Da masifar su suka shigo
"wallahi sai an fito mana da ɗan mu" yayar badia ce hauwa a gaba tana masifa tana ƙarawa
A zaune suka ga mummy da sabit sun zuba uban tagumi suna sharɓe kuka
"badia wallahi baki sa ar miji ba, ace namiji da kuka ke kuma kiyi me" wannan maganar ta ƙonawa mummy rai sai ta tanka
Aikuwa nan da nan aka hau zage zage, mmn badia ce me cewa
"wallahi sai mun kai yarinyar nan kotu sai alƙali yai mata munmunan hukunci, wallahi sai tayi zaman gidan yari, ku ma baku tsira ba wallahi sai an ƙwatar wa badia ƴancin ta a gidan nan kun mai da ita baiwar ku"
Faɗa sosai shi dai sabit yana zaune ya kasa taɓuka komai yana jin yadda ƴan uwan badiar suke ci masa mutumci duk da dai yana ganin laifin su amma asmau ta fi kowa ƙona masa rai
Cikin hukuncin Allah sai ga muktar wan sabit shi ya shigo yai musu jan wuya sannan suka haƙura suka tafi akan su jira kiranye daga court
"kuma wallahi idan court ta karɓar mana ɗan wallahi ya bar gidan nan ke nan har abada tunda dai baku iya kula da shi ba har kukai sake wata yar aiki ta sace shi wallahi annur ya bar hannun ku har abada"
Injimn badia ta faɗa tana yin waje
Sabit kara fashe wa yayi da kuka
"don Allah mummy ina zanga asmau wallahi yanzu bazan mata komai ba don Allah ta dawo min da ɗana wallahi na yafe mata wallahi na daina yi mata duk abinda nake mata, wallahi ina son annur sosai wallahi bazan iya rabuwa da shi ba"
"kai sabit wane irin mutum ne kai kamar ba namiji ba ka zauna sai kuka kake tayi, ita kuma mummyn tace me" inji muktar
"don Allah muktar kar ka bari a ƙwace min annur wallahi ina son ɗana" ya faɗa yana me riƙe ƙafar muktar ɗin
"wai mummy me yasa yarinyar nan ta ɗauke annur ɗin ne, ko faɗa suka yi, in banda abinta ai ko faɗa kuka yi ba kya ɗauki ɗan da ba naki ba" muktar ya tambaya
Sam mummy sai ta kasa cewa komai don bata ma san ta ina zata fara ba, sabit ma shiru yayi
******************
Fannah tana ɗakin ta suna waya da asmaun tana faɗa mata yadda gidan ya rikice, sam ko a jikin ta asmau bata ji komai ba, ita burin ta ma Allah ya sauke ta lfy wallahi ƙarawa gaba zatayi da ƴaƴan ta taje ta nemi dangin uwarta
Saboda tasan ko baɗe ko ba jima anty fannah zata iya tona mata asirin inda take
Sai da ta kuma jawa fannah kunne akan kar ta sake ta faɗi inda take sannan sukai sallama
Tun ana ɓoyewa daddy har yazo magana taje wajen sa, ranar mummy ta sha faɗa sosai kamar ba gobe daddyn yai mata yai wa sabit wanda a yanzu yake kwance saboda zazzaɓi da ya rufe shi
Takanas daddy ya saka mutane suka kama hanyar garin su asmai don ganin ko ta je amma ba same ta ba
Tas ya tara mutan gidan akan su faɗi ko akwai wanda yasan inda asmau take, amma duk ba wanda yasan inda take
"har ke fannah don naji ance kullum kuna tare" jikinta ne ya fara rawa don ita fannah Allah yayi ta surutu amma sam bata da zafi sanyi gareta da kuma sanyin hali
Amma da ta tuno irin cin kashin da sabit ɗin ya ɗinga yi wa asmaun sai ta dake tace
"nima ban sani ba"
"to duk lkcn da ta kira ki ki ce mata ta neme ni koma menene wallahi sai na ƙwatar wa yarinyar nan ƴancin ta tunda dai na lura kamar zaman haƙuri take yi da ku, in ba haka ba tayaya za ayi ace ta ɗauki ɗan da ba nata ba ta gudu an rasa ta ko sama ko ƙasa"
Ya juyo ga mummy
"anya fatima ke uwa ce kuwa tayaya za ayi ace wai a gidan ɗan ki ana samun matsala amma sam baki sani ba, wane irin abu ne wannan, kince ke ƴaƴan ki baza suyi nesa da ke ba amma kuma sam ba kya kwaɓar su
To wallahi ku sani duk wanda na same shi da laifi a guduwar yarinyar nan sai nayi mugun saɓa masa, kuma ku shirya jibi monday zamu fara shiga court don iyayen badia sun kai ƙara an aiko mana da sammaci sai ku shirya"
Sabit da ke zaune kamar mutum mutumi sai ya ƙara narke wa ɗan zazzaɓin da ke jikin sa nan da nan ya kuma hauhawa, shi sam be ma san ya zai yi ba
Miƙewa yayi don ya tashi dole duk yadda za ayi ayau sai ya nemo inda asmau take don kuwa wallahi bazai yiwu ace ya yi rashin ɗan sa ba
Don kuwa ya san indai suka shiga court ɗin nan da badia sannan suka ci case ɗin dole ne ace ya bata ɗan in kuwa ya bata shi ya zaiyi da rayuwarsa
Miƙewar nan da zai yi sai jiri ya kwashe shi ya faɗi ƙasa a sume, a guje akayi kansa inda mummy kuma ta fashe da kuka
Ruwa aka kawo aka yayyafa masa nan da nan ya farfaɗo jikin sa kamar garwashi saboda zafi
Yana farfaɗowa kuka ya saki ya riƙe hannun mahaifin sa
"daddy don Allah kar ka bari su raba ni da ɗana, ƙila shi kaɗai ne ɗan da zan so a duniyar nan don Allah daddy a nemo min asmau ta bani ɗana a maidawa badia ɗan ta saboda ta barshi a gidan nan"
Ko wa a wurin sai da hankalin sa ya tashi, isma'il ne ran shi ya ɓaci ya fara magana
"wallahi yarinyar nan idan na sake na ganta Allah ko su badia basu kai ta kotu ba ni sai na sa an hora ta wane irin abune wannan"
Lefi suka dinga ɗaurawa asmaun bayan sam basu san gaskiya suna ta ƙoƙarin cusa wa daddy magana saboda ya ji haushin yarinyar, da fannah ta ga haka sai kawai tace
"nasan inda asmau take"
Gabaɗaya kowa ya waigo gareta har da daddyn
"tana ina, suka haɗa baki"
Nan da nan fannah ta kwashe inda asmau take ta faɗa musu amma sam bata faɗi dalilin zuwan asmau gidan ba
Sabit shine a gaba ya fice domin tafiya, daddy ne ya tsai da shi
"kai baka da lfy yi zaman ka nida isma'il da ita fannah zamu je mu dawo da ita" inji daddy
"ka kira badia a waya su zo nan za a kashe maganar kafin aje court a kashe maganar a gida"
Amsawa sabit yayi ya ɗauko wayar sa yana neman number badia wacce tunda abin ya faru ta koma gidan su
Bayan ya samu badia ya faɗa mata ne ya zauna amma ba don ransa ba ya so ace yaje wallahi da sai asmau ta gane bata da wayo
Ina kwance sai jin muryar anty fannah nayi a kaina
"ki fito da daddy muke"
Rasa abinda zanyi nayi na ɗauka na ja mata kunne ashe sam bata ji
"asmau ki tashi mana na ce miki da daddy muke"
Miƙewa nayi jiki na a sanyaye, na fito na same shi yana zaune a falon gidan da isma'il da kuma wan anty fannah
Ina fitowa na gaishe su, daddy da fara'ar sa yace min
"me yaji munzo mai da ke ɗakinki maza ɗauko kayanki mu tafi"
Bazan iya masa musu ba na shiga ɗakin, anty fannah ce ta ɗauko min annur inda ni kuma na kwaso kayana muka fito
A mota ba wanda yace min komai sai ma ɗana dana karɓa daga hannun anty fannah na rungume shi duk da ƙaton cikin da ke jikina
Da sallama muka shiga babban falon gidan wanda yake cike da mutanen gidan harda mutan gidan su badia
Tana ganina ta yo kaina da zagi wai in bata ɗan ta
Daddy ne ya dakatar da ita inda yace duk a zauna a tattauna me yasa na ɗauke annur ɗin
Sai dana zauna sannan daddy ya buƙaci ai masa bayanin abin da ke faruwa, sabit ne ya wangale baki yai masa bayanin, yadda aka samu annur
Ba daddy ba hatta ƴan uwan sabit sai da suka jinjina maganar nan, daddy kuwa faɗa ya dinga yi yana ƙarawa sai da yai wa sabit wanki babban bargo sannan daga baya yace
"sabit wai duk bokon ne ya saka haka ko menene, dashe ka sa akayi wa matar ka saboda ɗayar matar taka ta cire mahaifar ta"
Rufe ido daddy yayi ya zage tas shi da badia bayan ya gama sannan kuma ya ɗaura da nasiha akan abinda muka aikata gabaɗayan mu haramun ne
Ko da kuwa dukan su matan ka ne bw hallata a ɗauki ƙwan ɗaya a saka wa ɗayar ba haram ne wannan
Duk wani abu daya danganci dashw na ciki indai akwai mutun na uku daya shigo cikin abun ko da kuwa ko wane kusanci ne tsakanin su to ya haramta
