Page. 16
Adila ta dubeni sannan tace,
"Baby tashi muje bedroom dina...".
Na mik'e suka wuce dani sama, wata kofa ta bud'e muka shiga suka jani wurin kujera na zauna ina kallon bedroom din wanda yake kamar na amarya itama wadda iyayenta suke masu kudi sosai, expensive royal bed, bedside drawer, expensive pure white tale, expensive curtain, sofa, shoes rack, closet, bathroom, high pure mirror then normal mirror, cabinet na ajiye books, expensive blanket, pillows, wow, Aalima tace,
"Nan ne bedroom dina...".
Adla tace, "Nawa bedroom din shine kusa da wannan...".
Na gyad'a kai, suka kawo min ruwa tareda drinks da snack, kishirwa nike ji na zuba ruwan nasha, lokacin sallah yayi, Adila ta mik'e ta shiga bathroom ta fito tace,
"Ki shiga kiyi alwalla...".
Na mik'e tareda zare hijab dake jikina na shiga bathroom din, wanda yake kamar a turai, alwalla nayi na fito na tarar da Adila ce kawai a bathroom din, ta shimfid'a min sallaya na zura hijab tareda tada sallah, lokacin da na sallame tana cikin sallah ne, ta sallame nace,
"Adila zan tafi gida...".
Adila tace, "Kinyi magana da broz ne?".
Nace, "Ai ban fito da wayar ba...".
Adla ce ta shigo tana k'ok'arin zama, Adila tace,
"Tafiya zata yi...".
Adla tace, "Amma tun yanzu, tou muje...".
Tare suka fito suka sauko kasa, Umma tace,
"Ya dai?".
Adila tace, "Baby ce, tafiya zatayi...".
Umma tace, "A'a sai taci abinci...".
Nace, "Umma na koshi...".
Umma tace, "A'a ku wuce dinning, food is ready...".
Babu yadda zanyi suka jani zuwa dinning table, sukaja min kujera na zauna sannan suka zagaya suka zauna opposite dani, Aaryan ne ya karaso ya ja kujerar kusa dani ya zauna, na kalleshi yayi min shiru, Aalima ce ta zauna a daya side din muka sakashi a tsakiya, Umma ta karaso, fried rice ne da pepper chicken, Adila da Adla ne sukayi serving kowa, a kunya ce nike tsakurar abincin ina turawa a baki, na juya nayi idanu hudu dashi na kalli gefe da sauri, ya mik'e ya fita nima na mik'e tareda yi ma Umma sallama nabi bayanshi tareda twins, Aalima ta biyo bayanmu, muna tafiya a jere, ya bude min bangaren mai zaman hakanan nayi masu sallama na shiga ya rufo sannan ya zagaya ya zauna a daya bangaren (driver seat), suna min waving har ya fice da motar daga katon mansion din, driving yake ba tareda ya dubeni ko yayi min magana ba, sai kuma can a hankali yace,
"Kinji yadda tace...".
Na fashe da kuka nace,
"Ai at least kun saurareni kuji abun da ya saka nace no, tou Abba yace sai na auri Mahmud koda zan mutu".
Wani burki yaci banda na saka belt da babu abun da zai hanani gwabruwa saidai ikon Aallah, ya zaro idanu yana kallona sai kuma ya dafe saitin zuciyarshi a lokaci guda yanayinsa ya soma sauyawa, da sauri na rikeshi ina kuka ina bubbugunshi....
"Please ka tsaya kadda ka mutu, ni ba zanyi kisan kai ba... Please kadda ka mutu ta dalilina...".
Yanayinsa ya rud'ani na rikice ina kuka ina bubbugunshi, can ya tureni tareda fashewa da kuka, abunka da d'an hutu voity shagwababbe, can yayi shiru tareda jan motar yana driving ba tareda yace dani komai ba, yana parking opposite da gidanmu ya zaro tissue tareda goge fuskarsa ya jawo leather daga backseat ya d'aura min akan jiki yace,
"Umma ce ta baki...".
Sai kuma ya juya ya kalli gefe, na zuba mashi idanu, can naga ya b'alle murfin motar ya fice ya zagayo tareda bud'e side din da nike, kallonshi nayi sannan na fita....
Yaa Ahmad ne ya fito daga gidanmu saida gabana ya yanke ya fad'i da na lura da kallon da yake min, ya kalleni ya kalli Aaryan dake gefena sannan ya karaso a fusace ya d'aga hannu tareda kwasheni da mari, ya k'ara min wani, na durkushe tareda fashewa da kuka, both marukan sun shigeni sosai, wani kallo yayi min da sauri na mik'e na shige gida da guduna, Yaa Ahmad yayi ma Aaryan wani kallo sannan yace,
"Daga yau kadda in k'ara ganinka da k'anwata, ka fita daga rayuwarta, ja wannan motar ka wuce now...".
Ashe bayan tafiyarmu Yaa Ahmad yazo ya tadda Mahmud shi daya, duk yadda Mahmud yaso ya b'oye mashi amma saida ya fahimci wani abu, ya tutsiyeshi ya fad'a mashi, wannan shine abun da ya faru....
Ina durkushe a daki ina kuka, naji a fusace yana kirana...
"Baby.....".
A tsawa ce yace,
"Ki fito.....".
Jim nayi sannan na mik'e na fita na zauna kasa nayi shiru, a fusace yace,
"Ina kukaje?".
Nayi shiru, a tsawa ce yace,
"Nace maki ina kika bishi...".
Nayi shiru, ya kwasheni da mari ya k'ara kwasheni da mari na fashe da kuka amma babu respond, yayi tambayar duniyar nan nayi shiru, kwafa yayi ya juya ya fice, na gama en matse-matsen kwalla sannan na wanke fuskata na koma daki na kwanta nayi lamo....
Washe gari ina da lectures kuma tun eight nike da lecture din farko and har four ina school don haka tunda safe na shirya na wuce school, ina cikin damuwa throughout tun kalaci da nayi a gida ban k'ara shan koda ruwa ba, duk nayi zuru-zuru dani, avoiding kowa nike, ina zaune a bus wayata tayi ringing na duba bak'uwar number ce saida nayi jim sannan nayi picking, murya macece naji tana magana cikin kuka....
"Baby... Aalima ce... Yana kwance a asibiti, ciwonshi ne ya tashi, don Aallah ki taimaka mamu kadda mu rasashi...".
Da sauri nace,
"Kuna wani asibitin ne?".
Ta fad'a min, kagara nayi bus din ta sauke mu a national, gani nike kamar bus din tafiyar hawainiya take, ina sauka na hau kekenapep zuwa asibitin, ya saukeni na bashi kudinshi nayi tsaye na kasa shiga ciki, wayata na zaro nayi dialing numbar da Aalima ta kirani da ita, tana picking nace,
"Idan Umma bata kusa ki kirani...".
Daga daya bangaren Aalima tace,
"Umma tana ofishin likita...".
Sannan ta sanar da ni bangaren da suke, da sauri na shige ina tafiya da damuwa a tattare da ni, tsaye na hangota gefen wani door, Aalima ce, da sauri na karasa ta glass dake manne a window na hangoshi kwance a lik'a mashi na'urori a jiki, hancinsa dauke da robar oxygen, na fashe da kuka, Aalima zatayi min magana na juya da sauri nabar wurin da guduna ina kuka, kekenapep na tsaida na shiga tareda sanar dashi unguwarmu, yana parking na fita na shiga ciki na dauko mashi kudinshi na kai mashi sannan na koma ciki, cike da damuwa na watsa ruwa nayi zuru na kasa cin komai ga yunwa dake addabata so badly, bayan sallar isha'i na soma kwarara aman kumallo, cikin kankanin lokaci na galabaita, Yaa Ahmad ya daukeni zuwa asibiti, yayi mamaki da likita ya sanar dashi yunwa ce take damuna da kuma damuwa da na saka a raina, saida aka k'ara min drips na huta sannan muka fito, Mahmud na hango jingine da motarsa, yace,
"Baby... Sannu... Ya jikin?".
