🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Assalam Alaikum sis, complete ne nayi maku shi a matsayin barka da sallah, tou idan kina akan what's app kiyi min magana inyi maki sending document dinshi, idan kuma facebook kawai kike, tou kiyi hakuri har kuzo karshen*
*Aallah ya isa duk wanda yayi min editing novel ko kuma ya sauyashi ta kowane bangare*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
Page. 1
Durkushe nike ina rusar kuka kamar wacce tayi loosing both iyayenta saidai ni a durkushe a gabansu nike rusar kukan, the more nike kuka the more nike ganin idan basu yarda da muradina ba, rayuwata ta shiga garari, kuka nike ina shedding tears babu ji babu gani, a karo na farko Abba ya dubeni yace,
"Baby mi ye yake damunki?".
Ban yi uttering koda word guda daya ba, gani nike the more na tsaida hawayena the more Abba zaiyi watsi da muradina, I feel inta kuka more and more koda ya yarda da abun da zan sanar dashi....
Ummy ta dubeni sannan tace,
"Baby ba kya ji ne, Abbanku yana magana?".
Na d'ago ina mai cigaba da shedding tears nace,
"Abba ni bazan iya auran Mahmud ba, bazan iya auranshi ba, a baya nace ina sonshi amma yanzu bazan iya ba".
Na mik'e na juya na bar dakin a guje ina gumjin kuka, wani k'aramin daki dake kusa da kofar da na fito na shiga na zube kasa nayi zaman en bori tareda fashewa da kuka, na had'a kai da gwuwa ina sharar hawaye, the more nike tuna abun da Mahmud yayi min the more nike shedding tears, wannan wacce irin alaka ce, wannan wacce irin soyayya ce, wannan wacce irin dauka ce yayi min....
Abba yace, "Ta fada maki wani abu da ya faru tsakaninsu ne?".
Ummy tace, "A'a sam babu abun da tace min".
Abba yace, "Shikenan zan kira Mahmud din inji ta bakinshi".
Sai kuma ya mik'e tareda goya hannayensa a baya yana kaiwa da komowa....
Ina kunshe a daki ina shedding tears, ina busy kuka autanmu ya shigo ya d'ane bayana yana kiran...
"Ba-by.... Ba-by.... Ba-by....".
Na zura hannu na jawoshi gaba yana kiran sunana ina tayashi, ina fara kiran Ummy.... Abba.... Da sauran brothers dinmu guda ukku ya soma wangame baki yana dariya, shekararshi daya da watanni hudu amma gudu yake sosai, ga baki, ga shi yana da zakin murya, yana gudu yana kiran Ummy.... Abba.... Baby.... Ayan... Sauran brothers dinmu guda biyu kiran sunayensu wahala yake mashi, tou kwaranci yake, na biye mashi muna dariya har na lallab'ashi yayi bacci, nayi jim ina tunani, wasu yadda ka daukesu ba haka suka daukeka ba, ban tab'a tunanin Mahmud zaiyi min haka ba, kallabi na jawo na tufke yalwataccen gashin kaina, wani kodadden zani ne a jikina da shirt, bani da wadatattun kaya, idan nace zan rink'a sakasu tsakar gida zasu kod'e ne in rasa na sakawa in fita shiyasa na yanko fallaye guda-guda na atamfa rubber ina had'awa da shirt ina sakawa a tsakar gida, fitowa nayi na tarar da Ummy tana tankad'en garin tuwo, nace,
"Ummy kawo inyi...".
Ummy ta girgiza kai sannan tace,
"A'a je ki had'a wuta...".
Na wuce kitchen na had'a kan itace (woods) sannan na banka masu wuta na daura tukunya na tsaida ruwa, ina fitowa naci karo da Yaa Ahmad ya dawo daga wurin aiki yana sanye da suit, kallona yayi saidai baice komai ba, da alama ya ji komai tunda ba haka muke ba, amma nayi mamaki da baiyi min maganar ba, ina ganin Abba ne ya hana kowa yayi min magana, tunda gashi itama Ummy ba tace dani komai ba, dakinshi ya shiga, ni kuma na zauna bakin rijiya na jawo mashi ruwan da zaiyi wanka sannan na soma tara wadanda zanyi wanke-wanke dasu, ina ji yana fama da Affan wato autanmu saida ya samu ya likama Ummy shi sannan ya zo ya dauki bucket da na cika mashi ya wuce bayi, ina wanke-wanke ya fito nace,
"Yaa Ahmad ba magana".
Yaa Ahmad ya juyo yana smile ya ja kumatuna yace,
"Akwai magana mana babyna, ai ni dake ba baki bane".
Mukayi dariya yace,
"Munyi magana da Ayan yana gaidaki".
Nace, "Aallah sarki mutanen London".
Affan yazo ya rik'e mashi hannu yana kiranshi...
"A-mad....".
Mukayi dariya, Yaa Ahmad yayi mashi wayo ya wuce, na lura yanayin kowa ya sauya a gidan har sauran brothers dina sunji komai amma babu yadda zanyi, tabbas an dauki lokaci da saka ranar wannan aure saidai yanzu wannan aure ba mai yiyuwa bane, bayan na gama sallar isha'i ina zaune tsakar gida ina cin tuwo da miyar kuka, wani yaro d'an makotanmu ya shigo yace,
"Baby wani yace kizo".
Na gane wanda yake nufi duk da kuwa ba wai ya fad'a min bane, bana da lokacin sauraren duk wasu maganganu na Mahmud don haka nace,
"Ka je ka ce mashi na ce a'a, yauwa kace ma Mairo ina gaidata".
Yaron ya juya ya fita, Yaa Ahmad da Ummy suna tsakar gidan kuma sunji abun da nace saidai babu wanda yace dani komai, yaron bai dawo ba, saidai Yaa Ahmad da yayi picking call ya mik'e ya fice ya jima sannan ya dawo, duk da nasan Mahmud ne ya kirashi amma sai naga baice dani komai ba, tsame hannuna nayi daga cikin akushin da nike cin tuwon a cikinshi na daukeshi na wuce rijiya na wanke komai, Ummy macece mai tsafta bata tolerating k'azanta, kayan da aka b'ata da dare basu kwana a gidan nan, saida safe nayi masu na dora da sanar da Ummy lokacin da zan wuce school....
"Ummy gobe idan Aallah ya kaimu karfe goma zan wuce school, lecture daya gareni".
Tace, "Aallah ya kaimu....".
Nace, "Aameen....".
Na wuce dakina wanda yake wayam, tsohuwar katifa ce kawai a ciki, sai karamin akwati da kayana masu kirki suke a ciki then tsohon bedsheet dake gefe wanda na kulle kayan da nike sakawa tsakar gida a ciki, already ina da alwalla kwanciya nayi saidai na kasa bacci, waya ta isheni da k'ara, nasan wanda yake kira kuma ni bazan dauka ba, na yarda Abbana ba mai kudi bane, saidai bazan yarda da abun da yayi min ba, bazan dauka ba, sam ba haka nike ba, karshe da wayar ta isheni da ringing na jawota na maidata silent na turata a bag, sai wurin karfe daya na dare sannan na samu nayi bacci, da asuba a daddafe nayi sallar subh na koma bacci, nice ban farka ba, sai karfe tara na safe, wata zabura nayi na mik'e, a gaggauce na wanke bakina nayi kalaci, tou ba na shan koko, kosai naci tareda zazafen tuwo na jawo ruwa nayi wanka tareda da brush na wuce daki ina d'aure da zani nayi mashi d'aurin kirji, vaseline kawai na shafa na goge fuskata da powder, na shafawa idanuna kwalli, wasu riga da skirt na atamfa na saka, na shafa humra, most of the time ina b'ata lokaci ne wurin tamke yalwataccen gashin kaina, dakyar na samu nayi mashi gammo na zura long hijab har kasa na rufe fuskata da niqab, kusan kullum haka dressing dina yake, bag dake dauke da materials dina na jawo na zura dari biyu da hamsin tareda zura takalma na fito na lek'a nayi ma Ummy sallama, kullum Ummy tana bina da addu'a, yauma bata fasa ba, cikin ikon Aallah ina fita daga santarmu na samu kekenapep, naira hamsin ya kaini national, na samu saura kadan bus ta cika na samu seat, babu jimawa bus din ta cika kasancewar coaster ce bata da wahalar cika, shiru nayi yayinda bus din ta dauki hanya, akwai en course dinmu saidai tunda muka gaisa ban k'ara uttering koda word guda daya ba, saida wata er course dinmu ta tab'ani sannan na lura da bus din tana tsaye ne a bus-stop dake gefen faculty dinmu ne, mik'ewa nayi muka fito, sunanta Zaynerb Abdul'aziz, duk da bamu magana irin sosai din nan amma mun san juna tunda course daya muke karanta wato BCH (Biochem) muna a 400 Level, degree muke had'awa, a hankali tace,
"What wrong with you mariam?".
