Page. 6
Na durkushe tareda fashewa da kuka, wannan wani irin abu ne duk da *BA NI DA LAIFI* amma an biyoni har gidanmu an zageni anci min mutunci, koda yake yanzu unguwarmu gulmata ake ko'ina suna cewa na samu mai kudi shiyasa na guji Mahmud yana neman mutuwa saboda sona amma ban damu ba, kudi sun rufe min idanu, duk zuwan da Aaryan yake wurina idanun magulmata yana a kai, the more yazo wajena suka ganni tsaye dashi the more zasu ce mayyar kudi, taga mai kudi mai kyau ta fasa auran talaka, tou ayi dai su gani idan tusa zata hura wuta, wai ita nan mai kyau, farin ne kawai ya ceceta, gulma iri-iri, da yawa maganganun suna dawo min amma ban damu ba, Aallah ya sani ba haka nike ba, ni kudi basu rufe min idanu ba, first wanda ya fara cewa yana sona babanshi mai kudi ne sosai shima yana dasu har kuka yayi min amma sam lokacin bana san auran mai kudi, ina ganin zai dauka na aureshi ne saboda kudinshi, gashi nan yanzu shi yaje yayi auranshi ni kuma ina nan talaka yana neman janyo min ciwon zuciya, yayi min k'arya amma kowa laifina yake gani bayan NI *BA NI DA LAIFI* sam, tunda na shigo Ummy ta shiga makotanmu, dawowarta kenan ta d'ago labule ta dubeni tace,
"Kukan mey kike?".
Nace, "K'anwar Mahmud ta rako cousin dinsu ta ci min mutunci".
Gani nayi ta saki labulen ta wuce, ina yawan tambayar kaina wai mi yasa kowa yake ganin laifina bayan k'arya yayi min, nikam bazan auri makaryaci ba, wuni nayi ina kuka saida nayi chatting da Aaryan sannan da salon barkwancinsa ya sakani farin ciki, shima wannan farin cikin washe gari tunda safe aka yi min spoiling dinshi, abun da ya faru shine takwas na safe nike da lecture din farko don haka tunda safe na wuce national ina tsaye gefen school bus ina waya da Jalila, abun da ya faru shine tun kafin in baro gida nayi waya da Jalila, shine na kirata take cemin tana cikin keke napep ta kusa zuwa wannan yasa naki shiga bus ina jiran tazo mu shiga tare, wannan babie din, ina nufin cousin din Mahmud, itace tazo wucewa ta hangoni, parking expensive car dinta tayi ta fito da alama da bala'i ta tashi, with anger ta tsaya gabana tareda rik'e kugu tace,
"Ke d'iyar talakawa....".
Na d'age niqab dita ne shiyasa ta ganeni, yadda tayi magana da karfi ya jawo hankalin tsirarun mutane dake wurin kasance da sassafe ne babu mutane da yawa, kallo ya dawo kanmu, nayi shiru kawai ina kallonta ta cigaba da cewa....
"Ke baki isa ba... Kudi ko? Don't worry you got it...".
Sai kuma ta zaro wrapper din en one thousand ta watsa min a fuska, I feel in fashe da kuka, Jalila ce ta shiga tsakaninmu tareda d'aga hannu ta kwasheta da mari, amma babie din ta maru sosai ta dafe cheek tana kallon Jalila, Jalila tace,
"How dare zakiyi mata haka? What did you think? Zaki ci bulus... Never... I said never...".
Sai kuma Jalila ta duk'e ta dauki kudin ta nuna mata sannan tace,
"Kin watsa mata su da wulakanci, yanzu zatayi kyauta dasu ta samu lada ke kuma kin k'are da mari".
Ta mik'awa wani mutum sannan taja hannuna muka wuce muka bar babie din tsaye tana dafe da kunci, muka wuce bus muka wuce inda napep suke parker, ina ji wani yana cema Jalila shine a layi ya nuna mata napep dinshi muka shiga, tace,
"Miye...".
Yace, "Akwai sauran wurin mutum biyu...".
Tace, "Muje, zan biya baki daya".
Ya shigo ya ja napep din, ni dai shiru nike ina shedding tears from inside cox na janyo niqab na rufe fuskata dashi, Jalila ranta ya b'aci sosai, tace,
"Mariam shiru-shiru da kike yayi yawa, kika sake sai wata ta janyo maki ciwon zuciya, yanzu banda nazo da barinta zakiyi ta wuce taci bulus...".
Shedding tears kawai nike babu sauti....
"Sunana Mariam Yusuf amma kowa da kowa da Baby yake kirana kasancewar dukkanin brothers dina maza ne zalla, lokacin da Ummy ta haifeni ta samu damuwa har ana tunanin ba zata sake haihuwa ba, wannan yasa suka dauki son duniya suka d'aura man, tou da yake haihuwa ta Aallah ce bayan shekaru biyu ta haifi Nadiya sai kuma Affan data dauki shekaru sosai before ta haifeshi almost tare da Nadiya suka haihu, duka watanni biyu ne a tsakaninsu, a lokacin Ummy tana da tsohon ciki Nadiya ta dawo wanka har saida ta koma sannan Ummy ta haihu... Both iyayenmu en katsina ne fulani farare sol shiyasa dukkaninmu muke farare sol don ni har naso in zama kamar zabayyana, Yaa Ayan dake karatu a london shi kadai ne chocolate kuma duk ya fimu kyau, ya fimu shiga mutane, kasancewar mu duk inda muka shiga idan aka kallemu sai an k'ara, if care is not taking wani ya sakar maka baki ka dawo kana fama, shi kuma skin dinshi normal ce shiyasa ba ya damuwa yake shiga inda yake so, duk a cikinmu nafi tsanar kallo na tsani inga mutum yana kallona shiyasa nike saka niqab... Muna rayuwa tsaka-tsakiya, mahaifinmu yana da albashi mai kyau saidai duk kudin suna k'arewa ne akan karatunmu, ya yarda ya bamu ilimi koda zamu rayu babu wadata, muna rayuwa ne babu wadata sosai, babu sutura mai kyau amma dukkanin wannan lokaci ne, Yaa Ayan shine nike bimawa tunda ya tashi yake da brain sosai shiyasa Abba ya turashi karatu London, Yaa Ahmad ya fara aiki da albasi mai kyau shine suke had'awa suna biyan kudin karatun Ayan, kamar yadda kuka sani yana karantar medicine ne a can, wannan shine abun da zan sanar daku, sauran zakuji nan gaba a cikin labarina....
*Shin miye asalin komai? Shin a ina na had'u da Mahmud? Shin ya aka yi na fara soyayya dashi har aka saka mamu biki, yayi min k'arya?*
*ASALIN KOMAI*
Karfe hudu na marece na gama lecture don haka saida na tsaya nayi sallar asr sannan na biyo bus, macpolo ce don haka anyi tsaye-tsaye wajen sauke mutane kafin finally tayi parking a national, baki daya daliban da sukayi saura suka soma fitowa ciki har dani na matsa tareda tsaida kekenapep zuwa unguwarmu da yake akwai nisa, tun daga nesa na hango wani d'an saurayi jingine da bike (rubber-rubber) a kofar gidanmu ya bada baya da alama yaron da zai aika ciki yake nema, a hankali nace,
"Nan yayi.....".
Kekenapep din ta tsaya na zaro er poss dake cikin handbag dina na zugeta na zaro kudin mai napep na bashi sannan na maida poss din cikin bag tareda zuro kafafu na sauko, sanye nike da long hijab har kasa kalar duhu ce wadda ta kasance ta plain yard babu pattern babu design babu flower babu daukar hankali, fuskata tana rufe da niqab kuma na k'ara jawo ta saman ta saman kaina (linki biyu) don haka koda idanuna ba'a hangowa, saurayin dake kofar gidanmu na kalla, fari ne sosai don koni da haskena yaso ya zama kamar zabayyana da kadan zan nuna mashi haske, kallona yayi sai kuma ya kalli wani wurin da alama kwarjini nayi mashi, a hankali nike taking steps kamar iska zai kaini kasa kasancewar na gaji sosai, har na gotashi na dawo da baya tareda d'age niqab dake a fuskata, a hankali nace,
"Kana neman Yaa Ahmad ne...".
