "Tashi ki je Samha we'll talk later" kamar jira take ta mike da sauri don da alama bata son xancen ta fita daga dakin Ummi ta bi ta da kallo cike da tausayinta. Daki ta koma tayi kwanciyarta, tayi kukanta me isarta snn bacci ya dauketa.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By Khaleesat Haiydar📚✍🏻
45.....
Sai bayan Khadija ta dawo daga islamiyya Ummi ta wuce clinic don bata son barin Samha ita kadai, karfe uku saura Abuturrab na xaune office yana attending ma patient kiran Ummi ya shigo wayarsa, dauka yyi ya kai kunne hade da yi mata sallama, Ummi ta amsa tace "Kana office boy?" Abuturrab yace "Ehh Mami..." Tace "Toh ina jiran ka" daga haka ta katse wayar, yana sallaman patient din ya mike ya fita xuwa office dinta, sai da tayi masa izinin shigowa bayan ya kwankwaso kofar snn ya shiga da sallama, kallonsa take ganin yanda ya rame sai taji tausayinsa ba kadan ba, ya karaso kansa a kasa ya xauna kujera yace "Gani Mami" ajiyar xuciya ta sauke tana kallonsa har lkcn tace "You will think i'm mean ko boy, ko daya wllh am only trying to put u on d right way ne, kaga yarinyar nn ba muharramar ka bace, it's nt decent it's nt proper ku xauna roof daya da ita... Kasan da haka kuma, ni ban ga laifin ku ba Aliyu, nasan soyayya gaskiya ce amma tunda har ka buda min cikin ka i can't continue watching u disobey Allah, ina son ka tamkar d'an da na haifa a cikina right frm d time i saw u... Yanxu kai ka gaya min me xuciyar ka ke raya maka a kan yarinyar nan... What's d next step u wanted taking kafin abinda ya faru ranan da daddare" bai iya ya dago kansa ba cikin sanyin murya yace "Mami ni bani da niyyar cutar ta aurenta nake son yi...." Ummi tace "Aure? Ta ya amma" ya langwabar da kai yace "Kin ga idan na aureta conversion dinta xuwa islam baxai dau lkci ba..." Murmushi Ummi tayi tana girgixa kai tace "Na xaunar da ita mun yi magana daxu kasan abinda tace min?" Girgixa kai yayi, Ummi ta ci gaba "She said she don't have interest for islam boy, haka tace min, na kuma yi mamakin jin hakan" Da sauri Abuturrab yace "Noo Mami, she's just confuse ne wllh, buh wanda bai da interest ae baxai dinga sllh ba, kinsan Mami tun da dadewa fa na rabata da duk wani abu da xai dinga kusantarta da Christianity, kuma duk ta hakura ta bari" Ummi tace "That's because she love's you, soyayya yasa ta biye maka boy" yace "No Mami baya ga soyayya ma idan mutum har xuciya yake abun sa ai bbu abinda ya isa raba sa da shi.. Her dad was a muslim then fa, kakanta ma Musulmi ne har ya rasu, kawai mahaifinta bai da rabo ne, amma in shaa Allah shi ma xai dawo hanya madaidaiciya, uwar ta kam dama ba a magana tayi nisa sosai" Ummi dake ta kallonsa ta gyada kai cike da gamsuwa tace "Haka ne boy, na kuma lura abinda yasa ta fara loosing interest sbda nisanta ku da juna da nayi ne, buh i have no other alternative kada in xamo uwar banxa, abinda baxan bar d'a na yayi ba to d'an wani ma baxan bari yayi ba.... Kuma xancen xaka aureta ynxu bai taso ba boy, ka bari sai ta amshi islam don kanta ba don auren ka ba... Xaka aureta amma not so soon, ynxu dai ka dinga yawan shigowa a kai a kai ta daina jin kadai cin da take ji, komawanta can ne dai baxae taba yiwuwa ba, kai da Yusuf kuyi xaman ku a can tunda xai jima sosai a nan, one more thing boy pls pls ka daure kaje gida ko don mahaifiyar ka..." Kallonta yayi da sauri yace "Sai ince Samha tana ina, baxa ki gane ba Mami ai ina kai kaina gida yanxu ni nasan kano yayi ma Abbana kadan yyi min hukunci sae dai Abuja, xan je gida amma ba yanxu ba" kallonsa kawai Ummi take, can ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn boy, kai ma ka rage ma kanka damuwa bana son kana raman nn, Samha dai ba rabaka nayi da ita ba, duk lkcn da kake son ganinta sai ka shiga har hira ma kuyi, i won't stop that" ya d'an yi shiru sai kuma yace "Toh Mami nagode, amma plss let this continue to be a secret btwn us bana son a san she's nt my wife" da damuwa ya kare maganar, Ummi ta gyada kai tace "Alryt boy" a hankali cikin sanyin murya yace "Mami... mami ko yusuf ma fa kar ki ce masa ba matata bace...." Shiru Ummi tayi tana kallonsa, Gabansa ne ya fadi sosai ganin kallon da take masa, sai kuma tayi saurin gyada kai tana murmushi tace "Aiit, u can leave now boy.... I will let no one know" Mikewa yayi ya mata sallama ya fita, for the 1st time tun bayan faruwan incident din ranan yaji hankalinsa ya kwanta sosai. Fatima ce xauna balcony da kawayenta biyu handouts a gabansu Khadija da Samha suka fito, Khadija tace "Sister xa mu je siyo airtime..." Fatima tace "Ohk" Bin su da kallo fatima tayi suna yin nisa billy tace "Kin ki gaya min dalilin dawowar yarinyar nn part din ku..." Fatima tace "How many times do i have to tell you nima ban sani ba kuma ban san ta yanda xan sani ba Billy, I've snooped, I've put an eye