Ina zamu je yanzu ? Al ' Ameen ya tambaya ? Muje gidana Momy tana can tana jiranmu , juya kan sitiyarin yayi muka kama hanyar gidan Dikko , babu wacce nayi ma magana a cikin su kuma banyi ta wani fizge² ba kawai na tsaya ne naga iya gudun ruwansu nasan dai bana kasuwa a wurinsu saidai su dakeni , murmushi nayi mai sauti tare da binsu dukansu da kallon rainin hankali ,
Jiddah harararki takeyi , wacce aka kira da Jiddah ta juyo tare da yankamin wani irin lafiyayen mari harsai da gefen bakina ya fashe , murmushi nayi cikin takaici nace wallahi kinyi sa'a rayuwa taimani duka amma da yanzu²n nan na kifar da motar nan kowa ya mutu , me nayi muku kuka shigo rayuwata a dai² lokacin da nake kukan mutuwar mahaifina ?
Ɗayar tace munafika ji tana nuna kamar bata san komai ba , idan kin manta bara a tuna miki , ai kinsan Dikko ko ? Wannan matarsa ce ta nuna Jiddah ke ɗin banza ɗiyar mashayin giya jikar matsafi ki haɗa ƙirji da mijin ɗiyar masu wankakken asali , da sauri na rufe idona amma kafin ta rufe bakinta tuni nakai mata kaina da ƙarfi hancinta ya fashe jini yaci gaba da kwarara , cikin tsananin ɓacin rai nace ita jakar da kike magana itace baƙuwar Dikko ,
Da tun farko kun faɗamin ko suwaye ku da ba'asha wahala ba , domin ido na a buɗe yake inga macen da zata kalli mai girma Dikko in tsiyaye mata kwayar idanuwa ke dan ganganci ma aurenshi kikayi ko ? Hmm hawan doki ba linzami muguwar kasada ne domin in baka faɗo ba kasha wahala , idan kin isa ki kira Dikko a waya na kirashi dani dake a ga wayar waye zai riga ɗauka , matar sadaka dake ,
Gaba ɗayansu suka rufeni da duka a dai² lokacin da muka iso cikin harabar gidan , dukana suke tun daga cikin mota har waje suka jawoni , matar Dikko ta bugamin kai a jikin mota sai dukana sukeyi babu ji babu gani kamar an kama musulmin ɓarowa a chochie , murmushi nayi cikin wahaltuwa nace kinji haushi ko ? Nace miki matar sadaka !
Kiyi haƙuri mace ɗaya ce a zuciyar gwarzon namiji idan har akwaita to ba kowa bace nice , haka yake faɗamin kullum rana , kuma yacemin babu wata mace a duniya saini domin zuciyarshi da idanuwan basa ganin kowa saini , kunnen sa bayajin maganar kowa sai tawa ,
A dai² lokacin da Umar ya iso wurin yana ranki ya daɗe lafiya ya tambayi matar Dikko , sai kuma ya kalleni yace Sultana ya akayi kika zo nan ke kuma ? Goge hawayen baƙin ciki nayi sannan nacewa Umar Al ' Ameen ne yaje har gida ya ɗaukoni da ƙarfin tsiya , a gigice Umar ya kalli Al ' Ameen tare da zaro idanuwa yace da kanka ?
Wayarshi ya ciro daga aljihu yana wallahi saina faɗa mishi , ka kamo An mata da tsiya² ka rungumar mishi An matar shi ? Hmmm lallai akwai matsala dan nasan idan har naga mala'enka mutuwa tabbas nasan tafiya tazo wallahi yau babu abinda zai hana mai gida dawo katsina cikin daren nan ,
Jiddah tace ka kirashi ka faɗa mishi ni banajin tsoronshi , Umar yace yau zaki fara ji ki jirayi zuwanshi a dai² lokacin daya fara cewa ranka ya daɗe Al ' Ameen yaje har gida ya ɗauko Sultana kuma da ƙarfin tsiya ya jawota gata nan sai dukanta sukeyi kamar agola yaci zarafin ɗan masu gida !
Banji yadda Umar da Dikko suka ƙare ba suka jani mukayi ciki , a gaban mahaifiyar Dikko suka gurfanar dani tare da cewa Momy gata nan , kallona tayi sosai irin yanayin kallon da Dikko yakeyi irin kallon takeyi , itama dai kyakkyawa ce kamar buzuwa hutu ya tabbata ga kyakkyawar matar nan ,
Ɗan zamowa tayi daga cikin kujera tace yarinya ya sunan ki ? Ɗan kauda idona nayi dan bata girmanta nace suna na Sultana , meye tsakaninki da ɗa na ? Cikin ladabi nace babu , miye dalilin da yasa ya ɗauki mota ya baki ? Shiru nayi dan banda ansar bata , dake nake , nayi shiru , tace tou saurara kiji da farko zaki bada makullin motar nan aka kawomin shi , na biyu kuma ki fita daga harkar Dikko idan ma yana miki ƙarya yana sanki tou ƙarya yake miki baya sanki , ya faɗamin bakina da nashi yace halakar dake zaiyi da soyayyar shi ya kaiki ya baro ki , kuma tun yanzu ya kaiki ya dawo domin kin tafi kuma Dikko ya dawo , dama in banda baki da lissafi ya za'ayi a haɗa doki da jaki ? Siga ko a faɗar sunan ba iri ɗaya ne ba , ina ke ina zinari ? Matsayin Dikko ya wuce naki ki tuna idan kin manta , gidajen da kuke haya gaba ɗaya ya tattara ya siye ya mayar dasu gidan kiwon dokunan shi ,
"Yar talaka waye ya kaiki kiwon doki ? Jidda tace kuma ita ba jinin sarauta ba , Momy tace duk dinari sunanshi dinari akwai na talaka akwai na masu kuɗi wallahi Dikko babban zinari ne koda kuɗinka saida rabonka kuma ba'a saka irin kaɗɗararshi a caca tsaftatacce ne shi baida sirki ba'a haɗashi da komai ba ko goro baya ci bare yasha sigari ke ko naki uban kwalbewa yakeyi kuma saiya raba titi biyu tirrr da sanin zuri'ar da ubansu baya ciyar dasu ,
Tadai wulaƙanta ni sosai ta faɗi duk wasu sirrika na gidanmu abun dai babu daɗin ji , ta tozartamin Babana bawan Allah da yana can lahira duk a gaban Jiddah tayi min wannan wulaƙancin sannan ta rufe da cewa in tattara inbar garin katsina saboda jahar mijinta ne idan taji labarina kusa ² wallahi zata ɓatar dani , Al ' Ameen maida banza ka taho da makullin motar ɗana ,
Jiki a sanyaye na miƙe na kalli Al ' Ameen dake gefena nace mu haɗu gidanmu in baka , Momy tace ku haɗu a ina ? Ki bishi ku tafi tare , ko inda take ban kalla ba nayi gaba abuna yau banda inajin mutuwar Babana tana yagarmin zuciyata da babu abinda zai hanani na faɗawa matar nan miyagun kalamai masu zafi .
Da sauri na fita daga gidan zuciyata tana tafarfasa kamar zata zubo ƙasa saboda azabar zafi , nayi tafiya mai nisan gaske sannan na samu abin hawa , gashi banda ko sisi kuɗina an sace su duka , a ƙofar gidanmu na samu Al ' Ameen nacewa mai napep in ya jirani ina zuwa yace to ,
Gida na shiga na ɗauko mukulin mota na bawa Al ' Ameen ya tafi , shi kuma mai napep nace masa kana san katifa ? Dan gidan babu kowa duk kowa ya kama gabanshi , mai napep yacemin hajiya siyarwa zakiyi ne ? Nace Eh idan na samu masu siya dan siyar idan ban samu ba sai na bayar kyauta tashi zamuyi ....
Dame ² zaki siyar ne ? Nace katifa labulaye sai gas sai tukunya ɗaya bokitin wanka da dai sauran tarkacenmu na mata idan kuma kana da kuɗi kawai ka bani dubu 3 ka kwashe duka , da sauri ya warwaro 3k ya bani , muka koma dashi gida har ledar tsakar ɗakin saida ya cire ganin katifar mai mutunci ce yace hajiya bara na ƙara miki ɗari biyar nace ngode ,
Yana cikin kwashe kayan wayar Mamy ta fara ringing da sauri na ɗauka cikin wahalalliyar murya tace Mamy mu haɗu dake general yanzu ² tafiya za'ayi dani gida a daren nan , wane ɗaki kike ne ? Emargency da kinzo ki kirani amma karki daɗe nace tou , a wurin nabar mai napep na fice daga anguwarmu ina mai cike da kewarta.
Napep nahau babu ɓata lokaci muka isa general a lokacin har an fiddo matar za'a sakata a mota ina kiranta ta ɗauka na faɗa mata na iso , tace ta ganni itace aka kamo in matso inda suke , da sauri na matsa wurin duk na gaishe su suka ansa tacemin ina Mamyn take ? Cike da damuwa nace mata Aunty ta rigamu gidan gaskiya , ni nice Sultana , salati matar tayi tare dayin kabbara tace tou Sultana shiga mota muje , nace tou babu wani wasi² ko kokonto na shiga mota ahalinta suka shiga muka fice daga asibitin bansan garin da zamu ba....
01:30am ihun Al ' Ameen ya karaɗe kaf ilahirin girman gidan gwamnati , a ɗakinshi ya farayi mishi wata irin azzalimar shaƙara bayan an ƙwaƙwale Al ' Ameen daga hannunshi dakel , shine Al ' Ameen in ya fito da gudu ya nufi inda zai haɗo da Dady dan yasan duk girman gidan nan babu wanda ya isa ya hana Dikko yayi mishi wani abu saishi , kuma duk Umar ne ya ƙara zuga Dikko yadda ya kamata kuma duk zagi dacin zarafin da akayiwa Sultana saida ya laɓe yaji kuma ya faɗawa Dikko , tsakanin Abuja da katsina ji yayi tayi mishi nisa yaci titi yadda ya kamata Allah dai kawai ya kawoshi katsina dan Ashiru ma baiyi tunanin zaizo katsina da rayuwa....
Ihu Al ' Ameen yakeyi a taimakeni zai kasheni yayin da Dikko ya koma mota cikin ɓacin rai yabi Al ' Ameen da gudu , na bani na lalace gefe² ya riƙe hayewa inda mota bata hawa amma hankalin Dikko ya fita daga jikinshi duk mai lumfashin dake gidan nan babba da yaro babu wanda bai fito , cikin tashin hankali Dady ya tunkari motar yana Babana meye haka kakeyi wai ?
Da gudu Al ' Ameen ya ɓoye a bayan Dady cikin tsananin ɓacin rai Dady yace meya haɗaka dashi ne ? Al ' Ameen yace babu abinda nayi mishi kawai ina ɗaki kwance yaje yaita dukana da ya gaji kuma shine ya shaƙeni ,
Dikko da aka fito daga mota dakel yace babu abinda kamin ko ? Dady yace Babana wai meke damunka ne ? Cikin tsananin ɓacin rai yace saifa na kasheshi matsalata kafin na gano kanamun munafinci ne amma da zaran na gano ka tou babu sauran amfaninka a duniya da ƙarfin bala'e zan shaƙeka saina kashe ka hankalina zai kwanta ,
Momy data iso yanzu tace ka kashe tunda kai mahaukaci ne , kamar jira yake tayi magana ya fizgo Al ' Ameen yayi mishi kyakkyawar shaƙa yana zaka sake shiga sabgata ? Ina makullin mota ta dan ubanka ? Dady yace sakarshi Babana ! Dikko yaci gaba da cewa tunda kake kaga ina shiga sabgar wani a gidan nan ne ? Ubanka ne ya bata motar ko ni ? Har kaine ka isa ka taɓa An mata ,
Saida Al ' Ameen yayi fitsari a wando saboda azaba kuma anyi a cire Dikko daga riƙon da yayi mishi an kasa , saida Dady yasa hannu aka ciroshi dakel bayan Al 'Ameen ya suma , wani irin ihu Dikko yayi mai tada hankali yayi wata irin jijjiga ya sake tattaka Al ' Ameen zaiyi magana lumfashin ya tsaya ,
Su Ashiru suka ɗaukeshi aka shiga dashi ciki kamar yadda Dady ya bada umarni , cikin bedroom aka kai Dikko saman gado aka kwantar dashi , koda Momy ta shigo Dady cewa yayi ta fita baisan ganinta kuma wallahi idan bata fita harkar Baban shi da yarinyar nan da yake magana wani abu ya sameshi wannan Jiddah da kika matsa kika auro mishi wallahi saina sashi ya saketa , Dady yaci gaba da cewa ai nima ina da "yan uwa kuma suma suna da"ya "ya sai yaje ya auro yarinya mai ɗa'a da tarbiyar.
Kullum kina gidan yarinya ke ko kunya bakyaji kin hana yarinya ta zauna ɗakin mijinta kullum tana gidan surukai , tou kayi mata gori tazo ta kwana kuma ko Dikko baya aurenta nan gidan uwarta ne saita kwana kaje ka koreta tana can ta kwanta , tsoki Dady yayi mai nuni da bata da hankali ,
Nan yabar Momy tsaye ya ɗauko maganin Dikko ya zuba mishi a baki , da sauri ya buɗe idonshi maganar Umar taci gaba da dawo mishi wai Jiddah ta bugawa An mata kai a mota , ta daketa har ta fasa mata baki , kuma ka faɗawa Dikko saboda ni banajin tsoronshi , murmushi yayi ciwon mugunta ya tashi da sauri ya diro daga saman gadon ya fita Momy tabi bayanshi da sauri , kafin ta fito harya ɓace mata ya nufi part inta ,
Kwance ya samu Jiddah saman gado tayi ɗai² tana shan iskan A C bata da wata damuwa hankalinta kwance , ƙafarta ya riƙo ya jawota ƙiyyy a firgice ta buɗe idonta wayyo Allahna Yaya me nayi maka ? Dake da waye kuka je gidansu An mata ? A tsorace ta nuna mishi ƙanwarshi dake kwance gefenta tana bacci , kallon ƙanwar tashi yayi sannan ya sake kallon Jiddah yace bana dukanki amma ki tattara ki kama gabanki ki tafi gidan babanki babu wanda yaji babu wanda ya gani har sai na gano An mata ,
Idan baki tafi ba na rantse da Allah sakinki zanyi kuma saki na wulaƙaci da tozarci amma in kika haɗa ya nayi ² sai ki ɓace abinki babu wanda yaji babu wanda ya gani , idan wani ya kirani ya bani haƙuri zan sakeki ne , idan kika sake dawowa gidan nan ba tare da An mata ta dawo ba saki ne , idan har kika bari Momy taji ta zageni ko tamin faɗa saina sakeki ya ƙarasa maganar yana fizgo ƙanwarshi itama da sauri ta buɗe idonta wayyo Allahna na shiga 3 tasan haukan Dikko Yaya wallahi Momy ta aikeni itace tace naje , wani irin mari yayi mata saida ya bata kashin bala'e yace idan ta aikeki gobe sai kije ,
Kuma a gidan nan An mata zata dawo da zama idan akwai wanda ya isa saiya hanata zama na gani , wasu kwashe ² ma sunzo bare kuma matar ishashsshe , wallahi idan dai na ganta a daren nan saita kwana gidan kallon banza ko harara wani yayi mata saina makantashi har abadan duniya , Momy data shigo yanzu tace da Allah rufemin baki sakaran banza ka kawota gidan nan kaga yadda zanci mutuncinta a gaban idonka , baiba Momy ansa ba yace ma Jiddah kuma ki anso mata makullin motar ta kafin kiji babu daɗi ,
Momy tace makullin mota yana hannuna Jiddah zata riƙa hawa motar , taɓe baki Dikko yayi yace ba komai An mata dai ta hau ta bata kwance yana faɗin haka ya fita yaci gaba da kiran wayar An mata...
Dikko na fita Jiddah tace Momy idan Allah ya kaimu gobe zanje gida , Momy tace lafiya ? Jiddah tace tunda muka dawo daga america nake cewa zanje ² Allah bai bani ikon zuwa ba , Momy tace sai kuma cikin dare zaki faɗamin zaki ? Jiddah tace kiyi haƙuri Momy ai kwana biyu zanyi in dawo , Momy tace tou Allah ya kaimu , sun dai daɗe suna ɗan firarsu sannan kowa ya kwanta yayin da Jiddah tayi ƙudirin warware soyayyar Sultana daga zuciyar Dikko ,
Wurin Dady ya koma har yanzu yana kiran An mata amma taƙi ɗaukar waya ita ai dole tayi fushi , shi kuma bai daina kiranta ba , a gaban idona kiranshi yake shigowa kuma a gaban idona yake tsinkewa dukan kiraye ²n da yayi min ina ganin su,
Dan sai 10:58pm muka iso garin Daura , kuma tun muna hanya Dikko yake kiran wayata har yanzu kusan biyu da rabi yaƙi daina kirana , ni ɗaya ce kwance a ɗakin da aka bani gidan "yan gayu komai dai yaji bakin gwargwado matar da ta taho dani tace na kwanta da safe zamuyi magana ,
Hawaye ya cikamin ido tausayin Dikko ya kamani sosai dan abinda na lura idan za'a kwana a haka bazai daina kirana ba haƙura nayi na ɗauki wayar cikin kuka nace ka daina kirana mayaudari mai yaudararin kalamai , Dikko yace An mata wai mi yasa ke birkitaccen tunani gareki ne ? Kaine mai birkitaccen tunani ashe da kake cewa ka ƙagara gari ya waye kazo gareni duk yaudara ce , ka shirya munafircinka shine kasa aka wulaƙantani aka tozartani aka zage Babana da baisan irin rayuwar da nakeyi ba a halin yanzu , to na bar katsina sai ka zuba ruwa ƙasa kasha kuma daga nan gaba naci kada Allah yasa na sake ganinka ko a mafarki na , a haka dama kake tunanin zance ina tsanka ? Tou bana sanka na tsanake ׳ ,
Cikin hayani Dikko yace kada Allah yasa ki soni An mata idan baki so ni ba zan mutu ne ? Sai lallaɓaki nakeyi kin ɗaukeni kamar wani sakarai sai gagari nake tsakanin rayuwata da taki , baki saurarawa kiji abinda zan faɗa miki kije kiyi duk abinda kika ga dama idan kin tashi ma kibar Nigeria ƙarewar katsina nima kada Allah yasa na sake ganinki a barci na sai me , ƙaramar yarinya dake , sassauta murya yayi yace kiji tsoron Allah An mata domin ubangiji yana iya jarabtarki da irin soyayya da ya jarabeni da ita taki , me nayi miki haka kika tsaneni don Allah ? Haba An matana nasan kina san Dikkonki kuma kina tausayina kiyi haƙuri yanzu kina ina inzo ?
Fashewa nayi da kuka idan har nace bana san Dikko nayi ƙarya ina sanshi ׳ amma nasan babu yadda za'ayi gidansu su bari ya aureni saidai kawai mu dawwama muna soyayya , duk soyayyar da babu aure a cikinta ta zama shirme ni haka rayuwata zata ƙare tsanin sama da ƙasa ? Saina hau sai na sauko ? Me yasa zuciyata ta cuceni ta koyi soyayyar wanda tasan yafi ƙarfinta ,
A gajiye Dikko ya kwanta saman kujera 2siater yace inajinki kina ina ne ? Ina ina sai kuma nayi shiru , kina ina Nidai kayi haƙuri bazan faɗa ba , cikin sigar lallashi yace ai nasan zaki faɗa irin ɗan jan ajin nan ne na mata kuma duk a rasa wanda za'aja ma aji saini An mata ni ko bana iya ja miki aji wallahi saboda baida wani anfani inja miki aji ince na jawa wa aji ? Da kinsan yadda na ɗaukeki wallahi da baki fara tafiya kika barni ba , amma nasan kema wasa kike kina katsina ,
Ina katsina amma bana cikin katsina , yace ai na sani saboda wallahi inajinki kusa dani amma zaki ɓatamin rai a daren kuma dole sai kinyi saboda yarinta , baza ka sake samuna a waya ba , kuma baza ka sake gani na har abadan duniya ba , murmushi yayi tare da cewa ƙarya kikeyi , zaka gani shima yace kema zaki gani , yana faɗin haka na kashe wayata gaba ɗaya ,
Koda Dikko ya sake kiran wayar Sultana yaji ta kashe cikin ihu yace Dady ta kasheni , dan dama a gabanshi yake wayar , wallahi idan bata buɗe layin nan nima zan rufe rayuwata kowa ya huta ,
Cikin tashin hankali Dady ya dafe zuciyarshi yace Babana idan dai ka kasheni ka huta , shima Dikkon yace nima idan na mutu kowa ya huta wallahi idan bata buɗe wayar nan ba zan zama shafaffen a cikin "yan kwanakin nan , cike da iskanci ya sauko daga saman kujerar yana layi kamar yasha giya ya ƙoshi wurin firij ya nufa yana Allah kasa inyi kyakkyawan ƙarshe ashe iyakar ibar da nayo kenan ,
Da sauri Dady ya tashi ya nufi wurinshi a lokacin harya ɗauko ruwan sanyi ya fara sha hawaye na fita daga idonshi Dady ya riƙeshi yana cewa Babana wai miye kakeyi haka ne ? Ɗora rober ruwan yayi saman firij yace kaima ka fara jiyo ƙanshi mutuwar ne Dady ? Ka riƙe wannan daren domin zai riƙa ebe maka kewa idan bana raye , riƙeshi Dady yayi yana cewa baka dai so ka bar in zauna lafiya ko ? Dikko yace gangar jiki kaɗai ake tattali ba ruhin ba , idan akwai wani wanda ba'a so ya zauna lafiya to ba kowa bane nine ,
Wai me An mata tayi muku ne kuka tsane ta haka da yawa ? Naga shege ma mara uba ana aurenshi bare ita ba shegiya bace ba , kuma nasan namiji yana zuwa gidan karuwai ya auro mata ita a gidan wane karuwan take zaune ? Caca ² kowa saboda Babanta yayi caca sai ace bana aurenta ? Tou nima zan zama ɗan caca kuma na fara neman matan na sha giya shikenan sai ta zama matar mashayi , sassauta murya yayi cikin kuka yace na wahalar da An mata na bata azabar da duk lokacin dana tuna abinnan sai naji kunyar kaina....
