Mintuna kadan Suka Kai Mamy har kofar gidan Su feenah. gidan tashiga Kai tsaye babban parlon Nasu ta nufa da Sallama. Twins ne kawai A parlon Suna ganin ta Suka tashi d gudu Sukai kanta. Oyoyo Mamy Oyoyo mamy Abinda Suke fada kenan Rungumesu tayi lokacin data karasa ta Xauna kan kujera. Twins kun kara girma Shiyasa bakuzomun ba 2days koh?. Mamy gobe Zamuzo miki ai. Kacika wayo Mubeen gobe kunada Skul ba Zuwa Zakuyiba Nasani. Mamy Nidai yau Zan biki. Yawwa mubeena Kinga Saiki Kwana wajena ko? Kiga mai Kyau da Aunty leemah. Kada kai mubeena tayi Alamar eh. Ina Mumyn ku? Mum tana Sama taje daukoma Mubeen kaya. Aima gani Nazo mum dake Sakkowa ta fada. Ashe babban bakuwa Nayi! daria Mamy tayi Aikuwa keda bakya Son Zumunci Sosai ba. Kai Fatima da kenan kika Sani duka duka yaushe nabar gidan ki? Kindai Cika kare kanki. Murmushi Mumy tayi yayin data tashi, Bari Nakawo miki Abunda Zaki motsa baki. bata wani dau lokaci ba ta dawo. Sannu Hafsat. Sannu Fatima y Leemah kwana biyu batazo mana ba. Tana gida nabarta Suna fira d Inno, Halan feenah bacci take koh? umm Feenah tana Sama batajin dadi kinsan tun lokacin da'akai maganar bikinsu take faman Tunani wanda Narasa Na miye. Kenan Shiyasa yanzu take kin Zuwa gidanmu, tunanin nata be wuce Na Zaman yola da Zatai ba Hafsat! Toh tunda dai basajin magana basaisuyi hakuri ba. Inafa Zasuyi Hakuri Hafsat,kina ganin yazeed Abunda yasaka ma Zuciyarshi yanzu, tundaga lokacin Shima da'akai maganar bikinsu Narasa kanshi, Ni dama Sabida Shi nazo Nan, Hafsat gaba daya Al'amarin yazeed yanzu tsoro yake bani yaron da ada idan kika Saka mishi yatsa kikace ya Ciza bazai iyaba, Amma yanzu Shine yake ja'inja da Mahifinshi bama niba, Yanzufa Sai Abinda yarinyar nan Mufeeda tace mishi yakeyi, Ko'ina tayi yarinka binta Kaman Rakumi da Akala. Nisawa Mumyn feenah tayi Gaskiya Fatima Ina tunanin Akwai Wani Abu Akasa, idan baki mance ba Akwai Sanda yazeed yakusa dukan yarinyar Agabanmu, baya sonta wancen lokacinma daya kawota yace zai Aura ina tunanin dan Abbanshi yace ya fiddo mata ne yasa y kawota badan yana Sonta ba, Amma Gaskiya Abin nashi na wannan karon bayin kanshi bane, yakamata muyi binciki Akai. gaskiyane Hafsat Abinda inno tace kenan harta Saka wani Malamin Sunnah A Katsina ya farama yazeed din Addu'a! Tabbas Itace kuwa Mafita dan duk wanda yaji wannan Al'amarin yasan Akwai Sihiri Aciki, muma kanmu Mudage da Addu' a kawai Allah yakareshi daga Sharrinta d Sauran mutane gaba daya. Hakane Nifa Sam banason Auren nan nashi da'ita Hafsat. gaskiyane nima lokacin danaji Raina beso ba Wlh Addu'a din dai idan ba Alkairi Cikin Aurensu Allah ya Chanza Al'amarin. Amin dai domin Kwata kwata bata dace da Rayuwan yarona ba. Kinsan ma miye fatima kisaka Amishi Saukan Qur'an Ki yawaita Sadaka itama maganin masifa ce. Insha Allah Zan dage Hasfa Allah yamana maganin Abinda yafi karfinmu. Ameen ya Allah, Shima yazeed din yakamata kirinka lura da yanayin ibadarshi, kirinka Sakashi Agaba yanayin addu'oe da Azkar, Bari Nakawo miki Ruwan Zamzam kirinka Shafa mishi kuma yanasha insha Allah Za'a dace, Sannan kisamu ganyen magarya kinamishi Amfani dashi Shima yana karya Sihiri da izinin Allah. Shiyasa Shawara yake da dadi Ina Zaune kawai Nayanke Shawaran Zuwa wajenki, Allah yakara Zumunci Surukata. dariya mum tayi Amin dai, Amma kisani leemah yatace bana Surukar dake. dariya Mamy tayi Sukacigaba da firarsu ta Aminai. Bari kiga Naje na duba feenah natafi. da Wuri haka mamyn yazeed? Eh Zanje nafara lura da yazeed din ne. Hakane kuma! Ai yar taki tana Ciki Saikin Sakko. Sama Mamy ta hau ta Nufi dakin Feenah, kwance take idonta Alumshe kamar mai bacci Amma ba baccin take ba, blanket taja ta Rufe iya kafafunta. tura dakin Feenah Mamy tayi da Sallama. Kasa kasa feenah ta Amsa Sallaman still idanunta A Rufe. Karasawa Mamy tayi bakin bed din ta Xauna kallon feenah tayi ganin idon feenah Sun kumbura ya tabbatar mata dacewa kuka tayi, Ajiyar Zuciya Mamy tayi yayin datake karajin Son feenah Azuciyarta, yarinyar Na burgeta har Cikin Ranta takejin Son yarinyar. Cikin Ranta tafara magana. " me yasa yaran Nan Suka kasa fadan Abinda ke ransu? Zanso Ace feenah tazama matar yazeed domin Itace ta dace da Rayuwar Shi, me yasa Abban yazeed be hada Auren yazeed da feenah ba?, Maybe ba Alkairi bane Zuciyarta tabata Amsa" motsin da feenah Tayi ya katsemata tunaninta. Kara matsawa tayi my daughter bacci kike? bude ido feenah tayi jin muryan mami, Murmushi Mamy ta Sakar Mata, itama Murmushi tayi tana kokarin tashi. mami ina hini, yanzu kikazo? lfy yar Albarka,tun dazu Nazo, Nazo bikonki 2days kin kujemu. durkusar da kai feenah tayi kasa dan'ita nauyin mami takeji,ba haka bane mami. toh yaya ne?kodan kinga Mumy ta kara gyaraki bakya Son kifita Rana ya bata gyaran jikin dakikama Angonki,kamar yanda Leemah tace itama. da Sauri feenat ta daura kanta jikin mami hade ta tura kan Cikin Cinyoyinta tana boyewa. dariya Abun yaba mami Menene Najin Kunya, ko angon ne ya koya miki? mami Nifa ban Sanshi bama, kuma nacema mumy ta daina Sakawa Anamun gyaran jiki taki, ni banason Auren Mami, kuma...kafin takarasa maganar kuka ya kwace mata, pls Mamy kinga Leemah wanda takeso Xata Aura,itama Kausar Wanda takeso ta aura, nima kicema Abba da dad Subari nafada musu Wanda nakeso pls. Rungumeta Mami takarayi. Ya'isa Feenah, yanzu Zakifadamun wanda kikeso din inyaso Saina fadama Abban yazeed Kinga sai'afasa Auren Da Wanda inno tace! Shiru feenah tadanyi Kadan, mami ni bansan Wanda nakesoba kawai inason ajanye maganar Aurena da Wanda bansanshi ba. Murmushi mami tayi Kidaina damuwa feenah kinsan Komai yafaru daga Allah ne kawai kiyi addu'an dacewa da miji nagari, Abbanku yayi fishi da yawa bazai janye maganar Aurenku ba. bakya ganin yazeed ya hakura Zai Auri Balaraba din? Turo baki feenah tayi Mamy Shifa yanasonta. bayasonta feenah kawai ya hakurane kema inason kiyi hakuri pls. Shiru feenah tayi batace Komai ba, ganin haka yasa mami ta tashi Bari natafi kicire damuwa Aranki daughter dan Allah. toh feenah tace takoma ta Kwanta Sabon hawaye nabin face dinta.
Waike Khady Atunaninki bansan me kike munba? yatsina fuska khady tayi Kaman miye Kenan? Wani banzan kallo mufeeda ta Watsama khady Na Abinda kike kokarin yi yanzu Kika kasa. Idan wancen karon kin batamun Ayyukana kisani wannan karon nagaba yayi gaba, yazeed ba Sa'anki bane dazakice Kinason Shi, yazeed Nawane Ni kadai mallakina, dama danni Uwarshi ta haifeshi, Auren ma dazaiyi nice Nace yayi ba matsala domin Nasan nawuce da Ajin kowace mace. Anma dani kadaice matar yazeed. Garama kirufama kanki Asiri kikoma Katsina Kiba iyayenki hakuri kan bijerewar dakikai musu, domin yazeed Yamiki nisa. khady taji Zafin maganar mufeeda matuka bangare guda tayi mamakin ya'akai mufeeda tasan ita ke Karya mata Asiri, koda yake ba'abun mamaki bane bokanta ya fada Mata inaganin. komawata Katsina ba damuwar ki bace mufeeda, kuma kisani bani kadai yazeed yafi karfin ya Aura ba hardake. Kedin banda tsautsayi mai yazeed Zaiyi dake, kardai kimance komin dadewa Asirinki Zai tuno,koda bayan aurenki da yazeed ne Sai Asirin dakike takama dashi ya karye,ke bama Kyau tunanin Wannan Ranar ko kadan, kisani Itace dai Ranar dazakigane Kuranki. Ke dallah malama ya'isa✋ Ni Matar yazeed ce Har Abada babu Abinda Zai Rabani dashi, idanma takamarki kije kikarya mun Asiri toh karyarki tasha karya Wlh, domin Ashirye nake dana Halaka duk wani maishirin Shiga tsakanina da yazeed. Hmmm mufeeda Aini yanzu nadaina wahalar dakaina kan Abinda nasan bazai yuwuba, Kije gaki ga yazeed, Amma tun yanzu yakamata kigane Cewa Asiri bakomai bane illah Shirme, tunda haryanzu dason feenah Akasan Zuciyarshi, Hasalima son dayake mata yaninka naki duk dacewa Ansaka mata Ranar Aure. Yaje yayita sonta mana daga sanda tayi Aure dole yacire sonta Aranshi Wlh. Ina tausaya miki mufeeda! Kidai tausaya ma kanki khady, Ni yanzu me narasa babu. Hamm Nima yanzu inada Wanda zan Aura mufeeda Shaharren Alhaji ne babu Abinda baya takama dashi infada Miki. Jin da mufeeda tayi khady tabar son yazeed yamata dadi danhaka tasaki Ranta, muga picture din Aalhajin. Waya Khady taciro tashiga nunama mufeeda photos din Alhajin. Tabe baki Mufeeda tayi ko kwatan yazeed beyiba wannan mutumin, daga ganima yasha miya. kudi banza idan da kudi ko tuwo yasha banida matsala. kudinma ai bekamo kafar yazeed ba. Eh Anma ai yanada Shi ko? Oho dai dole Zaki hada da Asiri domin bazaki Iya daina lesbian ba Ayanda kikai sabo dashi, kinga daga sanda yagano zai kadaki titi gara ki tashi tsaye. Tunani khady tayi kadan kumafa Hakane Wlh. Kwarai Nima bazan iya hakuri dake ba, har gidanki zanrika biyoki inajin duminki Seemah dake Shigowa ta fada.dariya Duk Sukayi atare Sukace lol dole mufeeda tarakani wajen bokanta na toshe bakin Alhaji. Hakan ma yayi Seemah ta fada. Ai Wlh koda Zan Rakaki Sai bayan bikina da yazeed domin ina tsoronki khady. Dariya duk Sukayi Ai nariga nabar miki Yazeed mufeeda kwantar d Hankalinki. duk da hakan dai.duka duka bikin naku ba Saura Sati daya ba? Hakane Toh na hakura Ayi bikinku Saiki Rakani. Shine magana mufeeda ta fada yayin data tashi bari naje Wajen yazeed minti talatin kawai Zanyi. Chaff Seemah ta fada Shidai yazeed din Nan Asirima baya cin miskilancin Shi sabida yayi yawa. Tabe baki Kausar tayi barshi Nidai Tunda yazo Hannu. me Zakije kimai yanzu Toh? Rage Zafi zanyi, Dan haryanzu fa be yarda yayi sex dani ba! Tohh fa Agaidaki duk kinwani makale mishi, Ashema duk fadin Ranshi begama wayewa ba tunda yana tsoron yin Sex. week y rage mana, dole dai yayi idan mukai Aure mufeeda tafada yayin data bar dakin.