Faɗa sosai daddy yayi musu duk sai suka rasa bakin magana
"ai asmau tana gaskiya ɗa ɗan ta ne babu wata badia, tai wahalar ɗaukar ciki ta sha naƙuda yanzu kuzo kuce wani ɗan badia tayaya akayi ɗan ya zama nata, to ku sani wallahi daga yanzu na gama case ɗin nan asmau ki ɗauki ɗan ki zan ga wanda zai kuma kawo maganar annur anan, kai in banda ma kai sha sha sha namijin kawai ka ɗauki ƙwan matar ka ka dasawa wata idan ɗan ya girma kace masa wacce ce uwar sa, wacce ta ɗau cikin sa ko wacce yake da jinin ta"
Dukkan su jikin su ne yayi sanyi in banda badia wacce tace
"wallahi sai kotu ta ƙwatar min ɗana" ta faɗa tana kuka
"ai dole ne ɗa jinin ki ne duk inda aka je akai gwajin jini jinin ki za agani don haka ban ga dalilin da zai sa ace don mace bata da mahaifa ba ace kuma sam bazata
mallaki ɗan kanta ba" inji maman su
Gyara zama daddy ya yi ya fahimtar da mmn badia sharia akan duk wacce ta ɗau cikin ɗan adam ta kawo shi duniya itace mahaifiyar sa amma sam matar nan bata yadda fuuuuu haka ta ja badia suka fice
Sabit wanda jikin sa yai sanyi ya ƙaraso kusa da ni zai ɗau annur daka masa harara nayi na miƙe tare da daukar ɗana na fice
Babu wanda ya bashi gaskiya kowa sai rashin gaskiya yai ta bashi,
Ɗakin na da ke part ɗin mummy nan na koma na kwanta, sabit ne dai ya kuna shigowa,
" Na fahimci har yanzu taurin kan ki na nan, kina gani idan munje court gobe zasu baki annur ni ne dai uban annur kuma nace baza ki renar min ɗa ba"
"kai ma ai bamu fara da kai ba, idan an gama case ɗin annur a court ɗin dole ne ka bani takarda ta don kuwa na gama aure da kai"
"zan ga wanda ya isa ya sani sakin ki" ya faɗa a fusace
"wannan kuma in munje court ɗin na gabatar wa da alƙali buƙatata idan ya saka ka sake ni kace kai baka yadda ba"
Haushi ne ya kama shi sosai ya fice daga ɗakin ko ganin annur ɗin ma be yi, nima na bi ƙofar da mukulli sannan na kwanta sai da safe Allah ya kaimu court ɗin inga in za abata ɗan bayan bata san komai nashi ba
*******************
Kashegari da wuri na tashi na shirya ɗana don zuwa court duk da dai yanzu sam hankalina ba a kwance yake ba ga ciki amma hakan be hanani gyara fuskata ba
Mummy ce ta shigo wai daddy na kirana
Hijab ɗina na ɗauka na same shi a falo yana zaune, har ƙasa na durƙusa na gaishe shi ya amsa min sannan ya kuma kwantar min da hankali na
"nayi wa lawyer na magana shine zai kare ki koda kuwa jinin badia ne wannan yaron. Amtsayinki na wacce kika ɗau ɗawainiyar yaron nan sharia ta baki naki ne ko ina suka je ke kika haife shi ɗanki ne"
Hankali na ya kuma kwanciya, anty fannah ce ta shigo itama taci laffayar ta,
"daddy nima dani za aje, don kuwa nima shaida ce, kuma ina kamun ƙafa idan an gama case ɗinnan ni zan karɓe shi ko asmau" gyaɗa mata kai kawai nayi amma wallahi bazan iya bawa kowa ɗana ba
"to ai shike nan wannan ɗan ƙaramin case ne nasan ayau za a gama shi ma idan kun shirya sai ku fito"
Mummy har gabana ta zo nasiha tai min sosai wallahi har jikina yai sanyi, akan kar in sake in bari a ja shariar da tsaho don mafi akasari idan ana faɗa akan ƴaƴa to wallahi su take shafa
Gabana ne ya faɗi na ƙara matse abina a jikina in shaa Allah yau za a gama case ɗin tunda dai ƙiri ƙiri ga yadda abin yake
********************
Badia ce da mmn ta sai lawyern da suka ɗauko a zaune duk abin duniya ya ishe su,
"gaskiya hjy kamar yadda na faɗa miki duk inda aka je indak ƙasar nan ne baza a taɓa badia ɗan nan ba tun da dai a ƙundin tsarin mulki na ƙasar nan wacce ta kawo ɗa duniya itace uwa"
Kuka badia ta saki
" wallahi ƙwai na ne fa, ya za ayi in ɗau ƙwai na in bawa wata ƴar iska ita in banda rashin godiyar Allah ma gawani ɗan iskan ciki nan a jikin amma kuma bata godewa Allah ba sai ƙwaya ɗayan nan shine zata ce sai ta raba ni da shi, mummy don Allah ya zamu yi wallahi zan iya rasa rai na idan aka ƙwace min annur"
"yi shiru yi shiru inji mummy yanzu kai barister ya kake ganin za ayi"
Shiru yayi can sai ya e
"to akwai mafita amma sai in me gidan ya yadda da hakan" nan da nan ya tsara musu yadda za ayi
Ba musu suka yadda nan da nan badia ta kira waya lagos ta faɗa wa dr. ɗin nan da tayi dashe akan ta bar asibitin na ɗan wani lkc kuma ta kashe wayar ta
Shi ma sabit ta kiɗa shi ta faɗa masa shawarar da barister ya yanke, nan da nan ba tare da wani shawara ba yace ya yadda duk yadda suke so hakan za ayi
********************
*COURT*
Sai da aka gabatar da case 4 sannan aka kira su, inda magatarda ya gabatar da case ɗin su, aka kirawo badia da asmau kowacce ta gabatar da kanta
Alƙali ya nemi badia tai bayanin abinda ya faru
"asmau kishiyata ce, kusan a tare Allah ya azirta mu da samun ciki, amma ta riga ni haihuwa inda ita ɗanta be zo da rai ba, ni kuma nawa yazo da shi, kuma shine wannan na hannun natan
To kasancewar ban da ruwan nono sai mijin mu yace asmau ta dinga bawa ɗana nono, shine yanzu ta ɗauke min shi ta gudu da shi wai nata ne"
Sakin baki kawai su anty fannah sukai suna kallon ikon Allah, sai da alƙalin ya gama rubuce rubucen sa sannan ya tambayi asmau ita kuma ta faɗi me ya faru
Nan da nan na zayyano duk yadda akayi na samu cikin annur, kowa a court ɗin sai ya ɗau salati aka fara ƴan ƙananan surutai
Sai da alƙalin ya doka ƴar gudumar sa sannan akai shiru,
"ina me gidan nakun"alƙali ya tambaya
Nan da nan aka taso ƙeyar sabit ya fito, alƙalin ya tambayi cikin mu wake faɗar gaskiya, mutumin nan be ji kunyar Allah ba sai buɗar bakin sa yace
" badia ce take faɗar gaskiya"
Hmmm sabit in bakai haka ba ai baka cika ɗan halak ba
"to malama asmau kinji abinda mijinku yace ko ke kina da taki shaidar"
Gyaɗa kaina nayi sannan ya bani damar faɗar menene nan nace masa dr. ɗin da tayi min dashen kasancewar bata nan ya sa aka ɗaga ƙarar har sai dr. ɗin tazo da kanta
Daga nan sati biyu akan mu zo da dr. ɗin, aka sallame mu bayan alƙalin ya ja min kunne akan kar ya sake naji na bar gidan balle in tafi da ɗan
*******************
Tun a mota daddy yake faɗa akan abinda sabit yayi, yana komawa gida ya faɗawa mummy ita ma sam bata ji daɗin hakan ba
Daddy ya tambaye ni number dr. ɗin don a kira ta a faɗa mata abinda alƙalin yace
Tooo nan fa ake yi don gabaɗaya ban san komai na dr. ba ni ko sunan asibitin ban sani ba, don inda akai min dashen daban inda kuma muke zuwa nan ma daban ne
Babu yadda zasu yi dole ne aka nemo sabit don ya faɗi a ina za a samu, abin takaici wai sai sabit yace shi ma be sani ba wai badia ce ta san ta
Haka daddy ya zaunar da sabit yai mai masa nasiha, tunda ya ga faɗan ma sam baya shiga, amma ƙiri ƙiri sabit yace shi be san zance ba
Daddy ya rasa yadda zai yi da sha'anin mu, don yasan ko ana ha maza ha mata badia baza ta taɓa faɗar address ɗin dr. ɗin ba balle ayi contacting ɗin ta
Zaunar dani yayi yai ta min nasiha, sannan yace min in Allah yayi annur zan rayu a matsayin ɗana too in kuwa Allah yayi kotu zata bawa badia to a matsayi na na uwar sa ba abinda zai so daga gareni face in kasance ina masa addu amma shi sam baya son ai ta ja'inja akan yaron don kar abin yai affecting ɗin sa
Tabbas maganar daddy haka ne amma kuma in shaa Allah addua zan dage da ita kan Allah ya bayyana mana da dr ɗin nan
[7:15PM, 5/4/2018] +234 806 779 9926: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
*HIKIMA WRITERS ASSO.*
P⃗a⃗g⃗e⃗ 24 🌹
Renon ciki na nake yi hankali na a kwance ga ɗana a kusa dani, sam su sabit basu tafi da shi ba nima na so hakan