Cike da damuwa Dady yace a , a Babana da hannu Dikko ya dakatar dashi bai sake magana ba ya ɗauki robar ruwan daya fara sha ya matsa wurin kujera ya ɗauki makullin motarshi ya fice , a lokacin har 3 na dare yayi , shida Ashiru suka fita daga gidan suka koma g r a gidan Dikko ,
Fitar Dikko Dady ya zauna ya zabga tagumi yana tunanin da bashida da gaira bare dalili ,
Ni kuma bayan na kashe waya na fashe da kuka nima wanda bansan dalilin yinshi ba , ji nake kamar in taho katsina in haɗu da Dikko zuciyata ta tabbatarmin cewa Dikko bazai taɓa wulaƙantani ba har abadan duniya , kwana nayi ina kuka kafin gari ya waye fuskata tayi jajir saboda kuka , idanuwana sun kumbara saboda rashin bacci , ko kalaci kasa cin komai nayi ina ta tunanin Dikko ,
Kwance yake yayi ruf da ciki ya kifa kanshi a katifa shi kaɗai yasan masifar da yakeji , bayan wani lokaci kuma ya juyo shima dai yaji masifar so yayi kuka har ya gode Allah , shi mamakin da yakeyi duk girmanshi a shekarunshi wai yake ma mace kuka , macen ma "yar ficiciyar yarinya wahalallen murmushi yayi mai ciwo a bayyane yace An mata baki da adalci kanki kaɗai kika sani , kema Allah sai kamaki bazai barki ki huta ba tunda kika hana marawuta zaman lafiya ,
A hankali ya lumshe idanuwan shi ya fara tunanin tun farkon haɗuwar shi da An mata , da abinda yayi mata da gishirin daya zuba mata ya korashi da ruwa , wayyo Allahna me yasa nayi haka ? A lokacin ina hankalina ya tafi ? Ina tunani na ? Dama baya zata dawo dana gyara wannan kuskuren wayyo Allahna , me yasa ² ? Wai me yasa sai nine aka zaɓa ? Wai wane hauka ya kani ? Kai An mata me ya sa kin cika taurin kai haka da yawa insha Allah ubangiji bazai barki kimin wasa da rayuwa ba wallahi sai kin nemo Dikko ina nan ina jiranki bazan sake zuwa ko ina ba sai kin dawo kuma sai kin kirani nima bazan sake ɗaukar wayarki ba sai kinzo kin bani haƙuri , yafa san baya hanani kuma baya ɗaga murya shine yakeyi ,
Ashiru yace mai gida dan girman Allah kayi haƙuri , Dikko yace kai baka da hankali na cuci yarinyar nan babu wanda yasan abinda ke tsakani na da An mata daga ni sai ita sai Allah , murmushi yayi yace An mata manya duk duniya inba ita ba waya isa ya mari Dikko ya kwana lafiya sai ita ta ɗaga hannunta mai daraja ta zabgagamin mari kuma nace ina santa tace na tsanake Dikko inba Ubangiji ba waya isa yayi wannan tsarin ? Saishi ubangijin samman da ƙassai , a hayaniyance yace sai kin dawo wallahi........ Tari yayi yaci gaba da cewa kema Allah ya zargeki tunda na dawo daga america na gani sama lumfashin ya farayi , a wahalce yace kuma wallahi bazanyi shiru ba saina faɗa , riƙeshi Ashiru yayi cikin damuwa yace mai gida don Allah , idon Dikko cike da hawaye yace shitttttt🤫 ya karasa yana fiddo kyawawan idanuwanshi , Ashiru yace don Allah , cikin hayani yace kaimin shir bai ƙarasa faɗa ba lumfashin shi ya ɗage.
Ƙarfe sha ɗaya da rabi na safe Al ' Ameen ya ɗauki Jiddah suka fara laluben hanyar kaduna ranta a ɓace amma babu yadda za'ayi ta faɗawa wani ayi ma Dikko magana kuma tasan wallahi kamar yadda yace zai saketa zai saketa addu'ar ta Allah yasa aga Sultana da wuri , kuma ko ta ƙarƙashin ƙasa saita shiga ta fita ta raba wannan tarayya...... Murmushi
Zaune nake a gaban matar da tazo dani , kwalbar data faɗin a waya ajiye a gefenta babu abinda ke cikinta sai tsutsotsi da wasu irin mahautan layu mataccen ƙwaɗon da Babana ya faɗa gashi ina kallo , gyara zama tayi tare da cewa jira Yayata tazo tacemin ta kusa isowa , cike da ladabi nace to Aunty , ji nake dama Dikko yana tare dani shima yaga abinda nake gani yana tayarmin da tsikar jiki........
08/10/2019
*JAMILA MUSA....*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 53
*_ƊAN MACE...! Sabon abinci yafi ɗumame daɗi 😋 na zaune makahon duniya , wasan kokowa bana gurgu bane hanzarta ki nemi naki karki sake ki bari a baki labari , tsohon hannu ce tuni ta shahara wannan marubiciya kuwa itace HAWWA MUH'D USMAN {{ real smasher }} ina tayaki murnar fara sabon littafinki ubangiji yasa yadda kika fara lafiya ki gama lafiya , Am3n..._*
Cikin tashin hankali Ashiru ya fara kiran wayar Momy dan ya sanar da ita halin da mai gidanshi yake ciki , koda ya faɗa mata cewa tayi ko nazo ba abinda zan mishi dan maganinshi yana hannunshi ka nema ka zuba mishi a bakinshi ,
Kallon Dikko yayi yace Hajiya wannan ba irin waccan ciwon bane ba , tsoki tayi tare da kashe wayarta tana masifa cewa ni mutuwarshi bata wani hanani nayi rayuwata dan wanda ya mutu shi jin daɗi ya ƙare mawa danni a halin yanzu banda wani abinda ya isa ya tashi hankali na , mijina kawai zai kwanta ya mutu in tashi hankali ba Dikko ba ,
Ƙanwar shi daya zane jiya tace Momy miye ? Cike da masifa tace Dikko ne kinsan shi idan bai ɓatawa mutane rai ba hankalinshi baya kwanciya ni yanzu bazai sake tayarmin da hankali ba saidai ya tada ma ubanshi danni na gaji da iskanci shi , tunda na haifi Dikko duniya ya hanani in zauna lafiya dan yaga bana so ya shiga damuwa shi yasa duk hanyar da yasan zaibi ya tadamin hankali yasanta ,
Meya sameshi yanzu kuma Momy ? Ta tambayi mahaifiyarta cikin damuwa , tashi Momy tayi daga palon tana cewa koma miya sameshi cansu ta dama ba abinda ya dameni , ɗan uwa da ɗan uwa sai Allah duk dukan da Dikko yayi mata jiya ta manta dashi ta ɗauki wayarta ta fara kiranshi , Ashiru ya ɗauka tace ina Yaya ? Ashiru yace baida lafiya ,
Bashi waya mana , cikin damuwa yace ai baya iya magana , kamar ya baya iya magana ne ? Tayi maganar cikin tsawa , shiru Ashiru yayi tare da kashe wayar , wayyo Yaya...... Momy Yaya fa baya magana kuma an faɗa miki zakice ba ruwanki ? Daga ciki Momy tace ba ruwan nawa ke mai ruwa sai kije kiyi.
Cike da tausayin ɗan uwanta ta fara kiran wayar Dady amma bai ɗauka ba ta kirashi yakai ×3 baya ɗauka kawai ta tura mishi text Yaya bashi lafiya !
Ashiru kuwa ya ɗako magani ya zuba² amma kamar ana zubashi a ƙasa Dikko ya ɗauke gaba ɗaya sai hawaye dake gangarowa daga gefen idonshi , cike da tausayi Ashiru yabi mai gidanshi da kallo yana tunanin tou wane irin sirrin ne yakeyi da Sultana da yace Allah kaɗai yasan tsakaninsu yace babu wanda yasan abinda ke tsakaninsu daga shi sai ita sai Allah , wannan wane irin sirri ne mai ƙarfi haka......?
A wannan hali Dady yazo ya samu Dikko , fuskarshi ɗauke da damuwa yace ma Ashiru ya koma palo , fita Ashirun yayi Dady yabi Dikko da kallo bayan wani lokaci ya saka hannunshi a aljihu ya ɗauko wani garin magani ya shaƙa mishi a hanci tari Dikko yai tayi yana atishawa , saida ya ɗauki wani lokaci yana tari da atishawa sannan ya dawo dai².
Cikin natsuwa Dady ya kalleshi yace Babana kana neman dai ka kasheni ko ? Ka hanani in zauna lafiya kullum jini na a saman akaifa ko wadataccen bacci bana samu kullum zuciyata a takure take banda walwala bare kwanciyar hankali wannan fitinar daka tsiro da ita ba kanka kake wahalarwa da ba , ni kake ba wahala duk duniya baka da jigon daya wuceni idan har ka bari wani abu ya sameni ko na mutu taka ta ƙare ,
Cike da ladabi yace kayi haƙuri na bari , Dady yace kai zan ba haƙuri , Dikko yace insha Allah bazan sake ba , Dady yace da ka taimaki rayuwata , saida ya tabbatar Dikko ya dawo hayyacin shi sosai ya tafi tare da jaddada mishi ya daina fushi da tunani tunda yasan baida cikakiyar lafiya , kuma yaje gida da daddare yana nemanshi , da kanshi yayi ma Dady rakiya har wurin mota saida ya tafi sannan ya dawo palo wurin Ashiru ya kwanta.
Ni kuma ɗaki na koma na cire wayata daga jirgi na fara kiran wayar Dikko , duk kiran da nake mishi yana gani yaƙi ɗauka dan yayi alƙawari cewa sai nazo da ƙafafuwana na sameshi idan dai ya furta zaiyi ko zai mutu saiya yayi , tun ina kiranshi yana basarwa ƙarshe sai ya riƙa rejecting , nima na daskare naci gaba da kiranshi bayan wani lokaci ma kashe wayarshi yayi gaba ɗaya ,
Murmushi nayi maicin rai a bayyane nace ni zaka wulaƙanta ina kiranka ka kashe min waya nima har abadan duniya bazan sake kiranka ba na ƙarasa maganar tare da maida wayata a jirgi.
Ranshi a ɓace ya kalli Ashiru yace zanyi tafiya zakaje ? Dariyar jin daɗi yayi tare da cewa mai gida zanje mana amma kace baza ka sake zuwa ko ina ba sai Sultana tazo , hmmm manta da An mata Dikko ya bashi ansa...
Saida na ƙara yin kuka sosai sannan na sake cire wayata daga jirgi na ƙara kiran Dikko , har yanzu wayar a kashe take ci gaba nayi da kira har matar da ake jiran zuwanta ta iso amma Yaya DK bai buɗa waya ba , yayi fushi dani yayi tafiyarshi London ya manta dani ,
Sultana ....! Aka kira suna na daga palo da sauri na tashi na fita ba tare dana ansa kiran ba , gaishe da matar nayi bayan na samu wuri na zauna , ansawa tayi cikin sakin fuska tace sannu baiwar Allah , murmushi nayi mai ciwo dan yanzu duk duniya banda damuwar da tafi rashin Dikko a tare dani...
Auntyn da tazo dani tace Yaya kinga kwalbar nan kallo ɗaya tama kwalbar ta kauda idonta tare da neman tsari daga azaluman mutane a wurin ubangiji , abin babu kyan gani gwanin tashin zuciya da tashin hankali , Auntyn da tazo dani tace tare da ita za'a tafi ne ? Yayar ta tace a , a cewa yayi kawai na anso kwalbar na kai mishi , Aunty tace gata nan , kwalbar matar ta ɗauka tare da cewa saina dawo zuwa jibin insha Allah , godiya Aunty tayi sosai wa "yar uwar ta , ita kuma ta tafi tana mai addu'a ubangiji ya yanke wahala.
A daddafe nayi kwana ukku , ga ciwon mutuwar mahaifina dake nuƙurƙusar min zuciya , ga maraicin Dikko dake damuna gashi banda abokin fira kuma gidan ba'a fita gashi ni ban saba da Auntyn da tazo dani ba , abubuwa dai duk sun dameni na rasa inda zan saka raina naji sanyi , duk alƙawarin da nayi bazan sake kiran Dikko ba na kasa kullum saina kirashi kuma har yanzu wayarshi ya rufeta.
Al' Ameen da yakai Jiddah ƙin dawowa yayi wai sai ranar da zata dawo zasu taho tare , haɗuwa sukayi sukaci gaba da gulmar Sultana yayin da Al ' Ameen ke cewa ai Sultana asiri tayi ma mai gida ta gama dashi danshi tunda yake duniya ma bai taɓa ganin mai gida yana shiga sabgar mace ba sai akan yarinyar nan , tayi mishi asiri na gani kasheni , idan dai kina san zaman lafiya ki miƙe tsaye ki fitsare ƙafafuwanki.
Jiddah tace aini bansan ta ina zan fara ba , Al ' Ameen yace ina da malami a zaria zan kaiki amma karki fara neman mai gida dan ɓannar kuɗinki zakiyi saboda yana da addu'a sosai , banda toshewar basira irin na Jiddah yanzun nan Al ' Ameen ya gaya mata cewa Sultana ta nemi Dikko da asiri fa , amma ita yace mata kar ta nemi Dikko da asiri wai ɓannar kuɗinta zatayi , yaci gaba da cewa saidai ita yarinyar a firgitata a saka mata shakkun mai gida a zuciyarta , idan ta ganshi tayi kamar taga cici , Jiddah tace tou haka yayi yaushe zamu je ?
Al ' Ameen yace bara inyi waya dashi saiya fitar mana lokaci da kanshi , Jiddah tace ngode Al ' Ameen da Allah ya haɗani dakai da na shiga gararin rayuwa , tayi godiya sosai shima ya gode tare da fitowa daga palonta ,
Bayan ya fito yayi dariya yace sakarar banza zan kaiki malam yayi ta ɗirka miki asirin da ke da kanki zakice mai gida ya sakeki , ina ansar taimako ina kaiwa Mardiyya insha Allahu sai mai gidana ya auri Mardiyya zuri'armur zasu fita daban yarinyar "yar uwata ta samu sa'ar rayuwa , ita kuma Sultana zamu goge labarin mai gida daga zuciyarta , shi kuma mai gida soyayyar da yake ma Sultana sai a juya sunan Mardiyya a kan soyayyar da yake ma Sultana , sai ya koma san Mardiyya wannan shine mafita , Yeeee wannan shawara tayi , yayi "yar rawa tare da taɓawa cikin farin ciki.
*_London_*
Dakel ya juya kwanciyar shi cikin yanayin gajiya idanuwan shi a rufe , miƙa yayi sosai yace An mata , saida ya gyara kwanciya yace duk ki gama yarintarki da duk abinda kika ga dama insha Allahu duk duniya baki da miji saini , buɗe idonshi yayi a hankali yaci gaba da cewa ni wallahi tausayi kike bani dana tuno na tattara fushi na da ƙarfina na sauke a kanki sai tausayinki ya kamani , tsoki yayi tare da saukowa daga saman gado yana cewa banso ranar tazo a haka ba , amma ya na iya yadda ubangiji ya tsara kenan.
Toilet ya shiga bai wani daɗe ba ya wanko bakinshi da fuskarshi ya fito , Ashiru ne ya shigo cikin bedroom in ya miƙawa mai gidanshi waya wai Jiddah tana kira , ansa Dikko yayi ya kara wayar a kunnenshi tare da cewa inajinki ,
Cikin soyayya da gogewar kalamai tace haƙuri na kira in bada ranka ya daɗe , sai yanzu na gane nayi kuskure kishinka ne ya rufemin ido har na aikata abinda bakaji daɗi ba , amma ka gafarceni insha Allah haka bazai sake faruwa ba kayi haƙuri don Allah , waye ya faɗa miki bana nan ne ? Cike da ladabi tace Momy ta kira Hajiya tace kayi rashin lafiya , sai tace zata zo ta ganka shine Momy tace baka nan amma zata turo mata number ka ni kuma data turo saina ɗauka in bada haƙuri.
Ajiyar zuciya Dikko ya sauke shima cikin kulawa yace ba komai ya wuce , tou Yaya zan koma dan Allah , a , a , haba Yaya ka rufamin asiri don girman Allah ka barni na koma , Dikko yace keyy..... Jiddah tace Allah baka lafiya yasa kaffara ne , yayi kyau ya ƙarasa tare da kashe wayarshi.
Kallon Ashiru yayi bayan ya gama wayar ya nuna mishi hanyar fita da hannunshi , da sauri Ashiru ya fita shi kuma yaci gaba da tunanin An mata......
Kwance nake saman gado na ƙurawa wayata ido dan yanzu na cireta a jirgi kwata² ina tsammanin kiran Dikko ko wane lokaci , Yayar Aunty ce ta shigo dan sun daɗe suna kirana banji ba hankali ya tafi tunanin Dikko , dan na kalli hotonshi dake cikin wayar Aunty Mamy wanda Al ' Ameen yasa a d p inshi Aunty kuma ta ajiye hoton a ma'ajiyar hotunan cikin wayarta , nasha kuka har na gode Allah dan idan zan kalli hoton shi so goma sai nayi kuka sau adadin kallon da nake ma hoton.
Dafani tayi na dawo a firgice tare da goge hawayen idona ina sauke ajiyar zuciya , murmushi tayi mai haɗe da cewa sannu , nima murmushin nayi na sauko daga saman gadon na gaisheta , ansawa tayi cikin sakin fuska tace muje tayi gaba nabi bayanta ,
A palo , Auntyn da tazo dani ce a saman keken guragun ta , sai Yayar Aunty sai wani babban mutum yasha rawani zubinshi dai irin na malam zaure ne , duƙusawa nayi na gaishe su cikin ladabi , cike da kulawa ya ansa tare da cewa sannu baiwar Allah , nace yawwa,
Shi kuma yaci gaba da cewa cikin hukuncin ubangiji abinda ya faru shekaru da dama da suka wuce Allah ya bada iko cikin hukuncin sa da yaddarsa ya warwareshi , bamu yi ƙoƙarin bincike ba saidai nayi amfani da bayanin da Hajiya Suwaiba tayimin ya nuna Auntyn da tazo dani yaci gaba da cewa.
Hajiya Mamy kafin ta rasu tace duk musabbabin abinda ya janyo wannan rikici da tashin hankali da jefe² duk sanadin ɗaukar budurcin matar Bello ne wanda shi Binna yayi a matsayin ɗaukar fansar abinda akayi ma yarinyar da ya zauna gidansu ,
Wannan dalili yasa shi Bello ya ƙwallafi marigayi Binna a zuciyarshi wannan itace ƙiyayyar dake tsakaninsu , kafin haka kuwa abinda ya shigo da Bello a rayuwar Binna shi ɗan uwan Binna wanda suke Baba ɗaya shine ya turo Bello a rayuwar Binna bayan mahaifiyarshi ta haɗa tuggun da mahaifinshi ya korashi daga gida ,
Taga ya tafi bai lalace ba shine ta tashi hankali su kuma "ya "yanta suka taimaka mata wurin ganin sun cika mata muradin ta na ganin Binna ya lalace dashi da ɗan uwanshi kuma babu abinda sukayi mata haka kuma mahaifiyarsu Binna batayi mata komai ba , da sukaji labari su Binna sun samu gidan aiki da ake kula dasu , shine suka nemi hanyar lalatashi wannan dalilin yasa suka tura Bello ya shigo rayuwarshi ya shanmace shi da sihiri ya samu damar afkashi a wasan caca kuma suka fidda ma Binna tunanin waiwayar gida , ana cikin haka ne kuma Bello ya lalatawa yarinyar gidan dashi Binna yake zaune rayuwa sai aka korasu , Bello kuma yajasu suka zama suna ƙarƙashin ikonshi har Allah yasa shi Bello yayi aure Binna ya ɗauki budurcin matarshi a daren ranar da ango zai shiga ɗaki.
Daga nan sukayi faɗa na tashin hankali suka rabu , bayan rabuwarsu ne "yan uwan Binna suka tura Bello akan kar ya sake ya yadda ya nemi Binna ya bashi haƙuri idan ya dawo rayuwarshi shima ya ɗauki fansa akan kaff ahalinshi ,
Haka yabi kaf ahalin Binna yaci gaba da jifarsu , amma saiya lura hankalin Binna baya kansu bai kuma damu da lalacewarsu ba , yaci gaba dai bai daina ba har Allah ya kawoki kuma mahaifinki ya ci buri akanki kuma yaso kiyi ilimi mai zurfi ganin Binna dai ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗora miki yasa Bello ya juya akalar tsafinsa akanki shine yaje yayi wannan tsibbacin nasa wanda kuma ubangiji ya kawo ƙarshenshi da izininshi da yaddarshi kuma an warwareshi , ga magunguna nan Hajiya zata faɗa miki yadda zakiyi amfani dasu.
Gyara zama nayi na kalli Hajiya Suwaiba nace Aunty da kika kirani kince an tafi a kashe Babana su waye suka tafi kashe shi ? Kuma ke me kikeyi a wurin lokacin da kikemin waya me yasa kikayi ihu bayan ke kuma na ganki baki da ƙafafuwa ya akayi kika je wurin..........?