all to no avail.. Ummi ba gaya min xata yi ba, that silly khadijah of a being ma ko da tasan abu she won't tell me" farida tace "Buh guy din ya fara sake maki kuwa?" Fatima bata ce komai ba ta dau handout din gabanta, Billy tace "i have a plan for you teemah..." Yusuf na xaune karkashin artificial tree dake compound din gidan yana waya amma idonsa da hankalinsa na kan Samha da khadijah dake tahowa, Samha ta saci kallonsa suka hada ido ta dauke nata da sauri, khadija tace "Yaya xa mu je siyo card..." Yace "Card?" Tace "Eh, airtime" yace "Ohk, taho in maki transfer" Tace "Toh yayana thank you..." Daga haka ta kama hannun samha suka nufi inda yake, kujera ta ja ta xauna tana kallon Samha ta dauko mata wani kujerar tace "Sit" Samha ta kirkiri murmushi ta girgixa kai tace "Thank you" Yusuf dake kallonta yace "Why?" Bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, yace "Ki xauna" bbu yanda ta iya haka ta xauna kan kujerar, yana danna waya yace "1000 ya maki yawa koh?" Ta xaro ido tace "Noo yaya, ya isa fah" yayi murmushi yace "Tohm! Waec bai fito ba har ynxu koh" tace "Ehh muna ta jira..." Samha dai kallonsa kawai take, height dinsu xae xo daya da Abuturrab haka ma haskensu, tana kkrin tantance wanda ya fi kyau cikinsu ya dago kai ya ga tana kallonsa, mikewa tayi da sauri tana kallon khadija tace "Amm, xan... bari in shiga ciki in taya usaina..." Daga haka ta bar wajen kmr warce aka kora ya bi ta da ido yana murmushi, Khadija tayi tagumi tana kallonsa, can dai tace "Big bro.... She's someone's else property fah?" Kallonta yayi da sauri yace "Whose?" Ta hade rai tace "Ba na gaya maka ba Dr Aliyun nn mana...." Yusuf yace "Hmm yeah... Amma yaushe suka xo gidan nan?" Khadija tace "Xa su kusa 5 weeks fa" yace "Ohk, but why is she staying a part dinmu?" Ta bude ido tace "Nima ban sani ba wllh, at 1st nayi tunanin ko bata da lafiya ne ma" yace "Ohk, a ina Aliyun yake aiki?" Khadija tace "A clinic din Ummi..." Kallonta kawai yake can yace "Ohk, da suka xo garin nn baya aiki ne?" Khadija tace "Toh, nima dai bn sani ba amma Ummi dae ta basa aiki a clinic" Yusuf na gyada kai yace "Ohkk, daga wani gari suke?" Tace "Kano wai..." Yace "Ohk, amma bata gaya maki komai a kan ita da Aliyun ba, i mean ko a hira bata gaya maki san da suka yi auren ba...." Khadija da ta fara isa da tambayoyin tace "A'a ni fa ban taba tambayarta komai ba" Yace "Ohk, but is dis their 1st time in Gombe?" Mikewa khadija tayi don tasan in ta ci gaba da basa amsa sae su kai dare a gun, ta turo baki tace "Kai yaya, sai kace ka samu case.... Wnn ko a court sai haka ae ta ya ni xan yi in san ko sun taba xuwa gombe, ni dai tnx for d airtime xan je mu ci gaba da girki..." Daga haka ta kara gaba ya bi ta da kallo yana murmushi.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
46....
Karfe shidda saura Abuturrab ya dawo daga gun aiki, yana gama parking ya fito yana kallon Yusuf dake compound din har lkcn, karasawa yyi ya basa hannu suka gaisa, Yusuf yace "Welcome back..." Abuturrab yace "Thank you, iska kke sha knn" Yusuf ya shafa kai yace "Not really am making a call...." Abuturrab yace "Aiit" daga haka ya wuce part dinsa, har aka kira Magrib Yusuf na xaune waje, sai da ya ga fitan Abuturrab masallaci snn ya tashi ya karasa tap din dake compound din yyi alwala ya bi bayansa. Kusan a tare suka shigo da Ummi compound din hakan yasa suka karasa can part din gaba daya don gaisheta, Abuturrab bai jima parlon ba ya koma part dinsa don tun da ya shiga bai ga Samha ba, yana kwance idonsa kan news da ake a tv aka bude kofa hade da sallama, Khadija ce ta shigo tare da Samha rike da abinci hannunta, har suka karaso inda yake idonsa na kan Samha, khadija ta ajiye abincin hannunta tace "Ina yini Uncle" ya kalleta ya amsa yace "Lafiya dija, sannu da aiki" tayi murmushi bata ce komai ba, Samha da kanta ke kasa tace "Ina yini?" Ya kalleta yace "Lafiya lau..." Sai a snn ta daga ido ta kallesa, murmushi tayi ganin yanda yake kallonta, tace "Ya aiki?" Yace "Alhmdllh...." Mikewa khadija tayi tace "Bari in dauko plate...." Daga haka ta wuce kitchen, saukowa kasa Abuturrab yyi yana kallonta har lkcn, cikin sanyin murya yace "Kin guje ni Heart beat...." Murmushi take ta girgixa kai tace "A'a" Dago kanta yyi ya kamo hannunta yana kallon kwayar idonta yace "I love you Samha...." Murya can kasa tace "I... i love you more" rungumeta yayi kan idon yusuf da ya shigo parlon a lkcn, Khadija kuma ta fito daga kitchen rike da plate, a hankali Samha ta xame jikinta, Yusuf kuma pretends he saw nothing yana danna waya, mikewa Samha tayi tana kallon Khadija da ta ajiye abun hannunta tace "Ba mu kai ma Ummi abinci ba" Daga haka ta nufi kofa Khadija ta bi bayanta. Ummi na xaune bedroom dinta Yusuf ya shigo, kallonsa take har ya nemi waje ya xauna, ta kalli agogo ganin