Haba ummu kiyi tunani mana ai kinsan ko da Abbakar ba abokin Mahfuz bane babu ta yadda za'ai ya yadda ya aureki kina ganin yadda yan mata masu aji ke faman sansa kuma ya sani bawai be sani ba anman ya sharesu.
Ki daurewa zuciyarki karki zama butulu Yah nasir be cancanci haka ba yacancanci duk wani karamci daga gareki ya miki duk wani halacci na rayuwa kidaure ki sake tunani wallahi.
Nifa ba cewa nayi bazan aureshi ba ni wallahi amatsayin uba na daukeshi koma uwa da uba na taya kuke ganin zan iya zaman aure da wanda nakema kallon iyayena.
Daurewa zakiyi ahankula inkika ce kin amince kuka fara soyayya tuni zaki mance da a ina kika ajiyeshi kina kallonsa haka simi simi zai baki mamaki dan irinsu sunfi sanin takan mace batasan sanda tai dariya ba wallahi baku da dama ko kadan.
Sunji dadi datai dariya yawwa ko kefa ki dena yawan kuka da damuwa kisama ranki dangana yanzu ki daure in yazo ki fada masa bacin yai fushi ya dena zuwa kingani ko duk haqurin bawan Allahn nan.
Yanzu ki kirashi ki bashi hakuri kice kin amince wa ni tab inba bazan iyaba kuma tunda ya hanani kiransa iyanzu sabida yace yana gida ok to ki bari sai dare lokacin ya shiga daki tai jim tana tunani kinga inbazaki iya kiransa ba ki tura masa saqo kawai to shikenan sai na koma gida.
Shi kuwa Abbakar tun da ya qwace paper din ummu yana kallon ta time inda take singing hawaye na bin fuskarta jiyai kamar ya bita ya rarrasheta ko ya goge mata hawayen saidai ba dama.
Yar firar ma dasuke da daya malamar duk sai ya kasa ransa gabaki daya ba dadi yaji sai faman fada kawai yake qarshe ma tasauran student din karbewa yai danji yai gabaki daya ya tsani ajin.
Futowar da zasuyi hangota tana faman kuka ana bata baki nanma jiyai kamar yaje yashiga sahun masu bata bakin yadai dake kawai.
Sai mangariba ya koma gida shima dan kar hajiyarsa taji wani abu badan yaso ba dam jiyai gabaki daya baisan hayani yama mance da qanwarsa tazo duk dokin da yake na yaje ya dawo su kwashi fira ya tafi.
Saida ya shiga falon yama tuna hakan yasa ya fada da murmushin fuskarka ya shiga da fara'a.
Tana ganinsa ta quntse fuska inba nayi fushi ba aikasan da zuwanmu shine sai yanzu zaka dawo yazo ya zauna kujerar dataje inba bakiyi fushi ba ya fada yana irin yadda tayi tasa dariya Yaya ta fada shima yasa dariya qanwa bari in shiga in rage kayan jikina sai in sauko to se ansakko.
Danqaramin danta yasa kuka ya daukeshi ya daukeshi sukayi saman tare yana masa fira irin tasu ta yara.
Tare suka sauko yana dauke dashi da alawa ahannunsa aikuwa yana direshi mai bi masa ya sauko daga kujerar da yake faman game ya kwace alawar ya tura baki aikuwa ya tsanyara kuka dasauri Abbakar ya juyo OMG this boy me aka ma ya fara nuna yayan nasa da alawa abaki.
Ah wahid ya zama babban kwabo yai saurin miqa masa alawar wasa nake masa fa suka sa dariya dan wahid bayasan ace masa babban kwabo dan zatonsa kwabon wani abu ne marar kyau.
Shima wata Abbakar yadauko a aljihu ya miqa masa yakoka yana tsalle thank you uncle dayan ma ya taso ya miqa masa sai muskilin nasu baya maga sai yaga dama mutane da yawa nacewa Abbakar yayo musanman babansu danshi yace duk danginsu babu muskili aikuwa ganin anbawa kowa ba'abashi ba ya zumburo baki ya huro hanci sai hawaye da sauri Abbakar yai gunsa haba nawan mene na kuka kuma yai shiru to shikenan ya goge masa hawaye.
Ya bude alawar ya vashi to ungu kaga takama ni na bude maka ya miqe zai koma ya zauna ya riqo rigaraa ahankula yace thank you uncle yai dariya kawai.
Hira suke sosai gabaki dayansu har hajiya tace kunga ni na gaji saida safenku duk an miqe sai ummi yah Zainab sai da safe inkika biyewa yah Habu saiku kwana anan ya kalleta wato yau rashin mutuncin naki kaina ya koma ko.
Tai dariya ai tunda kasa nai kuka asch na yah Habu zan dinga cewa tai daki da gudu ya kada kai yana dariya dan in ummi ce komaima zatayi shi yamayi mamaki da ya dawo bata sa hajiya ta cakcakeshi va dan yasanta da sharri.
Zainab ce ta juyo daman tun dazu wallahi nakesan muyi magana ya kalleta me ne kuma daman Babansu wahid ne nace masa inasan in koma sch in cigaba da karatu qeme me ya hanani yai saurin kallonta to me kike nufi yaji kika yo kome.
A'a ba yaji nayo ba wallahi kawai ziyara ce nadai fada ma ne dan Allah ka roqarminshi ya yadda ehto ba roqarsa zanyi ba zan saneshi muyi magana in ya yadda to inbe yadda ba ki haqura masters dinki ya isheki keda ba aiki kike ba ina jarin dana baki kwanaki tahau sosa qeya duk sun qare ko tai dariya kawai.
Shikenan kibari inasa ran shigowar kudi na kayan gonata danake na sayar zan yi qoqari in bude miki dan qaramin store in kikai maintaining dinsa ya isheki rayuwa mijinki ba abinda ya rageki to yah na gode.
Sauran daya maganar inajinki yah dan Allah kafadan meke damunka duk kayi baqi ka rame yai dan murmushi me kuwa ke damuna kawai yanayin aikine kullin cikin jele daga han zuwa old site daga can zuwa new site ba dole mutun ya rameba anman yah anman qarya nake ko a'a ni ba haka nake nufi ba.
To tashi muje ku kwanta kar gobe yarannan su tashi da wuri su hanaki bacci kanki yazo yana ciwo ta miqe ta sabi yaro guda shima yadauki biyu qananan ta tashi babban suka wuce dakin da zasu kwanta saida ya kwantar mata dasu ya mata saida safe ya wuce dakinsa.
Zaune take tana ta faman rubuta saqon da zata tura masa tana gigewa ta rasa me zata tura mai qarshe dai ta rubura
_Assalamu Alaikum
Yah nasir barka da dare daman cewa nayi na Amince Alkah ya bamu zan lpy_
Gabaki daya tama kashe wayar tahau kuka bayan ta tabbatar saqon ya tafu.
[11/28/2017, 5:38 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*wattpad Fadimafayau*
*75-80*
Yana kwance idonsa akan fanka shi kansa besan tunanin me yake ba yaji alamar shigowar saqo a wayarsa kamar kar yadauka ya duba yadai daure ya miqa hannu yadauko.
Ganin sunan ummu yasa shi miqewa ya zauna tunkan yaga saqon yai saurin budewa duda ba wata magana bace me yawa sai saqon ya masa dadi sosai jiyai kamar yai tsuntsu yaje ya tabbatar ita dince ta turo ba kuskure bane.
Yaso tashi da wuri saidai kasantuwar bai kwanta da wuri ba yasa sai wajen tara da rabi ya tashi.
Wanka ya fara yi shi kansa baisan meyasa yake dokin zuwa ganinta dinba besan me yasa yake ta dauko kaya yana sauyawa ba duk dan ya burgeta duda yasan tasanshi batun yauna.
Shadaya dedai ta masa a gidan ummu Farida ce a farfajiyar gidan tana karatu abokiyar zaman ummun tana ganinsa ta saki fuska sir barka da zuwa yadan hada rai sau nawa zance a dena cemin sir dunnan a gida tai dan murmuahi sorry sir kika kuma yai shigewarsa ciki ta biyo bayansa tana dariya.
Yai saurin cafe Abbakar ko ince mahfuz da ya rarrafo zuwa bakin qofa yana bin ball insa ya ko tsanyara kuka dan besan waya daukeshi ba Nasir yai saurin juyo da fuskarsa haba yaron babansa jin muryar nasir yasashi yinshiru yana ganowa a hannunsa yake ya bangale da dariya alamar farinciki.
Dan rigima wato da bani bane shikenan sai ayita kuka ko Ummi da ta zo daukansa tasa dariya itama lah yah nasir ashe zakazo yai dariya ce miki akai da nadena zuwa a'a nadai ga kwana biyu baka zuwa ne suka shiga falon gabaki daya har Farida.
Wallah yah nasir nayi missing inka da yawa eyye ko eh mana inji Farida duk ganina da kike a sch ta dan rausayar dakai bayan a sch din nuna wa kake baka san mutane ba Allah ko eh mn inka wani hade rai to shikenan maida wuqar zan dinga dariya sukai dariya baki daya.
Ta miqo masa littafi Allah tun jiya nake karanta nan nakasa pls koyan yakarba ya duba eyye wato duk lecture din da muku bakima gane ba tadan juyar da kai time inne inajin bacci to ynx ma ai inna miki cewa zakiyi bacci kike ji dan Allah yah nasir to shikenan bari sai anjima.
To wannan fa ta miqa masa paper a'a banda wannan ai assignment na baku pla yah inkika isheni ko sauran bazan koya miki ba wai ina Ummu ne ta dan fita ne nasan yanzu zata dawo.
What ina taje mene anfanin ummi da na kawo mata tace batasan aiken ummi bata rufe vaki ba Ummun ta shigo ya hade rai daga ina kike naje shago ne ko dan kinga kwana biyu bana zuwa shi yasa kika tsiri futa yawo.
Idonta yai rau rau kamar zatai kuka haba yah nasir kasan bana maka qarya to me yasa baki aiki ummi ba naga batasan zuwa ne what no bawai qi take ba aikenne kamarta dole taji kunyar zuwa wane irin aikene ta miqa masa always ya gani oh basai ki fadanba da wake sayo muku tadan turo baki to inama muka ganka bacin ka dena zuwa yadan sosa kai aishi kenan.
Farida ta miqe tai waje yah bari inje inci gaba da karatuna ummi tasa hannu zata dauki Abbakar yako sa qara Nasir ya ce jeki abinki kyaleshi tai ciki.
Ummu ta zauna yah ina kwana lafiya kalau yace ya dannawa ta kalli Abbakar ganinan ai.
Jiya sai naga saqo tai murmushi ashe ma shi ya kawoka yai dan murmuahi dadinsa da ita akwai bawa mutun amsa haka nace miki shi ya kawoni to yaya rabonka damu kwana nawa bakiga exam ake a sch ba bani da time inkuma nakai dare kinsan hajiya tai dan murmuahi batare da ta amsa ba.
To anman yah kana ganin family dinmu zasu yadda da aurenmu yai dariya gami da sauko da Abbakar to aiko basu yadda ba abinda nasani ni shine dolene su yadda tunda kin yadda ta kalleshi ya daga mata gira.
Fira sukai sosai sai da aka kira sallah ya miqe bari in sallah ya fice.
Haka kawai ummu kejin takaicinsa ya ragu aranta haka kawai takejin hirarsu ta mata dadi koda tana sallah lokaci kadan kadan take dan murmusawa kodan yadda nasir kesan Abbakar dinta ne oho dan rabon da taga yaron na kyakyata dariya yanata warkajaminsa tun dena zuwan nasir abu kadan ma aka masa sai kuka kodan farin cikin danta zata haqura ta takurama zuciyarta taso nasir .