Na kalleshi kawai, ya bud'e min backseat na shiga ya zagaya side din direba yayinda Yaa Ahmad yake zaune a daya side din, tou daman a kekenapep muka zo asibitin, yana parking na fito na shige gida, har shigowa Mahmud yayi ya gaida Umma, Yaa Ahmad yayi mashi rakiya can ya dawo wani kallo yayi min yace,
"Ke baby wato tunda kikaje school ba ki ci komai ba sannan kika dawo gida still kika k'i cin komai, trust me idan kika k'ara ganin likita yace yunwa ce take damunki tou ki manta da shekarar karshe kike a jami'a...".
Da sauri na dubeshi yace,
"Yeah koda kuwa zakayi kukan jini ne, kuma Mahmud ne sai kin aureshi...".
Saida na raba dare ina kuka sannan na samu baccin wahala yayi awon gaba dani, kwana biyu a tsakani ina zaune naji wata familiar murya tana sallama, kallon kofa nayi tareda amsa sallamar, Aalima ce tana sanye da long hijab har kasa, Ummy dake gefena na kalla itama kallonta take, na juya nace,
"Aalima sannu da zuwa...".
Saidai kallo daya nayi mata naga damuwa a tattare da ita, ta gaida Ummy sannan na mik'e na jata dakina, da kukanta tace,
"Don Aallah baby ki taimaka mamu kadda mu rasashi...".
Hawaye ne suka zubo min akan fuska nace,
"Abba yace dole sai na auri Mahmud koda zan mutu kuma babu yadda zanyi, nasan Abba nasan halinshi koda zan mutu bazai janye ba...".
Aalima tace, "Baby!...".
Na had'a hannuwana wuri guda nace,
"Don Aallah ki fahimceni babu yadda zanyi ne".
Aalima tace, "Ni ban ce ki bujirema maganar mahaifinki ba amma na rokeki da girman Aallah kiyi mamu alfarma guda daya kadda ki daina kula Yaa Aaryan, muna tsaka da soyayya aka nemeni aka rasa, ya shiga damuwa sosai, ya kwanta asibitoci sau ba adadi, zuciyarshi tana da damuwa idan kika daina kulashi zai iya rasa ranshi, please I beg you don Aallah ki cigaba da kulashi har lokacin da zai hakura, don Aallah ki tausaya mamu kadda mu rasashi".
Na kalleta tausayi ta bani ta damu sosai bayan tana matuk'ar sonshi shi kuma yana matuk'ar sona kamar yadda yake matuk'ar sonta, da sauri na rik'e hannunta nace,
"Aalima indai wannan ne baki da damuwa dani, trust me daga nan har zuwa before a d'aura min aure indai Aaryan zai tako yazo gidan nan tou ni kuma zan fita, idan ya kirani zan dauka...".
Ta jawo gefen hijab ta goge fuskarta sannan ta fita ina ji tayi ma Ummy sallama sannan ta fice, na fashe da kuka sannan a hankali nace,
"Kuyi hakuri amma *BA NI DA LAIFI* zan auri Mahmud amma dole in cigaba da kula Aaryan, babu yadda za'ayi ina gani innocent Aaryan ya rasa ranshi saboda ni bayan kuma bashi da laifi...".
Washe gari ina duba note Yaa Ahmad ya shigo yace,
"Ki tashi kije Mahmud yana jiranki a waje...".
Na mik'e na zura long hijab tareda zura takalma na fice tareda tsayawa gefenshi, Mahmud ne, yana min magana nayi zuru ina tunanin duniya....
Motan Aaryan na hango tana matsowa har yayi parking ya fito, ya rame ya koma wani iri, kallo daya za'ayi mashi a gane yana cikin damuwa sosai, kallon Mahmud nayi sai kuma nayi taking steps zuwa inda Aaryan yake, kamar zaiyi kuka yace,
"Baby kiyi hakuri ina cikin damuwa, ke kadai nike son gani shiyasa nazo amma idan baki so bazan k'ara zuwa ba...".
Da sauri na girgiza kai, yace,
"Na gode...".
Sai kuma yayi shiru yana kallona, ji nayi an kwasheni da mari, Yaa Ahmad ne, ya k'ara kwasheni da mari sannan ya nuna min kofa, da gudu na wuce gida ina kuka....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest Deena babie, Aallah ya albarkaci rayuwarki, wish you all the best....*
*Hope kinyi sallah lafiya Fateema, our greatest small cute hajja, wish you all the best....*
Page. 17
Ban san abun da ya faru ba, lokacin da Yaa Ahmad ya shigo ya tusani gaba kamar zai dokeni, ya hau ni da fad'a ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, nayi shiru, saida ya k'ara kwasheni da mari saboda yana magana nayi mashi shiru, na fashe da kuka, yace,
"Indai taurin kai zaki nuna min, tou kadan kika gani, na rabaki da wancen saurayin amma kinki ko, tou zakiji a jikinki ne".
Sai kuma yayi min wani kallo kamar zaiyi kwollo da ni, yayi kwafa ya fice, Ummy tana daga gefe amma bata ce komai ba, sai ma ta mik'e ta wuce dakinta, na mik'e na dauki buta na wanke fuskata sannan na wuce daki na zauna ina shafa fuskata ina feeling yadda fingers dinshi suka kwanta, indai akan Aaryan ne saidai a kasheni, ta dalilina yake cikin damuwa, sam bashi da laifi, saboda ni bazan bari ya rasa ranshi ba....
Washe gari bayan na dawo daga school na tadda sister din Abbanmu tazo, Inna safiya, nasan halinta bata san raini ko kadan, wanka nayi sannan naci abinci, ita da Yaa Ahmad suka tusani gaba suna min fad'a, nidai shiru nayi ina sauraronsu, Yaa Ahmad yace,
"Inna kin ganta nan ta rainani na rabata da wannan saurayin amma taki daina kulashi...".
Inna tace, "Ahhh tou wa ya sani ko asiri yayi mata".
Yaa Ahmad yace, "Babu asirin da yayi mata, taurin kaine kawai da raina mutane da tayi, bata jin maganar kowa sai tashi...".
Inna tace, "Wannan wani irin ja'irin yaro ne yake zuwa yana hure mata kunne, idona idonshi sai naci mashi mutunci".
Yaa Ahmad yace, "Kuma yasan an saka mata biki amma bai fasa zuwa ba itama bata fasa fita ba, idan yazo inyi duka inyi fad'a amma saboda taurin taki daina kulashi...".
Inna tace, "Ai duk laifinku ne kuka zuba mata idanu tana abun da ranta yake so, a fili kuke nuna kun fi sonta, k'anwarta tayi aure amma ita tana zaune wai boko...".
Sai kuma tayi min dak'uwa tace,
"Keh Maryamu uwaki, nace uwarki, k'anin nawa yayi maki miji shine kikeyi mashi haka, wato so kike shi daya da ya rage min ki karasa min dashi, tou kinyi kadan, kaji ja'ira mai manyan kunnuwa...".
Yaa Ahmad yace,
"Mahmud ba ya da damuwa, kowa yabon halinshi yake amma ita a fili take nuna bata sonshi, zai tako yazo zance wurinta amma wancen saurayin yana zuwa zata tsallakeshi ta wuce wurinshi...".
Inna tace, "Lallai Maryamu kin giga...".
Wayata dake kuguna ce ta soma tsuwwa na zura hannu na jawota tareda kangawa a kunne, daga daya bangaren Aaryan yace,
"Mariam kiyi hakuri...".
Nace, "Aaryan ya aka yi?".
Da damuwa yace,
"Ina kofar gidanku yanzu haka...".
Nace, "Kadda ka damu Aaryan... Alright then gani nan fitowa...".
Da mamaki suke kallona, na mik'e tareda zura long hijab na tsallakesu na fita waje tareda zura takalma na fice, Aaryan ne jingine da motarsa, suit ne sanye a jikinsa da alama daga wurin aiki yake, tausayinshi naji saboda yadda ya koma wani iri, na karasa tareda tsayawa gefenshi, da damuwa ya dubeni yace,
"Mariam kiyi hakuri daga wurin aiki nike ina son komawa gida amma ban ci komai ba, bana san su fahimci halin da nike ciki, baby ke kadai ce zaki iya tursasani inci abinci, baby koda ni kaina bazan iya tursasa kaina ba".