*ALLAH KASHIRYA MANA BAYINKA MASU AIKATA ABUBUWAN SABO SON RANSU*. (AMIN)👏👏👏👏👏
Tun Sanda mamyn yazeed tayi Shawara da mamyn feenah ta dage dayima yazeed Addu'oeh, kamar yanda Mum ta fada mata tasa Ayimai Saukar qur'an Hakan tayi, takuma Cigaba dasashi yin ibada duk da yana nuna bayaso, kusan kullum da fada take mishi Amfani da magarya da Ruwan Zamzam. Aduk lokacin da takemai mufeeda tazo haka Zai tsallake Mamy yatafi wajenta, Sam mufeeda bata fahimci Komai game da Abinda Ake shafama yazeed Ajikinshi cikin Wannan Lokacin ba, tafi kawo tunanin Ko Al'adansuce haka idan Za'ama mutum Aure,Dan haka bata Wani damuba. inno, yusuf, da Mamyn feenah suma ba'a barsu Abaya wajen yima Yazeed addu'a ba. Raba dare Suke Suna mishi addu'a. Tunda yafara Rashin lafiyan Saudaya feenah tasashi a idonta,yanda Ake fadan Al'amarin yazeed bewani dametaba, Amma Ranar data ganshi taga yanda mufeeda keyi dashi kamar wani waina tayi matukar mamaki,takuma tausaya mishi Sosai, dukda bangaren Zuciyarta guda bataga laifin mufeeda Akan Abinda tama yazeed ba, tafi ganin laifin yazeed din Acewarta tunda kullum saisun Aikata Zunubi tare tayaya Saida yagama batata tukun zaice bayasonta, gara datamai haka Shine Zai Aureta dole,idan kanwarshi Akaima haka bazaiji dadi ba. Haka Ranar tarinka sake sake, Saidai idan t tuna Aranar yanda yazeed duk ya daburce kan ganinta din dayayi tana mamaki, babu yanda Mamy batayi dashi aranar yasha magani ba yaki,Amma data mikama feenah tace tabashi hannu n Rawa ya karba yasha, Uhum Maybe nadamar wulakancin dayayimun Abaya yake. Haka tarinka Sake sakenta ita kadai. Saidai Zuwa yanzu tariga tahakura kan Auren daza"a mata ganin babu makawa Sai Anyi,Abu daya ke bata Ranta yanda batama san kalan mijinba. Amma ta Zage Sunata shirye shirye Kamar ba'itace mai kuka ada ba. Kausar itama da ita Ake shirye Shiryen Komai duk da cewa Cikin dake jikinta yana dan bata wuya yanzu,daurewa kawai take dan kada Su feenah sugane Tanada ciki Acewarta surprising dinsu Zatayi. Bangarensu Yusuf ma komai Cikin natsuwa Suke gudanar dashi duk tare da dr Khalid d Nazeer Suke komai Sai idan mufeeda tabar yazeed Shima yakanzo Ayi dashi. Lokacin da Bikin ya rage Saura kwana3 Alokacin baki Suka Cika gidaje biyun nan, yan yola duk Sunzo, haka yan'uwan mum Suma suncika gidan. Bangaren Su Mamy itama ya'uwanta Dana Abba duk Suncika gidansu. Mufeeda Shirye take inda takashe Uban kudi cewa Za'ayi bikin dababu Wanda yataba irinshi. Gaba daya yan'iskan kawayenta ta gayyacesu dan haka bikin kawai duk Suke jira. su Leemah suma kawayensu duk sun hallara na nesa gidan Kausar Suka sauka Achan zasuyi taron su. Ganin tabbas mufeeda Saita auri yazeed yasa Mamy duk tayi Sanyi, ta tsani ta bude Ido taga mufeeda Cikin gidanta, Saidai bata fasa Cigaba dayimishi addu' ba. Inno ba baka sai kunne Ranar datake ta jira gashi tazo dan haka ita kadai tasan Abinda tashirya ma bikin tsaka! tadai gayyato kwayenta tsofaffin na nesa dana kusa. partyn da yusuf ya Shirya ma yazeed da Nazeer Shi Zaayi gobe dan haka mumy ta dauko ma yaran nata Shahararun Masu Shirya Amare dake Abuja. Jiran goben kawai Suke dan partyn babba ne. Cikin dare feenah tasakama mum Rigima ita dole tanason taga mijin dazata aura. Dan haka mum tashiga ta Sanar da dad. Shima yayi lallashi taki yarda dan haka yakira Abban yazeed ya Sanar dashi. bani feenah din. Mikamata wayar dad yayi ta karba. bangaren Abba Naji yana fadin Kiyi hakuri yata! Mijin Nakine Wani Abu Mai muhimmanci y rikeshi gaba daya yace bazai Samu Zuwa bikin ba dan haka nayanke Shawaran yazeed yazama kamar Shine Musa har agama bikin,tunda Shima yazeed Balaraba Achan Zasuyi komai. toh Abba Ai yazeed yanada Wata Matar tayaya zai wakilci musa? eh Feenah saiyazama Amatsayin keda mufeeda Zai aura!bata iya yima Abba musu dan haka tace Abba yaushe musan Saigama komai Toh? Inno ce ta karbi wayar kinkosa kiganshi kenan?karki damu Ranar da'a kaiki zezo kiganshi kishafa Abinki son Ranki. da Sauri feenah t aje wayar tabar wajen d gudu. Dariya mumy da daddy sukai daman inno ce maganin yaran Nan
💖💋💋💋💖💋💋💖
YAR LESBIAN CE
💖💋💋💖💋💋💋💖
By
Nadeeya mohd Ahmad
(💖Nadseer💋)
dedicated to
Xaynab Ummu mahbub
Page....67
Washe gari yakama Ranar Thursday Ranar dazasuyi partyn da yusuf ya Shirya. Kowa ka gani Cikin farin Ciki yake da Walwala, wasu tun yanzuma Suka fara Shirin Zuwa partyn musamman Kawayen Mufeeda da ita kanta dasukafi Kowa Zakewa. bangaren Su feenah dayake komai tare Suka hada da Leemah gidan Kausar Suke Nasu Shirin inda Hajiyar Kausar ta Samo musu Shaharraun Masu Make-up tun Safe Akafara Shiryasu inda Akafara da Zana musu Hinnah A hannu. duk Cikin taron yan'matan dake gidan Kausar feenah ce kawai Zaka kalla Kasan cewa tabbas Cikin damuwa take. Dr Zainab Nagani bangarenta dafe da kafadar feenah. Magana Naji tana mata dan haka nakarasa na Xauna Dan nesa dasu tayanda Xan jiyo Abinda Suke fadi. feenah bansanki da Karya ba, tun jiya Na lura damuwarki tafi ta kullum dan Allah kifadamun Abinda ke damunki, kigafa taron nan duk danku biyu Aka taru Amma Ace yanda kowa ke farin Ciki ke kadaice damuwa ta bayyana A face dinki. Shiru feenah tadanyi na lokaci Kafin Hawayen datake makalewa Yashiga Xubowa. Nifa feenah ba kuka nasaki kimun ba tambayarki kadai nayi pls kifadamun damuwarki mana. Dr Zainab Nima bansan meke damuna ba, kawai banajin dadi ne kuma gabana Saiya Rinka yawan faduwa. Kuma kina addu' a feenah? Inayi Dr Zainab! Amma feenah duk da Haka kicire wata Damuwa mutane fa Suna lura da irin yanda kike Sukuku. Dr Zainab tayaya Zancire damuwa bayan Mijin dazan Aura ba Sonshi nakeba, Sannan Karin wulakanci kinaji bazai Samu Zuwa bikin ba yana Wani Abun daban, har Akwai Abin farin Cikin dayafi yazo daurin Aurenshi Dan Allah? Bama wannan ba Arasa wanda Za'a hadani dashi wajen party nan Amatsayin mijina Sai yazeed! Wanda Sam bana kwanar Zama waje daya dashi, Ni wlh da dayanda Xanyi kada naje partyn nan danayi, kawai dan banason bata Ran iyayena ne. Hakuri Xakiyi feenah daga yau Saifa gobe ne kadai Zai wakilce mijin Naki, kuma kikarama mijinki Uzuri Maybe Ba karamin Abu yahanashi Xuwa ba. Naji Dr Zainab kokinsan bantaba ganin koda idonshi daya ba? Mamaki Dr Zainab tayi Cikin Ranta take faadin " gaskiya konice Akaima yanda Akaimawa feenah Xan damu, Auren mijin da baka Sani ba Chaff" Afili cewa tayi kiyi hakuri feenah komai yafaru tsarin Ubangiji ne ba tayanda iyayenki Xasu Zaba miki Abinda Zai Cutar dake. Nifa Dr Zainab ba Xabin iyayena bane Zabin kakar Leemah ce Wannan tsohuwar da Bakinta bayada Control. dariya Abun yasoba Dr Zainab gudun kada tayi feenah takara Hasala yasa ta Shanye, Aini idan nice ke feenah bawata damuwa dazan Nuna Haushi zanba inno na nuna inason Auren. Nima Danice haka Zanyi wlh Kausar dake karasowa wajensu ta fada. Tabe baki Feenat tayi dan kunga Baku din bane, ke Kausar da bakida Hakuri da tuni kin tarwatsa taron. dariya Su Kausar Sukayi, Nidai banason kina damuwa pls kibari Agama bikin nan lfy, Ni dama Inno din yazeed ta baki dayafi dan naso Ace Yazeed Shine mijinki. yamutsa fuska feenah tayi Wlh dasun Yabama Aya Zakinta, Dan dana Auri yazeed gara na mutu ba Aure. Murmushi Dr Zainab tayi feenah Rigima bakisan Wanda yadace da Rayuwarki ba.indai yazeed ne yadace da Rayuwata Toh kuwa kune bakusan daidai ba. Shikenan Dr Zainab ta fada inama Mafarkina yazama gaskiya. Magana Kausar Zatama Dr Zainab cewa wani mafarki, Kawai taji bakinta yayi Nauyi, tashi Take Kokarin yi Amai ya kwace mata, kafin ta tashi ta wanke feenah dake kusa da ita dashi, Amai kawai take ba kakkautawa. Dr Zainab da feenah ba karamin Rudewa Sukai ba dan har feenah tafara kuka. Saida Kausar ta Amayar da duk Abinda ke Cikinta tukun feenah ta taimaka mata Xuwa toilet. Saida ta gyarama Kausar jiki Kafin ta gyara Nata jikin, tare Suka dawo bedroom din Kausar inda Dr Zainab take Zaune. Sannu tai mata, dama bakida lfy ne Kausar?? Lfy ta qalau Maman Haneef Kawai Zuwa Aman yayi! Murmushi Dr Zainab tayi Ok bari na duba ki. Noo dakin barshi Maman Hanif. Kausar Akwai Abinda kike boyewa! 😤Ni bawani Abu danake boyewa Dr Zainab. Shikenan idan tayi Wari maji Ai. turo dakin Akayi were ar u my besty? Jin muryan Leemah yasa feenah cewa besty gani Nan. Karasowa tayi, ganinsu Su3 yasa Leemah Shagwabe fuska Shine kuna fira bawanda ya tuna dani. dariya Dr Zainab da Kausar Sukayi yayin da feenah tace kina Raina besty yanzu nayi niyyar kiranki. Saigani koh? Kunsan menene wai kawayen Mufeeda Ashe irin Ankonmu Sukayi. ba dole Suyi ba tunda munki muyi Nasu Kausar ta fada. magana Leemah Xatai Umma tashigo dakin Saiku fito Afara Shiryaku kunsan lokaci na tafiya. Toh Sukace yayin da Suka tashi Suka fita Atare.