Duk wani siyayya mummy tayi haihuwar kawai muke jira, amma saɓanin saɓanin cikin annur wannan cikin girma gare shi sosai da sosai
Har anty fannah tana cewa ko dai ƴan biyu ne, ko da muka je scanning twins ɗin ne kuwa
Muna dawo wa anty fannah ta faɗawa mummy, bashiri mummy ta kwashi anty suka tafi kasuwa aka sake sabuwar siyayya
Cikina yana da wata 8mths sabit suka dawo shida badia, sam duk wannan abunda ake yi badia bata san da cikin ba
Tun da suka zo bamu haɗu da sabit ba, dana ji alamar zai shigo sai in gudu ɗaki duk wannan abun Allah bai taɓa haɗa mu da shi ba
Kwanan su uku da dawo wa ya badia ta zo da kanta lkcn ina ɗaki ina bacci ta ɗauke annur, ita kanta badiar bata san da cikin ba
Ko da na tashi, sai ban ganshi ba, sai na tambayi mummy yana ina sai mummy tace min ai badia ce ta ɗauke shi
Ba badiar ba hatta mummyn ta bani haushi yadda har ta bar badia ɗaukar sa bayan tasan ƙyuya gare shi
"mummy bari inje in ɗauko shi kin san halin annur idan ya tashi be ganni ba"
"to shike nan ni sai da na hanata sai tace wai sabit ne yace ta ɗauke shi"
Ficewa nayi daga part ɗin na doshi part ɗin sabit da tsohon ciki na, a hankali nake tafiya don kuwa cikin yai girma dayawa fiye dana annur
Tun kafin in ƙarasa ciki nake jin kukan yaron nan yana kira na, sai na ƙara ɗaga ƙafa, da sallamat na shiga tana zaune akan kujera tana kallo shi kuma yana zaune a ƙasa a kusa da ƙafar ta yana kuka
Sallamata ce ta sata juyowa, ai kuwa ta ci karo da ƙaton cikina, wani ashar ta daddage ta ɗura sannan ta ƙaraso inda na ke kamar wacce zata dake ni
"uban waye ya miki cikin nan"
Kallon ta na tsaya ina yi yadda take huci kamar zaki, sai nishi take yi kamar wacce take shirin yin dambe
"tambayar ki nayi uban waye yayi miki cikin nan" ban kula ta ba saboda tsayawa ma kula ta ɓata lkc ne ai ta san zaman aure nake yi
Wuce ta nayi na ƙarasa kusa da annur zan ɗauko shi, ji nayi ta jawo ni sai saukar mari naji a fuskar ta, kammm bata ajiye ba nima na kai mata bama ɗaya nayi mata biyu
Sannan nace mata
"kina san ki san wanda yai ciki tooo mijina ne, kafin wannan ma na taɓa ɓari, kafin in haifi annur banza kawai wacce bata san inda yake mata ciwo ba"
Ban ankara ba kawai sai jin matar nan ta hau ni da kokawa tana ihu tana kuruwar
"ƙarya kike yi me sabit zai yi da ke" faɗa sosai mukai da ita
Kasancewar cikin da ke jikina yai min nauyi ya sata samun galaba akai na hai ta kaini ƙasa ta shaƙe ni tare da cewa
"wallahi duk macen da tace zata haihu da sabit sai na kashe ki na kashe abinda ke cikin naki inga abinda za ai min tunda ba wani gata gare ki"
Duka ni kuma na dinga mata inda tana ta ƙoƙarin haye min ruwan ciki Allah ya jeho anty fannah, da saurin ta ta zo ta hankaɗe badiar daga kaina
Tafiya tayi taje ta daki bango wanda har sai da kanta yai ciwo amma sam bata daddara ba kafin anty fannah ta ɗago ni tuni ta yo kaina
Wannan karon da ƙarfi anty fannah ta hankaɗa ta sai kuwa ta faɗa kan annur inajin yaro na ya ƙwalla wata irin ƙara, hankali na ne ya tashi na miƙe da ƙyar na yi wajen sa amma anty fannah ta hanani ta janye ni muka bar part ɗin
Hankalina sam ba a jikina yake ba naso in san me ya samu yaro na amma anty fannah ta hanani
Part ɗin mummy muka nufa anty fannah tana bata lbrin yadda ta ganmu ni kuma ina ce mata annur fa yaji ciwo
"ai dole sabit ya san wannan rashin hankalim da matar sa tayi" inji mummy
"Baki ciwo ba ko" girgiza kaina nayi,
"amma mummy annur kamar ya ji ciwo faaa"
"ina ruwanki da wani annur duk kin bi kin ɗaga hankalin ki akan yaro bayan uwar sa ba sanki take ba"
Kuka na saka musu ni kaɗai na san abinda yake damuna akan irin abinda sabit yake min gaskiya na kai matuƙar ƙarshe a haƙuri
Ganin ina kuka yasa mummy tace min in daina sanna in shiga ɗaki na in kwanta in huta tunda ba abinda ya same ni ita kuma badiar bari sabit ɗin ya dawo za ta ja masa kunne ya faɗawa matar sa ta fita hanya ta
Anty fannah ce ta taimaka min duk da bana jin komai har ɗakin nawa, ban daina de kuka ba, abin ya min ciwo, anty fannah ce ta zauna kusa da ni tana bani haƙuri
"wallahi anty fannah haƙuri na ya ƙare na zo ƙarshe wallahi sai na nuna wa duniya wacece mahaifiyar annur"
"ban gane ba"
Nan da nan na hau mata bayanin yadda aka samu annur, sai da naga tas sannan ta hau ni da faɗa wai nayi wauta ai duk inda muka je bani da gaskiya, tunda ga yadda aka haife shi har kuɗi na karɓa
Kuka na dinga mata ni dai a gaskiya ɗana nake so a hannuna, kukan da nake mata ne ya sa jikin ta yin sanyi, kuka wiwi haka na dinga mata
"yanzu asmau ya kike son in miki"
"ni wallahi in ba barin gidan nan nayi ba wallahi zan iya mutuwa don na gaji da matsalar gidan nan" kuka na dinga mata
Kasancewar tana sanyi ya sa ita ma ta saki kuka, muka haɗa kai muka dinga kukan,
"don Allah anty fannah ki taimaka min"
Kuka ne ya kuma ƙwace mata, mu kai me isar mu muka lallashi sannan ta hau ni da nasiha, ita dama anty fannah haka take sam bata da zafi bata taɓa ce min rama ba
"asmau wannan matsalar ke kika jefa kanki a ciki don haka ki cire annur a ranki ki mai da hankalin ki akan wannan Allah ya raba lfy"
"anty annur ɗana ne don me zaki ce in ƙyale shi"
"ba wai nace ki ƙyale shi har abada ba, amma 4 now ki ƙyale shi"
"wallahi anty na gaji da zaman gidan nan, don Allah ko wani gurin ne ki kai ni in huta in samu in sauka lfy kafin in haihu"
"in banda abin asmau ina kika taɓa jin gidan miji yai zafi, komai aka yi miki haƙuri zakiyi, kuma in shaa Allah wataran zai zama tarihi, dukkan me haƙuri wataran dole ya ga amfanin hakurin"
Kuka na dinga yi tana bani haƙuri tare da cewa ita ba inda zani kawai in zauna in shaa Allah akwai ranar ƙin dillanci, amma don Allah sai yaushe ne zan ga wannan lkcn Lallashi na ta dinga yi tun ina kuka har na zo na haƙura amma wallahi daga yanzu bazan kuma ɗaukar cin kashin shi ba
Sai da ta tabbatar na haƙura na kwanta sannan ta tafi, kuka na kuma fashewa shike nan ni ke nan a haka zan ƙare banni da wanda zai kare min ya Allah ka kawo min ɗauki, bacci ne ya kwashe ni
********************
Sabit yana wajen abokan sa yaji call ɗin badia tana kuka wai ya zo yaga asmau da fannah sun haɗa su ita da annur sun musu duka
A guje ya garzayo ya zo ya tarar da su cikin jini, shi ma kanshi annur ɗin ya kuje a goshin sa
Ita kuma ta ciwo a ƙafar ta yana ta jini, tana ganin shi ta fashe masa da kuka
"sabit kaga abinda asmau tai min, wai don kawai na ganta da ciki na tambayeta na waye shi ne tace nata ne wai zuwa tayi ta kashe mu ni da annur tunda yanzu ta kusa haihuwa bata son ƴaƴan ta su samu ɗan uba"
Sam sabit be fahimci abinda badia take cewa ba shidai kawai kallon annur yake wanda yake kwance a yashe goshi na ta jini
Ɗaukar shi yayi ya shiga da shi toilet ya wanke masa sannan ya fito da shi ya gyara masa ciwon ya saka masa plaster sannan ya ajiye shi
Itama badiar first aid box ɗin ya ɗauko ya gyara mata ciwon nata wanda daga gani wuƙa ce ta yanke da ita
Takaici ne ya hana sabit magana, yana gama gyara su ya shirya su sai da ya tabbatar sun kimtsu sannan ya fito daga part ɗin nasan directly part ɗin mummy ya taho a fusace
Ina kwance kawai naji an janyo ni daga kan gadon na faɗo ƙasa sannan ya shaƙe min wuya tare da miƙar da ni sama sannan sauke min yatsun sa guda biyar a kan fuska ta
Tuni na watstsake na ware ina kallon sa
"sabida baki da mutunci har ki shiga part ɗina ki yi mata ta illa sannan ki cutar min da ɗa........