Before inyi uttering word naji saukar mari a kuncina wanda ya gigitani na fashe da kuka, Yaa Ahmad ne, ya nuna min kofa yace,
"Wuce....".
Na wuce da gudu na shige gida karo naci da Inna tana fitowa, na shige ciki da gudu na zube a kasa ina kuka, shigowa sukayi....
Yaa Ahmad ya kwasheni da mari sannan yace,
"Don kin raina mu shine muna maki fad'a kika tsallakemu kika wuce wajenshi wato ga kanin Abba yazo kadda kik'i zuwa ya tsine maki albarka...".
Inna dake tsaye gefe tana maida lumfashi, da alama ranta ya b'aci sosai, a fusace ta tureshi tace,
"Matsa ka bani wuri, wannan shine duka, ai wannan ba duka bane, miye a hannunta?".
Da sauri Yaa Ahmad ya kalli expensive android dake hannuna yace,
"Gidan uban wa kika sameta?".
Nayi shiru, yace,
"Tambayarki nike...".
Inna tace, "Bakya ji yana maki magana".
Yace, "Inna wannan wayar tana da tsada sosai da sosai, ta linka wayata kudi sau goma ko ma fiye da haka".
Inna tasa salati tana sallallami, yace,
"Koda bata fad'a nasan wancen saurayin ne ya bata ita".
A fusace Inna ta mik'o min hannu tace,
"Kawota nan...".
Da sauri yace,
"Tunda ta amsa kibar mata, ai ta rainamu ne, duk gidan nan babu wanda yasan da wayar nan...".
Na lura da wani abu, yasan idan ta amshi wayar daddak'ata zatayi shiyasa yace mata haka, tayi mashi wani kallo tace,
"Tou ai shikenan amma yau sai na cire mata wannan taurin kan da takeji dashi".
Sannan ta jani dakin Abba ta kulleshi tayi min dukan tsiya, kuka kawai nike, naji jiki, na had'a majina, ta bud'e dakin ta fito tana bala'i ta barni kwance ina kuka, ta dage tana bala'i wata maganar kai tsaye da Ummy take, tace,
"Ai rashin mutunci ne ya hanata magana, ita da d'iyarta uwayen son abun duniya, tou daga ke har ita kunyi kadan, aikin banza, aikin wofi...".
Dama bata shiri da Ummy duk da kuwa kyautatawa da take masu, gani suke ta mallake Abba ta hanashi aure, komai ya samu ita da yaranta, surutu sosai sukayi akan fitar da Ayan karatu kasar waje, Ummy dai tana jinta amma bata ce komai ba, na fito na rarrafa na shige dakina, na jima sannan na fito na jawo ruwa na hada da na zafi na shiga bayi na gasa jiki don na daku iya dakuwa, na bugu iya buguwa, na fito tareda shigewa daki na dauko wayata na dannawa Aaryan call yana picking nace,
"Kana ina?".
Daga daya bangaren Aaryan yace,
"Na kasa tafiya, ina akan titin unguwarku, mariam yunwa nikeji sosai".
Nace, "Yanzu zan fito, kadda ka tafi, kaji".
Daga daya bangaren yace,
"Tou baby...".
Tausayi ya bani na mik'e na zura hijab tareda shiga kitchen na dauki kwanon tuwona na zuba mashi miya na fice, ina karasawa bakin titi na hango motarshi na karasa, Yaa Ahmad na hango daga gefe, da sauri na shige tareda rufo motan, Aaryan da ya d'aura kanshi akan starry ya dago yana kallona, da sauri nace,
"Kaga ja motar daga unguwar nan".
Babu musu yayi mata key ya hau titi saida yayi tafiya sosai sannan nace,
"Ka tsaya nan....".
Babu musu ya gangara gefen titi yayi parking, na bud'e kwanon tareda daukar cokali nace,
"Ka daina zama da yunwa kaji".
Aaryan ya gyad'a kai kawai, na ciko spoon da tuwo nasa miya sannan na nufi bakinsa dashi, babu musu ya bud'e baki na saka mashi, ina feeding dinshi yana kallona, saida na tabbatar ya koshi sannan na rufe kwanon nace,
"Akwai ruwa a motarnan?".
Ya girgiza kai, nace,
"Then kawo kudi in siya maka".
Ya zaro wallet dinsa daga pocket din trouser ya mik'o min na zari naira dubu na fita tareda tsallake titi na shiga wani canteen na siya mashi ruwan rubber, lokacin gab ake da fara kiran sallar magrib shiyasa suke sauri-sauri su rufe canteen, na amshi change na tsallako na bud'e motar na shiga na dauki wallet din na saka mashi changing kudin sannan na mik'a mashi ya saka a pocket din wandonsa, na mik'a mashi gorar ruwan nace,
"Ka kuskure bakinka...".
Babu musu ya amsa ya b'alle murfin motar ya fita ya kuskure bakinsa sannan ya shigo tareda mik'o min gorar ruwan na amsa na b'alle murfin tareda kafa mashi ruwan a baki yasha ya koshi har saida ya ture gorar ruwan sannan na maida murfin na ajiyeta na dubeshi nace,
"Ka maidani gida, lokacin sallar magrib gab yake...".
Aaryan ya gyad'a kai sannan a hankali yace,
"Mariam kiyi hakuri bana jin dadin dukan da yake maki saidai babu yadda zanyi brother dinki ne...".
Sai kuma ya ja motan, yayi parking motan a daidai santar gidanmu kallonshi nayi sannan na juya na b'alle murfin motan na fita tareda maida murfin motan na rufe na wuce ina taking steps a sanyaye, tausayi Aaryan yake bani, ina shiga na tarar dashi a tsaye, Yaa Ahmad ne, nayi crossing dinshi zan wuce ya jawoni tareda kwasheni da mari, kwanon dake hannuna ya subuce sauran tuwon da ya rage a ciki ya b'are a kasa, Inna dake gefe ta saki salati tace,
"Ina kikaje da abinci?".
Yace, "Saurayi ta dauki abincinta ta kaimawa".
Inna tace, "Dalla matsa ka bani wuri ko kuma in had'a da kai, ai har da kai aka taru aka zuba mata idanu tana tsula tsiyarta...".
Ya mangareni sannan ya fice, saida Inna ta k'ara likad'a man wani duk'a sannan tayi alwalla ta wuce daki, dakyar na mik'e tareda cire hijab dake jikina na daurata akan igiyar shanya na dauki buta na shiga bayi na fito tareda yin alwalla na wuce daki....
Bayan Abba ya dawo, Inna ta tusashi gaba ta zayyana mashi komai, ina ji ya rufe Ummy da fad'a, hakuri kawai ta bashi, Inna ta sanar dashi kwana biyu zatayi sannan ta koma....
Zaune nike a dakina nayi zuru, Ummy ta shigo ta zauna kusa dani ta dubeni da damuwa tace,
"Mariam kin san dalilin da ya saka nayi shiru? Tou saboda idan nayi magana sai ya zamo cewa tawa tafi zafi amma duk da hakan ban tsira ba saida nayi laifi, don Aallah baby kiyi biyayya ga mahaifinku kadda kiyi silar da saboda rigimar wannan auren ni in rasa igiyoyin aurena wadda nayi shekaru sama da talatin ina tattalinsu...".
Na gyad'a kai kawai, Ummy ta mik'e ta fice, wayata tayi ringing na duba Yaa Mustapha ne, nayi picking yace,
"Baby why are you doing this?".
Nace, "Am doing the right thing ne, bazan bari ina gani innocent Aaryan ya rasa ranshi saboda ni ba, ai bashi da laifi, ai na yarda zan auri Mahmud, ai at least an barni da wannan".
Nayi hanging call din, dukkaninsu wurin Ayan ne kawai nike samun sauki, Nadiya gani take ina neman d'aurawa Ummy ciwo ne inyi silar da zamu rasata, kallonsu kawai nike, ace dukkaninsu mutum daya ne ya fahimceni....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest mariam, tou ina nufin masu suna mariam, tou mariam, maryama, mairo, mariya, maryoyi, tou wish you all the best....*
*Hope kinyi sallah lafiya Zaynerb, our greatest zeezee, wish you all the best....*
Page. 18
Washe gari muna zaune wani yaro d'an makotanmu ya shigo wai ana kirana, nace,
"Inji wa?".