Cikin Wasu yan'awanni Akagama Shirya Amaran da duk wanda yagansu Saidai yace Masha Allah. Tsayawa misalta yanda Sukafitoh Sukai Kyau Zai'iya jaaan lokaci dan Haka Nabarma masu karatu Su kwatanta. Karfe8 Na dare jama'a Suka fara tafiya Zuwa babban hold din da yusuf yakama. bayan tafiyar Wasu motoci da kamar Awa1 Akafara iban kawayen Amarya yayinda Aka jera motocin Cikin Kwarewa. Lokaci kadan Nazeer yazo ya dauke Amaryarshi A mota Sukai gaba. Mintuna Kadan tsakani Yusuf yashigo yanama Kausar magana. Madam kutashi muje ko. tare da feenah Xamuje kenan?eh tare Xamu kufito. Jerawa Sukai Suka fita. Kausar Naji dadi da yusuf ne Zai kaimu Wlh. dariya Kausar tayi feenah duk A tsorace kike why? Nima bansan me yasa ba feenah ta fada daidai Sanda Suka karasa Wajen motar yusuf. budema Kausar gaba yayi tashiga yayin da yadawo ya budema feenah. batakawo Komai ba tasaka kai tashiga Cikin natsuwa. ganin tashiga Yusuf beja motar ba yasa Kausar yin magana kana jiran wani Abun ne? Yeah Abokina nake jira! Wake nan? Yazeed! feenah jitayi gabanta Yafadi ba haka taso ba taso Ace tafiyarsu batazo daya ba, Amma yazatayi Mijinta yaja mata. bata Ankara ba taji An bude kofar motar Take bugun da Zuciyarta take yakaru. Sallama yayi cikin Sanyin muryarshi yashiga, kasa Amsawa tayi Sai yusuf ne ya Amsa. Yana Xama Mufeeda dake bayanshi itama tashigo. yamutsa fuska feenah tayi Cikin Ranta tace garama dayazo da matarshi. Shigowa mufeeda tayi tana yamutsa fuska Honey kadawo Nan Nakoma tsakiya mana. da Sauri Yusuf yaja motar yana fadin Zaman ma yayi Ahaka. dan tsaki mufeeda taja yayin data kara matso yazeed Sosai. Shiru yayi becemata komai ba danshi tun lokacin dayashigo yaga Feenah ya fita Hayyacinshi,duk dacewa babu Wani haske Cikin motar bekasa misalta irin kyan da feenah tayi ba, bangare guda kamshinta duk ya cikashi Ji yake inama matarshi ce feenah da babu Abinda Zai hana ya Rungumeta Ayanzu. Kasa daurewa yayi So yake yaji muryarta ko yasamu Sauki, feenah inayini ya taro???? Jin muryarshi kawai tayi Asama hakan Saida yadan daburta ta Cikin Sanyin murya tace lfy. taro Alhmdllh. Ashe mijinki bazai Samu Zuwaba koh? da Sauri mufeeda data kufula tace Honey babu Ruwanka da damuwarta, Nasan dalilin Rashin Xuwan mijinta kawai dama Sotake ka wakilci Shi Shiyasa tahanashi Xuwa, Toh komadai me mutum zeyi Mijina yafi karfinshi Dan daga Sanda Aka gama bikin Nan bama kara ganinshi Za'ai ba. Allah Sarki yar wahala feenah ta fada Azuciyarta. Afili yitayi kamar bataji ba, Haka Kawai taji tanason biyema yazeed Suyi fira kodan tarinka sauraran Haukan mufeeda. Wlh kuwa bro Yazeed yana dan Wasu Abubuwane yasa bazai Samu Zuwa ba, Hope bamu takuraka ba? Lumshe ido yazeed yayi yana Sauraran yanda take magana kamar Mai Rera waka. Nop ba takura sweet Sister kisaki jikinki Xanyi Komai Kamar nine Shi. eh Amma daga Sanda Aka gama bikin Zaka rabu da ita ko? Kaga maganar yin komai ta kare mufeeda ta fada Cikin fushi. dariya Kausar da yusuf Suke kasa kasa Sunsan Cewa feenah da biyu ta biyema yazeed. Alright Sweet brother ai dan bancika Son ka gajiyar da kanka ba. WOW😍😍 yazeed yafada Cikin Ranshi Ashe tana tausayamun, gaskiya ba'ama Zuciyata Adalci ba. Sorry Karki damu dear. mutum dai yaji dashi kauyen yola ne dole yaje, mijin da bedamu da kaiba wai biki guda yace Uzuri, dama Chan dai bayaso aka manna mishi! tabbas Feenah taji Haushin maganar Mufeeda Cikin Ranta Amma yazatayi Gaskiya ai mufeeda ta fada da yanasonta dazaizo. Afili Cewa tayi Sweet bro Ina Auntyn tawane banganta ba?? Murmushi yazeed yayi ya nuna nata Mufeeda gata. dan tsaki feenah taja wannan kayan wanki ne Antyna balaraba Nake fada wadda Xata iya kulamun da brother ta Hanyar son gaskiya da..... kara wayarta tayi yasa takasa karasawa, dubawa tayi text din Kausar ne yashigo kamar haka. "feenah kishareta pls batada hankali yanzu saita nema kuyi fada Cikin mutane, kuma Kinga yanxu ke Matar Aurece" Amsa feenah ta mayar ma Kausar Kamar haka." bana tsoranta Kausar idan da tasan yanda Naji haushin Xama waje daya da mijinta dabatace dani Haka ba, gara na Nuna Mata nima ba kanwar lasa bace, kuma Ni Abinda yasa Nake biye mishi ba'ariga Andaura Aurena bane" Sakon Na tafiya Kausar ta kara turo mata da Alamar kuka😭😭 I know feenah but duk da haka Shareta pls. O.k. feenah ta turama Kausar dashi. Mufeeda dake A kufule kwantowa tayi jikin yazeed Honey Sabida inasonka kana sona Nayima Wasu fintinkau shine Akejin haushina. Shafa kanta kawai yazeed yayi yana Murmushi. Honey kajama yarinyar Nan kunne Akaina. Wace ce Mufeeda? gata nan feenah take kowace. Murmushi yazeed yayi feenah bata tsokaneki ba Mufeeda feenah bata jaaan fada. batai mamaki ba domin bokanta yacemata yazeed yafison feenah fiye da Kowa badan boka yace kada ta takurama yazeed ba datasan yanda tayi ta Rabashi da feenah, Amma bawani damuwa daga gobe ne kawai. gobe iyanzu ina dakinka honey.murmushi yazeed yayi daidai Sanda Suka karasa kofar get din Hold din. yusuf na tsayar da Motar feenah ta bude Xata fita. yazeed naganin Haka besan Sanda yajawo hand dinta ba. Baby Kinmance yau Amatsayin mijinki Nake? marairaice face tayi Namance fito koh. gira yadaga mata Ok. Amma yazeed baby fa kace mata, barta Mana tafara Shiga Ai Hakan ne daidai. kidaina damuwa da irin Wannan Abun mufeeda. Kwafa tayi tafita ta bangarenta, Suma Suka fita. Leemah dake waje tana ganinsu ta tawo Tana Sambatu Cikin Ranta" Oh my God Ji besty da bro Yazeed yanda Sukayi Kamar Shine mijin" besty mekike tunani kike kokarin shigewa jikina? dariya leemah tayi Kinga yanda kikai Kyau kuwa besty! Uhum kema ai kinyi Leemah. Karasowa wasu mata Sukayi Su biyu Inda Sukaja hannun Amaren Wucewa Zasuyi wata Kawar mufeeda tace ga dayar amaryafa. Oho wata ta fada tace mufeeda ta biyota. yanda Akashirya Wajen partyn baya faduwa lokacin da Amare Suka Shiga kowa yaba kyan dasukai yake, kida Akasaki mai Sanyin dadi dan haka kawayen Amaren da Rawa Suka Shiga har Sanda Suka karasa Suka Xauna. Atsakiyan feenah da mufeeda yazeed ya Xauna Sai bangare guda Leemah da Nazeer Zaune inda gabansu Kausar da yusuf ne. Cikin natsuwa da tsari Ake gudanar da Komai. daya bayan daya Aka rinka kiran Abokan Angwaye da kawayen Amare Zuwa iyayen Amare da Sauran Abokan Arziki Suna taka Rawa da Nuna farin Cikin dasuka shiga Awannan Rana, dayawa daga Ciki fadi Suke Saima gobe. Lokacin da Aka kira inno babu Wanda be dara ba hatta yazeed dakejin kanshi kamar ya tarwatse yakuma Rasa dalilin Hakan. dukda damuwar da feenah tayi Kan Rashin Xuwan da mijinta beyiba Hakan be Hanata beyema yazeed kan yanda yake janta da Surutuba.badan komai ba Saidan ta kular da mufeeda. Haka Akarinka gudanar da Komai Cikin Natsuwa. Karshe Amare da Angwaye Aka kira inda Suka taka ba karamin kudi Akarinka watsa musu ba kuwa. tunkan Atashi wajen partyn Mufeeda taja yazeed Sukabar wajen Acewarta Ansaka mishi ido, Cikin Ranta kuwa yanda duk ya maida hankalinshi kan feenah ke bata haushi, musamman dataga Masu Camera Su feenah kadai suke dauka. Koda Akatashi mutane da yawa Suka rinka neman yazeed Saidai Ace yatafi. yusuf ne yadauke su feenah dan komawa tafiyar yanzu hartafi ma Feenah dadi. Saida Kowa ya watse Su Mamy Suma Suka fito. yazeed ta hango Shida mufeeda Suna niyar Shiga wata mota dan haka takarasa Wajen, Ko Amsa gaisuwar da mufeeda kemata batai ba tace my Son yau bakasha magani ba. Kafin mufeeda tagama tunanin maganin me taji yazeed na magana. Haba Mamy yau dinma Saina Sha? Kwarai kuwa yazeed kazo mutafi tare dakasha Saika kwanta. Mamy Dan Allah kibar maganin nan yau banajin dadi. Hakanan Xaka daure dan Albarka. muje Toh Mamy. Haba Honey waye Xai maidani?? dafe kai yayi Hakane mamy Xankai mufeeda gida. dan tsaki mamy tajaa taciro magani ajakarta. Ansa kasha karka dade daka kaita kajuyo. Amsa yayi yasha ya amsa d toh mamy. Wucewa Mamy tayi tana kara tsanar Mufeeda Cikin Ranta. Motar Suka Shiga yazeed yaja Suka bar wajen