Jim yayi sannan yace,
"A'a sako ne daga mai gida...".
Sai kuma ya mik'o min leather dake hannunsa na amsa na wuce cikin gidan wanda ya kasance mallakin Abbana, gidan yana da girma, ginin kasa ne yana da fluster saidai yaji jiki, gida ne daidai na rufin asiri, ban zame ko'ina ba sai dakin Ummy inda Yaa Ahmad yake zaune yana ma autanmu Affan wasa shi kuma yana wangame baki, Yaa Ahmad ya d'ago da murmushi akan fuskarsa yace,
"Aaaahhhh babynmu an gaji...".
Na zube kasa nace,
"Kai dai bari, indeed na gaji, tun eight fa har four, yanzu ma ai five tayi, wayyo Aallah yunwa...".
Yace, "Bari kiga...".
Sai kuma ya mik'e ya ciko min kofi da ruwa masu sanyi ya mik'o min, nace,
"Yauwa na gode shiyasa nike k'ara sonka our lovely brother".
Yace, "Ke kuma our lovely sister".
Mukayi dariya na amshi kofin na kafa lips na shanye ruwan tas, nidai a rayuwata ina ma ruwa one love musamman masu sanyi, before idan na dawo daga school kankarar loli nike siya in sha saida Ummy ta cashe min akan shan sanyi sannan na daina....
Ummy ce ta shigo na jawo leather da na amsa wurin saurayin nan, nace,
"Abba ne ya aiko wani mai kyau ya kawo".
Yaa Ahmad ya kalleni, nace,
"Yeah, tou kyanshi ne yayi appearing more shiyasa nace kadda ka fassara ni...".
Yace, "Baby ai ban ce komai ba".
Na fice na watsa ruwa, ni da nike kukan yunwa amma naita jan jiki saida nayi sallar magrib sannan naci abinci, Affan ya dauki wayata yana wasa da ita na amsa kadda ya tarwatsa min ita, karamar waya ce taci duniya har da rubbery na saka na nannad'eta, lokacin da Yaa Mustapha zai koma school aka sace mashi waya kuma babba ce, android, shine na bashi wayata infinix hot four wadda lokacin da na siyeta wadda nike da ita na bada na cika da wasu daga cikin kudin scholar dita aka bani ita saboda lokacin wadda nike amfani da ita tana bani damuwa, ya fini buk'ata shiyasa na bashi ya siya min wannan wayar naira dubu daya....
Tunda wuri na kwanta kasancewar washe gari tunda safe zan wuce school, tunda safe nayi kalaci nayi wanka na shirya cikin wasu riga da skirt na material na tamke kaina da kallabi sannan zura long hijab tareda daura niqab naja handbag, flat shoes ne na zura kasancewar nima ina da tsayi daidai nawa, tou ba za'a cemin doguwa sosai ba hakanan na wuce ace min tsaka-tsakiya, tou ina da tsayi daidai nawa, a gurguje na fita nayi ma Ummy sallama na wuce school, bayan mun fito daga lectures muna zaune muna catching fun before mu shiga lecture ta gaba, wasu suna duba note, wasu suna shafa wayoyi, mu hudu ne, ni da Jalila then Bindawa da wata er course dinmu Bintu....
Jalila k'awata ce sosai, tun 100level muke tare, itace mutum ta farko da na fara haduwa da ita a cikin en course dinmu, tou bata da damuwa, saidai ita bata da b'oye-b'oye kai tsaye take fadin ra'ayinta saidai mutum yaji haushinta, muna good time sosai, tasan komai nawa, nasan komai nata, family dinsu suna da kudi, cousin dinta zata aura tun tana yarinya aka bashi ita, shima yana da kudi....
Jalila ce ta mik'o min wani expensive invitation card tace,
"Ga shi kuma dole muje, aure suhail zaiyi ya gaji da wulakanci da kikeyi mashi ya samu matarshi zankad'ed'iya son kowa kin wanda ya rasa, tunda ke kince ba za ki auri mai kudi ba, ni mamaki kike bani tou arziki yana binki har gida amma kina gocewa kina bin talauci har inda yake, ai talauci baiyi ba, arziki kuwa yayi kaci mai kyau kasha mai kyau kayi suturu na alfarma kayi kyauta kayi sadaqa, kayi Hajji da Umra, ka taimaki addinin Aallah...".
Na kalleta kawai sannan nasa hannu amshi invitation card din, nace,
"Kema don kin san Jalaludden zaki aura kuma yana da kudi shiyasa kike cewa haka".
Jalila tace, "Aaahhh tou ga arziki har gida ai bana fita ina neman talauci ba...".
Bintu tace, "Ai arziki yayi, nikam ina ganin mai kudi kuma ba ya da damuwa ai bazan auri talaka ba...".
Jalila tace, "Fad'a mata ai a both masu kudi da talakawa akwai masu kirki da na banza, ba'a taru aka zama daya ba...".
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak Ayusher Thalith our greatest bride to be, Aallah ya albarkaci rayuwarki... Aameen... Ina jiran barka da sallah na anty fiddy, ki karkaro min cikin wadanda sayyadi ya bada... Ayusher daheerou kema ina jiran barka da sallah na har dake bilkin inna (bulkuma)...*
*zaynerb Abdullahi, zeeabdullahi hope kinyi sallah lafiya, tou ina jiran barka da sallah na*
Page. 7
A lokacin jinsu kawai nike....
Bindawa tace, "Cheese en mata in kashe mamu selfie...".
Muka juya ta kashe mamu selfie, tana viewing selfie din tace,
"Kai amma sunyi kyau, bari kuga inyi status dasu....".
Jalila tace, "Za ki koma gida ne?".
Bindawa tace, "A'a saidai zuwa upper week haka...".
Na duk'e da kaina ina duba invitation card din wanda yake rik'e a hannuna, naga za'ayi kamu, dinner, bridal shower da kuma wa'azi, kaina a duk'e nace,
"Bestie yanzu kuma sai munyi attending dukkanin programs din?".
Jalila tace, "Yeah... Kuma dole...".
Wata expensive car ce tayi parking, suhail ne ya fito, farin saurayi mai kyau ma'abocin fara'a, cikin wani expensive kaptani, da smile ya k'araso inda muke yace,
"Jalila... Bindawa... Bintu... Sannunku...".
Sai kuma ya juyo yana kallona, yace,
"Baby gashi....".
Sai kuma ya mik'o min wani book na amsa nace,
"Na gode...".
Da smile akan fuskarsa yace,
"Never mind ai I love you...".
Nayi smile kawai, ya lura da invitation card din dake hannuna ya amsa ya ware idanu yace,
"Ohhh Jalila ya zakiyi min haka, ohhh Faruk ne ya baki, ai zamu hadu, kuna so ku hadani da baby...".
Jalila tace, "Aallah?".
Suhail yace, "Yeah... Amma za ku yi attending ko? Ina son in nunawa mai sona wacce nike so...".
Jalila tace, "Za mu yi attending mana...".
Suhail yace, "Yauwa ki zo da baby".
Jalila tace, "Sure!".
Nace, "Aallah yasa alkhairi...".
Ni har wannan lokaci babu abun da naji, tou bana sonshi ballantana inyi kishi, da smile yace,
"Aameen... Mariam I love you har yanzu... Baby please...".
Wayarshi ce tayi k'ara yayi picking....
"Assalamu Alaiki... Alhamdulillah... Ohhh tou... Ina school gani nan tare da wacce nike so... Ohhh tou bari inyi mamu selfie kiga... Alright then...".
Sai kuma ya kalleni idanunsa suna a kaina ya bud'e lips a hankali yace,
"I love you...".
Sai kuma yayi hanging call din, ya matso ya kashe mamu selfie ni dashi, yayi mamu sallama ya juya ya shige motarsa ya wuce....
