Page. 21
Na dubeshi ya d'ago ya saki murmushi yace,
"Kinyi kyau... You look muah...".
Sai kuma ya yaye veil dake kaina tareda janye kallabin da na tamke kaina dashi, ya warware gashina yana wasa dashi, yace,
"Ina son gashin nan, ashe haka yake da tsayi sosai, da alama idan kika tashi tsaye zai iya wuce gwuwarki".
Ya jawo waya ya kashe mamu selfie, da wayo da dubara ya cire both jeweleries dake jikina, sannan ya mik'e yace,
"Wayarki tana bedroom dina, da safe zan baki ita...".
Ya cire kayan dake jikinsa ya rage daga shi sai d'an karamin wando (skin tide karami), ni kunya naji na rufe idanu, tou bashi da riga daga shi sai wannan d'an guntun wando, duk da brothers dina suna zama da boxer amma basu yawo babu riga, a rayuwata ban tab'a ganin babban namiji a haka ba, ji nayi ya sureni, idanuna a rufe na soma dukanshi a kirji ina mutsu-mutsu, ina bud'e idanuna ya bud'e bathroom ya shige da ni, duk rigimata amma saida ya danneni yayi min wanka, saida mukayi alwalla sannan muka fito ina turo baki daga ni sai guntun towel daidai kugu, farar jallabiya ya zura ya jawo wata farar half gown yayi min dropping dinta yace,
"Ki saka...".
Na d'aga farar half gown din, ina k'are mata kallo sannan nace,
"Kalli yadda take, Aallah bata da maraba da matacin da nike tace kullun koko dashi...".
Mahmud ya ware idanu yace,
"Yeah... Kuma idan kikayi min musu babu ke babu bacci har a kira sallar subh, kin gani am strong...".
Na zaro idanu while shi kuma ya wuce ya zauna gefen gado tareda jawo wayarshi yana sarrafata, yace,
"Kiyi sauri, akwai hijab a closet...".
Na jima ina drying dogon gashina da hand dryer sannan nayi mashi gammo, naga under wears farare abun haushi bra da pant ne kawai, saida na sakasu sannan na zura gown din na karasa da sauri na bud'e closet na jawo long hijab na zura....
Mahmud ya mik'e ya shimfid'a mamu sallaya ya jamu sallah raka'a biyu yayi addu'o'i sosai sannan ya dafa kaina yana jero addu'o'i, leather da ya shigo da ita ya jawo sai kuma ya mik'e ya fita jim kadan ya dawo yana dauke da tray wanda yake dauke da plate, glass cup, fork and knife, ya zauna kusa dani yace,
"Remember babu musu babu gardama or else...".
Sai kuma yayi shiru tareda sakin wani wicket smile, kaji ne masu zafi da lemu mai sanyi, da wayo da dubara ya sakani na cika cikina, na kora da lemu, shima ya cika cikinshi ya kora da lemu, nayi zaune ya tattara abubuwan da muka b'ata ya fice jim kadan ya dawo ya jani bathroom mukayi brush, light off yayi ya jani wani room, royal bed ne a ciki wanda yake dauke pure white blanket, da pillows kusan guda shidda, ya saki hannuna ya karasa ya kashe light ya rage saura light dake gefen both bedside drawer ne kawai, ya zare jallabiya dake jikinsa ya rage dashi sai farin guntun skin tide, ya karasa gefen gado ya kwanta tareda kallon gefe, nayi tsaye, ji nayi yace,
"Kadda ki sake ki kwanta da hijab or else uhmmm".
Saida cikina ya bada kululu na kalleshi naga ba ya kallona, da sauri na cire hijab na karasa da sauri na kwanta saman gadon a daya side din, tsoro ne ya kamani na juyo ina kallon bayanshi, can na lumshe idanuna, ashe wayo yayi min saidai jin mutum nayi ya shiga jikina, duk kuka da rok'o da nayi mashi amma yayi min banza, wata k'ara na kwalla, nasha azaba, I feel Mahmud kasheni ka huta, rama abun da nayi maka kake, bayan ya gasani ina kwance saman doguwar kujera ya yaye bedsheet wanda ya b'aci da jini ya linke ya saka cikin wata leather, ya sauya bedsheet ya karaso ya daukeni ya wuce dani akan bed ya kwantar dani shima ya kwanta ya jani jikinsa, babu b'ata lokaci bacci yayi awon gaba dani, a hankali yace,
"Aallah yayi maki albarka...".
Sai kuma ya rufe idanunsa tareda min peck a kumatu, yayi hugging dina sosai....
Washe gari da asuba ya tadani, kallon gefe nayi na wuce ba tareda na kalleshi ba, yace,
"Baby babu magana...".
Na wuce bathroom da sauri ina dingishi, ya kwashe da dariya, lokacin da na fito ba ya nan, da alama masjid ya tafi, na zura hijab tareda shimfid'a sallaya na tada sallah saida nayi raka'atanul fijr sannan nayi sallar subh, ina zaune ya shigo na kalli gefe, yace,
"Kunya...".
Sai kuma ya karaso tareda zama kusa dani, nace,
"Ina kwana?".
"Lafiya lau....".
Nayi zuru, yace,
"Miye?".
Nace, "Kayi hakuri don Aallah...".
Yace, "Mi yasa lokacin baki saurareni mukayi magana ba?".
Nace, "Tsoro nike kadda ka karantani...".
Yace, "Ya jikin?".
Na kai mashi duka a kirji nace,
"Ina kuka ina rokonka kayi banza dani, idan na mutu fa".
Mahmud ya saki dariya sannan yace,
"Ramawa nayi, nima lokacin ina maki kuka ina rokonki kikayi banza dani, nima na kusa mutuwa".
Na ware idanu, yace,
"Yeah...".
A jikinshi nayi bacci na rikeshi gam shima a nan bacci yayi awon gaba dashi, lokacin da na farka na ganni a jikinshi, kallonshi nayi yace,
"Good morning...".
Na mik'e zaune sai kuma na kalli gefe na mik'e, ya jawoni tareda hugging dina, nace,
"Please...".
Ya bani peck a kumatu yace,
"Guduna kike?".
Na turo baki ya sakeni yace,
"Kiyi kwalliya mai kyau and kadda ki manta uhmmm".
Ya kalleni, ina dingishi na wuce bedroom dina, towel na dauka na wuce bathroom saida na gasa jikina a bathtub sannan na saki ruwan na tara wasu na murje jikina da kumfa, na saki shower, na jawo towel na daura sannan tayi taking steps zuwa wurin mirror nayi brush, na fito na samu wata fitet gown akan bed na kalleta na wuce gaban mirror saida na shafe jikina da cream sannan na goge fuskata da powder, hakanan naji ina sha'awar inyi makeup, nayi applying mascara da lipstick shikenan, ina k'ok'arin daure gashina naji muryar Mahmud daga bayana yace,
"Ki barshi yadda yake, kadda kiyi mashi gammo...".
Da sauri na juya ina kallonshi, tou yaushe ya shigo, waving hannu yayi min yana smile na juyo tareda kama gashina na saka mashi band na rage mashi tsayi nayi mashi design mai kyau, so cute, nace,
"Yaushe ka shigo ban gani ba?".
"Kina can kina tunani na shigo, ko tunanin mey kike? Oho, Idan nine kadda kiji komai ki sanar dani kawai, ai am all yours...".