goma ya wuce tace "Baka tafi can ba?" Yace "Yanxu xan wuce" Bata kuma cewa komai ba ta ci gaba da shan fruit din gabanta, Yana kallonta yace "Ummi...." Kallonsa tayi tace "Ya aka yi?" Ya shafa kai yace "Ummi ya Aliyu suke da yarinyar nn ne..." Wani kallo tayi masa tace "What's ur problem with that Yusuf, if am nt mistaken you've asked me that before, fine... Matar sa ce are you okay by that?" Yar dariya yyi yace "Buh few days ago ce min kika yi ba matarsa bace Ummi, how's this? Hmmm?" Hararansa tayi tace "Yea sun rabu ne then buh ynxu everything is normal" kallonta yake ko kiftawa bbu kmr me son gano abu, ta ci gaba da cin fruits dinta ba tare da ta kuma kallonsa ba, can ya dai yace "Toh mai take xama yi nan har yanxu?" Cike da masifa tace "Lemme rest pls Yusuf, i want him to know her value shi yasa har yanxu bata koma ba, kuma baxa ta koma ba..." Shiru yayi yana kallonta, can yace "Amma within dis short period din xamansu a gidan nn har kuka saba haka kika gano suna da prob... buh em fatima told me sabon aure ne, sabon aure shine har aka fara samun matsala, from my investigation na gano abu Ummi...." Mikewa tayi a fusace tace "Enough! Leave right away" mikewa yayi yana shafa kai fuskarsa dauke da murmushi ya nufi kofa ya fita, Ummi ta xauna hade da sauke ajiyar xuciya underneath her breathe tace "Damn it! Shi wai Barrister, Ya Allah kar ka bari ya gano komai kar in xama mara alkawari, i spoilt everything at d beginning" Yusuf na fita har xai nufi kofa yaji motsi kitchen a tunaninsa Khadija ne ya karasa kitchen din, Samha ya gani tana wanke wanke, suna hada ido ta dauke kai ta ci gaba da abinda take, shiga kitchen din yyi ya rufe kofa yace "Sannu da aiki" tace "Na gode" yana gyada kai yace "Ohk, ya ma sunan naki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Samha" yace "Nyc.... Ain't you missing home" da sauri ta kallesa sai dai bata ce komai ba, ya mata murmushi yace "You re nt tunda ga Aliyu koh" dauke kai tayi, dai dai nn aka bude kofar kitchen din, juyawa yyi da sauri, Ummi ta shigo, kallon Mamaki take masa tace "Me kke nn kuma Yusuf?" Yace "Ummi ruwa na xo sha, just came to take a glass of water...." Hade rai tayi sosai tana kallonsa, ya kalli Samha yace "Good nyt" a hankali tace "Thank you" daga haka yace ma Ummi ma sai da safe, ya fita ba tare da Ummi ta tanka sa ba. Ummi ta ajiye bowl din hannunta duk jikinta yyi sanyi ta juya ta fita. Ko kadan Abuturrab bai rintsa ba cikin dare, he was just planning on what to do next, yasan Ummi is truly good to him but bai jin xai iya ci gaba da xama garin when yusuf is around, May be some other time xai dawo gun ta don baxai taba mance irin halaccin nn da tayi masa ba, But he can't stay in gombe with his Samha any longer, kafin assalatu ya gama concluding next step din da xai dauka, and he was relieved.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By Khaleesat Haiydar📚✍🏻
47.....
Washegari Yusuf na bacci Abuturrab ya gama shirinsa, atm cards dinsa kawai ya dauka snn ya fita tun bakwai da rabi bai yi ba, bai fita da mota ba don kar ma Ummi ta ji fitarsa, clinic ya tafi, sai da ya tabbatar Ummi ta iso asibitin kusan karfe goma snn ya fita, gida ya nufa direct, khadija ce da Samha kadai gidan da yake ranan alhamis ne Khadijar bata je islamiyya ba, Gaishesa khadija tayi ya amsa yace "Samha fah?" Tace "Tana daki" daga haka ta wuce dakin sai ga su sun fito tare, kallonta yake har suka karaso, ya kirkiri murmushi yana kallon khadija yace "We will be back soon khadija, Cafe xamu" daga haka ya juya Samha da ta bi sa da ido ta ji yace "Ki dauko Hijab" juyawa tayi ta koma ta sako hijab dinta ta fito ta samesa yana jiranta waje, idonsa na kanta har ta karaso kusa da shi, yace "Mu je..." Tace "Ummi ta sani" yace "Yeah" daga haka ya kama hannunta suka fice. Mamaki ne ya cika ta ganin inda suka nufo, ya sauka ya ba mai adaidaita kudi, fitowa tayi ita ma tace "Doctor..." Hannunta ya rike ya nufi cikin park din, direct inda ake kiran passenger din Kaduna ya nufa, lkci daya hawaye ya cika idonta cikin sanyin murya tace "Doctor Ummi fa bata sani ba" bai ko kalleta ba bare ya kulata, bbu bata lkci ya biya masu kudin mota, ya nemi bench yyi xamansa kafin motar ta gama cika, can ya kalleta yace "Yea we will be back some other day..." Hawaye sosai take, bata xauna ba har mota ya cika ya mike ya shiga motar, sai da wata mata tayi mata maganar baxa ta shiga mota bane, snn ta shiga ta xauna kusa da matar. Throughout Journey din Abuturrab hirarsa da mutumin da ke kusa da shi yake don mutumin ba dai surutu ba, Samha kam duk jikinta a sanyaye yake, to ina kuma xa su, ganin bata da amsan ba kanta ta hakura kawai, lkci daya bacci ya dauketa. Kusan la'asar suka shigo kd, tana fita mota ta je ta tsaya wani gefe ta rungume hannayenta, shi kuma ya tsaya sallama