Naji wayata dake a bag ta soma tsuwwa, waving hannu kawai nayi mata ta wuce tareda wasu course mate dinmu, zaro wayar nayi wadda ta kasance baby Nokia ce, taci duniya har rubberly na saka na nannad'eta, picking call din nayi tareda yi mata sallama....
"Hello babie... Yeah na shigo... Gani nan a tsallaken bus stop... Ohhh kina a medicine classes... Alright then, ki fito gani nan zan tafo...".
Saida na maida wayar a bag sannan na soma tafiya, ina gab da library na hangoshi yana tafowa daga bayana, kamar wanda aka jefo, ba ya tare da nutsuwa ko kadan, da alama kekenapep ya biyo, daga nesa na kalleshi ya kalleni, Mahmud ne, Jalila zata fara min surutu na jata tareda k'ara sauri, wuf muka shige library, na sani duk nacinshi ba za'a barshi ya shigo library ba, upstairs muka haye, Jalila tace,
"Mahmud na hango ina maki magana kika wani jawoni".
Na zauna akan kujera ina hango waje ta glass nace,
"Na hangoshi shiyasa na jawoki nan".
Da alama tayi mamaki sosai tace,
"Mahmud nike nufi... Suitor dinki... Wanda zaki aura...".
Nace, "Of course shi...".
Da mamaki tace, "Kunyi fada ne...".
Bana san tattaunawa akan maganar a lokacin don haka nace,
"Ki bari kawai idan na shirya munyi maganar".
Jalila tace, "Alright then amma abun da mamaki".
Daga sama muna hangoshi ya duk'e kasa tareda dafe kai, bayan wani lokaci ina lekawa naga wurin wayam, ashe wani friend dinshi dake masters ne ya zo wucewa ya ganshi shine ya jashi suka wuce, wayata na duba tareda dafe kai nace,
"Gosh, lecture....".
Da sauri na jawo Jalila muka sauko muka fice bayan da muka dauki bags dinmu da yake ba'a shiga ciki da bag, lokaci ya k'ure, gashi idan lecturer din ya shiga ba ya bari kowa ya k'ara shiga, sauri kawai muke, Aallah ya taimakemu muka shiga before yazo, muna zama ya shigo, tabbas mun bugi lucky, lecture din twelve to two ce, karfe biyu saura muka fito saida muka wuce central mosque muka yi sallar zuhr na rakata hostel ta amso note sannan muka biyo bus, luckily muka samu coaster ce kuma ta kusa cika, daga national muka hau napep guda ya fara sauke Jalila a unguwarsu sannan ya wuce dani, tun daga nesa na hangoshi, Mahmud ne zaune a dakalin dake opposite da kofar gidanmu, matasa suna yawan zama wurin musamman idan suka dawo daga wuraren ayyukansu, shi daya ne zaune, he is lost a tunani, yayi zuru har napep din tayi parking bai sani ba, da sauri na mik'awa mai napep kudinsa nayi hanzarin fitowa na durfafi kofar gidanmu, saida na kusa karasawa kofar gidanmu sannan ya farga yayi firgigit ya mik'e da sauri yana kiran sunana....
"Baby... Baby... Baby...".
Nayi banza dashi na shige ciki, bansan yadda ya k'are ba, naga dai bai aiko kirana ba, kuma koda ya aiko ba fita zanyi ba, da daddare ina zaune a daki, Abba ya kirani na wuce dakinshi na durkushe a kasa, yana zaune akan kujera, Ummy tana zaune a gefenshi, Abba yace,
"Baby.....".
Na d'ago na dubeshi, yace,
"Miye dalilinki na cewa kin fasa auran Mahmud?".
Na fashe da kuka sannan nace,
"K'arya yayi min, ai ni bance sai mai kudi ba, kowa yasan halina, na soshi tun bansan matsayinshi na aiki ba, amma daga baya yayi min k'arya yace staff ne bayan kuma ashe guard ne, Aallah ya sani, kudi basu rufe min idanu ba, NI *BA NI DA LAIFI* bazan iya auranshi ba".
Na k'ara fashewa da kuka, Abba ya dubeni da mamaki sai kuma yace,
"Shikenan tashi ki tafi, ai bazan maki dole ba".
Na mik'e na fice da gudu ina gumjin kuka......
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Assalam Alaikum sis, complete ne nayi maku shi a matsayin barka da sallah, tou idan kina akan what's app kiyi min magana inyi maki sending document dinshi, idan kuma facebook kawai kike, tou kiyi hakuri har kuzo karshen*
Page. 2
Abba ya dubi Ummy da mamaki yace,
"Amma abun nan akwai mamaki, nasan Mahmud, nasan halinshi, kai abun nan akwai mamaki....".
Da gudu na fad'a dakina na durkushe tareda fashewa da kuka, na dauki lokaci ina kuka sannan na jawo kodaddiyar wayata na duba balance naira hudu ne, text message na turama Jalila....
"Assalamu Alaiki... Babie gobe idan Aallah ya kaimu ki shigo school da wuri before lecture, akwai maganar da nike so muyi".
Message din yana shiga babu jimawa call dinta ya shigo saida na matse na daidaita kaina sannan nayi picking....
"Wa alaikis-salam... Eh... Ahhh tou amma tunda goma ne kamar wurin tara haka... Aha...".
Na jima zaune ina kuka sannan na mik'e na fita na dauko buta a dakin Ummy nayi alwalla na bulbula ruwa ciki sannan na maida mata na wuce dakina na zube akan yamutsatstsar katifa dake a ciki, na jima before na samu bacci ya kwasheni....
Washe gari tunda na tashi da asuba ban koma ba, saida nayi helping Ummy da ayyukan gida sannan nayi kalaci, na bud'e rijiya na cika bucket da ruwa na daukeshi na wuce bayi nayi wanka, bayan wani lokaci na fito na wuce dakina na soma shafa vaseline sannan nayi applying powder da kwalli na shirya cikin wasu riga da zani na atamfa na shafa humra, na zura long hijab har kasa na rufe fuskata da niqab sannan naja bag dita tareda wulla dari biyu da hamsin a ciki, fitowa nayi na lek'a nayi ma Ummy sallama sannan na fice saida na shanye santar gidanmu na hau titi sannan na samu kekenapep ya wuce dani national na hau bus, karfe tara daidai na safe bus ta saukeni a bus-stop dake gefen faculty dinmu, na fito a jerin dalibai dake fitowa daga bus din, na matsa baya tareda zama a karkashin veranda dake saman bus-stop din amma ta baya, call ne ya shigo wayata na jawo bag dita na zaro wayar na duba, Jalila ce take kira nayi picking call din tareda tura wayar ta hijab na kanga a kunne....
"Wa alaikis-salam... Ohhh kun shigo get?.... Gani a bus-stop dake gefen faculty dinmu... Alright then, ina jiranki...".
Jim kadan, kekenapep ce ta tsaya, Jalila ta fito tana sanye da wata cute gown mai hawa biyu, ta kasan rufe take while ta saman take bud'e, tayi rolling veil a saman kanta, tana tafiya tana murmushi, na mik'e mukayi hugging juna, naja bag dina, Jalila tace,
"Besty kinga na manta pen dina a gida, zamu lek'a containers din can in saya before mu wuce....".
Nace, "No need....".
Jalila ta harareni sannan tace,
"Ohhhh dake zanyi jotting kenan....".
Dariya ta bani tou katseni bata bari na karasa magana ba, nace,
"Kai bestiee, I mean akwai extra pen a bag dina".
Mukayi dariya sannan muka jera mukayi taking steps muka tsallake titi, tace,
"Yanzu ina mukayi?".
Nace, "Medicine classes amma saman benen, I mean upstairs...".
Tace, "Kinga tun gida ina ta tunani akan abun da zamuyi magana...".