Yaron yace, "Mahmud yace...".
Nace, "Je ka kace gani nan fitowa".
Na mik'e zan suri hijab, Inna tayi sororo tana kallona sannan tace,
"Kee dakata ina zakije a haka...".
Sai kuma ta kwalawa yaron kira tace,
"Kace yayi hakuri zata shirya".
Sai kuma ta dawo kaina tace,
"Da ace ba ni kusa a haka zaki fita, tou wuce maza kiyi wanka ki shirya, saura kuma inga kin zunbula hijab...".
Saida nayi wanka sannan na shirya nayi applying lipstick gudun kadda ta koroni tace sai nayi kwalliya, na saka wasu riga da zani na atamfa tareda yafa veil na zura takalma flat, tou vaseline kawai na shafa na goge fuskata na shafa powder nayi applying kwalli then lipstick amma nayi kyau sosai, na wuceta a tsakar gida tace,
"Ko kefa saura kije kiyi mashi rashin kunya ki dawo in casaki a gidan nan".
Na fice na hangoshi jingine da mota yana sanye da kananan kaya, jeans da shirt mai wani irin neck, ina yawan ganinta a series, shirt din design ce mai kyau, na karasa tareda tsayawa gefenshi nayi mashi sallama ya amsa, nace,
"Ina wuni?".
Mahmud yana kallona yace,
"Lafiya lau... Ya kike?".
"Lafiya lau....".
"Shopping zan kaiki...".
"Saidai bana hawa motar samari".
Mahmud ya ware idanu sannan yace,
"Shi kuma da kike shiga tashi...".
"Wannan kuma daban... Kayi kyau...".
Smile ne ya sub'uce akan fuskarsa yace,
"Na gode... Kema kinyi kyau...'.
Nayi dariya kawai, yace,
"Ina son wannan dariyar...".
Nayi murmushi sannan nace,
"Idan kana so kawai kayi min magana zanyi maka".
Yace, "Ya su Ummy?".
Nace, "Suna nan lafiya lau, Inna ma tazo...".
Gani nayi ya dafe goshi, yace,
"Ohhh gashi kuma kananan kaya na sanyo amma da daddare zan shigo in gaidata...".
Nace, "A'a yanzu dai, bari kaga inyi mata magana...".
Ya ware idanu na kwashe da dariya, yace,
"Rufa min asiri....".
Nace, "Asirinka a rufe yake...".
Ya bud'e mota ya zaro kwalin waya iPhone 8 tareda mik'o min yace,
"Gashi na sawo maki...".
Na kalli gefe kawai, yace,
"Amsa.....".
Nace, "I like sumarka, tayi kyau".
Mahmud yayi murmushi, mun jima sannan ya wuce na juya na koma gida, bayan sallar isha'i sai gashi yazo gaida Inna, fita nayi na shigo dashi, lokacin da ya fita ta hau ni da fad'a kamar zata dokeni....
"Yaron kirki, bashi da damuwa amma kike mashi wulakanci saboda wani can shashasha....".
Saida naji babu dadi akan abun da ta fad'a akan Aaryan, wani yaron makotanmu ne ya shigo da katuwar leather na amsa na mik'a mata nace,
"Naki ne, inji Mahmud...".
Na wuce daki ina ji tana zunduma mashi albarka, yanzu kam na ware da Mahmud, idan ya kira zan dauka idan yazo zan fita kuma bana mashi magana mara dadi saidai bana amsar abun hannunshi, indeed ni ba mayyar kudi bace, bayan kwana biyu Inna ta wuce, damuwa tayi min yawa amma tun daga wannan lokaci na yanke shawarar bazan k'ara sawa kaina damuwa ba, gab nike da fara zana jarabawata ta karshe a jami'a ga project da nike rubutawa, idan na saka wasa zan lalata CGPA din da nayi shekaru ukku ina tattalinsa, wannan yasa na cire kowace damuwa daga raina, dukkanin abun da ya faru a inda ya faru a nan nike barinshi, tou the more Aaryan yazo gidanmu the more zan fita the more kuma idan Yaa Ahmad ya gammu zai kwasheni da mari, nasha maruka marassa adadi amma ban damu ba, Aaryan ba ya jin dadin abun da yake faruwa amma koda yayi niyyar kasancewa away from me bazai iya ba, wani lokacin ji yake idan bai ganni ba yana iya mutuwa, ni idan har ya kirani yace yazo tou zan fita saidai na lura idan yaga ina tareda Mahmud komawa yake ko kuma yayi parking gefe, yana kirana a waya musha hira, gulma iri-iri a unguwarmu, unguwa ta dauka cewa ga wanda aka saka min biki dashi amma har yanzu ban daina kula saurayina ba, ko'ina surutun ake, nikam ta exam dake gabana nike ga kuma project da nike rubutawa....
Ranar wata laraba Nadiya tazo mamu wuni, muna zaune tace,
"Baby abun da kike sam bai dace ba, ai at least tunda kin san Mahmud zaki aura sai ki daina kula Aaryan, haba, abun yayi yawa, kina sakawa mahaifiyarmu damuwa, ai koni da nike k'anwarki ba zanyi haka ba".
Na dubeta na saki murmushi sannan nace,
"Nadiya na ce ke wanda kike so kika aura? Ni kuma anyi min dole kuma na yarda zan auri Mahmud... Ummy kuma gatanan saboda ita na kwantar da hankalina akan wannan auran...".
Daurin kirji ne kawai a jikina, wayata ce tayi k'ara ina dubawa naga Aaryan ne, picking nayi tareda kangawa a kunne, nace,
"Ina jinka Aaryan... Shikenan gani nan fitowa...".
Nadiya ta zaro idanu tana kallona, na mik'e tareda shiga daki na zura long hijab na fito, Nadiya tace,
"Baby ina zakije?".
Nace, "Wurin Aaryan...".
Sannan nayi mata wani kallo na fice, lokacin da na dawo na tarar da Yaa Ahmad a tsaye fuskarsa a murtuk'e, kallonshi nayi zan wuce daki ya jawoni tareda kwasheni da mari saida hijab dake jikina ta d'age....
Yaa Ahmad ya ware idanu yace,
"Yanzu saboda baki da kunya haka kika fita daga ke sai daurin kirji".
Sai kuma ya cigaba da jera min mari a baya, Nadiya tace,
"Baby ki bashi hakuri mana...".
Nayi banza da ita, tace,
"Yaa Ahmad kayi hakuri...".
Yayi banza da ita, dakyar ta shiga tsakaninmu, yayi kwafa sannan ya wuce dakinshi, Ummy kam idanu ne nata, ina durkushe ina kuka, Nadiya tace,
"Ai kinga abun da kika jawa kanki...".
Ta wuce kitchen ta kawo min ruwan zafi, tace,
"Ki saga kuncinki...".
Wani kallo nayi mata na suri kwanon na wuce dakina, nayi zuru ina gasa kuncina, abunku da farar fata, fingers dinsa suka fito suka kwanta tareda appearing akan both cheeks dina....
Bayan kwana biyu ina sanye jeans da shirt ina duba note, Aaryan ne ya kirani nayi picking yace,
"Please baby ki fito ina akan titin unguwarku...".
Na mik'e da sauri na zura long hijab na fice a rud'e gani nike wani abun ne ya sameshi, ina fitowa bakin titi na hango motarshi na karasa tareda bud'eta na shiga, Aaryan ya dubeni cike da damuwa yace,
"Kiyi hakuri Baby I feel....".
Sai kuma yayi shiru yana kallon wani wuri, nima da sauri na kalli inda yake kallo zaro idanu nayi ganin Yaa Ahmad ya nufo motan, da sauri na fito nayi santarmu ina taking steps da sauri-sauri, ina shiga gida nayi tsaye ina maida lumfashi, Yaa Ahmad ne ya shigo tareda kwasheni da mari, ya k'ara min wani, na fashe da kuka, salati yayi yana kallona sannan yayi kwafa yace,
"Nasan maganinki...".
