Page. 11
Washe gari na saka wayata charge a dakina na fita, Affan ya shiga ya zareta yayi mata daya-daya, saidai shiga nayi na tadda yana bacci ga wayata a gefe, na dauketa na had'a shine ta samu damuwa a speaker, bayan kwana biyu naba wani d'an unguwarmu naira dubu daya ya siyo min baby nokia, yadda aka yi na gane k'aryar da Mahmud yayi min, wata rana ni da Yaa Ahmad muna zaune muna hira muna having hilarious moment, nace,
"Yaa Ahmad gaskiya ya kamata in zama staff a wurin aikinku".
Yaa Ahmad ya kwashe da dariya sannan yace,
"Yadda kike lagwai-lagwai din nan ai ba zaki jure ba".
Nace, "Kuma nike jure wahalar school".
Yace, "Ai wannan daban, wancen daban, yadda kike haka koda gudun kirki baki iyawa".
Nace, "Babu wani nan...".
Yace, "Dubeta matsoraciya...".
Nace, "Naji, dadin abun sweety na shima staff ne".
Ya ware idanu yace,
"A'a kinyi b'atan kai, Mahmud guard ne".
Da mamaki nace,
"Guard kuma? Amma zolayata kake...".
Da mamaki ya girgiza kai sannan yace,
"Nope... Ehhh tabbas guard ne, baki sani bane...".
Jim nayi yayinda muryar Mahmud takeyi min yawo a brain a lokacin da yake tabbatar min dashi staff ne, na fashe da kuka na mik'e na wuce dakina ina kuka, ranar kwana nayi ina kuka, yadda naga rana hakanan naga wannan dare idanuna biyu ina shedding tears wannan wani irin abu ne, na guji mai kudi ina ganin zaiyi tunanin na aureshi ne saboda kudinshi, gashi talaka yana min kallon mayyar kudi yana ganin bazan soshi saboda Aallah ba, abun nan da haushi, broken heart ne, broken truth ne, tabbas before nayi ma masu kudi mummunar fahimta, ai ba duka aka taru aka zama daya ba, I feel ace zan iya maido da lokaci baya, tou da kuwa zan mallakawa suhail baki daya zuciyata, na sani yana sona matuk'ar so, kowa ya sani yana sona amma na qi shi, gashi talaka yana neman janyo min ciwon zuciya, a wannan dare na yanke shawarar bazan auri Mahmud ba, wannan sam ba mijin aure bane, shine washe gari na tusa Abba da Ummy a gaba ina masu kuka (farkon labarin kenan)....
************
Zuru nayi ina shedding tears from inside, har muka karasa school ban sani ba, Jalila ta zaro five hundred naira ta mik'awa mai napep tace,
"Ka dauka duka...".
Ta jawoni muka fito, tace,
"Baby kiyi hakuri ki daina kukan".
Nayi nodding head kawai, ta zaro gorar ruwa daga bag ta mik'o min na amsa na duk'a tareda d'age niqab dita na wanke fuskata da yake ruwan basu da sanyi sosai, sai idanu sukayi kamar sleeping eyes saboda kukan da na sha, muka wuce muna taking steps sannu a hankali, tun eight eight har four muna school, a can mukayi both sallar zuhr da asr, mun fito daga masjid muna tafiya, suhail ne yasha gabanmu, ya dubeni sai kuma ya kalli Jalila yace,
"Jalila mey yake damun baby? She looks strange".
Jalila ta tab'e baki sannan tace,
"Talakan saurayinta ne yake neman janyo mata ciwon zuciya".
Suhail yayi jim sannan yace,
"Muje in kaiku gida...".
Jalila tace, "A'a... Na kira wani yanzu haka yana cikin school din nan".
Suhail ya dubeni da damuwa yace,
"Tou... Baby kiyi hakuri...".
Na kalleshi I feel zan iya mashi magana amma bazan iya ba, yayi min murmushi yana waving hannu sannan ya juya ya wuce, wata expensive Jeep ce tayi parking, Aaryan ne ya fito yana sanye da wani expensive yard, dinkin zamani mai circle neck tareda design a gaba, he look extra ordinary handsome, breathtaking, cute, charming, yayi kyau more and more, da mamaki nike kallonshi don ban san lokacin da Jalila ta kirashi ba, ya zagaya ya bud'e din side din dake gefen direba na shiga ya rufe, Jalila ta zauna a back seat, Aaryan ya zagaya ya zauna bangaren direba yayi ma motar key tareda shan round about, shiru motar take babu wanda yake magana, Jalila tace,
"Yauwa kayi min sending picture dinku".
Yayi mata sending ta saka a group dinmu na what's app, ita ya fara saukewa a bakin get din gidansu sannan ya wuce, gani nayi ya dauki wata hanya nayi tunanin hanyar zata kaishi unguwarmu ne amma sai naga yayi horn a bakin wani tangamemen get na dubeshi da sauri, yayi banza dani, gani nayi an wangame get din ya shiga da motar cikin katon mansion din mai kama da aljannar duniya, a rayuwata ban tab'a shiga gida mai kyanshi ba, parking yayi a jerin expensive motoci dake parker, na dubeshi yace,
"Gidan auntyna ce, k'anwar Ummana, muga jikkarki ki goge fuskarki kadda ta ganki a haka ta gane kinyi kuka, nasan a jikkunanku na mata ba'a rasa kayan make-up... Right?".
Na dubeshi kawai, ya dauki jikkata ya budeta yana dubawa saidai babu kayan make-up babu dalilinsu, ya ware idanu yace,
"Handbag dinki kamar bata mace ba, babu powder balle lipstick da blusher aw barbad'a kumatu... Uhmm handbag dinki babu kayan make-up, tou suna ina? Uhmm ai en mata suna yawo da kayan make-up ne na sani".
Nayi mashi shiru, ya zaro handkerchief daga pocket din wandonsa ya mik'o min yace,
"Amsa ki goge fuskarki...".
Na kalleshi nayi sai kuma na amsa na nufi fuskata dashi, wani kamshi ne mai sanyi ya ziyarci hancina na tsaya cak da hannuna, na dubeshi nace,
"Kamshi yake....".
Aaryan ya ware idanu yace,
"Aww sorry ashe kamshi yake ba wari ba... Baby kina da abun dariya, tou miye don yayi kamshi, Uhmm".
Na kalli gefe tareda sakin dariya shima dariya yayi, na goge fuskata na mik'a mashi ya amsa before yace,
"Yeah... You look lovely...".
Sai kuma ya fita ya zagaya ya bud'e side din da nike na fito ya maida murfin motar ya rufe, yace,
"Let go...".
Nace, "Aha...".
Aaryan yayi gaba na bishi, yana gaba ina biye dashi, kofar shiga ciki ita kanta abun kallo ce, ga punch of flowers masu kyau, ya danna bell, wata yarinya ce ta bud'e door da alama maid ce, ta gaidashi ta gaidani ta matsa, ya shiga nabi bayanshi, a katon parlour mukayi appearing wanda a kalla yana dauke da set din kujeru guda hudu, girmanshi yafi girman gidanmu, babu kowa a parlourn, na dubeshi, yace,
"Ki zauna...".
Na dubeshi ya nuna min kujera mai daukar mutum biyu, na zauna, yace,
"Bari inje inyi ma aunty tawa magana".
Sai kuma yayi min waving hannu yana murmushi sannan ya juya ya haye stirs, nayi shiru ina kallon parlourn wanda yake kamar a turai, babu abun da babu, wata babie ce ta ajiye min drink mai sanyi da ruwa tareda kayan marmari, nidai kallo daya nayi masu nayi gefe da kaina, Aaryan ne ya sauko tareda zama kusa dani, yana murmushi yace,
"Gata nan saukowa...".
