daddafewa yayi daker yabar wajen yayi part dinshi. gado yafada yana Ajiyar Zuciya haryanzu kuma bebar fadin innalillahi ba. Abin da yaji Akunanshi yake tunanowa. Toh yaran Nan me Sukeyi haka? Nishifa naji Sunayi Gawasu Surutai barkatai. Namiji Suka kawo gidan? Kai "Aa" ta Ina? toh Ko yaran yan lesbian ne? "Banajin haka yaran guda nawa Suke"basuma San me'ake nufi da Hakan ba. Ajiyar Zuciya yakumayi duk yanda Akayi blue-film Suke kallo, idan ba Haka ba Menene yasa Su Suke nishi da Surutai irin Haka? Ya banji Leemah ba? Kai kanwata bazatai Hakan ba, Shiyasa duk natsani yarinyar Nasan Itace Sila, tun yaushe nake gaya ma Yusuf kananun yaran Nan idonsu Abude yake da Rashin kunya, kaini Ina Ruwana ne ma kome Suke Suda Allah n Su. Kwanciya Yayi yadafe kanshi yana So ya kauda tunanin Chan.
Fitowa tayi dafe da girjinta ta kunnah wutar dakin, Yan iska yakamata ku tashi haka tunda mun tsallake rijiya da baya. Feenah ce tayi karfin Halin cewa wai besty me kika gani kika wani kashe wuta? Ke bro Yazeed fa na hango ta windown toilet yana tawowa kuma da Alama Nan Zai tawo, Ko na tsayar daku ba Lallai kusan me Nake ba,Shiyasa na kashe wutan kawai. Lumshe ido feenah tayi takasa magana. Kausar yakamata Ki Sarara ma kanki haka,ko bakiji mai nake fada bane? Cikin muryan da bata fita Sosai kausar tace "tunda be ganmuba Ai Shikenan" Amma kinsan bazai rasa jin irin Abunda kuke ba? ba Lallai ya fahimci komai ba Kausar tafada A takaice tana kara Shafa jikin feenah. Shikenan tunda Baku Shirya fitaba ni Zan fita, Aa besty tsaya pls. Tashi Leemah tayi tana ni bazan iya da jarabarku ba kamar Akanku Aka fara Saka Sha'awa bude kofar tayi yayin da Ake Shigowa kuma. Trus ta tsaya ganin mumy ce, Wai inasu feenah dinne kunzo kunyi Zamanku Ana jiranku, A...aaa. .m...Mumy dama wanka Suke yi Shiyasa, Leemah tafada tana inda inda, toh matsa Nashiga, kaya feenah ke Sakawa mumy, my daughter kada kidamu koni Saina Saka mata, mumy!...tura kofar mumy tayi tashiga. dafe kirji tayi ta fiddo ido farar daya tana karanta Sunan Allah. Firgitgit Kausar tayi tajawo wani hijaf ta Saka yayin da feenah taja rigarta Sama ta miki Zaune. Sulalewa Mumy tayi tafadi Akasa da gudu feenah da Kausar Sukayo Kanta, Leemah fita tayi ta wuce palon da murmushinta ta gaida mutanin dake parlon, komawa tayi kusa da Mamy tana magana, Mamy Zomuje Ciki Mumy ta fadi. da Sauri Mamy ta kalleta farar daya Kuma ta tashi tabar palon Leemah na biye da ita. Subhanallah Menene ya Sameta? Kuka kawai Suke babu mai bada Amsa, Leemah bani Ruwa, toilet tashiga ta ibo Ruwan, Mamy na yayyafa mata tayi Ajiyar Zuciya ta bude ido Saikuma Hawaye Sharrr.....Hafsa lfy me yafaru Dan Allah. Wai Halima Badaku Nakeba Menene ya Sameta? Feenah ce cikin kuka tace Nice Mamy.......kece mai kika mata? Leemah ce taci mamy Wlh Sharrin Saidan ne ta kamamune........Haba Leemah kada kidaurama kanki laifin dabaki taba Aikatawa ba mana feenah tafada tana girgiza ma Leemah Kai. Ke Kausar me Tayi ma Mum din Tata? Amma Wlh Mamy ba laifinta bane nice.....kada kumaida ni mahaukaciya mana, Ina magana Wannan tana wannan menene Hakan? tashi mum tayi takama Hannun mamy tana kuka maicin Rai, "fatima ban San dame muka Ragi Nafisat ba A Rayuwa, me namata Zata Saka Mun da makamncin irin wannan? Sabida nace tayi karatu, ko mene? Fatima....muryartace ta Sarke. Hafsa kinga natsu kimun bayani me yafaru, Fatima Abinda Allah yake tsananin fushi damasu Aikatashi wai feenah Shi takeyi lesbian fa, ni Wlh gara Ace nakamata da Namiji Akan yanda naganta Ayau din nan. Rufe mata baki Mamy tayi tana maimaita "Innalillahi" kallonsu tarinka yi daya bayan daya daga bisani tace Sutashi Su fita, Tashi Sukai feenah takama Hannun mum mumy dan Allah kiyafemun, tsawa mai karfi mumy taimata, Mamy tace tashi kifita feenah. "Fita Sukay"Mamy ta juyo tana fuskatantar mum, Haba Hafsa Ai koda da Namiji kika kama feenah Ansan da bacin Rai toh Amma Zaki iya gayamun Baki taba fuskantar Feenah Nason Aure ba kokin taba? Tunani mum Tayi kadan daga bisani tace na fuskanci Hakan hasalima dakanta tasha gayamun Tanason Aure, tana yawan cemun tana Sha'awa Amma Ni da dadyn ta mundau Abun A Matsayin yarinta ne. Lallai Wlh Hafsa kunyi babban gangancin A Rayuwa, tayaya kunsan matsalarta tagaya muku Sannan Yanzu Dan kin ganta tana Aikata wani Abu kidaga Hankalinki, Ainicema yakamata Nayi mamakin Leemah Abbanta Sau Nawa Yana kiranta Akan ta fiddo da miji, yanzu kinga dagani harshi babu wanda yashiga hakkinta Amma kinga duk dahaka bamu tsiraba, ballantana ku Hafsa Wanda Hakkinta kuka Shiga kada kimanta "manzon Allah S.A.W. yace Idan kuka fuskanci yarku tafara Haila toh kada kuyarda takara Jini na biyu Agabanku kuyi mata Aure idan har Ansamu miji nagari. Cikin Saihihul Muslim" Hafsa ke Haka Akamiki? Kinkai Shekarun feenah lokacin dakikai Naki Auren? Meyasa kin fuskanci yarki tana da matsananciyar Sha'awa kika ki kimata Abinda takeso? Yau koba feenah kika fuskanci Tanada wannan Matsalarba Ai kya temaka Tunda ance matsalar ya mace ta ya mace ce, Haba Hafsa haka kikataso Anamiki A Rayuwa Wlh Na fuskanci bayan Rashin Son Zumnci kinada Sakaci Akan Rayuwar yaranki, Shin karatun boko din Nan Dolene Wai? Shi Zai kaita Aljannah kokuma Shi Za'a tambayeta A kabarinta? Sannan kisani feenah yarinya ce mai natsuwa da ilimi kema Zaki bada Shaidar Hakan, Rashin kulawarki da Rudin Shidan,Sa'anan da kawaye Nasan tabbas Sune Suka Shiga Rayuwar yarki. Kiyi hakuri Hafsa ki fahimceni bawai ina goyon bayan Abunda Suka aikata bane Amma muyi musu Uzuri, Muji ta bakinsu Nasan ba Halinsu bane wannan. Ajiyar Zuciya mum tayi tace Lallai Fatima na gamsu da maganarki kuma tabbas Gsky kika fada Mune Silar koma miye da feenah tashiga, Amma Insha Allah yanzu Na fahimci ba daidai muke Aikatawaba, Na Amince Feenah takawo mijin Aure.Alhmdllh ma da Abin yazo da Sauki tabbas munyi kuskure kuma nayi nadama. Amma Fatima kina ganin Zata bar wannan Halin? Zasubari insha Allah itama Kausar Zan neme Mahaifiyarta namata bayani Amma kafin Nan Zansamesu yanzu namusu Nasiha wata kila muyi Nasara Subar Aikata Hakan. toh Fatima ngd Insha Allah Zansamu dadynta da maganar. Babu gdy a tsakaninmu tunda duk yashafemu. Fatima kidaina Zargin Halimatu bata cikinsu bazatai Hakanba, Hafsa ba'a yabon Dan yau gaba dayansu Zan hada namusu, tashi muje parlon kada kibari Afuskanci Komai kinga Su Umma Suna Nan.
