Fun cike hannunta ummu tayi cikin kuka take magana wallahi banasansa ba kuma zan aureshi ba ko gawata bazata zauna dashi ba yayin da Abbakar cikin qunar rai yai waje danshi kadai yasan mai yakeji aransa ji yake kamar girjinsa ya tsage zuciyarsa ta fado.
Hajiyarsa ce ta matsa inda ummu take dan tun dazu da Abbakar in ya kamo ummu ta biyosu dakin takuma ji komi.
Dafa ummun tai tace ki dena kuka kimki indai ina raye ba zaki kuma maraicin uwaba indai ina raye ba wanda ya isa ya aura miki mahfux duda shima dana ne anman kema yatace.
Tace cikin murya mai kaushi Habu dakata yaja ya tsaya taje ta juyo dashi yana kallonta tana kallonsa tace indai ni na haifeka inaso yanzu ka maida ummu amatsayin matarka ya kalleta zai yi magana tace karka cemin komi wannan umarni ne nake baka bawai shawara ba dan haka kayi abinda nace.
Cikin rawar murya yake magana na maida mata ta ummu hajiya ta saki ajiyar zuciya kamin tace kuma wallahi ko bayan raina kasaki ummulkairi kan Mahfuz bazan yafe maka ba zan iya maka afuwa in kan wani dalili ne.
Ta juya ta kalli hajiyar mahfuz kamar zatai magana kawai taja hannun Abbakar da ummu sukai waje sai kace qananun yara.
Suna fita Mahfuz ya muqe zai bisu hajiyarsa ta gyada masa kai alamar a'a kar yaje ya dawo ya zauna gami da rushewa da kuka yana fadin wannan wacce irin jarrabar so ne nake miki ummu hajiya ki temaka ki ko ragen santa ne dan Allah ta dora kansa a qirjinta tana lallashi kamar wani yaro.
Sai da su Abbakar suka isa gida hajiya ta ja ummu sukai daki suka bar Abbakar nan tsaye yana kallonsu sai yanzu ya gane kuskurensa lallai ya tafka kuskure yasan ko zai hadiyi laya ummu bazata yadda yanasanta ba zatayi zaton tafi san abokinsa kanta bacin ba haka bane yasan duniya bayan hajiyaraa it yakeso bema san me yasa ya ce yabarma mahfuz din ita ba can wani bari na zuciyarsa yace sabida kaima kanasan kyautatama aboki ka koda sau daya ne.
An sallami mahfuz dan ba wani serious abu bane, agida mahfuz mahfux duk yabi ya tashi hankalinsa ji yake kamar ya kashe kansa ya wuta dan dai kawai yana tsoron jahannama ne ya daure anman ji yake gabaki daya duniyar ta masa zafi.
Kwance yake akan gadonsa yana kallon fanka da take ta faman kadawa idanunsa na zubda kwalla ji yake kamar yaje ya sato ummu ayanzu ma azuciyarsa tunani yake tayi inda zai satota ina zai kaita santa ne ita da danta keta ruruwa aransa.
Hajiyaraa ta shigo ganin yana kukan ne yasa tai saurin yin gurin tana fadin subhanallahi haba mahfuz mene haka karka kashe kanka kan wata banza dan Allah, ya dago a fusace hajiya ummu ba banza bace masoyiyata ce to naji me yasa ka kuka.
Cikin shessheqar kuka yake fadin hajiya yarona inasansa wallahi in na rasa ummu bazan iya jure rashin dana ba hajiya ta dafe qirji wane yaro kuma kaida ba mata ba.
Hajita dan gurin ummu wallahi yarona ne ni nayi cikinsa tai saurin rufe bakinsa kul yi shiru vaka da wani da Allah ya rufa mana asiri shine kakesan tonawa indai yaro kakeso zanma aure sai matar ta haifa maka wani abin da yasa hajiya bata damuba da jin kalaman Mahfuz kan dan ummu sabida tasan halinsa tun futowar cikin tasan shi yayi da gaske din tsanar ummu da tai da san zuciya yasa taqi yadda.
Shiru yai kamin yace wallahi ni shi nakeso inasan dana nasan na cuce shi nasa an haifeshi bada aureba anman wallahi yanxu inasansa inasan riqeshi matsayin nawa.
Yace wallahi hajiya inasan yarona nasan ko yara dari zan haifa bazan dena sansa ba inasan amsoshi in nuna masa gata in sauya masa suna daga Abbakar zuwa mahfuz dan Allah ki yadda.
Da qyar tasha kansa ya yadda zai aure bawai san dagaske ya haqura da yaron nasa ba .
A can gidansu Abbakar na dai babu dadi sosai dan hajiya ta rage shiga sabgarsa zaman faloma ba cikayi tayo ba kusan ko yaushe tana daki ita da jikanta Abbakar qarami inyaje tayi kicin kicin tace me ya kawoshi, ummumma kullin idanunsa cikin sam ganinta suke sai dai baya ganinta inma yaganta daga ina kwana, barka da rana ko barka da dare shi kenan sai tayi dakinta.
Yakan kwan uku bai ma ganta ba abubuwa kawai yinsu yake babu dadi.
Yau Abbakar baya nan ya tafi aiki dan sun koma mid semister yanaso yai qoqari ya qarasa ma dalibai lectures insu da tunda ya tafi hutu malamin da aka sauya musu ba wani zuwa yake ba basuyi wani abin kirki ba.
Ummu na zaune suna kallo dan ita din ba me yawan magana bace hajiyan ma haka hakan yasa basu cika fira ba Abbakar qarami ne kan hajiya yanata dab dalarsa.
Su Aisha kabir ne suka shigo da gudu ummu ta miqe tai gunsu ta fada jikinsu Fatima ta tureta dalla ni mataa bakisan haushinki nakeji ba baki daukemu aminai ba lokacin da kika shirya guduwa kika daqa mana hankali tai gurin hajiya suma suka tureta sukai gun hajiya ta tatsaya tana kallonsu kawai kafin itama tai gurin.
Sun gaisa da Hajiya ummu ta mata bayaninsu kafin tajasu zuwa dakinta suna shiga ta shiga musu kuka dagar tai shiru sun rasa kukan me take.
Cikin kuka ta basu labarin komi har aurenta da Abbakar sukai ta murna to mene na kuka ai naga shi din mutumin kirki ne, kukan asarar sch dina danai nake yanzu fa sai na sake jamb fa na kuma jira, Aisha ta miqe af kin ganmu ko munata fira da baqo fa mukazo wakenan ba gurinki yazo ba tai waje ummu ta bita da kallo kawai.
Gurin Hajiya tai tace hajiya mun mance da baqo mukazo yanasan ganinki hajita tace towo baqo kuma waye kenan.
Eh muda Yah Nasir ne hajita tace Nasir kuma wanne Yah nasir dai na ummu na gidansu mahfuz........
[12/22/2017, 12:51 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*145-150*
*Wattpad Fadimafayau*
Hajiya ta danyi shiru kamin ta nisa tace to me yasa be shigo ba banda a abin Nasiru da dayake shigowa ai ba wani ke masa iso ba kosan zainab mutuniyar tasa bata nan.
Wato zainab qanwar Abbakar duda kasancewar Abbakar ya girme mata anman tanasan yayan nata sosai fiye da kowa agidan dan haka duk girmanka in ka tabashi ka banu abinda ke hadata da Nasir kenan indai ya daki Abbakar sai tazo qofar gida ta labe indai nasir ya zo wucewa ta jefeshi ta gudu ya biyota har gida ya daddaketa.
Lokacin da ya qara girmane batafi shekaru goma ya dena dukanta sai dai in yaganta yace ke tsattsewala tasa kuka duda har yanxu in abu ya hadashi da Abbakar ya daddakeshi sai ta masa rashin kunya.
Data girma mutunci ya shiga tsakaninsu karatu ma da Abbakar ya tafi waje karatu shi yake koya mata dan basa shiri da mahfuz ko kadan dan ta ganshi yanashan taba ita kuma indai kanashan taba ta dena ganin girmanka yayin da mahfux mutun ne me dan banzan san girma.
Jeki kice ya shigo tai waje suka shigo tare Aisha ta dauki qaramin Abbakar sukai cikin dakin ummu Nasir ya zauna yana sun sun da kai.
Sun gaisa kafin hajiya tace yanxu Nasiru dan zaka shigo gidannan shi ne sai anma iso da wani kema yadan sosa qeya yana murmushi yayi kyau yanzu yaushe rabonka da gidannan ina zaton tin haihuwar zainab ta farko da tazo wankan gida ya sosa kanshi gami da sun kuyar da kai wallahi abubuwa sukamin yawa.
Eh haka ne shi yasa ai kake iya zuwa katsina ziyara yai dariya ni kuma ga hanci ga baki baka iya zuwa sabida abubuw sun maka yawa can dinma saifa aiki yakaini uhum tace ai shikenan. Tinda yanzu na dauko qanwarka ai dole in ganka Allah hajiya ba haka bane Nadiru kenan ta fada gami dayin shiru.
Daman magana nazo muyi to inajinka kan mene kan karatun ummulkairi ne ok inajinka.
Kinga tayi nisa yanzu ace saita sake jamb ta jira admission kamar abin beba shi ne naga tunda anyi sa'a ta dawo ba'ayi exam ba mai zaisa ta koma ko co tasamu ta gyara nan gaba.
Haka ne kayi magana zanma mijin nata magana yawwa yace wasuma sunyi test anman na roqesu zataje su mata inyaso inta koma sai taje din abinda bata ganeba sai shi Abbakar din ta koya mata bama sai ya koya mata ba in qawayenta sun kasa in yaso saita kiraka to yace gami da miqewa ya dire handouts din da ya shigo dasu gashi sai abata wadanda ta siya kan hutune sai wasu kuma wanda malamansu suka bada ne na sayo mata godiya hajita tai yai waje ransa fal farin ciki danshi daman burinsa ummu tasamu inda ake santa.
Sai yanma su Aisha suka tafi tunda ansan da zuwansu daga gidajensu.
Koda ummu taji batin komawarta makaranta tai ta murna tanama Yayanta addu'a nasir koma ince uba dan ita aranta jinsa take yafi qarfin matsayin yaya gareta saidai uwa da uba.
Washe gari sai gasu Hafsa ita da Ahmad Ahmad ummu tai murna sosai suka sha firarsu anan su ummu suka tafi suka barshi dan zai koya mata wasu abubuwan da bata ganeba cikin wanda taga yah nasir ya rubuta mata zatai test.
Ummi (me aikin ummu) dan tun dawowarsu Abbakar ya maida ita sch duda kafin su gudu ma Nasir yasata dan basu barta a niger ba shigowa tayi sanye da kayan islamiyya ta qaraso inda suke karatun tana washe fuska da yake tasan Ahmad sosai lokacin suna zuwa buk namata namatansu ummu kenan kullun yana cikinsu baifi sa'ansu ba ko su ya girme musu da kadam shine kuma captain dinsu.
Mutuncinsu da ummu ya fara tun wata rana baya zama a baya suma su ummu haka saidai suk qawayenta sun gudu gida kan bazasu ji GSP ba tace ita kota koma gida ba kowa zamanta zatai.
Ta shigo theatre din inda ta aje jakarta sai dai ya sauke yai dare dare kan kujerar aikuwa cikin fada ta qarasa sai dai ganin captain ne yasa tadan sassauta captain pls tashi kaban gurina yai banza da ita ga malami a ajin ko tsoronsa bataji ba ta kuma magana katashi nace yace bazan tashi va wani yace ki fuce eyye yana murguda baki dan ya iya abubuwan mata da yawa.