Cike da damuwa tace bani bace kikayi waya dani , yadda kika ga wannan kwalba da wannan waya da na kiraki da ita ina kwance a saman gadon asibiti Allah ya kawo min matar da kikayi waya da ita batamin bayanin komai ba tadai bani wayarta tacemin amana ce aka bata kuma itama ta bani amana , tabbas tamin maganar Mamy idan baki manta ba da kika zo asibiti ai kinji nace miki ina Mamyn take ? Bansan Mamy ba amma matar ta nunamin hoton Mamy a cikin wayarta ,
Wannan bawan Allah kuma da kike gani itace tace in duba cikin wayar ta zanga lamba an rubuta malam ɗayyu inyi ƙoƙari na nemeshi shine zai kawo karshen matsalarki domin tamishi bayanin komai , ni banda ƙafafuwa shi yasa na kira "yar uwata bayan ni nayi waya dashi malam ɗayyu ya faɗa mana mazauninshi shine na tura Yayata takai mishi kwalbar ,
Idona cike da hawaye nace shin ina ita matar data baki wayarta da kwalbar nan take ? Aunty Suwaiba tace bansan inda take ba domin tana saƙamin a cikin bargon da nake lulluɓe dashi naga wasu mutane sun shigo suna nemanta ita kuma tabi ta wata hanya ta fice , ba'a sallameni ba gudun bi baya yasa nima na baro asibitin dan bana san rayuwata ta sake komawa cikin matsala.
Kai ׳ innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , Allah ngode maka ubangiji ya bayyani min duk masumin wannan bita da ƙulli , an kashe Aunty Mamy , an kashe Babana ita kuma wannan tana raye ko tana mace oho ? Ya zamar min dole nabar gidan baiwar Allah nan da bata san sake mayar da rayuwata a damuwa ita kuma meya faru da nata rayuwar ?
Kallon malam ɗayyu nayi tare da cewa shin ko kasan inda gidansu Babana yake ne ? Yace yasan gidan a katsina yake ƙofar marusa , nace kai a wane gari kake ne ? Yace katsina yake , miƙewa nayi tsaye tare dayi ma Aunty Suwaiba godiya na koma ciki na tattaro wayoyina ina dawowa palo nace ma malam ɗayyu muje katsina.
Miƙewa yayi tare da tattara magungunan daya zo min dasu yayi gaba , ni kuma na duƙa a gaban keken guragun ta nace Aunty ngode sosai zan tafi amma zan dawo domin ina sha'awar jin wace irin rayuwa ce kikayi ta baya wacce har baki so ki sake komawa cikinta , miƙewa nayi tare dayi ma Yayarta sallama na fice daga palon ina kewar mutanen kirki irinsu Aunty Suwaiba amma tabbas akwai dawowa bayan kowa ya ajiyewa kowa lambarshi a cikin wayarshi......
Ƙarfe 7:43pm acikin garin katsina tayi mana wanda malam ɗayyu shine ya jawo motar tun daga daura har zuwa cikin birnin garin katsina , kai tsaye ƙofar gidan su Babana muka tsaya , ina ƙoƙarin fita daga motar naga Baban Hafsa ya fito , kallonshi nayi sosai yayin da Bello ke biye bayanshi , kallon malam ɗayyu nayi nace lallai² nan gidansu Babana ? Yace shakka babu wannan shine .
Dogon nazari na tafi anya Baban Hafsa yasan ni ɗiyar ɗan uwanshi ce kuwa ? Da babu Bello dana sauka nayi masa magana na gani ko zai ganeni ? Kenan wannan shine dalilin da yasa Mamy tace da Binna yasan wace ce Hafsa a wurinshi da ya haɗiye zuciya ya mutu , a bayyane nace ummm tare da taɓe bakina naci gaba da cewa ƙaddara da ajali ba'a kauce musu tou amma kuma meke tsakanin Hafsa Amisty da Babana ? Wannan ansa banda mai bani ita itama.
Daga gidan su Baba gidan Baba Ƙarami muka nufa na nuna masa zan zauna ne zuwa wani lokaci amma saboda tsabar shi butule ne ya manta da irin karamci wanda mahaifina yayi mishi ya shafawa idonshi kwallin rashin mutunci yayi min wulaƙanci na ƙarshe tare damin gori karuwar banza karuwar wofi wacce ubanki ya mutu a gidan caca.
Kallon Baba Ƙarami nayi ƙasa da sama nace aiko caca ta gama maka komai tunda harya ciyo gida ya baka kake zaune dan na tabbata da "yan uwana sunsan wannan magana wallahi da sai sun ƙwace gidan nan sunce na magada ne , kuma da kake cewa ya mutu a wasan caca kai kaga yadda taka ƙarshen tazo maka ne ? Kuma da kacemin karuwa inda na gode Allah tambarin ba a kaina kaɗai yake ba kaima kana da taka karuwar zaune a gida.
Cikin hayani yace ni ban haifi karuwa ba kuma bazan haifeta ba har abadan duniya idanma nasan ina da karuwa a gidana saina kashe ta ko an faɗa miki ni lusarin ubana ne ? Nace shima uban nawa ba lusaranci ya janyo mishi haka ba ƙaddara ce kuma babu wanda ya isa ya goge ƙaddara , haka kuma shiriya ba iyawar kowa bace ba daga Allah ne kuma na rantse da Allah idan baka barni na zauna gidan nan ba saina nemo "yan gidanmu sun anshi gidan ubansu tunda ba takadda ya rubuta ya baka shi daga duniya har lahira ba ,
Matanshi suka sako baki wallahi bazan zauna musu gida ba na lalata musu tarbiyar "ya "ya inji maman safiya , kallonta nayi nace aike taki ta daɗe da lalacewa ko kina tunanin bansan komai ba ? Naci gaba da cewa ƙofar soro , asibitin da akayi komai ke hatta gidan da aka samo tukuicin da niƙaf taje , da sauri Safiya ta tashi tayi cikin ɗaki , uwarta ko ta kama bakinta bata sake magana ba gudun kar in tona mata asiri a gaban kishiyoyi ,
Tunda abokan zama sukaji haka kowa ta fara ɗakinta zan zauna sarai na gane dan suji labarin abinda Safiya tayi amma sam nace ɗakinsu Safiya zan zauna , uwar Safiya kuwa bata sake magana ba shima Baba Ƙarami ɗaureren azumin magana ya ɗauka , waje na koma wurin malam ɗayyu na anso magunguna na bayan yamin bayani duk yadda zanyi amfani dasu , godiya nayi masa na anshi lambar wayarshi tare da cewa saina shigo.
Satina biyu a gidan Baba Ƙarami na kammala kaf magungunan da Malam Ɗayyi ya bani , natsuwa ta shigo cikin kaina tsoron Allah da gudun duniya ya dawo amma kaf iskancin da kuka sani yana nan ɗibge akaina saidai idan ba'a latsomin wurin ba ,
Ranar dana cika sati biyu cif ranar na ɗagawa Baba ƙarami hankali saiya maidani makaranta , yace min baida kuɗi nace aiko ni ba'a gayamin babu duk inda zai samo kuɗi saiya samosu ya maidani makaranta , yacemin wallahi baida inda zai samosu , dole na haƙura amma na yanke zan kira Alaji in jaraba sa'a na gani ko an dace amma kafin nan zan koma islamiya in fara hadda.
Da daddare na tambayi Baba Ƙarami ƙarfe nawa yake rufe gida ? Yace min ƙarfe 10 idan har goma ta wuce koda minti ɗaya ne saidai mutum ya kwana waje , nace tou babu damuwa , saida nayi alwallah sallar isha'e na kira Alaji nayi masa kwatancen gidan Baba ƙarami nace mu haɗu dashi yanzu da Allah ina san ganinshi yace yana zuwa.
Ban daɗe da gama sallah ba yazo , bayan na fita ko gaisawa bamuyi ba nayi masa kwatancen wurin da Baban su Hafsa yake zama nace masa can zaka kaini , ya tada mota muka tun kari wurin kai tsaye....
12/0/10/2019
*JAMILA MUSA...*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 54
Har muka isa daga ni har Alaji babu wanda yayi ma wani magana a cikinmu , kuma munyi sa'ar samun Baban Hafsa kamar dai yadda nayi tunanin dama zamu sameshi , gabansu nasa Alaji yayi parking ban fito daga cikin motar ba na sauke gilashin gefe na tare da cewa Assalamu Alaikum....
Cikin farin ciki ya ɗago daga latsa wayar da yakeyi jin muryana , ba tare daya ansa sallamar ba yace Hajiyata da kina duniyar nan ? Kin kama waya kin rufe ruff , saboda kunsan layina na farko Dikko ne ya karya shi , nace Ey wallahi , tasowa yayi daga cikin mutane yana kaucewa inda babu jama'a cewa fito kiji mana.
Fita nayi daga cikin motar nabi bayanshi bayan wata container dukanmu muka tsaya , kusa dani ya matso sosai ya riƙemin ƙuguna magana ƙasa² yayi cewa haba ina kika ɓoye haka kika barni ina ta garari a garin nan na rasa ina zan samu labarinki ? Shiru nayi ban bashi ansa ba kuma ban cire hannunshi daga riƙo da yayi min ba ,
Yace ya na ganki duk rai a haɗe ko anyi miki wani abu ne ? Ajiyar zuciya na sauke tare da cewa Binna , me Binna yayi miki ne ? Neman sa nake saina ga bayanshi , kashe shi zakiyi kenan ? Nace tabbas kuma ba gudu babu ja da baya , amma me yayi miki haka da ciwo wanda kikayi ƙudirin ɗaukar fansa rayuwarshi haka babu sassauci.....?
Cikin ƙunar rai nace shin ko kasansa ne ? "Yar dariya yayi ta duniyanci sannan yace ai wani ya rigaki shafe labarinshi a duniyar nan , ɗago kaina nayi na kalleshi nace wane mai zarra ne haka wanda yafi mace zafin nama ? Baban Hafsa yace abin duhu ne amma ke wane irin duhun ya baki na rayuwa haka ?
Sauke hannunsa nayi daga riƙon da yayi ma ƙuguna nace , shin wai da kake tambayana duhun da Binna ya bani kama san waye Binnar tukunna ? Ni kuwa nasan Binna domin Babanmu ɗaya dashi , kamar walƙiya haka naji duniya ta juya , cikin dakiya nace amma kasan ɗan uwanka ne ka barni nake furta kalmar kisan sa daga bakina ? Sake rungumoni yayi ya rumgumeni sosai , kunsan akwai runguma akwai rungumewa tou rumgumewa yayi ya kwantar da fuskarshi a saman ƙafaɗata , hawaye ya cikamin ido wato wannan shi Yayan Babana ne ?
Goge hawaye na nayi tare da saita muryata nace me yasa bakwa zuminchie da Binna ne ? Har yanzu yana kwance a saman jikina , cikin disashshiyar murya yace aishi kanshi Binna bai isa yasan ni wayen shi ba bare kuma "ya "yanshi , banma san gidan da yake zama ba amma kaf rayuwarshi da duk wani motsinshi a tafin hannuna yake ,
Amma me yasa ka sakawa rayuwarshi ido bayan kuma ya fita daga rayuwarku ? Ai bashi ya fita daga rayuwarmu mune muka fitar dashi , akan wane dalili ? Ɗago kanshi yayi tare da sunbata ta yace labarin yana da tsayi ni kuma na yanke miki wahala tunda an sheƙar miki da Binna zuwa duniyar mutuwa...
Murmushi nayi mai nuni ina farin ciki amma a baɗinance ina cikin tashin hankali , ƙarfin hali nayi tare da cewa labarin yana da tsayin gaske amma duk meye musabbabin fitinar taku ne.... ? Murmushi yayi tare da shafa gefen fuskata yace keko kuɗi ne silar komai , yanzu dai zamu ɗan rage dare ne ko yadai.... ?
Share maganar nayi da cewa wai kasan "ya "yan Binna kuwa ? Taɓe baki yayi cewa shi kanshi Binnar dakel na sansa bare wasu "ya "yanshi can na wahala , dariya nayi nace tou ina da sharaɗi ɗaya tak zanyi tarayya dakai amma duk wata so ɗaya ka yadda ? Yace Eh na yadda , nace yau nawa ga wata ne ? Ya faɗamin , nace tou ni bana zini a farkon wata da tsakiyar wata sai ƙarshen wata kuma shima ƙarshen wata sai daren da wata zai fita haka yayi maka ne ? Eh na yadda nace tou idan Allah ya kaimu gobe dani dakai mu haɗu a *Erudite comprehensive sch*.
Me zamuyi a makaranta kuma ? Zubin adashe zaka fara dan zan koma makaranta ne kuma itace makarantar da nake so , sabon machine uniform littafai da duk abinda makaranta ta buƙata zaka biya ne sai ka biyamin kuɗin makaranta tun daga aji 1 zuwa aji 3 idan haka yayi maka mu ƙulla tarayya dakai bana san surutu ka kame bakinka kayi shiru abinka kamar yaro ya kama nonon uwarshi....
Zai sake magana nace yi haƙuri 9:44pm zan tafi gida ana rufe mana ƙofa 10:00 , mu haɗu makarantar idan Allah ya kaimu gobe misalin 12:30pm kuma karka zo da aboki ko ɗan rakiya , ina faɗin haka na wuce da sauri na koma cikin mota Alaji yaja muka tafi...
Tunda na shiga motar wasi² nakeyi kenan Hafsat "yar uwata ce da Baban Hafsa da Babana babansu ɗaya ? Tou wane irin sirri ne kuma Aunty Mamy ta ɓoyemin wanda tace da Binna yasan matsayin Hafsa a wurinshi daya haɗiye zuciya ya mutu ? Tunani nayi mai zurfi zuciyata ta faɗamin cewa ko shima Baba kwarto ne ? Da sauri nace astagafurillah , ita kuma Amisty ya muke da ita ne ? Hmm Allah ka iya mana ,
9:57pm a ƙofar gidan Baba Ƙarami tayi mani nacewa Alaji yayi haƙuri yaje zamuyi waya idan na shiga ciki yace tou , kuɗi ya bani har 10k ina san Alaji ko ba komai akwai kyauta , godiya nayi na shige ciki , ina shiga Baba Ƙarami ya fara banbamin bala'e daga gidan uwar wa kike a tsohon daren nan ? Balbaɗaɗɗa irin iskanci da kika saba a gidanku idan kikace zakimin shi nan saidai ki tattara ki kama gabanki "yar iska karuw...... Kuɗin hannuna na miƙa mishi duka sai yaci gaba da cewa Allah yayi miki albarka ubangiji ya ƙara koro kasuwa yasa kifi haka matsayi.
Ban mishi magana ba nayi cikin ɗaki , maman safiya kuma tace sai ki kwashe duka ki bashi ai ya kamata ma ki riƙa biyan kuɗin hayar ɗakin nan , ko inda take ban kalla ba na kwanta tare da saka airpiace a kunne na ina sauraron firata da Baban Hafsa , bayan na gama ji tass nayi murmushi tare da kiran wayar mutumina amma a kashe take har yanzu , saida na kalli hotonshi sannan nayi bacci.
Jiddah da Al ' Ameen zaune a gaban bokansu ya kwarara ihu tare da ɗirkaka uwar ashariya bayan duk sun kora mishi bayani , roƙo na farko abinda aljannu suka buƙata shine a basu jinin jariri sabuwar aihuwa , matakin farko kenan , mataki na biyu kuma idan ba'ayi wannan ba ita Jidda zata kawo jinin al'adarta , mataki na ukku shine za'a kawo maniyin Dikko , wane kuka zaɓa ne ? Boka ya tambaye su ,
Cikin rawar jiki Jiddah tace haba a ina za'a samu wani jinin jariri ne ? A daina maganar jariri gaskiya , wata irin dariya bokan yayi mai firgitarwa , yace arne zaisha jini ne shine zai shiga zuciyar ita yarinyar ya sanya mata wasi² , idan kuma kika bayar da jinin al ' adarki duk duniya yadda Dikko zaiji maganarki ko ta uwarsa bazaiji haka ba , idan kuwa aka kawo maniyinsa labarin yarinyar ya goge a zuciyarshi kwata² har abadan abada zaima manta daya taɓa sani wata yarinya wai ita Sultana , bazai sake san wata mace ba sai ke , ke ɗaya ke ya sani kuma ke zaiyi ta ƙauna har a mutu , Hahahahaha.....
Jiddah tace boka aini yanzu bana tare dashi ya koroni gida yace sai yaga ita Sultanar zan koma kuma babu wanda yasan ma inda take zaune a halin yanzu dan ita mahaifiyar Dikko tace tabar katsina kwata² , dariya bokan yayi sosai sannan ya ɗaga hannunshi daga gefen shi yace tana katsina gata nan , lafiya lau aka nuno hoton Sultana kwance , Jiddah tace Eh wallahi itace , itace boka , dariya yayi tare da ɗaukar kaza ya wurga sama cikin seconds ta dawo ƙasa har an tsotse mata jini , Jiddah ta firgice sosai boka yace idan har kika faɗa masa tana katsina sai ya dawo , idan ya dawo daga nan komai zai tafi mana a sauƙaƙe ,
Al ' Ameen yace haka za'ayi ranki ya daɗe kinga idan kika samu kika samo sai ki bani ni kuma sai nazo na kawo ko ? Jiddah tace Eh , tadai daɗe tana faɗawa boka yadda take san aikin ya tafiyar mata yadda take buƙata , da suka tashi tafiya ta yayyafawa boka ruwan kuɗi shi kuma ya watsa kuɗin sukayi sama.....
Koda suka koma gida Al ' Ameen sai ƙara jaddadawa Jiddah yake tayi ƙoƙarin samo sperm in mai gida idan aka goge ko wace mace a zuciyarshi aka sakata ai taci lafiya , Jiddah tace ai yanzu wanka zanyi na kirashi , Al ' Ameen yace ki bada himma dai karki tsaya sanya , tace insha Allah , sallama yayi mata ya fice daga palon ,
Yana fita ya kira Mardiyya , bayan ta ɗauka yace doughter nasara tana ƙara tunkaro ahalinmu , lallai ke mai nasara ce kuma kece tauraruwarmu gaba ɗaya , fitila mai haskawa amarya a gidan mai gidana , dariya Mardiyya tayi tare da cewa Uncle ya ake ciki yanzu ? Al ' Ameen yace boka yasa a samo masa sperm in mai gida kuma na faɗawa boka yadda zaiyi kinga ina kai masa za'a goge Jiddah a goge banzar Sultana , filin zuciyar mai gidana naki ne ke ɗaya my doughter , Mardiyya tace godiya nake Uncle Allah ya taimake ka ya bada sa'a , Al ' Ameen yace am3n. Sukayi sallama !
Koda Jiddah ta faɗawa Dikko Sultana ta dawo katsina cewa yayi da kyau , ta tambayeshi ranar da zai dawo yace shi daga nan ma gaba yaci , tace haba Yaya nidai tunda an ganta ya kamata kayi haƙuri ka dawo , Dikko yace kiyi wata maganar bana san wannan , Jiddah tace dawowa na ne baka so ko kuwa zancen Sultanar ne yanzu baka so ? Tsoki yayi ba tare daya bata ansa ba ya katse kiran ,
Yana katse kiran Jiddah ya fara kiran mai gadinsa na goruba gidan daya ajiye Sultana , bayan sun gaisa Dikko ya tambayeshi ko An mata tazo nemansa ne ? Yace A , a , gaskiya bata zo ba , katse kiran yayi ya kira Umar yace masa An mata ka ganta ne a katsina ? Umar yace gaskiya bata dawo ba , shima katse kiran yayi tare da cewa "yar ranin hankali ashe kinga dama kin dawo , hmmm kedai kika sani mara aikinyi kuma aradu bazan kiraki ba.
Washe gari bayan na gama duk abinda nakeyi na kira Aunty Suwaiba muka gaisa , nayi mata sannu da jiki ta ansa cikin farin ciki da faɗamin tayi kewata , nace mata insha Allah ai zanzo , tace Allah ya yadda , nace ko Aunty ta kira waya ne ? Aunty Suwaiba tace har yanzu dai shiru gaskiya bata kira ba saidai wata number ake ta kiran wayar da ita , nace kin ɗauka ne ? Tace tunda naji namiji ne ban sake ɗauka ba , ki turomin number , Aunty Suwaiba tace a , a gaskiya Sultana kiyi sabgar gabanki ki fita daga rayuwar wani zaƙule² , Aunty turomin number da Allah , Aunty Suwaiba tace gaskiya bazan turo ba , juyin duniya nayi amma taƙi haka nan na gaji na haƙura mukayi sallama.
Dani da Baban Hafsa dukanmu 12:30pm a cikin makarantar tayi mana , a napep nazo bayan na iso na anshi kuɗi a wurinshi na sallami mai abin hawa , daga nan kuma muka ɗunguma zuwa Ofishin shugabar makaranta , bayan gaisuwa Baban Hafsa da kanshi yayi bayani tare da nema min gurbin karatu a makarantar , duk dai abinda ya kamata shine yayi , duk wani rubuce² shine ya cike komai da hannunshi da sunan MARYAM ALIYU ,
Bayan ya gama ya tambayi shugabar makaranta shin ko zai iya biyan kuɗin makaranta na daga aji 1 har zuwa 2 tace anayi zai iya kuma ta ƙara masa da cewa ana shiga aji dan koyon karatu na musamman bayan ɗalibai sun tashi , extra lesson , tambayana yayi ko ina ra'ayi nace masa ina so , gaba ɗaya akayi lissafi yayi mata transfer kuɗin zuwa cikin asusun makaranta ,
Ranar da zan fara zuwa makaranta aka faɗamin fita nayi daga ofishin na basu wuri domin su ida abinda suke san kammalawa , bayan sun gama ya fito dani dashi duka wurin motarshi muka nufa , bayan munje muka buɗe kowa yayi ma kansa mazauni.
Bayan mun zauna yace min Hajiyana gaskiya baza ki hau machine ba wurin zuwa makaranta , motar makaranta zata na zuwa tana ɗaukarki , sch bus , nace kuɗi ne baka da ko a ina matsalar take ne ? Yace ina da kuɗi kawai dai girmanki ya wuce ki hau machine , faɗuwa gabana yayi kardai yaga hotona a lokacin da akayi ta yamiɗiɗi dani a social media lokacin da Dikko ya bani motarshi ?