Shiga Sukayi Suka Zauna Umma tafara Zolayarsu Aminan juna yau Anhadu Shine Aka tafi tattaunawa, Murmushi Mamy tayi tace Kekam Ai Shekaru da yawa ba'a haduba, Abba yace toh Ni ko rowar ganin Nafisat din Akemun, kana ganintafa kullum, Sunachan Suna karance Karancensu. Toh Atasota mutafi Gida daddy yafada, da Sauri Mamy tace daddyn Mubeen Ai batare kukazoba zata tawo daga baya. dariya yayi yamike Hafsa taso muje, tashi mumy tayi Suka fita mamy da Abba Suka musu Rakiya, ina Nazeer ne? Ganinan daddy kutafi Zamu tawo da feenah muna fira da yazeed ne, toh Ai Shikenan fita Sukayi Su Mamy Suka koma Ciki, tsayawa Nazeer yayi yana tuno dazun kamar yaga Leemah a firgice lokacin da tashigo Palo, taban tausayi yafada Aranshi, Turo get din Akayi ya juya ganin Yusuf ne yasa yakarasa Suka Rungume juna, Kai yanaganka Anan kodama Kasan gidan Su yazeed ne? Aa Yusuf nima yau nasan gidan Nazeer ya kwashe komai yafada ma Yusuf, gaskiya Abu yayi Kyau kusanma yan'uwa Za'a kiraka kaida yazeed. Aikuwa dai. Amma Nazeer kamar kana Cikin damuwa ko? Ahha bakomai Yusuf muje. Mamy ce ta Rako Umma Yusuf ya gaishesu Suka wuce part din yazeed. Akwance Suka Sameshi Yusuf yace miskilin mutum kafi mugu iya Shege, dagowa yayi ya kalleshe ya wurga mishi Harara, Nazeer yace yadai Dr? bakomai Nazeer Yusuf din nan ne yakamata Na Chanza Shi, Kodai ni na chanza ka ba, Kasan me ya kawoni gidanku? Ciki ciki ya amsa da "Aa" Nazone Naga Kausar kawar Sister dinka Allah yasa bata tafiba. Bansaniba Banza Sa'an yara kawai, Ka ganshi Nan Nazeer kullum yara kanana yake bibiya.Murmushi Nazeer yayi yace Ai inaga da Akwai magana ne, Au kaima biye mishi Zakai? Yawuce yace Sonta yake Kuma ai irin yaran Sune irin matan dasuka dace damu. dakudai wlh Yazeed yafada Rai Abace, kai Anma Anyi kuskure da'aka baka matsayin Captain, tunda duk karfin ka din Nan Akan tunanin Auren Karamar yarinya ya tsaya. Shidai Nazeer bece komaiba. Yusuf yace Adai juri Zuwa Rafi Angon yar 30yrs.
Mumy ce ta tura dakin tashiga Zaune tagansu kowanne kuka yake Rusawa babu mai lallashin kowa. "Kubiyoni dakin Leemah mamy tafada Atakaice ta fita" feenah cikin muryar da bata fita Sosai tace Na Rokeki Kausar duk Abinda Mamy Zatace kada kice mata Leemah nacikin masu Aikata Wannan Abun, ta juya Wajen Leemah besty Dan girman Allah kada kisanar da mamy kina Aikata Wannan Abun Sabida bakida hakki Akan Hakan. Haba feenah nima Kibari Ayimun waya gaya miki banida Hakki dunbin Zunubin Dana Aikata nakaishi ina Gara Mamy tasani tun Anan gidan Duniya domin ta yafemun, idan ku kunada Hujjar Cewa iyayenku ne Sila ni mecece Hujjar? Eh duk da haka Leemah Tunda Allah ya Rufa miki Asiri kema kirufa ma Kanki ba danniba. Nayarda kutashi muje. Shiga Sukayi Suka Zazzauna Akasa. Mamy ta dago ta dubesu gaba dayansu Sannan tafara dacewa....... kunbani kunya bakuma Kanku Adalciba, Nasan kunsan Abunda kuke Aikatawa Yanada dunbin Zunubi kuma kunsan makomar mai Aikatawa Son Zuciya ne yasaku yin Hakan kokuma banzar hujjarku da batada ma'ana, Shin dan iyayenku Sunce Saikunyi karatu Kunfi karfin kuyi musu biyayya ne? Kokuma dan basu isa dakubane yasa kuka zabi kusaka musu ta wannan Hanyar? Miye Ribarku dan kun Aikata Hakan? Raguwafa kukayi kusani Rayuwarku tana Cikin babban hatsari, Halima nagode da Abinda kikaimun, feenah ce tayi Saurin dagowa Mamy kiyi hakuri Leemah bata Aikatawa, yimun Shiru banson magana kedin feenah Ai Nasan wannan ba Halinki bane haduwa da kawayen banza Shine yajawo muku, dakuma laifinmu nabarinku kuyi karatu Anesa damu. Kausar ce ta dago ta dubi Mamy kiyi hakuri Mamy nice naja Mus......naja mata, kausar labari tashiga ba Mamy har irin Halin da Feenah keshiga a School dakuma yanda khady itama ta daurata Ahanya takara dacewa Shidanne yayi Nasara Akansu, Mamy ta jinjina Al'amarin taji tausayin yaran Inda daga Sakancinsu su iyayen yara masu daura Burinsu kan dole yara Saisun Kammala Karatun boko tukun Suyi Aure. Afili cewa tayi maganar banza ai ba wannan bace Hanyar magance matsalarku. Kunsan Sharrin Aikata lesbian kowa???? "Sha'awa fitanace daga dabi'ar da Allah ya hallice mace Akanta,ta jin dadi da namiji ba mace yar'awarta ba, Cikin Aikata lesbian Akwai Rashin kunya da fitsara, Alhalin Manzon Allah (S.A.W.) yana Cewa Kunya Alherice gaba dayanta, "awata Ruwayar"kunya bata kawo Komai Sai Alkairi. "Bukari ne ya Ruwaito" Sa'annan lesbian yanada illah ta yanda Zai iya haifar da cututtukan Zamani kama daga kan H.I.V idan kana aikata hakan dame ciwon. Ana Iya Rasa budurci ta Hanyar wanda hakan Ba Karamar tozarta bace ga ya budurwa. Abu nagaba Akwai cin Amanar Allah Aciki Sabida An Aikata Abun da yai hani Akanshi. Mai Aikata lesbian takan Rayu Cikin kuncin Rayuwa Sabida Allah S.W.T. yakan dibe Ni'imarshi Akan mai Aikatawa, wanda Hakan zesa Komai na Rayuwa yaki cimaka gaba. Sannan duk wanda yake Aikata Hakan harya mutu be tuba ba yasan makomarshi" kuji tsoron Allah wanna Ranar yazama Shine Ranar Karshe na Aikata Hakan A Rayuwarku" kuka Suke Sosai daga dukkan Alamu Nasihar Mamy ta Shigesu. Hada baki Sukayi wajen fadin Mamy muntuba Insha Allah yauce Ranar karshe bazamu karaba. Rungumesu Mamy tayi tace Suyita istigfari kuma su nimi gafarar iyayensu, daga bisani takarbi number din Hajiya maman kausar. kutashi kuci Abinci kuyi Wanka. Daga haka tafita tabar dakin.
💖💋💋💋💖💋💋💖
YAR LESBIAN CE
💖💋💋💖💋💋💋💖
By
Nadeeya Muhammad Ahmad
Page....18
A mota daddy ne ya fahimci kamar mumy bata cikin natsuwa Don firar Shi kawai yake dasu Mubeen ita bata Saka baki. Hafsa lfy dai Naga kamar kina cikin damuwa! Alhji Gaskiya ya kamata mudawo da natsuwarmu musan Abunda yadace A Rayuwa, Wani Abu ya farune Hafsat? Eh Alhaji yau feenah nagani da idona tana......kwashe komai tayi tagaya mishi har irin Jan Hankalin da mamy Tamata, daddy ya girgiza da lamarin gaba daya! daker yasamu yayi parking motan ya juyo yana fuskatar mum, Gaskiya Hafsa munyi babban Sakaci tare da kuskure, musamman ni lokacin Dr yaso ya fahimtar dani Naki yarda Sabida wani nufi nawa na daban, Amma yanzu Allah yanuna mana tun daga nan kuma nadau Alwashin Hakan Bazata kara faruwa da wani da nawa ba, yanzu me kike gani yadace muyi Akai? Alhaji ni inaga kawai Kabeer Dan wajen yaya Nazir Shi Za'a aura mata Kamar Yanda Inna Nafisa Tayi Magana kwanaki. kin kawo Shawara mai Kyau, Amma bazamu Bari takarasa karatunba tunda Shekara ya Rage ta Kammala gaba daya? Alhji ni yanzu Ina tsoro Amma Muji ta bakinta idan Zata iya, Hakane Bari Muji Toh.