da sabon abokin da yayi, har suka yi exchanging number da xumar xa su hadu wani lkci idan Allah ya yrda, Mutumin da yace sunansa Bashir yayi ma samha sallama don Abuturrab ce masa yyi matarsa ce, Abuturrab ya karasa yana kallonta yace "Kin gaji koh baby?" Dauke kai tayi bata ce komai ba, yace "Don't worry Sweet baxa mu taba mance Ummi ba, wataran xa mu kai mata xiyara amma as husband and wife, may be with our kid ma then.... Yanxu ina muka nufa?" Sai a snn ta kallesa kmr xata yi kuka tace "Da baka san inda xa mu ba muka taho nan?" Yace "Noo mana baby, yanxu dai mu fara xuwa gun aunt da kika ce tana nan garin koh..." Kallonsa tayi da sauri tace "Da gaske?" Yace "Yea mana, a wani anguwa take?" Tace "Familyn mijinta na can mararraba, lkcn can Abbana ke kai ni, amma wani lkcn suna xama Makera" yace "But mun wuce mararraba ai" shiru tayi bata ce komai ba, can yace "Toh mu je makeran ne ynxu?" Kai ta gyada masa, ya tsayar masu da Napep suka wuce Makera, amma cikin rashin sa'a yan gidan suka ce ai sun ma saki gidan sun koma can maraba, bbu yanda suka iya haka suka fito, Abuturrab na kallonta yace "ki xauna dakalin can dear, xan yi sllh in sama maki abinda xa ki ci sai mu tafi can maraban" xama tayi ta jira yyi sllh masallacin dake layin, ya fito ya nemi shago ya siya mata soft drink da snacks shi ya siya Malt, kallon mutumin dake xaune bakin shagon yana ta xukar taba yake, tunani ya shiga yi me ma yasa ya daina shan abun nn, sai yaji kmr ana tempting dinsa ya siya ya juya kawai ya bar wajen da sauri, taxi ya samu drop da xai kai su har maraban, ba su suka isa ba sai kusan biyar da wani abu, tana gaba yana biye da ita a baya yana kare ma garin da baxa a kira da kauye gaba daya ba kallo, Ita ce ta fara shiga d'an gate din gidan da Sallama ganin ya ki shigowa ta juyo tana kallonsa tace "Come in mana" Murmushi yyi ya bi bayanta, tsakar gida ne madaidaici me dauke da dakuna hudu a jere sai bandaki da kewaye a gefe daya, bbu kowa tsakar gidan sai murhu me dauke da tukunyar shinkafa a kai, kallonsa tayi ya wara mata ido a hankali yace "Shiga mana baby" kallon bangaren bayi tayi jin kmr akwai mutum a ciki sai kuma ta karasa bakin kofar daya daga dakunan dake a matsayin parlor ta bude labulen xaune taga Anty Maryam tana yankan alaiyahu sai wata mata dake kwance tana bacci ta juya baya, sake wukan hannunta tayi ta bude baki tana kallonta, can ta kalli matar dake kwance da Samha ma ke kallo ganin kamar Anty Sarah, mikewa Anty maryam tayi da hanxari ta karasa bakin kofar kawai ta kama hannunta suka fito, turus tayi ganin Abuturrab, ae yana ganin reaction dinta ya gane ba lafiya, murya kasa kasa tace "Ku taho...." Bude wani kofa tayi, dai dai lkcn da Samha taji muryar Mahaifiyarta daga cikin bandaki tana kwalo ma Anty Maryam kira wai ta miko mata zani, ai samha bata jira ta gama bude kofar ba ta shige a mugun tsorace, shi kansa Abuturrab ya rikice ba kadan ba, xae fito da ita daga dakin tun kan ta karasa shiga Anty Maryam da ita kanta a gigice take murya can kasa tace "Ku shiga i will close the door now" hakan yasa Abuturrab ya shiga dakin Anty Maryam ta garkame da makulli ta juya da sauri ta koma parlor tana amsa kiranta. Kuka Samha ta dinga yi tana cewa Abuturrab kashe ta mumy xata yi, bbu irin lallashin da bai yi ba amma kamar yana da da tunxurata duk tayi mugun tsorata gani take kmr Mumy xata fado dakin, shi kansa Abuturrab kansa ya daure ae da kawai Anty Maryam ta bari su fita kawai. Kin koma parlor Anty Maryam tayi don gani take kmr Rachael mahaifiyar Samantha xata ce xata shiga dakin da ta rufe, ai ko tana fitowa tace "Ki duba min kaya a jaka ki kawo min dakin can..." Daga haka ta nufi dakin da su Samha suke, Anty Maryam da gabanta yayi mugun faduwa tace "Anty dakin a kulle yake ai, baban su Asiya ne... Ina jin ajiya yyi" Rachael ta juyo tana kallonta sai kuma tace "Ina ce a bude naga dakin daxu kuma ai Aminu bai dawo gidan nn ba" Tabe baki tayi tace "Toh muje nan din, nagansa very untidy ne" Xaune tayi parlon tana shafa mai tace "Ai Maryam tunda pastor din nan na celestial church jiya yace min ina xaune xan ga Rebecca da musulmin nan very soon hankalina ya kwanta, idan kin kula jiya baccin da nayi har da minshari, rabona da bacci haka fa tun daren da Rebecca ta gudu..." Ta girgixa kai tana wani murmushi tace "Yesu ka ga irin tarbiyar da nayi ma yarinyar nn, yesu nasan baxa ka kamani da laifi ba, Toh kayi gaggawan bayyana min ita!" Ita dai Anty Maryam cukuikuye Alaiyahu kawai take duk hankalinta bai gun, Rachael tace "Ya kina ma alaiyahun haka, tunanin me kike" Da sauri Anty Maryam ta xubar a cikin farantin gabanta tace "Babu komai Anty...." Rachael ta gama xura rigarta ta dau Bible ta fita, Anty Maryam ta bi ta da ido xuciyarta na bugawa.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
48.....