Dakewa nayi nace shin wane irin girma ne kake gani ina dashi wanda har kake tunanin nafi karfin hawa machine ? Jawoni yayi jikinshi yana cewa aike babbar ƙaddara ce samunki sai namiji mai babban rabo , tarayya dake kuma sai jarumin namiji irina , matsayinki da darajarki saima kin ɗora mutum a linzaminki zai tabbatar da haka nine zan tabbatar idan har muka keɓe na samu nasarar taka ruwan cikinki , murmushi nayi tare dayi mishi kallon ɓatacce.
Lalube jikina ya farayi , kallon sakarai nayi masa tare da ƙara ƙureshi da ido sosai yanzu na tabbar da ɗan uwan Babana ne dan naga kamarshi da Baba harta ɓaci wallahi kuma sai yanzu na fahimci maganarsu iri ɗaya sukeyi yanayin kallonsu da komai dai iri ɗaya saidai shi Babana yafi shi haske sosai kuma yafishi hanci da ƙaramin baki amma gadai jinin nan yana yawo a jikinshi.
Hannunshi ya tura cikin rigata tare da ƙoƙarin haɗa bakina da nashi na riƙe hannunshi na kauda fuskata gefe ɗaya idona ya cika da hawaye dan wallahi kallonshi nakeyi kamar Babana , cijewa nayi cikin jarumta nace kar ka manta da nace maka bana ci sai ƙarshen wata , ƙara riƙoni yayi yana cewa tou ai ba cewa nayi zanyi ba koma zanyi kina tunanin zanyi a mota ne ? Kuma a motar ma tsakar gari da tsakiyar rana ? Murmushi nayi tare da cewa ai ba matsala bane ba ra'ayinka ne cin duk abinda kake buƙata yayin da yunwa ta taso maka dan ba'a tarar abinda za'aci a dai² irin lokaci buƙata ɗaya kawai aji ciki yayi nauhi ,
Kin san da haka tou kike ta wahalar da rayuwata ? Kika ɓace min ɓat kuma da kika dawo sai kika zo da wani tsarin banza , jifa yanzu ko hidimar da nayi miki ai ya isa ki bani tukwuici mana , tou kayi min gori ka biyamin kuɗin makaranta , a , a ba gori nayi miki ba ina so dai kisan yadda akeyin halakkaci da sakayyar farin ciki yayin da akayi maki karamci ya ƙarasa maganar tare da haɗe bakina da nashi wuri ɗaya zuyzuy ya riƙa lashewa yana tsotsewa wani irin ihu nayi tare da cewa nace bana so wai kai maye ne iye ?
Dariya yayi irin dariyar Babana yace maye ne ni mana , kin taɓa ganin namiji ba mayen mace ba ? Duk uztazancin namiji duk imanishi duk haukarshi ko hankalinshi duk talaucinshi ko arziƙinshi duk wani matsayi da yake taƙama dashi mace ce remote control inshi , ke yaufa duk masifarki saina sha wannan dadɗan bakin naki wallahi , matsowa yayi daga saman kujerar da yake zaune yayi sosai dan sai zuƙewa nakeyi inayin baya amma maye ɗan mayyar saida ya jawoni ya ƙara lasar bakina , cikin kuka nace haba Bab..... Kimace Baban ai na isa in haifeki tunda yarinyata ta huɗu ma nasan zata girmeki amma dady suke cewa. Kema sai kice Dady daga yau....
Cikin kuka nace dan Allah ka daina irin wannan abun mana ! Ai yanzu na fara miki irin wannan abun dan ni daɗi nakeji idan inayi miki , haka zamuyi dake ƙarshen watan iye ? Haka zaki ta ihu kina kiran Dady har maƙota suji kukanki ? Fuskata kaca² da hawaye nace tou ka bari sai ƙarshen watan yayi mana ka bari ƙarshen wata yazo idan bakayi abinda kake so ba sai kacemin marowaciya ce ni mana , Allah ya taimakeni yace Allah ya kaimu yayi maganar tare da gyara rigarshi ya gyara fuskarshi dana daƙune hawaye ,
Ajiyar zuciya nayi a lokacin daya fara tafiya da motar yana cewa ina zan ajiyeki ne ? Ajiye ni kasuwa , me zakiyi kasuwa ? Yayi tambayar yana kallona nace hijabi zan siya , sai me kuma ? Nace shikenan , yace tou a siyo hada niƙaf dan banasan ayi ta kallemin wannan kyakkyawar fuskar mai ɗaukar hankali ya karasa maganar tare da shafo fuskata nace tou ,
Har muka zo kasuwa daga haka babu wanda ya sake magana sai shashshekar kukana dake tashi kaɗan² , bayan ya ajiyeni kasuwa ya bani 30k yana cewa sun isheki ? Da sauri na buɗe mota nayi gaba ko ansa ban bashi ba , murmushi yayi tare da bin Sultana da kallon mai tattare da tsantsar so , saida ya daina hangota ya wuce yana mai addu'ar Allah ya bashi sa'ar "yar yarinyar can ya more abunshi.....
Ta bayan kasuwa nabi na fice daga kasuwar ina ta kuka tare da goge bakina wai Yayan Babana shine yake haɗa bakina da nashi har yake addu'a Allah ya bashi sa'ar hawa saman ruwan cikina ? Wayyo Allahna wai meya haɗa wannan bala'e wanda yasa "yan uwa suke cuɗanya da "yan uwansu babu wanda yasan matsayin kowa , wayyo Allahna Aunty Mamy me yasa tun farko baki faɗamin abinda ke tsakanin Babana dasu Amisty ba ? Juyawa naji garin yanamin , Malam Ɗayyu ya faɗomin a rai dan haka na fara kiran wayarshi !
Bayan ya ɗauka muka gaisa nace Malam kamin bayanin abinda ka sani akan abinda ke tsakanin Babana da Bello tou ko kasan dalilin da yasa matar Babansu Babana ta kori su Baba daga gidansu ? Malam Ɗayyu yace a , a , nace Aunty Mamy ta faɗa maka tsakanin Amisty Hafsa da Babana ? Karka ɓoyemin komai ka faɗamin abinda ya riga ya wuce ya wuce ka faɗamin meye tsakanin Babana dasu don Allah........?
Malam yace Eh gaskiya abinda mariganya ta cemin shine , tace shi Bello yace yana san ya jefe ƙiyayya mai girma a tsakanin ahali ɗaya duk akan fansar budurcin matarsa da Binna ya ɗauka a ranar da yake tunanin itace ranar sa ta farko a angwanci , shine yayo dillacin ita Hafsa da Amisty wadda ita Amistyn da Baban shi Binna da Kakan Amisty suke Baba ɗaya , da sauri nace tirrr da wannan ahali , malam bana san sanin zuminchie su sauran bincike da sanin dalilin da yasa aka kashe min Babana da wanda suka kashe shi bana kowa bane nawa ne , miye tsakanin Babana dasu Hafsa ?
Malam yace muradi ne , nace wayyo Allahna wane irin muradi Malam ? Malam yace muradi wanda baya buƙatar kawaici kunya ko kara , tirrrr Allah ka tsinewa Bello albarka tsinannen Allah ubangiji ma bazai barka ba kuma nima bazan barka ba da zaran na gama haɗa abinda nake buƙata ƙaryarka ya ƙare aihuwar asara ban yafe maka ba kuma kada Allah yaba uwarka ladar aihuwarka , kashe wayata nayi tare da dafe goshina da hannun damata kaina naji yanamin ciwo kamar zai faɗo ƙasa , Aunty Mamy tayi gaskiya da tace gaba ɗaya ahali sun zama *KWARATA...*.
Baba ya nemi Amisty kuma ya nemi Hafsa , ɗiyar Yayanka , da ɗiyar shi ta zumincin Allah , kowa mayunwanci ne duk wanda aka bashi saiya ansa yaci babu mai haƙuri inama anfanin irin wannan muradi , yanzu nima gashi Baban Hafsa yana muradina a hayaniyance nace ni kuma ba muradikanka nakeyi ba dukiyar da tasa mahaifiyarka ta lalata zuminchie itace muradina kuma saina ga bayanta kaf saina mayar daku faƙiran ƙarfi da yaji , tunda har tayi sanadin lalacewar zuminchie ta fasa kan "yan uwa saina tarwatsa komai har gobe dai zata rayu da taƙaicin *BINNA* kuma saikin mutu da nadamar sanin *BINNA* , kun kashe maciji amma baku sare kanshi ba , kun kashe *BINNA* amma baku sani ba *BINNA* yana nan a saman doron ƙasa na ƙarasa maganar tare da buga ƙafata ƙasa , sai kun mutu dukanku da baƙin cikin *BINNA* domin Binna ya dawo daga duniyar mutuwa.........
A sassauce nace koma miye yasa kuka korashi daga duniya kuma sai kun tafi baku ci koma miye ba kuma haka zaku tafi ku barshi kunaji kuna gani...
A gajiye na koma gida zuciyata cike da masifu iri² , a ƙofar gida na samu Baba ƙarami zai fara magana na bashi kuɗina kaff amma bai ansa ba yace ki tattara naki ya naki ki kama gabanki domin zamanki a tare dani babban haɗari ne da kuma barazana a rayuwata , cike da ladabi nace yanzu kuma laifin me nayi maka ne ? Idonshi cike da hawaye yace babu abinda kikamin amma yau duk mutumin dake anguwar nan babu wanda bai shiga tashin hankali ba da ɗimuwar rayuwa ba sanadinki ,
Ƙara tausasa muryata nayi cikin kuka nace sanadina kuma Baba ? Nida bana nan me kuma ya faru ? Baba yace wasu mutane ne suka zo ni banma taɓa ganin irinsu ba sai yau suka shigo anguwar nan sai hauka sukeyi sukayi ta harbe² suna nemanki duk gidajen anguwar nan babu gidan da basu binke ba suna nemanki , nace su waye su ? Hukuma ce ko kuwa "yan gani na iya ne ? Baba yace koma "yan waye ki tafi daga anguwar nan dan zasu iya dawowa ko wane lokaci , murmushin ƙarfin hali nayi tare dayi ma Baba godiya na wuce......
Ina tafiya ina nazari , babu yadda za'ayi Bello ya fito fili yasa a nemo mishi ni saboda ta ƙarƙashin ƙasa yakeyin cutarsa kuma idan ma banda wata sahihir sheda babu yadda za'ayi nayi shara'a da Bello , tou wane sabon abokin gabar ne ya ɓullo haka a lokacin da abubuwa sukayi ma kaina yawa ? Wata zuciyar tacemin Mardiyya ce , kaina na girgiza tare da cewa a , a , Ummu Affan ce ? Ba ita bace , su Amisty ne ? Um ummm basu bane ,Momy ce , tabbas itace tunda dama tace idan aka sake gani a garin katsina aka faɗa mata zatamin tire² tabbas itace ba kowa ba , wallahi itace ma , dariya nayi tare da cewa nayi gidan ɗanki kije can ki kamoni , na karasa maganar a dai² lokacin dana tsaida napep nace mishi kaini goruba road.
Tafiye muke a napep ina kiran wayar Dikko a kashe dai take har yanzu , amma ina mamaki ya akayi Momy tasan nazo katsina ? Murmushi nayi koma dai miye na tafi wurin Dikko naga yadda za'ayi dani dan na lashi takobin zama katsina ko za'a kasheni , tunani dai iri² a zuciyata muka isa goruba road 1k naba mai napep saboda babu canji , yana wucewa nima na shige gidan ,
Gidan a buɗe yake , gaisawa nayi da mai gadin na wuce ciki , palon kuma abokan Dikko ne cike wasu nacin abinci wasu kuma hankalisu yana kan tv suna kallon boll duk yadda akayi Dikko yana nan ko kuma zaizo dan ba'a irin wannan zaman sai idan yana nan ko kuma idan zai dawo daga tafiya ,
Banma kowa magana ba na wuce ciki kuma suma babu wanda yayi min magana dan ko sallama banyi ba , ɗakin da nake zama na wuce na shiga da sallama , yana nan dai yadda nasanshi tun farkon farko , kayana a gefen katifa lulluɓe kamar dai yadda aka saba lulluɓesu , zama nayi gefen katifa na rufe wayata na ɓoyeta dan idan har Dikko yazo nasan zaiyi bincike , kuma bana buƙatar yasan matsalar data shafi ahalina da rayuwata saboda wata rana dan bansan inda abun zai tsaya ba , kuma babu wanda yasan abinda gobe zatayi sai Allah ,
Rufe ɗakin nayi na wuce bayi nayi wanka bayan na fito na canja kaya , kwanciya nayi naci gaba da tunanin rayuwa irin tawa , sai kuma su Amisty suka faɗomin a rai ko sun daina karuwanci yanzu ? Allah sarki Hafsa har tasan Babana ya gogeta taso ita da Amisty su gurjeni suma , hmmm ko ina labarin Ummu Affan ? Ina san sanin rayuwar Aunty Suwaiba duk yadda akayi cire mata ƙafafuwa akayi tou fa , naji dai da rayuwata naga wannan irin rayuwa.
Dariya nayi tare da cewa kema uwar Dikko har yanzu baki gano inda nake ba ? Tou zo kiji in faɗa miki ina nan gidan ɗan rainin wayan ɗakin a ɗakinshi kwance saman katifa an tada man gen ina shan iskkan A C babu abinda ya dameni da zafin gari , kuma yazo ya bani abinci mai kyau inci ga masu gadi suna gadina duk ɗiyar ɗan caca da kika raina ɗanki kuma yasan darajata tou nice na samu wannan matsayin , ummm turo bakina nayi tare da gyara kwanciyata nace bacci mai daɗi.........
13/10/2019
*JAMILA MUSA....*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 55
Tunda na samu na kwanta bacci har gari ya waye ko fitsarin dare ban farka ba , wadataccen baccin dana samu shine ya bani damar tashi asubahin farko , kuma tunda na tashi nayi sallah asuba ban koma bacci ba , wayata na ɗauka saidai na kunno maganar mutumin nan da nake tunanin shine ya kwakwalewa Aunty Mamy ido ta mutu , Allah ɗaya gari ban² shi nan magana yake , da , da yare na yakeyin magana zanji abinda yake cewa to banaji saidai na saurara amma ba damar na fihimta , hmmm ya zamar min dole na miƙe da zuciyata da kwalwata nima nayi ilimi kodan ceton rayuwata daga duhun jahilci....
Bayan na gama saurare na kashe wayar na saƙata a gefen katifa na koma nayi kwanciyata ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni , na ɗauki lokaci mai tsayi ina bacci hankalina kwance banda wata damuwa data wuce yunwa , sai ɗaya saura na farka ,
Koda na farka wanka nayi nayo alwalla kaya na canja ni "yar gayu dan ina cire kaya na ajiye a palo za'a ɗauka a wanke a gogemin shi yasa ni kuma kullum saina canja kaya sau biyu , idan nayi wankan safe na saka idan nayi na marece ma na sake !
Bayan na gama sallah azahar na ɗauki kuɗi na fito da zumar in ba mai gadi ya siyomin abinci , amma ina shigowa palo naga ɗika²n kulolin abinci da filets da cokula kamar dai yadda aka saba ajiyewa a kullum idan Dikko yana gari idan har yana nan haka ake ajiye wannan abinci da rana da daddare shi yasa ko wane lokaci gidan baya rabuwa da mutane kalacin safe ne dai bana tunani ana kawowa gaskiya dan bana gani saidai iya wanda zan karya dashi.
Saida na zuba abinci dai² wanda zai isheni nakai ɗaki na ajiye sannan na dawo nace ma mai gadi wai Dikko baya nan ne ? Yace min yana nan mana , nace tou ai ban ganshi ba , yace min yana nan ciki tun ɗazu ya shiga kila bacci yakeyi , nace yayi mishi kyau , na juyo na dawo a raina ina cewa miya faru bai nemeni ba ? Wurin mai gadin na sake komawa nace yasan nazo kuwa ? Yace Eh na faɗa masa , ya yace maka ? Baice komai ba , daya zo yace ina ne ? A , a bai tambayeki ba , tou ya yanayin fuskarshi ? Yayi farin ciki ko yayi yanayin damuwa ne ? Yace ni bansan ya yayi ba.
Ban sake magana ba na koma na ɗauki abinci na naci gaba da ci , bayan na gama nazo na ajiye filet in a inda na zuba abincin , ban daɗe da komawa ɗaki ba gidan ya fara ɗaukar taron mutane kamar yadda ya saba a ko wace rana , wannan zama haka zasuyi tayinshi har sai dare yayi sannan kowa zai kama gabanshi.
Hayaniyar sai ƙara ƙaruwa takeyi palon sai ƙara cika yakeyi harabar gidan kuwa an cika ta da motoci , aikin gardamar suka fara kenan basu da aiki sai maganar "yan kwallo , ƙaramin palon na fito na zauna inga ta ina Dikko zai fito amma har akayi la'asar naje nayi sallah na dawo banji Dikko ya fito ba , gajiya nayi na koma ɗakina naci gaba zaman jiran tsammani.
Yau ko abincin dare banci ba inayin sallah isha'e nayi kwanciyata jiya banga Dikko ba yauma ban ganshi ba haka nan na haƙura na kwanta , amma ba haka naso ba naso mu haɗu ko so ɗaya , tou ko baiso nazo masa gida bane shi yasa yake ta ɓoyewa kila yayi haka ne idan na gaji da zama in kama gabana ,
Bandai yi bacci ba ina kwance ina ta tunanin duniya har 11:05pm a hankali gidan ya fara ragewa har yanzu banyi bacci ba , wurin misalin 11:49pm gidan yayi shiru gaba ɗaya , yau gaskiya sun tashi da wuri dan wani lokaci suna kai har 1:30am suna fira !
Duk masu fita gidan akan idona suke fita amma har yanzu babu Dikko a cikinsu kuma har akayi zaman nan aka tashi banji an kira sunashi ko so ɗaya ba , kuma banji maganarshi ba , saida gidan ya zama babu kowa na haƙura nayi bacci.
Wasa² har nayi kwana 3 gidan banga Dikko ba kuma mai gadi ya tabbatarmin yana nan ya dawo , na duba ɗakinshi ban ganshi ba , kuma idan na kira wayarshi yanzu tana shiga amma baya ɗauka , haka nan naji duk na takura gaba ɗaya na kama kaina saima na daina cin abincinsu kwata² saidai in tura a siyomin abincin da nake so naci lashe ² da duk wani abun kwaɗayi da zuciyata take sha'awar ci ko sha da kuɗin da Baban Hafsa ya bani,
Ranki ya daɗe yau kwananki 2 da dawowa amma har yanzu shiru nakeji , gyara zama Jiddah tayi tare da cewa waini tayama zan fara samoshi ne ? Kwantar da murya Al ' Ameen yayi cewa haba ranki ya daɗe duk wayewarki da gogewarki kice baki san yadda zakiyi ki samo ba ? Tou taya akayi kika kwanta da shi ? Jiddah tace kwanciya daban maganar samun abinda boka yake magana daban ya bani "yar ƙaramar kwalba yace a ciki zan matso taya zan fara tara kwalbar nan na matso bayan kuma yana kallona.
Al ' Ameen yace ranki ya daɗe idan ya kwanta dake bayan kun gama abinda kukeyi sai kiyi kamar irin kina masa wasa naku na ma'aurata saiki lallaɓa kiyi dabara ko a hannunki ki samu , dama kin ajiye "yar kwalbarki a toilet kina matsowa sai ki tafi toilet kamar zaki wanke hannunki kina shiga sai ki zuba a kwalbar , ki maida hankali kinga abun kullum gaba yakeyi , kuma anje kamo yarinyar nan ta gudu yanzu babu wanda yasan inda take ma ,
Jiddah tace gaskiya wannan shawara haka tayi , tou insha Allah zanyi , Al ' Ameen yace dadai kin taimaki rayuwarki , haka yaita ɗora Jiddah yana kaita yana baro.
Da marece bayan na gama abinda nakeyi na fice daga gida , kasuwa na fara zuwa na siya niƙaf kamar yadda Baban Hafsa yace , banyi hijabi ko ɗaya ba saboda ina da hijabai sunkai goma a gidan Dikko , ina sayen nikaf in na lulluɓe fuskata na haye napep , ban sharce ko ina ba sai majalissar su Baban Hafsa , mai napep na sallama ya tafi ni kuma na isa wurin tare da sallama.
Gaba ɗaya suka ansa sallamar yayin da Baban Hafsa ya taso fuskarshi ɗauke da yanayin kishi yana cewa sai ki kama kizo nan kuma bazaki faɗamin ba ? Wurin motarshi ya nufa ya ɗauko leda yana cewa da Allah kada ki sake zuwa nan kinji ko ? Nace tou , yawwa ga kayan makarantarki nan da littafanki komai akwai a ciki , nace ngode Dady shi kuma yacemin idan Allah ya kaimu goben zanzo makarantar taku nace Allah ya kaimu lafiya , ya ansa da am3n da kanshi ya tsaida min napep ya biya kuɗin , saida na samo abinda zanci da daddare da wanda zanyi kalaci da safe idan Allah ya kaimu sannan na wuce gida.