Bindawa tace, "Har yanzu bai hakura da baby ba...".
Jalila tace, "Ai taga yana sonta ne shiyasa take mashi iskanci, yaro ga hali ga kudi ga kyau ga k'ananan shekaru amma take mashi wulakanci...".
A lokacin banza nayi masu saboda gani nike idan na auri mai kudi dauka zaiyi saboda kudin dake gareshi ne na aureshi, na manta cewa kowa yana da halinshi, gani nike idan na auri talaka mukayi kudin a tare ai yasan tun yana talakanshi nike tare dashi tou bazai wulakantani ba, na manta cewa wani zai iya yin kudin tare dake amma ya manta zaman da kikayi dashi tun ba ya dashi ya auro wata ya wulakantaki, ai ba duka aka taru aka zama daya ba, tabbas suhail yana matuk'ar sona...
Muna zaune har lokacin daya lecture din ya kawo jiki muka wuce venue, bayan mun fito, suhail ya k'araso wajenmu yace,
"Jalila sai ina?".
Jalila tace, "Gida mana...".
Suhail yace, "Nima gida nayi muje in saukeku before in wuce gidanmu...".
Jalila tace, "Alright then...".
Yace, "Yauwa... Baby babu magana ne".
Nace, "Ina wuni?".
Mukayi dariya ya wuce, muna zaune a bus stop yayi parking motarsa, ya bud'e min gaba na shiga while Jalila ta zauna a baya, ya zagaya bangaren direba ya ja motan yana driving muna hira akan karatunmu, can yace,
"Baby zan kawo maku ankonku...".
Nace, "Mun gode...".
Saida ya sauke Jalila sannan ya wuce dani ya saukeni a unguwarmu, wai muje ya gaida ummy na, nayi dariya kawai na b'alle murfin motar na fito, indeed ya bani dariya, tou idan ya je yace mata mey tou....
Bayan kwanaki biyu, bayan mun fito daga lectures na raka Jalila muka wuce hostel zata amshi note ne a wurin bindawa, bindawa tace,
"Yauwa baby... Ina kika san Mahmud?".
Da mamaki nace,
"Mahmud kuma?".
Tace, "Ehh wani d'an unguwarmu ne da nayi status da selfie da nayi mamu, yake tambayata inda na sanki har da cemin wai ina kika san mai kyau...".
Sai kuma ta mik'o min wayarta tace,
"Kin ganshi nan...".
Na kalli hoton dake akan screen din wayar nayi jim saidai naga kamar na sanshi amma na manta a ina, kai watakila yayi min yanayi da wani ne, na d'ago nace,
"Ban sanshi ba... Ohhh na tuna, na sanshi, Abba ya tab'a aikoshi ne".
Saida baya na ganeshi shine the same saurayin da na amshi sak'o wurinshi, Jalila tace,
"Baby tashi muje...".
Na mik'awa bindawa wayarta muka fito munyi tafiya sannan muka isa bus stop dake student center muka biyo bus....
Washe gari ina zaune a dakin Ummy na rik'e Affan ina mashi wasa yana wangame baki yana kiran sunana....
"Ba-by...".
Nima ina maimaita mashi ina dariya, Yaa Ahmad ne ya shigo ya mik'o min wata waya android ce saidai yau na fara ganin irinta, yace,
"Baby raba mamu wannan gardamar, shin wa yafi kyau a cikin wannan hoton?".
Na amshi wayar na duba, Yaa Ahmad ne da the same saurayin da ya kawo sak'o, sunyi kyau dukkaninsu, both suna sanye da manya kaya, da smile kwance akan fuskar kowanensu amma koda wanda ba ya gani idan ya laluba zai san Yaa Ahmad yafi kyau a hoton, na dubeshi nace,
"Ohhh ai wannan hoton ba ya buk'atar gardama, of course kaine ka cinye hoton".
Yaa Ahmad ya harareni sannan yace,
"Ahhhh wato d'an gidanku kika shigarmawa, ai yafi kyau, dubeshi d'an handsome".
Nace, "And you are extra ordinary handsome".
Yaa Ahmad ya ware idanu sannan ya sunkuya ya dauki Affan ya fice, can naji sound a gefena ina dubawa naga the same wayar da Yaa Ahmad ya mik'o min ce, na dafe goshi nace,
"Gosh ya manta da wayar".
Call ne yake shigowa kuma yana tsinkewa wani yake shigowa, da sauri na dauki wayar na fito na lek'a dakinshi saidai babu shi babu alamarsa, na koma na zura long hijab na fito kofar gida, the same ba ya nan saidai the same saurayin nan, yana zaune akan bike rubber-rubber yana washe baki kamar mai tallar man goge hakora, nace,
"Yaa Ahmad fa?".
Ya ware hannuwa, na mik'a mashi wayar yace,
"Ana kira...".
Ya amsa saidai kiran ya tsinke na juya naji yace,
"Bamu gaisa ba, kuma kamar na sanki...".
Na juya nace,
"Ina wuni?... Barka da dare...".
"Lafiya lau... Kina lafiya...".
"Lafiya lau...".
"Ni kam ina na sanki, ohhh k'awar Haulat hakane...".
Na lura da wani abu yana sone ya tsaidani da hira kuma ya rasa abun da zaice, nace,
"Ni kuma, tou saidai ba ni da k'awa haulat...".
Ya kunna wayarsa yayi en shafe-shafe a wayarsa sannan ya mik'o min yace,
"Kin ganta nan wadda ta kwaso selfie din...".
Na amsa na duba wai ashe bindawa yake nufi, ai ni har mantawa nike da sunanta haulat saboda kowa da bindawa yake kiranta, ai kamar nice idan mutum zai kwana yana cewa mariam ba za'a gane ba har sai idan yace baby ko kuma yayi describing dina da wacce tafi en course dinmu haske, mutane da yawa suna describing dina da haskena, wasu suce ai tafi kowa haske ga kyau, sai kuji ance hasken ne kawai ya ceceta, ai idan bak'a ce ba zata kallu ba, miye, daga farin fatar sai idanun sai dogon hancin shikenan, tambaya tou wai mey ake buk'ata a kyau bayan wadannan abubuwa, mutanen mu kenan, tou b'arb'ela dai tun taltala take da farinta na tabbata banda haka da wasu sunce wanka da sabulu ne yasa tayi haske ko kuma suce bilicin tayi....
Muryar Yaa Ahmad naji a bayana, da sauri na juya na dubeshi ya kalleni nace,
"Wayarshi na kawo mashi...".
Nayi crossing dinshi na koma ciki....
Washe gari tunda safe na wuce school, abun mamaki ina had'uwa da bindawa tace min d'an unguwarsu yana gaidani, ni abun dariya ya bani, tou ni da ya gani jiya da daddare wai kuma har da aiko min da sakon gaisuwa ya gaisheni da kansa mana....
Bayan kwana biyu muna zaune ni da Ummy da Affan wanda ya mak'alk'alewa Ummy, ina mik'a hannu ba ya zuwa amma idan na mik'a mashi wayata sai ya tafo ni kuma bazan bashi wayata ya karasa min da ita ba, tou dama ya lafiyar giwa ballantana kuma tayi ciwo, ina lallab'awa da wayata ai ina bashi zaiyi pieces da ita, akwai lokacin da na saka charge na dawo na tarar ya cireshi yayi ma wayar pieces, Aallah ya taimaka bata samu damuwa ba, diramarmu muke muna shan dariya abunmu, yana taking steps zuwa inda nike amma ina janye wayar sai ya juya ya gudu wurin Ummy, nayi dariya nace,
"Yaro bazan baka wayata ba, hakanan kayi mata daya-daya...".
Mukayi dariya, Ummy tace,
"Kuma yana amsa kangawa zaiyi a kunne yana kiran hello, hello, hello, Abba, Ummy, Baby, Ayan...".
Yaa Ahmad ne ya shigo ya daukeshi yace,
"Ai ni sai in baka tawa".