Yana dawowa yace ni zan wuce sai kinjini yah mun gama abinci kazauna kaci inji ummi ok to kamar kinsan yunwa najeji tai dariya gami da komawa kitchen din.
Farida ta shigo yana cin abinci yanzu yaya da abinci be tsaidaka ba shikenan karatuna yasha ruwa yai murmushi sorry mangofa ynx zamuyi.
Sai da suka gama karatun Nasir ya musu sallama ya tafi cike da kewarsu ji yake kamar karya tafi.
Gidansu Abbakar
Wahidi ke ta faman kuka shi bazai tafi ba shi anan za'a barshi daqyar sai da yaga babansa yazo ya hau murna sannan ya yadda yabisu zainab sun tafi cike da kewar yan uwanta da ummanta.
Shi kansa Abbakar sai yaji gidan wani iri dan dan kwana biyun da sukai agidan gwanin dadi kullin cikin hayaniyar yara hakan yasa zainab suna tafiya yace ma hajiya zaije waje sai dare zai dawo sao kadawo tace ta koma ciki.
A teburin me gadinsu yazauna a qofar gida suka hau fira sai mangariba yabar nan din yai gidansu mahfuz dan ya kwan biyu bai ganshiba kamar yadda ya zata kamar koyaushe Mahfuz baya bangaren mazan gidan dole ya zayayo cikin gidan aikuwa abunda bayaso yan matan gidan sunata sha'aninsu waccan na zaune waccan na shanya ko wacce da abun da take bawai abubuwan da suke ke bashi haushi ba face shigarsu basa shigar kwarai indai sina gida duda kuwa abokan yaran gidan kowa shiga gidan yake haka mazan bakowa ne suke shaqiqaiba kawar da kai yai zai yi ciki.
Ya jiyo Aisha na fadin lah yah Abbakar sannu da zuwa yadan saki fuska yawwa qanwarmu ina kuwa mutumin naje dakinsa baya nan lah ai yadawo ban garen hajiya tun rashin lafiyarsa yana nan ma yanzu ok to bari inje.
Yana zaune a falon kansa kan cinyar hajiya Abbakar ya shigo ganinsa hajiya ta fada da murmushinta mahfuz ya miqe zaune a'a ai da kayi kwanciyarka dan gatan hajiya yai dariya zaka fara ko sun gaisa da hajiya ta miqo ai qwanda da kazo duk yabi ya damu kansa kan ummu ka masa nasiha nasan yafi jin maganarka akan ta kowa.
Sun taba fira Abbakar ya miqe sukai masallaci agidan yaci Abincin dare sannan mahfuz ya leqa dakin hajiya zai tafi zan rakashi shima ya leqa hajiyarmu sai da safe au ba'a nan zaka kwan ba eh hajiya ban fadama hajiyata ba to agaisheta sai da safe suka fita tare.
Sun dade a qarshen layi suna tattaunawa kan batun ummu kasan Allah Aminin in yau akace inada ciwon zuciya ba mamaki kullin cikin tinanin ummu nake bacci ma bayinsa nake sosai ba kai mahfuz kadaure ka cirema kanka damuwa kodan hajiya kasan yau in wani abun ya sameka tafi kowa tashin hankali haka ne shi yasa nake daurewa yawwa ka ci gaba hakuri kaji nawan sukai dariya gabaki daya gami da sallama suka rabu.
Hajiya daman so nake muyi magana inji Nasir ta maida hankalinta kansa inajinka akan nefa yadan sosa qeya eh daman ta miqe kaga inbaka shirya ba inka shirya sai ka same daman hajiya tada miki zanyi na samu matar aure tai saurin juyowa da fara'arta da gaske kake eh hajiya wace kuwa wannan Hajiya ummulkhairin baba yasir what ta fada eh Hajiya alamar faduwar da sukaji yasasu juyawa da sauri Mahfuz ne zube da alamun yaji maganarsu ne hajiya tai gunsa da gudu itama hippp ta fadi a sume.............
[11/29/2017, 6:10 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*80-85*
Rasa ma kan wazaiyi yayi ta maza yai yadauko ruwa yai kan Hajiya cikin sa'a ta farfado da tana bude ido ta tankade nasir tai kan mahfuz dake kwance tahau jijjigashi miqon ruwa mana ta fada cikin qaraji.
Dasauri ya miqa mata ruwan ta hau shafa masa bai far fado ba da sauri Nasir ya daukeshi sai mota hajiya na biye dashi ganin haka yasa sauran mutan gida dake farfajiya sukayo kansu suna tambayar lafiya basu basu amsa ba suka bar gidan hakan yasa suma suka biyosu amota sai kadan aka bari agidan.
Kai tsaye asibitin nasarawa suka wuce basu wani sha wuya ba dan babu marasa lafiya sosai a emergency din yau aka karbi mahfux din.
Tun wajen awa guda da'aka shiga dashi dakin bada temakon gaggawa hajiya keta faman kai kawo tana hawaye babu yanda ba'ai da ita tazauna ba taqi da nasirma ya mata magana saita haushi da fada daqyar tai shiru shima dan nurse ce tazo tace ta ishe su.
Ganin hajiya zata iya masa baki yasashi miqewa yabar gurin yai dan nesa kadan dasu dan yaga irin hararar da take sakar masa lokaci lokaci gami da tsaki da qwafa da take ja in suka hada ido.
Doctor yana fitowa sukai kansa bai kulasu ba yai gun Nasir dan yasanshi aikuwa hajiya na ganin haka tabi bayansa tana fada yau naga mara mutuncin likita ya jiyo zai yi magana Nasir ya dafoshi Am sorry Abdul mum dina ce yadan saki fuska kadan gami da cewa Hajiya bawai na share ku bane kunsan irin haka namiji yafi karfin rai.
Eyyye qarfin rai har yafi na cikin sa da nadauka nai naqudarsa ni nasan zafinsa dan haka zanfi kowa iya jure abinda ke damunsa dan in kula dashi ganin tadau zafi yasa Doctor din yace ai yamaji sauqi dan mun shawo kansa dakyar muka dai daita numfashinsa zaku iya shiga ku ganshi bata jira cewarsa ba tayi gaba.
Nasir ke biye da ita saida suka zo dedai dakin ta juyo ta watsa masa harara me kuma zaka shigo kayi masa bai ce komi ba ya koma baya ya tsaya.
Kwance yake idonsa a rufe da alamun bacci yake hajiya taja kujerar gefensa ta zauna gami da kamo hannunsa ta riqe yai saurin bude idanunsa zatonsa Nasir ne ganin hajiya yasashi fashewa da kuka ta hau rarrashinsa dakyar yai shiru.
Da sassafe nasir yabar asibitin saida ya biya ta gida sannan yai wanka ya shirya yai gidan ummu acan yakarya sun dan taba fira kafin ya miqe ni zan wuce yah tun yanzu eh ummu tadan shafa kan Abbakar Allah ji nake kamar karka tafi yai saurin kallonta da alamun har zuciyarta take magana anman bai fasa cewa da gaske kike tai dan murmushi Allah kuwa to banda abinki ai kwanan nan sai kinmace in fita ta rufe fuska anya kuwa yai dariya ina nan dake.
Har waje ta rakoshi ya miqo mata Abbakar yako sa kuka haba dan rigima yi shiru anjima zan dawo ya zura hannu a aljifu ya miqo masa alawa yako amshe yana kiciniyar budewa.
Har ta juya yace aff ban fada miki ba gobe ba lallai inzoba tadan juyo sororo sabida me yah eh mahfuz ne ba lafiya jiyama a asibiti ya kwan tadan tabe baki ayya Allah bashi lafiya gami dayin ciki abinta abinka da dan uwa sai gabaki daya baiji dadin abinda tai ba aqalla ta nuna tadan ramu ya gyada kai kawai yai gaba.
Ai kuwa da Nasir ya koma asibiti ya sha fada gun hajiya kan yasan dan uwansa ba lpy yai tafiyarsa yawonsa ba ita tai shiru ba sai da Mahfuz yace dan Allah hajiya kice ya fice daga dakinnan inna tanshi numfashina hadewa yake jin haka yasa yace ya fice.
Wajen qarfe uku na rana Abbakar yazo shida Hajiyarsa da qannensa biyu mata sukaita fira da hajiya inda shima sukaita fira da amininsa.
Kwanan Mahfux biyu ummusalma yayar Abbakar tazo dubashi aiko tasha qorafi dan sun saba sosai da Mahfux inma mutun ba sani yai ba zaiyi zaton Mahfuz ne qaninta ha Abbakar ba.
Bakowa adakin sai Mahfuz da ummu salma aikuwa mahfuz yasa mata kuka daqyar ta rarrasheshi yai shiru tahau tambayarsa mene yahau bayani kan ummu ne yar gidan baba yasir yah nasir yasan ita nake so anman yace shi zai aureta tahau masa nasiha haba nawan kabari zamuyi magana dashi nasan baisan kanasanta va inda yasani da tuni ya aura ma ita Allah yasani nace kabar min komi a hannu na zan mai magana ya riqo hannunta nagode yayarmu.
Sai dare ta bar asibitin shima saida Abbakar zai tafi ya tafi ita dan bada mota tazo ba.
Washe gari ta kira nasir a waya har gida yazo ya sameta ta mai bayanin komi yai dan murmushi kafam ummusalma kenan ai duniya ko hajiya bata isa tasa in fasa aurenta ba lokaci yayi da mahfuz zai dena abin da yaga dama lokaci yayi dazai gane vawai komi kake so kake samu ba arayuwa, tai sakato tana kallonsa eyye tunda hajiya ma bata isa ba inaga ni yar karoro yayi kyau ta miqe ta bar falon shima ya kade rigarsa ya bar gidan.
Kwanan Mahfuz hudu aka sallamesu sina zaune gabaki daya a falon mahfuz na kwance kujerar da Hajiya take Nasir ya shigo dauke da Abbakar dansa hajiya ta bishi da kallo gami da yaron wannan fa ya dubeshi dana ne what danka kuma eh hajiya dana ne da muka haifa da ummulkhairi ta miqe ashe nasiru haukan da kake cewa Mahfuz yayi ashe kai kayi yai dan murmushi hajiya aikinsan ba qarya nake ba kuma kinsan da hankalina.
Mahfuz ya miqe qarya yake hajiya dana ne wallahi qarya yake kumin shiru da Allah injita ta fada ra qarfi sukai shiru baki daya kafin nasir ya fara magana eh hajiya ki yadda dani gama kamarmu nan kina gani da yaronnan sabida shi na yanke shawarar auren mahaifiyars dan Allah ki yadda in aureta kodan kare mutuncin bawan Allahn nan tai shiru kawai tana kallon yaron da yaketa faman wasansa tabbas kamarsu nan sosai jitai tsanar yaron ta cika mata rai sosai tai kansa zata takeshi mahfuz da yake atsaye yai kasa asume tai saurin yin kan danta.
Sun samu ya farfado aikuwa ya hau kuka hajiya qarya Nasir yake yaronnan dana ne dan Allah karki yadda ya aure min mata wallahi inban aureta ba mutuwa zanyi Nasir dake zaune tun dazu ko motsi beba tun suman Mahfuz yana ta faman wasa da dansa yace aikuwa sai dai ka mutu Hajiya tahau rarrashinsa dagyar yai shiru tasa aka kai mata shi daki.
Adakin rokonta kawai yake kanta yadda adaura masa aure da ummu tai shiru kawai da ace wani ne cikin yaranta ke faman kiran suhan wannan yar maqiyarta ta da tuni ta yi maganinsa dan dai kawai mahfuz ne.
Haba mahfuz kayi tunani kwata kwata baku dace da ita ba ko kadan ya miqe haba hajiya inban dace da itaba da waxan dace zuciyata da gangar jikina ita suke so.