Malamin yace dakai da ita duk kuyi waje ta jiyo anman malan yimum shiru nace kuyi waje ya miqe pls sir harsun kai waje malamin yace ku dawo ga kujera can abaya guda biyu kuje ku zauna ya nuna baya.
Ummu tai can gefe yace madan guri guda nakesan kuzauna ta dawo tana turo baki Ahmad na hararta sai dai kamin atashi har fada ya koma fira dan Ahmad surutunsa yai yawa ko sati ba'aiba duk insa ya gansu sai yaje yana tsokanarta wai ta fiye fada har suka saba sosai ya zama amininta bama aboki ba tun qawayenta na tsokanarta mai aboki namiji kodai kodai har suma din ya zama abokinsu dan shi din mai saurin sabo ne kasantuwarsa duk yan uwansa mata yasa baijin komi dan yana cikinsu.
Ummi ta dan durkusa ta gaidashi ya amsa yana murmushi maman Abbakar andawo tai dariya eh to sannu da zuwa ina tsarabar guduwa ta rufe fuska abinka da yarinta batafi goma sha biyu ba zan kawo maka ai na dauka bazaka zoba yai dariya to gashi na baki mamaki tai ciki tana dariya.
Sun ci gaba da karatunsu ummi ta dawo riqe da kaya irin na yan niger gashi tace ya amsa yana dariya duk wannan eh tace to na gode tai ciki abinta.
Ya kalli ummu Allah diyar nan taki tayi kinga da ace na isa aure ai bada nan ba ummu tasa dariya kaifa shaqiyancinka baya kadan.
Allah da gaske nake to banda abinka kana shekara sha takwas wazaima aure yadan hade rai ashirin dai au haka ne kaka tsoho kawai ki dinga ragen shekaru da girmana da mutuncina sukai dariya baki daya kinga fa dagaske nake ya za'ayi ina ciki fa to kabari ka qara hankali in naga zanbaka sai inba eyye wato yanzu bani da hankali suka saka dariya baki daya.
Hakan yai dedai da shigowar Abbakar a mota aikuwa idanunsa kan ummu dake faman sheqa dariya wani malolon takaici yazo masa wuya gami da kishi afusace ya bude motar yai gunsu shi kansa baisan me zai yimusu ba in yaje anman yasan tabvas bazasuji da dadi ba....
[12/22/2017, 12:53 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*150-155*
*Wattpad Fadimafayau*
Ransa duk a bace yayo gurrin baiyi shi kansa baisan yana da kishi irin haka ba sai yanxu ganin ummu da wani da daga nesa bai gano ko wane ba.
Sai da yazo dan kunya ta kamashi ganin Ahmad dan yasanshi abokin su ummun ne qoqari yai ya qaqaro murmushi kamin ya qarasa din, Ahmad na ganinsa yai saurin sauko daka kan kujera yana fadin lah sir sannu da zuwa Abbakar yadan saki murmushi kamim yace ah Ahmad yau kaine a gidan namu yai dariya eh tun daxu muka zo dasu Hafsat su sun tafi nima nakusa muna dan yin abunda zatai test ne ok yayi kyau yace.
Ya maida kallonsa ga ummu yace shine baki fadan zaki fito farfajiya ba ko tai masa banza ince dai baki tafi yawo ba da sunan raka qawaye hawa mota ta juyar da kai tana fadin to sabida me zan fada maka qasa qasa take maganar eyyi me kika ce tace cewa nayi ai naga na fadawa hajiya ok ya miki kyau ya koma gurin motarsa.
Ahmad ya dubeta ashe daman kinsanshi baki taba fadanba tai dariya bansanshi ba kawai dai ashe shine frnd dina da nake fadama na facebook kai dan Allah kice chat ya hadaku tai q wayasan masa baifa taba ganina va time in muna chat kai da gasqke ka mance su haka nefa.
Bama kasan wani abu ba ya kalleta yana fadin mefa wai nan mijina ne wai mijina ne ya tafa hannu gami da riqe haba kai dan Allah tai dariya Allah ya shiryeka ka dinga abu sai kace mace.
Nan ta bsshi labarin komi har aurensu tunda daman tuni yasan tarihinta ya kuma tafa hannu ai mukam kice A abagas zamu sameta a course dinsa tai dariya ai seku dena karatu shima yai dariya.
Ko da Abbakar ya shiga ciki Hajiya ta masa maganar batun Nasir yace ina sam shi yadda ba tunda ummu matarsa ce ba wani karatu da zata ci gaba wanda tayima ya wadatar.
Aikuwa hajiya binsa kawai tai da ido ganin ta miqe zai tafi dakinsa ne tace Habu zonan ya dawo ya zauna .
To bari kaji wallahi kayi kadan ka hana yarinyar nan karatu dan zalunci inma kana ganin kudine bazaka iya biya mata ba ni zan dauki nauyinta balle kuma tanada yaya wanda zai dauka yai shiru.
Maganar aurenka in dan kana aurenta ne kake ganin bazaka barta tayi karatu ba to hanya mafi sauqi ka sawwaqe mata Inada wanda zan bata yai saurin kallinta a'a hajiya bama sai ankai ga haka ba tai tsaki gami da yin dakinta.
Acan kuwa gidansu maganar aurensa tai nisa dan tuni hajiyarsa ta gama magana da aminiyarta zasu hada auren zumunci tsakaninsu badan komi yasa aminiyar amincewa ba sai dan sanin halin diyarta.
Duda cewar tasan halin mahfux sai dai tasan da cewar yafi yarta nutsuwa nesa ba kusa ba.
Dan yarinyar tata takai matuka wajen rashin mutunci dan in iskancin ta da rashin mutuncinta ya motsa har gida take kawo qato inko ta bar gidansu sai anganta.
Bakomi yasa salma yadda da aurenba sai dan daman tun da tana san mahfuz dan yana cikin mazan da take so shi yasa koda mum din ta tazo mata da tanaso tai aure ta fara fada jin wazata aura yasa ta hau murna ta rungume mum dinta gaskiya mum kin gama mun komi da kika neman auransa.
Mum din tata tasa dariya cike da farin ciki yawwa yar gari.
Kinga kafin ai aurannan sai mun gama dashi dan tuni na gama da uwassa so nake kiyi zaman farinciki gidan aurenki dan haka dole musan yadda mukai sai abinda kika ce masa suka tafa kai kace ba uwa da 'ya bane.
Shiko mahfuz ko kadan baya wani farin ciki da auren kawai dai yana dan shassharewa ne dan kar hajiyarsa ta gane.
Shi kadai yasan me yake shiryawa dan ya qudiri aniyar kwato dansa kota yaya ne.
Zaune yake shida lauya dinsa yace wai mansur yaushe zamu fara zaman kotunnan ne wallahi na qagu inga yarona jikina nafiso da ya fara magana ya fara da kirana baba ba wani qaton kawai ba mansur yai dariya yanzu mahfuz aminin nakane qaton kawai yaja tsaki kaga gyara maganarka ba amini na bane.
Ya dafashi da zanbaka shawara kabi da kadaure ka janye qarar nan inaganin in yana gun Abbakar ai kamar yana gunka ne mahfuz ya daga masa hannu kaga malan in bazaka iya kareni bane ka fadan in canja lauya a'a ni ai shawara na baka ba komi.
To yanxu yaushe zamu fara shiga kotun mansur yace eh yau dai akace za'a kai mata san masu ok ai gwara ayi ayi.
Hajiya na zaune Badaru ya shigo hajiya anada baqo to jeka kace ana zuwa ta dubu Abbakar jeka kaji waye ya miqe yai waje.
Mutumin yace daga kotu nake ina san ganinmatar gidan towo kotu lafiya dai ko lafiya kalau kirata.
Ya dawo yama hajiya bani ta fito yace hajiya kece ummulkairi tace eh nice to gashi ya miqa mata takarda ta mece inkin duba zaki gani.
Abbakar ya amsa ya duba sammaci ne ankai ummu qara kan ta riqema Mahfuz yaro ta baima wani ya dafe kai oh my God ya fada hajiya tace mene ya miqa mata takardar ta karba jiki na bari.
Ganin meke ciki ne yasa ta saka salati yanxu abinda mahfuz zai mana kenan sika koma ciki hankali tashe ganin ummu ta tawo dan basa son tamasan me ake ciki.
[12/24/2017, 5:28 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*155-160*
*Amina-yarzazzau Oumyasmin AeshaKabir Safiyya kabir da Fatima Ahmad wannan page in naku ne kunfi kowa san wannan littafin ina godiya sosai Abbakar ma na godiya, Ummu tace itama a miqo mata saqon tata godiyar gareki, Mahfuz kam cewa yayi agaisheku da kyau dakyau, Nasir kam tsabar Farin cikin yadda kuke san littafin murmushi ya hanashi yin bayanin saqonsa*
Ciki sukai kowa da tunanin abinyi Hajiya ce tace Habu miqon wayata yai saurin miqa mata sunan Babbar yaya ta hau kira bugu biyu aka dauka.
Tsohuwa barka da rana aka fada daga daya bangaren tai dariya wadda inkana kusa da ita kana kallonta kasan yaqe take dan ranta duk a cakule yake.
Dan rikishi miqama uwarka wayar Sudai yasaki qara kai Hajiya zagina fa kikai itama tai dariya ai nima kasan ba tsohuwa bace ko, Sudais kenan jikan Hajiya na biyu, maza ni kai mata inasan magana da ita jitai ance Hajiya na karba ok sai da ta gaida Umman tasu kamin ta ce umma kiyi Hakuri nayi nayi subar daukan wayata in ankirani anman indai sukaga kece sai sun dauka.
Hajiya bata bata amsa ba tace in Abbansu ya dawo inasan ganinku baki daya to umma fatan lafiya, lafiya qalau kamar yaushe kenan kike san muzo yau ko gobe da sassafe to insha Allah zamu zo mu duka kike san gani ko mu biyu a'a banda yara tam se munzo sukai sallama.
Hankalin Babbar yaya duk ya tashi dan Hajiya bata musu neman gaggawa haka kawai, Hakan yasanya ta kammala komi da wuri mijinta kawai take jira.
Koda ya dawo abinci kawai yaci dan ita bama taci ba saida ta tabbatar ya qoshi yana shirin zama kallo kamar ko yaushe tazo ta masa bayanin kiran hajiya yako hau fada kinsan da kiran tun dazu da na dawo baki fadanma yanxuma nasan ta gaji da jiranmu ita dai tai shiru kawai.
Maza dauko gyalenki muje ta miqe tana qwalaw Nurat babbar yarsu kira ta fito da gudu mum gani daukon gyalena a daki ta kawo mata tana sanyawa tana mata bayani.
Nurat ki kula da qannenki bankuma san duka kinji ko zamu fita bazamu dade ba gidan hajiya zamu in 10 tayi kuje ku kwanta to mum Dady yace zansa tijjani in 11 tayi ya kashe gen to kai sudais kazo muna futa ka rufe qofar shigowa nan shima to yace.
Sai kun Dawo Nurat tace gami da komawa kujera tai kwanciyarta tana ci gaba da karatun littafin da take na Aisha Kabir a wattpad mai suna Step mother ( Aziza's Story) danma writer din tana bata haushi bata cika update da wuri ba anman duk sanda tayi sai tasa ta mance da haushin da takeji dan zata kawo chapter mai dadi data fi ta da.