Saida nayi jim sannan nace,
"Akan Mahmud ne... Can you imaging abun da yayi min... Ina ta shedding tears baki kusa... Nayi kuka kamar zan mutu...".
Jalila tace, "Ohhh... So sad...".
Na lura da yanayinta da alama taji haushi, babu wanda ya k'ara magan daga cikinmu har muka isa medicine classes muka haye stairs muka samu wani class wanda babu kowa a ciki, muka shiga, wayata tana ta ruri, Jalila ta dubeni sannan tace,
"Kiyi picking call din mana".
Nace, "Bestiee manta kawai, na duba wannan Mahmud din ne".
Jalila tace, "Ai bana ce komai ba tunda a kanshi zamuyi magana...".
Muka samu kujerun baya muka zauna, nayi shiru kawai ina takaicin abun da zan fad'a mata, ji nayi tace,
"Baby... Ina sauraronki... Mey ya hadaku fad'a?".
Nace, "Jalila....".
Ta dubeni sannan tace,
"Yeah... Ina sauraronki...".
Nace, "Kin tab'a jin nace ni sai mai kudi zan aura?".
Da mamaki Jalila ta dubeni da alama tayi mamakin tambayar da nayi mata, jim tayi sannan tace,
"Of course amsar itace a'a, ai wannan abu ne da kowa ya sani, sam baki damu da abun duniya ba, ai mun sha magana akan haka, kin sha fad'a min ke miji na gari kike so koda bashi da ko sisi...".
Na dubi gefe kamar zanyi kuka sannan na juyo na dubeta nace,
"Amma duk da haka saida Mahmud yayi min k'arya, he hurt me so badly, nayi shedding tears kamar zan mutu, wai ashe Mahmud guard ne amma yayi min k'arya yace shi staff ne".
Jalila ta zaro idanu sai kuma ta kwashe da dariya har da rik'e ciki tace,
"Ahhh... Hilarious... Unbelievable... Kai... Woah... Amma wannan gayen ya raina maki wayo, tou wai for the first time ina shi, ina ke, haba ya kalleki kuwa before yace sonki ai ke matar manya ce, aww na manta ashe ke babu ruwanki da sai mai kudi".
Na kalleta, tace,
"Sorry bestiee... Gaskiya bai kyauta ba, ai ita gaskiya dadi gareta komi d'acinta kuwa, ai k'arya bata dadi".
Da damuwa nace,
"Jalila... Mey yasa yayi min k'arya? Gaskiya tayi a rayuwa, ya fad'a min gaskiya mana koda kasheni zatayi, tunda na soshi tun bansan matsayinshi ba ai k'aryar ba zata saka in k'ara sonshi ba, sam wannan ba mijin aure bane".
Jalila tace, "Tabbas ba mijin aure bane, Mahmud bai kyauta ba, ban tab'a tunanin wannan daga gareshi ba, koda yake ai maganinki kenan, kince ba zaki auri mai kudi ba saboda kadda ya dauka saboda kudinshi kika aureshi, ai gashi abun da talakan yayi maki, ashe dauk'ar mayyar kudi yake maki, dubeshi a idanu kamar wani mutumin kirki sumi-sumi dashi ashe bakin halin nashi yana a zuciya, indeed na yarda, don't judge book by it's cover....".
Saida naja lumfashi sannan nace,
"Bestiee ki bani shawara, bina yake ko'ina, yana ta ajiye min miss call...".
Jalila ta girgiza kai sannan tace,
"No... A'a kadda ki yarda ki saurareshi, kin san gayun nan da iya karanta mace, kina tsayawa dashi zai karanceki tsaf kuma ki yarda da abun da yace, akul kadda ki sake yace zaiyi maki bayani, ai makaryaci ba mijin aure bane, ka aureshi kace ma y'ay'anku mey, tou ana gadon baya... Ai kema maganinki kenan har kuka gayen nan suhail yayi maki amma kika nuna baki sonshi saboda kawai babanshi yana da kudi, tou ai gashinan shi baiyi maki dauk'ar mayyar kudi ba, shi talakan yayi maki".
Da sauri nace,
"Jalila...".
Tace, "Shikenan, na daina, kin gane kadda ki yarda ki saurareshi, kadda kiyi picking call dinshi, kin san Aallah da ce maki zanyi ki karye sim dinki ki zubar sai kuma na tuna numbar ce akan portal dinki da I.D Card dinki".
Nace, "Na fasa aurenshi kuma na fadawa Abba yace bazai min dole ba".
Jalila tace, "Yauwa haka nike son ji, kinga abun yazo da sauki, kinga wayata tana ringing...".
Picking call tayi....
"Hello... Yeah na shigo... A'a ina medicine classes tareda baby... Ohhh kun baro hostel kenan... Alright then...".
Sai kuma tayi hanging call din sannan tace,
"Bindawa ce, wai tana son ganinki, akan makaryacin d'an unguwarsu ne".
Nace, "Mahmud ba...".
Jalila tace, "Bestiee ki daina kuka a kanshi, ki manta dashi ki cigaba da rayuwarki kamar yadda take before, kinga tashi muje lokaci yana kurewa, kinga amsa ga ruwa kisha before mu tafi".
Ta mik'o min gorar ruwa na amsa na kafa lips, na cire gorar ruwan daga lips dina na rufe murfin na mik'a mata, tace,
"Mey? Ai kina da bag, ko kina nufin ni zanyi maki dakon ruwan".
Mukayi dariya, ta ciro gorar ruwa tasha ta rufe murfin ta maida a bag ta mik'e muka sauko kasa, muka wuce venue din da muke lecture din, muka zauna a seat daya, muna zama na d'age niqab dake fuskata, karfe sha biyu daidai muka fito daga lecture din, na fito tareda bindawa, tace,
"Baby dama ina son magana dake".
Na katseta da cewa....
"Babie you don't have to waste your energy na sani akan Mahmud ne, ki fad'a mashi bazan aureshi ba, wannan auren ya riga ya wargaje yaje ya nemi wata".
Na jawo Jalila muka wuce, ina ji tana cewa....
"Ai shima talaka mutum ne kuma arziki na Aallah...".
Jalila tace, "Mey bindawa take cewa ne?".
Nace, "Manta kawai, d'an unguwarsu take shigarmawa, watakila tausayi ya bata...".
Jalila tace, "Sweety ya shigo daukata bari kiga in kirashi...".
Ta danna mashi call, muka zauna a bus-stop amma ta baya muna tab'a hira, wata zukekiyar expensive mota mai matuk'ar kyau ce tayi parking, Jalaludden suitor din Jalila ne ya fito tareda wani breathtaking handsome saurayi fari, lokacin da na kalleshi saida gabana ya yanke ya fad'i, duk da gidanmu akwai maza masu kyau amma wannan kyanshi na daban ne, da smile suka karaso inda muke na d'age niqab dina tareda waving hannu nace,
"Sweety....".
Da yake haka muke kiranshi, Jalaludden yace,
"Yeah... Baby.... Yane....".
Nace, "Normal....".
Cute saurayin da suke tare naji yana min magana....
"Baby babu magana ne....".
Nayi dariya sannan nace,
"Aaahhh tou ina mik'o gaisuwa...".
Yayi dariya har cute dimple dake mak'ale a both cheeks dinsa sukayi appearing, yace,
"Ina amsawa... Kinsan mey ina sonki".
Nayi dariya kawai, yace,
"You look cute".
Nace, "Kana da barkwanci".
Yace, "Kina da daukar abu da wasa, kince mashi sweety ai nima sweety ne".
Jalila ta mik'e tareda dubana tace,
"Besty muje....".
Ya ware idanu sannan yace,
"Hira muke...".
Jalila tace, "Ni kuma gida nike son zuwa, ehe...".
Jalaludden yace, "Kuma dole akai gimbiya gida...".
A tare mukayi dariya mukayi baki dayanmu, yace,
"Alright then, ai nima ina da magana da ita".
Muka mik'e muka karasa, Jalaludden ya bud'e side din mai zaman hakanan, ya d'age seat, saida Jalila ta shiga sannan nima na shiga, ya maida seat din ya zauna while abokin nashi wanda har yanzu ban san sunanshi ba, ya zagaya bangaren direba, ashe motarshi ce, yana driving suna kus-kus, Jalaludden ya juyo yace,
"Baby.... Ina Mahmud?".
Kaina a kasa nace,
"Mun rabu...".