Nasir ya shigo dauke da yaron yanata faman dariya yace hajiya ni zan mayar dashi kuma gobe ne za'a daura mana auren kawu nazifi ne wakilinta ni kuma nazama wakilin kaina banasan ko kadan kosau daya yarona yai kukan rashin uba nasan ban kyauta miki ba anman nan gaba nasan zakiyi alfahari dani tai zuru tana kallonsa tama rasa ta cewa wai yau nasirun da ko uhum baiso yaji yace shi ke fada mata baqaqen maganganu haka.
Bai jira cewarta ba ya juya zai fita mahfuz yasa qara wallahi hajiya indai baki dakatar dashi ba ta auren masoyita wallahi yau zan kashe kaina tai saurin kiran sunan nasir yai gaba batare da ya tsaya ba tace nasiru wallahi ka qara taku daya Allah ya isa kuma sai ka biyani shayarwar da naima inyaso ka canja uwa yaja ya tsaya hawaye ya biyo idanunsa.
Juyo nan ka kalleni ya juyo ya kalleta kasani ni uwarka dana haifeka hai haqudarka na shayarda kai na haramtama auren yarinyar nan inko ka aurenta Allah ya isa bazan kuma yafe maba ka kuma sani koda bayan raina ne.
Anman hajiya ta daga masa hannu na riga na yanke wukunci dole agoben za'a daura mata aure anman bada kaiba da mahfux shi kuma yaron da kake cewa naka ne koma nawaye na qwaceshi na baima mahfuz tunda shi zai auru uwadda............
[12/7/2017, 7:56 PM] Fadimafayau: 18
*Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*85-90*
*Wattpad Fadimafayau*
Jiyai kamar an sheqa masa ruwan zafi qafafunsa sunkasa daukansa yana qoqarin yada Abbakar a hannunsa zubewa yai qasa jabas hawaye na bun fuskarsa.
Ummu ce ta fito daga daki tana kwalama ummi kira da sauri ta qaraso gani aunty ina Abbakar tace sun fita tare da babansa tun yaushe wajen magariba ta gyada kai kawai ta koma daki.
Har kusan qarfe takwas bai dawo ba ummu ta kuma futowa wai ina yace zai jene farida tasa dariya Allah umma bakida kara indai akan wannan yaron naki ne tai kwafa gami da turo baki kuban amsa tukunna kafin afaramin qorafi ummi ce tace cewa yai zashi gidansu dashi zai nunama hajiya shi what ta fada tana zare ido mai yasa kuka kuka barshi baku fadanba ummi tace cewa yai bazai dadeba.
Kuka kawai ummu ta fashe dashi gami da fadin shikenan nasan hajiya bazata barmin shi da raiba kuka take sosai farida na bata haquri.
Zumbur ta miqe tai daki hijabi ta dauko da wayarta sai kudi dabatasan ko nawa bane ta zari jaka tai waje ummi taso muje tace bata jirata ba tai waje ummi tai saurin binta dan tunda tadan fara girma tadena cire hijabi ko ina dashi take shiga ko bacci zatai duk yadda su ummu sukai da ita taqi ita kunya takeji.
Farida ce tai saurin miqewa ta ruqo ummu haba ummu ina zaki cikin daren nan zani inga halin da yaro na yake ciki ta riqeta dan Allah ummu ki rufa mana asiri karkije dan farine fa tai dan murmushi daga gani na takaici ne tace farida sakeni koma dan mene bazan zauna inaji ina gani akashemin shi ba wai da sunan kunya.
Haba ummu aikin san babu ta yadda za'ai Yah Nasir yabari wani abun ya sami Abbakar kema kinsani ta gyada kai nasani Farida saidai nasan makircin mahaifiyarsa bata jira cewar Farida ba sukai waje ummi ta bi bayanta.
Adai daita sahu ta tara sai da suka fara tafiya yace haija ina zamu ne sunan unguwar ta fada masa.
Adai dai qofar gidan ya parker dan sahun yace hajiya mun iso ta ciro dubu ta miqa masa ya amsa ta juya tana kallon kofar gidan yace hajiya canjinki riqe tace ya juya yana murna dan be mamakiba ganin tamfatsetsen gidan da yasaukesu da alama yarinyar gidan ce ya fada.
Gidan su Abbakar
Tun jiya suke ta gyare gyare da kin tse kintse yau kam girki siketayi tun safe dan hajiya da kanta tashiga madafa ita da maryam da ummi dan yau muktar zai zo hutu da autan hajiya.
Yadda hajiya ta zage tana ta hada kayan datasan yanaso koya kai mistake yanzu ta hau fada abinda ba sabonta bane haushi duk yabi ya ishi ummi dan duk fadanda hajiya dake yawanci akanta ne koya tai mistake. Sai kace ba ita ce take kuka lokacin da zai tafiba kishin sakun takan ya motsa.
Tana sane cikin zobon da hajiya ta gama masa ta zuba zuma duda tasan bayasan zuma a abu me sanyi aikuwa hajiya ta hau fada har saida taji dama batasa ba aikuwa idonta yai rau rau kamar zatai kuka maryam ta faki idon hajiya ta mata gwalo nan da nan hawayen ya zubo hajiya kinganta ko hajiya ta cillama maryam harara fita idona maryam tunkan raina ya baci bansam tsokana ummi tasa dariya gami da mata gwalo zatai magana hajiya tace karki kawon qara aike kika fara shiru maryam tai tana hararar ummi dan tasan kobata ummi komi ba hajiya bazata mata magana ba dan duk gidan sun sani in abu ya hadaka da ummi dole kaine mara gaskiya sedai in ita da dan autane to dole ta dau rashin gaskiya.
Sun gama komi sunyi wanka inda hajiya tai tafiyarta dan cewarta bazata bar dan lelenta ta jirasu ummi su bata mata lokaci wajen kwalliyarsu ta tsiya ba.
Suma sun fito tsab shigarsu iri daya sunyi kyau sosai ummi tai daki da gudu tana kiran hajiya wayam ta gani gaji mai aiki ce take fada mata ai tuni hajiya ta tafi aikuwa ta zunburo baki tai waje tana bubbuga qafa ita ala dole taji haushi da Abbakar taci karo ya riqota yar kelen hajiya ya akaine ta kuma kumburo fuska ba hajiya ce ta tafi ta barni ba yasa dariya ba dole ta tafi ta barki ba mowanta zaizo kin zama bera tasa kuka yaya yai saurin goge mata hawayen da wasa nake muje inkaiku ta tirje ita bazata ba haba mowar hajiyarta kidaure muje kinji tawan ta dan murmusa yajata suka fice maryam biye dasu.
Seda suka Abbakar ya amshi powder gun maryam yashafa mata kar yaroncan ya rainaki yaga kinyi kuka tai dariya tanasan yayanta sosai duda duk sauran yan uwanta haka sijeji dasu ita da autan hajiya shi yada suke tsula tsiyarsu se kace yara inda azahiri shekarunta ashirin cif kazalika autan hajiya twins ne ita dashi saidai ita aka fara haifa saidama takwana biyu akama hajiya CS aka ciroshi.
Gabaki daya sunyi mamakin yadda autan hajiya ya girma inba kasani ba kai ka rantse shidin yayan maryam nema ba ummi bama.
Tun saukowarsa ajirgi hajiya na hangoshi ta gilas sai washe baki take aikuwa suna fara tawowa suka fito inda zai hangosu ganin yan uwansa wanda rabonsa dasu shekara uku kenan yasa sanyi ya ziyarci ransa.
Yana zuwa inda suke yai gun ummi wanda tunda ta hangoshi murmushinta yaqi tsayawa hajiya ta zuba musu ido eyya wato abun haka ne yar uwarka ka sani banda uwakka yasaki ummi yazo gun hajiya ya rungumeta yana cewa haba hajiyata aikema kinsan ke nafara gani kinsan kishinta ina kula wani ba itaba har in koma ana mita suka saka dariya baki daya.
Agida ummi ce tai dakinta da gudu ta fito riqe da roba tace qanina bude bakinka yasha kunu waye qanin naki ta dubi Abbakar tace yaya dan Allah waye babba yai dariya gami da daga kai alamar tunani bari in tuna kai yaya ya auta shine auta ya daka tsalle yeeee tasa kuka yaya yai saurin cewa shine qarami tai dariya muktar ya amsa yakalla gami da tabe fuska wannan wace qazantarce ta gallah masa harara gami da amshe abunta tai ciki yai saurin bunta sorry babbar yaya ya amsa ya fara sha Vanana ice cream ce tamai dan yanasanta sosai.
Sai da yai wanka yazo yaci abinci sannan suka hau hirar yaushe gamo yadinga basu labarin qasar waje basu ankaraba sukaga daya duk suka miqe sukai daki dan kwanciya.
[12/7/2017, 7:56 PM] Fadimafayau: 19
*Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*90-95*
*Godiya gareku masoyan books dina inajin dadin yadda kuke karantawa gami da addu'o'inku garenk nagode sosai ina Alfahari daku*
Wajen qarfe bakwai Babbar yayarsu ta iso gidan ganin duk suna bacci yasa tai kitchen ta hada musu kari ita da gaji da sauran masu aikin gidan tana cikin jerawa Hajiya ta fito itada ummi ummi ta daka tsalle yaya saikar yaishe tun jiya nazo kunyi bacci gami da durkusawa ta gaida Hajiya ummi tai waje.
Wajen takwas aunty zainab tazo hajiya tai ta fada dan tace tasan ita tasa dole sukayi irin wannan sanmakon bacin tasan cewa batasan tafiyar duhu hajiya wallahi seda aka idarda asuba muka tawo ahab ai duk daya nan cikin wayo zainab ta basar da batun suka shiga wata hirar.
Gabaki dayansu sun taru a falo suna fira Muktar ya sawko suka miqe suprise suka fada da dan qarfi yasauko yana murna sosai yaji dadin ganinsu.
Durkusawa yai ya gaida hajiya da sauran yayyansa kafin yaya babba tace haba autana come give me a hug i miss u sosai ya manne kai bacin jiya kika qi zuwa taroni auni din kaima haka zainan tasa dariya zonan nawan ya juya qeya bacin kinmin buqulu naso yau inzo katsina ke kuma kika wani diro da sassafe gabaki daya suka sa dariya daman sun san halinsa ba'a iya masa fakar yaya babba yai ya fada kanta yana fadin suprise hug wayyo zai karyani ta fada ya miqe yana dariya zainab ta miqe yai dinning wannan suprise din badani ba akaini a baro suka saka mata dariya.
Ita ko ummu gidan take bi da kallo yayin da wani abu dabatasan ko mene ba yazo ya tsaya mata a wuya ada tasa aranta tabar gidan kenan ko unguwar bazata qara zuwa ba sedai yau tanajin kome za'ai ba wanda ya isa ya hanata shiga.
Kukan karen da taji yafara tashi yasa tai saurin dawowa daga tunanin data tafi ta fara buga gidan daga ciki me gadi yace waye ummulkairi ce ta fada bai dauki murya ha be kuma gane sunanba anman jin mace ce yasa ya bude.
Qofar gidan cike yake da hasken wuta hakan yasa yana budewa ya ganeta yadan saki fuska a'a ummu daman kinanan idonta kuwa ya kuma cikowa da qwalla kamin tace baha Sale ina wuni ya amsa lafiya qalau ban taba zaton ganinki yanzu ba.
Ta qaqaro murmushi wanda kana ganin kasan na yaqene nima baba ban taba zaton zuwa na nanba ya gyada kai kafin ya kuma magana tace Yah nasir kuwa yazo.
Eh yazo da wani dan kyakkyawan yaro gabanta ya fadi cikin rawar murya tace ya fito dashi yace a'a tun dazu inanan banga fitarsa ba to baba bari mu shiga ciki.
Bata jira amsarsa ba suka yi ciki.