Wanka Sukai Sukaci Abinci Suna kara nadamar Abunda Suke Aikatawa Nasihar mamy ta Shigesu kwarai Dan gaba dayansu yanzu komai yin Shi Suke batare da kuzariba, palon Suka dawo wajen mamy Suka Zauna, kausar tace Mamy ni nashirya Zan wuce Zaria yanzu, yawwa yata kundai Ji Abinda nace muku, yanzu idan kuka Saba Alkawari kamar kunyi butulci ne. Mamy Nasiharki ta Shigemu insha Allah kuma mun dauka, Hakan bazai kara faruwa ba, Allah ya muku Albarka, Amin Suka Amsa gaba dayansu, Mamy ta tashi ta kwaso wasu turaruka ta hada taba Kausar, gdy Sosai kausar tayi ma Mamy, bakomai yata yanzu Bari na kira Hajiyar taki Awaya don namata bayani, toh Mamy. Wannan number din Ai inada ita Cikin Contact dina number din Hajiya Sara Dubai ce! Gaba daya Suka maida Hankalinsu kan Mamy. Mamy Ai mahaifiya tace Kausar ta fada. Lallai kam Hajiya Sara Itace mahaifiyarki dole Ace Saikinga karshen boko, kawata ce Sosai a Dubai muka taba Haduwa da ita muke Zumunci Tasan halina nasan nata, kwanaki Har Zaria naje mata gaisuwan Mahaifiyarta data Rasu. Laaaa Mamy dama gidan Su Kausar kikaje gaisuwa, Chan naje Leemah. Kausar tashi Kije Zan kirata namata bayani idan takama ma har Zarian Zanzo. toh Mamy Allah yakara girma, tashi tayi Suka Rungome junansu, toh Kausar Adaiyi Shirin komawa Skul jibi,karki damu Leemah inacikin Shiri. daga haka tafita, mamy takara Zaunar dasu Leemah da feenah tamusu nasiha duk da ita Aksan Zuciyarta Tasan Leemah itama na Aikata Hakan Sundai boye mata ne. Gdy Suka kara mawa Mamy Suka haura Sama.
Kausar Nafita taci karo da Yusuf Wanda yanzu yafito daga Part din yazeed domin yashiga ciki. Kallonshi tayi ta kauda kai tana kokarin fita, Malama Kausar Sannu da gida, yawwa tace Ataikace ta fita daga harabar gidan Zuwa inda drivernta yayi parking. Binta yayi pls Kausar magana nakeson muyi, "inajinka" Shiru yayi Na dan lokaci yarasa mai Zaice mata daga bisani yace i Need ur phone number pls, kamar bazaita mgn ba Saikuma tace "why"? Kausar there are some words we have here, but Naga kina Sauri bakida tym that is why I want you to give me ur phone number Sabida muyi magana daga baya. Karban wayan tashi tayi tasaka mai number dinta tashiga driver yaja Suka huce. Juyawa yayi yakoma Cikin gidan Su yazeed yana jin dadi Aranshi. Kai dama ba tafiya kayi ba yazeed yafada yana kallonshi, Lallai yazeed Nafita na nemo Abinda nazo Dan shine kuma Nasamu,yanzu dai Zantafi. dogon tsaki yazeed yaja yace Allah yasa ba binta kayi kamata magana ba. Yazaka Misilta Abun idan Hakan nayi? Yusuf ya fada yana kashe ido daya, ya Zan misilta kuwa banda nayimaka jaje Ka Zubda girmaka gaban yarinya kara ma. Kajifa Nazeer Abinda Dan uwanka ke fada Dan Allah kayi mishi Bayanin Soyayya mana, dariya Nazeer yayi yace bazai ganeba Saiya kamu da Soyayar Jariryar yarinya wacce Zai gwammace yayi Rainonta harta girma. Tsaki yazeed yaja ya tashi yabar dakin, da karfi Yusuf yace toh Angon yar 30yrs ni Natafi Tunda nayi Nasara. dariya Sukai Shida Nazeer Suka cigaba da firarsu. Yazeed Shiga yayi yaga bakowa a parlon yasamu kujera 1sitter ya Zauna, Remote yajawo ya Chanza Channel Zuwa "ZeeAlwan " haba Malan bakaga Kallo Akeba, juyowa yayi Adan tsorace ganin mai maganar ya Saisaita kanshi yakara tamke fuska, Naga Nan ba gidanku bane dazakizo kina mana Alfahari da isa, Sakin baki tayi Cikin Ranta tace "Wai Wannan Sarkin girman kan da isa yau yake cema wani yana yi" Afili cewa tayi "idan fitsari banza ne kaza tayi mana" Alfahari ai wanda ya isane yakeyinshi, Ke Wlh ni ba Sa'anki bane yanzu zan iya takaki a gidan nan jarababban mace kawai, feenah dabata fahimce me yake nufi ba tace Ai jarabbabun dayawa Ciki harda Kai. Tashi yayi A fusace yayi Kanta. "Toh dake ta mana kadaketa nace" Mamy tafada tana karasowa Cikin parlon, Mamy bakiji Rashin kunyar da takemun bane, tayi din banza mai bakar Zuciya fita kabani waje, Tashi yayi yafita yana huce Aranshi yana Ayyana Abubuwa da dama. My daughter kiyi hakuri da Halin brother dinku, durkusar dakai feenah tayi kasa batace komaiba, Nazeer ne yashigo da Sallama Suka amsa. feenah tashi muje ko, Ahhh yazaka tafi da ita Nazeer? Mamy daddy ne yace mutawo tare Akwai maganar dazai mata, toh feenah tashi kishirya, Tashi Mamy tayi ta Haura Sama feenah tashiga dakin leemah dan ta Shirya. Fitowa tayi daga kitchen besty kinji kausar harta kusa, durkusar da kai tayi kasa ganin Nazeer, my Sister Abinci kike mana? Aa yaya Nazir, Anjuma Zanzo nakawo miki tsarabarki da kaina, toh yaya Nazeer Ngd. Never mind Sister. Feenah ta fito tasamesu Ahaka tace muje yaya Nazeer, besty tafiya kuma? Eh Leemah, Saimun hadu kigaida mum kuma kishirya ma Skul, ok my Leemah. Fita Sukai suka kama hanyar Gida. Suna Shiga daret Feenah parlon daddy ta wuce tasamesu zaune da mum, tshogunnawa tayi tafara kuka mai cin Rai, mumy Dan Allah kugafartamun Wlh bazan kara Aikata makamancin irin wannan Halin ba. Saida tayi kuka Sasai tukun mum tajawota jikinta tace "promise daughter" nayi Alkawari mumy insha Allah. mun yafe miki Ummina kiyita istigifari kinji? daddy yafada Cikin kulawa, gyada kai tayi Alamar Toh, yanzu kinada tsayayye wanda kikeso ne? Aa daddy tun kwanaki dakace bakaso nadaina tsayawa da kowa, Yanzu Ummina Zaki Cigaba da karatun ne kokuma Na hadaki da Kabeer? Shiru Tayi chan tace daddy Zan karasa karatun.Toh Allah ya miki Albarka kinga idan kika karasa dakin dawo Sai Afara maganar auranki da kabeer din. Sunkuyar da kai tayi kasa tace Amin.