Da mamaki yace,
"Ban gane ba, kunyi fad'a ko kuma kun rabu?".
Jalila tace, "Sun rabu sweety, wacece zata yarda ta auri makaryaci... Aaryan babu magana ne...".
A cikin raina nace,
"Ohhhh ashe sunanshi Aaryan...".
Idanunsa suna akan titi yace,
"Yeah... Akwai... Ai nemanki nike... Kedai ki bari kawai, zamuyi magana ne...".
Ni suka fara saukeni a unguwarmu, Jalila tace,
"Baby ki gaida min Ummy...".
Nace, "Ai kusa kike da gidan...".
Mukayi dariya, Jalaludden ya fito tareda d'age seat na fito, ya koma suka wuce, tou a bakin titi ne sukayi dropping dina, na matsa tareda shiga santar gidanmu, tun daga nesa na hangoshi, Mahmud ne tsaye duk ya rame ya fita hayyacinsa ya koma wani iri, yana tsaye yana kallona, dauke kai nayi nai gaba domin bazai tab'a bani tausayi ba, shi makaryaci ne, crossing dinshi nayi, da sauri yasha gabana yace,
"Mariam ba kice komai ba....".
Ji nayi raina ya b'aci bayan duk abun da ya faru amma shine yazo gabana yana min wannan magana, don't he feel despair, wani kallo nayi mashi nace,
"Ohhhh so kake inyi magana... Alright then, you got it... Tabbas kai makaryaci ne, kuma bazan aureka ba, nace bazan aureka ba, kaje ka nemi wata, ai bani daya bace, akwai sauran mata a duniya, fara, bak'a, doguwa, siririya, budurwa, zawara, sai wadda ranka yake so... Ka manta dani...".
Dafe saitin zuciyarshi yayi, nayi crossing dinshi na shige gidanmu...
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Assalam Alaikum sis, complete ne nayi maku shi a matsayin barka da sallah, tou idan kina akan what's app kiyi min magana inyi maki sending document dinshi, idan kuma facebook kawai kike, tou kiyi hakuri har kuzo karshen*
Page. 3
Ummy tana zaune tsakar gida na gaidata na wuce dakina, raina a b'ace na rage kayan dake jikina na jawo zani na daura sannan na fito na dauki bucket na bud'e rijiya na jawo ruwa na wuce bayi nayi wanka, bayan na fito na dauki buta nayi alwalla, saida nayi sallar zuhr sannan naci abinci, wai ashe bayan na shigo gida Mahmud zubewa yayi kasa ba ya lumfashi aka wuce dashi asibiti, ban sani ba, kuma babu wanda ya sanar dani....
Da marece ina zaune daga dakina na jiyo Yaa Ahmad yana cewa Ummy ta bashi abinci ya kai asibiti, bayan ya wuce, na fito na dubeta da mamaki nace,
"Ummy wanene bashi da lafiya...".
Ummy tayi jim tana kallona saidai bata ce komai ba, nima kuma ban sake mata maganar ba...
Washe gari tunda muka shiga lectures har muka fito call yana shigowa a wayata, Aallah ya soni na sakata silent, tou before kowace lecture ina saka wayata silent, muna zaune a bus na jawo wayar nayi zuru ina kallon kiran dake shigowa, Jalila tace,
"Kiyi picking mana...".
Na girgiza kai nace,
"A'a... Ammi ce take kira, mahaifiyar Mahmud...".
Jalila tace, "Tou ki kashe wayar mana...".
Na k'ara girgiza kai nace,
"A'a... Bazan iya ba...".
Sannan nayi typing message da sauri na tura mata....
"Ammi kiyi hakuri, *BA NI DA LAIFI* Sam".
Shine abun da nayi typing na tura mata....
Jalila tace, "Miye?".
Nace, "Message na tura mata".
Tace, "Better, ai d'an nata shine ya jawa kanshi".
Nace, "Har yanzu tana da k'ima a idanuna... Ammi wacece mai kirki, bata da damuwa".
Jalila tace, "Indeed?".
Na kalleta kawai saidai ban ce komai ba, tou har na koma gida Ammi bata sake kira ba, bayan na fito daga wanka, wani yaro d'an makotanmu ya shigo wai ana kirana, jim nayi sannan nace,
"Ka sanshi ne?".
Yaron ya girgiza kai, wannan ya tabbatar min da ba Mahmud bane don idan shine zaice min ya sanshi tunda yasha aikoshi kirana, tou waye? Oho, jim nayi sannan nace,
"Ka je ka ce mashi gani nan....".
Yaron yayi nodding kai sannan ya juya ya fice, nayi jim sannan na shige daki, vaseline kawai na shafa na goge fuskata da powder sannan nayi applying kwalli na zura long hijab na fito tareda zura takalman rubber na fice, sai naga ashe abokin Mahmud ne, sunanshi Ibrahim, bayan mun gaisa yace,
"Baby kin san Mahmud bashi da lafiya?".
Na girgiza kai, yace,
"Tou bashi da lafiya yana can rai a hannun Aallah... Jiya bayan kin shiga gida ya zube kasa ba ya lumfashi...".
Nayi jim sannan nace,
"Tou Aallah ya bashi lafiya...".
Ibrahim yace, "Baby, ina ganin ya kamata kuyi magana...".
Da sauri na girgiza kai nace,
"A'a....".
Yace, "Amma mey yayi maki?".
Nace, "K'arya yayi min...".
Da mamaki yake kallona, na lura duk wanda yasan Mahmud idan na fad'a mashi yana mamaki amma wannan ba damuwata bace, na cigaba da cewa....
"I have already made of my mind, magana ta k'are, ni bazan aureshi ba, ni ba mayyar kudi bace, tunda k'arya halinshi ne sai yaje ya nemi mak'aryaci irinshi, not mariam, over my dead body, amma kayi hakuri NI *BA NI DA LAIFI* wannan shine abun da zan cigaba da maimaitawa duk da mafi yawa ba zasu fahimceni ba, amma da in auri mak'aryaci gwara ace saboda bashi da kudi na gujeshi, Aallah yasan zuciyata, yasan *BA NI DA LAIFI* indeed".
Na juya na shige gida na barshi a tsaye, a bakinshi naji rashin lafiyar Mahmud sai a lokacin na fahimci shine wanda Yaa Ahmad ya kaima abinci asibiti, jim nayi na d'age kafad'a na shige dakina na zauna tareda jawo wayata naga wata number ta turo min message....
"I love so much and you are part of my prayers... Ina da barkwanci ke kuma kina da daukar abu da wasa...".
Wannan shine abun da aka turo, Aaryan ne, message na hudu kenan yana turo min tun bayan rabuwarmu amma bai tab'a kira ba, ni dai abun da na sani shine na fara sonshi, wani message ya k'ara turowa saida na saki murmushi sannan na bud'e, ga abun da ya rubuta....
"Ga kyauta daga gareni, kiyi farin ciki".
Sallama naji na fita ina rik'e da waya a hannuna, wani yaro d'an makotanmu ne ya mik'o min wani karamin kit da aka yi wrapping, daidai rik'ewa a palm....
"Wani mai mota ne yace in kawo maki...".
Saida na amsa sannan nace,
"Ina mai motar yake?".
Yace, "Ya tafi...".
Smile ne ya sub'uce akan fuskata nace,
"Na gode, kace ma Naja'atu ina gaidata...".
Yaron yayi nodding kai sannan ya juya ya fice, nayi tsaye ina murmushi, ina juyawa na hango Ummy tana kallona saidai bata ce dani komai ba, da sauri na shige daki na zauna na soma cire wrapping din, wow wani karamin kit ne, daidai rik'ewa a palm, ina bud'eshi naga ashe madubi ne a ciki, murmushi nayi, ranar wuni nayi ina kallon fuskata a madubin ina murmushi, washe gari throughout bamu da lectures, ina zaune gida, ina zaune a daki ina k'ara karanta message da Aaryan ya turo min ina murmushi, Jalila ce ta fad'o, na d'ago da sauri nace,
"Kai besty har kin bani tsoro".
Jalila ta rik'e kugu sannan tace,
"Aaahhh lallai wato har bakin magana gareki, ina sallama amma baki amsa ba, kin zubawa wannan gwaramar wayar taki idanu kina murmushi kamar wacce ta fad'a soyayya da wayar salula...".