Yauma gidan ɗinke yake da mutane babu masaka tsinke ko dana tunkari palon dole tasa na dawo saboda babu ta hanyar da zanbi in wuce , gaba ɗaya palon ya gauraye da ƙamshin turare iri² har baka iya gane na wani , kowa dai ɗan gaye ne babu sakarai kuma babu ƙazami dan duk "ya "yan attajirai ne , kowa dai yanaji da kanshi dan babu wanda yake so a fishi ,
Bayan gida na zagaya wurin masallacin dake cikin gidan , a ƙofar masallacin na samu wuri na zauna sannan na fara duba kayan da nazo dasu , hada waya a ciki da layin waya kila Dady yana tunanin banda waya shi yasa ya haɗomin da ita , ƙaramar waya ce nokia ko kwali bata da sai caja , murmushi nayi tare da maida wayar na fiddo abinci naci gaba da ci saboda yunwa nakeji ,
Ban daɗe da gama cin abinci ba suka fara fitowa danyin sallah magrib dan haka na tashi na zagaya ta ɗayar hanyar dan gaba ɗaya a wurin ƙofar masallacin suke alwallah , lokacin dana zagayo gaba ɗaya babu kowa a wurin sai Dikko kaɗai dake alwalla a ƙofar palon , gaishe shi nayi tare da mishi sannu da zuwa kallona yayi amma baiyi magana ba ,
Sake gaishe shi nayi ya ƙara basarwa , raɓashi nayi zan wuce ciki a dai² lokacin daya gama alwalla ya ciko bakinshi da ruwa kamar da yayi niyar watsamin su sai kuma ya zubar a gefe yana warware hannun rigarshi daya naɗe yace ina kikaje tun ɗazu ? A daburce nace ina ina ta can na nuna mishi baya da hannuna , kina ta can ko ? Yayi maganar tare da jinjina kanshi yace yayi kyau,
Daga haka bai sake magana ba ya wuce nima na shige ciki , ina shiga ɗaki na ajiye kayan dana zo dasu nayo alwallah nayi sallah , ina gama sallah na fara haɗa littafaina a cikin jikkar makaranta wani irin farin ciki nakeji naga Dikko kuma naji daɗi dana ganshi kullum nidai ƙara burgeni yakeyi addu'a ta ɗaya Allah yasa idan ya gama sallah yazo , ni kuma ince masa me yasa baka ɗaukar wayata idan na kiraka......?
Zuciyata tace karki sake ki tambayeshi raina ki zaiyi , a bayyane nace ko yane gaskiya ya kamata nasan miye dalilin da yasa baya ɗaukar wayata , zuciyata ta sake gargaɗina a karo na biyu cewa ki kama kanki shi namiji ma ya riƙe ajinshi sai ke banza zaki damu dashi , murmushi nayi a bayyane nace ina wani maganar aji kuma bayan ina zaune a gidanshi , anya akwai wanda ya taɓa shiga rayuwa irin tawa ? Nidai ko a labari ko littafi ban taɓajin wanda yayi bahaguwar rayuwa mai tattare da ƙalu bale ba kamar tawa ,
Babana ya rasu , gidana kuma dana siya "yan uwana sun siyar dashi , ƙanin Babana kuma yace min zamana a tare dashi babban riskine , Yayun Babana kuma basu ma sanmu ba , Mamana ta gujeni ta tafi ta barni ina ta gararin rayuwa me nayi ma duniya ta juya min baya haka da ƙuruciyata ? Dole in cire wani girman kai inbi Dikko in zauna lafiya idan ba haka ba shima ya juyamin baya bansan ya rayuwata zata koma ba , ga mahaifiyarshi ta ɗanawa rayuwata tarko idan kuwa har nayi kuskuren bari ta kamani kashina ya bushe ,
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" Allah ngode maka ubangiji ka yafemin ka yaye min ƙunci da damuwa dan alfarmar sayyadis sadati , ka tausayamin ka karkato da hankalin mahaifiyata gareni kaji ƙaina badan halina ba , Inna kina wace duniya haka kika manta dani ? Niko duk halin dana shiga bana mantawa dake har abadan duniya kuma ina sanki Allah ya dafa miki ya jiƙanki a duk inda kike a faɗin duniyar nan kuma ya huci zuciyarki , Allah kaji ƙan Babana kasa ya huta....
7:19am a cikin makaranta tayimin , ina cikin ayarin ɗalibai har a wurin taron assembly ko a wurin taron komai da turanci ake faɗa kuma abinda na fahimta kowa idan zaiyi magana da ɗan uwanshi bayayi da yaren hausa saidai da harshen bature ,
Bayan an gama ko wane ɗalibi yayi ajinshi nima nayi nawa ajin JSS 1B shine ajina , duk "yan ajin nafi su girma kuma sai dariya sukemin suna kallona , wuri na samu na zauna ina tunanin idan har yaran nan nabar suka shiga gabana a karatu raini zasumin bana wasa ba , idan har na bar wani ɗalibi yayi na 1 a ajin nan bani ba naji kunya , dan haka na tattaro hankalina da natsuwata na fara ɗaukar karatu yadda ya kamata domin malamai sun fara shigowa.
Babu laifi ina fahimta dan ina da ilimin addini sosai shi yasa nake ganin karatun boko bazai wani bani wahala ba , lokacin da aka fita break banje ko ina ba ina cikin aji ina ta naci , bayan an dawo malamai suka ci gaba da shigowa har aka tashi daga makaranta , bayan an tashi saida nayi azahar tare da addu'a ubangiji ya dafamin sannan na shiga ajin koyon darasi na musamman ,
Saida la'asar muka tashi muna tashi saida nayi la'asar nabar makaranta kuma Dady bai zo ba , daga makarantar boko tsohuwar islamiyarmu na nufa na siya form na shiga ajin harda kuma ni na cika abuna da kaina da larabci , daga islamiya na wuce kasuwa na ɗinka hijabi da wando na islamiya sai gab magrib na isa gida.
Yau duk taron su bai hanani wucewa ba , tunda na shiga kowa yabi ni da kallo har na shige , ina shiga wanka nayi tare da ɗauro alwallah na saka kayana ko mai ban shafa ba nayi sallar magrib dan an kira sallah , ina gama sallah wayar da Dady ya bani ta fara tsuwa tashi nayi na ɗauko ta a inda na ajiyeta , bayan na ɗauka muka gaisa yacemin kiyi haƙuri don Allah yau baƙi nayi a Office amma ina san ganinki yanzu ina zan sameki ne ? Nace saidai kai ka faɗamin a inda zan sameka , inda zan sameshi ya faɗamin nace tou gani nan zuwa yace sai kinzo ,
Daga saman abin sallah dana miƙe wayata kawai na ɗauka wanda zanyo recording idan an taɓo labarin daya shafi Babana , haka na sake ratsowa na fito ina fitowa Dikko yace ina kuma zaki ? Nace yanzu zan dawo ina faɗin haka nayi gaba , yace ke karki sake fita daga gidan nan sai kuma gobe idan Allah ya kaimu , banma saurareshi ba na fice abuna.
Ina fitowa daga palon na samu wuri na ɓoye dan nasan dole saiya biyo bayana , ina ɓoyewa kuwa ya fito yana kirana amma abun mamaki ya fita waje ko sahuna bai gani ba na ɓace kamar walƙiya , mai gadi ya tambaya ta wace hanya "Yar mata tabi ? Yace mai gida banga fitarta ba , Dikko yace baka ga fitarta ba ? Yace Eh , tabi ta gabanka ta wuce kace baka ga fitarta ba dan ka ɗaukeni sakarai ? Cikin girmamawa yace wallahi mai gida ban ganta ba , kallonshi Dikko yayi yace amma ai duk wanda zai shiga ko fita a gabanka idonka , kusa dashi ya matsa yace ta wace hanya tabi ? Mai gadi yace mai gida wallahi bata fita ba ,
Dikko yace to rufe ƙofar karka sake kabar wani ya sake shigowa kuma karka sake ka bar kowa ya sake fita yace tou , daga ƙofar palon ya koma ya tsaya bayan wani lokaci kuma ya taho da sauri ya tunkari hanyar fita daga gida bayan yaje ya sake komawa ƙofar palon ya tsaya , magana yayi ma mai gadi cewa lokacin dana fito ƙofa a buɗe take ko a rufe ?
Mai gadi yace a buɗe , Dikko yace buɗemin ƙofar , buɗewa yayi Dikko ya sake tahowa saida yazo fita yace tabbas bata fita ba tana cikin gidan nan dan ko da gudu ta fita fitowa ta ya isa na hangota ko yane , zanga ta inda zaki bi ki fita yarinya , yana faɗin haka ya koma motarshi ya zauna , dariya nayi a raina tare da cewa mu zuba wallahi babu wanda ya isa ya hanani fita a daren nan saina fita.
Har aka kira sallah isha'e ina tsugunne cikin filawowi Dikko yana cikin mota , gaba ɗaya suka fito suka zagaya hanyar masallaci Dikko yace ma mai gadi karka sake ka bar wani ya shigo kuma kar wanda ya fita bari muyi sallah , dariya nayi nace aiko na fita na gama kuma tunda har ka bar motarka buɗe da ita zanje ,
Yana zagayawa na fito na shige motarshi tunanin mai gadi Dikko ne ya buɗemin get na fice da gudu sakarai ya manta Dikko yace mishi zaiyi sallah , ina fita na kira Dady nace har yanzu kana wurin ne ? Yace min yabar wurin daya ji shiru kuma ya kira wayata a kashe , nace tou yanzu kana ina ne ? Yace ina nan asibiti , nace lafiya a asibiti ? Yace Hajiyarmu ce batajin daɗi , nace wace asibiti haka ? Yace min fmc nace wane ɗaki yacemin zuwa zakiyi ne ? Na gane wayanshi idan zanzo bazai faɗamin ba , dan haka nace aini tsoron asibiti ma nakeyi Allah ya bata lafiya dama ko nazo sauƙi zan nema mata daga nan ma nayi mata addu'a Allah ya bata lafiya , yace amin , cikin nuna damuwa da tausayin matar nace amma dan Allah da kun sake mata asibiti , yace ai anan likitan ta yake , nace tou Dady ai kuma da ɗakin sarakai kuka kaita tunda Allah yasa kana da iko , yace ai nan take nace tou Allah ya sawaƙa yace amin , sallama mukayi dashi na dawo gida ,
Ina dawowa nayi horn ya leƙo yaga Dikko ya buɗe na shige a inda ya ajiye motar na ajiye na shige ciki da sauri , ina shiga nace fmc ɗakin sarakuna , gani nan zuwa gareki muguwar tsohuwa , hayaniyar Dikko najiyo yana cewa waye ya fita kuma waye ya shigo ? Ina alwallah naji ka buɗe ƙofa yanzun nan ina fitowa naji ka sake buɗewa , mai gadi yace mai gida ai kaine ka fita , Dikko yace na fita naje gidan wa ? Mai gadi yace na rantse da Allah kaine ka fita , Dikko yace idan ka sake cewa nine na fita saina mareka wallahi , mahaukaci ka ɗaukeni ko kuwa me ? Shiru yayi yana nunawa da hannunshi wallahi Allah kaine ,
Dikko yace aiko ubanka zanci , abokanshi suka bashi haƙuri tare da cewa ya canja mai gadi kawai , mai gadi yanajin za'a canja shi ya fara wallahi ײ Dikko yace idan bakaimin shiru ba saina harbar maka baki da ƙafata , duk inajin hayaniyarsu na koma nayi kwanciyata na ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya ina ɗigawa bakina fura ina lashewa ,
Motarshi ya koma yayi "yan dube² sannan ya rufeta bai ciro makullin ba yayo ɗakina , kwance ya sameni ina ta ɗiga fura a bakina hankalina kwance kuma ko inda yake ban kalla ba na ƙaddara ma babu shi kawai a wurin , An mata ina kikaje ? Ban kalleshi ba nace naje saman katifata ne kuma gaka ka ganni kwance ina shan fura ko zaka sha ne ? Bana san sakarci ina kikaje ? Tashi nayi zaune nace to ko nima mai gadin zaka maidai ni ne ?
Rufe idonshi yayi yace ina kikaje nace ? Shiru nayi na koma na kwanta naci gaba da shan furata , har yanzu idonshi a rufe yake ya maimaita ina kikaje ? Ni nace maka babu inda naje sai tambayata kakeyi ina naje idan naje wani wuri zaka sameni ina kwance wai ?
Shigowa yayi cikin ɗakin ya shaƙoni ya ɗagani tsaye yace zaki faɗamin inda kikaje ko saina buga miki kai da bango ? A tsorace nace babu inda naje ina nan tunda kace karki in fita na dawo na faɗa mishi duk yadda sukayi da mai gadi da lokacin da zai tafi sallah nace idan bana nan taya na san haka ? Naji kina nan amma dana tafi sallah ke kuma sai kika fita da mota ta , nace wai na fita naje ina ? Murmushi yayi tare da sakarmin wuya daga shaƙar da yayi mini yace Allah ya sawaƙe miki ganin ɓacin raina , wallahi dan ina tausayinki amma yau dasai kinsan kinmin gardama ,
Fita yayi daga ɗakin yana magana ƙasa² , ajiyar zuciya na sauke daga tsaye na ida shanye furata na wuce nayi alwallah nayi sallah isha'e , ina gamawa nayi kwanciyata dan yanzu bana daɗewa banyi bacci saboda makaranta dan banda lokacin baccin safe kona rana !
Yau da kanshi ya kaini makaranta kuma bai tambayeni wanda ya sani makarantar ba haka kuma bai tambayeni dalilin da yasa na koma makaranta ba , kawai dai tunda safe yazo dana fito zan tafi yace muje in saukeki , kuma daya saukeni yacemin zai dawo ya ɗaukeni , nace masa idan na gama zan kiraka saboda munayin lesson banza yayi yai tafiyarshi bai cemin komai ba ,
Caf lallai ni zaka sakawa rayuwata ido ? Hmm idan kasan wata baka san wata ba malam Dikko , wallahi sainaje asibiti naga kishiyar kakata , yauma "yan ajinmu dariya sukemin hada wanda bama aji ɗaya dasu an gayyatosu suzo suka ƙatuwa a JS 1 , nima dariya abun ya bani dan haka basu bani haushi ba ,
Ana tashi makaranta na fice saida naje fmc nayi waya da Dady nace masa yamai jiki ? Yace da sauƙi , nace kana asibitin ko kana office ? Yace idan ina asibitin miye ? Nace wai da ka haɗani da ita in mata sannu da jiki jiya da tunaninta na kwana ko da nayi sallah dare saida nayi mata addu'a Dady , murmushi yayi tare da godiya sannan yacemin yana Office ! Nace Allah ya sawaƙe ya bata lafiya yace am3n ya gode , mukayi sallama dashi ,
Bayan mun gama waya da Dady nace ma mai napep muje , tada motar yayi muka isa ɗakin , da tambaya na gano ɗakin da take a nuste na shiga da sallama , suka amsa min cikin sakin fuska tare damin sannu da zuwa , wuri na samu na tsugunna na gaishesu cike da ladabi tare da tambayarsu ya mai jiki ? Sukacemin da sauƙi nace Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne , suka amsa da am3n , wurin tsohuwar na matsa nayi mata sannu ta ansa da yawwa nace ni ƙawar Hafsa ce , tace Allah sarki aiko yanzu ta tafi ita da ƙawayenta nace Allah sarki , 5k na bata cikin kuɗin da ɗanta ya bani nace ayi haƙuri daga makaranta nake , godiya sukayi tayi tare da tambayata idan Hafsa tazo wa za'ace mata , nace ace mata uwar ɗakinsu ce , sukace da ance haka shikenan nace Eh kuma ai zan sake dawowa sukace Allah ya yadda , godiya sukayi sosai ni kuma na fito abuna.
Kai tsaye makaranta na koma saidai nayi sallah na shiga aji kuma malam yamin faɗa kar na sake na sake makara nace insha Allah .
A asibiti kuwa abinda yasa nace musu su faɗawa Hafsa uwar ɗakinsu ce dan kada a faɗa Dady yana nan idan yaji Sultana kila hankalinshi zaikai kaina , tou dukansu babu wanda yasan nasan kowa a cikinsu , Dady nasanshi ya sanni , Hafsa ta sanni na santa amma gaba ɗayansu babu wanda yasan ina tare da wani a cikinsu , Hafsa tasan ni ɗiyar Binna ce amma bata san ina da zuminchie da ita ba , Dady kuma bai sanni ba kuma baisan daga ina na fito ba yasan Binna amma baisan ni ɗiyarshi bace ba , su kuma asibiti basu san ko wace ce ni ba ni kaɗai nasan ko suɗin su waye.
Yauma sai gab magrif na koma gida saboda naje islamiya , kuma Dikko yayi masifa sosai yace har makaranta bokon bazan sake zuwa ba duk abinda nake idan ban sani ba motsina ɗaya a waje wallahi saman tafin hannunshi yake kuma ya faɗamun naje asibiti saboda kin ɗauke ni bansan abinda nakeyi ba ni zaki gayamin idan kin gama zaki kirani , wallahi kallonki kawai nakeyi amma ki sani koda gira kikayi magana nasan ƙafar dake miki ɗingishi ,
Na fiki hankali na fiki wayau nafi sanin rayuwa shekaruna da naki ba ɗaya ba gogewa ta da taki ba iri ɗaya ba duk wani wayau da kike tunanin kina dashi ni a wurina Xeyro , mu zuba dani dake tunda kin rainani zanyi miki maganin rashin kunya.
Nace yi haƙuri don Allah kuma dama ai kasan zan faɗa maka kuma saida na faɗawa mai gadi nace nabi ƙawata zan gano kakarta ko Yayana yazo , ki rufemin baki ke ɗaya kika shiga napep sannan kuma kika fito daga cikin makaranta kina waige² yaushe kikayi magana da mai gadi ?
Ba mai gadi ba malam na faɗa mawa , tou malam kika faɗa mawa koma dai waye na soke makaranta daga yanzu , dan girman Allah kayi haƙuri wallahi bazan sake ba , na gama magana yana faɗin haka ya wuce ɗakinshi , binshi nayi naci gaba da magiya ina bashi haƙuri , banza yayi dani ya wuce toilet yana alwallah , saida ya fito nace dan Allah kayi haƙuri Yaya Dikko , murmushi yayi yana maida agogonshi yace da kince Yaya cuta na zakiyi ya ƙarasa maganar yana kallona , nima murmushi nayi ina kallonshi cike da soyayya , shima cike tsantsar ƙauna yake kallona kowa ya kasa daina kallon kowa.
Dafa kujera yayi yace An mata wai a haka baki so na ko ? Ɗan turo baki nayi banyi magana ba , yace Hmm irin wannan kallo haka idan kuma kika fara so na wane iri zakimin kenan ? Kunya naji dan haka na juya na fice da sauri daga ɗakin murmushi yayi tare da cewa Allah ka kamamin zuciyar yarinyar nan kasa mata tsantsar sona da tausayin rayuwata , ubangiji ka ƙaramin haƙuri akan duk abinda zatamin ka wadatani da tausayinta ka bani ikon riƙeta da gaskiya ka kauda sharrin shaiɗan tsakani na da ita dama duk ko wane namiji dake zuwa gidan nan har ta gama zaman ta a gidan nan , ya ubangiji ka ɗauke idon duk wani namiji akanta , ka janye mata tunanin ko wane irin namiji saini ,
Ina shiga ɗaki saman katifa na faɗa tare da rufe idanuwana na kwantar da fuskata a saman bargo daɗi kawai nakeji Dikko yayimin murmushi kuma nasan wasa yake bazai hanani zuwa makaranta ba dan yaɗan latsani ne , wallahi Dikko ɗan gayene mai kyau na burgewa yanayin magana cikin salo mai ɗaukar hankali , ihu nayi tare da murginawa nace ina sanka mutumina , ina sanka ׳ , juyowa nayi na kwanta rigingine fuskata tana kallon sama na rungume hannaye na a ƙirji na lumshe idanuwana cikin yanayin jin daɗi nace kuma wallahi bazan sake tafiya na barka ba dan ina shan wahala idan bana tare dakai ,
Jiddah tsaye a gaban Al ' Ameen duk ta fita hayyacin tace ni wallahi na kasa , Al ' Ameen yace haba ranki ya daɗe kamar dai ba wayayya ba ? Saboda rashin wayau aiko ƙawarka mace bakya faɗa mata yadda kike kwanciya miji ba bare yaron mijinki , Jiddah tace ai idan ya kwanta dani baya sauka daga jikina sai bayan mintuna 15 , Al ' Ameen yace basai ki saukeshi da dabara ba ? Jiddah tace wallahi baya sauka , tsoki Al ' Ameen yayi yace haba Aunty Jiddah karki bari kiyi wasa da wannan damar ki sake jarabawa a ƙaro na ƙarshe mu gani , Jiddah tace to saidai idan ya dawo ya tafi Abuja Al ' Ameen yace Allah yasa ya dawo lafiya ta ansa da am3n ,
Haba Jiddah waye ya faɗa miki Dikko na Abuja.......?
14/10/2019
Taku a kullum mai san farin cikinku 👇🏻
*JAMILA MUSA...*💅🏻
⚜*BRILLIANT WRITERS ASSO🖊~{{-pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}
*KWARATA*
{{kalu bale gareku matan aure}}
*JAMILA MUSA* {Meelat musa}
sadaukar wa gareku,👇🏻
*ASMA'U ZAYYANA{{Asmeenat}}
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿-----56
```kuyi hakuri yau baxaku samuba saboda matsalar charge da banda amma insha Allah gobe zakujini```
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 56
*_MAIMOUNATH O . G {{ Mahnoor }} ni bansan da irin kalaman da zanyi amfani dasu wurin miƙa saƙon godiya ta a gareki ba , idan zanyi ta rubuta ngode² sai cajin wayana ya ƙare ban gama cewa ngode ba , duk da haka dai ngode sosai Allah ya saka da alkairi ubangiji ya ƙara arziƙi ya ƙara zaman lafiya tsakaninki da naki master ya kawo zuri'a masu albarka..._*
*_Ummu Farhana ta sake zagayo muku da wani sabon salon labari nata mai taken FANNAH {{ marainiya }} hanzarta ki samu naki karki sake ki bari a baki labari , ina miki barka da fara sabon littafinki Allah ya taimaka yasa yadda kika fara lafiya ki kammala lafiya...!_*
Saida Al ' Ameen ya tafi sannan Jiddah ta koma ɗakinta cikin tashin hankali , ta zagaya ƙaton palon ta bata san adadi ba , mafita ta farko da zuciyarta ta yanke mata shine duk yadda za'ayi kawai a fara kamo mata Sultana , shawarata ta biyu kuma sai gata ga Dikko...