Ya wuce ya barni a durkushe ina kuka....
Washe gari ina zaune nayi picking call dinshi, Aaryan ne, daga daya bangaren yace,
"Baby kiyi hakuri amma ke kawai nike son gani, bana son in k'ara jawo maki damuwa, ina son ganinki amma bazan iya zuwa gidanku ba...".
Sai kuma naji yayi hanging call din, nayi shiru ina tunani, ji nayi Ummy tana kirana na amsa sannan na fito da sauri tareda zama kusa da ita, tace,
"Baby ya kamata ace kin lek'a gidan Nadiya tana yawan min korafin bakya son zuwa gidanta...".
Nace, "Kuma gobe zan shiga school in kai project dina amma bari in shirya yanzu in wuce sai inyi mata wuni...".
Ummy tace, "Hakan yayi....".
Na mik'e na wuce wurin rijiya na jawo ruwa na cika bucket naja kwandon wanka na wuce bayi nayi, ina fitowa na wuce dakina na shirya tsaf na zura long hijab har kasa nayi ma Ummy sallama na fice, lokacin wurin karfe sha daya ne haka, ina tare kekenapep na shiga tareda fad'a mashi unguwar da zai saukeni, akan hanya na kira Aaryan na fad'a mashi inda zamu hadu, ashe yana kusa da unguwar ina mashi kwatance ya gane har gidan yana da friend a nan kusa dasu, kekenapep ce tayi parking opposite da gidan na zaro kudinsa na bashi tareda fitowa na shige gidan, flat house ne mai kyau, ko'ina tsaf-tsaf, gini ne na zamani, two bedrooms and parlour then wani room daga gefe wanda suke sauke baki then store da dakin yara, ginin yayi babu karya, wani expensive tale ne malale a kasa, sallamar farko ta amsa saida na kashe selfie sannan na shiga, tana zaune a parlour tana fama da Najib yana mata rigima yana ganina ya mik'o hannu na daukeshi ina mashi wasa yana dariya, Nadiya tace,
"Kin tuna dani kenan ko kuwa b'atan hanya kikayi...".
Nace, "Nazo inyi maki wuni ne...".
Ta kawo min drinks masu sanyi, wayata ce ta soma tsuwwa nayi picking jim nayi sannan nace,
"Na'am... Ohhhh kana kofar gidan... Aha, tou gani nan fitowa...".
Nadiya ta kalleni, nace,
"Ina zuwa, yana jirana a waje ne".
Na mik'a mata Najib na fita, Aaryan ne, muna tare har aka yi kiran sallar zuhr ya wuce masjid dake unguwar while ni kuma na koma ciki, Nadiya ce ta fito daga kitchen, nace,
"Najib fa?".
Tace, "Na lallab'ashi yayi bacci, da alama yau rigima yake ji, ni zuwa zanyi in yayeshi...".
Nace, "Ki bari mana dai ya k'ara girma".
Tace, "Amma Baby waye ya kiraki kika fita?".
Wani kallo nayi mata sannan nace,
"Aaryan ne kinga sai kiyi harama ki dauko wayarki ki kira Yaa Ahmad kice mashi gani nan tareda Aaryan...".
Nadiya tayi shiru kawai ta koma kitchen na wuce dakinta nayi alwalla a bathroom dake ciki, na fito na shimfid'a sallaya tareda tada sallah, bayan na sallame Najib ya tashi daga bacci ya mak'ale min, Aaryan ya kirani na mik'e ina dauke da Najib na fice, tou ina ficewa waje Aaryan ya amshesa tou a jikinsa yayi bacci ya kwantar dashi a backseat, muna tsaye mijin Nadiya ya dawo don har gaisawa sukayi, wristwatch dake hannunsa ya duba before yayi min sallama saboda lokacin sallar asr gab yake saura mintina basu wuce biyu ba, ya dauki Najib ya rakoni har kofar gidan sannan ya bani shi har da bashi kudi na amsa nace,
"Ya gode...".
Aaryan yayi nodding head kawai sannan ya juya yana taking steps yana juyowa yana kallona har ya shiga motarsa saida ya wuce sannan na shige ciki, na kwantar da Najib akan doguwar kujera....
"Bacci yayi a hannunsa....".
"Baby....".
"Na'am k'anina... Ya kake?".
"Lafiya lau... Baby kinyi wahalar gani...".
"School ce ta b'oyeni, yau nazo kadda rashin kirkin nawa yayi yawa...".
"Ai kin kyauta...".
Masjid ya wuce, saida na damkawa Nadiya kudin da Aaryan yaba Najib sannan nayi alwalla na tada sallah, bayan na sallame ta kawo min abinci naci na kora da drinks....
Call din Mahmud ne nayi picking....
"Assalamu Alaiki....".
"Wa Alaikas-salam...".
"Baby kina ina wani friend dina zan kawo maki ku gaisa....".
"Ban shiga school ba, kuma ba na gida, ina gidan Nadiya zuwa nayi nai mata wuni....".
"Alright then, bari muzo sai inyi dropping dinki a gida...".
"Kuma, tou shikenan sai kazo...".
Jim kadan sai gasu saida mijin Nadiya ya fita suka gaisa sannan na fita muka wuce, bayan da Nadiya ta had'a min kayan kwalliya, ina backseat while Mahmud da friend din nashi suke a front seat, akan hanya Mahmud yayi picking wani call don haka suna dropping dina a unguwarmu suka wuce....
Cikin hakane na gama zana jarabawata ta karshe har project na gama, na kammala degree dina kuma bana fatan spilled over (level 500), biki yazo tareda Jalila nike rabon invitation card, na bata na suhailat (matar suhail) kuma ta kai mata, duk kawayenmu mun kai masu, a motar Jalila muke zuwa rabon invitation card din, yau aka kawo lefe akwatuna har set daya abun har da gayya, tou akwati sha biyu kenan har da makullin latest car tareda naira million daya, tun daga kallon da en kawo lefen sukeyi min nasan akwai damuwa, ina makotanmu wasu en mata daga cikin wadanda suka kawo lefe suka shigo, kaya ne sosai kuma kowane expensive, akwati guda daya aka cika da jeweleries na gold har da na diamond, gown kala-kala design na kasashe daban-daban, atamfofi, shaddodi, ready made, less, shoes, handbag da sauransu, night gown ne babu kuma ya fad'a man ya barsu wurinshi ne, naira dubu dari aka basu tukwuici, tun daga kallon da en matan nan sukeyi min nasan akwai damuwa, suna wucewa en unguwa suka fara zuwa ganin lefe wasu kuma gulma ce take kawosu, su k'ara gaba suna fadin ai kudi nike so kuma na samu amma saboda bakin hali nak'i daina kula wancen saurayin, wai ni fara, gulmace-gulmace iri-iri....
Na samu gyara sosai, abubuwan gyara skin da na sha har na soma sauyawa nayi kyau, skin dina yayi haske na kara cikowa, kamshi na musamman ya zauna a jikina, abun saidai ace Maa shaa Aallah....
Ina zaune nayi picking call din Aaryan, daga daya bangaren yace,
"Baby ki fito ina kofar gidanku...".
Sai kuma yayi hanging call din, saida nayi jim sannan na mik'e na zura long hijab na fice na samu motoci ne guda biyu parker opposite da gidanmu....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest deejerh beauty, Aallah ya albarkaci rayuwarki, wish you all the best....*
*Hope kinyi sallah lafiya bestietie, tou ina jiran barka da sallah na, wish you all the best....*
Page. 19
Aaryan ne ya fito daga daya daga cikin motocin, yana taking steps cike da damuwa ya karaso inda nike tareda mik'o min wani karamin kit yace,
"Baby waccen motar da sunanki na siyeta, Aallah yayi ba ni bane mijinki, gata can duk abun dake cikinta da sunanki na siyeshi".
Na kalli inda yayi pointing, expensive car ce kirar Benz, latest kuma, jim nayi sannan na amshi kit din tareda juyawa na shige gidanmu....
Yaa Ahmad ne ya shigo yace,
"Baby kina ina?".