Page....19/20
family din Zaune Suke gaba dayansu A makeken parlon dake Sama, firarsu kawai Suke cikin Nishadi da walwala Yayin da Mubeen da Mubeen Suka Cika wajen da Surutu, Nazeer ne yace Bari nakawo muku tsarabarku yanzu murna Suka hau yi, bayan mintina kadan ya dawo dauke da makeken Akwati ya dire a tsakiyar parlon, feenah dake kwance ta daura kanta bisa cinyar "mum" domin yanzu mum Kowacce kulawa da Uwa keba danta yanzu Shi takeyi Acewar ta tayi Hankali yanzu dole tashiga Rayuwar yaranta Tasan Menene matsalarsu musamman feenah da'Itace budurwa kuma mai Raunin Hankali da yawan Sha'awa. tashi Feenah tayi tadawo kusa da Nazeer ta Zauna, wasu back back ne Acikin Babban Akwanting wanda kowace Jaka cike take da kaya, cirowa yayi Yamika ma Mubeena da gudu tayi part dinsu wajen Baba Ladi batama tsaya naga Menene Aciki ba Lol Haka Mubeen Ana bashi Shima yabar wajen, Wasu guda biyu Nazeer yakara Cirowa ya Aje gaban "dad" da "mum" Allah yamaka Albarka Suka fadi Atare, Amin yace Yayin da ya dauko wani big back daga Akwantin ya mika ma feenah, tsalle murna tayi tayi hungging brother din nata tace "thanks So much my big yaya" Uw wlcm my Sister, mumy ce tace Lallai dayake ita yar'uwarka ce Shine nata yafi namu! dariya Sukayi daddy yace kishi kike da Ummin tawa, Ummina tashi kije ciki ki duba kada mum dinki tagani ma, (Kai daddy nima fa naso Naga ko Menene Aciki gashi kamana bukulu nida Readers lolz) da Sauri Feenah ta tashi tayi Ciki, wani back dinne Aciki mumy ta hango toh Wannan kuma Na waye? Mum dama daya Zanba Yusuf ne daya Kuma Na Leemah Kawar feenah ce Nazeer ya fada yana Sosa keya, toh bude mugani mana, kai hafsy kinada Sa ido bazai bude ba, tashi Nazeer Anjuma Saika kaimata gida ko? toh daddy yafada yabar wajen, mumy ce tace idan Zaka gidan kayima Feenah mgn kuje tare dazun mamynku ta kirani wai Feenah taje ta Kwana da Safe yazeed Zai wuce dasu Abuja, mum gobe Zasu koma School ne?? Eh mana Nazeer bakaji dazun feenah ta kara fada ba, ok Allah ya Kaimu. Amin mum tace, yazeed nabarin wajen ta fuskanci daddy, Alhaji yaron Nan Sai Rawar Kai yake Akan Halimatu Anya kuwa! Anya mene Hafsat? Sai nake Ga Kamar Akwai magana, yana bata kulawa ne Sabida feenah daddy yace, tabe baki mum tayi tace Bari naje na daura girki.
Yusuf ne ya Shigo gidan Su Leemah daret part din yazeed ya wuce, tura dakin yayi da Sallama kan tsakiyar bed ya hango Yazeed yana duba laptop da'alama wani Aikin yake, miskilin mutum Na yar 30yrs Sallaman ma bazaka iya amsawa ba ko? Yatsina fuska yazeed yayi yace waye yasan ma kashigo Malan, Oho tunani kakeyi kenan ba aiki ba, ina Ruwanka ne wai? Ruwana Ai nashanye, mtswww yazeed yaja tsaki yace waima Menene ya kawoka nan? Yusuf yace Nazone ka koyamun yanda Ake Kiran budurwa Awaya, tun 4days dasuka wuce na karba numbern ta nakasa kira. dafe Kai yazeed yayi yace Amma ka Raina ma kanka wayo Wlh, So koba wannan yarinyar Zaka kiraba bazan iya bata lokacina Akan ka ba. toh yayi inda budurwa Kace bazakace Haka ba Ai. Wani tsakin Yazeed yakara ja ya juya yacigaba da Aikinshi. Yusuf wayanshi ya ciro yashiga dialling numbern Kausar, Saida kira ta katse ba'a daga ba, cije baki yazeed yayi dan Shi haushin Yusuf yakeji yanzu baga irintaba ka kira yarinya ta Raina ka bata daga ba, ba ruwanka yusuf yace yakara dialling numbern Saida takusa tsinkewa Aka daga, HELLO! Kallon yazeed yayi Alamar ya gayamai Abinda Zaice, juyar dakai yazeed yayi be tanka ba. Hello waye ne? Am....Kausar am Yusuf, ya gida. Lfy tace kawai, Shiru nadan lokaci Yusuf yace "dama magana Zamuyi Kausar, tun Ranar damuka fara haduwa dake gidan kawarki Minal naji......bigeshi yazeed yayi Ahankali yace wawa da gaske Saika Zubda girmanka gaban yarinya karama, juyar dakai Yusuf yayi yana mai Alama da ba ruwanshi. Yacigaba Wlh Kausar tun Alokacin naji Kinzama Wani Abu Acikin Raina,pls Kausar ki karbeni Amtsayin mijin Aurenki nayarda Zan jiraki har lokacin dakika Shirya,fatana kibani waje Acikin Zuciyarki Mugudanar da Soyayya mai tsafta. Kausar daskarewa tayi daga bangarenta yayin da wani Murmushi ya Subucemata Cikin Ranta wani Nishadi take ji domin dama Mamy takira Hajiyarsu ta Sanar da Ita Halin da Kausar tashiga Sanadin kin Bata Hakkinta dasukai, Alokacin kuma Hajiyar Kausar tayi nadama kuma dayake tana karbar Shawarar Aminiyarta Mamyn Leemah Shiyasa ta Sami kausar tace ta fiddo miji Ayi mata aure, Amma duk dahaka Saita karasa Karatun ta tunda 1yr ya Rage mata. Kausar taji dadi Alokacin tayima Hajiya Alkawarin ta daina Yin lesbian har Abada kuma Zata Samo miji, toh yau Saigashi Yusuf din da tunda tafara ganinshi taji ya kwanta mata Arai Kuma yau Shine yazo mata da maganar yana Sonta, murna tarinkayi bangare guda tana tsoro kada Yasan ta taba Aikata lesbian yace baya Sonta.....Kausar kinyi Shiru ba Amsa Yusuf ya katse mata tunaninta. Shiru tayi daga bisani tace mishi Zatai Shawara, pls Kausar nabaki Zuwa Nan da gobe Kinga Zaku koma Skul, ok tace ta kashe wayar, tacigaba da tunanin Wayyo gashi naji mamyn Leemah tace budurci Shine martabar diya Mace Toh Anya nidin Virgin ce ma kuwa, Nashiga Uku Wlh lokacin khady har yatsa tana Saka Mun, gashi Ran nan A grp naji Ance Saka yatsa yana Maida mutum dis Virgin, Wayyo ni Kausar dole Yusuf Yasan Abunda na Aikata Abaya khadija ta cuceni Allah ya'isa harta So na cutar da wasu,Allah yasa Su feenah basa yarda dasaka yatsa da yanzu Suma Saisun koka,kai Innalillahi haka kausar tayita tunanin mafita. Shiko Yusuf Murna yarinkayi harda yar Rawa, Kafin ya juya dan yafada ma yazeed yanda Sukai da Kausar yaga wayam ba kowa Awajen,tabe baki yayi yafita Shidai Sai Murna yake.
Sisto kin Shirya kifito mutafi Nazeer Kema Feenah magana, Nashirya big bro Naga kafini dokin Zuwa gidan Su Leemah dinma, "Aa" Feenah Sabida dare ne, toh muje Nashirya,fitowa Sukai Suka Samu Mumy dasu mubeen tana koya musu homework dinsu, mum mun fitofa, my feenah kin Shirya komai ko? "Eh mumy Nashirya" Zomuje Akwai maganar da Zan miki tashi mum tayi feenah Nabinta Abaya Zuwa Room dinta, Zama sukai mum ta kamo Hanunta,my daughter Kinga Nasihar da mamynku tayi muku koshi kadai ya isheku, Zan kara Miki da nawa Kadan,feenah Abunda kuka Aikata Abaya inaso yazama Labari,na hadaki da girman Allah kada Ki kara aikata makamancin irin Abunda kikai Abaya, Nasan wanchen ma Sharrin Shedan ne ba Halinkin bane,Amma kinsan wajibine Dan Adam yayi yaki da Shedan A Rayuwanshi,kusan duk Abinda mutum ya Aikata na Zunubi Son Zuciya ke Angiza Shi,pls Feenah banason kara jin kin Aikata Abu makamancin wanchan badan niba Dan Allah. Sa'annan game da Sha'awa wannan wani Abu ne da yake damun duk wani baligi ko baliga mai lafiya, Inason kisani Aduk lokacin dakikaji zaki iya Samun natsuwa ta Wajen karanta aur'an,Azkar da yawan yin Azumi, Insha Allah dakin gama karatunki kin dawo Za'a fara maganar Aurenki da kabeer inhar kinasonshi kinji my daughter kimun Alkawarin bazan ji kin Aikata wani mummunan Abu ba koda Aboyene. Rungume mum feenah tayi tana kuka tace Mumy nadau maganarki Bazan kara Aikatawa ba da izinin Allah Koda Chan ma ba halina bane Sharrin Shedan ne! ( wai komai Ace Sharrin Shedan Zaku hadu dashi masu aikata Abu da gangan kuce Sharrin Shedan😄) Allah yamiki Albarka yata, Amin mumy ta! Ki kara Maida Hankali A Skul kisamu Abunda kikaje nema, insha Allah mum. Tashi muje Toh kigaida mamyn Leemah din, toh tace Suka fito atare palon Suka dawo Nazeer har ya karasama Su Mubeena homework dinsu. Yaya Nazir muje Ko, ok Sister muje. Su Mubeen ne Suka tashi suma Zasuje, mum tace kunga Auntyn kuce ba lfy Allura Zasuje Ayi mata,duk maiso saiya bisu. Ai da Sauri Suka koma Suka Zauna feenah da Nazeer Suka fita Suna dariya.