Wayarta ta ɗauka ta fara kiran Momy bayan ta ɗauka suka gaisa tun kafin a gama gaisuwar Jiddah tace Momy har yanzu dai kin kasa wani abu akan yarinyar nan , Momy tace waye yace miki na kasa.....?
Jiddah tace to ai naji shiru har yanzu babu wani ci gaba , murmushi Momy tayi tare da cewa kwantar da hankalin ki an gano komai nata tana shiga makaranta kullum da ƙarfe 7 da wani abu na safe ,
Tana fita daga makaranta kullum karfe 4 , daga nan tana wucewa islamiyya , tana zuwa a napep idan aka tashi kuma ta shiga motar makaranta ta sauka islamiya , yau ba'a napep taje ba ance wani yakaita kuma basu san ko waye ba ,
Momy tou mi yasa basu kamata ba ? Kinsan komai yana san bin diddiƙi kuma har yanzu sun kasa gano gidan da take zaune , saboda sunce daga Islamiya kullum take ɓace musu saboda tana amfani da abun rufe fuska { niƙaf } mafiya yawan ɗalibai dashi suke amfani , Momy basai an gano gidan da take zama ba nidai burina kawai a kamota idan ba haka ba zata iya sake sulɓewa , Momy tace babu damuwa ,
Sun dai daɗe suna saƙawa yadda zasu ci mutuncin Sultana idan aka kamota daga baya sukayi sallama , Jiddah kuwa taci alwashi idan har aka kamo Sultana tunda dai har take tarayya da mijinta tou tayi alƙawari sai tayi mata tsarki da ruwan tsidagu bayan ta jajjaga attaruhu ta zuba abonaki a cikin ruwa zafi zata zaunar da ita a ciki , sai taci ƙaniyarta yadda gobe ko ance tayi iskanci da Dikko sai tace ta tuba....
Kamar yadda na saba fita daga gida yauma haka na fito sanye cikin kayan makaranta na , a palo na samu Dikko zaune saman abin sallah ya jingina da kujera ya miƙe kafafuwanshi ɗaya saman ɗaya yana karantun al'qur'ani mai girma ,
Kallona yayi amma baiyi min magana ba , hannu na ɗaga mishi alamar saina dawo nayi gaba , gab da zan fita daga palon yace An mata nace karki je makarantar nan ko , cikin muryar lallashi nace haba Yayana na ƙarasa maganar ina kwantar da kaina nayi kalar ban tausayi , rufe al'qur'anin yayi yace nidai banajin daɗi , jikina yana min wani iri inajin kamar wani abu zai faru dake wallahi , nidai dan Allah kiyi haƙuri da makarantar nan !
Nidai zanje a haka , a kasalance ya lumshe idanuwan shi yace a , a , nace dan Allah , kallona yayi tare da cewa kiyi shiru zanyi fushi , zama nayi saman hannun kujera ina magana ƙasa² cewa kayi fushin mana ko an faɗa maka nima banda zuciyar ne ? Na ƙarasa maganar ina hararar bango ,
Ɗan kintsa bakinsa yayi ya kallo inda nake yace banji abinda kika ce ba , ai dama bana so kaji , saboda kinajin tsorona ko ? Sallamar Ashiru ya hana na bawa Dikko ansa , gaishe shi nayi bayan na ansa sallamar da ina kwana , maidomin gaisuwar yayi da ina kwana ranki ya daɗe , kunya naji dan haka na kwantar da kaina jikin kujera banyi magana ba ,
Daga inda yake tsaya ya haɗa hannayen shi ta baya tare da rusunawa cikin girmamawa yace mai gida barka da safiya , yawwa Dikko ya faɗa a taƙaice ,
Matsawa yayi ya duƙa kusa da Dikko yana magana , ya daɗe sosai kuma banajin abinda suke faɗa amma duk yadda akayi gulma sukeyi , bayan ya gama maganar ya fita , shima Dikkon tashi yayi ya maida al'qur'an inda yake ajiyewa ya fita , nima na tashi nabi bayanshi...
A ƙofar fita mukaci karo , shi yana ƙoƙarin dawowa ni kuma ina ƙoƙarin fita , cikin faɗa yace ina zaki je ne wai ? Komawa nayi na zauna banyi magana ba , ciki ya koma bai wani daɗe ba ya fito , yana fita yace jeka kawai zanzo bayan la'asar in Allah ya kaimu ,
Saida Ashiru ya tafi Dikko ya dawo , ba tare daya tsaya ba ko ya kallo inda nake yace fita zanyi idan kina zuwa ki cire uniform in sai in tafi dake , kaje bazan je ba , sai kinje ya faɗa a dai² lokacin daya shige ciki....
Tunda naga ya daɗe bai fito ba raina ya bani wanka yakeyi zaman toilet sai kace mai jego , tashi nayi na ɗauki jikkar makaranta ina na koma ɗaki ,
Wayoyina na ɗauko na fara dubawa , tarin miss calls a wayar da Dady ya bani ya kira sau adadin da bazan iya ɓata lokacina wurin faɗar su ba , Alaji ya kira Aunty Suwaiba , Malam Ɗayyu da baƙin numbers wanda banda su a cikin wayana !
Cikin baƙin numbobin na fara kira , ana ɗauka naji ya fara babbaka min ashariya tare da cewa duk inda kike a faɗin duniyar nan idan na kamoki kwanakin rayuwarki ya ƙare , Lahaula wala kquwwata illa billahil aliyyul azeem , waye kai ...? Tsoro , tsoro ne , ni tsoro ne mai ban tsoro kuma na duƙufa akan cewa saina ɗan ɗana miki ɗanɗano tsoro sannan na kasheki ,
Na ganki nasan inda kike ƙoƙarinki ya ƙare kuma na tiso rayuwarki gaba saina ga kin shaƙe kinbi iska hankalina zai kwanta wuƙa zan caccaka miki a zuciya a wurin zaki mutu ko harbawa bazakiyi ba yau zan kashe ki....... Yanzu ne ? Ko anjima koma dai yaushe ne kici abincin bankwana gani nan tahowa.....
A firgice na juyo zufa ta tsatsanfomin dan ya faɗi kalaman nashi da kaushi , a wahalce nake fitar da lumfashi dan wanda baya cikin ɗakin yana iya jin sautin fitar numfashi na , zufar goshina na goge da sauri na juyo Dikko na gani tsaye yace me ya sameki ne ?
Mutuwa zanyi..... Na bashi ansa kai tsaye , cikin rashin fahimta yace wace irin mutuwa kuma ? Cikin kuka nace nima zasu kasheni kamar yadda suka kashe Babana kuma suka kashe Aunty Mamy suka kashe wata Auntyn wacce ma bata samu damar isowa wurina ba suka shafe labarinta ,
Tsoki Dikko yayi ya juya yana aike kanki rawa yakeyi kullum baki gajiya da sakin layi kamar zararriya , yadda yayi min sai abun ya tunomin ranar da za'a kashe Babana daya faɗamin nace masa shirmen mafarki ne ni kuma yau gashi na faɗa amma ni an danganta ni da mai rawar kai.
A tsorace na sake lalubo wata baƙuwar lambar na sake kira , itama wata murya ce daban ta tabbatar min da mutuwa ta yau babu gudu babu ja da baya , kashewa nayi na kira wayar Dady bayan ya ɗauka muka gaisa na tambayeshi mai jiki yace da sauƙi , ya akayi baki je makaranta ba yau ? Ya tambayeni ,
Cikin faɗuwar gaba da dakiya nace naje mana , abinda naje makarantar ban sameki ba , nace da wane lokaci kaje ne ? Tunda safe ina bakin get in makarantar ban ganki ba , jinjina kaina nayi tare da cewa amma me yasa kaje kai tsaye bayan baka saba zuwa ba saika faɗamin zaka zo , yau shawara na sake shi yasa naso yi miki bazata kawai , yanzu kina ina ne ?
Kai kana ina haka ? Har yanzu ina bakin get in makarantar ku ? Ka jirani gani nan zuwa , ina faɗin haka na kashe waya , lambar Alaji na kira bayan na gama waya da Dady , tana shiga ya ɗauka ko gaisawa bamuyi ba yace Sultana kina ina ne ? Ina Lokoja na bashi ansa kai tsaye , wace irin Lokoja kuma ? Nace lokoja nawa ka sani ? Tou ke meya kaiki lokoja ? Idan aka ga kuɗi katsina aka gansu a lokoja abin mamaki ne ? Ai kuɗi yawo sukeyi babu inda basa iya zuwa a cikin ƙanƙa lokaci , nace to karkayi mamaki domin karuwa da kuɗi duk ɗaya suke yanzu nan zaka ganni anan zuwa anjima kuma in ɓace , nabar katsina ina lokoja , zai sake magana na katse kiranshi na kira Aunty Suwaiba , bayan ta ɗauka muka gaisa nayi mata sannu da jiki ta ansa cikin kulawa tare da cewa Sultana kina ina ne ? Aunty ina kaduna , yaushe kika tafi ne ? Tunda muka rabu da malam ɗayyu a katsina ranar nabar katsina da daddare !
Amma me yasa baki faɗamin ba , murmushi nayi sannan nace kiyi haƙuri Aunty , tsoki tayi tare da kashe wayar bata sake magana ba , tana kashewa na kira malam ɗayyu shima mun gaisa muka ɗan taɓa fira sannan yace min kina katsina kuwa ? Nace masa kana san gani ne ? Yace Eh nace ina Abuja , yaushe kika tafi ? Nace jiya da daddare , yaushe zaki dawo ? Sai bayan wata ɗaya ina faɗin haka na katse kiran malam ɗayyu.
Lallai kawai abinda zai faru , tabbas akwai masu farautar ruhi na , mutum ya bashi da tabbas kuma yakan iya canjawa a cikin ƙanƙanin lokaci , kuɗi sunkan canja mutum tsoro yana canja mutum , nacewa Alaji ina Lokoja , Aunty Suwaiba nace mata ina Kaduna , na faɗawa Malam Ɗayyu ina Abuja , Dady kuwa na faɗa masa ina Katsina....... Murmushi nayi tare da ajiye wayoyi na a gefen katifa dani daku mu zuba lumfashina yana hannun ubangiji idan mutuwa ta yazo wayau ko tsimi da dubara bazai hanani ansa kiran mahalicci ba , fatana Allah yasa inyi kyakkyawan ƙarshe.
Amisty da Bello zaune a mota , bayan ya kora mata wani birkitaccen sharhi ya ɗora mata da cewa yayi tarayya da Sultana ne ta ɗauki hoton videon abinda mukayi tana ta bazashi a social media gashi yanzu ta durƙusar dashi a harkar wasan caca idan Amisty zata iya tou da Allah ta kawo mishi Sultana ko ta faɗa mishi wurin da Sultana ke zama idan kuma bata sani ba ta binkico mishi inda Sultana take a cikin sa'o'e 24 zan bata naira dubu ɗari ,
Su Amisty anji zancen kuɗi dan haka tace ai sanin inda take ba abu bane mai wahala dan nima haƙe nake da ita saboda ta ɗauki tsiraicin mahaifina ta turomin , naso na ɗauki na ubanta nima na tura mata dan kai kanka kasan nidai Binna Allah kaɗai yasan iyakar abinda ke tsakaninmu , ina san Binna tunda nake ban taɓa huɗɗa da wani namiji ba sai akan Binna , shine ya koyamin ya gogar dani tun ban iya ba har na ƙware dan Binna aharkar mata yai zarra , na jaraba bin wasu mazan amma banji daɗinsu ba nayi niyar ɗaukar videon tsiraicin shi sai nayi tunani idan har ya sani nice nayi masa zai rabu dani ni kuma idan ya barni bansa ya zanyi rayuwata ba , kwatsam kuma sai ga mutuwarshi dan da na lashi takobin auren Binna dan in dasawa Sultana baƙin dafi mai wahalar amayarwa amma sam Binna yace bazai aureni ba.
Murmushi Amisty tayi mai cin rai tare da cewa Hmmm Allah ya jiƙan "yan maza a ƙiyama , Binna namijin duniya jajirtaccen namiji mai kafawa mace soyayyar shi a zuciyarta mai wahalar goguwa ya tafi ya barni da maraicinsa , na tsine kuma bazan daina tsinewa wanda yayi sanadiyar mutuwar Binna ba , amma a tsaye nake saman ƙafafuwana saina wulaƙanta rayuwar Sultana idan dai har ina numfashi a duniya...
Ta ƙarasa maganar tare da fara kiran wayar Sultana , ni kuma lokacin da kiran wayar Amisty ya shigo cikin wayata a lokacin muna gidan abokin Dikko su suna saman tebirin cin abinci sunayin kalaci dan tunda Ashiru ya kawo abin kalaci Dikko bai fito dashi daga mota ba yace idan yazo nan zamuyi kalacin tunda jiranshi akeyi wai wasu dokuna ne aka kawo mishi zai gansu , shi kuma abokin nashi ya uzira mishi wai zai tafi ɗauko matarshi ,
Ko ina zai ɗaukota Oho mishi , ɗaukar wayar nayi muka gaisa , bayan gaisuwa Amisty tace uwar room gaba ɗaya kin manta damu , miye duniya dake abu baya wucewa wurinki ? Da Allah kiyi haƙuri idan dai akan abinda ya faru baya ne muyi haƙuri abinda ya wuce ya zama labari muyi haƙuri dukanmu mu fuskanci sabuwar rayuwa ,
Labarin Babana ne ya dawo min a kaina da yace bayan nayi fushi da Bello saida yayi yadda ya yaudareni ya sake dawowa dani cikin rayuwarshi ya jagwalgwalamin rayuwa , murmushi nayi cewa ba komai Amisty ya wuce , to kina ina ne yanzu dan ina so inzo har gabanki in durƙusa a saman guyawuna in baki haƙuri , ina kano aiko yanzu ma sa'a kikayi kika sameni gab nake da kashe waya kiranki ya shigo ,
Amisty tace me kikaje yi kano uwar ɗaki ? Zanje Lagos ne kuma a jirgi zan tafi , tou yaushe zaki dawo ? Ƙarshen wata ina faɗin haka na kashe wayata murus ,
Shiru Bello yayi bayan ya gama jin wayar Sultana da Amisty , bayan wani lokaci yace ma Amisty jeki kawai zan dawo anjima , fita Amisty tayi daga cikin motar tana mishi addu'a Allah ya dawo dashi lafiya ta wuce ,
Fitar Amisty Bello ya dunƙula uwar ashariya yace lallai yarinyar nan ta ɗauki mutane "yan iska , dan duk wanda sukayi waya da Sultana banda Dady a gaban Bello akayi ta , saboda Bello yaje gidan Baba Ƙarami ya tambayeshi inda Sultana take a matsayinshi na aminin mahaifinta , Baba Ƙarami yace baisan inda Sultana take ba tunda shi Baba baisan baƙin halin Bello ,
Bello yace masa ko kasan mutanen da take huɗɗa dasu ? Kai tsaye Baba ya faɗi Alaji da malam ɗayyu , kuma duka mutanen nan babu wanda yasan Bello sunansa kawai sukeji , kuma babu wanda yasan akwai tsama tsakanin Bello da Baba , koda yaje wurin malam ɗayyu cewa yayi shi aminin Baban Sultana ne kuma yana nemanta dan ta tattaro mishi kan "yan gidansu ya taimake su , kuma ya kira wayar Sultana bata ɗauka kila bata ɗaukar baƙuwar number , shine yace malam ɗayyu ya kira Sultana suji ko tana ina ? Tunda shi tana da number shi ,
Da malam ɗayyu ya kira bata ɗauka ba shine ya kira Aunty Suwaiba , kuma duk da suka samu damar yin waya da Sultana ta rarraba musu , tacewa Alaji tana lokoja , ta cewa Aunty Suwaiba tana Kaduna , ta kuma faɗawa malam ɗayyu tana Abuja da sukayi waya da Amisty kuma tace tana filin jirgin kano a cikin jirgi zasu tashi yanzu zuwa Lagos ,
Itama Momy da aka faɗa mata cewa Sultana bataje makaranta ba cewa tayi karsu sake su dawo sai sunganta ,
Shi kuma Bello bokanshi yace dole sai an kashe Sultana idan ba haka ba masifa da balbalin bala'e tsutsar magana zata cizar mishi harshe zai tonawa kanshi asiri duk abinda yayi zai faɗa da bakinshi makarin wannan masifa shine kisan Sultana....
Dikko kuwa bayan sun gama kalacinsu da kanshi ya tattara komai ya bani yace in mayar a mota , ansa nayi naje nakai mota na dawo na samesu a inda suke ta tattaumawa , maganar dokunan kawai akeyi a hankali abokansu suka fara cika gidan sai an zakuɗa doki yayi sama yana haniniya sai ayi mishi hoto , hanayi kawai ke tashi ganin inda muke tsaye mutane sun fara yawa Dikko yace in koma mota in jirashi yana jiran Umar yazo ne , dan abinda na lura shima gidan babu mata a ciki,
Wurin mota nazo na tsaya ina neman sa'a inyi waje , ina tsaye ina neman sa'a nake ganin rashin aikinyi na maza ko kuwa rashin sanin darajar kuɗi ne , dan naji wai duk doki ɗaya ana maganar miliyoyi gaskiya Dikko baisan darajar kuɗi ba , wato rayuwarshi zata ƙare a mota ne da dokuna sai yawon tsiya kamar kuɗi , na daɗe a wurin sannan Umar yazo.
Umar na shigowa na samu nasarar fecewa daga cikin gidan , da gudu na fita ina gudu ina ɗaura niƙaf ina ,gidan baya da nisa da titi saidai kawai ace anguwar gayu ba'a samun abin hawa tunda mafiyan su kowa da mota yake amfani ,
Wayar da Dady ya bani na ciro na kirashi yafi a irga amma bai ɗauka ba , na kirashi har na gaji yaƙi ɗauka , ganin bai ɗauka ba kawai nahau napep na nufi makaranta dan a tunanina yayi fushi na ɓata mishi lokaci ,
Ina fitowa napep da Al ' Ameen na fara cin karo ina ganinshi na nufi napep da gudu da zumar komawa , dan tunda Dikko yacemin Al ' Ameen baya so na yana biye da rayuwata dan ya ɓatamin suna yasa ina ganinshi na nufi hanyar komawa dan karya bawa Dikko labari ya ganni tare da wani , yawwa gata can ku kamota , inajin ance a kamoni ai banma yi gigin komawa napep ba na ibi santa nabi ta lunguna na yanki fili naci gaba da gudu , ai kamar kura taga kare haka suka biyoni da gudu , ganin da gaske ni suke bi yasa na sake tattarewa naci gaba da gudu kamar raina zai fita.
Dikko kuwa bayan Umar yazo ya dawo mota bai samu Sultana ba , idan hankalinshi yayi dubu ya tashi da guda² cikin palon ya koma dan a tunaninshi ko ta gaji da tsayuwa ta koma ciki , ya duba bai ganta ba ya dawo ya duba iya inda yasan mutum zai iya lafewa a gidan babu Sultana babu ma mai irin siffar mata a gidan kawata² ,
Wayarshi ya ciro daga cikin aljihu ya fara kiran wayarta amma a kashe , dan tunda ta gama waya da Amisty ta kashe wayar , cikin tashin hankali Dikko ya shiga mota ya fita daga gidan da gudu wallahi kai tsaye makarantar su Sultana ya nufa dan a iya fahimtar da yayi mata tana da taurin kai da kafiya abinda tasa kanta shi zatayi bata jin bari kuma bata san yi haƙuri ba , tunda tasawa ranta zuwa makaranta yasan sai taje can wallahi.
Shi kuma yau yayi alƙawari idan harya kamata sai taji babu daɗi saiya jagula mata rai yadda ko baya nan idan yace mata kar tayi abu zataji tsoron fushinshi ,
Ta wata ƙatuwar santa na ɓullo ina ta raba idanuwa kamar nayi ma sarki ƙarya , ina ta murna na samu wurin ɓoyo , duƙawa nayi tare da cire niƙaf ɗina ina fita da hijabina dan nasha gudu zafi ya tasomin , ɗan lumfashe idona nayi ina maida numfashi bayan na sarara buɗe idon da nakeyi mukayi ido huɗu da Bello , kamar a mafarki da sauri na ƙara buɗe idanuwana wata irin harara ya zabgagamin bara'uban nan wani irin tsalle nayi na haura wata katanga na tsula da gudu Bello ya biyoni , tashin hankali abinda na ambata kenan yayin dana juya naga rundunar da suka biyo bayana , ga masifar yunwa da nakeji duk yau babu abinda naci gashi juwa ta fara ibana , har bana ganin gabana sosai saboda wahala......
Dikko kuwa bayan yaje makaranta yayi bincike ce masa akayi Sultana bata zo ba , jinjina kai yayi cikin tsananin ɓacin rai wallahi idan har An mata ta bari ya kamata yana cikin fushin nan kashin ta ya bushe ,
Bello kuwa cewa ya farayi wayyo jama'a ku tare ku taremin ɗiyata ku agazamin don Allah , dariyar mugunta nayi tare da addu'ar Allah yasa masu bin bayana su riƙe Bello suce tunda shine ubana su bashi azaba mai tsanani.........
13/10/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 57
Follow me on wattpad meelatmusa
Muryar Al ' Ameen naji yana cewa daga duniyar mutuwa ka dawo bayan ka mutu kuma kowa ya sani , Bello yace wallahi nine ubanta ni na haifi abuna ku baku lura da kamin mu ba shi wancan ai uban riƙonta ne , cikin shashsheka ta wanda yasha gudu harya gode Allah ya ɗaga murya cewa ki tsaya mu tafi gidan Sultana , muryar wani daban naji shima cikin haki yace kai kuma neman me kake mata ?