Yaya babba ce zaune ita da mijinta gaban hajiya suna kwasar gaisuwa ganinta lafiya qalau gasu maryam duk zaune suna fira yasa yaya Babba samun kwanciyar hankali.
Bayan sun gaisa ne Hajiya ta kuma kai dubanta ga ummu tace wannan itace Bilkisu babbar yayar su Habu wannan mijinta ne ummu ta kuma durkusawa ta kwashi gaisuwa duda dazun ta gaidasu, Hajiya ce ta baima su maryam harda ummu umarnin su koma daki zata gana da diyarta.
Maryam ce takaima Abbakar qarami sura zata daukeshi yana kan Cinyar hajiya yako sa kuka shi bazai bitaba Hajiya tace qyaleshi maryan ta watsa masa harara gobe kace zaka bini ko kallonka bazanba sukai mata dariya baki daya.
Idon hajiya nakansu ummu sai da tada sun haye sama ta dawo da idonta kan su bilkisu nan ta musu bayanin komi gami da basu takardar sanmacin.
Mubarak kai nakesan ka zama lauya dinmu inso samune banasan ko kadan yarinyar nan taje kotu tam shikenan hajiya anman inaga kamar zuwanta zai iya zama dole anman dai bari muga kamun ludayin shari'ar.
Yaya babba tace anman dai mahfuz bai kyauta ba zan je in sameshi gobe ko zai janye shari'ar Abbakar da tun dazu yake sauraronsu baice komi ba sai yanxu ai yaya dama kin gyaleshi wallahi ta watsa masa harara kai ba abin kunya bane wasu sujiku a kotu dashi to aishina ya rufe idanunsa ya mance da alaqarmu, daquwa ta watsa masa ungo nan inshi san zuciya ya rufe masa ido sai kaima ya rufema.
Gobe zanje insha Allah ai kowa nasan sulhu yawwa kije in inji Hajiya dan wallahi inajin tausayin yarinyar tana cikin matsaloli da yawa tayi qanqanta dudu batafi sekara sha tara ba yan biyu inzan iya tunawa sun girme mata.
Washe gari da wuri Yaya babba tazo gida anan ta aje motarta tai gidansu mahfuz tai sa'a alokacin zai fita yana ganinta ya washe fuska kai kace ba abinda ya shiga tsakaninsu da qaninta itama ta saki fuska suka gaisa bayan futowarsa daga mota.
Tace Allah ya temaken ban daki gurbi ba gurinka nazo towo to mushiga ciki a'a namma ya isa zatonta ko hajiyarsa tasa shi kai qarar dan bataso ta hanashi janyewa basshi namma ta isa taja ta zauna a teburin me gadin su.
Yanzu mahfuz abinda kai ka kyauta kenan ya kalleta da mamaki kamar ba abinda yai yace ni kuma me nayi ta kalleshi sosai kamin tace yanzu bakasan me kayi ba eh wallahi yayi kyau tace.
To Bari in fada maka daka kai amininka kotu mana ya dafe qirji ni kuma me yamin zan kaishi kotu ta kalleshi da mamakin yadda yake maganar kamar besan yayi ba.
Ka mance kace ya riqe maka yaro oh ya fada haka yace miki shi nakai ni wallahi bashi nakai ba ai komai yamun ya wuce in kaishi qara tai dan murmushi ai kamar shi kakai tunda ka kai matarsa yai shiru kamin yace ni wallahi bashi nakaiba ko sunansa babu cikin qarata.
Ok naji bashi kakaiba kayi haquri ka janye qarar in yaso inkayi aure sai yaron ya dinga zuwan maka hutu kaga yanxu ko yayeshi batai ba.
Ina wallahi baxan janyeba ace nida yarona sai dai yadinga zuwa min hutu to ni so nake in amshi yarona tun kan ayayeshi inasan jinsa kusa dani ajikina akullin inasan ya taso da qaunata.
Yaya Babba ta gyada kai ai shikenan se aje kotun inga me baka yaron yanajin nauyinta hakan yasa cikin qunquni yace ai kota yaya ne sai na amshi abina.
Bataji mai yace ba tai gaba kawai.....
Waye Abbakar
Alhaji ukashat Fadal shine sunan mahaifin Abbakar haifaffen garin kano ne unguwar yakasai komi nasa yayi shi ne agarin kano wato girma karatu duk a kano yayi su.
Yayi karatun likitancinsa inda ya fara aiki anan Muhammad Abbdullahi wase hospital, Fiddausi daliba ce cikin daliban sch of nursing kano practical ya kaisu asibitin sannu a hankali shaquwa ta shiga tsakaninsu da da Dr Ukashat har ta kai su ga aure.
Shekararsu guda da aure ta sami ciki ita din mutunce me laulayin tsiya hakan yasa da kanta ta ajiye aikin da take dan tuni ta kammala school of nursing in.
Sai dai tun haihuwar diyarsu ta fari basu qara haihuwa ba san duniya suka dorawa Bilkisu tun basa damuwa har suka fara damuwa.
Bilkisu na primary 1 suka kuma haihuwar namji yaci sunansa Abbakar yayarsa ke kiransa da Habu sai dai yaro nada shekara uku bilkisu na primary 4 yaro ya koma tai ta kuka cikin ikon Allah fiddausi ta kuma samun ciki lokacin da ta haihune Aka maida masa da sunan marigayi Abbakar.
Abbakar nada shekara biyu fiddausi ta kuma haihuwar mace ta ci sunanta zainab.
Abbakar nada shekara hudu zainab biyu bilkisu sha biyu tana Jss one yanzu kam arziqi sosai ya zaunawa Ukashat dan asibitinsa ya bunqasa sosai gami da shahara a ko ina a nigeria dan tuni yai asibitinsa mai zaman kansa inda kwararrun likitoci ke aiki cikinsa, makarantar koyon jinya ma tuni ya kammala gininta kawai jira yake amasa register ta fara aiki.
Su Abbakar basa futa sai dai in Bilkisu zata makaranta ta tafi dashi ajinsu daya da Muktar yayan mahfuz shima yakanzo da Mahfuz Nasir na aji daya sai dai su mahfuz basa zama a ajin yara sai gurin yayyensu zamansu aji daya su kadai ne sa'anni yasanya shaquwa ta sosai tsakanin Mahfux da Abbakar.
Hartakai in ba islamiyya mahfuz zaita kuka sai ankawoshi gidansu Abvakar danshi Abbakar bayasan zuwa gidansu mahfuz danshi mahfuz irin yarannanne inyaga agidansu ne yaita dukan yaro inko agidansu Abbakar ne sai dai suyi ta wasa.
Lokacin da suka isa shiga sch baban mahfuz yakaisu makaranta tare aji daya Mahaifin Abbakar yaso cire Abvakar Fiddausi tace ya kyaleshi kar baban mahfux yaji ba dadi.
Abbakar da mahfuz abokaine sosai sai dai hakinsu ya vanbanta dan shi mahfuz ya cika rawar kai duk yan iskan aji da sch insu abokansa ne.
Suna jss 3 aka haifi maryam su Abbakar murna kamar me.
Tuni makarantar mahaifinsu ta fara aiki kudi sun qara zauna musu sai dai ko kadan Abbakar ba irin yarannan bane masu nuna su wasu ne.
Da suka shiga SS ne ya zabi science mahfuz art yakeso sai dak bayasan rabuwa da Abbakar hakan yasa ya haqura da art din ya shiga science.
Bilkisu babanta ta gada dan medicine take tana lecel 4 aka mata aure .
Zainab na Jss 3 Abbakar Ss3 yayin da maryam primary 1 Hajiya nada wani tsohon cikin Alhaji ukashat yai hadari kan hanyarsa ta dawo wa gida daga kaduna sai gawarsa aka kawo gida kuka gurinsu kamarme.
Kwana uku da rasuwar Hajiya Fiddausi ta haifi yaranta guda biyu macen ta fara haifa da kwana biyu wank ciwon ya taso dan agida ta haihu ko asibiti basu je ba ta kuma haihuwat namiji.
Abbakar ko kadan bayasan yayi medicine math yake so ko engineering hakan yasa da suka fara medicine aka tafi yajin aiki yasa kawonsa ya masa komi na tafiya japan karatu yai sa'a dagyar Hajiyarsu ta yadda.
Lokacin da ya samu mahfux da batu ya yadda shima zashi sai dai daya fadawa wani abokin shaye shayensa yace kar yaje haba Baba kaima kazama mutumin kanka mana ace kullin sai abinda guy dincan yace zakayi yaita zigashi har ya yadda....shi kuwa salim badan komi yake zugar ba dan sanin in Mahfuz ya tafi babu mai siya masa kota yar lasa ce wato kwaya.
Samun Abbakar yai ya fafada masa Hajiyarsa taqi yadda Abbakar yace zai sameta yace kar yaje nima inasan koda sau daya ne inma mahaifiyata biyayya Abbakar yaji dadi dan zatonsa shiriya tasamu abokin nasa.
Duda Abbakar basa tare da mahfuz anman komi yai sai ya fada masa lokacin Abbakar ya kirashi tayashi murnar kammala masters insa ne Yakr fada masa abinda yai ma ummu batare dajin komi ba zatonsa Abbakar ma bazaiji komi ba kamar su salim da sukai ta sara masa.
Saidai Abbakar fada yai ta masa har saida mahfuz yai danasanin fada masa.
Yaya Babba da zainab ke kula da Dukiyar mahaifinsu asibiti da makaranta sai dai lokacin da zainab ta samu miji tai aure a katsina abubuwa suka dawo kan yaya babba duka hakan yasa Hajiya tilastawa Muktar auta yin karatun likita tunda shi namiji ne tashi Abbakar yaqi.
Koda ya kammala secondary ya tafi india yin medicine ummi tagwai insa take law maryam pharmacy.
Ci gaban labari
Ranar da aka saka za'a zauna a kotu yazo ta kuwa cika ba lefi duda bakowa yasan da qarar ba.
Lauyoyi sun bayyana kansu inda maga takarda ya karanto bayanin qara kamin shari'a ta fara gudana.
Bayan bugawa da lauyoyi sukai tsakaninsu aka daga qara zuwa sati biyu ba tare da tabbacin wazai nasara ba cikinsu dan ko wanne kwararrene.
Yaya Babba ce tazo gida tana fadawa Hajiya abinda mijinta yace dole sai sun kai ummu kotu da ita da Nasir dan sune shaidun fyade ya mata dagyar hajiya ta aminta.
Bikin mahfux kam yai nisa dan gobe ake saka ran daurin aure yayin da shi tuni ya mance dan hankalinsa gabaki daya ya tashi ganin kamar bazasuyi nasara ba.
Yau akai za'ai zaman kotu dagyar Nasir ya yadda zaije sai da ummu da hajiya Hajiya da yaya babba sukai ta roqonsa ya yadda yaje.
Bayan saurarun shedu da DNA da akai aka tabbatar yaro na Mahfuz ne alqaliya tai gyaran murya kotu tai tsit kowa nasan jin me zata zartar.
Tace ina mahfux ya miqe ina yaron da ake qarar kansa shima ummu ta miqe gashi ranki ya dade ina uwattasa tace nice.
Miqa masa shi ummu ta kalli alqaliyar alamar in miqa masa kamar yaya tace nace ki miqa masa shi ko ummu ta qara qanqame yaronta police mace ce ta amshi yaron ta miqawa mahfuz dake faman washe baki ummu ta zube gurin tana kuka..........
Zan cigaba insha Allah
[12/29/2017, 12:55 AM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*160-165*
.