Na fito yace,
"Mey waccen Benz take a kofar gidan nan...".
Nace, "Aaryan ya kawota, da sunana ya siyeta, duk abun dake ciki tou da sunana ya siyeshi, shine ya kawo min ita...".
Yaa Ahmad yayi min wani kallo kamar zaiyi kwollo dani sai kuma yayi kwafa yace,
"Bani makullin motar maida mashi abunsa zanyi".
Na ware hannuwa don ni Aaryan bai bani makullin motar ba, Yaa Ahmad ya wafce kit din dake hannuna ya budeshi makulli ne yayi appearing tareda wata karamar paper dake linke, wani kallo yayi min yace,
"Da wayar da ya baki, da wannan zoben da duk wani abu da ya fito daga gareshi ki tattaro had'awa zanyi in maida mashi".
Na juya na shige daki na cire sim card dina dake cikin wayar na maidata cikin kwalinta, na zare zoben diamond dake a finger dina na maidashi a kit, na dauko madubin da ya fara bani, na tattara dukkanin wani da Aaryan ya bani na fito dasu waje, ya kalleni nace,
"Sauran da kuka rage antinshi ta bani, mom, da kuma ummarshi da kuma k'annanshi, wad'annan kam daban suna da k'ima a idanuna bazan iya mayar masu da abun da suka bani ba...".
Wani kallo yayi min ya kwashe kayan ya wuce, na koma daki tareda zakulo wayata Baby Nokia na saka sim card dina a ciki, lokacin da Aaryan ya kirani har kuka yayi min, gara kawai iyayena sukayi min saboda Mahmud yace an zuba komai, tou ni tsurata kawai za'a kaini sai kuma gara da aka yi min, party kusan kala biyar ne, daga ni har Mahmud babu wanda yake son party amma babu yadda zamuyi saboda lokacin da aka tsarasu banda mu, wannan aikin Jalila ne da Yaa Ahmad, expensive kaya design na musamman ya kawo min kowane da sunan program din da zanyi attending dashi, sun kashe kudi don koda poss, heel shoes da head idan mutum yaji kudinsu sai ya rik'e baki, abun har mamaki yake bani yadda daga bangaren ango suke kashewa wannan biki makud'an kudade koda yake wani abun har da gayya, gidanmu kam anyi mashi shafe da sabon paint tareda shafen kasa, gida yayi fes dashi, yanzu Aaryan ya gane kirana mu jima muna hira, tou satin biki ya shigo tun daga Monday aka fara gudanar da party, an zana min unique henna abun saidai Maa shaa Aallah, nasha gyaran jiki, makeup artist suka dauko domin ya kasance tana min kwalliya har a gama bikin, before bana son kwalliya am not fan and ina ganin ba zatayi min kyau bane shiyasa ba nayi amma tunda week din bikin ya kama makeup artist ta soma min applying makeup ina looking more cute and cute, gorgeous and breathtaking, tun daga wannan lokacin na tabbatar da kwalliya ta nayi min kyau matuk'ar kyau kuwa, abun haushi haka za'a sakani fita babu veil gashi kayan suna suiting dina su matseni figures dina suyi appearing, gashi Aallah ya azuratani da boobs ga kugu da hips, just like slander, ranar bridal shower na saka wata breathtaking fitet gown da head, poss da high heel shoes, nayi matuk'ar kyau a wannan shiga saidai ban iya tafiya da high heel shoes ba, tou ina tafiya kamar zan fad'i wani lokacin saidai inji na fad'a mashi kuma babu kunya zaiyi hugging dina yana smile tareda waving ma mutane hannu, ni kunya yake bani....
Ranar dinner na saka ashobe riga da zani tareda gwargwaro ga heavy makeup dake kwance akan fuskata, wow abun ba'a magana, nikam idanu ne nawa sai yadda sukayi dani, haka expensive motoci latest suke jan line akan titin santar da gidanmu yake, wasu daga ciki saidai empty suke tafiya, mun fito tareda besties dina wayata tayi ringing na zarota daga poss ina dubawa naga Aaryan ne da sauri nayi picking na koma da baya jim nayi ina sauraronshi sannan a hankali nace,
"Alright then, gani nan zuwa...".
Na dawo tareda crossing dinsu na wuce nayi wata hanya, opposite da hanyar da zata kaini bakin titi, ina taking steps da sauri-sauri gashi high heel shoes ne kamar zasu kaini kasa, wata santa dake bayanmu nayi appearing, Aaryan ne yana jingine da motarshi ya zuba min idanu yana goge hawaye wasu sabbi suna zubowa, na tsaya gefenshi ina kallonshi cike da damuwa duk ya rame ya koma wani iri, ya fashe da kuka tareda zaro wani rectangle shape abu da aka yi wrapping da k'yalli ya mik'o min, kallonshi nayi yana goge hawaye yace,
"Congratulation, wish you all the best, yara masu albarka...".
Ji nayi an rik'e hannuna tareda jana gaba, ina juyowa naga Yaa Ahmad ne yana sanye da wata expensive brown shadda da aka yi ma aikin hannu da coffee brown zare, yana jana ina binshi yayinda idanunsa suke kallon gabanshi fuskarsa a murtuk'e, na juyo ina kallon Aaryan da ya zuba min idanu yana zubda hawaye da gift din a hannunsa, lokaci zuwa lokaci ina juyowa ina kallonsa har muka sha corner ya b'ace min daga gani, tun daga nesa na hango en matan amarya sunyi cirko-cirko tou Bride ta b'ace, suka ware idanu suna kallonmu, Yaa Ahmad yace,
"Anya kuwa, da ace saceta nayi saidai kuce baku san yadda aka yi ba...".
Jalila ta kalleshi kamar ta fahimci wani abu, bindawa tace,
"Ka tada mamu hankali, Bride tayi disappearing ai babu zance...".
Yaa Ahmad yace, "Sorry kunji...".
Ya bud'e wata zureriyar mota ya sakani, wani kamshi mai sanyi naji na kalli gefena, Mahmud ne zaune a daya side din looking more cute and more cute, yana sanye da wata expensive shadda dinkin babbar riga da er ciki da wando, daga ganin yanayin aikin da dinkin mutum zai tabbatar popular tailor ne ya dinkashi, ya murza wata expensive k'ube, akan hannunsa wristwatch ce kirar rolex, a kafarshi expensive silifas ce amma ni aka had'a ni da high heel shoes idan ina tafiya saidai in rinkayi very carefully don ji nike kamar zan zube kasa in karye kafafu, kallona yayi yai murmushi yace,
"Kinyi kyau, you look breathtaking...".
Na gyad'a kai, yace,
"Mey? Kunya kikeji?".
Na d'ago na kalleshi sai kuma nayi kasa da idanu, ya d'ago hab'ata yace,
"Mariam... Baby rigima, ku babies saida madara...".
Nayi mashi wani kallo tareda buge hannunsa, yasa dariya kasa-kasa, motar aka yi parking, Mahmud yayi min waving hannu yana smile ya fice tareda zagayowa ya bud'e side din da nike, ya mik'o min hannu yana smile na kalli gefe sannan na zuro kafufuna dake sanye da high heel shoes na fito, na zame tareda yin taga-taga zan fad'i ya taroni yana murmushi, na kalleshi tareda rik'eshi na daidaita tsayuwata muka wuce, tun daga kallon da relatives dinsa (d'anginsa) sukeyi min na tabbatar akwai damuwa, muka wuce high table, na zauna sannan ya zauna, duk abun da ake hankalina yana wani wurin saidai murmushi da nayi keeping akan fuskata wanda yayi min kyau matuk'a, lokacin da ake cashewa nak'i cashewa saida besties dina suka sakani tsakiya sannan na soma cashewa ina daukar steps ina silent dariya, kallon wata mata nayi tana magana tana kallona kuma daga gani ba maganar arziki take ba, ina karantar bakinta na fahimci abun da take cewa, cewa take....
"Fitsararriya koda kunya bata ji tana rawa haka, kyau babu kyan gani, son abun duniya...".