Allah ya kama bakin Bello yace wasu ke harinta kuma kasheta zasuyi shi yasa zan tafi da ita in ɓoyeta , shi a tunanin shi wannan wayau ne , domin gani yake idan ya kamani ko wani abu ya sameni baza'a zargeshi ba , a gajiye na kurɗo ta wani siririn lungu na sake bullowa bakin get in makaranta mu , kai tsaye na hawo titi yayin da Al ' Ameen ya ɗauki wani irin lafiyayen dutsi ya saitani ya jefoni da ƙarfi , na tafi tangal² zan faɗi kafin in gama saita kaina ya sake dan ƙaromin wata jifar ,
Jama'a suka fara kai ׳ lafiya ? Al ' Ameen baya saurarar kowa gaba ɗaya sukaci gaba da jifata kamar muslmin da yayi ridda yayin dana raba tsakiyar titi biyu na kasa gaba na kasa baya , tsayuwar da nayi ne na kasa tafiya saboda jifar dasu Al ' Ameen sukayi min suka samu nasarar riƙeni sukaci gaba da dukana wai na basu wahala yayin da suka kasu gida biyu wasu suka riƙe Bello suna kai ɗan iska kaine ka ɗaure mata ƙugu take abinda taga dama ko ?
Kai tsaye yace Eh , saida suka bashi kashin bala'e ko motsi baya iyayi sannan suka ɗaureshi suka jefa banza mota kamar kare , lokacin da aka kai Bello mota aka dawo neman Al ' Ameen aka farayi amma tuni yayi layar ɓata babu wanda yaga ta inda yabi ya wuce.
Gaba ɗaya hankalin kowa ya koma wurin Dikko dake zaune cikin mota yana kallonmu , a tunanina ni bai ganni ba , dan haka ina ganin sun juya hankalin su ya tafi wurinshi nima na samu sa'ar ɓacewa daga wurin , cikin ƙanƙanin lokaci na isa gida jikina sai ciwo yakemin ina zuwa wanka nayi da ruwa masu ɗumi , bayan na fito na canja kaya naje na zuba abinci naci nayi kwanciyata ,
Gaba ɗayansu wurin Dikko suka nufa cikin farin ciki dan ba saboda Dikko suka saki Sultana ba sundai tafi maularsu ne kawai , kuma shi kullum ranshi a haɗe yake shi yasa baka iya gane a wane irin yanayi yake farin ciki ko damuwa ,
Sudai umarni kawai aka basu su kamo Sultana saboda haka basu san komai game da ita ba , sundai ga Dikko kawai sunzo su gaishi dan sun san zasu samu kuɗi ne a wurinshi shi yasa suka saki reshe suka kama ganye , suna isowa suka fara kirarashi irin dai yadda "yan maula sukeyi , kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke kanshi yana so yaga ta ina Al ' Ameen zai ɓullo ,
Shi kuma Al ' Ameen bayan wasu mintuna a tunaninshi Dikko ya tafi dan haka ya fito daga maɓoyar shi , fitowar da zaiyi yaga Dikko dan haka baiyi gigin komawa wani wuri ba ya nufi mota da gudu ya shiga yaja ya tafi a haukace , da gudu Dikko yabi bayanshi dan yayi alƙawari yau da Al ' Ameen da An mata babu abinda zai hana ya tabbatar da baƙin ciki a zukatansu ba ,
Abinda yasa zai ci mutunci Al ' Ameen saboda yadda yaga yana jifar An mata ya wulaƙanta mishi "Yar matanshi kuma shima sai ya wulaƙanshi ko da kuwa haka zaiyi sanadiyar gogewa farin ciki daga rayuwarshi har ƙarshen numfanshin shi , in banda ƙasƙanci "Yar mata ma zai jefa ? Kuma saman titi kowa yana wuce yana gani sai kace ta aikata wani babban zunubi....?
Ita kuma yau zai nuna mata shi cikakken mai zuciya ne in bata san haukarshi ba yau zata sani kuma zatayi baƙin gani da dana sanin saninshi tunda yana tausaya mata bata sani ba , ya ɓarar da farin cikinshi da komai ya zauna tare da ita dan dai ya sama mata farin ciki da natsuwa , yabar matarshi ya taho wurinta shi zata maidai baisan abinda yakeyi ba , zuciyarshi kuma sai ƙara tunzurashi takeyi tana hasko mishi irin balbalin azabar da zai horar da ita da ita.
Ai jima yayi bazai iya bin Al ' Ameen ba saiya fara da An mata , wani irin mahaukacin burki ya taka ya fara ƙoƙarinyin kwana saman tsakiyar titi yayin da mutane suka fara kaucewa dan kar ya gogar musu abin hawa , aiji yayi ma bazai iya tsayawa ɓata lokacin yin kwana ba , da ribos ya fita daga titin yana kai ƙarshe ya juya sitiyarin motarshi ya yanki hanyar goruba , yanda yake tuƙin ne yasa hankalin jama'a ya tafi wurinshi , yayin da wasu ke cewa ko lafiya wancan wasu kuma na cewa ai shi dama haka yake wannan iskanci babu abinda ya dameshi da rayuwar da wani zai shiga shi kanshi kawai ya sani dan Allah ya basu damar duniya shi yasa basu san darajar kowa ba , a , a gaskiya sun san darajar mutane shi dai kaɗai keda wannan halin , waye wai ...? Wani ya tambaya.
Dikko ne ai shi kaɗai keda wannan baƙin halin mahaifi shi ba haka yake ba , wasu kuma cewa sukeyi ai ɗan iska ne , yayin da wasu kuma suke cewa aini burgeni yakeyi ko nine matashin da na samu irin damarshi saina fishi iskanci kasan su kuɗi jigo ne masu nuna isashshen iko ku barshi yayi Allah ya bashi gara yaji da ƙuruciyarshi wata rana ko ance yayi shekaru sunfi karfinshi baya iyawa , wani yace gaskiya izzar kuɗi da ƙarfi take muma Allah ka bamu masu amfani dan idan kana da kuɗi ji kakeyi kai kafi karfin kowa ka taka wanda kake so ka murje wanda ya shiga gabanka , magana dai ce ta kuɗi su zasuyi bayani kuma da kansu kuɗin zasu baka hakuri kuma ka haƙura , niko dai nace hmm ita dai rayuwa duk abinda mutunci baiyi ba rashin mutunci bazai yi ba , idan an ciza dai a busa dan ita duniya bata da tabbas yanzu takeyin ka anjima ta barka , idan ka raga sai ta raga maka dan duk abinda kake tunani kafi karfinshi sai a wayi gari ya gagareka Allah dai yasa mu dace ,
Bansan ta inda ya biyo ba kuma banji shigowar shi ba ina kwance dan har na fara bacci saboda gajiya , bansan yadda akayi ba kawai dai na farfaɗo naga ana ta riƙe Dikko yana wata irin zabura yana magana da turanci saidai inji yace An mata sai yace Momy yace Dady ,
Jini na gani a jikina bansan ta ina ya biyo ba , duk inda na shafa fuskata jini ne bansan da ina da ina ya fasamin ba , tunda nake ban taɓa ganin irin masifa ta Dikko ba ɗan bala'e ne na ƙarshe duk taron abokanshi sunfi su nawa amma wallahi girgiza ɗaya yakeyi ya zuddasu sai su sake riƙoshi so kawai yake ya iso wurina amma sun san idan ya sake riƙeni tawa ta ƙare ,
Ciƙin ɓacin rai yaci gaba da magana da hausar shi irin kamar bata riƙe mishi baki sosai ba wata irin magana yakeyi , kuma ba irin ta yare ba wata irin murya dai gareshi cikin sanyi yakeyin magana ko yana fushi maganarshi bata canjawa yarinyar can saboda ta ɗaukeni ɗan iska har marina tayi , yana nuna inda na mareshi yaci gaba da cewa idan aka buɗe min fili da irinki dubu duk wanda nayi ma duka ɗaya ya tafi bazai sake dawowa ba har abadan abada ko kina ganin tsoronki nakeji ? So hauka ne ? To ki sani bani na ɗora ma kaina ba Allah ya jarabceni kuma kema idan ya juya alƙamin sa akanki naki ya ƙare ƙaramar yarinya dake babu abinda ke cikin kanki sai wawanci da ƙuruciya , ke banda ƙaddara da hukunci Allah har kin isa kisha inuwa ɗaya dani ina ɗaga miki bakya gani tou yau ƙaryarki ya ƙare saina raba gangar jikinki da ruhinki , badai ina cewa kada Allah yasa kiga fushina ba ko ? Yau yazo kuma bazai tafi ba kin bani ׳ ya ƙarasa maganar yana nunani da ɗan yatsa , kwacewa yayi daga riƙon da sukayi mishi ya fita ,
Wani abokinshi da naji yana cema Yazeed yace ke An mata kike baki kyautawa abinda kikeyi ba'a rayuwa haka yana ƙoƙarin kare miki mutuncinki da martabarki bakya gani , tunda yace karki je dole sai kinje , yace miki bayajin daɗi yaji wani abu zai faru dake ai sai ki tausaya mishi kamar yadda yace miki jarabta ne daga Allah kiji tsoron jarabta ya dawo kanki , ke da kinsan halin DK da kuɗi idan yace kar kiyi wani yace kiyi zakiji tsoron fushin shi , Allah ma ya rufa miki asiri da mutane a gidan yau da kin gwamce ma aya zaƙinta ,
A tsiwace nace dan naje kawai sai ya dakeni ko ni baiwa ce ne ? Da mamaki Yazeed ya kalleni yace tou ai da yake yanzu zai dawo sai ki tambayeshi abinda yasa ya dakekin yama iya saka suna da yace miki An mata... "Yar ƙaramar yarinya dake sai tsattsaga masifa Dikkon ne ma dai² dake.
Dama nace kaine dai² ni ? Dariya yayi yace ai riƙon mahaukaci sai sarki , nice mahaukaciyar ? Yace ah ah karin magana ne ni na isa ince miki mahaukaciya ai ke da ss kikayi kama sarkin bincike , dariya sukayi tare da tafawa suka koma palo sukaci gaba da kallon boll insu.
Wallahi Allah yau sai an faɗamin abinda yasa ba'asan An mata a gidan nan , laifin me tayi muku ne wai ? Momy tace na tsani yarinyar nan Dikko idan zakayi rai kayi rai idan zaka mutu ka mutu dan ubanka bansan yarinyar nan kuma har abadan duniya bazan taɓa santa ba , kuma har gobe har jibi ina nan zaune akan bakana sai an kamo min ita kuma saina wulaƙanta mata rayuwa kamar yadda nayi alƙawari bazan fasa ba ,
Haba Momy wai me tayi miki haka da ciwo don Allah ? Me tayi min ma kake tambaya ko ? Tou ubanka tayi min kaji ko ? Momy bana so ayi abinda za'azo aji babu kyau ki sauƙaƙa zafin ƙiyayyarki akan ta kafin aji wani iri wata rana , ko wata ranar tazo banajin komai kuma babu abinda zai faru idan wanda ya mutu zai dawo naga yadda zakayi ka auri karuwa ina numfashi ,
Wai waye yace karuwa ce ? Abinda kowa ya sani duniya da mutane sunyi mata tofin Allah barbaɗe , murmushi Dikko yayi mai ciwo yace duk bakin daya tofawa An mata Allah tsine insha Allah saiya tofa mata albarka babu daɗewa ,
Momy tace mahaukacin banza ka taɓa ganin albarka ta sauka akan tsinuwa ? Ko ka taɓa ganin iccen da tsawa ta faɗa ma ya sake tofowa ? Ai tsawa so ɗaya take faɗawa icce ya mutu shikenan ya gama rayuwa a duniya dai , juyawa Dikko yayi bai sake magana yana tafiya cikin yanayin mai wahalar fassaruwa ,
Yace gaskiya ne nine tsawar da na sauka akan An mata , kuma Allah zai taimakeni ita bazata mutu ba zata rayu cikin farin ciki kuma zatayi ganye tayi rassai zata zama alfahari a wurinki Momy idan har na auri An mata zaki sameta mai biyayya , ajiyar zuciya ya sauke dakel tare da lumshe idanuwanshi a bayyane yace Allah dai ka taimakeni a gano min inda mahaifiyarta take da wuri in miƙata cikin aminci da salama.
Harya taho bai samu nasarar ganin Al ' Ameen ba amma ya ja mishi layi zasu haɗu komai daɗewa kuma wallahi yadda ya jefi "Yar matanshi sai yayi mishi wulaƙanci na kafa tarihi marar gogewa a rayuwa.
Da tunanin Sultana ya isa gidanshi baiji daɗin abinda yayi mata ba amma ya zama dole ya koya mata tsoronshi dan idan harya aureta da wannan taurin kan nata matsala za'a samu , dole ta yadda shine a samanta kuma dole ta koyi bashi girma idan dan tana ganin murmushin shi zaisa ta rainashi zai tsare girmanshi bazai ma sake mata wasa ba tunda ita bata da wayau ,
Cike da tsantsar sha'awar kasancewa da Jiddah ya shiga gidanshi , shi baisan abinda yasa idan harya haɗa jiki da An mata yakanji yawan buƙatar kasancewa tare mace ba , dakel yayi wanka yana fitowa ya samu Jidda zaune a gefen gadonshi tasha wanka na ɗaukar hankali sai zabgaga ƙamshi takeyi mai tada hankali duk mai wata "yar guntuwar sha'awa ,
Cikin bariki ta fara mishi sannu da zuwa dakel ya ansa dan rabi da kwata hankalinshi baya nan ya tafi wata duniyar , yau tafiyar safe kayi my excellency ? Kallonta yayi tare da tambayarta ina naje ? Murmushi tayi mai ɗaukar hankali tace Abuja mana , waye yace miki ina Abuja ? Ai naga kwana biyu baka nan nasan kuma idan kana gari ina zaka je bayan gani ta ƙarasa maganar tare da "yar karairaya dai ta matan da suka san hannunsu wurin iya tattalin miji ,
Wani irin kallo yayi mata mai tayar da tsikar jiki cikin salon tafiya da hankalin mace yayi magana cewa Ey to miye ? Yayi maganar tare da miƙa mata hannunshi , tasowa tayi bayan ta bashi hannun nata saida ya sumbaci bayan hannun sannan ya buɗe tafin hannun yayi tsini da harshenshi yayi mata wata irin lasa a tsakiyar tafin hannun nata ya ƙare da sumbatar inda ya lasa ciki tako mai nuni da yayi rashinta , lumshe idanuwanta tayi tare da sauke ajiyar zuciya cikin yanayi mai nuni da saƙonshi yazo.
Jiddah fa ba'a baya ba shima Dikko jajirtacce cike da kulawa da junansu suka shiga masayar soyayyar ta hanyar ƙoƙarin dasawa junansu farin ciki irin na ma'aurata daga baya aka koma saman gado domin doguwar tafiya dole saida guziri , suma dai sunyi ma kansu guzirin gado , a sama aka caskale yadda ya kamata saida Dikko ya tabbatar ya kore duk wata tsohuwar ƙishirwar dake tattare da ita sannan shima ya samu natsuwa , amma wani abu da Jiddah tazo dashi shine ,
Kai tsaye ta nunawa Dikko kwalbar da bokansu ya bata cike da rashin wayau tace Yaya da Allah ka ɗan taimakamin , idonshi a rufe yana samanta bai sauka ba yace wane irin taimako ? Wani magani ne zan haɗa kuma da sinadirin namiji ake amfani dashi dan Allah ɗan kaɗan zaka zubamin anan ta miƙa mishi kwalbar , jin kwalba a hannunshi yasa ya buɗe idanuwanshi yace wane irin magani ne ake haɗawa da najasa dan tsabar ƙazanta ,
Nidai don Allah , tou ke me zai hana baza kiyi da naki ba tunda kece kike ra'ayi , ai na namiji akace , um umm aini ba namiji bane ba , nidai haka nan don Allah murmushi Dikko yayi a rashin shi yace kila wani fahami aka bata ta jiƙamin a soɓo mata ni sharrinku ai sai in rubuta littafi tunda cikinku nayi rayuwa , kallon agogo yayi ya jinjina kanshi yace da 15 yanzu zan koma 20 duk masifarki lokacin ya tafi bazai dawo ba , wato harma na namiji ,
Jiddah taci gaba da dan Allah dan Annabi , banza Dikko yayi bai mata magana ba , saida lokacin daya iba ya cika ya sauka daga saman gadon ya nufi toilet , bayan mintuna 30 ya fito , ƙananan kaya ya saka bayan ya feshe jikinshi da turare ko inda Jiddah take bai kalla ba ya ɗauki wayoyinshi ya fice.
Yana fita ta ɗauki wayarta ta kira Al ' Ameen ta rattafa mishi yadda sukayi da Dikko , faɗa yayi mata cewa haba ranki ya daɗe ya akayi kikayi wannan kwaɓar kinja ma kanki nayi imani da girman Allah mai gida ya taso ki gaba da bin bincike kinja mana kuma ki rubuta ki ajiye wallahi ko ruwan gidanki bazai sake sha ba , ke kina wasa da mai gida ? Wai kin kuwa san yadda yakeji da rayuwarshi ? Kai gaskiya kin ɓata wallahi mi yasa kikayi haka ???
Jiddah tace no ka gane Al ' Ameen wannan ba damuwa bane ba idan haggu taƙi kawai mu dawo dama , ka bari saura sati ɗaya na fara period sai in zuba kawai ka kai mishi , tunda malam yace idan akayi amfani da jinan al'adata sai yadda nayi da Yaya , sperm in nashi ne yace idan anyi amfani dashi za'a goge mishi ko wace mace daga zuciyarshi saini ɗaya...
Ba haka Al ' Ameen yaso ba kawai dai yace to , bayan sun gama waya da Jiddah ya kira Mardiyya tana ɗauka yace Doughter zan shigo kaduna zuwa cikin sati na gaba yaushe kike fara al'adarki ? Uncle meya faru ? Boka yace a kawo sperm in mai gida tou naso ace an samu amma matar tashi wata aljihun gefe ce ta kasa , wai dan wawanci irin na sakakkin "ya "ya kawai taba mai gida kwalbar wai ya zuba mata maniyinshi kiji hauka da ɓacewar hanya , dariya Mardiyya tayi tare da cewa Uncle ni zanzo in kawwo ƙarshen film in nan haka nan ,
Al ' Ameen yace karki zo dan in faɗa miki yauma nemana yake saboda tsigaggiyar yarinyar nan , yanzu dai yaushe kike fara naki jinin ? Mardiyya tace jiya na fara , Al ' Ameen yace tou zan shigo kadunar gobe in ansa in kaiwa boka , dan dama nama boka bayani akan ki zai haɗa maganin kinga idan akayi sai a kawo ma Jiddah sai mu samu tayi mana amfani dashi wurin ba mai gida , tana jiran taji soyayya sai kawai tajita a out... Cikin jin daɗi Mardiyya tace na gode Uncle Allah ya kawo ka lafiya yace amin my doughter ki gaishe da Yaya saina zo , zataji sukayi sallama.
Wallahi ni ba Babanta bane ba , wani irin mari aka wanka mishi harsai da haƙorinshi na ƙurya ya fita , cikin kuka yace wallahi ranka ya daɗe ɗiyar abokina ce , wani ne yakai mishi duka a ciki tare da cewa idan tafi ƙarfinka batafi karfin hukuma ba , Bello cewa yakeyi wallahi ranka ya daɗe ba "yata ce ba , saida sukayi ma Bello lullusar fitar hayyaci sannan suka wurgashi a cell suna cewa idan ka kawota sai mu fitar dakai.
Nayi ² na tuna abinda ya faru dani ban sani , na kasa sanin ta yadda akayi Dikko yayi min wannan dukan har yajimin ciwo ba tare dana sani ba , ko dami ya dakeni ? Duk yajimin ciwo fuskata kuma duk sahun mari ne lallai duk yadda akayi bugun bala'e yayi min tou meya ɓata mishi rai haka .... ?
Dakel nayi sallah isha'e kafin in tashi daga inda nayi sallah masarar ta lulluɓeni kasa komawa nayi saman katifa duk jikina ciwo yakemin na kasa wani ƙwaƙƙwarar motsi gaskiya nasha azaba ta ban mamaki a ranar nan !
Tunda na kwanta ban iya wani isashshen motsi ba har gari ya waye , haka na tashi jikina yayi tsami dakel na iya yin wanka nayo alwallah dan yau na makara tunda na kwanta sai 8:39am na farka ,
Bayan nayi sallah ko mai ban shafa ba na saka kayana na fita palo , kamar jiya yauma yana zaune a inda ya zauna jiya ko inda nake bai kalla ba ya ƙaddara ma baisan Allah ya ajiyeni ba , daga nesa dashi na tsaya nace ina kwana ,
Bai ansa ba , kuma bai kalleni ba hankalin shi nakan wani littafi yana dubawa , wuri na samu na zauna kamar an sani na zame gefen hijabin nace duk wanda jamin ciwo anan ban yafe mishi ba , kuma tafiyata zanyi tunda bansan abinda nayi maka ka dakeni ba , na ƙarasa maganar ina kuka ,
Ba tare daya kalleni ba yace An mata zo nan , tashi nayi na tafi kusa dashi ina kuka , wuri ya nunamin na zauna , cikin tausayi ya kalleni yace nine baki yafe mawa ba ? Ni badai nake ba , to dawa kike bayan dagani saike a palon , aini ba kai nake jama Allah ya isa ba , to kin yafemin ni ? Kaina na ɗaga alamar Eh , yace kiyi haƙuri ni bana iya sarrafa fushi bansan abinda yake damuna ba idan nayi fushi saina sauke ki daina ɓatamin rai kinga dai ina sanki bana so kina shiga rayuwa mara kyau , kowa dariya yakemin wai An matar ma da nake taƙama da ita abida batajin magana kuma bata so na , kinsan me nake cewa ?