Xama tayi tsakar gidan ta bude Bible din hannunta tana dubawa, Anty Maryam ta mike da kyar ta fita tsakar gidan, ta ja kujerar tsugunno ta xauna tana ci gaba da aikin da take, can ta sace kallon Mumy tace "Hayakin nn bai damun ki Anty?" Rachael ta kalleta snn ta kalli Murhun tace "Yo ba gwara ya dame ni ba da xafi ya kasheni a d'an akurkin parlon nn naki Mary.... Ai dai kinga ribar musulunci da auren Musulmi" Anty Maryam ta hade rai tace "Don't start that again aunt, shi da ma Christianityn forcing mutane ake yi su yi?" Tsaki Rachael tayi tace "Mu dama bama bukatar irin ku, ku kare rayuwar ku a musulunci don yesu bai so ku da rahama ba" Tsaki Anty Maryam tayi ta mike ta bar gun ta koma can gaban murhu, Rachael ta tabe baki tace "What a pity" Tunani Maryam ta dinga yi abinda xata ma Mumy taji haushi ta bar gidan ko ma ta wuce church kawai, can dai tace "Ga ku abun tausayi amma ku wani ce kuna tausayin mutum, Astagfirullah... shi Annabi Isan da ku ke bautawa ku ke kiransa da d'an Allah ance maki......" Tsam Mumy ta mike a fusace tana huci tace "Kee Maryam kar ki kai aya, maxa ki tofe yawun bakin ki kan fushin Jehovah ya sakko ya same ki ynzun nn, shi d'an nasa kike xancensa cike da izgilanci??" Maryam ta tabe baki tace "Ni na isa in ma Annabin Allah, ma'aikin Allah izgilanci, ni dai nasan Allahu bai haifa ba ba'a haifesa ba, Annabi Isa kuma messenger dinsa ne haka zalika Annabi Muhammad...." A mugun fusace Mumy ta katse tana hakki tace "Toh kuwa Allah ya tsine maki da wnn furucin, a kan ke musulma ce xa ki dinga fadin wa ennan maganganu, waye kuma Muhammad?" Mikewa Maryam tayi "Annabin Allah ne shi ma, kuma comforter din da Annabi Isa A.S ya gaya maku xai xo, if am nt mistaken bible ne a hannunki, idan kuma baki mance ba nima fa kusan nasan komai a Christianity din nn naku, Anty ki bude john 16:5-8....." Ganin Mumy ba budewa zata yi ba sai kumfar baki take ita a dole an tabo Yesu ta karasa ta karbe bible din ta bude, sai da ta duba tas snn ta rufe bible din tace "Let me make it short, the verse goes thus 'For if i go not away, the comforter will not come unto you, but if i depart, i will send him unto you, and when he comes, he will reprove d world of sin, and approve righteousness nd Judgement..." Murmushi tayi tana kallon Mumy tace "And who is Isa A.S referring to you all as a comforter?? That's prophet Muhammad S.A.W, he is the comforter" Mumy tace "Jehovah ya dawwamar dake cikin duhu, kada ya taba baki ikon gane gaskiya, sha sha sha kawai, talauci kadai ma da ya bar ku da shi ai ya ishe ku" Mai Abuturrab xai yi bnda dariya, sosai Mumy ta basa dariya, ya rike kai ya dinga yi, Samha ta rikesa a tsorace tace "Noo Doctor xa ta ji plss ka dainaaa" hadiye dariyar yayi ya rike baki, Maryam ta tabe baki tace "Ae ba don Allah bai sonmu bane ya bar mu a haka, sai ki ga mu samu in the world here after" Mumy tace "Inaaa ai kwalelanku ku da arziki, baku yrda da d'an sa ba ku ke zaton xai maku arxiki... Baki ganin ynda ubanku ya mutu ko tinkiya daya ba shi da..." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Da yau xan ga Rebecca gwara in kasheta in yi layyarta" Anty Maryam tace "Sai kuma ki ga kafin ta dawo ta musulunta, kila har ma ya aureta da ciki jikinta" wani kara da ya firgita sarah dake bacci ta fito da gudu Mumy tayi, Ta isa gun Maryam da gudu ta shakota tace "Jehovah ya isa tsakanina dake, Jehovah ya kona bakin ki da ya furta haka, Jehovah ya hanaki farin ciki da shegen talakan musulmin mijin ki...." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Sarah dauko min jakar kayana in wuce hotel, Idan na ci gaba da xaman gidan nn nasan xan shiga fushin ubangijina...." Sarah tace "Haba sis Rachael me ya hadaku haka duk makwabta na ji?" Tura Maryam Mumy tayi ta shige daki sai ga ta ta fito da jakarta tace "Idan kin ga dama ki fito da taki jakar in kuma so kike mu kone a gobarar da xa a aiko masu yau ne sai kiyi ta xama" Daga haka ta fice fuuuu daga gidan, Sarah tace "Maryam me ya faru haka ne" Maryam ta koma kujera ta xauna hade da sauke ajiyar xuciya tace "Toh ma ina na sani magana kawai muke sai naga kuma kmr warce aka ma allura" Sarah ta sa takalmi ta bi bayanta da sauri, murmushi Maryam tayi tayi hamdala a xuciyarta, ba a dau lkci ba Sarah ta dawo ta dau dankwalinta ta daura da jakar hannunta tace "Gobe xan xo Maryam, ban san me ke damun Sis Rachael ba" daga haka ta fice daga gidan, Maryam ta mike ta sa sakata a gidan ta dawo.
*Haske writers asso*
💫 *Noorul Huda*💫
By Khaleesat Haiydar📚✍🏻
49.....