Mahfuz yakai hannu ya amshi yaron tuni kotu ta hargitse da hayani kowa na fadin albarkacin bakinsa domin yau kotun ta cika sosai da yawa cikin mutanen kotun abu daya suke fade yake kuma basu mamaki wato wannan wace irin alqaliya ce wannan zalunci ne.
Maganar da alqaliyar ta fara ne yasanya kotun fara yin shuru kafin daga bisani kuma tai shiru.
Yanzu daman innace ka amshi yaron nan saika amsa ya kalli alqaliyar da mamaki, ina kai musulmi ne ko baka da labarin in mace ta haifi yaro a muslunci batare da aure ba yaron nata ne bana wanda yai cikinba.
Kai wane irin azzalumi ne da har zaka ma yarinya fyade ta haihu kakuma zo ka kawota qara ko dan ita batasan haqqinta ba ta gaza kawoka qara.
Wato kazo nan aqwace yaro abaka ko kai gaka uwa da uba na doka ko to abaka shi kamasa me ka kasheshi ko yai saurin kallonta da mamaki fiye da dazu eh mana kanasan karbar sa ka kasheshi dan karya girma ya zargeka da rashin kawoshi ta hanya dedai.
Mahfux cikin fishi yake magana Haba malama wannan ai bayi bane zaki dunga mun sharri kawai dan kina alqaliya tsawa ta daka masa kai malan kasan a inda kake kotu ba sa'ar wasan ka bace.
Sakamakon samun wanda yake qara da rashin ta ido da kotu saka makon haka kotu ta bada dama a sakaya shi nanda wata guda sannan yaro na mahaifiyarsa ne kotu ta masa katanga da yaron indai ba mahaifiyarsa ta yarje yaje gunsa ba.
Duk yadda yan uwan mahfuz sukaso kar yai firxin na wata guda abin yaci tura dan alqaliyar iya wuya yazo tace da a qyaleshi gwara ta bar aiki.
Har gida alqaliyar mai suna Salma tazo ta sami ummu tasamu karba ta mutunci sun gaisa da hajiya kamin ta fara bayaninta.
Indai kun amince ni zan tsawa ummulkairi ta kai yaroncan qara kan cin zarafinta da yai na keta mata haddi tunda duk wata shedu munadasu na zaman kotun da mukai.
Kafin hajiya tace wani abu ummu ta dora a'a ni zaman yarona agurina wallahi ya fiyemun komi na riga nakai shi qara gurin sarkin da baya zalinci nakuma san ko aduniya ko alahira zai saka min nagode sosai aunty sukai sallama ta tafi.
Hankalin hajiyar mahfuz yafi na kowa tashi gashi gobe daurin aurensa abin haushi dik gidajen radio da tv sun nuna shi sakamakon rashin mutuncin da yai akotu balle tace ko tafiya yai.
Ban garen gidansu amarya basu wani ji komi ba dansu burinsu kawai su aurar da salma gama ko wane ko sa samu su huta da halinta, itama bangaren Amarya bataji komi ba saima murna da tayi na rashin bashi shegen dansa dan mum dinta ta fada mata irin son da yake masa shi yasa tun kan tashiga gidan kishin duniya ta dora kan yaron, na biyu kuwa ta samu abinyi in ya mata gori zata rama da cewar ai gwara ita bata taba bursinba.
Mahfuz duniya ta masa zafi ba abinda yake tunawa sai sa'adda police suka saka masa ankwa Abbakar yasa hannu ya amshe takwaransa dake hanunsa ya miqawa ummu.
Gabaki daya yai baqi ya rame danshi mutunne da bai saba da wahala ba bakuma yasanta ji yake wata guda dinma taqi qarewa ji yake kamar shekara ce zaiyi ba wata ba.
Sanye taje cikin baqar abayarta mai adon ja ta nada mayafin abayar akanta sai yar jaka mai dauke da littafanta gudu uku kacal ita ma jace sai dan duwatsun baqi jikinsu takalminta mai sauqin nauyi tai kyau sosai.
Ummu kenan wadda ko wacce kwalliya tai tana mata kyau musanman a idan Abbakar wanda yanzunma tunda take saukowa ita da ummi qanwarsa yake binta da kallo gashidai shiga iri daya sukai anman gani yake ina ummu ai babu ya ita.
Ummu doguwa ce bacan ba komi nata me kyau ne ita din bata cikin fararen fata bakuma za'a kirata baqa can ba tanada dai duhu irin na yan Nigeria wato duhunta me kyaune fatarta ma me kyauce idanunta yan madai daita wanda hancinta da baqinta sun dace da yanayin fuskarta kana kallonta zaka san ta hada jinsi da larabawa ko ka kirata irin fulanin asalin nan kamarta daya sa babarta saidai ita batayo hasken babar tata ba.
Sai da suka zo dab ummi ta tabashi yah munata gaisheka bakaji ba ya dake irin karsu gane ita yake kallo yayin da tuni hajiya ta rafkoshi yace oh banji ba inadanjin bacci ne, ina zuwa haka zamu sch ne ok to ku jira in kaiku ya fada gami da miqewa.
Ajikin motar suka tsaya yazo ya bude duk suka shige baya shima yai zamansa agaban motar yaci gaba da daddana wayarsa yayinda lokaci lokaci yake satar kallon ummu.
Ganin bazai tafi bane yasa ummi qanwarsa cewa yaya muje ko ya juyo ya watsa musu harara baki dayansu muje ina? sch mana kai kace zaka kaimu ai, nace dai zan rage muku hanya ko suka kalli juna ita da ummu shi kuma ya ci gaba da danna wayarsa.
Ganin da gaske bazai tafiba yasa ummu daurewa tace pls sir karmu makara asanyaye tai maganar yadan kalleta watoma agidanma kallom wancan lecturer din nasu na thermodynamic take masa yace au ai nazaci baku shirya tafiya ba ummu aranta tace lallai mutumin nan dan rainin hankali ne bamu shirya tafiya inba zamu shiga mota ummi ta miqe daga bayan ta koma gaba.
Ko rufe qofar taiba ya tada mota ta jawota suka tafi, ummi ya fara saukewa a old campus dan zatai wani abu yaja yai tsawarsa ganin yana bata mata lokaci yasa tace pls dan Allah sir mu tafi.
Ya leqo gidan bayan ni direbanki ne ya fada yadda yai yamata kwarjini hakan yasa ta fito ta shiga gidan gaba yaja suka tafi.
Adai dai faculty insu ya paker ta bude kamin ta sauka ta juyo tace thank you sir ya ruqo hannunta da sauri ya juyo ta kalleshi ba sunana Sir ba, nakuma sanda kinsan da hakan dan haka akiyaye ya saketa tai waje dasauri.
Su Aisha ta gani can gefe suna sheqa dariya harda tafi iyye kaga masoya wato abin har yakaiga adinga kawoki inkuma ankawoki a zauna a mota a kwashi love ta turo baki to 'yan sa ido masu zuwa lahira da qoqom danbu anayi kuna irgawa to ya ranku.
Ahmad yace ransu fes birgesu kikai shi tasa suka kasa shiru Hafsat takai masa duka da littafinta kaifa dan is ne ah kinga yarinya dena iskantani da mutunci na har yanzu suka saka dariya baki daya.
[12/29/2017, 12:57 AM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*165-170*
Yau kwanan mahfuz uku kenan da fitowa duk yai baqi abinci ma ba wani da dinsa yakeji ba kawai dai yana daurewa ya cine dan kan abin ya masa yawa ga yunwa ga rashin dansa.
Ganin ya kwan uku ne bai maganar matarsa ba hajiyarsa ta sameshi adakinsa yana kwance da alamu tinani yake tace mahfuz magana nazo muyi ta Fahinta ya dago gami da jin gina da gadon to hajiya inajinki.
Maganar matarka ce Naga tunda ka dawo bakamin maganarta ba adan razane ya kalleta mata kuma hajiya eh matarka danshi a zahirin gaskiya yama mance dawai za'a daura masa aure balle yasan an daura.
Haba hajiya da wanne zanji da auramin wadda banaso ko kuwa da kwacen yarona da akai ta daga masa hannu kaga ni yimun shiru kai inbanda butulci naka yarinyar duda sanin kana da yaro shege ta yadda ta aureka kace aura maka ita tashin adalcine kai inbanda amincin dake tsakanina da uwatta aikasan kamin kasamu me aurenka saika shirya.
Dan haka ina baka umarni kayi maza ka hada naka yanaka ka koma gidanka na court road dan can nasa aka kaima ita idanunsa sunyi jawur rannan abace ya miqe ya hau dibar kayansa.
Ko sallama baima Hajiya ba ya fice daga gidan danshi yanzi haushinta yakeji gani yake ita ta cuceshi data sangarta shi ta nuna masa komi yayi dedai ne gashinan tasa yaje yai abinda sakayyarsa ke neman haukatashi.
Gidansu Abbakar
Yau shirye shirye suke sosai dan har su Nurat sunzo aunty zainab ce zatazo dan ganin amaryar yayan nata dan ita batasanta ba.
Lokacin da tazone aunty zee tasha mamaki qanwarmu ashe kece amaryar tamu ummu ma ta mamaki aunty zee daman ke yar nance eh aure yakaini katsina kowa yai mamakin sanin juna da sukai.
Aunty zee ta dubu Hajiya umma ai nasanta qanwar Yah Nasir ce kuma qawar Farida qanwar salma wato qannen mijinta Hajiya tace ikon Allah.
Da yake duk gida daya suka zauna da su salman yanzu ma tare suke ra Farida ummu tai dariya kawai Abbakar yace a'a yanzu ta dawo nan daiko suka saka masa dariya baki daya.
Zainab ta dubi ummu waiko in tambayeki ummu ta zuba mata ido alamar inajinki, Yah nasir kuwa ya fadawa Farida yana santa ummu tadan dubeta wato itama tasan yanasan Faridan a'a tace.
Kai yaya Nasir da zurfin ciki yake wallahi tun yarinyar nan fa na Jss yake fama da santa yasha fadan yadda yakejin santa aransa anman ya kasa fada ai shikenan nasan me zan masa.
Suna gama cin abinci ta kira Nasir din awaya Yaya na nafazo garin naku eyye watoma garinmu ko to ganinan zuwa gidan naku.
Sun sha fira kamin zainab tace daman jaje zanma bikin Farida ya gabato sauran wata uku what ya fada yana miqe ina wallahi bazai yiwuba farida tawa ce ni daya.
Yai waje zainab ta bishi a baya sedai kamin tazo ya fice a motarsa ita dai hankalinta duk atashe kar yaje yai wata baran baramar.
Kai tsaye gidan Farida ya wuce ya dade baije ba dan yanzu ita kadaice hakan yasa gudun shedan ya rage zuwa duda ta ce masa qannenta uku sunzo mata hutu baida niyar zuwa.
Kullin cikin kiransa take awaya ko a sch nunawa yake baisanta ba yama hanata zuwa office dinsa gabaki daya.
Kai tsaye gidan ya shige yana kwala mata kira Basira na shanya tasanshi hakan yasa bata tsorata ba se ce masa datai tana ciki.
Da gudu Farida ta fito yah lafiya kuwa cikin kwalla yake magana yanxu Farida kin kyauta min kenan kinsan da ke daya nakeso a duniya shine zakiyi aure ki barni ta kalleshi yah ban gane me kake magana akaiba yaushe muka taba maganar soyayya dakai.
Ko kuwa nace inasanka ne what eh bakice kinasona ba anman aikin nuna ta zaro ido ni wallahi a'a kawai irin kulawa da wa da qanwarsa ce .