Na zaro idanu ya kwashe da dariya, pure white shirt, short sleeves mai circle neck ce a jikinsa tareda cotton trouser three quarter, nayi shiru kawai nayi taking steps na dauki fitet gown din na juya tareda shigewa bathroom na sakata bayan na saka under wears, fitowa nayi na dauki kallabi tareda murza dauri irin ture inga tsiya din nan (irin na soffinmu, hhhh, lols), Mahmud ya mik'e tareda taking steps zuwa bayana yayi hugging dina ta baya tareda turo kanshi gefen fuskata yana sauke lumfashi yace,
"Kinyi kyau...".
Nace, "Kai kuma kayi muni...".
Ya ware idanu yace,
"Na gode...".
Nace, "Nima na gode...".
Yace, "Breakfast is ready...".
Na zaro idanu nace,
"Don't you think zan ci abun daka girka, ba zan ci abun da namiji ya girka ba, ban shirya amai ba, brothers dina duka babu wanda na yarda ya iya girki".
Ya kwashe da dariya sannan yace,
"Aiko dura zanyi maki...".
Nace, "Ni kuma inyi maka amai a kaya..".
Yace, "Sai in sauya wasu...".
Nace, "Ni kuma in girka wani inci in hanaka...".
Yace, "Then we will see...".
Ya sunkuya saidai ji nayi yayi sama dani ya juya baya, na zaro idanu, ya kwashe da dariya yace,
"Matsoraciya kawai, tou mey kike tunani? Ohhh na gani...".
Na rufe mashi baki da sauri, ya juya ya fice yana dauke dani ya sauka downstairs ya wuce dinning table ya ja kujera ya zauna tareda daura ni akan cinyarsa yayi serving plate daya, cup biyu, na kalli delicious breakfast din sannan nace,
"Don't you think zan yarda kaine ka girka wannan delicious breakfast din...".
Mahmud ya ware idanu sannan yace,
"Amatullah ce ta kawoshi, shikenan, ai idan ba kici girkin namiji ba, kin ci girkin da baki san wanda ya girkashi ba".
Tare mukayi breakfast muka wanke abubuwan da muka b'ata, ya sureni yayi sama dani, wani door ya bud'e ya shiga, da alama bedroom dinshi ne, ya saukeni akan sofa tareda dauko wata expensive waya cikin kwalinta ya mik'o min, yace,
"Wayarki ce, akwai sim card a cikinta...".
Na amsa tareda sakin murmushi nace,
"Na gode...".
Yace, "Aallah yayi maki albarka...".
Nace, "Aameen....".
Sai kuma na zaro idanu ganin ya dauki leather dake dauke da bedsheet din jiya, da sauri nace,
"Ka barshi zan wanke da kaina...".
Ya ware idanu yace,
"Ammi zan kaimawa kuma dole ne...".
Na mik'e da sauri tareda zaro idanu na dafe kai, da karfi nace,
"No zaka tona mamu asiri...".
Mahmud yayi dariya tareda min waving hannu ya fice ya barni tsaye ina kafkafta idanu, bayan wasu mintina wayar dake hannuna tayi ringing, Ummy ce take kira, da sauri nayi picking ina murmushi, bayan mun gaisa tace,
"Baby mey kikayi Ammin Mahmud ta kirani tana zuba min godiya...".
Na zaro idanu yayinda cikina ya bada kululu, I feel kasa ta tsage in shige, muryata tana rawa nace,
"Bedsheet ya kai mata...".
Daga daya bangaren Ummy tace,
"Bedsheet kuma?".
Na rumtse idanu nace,
"Ehhh... Ehhh... Bedsheet mai jini...".
Sai kuma kunya ta kamani nace,
"Ummy shine babu ruwana...".
Daga daya bangaren Ummy tayi dariya sannan tace,
"Tou ina ruwana, ai mijinki ne, see you silly girl...".
Tayi hanging call din, da alama itama kunya taji....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest Ayusher and Mardiyya, Aallah ya albarkaci rayuwarku, wish you all the best....*
*Hope kinyi sallah lafiya Mrs Kamil, wish you all the best....*
Page. 22
Kamar zanyi kuka nike kallon wayar na maida lumfashi tareda yarfe hannuwa na dafe kai nace,
"Wannan abun kunyar da mey yayi kama, shikenan duk sun san komai...".
Na soma kaiwa da komowa kamar wadda ta soma hauka....
"Mahmud ya kasheni, Aallah kuwa...".
Saida na gyara bedrooms din sannan na sauko kasa na shiga parlour tareda kwanciya akan doguwar kujera na dauki remote ina sauya channel na samu wata channel suna turkish series amma maganar an saka ta turanci, series din ya tafi dani sosai, kuma nayi sa'a a ranar suka fara haskashi, sun gama suka soma wani program, bacci ne yayi awon gaba dani, a hankali na bud'e idanuna jina nayi a jikin mutum na d'aga kaina da sauri naga Mahmud ne, na mik'e zaune nace,
"Yaushe ka dawo?".
Yace, "Kina bacci na dawo, sleeping cute...".
Wannan cousin din tashi na gani a gefenmu, na ware idanu ina kallonta, tace,
"Ina wuni? Nace zan tafi ya hanani wai in tsaya mu gaisa...".
Nayi mata wani kallo, Mahmud yace,
"Baby rigima, tou ba waccen bace, er biyunta ce, twins ne".
Na zaro idanu abubuwan da suka faru suna dawo min a kai, na dubeta sai naji kunya ta kamani, nace,
"Kiyi hakuri na dauka itace, tou bamu shiri ne".
Babie din tayi murmushi tace,
"Babu komai, sunana Amatullah Abdullahi ita kuma Amaturrahman, nice Hassana, Yaa Mahmud cousin dinmu ne, da late Abbu da dadynmu same father same mother suke...".
Nayi murmushi nace,
"Sunana Mariam Yusuf amma kowa da Baby yake kirana".
Ta gyad'a kai, na kalli wall watch nace,
"Zanyi sallah...".
Na mik'e na haye sama na wuce bedroom dina saida nayi wanka sannan na dauro alwalla na fito na shafa cream tareda gyara fuskata na saka riga da wando en kanti masu kamar biri da wando, design din mai kyau, nayi kyau sosai, hijab na zura tareda shimfid'a sallaya na tada sallah, bayan na sauko na tarar bata nan, da mamaki nace,
"Tana ina?".
Yace, "Ta tafi, dama lunch ta kawo mamu".
Nace, "Ohhh I thought zata shigo tayi sallah".
Tare mukayi lunch ya sureni ya wuce dani garden ya jefani saman wani shillo yard ya bini ya danne yana dariya....
Tunda gari ya soma duhu hankalina ya tashi, a tsorace nike dashi, nayi tsuru-tsuru dani, bayan sallar isha'i muna zaune a parlour muna kallo ya kashe kallon ya sureni before yayi light off sannan yayi sama dani, a bedroom dina ya direni ya zaro wata shedaniyar half night gown ya ajiye min yace,
"Ki sakata ki sameni a room din nan kuma idan kika shanyani uhmm, I love you...".
Ya juya ya fice, na turo baki nace,
"I love you din banza, ace maka I love you a nemi kasheka da mugunta" (hhhh lol)....
Na rage kayan dake jikina na fad'a bathroom saida na murje jikina sannan na saki shower nayi brush tareda dauro alwalla na fito tareda karasawa gaban mirror na shafa cream kawai, na goge fuskata na saka bra da pant tareda zura gown din na feshe jikina da turaruka iri-iri sannan na fice, a hankali na kama handle tareda tura door din na shiga nayi tsuru-tsuru dani kamar ace kyat in gudu, yana kwance akan bed yana duba waya ya mik'o min hannu yace,
"Zo ki ji... Baby... Wow... Kinyi kyau... You look hot...".
Na b'ata fuska kamar zanyi kuka nace,
"I love you...".
Mahmud ya ware idanu tareda kwashewa da dariya yace,
"Miye?".