💖💋💋💋💖💋💋💖
YAR LESBIAN CE
💖💋💋💖💋💋💋💖
By
Nadeeya mohd Ahmad
(💖Nadseer💋)
dedicated to
Xaynab Ummu mahbub
Page....68/70
Cikin Natsuwa yazeed yake driving dinsu,yayin da mufeeda keta Xuba mishi Surutu d Korafi kan yanda yakema feenah Ayau. Murmushi kawai yakeyi,Sai Uhum dayake Cewa. Ganin yasha kwanar gidansu yasa Mufeeda Sakin Wani Murmushi wanda ita kadai Tasan ma'anarshi. parking yayi daidai kofar gidan Su Mufeeda kallonta yayi yadaga mata gira yana mata Alamar ta Sauka. Marairaice face tayi Honey Ina tsoron Sauka dare ne fa pls kafito idan Nashiga gida Saika tafi. ba musu yazeed yafito daga motar yaja hand dinta Xuwa kofar gidan. Murda door din yayi yaji Arufe kallonta yayi bemata magana ba. Eh Honey inaganin Sunyi bacci ne. Cikin Muryan gajiya yazeed yace bakida key ne? I have; let me Check my back Allah yasa ban yardashi ba. Laluben jakarta tafarayi Shidai yazeed kallonta kawai yake. Oh my God wlh Honey banga key din ba! Ki kira friends dinki Su bude mana. Good idea Mufeeda ta fada taciro phone dinta gefe takoma Cikin Ranta tana fadin babu wanda Zan kira Saidai Kasan yanda Xakai dani. Mintuna kadan tayi ta dawo kusa dashi Honey duk wayoyinsu Akashe maybe bacci Suke,Ni yanxu yazanyi Kenan Mufeeda ta karashe maganar tana Hawayen gulma😢 Ko Zaki gidanmu ne??, ido Mufeeda ta Zaro😲 No Honey Ga Mafita kaini hotel na kwana inyaso da Safe Saina Saka Seemah tazo ta daukeni. Alright yazeed yafada ya juya Xuwa Motar Shi, Bin bayanshi Mufeeda tayi tana kwafa. daidai Hamdala Hotel yazeed yayi parking Motarshi kusan tare Suka fito Suka nufa Cikin Hotel din, Saida ya biya kudi yayi komai Kafin ya Amshi key. mikama Mufeeda yayi Room7 Sukace, kitashi da Wuri kafin Anemiki Ki koma bye. Shan gabanshi Mufeeda tayi Waite yazeed kana Nufin....d Sauri ta mayar da face dinta Xuwa Na tausayi pls Rakani Room din dan Allah. Jan Hannuta yayi yanufa Sama da ita inda Anan Room din yake,yana Xuwa ya karbi Key din hannunta ya bude bakin bed ya Xauna. Ki kwanta bari na tafi kinsan Mamy tace na koma da Wuri. Ok honey b damuwa Saida Safe. Tashi yayi Yanufa kofa....Oh Honey Namance! dame fa? Yazeed ya tambayeta. da Ruwan Nan Zo kaga. dawowa yayi ya Xauna, kusa dashi ta dawo lokacin data Ciro wata Robar Ruwa Cikin jakarta. dafe kai yazeed yayi Naxata Wani Abun ne ma but dan Ruwa kibari idan naje gida Xansha. pls Honey kasha duk yau baka wani Sha Ruwa Sosai ba. karba yayi yakafa kai yashanye tas, tashi yake Sonyi wayarshi tafara Kara. dagawa yayi Hello Mamy! daga dayan bangaren Mamy tafara mgn yazeed ban'isa dakai bako? Cewa Nayi kana kaita kadawo Shine kaje ka Xauna,kasan kana da baki a part dinka,Yusuf nason tafiya babu mai kula dasu yayi Kyau. Mamy kiyi hakuri Mufeeda na rako hotel. Hotel kuma?! Eh Mamy gidansu A Rufe yake. maza kataso Ka tawo yazeed tunda ka kaita ina jiranka. Cikin wata irin murya yadawo yin mgn Toh Mamy yanxu Xan dawo. Yazeed Meke damunka ko bacci kakeji Azo Adauke ka? Shiru yayi bece komai ba Saima katse wayar d yayi. ganin haka yasa Mufeeda tashi tayi kofa honey tashi ka tafi Mamy nason ganinka koh. yamutsa fuska yazeed yayi ya kwanta kan bed din. Murmushi mufeeda tayi tasama kofar key. Rage kayan jikinta tayi ta hau kan bed din yayinda data matsa kusa d yazeed.honey Kasan Mamy Xatayi fishi nidai katafi. yanayin yanda tayi maganar da kamshin turarenta dayake Shiga hancin yazeed Shi yakara saukar mishi d Kasala, Janyota yazeed yayi da Karfi yashiga Wasa da dukkan illahirin jikinta. Ganin haka yasa Mufeeda jawo wayar yazeed daketa faman Ruri takashe gaba daya, Martani tafara mayar ma yazeed Azafafe Lokaci guda duk Suka Rikice gaba daya Sukafita hayyacinsu ganin Haka yasa Nafita Naja dakin ina me kara tsanar Masu halaye irin Na Mufeeda. bayan Wasu Awanni Nakoma dan ganin maike faruwa. Mufeeda nagani tana girgiza Yazeed Honey pls katashi karka Mutu gobe ne Zai kasance Ranar Cikar burina Dan Allah katashi. Cikin Ranta ta dawo yin magana meyasa na tilastama yazeed kan dole yashige ni???? Nashiga3 kardai faduwan Nan da yazeed yayi yasa Asamu matsala!!!! Wayarta taciro tashiga kiran Seemah,tana dagawa Mufeeda tafara magana, Seemah nashiga3 Wlh. daga dayan bangaren Akace Lfy? Dame? Seemah yazeed Nasa yakawoni Hotel muna Xuwa Nasamishi maganin Nan dana dauka wajenki, Nan da nan feelings yatasan mishi Mukafara harka, Saida yaga ina bukatar yashigeni tukun yatashi, Shine Narinka mai Naci Saiya Shigeni Shikuma yana Aa Zunubi Xamu'aikata, dana nace d yawa gani kawai nayi ya Rike kanshi daga baya Yafadi Kasa😭😭Seemah yazanyi kar Aje Asamu matsala fa. tsaki Seemah tayi bafa wata matsala Mufeeda inaganin Shima yana bukatar Abun ne tsoron Allah yazo mishi, Kawai yanzu ki kira ma'aikatan hotel din sutaimaka miki Akaishi Asibiti. Allah Ko Seemah? Toh Xama Xakiyi kitasashi Agaba kina kallo? Aa bari Nakira Ataimakamun. Kashe wayar mufeeda tayi ta fita. Ba'adau lokaciba ta dawo tare da ma'aikata guda2 Na hotel din. Asibiti mafi kusa Xaku taimakamun na kaishe. Hajiya dole Xamu kira police gudun matsala. Kai nifa bawani Abu nayimai ba mijina ne temako Zakumun Zuwa kasa. Jin Cewa mijintane yasa Ma'aikatan daukan yazeed Suka Sauka kasa dashi motar dasukafito tasa Akasashi Abaya yayin da tashiga tafara tuki. Asibiti mafi kusa tayi dashi, Kasancewar dare ne babu wasu mutane A Asibitin yasa Aka karbesu da wuri. Awaje Suka tsayar da mufeeda Suka Shiga dashi ciki inda likitoci biyu Suka dukufa kanshi.
Mamy tunda tayita kiran yazeed tanajin wayar Akashe Hankalinta yakara tashi, gaba daya takasa Natsuwa gashi ba Abun tayi magana Cikin taron mutane yan biki ba. dakinta takoma tana tunani barkatai Cikin Ranta. Kar mufeeda ta Cutar mun da yaro Tunanin da mamy keyi kenan Cikin haka Leemah tashigo ta Sameta. Mamy! Mamy! Saida takirata Sau3 Kafin Mamy ta dago. Mamy bakida lfy ne? Lfy ta qalau Leemah me yakawoki gida Cikin dare? Mamy Wajen bro Yazeed nazo banganshi ba! Wani Abun Zai miki halan. Mamy kawai Son ganinshi Naji inayi. baya Nan Ai yakamata Ki kwanta dare yayi Sosai. toh Leemah ta fada tahau kan bed din mamy ta kwanta. Cigaba mamy tayi da tunaninta daga bisani ta yanke Shawaran kiran mumyn feenah ta fada Mata. bangaren Mufeeda ganin Har karfe4n dare yayi yazeed be tashiba yasa tafara fargaba Cikin Ranta. Excuse ta nema wajen Nursing din Suka barta tashiga. Inda yake ta nufa ganinshi kwance kamar gawa yasa takara daburcewa, dafa kanshi tayi dan Allah yazeed katashi Wlh baxan kara tilasta maka Kan wani Abun ba, pls katashi bansan me Xanfadama Duniya idan ka mutu a hannu na ba. Wayyo meyasa Nayi Haka ne? Baiwar Allah kiyi hakuri mijinki Zai tashi amma yanzu Ana bukatar yasamu Hutu wata nursing tafada. Amma dan Allah zaitashi kuwa? da izinin Allah kuwa. Ajiyar Zuciya mufeeda tayi yayin data jingina jikin kafadarshi bacci mai Nauyi ya dauketa. "HELLO" Fatima Naga kiranki Cikin dare bacci Nayi,ya hidima?? Hidima Alhmdllh Hafsat, Tun jiya ban Samu nayi bacci ba, tun daga wajen party jiya da Mufeeda ta dauki yazeed haryanzu bata dawo dashi ba! Ajiya da dare nakirashi munyi mgn daga bisani yakashe wayar tun Alokacin nacigaba da kira wayanshi Akashe Shine hankalina yatashi Sosai. Subhanallah. Toh ko Katsina ya wuce wajen balaraba? banajin haka Hafsa danjiya hotel yacemun yakai Mufeeda daga baya muryarshi takoma tamai bacci gaskiya ni inazaton Akwai wani Abun,kigafa yanzu karfe6 na safe, karfe10 Xa'a daura mishi Aure idan Abbanshi yafara nemanshi bansan me Zan fada mishi ba. Gaskiya ne da matsala Sosai Bari nakara trying number din tashi,idan batashiga ba Sai nazo Asamu Mafita,Saidai Kada kidaga hankali Har mutane Su gane. Shikenan Hafsa saikinzo din.