Oho ke kika sani ni kawai abinda nasani ke din matata ce kuma dole koma wazaki aura a fasa ayi dani cikin dan murya me qarfi take magana wai yaya wane aure kake magana yaushe nace ma zanyi aure.
Wayarsa da tun dazu ke ringing ya daga bema duba ko waye ba ya amsa muryar zainab ce cikin muryar kuka take fadin yah wallahi da wasa nake tsokanar ka kawai fa nake ba wani aurenta da aka saka.
Kunya duk ta kamashi sun sun ya fice yabar gidan Farida na kiransa yai gaba ita dai tasan yaya nasir baya shaye shaye dasai tace ko ita ta fada masa qarya.
Gidansu zainab ya koma anman kin gama dani kinsa nayi abinda banniya ba tasa dariya to ai kaga na temakeka kaidinne inata ka tsaya katsaya kai gaba ummu tai dariya ke kuwa aunty zee yaji zuciyarsa zata tafi gidan wani yace eyye kema harda ke ko suka saka dariya Abbakar mamaki yake daman tana magana da dariya haka.
Gidan Mahfuz
Duk ransa abace ya shiga gidan sai dai me yana shiga yaji yamanta komi ba abinda yake sai burin ganin matarsa ko rufe murfin motar baiba yai ciki ita kuwa gwanar daman su suka tunzuro Hajiyarsa ta koroshi dan tuni ko wanne aiki da bokansu ya basu sun kammala.
A tsaye ya hangeta da wata arniyar shigarta suna hada ido wanda yaci kwallin boka yaji ya kasa koda motswa zuwa tai taja hannunsa sukai ciki gurin dinning area ta kaishi ta zuba masa lemon abarba da yasha magani ta miqa masa ya amsa ya hausha saida ya shanye ta zuba masa abinci yaci yai nak.
Komi ya tafi yadda suke so dan basu wani sha wuyaba asirunsu ya kama mahfuz dan shi din ba gwanin ibada bane .
Mahfuz ya zama kamar wani sauna sai abinda matarsa ta fada masa yake ta zama kamar itace mijin shi kuwa irin baiwar matarnan danma bazamu kirashi matarso ba.
Rabonsa da gidansu tun randa ya baro sati biyu kenan ko wayoyinsa matarsa ta kashe cewarta ita bata gama cin amarcinta da angonta ba aiki ma dan dole take bari ya fita shima sai yasha kashedin in ya dade ko ya kula wata shi da ita ne gabaki daya tsoronta ya gama rufe zuciyarsa.
Gidansu Abbakar
Zainab ce tsaye suna magana da Hajiyarsu umma wai yaushe ne Amaryar zata tare nama yaya magana yamin shiru Hajiya tace se randa ya shirya inkuma be wasa ba wallahi sawa zan yasakar min ita tunda naga baya santa inyaso na bata sulaiman kai hajiya kema kinsan yah nasanta sulaiman da tunda ya taso yake qasar waje ai bazai yadda da auren dole ba au haka kika ce zakusha mamaki tai dariya kawai sikai sallama suka tafi.
Soyayya tsakanin Farida da Nasir kamar sa hadiye junansu ko yaushe suna maqale awaya ko yana gidansu Abbakar dan tuni Farida ta dawo gidan da zama.
Magana tai nisa aure saura wata guda duda farida taso sai tana level five yace shikam ya gaji da yaquri tanaji tana kallo ya mata fun qarfi.
Rana bata qarya yau laraba ake kamun Farida su ummu ne manyan biki duda kuwa gogon nata baisan budirin da take ba dan ko ta kanta baya bi qarqari yazo ya dauki takwaransa girin hajiya su fice yawo dan yaron ya saba dashi sosai.
Yau zasu wuce kaduna dan acan za'ai bikin dagyar hajiya ta barsu sun fito da akwatu suna zubawa a bayan mota ya shigo da motarsa idanunsa kansu yai parking ya qaraso.
Ku ina zakune haka kuke jidar kaya cikin sauri ummi tace yah ka mance bikim yah Nasir to nan nan din sekun dibi kaya kai yah Kaduna fa zamu.
Me kaduna ku ai yan uwan angone ba inda zaku munfa tambayi hajiya ya doka mata harara zaki matsa ko sai nai ciki dake tai cikin gida da gudu tana kuka ummu ta huro baki gami da qamewa wajen.
Eyye sannu mara mutunci wayo ke bazaki bar gurinba ko tai masa banza wallahi ki kiyayeni ta kiyayeka ko kai ka kiyayeni.
Hajiya ta fada suna fitowa da ummi kuma biki ne se sunje haba hajiya dan Allah nifa mijin tane anman kin hanani matata kuma kina nunan iko kanta ai inzata fita ya kamata ta tambayeni.
Haba hajiya ta riqe iyye sannu me mata kai inkana da kunya kace matarka ce ka taba bata kwayar shinkafa eyye.
To anman hajiya ai baki kawota gidana kinga na kasa ba me kace yace bakomi cewa nayi se sun dawo yai ciki hajiya tace dan nema ashe rashin kunyar qarya kake.
[12/29/2017, 1:00 AM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*170-175*
Duda ummu taji dadin shigar mata da hajiya tayi can qasan ranta bata ji dadin zatayi tafiya me nisa ba tare da izinin mijinta ba duda shi din bai nuna wata kulawa na shi din mijin ta ne.
Yau take daurin aure cikin wadanda sukazo kaduna har da Abbakar tunda suka iso yake baza idanu ko zaiga ummu amma bai ganta ba ko ya manta da mata basa fitowa gurin daurin aure oho.
Su ummu se hotuna ake sha da angwaye wadanda suka shigo cikin gida bama tasan da zuwan Abbakar ba tai kyau sosai kai kace itama din amarya ce.
Ummi qanwar Abbakar taxo ta riqota madan yaya fa zai tafi baku ko gaisa ba balle kuyi hoto ta dube ta wane yayan, Yah Abbakar au yazo ta fada eh to shida yazo be nememu ba se mu zamu nemeshi, ta dan dafata haba tawan ki daure badanshi ba danni to kije kisa ya shigo se muyi photon pls ummu ki temaka danni kije ki kirashi ummu tai jim kamin tace amman ummi..... Bata qarasa ba ummi tace pls harda dan rissinawa.
Sai da ummi ta rakata har zaure ta tabbatar ta fita farfajiyar gidan sannan ta juya cikin gida.
Ware idanunta ummu ta shiga yi dan su bata ikon hango ko gani Abbakar cikin dan dazon mazan da ke gurin.
Baba mahmud da wasu yayun babanta ta hanga da sauri cikin murna tayi wajensu ta durqusa har qas ta gaidasu babu wanda ya ganota dan an riga da anmusu asirin farraqu nasu mance da ita da shafinta.
Baba mahmud ne yaso ganota sai dai ya rasa inda yasanta kawai dai yanaji ajikinsa kamar ita din jininsa ce sosai suka gaisa taji dadi dan zatonta sun ganeta Baba mahmud harda zaro kudi ya miqa mata gashi a qara a hidimar biki ta amsa tana godiya duda bataji dadin rashin tambayarta ina take ba ko me yasa tabar gida.
Shiko gogon nata kamar ance ya kalli qofar gidan idanunsa akanta kishi ne ya rufeshi ji yake kamar duk gurin kalle masa ita suke yayin da ya kasa dauke idanunsa akanta.
Jikinta ya bata ana akallonta hakan yasa ta maida idanunta inda take zaton tanan ake kallontan hangensa tai jikin motarsa shida wasu su uku tai saurin qarasawa.
Batasan me yasa ba lokacin da taje daf dashi ta tsinci kanta da yi masa murmushi, shima din ganin murmushinta da in ba daga nesa ba tanaima wasu bazaice ta taba masa ba ji yai kamar su kadaine awajen ya hau mata murmushi duk ya nemi fadan ya rasa.
Yah barka da safiya tace barkanki dai daman naga baka shigo bane shine nazo in kiraka kazo muyi hoto da angwayen.
Hoto kuma eh a'a ni gaskiya ban iya hoto ba balle cikin mata pls yah tarihine tai maganar cikin wani salo dama batasan tayi ba yayin da shi kuma baima sanda yace muje ba, tana gaba yana biye mata baya har suka isa gidan.
Sunyi hotuna sosai wasu shida ita dasu ummi da su Nasir din ji yake dama ranar aurensu ce shida ummunsa da yafi kowa jin dadi har ya juya zai fita ummi ta tawo da gudu riqe da Abbakar qarami yah bakuyi dashi ba tace ya amsheshi ya tsaya za'a daukesu su biyu ummi ta tura ummu kuyi tare tarihine, su uku me hoton ya dauka ita Abbakar da takwaransa sunyi kyau sosai.
Duk yadda akai da Nasir ango ya yafi yaqi yace ina shifa sai an bashi amaryarsa dole dole ya tsayar da Abbakar kan ya bari zuwa qarfe uku sai su tawo in andauko amarya.
Su hudu ne cikin motar Abbakar keja ummu agaba azaune sai ango da amarya, Hirar ummu da Yah nasir da Amarya kawai kakeji yayin da Abbakar tuqinsa kawai yake dan bashi da ta cewa sai in Nasir ya sako shi ciki ne yake dan tofa tasa.
An kawo amarya gidansu Nasir aka fara kaita ummu bata shiga ba a aqofar gida ta tsaya cikin motar Abbakar yai yai da ita kan tazo su tafi gida taita roqonsa ya bari ta kai amarya shi kansa mamakin kansa yake me yasa komi tace yake amin cewa uhum Abbakar kenan wato bakasan power of love ba kadan ma kenan.
Su Farida se wani kuka take tun shugarsu har fitowarsu se kace ba ita ce dazun suketa kwasar fira a mota ba.
Sun shiga kamar dazu ummu a gaba ita abaya sedai angon be shigo ba shima Abbakar yana daga waje ummu ta leqo ke mu dallah ki mana shiru ai kin fito daga gidan sirikan da kukan naki zai yau dara, Farida ta daqa mayafin gami da dan shan mur.
Ke nice dallah din maza ki nitsu yanzu ni yayarki ce tunda ina auran wanki ummu tace ayi haquri aunty gyanbo sarkin san girma suka saka dariya baki daya, Ummi ta leqo ta taga anti Farida pls ki dena surutu ko yaya Nasir yazo kinga in kina magana ai bazamu samu kudin siyan baki ba kidan daure kiyi shiru awa daya ne kawai munje mun tafi, Farida ta kai mata duka ta jikin taga tasa dariya tai gefe.
A mota ma da Nasir ya shiga kuka ta cigaba da yi abinta shiko yahau rarrshinta haba tawan ki daure kiyi shiru kar nima kisani kuka ko kunyar su ummu baya ji harda wani jawota jikinsa yana lallashe ita kuma taqi magana se shessheqar qarya take tana kuma lafkewa, ummu tai gyaran murya gami da daga waya tana fadin ummi albishirinki anbi umarninki ki shirya karbar masu kauri Farida tace to mugaye ce miki akai.....bata qarasa ba ummu tasa dariya maza ki tonawa kanki asiri itama tasa dariya.
Ankai amarya da yake ba wani qawayen azo agani take da ba su ummu ne sai wata aminiyarta da suke buk tare su ummi sarkin san kudi tun aqofa ake radawa Farida kartayi magana intayi kuwa gidanta bazata dinga zuwa ba, ansamu abinda akeso dan dubu hamsin Abbakar ya lale ya bada dan Nasir din tun safe abokanansa sun tafi sai Abbakar din din da mansur duda duk qannene ga Nasir din.