Tuni na d'age niqab dina, nace,
"Ka tashi kadda ta sauko ta ganka kusa dani".
Aaryan ya ware idanu yace,
"Tou miye?".
Wata cute hajiya ce ta sauko daga stirs cikin shiga ta alfarma tana zuba kamshi, tasha gold, tana murmushi ta zauna akan doguwar kujera, Aaryan yace,
"Sai mom...".
Da kamilalliyar muryarta tace,
"Boy gaskiya ka kyauta daka kawo min surukata, Maa shaa Aallah...".
Nayi kasa da kaina nace,
"Ina wuni?".
Tace, "Lafiya lau daughter...".
Aaryan yace, "Baby...".
Mom tace, "Baby kuma? Daughter ya sunanki".
Nace, "Mariam....".
Mom tayi murmushi tace,
"Mairo... Maryamu... Ya Mamanki?".
Nace, "Tana nan lafiya lau".
Mom tace, "Ki sha ruwa...".
Nayi kasa da kaina, Aaryan ya tsiyaya ruwa a glass cup ya mik'o min na kalleshi nayi banza, Mom tace,
"Kyaleshi amsa ki sha... Kai son ka kyaleta ko kuma in koraka...".
Na amshi cup din na kafa lips nasha ruwan kadan sannan na ajiye cup din, Mom tace,
"Tubarkallah boy ka iya zabi... Daughter ya kike?".
Nace, "Lafiya lau... Mun sameku lafiya?".
Tace, "Lafiya lau...".
Wasu yara ne guda biyu mace da namiji suka rugo suka haye Aaryan, da alama jikokinta ne, daya namijin ya dubeni yace,
"Uncle... Who is she?".
Aaryan yace, "She is my fiancé".
Yaron yace, "I like her".
Aaryan yace, "Greet her sultan".
Yaron wanda Aaryan ya kira da sultan yace,
"Ina wuni?".
Nace, "Lafiya lau...".
Itama macen tace,
"Ina wuni?".
Nace, "Lafiya lau...".
Macen tace, "Kina da kyau...".
Nayi murmushi kawai, yaran suka wuce, namijin yana cema macen....
"Sultana tsaya...".
Mom tace, "Daughter zan baki numbata kadda kiji komai idan yayi maki laifi ki kira fad'a min, ni da ummarshi same father same mother muke".
Nayi nodding kai kawai, tace,
"And kadda kiyi hurting dinshi kinji".
Kunya naji sosai, tace,
"Zuciyarshi tana da damuwa... Kici Apple...".
Na girgiza kai, Mom tace,
"Gardama zakiyi...".
Da sauri na dauki apple guda daya na gutsira kawai, ta mik'e ta haye sama, nace,
"Ka tashi muje...".
Aaryan ya mak'e kafad'a ya kira yaran nan sultan da sultana, namijin ya tsaya wurina while macen ta tsaya wurinshi, yaba wata maid wayar tayi mamu snapping pictures, ya amsa ya kashe mamu selfie sannan yayi min, yayi min dasu, pictures din baki daya sunyi kyau, ya jasu suka haye sama, jim kadan ya sauko tareda Mom, da smile tace,
"Aaahhh daughter har zaki wuce, tou na gode ki gaida Mamanki, Aallah ya kiyaye hanya...".
Nace, "Aameen na gode...".
Ta koma sama ya matso kusa dani ya dauki apple guda daya, na tashi yayi gaba ina biye dashi, sultan da sultana suka rakamu har bakin mota, ya bud'e min side din mai zaman hakanan na shiga ya maida murfin ya rufe before ya zagaya bangaren direba, yaron ya lek'o yace,
"Ki k'ara zuwa kinji... Uncle ka k'ara zuwa da ita...".
Suna tsaye suna mamu waving hannu har motar ta fice, nace,
"Mey yasa kayi min haka?".
Yace, "Daga na kaiki kin gaida Aunty na...".
Nayi mashi banza, can nace,
"Tana da kirki, I like her, bata da damuwa".
Yace, "Hakane.... Yanzu kuma wurin Ummana zan kaiki ki gaidata...".
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest doctor and your cold friend, tabbas bashi da damuwa....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 12
Da sauri na dubeshi idanuna a waje, yace,
"Wasa nike maki...".
Na maida lumfashi, yace,
"Matsoraciya...".
Nace, "Nice kai, ai naji komai lokacin da kuka fara zuwa".
Aaryan ya ware idanu na kwashe da dariya, yana parking opposite da gidanmu ya mik'o min wata katuwar leather yace,
"Gashi mom ta baki...".
Na dafe kai, yace,
"Yane...".
Nace, "Ban mata godiya ba".
Yace, "Kawo wayarki in saka maki digit dinta, mantawa tayi bata saka maki ba".
Na zaro expensive android da ya bani na mik'a mashi ya saka min numbarta yayi min saving tareda mik'o min wayar yace,
"Bari in gani miye a ciki...".
Ya bud'e, expensive perfumes ne kala-kala har guda hudu da wani hadaddan expensive less da atamfa super English tareda wasu gown masu tsad'a guda ukku, yace,
"Aahhh gaskiya mom ta kyauta, yanzu wannan less da atamfa zan tafi dasu in kaima tailorn da yake ma twins dinki ya dinka maki".
Ya zarosu ya wulla backseat, nace,
"Na gode...".
Ya d'aura yatsanshi akan lips sannan yace,
"Shhhhh keda kika bani zuciyarki fa?".
Dariya ya bani na amshi leather din tareda b'alle murfin motar na fito ina dariya, na shiga gidanmu na samu babu kowa a tsakar gida na wuce dakina na bud'e akwati na saka leather din kasanshi sannan na rufe, already nayi dropping handbag dina, na zare hijab tareda rage kayan dake jikina na d'aura zani a kirji na fito na bud'e rijiya na jawo ruwa na cika bucket na daukeshi na shiga bayi, tou ina daukar bucket amma bana daukar jarka kwata-kwata, ina fitowa, Ummy tace,
"Baby har kin dawo kenan...".
Nace, "Dawowata kenan na shiga bayi".
Daga nan bata sake cewa komai ba, taja buta ta shiga bayi, saida nayi alwalla sannan na wuce daki, tou an fara kiran sallar magrib, saida nayi sallar isha'i sannan na fito naci abinci nasha ruwa na koma daki ina chatting da Aaryan, bayan wasu mintina mukayi sallama na fito na dauki buta nayi alwalla na k'ara cikata na wuce da ita daki na kwanta.....
Washe gari bani da lectures, da marece bayan nayi wanka na shafa vaseline tareda goge fuskata nayi applying kwalli, wani material na saka dinkin gown ne k'irar bubu, naja dogon gashina wanda idan ya bazo har gwuwata yake wucewa, haka yake, gashi wara-wara kamar rubber, dakyar nayi mashi gammo na d'aura kallabi yayi zororo a baya, nayi rolling veil na dauki poss tareda applying humra na zura takalma flat na fito, Ummy bata a tsakar gida kuma ni bazan iya fad'a mata inda zanje ba don haka na fita kawai ba tareda na fad'a mata ba, bakin titi na tsaya na tare adaidaita na shiga tareda fad'a mashi inda zai kaini, bakin wani katon mansion yayi parking na bashi kudinshi sannan na fito tareda matsawa nayi knocking akan door dake gefen get, wani mutumi ne ya bud'e door din yana kallona, nace,
"Suhail yana ciki...".
Yace, "Ehhh....".