Kai tsaye bangaren yan mazan gidan tai gabanta sai faduwa yake zuciyarta fal tsoro ta dai daure ta shiga qofar da zata sada ta da gurin nasu.
Ba qaramin mamaki abin ya bata ba ganin gurin shiru ba kowa dan ada saninta dedai wannan lokacin inkazo gurin cike yake da samari kowa na sabgarsa masu hira nayi masu chat masu tireni dan duk suna da kayan yi.
Hakan yaqara tada mata da hankali da sauri tai dakunansu kai tsaye dakin da tasan na Nasir ne ta nufa ta tura a bude take sedai bakowa duk ta shiga ba kowa tabbas akwai abinda ke faruwa ta fada tai cikin gida.
Ai kuwa afalo ta taddasu tsai tsaye sunyi jugun jugun hajiya nata zazzaga bala'i Nasir ta hanga can nesa azaune hawaye nabin kuncinsa Abbakar na gefensa yana ta faman wasansa a jikinsa ba abinda ya shafeshi sai lokaci lokaci yakan daga ido ya kalli Hajiya dake faman fada.
Da sauri ummu ta qarasa ta suri danta gami da juyawa zata fita aiko mahfuz da sauri ya miqe cikin murna yayo gun ya rungumeta tai wani kukan kura ta tankada shi gami da bashi mari ya riqe gun yana kallonta dan gaskiya yaji zafin marin daga hannu yai zai rama kome ya tuna kawai yasauke hannun yana murmushi yaja tsaki gami da fadin kada ka qara kuskuren tabani dan akuya kawai.
Murmushi ya kumayi yai gabanta ya durkushe yana kuka pls ummu kiji kaina duniya ke kadai zuciyata takeso nasani inban aureki ba mutuwa zanyi ta ja hannun ummi gami da fadin wallahi saidai ka mutu in dagani kadai muka rage aduniya to gwara in mutu ba aure wallahi inda zaka mutu zanfi kowa farin ciki ta juya zata fita.
Hajiya tai saurin fizgota ganin cikin yaran nata bame iya tsai da ita tasa hannu zata fizgi Abbakar tana fadin inadai yaro jika nane dan haka baki isa kin fita dashi a gidan nanba kema kanki baki isa ki fita ba aure keda Mahfuz yazama dole.
Fizge rigarta tayi gami da fadin wallahi ko gawata ta fi qarfin auren dan iskan danki tasa hannu ta mareta har ta daga hannu zata rama ta sauke gami da fadin wallahi kinci darajar yah nasir da sauri ta faki idonta tai waje da gudu ita da ummi Abbakar na faman sheqa dariya zatonsa wasa take masa.
Mahfuz ne ya miqe zai bisu saidai jirin da ya dibeshi yasashi faduwa kasa tim da sauri kowa yayo kansa hajiya cikin tsawa take fadin ku bita ku bita dasauri su muktasir suka miqe sukayo waje dan nemanta saidai fa ina duban duniya batanan.
Ita kuwa ummu tana fita abakin gate taji an rufe mata baki da tsumma haka ma Ummi cikin qarfi aka jawota zuwa dan dakin da ke qofar wajen tanata wutsil wutsil din so ta juya taga ko waye ina abu yaci tura..............
*Da yawa suna min test wasu nakan samu in amsa musu da wuri wasu kuma sai ya jima ina mai baku hakuri kan hakan dan bawai hakan na nufin wulaqanci bane saidai abubuwa sukamin yawa anman kusa aranku F.A.Ya'u mai san masoyanta ne ako ina suke*
*Ban cika qorafi kan readers ba koma ince ni ban taba ba saidai wani abu da yadan fara batan rai dasu shine insun ma magana kadan dauki time baka amsaba wani dan rashin kyautawa irin tasa sai yafara zagi ko faden maganganu marasa dadi hakan bayamin dadi danshi rubutun online sa kaine kawai bawai rashin abinyi ba sai sha'awaryi dan kawai ina rubutu online bashi yake nufin duk sanda kaso ko kika so zaki min magana in amsaba dan kuwa inada abubuwanyi da dama masu mahin manci arayuwata fiye da rubutun online*
*Readers kance writers basu da mutimci musanman na online sai dai kuma yawancin readers masu fadin haka asannu na gane sune marasa mutinci ta yadda suke zagewa su dinga cima mutun mutinci beji ba be gani ba.*
_pls those who love my novels who are on wattpad should follow so as to read more of my novels but don't forget to vote and comment to that's the only way to show how mush u like my books_
*Don't forget to follow*
_Wattpad Fadimafayau_
[12/9/2017, 12:28 AM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*95-100*
Ruwa Hajiya ta shafawa mahfuz a fuska ya farka a gigice yana fadin hajiya karki barta ta tafi dan Allah inban aureta ba bazan iya rayuwaba hankalinta yai matuqar tashi.
Malan ka ishemu da kuka da kasan kanasanta kai sana diyar barinta a gidan nan mansur ne ke fadin haka hajiya ce ta daka masa tsawa yai shiru yana dan qunquni.
Shiko nasir jin su muktasir sunce basuga su ummu ba hankalinsa ya tashi dan tazararsu da futarta beci ace har ta bacema ganinsu ba.
Miqewa yai zaiyi waje hajiya tace ina zaka mara san yan uwa dan uwanka na wani hali zaka fice yadawo jiki ba kwari ya zauna.
Mahfuz ne ya miqe hajiya bari kawai inje gidan da take in roqota hajiya ta zaunar dashi kayi haquri yanxu dare yayi gobe maje da sassafe inyaso sema mu tafi da masu daura muku aure inma acan zata zauna ita taji shidai Nasir abin duniya duk ya isheshi ji yake kamar qirjinsa zai tsage zuciyarsa ta fito tausayin ummu duk ya cika masa zuciya.
Gidan su Abbakar.
Gidan cike yake da farin ciki kana shiga zaka san tabbas yau suna cikin farin ciki shi kansa Abbakar wasai yake jin kansa bakamar kwanakin baya ba da zuciyarsa take cikin kunci duda farin cikin da suke ciki yanzu koya ya tuna da ummu da nahfuz sai gabansa ya fadi dan baijin zai iya rayuwa batare da ummu ba saidai baijin zai iya auren matar da Amininsa yake masifar so yanajin zai iya sadaukar da komi akan abokinsa ada duda zatonsa natana da aure yanajin wataran zai iya aurenta tunda yayi yayi ya cire santa ya kasa saidai tun lokacin da ya gano ita mahfuz yake so yasa ma ransa koda zai mutu ya haqura da ita.
Kamar kullin tun zuwan muktar hutu yau kwana hudu kenan gidan cika yake da yan zuwa sannu da zuwa dare yayi kowa ya miqe yai makwansa cikin shauqi da farin ciki haka shima Abbakar saidai yana tura qofar dakin ya nemi farin cikin ya rasa haka kullin yake dan da ya zauna shi daya shikenan tunanin ummu ne ke cika shi in bacci yake baccin cike yake da ummu ya rasa yadda zaiyi addu'a kullin yake kan Allah ya temake shi ya cire masa ita aransa anman kamar addu'a yake Allah ya qara masa santa.
Juyi kawai yake akan gadon hawaye na bin fuskarsa yama kasa rufe idansa dan ko rufewa yai ita yake gani tana masa murmushinta me ratsa zuciya.
Gidan su mahfuz da sassafe ya farka dan be niyar komawa ba bayan yin asuba saidai bacci barawo yai gaba dashi ko wanka be ba yai dakin hajiya dan dama ya dade da dawowa bangarenta.
Qofar a bude take ya tura ya shiga ko taisheta beba tana zaune tana lazimi yace haji pls taso mu tafi ina tace yadan zaro ido kin mance gidan ummu taja tsaki kabari sai anjima dan ita dan kawai tana san mahfuz ne sosai shi yasa take iya haqurin jin sunan ummun dan batasan ransa ya baci anman a haqiqanin gaskiya ta tsani yarinyar sosai.
Hajiya inbazaki ba ni zani ta miqe muje suka fice sai da suka biya gidan malan habu suka daukoshi shida almajiransa guda hudu masu jire masa dalibai dan daura auren.
Bakwai dedai a gidan ta musu sunsha bugu kafin Farida tazo ta bude tana murza ido alamar bacci tana fadin ummu badai yanxu kika dawo ba sai dai ba ummu ta gani ba tadan zaro ido tana ja da baya.
Hajiya da mahfuz da sauran mutanen suka shigo suka tsaya hajiya na bin gidan da kallo ba lefi yana da kyau sosai da kuma dan girmansa.
Mahfuz ne ya daure yace ina ummulkairi pls Farida tace wallahi tun jiya da ta tafi dauko danta a gidansu bata dawo ba what ya fada pls karki mana qarya ta ce sabida me zan muku qarya.
To me yasa baki nemeta ba taja tsaki kaji malan taya zaka zo ka isheni da tambayoyi.
Nasir Hajiya ta kira tace ya sameta gidan ummu gin tana gidan da sassafiyar nan ya daga masa hankali hakan yasa yashararo mota ya tawo Allah ne kawai ya kawoshi lafiya.
Koda yazo ake fada masa ai tun jiya bata dawo gidanga hankalinsa ya kuma tashi cikin tsoro da rawar murya yake tambayar Farida.
Farida dan Allah ki fadan gaskiya da gaske bata dawo ba ta gyada kai cikin kwalla dan itama yanzu hankalinta ya tashi wallahi yaya bata dawo ba ta kirani bayan wajen awa uku da tafiyarta tace ai an dai daita komi yanxu dan haka a gidan zata kwana salati ya saka Farida me yasa baki kirani ba tace ai saida ta bani kai a waya ka tabbatar min hakane batunta innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni kuma Farida wallahi muryarka naji.
Aikuwa mahfuz yai kansa ya shaqeshi yana fadin wallahi saika fito min da masoyita mugu kawai da sauri Nasir ya fuzfe wuyansa ya tankadashi baya kai malan bansan hauka kabarni inji da abinda ke damuna.
Ita kuwa Hajiya can kasan ranta dadi taji da batan Ummu dan gaskiya batasan ko kadan danta ya aureta dan kawai ta fuskanci in bai aureta ba komi zai iya faruwa zai iya mutuwa.
Wayarsa Nasir ya dauko ya fara kiran Aisha qawar ummu batare da la'akari da cewar ai safiya bace bugu uku ta dauka cikin muryar bacci tai sallama a gaggauce ya amsa bai jira tace komi ba yace Aisha ummu tazo gidanku kuwa ta gyada kai kamar tana gabansa tace a'a me ya faru fatan lafiya bai bata amsa ba ya katse ya fara kiran Fatima ita ma din haka ne duk wadda yake da number dinta ya kira ummu bataje ba.
Jiyai qafafunsa sun kasa daukansa ya tsugunna gami da dafe kai dan yadd yaji yana sara masa.
Duk inda suke saka ran ko ummu taje sunje ba ita ba dalilinta hankalinsu duk ya tashi sun rasa me zasuyi cigiya suka kai gidajen radio.
Hankalunsu bai qara tashi ba sai da police suka tsinci kayan Abbakar da wayarta a wani kango da ake zube shara hijabin ummi anan dan gaba da qofar gidansu mahfuz din.
Gidansu Abbakar
Muktar ke magana yaya wai me nayima Yaya mahfuz ne tunda na dawo baizo ba Abbakar yai dan murmushi kwana biyu bai cika jin dadi ba inajin jikin ne ka bari anjima maje mu gano ko lafiya to yaya yace.
Abi ne dan gidan zainab keta sukuwa kan muktar yanata wasansa ta sauko dauke da jaka Abbakar ya miqe ya amshi jakar qanwar an an gama shiryawa tai dariya bari yaya babansu Abi ne yace lallai lallai inshiryo in dawo gida nayi nayi yabari in sati biyu yaqi.