Nace, "Bacci....".
Yace, "Zo ki yi baccinki a jikina kinji baby na".
Da karfi nace,
"No....".
Gani nike wayo zaiyi min, trouser ne kawai a jikinsa shima boxer, yace,
"Alright then, zo muyi catching fun".
Nace, "Bacci...".
Ya dafe kai sannan yace,
"Ohhh baby rigima, zo in baki madara tou, in rirrigaki kiyi baccin...".
Na zaro idanu ya saki murmushi tareda durowa daga saman gadon nayi baya da sauri, yayi tako daya biyu ya sureni yayi sama dani, nace,
"No...".
Yana kallon gabanshi yace,
"Of course No mana...".
Ya kwanta akan gadon tareda matseni yaja mamu blanket yace,
"Shhhh kiyi baccinki ko kuma idan kika matsa min in sakaki baccin dole".
Nayi lamo a jikinsa, yace,
"Good girl...".
Bacci ne yayi awon gaba dani....
Washe gari da rana muna a bedroom nayi pillow da cinyarsa muna dariya, k'arar bell mukaji, yace,
"Lem me go and check, uhm bari in duba waye".
Na matsa da kaina, ya duro daga saman gado tareda zura jallabiya ya fice, jim kadan ya dawo yace,
"Su Aunty ne tareda Nadiya, zan tafi, ga kudi ki basu".
Sai kuma ya zaro wrapper din en five hundred ya mik'o min na amsa nace,
"Sun gode....".
Yace, "I love you...".
Nace, "Aallah ya k'ara bud'i...".
Yace, "Aameen...".
Sai kuma ya zare jallabiya dake jikinsa ya saka white vest tareda fiddo wani expensive yard ya saka tareda murza hula, ya zura takalma na jawo perfume na fesa mashi, yayi hugging dina na tureshi muka fito a tare suka sauko kasa yayi masu sallama ya wuce while ni kuma na zauna tareda gaidasu, lefena ne suka kawo tareda gara, nace,
"Nadiya... Ina Yaa Ahmad?".
Tace, "Yana gida...".
Nace, "Yace ki gaidani?".
Tace, "A'a....".
Na turo baki nace,
"Aiko zamu hadu, nima kadda kice ina gaidashi, kullum saidai ya dawo yace min basu jima da rabuwa ba".
Tareda Nadiya na shiga kitchen muka girka abinci suka ci sun jima sannan suka soma haramar tafiya, Nadiya ta mik'e, nace,
"Ke ina zaki? Tou dawo ki zauna babu inda zaki, tsayawa zakiyi ki tayani jera kaya a closet, ina zuwa...".
Na koma sama na jawo kudin tareda zare nata sannan na fito da sauran na basu....
"Gashi yace in baku...".
Dakyar na samu suka amsa, Aunty Usaina tace,
"Shine saboda shashanci baki fad'a mamu mukayi mashi godiya ba, k'anwarki ta fiki hankali".
Nadiya tace, "Nima tafiya zanyi...".
Nace, "Shikenan ki tafi amma babu Najib...".
Dole ta koma ta zauna, na rakasu har compound, ashe yace direba ya maidasu har gida, saida motar ta fice daga get sannan na koma ciki, na zauna ina ma Najib wasa yana wangale baki, hira muka sha na koma sama na dauko wayata na daukar mamu apples a bowl muka wuce garden muna ci muna having hilarious moment, saida muka sha selfie sannan suka koma ciki ta tayani na jera kayana a closet, wadanda suke ba dinkakku ba na barsu a cikin akwati muka jerasu a cikin closet din wanda yake kamar wani room, kamar kadda ta tafi, bayan munyi sallar asr na kirashi ya saka direba ya maidata gida, na bata kudinta, na dawo parlour na zauna....
Bayan mintina ashirin yayi knocking tareda sallama, Mahmud ne ya shigo yayi tsaye tareda ware hannuwa yana smile, na mik'e tareda rugawa da gudu na fad'a jikinsa yayi hugging kuguna tareda yin sama dani yana jujjuyawa muna dariya, ya saukeni tareda rik'e hannuna yace,
"Barka da gida...".
Nace, "Yauwa... Sannu da zuwa...".
Yace, "Yauwa amma na gaji, zo mu je sama".
Ya jani muka wuce sama, a tare mukayi both sallar magrib da isha'i sannan muka ci dinner da aka kawo daga gidan uncle dinshi, ina kwance nayi pillow cinyarshi yana duba waya na turo baki nace,
"Kaga Aunty tace wai Nadiya ta fini hankali, wai shashanci ban fad'a masu ba ballantana suyi maka godiya".
Yace, "Ayya sai ki daina shashanci tou...".
Na had'e fuska nace,
"Shine wato kaima ka yarda ni shashasha ce".
Ya ware idanu, nace,
"Kaga lokacin da zasu tafi, Nadiya zata bisu na hanata ta tsaya muka jera kaya a closet har mukaje garden muka sha selfie".
Na jawo wayata ina nuna mashi yace,
"Sunyi kyau...".
Nace, "Yauwa kuma....".
Yace, "Baby kiyi bacci ko kuma in sakaki kiyi dole".
Nace, "Ni ban jin bacci...".
Sai kuma na zaro idanu nace,
"No....".
Yace, "Ai kin makaro...".
Ina kokarin gudu ya kamoni ya danne, nace,
"Bacci...".
Yace, "No... Hira...".
Washe gari bayan munyi breakfast ya shirya zai fita har bakin mota na rakashi, yace,
"Take care...".
Nace, "Mey zan girka maka?".
Yace, "Delicious amma banda jagwalgwalo, ban cin jagwalgwalon yara".
Na turo baki, yace,
"Miye?".
Nace, "Ni ba yarinya bace...".
Smile yayi ya kama kumatuna yana jansu yace,
"Uhmmm ke baby ce shiyasa zan sawo maki madara, baby rigima zo mu je in rirrigaki kiyi bacci".
Na mak'e kafad'a yace,
"Alright then... Bye... Take care...".
"Aallah ya kiyaye... Aallah ya tsare...".
Yace, "Aameen...".
Sannan ya shige mota ya jata ina tsaye ina mashi waving hannu har ya fice da motan na koma ciki, wanka nayi na shafa cream tareda goge fuskata nayi applying kwalli, wata cute gown mai kamar bubu na saka na tamke kaina da kallabi, na sauko parlour nayi kallo sannan na shiga kitchen na dafa shimfid'a fara da delicious soup tareda pepper chicken, na had'a zobo na saka a fridge sannan na koma na tattarasu na jera komai akan dinning table sannan na koma sama nayi wanka tareda zura wata cute gown itama kamar bubu take, na gyara fuskata nayi applying powder then kwalli, na sauko kasa ina k'ok'arin daura kallabi, mace na hango akan dinning table tana cin girkin da nayi, har da zobo a gefe abun da na bari a fridge, ji nayi kamar in jawo ashar sai kuma na fasa nace,
"Wacece a nan?".
Yarinyar ta juya tana min wani kallo, Amaturrahman ce, cousin din Mahmud, na nunata nace,
"Ke....".
Tace, "Ehhh kuma babu yadda zakiyi, abincin gidan cousin dina naci, bari kiji zai iya sauyaki amma kinga ni babu yadda za'ayi ya sauyani, ni jininsa ce...".
Ji nayi raina ya gama b'aci nace,
"Sai ki bari idan shine ya girka da kanshi sai kiyi takama amma yadda kika tab'a min girki baki tambayeni hakanan zanyi maki dukan tsiya a gidan nan, wato don kinga kin bini har gidanmu kinyi min rashin mutunci kinci bulus shine kikazo gidan mijina kiyi min the same... Ohhh no yadda wancen na biyu kika sha mari hakanan wannan zaki sha duka".