Tareda matsawa na shiga, mansion ne babba, ginin masu kudi da suka amsa sunansu masu kudi, an zuba naira babu k'arya, direct hanyar door nayi na danna bell, suhailat ce ta bud'e door kallona tayi na kalleta sai kuma ta matsa tareda cewa....
"Ashe kece... Shigo... Barka da zuwa...".
Na shiga ta rufe door din tayi gaba, na bita ina k'arewa parlourn kallo, babba ne, komai yaji, abun ba'a cewa komai, ta nuna min kujera na zauna ta kawo min ruwa na dubesu kawai, wasu matan yanzu bakin kishi garesu, tace,
"Ki sha...".
Na girgiza kai kawai, nace,
"Wajan suhail nazo idan yana nan...".
Jim tayi sannan tace,
"Ehhh yana nan...".
Nace, "Wajenshi nazo, please kiyi mashi magana".
Kallona tayi tai jim sai kuma tace,
"Alright then, bari inyi maki magana dashi".
Ta mik'e ta haye sama, jim kadan ya sauko, suhail ne yana sanye da wasu breathtaking jeans da shirt, he look cute more and more, kallo daya nayi mashi na maida idanuna akan expensive android dake hannuna, da smile yace,
"Baby... Yau ina zan saka kaina baby tazo har inda nike, amma kinyi kyau, you look muah, but hala b'atan kai kikayi...".
Nayi mashi banza na kalli suhailat dake tsaye akan stirs, waving hand nayi mata na mik'e tareda wucewa na nufi door, ya biyo bayana, na fice na tsaya a compound ya karaso tareda tsayawa gefena, na had'e hannuwana da alamar bada hakuri sannan da pity face, nace,
"Don Aallah suhail kayi hakuri ka yafe min, ka soni so na gaskiya, ka nuna min so matuk'ar so amma na gujeka, wani lokacin ina making fun of you ne, har kuka kayi min amma na dauki abun wasa, kace kana sona na dauki abun da wasa, saboda kana da kudi ne amma yanzu na gane kuskurena na gane a both masu kudi da talakawa akwai na kirki akwai na banza, wasu ne suke b'atawa wasu suna, na rokeka da girman Aallah kace ka yafe min a bakinka har zuwa zuciyarka...".
Suhail ya kama hannuna yace,
"Baby ni ban tab'a rikeki a raina ba amma tunda so kike ince tou na yafe maki... Naji engagement dinka was called up, sorry... Mariam!".
Yadda ya kira sunana ya saka na kalleshi da sauri, ashe suhailat tana tsaye daga saman bene tana kallonmu, suhail yayi murmushi yace,
"Mariam har yanzu ina sonki... Please kice kina sona, zan aureki...".
Da sauri na fizge hannuna tareda fashewa da kuka nace,
"No... Kayi hakuri lokaci ya kure... No way... I wish ace zan iya maida hannun agogo baya, tou zan karbi soyayyarka kuma in aureka amma yanzu lokaci ya kure, kawai kayi hakuri... Kaji... Don Aallah kayi hakuri...".
Da karfi yace,
"Baby....".
Sai kuma yayi kasa da murya yace,
"Please mana...".
Na girgiza kai tareda fashewa da kuka na durkushe kasa, suhail ya dafe kai yace,
"Baby why!?".
Sai kuma ya duk'e tareda kamoni, na fizge tareda wucewa na bud'e pampo dake gefe can, na wanke fuskata, gani nayi ya mik'o min handkerchief na rufe pampon sannan na amsa na goge fuskata na mik'a mashi nace,
"Na gode daka yafe min...".
Na wuce na barshi tsaye yana kallona, mai guard ya bud'e min door na fita tareda tsayawa bakin titi wanda yake wayam ina jiran kekenapep saidai babu ita babu alamarta, da alama abun hawa yana wahala akan road din....
Yaa Ahmad ne yazo wucewa akan bike dinsa ya hangoni, na zaro idanu, yayi parking gabana yace,
"Ina kika zo?".
Nayi shiru, yace,
"Hau muje...".
Saida gabana ya fad'i na hau ya jashi, akan hanya yana tambayata inda naje nayi shiru, can yayi shiru da alama ranshi ne ya soma b'aci, yana isa kofar gidanmu na sauko na shige ciki, Ummy tace,
"Ke kuma daga ina? Kin barni inata nemanki...".
Nayi shiru, Yaa Ahmad ne ya shigo da bike dinsa, Ummy tace,
"Ohhh ashe tare kuke...".
Yaa Ahmad yayi parking bike dinsa sannan yace,
"Ummy ina tace maki zataje?".
Ummy tace, "Ai ni babu inda tace min zata... Nemanta nayi na rasa...".
Yaa Ahmad yace, "Tou G.R.A na ganta...".
Ummy tayo waje da idanu tace,
"Tou ina taje?".
Yace, "Shine nike tambayarta tayi banza da ni...".
Sai kuma yayo inda nike a fusace, yace,
"Ke ina kikaje...".
Nayi shiru, tou mey zance mashi, ai da ace zan iya fad'i da tun kafin in fita zan sanar da Ummy, a fusace yace,
"Ina kikaje?".
Nayi shiru, yace,
"Tambayarki nike...".
Nayi shiru, kwasheni da mari yayi ya k'ara kwasheni da mari, na fashe da kuka don marukan guda biyu sun shigeni, yace,
"Yanzu fad'a min inda kikaje ko kuma in saka belt in zaneki...".
Nayi mashi shiru, yayi min maganar duniyarnan amma bance komai ba, yayi kwafa sannan yaja bike dinsa ya fita, Ummy tace,
"Maganinki kenan, ai da ya tsaya ya zaneki".
Ta mik'e ta shige dakinta, Ummy bata bugun yaro, tunda na tashi wannan shine karo na farko da aka dokeni a gidan nan, saida nayi kukana na gaji sannan na koma dakina nayi shiru saida na gaji before na mik'e na rage kayan dake jikina na d'aura zani da shirt na fito tsakar gida ina duba note, Yaa Ahmad ne ya shigo yayi parking bike dinsa ya dubeni yace,
"Wato kin san inda kikaje shine ina tambayarki kikayi banza dani kika kyale, don kinga muna nuna maki so shine kike nema ki botsare wato taurin kai, aiko shine zai wahalar dake don bugu yanzu na fara".
Ummy tace, "Ina taje ne?".
Saida ya zauna sannan yace,
"Course mate dinsu wanda yayi aure kwanaki, ashe gidanshi taje amma saboda ta rainani shine ina tambayarta tayi banza da ni...".
Ummy ta girgiza kai sannan tace,
"Baby wannan halin da kika tsurowa kanki ba hali bane, ace ki shirya kiyi tafiyarki ba tareda kin ce dani ga inda zaki ba...".
Kamar zata sake magana sai kuma ta kad'a kai tayi shiru kawai, washe gari tunda safe na shirya na wuce school, bayan kwana biyu ina chatting da Aaryan shine yake cemin shi so yake ya ganni kawai, ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi gabana, karanta nayi amma naqi tura reply, ya kara magana *_am serious gobe in shaa Aallahu zanzo_* na k'ara karantawa naqi reply, ya k'ara turo wani *_Baby kin karanta amma babu reply_* shima na karanta amma babu reply, ya turo min alamar kuka na kunshe dariya shima nayi the same, can sai ga call dinshi ya shigo, dama don ya kira nayi mashi haka, nayi picking da murmushi akan fuskata, daga daya bangaren cikin husky voice dinsa mai sanyi yace,
"Assalamu Alaiki...".
Saida na saki murmushi sannan nace,
"Wa-alaikas-salam...".
Saida yaja lumfashi sannan yace,
"Shine ina magana kika shareni...".