Na share na cigaba da cashewa abuna, ashe na iya rawa, ranata ce, gwara in cashe aiko nasha liki, en course dinmu sunzo har da mazan, nayi introducing dinsu ga Mahmud, wannan babie cousin din Mahmud ta karaso da murmushi akan fuskarta tana min magana kasa-kasa tace,
"Kin gani, ai dama na fad'a maki koda kina so koda baki so dole sai kin auri Yaa Mahmud...".
Sai kuma tayi gaba, ni har yanzu ban san sunanta ba, I feel inyi mata dukan tsiya, dawowa tayi saidai daga wani direction daban, da smile tace,
"Congratulation....".
Nayi mata wani kallo, tayi ma Mahmud magana sannan ta wuce, ana tashi sukayi dropping dinmu a gida, na gama shirin kwanciya wayata tayi ringing na jawota ina dubawa naga Aaryan ne, picking nayi tareda kangawa a kunne, kusan raba dare mukayi muna waya sannan ya kyaleni na kwanta bacci....
Thursday aka yi wa'azi, tou ranar Friday aka yi Fulbe day na iya yaren fulatanci, kamar yadda nike jin yaren hausa hakanan nike jin fulatanci, sometimes dashi kawai Ummy takeyi mamu magana, shigar kayan Fulani aka yi, nima sune a jikina kuma sunyi suiting dina sosai, nasha heavy makeup tou nayi matuk'ar kyau....
Mahmud ya kasa dauke idanunsa daga kaina ni dariya yake bani, welcoming speech din guest da speech da nayi lokacin da aka tashi duk da fulatanci nayi....
Washe gari tunda safe Aaryan ya danno min call yana min magana cikin damuwa, baiyi hanging ba nima ina rik'e da wayar ina sauraronshi sometime ina magana, can yace,
"Baby biki babu gayyata ai ban san abun ya kai haka ba".
Nayi shiru yana magana kudinshi suna tafiya amma baiyi hanging ba, karfe biyu daidai ya sauke lumfashi sannan yace,
"Baby shikenan na rasaki...".
Sai kuma ya fashe da kuka, call din ya tsinke dif, saida naji gabana ya yanke ya fad'i, Jalaludden ne ya dannowa Jalila call ya sanar da ita cewa an d'aura, en matan dake cikin dakin suka dauki gud'a, ji nayi kawai na soma hawaye, na jawo paper da na rubuta ina karantawa a cikin zuciyata....
"Assalamu Alaika, Yaa Ahmad na sani kana kallona ne a matsayin wadda ta nuna maka taurin kai akan saurayi, kana kallona a matsayin wadda ta fifita saurayi a kanka, kana ganin kun nuna min so fiye da komai ni kuma nayi maku haka, saidai sam ba haka bane, Yaa Ahmad kai shaida ne akan ban tab'a maka rashin kunya akan Aaryan ba saidai inyi shiru, kasan dalilin da ya saka nike shiru saboda babu wanda ya fahimceni koda nayi magana ba amfani, tou duk da kun san abun da Mahmud yayi min amma kunfi fahimtarshi a kaina, kasan dalilin da ya saka nace na fasa auran Mahmud amma sam baka san dalilin da ya saka na cigaba da kula Aaryan ba, yanzu zan fad'a maka, saboda yana matsalar zuciya kuma yana matuk'ar sona, akwai wadda yake so tare suka tashi karshe ta b'ace, ya hadu dani rayuwarshi ta samu d'an daidaita, danginsa suna yawan rokona akan kadda inyi hurting, abun kadan zai iya sawa zuciyarshi ta buga, ta dawo kuna son in rabu dashi farat daya saidai bana san akan abun da bashi da laifi ya rasa ranshi, nice da kaina na hana yayi introducing kansa, yana da matsalar zuciya abu kadan zai iya sawa zuciyarshi ta buga ya rasa ranshi, yana da k'anne mata tagwaye da mahaifiya, mahaifinsu ya rasu, marayu ne, a gefe guda masoyiyarshi ce Aalima, har gida tazo tana rokona akan in taimaka masu kadda su rasashi, saboda ni saida ya kwanta asibiti ya kusa rasa ranshi, dukkaninsu kuka suke, idan ya rasa ranshi nice sila and bana san saboda ni innocent Aaryan ya rasa ranshi, wannan shine abun da bana so shiyasa na cigaba da kulashi amma kayi hakuri... Yaa Ahmad wannan shine abun da nike so ka sani...".
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak Mahmud fans, Aallah ya albarkaci rayuwarku, wish you all the best....*
*Hope kunyi sallah lafiya baby fans, tou ina jiran barka da sallah na, wish you all the best....*
Page. 20
Na goge hawayen dake fuskata sannan na linke paper din tareda shiga bathroom nayi wanka da yake yanzu ina gidansu k'awata ne dake nan kusa damu, can muke ni da k'awayena, bayan na fito na saka wani expensive less dinkin riga da zani, makeup artist tayi min applying makeup bayan ta murza min daurin kallabi, ta zuba min jeweleries, Maa shaa Aallah, nayi kyau looking muah, a kauyenmu aka d'aura auren, Yaa Ayan baizo wannan bikin ba saboda kudin transportation kansu aiki ne amma Yaa Mustapha yazo tareda abokanshi likitoci, Yaa Ahmad da Yaa Mustapha anko sukayi, farar shadda mai kyau....
Tareda k'awayena ne muka fito tsakar gida muka sha selfie, tou ni bani da waya mai selfie, munyi hotona na card da na waya tareda video clip, muka koma daki, khairat wadda a gidansu ne muke tace,
"Bindawa wakokin bikin nan guda nawa ne?".
Bindawa tace, "Guda ukku ne kuma dukkaninsu babu ta banza, bud'e xender inyi maki sending amma sending zakiyi inyi receiving...".
Bayan angwaye sun dawo daga daurin aure muka wuce gidanmu suka shigo tareda en uwansu en mata aka yi hotuna da selfie, nayi da Yaa Ahmad, nayi da Yaa Mustapha, sannan aka yi mamu mu ukku sukayi hugging dina kowane ya bani peck a kumatu muna dariya, wata farar shadda Mahmud ya saka dinkin babbar riga yayi matuk'ar kyau, mun sha hotuna har da uwaye da en uwa, mukayi ni da Nadiya da brothers dinmu tareda Affan and Najib, nayi ina rik'e da Affan shima shi da Najib the same shadda suke sanye da ita irinta su Yaa Ahmad, anyi masu babbar riga, dinkin daidai size dinsu, looking more cute and more cute, na rik'e hannun Yaa Mustapha gam, yace,
"Miye?".
Nace, "Zo ka ji...".
Na jashi gefe tareda zaro paper din dake a linke na mik'a mashi, nace,
"Gashi ka ba Yaa Ahmad....".
Yaa Mustapha ya dubeni sai kuma ya amshi paper din ya saka a pocket din wandonsa sannan ya zaro wayarshi tareda jawoni na kwanta jikinsa ya kashe mamu selfie sannan yaja hannuna muka koma....
Mahmud ya kama hannuna na fizge yayi hugging dina, bayan sun tafi nayi zuru ina tunanin yau ne za'a rabani da gidanmu, na fashe da kuka, wuni nayi ina kuka....