Misalin karfe7 Wani dacter yashiga dakin da yazeed yake, tashin Mufeeda dake bacci yayi Munason muduba jikinshi. Tashi Mufeeda tayi tunowa datayi ainda Suke. Dr tun jiya be tashi ba Wlh. Karki damu mun hadamishi da maganin bacci ne Zuwa wani lokaci Zai tashi insha Allah dan kamar yanada damuwa ne, yanzu inason Naga mahaifinshi ko dan'uwanshi na miji. tunani Mufeeda ta tsayayi Yes tafada lokacin data ciro wayar yazeed ta kunnah. Kamar jira Ake nan da nan Messages Suka rinka Shigowa,ga yawan kiran da mutane Sukai mishi.Kafin tayi yunkurin Shiga wani wajen kiran yusuf yashigo wayar. dagawa tayi batai magana ba. Haba yazeed Kasan katara mutane ya Zakayi tafiyarka tun jiya Nake kiranka waya Akashe why? toh Sarkin jaraba ba yazeed din bane. dallah malama ina kika kaishi? Kamin Ahankali Wlh Yusuf ni ba tsararka bace. Mtrwww Mahaukaciya Ina yazeed na tambayeki? kaima mtsww yazeed bashida lfy nakawoshi Asibiti. What? yusuf ya fada da karfi. Idan Xakazo ne kazo Minal hospital kusa da Hamdala Hotel daga haka mufeeda ta kashe wayar.
yusuf be tsaya yima kowa bayani ba yanufa Minal hospital Cikin gudu yake tuka motar Dan haka cikin mintuna kalilan yakarasa Asibitin. Besha wuyar kai kanshi dakin da yazeed yake ba, Shiga yayi ya hangoshi kwance yayinda Mufeeda Na gefe tana chating Awayarta.karasawa yayi da Sauri wajen yazeed daidai Sanda doctor yashigo. Dr yusuf kaine da kanka? Dr Amin dama Nan ne hospital dinka? Wlh kuwa Ashe patient din dan'uwanka ne? Yes yazeed din danake fada Maka ne. badai angon daza'ayi Aurenshi yau ba? Shine Wlh Amin. Oh God wannan itace matar dazai Aura? tabe Baki yusuf yayi eh Su2 ne ma. Ok dr Amin ya fada yayin da yakara duba jikin yazeed. Namishi Allura ne Maybe koyanxu kaga yatashi. Allah yasa Hakan yusuf yafada yayinda yaciro wayarshi.Mamy yakira yasanarmawa komai,tare da Asibitn dasuke. tashi mufeeda tayi ta kalli yusuf ni bari Naje gida nashirya tunda Ance Zai tashi Kasan bayan daurin Aure Akwai partyn dana Shirya Xa'ayi. Ko kallonta yusuf beyiba bare yabata Amsa ganin haka yasa Mufeeda tafita. Bayan tafiyar ta ba dadewa mamy da mumy Suka karaso tare da inno. ganin yazeed Ahaka yasa mamy kara damuwa Sosai. . Karfe tara daidai Abban yazeed ya kira wayar yazeed, yusuf ne yadaga yasa a hands-free Abba ne yafara fada tayaya kowa yashirya tafiya bakai ba yusuf kasani Mata biyu Za'a daura maka Aure dasu bare Kace bazaka Zoba. Cikin Sanyi yusuf yafara magana kayi hakuri Abba yanzu Zamu karaso Wanka yazeed din yake. Kashe wayar Abba yayi yana kwafa. daidai Nan yazeed yafara motse da hannunshi inno ce ta lura dan haka d sauri takarasa bakin gadon ganin haka Suma duk Suka karasa. Ruwan magaryan dake hannun inno mumy takarba tafara Shafamishi hade da tofa mishi addu'a Salati Yayi da karfi lokaci guda ya bude ido yana karanto addu'oeh. Sannu kawai sukemishi harzuwa lokacin dayayi Shiru. Kallonsu yadawoyi daya bayan daya daga bisani yafara mgn. Mamy inane nan? Shafa kanshi Mamy tayi hade d kwallah Asivitine yazeed Matarka ta kawoka. Matata yazeed ya maimaita Cikin Ranshi. Afili Cewa yayi mamy yaushe Nayi Aure kuma? magana mamy Zatai wayarta tayi Kara ganin Abba ne yasa tasa a hands-free fatima duk inda yazeed yake kituroshi tayaya zaimaidani karamin yaro tara da rabi Ace baya wajen daurin aurenshi Kuma yasan mata2 Zai Aura! Kayi Hakuri Abban leemah bari nakirashi. Kigayamai idan bezoba karfe10 daidai za'adaura Auren baza'a tsaya jiranshi ba. Yanzu Zan Sanar dashi zaizo. Kashe wayar mamy tayi gudun kada yakara wata maganar.yazeed da kanshi Ya kulle kasa Shiru yayi, mamy wani yazeed ne Zai Auri mata biyu Ayau?? Da mamaki Suke kallonshi duka. Inno ce tayi magana kingani ko Fatima nagayamiki duk abinda yazeed yake Aikin Asiri ne. Juyawa kan yazeed tayi kaine Nan mijiin balaraba da Mufeeda. Mufeeda Kuma inno! Bayan balaraba din dakikasa Abba ya auramun harda wata mufeeda kuma yanxu? Sakarai kaidin mace kashiga Har na tsawon watanni, Mufeeda kafura kaine kace dole Sai'an dauramaka Aure da ita, Sakacin addu'a yasa tamaka Asiri barikaji.kwashe duk irin Abinda yazeed kema Mufeeda Abaya inno tayi tafada mishi. Tashi yayi daga kwancen dayake yashiga rokon Mamy kan tasa adakatar da aurenshi da Mufeeda Shi bece yanasonta ba. Duk murna Suka Shiga yi Nan da Nan Mamy tashiga kiran Abba Saidai kash baya daga wayar har kusan kira10 tamishi. Ganin haka mumyn feenah tacema yusuf Maza kaje Yusuf kasanar kafin a daura. Kafin nakarasa mumy andaura kallifa10 yanxu. Kaje insha Allah Za'a dace. Fita Yusuf yayi yashiga Motarshi inda yajata d gudun gaske. Nima bin yusuf nayi Abaya dan jin Sadaki Nawa Akabayar😄 Lokacin damuka karasa jinayi Ana Abisa Sadaki naira dubu 60 lakadan ba Ajalan ba. dagani har yusuf jikinmu yayi Sanyi Afili yusuf yace Shikenan andaura. Karasawa yayi wajen Nazeer andaura koh? Yashe baki Nazeer yayi yeah Andaura Nawa akafara Sannan yanzu Akai daya na yazeed. da Sauri yusuf yace wace Matarshi ta farko? balarabace Nazir yaba Yusuf Amsa. (😭😭😭Nidai naso Naji Sunan balaraba na gaskiya. kufa??) Alhmdullah Yusuf yafada yakarasa inda Abba yake recording din maganar yazeed dayayi y kunnah ma Abba. Tabbas Nasan yazeed ba'a hankalinshi yayi Abunda yamun ba. Tashi Abba yayi dasauri yana fadin Adagata kada adaura dayan Auren
💖💋💋💋💖💋💋💖
YAR LESBIAN CE
💖💋💋💖💋💋💋💖
By
Nadeeya mohd Ahmad
(💖Nadseer💋)
dedicated to
Xaynab Ummu mahbub
Page...71/73
babu wanda yayi yunkurin tambayar Abba meyasa yace Adakatar da daurin Auren ba Kuma Shima beyi ma kowa bayani ba Har Akagama gudanar da walimar bayan daurin Aure. Iyayen Mufeeda Ganin dasukai mutane Na tafiya kuma ba'Ayi maganar daurin Auren yarsuba yasa Suka tunkaro Abba danjin ba'asi. Alhji Ahmad yazakace Adagakata da daurin Auren yazeed da Mufeeda Sannan bawani bayani mutane harsun fara tafiya. Hakane Alhaji Rabi'u Naso mubar Zancen dagani Sai Kai Amma tunda kanason jin ba'asi Bari Namaka bayani. Yarka Mufeeda idan ka kasance kabata tarbiyya toh Lallai baka lura da yanda take gudanar da Rayuwarta. kaje katambaya duk wanda kakeso yarka karuwace Cikakka, bayan Haka batada tarbiyya,batada kunya,batada imani bare tausayi.... ✋dakata Alhji Rabi'u danka Shi yasa Aka nemomu domin Son yarmu dayake duk da Chan bakusan da wa'innan Halayen ba Saiyanzu dakake Son tozartar damu Cikin dinbin jama'a??? Idan Kai kana takama da Rashin Mutumci Wlh nafika baka'isa Ka wulakantani Cikin mutane ba! Me yasaka tun Kafin muxo nan baka gane danka beyi dacen mace ba Sai yanzu? Murmushi Abba yayi dagakata Alhji Rabi'u Ni ban dakatar da daurin Auren yarka da Dana dan tuzarta ba, Nayine domin kare Dana daga Sharrin yarka, duk da Kace meyasa bansan yarka karuwa bace tun farko, ba Haka Abin yake ba Nasani. kaddarace tasa Dana ya Amince Zai Auri yarka Amma falillahil Hamdu dama Allah ba Azzalumin bawa bane Saidai bawa ya Zalunci kanshi,kuma dama hausawa Sunci Rana bata Karya. Yau Allah ya Sawwakema Dana Kaddarar data Afka mishi. Yarka taso Cutar da yarona ta mishi Asiri dan wata manufarta ta daban. ..... Dan Allah Alhji Ahmad kadakata da Zancen banzar dakake Wannan Ai Shirmene tayaya yata Tasan Asiri bare tasan wajen boka? Zaka iya tambayarta Amma Ni yanzu mataki Zan dauka Akan Abinda yarka tama yarona Na tsawon Watanni! daya daga Cikin Wadanda Suke tare da Mahaifin Mufeeda ne yaja mahaifin Mufeeda dan gefe, magana Sukayi natsawon Mintuna daga bisani Suka dawo. Toh Toh toh Hakane mufeeda bata