Duk masu rako amarya na kaduna wato yan uwanta a gidansu Nasir zasu kwana hakan yasa su Abbakar na fita ya dubi ummi yace to lashe money se a yunqura ayi gaba ko tace lah yah kora yace wah ni ban koreku ba kawai dai ta miqe bari to muje kar akoremun da dai yafi inji farida ta kamo kunnenta ta fada mata kai aunty Farida.
Nace su Yah Nasir seda safe su farida uwar rawar kai kuma uhum to ba wani abin zance ba ita ma din seda safe ne asha amarci lafiya.
Zaton ummu yah Abbakar ya tafi sai dai tsaye ta ganshi jikin motarsa ummi tai kamar bata ganshi ba ta shige motar mansur ita da wasu qannensa.
Ummu ma tazo shiga taga ta cika ta dawo gurin Abbakar din bai ce mata komi ba ta bude ta shiga gami da kwantar da Abbakar dinta a baya.
A dedai inda zai kaika ga bangaren da zai kaiga bangaren hajiya ya parker kagaba kadan ummu ta da juya ta dauko Abbakar qarami dake bacci ta riqe qofa zata bude yai locking din motar gabaki daya gami da ruqo hannunta tai saurin kallonsa a tsorace cikin sanyin murya yake magana kai kace bashine wannan Abbakar din data sani ba me fada da tsare gida .
Ummulkairi dan Allah su yaya Nasir basu birgeki ba tai shiru be damu da shirunta ba ya kuma Fadin yaushe zamu tare muma anamu gidan ta kalleshi gida eh gidanmu........
[12/29/2017, 1:02 AM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*175-180*
Gidansu mahfuz
Hankalin hajiyar mahfuz ya gama tashi musanman ganin anyi bikin Nasir an gama babu Mahfuz babu labarinsa tun tana tsanmaninsa harta dena hakan yasa ta kira number din matarsa danshi ko ankirashi akashe take.
Bugu hudu ta qari ringing dinta baza'a dauka ba sai ana biyar dinne aka daga cikin tsiwa take fadin wai waye haka ya isheni da kira na tsani irin haka ka kira sau daya sau biyu ba'a daga ba basaika haqura ba.
Eyye sannu maras mutunci to uwar mijinki ce taja tsaki in uwar mijina ce ai ba ita ke aurena ba sannu salma yanxu rashin mutuncin naki har ya kawo kaina aiko ba mahfuz kike aure ba na fice rashin mutunci gurinki balle duk asirin da muka rufa miki, wa kul hajiya kima dena cewa kun rufan asiri ai in bazaki ce na rufa muku asiriba na auren dan iskan yaronku zaifi kyau kice mun rufawa juna asiri tunda kinsan duk iskanci na banyi dan shege ba, ban kuma yi zaman prison ba.
Yanzu salma ni kike fadawa haka ai kedin ce naga kina neman kawo qabli da ba'adi yayi kyau daman ai gado kikai ni ban dana inaso muyi magana tsaki taja mai qara mtttwwwww gami da fadin au baki da number dinsa in da tana kunne aikinsan babu ta yadda za'ai in kiraki ko.
To yanzu yana hutawa ne banasan atakura masa zaki iya kiransa anjima bata jira cewar hajiyar ba ta kashe wayar.
Bin wayar da kallo hajiya tai ranta na quna wato rashin mutuncin salma har kanta.
Wayar Batulu ta kira bugu daya ta daga aminiyar ya akaine cikin fada hajiyar mahfuz ke magana ba wata amininyar yanzu batulu rashin mutunci da asirinki har kan yarona vatulu ta riqe ha6a kai kace tana gabanta tace haba Aminiyar me yafaru haka ai kema kinsan babu ta yadda za'ai inma mahfuz asiri to mene ribata ai dashi da salma ni duk daya ne me ya faru ne kike irin wannan batun.
Nan ta kwashe komi ta fadawa Hajiya batulu itako sai salati da tafa hannu na munafirci take haba Aminiyar sai kace bakisan halin salma ba aikinsan rashin mutuncinta harni ma yiwa take batun kuma mahfuz ai kinsan se ahankali zai huce balle yaga kinqi goya masa baya ya daukaka qara ya amso yaronsa shiru hajiya tai kamin tace kumafa haka ne.
Kiyi hakuri zan kirata zan mata fada bazata sake ba suka taba fira kamin suyi salama.
Hajiya Batulu ce ta hau kiran diyar tata bugu daya ta daga suka ta6a fira duk kan asire asirensu ne kamin hajiya batulu ta dora.
Dazun muka gama da mutuniyarki ta fadan duk yadda kukai sedai inasan ki kirata ki bata haquri ki kuma barmata yaro yana zuwa gunta.
Kai infa basshi kika ce eh kema kinsan ita din ba daga nanba duda ni nasata ahanya anman kinsan sau da dama dan koyo yakan iya fun malaminsa nafiso se itama an kama mana ita ta dena zaton asiri muka nasa in ba haka ba kuwa zata iya ruguza mana komi.
Allah momey ina kishin inganshi da mace to ai ita uwassa ce kuma banda abinki mun riga mun musu farraqu abunda zai dunga mata na rashin mutunci sai tafiso kar yazo Allah umma kishi nake, tsaki hajiya batulu taja tace ke wace irin mutunce kima rasa kishin wa zakiyi sai uwassa to umma ita ba mace bace.
Kinga nace ki kirata ki bata haquri inba so kike in cire hannuna akanki ba to zan kira ta kashe sukai sallama.
Mahfuz na zaune yana musu gugar kaya ta shigo tana fadin honey ka kuwa kira hajiya ya dago yana sakar musu murmushi eh mana jiyafa munyi waya tadan hade rai kasan wace hajiyar nake nufi.
Akwai wata hajiya da na ke kira da ya wuce hajiyarki tadan saki rai kadan a'a hajiyar ka nake nufi ya hade rai in kirata in mata mene.
Haba nawan mahaifiya ce fa kadai daure ko sau daya ne ka dinga kiranta ta miqo masa wayar pls call her ya amsa yana wani shasshan qamshi shi kenan zan kirata dan ke tai murshin jin dadi.
Bugu daya ta daga haba mahfuz yanzu ka kyauta gabaki daya ka gujemu kofa bikin Nasir bakazo ba bakuma ka turo matarka ba sai anan ya samu damar magana, a'a hajiya ni ne ya dace nazo ban kuma ga damar zuwa ba matata adena samin ita cikin matsal tsalun gida ni kika haifa ba ita ba ya kashe wayar.
Rashin mutuncin Mahfuz kullun yawa yake yayin da matarsa kullin cikin sake shiri take ganin dagaske za'a kwace mata yaronta yasanta hajiyar mahfuz ko ta kan mahaifiyar salma abokiyar zuwa gurin bokayenta ba tai zamfara gurin hatsabibin bokanta.
Qarya da gaskiya bokan ya fadawa wa hajiya tahau tazauna daram komi ya hada mata kai tsaye gida ta koma.
Washe gari gidan mahfuz tai dan ai watar sa aikinta baya nan ta shiga ciki daman haka taso dan tasan ahalin yanzu yafi ma matar tasa rashin mutunci.
Sai dai me shiru falon kamar ba kowa cikin kujera ta tusa daya cikin asirin nata bata taba zuwa gidanba tun kawo salma sai dai tasan gidan sosai hakan yasa ta miqe tai dakin da ke kallonta kai kanta ke da wuya ta dawo da baya abin ya mugun daga mata hankali bata gazgata abinda ta gani hakan yasata qara komawa sai dai me abinda ta gani gaske ne.
Bawai gizo bane Salma ta gani da wani qato ba mijinta ba wato mahfuz suna sa6ama Allah hankalinta yai matuqar tashi sosai.
Dakin ta fada hankali tashe ganinta yasa mutumin yin waje dasauri salma ta bishi ta ruqoshi haba Darling mene haka atsorace yake ka kintsa se ka fita ba abinda zata iya mana.
Mamaki ya cika hajiya ai ku shi dai tuni ya fice hajiya ta kwadawa salma mari gami da jawota waje ashe iskancinki ba iya fatar baki bane haba salma da aurenki aka.
Anan falo hajiya keta surfa bala'inta tama mance da me yakawota gidan dan nata.
Ai kuwa Mahfuz na dawowa Salma ta miqe cikin kuka ta fada jikinsa tana fadin hajiya tazo ta mata duka abinka da aikin asiri tuni ya hau ya zauna hajiya me ya kawoki gidana nan hajiya ta hau masa bayani komi har halin da ta tsinci salma budar bakinsa sai cewa yai yanxu hajiya dan kawai kinajin haushi na shine sai kinma mata ta sharri.
Hajiya ta hau rantse rantse dan ya yadda da gaske take yace pls hajiya kije gida ganinki na qaran takaici wallahi dan kece kawai anman babu wanda zai daki salma in raga masa kema inkika ci gaba da zama zan iya sauya ra'ayi.
Ba shiri hajiya tabar gidan ranta bace har wani jiri take ji.
Gidansu Abbakar
Ummu tace gidanmu kuma bayan wannan da muke ciki yai dan murmushi kamin yace ai kinsan ba wannan gidan nake nufi ba namu mu uku nida ke da takwara na ko shima yasamu qanne ta sunkuyar da kai ganin ya bata kunya yasa shi sauya maganar da fadin.
Wai me yasa bakya hawa facebook account dinki tace haka kawai kuma inna kira number din dana sanki da ita bata shiga tace ai ta bata tun kan na tafi Niger, to da wacce kike anfani babu tace.
Miqo masa ta hannunsa yai ungo kafin in siyo maki wata ta kalleshi yamata kwarjinin da bazata iya cewa a'a ba ta amsa.
Tace ka buden se kin amsan tambayata wacce tambaya ta tambaya yaushe zamu tare anamu gidan tai dan murmushi kamin tace sai randa hajiya ta yadda.
Ya kuma mai maitawa haka kika ce ko tai shiru yadan dubeta kadan kamin yace waini yaushe qanwata ta facebook me magana, fira da barkwanci ta koma miskila ne tai dariya ai daman ko waya muke ni kasan ba magana na cika ba basshi achat din yai dariya wato haka ne ta gyada kai nasan me zanyi ya dauki Takwaransa dake kan cinyarta ya bude qofar sukai cikin gida.
[1/2, 5:29 PM] Fadimafayau: *Abbakar*
*Na*
*F.A.Ya'u*
*Wattpad Fadimafayau*
*180-185*
*Pls kusani a addu'a wallahi bani da lafiya sosai ni kadai nasan me nakeji dakyar ma nayi muku wannan zaku iya jina shiru kwana biyu*
Abun duniya duk ya ishi Abbakar gashi dai yanajin haushin mahfuz sakamakon abinda yai tayi bacin mugun kishinsa da yake ji sai dai kunsan in akace abotar gaskiya wacce take ta tsakani da Allah ko me mutun ya maka wannan san sabida Allah kullin yana nanne.
Gabaki daya ya damu musanman ganin anyi bikin Yah nasir ba Amininsa ya kuma tambaya yah Nasir yace masa wayasan masa tun lokacin yakesan zuwa gidansu sai dai yana tsoron jarrabar Hajiyarsa dan inta mahfuz ne daman sun saba suyi su shirya.
Yanke shawarar zama abakin lokonsu yai ko zaiga aqallah wucewar Aminin nasa dan tabbacin lafiya yake sedai yau kwana hudu babushi bare labarinsa.