Yadan zaro ido sati biyu tab ai kwana biyar dinma yayi qoqari wallahi inni ne ai kwana daya ma sai ikon Allah zakiyi tadan zaro ido tab kaji yayan nan kace kulle zakayi yai dariya no ba haka bane kawai dai ni atsarina ba zuwa akwana ko kai dare tab matarka ta banu koda yake kai ko yar budurwar ma baka da ita gabansa ya fadi ya tuno da ummunsa yai saurin cire sa din yaha fadin ba tawa bace azahiri yai dariya haka nace miki bani da ita.
Ta zauna yawwa yayana nakaina fadamin ya miqe to sarkin san gulma bazan fada ba yai waje da kwatin nata dan kai mata mota.
Wajen biyar Abbakar da muktar suka fito dan zuwa gidansu mahfuz bayan tafiyar zainab.
Gidansu mahfuz.
Yadda Abbakar yaga mutanen fidan basa wani nishadi kamar da kana ganinsu kamar marasa lafiya yasa yasha jinin jikinsa kasan tuwarsa mutun bame san shiga sabgar kowa ba yasa ya basar yai bangaren hajiya.
Sun gaisa ba tabo ba fallasa ta fara tsokanar muktar a mutanen qasar waje haka ka girma jibeka kamar bakaine ka tafi kana dan tatsitsi sukai dariya gabaki daya.
Abbakar ne ya miqe yai dakin da yasan mahfux ya koma yabar yajiya da muktar suna ta fira.
Kwance ta taddashi yana kallon fanka sake faman wulwulawa wanda har Abbakar ya zauna mahfuz baiji shigowarsa ba.
Saida ya tabashi ya dawo dedai ya muqe zaune Aminin yaushe kashigo yaidan murmushi yanxinnan tunanin me kake cikin kwalla yace ummu gaban Abbakar ya fadi to me ya sameta.
Ummu ta bata what ya fada gami da miqewa yaushe me yasa baka fadanba cikin tashin hankali yake maganar mahfuz ya dafa shi kaima ka damu ko aminin nasani daman nasani Abbakar dina me damuwa da abinda na damu dashi ne.
Wai garin ya ta bace din nan mahfuz ya bashi labarin komi hankalinsa ya tashi jiyai jiri na dibarsa yai saurin zama gami da riqe kai shikenan an sace masa ummunsa wataqilma yan yankan kai suka tafi masa da ita.
Bai taba zato da tsanmanin haka yake san ummu ba irin tanzu yasan yanasanta da yawa anman yadda zuciyaraa ke bugawa hawaye na bin fuska bama yajin me mahfuz ke fadi yasa ya tabvatar indai ummu da gaske ta bace ansace ta komi zai iya faruwa gareshi.
Miqewa yai zaiyi waje jiri ya dibeshi dishi dishi yake gani yai karo da bango nan yayo baya luuuu yai qasa mahfuz ya miqe yayo gunsa yana kiran sunansa.........
[12/11/2017, 11:59 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*100-105*
Cikin sauri ya dago shi mamaki ne ya kamashi ganin Abbakar na murmushi daurewa Abbakar din yai ya miqe sannu mahfuz take cewa kawai ya gyada kai badai kaji ciwo ba ko ya kuma yin murmushi haba yar wannan faduwar sukayi dariya duka Abbakar yai waje majfux na biye dashi.
Muktar ne ya miqe yaya har ka fito eh naga magariba ta kawo kai saida suka gaisa da mahfuz shima ya masa tsiyar girma da yayi suka fito dan barin gidan.
Tafiyama dagyar yake yinta dan qarfin hali kawai yai anman dishi dishi yakeji gashi har yanzu jirin be gama sakinsa ba.
Masallacin sake qarshen lokon yai bari in je masallaci kaje ka fadawa Hajiya nashiga masallaci kartaga mun dade inyaso sekayo alwala ka tawo to yaya yace yai gida.
Yana shiga masallacin ya zube ya dade riqe da kansa kafin ya iya kwantawa sai da ladan yafara kiran sallah ya miqe yana bin kiran sallah din yai waje danyin alwa.
Koda ya yayo alwala dinma komawa yai ya kwanta yama rasa meke damunsa dan ayanzu bazai iya cewa ga abinda ke damunsa ba shi dai yasan kawai baya da lafiya.
Ita kuwa ummu tana fitowa daga gidan rasa inda zata tayi tayi qofar gidan da gudu jin datai an kamota yasa ta kwalla qara jin qararta yasa aka rufe musu baki dakin me gadin gidan taga anyi dasu zullo kawai take tana qoqarin juyowa dan ganin waye ya riqeta ta kasa.
Muryar baba me gadi taji yana fadin zan bude miki baki anman dan Allah kar kiyi qara gyada kai ta shiga yi alamar to ya saki hannunsa kafin tace wani abu yace karku fito ina zuwa.
Gurin gadinsa ya koma ya zauna yana zama saiga su muktasir tambayarsa suka shiga yi koyaga ummu eh yace musu naganta sun hau wani adai dai ta sahu da yazo wuce oppps suka fada gami da komawa cikin gidan seda suka jima da komawa ya miqe yai dakinsa.
Ummu ce cikin kuka take tambayarsa me yasa ya kawosu nan yai shiru kafin yace inda na barku kun fice tabvas kuwa zasu ganku su kamoku kuma dolene ki auri mahfuz din tadan kalleshi da mamaki wato duk yasan me ke faruwa.
Kamar yasan abinda ke ranta yace tun wancan lokacin naso temakonki saidai bani da dama yanxu ki miqe zansa akaiku titi inyaso saiki koma inda kike da zama to tace masa gami da masa godiya yasa dansa yakaita har titi suka hau dan sahu zuwa gidan ta.
Koda suka koma gida farida ta rufe gidan han yasa tabaima ummi Abbakar ta bude gidan tace su jirata a farfajiya tai cikin gidan.
Ahankula ta ke tafiya hartai dakinta ta dauko ATM dinta da yan kayan Abbakar sai takardun secondary dinta da sauran takardunta masu mahin manci da kala uku na kayan ummi ko nata bata dauko ba takulle dakin tai waje.
Saida ta kulle gidan sannan ta amshi Abbakar ta goyashi ummi ta kalleta anti ina zamu qauyenku tace can zamu can zan koma ummi.
Shi ko Abbakar bayan an idar da sallah yaita roqon Allah yasa ummunsa tana da rai cikin qoshin lafiya ya bashi lafiya kodan yasamu damar nemota ganinta da jin tana cikin qoshin lafiya koda bata matsayin matarsa ji yake yafiye masa wannan batan nata.
Sai isha ya koma gida bayan ya danji dadin jikinsa.
Abun duniya duk ya isheshi gashi ba sch balle ta tambayi qawayenta da ya saba ganin su tare gashi shi bashi da number din kowa.
Gidajen yada labaru washe gari ya kai cigiya gamida police stations yini daya tak duk yabi ya fada kana ganinsa kaga maras lafiya idanunsa duk yayi tsuru tsuru hankalin hayarsa gabaki daya ya gama tashi gashi tambayar duniya yaqi fada mata meke damunsa.
Inma ta tambayeshi sai dai yai dariya yace haba hajiya nifa wallahi gaskiya na fada miki ba abinda ke damuna kedai kawai kike ganin na fada anman garau nakeji na.
Mahfux ne zaune wani abu ne yabi ya tsaya masa arai ya kuma kasa gane dalili bakuma komi ke damunsa ba yadda yaga Abbakar gabaki daya ya kasa zaune yakasa tsaye yana wani nuna yafi shi jin zafin bacewar ummu yarasa dalilin Abbakar nayin haka.
Yanke shawara yai na yaje yasameshi ya fada masa me yasa yake abinda yake kan bacewar masoyiyarsa.
A qofar gida ya sami Abbakar yanajin radio ganin mahfuz yasa yasaki fuska gami da kashe radion sin gaisa gami da qara jajanta wa juna batan ummu.
Maganar da mahfuz yai ne tai mugun baima Abbakar mamaki cewa yai Wai Aminin mene naka nawani ishisshirewa wajen nemo ummu jibi yadda kabi kawani jeme wanda duk ni ya kamata inyi haka matsayina na masoyinta me shirin aurenta.
Dariya Abbakar yai masoyi manya ka mance ni kuma masoyinka ne aini me damuwa da abinda ka damu dashi ne mahfux ya washe baki hakane fa.
Kuma banda abinka mahfuz ka mance ummu frnd dina ce da muka shaqu achat ko ka mance aiko dan shaquwarmu na damu ko mahfuz ya daure fuska bai shiru ba ya qara da cewa kuma kamance ita student dina ce wadda ada nasota kamar raina naso aurenta.
Cikin fushi mahfuz ya miqe kai malan dakata bansan rashin mutunci haba dole ka damu mana tinda abar sanka ta bace Abbakar ya miqe gami da dafa mahfuz haba Aminin bakaji nace Ada ba yaje tsaki gami da ture hannun Abbakar din ya qara da cewa to tsaya kaji wallahi kama cire ta aranka inba haka ba zan rufe ido na cire amintar mu wallahi in cima mutinci kai barifa kaji akan ummu zan iya kawar da mutun wallahi.
Ido kawai Abbakar ya bishi dashi yakasa cewa komi ganin yadda mahfuz ya mance da shi waye dinsa kan mace yahau ci masa mutunci.
Atsaye ya barshi soro ro kawai yana kallon ikon Allah.
Ita ko ummu sun hau dan sahu kan yakaisu tasha suna cikin tafiya ummi ta dubi ummu tace auty zuwa qauyenmu da matsala ta dubi ummin me yasa.
Cikin kuka take magana wallahi in mukaje koro mu zasuyi me yasa sabida ummana bata gidan Abbana sai abinda umma rahane ta ce masa ita tasa aka kawoni ma aikatau shiru kawai ummu tai tama rasa abinda ke mata dadi.
Can ummi tace sai dai mutafi magarya inda ummana ke aure ummu batasan sanda ta rungume ummi ba ta farin ciki.
Me dan sahun har ciki yakaisu shi ummu ta roqa ta baima kudi ta kira farida ta bashi kan shine nasir kasantuwar tana bacci yasa bata dauki murya ba.
Dubu hudu ta bashi yaita godiya suka shiga motar da sukaji tana kiran babura magarya saura mutun biyu da sauri suka shiga.
Mota na shirin tashi tacema kwandas dan Allah ga dari biyar tukwici ga kakarbi wannan kasiyon sim da kati na sauran canjin ba shiri ya amsa ya tafi.
Bai jima ba ya dawo dauke da sim da kati ta amsa tana godiya gami da cire na kan wayarta tasa sabon.
Goma dedai motarsu ta tashi dan barin kano wani hawaye ne ya tawowa ummu dan gabaki daya bata taba zaton kwai rana irin wannan da zatazo mata ba ace wai ita take shirin guduwa tama koma wata qasar ba tare da sanin koma nata ba tunda magarya Niger ce wayyo ni ummu naga rayuwa...........
Zan cigaba insha Allah.
[12/14/2017, 2:44 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*105-110*
Sunyi nisa sosai a mota masu bacci nayi masu kalle kalle nayi cikin masu kalle kallen harda ummu gabaki daya ji take ranta babu dadi ji take kamar tasa motar ta tsaya ta sauka.
Duda kasantuwar garin yanayin sanyi gashi dare ne kukan tsin tsinye kawai kakeji gwanin dadi sai dai ita gun ummu ba abinda ke mata dadi baccin ma kwata kwata batajinsa juyawa gefenta tayi taga ummi nata sharar baccinta ta kalli hannunta inda danta ke maqale a qirjinta shima baccinsa yake har yana dan murmusawa akaro na biyu da tausayinsa ya cikata.