kyauta ba Alhaji Ahmad Kasan ba'a yabon dan yau,Ayi hakuri komai ya wuce Allah kawoma Mufeeda wani mijin, maganar daukan mataki abarta du Allah. dad din Feenah dake tsaye gefe ne yayi magana Akaron farko. maganar Shigar da kara baza'a janyeba Alhji Rabi'u dan ko Ahmad be Shigar ba ni Zan Shigar da kaina, Sabida yarku taso halaka yazeed dan duk wanda Akaimawa Asiri Anso halaka shine. farar daya Mahaifin Mudeeda tare da tawargashi Su4 Sukafara jaaan ido. Ganin da gaske Abban yazeed kotu Zai makasu yasa daya daga Cikinsu yafara magana. Alhaji. Kayi Hakuri idan Shigar da kara Zakai kashigar da Mufeeda din tunda Itace tayi laifi. Amma kune Mahaifanta ai dad din feenah ya tambaya. da Sauri Alhji Rabi'u yace Wlh Allah mu ba Iyayenta bane kudi tabamu masu yawa tace Muzo Ayi komai Amatsayin Iyayenta! Kallon kallo mutanen wajen Sukafarayi dad kasa Magana ma yayi, Abba ne yayi karfin Halin cewa Xaku iya tafiya. da Sauri kuwa Suka nufa motarsu Har Rige rigen barin wajen Suke. Nan dad da Abba Suka kara Hamdala da Abin ya wargatse Kafin daurin Auren. daga bisani mota Suka hau dan Zuwa duba yazeed din. Yusuf nagani tare da Nazeer gefe Suna magana. Nifa daman Nazir nadade ina Mamakin Yazeed kuma Nasan duk Abinshi daman bazai kawo Mufeeda Matsayin Matar Aure da gangan ba. Hakane Yusuf Nima Nadade Ina mamakin Halin dayashiga Gaskiya. Amma Yusuf Na lura kamar yakamu da Son Sister dinta koh? Tuni ma Nake fadamaka yazeed ya Mutu Akanta, Saidai kaga burinshi be Cika na Aurenta ba, Amma Alhmdllh tunda yarabu da Kaya. Gaskiya kam Ai itama Sister din tawa mijin data Aura Ashe Sunanshi yazeed Shima. Kallon mamaki yusuf yama Nazeer Ah haba Haka kaji Andaura Auren Kodai kanata Zumudi bakaji da Kyau ba??? Nidai kamar Haka kunne na ya jiye mun. garadai da Kace kama Amma banajin kafahimta yanda Aka daura Auren. gira Nazeer yadaga Sama Muje Asibitin Koh. Ok yusuf yafada yayin da yakarasa Suka Shiga Mota. Nazeer wai ita balaraba din yasunanta na gaskiya, ko da Sunan balaraba din Aka daura Auren. Kai haba dai Nafisat Sunanta. Yusuf bekawo komaiba yace Sunanta mai dade Ake kiranta balaraba. Gaskiya kam irin Sunan Sister dina gareta. Ido yusuf ya fiddo Waje tunowa da Sunan feenah Nafisa dayayi. Kafin yakarasa tunaninshi Sun karasa bakin Asibitin. Dan haka besamu damar tambayan Nazir dayakeson yiba. Sauka Sukayi daidai lokacin da Mufeeda ke Shirin Shiga Ciki itama. da Sauri yusuf yasha gabanta Amarya Sai ina kuma? Yatsina face tayi tana Shan kamshi wajen mijina Xani mana. dariya yusuf yayi Cikin Ranshi Afili Cewa yayi Lallai Gara da yazeed ya Sanar dani Ashe. Me kake fada yusuf?? kina tafiya yazeed yatashi Ashe bama wani Abu ke damunshi ba Rashin bacci ne,dan haka yana tashi Aka Sallamemu Yanzu haka yana gida yana Shiri, Shinema ya aikoni nan yanata kiran wayarki bata Shiga shine yace Nazo nafada miki kishirya da wuri 4:00 daidai Xa'a tafi wajen partyn Nan. Yashe Baki Mufeeda tayi Andaura Auren kenan? Eh mana tun yaushe Mufeeda Amaryar yazeed. Murmushi tayi bari Naje mufara Shiri Nida kawayena. Alright Saimun hadu koh. Juyawa tayi tabar wajen yayinda Yusuf yashiga Ciki. Karo yaci da Nazeer daketa faman dariya yusuf bakada Kyau. dariya yusuf yayi barta ai saita garu tukun. Karasawa Sukai dakin da Yazeed yake Nan Suka tarar dasu Abba yazeed kuwa kamar bashi bane mai ciwo Kara tattaunawa Sukai Kan maganar karshe Dr ya Sallamesu ganin yazeed din yasamu lfy. Fita Sukai gaba daya Aka dunguma gida dan cigaba da hidimar biki.
Amare da basusan ma me'Ake ba Shirunsu kawai Suke Suna nishadi.Dan yanzu gaba daya feenah tacire damuwar Wani dan yola dazata Aura tabar ma Allah Acewarta meyuwa Shine Alkairi Atare da ita,dan Haka bataga Amfanin yawan damuwa ba. Dr Zaynab ce ta katse firar da Kawayen Amaren keyi. Alhmdllh dai Leemah Anzama Matar Nazeer yau baki baya Rufuwa. dariya Leemah tayi Ai Anacemun Andaura Naji gaba daya banida wata matsala. dariya duk dakin Sukayi. feenah yasunan mijin Naki ne wai? Tabe baki feenah tayi Oho ina Nasani. mtsww wata kawar Su feena taja tsaki Sunan mijin ma Sai Anmana Rowa. da Sauri wata daga Cikin kawayen tace Nifa dazanzo gidan nan naji Anacewa Sunan mijinta yazeed harwasu mutane nacewa takwaran brother din Leemah. ido feenah ta fiddo waje Kafin tayi Magana Leemah tariga. Wooow besty Sunan mijinki me dadi kinga bakyason bro dina Amma Allah yabaki mai irin Sunansa. tabe Baki feenah tayi bahaka Naso ba Wlh Najima Nakara tsanar Auren Nan Sabida Sunan nan. dariya wasu daga Cikin kawayen Sukai kyadaiji dashi Sunan Akwai Dadi Wlh. da Sauri Dr Zainab tace Ashe da Rabon Zancigaba da kiranki Feenar yazeed. Kara tsuke fuska feenah tayi ni banaso Sunan nan. Sallaman inno ce ta katsesu Ayeririri ina Amaryar yazeed da Amaryar Nazeer. Kausar ce tayi Saurin cewa kingansu Nan inno. Toh Nafisatu dai Anki jikana tsaka gashinan kin kara Samo mai Sunanshi. tsaki Feenah taja toh Miye yashafeki? da farko hardacewa Sunanshi Musa! hehehe yashafeni mana tunda nice na hada dole Nayi magana, kuma manta Sunan yaron Nayi da farko. Ai Saikiyita tayi feenah taba inno Amsa. kyadaiji dashi yar'uwar tsaka kawai. Halimatu jikata. Na'am inno ta, kinshigo kinata damun besty dita.kinci gidanku kinfi sonta Akaina kenan? Wace ni inno kawai banason Kina damunta ne. dama Albishir nazo fada miki tunda bakyaso bari Nafita. Inno yi hakuri fadamun dan Allah. Kafuradai Asirinta ya tonu, yau Asirin datamawa tsaka ya karye yace kada Asake adaura mishi Aure da ita Saida balaraba kadai, kuma yanzu Angama komai bata sani ba dan haka kada kufada mata idan kunga tana hauka kubarta tayi tagama. Wani irin Tsallen murna Leemah tayi kwarai Addu'ata ta karbu Alhmdllh. Alhmdllh duk Sauran yan wajen Suka fada Dan babu wacce bata tsani Mufeeda Awajen ba. juyawa inno tayi Xata fita Nafisatu bakice komai ba. ✋kinga ni beshafeni ba kirabu dani inno. Kwaikwayon yanda feenah tayi Magana inno tayi dan Allah Kawayen Amare dani da feenah wayafi wani Kyau. dariya duk Sukayi inno wazai hada kinfita Kyau Sosai. Jujjuyawa inno takarayi tabar dakin dariya duk Suka Saka Hakan ba karamin batama feenah Rai yayi ba. Cikin fishi tafara magana badai tashigo tafita haka nan batai maganar Wani ba, ko waye yafadamata Mufeeda Asiri tama yazeed Oho? Mamy ce tashigo tare damasu Make-up gaisheta duk Sukayi. Gashinan Xa'a fara Shiryaku Zuwa 4 Xa'atafi party dan haka karku batamana lokaci. Toh Sukace Mamy tafita yayinda masu make-up din Sukafara yima yanmatan. Haka Amare suma Anware musu Wa'inda Xasu Shiryasu. Awa3 Aka bata wajen Shirya Amare tundaga kan makeup Xuwa dress idan ka kalla Zakasan ba karamin kudi aka Kashe ba. Ni kaina Nayi Mamakin Chanzawar Amaren Cikin kankanin lokaci. Abinka da fararen fata ga Kyau kuma Ankara da kwalliya da Ado. farin gown duk Suka Saka yayin da dan kune Sarka Xuwa Abin hannu duk na daham ne kai yanda ma Zan misalta Shigar tasu bansani ba dan Sunyi Kyau harsun gaji. Kawayen duk Ankon Material Sukayi golden Colour Suma Sunsha Kyau Ahaka Suka fita Xuwa motocin da Aka tanadar musu. bangaren iyayema ba'abarsu Abaya ba material kalan Maroon Sukayi Inda ka kalli Mamy da mumy Kasan Cewa matan manyan mutane ne Dan duk adon Daham Sukayi. Haka bangaren Angwaye da Abokansu Shadda Sukayi Calar golden yayinda Angwaye Sukayi fara. duk wanda ka gani Cikin farin Ciki yake musamman yazeed dayakejinshi Cikin kuzari da Nishadi. Ahaka Suka dunguma Xuwa Wajen partyn.