Zaune yake gaban hajiyar Mahfuz duk ta rame tai baqi yadda ta amshe shi ya bashi mamaki dan yayi zaton da fada ne sai wani nan nan take dashi.
Sun gaisa yake tambayarta mutumin me makon ta bashi amsa kawai sai ta fashe da kuka yai yai tai shiru taqi sai da tai me isarta cikin shessheqa take fadin Habu haqqine ke cina nakuma san bana kowa bane saina ummulkhairi da iyayenta.
Shi dai da ya samu tai shiru ya danji dadi kadan duda zuciyarsa cike take fal da tunanin me yasamu Aminin nasa "nace uhum Abbakar kenan Allah ya baka zuciya me kyau"
Hajiyar mahfuz bata boye komi game da halin da mahfuz ke ciki ba harda wanda data je gidan ta tadda matarsa, sai dai bata fada masa zuwa gurin bokan da taiba da dalilin zuwa Hankalin Abbakar ya tashi yasan mahfuz yana shaye shaye dan baya boye masa komi anman baya bin mata shi yasa lokacin ya fada masa game da ummu yaita masa fada yanzu tsoronsa daya kar matarsa ta saka masa cutar wannan zamanin.
Nan yaita lallashin hajiyar yana bata haquri yasamu ta dan dawo nutsuwarta kamin ya dora yanzu addu'o'i yakamata ayi tayi masa zansa a masallatai da makarantu ki yawaita masa sadaka da niyar Allah ya karya koma mene taji dadi sosai dan ita tama mance da batun addu'a din.
Kai tsaye gidan Nasir Abbakar ya nufa ya sanar dashi duk yadda sukai da hajiya shima hankalinsa ya tashi ya yadda da shawarar Abbakar tun daga lokacin su ka duqufa sosai ko sallah ce ta kai Abbakar masallaci sai ya roqi asa abokinsa a addu'a.
Sannu a hankali farraqun da aka masa da hajiyarsa yaji ya tsani zuwa gurinta ya kau dan yanzu yana zuwa sosai fiye da da, duda har yanzu cike yake da tsoron matarsa gidan nasu ma aboye yake zuwa.
Da zuwan da yake ne Babban wansu muktar yai anfani tofin da yake masa azam zam ya hada da dabinon ajuwa indai yazo se yasha in yaqi dole suke masa.
Awayo a wayo yayan nasa yake nusar dashi sallah dare in addu'o'i kamin kwanciya bacci da neman tsari dan shi din ba daga nan bane yasan illimin addini sosai kawai dai irin ansani ne bashi da anfani tunda ba'a aiki dashi.
Sannu ahankula tsoron matarsa ya fara barinsa har mamaki yake in yaga tazo ta tsaya masa aka tana bashi umarni kawai kallonta yake sedai ya kasa daukan mataki.
Hankalin Salma da hajiyarta yai mugun tashi ba kadan ba ganin har Niger sun kai sunan mahfuz gurin hatsabibin bokansu wanda duk wanda suka kai ya gama yawo anman kulin abubuwa qara tabarbarewa suke.
Yau sunyi da matarsa zaiyi tafiya zuwa university of ibadan dan yin wani abu murna take sosai dan ta gaji dashi sosai gashi tsoro ya hanata kawo kowa dan daya fita yake dawowa.
Wanda zasuyi tafiyar tare ke fada masa su bari se gobe hakan yasa ya wuce gidansu suka taisa da hajiya sukai yar fira kafin suyi sallama ya wuce gidansa.
Da ace nasan mahfuz yasan me zai tadda da tabbas da bazaiyi sha'awar zuwa gida ba hankalinsa yai matuqar tashi idanunsa duk ya rife bema san me ya rarumo ba yai kansu.
Duka kawai yake babu qaqqautawa ganin zai ita kashesu yasa kwarton yin ta maza yai waje a miliyan ya koma kan salma dake gefe a rakube tama kasa motsawa duka kawai yake tai mata lilis dagyar ta rarumi zanin gado ta arta aguce.
Biyota yai yana ci gaba da duka yana fadi Allah ya isa tsakani na dake na sake ki saki uku har farfajiyar gidan dagyar me gadi da driver suka riqeshi ita dai data samu tai waje adai daita ta hau se gidan ubanta.
Agurin Mahfuz ya zibe yana kwasar kuka shi kadai yasan abinda yakeji yanzu ransa bai taba yadda cewar inkayi zina da wata mace se anyi da wacce take mallakinka ba sai tau matarsa ta sunna kuka kam yayi shi bakadanba tausayin yaransa mata ya kamashi innalillahi wa'innailaihi raji'un yake fade kawai Allah ka temake ni katsayarmin iya nan wallahi nayi nadama ya Allah karka dorawa yarana abinda ni nayi sanbatu kawai yake.
Gidan ji yake gabaki daya ya zame masa kurku ku ba abinda yake gani sai matarsa da wani gidanma gabaki daya ya bari yai gidansu.
Cikin kuka yake fadawa hajiyarsu komi baima qarasa ba suka jiyo masifa a waje da sauri hajiya ta miqe tai waje Hajiya Batulu ke ta sirfa masifa salma na bayanta.
Fadi take ina Karimar take wallahi dukan da dan iskan yaronki yama yarinyata akanki zan rama mata ganin hajiyar yasa tai kanta gadan gadan aikan daga hannu tai zata zuba mata wayar dake hannunta aiko muktasir yako riqeta kul bazai yiwu kizo mana gida dan rashin mutunci kice zaki dakar mana uwa ba kinyi kadan.
Kamin ya qarasa tasakarma Hajiyar tasu nari itama taji kuwa an dauketa dashi wa zata gani mahfux ne namfa yaran suka mata lilis ita da salma sai da hajiya taga zasuyi kisa tasa baki suka kyalesu.
Hajiya batulu fadi take wallahi, Wallahi sai kinyi danasanin ni kika ma haka kinsan da cewar gabaki daya a tafin hannuna kike shirya karbar sakamakonki, hankalin hajiyar mahfuz ya tashi dan tasan me take nufi su kuwa yaran ina suka sani fadi suke abar mana gida yayanmu ya rabu da bunsurar yarinyarki ya wuta da kuda.
Kai tsaye maqabartar dan dole ta nufa daga gidansu mahfuz din yaron da ta baima aikin binne binne tace duk ya je ya haqo mata ya kawo mata yace an gama.
Inda ta sa aka kai na tsohuwar rijiya ma duk aka ciro ta tara shirgin asiri tim gabanta ta zuba musu kalanzir gami da kunna ashana tuni suka hau ci da wuta.
Tasaki wata dariya Wallahi hajiya karima dani kike zancen kin riga kinyi sake da kika bari ni nasan sirrin komi naki waike uwar san jiki sedai ki bada kudi ni inje miki gun boka inkuka miki aikin yadda nasa aka binne na haqesu yadda naje nayi miki kike rayuwar fantamawa kike mulkar kowa gidanki to kuwa kinyi kadan.
Tun safe hankalin Hajiyarsu mahfuz yai mugun tashi ganin Baba tijjani da baba usman matsayinsu na qannen mijinta me rasuwa da sukazo gaidata suke tambayarta ina Ummulkairi ne basu ga tazo gaidasu ba wato tunaninsu game da yar qanin nasu ya dawo yanzu in mahmudu ya dawo me zata ce masa wato wanda yake me matsayin babba gidan yanzu.
Tasan ko mijinta be kaishi san diyar qanin nasa ba.
Ilai kuwa yana dawowa yaran kowa yaje ya masa barka da dawowa yana ta zuba idon ganin diyar tasu sedai shiru bayan yai wanka yaci abinci ya debo tsarabarta yayo bangarensu wato bangarensu Hajiya karima tunda anan yasan take tun rasuwar mahaifiyarsu.
Dakinta ya shiga sai dai yadda yaga dakin ya tabbatar babu mutun aciki duk yayi qura yai cudun cudin.
Tun yayansa nada rai basu cika shiri da karima ba hakan yasa take shaskarsa afusace ya futo yake kwala mata kira ta fito da sauri ina kuka maida yarinyar nan cikin rawar murya take tambaya wace yarinya fa.
Cikin fada yake magana zan tambayi wata yarinya bayan ummulkairi ta gurin Yasir hankalunta yai mugun tashi tama rasa amsar bashi dan gabaki daya ta gama rudewa.
Nasir ne ya shigo jin rikicin da ake hankalinsa ya tashi daqyar ya samu kawun nasa yai shiru ya zauna ya masa bayanin komi game da ummu har aurenta yanzu sedai bai fada masa wata aura dinba.
Hankalinsa yai qololuwar tashi yanzu duk yaushe hakan ta faru bamu sani ba yama akai haka cikin kuka hajiya ke fadin abin duk tayi ya miqe yana salati wallahi karima kinban mamaki ashe zaki iya haka nasan duk bazai wuce kan wannan gidan ba da yake mallakinta to gabaki daya kinja muku kowa gobe zai bar gidan daman ai ba namu bane muna zaune dan iyayenmu ne yanxu tunda suma basa raye se abarma me gida gidanta.
Gidansu Abbakar
Sabo sosai da shaquwa me qarfi ta shiga tsakanin Abbakar da ummu kullin suna farfajiya tare duda yawanci da maryam ko ummi ake karatun anman kallonsu kawai kai kasan da masoya ne masu san junansu iya so.
Duk yadda Abbakar yai yayi da hajita tace ina itafa babu zancen tarewa yanxu dole se ummu ta gama katatu ganin da gaske take yasa zuwa ya sami kawunta ya rattaba masa komi.
Aikam yasha fada kanyin aure bada saninsu ba yaita bashi haquri yace zaije ya sameta yaje ya fadowa nasa kawunnan yace to.
Gidan qaramin kawunsa yaje ya fada masa dan yasan inyaje gidan wan babansa dukansa ne kawai bazai ba dan mutumin kwai fada.
Shima kawu Barau din da bai cika fada ba yau ya ta6a dakyar Abbakar yai ta bashi haquri har ya yadda zaije ya fadawa wan nasu.
Aiko dakyar yasha kan yayyen nasu suka yadda zasu saka baki akan auren dan nasu.
Hajiya ta yadda ummu zata tare da sharadin dole aje dangin ummu su san da batun auren ba musu suka amince.
Gidansu Mahfuz
Washe gari da sassafe Baba mahmud ya tara qannensa ya fada musu komi harda hukuncin da ya yanke sun yadda kan jibi iyanzu sun bar gidan agurin ma wasu cikinsu suka fara kiran motar da zata kwasar musu kaya.
Ba wanda bai jin jina halin da ummu ta shiga ba da tausayinta agurin suka yanke shawarar sanya cigiyarta dan nasir bai fadi inda take ba zatonsu ta bace yanxu, hankalinsu bai qara tashi ba sai jin abinda mahfuz yai wasunsu ma ji suke kamar su dakeshi tada kam yashashi harda masu cewa basu bashi tunda ya rasa wanda zai ci mutunci sai yar uwarsa.
Abbakar ne yazo gidan kan kawunnansa nason zuwa ganin su baba mahmud yai mamakin ganinsu gabaki daya mahfuz nafaman kuka.
Ada baba mahmud yace sedai in wani satin anman jin yace kan ummulkhairi ne yace su zo yau da yanma kawai.
Tarba sosai suka samu duda gidan a hargitse yake kowa na qoqarin hade kayansa ne sosai hankalin su Baba mahmud ya tashi kanjin har wani aure akama ummu bama da saninsu ba.