Tun randa aka miqo mata shi cikin zanin goyo randa ta haifeshi bata qara jin tausayinsa irin na yau ba aranta take qara tausaya masa koya zai tsinci rayuwa inya girma ko zai iya jure qalubalen dake gabansa wata kwalla ce ta zubo mata tai saurin gogeta duda kasantuwar motar da duhu ba wani zaiga hawayen ba.
A dai tashar babura suka yada zango inda da yawa a tashar zasu kwana dan daya tayi suma motarsu anan zata kwan kafin gobe ta tashi zuwa magarya.
Ba haka ummu taso ba taso cikin daren nan subar Nigeria sai dai ba yadda ta iya duda hankalinta bai yi zaton wani zaiyi tunanin suna jigawa ba balle azo babura nemansu hakan yasa ta dan samu damar yin bacci.
Da safe kafin mota ta tashi da yw na cikin motar tasu anan babura zasu sauka hakan yasa sai anyi lodi ummu barin ummi da Abbakar tayi ta fita dan nemo musu abinda zasu ci.
Sai da taje ta ciro rabin kudin account dinta ta sayo kaya kala hudu duda ba wasu masu kyau bane sai dai sun fi babu.
Sha daya dedai ta musu agarin seda suka hau mashin yaqarasa da su.
Yanayin garin ba qaramin firgida ummu yaiba qauye ne sosai ji take daqyar zata iya rayuwa a garin sedai babu damar komawa tunda ita bata da kowa wanda suke natan su sika fara gudarta.
Ai kuwa innar ummi tai murna sosai da ganinsu mijinta baya nan ya fice tun safe sai mahaifiyarsa sin gaisa cikin mutunci musan da ummu ta bata tsabar biredin da tayo musu tai ta godiya.
Malan tanimu shine sunan mijin innar ummi ko da ya dawo shima yai murna da ganin su ummun ba dan komi ba sai shima anbashi tsabar biredi harda madara yaita murna yana sa albarka duk ya mance da kishin da ya debo ana fada masa diyar matarsa ce tazo.
Yau satin su ummu biyu a gidan har sun fara sabawa da rayuwar garin dan hat ummu tai qawa me suna mero sun saba sosai dan mero mutince me san mutane kullin Abbakar na gunta hakan yasa ummu qara santa abinka da uwa kunsan ance in kanasan abin gurin uwa to kaso danta.
Yau malan tanimu mahaifiyarsa ta zugeshi tas hakan yasa ya fito yanata tafka bala'i yaha kiran ummu ita da ummi da gudu ummi ta fito riqe da Abbakar ahannu dan ummu bata nan mairo ce ta jata zuwa niyame dan canzo kudinta daga na nigeria zuwa na niger.
Kayan su yake watsowa waje ni na gaji da zamanku a gida tun ina kawaici na fiskanci baku fuskanta ba haka kawai bani nai cikin kiba ki dawo min gida da zama to wallahi bazai yiwu ba.
Kuka take tana roqonsa ya yadda ummu ta dawo yaqi ita kuma inna ta qi ko fitowa daga daki balle ta bashi haquri ya kyalesu azahiri ba qin fitowa tayi ba kasan tuwar ummi yar fari kuma da sanin halin mijin nata yasa taqi fitowa dan tasan in tai magana zai iya hadawa da ita ya kora.
Ummu ce tai sallama ta shiga ganin me ke faruwa yasa ta shiga da gudu aikuwa ya daka mata tsawa cikin muryarsa ta buzaye dakata daga nan kubar min gida ynx ynxunnan durqusawa tayi tana kuka tana roqonsa kinga malama wallahi sai kun tafi kinjini ko.........
Nigeria
Yau watan ummu guda kenan da bata har sun koma sch inda zasu shiga level 4 su Aisha duk sun sauya kullin tunaninsu ko ummu na lafiya gashi sinyi sabo sosai da Abbakar dinta da sunga yaro sai suga kamar shi.
Zaune suke suna tattauna lecture din yau dan ta musu wuya wayar maryam tai qara ta dauka wata qara ta saki tana fadin ummu me yasa kika gujemu da sauri Fatima ta amshe wayar danjin wace ummun ce.
Ke banza wallahi wayarku bata da anfani inji ummu na dade ina kiranku ace akashe wallahi kin daga mana hankali sosai wallahi Aisha ta amshe wayar pls ummu ina kika shiga kin tafar mana da yaron mu wallahi munyi missing dinsa sosai eyye wato ma shi bani bako eh mn tunda ke haka kikaga ya fiye miki pls ina kuka tafi kedai bari kawai muna Niger what niger fa kika ce wa kika sani acan tai dariya mutanen azziki mana dil wayar ta katse kiran duniya taqi shiga sikai saving din number din gami da ci gaba da tattauna matsalar rayuwa sinma mance da lecture din yau din.
Yau littinin Abbakar ya yanke shawarar kiran qawayen ummu dan yaji ko zai sami labarin ta tinda yasan mata sau tari suna daukan abota da mahin mance sukan fadawa abokansu sirrinsu.
Ai kuwa yana gama lecture yace Fatima keda qawayenki su Aisha ku samen a office aikuwa hankalinsu ya tashi sosai dan tunda ya shigo suke surutunsu gashi kuma agaba suke zaune ko tsoeonsa basa ji jin abinda yace ne ya sa sukai zaton hukuncin surutu zai musu.
Sun jima a Bus stop sina jiran mota bata zoba gashi office dinsa a old side yake can physics department miqewa sukai danyin yellow bus stop ko zasu samu.
Mota ce ta tsaya gabansu dan rage musu hanya ganin me motar yasa hankalinsu ya tashi Abbakar ne tsuru tsuru sukai suka kasa shiga ya leqo kufa naje jira dasauri suka shige gabaki daya baya duk su shiga wata kan wata dariya suka bashi ya juyo ke Hafsa keda Aisha ku dawo gaba da sauri suka fito suka koma gaba jiki na rawa dan tsoronsa sukeji sosai dabashi bane banajin zasu shiga motar.
Adai dai gurin parker motocin staff ya fakar motar suka fito da sauri sukai gun office dinsa.
Sunfi minti goma a tsaye bezoba fatima da hafsa suka hau mita aiki kawai yazo ya shanya mutane a guri kamar bashi ya ce muzoba ya kuma daukomu.
Basu ankaraba sukaga yana bude office din suka hau kwalalo ido beko kallesu ba yai shigewarsa ciki.
Kasa shiga sukai daqyar Halima da Amina suka fara shiga kafin daga bisani sauran su bi bayansu.
Yadda sukai zuru zuru ya bashi dariya duda ransa babu dadi.
Daman batun qawarku zan muku ko kun san inda take ko wacce tace bata saniba rabonsu da ita tun kan ai hutu bakomi kuje kawai suka fice sin sin dan har yanxu jikinsu da zuciyarsu be gama yadda da kan ummu ya kirasu ba.
Abbakar ne zaune a office dinsa abin duniya duk ya isheshi mahfuz ya dena shiga sabgarsa ga hajiyarsa ma kwata kwata fishi take dashi dan yaqi fada mata meke damunsa.
Alamun kwan kwasa kofar da yaji ne yasa shi dawowa daga dogon tunanin da ya tafi gami da fadin yes shigo aka shigo da sallama.
Captain din su ummu ne wanda ada kullin se yagansu tare da ummun sir daman assignment dinne an hada ya fada yana miqo masa ok ajiyesu nan.
Har yakai bakin qofa yaji ance Ahmad da sauri ya juyo dan yayi mamakin sanin sunansa da yayi danshi yasan kawai lazy yake cemasa ko a inane ko waya ya masa kan yasanar da yan class dinsu wani abu zaiji yace lazy ayi kaza da kaza.
Daman maganar qawar zanwa saida gabansa ya fadi wake nan Ummul khairi yadan zaro ido wadda ta bata eh ita pls badanni ba inkasan inda take dan Allah ka fadan.
Shiru yai na dan wani lokaci kafin yace jiya tamin waya dai sai dai ni bata fadan tana ina ba ya fada miqewa Abbakar yai what me tace ma to cewa tayi kawai ta bugo mu gaisa to muga number din sir ai unknown ce number din tayo hidden eh mugani kawai zanso gani ya fada yana miqo hannu jikin Ahmad ya hau rawa dan azahiri qarya yake bata boye number dinba ta kuma fada masa inda take rasa abin yi yai sai ji yai ya daka masa tsawa ba dakai nake bane baisan sanda yace tace min tana niger..........
[12/14/2017, 2:46 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*110-115*
Niger
Waje ya kora su ummu tana kuka ummi na kuka kayan da ta riqo a hannu kawai ta dauka sukayi waje ya banko qofar kwanon langa langansa yai ciki yana ci gaba da mita da fada.
Sun dade a tsaye hankalin ummu atashe tama rasa abinda zatai gidansu mairo qawarta ta nufa.
Mairon na tsakar gida suna ganin kayan da ummu ta siya mata sai murna take shigowar ummu ta ja hankalinsu da sauri ta miqe tai gurin ummun tana tambayarta me yasa ta kuka.
Cikin kuka take musu bayani hankalin innar innar mairo ya tashi ita da kishiyarta can innar ta nisa mero ba kince tana da kudi ha eh inna to kinsan malan wato mijin innar ummi da san kudi taje ta bashi wani abin zai bari tazauna kinga nan daki biyu garemu daga nawa sai na antinki.
In munce zata zauna anan ba guri tunda kuma kullin cikin sauyin daki kuke ran kwana na ku koma daya dakin ran kwanan ta ku dawo nawa kuma duk atunkushe can din ne dai da guri shiru ummu tai kafin tace to inna kije ki masa bayani zaifi fuskantarki to shikenan muje.
Har sunkai bakin qofar gidan ummu taja ta tsaya Innar mero ta shiga aiko yana ganinta yayo kanta da fada inma kinzo dan ban haquri bazan haqura ba gida nawa dole su tafi.
Ni ba haquri nazo baka ba shawara ce kasan yarinyar da sukazo da yar matarka qawar mero na ce ko ya gyada kai alamar eh kafin yace to ni me yashafen da abotarsu eyye to ka tsaya kaji mana.
To mero ta sanar min yarinyar me kudi ce sosai dan yanzu ma daga niyame suke da suka fita tun safen nan sunje sun maku siyayya kuma ta fadawa meron nawa inta dawo zata baka yan wasu fam inaji fa sun kai dubu hamsim na garinsu Nigeriya ya zaro ido kai innar mero tai dan murmushi dan ta gane ta shawo kansa to ai ba kai daya tace zata baima ba har gwaggwo dije ta sayoma shadda sai alokacin gwaggwo tai magana wai to tn inane maza kije kice ta dawo in bazai bata daki ba ni sai inkaita gidan bala wato qaninsa da sauri yace kinji inna wane bala kuma daman ke kika sa na koresu.
Da sauri innar mero ta kira su ummu suka dawo ciki gwaggo ita da shi suka maida musu kaya aikuwa ta basu kayan da ta sayo musu shaddoji ne sai atamfa kala uku uku innar ummi kala biyar sukaita murna.
Ta zaro kudi ajakarta ta hannu ta baima malan jiki na rawa ya amsa yana lissafawa dan tun da yake bai taba riqe kudi masu yawan wadannan alokaci guda da sunan nasa bane gwaggo ma aka irgo aka miqa mata miqewa tai ta hau murna harda rawa.
To ke yar nan me yasa tun farko baki fada mana ke attajira bace tai murmushi ai gwaggwo lokacin da mukazo kudin Nigeria ne dani yau naje na samo canji kudin ku.
Innar ummi na jinsu hankalinta duk atashe sai dai suka shiga daki ta fito tai dakin su ummun.
Nigeria
Cikin farin ciki Abbakar ya zagayo ya dafa Ahmad yaushe ta kiraka tun wancan satin anman wallahi ni bata fadan wace unguwa take ba kuma inna kirata din bata shiga kwata kwata.