Ya zaro wayarsa android ya mik'a mashi, nace,
"Ai kai mai kudi ne, ni kuma idan ya b'ata min tawa sai nayi er murya".
Yaa Ahmad ya tangare min k'eya na saki k'ara sannan cikin shagwab'a nace,
"Ummy...".
Ummy tace, "Mey? Babu ruwana, ai kunfi kusa".
Nace, "Babu ruwana da kai, mun b'ata...".
Kallona yayi yace,
"An baku assignment...".
Da sauri na dubeshi na zaro idanu nace,
"Aallah?".
Ya harareni yace,
"Daina kulani, ai mun b'ata".
Haka muke kamar abokan wasa, dariya ya kunshe ya amshi wayarsa daga wurin Affan ya mik'o min, yace,
"Duba ki gani...".
Na amsa nayi tsuru-tsuru da ni, ya kwashe da dariya sannan yace,
"Je ki dakina ki gani...".
Na mik'e na fita, da murna na dawo nayi hugging dinsa tareda mashi peck a kumatu, nace,
"I love you shiyasa duk nafi kama da kai... Ummy next week ake bikin wani course mate dinmu kuma Jalila ta matsa akan dole sai munyi attending programs da za'ayi...".
Ummy tace, "Indai tareda Jalila zakije, ba ni da damuwa".
Washe gari bayan mun fito daga tutorial din wani course, Jalila tace,
"Baby... Suhail ya bani ankonmu amma yana gida, dinkin ya had'u, kayan masu tsada, ohhh koda yake biki ne na arziki".
Nayi murmushi kawai, dinner ce aka fara, tou ita muka fara attending, tou a gidansu Jalila na shirya, expensive less ne brown da golden head amma abun mamaki kayana sunyi daban da na Jalila, duk yadda bana san yafa veil amma saida Jalila ta matsa min na yafa, dinkin fitet gown ne wadda tayi suiting dina amma bata matseni ba, simple make-up nayi applying amma nayi matuk'ar kyau kamar wacce zataje contesting din beauty, looking breathtaking....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest sofi, sofinmu I just imaging a ranar sallar nan sweety ya amshi handbag dinki ya cika maki ita da dollars don haka ina jiran nawa share din, ko kuma aradu inyi ma sweety sending picture dinki kina kwasar loma, hhhh, lols....*
*Baby d'iyar rubber cikin dare take kashe y'ay'anta murus... Baby d'iyar rubber cikin dare take kashe y'ay'anta tumus... Baby d'iyar rubber cikin dare take kashe y'ay'anta kurus rumus... Eid mubarak to you baby fans all over the world, ina jiran barka da sallah na....*
Page. 8
Da sauri na kalli high heel shoes dake jirana nace,
"Kin san Aallah Jalila bazan iya tafiya a wadancen takalman masu tsini ba, hakanan in fad'i in broken kafafu...".
Na nufi shoes rack dinta....
Jalila tayi dariya sannan tace,
"Dawo ai guda biyu ya sako maki heel shoes da flat shoes".
Sai kuma tayi min pointing flat shoes din na saka, tace,
"Ma shaa Aallah... Baby you look cute...".
Ni da kaina nasan nayi kyau babu k'arya, saida ta kashe mamu selfie mukayi snapping picture sannan muka fice muka sauka kasa mukayi sallama da Mami muka wuce compound, muka shiga wata dalleliyar mota direba ya jamu, mahaifin Jalila yana da kudi sosai, gidansu babban mansion ne, direba ne yayi parking muka fito tunda daga inda muke muna jiyo kidi da yake tashi daga ciki, Jalila tace,
"Baby muje...".
Na kalli hall din na girgiza kai, tace,
"Sai in tafi in barki...".
Nace, "Bismillah...".
Dariya na bata tace,
"Wato don kin san bazan tafi in barki ba, wai ke mey yasa kike da tsoron mutane, miye na tsoro kamar wacce za'a cinye, kina da kyau, kina da haske, aikuwa dole a kalleki, wadanda basu kaiki kyau ba an kallesu ballantana ke kuma...".
Nayi mata banza, ta jawo waya ta danna call, tayi jim sannan tace,
"Gamu nan a bakin hall... Baby ce kasan halinta... Tou shikenan...".
Jim kadan suhail ya fito looking breathtaking, kun san dai yadda groom suke shan kyau, da smile ya karaso yace,
"Baby you look breathtaking ai koda amaryar ba zata nuna maki kyau ba...".
Kallonshi nayi yace,
"Cheese...".
Sai kuma ya kashe mamu selfie, yayi min snapping picture sai kuma ya rik'e hannuna ya jani ciki yayinda Jalila ta biyo bayanmu, kallon hannunshi da ya rik'e hannuna nayi I feel kamar ina sonshi, yana da hali mai kyau kuma yana matuk'ar sona sannan yana da kyau kuma yana da ilimi and yana da brain, tou first class ne mai security wanda small wuru-wuru bazai saka ya sauka ba, saidai har lokacin ba na nadamar rashin accepting dinshi da nayi, sai yanzu da nike tunani sannan na fara nadama, tou kamar yadda kuka sani yana sona sosai kuma yana da hali mai kyau amma nace a'a, naqi mai kudi gashi talaka yana neman janyo min hawan jini, both a cikin masu kudin da talakawa akwai na kirki hakanan kuma akwai na banza, tabbas ba duka aka taru aka zama daya ba, sai yanzu na fahimci komai amma a wancen lokacin babu abun da na gane....
Suhail yana jaye dani ne yayinda muka bada wani perfect match, indeed I feel kamar ina sonshi, tunda muka shiga idanu suka dawo a kanmu, sai lokacin na lura ashe kayan da ya bani ba anko bane, wadanda Jalila take sanye dasu sune anko, expensive less din dake jikina yafi match da kayan dake jikinsa, har zuwa wannan lokacin yana rik'e da hannuna yana tafiya ina biye dashi kuma high table yake nufa inda bride dinsa take zaune, da smile yace,
"Baby ga mai sona... Suhailat ga wadda nike so...".
Suhailat ta yaye veil dake kanta tana kallona, saida gabana ya fad'i, kamarta daya sak da suhail, kallo za'ayi mata a gane jininsa ce, kallonshi tayi ta kalli hannuna da yake rik'e dashi, smile yayi, tace,
"Mariam ko?... Sannu... Ohhh baby...".
Ni rasa abun da zance mata nayi sai kuma nace,
"Congratulation, I wish you all the best Mrs suhail to be, suhail bashi da damuwa, hope zaki kula mamu dashi, muna sonshi...".
Suhail ya ware idanu sannan yace,
"Aahhh ashe baby kina sona...".
Na kai mashi a baya nace,
"Zanyi maganinka...".
Suhail ya turo lips yace,
"Zuciyata zaki sace ne...".
Nayi shiru kawai, tou babu bakin magana, yasa dariya yana kallona, Jalila ce ta raba hannuna da nashi aka daukemu hotuna muka wuce wurin en course dinmu, bayan da na baiwa bride abun da ya saka min a cikin anko ina ganinshi na gane abun da yake nufi, amma lokacin da na bata har da cewa....
"Mun gode wacce nike so...".
Duk wanda muka gaisa sai ya yaba kyan da nayi, wasu suce tubarkallah wasu kuma saidai ni ince a cikin zuciyata, bindawa tasha rawa hakanan Jalila, nikam saida suka matsa min sannan nayi aikuwa na sha liki, suhail yayi min wanka da wrapper din dollars, a hanyarmu ta komawa gida, Jalila tace,
"Baby duba ki gani...".
Sai kuma ta mik'o min wayarta na amsa naga suhail ne ya saka selfie din da yayi mamu akan dp, na duba wayata babu kudi nayi mashi please call me babu jimawa ya kira, nayi picking before inyi uttering koda word guda daya, yace,
"Baby i love you har yanzu...".
Naji kamar inyi mashi duka, nace,
"I love you din banza, ni kawai ka cire hotona daka d'aura akan dp...".