Na jawo veil tareda daura kuguna dashi, na jawota nayi mata dukan tsiya, tasha kuka har da majina, na saketa ina maida lumfashi nace,
"Ohhh ashe iskancin naki na k'arya ne...".
Amatullah ta shigo tayi tsaye tana kallonmu....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak to all Muslim all over the world....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 23
Amatullah ta dubeni sannan ta dubi er biyunta dake zube kasa tana kuka har da majina, wani kallo nayi mata na juya na wuce ina jiran itama tayi magana in hada da ita, saman bene na haye na wuce bedroom dina, na fada bathroom na watsa ruwa na fito na shirya tareda zura wata cute black arebian gown mai adon gold, har na manta abun ina zaune a parlour....
Mahmud ne ya shigo a fusace yace,
"Baby kina ina?".
Na mik'e nace,
"Gani... Miye?".
A fusace yake kamar zai dokeni, yace,
"Uban mey Amaturrahman tayi maki kika doketa...".
Na rik'e kugu sannan na kalleshi idanu cikin idanu nace,
"Samuna tayi har gidanmu ta jefeni da kudi bayan ta fad'a min bakaken maganganu ta zageni sannan yanzu ta biyoni har gidan mijina tana min gadara shiyasa nayi mata dukan tsiya, tsaya ai har bina tayi bus stop ta jefeni da kudi ta zageni, Alhamdulillah wancen karon an shigar min tasha mari, hot one kuwa...".
Mahmud ya daka min tsawa yace,
"Keh wannan wacce maganar banza ce, kina hauka ne zaki kama d'iyar mutane ki jibga, nace uban mey tayi maki kika doketa...".
Haushi ya bani nace,
"Kai daina min ihu a kai, ita da na buga kaje ka tambayeta mana ai itama zatayi maka bayani tunda itama ai tana da bakin magana...".
Ya d'aga hannu kamar zai dokeni yace,
"Nace uban mey tayi maki kika doketa".
Nace, "Kai tsaya idan kai ubanta yayi maka wankan arziki ne kana tsoron kadda don na bugeta ya amshe abunsa, tou ni bana buk'atar komai a wurinshi don haka duk er iskar da tazo gidan nan tayi min iskanci sai na casata...".
Yace, "Kehh...".
Nace, "Ehh....".
A tsawace yace,
"Tambayarki nike... Uban mey tayi maki kika doketa?".
Saida na dubeshi idanu cikin idanu sannan da karfi nace,
"Ubanta ya saka na bugeta, mai dirty cap...".
Mahmud ya dubeni a fusace sannan ya d'aga hannu ya kwasheni da mari, na durkushe tareda fashewa da kuka, ya juya kawai ya fice, ina kuka har da majina na mik'e na wuce sama tareda jawo wayata na dannawa Yaa Ahmad call, yana picking na k'ara sound din kuka na, kuka nike har da majina, ya rud'e yana tambayata abun da aka yi min, saida naci kukana na gaji sannan nace,
"Tunda kun nuna mashi ya fini a wajenku ai duk abun da ya gadama yi min zaiyi, ka mareni a kanshi gashi yanzu shima ya dora a kai, cousin dinshi har gida ta bini tayi min rashin mutunci ta jefeni da kudi sannan ta bini har bus stop tayi the same thing amma daga yau tazo tayi min rashin kunya na nuna mata iyakarta shine ya mareni kamar yadda kasha marina a gabanshi kuma saboda shi, ai dama tunda yaga baku sona aikuwa sai abun da na gani a gidanshi, wato er uwarshi itace d'iya ni kuma daga bishiya aka tsinkoni".
Nayi hanging call din tareda fashewa da kuka, ina gani yana danno call nayi banza da wayar banyi picking ba, ashe kiran Mahmud yayi sukayi mahad'a, Yaa Ahmad yana zuwa ya d'aga hannu ya kwashe Mahmud da mari sannan yace,
"Na bugeta na mareta saboda nasan kai mutumin kirki ne zaka riketa saboda Aallah amma wannan bazai baka damar wulakantata ba, ina sonta, muna matuk'ar sonta itama d'iya ce".
Sai kuma ya juya ya wuce yabar Mahmud tsaye yana dafe da kuncinsa abunka ga fari har yatsu sun fito tar akan kuncinsa, nikam a lokacin ina zaune daki ina kuka can na mik'e na wuce bathroom na tara ruwan zafi na gasa cheek dina sannan na koma parlour ina matsar hawaye, Mahmud ne ya shigo ya zauna, kallo daya nayi mashi na lura da yatsu da suke kwance akan fuskarsa, a nan take abun da ya faru yazo min a brain, na fashe da dariya tareda mik'ewa na wuce toilet dake parlour na wanke fuskata na fito na tusashi gaba ina dariya har da rik'e ciki, nace,
"Aaahhh wato kai mai er uwa na bugeta ka mareni, tou ai nima ina da d'an uwa kuma ya rama min...".
Yayi shiru, na k'ara fashewa da dariya sannan nace,
"Aaahhh yasha mari, wai da a tunaninka ka mareni ka mari banza ka mari wofi, impossible, Aaahhh kato dashi yasha mari...".
Kanshi a kasa har yanzu baiyi magana ba, ina d'agowa na hango k'anwarshi Safeena a tsaye tana kallona idanu a waje, d'agowa yayi ya kalleta sai kuma ya ware idanu yana murmushi, nayi mata wani kallo na mik'e na wuce kitchen tareda bud'e fridge na dauko drinks da apples na jera a tray na wuce garden na zauna akan shillo ina kallon comedy ina kwasar dariya ina gutsirar apple ina korawa da drinks, can Safeena ta fito tareda karasowa inda nike tana kallona tace,
"Aunty Mariam na tafi...".
Na dago ina kallonta nace,
"Ohhh har zaki tafi, tou ki gaida gida kinji, idan direba yana nan kice mashi nace ya kaiki gida...".
Safeena ta kalleni sai kuma ta juya ta wuce, haushinta nikeji, cikin raina nace,
"Kema kin ci sa'a ne, da yanzu nayi maki dukan rakawa da kikayi aka yi min rashin mutunci...".
Saida na shan dariyata da comedy sannan na koma ciki....
Da daddare ya kwana dakinshi na kwana dakina, I feel babu dadi ga kadaici....
Washe gari na tashi ban ganshi a gidan ba, ashe zuwa yayi ya samu Yaa Ahmad suka daidaita kansu....
Da rana ina zaune a parlour ina kallon series ya shigo ya kalleni yace,
"Zo mu je sama...".
Idanuna suna akan kallon da nike nace,
"Azumi nike...".
Ya ware idanu yace,
"Amma a matsayina na mijinki ai dole ne ki fara sanar da ni".
Nace, "Sorry mantawa nayi...".
Kallona yayi sai kuma ya juya ya fice, ashe tarani yayi saida ya bari na kai azumin nasha ruwa nayi both sallar magrib da isha'i sannan ya nuna min kurena yayi min nashi hukuncin, I feel banyi mashi abun da nayi mashi ba, wannan ai mugunta ce tareda fin karfi, nasha wahala....
Washe gari bayan na gama had'a breakfast ya sauko mukayi ya mik'e na rik'e hannunsa nayi rau-rau da idanu nace,
"Please kayi hakuri..."
Kallona yayi yace,
"Bamu da damuwa yanzu, kinyi min nayi maki, one-one".