Da sauri Anty Maryam ta karasa dakin da suke, tana bude kofar Samha ta mike da sauri ta karasa da gudu ta rungume ta, Anty Maryam kam kallon Abuturrab kawai take, Wanda hakan yasa ya mike ya gaisheta, bata iya ta amsa ba don duk jikinta yayi sanyi ganin kyansa da kwarjini amma ya gwammace yayi ta garari sbda wacce addininsu ya sha bam bam, can dai tayi karfin halin cewa "Bawan Allah don me xaka gudu da yar mutane, and what are you up to?" Sauke kansa kasa yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma a hankali yace "Saboda ina sonta Anty, so kuma na aure snn ina son musuluntar da ita ta dawo hanya madaidaiciya" Kallonsa kawai Anty Maryam take, ya karasa gabanta yace "Ki yarda da ni Anty ina sonta sbda Allah ba don in cuce ta ba...." Anty Maryam ta girgixa kai tace "Amma kana ganin hakan shine dai dai, rayuwa fa kake da warce ba muharramar ka ba, wanda addinin mu bai yarje mana da haka ba, ka sani amma ka bi son xuciya...." Yace "Noo Anty, i tried my best na ganin ban saba ma addinina ba all through our stay together" tace "Toh me ya hanaka auren nata har ynxu yau wataninku kusan biyu da barin gida?" Kallon Samha yayi sai dai bai ce komai ba, Anty Maryam tace "Kayi shiru?" Yace "Bana son watarana tayi tunanin ina using advantage din aurenta Anty...." Juyawa Anty Maryam tayi ta bar bakin kofar, Samha ta kallesa snn ta bi bayanta, Ko minti biyar basu yi da fita ba Anty Maryam ta dawo dakin, karasawa tayi inda yake ta zauna kan darduman dakin tace "Aliyu koh?" Kai ya gyada mata, tace "Kaga mahaifiyar Samantha na gidan nn ynxu haka nasan tana within,l.. ban san ka ba, ban san daga inda kake ba, ban san halin ka ba, amma nasan kai musulmi ne d'an uwana, hakan yasa xan baka yarda ta dari bisa dari, nasan da baka son Samantha tsakani da Allah baxa ka gwammace irin wnn rayuwar ba, don haka Aliyu kafin ku bar nan ina son ya kasance Samantha matar ka ce ta sunna, if you've tried ur best abiding to the laws of ur religion wataran hakan gagararka xai yi.... In har da gaske kake ka bari a daura maku aure komai xai fi xuwa da sauki" a sanyaye yace "Nima nafi son haka Anty, ban sai san ta inda xan fara bane...." Anty Maryam tace "Dawowar Samantha musulunci ba abu bane mai wahala ni xan taimaka maka, yanxu dai it's better ka tafi ka samu hotel, ita kuma xan kai ta gidan kawata, don mahaifiyarta na iya dawowa nn a ko wanni lkci." Yace "Toh nagode" tace "Amma all this while kuna ina da ita?" Babu bata lkci ya bata labarin d'an rayuwar da suka yi a gombe da Ummi, sai dai bai gaya mata ga abinda yasa suka bar gombe ba sai ce mata yyi kawai ziyara suka xo kawo mata" Ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn Aliyu Allah ya maku jagora, ni nafi kowa farin ciki da abunda ya faru Allah yasa lkcn fitowar yayana daga 6ata ne ya xo, Allah yasa ta dalilin haka ya gane gaskiya" Abuturrab yace "Ameen" mikewa tayi tace "Bari in xubo maka abinci" daga haka ta fita. Shinkafa da wake da mai da yaji sai kayan vegetables a kai ta kawo masa da ruwa a jug, yayi mata godiya ta fita. Mai gidanta ta kira ta sanar da shi komai ta kuma bukaci ya dawo don su hadu da Abuturrab, bayan yan mintuna ya shigo gidan, a tare suka shiga gun Abutturrab, ya gaida mai gidan nata da ladabi, Duk suka xauna dakin, Mijin Anty Maryam mai suna Aminu da ke ta kallon Abuturrab yace "Sannu da xuwa bawan Allah" Abuturrab yayi murmushi yace "Nagode" tambayoyi kmr yanda Anty Maryam tayi masa ya shiga yi masa shi ma, sosai mijin Anty Maryam ya jinjina karfin hali irin na Abuturrab daga karshe shi ma ya nuna gwara kawai ayi auren komai xai fi xuwa da sauki. A can Gombe kuwa tunda Ummi ta dawo Khadija ta fadi mata ai fa tun safe Abuturrab suka fita da Samha, jikinta yyi sanyi don lkci daya ta fahimci tafiya yyi da ita barin da taji wayarsa kashe tun daxu, amma bata nuna ba ta shige bedroom kawai ta kwanta tana tunanin wani rayuwar kuma xa su yi. Sun yanke akan cewa gobe Abuturrab xa su je gun mai gari da Mijin Anty Maryam daga haka kuma Anty Maryam tace ya wuce hotel kafin Mahaifiyar Samha ta dawo ita kuma xata je kai Samha gun kawarta, Sallama yayi masu ya fita, sai dai bai ji ddin rashin ganinta ba har ya bar gidan ita ko tana parlon aunt din tata bacci ya dauketa. Karfe shidda Anty Maryam ta sa ta shirya bayan tayi wanka ta bata nikab da hijabi snn suka fita a lkcn ma yaranta sun dawo daga islamiyya, bata bari sun lura da Samha ba har suka bar gidan, Addu'a Anty Maryam ta dinga yi Allah yasa Rebecca bata anguwannin don tana da kawaye yan coci kamar ta sosai a wajajen, tana rike da hannun Samha sai sauri take su isa bakin titi ta samu machine su hau, ta layin da ke gefensu taji