Na kwashe da dariya sannan nace,
"Aaahhh muryarka nike son inji shiyasa".
Aaryan ya saki murmushi har ina jinsa sannan yace,
"Aaahhh indai wannan ne kin tara kin samu amma kadda ki manta gobe in shaa Aallahu ina nan zuwa, so nike kawai in ganki...".
Nace, "Aallah ya kawoka lafiya...".
Yace, "Aameen....".
Ji nayi yayi hanging call din, da mamaki na kalli expensive android din, wai ashe komawa yayi akan what's app yayi recording muryarsa yayi min sending, ban tab'a sanin expert ne akan kalaman soyayya ba sai a lokacin, ina sauraron recording din bacci yayi awon gaba dani....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest Fateema and Fateema, aw Fateema and Teema, wish you all the best....*
*Hope kayi sallah lafiya Abbas Abubakar, wish you all the best... Lemme see idan zan iya guessing daya sunan, uhmm, kai no aw uhmm, a'a ba haka bane, tou na gaza tunawa, hhhh lols....*
Page. 13
Washe gari wurin karfe biyu na mik'e na jawo ruwa na cika bucket na shiga bayi na durje jikina sosai sannan na fito na shiga dakina na zauna kamar wacce zata shafe fiye da hour biyu tana applying make-up amma vaseline kawai na shafa na goge fuskata nayi applying powder sannan nayi applying kwalli, wata cute gown na zaro daga akwatina tana kyau, wata sallah ce har na fidda rai da zan saka kayan sallah saboda lokacin Abba bai d'ad'e da yi mamu registration ba, ba ya da kudi, ya buga gabas ya buga yamma amma ba shi da kudin da zaiyi min kayan sallah, ni har na hakura, ranar daren sallah ina zaune brothers dina maza suka kawo min, wai ashe suna tara kudi shine suka sayi wani farin yard mai cute pattern suka dinka babu surfani babu komai, ni kuma suka siya min ita, gown din tana da kyau, hawa biyu ce, ta kasan tana da circle neck sannan rufe take with yard marar pattern marar design while ta saman take a bud'e kamar after dress tana da madauri sannan kuma tana da pattern, wow, so cute, indeed tana da kyau, zurata nayi tayi matuk'ar suiting dina, na samu dakyar na tattara gashina nayi mashi gammo na d'aura kallabi sannan nayi rolling veil, Maa shaa Aallah nayi matuk'ar kyau more and more, wayata ce tayi haske, tou kullum silent take, na jawota tareda picking na kanga a kunnena....
"Assalamu alaiki wa rahamatullahi wabarakatuhu...".
Saida na saki murmushi before na amsa....
"Wa-ailaikas-salamu wa rahamatullahi wabarakatuhu...".
Daga daya bangaren Aaryan yace,
"Guess what?".
Nace, "Kana kofar gidanmu...".
Yace, "Tou fito in ganki heartbeat...".
Yayi hanging call din, saida na bud'e akwati na zaro diamond ring da ya bani na saka a yatsana kuma yayi suiting dina sosai, tou na zura takalma flat, ba ni saka takalma masu tsini, ina da tsayi duk da ni ba doguwa bace hakanan ni ba gajera bace sannan babu wanda zai kalleni yace min tsaka-tsakiya, kawai dai ina da tsayi daidai nawa wanda yayi suiting structure dina, indai diri ne ni kaina nasan both front and back ba ni da damuwa, komai yaji, kirjina a cike yake hakanan ina da kugu, sometime idan ban saka hijab ba sai a rink'a cewa ina tafiya kamar wata model, hakane kuma, fitowa nayi tsakar gida na fice waje na hangoshi yana jingine da wata expensive car wadda koda sunanta ban sani ba, yana jifata da murmushi har cute dimple dake mak'ale a both cheeks dinsa sukayi appearing, yana sanye da brown kaftani wanda yayi suiting dinsa, cute qube, expensive wristwatch, expensive shoes, wow I feel in sureshi in zura a bag kadda sauran mata su kalle min abuna, lol, na karasa gefenshi ina taking steps sannu a hankali tareda dropping kowace kafa a inda na sauke dayar, na tsaya gefenshi da murmushi nace,
"Ina wuni?".
Da murmushi akan fuskarsa yace,
"Lafiya lau baby...".
Sai kuma ya ware idanu yace,
"Baby amma kinyi kyau you look....".
Sai kuma yayi sauri yasa hannu ya rufe bakinsa yana kallona kamar yadda yara sukeyi inda aka yi manya-manyan ashar a gabansu, na saka dariya, ina kare bakina ina dariya more and more, ya bani dariya har na kasa dainawa, the more nike dariya the more nike k'ara kyau abuna, ya zuba min idanu ba ya koda blinking idanu, ashe ban sani ba video yake daukata, ina lura na juya baya da sauri nace,
"Mey haka? Are you silly? Idan banyi kyau ba...".
Idanunsa a kaina ya bud'e lips a hankali yace,
"Ai kinyi kyau na gani, thanks for making my day koda yanzu na tafi kin bani farin ciki".
Na bud'e baki kenan zanyi magana wata zawara er makotanmu tayi appearing, ai dama na sani idanun magulmata suna a kai kuma basu isa su hanani in tsaya da wanda nike so ba, kallonta nayi tace,
"Aaahhh baby kece da Mahmud?".
Na saki murmushi nace,
"A'a... A'a... Ba shi bane, wannan mai kudin ne, d'an handsome, kin ganshi dai ga hali ga kyau ga kudi ga ilimi ga iya wanka, daidai ni kenan, tou waye ba ya san d'ad'i, ai kowa yana san inda zai huta...".
Ina sane na yab'a mata magana, wai ita uwar gulma, tou ai ga ribar gulma nan ta samu....
Da sauri tace,
"Ehhh... Ehhh... Hakane... Hakane...".
Ta wuce, akwai wata er uwarsu Mahmud dake aure a unguwarnan, nan kusa damu ne....
Aaryan ya kalleni nace,
"Kayi kyau...".
Yace, "Mey yasa kikayi mata haka?".
Nace, "Ina sane nayi mata haka, gulma ce ta kawota kuma ta samu ribar gulma, ai tasan kaine amma don gulma tazo tana fad'in sunan wani, ai nice maganinta".
Aaryan ya ware idanu yace,
"Da alama baby bata daukar raini...".
Na kalli gefe ina dariya, ya bud'e backseat ya zaro leather ya mik'o min, na kalleshi yace,
"Dinkin kine ki kaishi gida ki dawo...".
Na kalleshi yayi nodding head, na amsa tareda mashi waving hannu ina smile sannan na juya na shige gidanmu, na fad'a dakina, koda kalar style din ban gani ba, na bud'e akwati na tura leather din kasan akwatina, na rufe na fito tunda na fito yake kallona har na karasa gefenshi, ya kalli kaina da yayi zororo a baya, nace,
"Ba kofi bane, gashi ne, ina shan wahala before inyi mashi gammo...".
Yace, "Ai na gani a hotunanki dake cikin wayata".
Nayi murmushi, yace,
"Cheese...".
Ya d'aga wayarshi ya kashe mamu selfie, na lura yana san daukarmu selfie, yace,
"Ina son hotunanki suyi yawa a wayata kamar na Aalima, am still missing her, I love her and I love you either...".
Saida gabana ya yanke ya fad'i na kalleshi da sauri, duk lokacin da ya ambaci sunanta ko kuma naga hotonta sai gabana ya yanke ya fad'i, yace,
"Kin ganta?".
Na girgiza kai, yace,
"Har yanzu raina yana bani tana raye...".
Nayi nodding kai kawai, yace,
"Aallah ya bayyanata...".
Nace, "Aameen...".