Be gama ba sai ga mummy ta shigo
"wallahi ko ka sake ta ko in ɓata maka rai"
Wancakar da ni yayi ya fice in da mummy ta ɗago ni sannan tace min
" kiyi haƙuri komai me wucewa ne"
Wucewa wallahi an gama da ni haƙuri na ya ƙare anzo wani abu wai shi d end
Miƙewa nayi na wuce part ɗin anty fannah ina mata kukan ta bani aron kuɗi zan tafi ni na gaji da wannan bala'i
Ta so ta lallashe ni amma da ta ga yadda na rufe ido na sai tace min,
"to yanzu in kika tafi ina zaki"
"wallahi ko ina ne ni dai in tafi kuma wallahi bazan bar musu ɗana ba wallahi da abina zan tafi kuma wallahi ko ki taimaka min ko kuma in tafi ko banni da ko ƙwandala"
Jawo ni tayi sannan ta zaunar da ni kusa da ita,
"kwantar da hankalin ki akwai gidan da zan kaiki ki zauna wallahi sai sabit ya gane kuren sa sannan zan dawo da ke"
Wani sanyi naji ya ratsa min zuciya, sannan nace mata
"to yaushe zamu"
"haba so kike a gano ni na fita da ke, ai ke kaɗai zaki fita da annur akan zaki kaishi asibiti nima idan na fita sai ku haɗu, gidan yayana ne shi da matar sa sai kiyi zaman ki a can har sai yadda hali yayi"
Daɗi naji kamar me na kama hanyar part ɗin mummy na fara haɗa kayana
Duk wannan abun da ake yi mummy bata sani ba, sai dana gama haɗa kayan tas sannan na ɗauko su na kawo su part ɗin anty fannah
Itace ta sato min annur sannan muka kama hanyar barin gidan, ƴar tafiya mukai kaɗan sannan muka iso gidan da zamu,
Amaryace ashe na ɗauka ma babba ce kasancewar dare ne yasa san anty fannah bata daɗe ba ta kama hanyar gida
Ɗaki guda aka bani wanka nai wa ɗana sai alkcn naga cieon goshin nasa
"Allah ya saka maka annur"
Sallah kawai nayi na kwanta sai bacci
*******************
Sai sha ɗaya na dare sannan sabit ya dawo gida yana can yana ta fafutukar yadda zai wa asmau rashin mutunci so yake yi tana haihuwa ya kwashe abinda ta haifa ya kai gidan marayu wallahi bazai zauna da baƙaƙen ƴaƴa ba
Yana shigo wa gidan directly ɗakin annur ya shiga yai mamakin daya ga baya nan don haka sai ya ɗauka ko yana tare da badiar ne
Sai da yayi wanka ya gama komai sannan ya shiga ganin shi kafin ya kwanta, badia tana ta sharar baccin ta amma sam be ga annur a kusa da ita ba
"badia badia ina annur yake"
Cikin magagin bacci tace
"yana ɗakin sa da wuri yai bacci na kwantar dashi"
"ban gane ba yanzu daga ɗakin yake sam baya nan"
Miƙewa tayi itama tare da yin hanyar waje domin taje ɗakin annur ɗin amma wayam kamar sabit ɗin ya faɗa
Nan da nan hankalin su ya fara tashi, kafin me wannan tuni gidan ya ɗauka asmau ta ɗauke annur ta gudu
Mummy sabit hankalin su ya fi tashi, fara neman su akai abin takaici ma shine sam ba a san lkcn da ta tafi da su ba
Sabit kamar yai hauka, kasa zama yayi inda ya shuri motar sa ya fice neman annur don ita asmaun sam baya ta tata duk inda taje ai dole wataran ta neme shi ko don abinda take ɗauke da shi
nema aka dinga yi har tsakar dare sannan mummy ta kira sabit ya dawo gida
Da kuka ya dawo mata
"wallahi mummy sai yarinyar nan ta gane bata da wayo, wallahi sai na haɗa ta ƴan sanda ta sace min ɗa na ta gudu"
Kamar zararre haka ya dinga magana lallai sabit ya shiga tashin hankali, ko da mummy ta nemi ya kwanta ƙin kwanciya yayi a haka ya kwana yana ta trying number ta
Da asussuba ya miƙe ya nufi part ɗin sa yana zuwa ya tarar badia itama ta shirya
"wallahi sabit sai mun shiga kotu da yarinyar nan sai ta gaya min menene dalilin ta na sace min ɗa"
Tanka ta be yi ba saboda yanzu haushin ta yake ji duk ita ce ta jawo sam bata san ciwon yaron ba wai har kana gidan amma a sace yaro sam bata sani ba
Kaya kawai ya canza yana ji tana waya tana faɗa wa mmn ta asmau ta sace annur, takaici ne ya ishe shi yadda yake ta jinta tana ta zage zagen sai kace bamagujiya
Yana canza kaya ya fito zai fita
"sabit ina zaka na ga ka shirya wallahi ko asmau ta dawo min da ɗana sai munyi sharia da ita akan sace min ɗa da tayi sai kotu ta raba su wallahi sai na saka an mana katangar ƙarfe tsakanin mu da ita, duk babu muna fiki sai kai ko kunya baka ji ƴar cikin ka kake kwanciya da ita saboda ka zama sallamamme wallahi kaji kunya"
Har ya fice sai ya dawo, wani kyakkyawan mari ya kwaɗa mata sannan ya juya yai ficewar sa, yana jinta tana zagin sa ta uwa ta uba amma sam ba ta ita yake shi dai kawai burin sa ya ga ɗan sa
Ɓangaren mummy ya shiga ya saka mata kuka, lallashin sa ta farayi sannan ta sanar da shi ai ta aika a gano musu ko asmau taje garin su
Kuka ya dinga mata wiwi
" mummy wallahi asmau ta cuceni ta raba ni da farin ciki na annur shine komai nawa shine farin cikina ya zanyi idan banganshi ba don Allah mummy ki taimaka min, don Allah mumy ki cece ni ki dawo min da ɗana"
Tausayi ɗan nata ya bata, gaskiya asmau bata kyauta ba duk da dai duk abinda sabit yayi mata ai bai kamata tayi masa haka ba
Sallamar hjy munnira suka ji, da sauri mummy ta tashi ta tare ta sabit wanda yake zaune yai shaɓe shaɓe da hawaye ya rarrafa yaje wajen su
"don Allah ina ɗana yake" ya tambaya
Mummy ce ta daka masa harara gabaɗaya sabit ya susuce
"wallahi hjy har garin su aka je bata je, babu wanda kuka san ta sani a garin nan, wallahi tunda kika kirani jiya wallahi hankalina yake a tashe na rasa kwanciyar hankali yarinyar nan a dalilina aka san ta kuma ace ta ɗauki ɗan masu gida ta gudu da shi wallahi tun jiya jiki na yake ɓari"
"wallahi hjy na san bata wajen ki, asmau ce tayi wauta sosai" inji mummy
kuka sosai sabit ya saki kamar wani ƙaramin yari, kunya ce ta rufe mummy kamar ta nutse ƙasa sam be ji kunyar hjy munnira ba, kun san tsakanin ɗa da uwa tun tana masa faɗa akan kukan
Har ya karyar mata da zuciya, ita ma sai ga hawaye, hjy munnira sai ta saki baki tana bawa uwa da ɗa haƙuri
Suna cikin wannan halin ne sai ga ƴen uwan badia nan sun shigo
[7:16PM, 5/4/2018] +234 806 779 9926: 🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
*HIKIMA WRITERS ASSO.*
P⃗a⃗g⃗e⃗ 25 🌹
Da masifar su suka shigo
"wallahi sai an fito mana da ɗan mu" yayar badia ce hauwa a gaba tana masifa tana ƙarawa
A zaune suka ga mummy da sabit sun zuba uban tagumi suna sharɓe kuka
"badia wallahi baki sa ar miji ba, ace namiji da kuka ke kuma kiyi me" wannan maganar ta ƙonawa mummy rai sai ta tanka
Aikuwa nan da nan aka hau zage zage, mmn badia ce me cewa
"wallahi sai mun kai yarinyar nan kotu sai alƙali yai mata munmunan hukunci, wallahi sai tayi zaman gidan yari, ku ma baku tsira ba wallahi sai an ƙwatar wa badia ƴancin ta a gidan nan kun mai da ita baiwar ku"
Faɗa sosai shi dai sabit yana zaune ya kasa taɓuka komai yana jin yadda ƴan uwan badiar suke ci masa mutumci duk da dai yana ganin laifin su amma asmau ta fi kowa ƙona masa rai
Cikin hukuncin Allah sai ga muktar wan sabit shi ya shigo yai musu jan wuya sannan suka haƙura suka tafi akan su jira kiranye daga court
"kuma wallahi idan court ta karɓar mana ɗan wallahi ya bar gidan nan ke nan har abada tunda dai baku iya kula da shi ba har kukai sake wata yar aiki ta sace shi wallahi annur ya bar hannun ku har abada"
Injimn badia ta faɗa tana yin waje
Sabit kara fashe wa yayi da kuka
"don Allah mummy ina zanga asmau wallahi yanzu bazan mata komai ba don Allah ta dawo min da ɗana wallahi na yafe mata wallahi na daina yi mata duk abinda nake mata, wallahi ina son annur sosai wallahi bazan iya rabuwa da shi ba"