an kwada mata kira, ta juya da sauri cike da faduwar gaba ta ga Sarah ce tsaye kofar wani gida, Anty Maryam da ke ci gaba da jan hannun Samha da ta tsorata ita ma taki tsayawa tace "nan kika xo ashe" ganin Sarah na tahowa yasa hanjin cikinta yayi mugun kadawa tace "Gani xan xo yanxu, bakuwa xan raka" Sarah da har ta kusa isowa gun su sbda saurin da take tace "Sis Rebecca nake jira tun daxu wllh, haba tun fa daxu fada take...." Tuni Samha ta janye hannunta a na Anty Maryam tayi gaba ko ina na jikinta na rawa, Sarah ta bi ta da ido, Anty Maryam na ganin haka ta tsaya gabanta ta ynda baxa ta dinga ganin Samha ba tace "Toh ko mu je in bata hakuri ni fa ban san me ya faru ba" Sarah tace "Jesus, yarinyar nan yanayin Samantha gareta, wacece ita?" Anty Maryam tayi dariyar yake cike da karfin hali tace "Samantha da Nikab kuma? yar wata uwar daki na ce... Haka take fama da rufe fuska" Sarah dake ta kkrin sake kallon Samha da tayi nisa sosai tace "Har tafiyar fa Maryam, Jesus of Nazareth" Maryam tace "Ohh don dai Samanthar ce a ranki, ynxu mu shiga in ba sister hakuri sai ta iya hada ni da yaya" Daga haka ta ja hannunta suka nufi gidan, Suna shiga Maryam tayi wani salati tace "Amma yarinyar nn Sha sha sha ce kinga kudin motar fa a hannuna bata karba ba" Sarah tace "Ayya to kiyi sauri ki isketa mana" bata rufe baki ba Maryam ta fice da sauri tace "Ina dawowa ynxu" Can bakin titi ta iske Samha ta rakube jikin wani shago, bbu wata wata ta tsayar masu da machine biyu ta fadi inda xa su suka hau suka bar gun tana hamdala a xuciyarta.
*Haske writers asso*
Plss ana min uxuri na rasa ynda xan dinga squeezing time ne, snn kuma there is shortage of power a inda nake ynxu wllh shi yasa yake taking time.
💫 *Noorul Huda*💫
By Khaleesat Haiydar📚✍🏻
50......
Suna isa gidan Anty Maryam ta shiga Samha na biye da ita a baya, Anty Maryam suka gaisa da aminiyar tata mai suna Amina daga haka tace mata xata bar Samha nan gidan xuwa gobe ta xo ta dauketa, bbu bata lkci ta bar gidan ta koma gida. Wani hotel Abuturrab ya samu yyi lodge, da ya tuna abinda ya faru gidan Anty Maryam sai abun ya basa dariya, sai dai hankalinsa ya kasa kwanciya ya rasa dalili, yana yin magrib Coffee kadai ya iya sha ya dawo room dinsa. Karfe takwas da yan mintuna Ummi na xaune daki gaban computer sai dai gaba daya hankalinta bai kai, sosai su Abuturrab suka tsaya mata don bata san halin da xa su je su shiga ba kuma, jawo wayarta tayi for the 5th time within that period ta sake dialing numbersa amma switch off ta dafe kai, bude kofar dakinta aka yi ta dago da sauri Yusuf ya karaso ya xauna kujera yana kallonta yace "Sannu da aiki Ummi" ba tare da ta kallesa ba idonsa a kan screen din computer tace "Yauwa" Ya d'an yi murmushi yace "Ummi kar fa ki sa ma kanki damuwa, dama ni ina ganin Aliyu nasan ba shi da gaskiya, as in the way he does his things ma xaka gane hakan, baka taba gane abinda ke ransa na lura, he can be a silent killer, at the first place na tambayeki hadinsa da Samha kika ki gaya min, daga bincikena tun a jiya na gano Samha ba matarsa bace, though bance xaman banxa suke ba, amma daga duk alamu rabo ta da iyayenta yayi may be for his selfish interest, tun daga lkcn da kika ce min bai ji na fara gano wasu abubuwan.... But Ummi me yasa kika boye min kilan da hakan da ya faru ynxu bai faru ba, i would have kept an eye...." Kallonsa Ummi tayi a karo na farko tace "Bana son xancen Yusuf" mikewa yayi yace "Aiit, buh am gonna fish him out idan Allah ya yarda" daga haka ya fita. Anty Maryam na xaune tsakar gida a ranan tana wanke kwanukan da suka ci abinci amma hankalinta na ga tunanin decision din da suka yanke da mai gidanta na aura ma Aliyu Yar d'an uwanta, bude kofar soro aka yi ta juya da sauri taga Rachael ce da Sarah, Duk da ba wuta tsakar gidan sai hasken wata hakan bai hanata ganin yanda Rachael ta daure fuska ba tana tahowa kamar xata tashi sama, Anty Maryam ta dauke kai tana murmushi ta ci gaba da wanke wankenta, sarah ce kadai tayi mata sannu da gida suka shige parlor, Anty Maryam ta mike ta dau abinci ta kai masu ta fito, ko da ta gama wanke wanken xamanta tayi tsakar gida tana sake saken yanda al'amarin gobe xai kasance, can ta mike ta shiga dakin mai gidanta ta xauna tana kallonsa tace "Abbansu Asiya ya kake ganin xa ayi gobe ne wai" Yace "Gun mai gari xa mu je a daura auren sai su tafi duk inda xa su, matukar xai iya kula da ita, na kuma ga yana sonta sosai don da ganinsa kasan ba karamin mutum bane." Da damuwa tace "To fa bata amshi musulunci ba har ynxu" yayi murmushi yace "Ba yar ki bace kin san yanda xa ki bi da ita ai, sai dai kuma kada a tilastata don in har aka yi haka