Ban number din ya tsaya qunquni zaka ban ko kuwa yai saurin daukowa ya miqa masa wayar nemomin number din ya dubo masa ita.
Tabas code din Niger ne wata +227 murmyshi ya saki aqallah yanxu yasan inda ummunsa take ya miqa masa wayarsa yace ka iya tafiya Ahmad ya fice cike da mamakin me malamin nasu zaiyi da number din ummunsa.
Sai da Ahmad ya fita Abbakar ya fara kiran number din sedai da gaske ne bata shiga hankalinsa atashe ya fara tunanin yadda zaiyi gobe ya ganshi a Niger.
Gashi farkon semester can ya yanke shawarar daukar hutu dan tun da ya fara aiki be dauka ba shaidar bashi da lafiya ya bada yana buqatar hutu dan neman lafiyarsa aranar ya bada komi zuwa gobe yake saka ran ayi signing.
Yai muguwar sa'a yasamu anyi masa komi aiko yai murna sosai tunanin me zai cewa hajiyarsu ya haushi dan yasan koya sha giyar wake be isa yace mata neman mace zai je gari har ya Niger.
Ko agida rasa me ke masa dadi yai yai uban taquri adaki iyakar tunaninsa ya kasa tunanowa ummi ce ta shigo dakin nasa riqe da littattafai tana kiransa yah kana ina ne kwata kwata bejita ba.
Ta shigo dakin yanayin da ta ganshi yasata yada books din ta qaraso gurin tana tambayarsa lafiya.
Hawayen fuskarsa ta hau goge masa jin haka ya dawo dashi daga tunanin da ya fada adan razane ya kalleta zatonsa hajiya ce.
Ummi lafiya naga kina kuka ta kalleshi yah tun dazu fa nashigo baka ganni ba kanata hawaye yai dariya na tuna da baba alhaji ne tai dan dariya yah pls yau daya ka fadan damuwar dan Allah ya kalleta tunda yake be taba ganin qanwar tasa ta zama serious irin yauba yai mamaki haka kawai yaji yana san fada mata.
Kimin alqawarin ko muktar bazaiji ba wato abokin taqwaitakarta. Dan shine amininta.
Allah yaya bazan fadawa ko hajiya ba ma yai murmushi kawai kafin ya bata labarin komi game da ummu har ya zuwa hutun da ya dauka.
Ta nisa cike da tausayin yayan nata yah kawai kacema hajiya a faculty dinku aka turaku maryam Abacca da ke Niger din dan yin wani research ai zata yadda be san sa'adda ya rungumeta yana murna ba that's my little sis shawarar ki tayi sosai wallahi ya dagata yana murna.
Itama dariya take ganin yayan nata cikin farin ciki.
Ya sauketa ta dauko books dinta yah pls aikinnan zaka koyan ya amsa ransa fal farin ciki ji yake kamar ma yaje yaga ummunsa sun dawo tare dan yaci alwashin inyaje tawo da ita zaiyi ya kawowa hajiyarsa ita.
Cikin jin dadi suke karatun sosai ummi take ganewa muktar ya shigo riqe da rake yabi littafin da kallo ke ynx wannan ne se an koya miki ta watsa masa harara ni sa'arkace yasa dariya to da sa'ar wace eyye.
Abbakar yace kai bansan rashin kunya fa bata girmeka bane ya kuma yin dariya da kwana biyun danma ta tureni ne ta fito ai da tuni ni zan fara fitowa Abbakar ya harareshi ko awa daya ne dole ka vata girma tunda ta girmeka dai bakaji kai hajiya ke cewa auta ba ummi ta saki qara kai yaya nicefa auta Muktar yai mata gwalo andai fi sona ta miqe ta bishi da gudu Abbakar yasa dariya yana san qannensa da yawa ya shuge toilet.
Hajiya na daki tana lazimi Abbakar ya shiga ya maya bayanin komi duda gabansa sai faduwa yake dan ba sabon sa hane qarye tsoronsa karta gane aikuwa yai sa'a bata fuskanta ba sai saka albarka take da addu'ar Allah ya sa adace ya kiyaye hanya.
Washe gari da sassafe a filin jirgi ta masa dan ta sama zai tafi tara dedai suka tashi .
Basu wani jima ba suka sauka a filin jirgi na Niger dake maradi Abbakar ji yake kamar atake yana saukowa daga jirgi zaiga Ummunsa.......
[12/14/2017, 6:01 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*110-115*
gidan da ummu take.
Innar ummi ce ta shigo ummu na gyara musu kaya ta ja ta zauna a gefen katifar su ummun tace ummul kairi zuwa nai muyi magana ta fahinta da ke jin haka yasa ummu ijiye kayan tazo ta zauna dab da innar.
Inna ta dafa ta ummu ada na yadda da abinda diyata ummi ta fadan kedin uwaddakinta ce wani abu me mahin manci ya baro daku da gida se dai ynx ganin kudin da kike kashewa hankali kwance yasa nafara tunani wani abu daban ummu dan Allah ki fadan gaskiya ke wace neme alaqarki da yarinyata inaji ajikina kamar baki da gaskiya.
Ummu tasa kuka wallahi inna abinda kike zato ba haka bane gaskiya muka fada miki ni ban yadda ba dan xuciya na fadan kodai satowa kikai ko kuma ke din karuwa ce ganinki danai da yaro qarami ko yaye ne isa ba balle kuka ta kuma tashewa dashi tace inna zan fada miki ko ni wace wallahi ni ha barauniya bace ba kuma katuwa ba kudi nawane na gado nane ban taba dauka ba sai yanzu.
Tashare hawaye kafin ta maida hankalinta sosai ga innar tace kamar yadda na fada miki ban kuma miki qarya ba sunana Ummul khairi yasir mahmud tarihina ya fara kamar haka.
Mahaifina haifaffen garin kano ne su tara mahaifinsu ya haifa mahaifina shine na taran wato autansu Bashir shine babba sai muktar muhd ha ukunsu Dahiru na hudu salisu da salman sune na biyar wato yan biyu ne sai kamal na bakwai Aliyu na takwas.
Lokacin da aka haifi Aliyu saida yai shekara goma sha hudu aka haifi mahaifina lokacinma mahaifinsu ya tsufa hakan yasa duk suka dauki san duniya suka dorawa Yasir yayyensa gabaki daya maza ne suma duk soyayyarsu sun dorata akan Yasir ne ko wanne yasamu abu to yasir zai kawowa.
Lokacin da aka yaye yasir ne Mahaifinsu ya dauki gidan da suke ciki ya baima yasir dan yanzu baya wani aiki yayyaensa basu ji komi ba dan sumadin kowanne da irin abinda aka bashi azahiri na yasir dinne yasamu abu mafi qanqanta.
Shekarun yasir uku Allah yaima mahaifinsu rasu babban yayansu wanda ya dade da kammala masters dinsa yana kasuwanci shi ya ci gaba da kula da kannensa da mahaifiyarsu azahiri Yasir shi Yaya bashir yake dauka matsayin mahaifinsa dan kuwa komi shi yake masa duda kuwa sauran yayyunsa ma ba abarsu abaya ba azahiri yasir dan gata ne nagaba da baya danshi besan wani abu waishi maraicin uba ba.
Yasir yaha jss 1 yayansa yai aure aikuwa mahaifiyarsu ta tubure ita danta bazai barta ba dole agidansu ya yanki guri yai bangarensa duda cewar sunsan da gida bana gado bane gidan yasir ne.
Yasir yana SS 2 sannan matar yayansa ta haihu dan qin yadda tai ta haihu lokacin farkon auren dan tace karatu zatai ta haifi danta namiji yaci sunan kakansa wato mahmud suke kiransa da mu'allim.
Shekarunsa biyu takuma haifar danta namiji yaci sunansa Yasir alokacin qannen mijin hudu duk sunyi aure suma agidan suke zaune wasu cikinsu ciki ke garesu daya harda danta me suna Abul fathi.
Duda cewar yayun Yasir sunyi yaransu saidai fa har yanzu sunaji da qanin nasu komi yakeso ake masa har sunfi kulawa dashi fiyema da iyalansu hakan yasanya duk matansu jin haushin yasir din karma matar Yah bashir tsanar duniya ta dauka ta dora kan Yasir dan yadda take ganin wani abun intace amata yasir yace yn buqatar wani abin shi mijinta kema yace ita tayi haquri sai yasamu kudi abinda bata saniba shi yasir da kudin gadonsa ake masa komi tunda sun yanke sai ya kammala degree zasu bashi gadonsa.
Shekarun Yasir goma sha biyar yai candy yana murna zai tafi jami'a dan yaci jamb saidai akace sai yajai 16 years aikuwa ya tashi hankalinsa danshi baiso ace yau wani cikin dan ajinsu ya rigashi tafiya jami'a.
Yadda yabi ya rame ya tsangwami kansa yasa dole badan yayyensa sunso ba suka aikashi india danyin karatun da yafi so wato karatun hada magun guna aiko yai murna sosai saida zai tafi ne ma yai kukan rabuwa da hajiyarsa da yayyensa dan yanzu yasan duk yayyensa ne sai dai har yanzu bai daina kiran Yaya bashir da Dady ba hakan nama yayan nasa dadi.
Shekarar da Ya tafi ne matar Bashir ta kuma haihuwar namiji yaci sunansa mansur ashekarar yan biyu da sauran yayyen Yasir sukai aure Yasir be samu zuwa ba saidai an tura masa da hotuna yai murna sosai yakuma so yazo din.
Shekarun ashirin cif ya kammala degree dinsa baibi shawarar kowa ba ya cike komi nayin masters dinsa ya bai samu wata matsala ba haka ya cigaba da karatunsa dan bashi da wata matsala yakanzo hutu gida ahankula ya fiskanci tsanar da matan yayyensa suka masa saidai ko ajikinsa.
Koda ya kammala masters dinsa ya fara aiki da jami'ar da ya kammala dan result yayi kyau sosai a nan yake lecturing ya kuma aiki a wani babban kanfani na sarrafa magun guna.
Lokacin da ya cika shekaru ashirin da biyar mamaki yayyensa suka bashi har india sukaxo dan tayashi murna yaji dadi sosai harda Hajiyarsa.
Dakyar ta yadda ta koma Nigeria da cewa tayi kodai ta zauna gurinsa ko kuma ta ya bita su tafi dan ita ta gaji so take yai aure dakyar ya lallasheta kan zaiyi auren bada jimawa ba tai tamasa addu'a kawai.
Tun bayan haihuwar mansur da Rabi matar tayi yau shekaru bakwai bata kuma haihuwa ba yaranta hudu hakan yasa ta tashi hankalinta dan matar mahmood ma yaranta shida kuma ta rigata shigowa gidan aure.
Cikin ikon Allah ta sami wani cikin murna kam ba kama hannun yaro cikin ikon Allah ta haifi danta namiji shima taso mace ce saidai yadda mahaifinsa wato mijinta yai murna yasa itama tayi sosai cewa yai ta zabi sunan da takeso asama yaron tace Mahfuz san duniya ta dauka ta dorawa mahfuz ko yayyesa ne suka masa abu to yanzu zasuga bacun ranta.
Lokacin da Yasir ya kammala PHD dinsa ya cika shekaru Talatin cif lokacin ma harda mahaifiyarsa akazo dan tayashi murnar karbar Doctoring degree dinsa as pharmacist bayan an gama bikin karbar Hajiyarsa tasa kuka ita dole yai aure inba so yake ta mutu bata ga jininsa ba
Ya tabbatar mata kwanan nan zaiyi aure tai murna sosai.
Wani aiki ne yakaisu Malaysia wata university da ake kira university of malay acan ne cikin daliban da yake koyarwa ya hadu da wata yarinya yar Jordan ce sun shaqu sosai har soyayya ta shiga tsakaninsu.