Kai tsaye Suna Shiga gidan parlon Sama Suka haura Anan Suka tarar da Mamy da Leemah Suna fira,Sallama Sukayi da gudu Leemah ta tashi Suka Rungume juna da Feenah Suna dariya. Mamy ce ta Amsa Sallaman tana Allah ya Shiryamunku yaran nan. Mamy Sannu da gida. yawwa my Son, yasu Hafsa din?Suna lfy Mamy tace A gaidaki, ina amsawa. Karasowa Feenah tayi ta durkusa tana gaishe da Mamy,jawota Mamy tayi tana Amsa gaisuwan,my daughter Shine baki kara Zuwa ba tun Rannan ko har Mum ta koya miki Rashin Zumunci ne? Girgiza kai tayi tace Aa Mamy ba Haka bane. Kin kayuta tunda ba Haka bane. Nazeer ne yace mamy Ina yazeed? Yazeed yana part dinshi inaga bacci yake kokuma bakin Ran yake. dariya Sukayi banda feenah data kauda kanta gefe, tashi Nazeer yayi yace Bari naje wajenshi kamun na wuce gida,toh yarona dan Albarka. Leemah jan Feenah tayi Suka Shige dakinta Ya rage saura Mamy A parlon. Kwance ya Sameshi yana waya da Yusuf da Alama fadan nasu Dasuka Saba Suke. Yazeed yana ganin Nazeer ya kashe wayan. Captain kaine A gidan namu? Murmushi yayi yace nine Dr yazeed na kawo Sister dina ne, gemtse fuska yazeed yayi yajawo wata fira Sunayi, Nazeer jiya Nasamu wata baby ita nakeson Aure, kai dacter ina kasamota? Wajen Malali take jiya naje wucewa ta wajen muka hadu, namaka Murna Amma zatakai Shekara 30 din ko? Tace Shekarunta 28 kaga kadan ya Rage, mun fahimci juna da ita tabani phone number dinta, bari kaga picture dinta, kai yazeed ina Zaka Kai Wannan katuwar macen dan Allah?kalletafa kamar.....katseshi yazeed yayi nidai Ahaka nagani Kuma Naji inasonta, Allah yabada Sa'a. Amin yazeed yafada yace bari naje wajen Mamy. Ok Saika fito. Waya Nazeer ya daga yashiga Kiran feenah,bugu daya Ta daga.....big bro tafiya Zakai? No sister turo Leemah ta karbi tsarabanta, ok bro. da ker Feenah tasha kan Leemah tukun ta yarda da tace saidai Suje tare. Tura dakin tayi da Sallam Cikin Siririyar muryanta. lumshe ido Nazir yayi yanajin Wani bugun Zuciya besan meyasa duk lokacin da yaga Leemah saiyaji hakanba tare da Nishadi Aranshi, Azuciyarshi yace tabbas maganar Yusuf Gsky ce Sonta nake, Amsa Sallaman yayi,Leemah ta nimi waje ta Zauna Agefe, Sister nazo baki bani Ruwa ba, Sorry yaya Nazir nazata....kinzata Nasha ko? Eh Hakane Nasha kamin nazo miki,dago kai tayi, yace "umm" yana daga mata gira danke Nazo, wannan na kawo miki ya daura mata Karamar back Kan cinyarta, Sannan Don namiki Sallama,pls Leemah kikula Mun da Kanki, Zaro ido tayi tace "why"? So kike kiji kawo kunnanki tashi tayi da gudu tabar dakin,tana Murmushi, karo taci da yazeed dake kokarin Shigowa,kallonta yayi ya tabe baki yashiga dakin. Leemah nashiga ta Zauna tana nishi, kekuma lfy? Bakomai besty. Toh naga kindade, eh yabani wannan ne. Bude muga,wlh bazan budeba tunda kema banga nakiba. Shikenan Feenah tafada ta juya bacci ya dauketa. Leemah daren Ranar kasa bacci tayi datayi juyi Yaya Nazeer take gani lokacin dayake mata magana.
Page....21
Yau takama Ranar Sunday Ayau Su feenah Suka Shirya komawa Skul. Zaune Suke kan bed Suna hira Leemah ce tace besty yakamata Ki kira Haruna driver yazo ya Kaimu, kinsan fa munce da wuri Zamu tafi. "Oh Leemah sau nawa Xance miki Haruna baya nan" wai Ina Ya tafi ne? Wai daddy ya Aike Shi fa. Yanxu waye Zai kaimu kenan? Muje Mu hau taxi feenah ta fada tana Ware hannuwa. Chaf Wlh badaniba Aje Asiyar dani Ahanyar Abuja Leemah ta fada tana kokarin fita. tabe baki feenah tayi tacigaba da hada kayan dake gabanta. Mamy! Mamy! Oh Leemah idan kina kira kamar makauniya, Mamy dake fitowa daga bed Room dinta ta fada. Mamy drivern Su feenah baya gari waye Zai Kaimu ne? Ai Saikije kice brother dinki ya kaiku "Zaro ido Leemah tayi tace Mamy pls Kije kice mai" Naji Kije kishirya. "Toh Leemah ta fada tayi hanyar dakinta" part din yazeed Mamy tanufa, tura dakin tayi tashiga, yana kwance yana waya juyowa yayi ganin Mamy ce yatashi yana Sosa Kai! Mamy Sannu da gida. "Yawwa Son" Mamy dakin kirani ma nazo Ai, Sabida kada naji firar taka ko? Murmushi yayi bece komai ba. dama So nake katashi kashirya ka Kai sisters dinka Abuja. Mamy....! daga mai Hannu tayi tace Umarni nabaka daga Haka tafita tabar part dinshi. dafe Kai yayi Cikin Ranshi yace wannan mai idon mujiyan itace Zatasa Ayi Hakan, Xanje! but Wlh Leemah nashiga Xanja motan nayi gaba, Kwafa yayi yafara Shiryawa Cikin Manyan kayanshi.
Yusuf ne kwance yana tunanin Kausar Aranshi. Yakamata na kirata Naji menene matsayina Awajenta kamin ta Koma Skul yau! dialling number dinta yayi.......Saida ta kusa tsinkewa Aka daga "Shirune yabiyo baya" daga bisani Yusuf yace Hello "Sweetheart" wani farin Ciki taji Aranta tace "Na'am" Murmushin Nasara Yusuf yayi yace Hope kinyi Shawara din? Shiru tadanyi daga bisani tace Umm Nayi, Alhmdllh Menene matsayina Azuciyar ki for Now? Na Amince But Akwai Abunda Zangaya maka......katseta yusuf yayi my Kausar nariga danaji Abunda nakeson Ji kuma naji dadi, kuma nasan Nayi Sa'ar Matan Aure Tunda kika kasance Kawar Su Leemah bangare guda kuma Kawar Minal yabon da Dr Khalid yake Akan Minal ma kadai ya isheni Shedan kedin kamammiyar mace ce,pls Kausar ki Amince mun na nuna miki Soyayyata,ki yarda Kuma Zaki kasance matata Nan da Dan lokaci! Kausar gaba daya jikinta yayi Sanyi tanason ta gayamai Ainahin Halinta, tana tsoro Shiyasa tace, Na Amince Allah ya nuna mana lokacin, Amin Yusuf ya fada yana jin dadi har cikin Ranshi. Yaushe Zaki tafi ne? Yanzu nama gama Shiryawa, ko nazo nakaiki ne? "Um"um"basai Kazo ba. Kina mun Rowan ganinki ko, No ba haka bane. "Alright " my kausar kikula mun dakanki "I love you" Ok darling love you more. Wow me kikace Dan Kara fada Murmushi kausar Tayi tace Saimun hadu. Alkawari kikai! Na yarda bye ta Kashe phone din, Kai Yusuf Badai Surutu ba ta fada Cikin Ranta kuma tanajin dadin hirarsu. tashi tayi tashiga wajen Hajiyarta, Nafito Hajiya, Ai na leka Naga kina waya, Allah ya tsare kindai Ji Nasihar danakara miki kikula da Kanki,kuma Na Rabaki da khadija din nan idan har na'isa, Insha Allah Hajiya na Rabu da Ita....Allah ya miki Albarka. Amn Kausar tace tafita tashiga mota driver yajata.