Nayi mata wani kallo sannan nace,
"Mey... Phone din tawa kike kira gwarama?".
"Ehh.....".
Nace, "Ohhhh, tou naji, ai d'an guntun gatarinka yafi sari ka bani....".
Mukayi dariya, nace,
"Ki zauna mana...".
Jalila ta harareni sannan tace,
"Ai nima gidanmu ne, idan zan zauna ai zama zanyi".
Nayi dariya kawai, tace,
"Ke tare nike da sweety har da Aaryan, kuma kin san Aallah bomb zan had'a masu, kiyi sauri ki shirya".
Ina mata magana ta fice, ina ji tana cewa Ummy su Jalaludden ne suka zo gaidata, Ummy tace,
"Aaahhh kice manyan baki gareni, tou je dakina ki dauko tabarma ki shimfid'a masu...".
Na ware idanu tareda kunshe baki ina dariya kasa-kasa, ina jin shigowarsu, Jalila ta shigo tana dariya kasa-kasa, nace,
"Aallah besty kina da damuwa...".
Saida ta zauna sannan tace,
"Kinga kuwa yadda suka zaro idanu da na fad'a masu abun da na had'a, haka suka shigo kamar wasu marassa gaskiya, suna can suna sunkuye-sunkuyen kai, besty tashi ki shirya....".
Da yake ban d'ad'e da fitowa daga wanka ba, already nayi applying vaseline, powder kawai na shafa nayi applying kwalli, na shafa humra, na jawo long hijab na aje gefe, can sukayi ma Ummy sallama suka fita, Jalila ta kwashe da dariya, expensive wayarta ce tayi ringing tace,
"Sweety ne....".
Muka kwashe da dariya, nace,
"Kiyi picking mana...".
Tace, "Bari kiga...".
Sai kuma tayi picking call din tareda kanga wayar a kunne ta wani mak'e murya tace,
"I love you Sweety....".
Saida tayi dariya son ranta sannan tace,
"Alright then....".
Ta cire wayar daga kunnanta tace,
"Tashi muje...".
Nace, "Ai hijab zan saka...".
Tace, "Aallah?".
Nace, "Aallah kau, barshi ya fara sona da long hijab sannan sai yaga beauty da nike hidden a cikinta...".
Muka saka dariya, na jawo long hijab din da na ajiye gefe na zura muka mik'e muka fito, ban san abun da zan ce da Ummy ba shiyasa na jera da Jalila muka fice ba tareda nace da ita komai ba, wata expensive Benz ce, suna zaune samanta daga baya, muka kwashe da dariya, na jingina da motar while Jalila ta wuce bayan motar ta zauna kusa da Jalaludden....
Aaryan ne ya tsaya gefena yana smile, na maida kaina gefe ina shakar wani sassanyan expensive kamshi dake fitowa daga jikinsa, yace,
"Kin san mey?".
Na girgiza kai, yace,
"I love you... Ina sonki...".
Sai kuma ya ware idanu yace,
"Yeah... I love you... Kin san mey? Kunya naji kamar in nitse kasa, Aallah ya soni manyan kaya ne a jikina, ai da Ummy tace ba zata bani ke ba...".
Nayi gefe da kaina ina dariya, na juyo sai lokacin na lura da kayan dake jikinsa, wata expensive shadda ce wadda koda nawa aka ce kudinta taci hakan, brown ce, tasha aikin hannu coffee brown, ya murza hula qube da tayi matching dasu, a hannunsa silver wristwatch ce kirar rolex, kafarsa kuma wasu expensive silifas ne, he look breathtaking, handsome, charming, da sauri nayi kasa da kaina, yace,
"Kin san mey? You look lovely...".
Nayi murmushi kawai, yace,
"Yauwa, aramin wayarki...".
Na kalleshi sannan na saka hannu na zaro wayar daga kuguna na fiddo hannuna waje na mik'a mashi, ashe tayi haske kuma ban fita daga text message dinshi da nike maimaita karantawa ba, gani nayi ya ware idanu sannan yace,
"You love me kenan...".
Sai lokacin na lura da abun da nayi, na kalli gefe kawai, hasken wayar ne ya dauke, yayi jim yana juyata da alama gani yake idan ya latsata zata samu damuwa ne, kuma iya gaskiyarsa kenan, ba wai izgili ba, tou nima ai lallab'awa nike da ita ballanta kuma shi wanda yake rik'e manyan wayoyi masu tsada, expensive, ya dubeni yace,
"Am scared kadda in latsa ta samu damuwa, amma bari kiga...".
Sai kuma yayi min waving hand ya juya ya wuce wurinsu Jalila, daga inda nike ina iya hango lokacin da ya mik'awa Jalaludden wayar ya ciro mashi sim card, ya amsa sannan ya amshi wayar very carefully, ya dawo ya bud'e seat din mai zaman hakanan, yace,
"Shiga, zamuyi magana ne...".
Da sauri na dubeshi na dubi murfin motar nayi jim sai kuma na shiga, ya rufe ya zagaya ya shiga daya side din wato bangaren direba, bai ce min komai ba, naga ya zaro kwalin wata expensive waya, android, ya zaro wayar ya saka sim card dina a ciki sannan ya kunnata yayi en danne-danne sannan ya zaro wayarshi ya had'asu da alama abu yake turawa, nace,
"Kaga bari in dauko Al-k'ur'ani a gida ka duba min, hardata nike jin kamar ta samu damuwa...".
Aaryan ya ware idanu yana kallona sai kuma ya fiddo Al-k'ur'ani ya mik'o min, na amsa na lura akwai inda ya saka alama wurin sama-sama, Suratul Nisa'i na bud'e daidai inda nike da damuwa ne, na mik'a mashi before nayi A'uziya sannan nayi Bismillah, na soma rero karatu a cikin kira'ata mai sanyi, ko lokacin da mukayi hadda en ajinmu suna yawan cewa nice ta biyu a dadin kira'a, nasha mamaki sosai da ya soma cina gyara yana gyara min pronunciation, ya burgeni sosai, saida na kai inda nike hari sannan nasa aya, yace,
"Ina da shekaru goma sha biyar na haddace Al-k'ur'ani mai girma, K'annena mata twins secondary suke amma kowace tana da sittin a kanta, ki rink'a kula da hardarki, mafi yawan dalibai suna sakaci ne akan bibiyar hardarsu shiyasa take zubewa, bibiyar yafi masu wahala akan hardar".
Nayi nodding kai kawai, before in kammala secondary school na haddace Al-k'ur'ani mai girma....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Assalam Alaikum sis, complete ne nayi maku shi a matsayin barka da sallah, tou idan kina akan what's app kiyi min magana inyi maki sending document dinshi, idan kuma facebook kawai kike, tou kiyi hakuri har kuzo karshen*
Page. 4
Aaryan ne ya mik'o min Alk'ur'anin sannan yace,
"Ki ja min duk inda ranki yake so...".
Na ware idanu sai kuma na bud'e na jawo mashi, tunda ya fara rera karatun ya tafi da ni, tou I feel kadda ya daina, the more yake rera karatun the more yake k'ara tafiya da ni, kira'arshi wata aba ce ta daban a dadi, maa shaa Aallah, ya burgeni sosai, nayi mashi haka ne saboda idan ba ya neman ilimin addini ya fara saboda namiji marar ilimin addini ba ya burgeni ko kadan, shima Mahmud farkon fara soyayyarmu haka nayi mashi saidai shi na samu ya sauke Al-k'ur'ani ne saidai ba ya da hadda, muna tare ya soma hadda, ji nayi yace,
"Ina er biyunki?".
Na dubeshi na ware idanu, yace,
"Yeah, twins sistornki".
Na girgiza kai sannan nace,
"Ni ba en biyu bace...".
Ya karkato min screen din wayarsa yace,
"Wannan ta kusa dake nike nufi...".
Na ware idanu ina kallon wayar sai kuma nayi murmushi, indeed mutane suna yawan cewa kamar twins muke saboda kusan tsayinmu gudu, Nadiya ce, nace,
"K'anwata ce, sunanta Nadiya...".
Ya ware idanu sannan yace,
"Amma kuna kama kamar twins, kirawota mu gaisa ta zama In-law dina...".