Daga daya bangaren suhail ya ja lumfashi sannan yace,
"Hotonmu dai, ai ni da ke ne a ciki, ko kin manta...".
"Whatever ma shi nike nufi...".
"Alright then, zo ki amshi wayar ki sauya da kanki, kin ganta nan a hannuna...".
Na biye mashi yana zaulayata ina cewa ni ya cire min hoto daga kan dp, koda kiran ya tsinke ya kara kira ya cigaba da zaulayata, sai bayan yayi hanging call din sannan na tuna da wani abu dole a wannan lokacin yana tare da amaryarsa zasu maidata gida, na ware idanu nace,
"Jalila na bani, yana tare da amaryarsa na kirashi kuma dole taji haushi, anya kuwa zan k'ara attending wani program".
Jalila tace, "Aallah dole kije ai ya gayyacemu kuma duk ya bada ankonsu, ai dole muje iyakarta idan amarya taga iyayinki yayi yawa tasa besties dinta suyi maki dukan tsiya, daman gaki da shegen tsoro kamar farar kura...".
Nayi mata wani kallo sannan nace,
"A'a kin manta dorowar kura...".
Muka saka dariya, saida na biya gidansu nayi changing kaya saboda ji nike bazan iya yawo da veil haka ba, d'azu ma don mota ce ta saukemu har hall din, shima saida naji kamar in komo in dauki long hijab dina in saka amma babu chance, Mami ce ta saka direba ya maidani har gida....
Kamu, wa'azi, bridal shower dukkanin program din babu wanda ba muyi attending ba, ranar d'aurin auren har da kirana yana fad'a min wai an d'aura zaizo ya kawo min goro koda yake ni tsohuwa bace, tou zai kawo min chocolate da ice cream, I feel in ganshi kusa da ni inyi mashi dukan tsiya, tou a wane dalili? Bayan bikin ciwo nayi sosai kamar zan mutu, rana daya en course dinmu suka zo ganina da kayan dubiya niki-niki, kuma har da suhail shine gaba, Jalila ce ta rakosu, tou wasu daga cikinsu sun san gidan, ina ji matar suhail ta kirashi babu kunya yake fad'a mata baby suka zo dubawa bata da lafiya, captain yace,
"Baby kodai ciwon sone...".
Suka saka dariya, suhail yace,
"Aiko da nayi murna...".
Nayi mashi wani kallo yace,
"Ko kin fara kishi ne?".
Suka saka dariya, Jalila tace,
"Barta sai ka rama abun da tayi maka sannan...".
Suka saka dariya, saida suka gaida Ummy sukayi mata ya mai jiki sannan suka wuce, nayi zuru....
Da daddare Yaa Ahmad yazo tareda wani da kayan fruit cike da leather, bayan ya tafi, Yaa Ahmad yace,
"Baby kin ganeshi kuwa?".
Nace, "A'a....".
Da mamaki yace,
"Kusan kullum sai yazo dubaki amma kice baki ganeshi ba".
Nace, "Tou Yaa Ahmad abokanka ne yau kazo da wannan, gobe kazo da wancen, kullum akwai wadanda zasu zo dubani, tou ta ya zan gane daya?".
Yace, "Mahmud ne fa?".
Nace, "Waye Mahmud?".
Yace, "Wanda nazo da wayarshi kika kai mashi ita kofar gida...".
Nace, "Ohhh na gane... Don Aallah taimaka min da ruwa...".
Saida jikina ya murmure sannan na koma school, ranar da na koma, Jalaludden ne ya daukomu ya kawoni har gida sannan ya wuce da Jalila, cousin dinta ne shi zata aura amma sai idan mun gama karatu sannan za'ayi bikin, bayan na shiga gida nayi wanka naci abinci sannan na kwanta ina hutawa, tou yau na kwaso ciwon kai....
Da daddare muna zaune tsakar gida, wani yaro ne ya shigo wai wani yana sallama dani, nace,
"Waye?".
Yace, "Ban sanshi ba amma saman rubber-rubber yake...".
Na kalli Ummy, tace,
"Kije kiga waye...".
Nayi nodding head sannan na dubi yaron nace,
"Kaje kace mashi gani nan fitowa... Yauwa, nikam Feena ta dawo daga faskari ko kuwa tana can".
Yace, "Bata dawo ba...".
Nace, "Shikenan je kace mashi gani nan zuwa...".
Yaron ya juya ya fita, zani ne da shirt a jikina don haka daki na shiga na zura long hijab na fito na saka takalma na fice, yana zaune a saman rubber-rubber, Mahmud ne yana sanye da kaftani, yace,
"Nine na aika kiranki".
Nace, "Ohhh d'an unguwarsu bindawa ko?".
Yace, "Ehhh daman nazo ne mu gaisa kuma in k'ara yi maki ya jiki..".
Nace, "Alhamdulillah... Jiki yayi sauki... Na gode...".
Yayi shiru, nayi shiru, can yace,
"Tou na tafi...".
Nace, "Aallah ya kiyaye hanya, na gode...".
Na koma gida shi kuma ya ja bike dinsa ya wuce, na lura akwai magana a bakinsa amma bai san yadda zai furtata bane, na cire hijab na koma mazaunina na d'azu, nace,
"Ummy... Wannan ne wanda kwana ki can Abba ya aiko ya kawo sako".
The same washe gari muna zaune wani yaron makotanmu ya shigo yace,
"Baby wani yace kizo...".
Da mamaki na dubeshi sai kuma nace,
"Je ka ce mashi gani nan zuwa...".
Nayi ma Ummy magana sannan na zura long hijab na fita, yau ma manyan kaya ne a jikinsa, da alama yana son manyan kaya, tou ban tab'a ganinsa da kananan kaya ba, watakila ba ya sakasu ne, nace,
"Ashe kaine...".
Yace, "Ehhh nazo ne in gaidaki".
Nace, "Aahhh tou na gode...".
Yace, "Na tafi...".
Nace, 'Aallah ya kiyaye hanya...".
Na juya na koma gida shi kuma ya tafi, ni dariya yake bani na lura dashi irin mazan nan ne masu tsoron suyi ma mata magana, tou idan yace yana sona cinyeshi zanyi ne amma ya tsaya yana b'atawa kanshi lokaci....
Washe gari bayan mun fito daga lectures, bindawa tace,
"An aikoni wurinki, Mahmud yana gaidaki...".
Na fashe da dariya sannan nace,
"Aahhh rabu dani da maganar wannan d'an unguwar naku mai tsoron mata, kullum saidai yazo yace yazo ne ya gaidani amma ya gaza ya bud'e baki yace yana sona, he is novice...".
Muka kwashe da dariya, Jalila tace,
"Miye?".
Nace, "In gaya maki sabon saurayi nayi amma kullum saidai yazo yace yazo ne ya gaidani yadda kika san idan yace yana sona marinshi zanyi, ai bazan mareshi ba ko...".
Jalila ta tab'e baki sannan tace,
"Hala talaka ne...".
Nace, "Indeed... Ai kin san zabina, talaka wanda zai rikeni tsakaninsa da Aallah...".
Jalila tace, "Ai suma masu kudin sun san darajar aure kuma suma zasu rikeki tsakaninsu da Aallah, ana fada maki bakya dauka ai sai kije kiyi tayi yadda kike haka idan kikayi aure gidan wahala, kin san Aallah ba zaki kallu ba, ni kuma ban iya tsallake kwatoci ba, kinga zuwa gidanki sai Aallah yayi...".
Na kai mata duka....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak our greatest mai awara, Afra mai awara... Da girman kujerarki aw da girman kaskon awarki hhhh... Ina jiran barka da sallah na kaskon farko inci in baiwa baby fans, kuma aradu dole ki cigaba da bani Aallah koro, ehe, hhhh lols....*
*Hope kunyi sallah lafiya, Fateema and Teema, kuna raina, tou ina jiran barka da sallah na....*
Page. 9
Jalila ce tace,
"Baby I don't think you can never understand, koda an fad'a maki a banza ne, tou let me see picture dinshi...".