feenah da Leemah ne Suka fito Sai Mamy dake biye dasu Abaya, Oho Sarkin bakin Ran bema fito ba kenan, yawwa Mamy tun da befito ba Bari naje nakara duba back din inda Na ajiye Leemah ta fada. Saikiyi Sauri kamin ya fito yafara Harare Harare, toh Leemah tace tanufi Cikin gidan. daughter dakiyita tsayuwa naga Motan Abude take Zoki Shiga kamin Su karaso! Mamy ta fada tana kallon feenah yayin da take bude Mata gaban motar, Mamy Bari nashiga Nan ya'isa, Aa my daughter dawo nan din dai idan Leemah tazo Saita Shiga bayan, bata iya musu da Mamy dan haka kawai tashiga gaban. Mamy tace Bari naje Na turo Shi. Zuwa tayi ta tura dakin nashi ya Shirya yana Zaune yana danna waya" yayi Sarkin fadin Rai tashi ga Sister dinka Chan Amota kamin dayar ta fito kutafi. tashi yayi Mamy nagaba yana binta Suna Zuwa Mamy tashige Ciki tace Bari na turota, dadi yaji Aranshi yace Ai Kafin ta fito Naja mota ta. Shiga yayi be kalli wacece gaban motar ba Kawai yaja yafita da Sauri...... kiyi Sauri Leemah najifa Kaman ya kunnah Car din, Ok mumy nama gani Ai. fitowa Leemah Tayi bataga kowa ba,ta kara leka waje nan ba Kowa, juyawa tayi takoma Cikin gidan, Mamy ya tafi da Feenah, tasowa mamy tayi tace muje dai kiduba waje. Mamy Wlh na duba. Kai Nidai ban San Irin Halin yazeed ba Allah ya Shirya. Mamy ni yanzu waye Zai kaini daddy baya gari? Shine Ai dole na kawo driver Sabida irin Haka. Yawwa bani phone dina nakira Mum dinku. Mika mata Leemah tayi ta neme waje ta Zauna. Kiran mum mamy tayi Suka gaisa, Hafsa Nazeer yana Gidane? Yana nan. Nakai mishi ne? Aa dan Allah Leemah Zaizo yakai Abuja, wannan miskilin dan naki daga taje neman Abu kamin tafito yayi gaba da daughter dina. Ahhh Fatima Kodai Halimatun nawa ta tsaya ba! Eh keda bakison laifinshi cema Nazir yazo yakaita. toh bari namai magana.... part din Nazeer mum tayi tasameshi Akwance kamar mai Naxarin Wani Abun...My Son! Tashi yayi yace Mum. Me kakeyi ne?? Bakomai mumy dazun Aka kirani Ake gayamun Anmun transfer gaba daya Aikina ya dawo Nan. Kai Alhmdullah! Allah ya Amsa Addu'a ta dama ni yanzu banaso kuna nesa dani. Nima Nayi farin ciki mum, Allah yakara temakawa Amin mum. Kana free ne yanzu? Kina son wani Abu ne mum? Mamynku ta kirani wai Yazeed ya tafi da Feenah be dau Halima ba, Shine tace kaje ka kaita. Kara tashi yayi Zaune yace bana komai mum bari natashi, Murmushi tayi kawai tabar dakin ganin Yanda ya daburce farar daya.... tana fita yahau Rawa💃💃Alhmdllh yau Zan Sanar da ita Abunda yake Raina. Shiryawa yayi Sharp Sharp yafita,lekawa yayi yace Mum na tafi. Zo mana Ai tace Anfasa! turus ya tsaya lokaci daya face dinshi ta chanza dariya mumy tayi tace wasa nake Safe trip Son. Murmushi yayi yace Tnx mum yafita yayi gidan Su Leemah. Yana Zuwa Mamy ya kira ya gaisheta yace yakaraso. fitowa tayi Cikin takunta na kasaita yana ganinta yayi Sauri ya fito ya Amshi kayan hanunta yasa a booth ya bude mata gaban mota Saida ta Shiga ya mayar ya Rufe yashiga Yajasu.
Saida yayi tafiya mai tsayi kamshin turaren jikinta yake Shaka yana lumshe ido, Leemah waye yabaki wannan turaren? kinma Shigo bako gaisuwa. Shirun da yajine yasashi juyawa. Keeeyyyyy ya tsayar da motar yana kare mata kallo,itako ta Dan jinginar da kanta Jikin kujera tana bacci Kasancewar jiya basuyi wani bacci mai yawa ba. Gashi tashigo gaban motarshi kamshi da Sayin Ac ya dibeta tun tana tunanin Meyasa be dauko Leemah va har bacci yayi gaba da ita. Innalillahi ya fada Afili ni wai Wannan yarinyar meyasa take Shiga Mun hanci nane? Why? Meyasa duk lokacin da banason haduwa da ita Saina ganta? Mtswww yaja tsaki yakara dago da kanshi ya Zuva mata ido.....baccinta take hankali kwance, Cikin Ranshi yace Ashe tana da Kyau Haka? Daga kai yayi y Zuba ma pink lisp dinta ido,kan Siririn hancinta yakara kallo, ga idonta dasuke Alumshe Gwanin Sha'Awa,kumatunta ya kalla wanda yake dauke da dimple. Cikin Ranshi yakara maimatawa Kai gaba daya Mufeeda batakai Rabin kyan yarinyar Nan ba,kuma ita da kullum face dinta yake dauke da Make-up ma, Amma Ji Wannan bataima make-up dinba Kalleta mai Kyau....mtswww yaja tsaki Afili yace Amma Sai Rashin Kunya da fitsara "iri" "iri" Shiyasa nakeson Mufeeda ba Ruwanta da Rashin Kunya irin na yarinta din Nan......katsemai tuninshi tayi yayin da yaji hanunta kan Cinyarshi, take yaji wani Abu ya wuce mai tun daga Kai har Zuwa tafin kafarshi. Wayyo gaba irinta ba tana mafarkin "blue film" din dasuka kalla Ji yanda takeson tashafa ni. Kara kallonta yayi yaga Still baccinta take, wayanshi ya Kunna yayi joining din Bluetooth Awayanshi zuwa Speaker din dake jikin motan, wata waka ya Saki yakure Volume har karshe. farkawa tayi Afirgice tana Zaro ido. Ganin Hanunta kan Cinyarshi yasata mamaki da sauri ta janye Hannun tana tsaki.....Rage Volume din yayi yace ke wakike ma tsaki? Ni Irin wannan Abun ne ban fiye Soba Ni ba irin manyan Matan yanmatanka bace Zaka dauki hannuna kana Wasa dashi. Cikin mamaki yake kallonta itakuwa ta juyar da kai kamar ba Ita tayi maganar ba. Cikin Ranshi yace Nice Voice! Afili yace Wlh kika kara Kiran budurwata babban mace Saina cire miki baki. Murguda baki tayi tajuya.....tsaki yaja yakira Mufeeda Awaya.....ganin Sai fira yake ya cika mata kunne yasa tace katsaya na koma baya......Wani kallo yajefa mata tayi saurin kauda Kai. Ahaka Suka Cigaba da tafiya bamai kula kowa. Saida Suka fara tafiya Leemah ta juyo tace yaya Nazeer Ina huni? Lumshe ido yayi ya bude yace lfy qalau my baby! da Sauri ta dago Kai tace yaya Nazeer ai nahuce baby yanzu. nikuma Sunan Dana Zaba miki Kenan...meyasa Yaya Nazeer? Kinaso kisani? Gyada Kai tayi Alamar eh. Nazir yace bazan fadaba, Saurayinki ya Xaneni. Ganin yanda Yayi maganar Cikin Shagwaba yasa Leemah dariya. Kikai dariya ko Karya nayi? Yaya Nazeer Ai banda Saurayi. Ban yarda ba. Allah kuwa katambayi Feenah Kaji...Okay Xan tambayeta. Tnx Once Again for d gift yaya Nazeer. ur wlcm baby! Kin bude kenan? No ban bude ba. Why? Banaso feenah tariga ganin nawa that is why. Nima Naso Hakan. meyasa Yaya Nazeer? Just because of Akwai Sakon danakeso ya'isa gareki Ke kadai, but tunda har Yau bejeba Shikenan.wani sako ne Yaya? Kinaso kisani? "Yeah" Idan nafada miki Zakiyi Accepting ne? Why not. Haka kikace ko? "Eh" daidai sun iso Abuja Suna Shirin Shiga Unguwar inda Skul dinsu take. LAAAA baby kalli motar yazeed. Maybe ya kaita ya juyo Leemah ta fada. Maybe toh Amma basuyi Sauri ba....inaga baya gudu Kamar yanda mukai. Eh hakane. Karasowa Sukai daidai bakin get din. Ta kalleshi tace "tnx Alot yaya Nazeer"tana kokarin fita. Yazaki fita ban gaya miki ba? Sorry namance nakosa naga feenah nd Kausar. dariya yayi yace "friends forever" tace insha Allah. "do you love me" ta tsinkayo muryan Nazeer Yana fadin haka! Joyowa tayi takura mai ido Dan taga shine Yayi maganar da gaske. Shima ita yake kallo. Jin Shiru yasa yace baby "tell me" batai mgn ba yace " Leemah I love you" bansan wani iri So nake mikiva tun lokacin da Feenah keban labarinki Nakamu da Sonki van tabbatar ba saida naganki, pls Leemah kitaimaka kisoni Koda Kadan ne. Kece kika dace da Rayuwata Kuma kece Nakesa Ran kizama Uwar yarana pls kisoni.....inasonki inasonki Leemah kedin kinada babban Waje Acikin Zuciyata. Matsowa yakarayi gab da Ita "kina Sona"? balle murfn motan tayi tafita da Sauri tashige Cikin Skul din. Murmushi Nazeer yayi yafita yaciro Kayan yashiga dasu.....