Sai kuma ya juya ya wuce sama ya shirya ya sauko yayi min sallama ya wuce, ina zaune Jalila ta kirani tana fad'a min zasu shigo ita da en course dinmu, da murnata na shiga kitchen na had'a masu delicious food tareda zobo na zuba mashi ice cube sannan na jera komai akan dinning table na juya na haye sama nayi wanka tareda saka wata black arebian gown mai adon skin din damisa, na tamke kaina da veil na sauko kasa, suna shigowa na mik'e tareda rugawa da gudu nayi hugging dinsu ina ihu tareda tsallen murna, bindawa tace,
"Kai amarya kin sha kamshi kinga kuwa yadda kikayi wani fresh dake, da alama d'an unguwarmu yana kula dake yadda ya kamata, miye sirrin?".
Nayi rolling idanu nace,
"Sirrin na matan aure ne ke kuma en mata ce, tou bazan fad'a maki ba".
Muka kwashe da dariya nayi masu jagora ciki muka ci abinci muka kora da zobo muka sha hira mukayi sallah sannan na sake wani sabon wanka na saka wasu riga da skirt na atamfa, rigar wrapper ce and hannun d'an short ne sannan a gaban rigar daga sama a tsakiya zuwa gefe an ratsa wani design, while skirt din yake pieces, powder kawai na shafa nayi applying kwalli da lipstick, na daura kallabi tareda zura takalma muka wuce garden muka sha hotuna da selfie kala-kala, iri-iri, design daban-daban, naba bindawa wayata ta daukeni ni da Jalila muna tsaye, aka yi min da Bintu, akan chairs muka zauna mukayi having hilarious moment yadda ya kamata can naja Jalila muka wuce sama muka barsu a parlour suna kallon series, bedroom dina muka wuce muka zube akan gado, tace,
"Baby kinji dadinki, kinyi kyau...".
Nace, "Na gode... Ya sweety?".
Tace, "Yana nan qalau yana gaidaki...".
Nace, "Ina amsawa, sweety mutumina... Jalila kin san mey?".
Jalila tace, "A'a sai kin fad'a...".
Nace, "Ashe hakanan na dauki alhakin Mahmud bashi da laifi, bari in kunna maki recording din kiji, ki saurara da kyau, ashe wani yake ma magana bani ba".
Na jawo wayata na kunna mata recording din ta ware idanu tana saurare yana karewa tace,
"Hakane, ashe bashi da laifi, har na fara jin kunyarshi, Aallah yaso banyi mashi rashin mutunci ba... Ya fita ne?".
Nace, "Ehhh tunda safe ya fice...".
Na kirashi na fad'a mashi zuwansu, nayi hanging call din, nace,
"Jalila kin san Mahmud bashi da kunya, don rashin kunya ya dauki bed sheet na first night dinmu ya kaima Ammi ta kira tana ma Ummy godiya, Ummy ta kirani tana tambayar dalili, ita kanta Ummy saida taji kunya da na fad'a mata...".
Jalila ta kwashe da dariya, nace,
"Wannan container din kunyar har ina...".
Jalila tace, "Baby... Wai container din kunya... Ahhhh....".
Ta fashe da dariya, saida naji haushi sannan ta daina muka sauko kasa na had'o masu kayan snacks da kayan makeup, Jalila ta sake sabuwar mota mai kyau muka fito na ganta na nuna masu motocina guda hudu, muka koma ciki, suna gab da tafiya Mahmud ya dawo, dukkaninsu mutanenshi ne, babu wacce bai sani ba, ya zauna aka sha hira da dariya, lokacin da suka tashi tafiya ya basu kudi muka rakasu har wurin motocinsu, tou da motoci ukku suka zo, saida motocin suka fita daga get sannan muka koma ciki ya zauna saman kujera tareda jawoni jikinsa ya kashe mamu selfie, na lura dashi yana son daukarmu hoto don the more nayi wanka the more zaice baby zo inyi mamu selfie....
Washe gari tunda safe ya wuce, wanka na sake na fito na shirya tareda saka trouser na sport da shirt mai circle neck itama ta sport ce, a samanta na daura rigar sport mai zip wadda take had'e da hula, na had'e gashina nayi mashi linki biyu na kamashi da band, na zura takalman da sukayi suiting shigar tawa, I look more cute and gorgeous a wannan shiga, na fice garden na jawo wani sabon keke (bicycle) da na gani na hau ina riding dinshi ina dariya har da kashe selfie, lokacin da ina yarinya brothers dina suka koya min riding bicycle saboda dukkaninsu sun iya shine nima suka koya min, wani zuwa da Inna tayi ta gani ta hana, ashe har yanzu ban manta yadda ake riding bicycle ba, ina cikin riding bicycle wasu mata guda hudu suka shigo nidai ban sansu ba, kallona sukayi na kallesu sai kuma na juya da bicycle din na maidashi inda na daukeshi, na juyo nayi taking steps na duba compound ban gansu ba, na shiga ciki na tarar dasu zaune a parlour suna faman tab'e baki, na karasa da fara'a na zauna tareda gaidasu nayi masu sannu da zuwa sannan na mik'e na wuce na dauko masu drinks tareda snacks na kawo masu, tun daga kallon da sukeyi min naji babu dadi amma na share na zauna, nace,
"Saidai ban ganeku ba...".
Daya daga cikinsu ta tab'e baki, tace,
"Ai shi da yake d'an uwanmu zai ganemu".
Da murmushi nace,
"Hakane...".
Duk da na gane magana ce ta yab'a man, tuni na fahimci ina da damuwa da dangin Mahmud kuma duk abun da ya faru before aurenmu shine sila, na jawo wayata na kirashi yana picking nace,
"Assalamu Alaika... Ka dawo gida yanzu... Ka dawo kawai kaidai... Tou lafiya lau amma dai ka dawo yanzu...".
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak to all Muslim all over the world....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 24
Nayi hanging call din sannan nayi masu magana na mik'e na haye sama na wuce bedroom dina, saida na rage kayan dake jikina sannan na daura towel na wuce bathroom na jima ina wasa da kumfa sannan na murje jikina da sabula masu kamshi, shower na sakarwa kaina na matsa tareda daura towel na karasa gaban mirror nayi brush na fito na karasa gaban mirror naja stool na zauna tareda daukar hand dryer nayi drying gashina mai tsayin gaske na hadeshi da mayukan hair masu kyau irin na arebian people sannan na shafa cream na goge fuskata da powder nayi applying kwalli da lipstick, na dauko wani riga da zani na atamfa na saka nayi kyau sosai, na tamke kaina da kallabi tareda zura takalma flat na fito na sauko kasa na tadda Mahmud tare dasu, yayi introducing dinsu a matsayin aunties dinshi, lokacin da suka tashi tafiya na amshi kudi wurinshi na had'a da snacks na basu....
Da kanshi ya koya min mota na soma hawan daya daga cikin nawa, ya bani sabuwar laptop kirar kamfanin apple sannan ya siya min wata latest car, cikin haka ne naje gidansu, Ammi bata nuna min komai ba hakanan k'anwarshi Safeena, sun tarbeni da fara'arsu, na wuni sannan na koma gida, bayan kwana biyu naje gidanmu na wuni saida marece gab da magrib sannan na koma gida, cikin hakane na rink'a samun ciki yana zubewa (miscarriage), miscarriage dina ukku ciki har da en ukku (triple) daga baya kuma ban kuma samun cikin ba....
Ranar wata litinin na shirya na hau motata na wuce school, na fito daga Senate ina taking steps na hango suhail, abun mamaki sai naga yayi kamar bai ganni ba, zai gotani nace,
"Suhail ba magana ne...".
Suhail ya juyo da murmushi yace,
"Baby ya kike ya mai gidan?".