Nace, "Bindawa nuna mata hotonshi...".
Bindawa tace, "Aha, tou amma anya kuwa yanzu ina da hotonshi a wayata, bari dai inyi checking ina jin na tab'a sauke hotonshi daga what's app".
Jim tayi sannan tace,
"Yauwa gashi nan...".
Jalila ta amsa can tace,
"Tou not bad yana da kyau amma suhail ya fishi kyau wannan farin ne kawai...".
Bindawa tace, "Jalila!...".
Jalila tace, "Ohhh ashe d'an unguwarku ne, tou ya zanyi duk abun da bestie take so ai mun tayata...".
Muka kwashe da dariya...
Abun dariya the same wannan ranar ma saida yazo a bike dinsa, ya matsa da bike dinsa tareda gaida Abba, na lura akwai aminci sosai a tsakaninshi da Abba, saidai Abba ya shiga ciki, yace,
"Dama nazo ne in gaidaki, na tafi...".
Nace, "Tou na gode...".
Na juya na koma gida, tunda na shiga daki nike dariya kai wannan saurayin d'an drama ne....
Washe gari da marece bayan Yaa Ahmad ya dawo daga wurin aiki muna zaune muna hira, yace,
"Baby miye tsakaninki da abokina?".
Saida na kwashe da dariya sannan nace,
"Sona yake amma ya gaza fad'i saidai kullum yazo da bike yace yazo ne ya gaidani ne, ni bike din ne yake bani tausayi kullum ana aikin banza dashi...".
Muka kwashe da dariya, nace,
"Amma barni dashi zan saka yayi magana, inga wayarka...".
Ya mik'o min saida nace,
"Shhhh....".
Sannan na danna recording nayi jim kamar muna hirar nan sannan nace,
"Yaa Ahmad kasan Aallah wannan abokin naka zabo ne saidai kullum yazo yace yazo gaidani, tsorona yake watakila tsoro yake kadda yace yana sona in kwasheshi da mari, novice ne, da alama tsoron yayi ma mata magana yake, hahahaaha, abun dariya...".
Na danna pause....
Yaa Ahmad ya ware idanu yana kallona, nace,
"Ka tura mashi ka nuna mashi muna hira ne kayi recording ban sani ba...".
Muka kwashe da dariya, yace,
"Wato so kike ki saka yayi magana dole...".
Nace, "Yeah... Ai kana tura mashi ya gama zuwa kuma yana dawowa bazai k'ara yin haka ba...".
Na mik'a mashi wayar kuma haka aka yi a gabana ya tura mashi recording din kuma lokacin yana online ne, tou tun daga ranar bai k'ara zuwa ba sai bayan sati biyu, wata rana ina zaune wani yaro ya shigo nace,
"Sagir kaine...".
Yaron da na kira da sagir yace,
"Kije inji wani saurayi...".
Da wasa na ware idanu nace,
"Saurayi kuma, tou kato ne ko siriri...".
Sagir yace, "Ke dai kika sani...".
Nace, "Tou je kace mashi ban nan...".
Sagir ya rik'e baki sannan yace,
"Tab gaki ina gani sannan kice baki nan, Aallah zuwa zanyi ince mashi kina nan...".
Ya juya ya fita ina mashi dariya, ban d'ad'e da fitowa daga wanka ba don haka goge fuskata kawai nayi nai applying kwalli na dauko wani less colour din brown na saka, kudinshi leather daya zai kai 20K babbar sallar da ta wuce ina zaune Nadiya ta aiko min dashi a dinkenshi inyi kwalliyar sallah, ashe adashe tayi ta siya mamu aka yi mamu dinki iri daya, da yake mijinta yana da hali, duk da er gidan nan ce amma ba komai bane zamu rink'a fad'a mata, long hijab na zura na fita na sameshi jingine da bike, Mahmud ne, da mamaki nace,
"Ohhh ashe kaine, kazo ka gaidani ne... Right? Aahhh tou na gode... Bye...".
Na juya yace,
"Baby....".
Na juyo nace,
"Ohhh ashe kasan sunana...".
Mahmud yayi murmushi kawai, nace,
"Tou ya aka yi?".
Muryarshi tana rawa yace,
"Ina sone mu zama abokai...".
Nace, "Saidai bana abota da maza saidai soyayya wannan zan iya...".
Yace, "Tou shikenan ina sonki...".
Na ware idanu sannan nace,
"Ta ya zan yarda kana sona...".
Mahmud yayi dariya kawai, nace,
"Kayi dariya...".
Yace, "Alright then... Uhmmm with time zaki gane idan ina sonki...".
Yaa Ahmad ne ya shigo santar suka gaisa, yace,
"Babynmu zance kike?".
Nace, "Kai Yaa Ahmad...".
Yace, "Uhmm babynmu ta girma...".
Ya shiga gida yana dariya, a lokacin ne na tambayeshi saidai a wannan karo baiyi min k'arya ba saidai yayi shiru akan wani abu....
Na dubeshi nace,
"Abokinka ne?".
Yace, "Wai Ahmad?".
Nace, "Ehhh....".
Yace, "Wurin aikinmu daya...".
Daga nan baice komai ba, tunda yace wurin aikinsu daya na gane wurin aikinsu daya da Abba kenan tunda da Abba da Yaa Ahmad wuri daya suke aiki, Yaa Ahmad yana da degree akan Bsc. Mathematics, guru ne sosai akan maths....
A lokacin ban tambayi Mahmud matakin da yake ba, shi kuma bai fad'a min ba, abubuwa da yawa sun faru a soyayyata da Mahmud saidai zuwa wannan lokacin da wadannan abubuwan suka faru sam ban san tuna wadancen lokuttan, ni dai abun da na sani shine naso Mahmud iya so, na nuna mashi so matuk'ar so amma daga baya ai kunga abun da yayi min, k'arya, wai k'arya, idan na tuna raina b'aci yake, tou ban san maraya bane sai wata rana da yake fad'a min cewa both iyayenshi en batsari ne dake nan jihar katsina amma mahaifinsu ya rasu tunda tsohon cikin k'anwarshi Safeena, na tausayi mashi sosai, rashin mahaifi babban ciwo ne, tabbas, don wani abun idan ya tsaya maka a wuya hmmm, wani lokacin zaka duba kaga ga abu da yake maka amma lokaci yazo da ba ya nan ballantana yayi maka, mun dauki lokaci muna soyayya na lura yana da hali mai kyau, sam bashi da damuwa, ina sone in gane idan yana da ilimin addini, wata rana yazo muna cikin hira nace,
"Kaga bari in dauko Alk'ur'ani ka duba min hardata...".
Na mik'e na shiga ciki, da yake a zaure (soro) muke zance sai in dauko mashi sallaya ya zauna while ni kuma sai in zauna daga gefe, na dauko Alk'ur'ani mai girma na dawo zaure (soro) tareda zama na mika mashi Alk'uranin, shi a lokacin suratul ma'ida na bud'e mashi wurin tsakiya shima na lura a lokacin yana da sani akan Alk'ur'ani mai girma tunda duk inda nayi b'ata yana gyara min, bayan mun gama yace,
"Ashe matar tawa mahardaciyyar Alk'ur'ani ce, kinga ni na sauke ne amma banda hadda".
Nayi murmushi kawai nace,
"Na gode, karanta min inji kira'arka".
Ya mik'o min yace,
"Then bud'e min duk inda kike so".
Na amsa na bud'e na mik'a mashi yayi auziya sannan yayi bismillah before ya soma rero karatu, yana da karatu mai kyau saidai tsakanin kira'ata da tashi banbancin a bayyane yake, ya burgeni sosai, kamar yadda kuka sani bayan hakan ne ya soma hadda, wata rana muna making call kamar da wasa yace,
"Zan kawo maki kanwata ku gaisa...".
Nace, "Ina jiran zuwanta".
Na dauka da wasa yake....
Bayan kwana biyu ina zaune ya kira, murmushi ne ya sub'uce min nace,
"Aaahhh yanzu wayar nan sai tayi recording komai, wow...".