Basu wani dade tare ba maganar aure ta shiga tsakani dakyar iyayanta suka bashi shima darajar yayansa Bashir danshi yaita kai kawo harsika yadda dan qanin nasa cewa yai bazai aure ba inba ita ba.
Anyi biki komi anan Malaysia suka ci gaba da zama dan ita Fatiha tana shekarar karshe ne shi kuma zaiyi shekara biyu ne kafin ya koma India.
Ta kammala karatunta tas anan ta fara aikinta temporary kafin ya kammala abinda ya kawoshi sukoma india.
Shekararsu biyar da aure basu samu haihuwa ba abinka da yan boko kwata kwata basu damu ba.
Sai da Hajiya ta tada hankali sosai sannan suma suka fara damuwa suna shekara ta bakwai sika samu haihuwa aiko ramar da Fatiha tace masa tana da ciki murna kamar me harda dagata yana rawa ya godewa Allah sosai aranar yasanar da Hajiya itama tai murna sosai.
Wata tara cif ta haife diyarta mace me kama da ita saidai batayo farin larabawanta ba sai tayo baqin yan Nigeria kamar babanta kenan.
A nigeria suka sauka bayan kwana uku da haihuwar dakyar Fatiha ta yadda akan suna gama kwanakinsu zasu tafi Jordan gidansu Yasir ya yadda da hakan.
Ranar suna yarinya taci sunanta Ummul khair. Sunan Hajiya ne taci hakan yasa suke kiranta da ummu mace ta farko acikin jikokin gidan aikuwa yayyen yasir sun nuna farin cikinsu sosai ji suke kamar diyarsu ce yayin da hajiya tafi kowa farinci dan tanasan mace sosai saidai kawai Allah ne be bata ba.
Watansu guda a Nigeria suka yafi jordan.
Watana goma sha daya a duniya mahaifina hau cuta wato ciwon qoda ne me tsanani ya kamashi ciwo ne sosai bana wasa ba hakan yasa dole suka dawo Nigeria bawai dan babu magani a Indian ba sedai kawai dan Hajiya ta takura.
Ganin ciwon gaskene yasa hajiya ta yadda suka dawo india harda ita dan jinyarsu.
Watansu uku da dawowa anmasa dashen qoda yadan koma normal har yazo gida hutu sai daime satin da zasu koma ciwo ya dawo sabo baiko kwana ba Allah ya masa rasuwa.
Kowa mutuwar ta girgizashi dan ba wanda ya bashi mutuwa ganin cewar Hajiyarsu nada rai ga kuma yayyensa duk araye saidai kash ita mutuwa ba ruwanta da shekaru girma ko yarinta.
Lokacin da Ummana ta gama takaba taso tafiya dani sai dai me Hajiya ta tubure ita abar mata ni ta dauki zugar mamar Mahfuz.
Haka mamata ta cireni a Nono ban isa yaye ba ina da wata goma sha hudu tabarni tana kuka ni inba a hoto ba bansan ummana ba balle Abbana.
Ummu ta kuma share hawaye gami da goge majinar da ta tawo mata ta dora.
Lokacin Hajiya nada rai banyi wani maraici ba abu daya ne damuwata shine mahfux dan ko a hanya muka hadu saiya maujeni wataran ya kaimin duka gami da zagina dan haushina yakeji sosai kan kakarmu tafi sona inka dauke matsalar mahfux babda ta komi dan komi tanai min lokacin da babana ya cika shekaru biyar da rasuwa ina shekara shida da watanni Hajiya ba lafiya ta tara yaranta tace kamar yadda kuka sani gida na Yasir ne sedai ya rasu yana diya mace daya tal.
Kenan kuna da gado a dukiyarsa ni nawa gadon na gidannan na yafe harga Allah nabarma Ummu diyarsa budar bakin Yaya bashir shima yace ya barmin duk sun barmin gadonsu na gidan.
Sauran dukiyar mahaifina aka raba aka baima baba Bashir nawa na ummana aka tura mata tumunin takabarta can jordan dagyar ta amsa.
Ina Jss one Hajiya ta rasu alokacin na fara wayo nasan mutuwa gashi duniya da ita na saba aikuwa naji mutuwar sosai nai kuka har na haqura.
Tun mutuwar Hajiya ba irin wahalar da bn sha agurin mutanen gidan nan babu me tausayina ko kadan. Musanman mahfuz dan ko kadan baida mutunci gashi hajiyarsa taita bin bayansa.
Lokacin da Baba Bashir ya rasu nan komi ya kuma cakudemin dan banda sakat inba dare ne yayi ba sauran yayun babana sun dawo duda akwai yanxu sakonnina mata jikokin gidan da yawa anman duk wata wahala nice.
Mahfux bashi da kirki baya hulda da kowa wanda yake na gari inka dauke abokinsa daya da yake so sosai tun suna yara wato Abvakar hausawa nacewa se hali yazo daya ake abota sai dai shi nasu ba haka bane dan kuwa Abbakar ba halinsu daya ba danshi miskiline vaikuma shiga shirgin iskancin mahfuz kawai soyayyarsu da abotarsu daga Allah take.
Lokacin suna yara kullin se Abbakar ya daki mahfuz hajiyarsa intai masa mayana mahfux yasa kuka yace ai abokinsa ne duk yadda taso rabasu mahfux yaqi duda shi Abbakar ke jibga se mahfux ya tafi wanj gurin hajiyar jahfuz ta kama kunnen Abbakar ta matse tace kar ya kuma dukar mata da. Sedai abinda bata sani ba shi mahfux dinne ke fara tsokanar Abbakar dun saidai shi ba qarfi gareshi ba shi kuma Abbakar zuciya gareshi in ya bashi haushi kawai saiya rufeshi da duka.
Sannu a hankali Abbakar ya dena dukan mahfuz koda ya tsokaneshi saidai kawai yai kamar be ganshi ba shaquwarsu ta qaru sosai ajinsu daya lokacin suba Ss2 Ina primary 4 Abbakar yazo yasanar da hajiya kan ta tsawatarma mahfuz dan ya fara shaye shaye tace ina qaryane tama haishi da fada.
Hajiyarsu ya fadawa dan haka taje tasamu hajiyar mahfuz aikuwa ta rufe ido taci mutuncin hajiyar Abbakar wai sunma danta sharri dan ita da kowa ma ta bata kan mahfux dan ba wanda ya isa ya fadi lefin mahfuz agabanta yanxu tace yama danta sharri.
Hajiyar Abbakar ce ta kira mahfux tamai nasiha yaji sosai hakan yasa ya dena shaye shayensa a gaban Abbakar yawanci ma sai dare.
Lokacin da sukai candy sun fara Karatun likitanci a ABU sai aka tafi yajin aiki Abbakar yace shi waje zai tafi dan can yatafi Japan yafara karatun qere qere wata engineering yayin da mahfuz ya ce ina ba inda zaije danshi mutunne da kullin yana manne da Hajiyarsa shiya shaquwarsu da ita kullin qaruwa take.
Lokacin da aka koma sch qin komawa yai dan damashi dan Abbakar yake science anman art yakeso hajiya tai tai ya cigaba da MBBS dinsa yace yaqi dole tanaji tana kallo ya kumayin Jamb ya dauko necon sa dan daman ita ya dade da biyan kudi aka masa ita a art bai samu matsala ba suka bashi abinda ya nema wata mass communication yafara karatunsa anan Bayero saidai rashin mutuncinsa kullin se abinda ya qaru.
Bayan shekaru Biyar
Zaune nake ina maida numfashi dan kam na gaji da yawa ba kowa a gida duk sun tafi BUK wajen taya mahfuz kammala degree dinsa ayau ni kadai ce a gidan ya shigo na kalleshi da mamaki.
Yah mahfuz kai da aka tafi taya murna kuma seka riga kowa dawowa ya galla min harara ke dan ubanki ni sa'anki ne zaki dinga min wannan tambayoyin eyye dan shima ya ya tsaneni sosai dan yadda mahaifinsu kan ya rasu yake nunamin soyayya.
Na murguda baki badai ubana ba sedai nawa nace ai babanka babana ne anman danace sedai naka what to me zakiyi inna kuma zaginki ka kuma dinmana ka gani lallai yarinyar han ko yau zanci kutmar....... Saukar marin da yaji afuskarsa yasashi dafe gurin tabdi kin jawoma kanki bala'i ni kikia mara anmare kan danmene zaka zagar min uba bacun ya dade da mutuwa.
Caraf ya daukeni yai dakina dani ina kuka ina ihuuu zatona dukana zaiyi tunda naga dakina yai dani saidaime abinda yamin yafi duka baqinci ya gama wulaqanta min rayuwa kafin ya miqe yace kinga gobe in akace ki mari wani me suna mahfux kan ya zageki kya kuma kallon yadda nake kuka ne yasa shi kwashewa da dariya kadan kika gani cikin shika shikan rashin mutuncina.
Yadda marin da kika min bazan tava mancewa ba yaka abinda namiki nasan bazaki taba mancewa ba Allah ya isa mugu azzalumi kawai nake fade ke kimin shiru ko yanzu ki kuma shan mamakina gum nai da bakina yafice daga dakin.
Yana fita ya hadu da yayansa Nasir wanda hai cika magana be bai cika shiga sabgar yan gidanba koni baya sani abu ko gaisheshi nayi amsawa kasa kasa yake ya wuce gurin ko a bangarensu ya ganni ina shara kirana yake yamin fada kan kar insake shigowa seda hajiyarsu ta mai fada sannan ta haqura ya kyalene sedai hijabai da ya siyon inxani yace indinga sawa sautari ina kula dashi ko fita zaiyi inyaga na shigo barinsu zama yake yace insauri in gama badon komi ba sedan kowane irin namiji shiga barin yake masu mutunci da marasa shi.
Mahfux me yakaika dakin yarinyar nan yafada hankali atashe ya watsa masa wani kallo rainan hankali tai naje na koya mata hankali what me kayi mata ya fada yana firgizashi kaje ka rambayeta mata yai cilli da hannunsa da ya riqeshi.
Kuka kawai take tausayinta fal ran Nasir kasantuwarsa likita kuma malami me koyarda yara masu san zama likitoci ne yasanya temaka mata ya bata magunguna ya hada mata ruwa yace taje tai wanka komi da ya cancanta shi ya fada mata yadda zatayi..
Bayan na fitone naita roqarsa kan yabar maganar ya rufemin sirrina daqyar ya amince ya haqura saudai gabaki daya ya sauyawa Mahfuz ko magana ma sundenayi.
Wata daya da faruwar al'amarin ciki ya bayyanarmin alokacin mun kusa fara lectures dan har Nasir ya amson komi aikuwa hajiya ta gane nan ta tara jama'a maza da mata kan sena fadi uban da yaimin nace ai mahfuz ne yahau ya tubure shi bashi bane qarya nake masa hajiyama haka ta yadda ina ita ba danta bane.
Nan kowa yai Allah wadai dani yah nasir bainan yayi tafiya haka suka ce inbar gidan ko hijabi balle takalmi suka turani waje nan na fadi na kukkurje.
Kuka nake sosai Baba me gadi yazo ya dagoni yana cewa inzo muje gidansa Hajiyar Mahfuz ta fito cikin fada take fadin Sale indai koda wasa naji ka temakawa yarinyar nan Allah kabar aiki kenan jin haka yasa na miqe kafin ma yaje ya gama roqota kan tayi haquri yakaini gidansa tuni nai gudu nabar lokon tafiya kawai nake banma san a tsakiyar kwalta nake ba dan kaina wani irin ciwo yake min daga idon dazanyi ne na hangi mota tayo kaina duk yadda nai in kauce mata ina.............
0 comments:
Post a Comment