Yace, "Kin san mey?".
Nace, "A'a...".
Saida yayi jim sannan yace,
"I love you...".
Na kalli gefe ina murmushi, yace,
"I like the way you smile...".
Nayi murmushi, yace,
"Baby zoben yayi kyau a hannunki kamar saboda ke aka yi shi...".
Nayi murmushi nace,
"Na gode...".
Ya jima sannan ya tafi na koma gida na tadda Ummy zaune akan tabarma bance da ita komai ba na shige daki....
Rayuwa sabuwa, adadin yadda nike tare da Aaryan shine adadin yadda nike jin sonshi yana k'ara shiga zuciyata...
Again washe gari ina zaune ya kirani in shirya yana akan hanya zaizo ya ganni, a gurguje na jawo ruwa na cika bucket na wuce dashi bayi nayi wanka na fito, saukina bana b'ata lokaci wurin kwalliya, as usual vaseline na shafa na goge fuskata nayi applying powder before nayi applying kwalli, lifaya na dauka na nade jikina da ita kuma tayi suiting dina tayi min kyau sosai, ita kuma Yaa Mustapha ne ya siya min ita, wayata ce tayi haske saida na zurata a bag sannan nayi applying humra na zura takalma mara tsini before na fita na fice waje, Aaryan ne yana jingine da mota yana murmushi, sannu a hankali nayi taking steps zuwa inda yake na tsaya gefenshi, yace,
"Kinyi kyau...".
Nace, "Kasan mey?".
Yace, "Kina sona...".
Na ware idanu nace,
"Amma ya aka yi ka gane abun dake zuciyata?".
Aaryan yayi smile before yace,
"Zuciyarki tawa ce, zuciyata taki ce, shiyasa...".
Sai kuma yayi dariya, na kalleshi wata expensive shadda ce a jikinsa yana zuba kamshi as usual, yace,
"Kin san mey?".
A tare muka ce,
"I love you....".
Sai kuma mukayi dariya, yace,
"Ya su Ummy?".
Nace, "Suna nan lafiya lau... Ya mom?".
Yace, "Tana nan lafiya lau...".
Yace, "Kin ganni na dawo ko?".
Nace, "Ai ka kyauta tunda kazo na ganka naji muryarka mai d'ad'i...".
Kekenapep ce ta parker Nadiya ce ta fito tana dauke da d'anta Najib, na kalleta nace,
"Ita ce Nadiya... K'anwata...".
Aaryan ya ware idanu, ta saka niqab ne shiyasa ba'a hango fuskarta, na karasa wurinta na amshi Najib muka shiga ciki, ta zube akan tabarma kusa da Ummy tareda gaidata na mik'a mata Najib nace,
"Amsa kinga na baro mutum a waje...".
Nadiya ta amshi Najib, Affan ne ya mak'ale min yana neman fasa kuka dole na daukeshi na fita, yana kallon Aaryan amma yaqi yarda ya daukeshi, Aaryan yace,
"Yau sai na daukeshi...".
Nace, "Tab aiko kana da babban aiki indai Affan kake nufi, wannan ba ya yarda da bakuwar fuska, kaci sa'a idan ya ganka ba ya fasa kuka...".
Aaryan yayi murmushi sannan yace,
"Maida shi ki dauko daya yaron...".
Na kalleshi sannan na juya na koma ciki na tadda Nadiya da Ummy suna magana amma suna ganina sukayi shiru, wannan ya tabbatar min da maganar Mahmud sukeyi, na ajiye Affan na dauki Najib na juya na fice, da smile Aaryan ya mik'o hannu babu gardama Najib yaje, yace,
"Then koma ki dauko Affan...".
Saida na kalleshi sannan na juya na koma ciki na dauko Affan na dawo, yace,
"Bari kiga...".
Sai kuma ya soma yima Najib wasa shi kuma yaron yana wangale baki suna dariya, idanun Affan suna a kai, mik'o hannu yayi abun mamaki sai naga Affan ya mik'a hannu ya yarda Aaryan ya daukeshi, na ware idanu nayi mamaki sosai don Mahmud duk dadewar da mukayi Affan bai yarda ya daukeshi, in fact idan ya ganshi kuka yake, wannan abun da mamaki yake, Aaryan yace,
"Kin gani, dama na fad'a maki...".
Da mamaki na amshi Najib na juya na maidashi gida, Nadiya tace,
"Ina Affan?".
Nace, "Yana hannunshi...".
Da mamaki tace,
"Kuma ya yarda...".
Nace, "Ehhh nima nayi mamaki...".
Na mik'a mata Najib na juya naci karo da Yaa Ahmad na kalleshi saidai bance komai ba, nayi crossing dinshi na fice, Aaryan yace,
"Baby ya kikaga, kinga ya yarda dani...".
Nace, "Ai ya kyauta...".
Yace, "Tafiya zanyi kuma ya kamata in gaisa da Nadiya".
Nace, "Indai wannan ne baka da damuwa...".
Na juya na koma ina dosar tsakar gida naji Nadiya tana cewa *_Mahmud_* saidai tana ganina tayi shiru, nace,
"Nadiya zo ki ji...".
Nadiya tace, "Ni kuma?".
Nace, "Kedai zo ki ji amma fara maida hijab dinki".
Nadiya ta saka hijab na rik'o hannunta muka shiga soron gidanmu, nace,
"Gaisawa zakuyi...".
Na jata waje muka karasa inda yake, nace,
"Aaryan ga Nadiya na kawo maka...".
Yace, "Kin kyauta heartbeat... K'anwarmu ya kike, ya baby?".
Tace, "Lafiya lau...".
Yace, "Ya mai gidan?".
Tace, "Lafiya lau yake...".
Yace, "Sunana Aaryan ina matuk'ar son sister dinki sosai da sosai, irin more and more din nan, I thought ku twins ne amma sai tace k'anwarta ce... Kuna kama sosai kamar tagwaye...".
Nadiya tayi nodding head kawai ya bata kudi amma bata amsa ba, ta juya ta shige gida, tana shiga gida Abba ya shigo santar akan bike dinsa, idanunsa suna a kaina, saida gabana ya yanke ya fad'i, nayi tsuru-tsuru, yayi crossing dinmu ya shige gida, nace,
"Aaryan... Abba ya dawo... Na tafi...".
Na amshi Affan na juya na shige gidanmu, saidai Abba baice dani komai ba, ina zaune daki Ummy ta d'aga labule tareda mik'o min en dubu-dubu, na mik'e na amsa sannan na dubeta da mamaki nace,
"Na miye?".
Tace, "A aljihun Affan na gansu".
Nace, "Na shi ne, ina jin Aaryan ne ya saka mashi, tabbas shine ya saka mashi kudin...".
Ummy tayi min shiru ta wuce ta barni tsaye, na durkushe kasa tareda dafe kaina, nace,
"Ummy NI *BA NI DA LAIFI* sam".
I feel in fashe da kuka....
Ranar Monday mun fito daga lecture, ni da Jalila muna zaune a bus stop, Jalila ta dubeni tace,
"Baby ina san ki rabu da Aaryan...".
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest kamal gombe, wish you all the best....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 14
Da mamaki na dubeta tace,
"Ehhh ki rabu dashi ko kuma nan gaba kizo kina nadama, nace ki rabu dashi ne saboda ina sanki bana san ki shiga damuwa...".
Ta sakani a duhu sosai, nayi jim sannan nace,
"Yana da damuwa ne wadda sai yanzu kika santa?".
Jalila ta girgiza kai sannan tace,
"A'a... Aaryan baida damuwa, yana da hali mai kyau, amma idan kika cigaba da kulashi kina sakashi a damuwa ne, kawai ki rabu dashi, kiyi yadda nace, kin san bazan sakaki a damuwa ba...".