Nace, "Tayi aure har da yaronta daya, Najib, ina ajin karshe a secondary nace karatu zanyi, Abbanmu ya siya min Jamb na zana naci na nemi admission na samu, ita kuma tana gama secondary tace aure, Abba yayi mata aure, da auranta ta fara diploma amma korafi take tana shan wuya ga baby ga karatu... Aure ibada ne bazan iya had'ashi da karatu ba shiyasa nace a'a... Mu shidda iyayenmu suka haifa, Yaa Ahmad yana aiki, Yaa Mustapha yana karantar MBBS a Abu Zaria, Yaa Ayan shi kuma a london yake karantar medicine, daga shi sai ni sai Nadiya sai autanmu Affan d'an shekara daya da watanni, shi kam ba ya san bakuwar fuska...".
Yace, "Sorry, Jalila ce ta tura min hotunanki...".
Nikam ai koda bai fad'a min ba, nasan wannan aikinta ne tunda a wayarta nike ajiye pictures dina kasancewar ni bani da babbar waya, ji nayi yace,
"Sunana Aaryan Muhammad both iyayena en garin nan ne, ina da k'anne mata guda biyu twins Adila da Adla, mahaifinmu ya rasu muna rayuwa ne tareda mahaifiyarmu da en uwansu, nayi both degree dina na farko da na biyu duk a kasar london, na karanci fannin zane-zane ne wato architectural engineering... Uhm... Ina jin kishirwa, zan samu ruwa?".
Nayi jim sannan nace,
"Eh akwai amma na tulu ne, tulun dake dakin Ummy, ruwan suna da sanyi".
Aaryan yayi murmushi sannan yace,
"Yeah, ai nayi missing dinsu tun last da mukaje kauyenmu...".
Nayi murmushi kawai sannan na b'alle murfin motan na fice na taka a hankali na shige gidanmu, na tadda Ummy inda muka barta, ta kalleni da tuhuma tace,
"Mi ya zaunar dake wajen?".
Nayi shiru sai kuma nayi sauri nace,
"Abokin Aaryan ne yake jin kishirwa shine zan d'ebar mashi ruwa a tulunki".
Ummy tace, "Amma mi ya hana ki amso mashi pure water gidan Maman en biyu".
Nace, "Ummy bazai sha pure water ba, ni kuma bani da kudin da zan siya mashi ruwan gora shiyasa nace mashi akwai tulu a dakinki yace tou".
Tace, "Shikenan amma nayi maki tambaya baki amsa ba... Mi ya zaunar dake waje?".
Nayi shiru na rasa abun da zance, tace,
"Shikenan jeki ki debo mashi ruwan".
Da sauri na shige dakin na dauko sabon cup din silver dinta na fito na wankeshi sannan na koma na cikashi da ruwan tulun Ummy mai sanyin dadi, ruwan suna da dadi, saida na rufe kofin silver din sannan na fito na zura takalma na fice waje, ina fita na b'alle murfin motar na shiga na mik'a mashi cup din ya amsa tareda bud'e murfin yayi motsi da lips dinsa sannan ya kafa lips, yana sha har yana lumshe idanu, nayi murmushi gaskiya Aaryan yana burgeni, ina sonshi, saida ya shanye ruwan sannan ya cire lips dinsa ya maida murfin, ya ware idanu yace,
"Wash dadinsu ya saka na shanyesu duka, ji nike kamar cikina zai fashe...".
Na lura Aaryan mutum ne mai barkwanci, tou yana da miskilanci, watakila saboda yana sona ne ko kuma don na samu lokaci dashi ne shiyasa na lura da haka, dariya mukayi ya mik'o min expensive wayar da ya saka sim card dina a ciki, yace,
"Ara maki nayi before inje in koyi wayarki".
Na kalleshi, yace,
"Yeah, aro na baki ba kyauta ba, don amsar abuna zanyi".
Duk da na gane inda ya dosa, dubara yake so yayi min amma babu yadda zanyi, ya cigaba da cewa....
"Na tura maki pictures dinki, and na bud'e maki what's app, nayi maki sending apps daga wayar Adla irin naku ne na mata, bestie, beauty camera, tou na mance sunan sauran...".
Nace, "Idan na fasa maka screen fa?".
Aaryan yayi dariya sannan yace,
"Then sai in sauya wani ai muna da kudi".
Dole na amshi wayar, ya mik'o min cup yace,
"Ki maida shi...".
Na lura yayi hakane saboda yana avoiding inyi mashi maganar wayar, amsa nayi na maidashi gida na dawo, gani nayi ya mik'o min wayarsa, na amsa, picture dina ne akan screen lock amma mey? Akan wallpaper picture dinshi ne shi da wata chocolate yarinya mai kyau, baki daya munyi smile, sun bada perfect match, saida gabana ya yanke ya fad'i na d'ago da sauri na dubeshi da alamar tambaya, gani nayi baki daya yanayinsa ya sauya, cikin damuwa yace,
"Sunanta Aalima, cousin dina ce, a gidanmu ta tashi, I love her so much, ta b'ace har yanzu bamu san inda take ba, tana raye tana mace bamu sani ba, first love dina ce, I love her and I love you...".
Nayi jim, yace,
"Baby zaki yadda min waya".
Na dubi wayar da sauri, ya ware idanu yace,
"Kinga wurin Umma zan kaiki ince mata ga Inlaw dinta, in rama abun da Jalila tayi mamu".
Na ware idanu da sauri, yayi dariya yace,
"Sorry, wasa nike maki".
Kiran sallar zuhr aka soma da yake garin akwai lullumi ne shiyasa mutum bai fiye fahimtar lokaci ya ja ba, na ware idanu ya duba silver wristwatch dake daure a wrist dinsa, yace,
"Lokacin sallah yayi...".
Na fito muka wuce tareda Jalila na fiddo masu butoci guda biyu suyi alwalla, Jalila ta hakime akan katifa tana danna waya, nace,
"Besty ki tashi kiyi sallah...".
Tace, "Am off...".
Nace, "Ohhhh...".
Na fito na tarar sun aiko wani yaro ya maido botocin, na dauki buta na shiga bayi na fito nayi alwalla na koma daki nayi sallah, can Jalaludden ne ya kira Jalila, mun fito tsakar gida Affan ya mak'ale mani dole na daukeshi muka fito, Jalila tana mashi wasa koda kallonta baiyi ba, Aryan yace,
"Affan... Right?".
Nace, "Ehh shine...".
Ya mik'o mashi hannu, mak'ale kafad'a yayi yaqi zuwa, ai daman nasan za'ayi haka, Affan kenan, da en gidanmu kawai yake yarda, ba ya yarda da bakuwar fuska, Aryan yace,
"Ya qi yarda dani...".
Nace, "Ba ya yarda da bakuwar fuska...".
Aaryan ya ware idanu, Jalila tace,
"Ina yawan zuwa amma ba ya yarda dani, wani lokacin ina shiga ya ganni zai hau kuka, may be gani yake kamar zan tafi dashi namu gidan ne in rabashi da nasu".
Mukayi dariya, Affan d'an drama ne, indeed, tou muna sallama ya mik'o hannu yana tab'a Aaryan amma yana juyowa sai yayi sauri ya makalkaleni, wai kadda ya daukeshi, ya mik'o hannu kamar zai daukeshi, ya k'ara mak'ale min yace,
"Ba-by... Abba... Ummy...".
Mukayi dariya, Aaryan yace,
"Baby...".
Nace, "Sunana Mariam...".
Yace, "Maa shaa Aallah... Wow... Nice name... Oohhh tou besty dinki bata fad'a min sunanki ba saidai tace baby, I thought rowar sunan kuke min shiyasa ban tambaya ba...".
A tare mukayi dariya suka shiga mota, na lek'a ta glass nace,
"Besty, wacece admin a group dinmu?".
Tace, "Bindawa admin ce...".
Nace, "Then ki tura mata numbata kice nice ta sakani a group, muga zata sakane ko har yanzu tana bin bayan d'an unguwarsu".
Ina tsaye saida motar ta b'ace min sannan na matsa, Aaryan kenan har da cewa bai siyo chocolate ba ballantana yaba Affan amma ga dubu daya, ya zaro sabuwar dubu daya ya mik'o mashi amma ya mak'ale min yaqi amsa, Affan kenan, murmushi nayi ina kallonshi yana kiran....
"Ba-by... Ba-by... Ba-by...".