"kai sabit wane irin mutum ne kai kamar ba namiji ba ka zauna sai kuka kake tayi, ita kuma mummyn tace me" inji muktar
"don Allah muktar kar ka bari a ƙwace min annur wallahi ina son ɗana" ya faɗa yana me riƙe ƙafar muktar ɗin
"wai mummy me yasa yarinyar nan ta ɗauke annur ɗin ne, ko faɗa suka yi, in banda abinta ai ko faɗa kuka yi ba kya ɗauki ɗan da ba naki ba" muktar ya tambaya
Sam mummy sai ta kasa cewa komai don bata ma san ta ina zata fara ba, sabit ma shiru yayi
******************
Fannah tana ɗakin ta suna waya da asmaun tana faɗa mata yadda gidan ya rikice, sam ko a jikin ta asmau bata ji komai ba, ita burin ta ma Allah ya sauke ta lfy wallahi ƙarawa gaba zatayi da ƴaƴan ta taje ta nemi dangin uwarta
Saboda tasan ko baɗe ko ba jima anty fannah zata iya tona mata asirin inda take
Sai da ta kuma jawa fannah kunne akan kar ta sake ta faɗi inda take sannan sukai sallama
Tun ana ɓoyewa daddy har yazo magana taje wajen sa, ranar mummy ta sha faɗa sosai kamar ba gobe daddyn yai mata yai wa sabit wanda a yanzu yake kwance saboda zazzaɓi da ya rufe shi
Takanas daddy ya saka mutane suka kama hanyar garin su asmai don ganin ko ta je amma ba same ta ba
Tas ya tara mutan gidan akan su faɗi ko akwai wanda yasan inda asmau take, amma duk ba wanda yasan inda take
"har ke fannah don naji ance kullum kuna tare" jikinta ne ya fara rawa don ita fannah Allah yayi ta surutu amma sam bata da zafi sanyi gareta da kuma sanyin hali
Amma da ta tuno irin cin kashin da sabit ɗin ya ɗinga yi wa asmaun sai ta dake tace
"nima ban sani ba"
"to duk lkcn da ta kira ki ki ce mata ta neme ni koma menene wallahi sai na ƙwatar wa yarinyar nan ƴancin ta tunda dai na lura kamar zaman haƙuri take yi da ku, in ba haka ba tayaya za ayi ace ta ɗauki ɗan da ba nata ba ta gudu an rasa ta ko sama ko ƙasa"
Ya juyo ga mummy
"anya fatima ke uwa ce kuwa tayaya za ayi ace wai a gidan ɗan ki ana samun matsala amma sam baki sani ba, wane irin abu ne wannan, kince ke ƴaƴan ki baza suyi nesa da ke ba amma kuma sam ba kya kwaɓar su
To wallahi ku sani duk wanda na same shi da laifi a guduwar yarinyar nan sai nayi mugun saɓa masa, kuma ku shirya jibi monday zamu fara shiga court don iyayen badia sun kai ƙara an aiko mana da sammaci sai ku shirya"
Sabit da ke zaune kamar mutum mutumi sai ya ƙara narke wa ɗan zazzaɓin da ke jikin sa nan da nan ya kuma hauhawa, shi sam be ma san ya zai yi ba
Miƙewa yayi don ya tashi dole duk yadda za ayi ayau sai ya nemo inda asmau take don kuwa wallahi bazai yiwu ace ya yi rashin ɗan sa ba
Don kuwa ya san indai suka shiga court ɗin nan da badia sannan suka ci case ɗin dole ne ace ya bata ɗan in kuwa ya bata shi ya zaiyi da rayuwarsa
Miƙewar nan da zai yi sai jiri ya kwashe shi ya faɗi ƙasa a sume, a guje akayi kansa inda mummy kuma ta fashe da kuka
Ruwa aka kawo aka yayyafa masa nan da nan ya farfaɗo jikin sa kamar garwashi saboda zafi
Yana farfaɗowa kuka ya saki ya riƙe hannun mahaifin sa
"daddy don Allah kar ka bari su raba ni da ɗana, ƙila shi kaɗai ne ɗan da zan so a duniyar nan don Allah daddy a nemo min asmau ta bani ɗana a maidawa badia ɗan ta saboda ta barshi a gidan nan"
Ko wa a wurin sai da hankalin sa ya tashi, isma'il ne ran shi ya ɓaci ya fara magana
"wallahi yarinyar nan idan na sake na ganta Allah ko su badia basu kai ta kotu ba ni sai na sa an hora ta wane irin abune wannan"
Lefi suka dinga ɗaurawa asmaun bayan sam basu san gaskiya suna ta ƙoƙarin cusa wa daddy magana saboda ya ji haushin yarinyar, da fannah ta ga haka sai kawai tace
"nasan inda asmau take"
Gabaɗaya kowa ya waigo gareta har da daddyn
"tana ina, suka haɗa baki"
Nan da nan fannah ta kwashe inda asmau take ta faɗa musu amma sam bata faɗi dalilin zuwan asmau gidan ba
Sabit shine a gaba ya fice domin tafiya, daddy ne ya tsai da shi
"kai baka da lfy yi zaman ka nida isma'il da ita fannah zamu je mu dawo da ita" inji daddy
"ka kira badia a waya su zo nan za a kashe maganar kafin aje court a kashe maganar a gida"
Amsawa sabit yayi ya ɗauko wayar sa yana neman number badia wacce tunda abin ya faru ta koma gidan su
Bayan ya samu badia ya faɗa mata ne ya zauna amma ba don ransa ba ya so ace yaje wallahi da sai asmau ta gane bata da wayo
Ina kwance sai jin muryar anty fannah nayi a kaina
"ki fito da daddy muke"
Rasa abinda zanyi nayi na ɗauka na ja mata kunne ashe sam bata ji
"asmau ki tashi mana na ce miki da daddy muke"
Miƙewa nayi jiki na a sanyaye, na fito na same shi yana zaune a falon gidan da isma'il da kuma wan anty fannah
Ina fitowa na gaishe su, daddy da fara'ar sa yace min
"me yaji munzo mai da ke ɗakinki maza ɗauko kayanki mu tafi"
Bazan iya masa musu ba na shiga ɗakin, anty fannah ce ta ɗauko min annur inda ni kuma na kwaso kayana muka fito
A mota ba wanda yace min komai sai ma ɗana dana karɓa daga hannun anty fannah na rungume shi duk da ƙaton cikin da ke jikina
Da sallama muka shiga babban falon gidan wanda yake cike da mutanen gidan harda mutan gidan su badia
Tana ganina ta yo kaina da zagi wai in bata ɗan ta
Daddy ne ya dakatar da ita inda yace duk a zauna a tattauna me yasa na ɗauke annur ɗin
Sai dana zauna sannan daddy ya buƙaci ai masa bayanin abin da ke faruwa, sabit ne ya wangale baki yai masa bayanin, yadda aka samu annur
Ba daddy ba hatta ƴan uwan sabit sai da suka jinjina maganar nan, daddy kuwa faɗa ya dinga yi yana ƙarawa sai da yai wa sabit wanki babban bargo sannan daga baya yace
"sabit wai duk bokon ne ya saka haka ko menene, dashe ka sa akayi wa matar ka saboda ɗayar matar taka ta cire mahaifar ta"
Rufe ido daddy yayi ya zage tas shi da badia bayan ya gama sannan kuma ya ɗaura da nasiha akan abinda muka aikata gabaɗayan mu haramun ne
Ko da kuwa dukan su matan ka ne bw hallata a ɗauki ƙwan ɗaya a saka wa ɗayar ba haram ne wannan
Duk wani abu daya danganci dashw na ciki indai akwai mutun na uku daya shigo cikin abun ko da kuwa ko wane kusanci ne tsakanin su to ya haramta
Faɗa sosai daddy yayi musu duk sai suka rasa bakin magana
"ai asmau tana gaskiya ɗa ɗan ta ne babu wata badia, tai wahalar ɗaukar ciki ta sha naƙuda yanzu kuzo kuce wani ɗan badia tayaya akayi ɗan ya zama nata, to ku sani wallahi daga yanzu na gama case ɗin nan asmau ki ɗauki ɗan ki zan ga wanda zai kuma kawo maganar annur anan, kai in banda ma kai sha sha sha namijin kawai ka ɗauki ƙwan matar ka ka dasawa wata idan ɗan ya girma kace masa wacce ce uwar sa, wacce ta ɗau cikin sa ko wacce yake da jinin ta"
Dukkan su jikin su ne yayi sanyi in banda badia wacce tace
"wallahi sai kotu ta ƙwatar min ɗana" ta faɗa tana kuka
"ai dole ne ɗa jinin ki ne duk inda aka je akai gwajin jini jinin ki za agani don haka ban ga dalilin da zai sa ace don mace bata da mahaifa ba ace kuma sam bazata
mallaki ɗan kanta ba" inji maman su
Gyara zama daddy ya yi ya fahimtar da mmn badia sharia akan duk wacce ta ɗau cikin ɗan adam ta kawo shi duniya itace mahaifiyar sa amma sam matar nan bata yadda fuuuuu haka ta ja badia suka fice
Sabit wanda jikin sa yai sanyi ya ƙaraso kusa da ni zai ɗau annur daka masa harara nayi na miƙe tare da daukar ɗana na fice