Wani kallo nayi mata nace,
"Banda na sanki nasan halinki da sai ince bakin ciki kikeyi min amma nasan wannan ba halinki bane, ba zakiyi haka ba, sam".
Jalila tace, "Baby bana so nan gaba kizo kina nadama shiyasa nace maki ki rabu da Aaryan...".
Nace, "Kinyi magana da Suhail kenan".
Jalila tace, "Ni banyi magana dashi ba, kuma ba saboda shi bane...".
Nayi shiru kawai na kyaleta tace,
"Baby...".
Nace, "Don Aallah kiyi shiru ki kyaleni I have heard enough...".
Ta b'ata min rai fiye da tunani amma babu abun da zai sauya a k'awancenmu, na zaro wayata na hau what's app, gani nayi wata er course dinmu ta shiga group tana tambayar gaskiya akan called up din engagement dina da take jin rad'e-rad'in anyi, bindawa ta tabbatar mata da hakane amma sai Jalila tace mata ta bita private taji, sai daga baya ta dawo group tace *_oohhh ashe haka abun yake_* Jalila tace *_hakane_* tab'e baki nayi ban sake mata magana ba har muka hau bus, har na koma gida ina mamakin abun da Jalila tayi min....
Washe gari ina zaune Aaryan ya kirani, picking nayi yace,
"Ki fito yanzu ina kofar gidanku".
Sai kuma yayi hanging call din, da mamaki nike kallon wayar, na mik'e tareda zura long hijab na duba fuskata sannan na zura takalma na fice, ina fita waje ya fito daga motarsa, kallo daya nayi mashi na gane yana cikin damuwa, na tsaya gefenshi, yace,
"Baby kinyi fad'a da Jalila ne?".
Da mamaki nace,
"A'a... Wani abu tace maka?".
Da damuwa yace,
"Cewa tayi in rabu dake bata son in shiga cikin damuwa, na tambayeta idan kina da wani hali na banza ne amma tace a'a baki da damuwa ko kadan".
Na girgiza kai nace,
"Nima haka tace min jiya amma ka rabu da ita kawai...".
Yace, "Baby na tsorata, bana fatan in rasaki heartbeat...".
Ya jima sannan ya tafi while na juya na koma gida, ina shiga daki na jawo wayata na dannawa Jalila call tana picking nace,
"Kin kyauta...".
Daga daya bangaren Jalila tace,
"Baby bana san ku shiga damuwa ne shiyasa, yanzu kam ya rage maki ne ki rabu dashi ki tsallake abun da nike gudu ko kuma ki cigaba da kulashi nan gaba kizo kina nadama".
Tayi hanging call din, nayi jim sai kuma na share koma miye ita ta sani....
Washe gari ina daga daki naji Yaa Ahmad yana fadawa Ummy jiya Mahmud suma ya rinkayi, da yayi wata doguwar suma anyi tunanin ya mutu ne ashe da sauran lumfashinsa, amma yanzu gab zuciyarshi take da bugawa, I feel babu dadi amma babu yadda zanyi sam *BA NI DA LAIFI* saidai nasan kowa haushina yake ji suna ganin laifina, tou daga wannan lokacin ban k'ara jin wani ya kira sunan *Mahmud* a gidan ba....
Bayan kwana biyu ina zaune a daki sai ga kiranshi, yace,
"Ki fito ina kofar gidanku...".
Nace, "Mey?".
Yace, "Yeah ina kofar gidanku".
Nace, "Shine kake zuwa baka fad'a min ballantana inyi maka kwalliya".
Ina ji saida ya saki murmushi sannan yace,
"Surprise ne shiyasa... Guess what?".
Nayi mashi shiru tareda hanging call din na fizgo hijab na zura koda fuskata ban duba ba, na zura takalma na fice, ina fitowa ya fito daga mota yana smile, Jeep ce baka, mai kyau, daga gani tana da tsada, na jingina da ita tareda bashi baya wai nayi fushi, ya zagayo inda nike tareda had'a hannuwa alamar bada hakuri sai kuma ya ware idanu yace,
"Kinga fuskarki kuwa...".
Na zaro idanu tareda jawo hijab ina goge fuskata, ya mik'o min wayarshi na duba fuskata naga babu komai, na kalleshi na turo baki nace,
"Please miye ka gani a fuskata...".
Shima Aaryan ya turo baki kamar yadda nayi yace,
"Sirri......".
Na shagwab'e fuska, ya kwashe da dariya, nace,
"Miye?".
Yace, "Wasa nike maki, babu komai akan fuskarki...".
Nayi mashi wani kallo, yace,
"Surprise... Juya ki gani...".
Ya juya tareda knocking akan glass, wata cute babie mai kama dashi ce ta fito daga side din mai zaman hakanan sannan wata mai kama da ita sak ta fito daga backseat, twins ne, Adila da Adla, kowacensu tana murmushi, murmushi nayi na dubeshi yace,
"Surprise, kawo maki su nayi suyi maki wuni...".
Wani expensive less ne suke sanye dashi, komai nasu iri daya, hatta handbag, heel shoes, jeweleries, veil duk iri daya ne, murmushi na saki nace,
"Aaahhh... Adila... Adla... Sannunku da zuwa... Amma na gode da wannan surprise heartbeat...".
Aaryan yayi murmushi tareda waving min hannu yace,
"I love you... Bye... Take care...".
Sai kuma ya dubi tagwayen yace,
"Idan kun gama ku kira direba yazo ya daukeku...".
Ya shiga mota ya jata, en gulma idanunsu suna a kai, na jasu muka shiga ciki, Ummy tana zaune tsakar gida, suka gaidata ta amsa tana kallonsu nasan taga kama, na jasu dakina suka zauna na d'age masu labule saboda ana zafi, na kawo masu fan tareda zama nace,
"Sannunku da zuwa amma naji dadin zuwanku, kun kyauta, nasan twins ne saidai ban san wacece Adila ba, wacece Adla...".
Sukayi dariya ta kusa dani tace,
"Nice Adla...".
D'ayar tace, "Ni kuma Adila...".
Nace, "Bari in kawo maku ruwa...".
Adila tayi murmushi tace,
"A'a mun hutar dake, da ruwanmu a bag, ai ba zamu wahalar da babyn broz ba".
Nace, "Kunzo lafiya?".
"Lafiya lau...".
"Ya su Umma da Mom?".
"Suna nan lafiya lau...".
Nace, "Gaskiya kuna kama dashi sosai...".
Suka saki murmushi, nace,
"Ga shi bai fad'a min zuwanku ba ballantana in tanadar maku da wani abu amma akwai tuwo, hope zaku ci".
Adila tace, "Zan ci...".
Adla tace, "Nima zanci amma idan miyar kuka ce...".
Nace, "Baki da damuwa itace, ai koda ba ita bace na shiga kitchen in kad'a maki...".
Na mik'e naje na zubo masu na had'o masu da spoon saida na shiga makotanmu na sawo man shanu na zuba masu a miyar sannan na kai masu, bowl din da miya take daban wanda tuwo yake daban, suka ci abunsu, Adila tace,
"Ruwa...".
Na dauko masu buta suka fita suka kuskure bakinsu suka koma daki kowace ta fiddo rubbar swan daga bag ta kafa lips, naji dadin zuwansu, muka sha hira, suna da kirki, basu da damuwa, har kayan da Mom ta bani na dauko masu suka gani, sun yaba, farat daya naji sun shiga raina, na rasa abun da zan basu, wani d'an karamin kit Adila ta zaro daga bag ta bud'e, wow sakar ce mai kyau daga gani zatayi tsada, tace,
"Da mukaje Dubai tareda Umma muka sawo maki ita...".