Lokacin dasuka karasa Angama Shirya komai inda Aka kawata wajen da adon golden and white duk Wani mai taya Amare da Angwaye murna ya yaba da tsarin wajen. Gaba daya Manyan mutane Suka Hallaci taron na yau. Kowa kagani Cikin Shiga ta Alfarma. jera kawayen Amarya Akai agaba Suka Shiga inda gagarumin kida Mai dadi ketashi. yazeed da feenah ne tsakiya inda Mubeena da mubeen Suke agabansu Rike da flowers.bayansu Nazeer da Leemah ne Sai Kawayen Amare da Abokan Angwaye Abaya inda kowacce take Jere da boyfriend dinta. Feenah Cikin Ranta ba karamin haushin yanda Akahadata da yazeed take yiba dan bayanda Zatai ne,hartafi sakewa Adayan partyn dayake Akwai Mufeeda, Wannan karon kuwa ba Mufeeda Dan haka duk ta takura. Cikin Natsuwa kowa tasamu wajen Xamanta inda Aka Raka Amare Nasu wajen Zaman.kowa yaga yazeed da Feenah fadi yake dama tare Aka hadasu, wainda basu sansuba kam fadi Suke Amarya da Angon Nan Sun dace. Cikin kwarewa Akafara Shirya partyn yanda yadace daga bisani Aka nema babbar Kawar feenah data taso tabada labarinta. Leemah ce ta tashi dan tayi Alkawarin ita Zatai attending din feenah. Cikin takun kasaita takarasa wajen take Akasaki tafi ganin Haka Nazeer yatashi yabi bayanta, da Sauri yusuf yace Uban yan kishi daganan kabada labarin ango. dariya Nazir yayi yakarsa kusa da Leemah inda tafara bada labarin feenah. """"Asslam Alaikum. My Name Is Leemah Ahmad am here to attend my friendly feenah Faruk. Feenah She's my frind from Nursery Skul, She's best nys lady, She's beautiful, She's jealous She have a good heart Kai feenah She have Everything I love her because She's Comes from a family that has no problems. And do you know what's her Secretly? She Can Cook Amazing food "wow" She Can Cook Arabian food, india,Turkey nd She meals tuwo Kai hardamaa dakan Sakwara duk Xatayi. Thank you to All peoples dasuka halarci Wannan bikin Allah yamaida kowa lfy."""" Tafi kawai kakeji Raf Rag Raf karshe Nazir ne yabada labarin yazeed yayinda Suka dan chashe. Daga bisani Kausar da yusuf Sune Suka bada labarin Leemah da Nazeer dan feenah kin tashi tayi. Haka Aka rinka gudanar da komai cikin tsari harzuwa lokacin tashi yayi. daret Kowacce gidansu Akawuce da ita fada kuma Akaimusu Cikin Natsuwa kamar yarda Ake ma kowacce Amarya daga karshe da kuka duk Akasasu Amotoci Dan kai kowacce gidanta. Saidai mutane duk mamaki Suke ganin gaba daya motocin waje daya Sukebi. ba kamar Kausar dataga hanyar gidanta Akeyi.kasa Shiru tayi ta tamayi Yusuf. Cemata yayi dama yazeed da Nazeer kusa da gidanshi Sukai gini Amma Shi feenah da Akayo da'Ita nan ne Abin yake bashi mamaki. Inaganin gidan yazeed Xa'aikata kafin mijin nata yazo ya dauketa shikuma Akawo mishi matarshi. Tabe baki Kausar tayi itadai Akwai Abinda take tunani. Haka kuwa Akayi Ana Sauka Akafara Shiga gidanjen biyu dasuka Saka na yusuf Atsakiya. Kasancewar Amaren Sanyi Suke da lullubi yasa basu gane me Akeba.kukan dasuke kuma ya hana Su Saurari me mutane Ke fadi. Saida yan'kawo Amarya Sukagama duba gidajen Kafin Suka kama Hanyar komawa Suna yaba irin tsare tsaren ginin gidanjen. Mamy Aka bari da feenah inda takara mata Nasiha Sosai daga bisani ta tafi durkushewa feenah tayi tacigaba da Raira kukanta Kamar Karamar yarinya. bangaren leemah itama mumy barinta tayi tacigaba da kukanta Kamar Wanda Akaimawa mutuwa.
(Mufeeda fa??????😨😨
💖💋💋💋💖💋💋💖
YAR LESBIAN CE
💖💋💋💖💋💋💋💖
By
Nadeeya mohd Ahmad
(💖Nadseer💋)
dedicated to
Xaynab Ummu mahbub
Page...74
Lokacin da Abokan Angwaye Suka Rakasu gidan yazeed Suka fara Shiga. barinsu yayi Sukacigaba da Surutansu irin Na barkwanci. daga bisani daya daga Cikinsu ya bukata da Afito da Amarya. Kai tsaye yazeed yace be daukotaba Dan haka Sutafi bacci yakeson yi. Tashi Sukai Suna fadin kaidai Kace A hannu kake Mun tafi Allah yabada Zaman lfy. Kala bece musu ba harsuka fita Xuwa Raka Nazeer. Dawowa baya yusuf yayi Zuwa wajen yazeed, Kai Ango yaushe Zamu dauko Balaraba ne??? Dan tsaki yazeed yaja Abba yace Anriga Ankawota. dan mamaki yusuf ya tsayayi Cikin Ranshi yake fadin kardai Abin da nake Zato Shine? Afili Saida Safe kawai yama yazeed yafita. Kusan dai duk irin barkwancin da'ake Ranar Aure Nan ma Haka Sukai A gidan Nazeer tare da Addu'oeh Zaman lfy karshe tashi Sukai Sukatafi, Yusuf nafadin Adaibi kanwata A hankali. dariya kawai Nazeer yayi dan yagane mai Yusuf Ke nufi. karasawa yayi dakin da Leemah take Cikin kuzari da kara gdy Ga Allah daya mallaka mishi Leemah gashi Gata Ayau. Tsakiyar bed take durkushe da kanta da Alamu har yanzu kuka take bata bariba. da Sauri ya Aje ledan daya Shigo da ita ya nufa kan bed din. jawota yayi jikinshi baby bakya farin Cikin kasancewarki tare dani Ayau Shiyasa kike kuka Haka koh? da Sauri Leemah tafara girgiza kanta Alamar Aa. baby feenah yola fa Aka Akaita kuma....batakarasa maganar ba takara Sakin Sabon kuka. Rungumeta Nazeer yayi yayinda yashiga lallashinta da maganganu masu Ratsa Zuciya. tuni ta kawar da tunanin da take tare da Shanye kukan Nata. bacci ke sonyin gaba da ita ganin haka Nazeer ya dauko ledan daya Shigo dashi. Kajine Aciki hade da free milk. da Ker yasamu ta yarda taci kadan Zuwa yanxu ita kanta tasan harda tsoron da take ji Nashi. Nazir ya ganota Dan haka Cikin Sanyin murya da lallashi ya Umarceta data tashi tayo Alwala. bata bata lokaci ba tafito Raka'a biyu Sukayi lokacin dasuka idar addu'oeh yarinka kwararomusu Na neman Albarkan Aure tare dasamun Xuri'a dayyiba. karshe tambayoyi yashiga mata tana bashi Amsa daya bayan daya har Xuwa lokacin da bacci yayi gaba da'ita Anan kan pray mat din. Murmushi kawai Nazir keyi yayin da yake kara godeya ga Allah. Haka kawai yaji Son Leemah na Kara Ratsa Zuciyar Shi. Lokaci daya ya kalleta yanayin yanda take bacci hade da Sauke Numfashi Ahankali ba karamin burgeshi yayi ba. dan yatsa yakai kan lips dinta yana Shafawa Ahankali yana lumshe ido. Wani irin murginawa tayi wanda yaja hijaf din dake jikinta yayewa Wow Nazir yafada lokaci daya yakai hand dinshi kan Brest dinta. Shafawa yarinkayi Ahankali yana fitar da Numfashi. Cikin bacci Leemah tajita Cikin wani irin yanayi tun tana tunanin mafarki takeyi hartaji Abun yana yawa. Ahankali tafara bube idonta ganin Nazir datayi Ahalin dayake ba karamin tsorata ta yayi ba. pls Nazir kadaina banaso bacci Zanyi....bakinshi yasa ya hade da Nata Lokaci daya taja wani irin Numfashi jin Haka yasa Nazir yashiga kissing dinta Cikin wani irin Salo hade da kwarewa. Kafin wani lokaci duk Sunfita hayyacinsu ganin kasan bazaimusu ba yasa yadauketa Zuwa kan bed. Wasa yake da duk illahirin jikinta yanda yakeso yanayin da bata taba Shiganshi ba Leemah ta tsinci kanta Ayau Dan tun tana nokewa harta Tsinci kanta da beye mishi. Lokaci guda tafara kukan ya Rabu da ita Nima jin danayi Nazir na karanta addu'an Saduwa da iyali yasa Nafita nabar dakin Ina Musu fatan Samun Zuri'a dayyiba
💖💋💋💋💖💋💋💖
YAR LESBIAN CE
💖💋💋💖💋💋💋💖
By
Nadeeya mohd Ahmad
(💖Nadseer💋)
dedicated to
Xaynab Ummu mahbub
*ina kara godiya gareku Masoya book dina masu kirana a Waya da masu turamun messages harma da masu Cigiyata a Sauran groups Ngd Allah yabar kauna👌 da wannan nake kara Baku hakurin jinkirta post danake Ayanzu, wanda Suka Sani Sunsan Cewa ada Ina post A kullum yanzu inafama da Rashin lfy Shiyasa kukejina Shiru. but Alhmdllh book din gangarane yanxu y Rage. Allah yabani ikon Kammala Shi lfy*
Page....75