Budar bakin Baba mahmud se cewa yai ai ina maganar tarewa bai taso ba yadda akayi mata dole barin gidan nan ina da tabbacin dole aka mata aka mata aure dan haka kawai kuce ya bata takardar ta yarinyar mu nada gata in ta sami wanda take so to lokacin zamu aurar da ita.
Komi suka ma Abbakar bayani game da yadda sukai da iyayen ummulkairi aikam hankalinsa ya tashi sosai da kansa yaje yasamu baba Mahmud aikan rufe ido yai kamar be sanshi yahau yazauna sakin ummu dole gida Abbakar ya dawo ya sanar da hajiyarsa.
Itama hankalinta ya tashi taje har gida ta sami baba mahmud sun gaisa cikin mutunci ta masa bayanin komi yai murmushi fiddausi kenan nasan kun mana da kuka riqe mana yarinyar nan anman hakan baya nufin zamu biya ku tukwici da yima yarinya auren dole dan kawai danku nasanta.
Duk yadda hajiya taso ya fahinta ya kasa fahinta haka ta tawo gida rai babu dadi.
Ganin yayi duk yadda zaiyi ne kan sakin ummu Abbakar yaqi yasa yanke shawarar zuwa har gidansu Abbakar din ya dauko ummu ya kuma sanar musu tabbas qara zai shigar indai nanda kwana uku bai kawo sakinba.
A gidansu Abbakar tabar yaron nata Abbakar gurin hajiya dan ta yaye mata shi.
Ummu tai mamakin ganin gidan da ya kaita can unguwar karkasara me makom nan naqotansu Abbakar bata tambayi dalili ba dan ranta duk babu dadi bataso barin gidansu Abbakar ba tayi sabo sosai dasu bana wasa ba tanajinsu aranta anman batasan nunawa kawun nata iyakarsa.
Komi sabo aka saka mata adakinta ita da Abbakar dinta ahankula tadan fara sabawa da zaman gidan babu inda take zuwa dan anyi hutun sch balle tasa masoyinta a idanunta ko bacci basosai take ba cikin tunaninsa take.
Bata taba zaton tanasansa haka ba sai yanzu dan ada tana qoqarin yakice shi zatonta bazai taba santa ba anman yanzu da ta riga ta saba dashi ta saba fira dashi ya koya mata sansa ji take raba ta dashi kamar ta'addanci ne babba sedai ita batasan me zatai ba.
Satinta biyu gidan baba mahmud yaje ya amso Abbakar qarami dan ganin ummu taqi sakewa zatonsa ko rashin yaronta ne tunda Nasir yasanar masa tanasan dan dayawa.
Kwana biyu yaron ya saba da kowa dan baida rikici musanman gidan da yake da yara sunzo hutu jikokin gidan sai warkajaminsa yake abinsa.
Tunda ummu tazo gidan bata ta6a farin ciki irin na yauba taji dadi sosai Baba mahmud ne yazo yafada mata ta shirya zasu Jordan can gurin ummanta tai murna ba kadan ba.
Nan ta shiga hada musu komi dan gobe ne tafiyar ita da Abbakar dan su uku zasu tafi daga ita sai danta sai baba mahmud.
Yanzu abu daya ke damun ummu rashin masoyinta Habunta anman indai fannin iyayene duk cikin yayun babanta kowa nan nan yake da ita danma taqi sakewa dasu kamar da.
Sun shiga mota ta tuno ta dauki wayarta ta turawa Abbakar saqo pls izini zamu jordan a samu a addu'a afadawa hajiya.
Baba mahmud na kallonta tai kamar be ganta ba yace kawo yaron jeki kice ma kadija ta baki saqona tace tota miqa masa yaron tai ciki ya dauki wayar yana duba saqon.
Har ya turo amsa Allah yasaukeku lpy abar sona dan Allah kiyi wani abu kar a rabamu pls ajiye wayar kawai yai ganin ta tawo.
A Jordan
Bayan sun sauka mota ta daukesu sai gidansu ummanta kowa yaji dadin ganinsu musanman kakanninta sai washe gari aka dibesu zuwa gidan umman nata.
Tunda ta shiga falon ummun nata kishi ya rufeta ummanta ce jikin bango a hoto sai yara suma larabawa uku manne jikinta mijinta gefe tai saurin dauke idanunta daga hoton duk inda ta duba sune.
Yan matan biyu masu kama da ita suka fito dan ganin su waye ganinsu yasa komawa ciki da gudu dan kiran momy dinsu suka fito tare har namijin wanda da gani shine qarami befi 9years ba kishi ya rufe idon ummu hawaye ya fara kai kawo aidonta.
Wato ummanta ta ma mance da tana da yarinya a Nigeria tayi aure ta samu wasu ita ta badda marainiya ba uwa ba uba tunda ta yayeta ta tafi bata kuma nemanta ba.
Danta ta sura taja baba mahmud mu tafi nafasa banasan ganinta muje Kawai take fada tana kuka ganin bazai tafi bane yasa sakinsa tai gaba.
Dasauri umman nata tai gunta dan tana dan fahintar hausa ba sosai ba ta ruqota gami da dorata a kafadarta tana lallashi dakyar tai shiru.
Haba ummu kin taba ganin inda uwa ta mance da danta kina raina babu yadda zanyi ne.
Yaran sukaita kawo mata abu buwa wasu duk hotunan tane jiki tana qarama sunata murnan ganinta seda ta kula sosai taga ashe hoton farko ma kana shigowa shi zaka gani kamin nasu dukansu itace rungume jikin umman nata da alamu ma ranar da zasu rabu ne tadan share hawayenta kamin tace cikin harshen turanci dan larabcinta be kwari sosaiba.
Anman mum me yasa haki kuma wai wayata ba.
Ummu babu ce tasa tun bayan dawowata daga qasarku babana yai rashin lafiya sosai duk abinda muke dashi dana gadona duk ya qare gurin jinya har bashi muka dinga amsa qarshe ya rasu.
Shekara daya da rasuwarsa na auri babansu Nasrin shi ba wani me arziqi bane da zai iya daukan nauyi na inzo nageria albashi nama haka muke hadawa gurin kula da yaranmu da iyayenmu dan da nasa iyayen da nawa duk suna buqatar temakonmu.
Ummu ta kuma rungume ummanta tana qara bata haqurin fahintarta bai bai.
Koda Dahir ya dawo bakowa falon sai ummu yana ganinta ya ganeta dan yasan basu da dan uwa baqar fata sai diyar matarsa bayan mugun kama da sukai da matar tasa.
Da sauri ya qaraso ya rungumeta yana fadin ummulkhairi ya kuma dubon fuskarta dadi ya cika ummu tabbas ummanta bata mance da ita ba tunda har mijinta da akasan larabawa da kishi yasan da ita.
Watanta guda cif taji dadin zama dasu sosai soyayyar uwa kam se yanzu tasan me ake nufi da ita dabadan tanasan mijinta ba babu yadda za'ai ta yadda tabi baba mahmud Nigeria.
Sunyi shawara dashi kan tanasan kudinta na account dinta ya cire mata zata baima ummanta dan ta fusksnci suna wani hali tunda ita ba abinda take dasu ya amince.
Aikam tasha albarka dakyarma umman nata ta yadda suka amshi kudin haka ummu ta tawo suna kewar juna.
Nigeria
Ummu ce biye da Abbakar yana ihu shi baza'a masa wanka ba ya 6oye jikin baba mahmud yai saurin dagoshi mutumin lafiya dai kake yawo ba wando se nasa anma kaciya ko baisan kaciya ba yasa dariya baban ya nuna masa gurin nan zansa a yanke ya tsanyara kuka ummu taja ta tsaya turus ganin abinda ke faruwa.
Hajiyar mahfuz ce tsaye tana kuka tana roqon baba mahmud ya batta taga ummu zata nemi afuwa, ganin ummu tayo gurin zata zube qas ummu ta dagota tana girgiza kai alamun a'a.
Umma ni na yafe miki karki durkusa min ha juma da mancewa da komi hajiya taita godiya harda daukan Abvakar taita masa wasa.
Tun daga lokacin ba'a sati sai hajiya tazo gidan se alokacin ummu tajiashe kowa yabar gidan taje taita roqon baba mahmud dakyar ya amince kowa ya koma gidan tace ita indai gida nata ne to kowa ta bar masa bangaren da yake bangaren Abbanta kawai takeso da kakarta.
Farin ciki ya dawo gidan kowa nasan ummu Abbakar qarami haka kowa nasansa ko yaushe yana gun hajiyar mahfuz.
Mutun daya ne ko kallonsa ummu batayi shine mahfuz dan sosai ta tsaneshi danma yanzu yana yawan shiga sabgar danta komi ya samu sai ya kawo masa yaron shima bini bini uncle mahfuz a bakinsa abinda kedan rage mata haushinsa kenan.
Ummu zaune gaban baba mahmud daman zancen rabuwar aurenki ne nayi shiru da batun zuwa ki dawo daga jordan wani satin zamu fara zaman kotun.
Tama rasa me zata ce hankalinta ya mugun tashi ko bakiji bane to kawu Allah ya kaimu ta miqe tana tangadi dan jin jiri na qoqarin kwasarta tana shiga daki ta fashe da kuka.
Yau aka dawo da Abbakar daga gidansu Abbakar babba daqyar ya dawo danshi in ya je guri dagyar yake yadda ya dawo sabida sabo seda Abbakar babba yai masa dabara ya tafi yanata kuka.
Baba mahmud ya bita da kallo kamin ya miqe yai cikin gida dan dauko Abbakar za'a masa kaciya dan sanyi yazo.
Kai tsaye gurin ummu yai da yaron ya tsaya abakin qofa jeka ka kiramin ummanka ya shiga da gudu yana fadin mome tizo mamu afi anguwa tai saurin goge hawayenta ta dubi yaron.
Ya mata kyau sosai jitai kamar tace abar kaciyar se ya kuma girma tadai daure muje to yasa kuka auke shi wai ta daukeshi tai dariya dan rikici gami da daukansa.
Har mota ta kaishi gami da shafo kansa suka fice yana daga mata hannu.
Yara da yawa an musu kaciyar a idansa yaga suna fitowa yadda yake ganinsu yasa shi fara kuka.
Hankalin masu kaciyar yai mugun tashi ganin yadda yake bleeding abin ya wuce hankali dole suka futar dashi daga dakin zuwa dakin temakon gaggawa.
Likitoci sun duqufa kansa tuni suka gano ai haemophiliac ne jini duk yadda sukai ya tsaya yaqi gashi babu allurar da ake musu masu cutar a asibitin se ma anje zariya babu tabbacin ma kan aje yana raye.
Jini na zuba ana qara masa wani yaron yayi mugun jiqata rai ahannun Allah hankalin baba mahmud ya tashi tuni ya buga waya zuwa gida.
Ko ummu va'a fadawa ba suka bayyana a asibiti harda su Abbakar kowa ya tausaya ma yaron kowa ya damu dan yaron ya shiga ran kowa.
Minti talatin tsakani Abbakar ya rasu dedai da baba mahmud duk dakiyarsa seda ya zubda hawaye dan mutuwar ta dakeshi kai kace wani babba ya rasu.
Su kansu ma'aikatan sunji mutuwar dan dan awannin da yaron yai gurin kamin fara kaciyar yadda yake da faran faran da surutu har sun saba.
Komi Baba sani ne yayi aka basu gawar sukayo gida dan baba mahmud ya kasa komi gani yake kamar qarya ne yaron be mutu ba yanzu yanzufa suke wasa da dariya dashi ina shibqarya ne be mutu ba......
0 comments:
Post a Comment