Babu wanda ya bashi gaskiya kowa sai rashin gaskiya yai ta bashi,
Ɗakin na da ke part ɗin mummy nan na koma na kwanta, sabit ne dai ya kuna shigowa,
" Na fahimci har yanzu taurin kan ki na nan, kina gani idan munje court gobe zasu baki annur ni ne dai uban annur kuma nace baza ki renar min ɗa ba"
"kai ma ai bamu fara da kai ba, idan an gama case ɗin annur a court ɗin dole ne ka bani takarda ta don kuwa na gama aure da kai"
"zan ga wanda ya isa ya sani sakin ki" ya faɗa a fusace
"wannan kuma in munje court ɗin na gabatar wa da alƙali buƙatata idan ya saka ka sake ni kace kai baka yadda ba"
Haushi ne ya kama shi sosai ya fice daga ɗakin ko ganin annur ɗin ma be yi, nima na bi ƙofar da mukulli sannan na kwanta sai da safe Allah ya kaimu court ɗin inga in za abata ɗan bayan bata san komai nashi ba
*******************
Kashegari da wuri na tashi na shirya ɗana don zuwa court duk da dai yanzu sam hankalina ba a kwance yake ba ga ciki amma hakan be hanani gyara fuskata ba
Mummy ce ta shigo wai daddy na kirana
Hijab ɗina na ɗauka na same shi a falo yana zaune, har ƙasa na durƙusa na gaishe shi ya amsa min sannan ya kuma kwantar min da hankali na
"nayi wa lawyer na magana shine zai kare ki koda kuwa jinin badia ne wannan yaron. Amtsayinki na wacce kika ɗau ɗawainiyar yaron nan sharia ta baki naki ne ko ina suka je ke kika haife shi ɗanki ne"
Hankali na ya kuma kwanciya, anty fannah ce ta shigo itama taci laffayar ta,
"daddy nima dani za aje, don kuwa nima shaida ce, kuma ina kamun ƙafa idan an gama case ɗinnan ni zan karɓe shi ko asmau" gyaɗa mata kai kawai nayi amma wallahi bazan iya bawa kowa ɗana ba
"to ai shike nan wannan ɗan ƙaramin case ne nasan ayau za a gama shi ma idan kun shirya sai ku fito"
Mummy har gabana ta zo nasiha tai min sosai wallahi har jikina yai sanyi, akan kar in sake in bari a ja shariar da tsaho don mafi akasari idan ana faɗa akan ƴaƴa to wallahi su take shafa
Gabana ne ya faɗi na ƙara matse abina a jikina in shaa Allah yau za a gama case ɗin tunda dai ƙiri ƙiri ga yadda abin yake
********************
Badia ce da mmn ta sai lawyern da suka ɗauko a zaune duk abin duniya ya ishe su,
"gaskiya hjy kamar yadda na faɗa miki duk inda aka je indak ƙasar nan ne baza a taɓa badia ɗan nan ba tun da dai a ƙundin tsarin mulki na ƙasar nan wacce ta kawo ɗa duniya itace uwa"
Kuka badia ta saki
" wallahi ƙwai na ne fa, ya za ayi in ɗau ƙwai na in bawa wata ƴar iska ita in banda rashin godiyar Allah ma gawani ɗan iskan ciki nan a jikin amma kuma bata godewa Allah ba sai ƙwaya ɗayan nan shine zata ce sai ta raba ni da shi, mummy don Allah ya zamu yi wallahi zan iya rasa rai na idan aka ƙwace min annur"
"yi shiru yi shiru inji mummy yanzu kai barister ya kake ganin za ayi"
Shiru yayi can sai ya e
"to akwai mafita amma sai in me gidan ya yadda da hakan" nan da nan ya tsara musu yadda za ayi
Ba musu suka yadda nan da nan badia ta kira waya lagos ta faɗa wa dr. ɗin nan da tayi dashe akan ta bar asibitin na ɗan wani lkc kuma ta kashe wayar ta
Shi ma sabit ta kiɗa shi ta faɗa masa shawarar da barister ya yanke, nan da nan ba tare da wani shawara ba yace ya yadda duk yadda suke so hakan za ayi
********************
*COURT*
Sai da aka gabatar da case 4 sannan aka kira su, inda magatarda ya gabatar da case ɗin su, aka kirawo badia da asmau kowacce ta gabatar da kanta
Alƙali ya nemi badia tai bayanin abinda ya faru
"asmau kishiyata ce, kusan a tare Allah ya azirta mu da samun ciki, amma ta riga ni haihuwa inda ita ɗanta be zo da rai ba, ni kuma nawa yazo da shi, kuma shine wannan na hannun natan
To kasancewar ban da ruwan nono sai mijin mu yace asmau ta dinga bawa ɗana nono, shine yanzu ta ɗauke min shi ta gudu da shi wai nata ne"
Sakin baki kawai su anty fannah sukai suna kallon ikon Allah, sai da alƙalin ya gama rubuce rubucen sa sannan ya tambayi asmau ita kuma ta faɗi me ya faru
Nan da nan na zayyano duk yadda akayi na samu cikin annur, kowa a court ɗin sai ya ɗau salati aka fara ƴan ƙananan surutai
Sai da alƙalin ya doka ƴar gudumar sa sannan akai shiru,
"ina me gidan nakun"alƙali ya tambaya
Nan da nan aka taso ƙeyar sabit ya fito, alƙalin ya tambayi cikin mu wake faɗar gaskiya, mutumin nan be ji kunyar Allah ba sai buɗar bakin sa yace
" badia ce take faɗar gaskiya"
Hmmm sabit in bakai haka ba ai baka cika ɗan halak ba
"to malama asmau kinji abinda mijinku yace ko ke kina da taki shaidar"
Gyaɗa kaina nayi sannan ya bani damar faɗar menene nan nace masa dr. ɗin da tayi min dashen kasancewar bata nan ya sa aka ɗaga ƙarar har sai dr. ɗin tazo da kanta
Daga nan sati biyu akan mu zo da dr. ɗin, aka sallame mu bayan alƙalin ya ja min kunne akan kar ya sake naji na bar gidan balle in tafi da ɗan
*******************
Tun a mota daddy yake faɗa akan abinda sabit yayi, yana komawa gida ya faɗawa mummy ita ma sam bata ji daɗin hakan ba
Daddy ya tambaye ni number dr. ɗin don a kira ta a faɗa mata abinda alƙalin yace
Tooo nan fa ake yi don gabaɗaya ban san komai na dr. ba ni ko sunan asibitin ban sani ba, don inda akai min dashen daban inda kuma muke zuwa nan ma daban ne
Babu yadda zasu yi dole ne aka nemo sabit don ya faɗi a ina za a samu, abin takaici wai sai sabit yace shi ma be sani ba wai badia ce ta san ta
Haka daddy ya zaunar da sabit yai mai masa nasiha, tunda ya ga faɗan ma sam baya shiga, amma ƙiri ƙiri sabit yace shi be san zance ba
Daddy ya rasa yadda zai yi da sha'anin mu, don yasan ko ana ha maza ha mata badia baza ta taɓa faɗar address ɗin dr. ɗin ba balle ayi contacting ɗin ta
Zaunar dani yayi yai ta min nasiha, sannan yace min in Allah yayi annur zan rayu a matsayin ɗana too in kuwa Allah yayi kotu zata bawa badia to a matsayi na na uwar sa ba abinda zai so daga gareni face in kasance ina masa addu amma shi sam baya son ai ta ja'inja akan yaron don kar abin yai affecting ɗin sa
Tabbas maganar daddy haka ne amma kuma in shaa Allah addua zan dage da ita kan Allah ya bayyana mana da dr ɗin nan
🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦🥦
*A̺͆U̺͆R̺͆E̺͆N̺͆ B̺͆A̺͆U̺͆T̺͆A̺͆*
🍷🍽🥛
👩🏽🍳~(t̸h̸e̸ a̸m̸a̸z̸i̸n̸g̸ c̸o̸o̸k̸)~👩🏽🍳
🍳🍜🥘🍲🍛🍝🥗🌯🍛🍢🥠
ʙʏ ᴍᴍɴ ᴡᴀʟɪᴅ ᴀɴᴅ ᴡᴀʟɪᴅᴀ (ᴍʀs ᴀʟɪʏᴜ)
*HIKIMA WRITERS ASSO.*
P⃗a⃗g⃗e⃗ 27🌹
Ina kwance sai anty fannah,
"lallai me jego kice kina hanya amma shine ba a kira ni ina can na saki baki ina ta bacci"
Murmushi kawai nai mata, ƙarasowa kusa da babies ɗin tayi tana ƙoƙarin ɗaukar ɗaya
"lallai maa shaa Allah kalar mu kalar da sabit baya so zan ga yadda zai yi yanzu da Allah ya haɗa shi da kalar mu"
Murmushi na kuma yi
"wallahi nima anty tunanin da dinga yi kenan"
Tattaunawa muka dinga yi da ita akan irin reaction ɗin da sabit zai ɗauka idan ya ji labarin ƴaƴan baƙaƙe ne biyu ma ba guda ɗaya ba
Sai gab da asuba sannan bacci ya kwashe ni bayan na sha tea me kauri da anty fannah ta haɗa min
Ban san lkcn da anty fannah ta kira mummy ba nidai kawai naji muryar ta ne a kaina tana cewa
"maa shaa Allah fannah kin yaran nan wallahi gaba ɗayan su kama suke yi sabit"
"haka ne kuwa
mummy amma inda za ai rikici da shi idan yaga kalar su"