bangaren Su yazeed tunda yashiga Room dinshi bekara tunanin fitowa ba dama Ga gajiya tunanin Halin da Mufeeda tasakashi yadanyi daga bisani bacci yayi gaba dashi, hankalinshi kwance yake baccinshi bedamu da wata balaraba dake Cikin gidan ba bare yabi ta kanta. bangaren feenah banda kuka babu Abinda take Zuwa yanzu harda kukan takaicin Wannan wani irin miji Ta Aura?! Anyi biki Ance Ayau Zaizo gareta tabbas Kuma taji Shigowar Abokan Ango har Xuwa lokacin dasuka tafi kenan beda niyar Zuwa ya ganni. Lallai besan wacece feenah ba indai nice Muzuba. Tunanin da feenah tarinka yi kenan Cikin Ranta. Koma dai maganar Mufeeda gaskiya ce datace mijin nawa baya Sona lika mishini Akai? Kuka ta kara fashewa dashi Lallai da yau Nakara tabbatar da iyayena basa Sona. Toh Amma iyaye Sun taba haihuwar yara Suce basa So kuma? Rasa Amsa tayi Ga bacci dake Cinta hade da yunwa karshe Leemah ce ta fado mata a Rai wani Sabon kukan ta Saki Saida tayi mai isarta kafin ta tashi ta dauro Alwala Nafila tarinka jerowa Dan batajin Zata iya bacci adaren yau. Bangaren Mufeeda tun lokacin data bar hospital Lokacin da yusuf yace mata an Sallame yazeed daret gida ta Wuce daga Nan Sukashiga Shiri da kawayenta Dan Zuwa wajen party. Sun Shirya tsaff tashiga jiran yazeed yazo daukarta tare da kawayenta. Saidai kusan Awa2 Aka kara kan lokacin da'akai Alkawarin Xuwa wajen partyn, ba yazeed ba labarinshi. ganin da Mufeeda tayi kawayenta Sun fara Surutu yasa tashiga kiran Number din yazeed domin taji ba'asi. Saidai tayi trying kusan sau30 numbern bata shiga Ga wani Karin takaici Sam Number din yusuf dake wayarta Itama bata Shiga. ganin lokaci na kurewa yasa Zuciyarta ta yanke mata Shawaran ta kawo hayan motoci. Hakan tayi kuwa lokacin dasuka karaso Cewa tayi yazeed ne ya turosu Sabida Bejin dadi Sosai yasa Zai wuce daga gidansu. da Haka kawayen nata Suka gamsu Suka hau motoci Zuwa wani babban hold wanda Mufeeda ce ta Zuba Uban kudi ta kamashi duk dan Cewa bikinta ne Zai kasance Abin kwatance A fadin Najeria. Lokacin da Suka isa mamakin Rashin ganin kowa kawayen mufeeda Suka Rinka yi. kauda Zancen Zucinta tayi yayin da tasheda musu cewa dama ita da kawayenta ne kawai wannan partyn bata gayyace kowa ba. Haka Suka Rinka gudanar da Shakiyancinsu Su kadai yayin da Abin Duniya ya ishe Mufeeda tama Rasa wani irin tunani Zatayi Alokacin. bata kara tsinkewa da Al'amarin ba Sai Alokacin dataga lokacin tashi daga party yayi babu Alamar yazeed. Tasan dole kawayenta A wannan karon bazasu yarda da ita ba,musamman idan tayi musu karya lokacin dazasu tambayeta motocin kai Amarya. Cikin damuwa tacigaba da kiran Number din yazeed Still Akashe babu Abinda bata Rayawa Cikin Ranta. da Haka lokacin tashi yayi. Wata Aminiyarta ce ta Sameta da maganar datake tunani Cikin Ranta. Cikin Sanyin murya da inda inda ta bata Amsa da ba gidan yazeed Za'a wuce da itaba Sabida bashida lfy tarewa Saidaga baya. Jin haka yasa kawayen Mufeeda Suka fara kuskus harda masu yada mata habaici.tayaya Angama party ace ba gidan Amarya Za'a wuceba hasalima Saidai kowa ya nemo motar dazata maidashi gida. bayanda Zatai Dan batada mafita bare bakin maida musu Amsa da Haka duk Suka watse Suna masujin haushin Mufeeda,wajen ya rage daga Ita Sai Aminan ta Khady da Seemah wanda Suma Sunfara tsinkewa da Al'amarin mufeeda Dan haka Suka karaso wajenta danjin takamaimain Abinda yake faruwa. Mufeeda Akwai matsala ko?? dago Kai Mufeeda tayi ta kalli khady data wurga mata tambaya! Lokaci guda tashiga girgiza Kai Nop bawata matsala kuzo mutafi. dafata Seemah tayi Mufeeda Akwai Abinda kike boye mana. Hawayen da take makalewa ne yashiga Zubowa Seemah Wlh nima nakasa gane Abinda ke damuna. Amma Mufeeda Ina yazeed? Ina yan uwanshi? Aiya Sanina wannan partyn hade da yan uwan yazeed Za'ayishi maimakon haka Sainaji kince dan kawayenki kawai kikayi, me Hakan ke nufi ne???? Seemah Hakan danafada Shine Mafita tabbas gaba daya na hada partyn Amma tun tuni nake kiran Number din yazeed bata Shiga, dan haka nace Mushirya Muzo Still kina ganin nan nima bashi ba danginshi Ni ina tunanin yana gida besamu Sauki ba. Nisawa Seemah tayi Alright idan ba damuwa muje gidansu yanzu dan muji komai tayaya Andaura Aurenku kuma Ace a gida Zaki kwana. Gaskiya kutafi Ku ni gida Zani dare yayi khady ta fada tana murguda baki. Ok Sukace yayin da Suka hau mota dan Xuwa gidansu yazeed. Lokacin dasuka isa gidan Shiru da Alama kowa bacci yashiga. Sallama Sukai inno kadai ce a parlon ta idar da Sallah. Ganin Su mufeeda yasa tayi Murmushi wanda ita kadai Tasan manufarshi. kunzo neman tsaka koh? da sauri Mufeeda ta daga kai eh Kaka yana Ciki ne? Chaf ai tunda muka taso wajen party Aka kaima yazeed Amaryarshi karfe9 Shima yabar Nan yanufi gidanshi. ba Mufeeda kadai ba hatta Seemah Saida tasha jinin jikinta. da ker Seemah tayi mgn kaka kina nufin yazeed yana gidan dayar matarshi? Kwarai Kuwa yanachan yana Raya Sunnah. Magana Seemah Zatai Mufeeda tajata Sukabar parlon. Tabe baki inno tayi Cikin Ranta take fadin Saima idan kinji Yafasa Aurenki. Mufeeda dakin Bari munji komai ko? No Seemah muje da Safe masan Abunyi.
Washe gari tunda Sanyin Safe Naji Ina Muradin kaima Amare Ziyara😄Dan haka Na yanke Shawaran Fara Zuwa gidan Halimcy. karfe 6 daidai Nakarasa gidan Captain Nazir.Nayi Mamakin ganin lovers din Xaune a parlo Leemah Sai faman Shagwava take Xubama Nazeer Shikuwa Sai lallabata yake Kamar egg. Cikin Raina Nake fadin ya'da tashin Wuri kuma Mrs Captain. Nazir naji yana fadin Sorry My baby Ki dauri kisha kadan. Zakiji Normal. Kara narkewa tayi jikinshi baby ni banasha pls. Oh God yazakisha magani bakici komai ba. Naji Sauki fa. Ok meyasaki kika kasa bacci toh? bakaine ba. Murmushi Nazir yayi iam Sorry Leemah bazan kara ba. Shagwabe face tayi toh katafi Room dinka Nidai. dariya yayi idan natafi Xakiyi bacci toh? Um'um ni banaji. U see leemah bakida lfy pls kisha tea din kadan. yamutsa face tayi tana kokarin tashi.ganin takasa yasa Nazir tashi daukarta yayi chak yanufi toilet da ita. Zillewa takeyi baby Nayi wanka fa. I know Amma bakiyi d Kyau ba.Ok kabari nayi mai Kyau da kaina. bebi takantaba yashiga cire kayan jikinta yayin da ya hada mata Ruwa mai Zafi Sosai da ker yasamu tashiga. Zakidaina jin Wannan kunyar Soon. turo baki tayi wanda Hakan yasa Nazir Kama Dan bakin nata kissing dinta yafara Sosai tun tana tureshi Harta hakura. Saida yagaji dan kanshi Kafin y yashiga gasa mata jikin. Su leemah Sai wani narkewa Ake hade da Shagwaba iri iri. Suna fitowa ya hada mata tea Nan ma da ker yasamu tasha kadan Saida yaga ta Shanye yabata magani kafin yashiga Wanka. bawani dadewa yayi ba ya fito gabanta yashirya inda take tafaman Rufe face.Murmushi kawai yake yana mamakin irin kunyar Leemah. Magana yakeson yi wayarshi tafara kara. dauka yayi ganin me kiran yasashi dagawa da Sauri. Sallama yayi. Yashiga gaisawa Cikin natsuwa. Eh Alhmdllh Abba. Toh insha Allah. Ok Zataji. Toh Saimun karaso.kashe wayar yayi ya fuskanci Leemah. Shafa kanta yayi Abba na gaidaki Leemah. turo baki tayi Shine Ni bekirani ba Saikai. dariya Nazir yayi Sosai yayin da yaja hancinta Cewa yayi nakai mishike yayi missing dinki. Ido Leemah ta fiddo waje lokaci guda ta tashi haba dai? Serious cewa yayi yana nemanmu karfe9 daidai. Murna Leemah tafara Bari nashirya tun yanzu.dariya Abun yaba Nazir kenan kinason Zuwa,bakisan ko laifi mukai ba! dariya Leemah tayi Saidai ko kaine kayi lefi Amma Amarya bata lefe, baby kasan yanda nayi missing din Mamy yau daya kawai? dariya Nazir yayi Sosai Ok Kafin kitafi Zokiji wata mgn. Matsawa tayi yayin data mika kunne.lokaci guda tafara girgiza Kai Nidai da Zafi banaso. Shikenan mufasa Zuwa. marairaice fuska tayi toh kabari mudawo. Murmushi Nazir yayi Alkawri kikayi. Na yarda Amma bada Xafi ba. dariya Nazir yayi Ok na yarda.
Sanye yafito da Sleeping dress da Alama tasowarshi daga bacci kenan, fuskan nan adaure kamar betaba yin dariya ba ya Nufa kitchen. bejima ba yafito yanufa dakinshi phone yafito dashi yakara komawa kitchen dafe da cikinshi ko ba'a fadamaka ba Zaka gane ba karamar yunwa yake jiba. indomie ya dafa hade da ruwan lepton yafito kamar ya wuce dakinshi saikuma ya yanke Shawaran Zama a parlon. Cikin Natsuwa yake breakfast dinshi bangare guda yana Chat a wayarshi. Saida ya Kammala yayi yunkurin tashi wayarshi daya dake gefe yaji tana Kara kai tsaye daya duba mai kiran yadaga hade da yin Sallama. daga dayan bangaren naji Ana fadin yazeed katashi Lfy? Lfy qalau Abba. Toh Alhmdllh idan kagama Abinda kake Xuwa karfe9 ina nemanka. Abba badai wata matsala koh? ba komai yazeed inada magana daku ne. Ok Sainazo Abba. Madallah katawo tare da iyalinka. dafe kai yazeed yayi danshi Shaf yamance da wata yake Zaune Cikin gidan, Toh wannan wace irin mace ce haka? Tabe baki yayi tasha Zamanta idan Saina nemeta. Ko bakajine yazeed? Inaji Abba me kace? Nace kazo da iyalinka. toh Abba insha Allah. jingina yayi da kujeran dayake kai Nikam yaushe Xanfara Samun Abinda nakeso? bashida amsa dan haka yatashi Xuwa room dinshi.daret toilet ya fada Wanka yayo yafito Cikin kankanin lokaci yashirya Cikin Shadda Sky blue colour. feshe jikinshi yayi da turaruka ya dau Makullin motarshi hade da wayoyinshi yayi Waje. kashe tvn dake kunne yayi yanufa waje. dafe kai yayi tunowa da maganar da Abba yamai. Yanzu nakii daukarta Abu yazama matsala mtsww yaja tsaki yanufa part din daya dabbatar Anan Amaryar take. Saida yayi tsayuwar kusan minti20 kafin yayi Shahadar yin Knocking din door din. Kwance take kamar Mai bacci Amma tunani ne fal Cikin Ranta. daga ganinta Kasan ba karamin Abu ke damunta ba domin face dinta fayau yayi ga idanunta dasuke a kumbure. Kamar daga Sama taji Ana knocking, hawayen dake face dinta ta goge kamar bazata bude kofar ba Saitayi tunani,tashi tayi tanufi kofar tana mai addu'a Allah yasa ko Kausar ce
💖💋💋💋💖💋💋💖
YAR LESBIAN CE
💖💋💋💖💋💋💋💖
0 comments:
Post a Comment