Nace, "Lafiya lau... Ya madam?".
Yace, "Tana nan kalau...".
Nace, "Ya Deena?".
Yace, "Tana nan kalau...".
Nace, "Nasan yanzu ta girma...".
Yace, "Hakane...".
Nace, "Ka gaida min ita da boy da kuma madam...".
Yace, "Sure...".
Nayi nodding head kawai na wuce nayi gaba while shi kuma ya shige ciki, saida na biya gidanmu sannan na koma gida, daman na fad'a mashi zan biya can, lokaci ya ja cikin hakane na gama komai jira kawai nike a saki list in wuce bautar kasa, bikin cousin dinshi ake don haka tunda wuri na shirya na wuce saidai babu wanda yake tani, kallon da sukeyi min kawai ya isheni, babu wacce takeyi min kallon arziki, sun wareni kamar ba auran d'an uwansu nikeyi ba, gulmace-gulmace iri-iri, wai hakanan Ammi ta bari ya aureni kyau babu kyan hali, tun kafin auren nike gasashi yanzu kuwa saidai abun da hali yayi, na nuna bana sonshi ya mak'ale min gashi yanzu don an raina mashi wayo da auranshi a kaina zan tafi in bar gari in shekara, gulma dai iri-iri, da na gaji da zaman na fito na shige motata na wuce gidan Nadiya nayi kwanciyata daman na fad'a mashi zan iya wucewa wani wurin idan ta kama kuma ya yarda, zamana nayi saida mijinta ya dawo sannan na kamo hanya na koma gidan bikin, da marece aka wuce da amarya gidan mijinta ni kuma na wuce gida, ina fuskantar damuwa daga dangin Mahmud amma nasha sanar da Ummy sai tace inji hakuri lokaci ne wata rana zasu daina kuma su kaunaceni, tace yanzu koda nahe hidimarsu sun wareni ni in shiga cikinsu ayi ta kai kawo da hidimar biki tareda hidimar guest tare dani, tou koda na samu damuwa dashi bana fada mata saboda nasan with time zamu shirya kuma zan iya fad'a ni in manta da abun while ita kuma tana kallonshi dashi, tou saidai cikin hakane list ya fito sunyi posting dinmu, sunyi posting dina a Kaduna, saida nayi sallama da en uwa tareda abokan arziki had'e da kawayena sannan na wuce tareda motata amma Jeep din, sister din Ummy Aunty Usaina a can take aure, munyi zaman camp before sukayi posting dinmu, a gidan Aunty Usaina nike zaune ina zuwa da motata, shekarata daya rabona da gida saidai Mahmud yana kawo min ziyara wasu lokuttan, bayan mun gama saida nasha gyaran jiki in side and out side tareda wata breathtaking henna da aka min design a both legs and hands, na shiga market sannan na kamo hanyar katsina, tou tareda da direba ta had'oni amma shi batagarawa ya shiga while ni kuma na shigo cikin gari, direct gidanmu na wuce, Yaa Ayan ya gama karatunsa hakanan Yaa Mustapha, sun sayi gidan dake bayanmu da wanda yake gefe da gefe aka rushesu aka k'era wani katon mansion amma flat ne, dakina yana nan sun zuba min expensive furniture da sauransu, ya koma kamar dakin wata sarauniya, a gajiye na fito daga mota na shige ciki, Ummy ta tarbeni da delicious girke-girke kala-kala, dakina na wuce na fad'a akan gado, brothers dina ne suka zuba min kayan, d'an uwa kenan mai dadi, wata rana kuyi dadi wata rana kuyi rashin dadi, saida nayi wanka naci abinci na huta nayi bacci sannan na wuce gida, na sameshi tsaf-tsaf Mahmud ne ya saka aka gyarashi, Nadiya taje ta gyara min bedroom, Mahmud ne yana tsaye a parlour na saki smile tareda rugawa da gudu nayi hugging dinshi ya dagani sama yana jujjuyawa dani muna dariya abunmu, yace,
"I missed you...".
Nace, "I missed you too...".
Yanzu kam nishad'i nike jina ciki....
Washe gari tunda na tashi da bacci a idanuna kuma sosai, na lallab'a na had'a mashi breakfast yayi ya wuce na koma sama nayi wanka tareda zura wata half night gown, na wuce garden tareda kwanciya gefen swimming pool babu b'ata lokaci bacci yayi awon gaba da ni, nasha bacci sosai, a hankali na bud'e idanuna, ihu na saki ganin kato tsaye a gabana daga shi sai guntun boxer, da sauri nayi baya saidai mey Mahmud na gani a tsaye totally speechless yana kallonmu, juyawa katon yayi ya gudu saidai Mahmud baiyi yunkurin komai ba, ni kawai yake kallo, na fashe da kuka shikenan anyi min bakin paint a idanunsa, da gudu na karasa inda yake na rik'e mashi hannu ina kuka ina girgiza kai ina fad'in....
"Ka tsaya ka saurareni abun da kake tunani bashi bane, nima bud'e idanu nayi na ganshi, ban sanshi ba...".
Mahmud ya daka min tsawa, nayi baya da sauri ina girgiza kai, Mahmud yayi murmushi tareda rik'e kafaduna yace,
"Baby kece baki yarda dani ba amma ni na yarda dake, na sanki nasan halinki nasan tarbiyyar da kike da ita, bari kiji koda bidiyonki na gani nasan had'ashi aka yi... Kin san dalilin da ya saka na dauki bedsheet dinmu na first night na kaima Ammi, tou saboda na tare da ita suna maki wani kallo ne saboda abubuwan da suka faru before auranmu ni kuma bana san ya kasance itama ta fara maki irin kallon, a lokacin ina ajiye mata bedsheet din na juya nabar gidan na tabbata idan ta gani tasan abun da yake nufi... Baby nayi maki ihu akan Amaturrahman ne saboda ina kokarin in gyara dangantakarki da dangina abun da kikayi kuma k'ara lalatata zaiyi, daga baya kuma fusatani kikayi na yanke hukunci cikin fushi...".
Sai kuma ya sakeni ya juya ya shige ciki, da mamaki nike kallonshi sai kuma nabi bayanshi da gudu, zaman lafiya muke babu fad'a babu damuwa, the more yake son abu the more zanyi mashi, the more ya nuna ba ya san abu the more zan barshi, saidai idan abun da yake so ya sab'awa addinin musulunci ne, wanda kuma ban tab'a fuskantar hakan ba, na samu hutu sosai nayi kiba sai tayi min muni, kowa abun da yake fad'i kenan, yanzu na tashi daga baby na koma bebilo, karamin ciki ne gareni ya tusani gaba da laulayi, yau lafiya gobe babu ita hakanan Mahmud yake fama da ni, har wata rama yayi ya fad'a....
Wata ranar alhamis wadda bana tunanin zan manta da ita, Mahmud ya shirya zai tafi kauyensu, har bakin mota na rakashi, hankalina sam bai kwanta da tafiyar nan ba, nace,
"Yanzu ba zaka fasa tafiyar nan ba...".
Mahmud yayi murmushi sannan yace,
"Baby zumunci zanje kuma zumunci yana da lada...".
Sai kuma ya sunkuya tareda sumbatar cikina yace,
"Ki kula min da little princess dina".
Nace, "Sure...".
Smile yayi yaja kumatuna yace,
"Yauwa good girl...".
Na turo baki sannan nace,
"Lallai wato erki princess ni kuma girl".
Mahmud ya ware idanu yace,
"Baby rigima... Uhmm kishi... Kin boni da erki kike kishi...".
Nace, "Ehhh ai so kake ta zama kishiyata tun kafin tazo duniyar".