"hmmm fannah sabit ɗin daa kika sani na yanzu ba me tsirface tsirface ba na yanzu yayi laushi, jiya dana koma gida ake bani labari har get ta bishi tana zagin sa tare da ci masa mutunci,
Hmmm wannan ƴar iskar yarinyar da badan daddyn ku yace inya sake ta sai ya sashi ya saki asmau ba wallahi da tuni ya manta ya rabu da ita
Wallahi yanzu zancen da nake gaya miki tun daya fita tun jiyan har yanzu be dawo ba, a hanya ma ina ta trying ɗin shi in faɗa masa haihuwa amma wayar shi a kashe"
Tausayi ya bani wallahi sosai, kai gaskiya banji daɗi koman lalacewar sabit uban ƴaƴana ne kuma bazan so wani abun ya same shi ba
Tunda indai akwai wani ya same shi sai dai ƴan uwan sa su koka amma kuma ƴaƴan har abada a rayuwar su haka zasu kasance suna masu rashin uba
Tashi nayi na gaishe ta da fara'ar ta amsa min da
"sannun asmau abinda bamu taɓa samu ba kika kawo mana ƴaƴa mata, tunda aka faɗamin na faɗawa daddyn ku yake murna don ma yana da meeting ne da wasu turawa amma ana tashi zaki gan shi, suma ƴan uwan naku nasan yanzu zaki gansu"
Bata rufe bakin ta ba kuwa sai ga sallama
Dukkan mutan gidan ne suka shigo, dole ne ya sank fitowa parlour saboda yawan su
Sai hayaniya ake tayi tare da murnar samun mace a dangi, barin ma mummy ta ɗauki babbar ta goye ta baya duk wanda zai ganta sai dai ya ganta a bayan ta sai dai ƙaramar ce ake ta passing passing da ita
"mummy don Allah muga ta bayan ki" inji kishiyar anty fannah
"wannan da kuke ganin ta takwara ta ce shiya sa bana son a jagwalgwala min ita" mummy ta faɗa
Ana haka mazan ma suka ƙaraso amma banda sabit ko ba komai ai zan ji daɗi idan na ganshi ko amma sam be zo ba
Duk wanda ya zo gidan nan murnar samun ƴa mace yake a dangin nan, don kuwa har zuwa yanzu mummy bata da jika mace sai maza sai waɗan nan baƙaƙen dana haifa
Abinda ya min daɗi da ƴan uwan sabit da matan su shine babu wanda ya luɗa da cewar yaran.ba farare bane sam ba wanda ya kawo wannan
Kawai yaba kyan yaran suke yi, suna ƙara musu adduar Allah ya raya su cikin addinin islama
Ana cikin hakan ne daddy ya zo, kasancewar parlour ɗin a cike yake yasa sam bamu ji sallamar sa ba duk an saki baki ana ta hira akan jariran da Allah ya hana kowa a dangin ya ba sabit
Sai da daddy ya daka tsawa sannan aka san ya shigo
"haba tun ɗazu na shigo a miƙo min yaran in gansu amma kun saki baki sai zuba kuke yi kamar ƴaƴan kanya, dan Allah a miƙo min da baƙi nake a waje
Na kasa zaman meeting ɗin ma sai ce musu nake yi ba a taɓa haihuwar mace a gidana ba sau yau kuma Allah ya bamu guda biyu"
Sai da kowa ya dara da maganar daddy, is'mail da muktar ne suka fita da babies ɗin sai a lkcn mummy ta sauko babbar
Sunfi awa guda sannan suka dawo inda daddy yace
"lallai yaran nan daga gani da albarka suka zo, mutanen nan suna ganin su sukai mana signing contract ɗin da mukai kusan wata biyu ana ta fama akan ta, lallai in gama suna suna da rabo in shaa Allah, ko ba"
Mummy ce tace
"Allah daga zuwan su har ka fara nuna banbanci tsakani na da su"
"yoo ke ba tsohon hannu bace, kinci kuɗin kinci kuɗin har kin gaji sukuwa ai kinga sababbi ne"
Raha suka dinga yi tsakanin su inda wasu suke goyan bayan mummyn wasu kuma suna goyan bayan twins
Ni dai ina gefe murmushi kawai nake yi ina jin daɗin yadda suke nuna kulawa ga abinda na haifa
Sai da suka gama sannan ya tasa ƙeyar mazan suka fice inda aka bar gidan daga matan sai ƴaƴan su
Mummy ce ta sa anty fannah ta kaini asibiti ko akwai wani problem, muka je suka duba ni tas ba komai, sai dai magani da suka bani muka dawo gida
Gidan ƙin kyau yayi sai da kowa ya bar gidan da daddare sannan gidan ya dawo hayyacin sa
Mummy ce kawai bata tafi ba, wai ita ta dawo kenan sai bayan suna
Muna zaune a falo wajen ƙarfe 10 :30na dare muna ɗan taɓa hira kafin mu kwanta sai nace wa mummy
"har yanzu ba a san inda sabit yake ba" juyowa tayi ta kalle ni, dagani ita ma abin na damun ta
"wallahi asmau tun rana nake ta trying mumber sa amma sam a kashe take wallahi kawai ƙarfin hali nake amma hankalina ba a kwance yake ba"
Hankali na ne ya tashi ya za a yi ace ba gan shi ba kuma ba wanda ya damu,
"mummy yanzu baza a duba a sani ko lafiyar shi ƙalau ba" na tambaya
"wannan daddyn ku ne kawai zai iya kuma nasan inna faɗa masa bazai yi ba saboda har yanzu haushin sabit ɗin yake ji akan abinda ya miki"
Kuka na saka mata nidai mummy don Allah ki sa a nemo shi, shekaran jiya ya fita ba a san inda yake ba amma ba wanda ya neme shi yanzu in wani abun ya same shi fa me zance wa ƴaƴana, wallahi duk lalacewar sabit na fi son ganin shi kusa da mu saboda ƴaƴana mummy dƙn Allah ki taimaka kiyi wa daddy magana"
Shiru tayi daga dukkan alamu bata son yin kuka ne yasa ta ƙin yin maganar, wayata ta ɗauko tayi dialing number daddy sai da ta fara ringing sannan ta bani
ringing ɗaya ya ɗauka tare da sallamar sa daga gani bashi da number ta
"daddy asmau ce"
"asmau kina nan lfy ko, ko akwai abinda kuke so ne"
Kuka na saka masa sannan nace
"daddy ba aga sabit ba don Allah ka sa a nemo shi don Allah daddy"
Shiru yayi kamar be ji ba sai da na sake bashi haƙuri na ɗauka ko be haƙura ba ne sannan yace
"asmau lallai ke ƴar halak ce kuma wallahi baza ki taɓa taɓewa ba, ki kwantar da hankalin ki mijinki nanan ƙalau yana lagos ne, wajen aikin sa can ya koma amma in shaa Allah zan koro miki shi"
Kunyar sa naji nai murmushi sannan nace
"ni fa daddy ba ni nake son ganin sa ba, kawai dai ya zƙ yaga babies ɗin ne"
"ato abu ne sauƙi kawai zan sa a aika masa hotunan su kinga shike nan ya huta da zuwa kooo"
"a a daddy don Allah ya dai zo" dariya yayi irin tasu ta manya sannan yace
"shike nan in shaa Allah zan sa a gaya masa"
Mukai sallama sannan na sanar wa da mummy abinda ya faru, ta nuna jin daɗin ta sosai itama tai ta sa min albarka kamar ba gobe
********************
Sabit yana kwance a kan kujerar gidan sa na lagos duk abin duniya ya gama isar sa, sam ya rasa farkn ciki, yana matuƙar kewar asmau daba dan daddy ya kafa masa doka akan zuwa wajen ta ba da tuni ya san yadda zai yi ya taho da ita lagos
Tabbas asmau tana da taurin kai amma kuma zuciyar ta tana da sanyi, shiyasa duk abinda yake mata yasan bata riƙo
Gashi yanzu wallahk yadda yake kewar to ko kaɗan baya kewar badia, wacce sam baya ma son ganin ta, burin shi kawai asmaun sa wacce yanzu aka kafa masa takunkumin ganin ta
Knocking yaji ana yi, agogon bangon parlour ya kalla 11 :20na dare, waye wannan da daren nan yake min knocking
Kamar bazai buɗe ba sai kuma ya tashi yaje bakin ƙofa yayi shahada ya buɗe
Wani yaron daddyn sa bola inda ya faɗa masa wai daddyn yace ya kunna wayar sa matar sa ta haihu
Ai ko sallamar yaron ma baiyi ba ya tafi ciki a guje shi sai a lkcn ma ya tuna da batun wayar sa tun da ya kashe ta lkcn da ya baro abuje
Watsappa ya shiga don yasan ta nan zai ga pics ɗin babyn, aikuwa messages ne sukai ta shigowa kamar ruwan sama
Message ɗin ƴan uwan sa kawai ya shiga dubawa, nan ya ci karo da wasu jarirai kyawawa an turo masa
Duk da dai yaran ba farare bane amma kuma sun masa kyau sosai ashe shima baƙi yana da nashi kyan
Duk da dai ƴaƴan shi baƙaƙe ne amma ya ga kyan ababan sa sosai kamar ba nasa ba, kamar su ɗaya da annur