Na juya na koma gida saidai zaro tsohuwar gwaramar wayata nayi nai zuru da ita, tou na gaza nuna wadda Aaryan ya bani tou ban san abun da zance ba, wai ashe har VTU yayi min sannan yayi min sending data, almost eleven thousand na samu a account dina, I feel inyi transfer din kudin a bani in sayi less din nine thousand in dinka in samu na shiga mutane, da daddare ina bud'e data na samu bindawa ta sakani group dinmu har da wani rubuta....
*_Welcome Mrs Aaryan to be_*
Wasu da suka sanni da Mahmud suka ce Mahmud dai, har gani nayi wata ta rubuta...
*_Babie ai har engaged anyi mata da Mahmud ko baki sani bane_*
Bindawa tace ai mun rabu, ita yanzu tana side din Aaryan ne, da alama akwai wata a kasa, daga nan abun ya zama topic of discussion, wadanda sukayi min sallama nayi masu reply na duba dp naga picture dinshi, yana sanye da wasu breathtaking k'ananan kaya, a London yayi selfie din, indeed he is damn cute, handsome, breathtaking, charming, alluring and mesmerizing, smile nayi na duba naga *Babie* ya saka min a sunan dake appearing a group, ban sauya komai ba, gani nayi yayi min sallama, da *heartbeat* yayi saved din numbarsa, murmushi abun ya bani, na amsa sallamar da yayi min, mun jima muna chatting, tou yana da murya mai d'ad'i amma bai tab'a kirana ba, koda yanzu typing kawai yake ba ya sending voice, sallama mukayi na kwanta saboda ina da lecture 8am, tou ya kamata in kwanta da wuri, tabbas hakane....
Washe gari tunda na tashi da asuba ban koma ba, bayan nayi sallar asuba nayi wanka na shirya tsaf sannan nayi kalaci a gaggauce, na mik'e tareda wanke bakina nayi brush, shadda ce blue a jikina lokacin naso nayi mata surfani saidai bamu da hali, lokacin saidai aka dinka min ita hakanan aka ratsa dark blue net a gaban shaddar sai dinkin yafi kyau sosai fiye da idan aka yi mata surfanin, long hijab har kasa na zura na rufe fuskata da niqab naja handbag dina nayi ma Ummy sallama na fice na tari keke napep, karfe bakwai da mintina ashirin tayi min a bus, hakanan naji ina sha'awar in shiga gallery, zaro wayar nayi na kunnata, wow, ashe har da pictures dinshi ya turo gasu nan birjik, looking breathtaking a kowane picture, har da hoton k'annanshi en biyu masu kama dashi, har da hoton wata cute mata ina ganinta na gane mahaifiyarshi ce, cin karo nayi da hotunan wannan chocolate din yarinyar, Aalima ce, saida gabana ya yanke ya fad'i, tabbas hakane ya faru da ni lokacin da na fara ganin hotonta, nayi gaba da sauri, tou bana son kasancewa a wannan yanayin, har da hoton wani babban mutum na gani wanda nike ganin shine late father dinshi, cin karo na k'ara yi da hotunan wannan chocolate yarinyar, da sauri na fice daga gallery din tareda bud'e data....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Assalam Alaikum sis, complete ne nayi maku shi a matsayin barka da sallah, tou idan kina akan what's app kiyi min magana inyi maki sending document dinshi, idan kuma facebook kawai kike, tou kiyi hakuri har kuzo karshen*
Page. 5
Messages ne suka soma rushing, suna gudun wuce mate, ashe bayan na sauka hirar maganarnan suka cigaba da yi a group, saboda kusan kawayenmu sun sanni da Mahmud kuma sun san anyi mamu engaged, nikam ban damu ba koda za'a ce saboda kudi na guji Mahmud na so Aaryan, ai Aallah yasan zuciyata, Jalila ce naga tayi magana, rufe data kawai nayi na maida wayar a bag, before eight ina zaune a lecture hall, bayan mun fito daga lectures, ni da Jalila muna zaune a bus, macpolo ce kuma mutane kadan ne a ciki, ta zaro kwalin waya tareda tsohuwar wayata ta mik'o min, daman na san za'ayi haka, dubara kawai yayi min ta yadda dolena in amsa, amsa nayi na saka a handbag, nace,
"Dubara kawai yayi min...".
Jalila tace, "Aaryan yana sonki sosai, abokin Jalal ne sosai, ba ya da damuwa, Jalal ya sanshi ciki da bai...".
Sai kuma tayi dariya tace,
"Ya love din?".
Nima nayi dariya sannan nace,
"Har na mance da wani Mahmud".
Tace, "Kuma kika kira sunanshi...".
Mukayi dariya, tace,
"Kin san kuwa Aaryan miskili ne, magana wahala take mashi, da alama jiya zancen kurame kukayi".
Mukayi dariya, nace,
"Nima na lura da haka amma ba haka yake ba, yana da barkwanci, farko da smile da nodding kai kawai nike amma saida ya saka nayi magana, yana da surutu a gabana...".
Jalila tace, "Ooohhh... Unbelievable... Don yana sonki ne, ya nuna maki miskilancin ya gani ai sai ki barshi da miskilancinshi ki nemi wani...".
Mukayi dariya, tace,
"No more shedding tears kenan...".
Nayi rolling idanu nace,
"Yeah, soyayyar Aaryan ta kawo man farin ciki a rayuwata".
Tace, "Ooohhh ai na gani, mik'o wayarki in kashe mamu selfie".
Na zaro wayar na mik'a mata, tace,
"Cheese...".
Ta kashe mamu selfie a different style, ta jawo wayarta tace,
"Bari kiga inyi sending...".
Wayata ce ta soma ruri, saida gabana ya fad'i, Ammi ce take kira wato mahaifiyar Mahmud, ban yi picking ba, saida kiran yayi yawa sannan na tura mata sakon text message....
"Ammi koda na dauka ban san abun da zance ba, amma Ammi kiyi hakuri *BA NI DA LAIFI* Indeed".
Nayi zuru baki daya yanayina ya sauya saida na bud'e hotunan Aaryan ina kallo sannan farin cikina ya dawo na manta da komai, soyayyar Aaryan tayi nutso deep a cikin zuciyata, i can't abroad loosing dinshi, d'an halak, ina saukowa daga napep na hangoshi yana zaune a cikin wata cute mota kirar Benz ya zuro kafarshi daya waje wadda take rufe da wasu expensive cover shoes, Aaryan ne, fitowa yayi yana murmushi, expensive suit ne a jikinsa saidai babu cot, shirt ce, necktie da trouser da wasu expensive cufflinks dake a sleeve dinsa, tareda wata expensive wristwatch, he looks breathtaking, yana taking steps yana smile yana k'ara appearing handsome, sumarshi baka wuluk tana kwance, yalwatacciya, ina k'ok'arin ciro hamsin in baiwa mai napep kudinsa, ya karaso tareda ciro wallet ya zaro sabbin en dubu-dubu guda biyu ya mik'a mashi, kallonshi nayi yana min smile, sama nayi da niqab dake fuskata tareda escaping murmushi, muka jera zuwa wurin motarsa, na jingina da ita while ya tsaya a gefena, na kalleshi yace,
"Kin san mey? I missed you...".
Nayi murmushi kawai, yace,
"Nazo ne kawai in ganki kuma na ganki daga wurin aiki nike, am leaving".
Na ciro wayar da ya bani na mik'a mashi, ya ware idanu yana kallona, saida nayi dariya sannan nace,
"Selfie...".
Ya shafi sumar kansa sai kuma yayi murmushi har cute dimples din dake a b'oye a left and right cute cheek dinsa sukayi appearing, na kalleshi na kalli wayar dake hannuna yace,
"Ooohhh....".
Ya amshi wayar saida yace,
"Cheese...".
Sannan ya kashe mamu selfie yayi kyau sosai, ya zaro wayarshi ya tura har da daurawa akan dp, yace,
"Inga handbag dinmu...".
Na kalleshi, yace,
"Yeah, ai handbag dinki tawa ce".
Nayi murmushi sai kuma na mik'a mashi ya tura hannunsa a pocket din wandonsa ya zaro sannan ya zura min wayata a bag yayi zipping ya mik'a min, wai ashe wani karamin kit ne mai kyau ya saka min a ciki, Yaa Ahmad ne ya shigo santar a bike dinsa, kallona yayi saida gabana ya fad'i, ya wucemu yayi parking dinsa ya shige gida, nace,
"Shine Yaa Ahmad".