Mahmud ya fashe da dariya yana kallona, yace,
"Tou nidai na tafi... Bye... Take care... Ki yafe nima na yafe maki...".
Nace, "Na yafe... Aallah ya kiyaye hanya... Aallah ya tsare...".
Yace, "Aameen...".
Tareda waving hannu ya bud'e mota ya shiga ya jata, ina tsaye ina waving mashi hand har motar ta fice daga get, na koma na zauna hakanan naji gabana yana faduwa sai kuma na fashe da kuka, jina nike babu dadi daga baya baccin wahala ne yayi awon gaba da ni, bayan na tashi na duba lokacin sallar zuhr baiyi ba, na bud'e *data* shine nike ganin labari cewa wasu mahara kimanin mutum talatin wadanda suke dauke bindigu sun shiga wani kauye a saman bikes sun kashe mutane sannan suka kwashe kudiyoyinsu, saida gabana ya yanke ya fad'i ganin sunan kauyensu Mahmud a matsayin kauyen da aka kai harin, neman kuka nayi na rasa nayi zuru kawai...
Yaa Ahmad ne ya fad'o gidan daga ganinshi ba ya cikin hayyacinsa, na fashe da kuka, ya wuceni ya haye sama jim kadan ya dawo yana rik'e da hijab, ya mik'ar dani ya zura min ita sannan yaja hannu muka fice ya sakani a mota while shi kuma ya zagaya side din direba yayi horn mai guard ya wangame mashi ya ja motan tareda ficewa da ita ya nausata akan flat kwalta dake shimfid'e akan road din, wannan itace fita ta karshe da nayi daga gidan ban k'ara komawa ba, yana driving ina kuka, kusan lokaci guda muka isa tare dasu Ammi, gawarwaki ne a kwance, na mak'ale a baya ina tsoron abun da zan gani, Ammi ta wuce tana taking steps cike da damuwa, yanayinta ya nuna itama ta daure ne kawai amma ita kanta tana fargabar abun da idanunta zasu gane mata, cin karo tayi da Mahmud kwance a cikin gawarwakin shima ya rasa ranshi a hannun wadannan mahara, baya tayi da sauri sai kuma tayi zuru saidai gani aka yi ta zube kasa bata lumfashi, ana dubawa aka ga she is dead ta mutu babu rai a tattare da ita, Safeena k'anwar Mahmud ta kalli gawar brother dinta sannan ta kalli gawar Ammi, yanke jiki tayi ta zube itama ana dubawa aka samu she is dead babu rai a tare da ita, zuru nayi na kasa koda hawaye, a hankali na soma tafiya gawar Mahmud na fara gani then ta Ammi sannan ta Safeena, Aallah sarki Safeena an saka mata biki da d'an uncle dinsu, wata daya ya rage ma bikin, durkushewa nayi yayinda jini yake bin kafafuna, tafiya nayi gajeran hutu na dawo daidai sai kuma na sume saidai farkawa nayi na ganni akan gadon asibiti har na kwana daya....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak to all Muslim all over the world....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
Page. 25
A hankali na bud'e idanuna, nayi zuru kawai, a bakin Ummy nike jin cewa cikin dake gareni ya zube har wankin ciki aka yi min, daga baya take sanar da ni mutuwar both Safeena da Ammi, tun jiya aka sallaci gawarwakinsu sannan aka wuce dasu gidansu na gaskiya, duniya kenan, shikenan baki dayansu sun mutu they were no more, na fashe da kuka, yanzu shikenan Mahmud, Ammi da Safeena duk sun mutu, matsawa nayi likita yayi discharging dina, kai tsaye na wuce gidan uncle din late Mahmud, a can ne ake zaman makokin, zama nayi nai zuru bana magana saidai idanu, ni kadai nasan yadda nikeji, ga mutuwar nan ga kuma ciwon ciki da mara, zaune kawai nike ina amsar gaisuwar amma bana magana, moment din da na kasance da late mijina Mahmud kawai nike tunawa, gashi yanzu ya mutu ba ya nan, he is no more, cikin da muke tattali ya zube, ashe bayan da maharan suka tafi ne aka kwaso gawarwakin aka tafo dasu cikin gari, a nan aka yi masu wanka, a inda mutanen garin katsina da kewaye dake tattare da wannan alhini suka halarci sallatarsu tareda wucewa dasu gidansu na gaskiya (wanda suke ganin cewa mutuwar Mahmud, Ammi da Safeena baiyi masu dadi ba, tou nayi hakane domin ku fahimci yadda dukkanin wadanda suka rasa en uwansa a wadannan hare-hare sukeji... Wadanda kuma suke jin cewa sunji haushin zubewar cikin da baby take dauke dashi, tou kamar hakane mutane da yawa suke rasa abun da suke matuk'ar so a dalilin wadannan hare-hare).....
Ranar lahadi aka yi sadakar ukkunsu wanda ya samu halartar mutane masu dumbin yawa, babu wanda zaice maka ga adadin mutanen, mutane ne bila adadin, Mahmud yayi mutane kuma duk wanda zai bud'e baki tou halinshi na kirki zai fad'a, kowa halayenshi masu kyau yake fad'i, tabbas Mahmud bashi da damuwa, ina kukan mutuwarshi ina mashi addu'a, idanuna sun koma wani iri, kallo daya mutum zaiyi min yasan nasha kuka ba kadan ba....
Washe gari da daddare na wuce gidanmu kusa da Ummy na, duk wanda zaiyi min godiya a can yake samuna, kullum ina daki sanye da hijab, daga wanka sai wanka babu kwalliya ko kadan, ba wai ina takaba bane, tou babu takaba a kaina, en uwanshi dake nuna basu sona tou ga mutuwa nan tazo ta daukeshi tareda mutane biyu da nike samun sauki daga gunsu, Aallah sarki duniya lokacin da ina yarinya karama ina yawan tunani akan idan na girma nayi aure koda mijin yana dukana ne zan hakura in zauna saboda kadda in fito a kirani bazawara, tou yanzu miye sunana amsar itace bazawara, kowace mace tana da kaddararta a rayuwa, kowane mutuwar aure yana da sila, wani lokacin baka da laifi, en course dinmu sunzo sunyi min gaisuwa....
Washe gari suhail yazo yayi min gaisuwa tareda matarshi suhailat, cikin hakane en uwan Mahmud suka fara maganar rabon gado, tou koda basu fad'a ba, na sani daga ni sai kayan jikina iyayena suka kaini sai kuma gara, tou lefena da sauran kayan sawana, motocina da sauran wasu k'ananan abubuwa kamar waya, laptop, iPhone, iPad, laptop, tou sune nawa sauran tarar dasu nayi....
Brothers dina tareda Nadiya sukaje suka dauko min kayana wadanda suka had'a da lefe, sauran kayan sawa, ATM card, laptop tareda sauran k'ananan kayan suka zo suka jibge min su, ina da ilimi koda ba'a fad'a min ba, na sani gadon Mahmud kawai gareni kuma both Ammi da Safeena suna da gadonshi tunda ya rigasu mutuwa, shi ba ya da gadonsu while Ammi take da gadonshi kawai while Safeena take da gadon dukkaninsu while ita kuma basu da gadonta tunda sun rigata mutuwa, ni duk maganar gadon nan ba ita bace a gabana, damuwa da nike tattare da ita ta mutuwar mijina itace take damuna har yanzu, kullum cikin damuwa nike da tunani, koda aka raba gado aka bani nawa fili Yaa Ahmad ya siya min a kusa da filin da ya siya min da sadakina, sauran kudin ya siya min gida, wadanda suka rage ya saka min a account....