Da daddare bayan nasihohi daga iyayenmu da en uwa, dakyar aka banbareni daga jikin brothers dina na makalkalesu ina kuka suna rarrashina, wata cousin dinmu tana ma Yaa Ayan recording, Aunty Usaina sister din Ummy dake aure a Kaduna ta jani sukayi waje dani ina waiwayen brothers dina ina kuka ina turjewa, ina ji ina gani aka rabani da gidanmu aka sakani mota za'a wuce dani gidan wani, motoci ne jere akan road din wata bayan wata, wasu saidai empty suka tafi, a cikin mota kuka nike har motar tayi parking aka fito dani, katon mansion ne mai girma, komai yaji, an zuba kudi babu k'arya, ina kuka aka jani aka wuce manya-manyan parlours dani aka wuce dani sama aka bud'e wani door aka shiga dani, shine bedroom dina kenan, aka yi min masauki akan gado nayi zuru ina sharar hawaye duk na b'ata heavy makeup da aka yi min applying, ni da k'awayena ne da en mata cousins dinmu muka rage a bedroom din, na d'age lullubi dake kaina, en matan suka kwashe da dariya, na kallesu da mamaki, tou kallona sukeyi suna dariya, Jalila ta mik'o min madubi na duba fuskata ta cikinshi zaro idanu nayi ganin yadda kwalliya ta zazzago ta maidani kamar horror, wani kallo nayi masu na duro daga saman royal bed din na wuce wani door wanda nike tunanin shine bathroom, ware idanu nayi ina kallon bathroom din wanda aka kashewa kudi ba kadan ba, yadda yake kamar a london, na shiga da addu'a na tsaya wurin madubi tareda bud'e famfo na tari ruwa a hannuna ina wanke fuskata saida na wanke makeup din tas sannan ta fito na kwanta akan doguwar kujera, Mahmud ya aiko min da waya, Yaa Ayan ne yake kira, video call yayi min, d'an uwa kenan mai dadi, raba dare mukayi muna video call idan yace zai tsinke ince a'a, saida na fara gyangyand'i sannan yayi hanging call din, na mik'e tareda fadawa bathroom nayi wanka tareda alwalla na fito na bud'e akwati daya da aka zo min dashi don sauran sai daga baya tukunna, wata doguwar gown mai hawa biyu na zura, short sleeves ce, tana da umbrella sannan kamar yadda nace a baya hawa biyu ce saida na saman daga wurin umbrella din a tsage yake, nayi kyau sosai, na had'e gashina nayi mashi gammo na tamke kaina da veil sannan na koma saman doguwar kujera nayi kwanciyata, su Jalila suna akan gado suna hira abunsu suna catching fun, Affan ne ya fad'o min a rai, Aallah sarki lil brotherna lokacin da zanyi bankwana da Ummy da yaga ina kuka shima sai ya fashe da kuka, ina jin en matan suna cewa ga chicken ango ya kawo nayi banza dasu, bacci ne yayi awon gaba dani....
Washe gari muna gama sallar subh na shiga bathroom na murje jikina da sabula masu kamshi sannan na sakarma kaina shower na jawo towel na d'aura tareda karasawa gaban madubi nayi brush sannan na fito na goge jikina tareda drying long gashin kaina na had'eshi da mayuka daban-daban masu kamshi mai sanyi, na shafa cream na goge fuskata nayi applying kwalli kawai, wasu riga da zani na atamfa Super English na saka, dinkakkarta aka sakata cikin lefe, style din ya tafi dani, early in the morning Safeena da wasu en mata suka kawo mamu breakfast mai rai da lafiya, bayan munyi breakfast kowace tasha wanka muka kashe selfie, muka fita balcony dake wajen wani door dake lullub'e da curtain muka sha selfie, wajen karfe sha biyu na k'ara wanka na saka wata bubu ta wani material mai sulbi amma daga gani yana da tsada sosai, abinci mai rai da lafiya suka k'ara kawo mamu, nikam kadan naci....
Da marece nayi wanka na saka wani expensive less, makeup artist tayi min applying makeup na koma kamar wata aljana saboda kyau, nayi alwalla before tayi min kwalliyar, wow amma nayi matuk'ar kyau duk wanda ya kalleni sai ya k'ara, da motoci aka daukemu aka wuce damu gidansu saboda a can ne za'ayi walima, a kuryar Ammi aka wuce dani, ita kam bani da damuwa da ita amma sauran dangin Mahmud tun daga kallon da sukeyi min nasan akwai damuwa don babu wacce takeyi min kallon rahama, wani kallo na daban suke min, suna ganin duk ciwon da Mahmud yayi laifina ne, yana neman mutuwa amma ban tausaya mashi ba, wannan cousin dinshi ce ta shigo da fara'a ta zauna kusa dani tace,
"Our greatest bride kinyi kyau, bari inyi mamu selfie".
Wani kallo nayi mata, ta ware idanu sai kuma ta mik'e ta fice, can ta dawo tana tafiya tana rausaya jiki tace,
"Amaryar Mahmud kinsha kamshi...".
Wani kallo nayi mata ta karaso kusa dani tace,
"Ohhh so sad, tou ya kika iya? Dole kika aureshi, Ahhh har kin bani tausayi...".
Sai kuma ta mik'e tareda fadin....
"Alright then... See you... Bye... Ki huta...".
Ta juya ta fice tana wani turo baki na kilbibi, an gudanar da komai lafiya, an basu korai wanda iyayena sukayi sannan aka damka masu amanata, murmushi kawai sukayi babu wacce tace ta dauka hakanan babu wacce take min kallon rahama, tunani nike, how zanyi surviving a cikin wannan dangin wanda bana ganin sona a tattare dasu, motoci hudu suka bani, daya Ammi, guda biyu wasu sunaye aka fad'i su suka bani guda daya-daya sai kuma uncle dinshi da ya bani katuwar Jeep, a can nayi both sallar magrib da isha'i sannan Aunty Usaina suka wuce dani gidan mijina, ashe en mata sun amshi kudadensu, dubara sukayi min amma kowace gidansu ta wuce, muna isa nayi wanka na saka wasu expensive kaya, makeup artist tayi min applying makeup sannan ta feshena da different design din perfume masu wani kamshi na musamman sannan ta wuce, Jalila ce muka zo tare itama Jalaludden ya kirata cewa yazo daukarta ta mik'e nayi rau-rau da idanu ta girgiza kai sannan ta wuce, nayi zuru ni daya tunda su Aunty Usaina sun wuce, can naji muryoyin maza har dariyarsu ina jiyowa, wani abu na tuna saida cikina ya bada kululu, yau kam na mutu, tawa ta k'are, Mahmud ne ya shigo yana sanye da wani expensive yard komai fari ya saka looking muah yana zuba wani kamshi mai sanyi, da sallamarsa ya shigo tareda haurowa saman gadon kusa dani, nayi baya da sauri, yace,
"Miye?".
Nace, "Bacci nikeji, ka barni inyi kaji...".
Mahmud ya kunshe dariya sannan yace,
"Naji amma sai idan kinyi duk abun da na umarceki".
Na kalleshi yace,
"Yeah... Ohhh ashe har yanzu kallon makaryaci kikeyi min, bari in ajiye wadannan kajin, uhmmm fad'a min yadda aka yi na zama makaryaci don ban san mu fara rayuwar aure kina min wani kallo wanda bashi bane, ina son mu fahimci juna".
Na kalleshi sai kuma na jawo wayoyina guda biyu baby Nokia da kamarar waya mai gidan memory, d'ayar na dauka wadda take da memory, na kunnata tareda kunna mashi recording, wayar da mukayi ce wadda yace min shi staff ne, abun mamaki gani nayi ya kwashe da dariya sai kuma ya amshi wayar yace,
"Dama saboda wannan kika cemin makaryaci, *BA NI DA LAIFI* amma kika dauki alhakina, tsaya kiga, ki manta da muryata ki saurari wata murya dake magana kasa-kasa".
Sai kuma ya kunna, muryarshi ce ta soma fitowa yana cewa....
"Kullum ina ganin Abba...".
Then muryata ina cewa....
"Tou ai wurin aikinku daya...".
Then sai naji wata muryar namiji kasa-kasa yana cewa....
"Miye matsayin Muneer a ma'aikatar?".
Then Mahmud yace,
"Ai staff ne...".
Kusan lokaci mukayi magana ni da daya muryar namijin, nace,
"Ohhh kai staff ne?".
Yayinda daya muryar dake fita kasa-kasa tace,
"Ashe staff ne...".
Then Mahmud yace,
"Ehhh staff ne...".
Mahmud ya kashe recording din yace,
"Yanzu na wanke kaina, ni ba makaryaci bane, uhmmm".
Na zaro idanu ya ja kumatuna tareda sakin murmushi yace,
"Baby rigima....".
Sai kuma ya rik'e hannuna ya zubawa tafin hannuna idanu kamar wanda yake karanta handout mai kananan rubutu, na kalleshi, yace,
"I like this henna...".
Ya kalli kafata yace,
"Har da na kafar...".
0 comments:
Post a Comment