tana iya komawa gidan jiya tun da ba da son ranta ba.... Ko kin mance yanda muka yi da ke Maryam" ganin dariyar da yyi ta hade rai tace "A'a ni baka aureni a Christian ba ni musulma ce a lkcn ma" yace "Amma a lkcn abubuwan da kike yi meye banbancin ki da Christians din, ba fa gori nake maki ba rabin rai kawae dai magana ce" ta tabe baki tace "Ae don ina gun yayana ne lkcn Kuma mahaifiyar Samantha ce matsayin uwata...." Yace "Toh kar ki ji komai ni nasan da kanta xata yi sha'awar addininmu ba sai an mata dole ba, at the first ma da bata son musulunci baxata yarda da musulmi ba har su gudu tare ta bar iyayenta" Anty Maryam tace "Haka ne, kuma kaga lkcn da take xuwa hutu nan bata kin yi duk abinda na sa ta tun daga kan sllh har xuwa tafiya islamiyya da su Asiya" yace "Toh kin ga" Mikewa tayi tace "Bari in je can parlor" daga haka ta fita. Washegari da ya kasance friday da safe Abuturrab ya fito ya nemi d'an boutique ya siya kaya da kudin dake hannunsa, daga haka ya nufi Atm machine don cire kudi, takaici ne ya ishesa don Atm machine din da ya gani bai fi biyu ba kuma duk ba kudi, kallon agogon hannunsa yayi yaga tara bata yi ba, kawai yayi deciding ya wuce cikin kaduna kawae, sai da ya koma hotel ya shirya snn ya dau hanya, yana isa ya kunna wayarsa tunawa da yyi sun yi exchanging number da mijin Anty Maryam, yana cire kudin ya shiga tunanin me xai siya kuma kafin ya koma wayarsa ya shiga ring Sadeeq ya gani jikin Screen din, har ya fara tunanin waye kuma sadeeq kawai ya tuna gayen da suka hau mota tare tun daga gombe, dagawa yyi, nan suka gaisa da fara'a Abuturrab yace "Kasan jiya fa can maraba muka wuce amma yanxu ina cikin kaduna na xo cire kudi..." Sadeeq yace "Au haba, a ina kake yanxun?" Abuturrab ya kalli gun yace "Ina bypass" Sadeeq yace "Haba to ka karaso nan gidanmu mana kafin ka koma" Abuturrab ya kalli agogo sai dai bai son Sadeeq ya ga kamar yyi shun dinsa, yace "Funny you, ni da nake sauri" Sadeeq yace "Sai in kai ka har maraban da motata" Abuturrab yyi jim don bai son exposing secret dinsa ma kowa kuma, can dai yace "Haba don xan xo gidan ku sai ince sai ka mayar dani, bari in taho sharp sharp in koma ba sai ka yi wahalan kai ni ba" Sadeeq yace "Alryt" address ya tura ma Abuturrab da yake yasan garin xuwa gidan bai yi masa wahala ba sai dai ba dai nisa ba don sai kallon agogo yake, babban anguwa ce ta masu abun hannu, Sadeeq ya fito daga wani kantamemen gida mai dauke da gate biyu kai da ganin gidan kasan naira ya xauna, nan suka gaisa sadeeq na dariya yace "Ashe dai xaka gane..." Abuturrab yace "Haba dai ai ba wani wahala" daga haka suka shiga gidan sadeeq ya kai sa har babban parlon gidan, Abuturrab na xama ya ji gabansa na faduwa ya rasa dalili, Sadeeq na kallon kanwarsa da ta fito yace "Kiyi setting mana breakfast a bedroom dina" tace "Toh" sannan ta gaida Abuturrab ta koma kitchen, Sadeeq yace "This is our home, you feel free frnd" Abuturrab yayi murmushin karfin hali yace "Sure" Ana bude kofar parlor ya waiga da sauri kamar jira yake, bai san lkcn da ya mike tsaye yana kallon mutumin dake kallonsa shi ma a bakin kofar ba, Sadeeq ma ya mike yace "He is my Dad...." Abuturrab ya kallesa ya kirkiri murmushi yace "Ohh alryt" juyawa Mutumin yyi ya fita, nan hankalin Abuturrab yayi mugun tashi, ya dake ya koma ya xauna, Sadeeq dake ta studying dinsa yace "Any problem Aliyu?" Wara ido yayi yace "Ohh nothing Sadeeq" ba a dau lkci ba mutumin ya dawo parlor, sai a snn Abuturrab ya gaida shi kansa a kasa, mutumin ya amsa yayi wucewarsa Sama, mikewa Abuturrab yyi yana kallon Sadeeq yace "Let me answer a call in dawo" daga haka yayi waje da sauri, wani mugun faduwa gabansa yyi ganin mutanen da bai gani ba lkcn da xa su shigo tsaye bakin gate wato dai soldiers in uniform, dakewa yayi ya karasa xuciyarsa na bugawa ganin kallon da soldiers din ke masa kawai ya juya ya koma ciki da sauri yana furta innalillahi a xuciyarsa, Yana shiga parlorn ya isa gun Sadeeq da sauri, Sadeeq ya mike da sauri ganin tashin hankali bayyane fuskarsa yace "Aliyu lafiya" Abuturrab yace "Nooo, help me out now plss!! ur dad.... Abokin Abba na ne" Sadeeq dake kallonsa da mamaki yace "Then?" Abuturrab ya kamo hannunsa yace "Don Allah make a way out for me nayi ma Abbana babban laifi i left home for months, nasan kilan yanxu ya ma kirasa wllh.... Plss" tsit Abuturrab yayi ganin Col Ishaq yana saukowa stairs, da sauri sadeeq yace "Haba to meye baxa ka hau sama mu yi break ba sai a nan frnd, plss mu tafi bedroom dina, it will be more convenient there."
*Haske writers asso*
Afuwan for the delay 😎
💫 *Noorul Huda*💫
By khaleesat Haiydar📚✍🏻
0 comments:
Post a Comment