Adla tace, "Kuma zatayi maki kyau".
Na amsa nace,
"Kai amma sunyi kyau, na gode sosai".
Adila tace, "Saka mu gani...".
Na saka kuma tayi min kyau na cire na maida, har hotuna mukayi, nayi excusing kaina na shiga makotanmu nayi amfani da kudin da Aaryan yaba Affan wadanda Ummy ta maido min, na siya masu kayan snack tare dasu aya mai suger, gyad'a da sauran kayan makulashe, na basu aiko sunji d'ad'i, suka kira direba koda yazo call ya danno ya sanar dasu, Adila tace,
"Kinga direba yazo... Yauwa don Aallah Aunty ki kula mamu da broz kinga tunda Aalima ta b'ace yake cikin damuwa saida ya hadu dake sannan walwalarshi ta dawo...".
Saida gabana ya fad'i, tace,
"Broz yana da damuwa, abu kadan zai iya sakawa zuciyarshi ta buga...".
Adla tace, "Please ki tayamu tattalinshi, shi kadai garemu...".
Nace, "Kadda ku damu...".
Suka yafa veil suka dauki bag tareda leather da na basu, muka fito sukayi ma Ummy sallama na rakasu har wurin mota suka shiga saida naga tafiyarsu sannan na juya na koma gida....
Washe gari ina zaune hakanan a daki na jawo wayata na kira Aaryan, yayi picking mukayi exchanging sallama and greeting, yace,
"Baby you called me, na gode...".
Nace, "Baby I miss you...".
Saida yayi dariya sannan yace,
"Nine baby kuma?".
Nace, "Ehhh mana... Kaga kai baby nima baby mun koma babies...".
Daga daya bangaren Aaryan yayi dariya sannan yace,
"Baby kin san mey? I love you...".
Sai kuma naji wayar tayi dif ina magana babu respond, kuma bata tsinke ba....
Abba ne naji yana kirana....
"Mariam...".
Saida gabana ya yanke ya fad'i na mik'e tareda tura wayar a bag sannan na fito, shi da Ummy ne zaune akan tabarma na durkusa a gefensu, Abba ya dubeni yace,
"Mariam maganar aurenki da Mahmud tana nan babu abun da ya sauya, lokacin da kika sameni da maganar kin fasa aurenshi na fad'i maki ne kawai shima na fad'i mashi maganar aure sai idan kun daidaita kanku amma na fad'i ma waliyanshi maganar aure tana nan babu fashi, tabbas nasan Mahmud nasan halinshi abun da ya faru can tsakaninku ne, ni miji na gari nike nema maki kuma Mahmud ya cika miji na gari, ina gani bazan bari ki rasa wannan mijin ba, kuma ina gani bazan bari ya rasa ranshi saboda ke ba, Mahmud yaron kirki ne, before sai kin gama bautar kasa sannan za'ayi auren amma yanzu kina gama karatu za'ayi...".
Tunda ya fara magana naji jikina ya zama very weak, mik'ewa nayi na tafi luu, next duhu ne, daga nan ban kuma sanin abun da ya faru ba, saidai bud'e idanuna nayi na ganni akan gado a asibiti....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest babies, tou ina nufin wadanda ake kira baby, ehe, tou wish you all the best....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 15
Na d'aga idanu Ummy na gani then Yaa Ahmad da Nadiya, fashewa nayi da kuka, suna min magana amma nayi shiru sai idanu kawai, Ummy ce fita jim kadan ta dawo tareda likita, dakyar ya samu nayi shiru ya dubani ya fita saidai kafafuna rawa suke koda mik'ewa bana iyawa, cire min drip aka yi, tou daga zaune nayi alwalla na rama sallolin da ake bina ashe kwana nayi, aka bani abinci naci sannan na koma na kwanta ina hawaye, Yaa Ahmad ne ya mik'o min wayarsa, Yaa Ayan ne akan layi, na amsa tareda fashewa da kuka, daga daya bangaren Yaa Ayan yace,
"Baby yi shiru zamuyi magana...".
Cikin kuka nace,
"Kana ji Abba yace dole sai na auri Mahmud, ni kuma Aaryan nike so and kasan Aaryan kasan halinshi tunda na bashi numbarka har gaisawa kuke, Yaa Ayan ka taimaka min ni bazan auri makaryaci ba... Tabbas shi makaryaci ne...".
Daga daya bangaren Ayan yace,
"Baby nayi magana da Abba amma ya nuna min ya riga ya yanke hukunci, bai damu ba koda zaki mutu bayan an daura auran...".
Na fashe da kuka nace,
"Aaryan fa?".
Yace, "Kece ya kamata ki fad'a mashi komai, kiyi hakuri ki rage damuwa muna sonki...".
Nace, "Ni sunfi sonshi dani kawai...".
Nayi hanging call din, na danna digit din Jalila da yake ina da digit dinta of head, tana picking na fashe da kuka tace,
"Jiya nazo baki farka ba...".
Nace, "Jalila... Abba yace dole sai na auri Mahmud ni kuma Aaryan nike so...".
Daga daya bangaren Jalila tace,
"Wannan magana ce wadda na riga na santa tuntuni, Abba ya hada ni da Yaa Ahmad ya fad'a mamu maganar aure tana nan amma ba yaso keda Mahmud ku sani, yace muje mu cigaba da shirye-shiryen biki a madadinku shiyasa nace maki ki rabu da Aaryan amma kikayi watsi dani, daman wannan ne abun da nike guje maki, kinga yanzu dole ki bi umarnin mahaifinki sannan babu damar ki rabu da Aaryan farat daya, dole ki cigaba da kulashi saboda yana da damuwa a zuciyarshi, idan kika rabu dashi lokaci guda zai iya rasa ranshi, yanzu ina school amma idan na fito zan biyo in dubaki...".
Na mik'a mashi wayarshi tareda fashewa da kuka, wannan wacce irin rayuwa ce, babu wanda na sake yi ma magana, da da marece Jalila ta shigo ta jima sannan ta wuce, mutane suna zuwa dubani saidai wasu gulma ce take kawosu musamman en unguwarmu, tou en course dinmu sunzo dubani har da suhail, Yaa Mustapha saidai kira yayi aka bani yayi min ya jiki na fasa mashi kuka, shima cewa yayi inyi hakuri babu yadda zaiyi, tashin hankalina ban san halin da Aaryan yake ciki ba, yau kwanana ukku a asibiti saidai har zuwa yanzu babu wani cigaba saboda naqi kwantar da hankalina kullum cikin damuwa nike, Ummy ce take jinyata amma Abba yana zuwa kullum hakanan Yaa Ahmad da Nadiya....
Ummy ta fita ne, motsi naji na juyo Mahmud ne tsaye, wani kallo nayi mashi na juya mashi baya, yayi taking steps tareda tsayawa bayana yace,
"Baby why?".
Sai kuma yace,
"Ke haka za'ayi auren ina maki magana kina banza dani...".
A fusace na juyo tareda durowa daga saman gadon na nunashi cike da tsiwa nace,
"Get out... You speak hausa... Right? Tou ka fita nace...".
Mahmud ya ware idanu yace,
"Baby baki iya tsayuwa amma yanzu kin tsaya akan kafafunki, ashe nine maganin...".
Wani kallo nayi mashi, Ummy ce ta shigo ta kalleni ta kalleshi, na juya tareda komawa akan gado na kwanta tareda rufe idanuna, ko fita Ummy tayi nidai ban sani ba, yazo yana min magana nayi banza dashi, ni ban san lokacin da ya tafi ba don bacci ne yayi awon gaba dani....