Page...22
*After 3months*
Su feenah yanzu Hankalinsu gaba daya yana kan karatunsu ne Sabida yanzu Zangon karshe Suka Shiga. Soyayya mai karfi tashiga tsakanin Yusuf and Kausar Su feenah duk Sun San da Haka yanzu! tunda Yusuf din Har Zuwa yayi Abuja..... bangaran yazeed ma dai har yagaji da Surutu Kan meyasa Yusuf ya Zubda girmanshi. Shima yusuf din yagaji da Surutu Kan me yasa yazeed yake Soyayya da babban mace Sabida Mufeeda budurwan yazeed Shekara daya kachal yazeed din yabata. Sai yazeed yace Ra'ayinashi Kenan Ahaka Yusuf shima ya fake dacewa Nima Ra'ayina karamar mace. Mufeeda da Yazeed Soyayya Suke Sosai Kullum Saita mishi korafi Akan ya kaita ta gaida Mamy Sai yace Toh,Cikin Zuciyarshi tsoro yake ya kaita Mamy tace batai ba, kokuma Ace ya Aureta yanzu! Shikuma yace Saiya karasa Shekara 30 Zaiyi Aure. Mum and daddy Suna yawan Ziyartan Feenah mum janta take Ajikinta Sosai, Kowani irin Shawara da ita takeyi. Hakan kuma ba karamin faranta ma Feenah Rai yake ba, matsalarta daya ita batasan ko wace irin mace bace mai karfin Sha'awa, bata kallon kowani irin films yanzu bare karance karance Abunda Zai jawo mata Sha'awa Still takanji tym to tym, Shawaran mum ta dauka na yawaita Azumi da Yawan karanta Qur'an . Bangaren Kausar ma Hakan take duk da batakai yawan Sha'awan da feenah keyiba Amma dukansu yanzu Azumin kamis da litinin baya wucesu kuma Suna kara neman gafarar Allah Akan kuskuren dasuka Aikata Abaya. Yanzu gaba daya Basa mu'amala da Khadija dama Sudin bama su kula kawaye bane A Skul din,Saidai kawayen Surinka Shige musu. Bangaren Islam ma Suna cigaba da Zuwa wajen malamin dasuka dauka yana koyar dasu kuma Alhmdullah Suna kokari ba laifi. Yaya Nazeer Yacigaba da Aikinshi A wani Barack dake Wajen gidan Governor Anan kd. Haryanzu tun lokacin da yakawo Leemah Skul be kara Zuwa musu ba, Ga Soyayyarta dake kara dasar mishi Azuciya, yanaso ya amshi number ta yana tsoron kada taki Amincewa da ba tun, Shiyasa yadan bari Zuwa wani lokaci. itama dai Leemah Anata bangaren tun lokacin daya gaya mata takejin tama Amince da Soyayyar Shi,Amma Akasan Zuciyarta kunya takeji tayaya Ga Abinda da Suka Aikata da feenah Sister dinshi kuma yanzu ta aureshi, da kunya inji ta bakinta Shiyasa bata wani Maida Abun Serious ba But aduk lokacin da ta kwanta Saitayi tunaninshi. Har feenah tasha tambayarta Akan meke damunta Saitace ba komai. Mamy ma tazo mata har take Sanar da ita cewa KaKarta mahaifiyar Abba ta dawo gidansu da Zama,dama Chan dai Anyi Anyi ta dawo taki,Saida ta gadama dan kanta. Haka dai Suka cigaba da tafiya Akan karatunsu.
Zaune Suke Su uku A babban bedroom dinsu Suna Fira Suna dariya. Akan Abinda Suka ga khdy da wata Kawarta Sunyi dazun. dariya Suke Sosai dan Leemah harda yar kwallarta😂 Kausar ce tace ""Kai Halumcy idan kika Samu Abin dariya bakida kyau" Leemah tace kedai kawai kice Dan Kinga da kawarki muke Shine kike so ki shigan mata, Wlh Abun dariya wai fa dan muji haushine tayi Hakan ko? Feenat tace Lallai tasha wuya gashi bamuji haushinba Saima dariya da Abun ya bamu. Kausar tace yanzu ba wannan ba gift din da yaya Nazeer ya baku nakeso nagani yau! dumm gaban Leemah ya fadi takuma Rasa dalilin hakan. feenah ce tace Kai yau idan baka nuna mawa Kausar wannan gift ba kashiga Uku da Saka ido da naci# dariya kausar tayi tace Naji dai dauko mugani, kema Leemah tashi Zaki Ki dauko muga Naki. Kusan atare kowacce ta dauko box din ta. Ajewa Sukai feenah tace Leemah bude Naki muga. Noo besty fara bude Naki mugani. budewa feenah tayi tashiga Ciru Abubuwan Ciki. Wani box dinne again cikin na hanunta Shi takara budewa kayan make-up ne Aciki irinsu foundation,eyeliner,eyeshadow,blush etc. Sai wani Abu wanda Zananshi Zanen Hart ne Shima budeshi tayi. Cikinsa eyewear ne da best perfume dinta. Wani box Dan karami takara budewa. Necklace ce Aciki yar Siririya ta Zinari da earrings dinta. "WOW Suka fada atare. Yayinda Suka kara bude karamin dayan box din."Ring ne Acikinsa na diamond" Oh My God Kausar da fada da karfi yayin da ta dau Ring din tana juyawa. Wata yar takarda Feenah ta jawo Aciki Rubutune mai Kyau Aciki Kamar Haka. """""There is No better friend than a Sister and No better Sister than you. Really miss you my Sister""""" Murmushi tayi data gama karantawa tace Allah Sarki Yaya Nazeer yana Sona da yawa nima nayi missing dinka but tunda kadawo yanzu komai yayi daidai. Kausar kidau Abinda Kikeso Aciki. Ring din Kausar ta dauka tace Wannan Shine Soyayyar da kike mun thanks So much my feenah. Leemah ce tace Saura Kije kisaka ma Yusuf dariya Sukai gaba daya kausar tace Ai wannan nawane yanzu dai bude naki Na zabar ma Sweetheart dina Aciki. budewa Leemah tayi kusan duk Abunda Ke cikin Na Feenah Shine Acikin nata, turarene kawai Ya bambanta Nata "princess Sunan Shi" Haka Nan taji Son turaren don ita Shi ta dauka, zobe ne kawai babu Aciki. Hango wata farar takarda tayi da Sauri da faki idon Su feenah ta dau dakardan tayi toilet. Tana Shiga tafara bude takardan tanayi tana Shinshinawa don kamshin dake jikin envelope din ba karamin dadi yake mata ba. budewa tayi tafara karantawa Ahankali. """"""it feel Amazing to be in love with a girl, who is beautiful both insade Out! You are the girl from my dreams,who I thought never existed. I love you baby"""""" lumshe ido tayi tana Ajiyar Zuciya lokaci daya taji wani irin Son Nazir yakara dirar mata Azuciya. " I love you too" ta fada Akasan Zuciyarta.....Leemah kifito muga me kike boyewa ne tajiyo muryan Kausar da Sauri ta boye pepper din tafita. Me Kuwa nake boyewa? Sainaga kamar kinshiga da wani Abu mai kamshi...kai kausar bakiyi ba Haka Kawai sainashiga toilet da Abu mtswww kyaleta besty Kinsan Halinta. Kiran Yusuf daya Shigo wayar tane ya hana takara magana.tashi tayi takoka chan karshen gado tana waya.