Abba yana yawan zaunar dani yayi min nasiha akan hakuri da dangana, hakanan itama Ummy, Nadiya tana zuwa ta zauna tare da ni, hakanan brothers dina guda ukku suna yawan zama tare dani, Affan ya girma har an sakashi school, wasu lokuttan nakan dauko wayata in rink'a kallon hotunan da late Mahmud ya daukemu gasu nan da yawa sune suka cike wayata, damuwar dake raina ta taru ta saka na rame na koma kamar yadda nike lokacin da ina budurwa, tou yanzu na koma baby na tashi daga bebilo....
Ranar wata talata ina zaune akan kujera ina sanye da hijab, Jalila da Jalaludden ne suka shigo, na ajiye waya dake hannuna na d'ago kai, na bud'e baki da muryata wadda ta koma some how mai sanyi, nace,
"Jalila kece... Sannunku da zuwa... Sweety...".
Suka zauna a separate kujeru, sukayi min gaisuwa tareda jerowa Mahmud addu'o'in samun rahama a wurin Aallah, nace,
"Aameen... Na gode... Ansha biki babu ni...".
Jalila tace, "Abun nan bai jima da faruwa ba aka yi bikin, naje har can gidan saidai lokacin baki gane mutane...".
Na gyad'a kai kawai, can nace,
"Sweety don Aallah ka bar Jalila a wurina har zuwa dare...".
Jalaludden yace, "Indai wannan ne baki da damuwa...".
Tafiya yayi ya barta muka wuni, naji dadin zama da ita, har take cemin da ace cikin da nike dashi ya zauna sai in wanko hotunanmu ni da Mahmud dake a wayata, inyi album dinsu idan macece idan ta tashi aure sai in batasu kyauta, hakanan idan namiji ne idan ya gama karatu sai in bashi shi kyauta, saidai kash cikin ya riga ya zube, muna tare saida dare sannan yazo daukarta har mota na rakata wannan itace fitata ta farko daga gidan tun bayan dawowata, sai naga unguwar ta sauya ta koma man wata iri, saida naga tafiyarsu sannan na juya na koma gida....
BAYAN SHEKARA DAYA....
Ina zaune a daki, Yaa Ahmad ya shigo, kamar kullum hira muka sha, har ina tambayarshi matarshi da yake yayi aure, wata cousin dinmu ce mai kirki da ita ga kyau, har yayi min sallama ya mik'e sai kuma ya koma ya zauna, yace,
"Mariam....".
Na dubeshi, yace,
"Mariam zuwa wannan lokacin ya kamata ace yanzu kin sake aure...".
Kallon gefe nayi tareda maida hawayen dake neman zubo min sannan na juya na dubeshi nace,
"Idan kana ganin ya kamata inyi auren tou zanyi amma na baka zabi, ka zabar min da kanka, na tabbata ba zaka zaba min mijin banza ba".
Kallona yayi sai kuma ya mik'e ya fita, Yaa Ayan ne ya shigo nayi pillow da cinyarsa nayi kwanciyata, bacci ne yayi awon gaba dani, Yaa Ayan yanzu babban likita ne wanda ake ji dashi a kasarmu nageria da sauran kasashen duniya, ya kware sosai, kudi sun zauna mashi, komai nike so babu b'ata lokaci yake yi min, shima Yaa Mustapha kwararren likita ne sosai, fiye da tunani, shima kudi sun zauna mashi, shi kam ba ya jira ince ina so yana ganin abun da zaiyi min zai siya min komai tsadarshi kuwa, shima Yaa Ahmad bashi da damuwa, sakar man kudi yake sosai, yanzu su ukkun sune suke komai na gidan nan, shekarar data wuce suka biya ma Ummy da Abba aikin Hajji (pilgrim), nima cikin ramadan naje Umrah tare dasu har da Nadiya, nasan dalilin da ya saka Yaa Ahmad yayi min wannan maganar saboda mutane suna ta fitowa har da samari amma bana kula kowa....
Bayan kwana biyu ina zaune ya shigo, yace,
"Baby maganar da mukayi na samar maki mijin, yaushe zaizo ki ganshi...".
Da sauri na girgiza kai sannan nace,
"A'a ni bani da damuwa akan sai na ganshi, idan har don nice tou yayi zamanshi na hutar dashi, idan kuma shine zai ganni tou...".
Yaa Ahmad yace, "A'a ai shi ya sanki, daman saboda ke ne...".
Nace, "Then na hutar dashi...".
Yace, "Alright then, good girl, babynmu...".
Mahmud ne ya fado min a rai, yana yawan kirana good girl ko kuma yace baby rigima zo in baki madara in rirrigaki kiyi bacci, duk sai naji babu dadi amma duk da haka saida na saki murmushi zuwa yanzu idan naga hotonshi ko kuma na tuna happy moment da muka samu sai inji na saki murmushi, shiyasa wani sa'in hakanan saidai a ganni na saki murmushi, bayan sati biyu ya sameni yake sanar dani biki nan da wata daya, hidimar biki ake sosai, tou Yaa Ahmad ya fada min angon yace yana da komai, tou ni dayata za'a kaini, koda aka kawo lefe ina daki, lefe kamar na budurwa akwati rabin seti, akwati shidda kenan, akwatu nan expensive ne irin masu high price din nan kuma latest, kayan dake cikinsu dukkaninsu expensive ne, kowa ya gani saidai yace Maa shaa Aallah, wannan biki no party no bidia, wa'azi kawai za'ayi a gidanmu, tun before satin ciki nayi gyaran jiki in side and out side tareda sauran abubuwan da suka dace, tou ni koda invitation card ban gani ba, tou koda sunan angon ban sani ba (our greatest fans wa kuke tunanin Baby zata aura?)....
Ranar jumuah aka d'aura min aure da angon da har yanzu ban sanshi ba, ban san waye ba, tsoho ne ko yaro ban sani ba, saurayi ne ko babban mutum ban sani ba, matanshi nawa ban sani ba, tou a ranar ne aka wuce dani, gidan part ukku gareshi amma dayan karami ne da alama na mai gidan ne, aka wuce dani part dake gefe babba ne sosai don yafi wanda aka fara kaini, banbancin a bayyane yake, wani katon bedroom dake saman bene suka wuce da ni, ina ji ina gani kowa ya watse aka barni ni daya, gidan yayi shiru, can na soma jiyo sautin takon takalma sannan ya turo kofa ya shigo da sallama, zaro idanu nayi jin muryar da tayi sallama, Aaryan ne tsaye yana kallona, da sauri nayi baya jikina yana rawa, tsoro nikeji, gani nike abun da ya faru laifina zai gani, zaiga nayi broken heart dinshi ne, muryata tana rawa nace,
"Don Aallah kayi hakuri sam ni *BA NI DA LAIFI* a lokacin ban san maganar auren tana nan ba shiyasa na kulaka...".
Aaryan ya kalleni sai kuma ya juya ya fice, na zauna ina maida lumfashi, a tsorace nike sosai, duk da mun rabu lafiya amma gani nike laifina yake gani yana jin haushina, gidan shiru babu motsin kowa, dukunkunewa nayi a gefen gado jikina yana rawa, can na kwanta tareda dukunkunewa wuri guda naja blanket idan bacci ya figeni na farka sai inji tsoro ya k'ara kamani in dukunkune jikina yana rawa, tunda asuba na tashi nayi sallar subh sai kuma nayi zuru ina kallon wall watch can na mik'e na shiga bathroom nayi wanka ina fitowa....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest auta umarsanda, Aallah ya raya mamu kai... Aameen....*
*Hope kunyi sallah lafiya dearies, wish you all the best....*
0 comments:
Post a Comment