Miƙewa yayi ya fara haɗa kayan sa dalilin ganin asmau ya kama shi yanzu inyaje gidan ba wanda zaice masa don me
In shaa Allah sai ya samu ya shawo kan asmau kafin a ƙara yi masa get da it don ba ƙaramin wahaltuwa yayi da rashin ta ba barin ma waɗannan ƴan kyawawan ƴaƴan nashin da ta kawo masa duniya
Sai yanzu yai dana sanin zubar mata da ciki da yayi, inda yasan cewar idan asmau ta haifo masa ƴaƴan sa ko da zasu kasance baƙaƙe amma za suyi kyau ai da tun farko be dinga wannan abin da yake ba
A gaskiya ya cuci asmau a rayuwa, sam shi sai yanzu yake jin kunyar kansa ma, yarinyar nan ba abinda tai masa kawai ya kafa mata ƙahon zuƙa
Hawayene su ka sauko daga idon sa da ya tuna irin abubuwan da dinga yi mata, lallai yayi nadama kuma yana fatan ita ma ta yafe masa
Da asuba ya kama hanyar abuja a jirgi inda yayi sa'ar samun flight na ƙarfe 06 :00 na safe, suna sauka diretly gidan da asmaun take ya wuce
Gidan da yake ganin sa kamar na wani shugaban ƙasa saboda tsabar takunkumi da daddy ya saka masa
*******************
Ina kwance ina bacci kawai naji mutum ya kwanta kusa da ni ko ban kalle shi ba nasan sabit ne don nasan duk duniyar nan babu wanda ya isa ya rungume ni sai shi
Da sauri na miƙe tare da haɗe raina
"lfy" na faɗa raina a ɓace, ai na waye yanzu ya za a yi in barshi ya same ni a banza bayan sam be san daraja ta ba
"my asmy godiya zan miki akan wannan kyauta da kika kawo min duniya Allah ne kaɗai zai biyaki"
Baki na taɓe sannan nace
"baka ganin baƙaƙe ne"
"au haba ban lura ba ni kawai kyan ƴaƴana nake gani"
"au ƴaƴan ka ma, ƴaƴan da ka so in zubar su sune yanzu kake kira da naka"
"wai har yanzu ba a yafe min bane"
"sabit ai tuban dole kayi tuban muzuru da kaga na dawo gareka shi ke nan sai a koma gidan jiya"
"ke kuma baza ki min fatan shiryuwa ba"
"wannan kai ta shafa ko da kai ko babu kai zan iya rayuwata"
Duk yadda ya so ya ga na sakar masa jikina sam yaga hakan be samu ba, da ƙwarin gwiwar sa ya shigo ɗakin amma ganin yadda na dage ban yadda da tuban sa ba ya sa jikin sa yin sanyi
Ƙarasawa yayi ya ɗauki ɗaya wacce itace ƙaramar addua ya hau yi mata ina ganin shi yana ƴar ƙwallar sa ko me ya tuno oho
Ganin zai karya min zuciya ya sani miƙewa na fice na bar masa ɗakin parlour na koma na zauna kusa da mummy
Sam bata tanka min ba, ya daɗe sosai sai gashi ya fito
"mummy ni zan wuce gida in ɗan huta, akwai abinda kuke buƙata ne"
Lallai ma sabit ɗin nan dama ba dan mu kazo ba don kazo kaga badia kazo kenan har da wani zaije gida kenan nan daji ne
Harara mummy ta bishi da shi inda ni kuma na miƙe na bar wajen, sam be fahimci manufar mu ba ya ɗauka daga mummyn har ni fushin muke da shi
Sim sim sim yasa kai ya fice shi sam ya ma rasa tudun dafawa wannan shine abinda ake cema rana zafi inuwa ƙuna
Ko da ya koma gidan nan har gidan asmau yafi ni'ima don badia tana ganin sa ta hau shi da zagi da cin mutunci, sam be kula ta ba
Ɗakin sa kawai ya wuce yana shiga ya rufe ƙofar da key kamar ya sani yana juyawa zai shiga toilet yaji bugu kamar za a ɓalla ƙofar
Share ta yayi ya shiga toilet, hmmm lallai badia har yanzu batai hankali ba wai ita har yanzu burin ta sai ya bada sperm ɗin sa sun ka nemo wacce za a sake mata dashen ta haihu ita lallai sai taga ƙwanta a duniya ta nuna wa asmau
Ƙin yadda dan da baiyi ba ne yasa kwanaki sukai fada ta bishi har waje tana ci masa mutuncin sa
In banda ma daddy wallahi da tuni badia ta manta da rayuwa da wani sabit don wallahi in ya tashi katse auren da ke tsakanin su ko duka ba tare ya rage ko igiya ɗaya ba don ya
: "wallahi sabit ka buɗe ƙofar nan ka ɗura min sperm ɗin ka a robar nan in kai asibiti a ɗura wa wacce za tai mana ɗaukar cikin, don baka isa ba kace wai bazan ga ƙwai na a duniya ba, wallahi ba za ta saɓu ba"
Surutai tai tayi wanda suka saka sabit ɗin yin nadama sosai gaskiya ada ya bi son zuciyar sa sosai na cewae shi bazai auri baƙar mace ba balle ya haifi baƙin ɗa amma yanzu in shaa Allah ko ƴaƴa zai dinga haifa kamar baƙaƙen tukunya zai so kayan sa kuma ya basu tarbiyya
Balle baƙin asmau ba me muni bane irin wanda yake da tsadan nan ne wanda bature yake cewa chocolate
Barin ma yanzu da haihu ɗin nan tai wani fresh da ita duk sai ya jishi ya matsu ya jishi a jikin ta tana sarrafa shi kamar yadda take masa idan suna shiri
Wani irin yarrrr yaji a jikin sa lallai akace wani kaya sai amale, asmau tayi wa badia nisa nesa sosai wanda duk abinda badiar zata yi ba lalle ne ta kamo ƙafar asmaun ba
Kai lallai wallahi dole ne ma in dawo da matata wallahi duk abinda za a yi sai na dawo da matata
Yana fitowa daga toilet ya tsiri haɗa kayansa shima gidan zai koma da zama duk yadda za ayi da shi wallahi sai dai ayi amma sam bazai iya rayuwa babu asmau ba
********************
Ina zaune a ɗakina takaici ya ishe ni wai sai yaushe sabit zai fahimci shi wani jigo ne a rayuwa ta da bazan iya cigaba da ita ba face da shi a kusa dani kusan kullum banni da buri daya wuce inga na mallaki mijina a hannuna yai treating ɗina kamar yadda ake wa kowacce mace amma ni sam har yanzu ba samu ba
Ina cikin tunani na naji muryar mummy tana magana
" lfy kai kuma meye haka sai kace me shirin hijara"
"ai mummy duk inda asmau take da yarana ni ma ina nan, zuwa nayi gida ai na kwaso kayana ni ma ayi jegon dani"
Murmushi nayi amma kuma sai na haɗe raina don kar ya shigo ya ganni ya raina ni
Na ɗauka zai shigo ɗakin ko ince naso ya shigo ɗakin amma har na gaji da gyaran fuskar da zan sauke shi da ita na saki fuskata ba shi babu dalilin sa
Sam be shigo ɗakin ba ina jin shi a parlour yata ta zuba cikin mata, kuna duk wacce ta zo sai ya shigo ɗakin ya ɗauke su don kai wa yan barka
Kuma shigowa goma fita goma sak ya min magana, ƙala bana ce masa amma baya gajiya
Haka aka dinga yi da shi ina jin anty fannah tana mai tsiya
"ni na taɓa ganin jego har da namiji"
"kin san ai autar mata ce ta haihu duk abinda take dole ne ai mata, ko da dai bazata yaba ba"
Murmushi kawai nake yi ina cikin ɗaki na
Har azore garin mu mummy ta aika da mota akan idan da masu zuwa suna
ƴan garin mu da yake ba hankali haka suka ciko motar wata akan wata ƴaƴan su da jikokin su, har da me tsohon ciki
Ɗadin abun ma acan gidan mummy akai sunan can muka je saboda kar a ɓata min gida, inda ƴaƴana suka ci sunan
*FATIMA & FATIMA*
sunan mummy da kuma suna mahaifiyata, ɗaya muna ce mata nur ɗayar kuma hoorain amma hoor in short
Hoor da noor sun shaa kaya sosai da kyautuka da kuma hotuna
Tunda aka fara sunan nan har aka gama sabit yana maƙele da ni kamar jaka, duk wani hoton da za ayi tare da shi yana riƙe da baby ɗaya
Wallah tun abin na bani dariya har ya zo ya faɗa bani haushi don kuwa tuni mutan garin mu suka fara magana
"shi mijin mau haka yake abin nasa sam ba kunya"
Ga dukkan kayan da na saka sai shima ya saka, ko kaɗan bansan ya akayi akai mana kaya iri ɗaya ba, ko da yake nasan aikin waye
Na anty fannah ne don kuwa itace akan komai na kayan da zan saka ranar suna,
Mun sha pics sosai da mu da ƴan biyun mu da annur
Suna yai suna haka akai suna aka tashi lfy a daren muka koma gidan mu don gidan mummy babu masaka tsinke
Fatana dai Allah yasa mijina ya shiryu kenan har a bada
0 comments:
Post a Comment