Yazeed ne da Dr Khalid Zaune a gidan Su Yusuf Suna fira. Yusuf yace Dr Khalid Dan Allah kayima Yazeed magana yafita harkar katuwar yarinyar nan inaga kai yaji maganar ka. Wani mugun kallo yazeed ya wurga ma Yusuf yayi kwafa, kallonshi Dr Khalid yayi da Murmushi yace Dr yazeed Kaji Abunda yusuf yace. Kai Dan Allah Rabu dashi ba Gara Ni babban mace Nake biba! Shifa dayake makale ma yarinya karama duk tabi ta Rainashi,idan yana waya bakaga yanda yake yiba kamar yayimata Sujada yake ji. Nikuwa kaga tawa da hankalinta bata wahalar dani kuma batamun Rashin kunya......katseshi Yusuf yayi kaga kai dakanka Kace babban mace kake Soyayya da ita, tayaya Zata maka Rashin kunya taga Dan Samari kyakykyawa Son kowa,Ai ko kanwata ce Zanso naga tabika Sau da kafa domin Ka aureta mu rage iri, don wlh Wannan katowar yarinyar idan Aka mata Aure Anrabu da iri. Furzar da iskan bakinshi yazeed yayi ya kalli Yusuf watoh Dan nazo gidanku Shine kake gaya Mun magana, Wani Abu dabaka Sani ba yau din Nan Zan Kaita wajen Mamy,Idan Aka Saka Aurena da Ita kaje ka Raba Shine Zansan baka Son Abunda Nake So, daga Haka yayi hanyar fita. Dr Khalid na kiranshi Bebi takanshiba yabar gidan Su Yusuf. Dr Khalid Kallon Yusuf yayi yace wai ya rinyar ya take ne? Wlh Dr yarinyar batada wani Hankali Ai munje dashi sau daya bakaga Yanda take Abuba kamar irin karuwai din Nan, daga ganima bleaching take, ga Wani gashin doki data kawo ta dankara Kamar ifiritu. dariya Dr Khalid yayi toh shi menene Ya burgeshi da ita? Kawai kasan Ra'ayinshi ya Aure mace mai Yawan Shekaru, har Office takawo mai tallan kanta Ranar ina wajenshi, 28yrs fa yace yarinyar tace Mai wayasanima ko tafi haka.Shekara daya Kawai yabata wani lokacin yazeed Kamar mai Aljanu haka yake,Amma Ace duk matan dake kawo kansu gareshi yarasa wacce Zai Zaba sai wannan jifa pic dinta....dariya Dr Khalid ya sheke dashi harda rike Ciki,Gaskiya yakamata mutaya yazeed da Addu'a Yusuf. Rabu dashi Dr yana Kaita gidansu Nasan Za'a koroshi,musamman wannan kakartasu data Zo Nasan bazata yarda ba. Allah yasa Hakan donni ina mai kwadayin feenah dinnan dan ba karamin dacewa Sukai ba. Aikuwa Dr dama itama yarinyar muskila ce irinshi. Hhh bari natafi Yusuf Minal nachan na jirana. Muje na taka maka Angon Minal. Yazeed na fita ya kira Mufeeda A waya yace tashirya yakusa Zuwa. Ashirye take tabashi Amsa. Yana karasawa yakirata tafitoh gaban motan ta bude tashiga tana karairaya ( kodai Karairaya da fari da idon mufeeda su Suka Ruda yazeed Oh!😄 don koni danaga Shigar da tayi saida nayi tunanin Ko irin Christian din nan ce lol) Honey Ka fada ma mamy Zanzo kuwa? na fada Mata tun jiya ma kuwa, Yusuf fa? Yatsina fuska yayi yace Menene hadinki dashi? No ba Komai naga Abokinka ne. Kincika Surutu! Am Sorry honey...Hannu takai gaban Rigarshi Yayi sauri ya bige Mata Hanun miye haka yafada fuska a daure? Honey kallifa kaman Abu ya zuba Maka, goge maka nakeso Zanyi Cikin muryan yanga tayi maganar, Sai duk jikin yazeed yayi Sanyi, kibarshi kawai yafada murya Kasa kasa. Ai nabari Honey kada kaga Kamar nayi Rashin kuny. Hmm yace lokacin dayake kokarin yin parking a harabar gidansu. fitowa yayi ya tsaya yana jiran fitowarta....juyawa yayi yaga bata fito ba mekike jira ne? Honey nazata kaine Zaka bude mun...kallonta ya tsaya Yi yace Kamar wata yarinya common fito mushiga..... Aidama Nasani ni kadai nake Sonka gaba daya baka nuna mun So. Juyawa yayi yashiga Ciki yabarta Anan. kwafa tayi tafito dan tasan kozata mutu bazai bude Mata ba.Cikin Ranta tace dana aureka Nima Zan watsar da kai bawai kana Alfahari da Kyau da kudi ba. kusan Atare Suka Shiga parlon bakowa ya nuna mata kujera Ta zauna yashiga Ciki. fruits din da Aka aje Kan table ta dau Apple tana ciki. ( wayaga Hanadi Anje gaida Surukai bako kunya😄😄😄😄) fitowa yayi yana kallonta ya kauda kai yace Yanzu Mumy Zata fito, Honey sister dinka fa? Tana Abuja. Ok. Zaki iya aje Abun hanunki kuwa? Bakomai Ai Honey gidanku gidanmu ne. Inno Ce tafito tana Oyoyo kishiyata ina kike Yau ko ruwan gidanmu baki Shanshi.....trus ta tsaya ganin mufeeda da Shiga irin ta yan bariki. Kallonta mufeeda tayi tace kaka ina huni daga Zaunen da take. Shiru inno tayi ta kalli Yazeed ta harareshi tayi Ciki mufeeda bata damu da Kin amsa gaisuwan inno ba tacigaba dacin Apple dinta... Shashin Abba inno ta nufa sanin Cewa mamy nachan. Fatima Fatima kitaso kiga kafurar Matan da yazeedu ya kawo Miki Wai Surika. Mamy ta dago Kai tace mama lfy? Taso kije kiga kafurar da danki ya kwaso nace. Tashi mamy tayi tabi bayan Inno suka Sakko kasa.....daidai Mufeeda na yanka lemo. Kinganta Nan Shedanin danki Mai bakar Zuciya Shine Ya kawo ta. Kallonta Kawai mamy keyi Saida yazeed Yayi mata Alama data Ajiye lemon tukun ta aje! Mamy inawuni ya gida. Lfy mamy tace ta kauda kai. Inno ta kalli Yazeed tace yazeedu Kayi Asara wannan itace matar dazaka aura kusan Sa'ar uwarka. Shege Ashe duk fadin ranka bakasan menene yadace da Rayuwarka ba. Kaje kasamo Mai jini Ajiki irin Su Halimatu shine ka kawo wannan katuwar. Toh wallahi karabu da Ita ko Nakira Ahmadi Nace ka kawo kafura itace matarka. Tunda tafara magana mufeeda da yazeed ke kallonta. Atare Mufeeda ta kwashe da dariya Yazeed kuma yaja karamun tsaki......kinma Ubanki dariya inno ta fada tana Nuna mufeeda Shegiya Mai Suffar yan huta...Kaikuma kama Uwarka tsaki banza tsaka Kawai...daga haka tabar wajen tana ka kara kawota Nan gidan Ka gani sharri zanma wajen Amadi.....tashi mamy tayi itama Ranta Abace tace idan Ka maida ta Kazo kasameni batajira amsarshiba tayi Sama. Taso muje Yazeed yafada cikin muryan jin haushi...tashi tayi Cikin Ranta tana Sunrabani dashi bansamu Abinda nakeso ba....Wayyo ni Mufeeda Nasan banida wata mafita kuma.kwafa tayi tunowa da Wani Abu datayi Aranta.... Afili Cewa Tayi Honey Kada kadamu banji haushi ba kasan Ana Samun tsofaffi haka......kallonta Yazeed Yayi yace Nasan bazakiji haushiba daman...Amma dole murabu don Wlh tsohuwar Nan tafi Yanda kike tunani,Yanzu nan Saita hadani da Abbana.....murabu fa Kace? Eh mana. Hadiye miyau tayi darker! Aranta tace wlh yanzu Zan Nuna maka bazaka Iya rabuwa daniba.......ihu ta kwala da karfi wayyo honey nataka Abu Akafana....juyowa Yazeed Yayi yakaraso wajenta muga kafan......bazan Iya Nuna Maka ba..daukanta Yazeed yayi chak Yayi hanyar part dinshi da ita, Murmushin Nasara mufeeda tayi tana Murna Cikin Ranta.....
0 comments:
Post a Comment