Sai kuma nayi picking tareda amsa cikakkar sallamar da yayi min, yace,
"Ya kike...".
Nace, "Kamar yadda kake...".
Yace, "Ashe kina fama ne da ciwon kaine...".
Da sauri nace,
"Mey... Inji wa?".
Mahmud yayi dariya sannan yace,
"Aaahhh ai da bakinki kika ce yadda nike haka kike, manta da wannan, gani a kofar gidanku na kawo maki Safeena...".
Da mamaki nace,
"Aallah?".
Yace, "Idan baki so sai na koma da ita".
Nace, "Aiko da kaima idan ka dawo ban fitowa".
Na mik'e na shiga daki na zura long hijab na duba fuskata a madubi sannan na fito na lek'a dakin Ummy tana zaune akan kujera nace,
"Ummy zan fita, Mahmud ne ya kawo min k'anwarshi...".
Ummy tace, "Tou kije ki shigo da ita".
Na gyad'a kai tareda juyawa na fice yana zaune akan rubber-rubber ta sauko, suna kama sosai, yarinya ce don na girmeta, tou shekarunta ba zasu wuce goma sha shidda ba, Mahmud yace,
"Ga k'anwata na kawo maki...".
Nace, "K'anwarmu dai, kaji fin karfi... Safeena sannu, ya hanya?".
Tace, "Alhamdulillah...".
Yace, "Wato na kawo maki ita shine kika manta da ni".
Nace, "Tou naga k'anwata wa yake ta kai".
Ya ware idanu, nace,
"Ehhh...".
Yace, "Ai zamu hadu... Safeena kinga an kirani, tou idan kin gama ki wuce a kekenapep".
Safeena tayi nodding kai, yayi min waving hannu yana murmushi sannan ya burka bike dinsa ya wuce, na jata muka wuce ciki ta gaida Ummy sannan na wuce da ita dakina, ana zafi don haka na d'age mata labule, nayi mata magana sannan na fita na shiga makotanmu gidan maman en biyu, na amso mata pure water da zobo tareda snack na dawo na jera mata a plate sannan na kai mata na zauna tareda zare hijab din dake jikina, nace,
"Sannu Safeena kunsha hanya... Ya gida... Ya su Ammi...".
Tace, "Suna nan lafiya lau...".
Nace, "Gaskiya naji dadin wannan zuwan naki, kin kyauta, ga ruwa da zobo da snack...".
Tana murmushi tace,
"Na koshi...".
Nace, "Ohhh har ana koshi da ruwa, tou bari in kirashi ince mashi na kawo maki abunsha kince a'a...".
Ta girgiza kai tace,
"Tou zan sha...".
Nace, "Mey ai har da snack zaki ci ko kuwa yanzu in danna mashi call...".
Wuni tayi sannan tayi ma Ummy sallama na rakata har bakin titi na tare mata kekenapep na fad'a mashi unguwarsu na biya mata kudin ta shiga suka wuce sannan na juyo, ban koma gida ba, na shiga gidansu wata childhood bestie dita, ina zaune a can na kirashi nike tambayarshi Safeena, yace ta isa gida lafiya....
Washe gari muna lecture bindawa ta soma ganin jiri muka wuce da ita clinic ta amshi magana muka wuce da ita hostel, bayan mun tafo ashe ciwo tayi kamar zata mutu, da sukaga abun yafi karfinsu aka wuce da ita general hospital, har asibiti mukaje ganinta tareda en course dinmu, tou bayan sunyi discharging dinta ta koma gida before ta ida murmurewa, Jalila ce take cemin ya kamata muje mu k'ara dubata, nace tayi fixing lokaci, shine washe gari bayan mun fito daga lectures, muka biyo bus, daga national muka tari kekenapep ta wuce damu unguwarmu bindawa wato filin samji, ya saukemu muka wuce da yake mun san gidansu, gida ne mai kyau yasha paint ga tale malale a kasa abun saidai hamdalah....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*BA NI DA LAIFI*
*By sl rimi family's*
🎀°°•°°🎀••°••🎀°°•°°🎀
*Update Of June, 2019*
*••°••In dedicated to our lovely sis late mariam sl rimi, we are still missing you, may your gentle soul rest in peace, Aallah ya jiqanki, Aallah ya gafarta maki, Aameen••°••*
*Eid mubarak online writers and publishers, wish you all the best....*
*Hope kinyi sallah lafiya mariam dabai, Aallah ya albarkaci rayuwarki....*
Page. 10
Muka tadda Mamansu ta fito daga kitchen muka gaidata ta amsa da fara'arta ta sanmu....
"Ya mai jiki?".
"Jiki yayi sauki...".
"Aallah ya k'ara sauki...".
"Aameen... Ku shiga tana dakinta...".
Muka wuce muka sameta kwance ta mik'e zaune tana murmushi tace,
"Sannunku da zuwa... Bari a kawo maku ruwa...".
Jalila tace, "Kamar kuwa kin san daga school muke".
Bindawa ta kira k'anwarta tace,
"Soffi dauko masu ruwa daga fridge...".
Nace, "Daga gani k'anwarki ce...".
Tace, "Ehhh...".
Nace, "Tubarkallah kuna kama...".
Yarinyar ta kawo mamu abinci da gorar ruwa tareda cup guda biyu, ruwan masu sanyi (but not as cold as ruwan da nasha a school, I feel idanuna zasu samu damuwa, lols...) fried rice ce wadda taji vegetables muka ci muka kora da ruwa muka sha hira abunmu, tace,
"Watakila next week in koma school...".
Da muka tashi tafiya mukayi ma Ummarta sallama, bindawa ta rakamu har bakin kofa muka fito ta koma, muna tafiya na d'age niqab din dake fuskata, ji nayi wata muryar mace tana kirana....
"Baby....".
Ina juyawa naga Safeena k'anwar Mahmud a kofar wani gida, I feel da ban d'age niqab dita ba, don ba ni da excuse din da zai hanani shiga gidansu ni kuma kunya nike ji, Jalila tace,
"Wacece?".
Nace, "K'anwar Mahmud ce...".
Tace, "Aikuwa naga kama....".
Nace, "Please bata uzuri kadda mu shiga, kunya nikeji...".
Jalila tace, "Ai bamu da uzuri".
Safeena ce ta karaso, nace,
"Safeena sannunki...".
Tace, "Da wucewa zakiyi?".
Nace, "K'awarmu muka zo dubawa da jiki...".
Tace, "Ohhh Haulat...".
Nace, "Ehhh bindawa...".
Tace, "Hakane... Muje ki gaida Ammi ko kuma ince mata kinzo kin wuce baki lek'ata ba".
Na nuna mata Jalila nace,
"Wannan k'awata ce tare muke karatu, sunanta Jalila...".
Safeena tace, "Hakane... Tou muje...".
I feel some how amma babu yadda zanyi, nace,
"Tou muje...".
Muka jera tayi mamu jagora zuwa wani gida, gida ne daidai rufin asiri, dakuna biyu ne sai rijiya, gidan ba ya da girma sosai, daidai-daidai yake, ta wuce daya dakin wanda da alama shine yafi girma, wata dattijuwar mata ce zaune akan kujera tana karanta husnil muslim, nayi kasa da kaina, Safeena ta nuna mamu kujera amma muka zauna kasa, matar ta d'ago tace,
"Ku koma akan kujera...".
Kallo daya nayi mata naga basu kama da ita, da alama mahaifinsu suka biyo koda yake ga hotonshi can suna kama sak, muka zauna akan kujera muka gaidata ta amsa da fara'a, tun wurin Mahmud nasan cewa da Ammi suke kiranta, Ammi tace,
"Safeena k'awayenki ne?".
Safeena tace, "A'a.....".
Sai kuma ta fita....
Ammi tace, "Sannunku da zuwa yaran nan".
Safeena ta dawo da ruwa pure water guda biyu daga gani a fridge ta daukosu, ta ajiye mamu tace,
"Ammi baki gane wannan ba?".