Aaryan yace, "Ooohhh kuna kama sosai".
Nayi murmushi tareda nodding kai, da murmushi yace,
"Am leaving, ki saka zaiyi maki kyau...".
Yayi min waving hannu ya juya ya shige motarsa ya jata, ina tsaye saida motar ta b'ace min daga gani sannan na juya na shige ciki, nayi crossing din Yaa Ahmad zai fito saidai baice min komai ba, yayi crossing dina ya fice, da kallo na bishi, a hankali nace,
"Kuyi hakuri NI *BA NI DA LAIFI* sam".
Na wuce ciki na shige dakina zan ciro wayata na lura da wani karamin cute kit, ciroshi nayi na bud'e wani karamin cute ring din diamond ne yayi appearing, jim nayi sai kuma nayi murmushi na bud'e akwati na turashi kasan kayana na maida akwatin na rufe....
Washe gari bayan na dawo daga school, ina saukowa daga napep naci karo da wata katuwar expensive Jeep parker opposite da gidanmu, wata farar babie ce ta fito tana sanye da fitet gown wadda ta matseta kanta tamke da kallabi, babu hijab a jikinta amma ta d'aura veil a kafad'a, gani nayi ta nufo inda nike kuma ni ban santa ba, wata yarinya ce ta k'ara fitowa daga motar, k'anwar Mahmud ce, Safeena, cikin raina nace,
"Ooohhh wai for how many time suke so inyi keeping ce masu NI *BA NI DA LAIFI* bazan iya auren makaryaci ba...".
Nayi crossing dinsu na shige gidanmu na wuce dakina sallama sukayi suka shigo suka zauna, yunwa nikeji kuma na gaji, na debo ruwa na ajiye masu na dauki zani da shirt na fita, rijiya na bud'e na jawo ruwa na cika bucket tareda daukar kwandon wanka na wuce bayi nayi wanka na sauya kayan dake jikina da zani da shirt, na fito na shiga daki na samesu zaune kamar yadda na barsu, vaseline na shafa na goge fuskata nayi applying kwalli, yunwa nike ji so badly, tamke kaina nayi da veil na fice na shiga kitchen na zubo zazafen tuwo na koma daki tareda masu bismillah suka girgiza kai, gyara zama nayi naci nayi nak sannan na kora da ruwa, na fita tareda ajiye kwanon a kitchen na kuskure bakina na koma dakin na zauna na dubesu nace,
"Yauwa ina jinku, da mey kuke tafe?".
Daya babie din ta dubeni a fusace tace,
"How dare zaki shanya mu...".
Na kalleta na ware idanu sannan nace,
"Ooohhh I see, amma ai ban gayyatoku ba ballantana kuce na kiraku kun zo nayi maku wulakanci, ku tashi ku tafi mana ai ban tsayar daku ba, na dawo daga makaranta da gajiya da yunwa ai bazan tsaya in wahalar da kaina ba akan maganar da an riga an gamata, wai don Aallah mey kuke so inyi maku, sau dubu nawa kuke so in cigaba da ce maku kuyi hakuri NI *BA NI DA LAIFI* bazan auri mak'aryaci ba...".
Na mik'e na karasa gefen katifa na zaro wata karamar waya mai gidan memory, before da ita nike amfani amma daga baya ta samu matsalar speaker idan ina magana ba'aji shine na ba wani d'an unguwarmu dubu daya ya sawo min waccen karamar Nokia din, ko lokacin da aka kawo min ita taci duniya, jim nayi ina juya wayar abun da ya faru shine a lokacin da nike amfani da ita duk wayar da nayi tana recording shiyasa sau da yawa idan bani aikin komai nike kunna recording call din da nayi da Mahmud ina ji ina murmushi, idan mutum yaci karo da ni a lokacin sai yayi tunanin radio nike saurare, tayi recording komai, kunna masu nayi sukaji komai, da alama suma sunyi mamaki, na gani a fuskokinsu, d'ayar babie din tace,
"Kai impossible....".
Na kalleta sai kuma ta sauya yanayi, a hankali tace,
"D'azu na b'ata maki rai, nayi maki ihu amma kiyi hakuri, Mahmud means a lot to me ne, kiyi hakuri ki koma gareshi, tabbas akwai kuskure a wani wurin amma sam wannan ba halinshi bane...".
Nayi mata shiru, Safeena kanwar Mahmud ta fashe da kuka tace,
"Don Aallah kiyi hakuri ki tausaya mamu shi daya muke dashi, Ammi kwana take kuka, yana can kwance akan gadon asibiti fighting for his life... Kin sani na sani kowa ya sani he love you so much...".
Nace, "Indeed he love me so much but I don't either said sai mai kudi zan aura, tou miye dalilin k'aryar, Aallah ya bashi lafiya, Aallah ya tsareshi daga kamuwa da ciwon zuciya amma ni babu ni babu shi, duk da yana can fighting for his life and please kadda kuga laifina NI *BA NI DA LAIFI* I don't think I deserve yayi min k'arya tunda ai ban ce sai mai kudi ba, ko miye ya faru shi ya janyowa kanshi NI *BA NI DA LAIFI* sam...".
D'ayar babie din ce ta daka min tsawa ta mik'e tareda zaro bandir din en naira dubu-dubu ta jefeni dasu tace,
"Kawai ki fito fili kice you are after abun duniya, don kina fara shine kike tunanin sai mai kudi zaki aura, kodadda kawai, no wonder kin tashi kina cin wannan dirty so called abincin da kikayi mamu tayi d'azu, aikin banza aikin wofi, dubi wannan gugurarran dakin babu komai a cikinsa sai talauci a haka kike nema ki wulakantamu, Mahmud yafi karfin wannan, dole sai kin aureshi koda kina mutuwa kina dawowa, mayyar kudi kawai, kudi kike so ko tou ai gasu nan dauka, kina banzar cima a gida shine kike burin idan kinje gidan ki sauya cima, kina so ki daina cin tuwo miyar kuka ki koma cin tea da bread da wainar egg, fried rice da pepper chicken, kina so ki daina shan ruwan tulu ki koma shan ruwan gora da drinks masu sanyi, kin gaji da wahala kina so saidai kina kwance ayi maki komai, mayyar kudi kawai, wato kin saba da wanka da ruwan rijiya wadanda sai kin jawo kin zuba a bucket kin cika sannan ki dauka kije bayi kiyi wanka shine kike dreaming din wanka a katon bathroom mai towel, bathtub da shower wanda kina juya makunni ruwa zasu zubo maki shaaa, kin tashi a wannan gurrurarran gidan kina so ki koma katon mansion mai garden, swimming, ac, upstairs, manya-manyan bedroom da parlours na alfarma wadanda daya daga ciki yafi girman wannan so called gidan... Idan ba wannan ba, miye abun kyama a auran mai guard... Yaa Mahmud yafi karfin yayi maki k'arya, bazai maki k'arya ba, kawai ki fito fili kice dreaming din auran mai kudi kike, ai mai kudi kike so ko? Ahhh tou kin samu, Mahmud cousin dina ne, Abbana attajiri ne, mai kudi na gasken-gaske, waccen motar da muka zo a kanta, zan iya siyen guda goma irinta ba tareda na girgiza ba... Mahmud yana da gatanshi, Abbana yana sone ya samar mashi da aiki mai kyau shi kuma ba ya son takurawa wani shiyasa yake guard, yana da diploma ya ajiyeta yana aiki da secondary, koda kina so koda baki so sai kin aureshi...".
Kallon gefe nayi tareda maida kwolla dake neman zubo min, bana san inyi kuka a gabansu, mik'ewa nayi na nuna mata kofa nace,
"Get out... Mahmud ne bazan aureshi ba...".
Safeena ta duk'a ta dauki kudin tace,
"Baby kiyi hakuri....".
Da sauri na katseta tareda nuna mata kofa nace,
"Babu abun da za ki ce min, ai kece kika kawota taci min mutunci, tou jata ku fice min daga gani, ai kina da brain ko? Tou Mahmud ne bazan aureshi ba, nice Mariam nace ba nayi sai kubi wani sarkin... Ai bani daya bace mace a gari, akwai babies da yawa... Nace ba nayi ai sai ku kyaleni... Aikin banza aikin wofi...".
Safeena taja daya babie din suka fice, duk da bana so amma saida suka sakani na fad'i bakaken maganganu....
0 comments:
Post a Comment