Washe gari aka yi discharging dina, Ummy ta tattara komatsanmu muka wuce gida a kekenapep, wanka nayi na wuce dakina na kwanta, magulmata suna ta shigowa, tou gulma suzo suga yadda nike a samu na fad'i, handbag na jawo na zaro wayata na duba abun mamaki na tarar da miss call da yawa amma babu na Aaryan hakanan bai turo min message ba, na duba what's app na samu ya jima ba ya online, Ummy ce ta lek'o tace,
"Ki zo inji Abbanku...".
Wayata dake bayana na kalla sannan na dauketa na zura a handbag na mik'e na fice na sameshi a dakinshi na durkushe kasa nayi shiru, yace,
"Mariam dole ki auri Mahmud koda zaki mutu, ehhh na yarda a dalilin wannan auren ki mutu, wanda kike gudu yafi wanda kike kuka a kanshi, ai shi Mahmud da ya ganki ni ya fara zuwa ya tuntuba da zancen sannan ya fara zuwa wurinki amma shi wancen fa, saidai yazo ya kiraki ki fita amma babu wanda ya tuntuba ya nemi izini, ni bazan hanaki kuka ba idan kika tashi kiyi na jini, idan kika tashi ki suma sai in daukeki a wuce dake asibiti amma wannan auren baki isa ki tsaidashi ba...".
I feel in sanar dashi gaskiya akan nice na hana Aaryan ya gabatar da kanshi amma no point tunda yace koda zan mutu sai na auri Mahmud kuma na sanshi nasan halinshi idan yace ehh ko a'a babu mai sauyashi sai ikon Aallah, tashi nayi na wuce, ranar wuni nayi a daki ina kuka, na kwana ina kuka, bayan nayi sallar subh na koma bacci nice ban farka ba sai wurin karfe sha biyu na rana, na dafe kaina da yake min wani azababben ciwo, na mik'e na fito tsakar gida na dauki bucket na wuce bayi nayi wanka na fito tareda komawa dakina, na jima before nayi kalaci....
Washe gari da rana ina zaune Yaa Ahmad ya shigo yace,
"Ki shirya yanzu Mahmud zaizo wurinki...".
Nayi shiru ban motsa ba, can wani yaro ya shigo yace,
"Ance baby tazo...".
Nayi shiru, Ummy tace,
"Je ka ce gata nan...".
Yaron ya juya ya fice, mik'ewa nayi na zura takalma na jawo long hijab daga saman door na zura na fice, Mahmud ne yana jingine da wata bak'ar mota kirar Benz, shadda ce a jikinsa wadda tasha aikin hannu, komai na jikinsa expensive ne, tab'e baki nayi na karasa tareda kallonshi, ya saki murmushi yace,
"Ya kike...".
Nace, "Ai kana da idanu ko ka ganni a gutsire ne, I don't think I look somehow bad...".
Mahmud ya girgiza kai, nace,
"Ashe kasan amsar....".
Yace, "Ohhh baby rigima...".
Nace, "Ohhh kai kuma k'arya ba...".
Mahmud ya rik'e hab'a yana dariya, yace,
"Relax mana baby, baki son mai guard, na daina guard nayi kudi, kawuna yayi min wankan talauci, ai kin ganni...".
Nace, "A banza aikin banza katoton zero a gaban decimal point ai bashshi da amfani...".
Na zaro baby Nokia dake kuguna yasa hannu ya wafceta yace,
"Zan siya maki expensive waya... iPhone 7plus kike so ko kuma iPhone 8...".
Wani kallo nayi mashi, haushi ya bani, nace,
"Ai ni ba mayyar kudi bace, abun duniya ba ya gabana, koda arzikin duniya zaka bani ba amsa zanyi ba, zan iya tafiya...".
Mahmud ya ware idanu yace,
"A'a ai zance nazo, kin manta ne...".
Nayi banza dashi, wata expensive Jeep ce tayi parking kallo daya nayi mata na gane ta Aaryan ce, taking steps nayi zuwa inda motar take na bud'e front seat na shiga na rufo na dubeshi kuka yake saida gabana ya yanke ya fad'i, I thought yaji komai ne, nace,
"Kayi hakuri kaddara ce...".
Aaryan yana kuka at the same time yana smile, yace,
"Kukan murna ne, Aallah ya bayyanar mamu da Aalima, yanzu haka tana gidanmu, naji dadi ki tayani murna, I love her and I love you zan aureku baki daya...".
Da sauri nace,
"No... Aaryan kayi hakuri akwai damuwa... Aurenmu bazai yiyu ba...".
Da mamaki yake kallona, yace,
"Baki son kishiya ne?".
Nace, "Itama kishiyar damuwa ce, opposite da gidanmu mata biyu ne daya tana da hakuri da kauda kai shiyasa suke zaune lafiya, nan kuwa kusa da gidanmu kowace bata da hakuri sune kullum cikin fad'a...".
Kallona yayi sai kuma yaja motar yayi reverse yayi gaba da ita, da mamaki nike kallonshi saidai ban ce komai ba, gudu yake sosai, ya tsaya a bakin wani katon get yayi horn aka wangame mashi get ya shiga tareda parker motar, ya bud'e ya fice ba tareda yace dani komai ba, ina gani akan idona ya shiga ciki ya barni ni daya a mota, can ya fito tareda wata babie, Aalima ce saida gabana ya yanke ya fad'i ganinsu tare, wannan ya tabbatar min da gidansu ya kawoni, a jere suka tafo ta bud'e side din da nike na fito ya juya ya koma ciki, Aalima ta dubeni da damuwa sai kuma ta had'e hannayenta alamar rik'o, tace,
"Don Aallah baby kadda kiyi mamu haka, Yaa Aaryan yana matuk'ar sonki kuma yana da matsalar zuciya idan kika rabu dashi zamu iya rasashi, zan iya hakura dashi in bar maki saidai nima yana matuk'ar sona, yace kince baki son kishiya, damuwa ce, tashin hankali ake, tou ni naji zan rink'a hakuri ina kauda kai kinga shikenan za'a zauna lafiya...".
Da sauri nace,
"A'a baki gane bane, akwai damuwa, aure na da shi bazai yiyu ba saboda...".
Muryar twins naji daga bayana suna fadin....
"Ga Aunty Mariam... Ga Aunty Mariam... Sannunki da zuwa... Zo mu je wurin Umma...".
Suka jani har parlour inda wata cute mata mai kama dasu take kishingid'e akan kujera, a tare suka ce,
"Umma... Surprise... Ga baby...".
Kallona tayi ta saki murmushi tace,
"Ahhh wa nike gani kamar surukata... Aaahhh lale marhabun, sannunki da zuwa, zauna and feel free nan ma gidanku ne...".
Na zauna tareda gaidata ta amsa da fara'a tana tambayata mutan gida, a kunya ce nike, tace,
"Mariam... Right?".
Nayi nodding kai, tace,
"Mariam ki saki jikinki nan ma gidanku ne... Maa shaa Aallah... Cwtheart ya iya zabe...".
Aaryan ne ya sauko daga stairs ya kwanta akan kujerar da Umma take tareda pillow da cinyarta yayi lamo, Umma tana shafa sumar kanshi tace,
"Cwtheart... Miye?".
Da shagwab'a yace,
"Umma kaina ne yake ciwo...".
Da damuwa tace,
"Ayya amma banda ciwon zuciyar ko? Cwtheart ka daina sakawa kanka damuwa, Aalima ta bayyana then what kuma?".
A hankali ya bud'e idanunsa ya kalleni sai kuma ya maida idanunsa ya rufe....
0 comments:
Post a Comment