Tayi pointing dina, nidai kaina yana kasa, Ammi ta kalleni tayi jim sai kuma tace,
"Kuma kamar na wayeta....".
Safeena tayi dariya tace,
"Baby ce, budurwar Yaa Mahmud...".
Ammi ta saki murmushi tace,
"Sai yanzu na gane, hotonta na gani, kice surukata ce...".
A lokacin ji nayi kamar kasa ta tsage in shige, tace,
"Ku sha ruwan mana...".
A kunya ce nasha, tou bazan iya mata gardama ba, tace,
"Ya Ummarki?".
Nace, "Lafiya lau take...".
Tace, "Kice ina gaidata..".
Nayi nodding kai, a kunya ce nike zaune, gwara Jalila ta fini sakin jiki, da muka tashi tafiya tace,
"Ni mey zan ba surukar tawa, baby gashi dakin nawa babu abu irin naku na en mata amma Safeena dauko mata wani littafi yana cikin locker ta kaima Ummarta zaiyi mata amfani".
Safeena ta shiga kuryar dakin, I feel Ummy kuwa zata ci uwata zuwa gidansu saurayi, ohhh no, jim Safeena ta fito muka wuce, Ammi tana mamu fatan isa gidajenmu lafiya....
Muna fitowa Mahmud ya shigo muka ci karo a soron gidan, ya ware idanu yace,
"Baby....".
Nayi banza dashi, Safeena ta bani karamin littafin na musulunci ne, sai kuma ta koma ciki, muka fito yace,
"Jalila kinga besty dinki tayi min shiru".
Jalila tace, "Ni, babu ruwana ai kunfi kusa...".
Yace, "Baby....".
Nace, "So kake Ammi ta gammu".
Mahmud ya ware idanu, nace,
"Bindawa muka zo gani, Safeena ta gammu".
Mahmud yace, "Ai ta kyauta...".
Nace, "Ni kuma naji kunya ba".
Yace, "Tou ya kikaga Ammi?".
Nace, "Bata da damuwa....".
Yace, "Kamarni kenan...".
Yana pointing kanshi, nace,
"Ohhh ji shi yana yabon kanshi da kanshi...".
Yayi dariya yace,
"Baby...".
Nace, "Mariam...".
Yace, "Ai dukkaninsu sunayenki ne".
Muka karasa bakin titi ya tsaida mamu kekenapep ya bashi kudi muka shiga, ya lek'o yace,
"Baby sai yaushe?".
Nace, "Sai lokacin da ka zo...".
Mahmud yayi nodding kai sannan yayi baya yana mani waving hannu yana smile, kekenapep ta wuce damu, saida ya sauke Jalila a unguwarsu sannan ya wuce dani unguwarmu, na zuro kafafuna ya mik'o min kudi nace,
"Na miye?".
Yace, "Kudin da ya bada sunyi yawa".
Na girgiza kai nace,
"Ai kai ya ba, ba ni ba".
Yace, "Na gode...".
Na juya ina taking steps a hankali na shige gidanmu, Ummy tace,
"Ya jikin nata?".
Nace, "Jiki yayi sauki, tace watakila next week zata koma school".
Bayan nayi wanka na dauko book din na fito, Ummy tace,
"Ina kika samu wannan littafin?".
Na dubeta da sauri nayi zuru sai kuma nace,
"Ammin Mahmud tace in kawo maki...".
Ummy tayo waje da idanu tana kallona, nayi baya da sauri tun kafin ta jawo takalmi, nace,
"Unguwarsu daya da bindawa, mun fito k'anwarshi ta gammu, babu yadda zanyi, Amminshi ce tace in kawo maki".
Ummy ta amsa tana dubawa yayinda na samu gefen tabarma na zauna, tace,
"Kuma yana da kyau, kiyi min godiya".
Wayata ce ta soma ringing Ammi ce takeyi min sannu tana tambayata na isa gida lafiya, Ummy ta kalleni na cire wayar daga kunnena tareda toshe speaker, nace,
"Ammin Mahmud ce take tambayata na iso gida lafiya".
Ummy tace, "Bani inyi mata godiya...".
Na maida wayar a kunnena nace,
"Ga Ummy zatayi maki godiya...".
Daga daya bangaren Ammi tace,
"Tou bata...".
Na mik'awa Ummy wayar bayan sun gaisa tace,
"Naga abun alkhairi na gode...".
Wannan shine asalin samun numbar Ammi da nayi, ya kasance tana da numbata, ina da numbarta, hakanan naji matar ta shiga raina, tana da kirki, bata da damuwa, tun wancen lokacin har zuwa yanzu da wadannan abubuwan suka faru still ina ganinta da k'ima...
Washe gari bayan na dawo daga school, Abba ya kirani na karasa dakinsa na zauna kasa, yace,
"Mariam....".
Na d'ago yace,
"Mi kike tunani akan Mahmud?".
Nace, "Ina sonshi...".
Yace, "Kin tabbata...".
Na gyad'a kai, yace,
"Kiyi magana...".
Nace, "Ehhh...".
Yace, "Tou shikenan tashi ki tafi, Aallah yayi maki albarka...".
Nace, "Aameen...".
Na fita, bayan kwana biyu iyayen Mahmud suka zo aka saka mamu rana bayan na gama degree dina, both brothers dina da Nadiya sun san Mahmud kowa yabonshi yake, yana da kirki, bashi da damuwa, bindawa ce ta tura hotuna da na Mahmud a group tana sanar dasu cewa anyi min engagement, wannan shine asalin saninshi da sukayi ya kasance en course dinmu baki daya sun sanshi har kawoshi school bindawa tayi suka gaisa, da kaina naba suhail sweet amma sai yayi banza dani ya wuce, sai daga baya ya dawo yana cemin haushi na bashi, day before ranar ya ganni yana min magana nayi mashi banza sannan wai engagement dina saidai ya ji labarin a bakin bindawa, na bashi sweet yace,
"Ai sweet na yara ne shi kuma babu yara a gidanshi".
Sai kuma yayi min waving hannu yana smile ya juya ya shige motarsa, nace,
"Kishi kawai...".
K'aryar da Mahmud yayi min ta faru ne a wata rana muna waya, yace,
"Kullum sai naga Abba...".
Nace, "Tou ai wurin aikinku daya...".
Sai naji yace,
"Ai staff ne...".
Nace, "Ohhh kai staff ne?".
Ji nayi yace,
"Ehhh staff ne...".
Nace, "Aaahhh tou ya aikin?".
Wannan itace asalin k'aryar da yayi min, wannan itace wayar da na kunnawa Safeena da cousin dinsu recording dinta amma duk da haka cousin dinsu ta ci min mutunci ta zageni, sis imaging kece kina da saurayi har anyi maku engagement yace maki staff ne daga baya kika gane cewa k'arya yayi maki guard ne, gadi yake, tsakaninki da Aallah ya zakiji, dole zakiji babu d'ad'i, zakiji ya daukeki mayyar kudi ne, wato yana ganin ba zaki soshi saboda Aallah bane shiyasa yayi maki k'arya don ki soshi saboda abun duniya? Idan ba haka bane, miye? Ai gaskiya daya ce, duk da *BA NI DA LAIFI* amma kina ganin abun da ya faru, mutane sun gaza fahimtata, en gidanmu sun gaza fahimtata *KOWA LAIFINA YAKE GANI* bayan *BA NI DA LAIFI* sam, rayuwa kenan, ban damu ba koda mey za'a ce nidai nasan ina akan gaskiya, in auri makaryaci ince ma yaranmu mey, imaging yayi k'arya waje a turkeshi su fita ayi masu gori idan suka zo suka fad'i min ai babu d'ad'i, wannan yasa sam bazan iya auranshi ba, makaryaci ne.....
💛🧡💚💙🖤💜
*ba ni da laifi*
*Mariam, Mahmud and Aaryan love saga*
*By sl rimi family's*
*one love*
💛🧡💚💙🖤💜
0 comments:
Post a Comment