A , a , na bashi ansa , kyakkyawan murmushin shi yayi tare da tsareni da idanuwanshi masu ɗaukar hankali yace ai nasan zaki faɗa ya ƙarasa maganar yana min hararar so , murmushi nayi cikin jin daɗi na gyara zamana ina kallon kyakkyawar fuskarshi gaba ɗaya sai naji masassarar da nake ji babu , yace ko nayi ƙarya ? Girgiza kaina nayi alamar a , a ,
Shi kuma yaci gaba da cewa ni ko nace zanyi fushi dake wallahi ƙarya nake bazan iya ba , da kinsan yadda kike da mutunci da daraja a wurina da kin daina wahalar da zuciyata da taki , kina ta fama da wahalar dakon so bayan nasan yanzu idan har zamu rabu sai kinyi kuka , tafiya zata iya riskata a ko wane lokaci zan tafi na barki da tunanina babu dare ba rana , zaki kasa bacci dare zai miki nisa wurin kwanciya zai miki girma zaki ga rana ta daɗe bata faɗi ba yayin da kika tuna Dikko baya tare dake , kawai ki daina wani ɓoyewa ki faɗi abinda ke cikin zuciyarki nidai tuni na faɗi nawa , ya ƙarasa maganar tare da miƙomin ɗan yatsan shi mu shirya , dan kinsan jiya na ɓata dake....
Miƙa mishi ɗan yatsana nayi ya lanƙwashi shi da nashi yace faɗamin me yasa bakya so na ? Shiru nayi yace amma ai kina so na mi yasa kike ɓoyewa ? Rufe idanuwana na nayi yace yi haƙuri An mata faɗamin matsayaina a wurinki me yasa kike min wasa da zuciya ,
Cikin kuka nace a wata rana kayi magana akan idanuwa na , to wannan ranar tayimin naji kamar in rungumeka a wannan ranar sannan nace ina sanka ,
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke da sauri tare da dafe dai² zuciyarshi da duka hannunshi biyu ya kwantar da kanshi saman kujera tare da lunshe idanuwanshi yace me yasa baki faɗa ba a wancan lokacin An mata ?
Shashshekar kuka nayi tare da cewa saboda ina tsoron kada na rasa ajina , sauko kanshi yayi ya kalleni yace wallahi Allah babu ranar da ajinki ko wani mutuncinki da zai rage a idona ko a zuciyata , ki taka yadda kike so ina tare dake tsakanin rayuwa da mutuwa , waccan ranar kinji kamar zakice kina so na , yau fa ? Yauma kinajin kamar kina so na............?
Su Yazeed ne suka shigo palon , cikin zaulaya yace An mata an shirya kenan a dai² lokacin daya iso yaba Dikko hannu suka tafa , bayan sun tafa Dikko yace aimu bama faɗa ko An matana ? Jiya ma sheyɗan ne yazo kuma mun koreshi bazai sake dawowa ba ko ? Shiru nayi zan tashi ya riƙoni tare da turani saman kujera shima ya dawo kusa dani ya zauna su Yazeed suka samu wuri suka zauna ,
Yazeed yace zakaje ko ka fasa ne ? Ya tambayi Dikko , ɗan gyara bakinshi yayi ya riƙe leɓonshi na ƙasa dana sama yace gaskiya banajin zanje , a , a kar kayi haka kayi haƙuri ko daga ƙarshe ne muje ai yafi bamu je ba , kallona Yazeed yayi yace ai kema zakije ko "Yar mata , dogon kallo Dikko yayi mishi sosai sannan ya kalleni tare da nunamin inda makullin mota yake yace jeki ki ɗauko abinci a mota , saura idan kinje ki ƙara gaba......
Ɗaukar makullin nayi na fita........
17/10/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 58
Follow me on wattpad meelatmusa
Ina zuwa jikin motar na buɗe na kame a mazauni driver na tada mota na gyara parking kawai dan neman magana , Yazeed yace ga mutuniyar ka can zata fita , murmushi Dikko yayi tare da cewa wai dan in fita inta hayani so take ta maidani lusarin namiji , fitowa nayi na buɗe but in motar na fara fiddo ƙattin food flakes ina ajiyewa ƙasa.
Ban gama fiddowa ba Dikko da Yazeed suka fito a dai² lokacin da aka buɗe get Umar ya shigo saman doki wasu motoci biyu kuma suka biyo bayanshi , ɗaukar ta miya nayi na nufi hanyar shiga palon ina zuwa na tsaya kusa da Dikko nace ka ɗauka fita zanyi ko ? Kallona yayi bainin magana ba , murmushi nayi tare da cewa dama dan inji yadda zaka ce , yadda zance ai a jikinki zakiji idan kin fita zaki dawo ki sameni ni kuma zan ɗora miki a inda na tsaya bazan gaji ba , yana faɗin haka ya gangare yana ba Umar umarni ya ida shigar da abincin ciki.
Ina ajiye miyar ɗaki na koma na kwanta , shi kuma Dikko mota ya koma yana cema Umar ka taho da allurar ne ? Innalillahi bara in koma in ɗauko ya faɗi maganar yana mai lalabu aljihunshi ya fita da sauri daga gidan.
Umar yana fita Yazeed yace DK yarinyar ka fa ta koma , gaba ɗaya hankalinshi yana cikin mota yana dube² yace ai zata fito yanzu , Yazeed ya fara ƙwala min kira An mata Dikko yace me zata maka ne ? Dariya yayi tare da cewa da Allah barta ta fito insha dariya , tsoki Dikko yayi yana fitowa daga cikin mota yace to ita abokiyar wasanka ce ?
Yazeed yace dan Allah barta ta fito , Dikko yace to ai bani ne na hana ta fitowa ba ita idan tanajin yunwa ragguwa take zama ya ƙarasa maganar yana leƙowa ta window ɗakina yace me ye ? Ba komai na bashi ansa ba tare dana kalli inda yake ba , taso ki zo ina kiranki , ba tare da nace tou ba na tashi na fito wurinsu.
Yazeed yace ke "yar yarinya sai kiyi ta zama a ɗaki sai kace mai jego ? Ki fito kisha iska sai fama kike da hijabi kamar matar mamaci , murmushi Dikko yayi yana kallona yaɗan shafo gemunshi da bayan hannunshi ta ƙasa yana cewa kai wallahi wannan matar ustaz ce ko An matana ? Ya ƙarasa maganar yana ɗagamin gira , murmushi nayi tare da matsawa kusa da Dikko hannu na yaja ya maidani mota yana cewa wani wuri zamuje kina zuwa in tafi dake ?
A , a , ni banajin daɗi , tou meya sameki ko kema in miki allura ne ? Wace irin allura ? Allura nawa kika sani ne ? Idan mutum baya lafiya akeyi , Dikko yace to aikema kince bakyajin daɗi idan nayi ma doki kema sai in miki amma bazan miki da zafi ba , ni doki ce ? Nayi maganar ina harararshi , murmushi yayi yace An mata kenan kanki baya ɗauka dana faɗa miki wata magana idan ma dokince ke da kanki zaki faɗamin ,
Ɓata raina nayi nace kaina baya ja ? Dikko yace ba haka nake nufi ba ina nufin kinyi "yar ƙarama ni babba dani in zauna in ta sakin layi , idan na faɗa miki baza ki bani ansa yadda zanji daɗi ba ina iya faɗa ki dangana abun da wani shirme daban ki bani ansar da zata ɓatamin rai shi yasa kikaji nace haka......!
Tou amma sai kace kaina baya ɗauka , Dikko yace a , a karfa muyi haka dake wai me yasa kikemin bahagguwar fahimta ne ? Kanki yana ɗauka mana abinda nake nufi maganganuna ni idan nayi miki sun girmi kwalwarki da lissafinki , fashewa nayi da kuka nace nice banda kwalwa banda lissafi , ɗaure fuska Dikko yayi cikin ɓacin rai yace An mata naje nace kiyi yadda zakiyi dani idan zaki iya mtsww ya fita daga motar yana sabbatu , Yazeed dake sauraren firarmu yayi dariya , tsoki Dikko ya sakeyi tare da ansar allura a hannun Umar ya nufi palo.
Bai daɗe ba ya fito da wata "yar madaidaiciyar kwalba a hannunshi ya soka sirinji ciki yana tsotsowa , hararar inda nake yayi cikin yanayin jin haushi , fitowa nayi daga cikin mota nima cikin ɓacin rai na tsaya ina kallonshi yana ma doki allura.
Bayan ya gama yake ma Umar bayani yadda zaiyi amfani da allurar yana ci gaba da cewa mantawa yayi da ya taho da ita kai kuma cewa nayi kawai kazo ka ansa ka kama ka taho doki ni bana san kuna hawan dokin nan tunda baida lafiya , wata takadda ya ciro a aljihunshi ya bashi yana cewa yayi sauri ya anso mishi , Yazeed kuma palo ya koma zaici abinci , wanda suka zo a mota suma fita sukayi tare da Umar , filin wuri ya rage daga ni sai Dikko.
Ciki na koma na sako dogon wando tunda har naga ya ɓata rai akan rashin san hawan dokin saina hau na ɓata mishi rai nima , ban daɗe ba na fito Dikko yana cikin mota yana waya , motar Yazeed na taka saboda dokin a kusa da ita yake , cikin fargaba Dikko yace An mata ki bari karki faɗo kiji ciwo wai me yasa kikeyin haka ne ? Idan an taroki ta nan sai ki koma tanan wai meke damun kanki da Allah......?
Banza nayi na ƙyaleshi na tattara hijabina na haye saman dokin , murmushin mugunta yayi ya koma palo makullin motar Yazeed ya ɗauko tare da rufe palon da makulli ta waje ya rufe gidan , ɗauke motar yayi daga inda take ya matsa da ita kusa da tashi , bayan ya kaita ya dawo kusa dani ya dafa dokin yace kinyi kyau bari in miki hoto ko kuma ba yanzu ba bari sai anjima , bakin dokin ya buɗe ya tura mishi wani abu bansan ko miye ya bashi ba , lokaci guda dokin ya firgice ya riƙa wata irin zabura yana jijjiga sai wata irin samarya yakeyi yana haniniya gaba ɗaya kukanshi ya cika kaf gidan...
Kallona Dikko yayi yace ai dan ki ɓatamin rai ko ? Kema naki zai ɓaci sai naga mai sakoki duk sai jikinki yayi ciwo , idan kuma kin bari kika faɗo wallahi ta samanki zaiyi wannan haukan kuma ko sannu bazan miki ba , Allah ya taimaka a sauko lafiya , yana faɗin haka ya koma mota ya kunnata ya ɗage glasses yaci gaba da wayarshi cikin kwanciyar hankali ya barni saman dokin daya haukata....
Kallon nisan ƙasa da saman da nake nayi lallai idan na kuskura na faɗo wuyana karyewa zaiyi in mutu , gaskiya Dikko mugune , riƙe dokin nayi sosai gashi yaƙi tafiya wuri ɗaya ya tsaya yana hauka ,
Riƙe wuyan dokin nayi sosai ina kuka , saboda abinda na fahimta duk bayan wasu seconds ƙara haukacewa yakeyi , saiya jirgoni na rabo daga samanshi sai inyi sauri na ƙara riƙewa , tun ina dauriya har ƙafafuwana da cinyoyina suka fara ciwo , dani da doki haka kowa yaita kuka ,
Yazeed kuwa da yaji ihun doki ya taho dan ya fito yaji ƙofa rufe , ta window ya leƙa yaga Sultana ta haɗa zufa da hawaye waya ya buga ma Dikko bayan ya ɗauka yace haba DK karfa yarinyar mutane ta faɗo taji ciwo , Dikko yace yarinya tace bata kowa ba duk faɗin duniyar nan nine nake da ita , inajin daɗine kawai tana wahaltuwa a sauƙaƙe ita kangara ni kuma cuta , idan ma ta faɗo taji ciwo nine zanyi jinyarta ba wani ba , dan Allah zo ka buɗe tafiya zanyi , idan na gama abinda nakeyi ai kasan dole zan buɗe yana faɗin haka ya kashe wayar.
Kwanciya nayi saman dokin na riƙe wuyanshi sosai naci gaba da kuka dan kawai na haƙura idan ma na faɗo duk abinda ya faru haka yazo a rubuce , tausayi na bashi ya fito yaje ya buɗe ƙofar ya saukoni da kuka na wuce da gudu na tafi ɗaki.
Cikin kuka nayi wanka ina fitowa na saka kaya ko abinci ban samu naci ba na kwanta sai bacci ,
Saboda azabar duka da fitar da haƙorinshi yayi har fuskarshi ta kunbura , fito dashi akayi dan ya anshi na safe , wato duka , bayan an fiddoshi akace ina take ne ? Cikin kuka yace wallahi ranka ya daɗe bansan inda take ba , saida suka sake mishi lullusar fitar hayyaci sannan suka sake tambayarshi ka tuno inda take ne ? Cikin kyarmar jiki yace Allah ya taimake ka wallahi bansan inda take ba , cire mishi rigar jikinshi sukayi suka bashi azaba saida sukayi ma jikinshi kaca² suka rufe sahun dukan da gishiri , wata irin ƙara Bello yayi kamar ana cire ran kafiri yace oficer bansan inda take ba ,
Saida aka sake tattaka Bello wanda ya takashi yace lallai soyayyarta mai girma ce a zuciyarka , wannan ɗiya kanaji da ita sosai ya ƙarasa maganar tare da halbashi ya tafi suuu ya shige cikin magarƙama ya kullu yana cewa ka tuno inda ka ɓoyeta kafin nan da wayoyi biyar.....
Cikin farin ciki Al ' Ameen ya ɗauki hanyar Kaduna , bayan ya gama zabgagawa Jiddah ƙarya ya anshi dubu ɗari biyar a hannunta kuma yasa tayi mishi full tank da motar da aka kwace daga hannun Sultana yace boka yayi kira na gaggawa za'a anso mata saƙo kafin zuwan jininta...
Yana isa Kaduna ko hutawa baiyi ba ya ɗauki Mardiyya suka dawo zaria wurin mushiriki , bayan ya baje kayan tsafinsa yaci gaba da koro musu jawabi maganar dai ɗaya akan Sultana kuma ya tabbatarsu da rabuwar Dikko da Sultana babu jimawa ya ƙara da cewa kuma sai Dikko ya ɗiga ma Sultana ruwan rashin mutunci bayan yayi mata wulaƙanci da gori na rashin arziƙi zai korata...
Bayan ya gama bayani ya anshi jinin hailar Mardiyya ya wurga kwalbar sama cikin ƙanƙanin lokaci ta dawo babu jinin a ciki sai garin magani yace Mardiyya ita da kanta zata zubawa Dikko a abunci ko abunsha idan dai tayi wannan tou magana ya ƙare , saboda Dikko zai zama nata ita ɗaya idan ta ajiye masa ƙara tace karya tsallaka bazai wuce ba saboda gudun ɓacin ranta , amma da sharaɗi a kiyaye kar wanda ya sake ta taɓa kwalbar nan saike idan kuwa wani ya taɓa bake ba tou kashinki ya bushe ya ƙarasa maganar yana nuna Mardiyya da ɗan yatsa !
Ansa tayi tare dayin godiya Al ' Ameen ya bashi dubu ɗari da hamsin tare da cewa dubu ɗari na aikin Mardiyya dubu hamsin kuma ayi mishi aiki akan mai gida ya maidashi bakin aiki dan gaskiya yana fama da talauci kuma gashi Dikko zaiyi tafiya yana so yaje dashi waccan tafiyar da Ashiru aka tafi , tafiya da mai gida kuɗi mutum yakeyi akafin a dawo....
Boka yace ya dawo sati na gaba ya anshi saƙo , godiya sukayi suka tafi har suka bar wurin boka basuyi maganar Jiddah ba , bayan ya maida Mardiyya gida ya bata cikon dubu ɗari 3 ya riƙe dubu hamsin yace ki sayi kaya masu kyau da turaruka wani satin idan na dawo sai in tafi dake wurin Momy ince kinzo gaisheta ta , ke kuma daga nan sai kici gaba da gyara aikinki har mu samu nasara , godiya Mardiyya tayi ma Uncle sannan sukayi sallama ya kamo hanyar katsina....
Sai bayan la'asar sakaliya na tashi daga bacci , shima bani na tashi da kaina ba Dikko ne ya tasheni wai in tashi haka nan inci abinci kada yunwa ta kama mashi ni , koda na buɗe idona na ganshi ɓata rai nayi na juya da niyar ci gaba da bacci , ke ki tashi haka nan nace fita zamuyi , basar wa nayi na rufe idona dan gajiya nakeji sosai tsakanin jiya da yau duk banji daɗi ba...
Hawowa yayi saman katifar ko takalminshi bai cire ba tsabar wulaƙanci yana janye abinda na lulluɓe , kallonshi nayi sannan na kalli ƙafarshi , shima kallon ƙafar yayi yace palo mota kawai naje babu wani datti a jikin takalmina ,
Tashi nayi na sauka daga saman katifar nace na tsanaka , wannan ai ba baƙuwar kalma bace wurina , kin tsaneni bakya so na duk nasansu , Dikkon banza Dikkon wofi shima wannan ai na sani sai me kuma ?
Baka burgeni , to aini kina burgeni ba lallai saini na burgeki ba , tunda ni ina sanki kuma kina burgeni kinmin a haka , fushinki da duk wani kunburinki bai damuna dan banma san kinayi ba ko aure mukayi kika ɓatamin rai sai nayi miki hukunci dai² da abinda kikayi kuma ko yanzu na zaneki miki jiki tass bazai hana in miki magana ba ko inƙi ansar haƙƙina a wurinki idan na biya buƙata ta kije can kita kunburinki , gara ki iya ki kuma koyi kauda fushinki ki koyi haƙuri dani ko kuma ki kiyaye ɓatamin domin da zaran nayi fushi bani ne ba gara ki koyi kaucewa fushina kawai sai ki zauna lafiya , wuce kiyi wanka kuma karki ɓatamin lokaci jiranki nakeyi.
Wanka na shiga ina tunanin rashin kunya ta Dikko wato shi ɗan iska ma har tunani yakeyi zai dakeni kuma yayi tunanin kwanciyar aure dani , to wai waye ma yace yana san sa bare yasa ran zan iya aurenshi zuciya akamar ahalin kutare.....
Koda na fito wanka a ɗakin na sameshi sai tattara duk wani abu daya shafeni yakeyi yana jibgawa a cikin trolley bag , jikina a sanyaye nace Yaya me yasa kake zubasu anan ko baka so ina ajiyewa a gefen katifa ne ? Shiru yayi baiyi magana ba yaci gaba da tattarawa amma yanayin fuskarshi babu daɗi ,
Cike da damuwa na matsa kusa dashi na duƙa nace D-kow wai miye ya faru ? A dai² lokacin daya zage ziff in jakar ya ɗago yace An mata dole rabuwa zamuyi , cikin damuwa nace mi yasa ko nayi maka wani abu bakaji daɗi ba ? Ba abinda kikamin kuma bana tunani har mutuwa ta zanji babu daɗi daga gareki , tou me nayi maka zaka rabani da kanka a dai² lokacin dana ke farin ciki kasancewa dakai , me yasa ka koyamin sanka kuma zaka rabu dani yanzu ina zaka kaini......?
Me yasa kakemin irin wannan wasan nidai bana so dan Allah , na ƙarasa maganar tare da duƙawa na buɗe jakar na zazzage kayana ina cewa babu inda zanje , ina ne kake tunanin zanje bayan kasan kaine hatimin sa'ata sai kawai lokaci ɗaya ka rusa min sa'ar rayuwa tou wa kake so ya zauna dakai idan bani ba.....?
Sake tattara kayan yayi ya maida cikin jakar ya rufe , cikin kuka nace wai me yasa kake min bana so bara na sake fiddo kayan idan ka mayar dasu nima zanyi fushi , riƙeni yayi yace gida zaki tafi , cikin hayagaga nace wane irin gida ? Dama inda zakuje dani kenan kaida Yazeed munafikai ne ku tou bazanje ba ɗin sai inga mai fitar dani haba da Allah ,
An mata , kafin yayi magana nace An mato Allah babu inda zanje sauƙaƙa kuka na nayi na rungume Dikko nace a gaban idonka jiya mutuwa tayi wasa da rayuwata , kuma kaga yadda tayi wasan kura da Babana , kowa baya so na Baba ƙarami ya koreni Aunty Mamy ta rasu , wata Aunty ta mutu ban ganta ba , shashshekar kuka nayi tare da sakin Dikko nace ita kuma Aunty Suwaiba cewa tayi in tafi dan bata san damuwa ta sake zuwa a rayuwarta , nazo wurinka shine zaka korani shikenan ka daina so na , goge hawaye nayi tare da ɗaukar kayan daya ajiyemin na saka ina kuka....
Cewa shikenan ba komai zan tafi amma ka bar kayanka bana so , dama ai badasu nazo ba , kusa dani ya matso zai riƙeni cikin hayani nace karka taɓani bana sanka , Allah ya gogemin kai a zuciyata na tsaneka , riƙe ƙugu yayi yana kallona cikin yanayin mamaki yace wai baza ki tsaya nayi miki bayani ba ko kuwa ke kaɗai kika iya fushi wai ? Ki bari bana so muyi rabuwar fushi dani dake ki tsaya ki natsu , bana san ayi rabuwar arziƙi ta bala'e nake so ayi , tsoki Dikko yayi tare da kiran Ashiru , babu ɓata lokaci yazo yace ɗauka jakar ina zuwa , ɗauka Ashiru yayi ya fita yana fita Dikko ya sake matsawo nace karka taɓani bana sanka...
Zuƙewa nakeyi amma da ƙarfi Dikko ya riƙeni tare da rungumewa a jikinshi ya sauke wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya mai saukar da kasala , tunda ya haɗani da jikinshi nayi shiru na kasa wani wadataccen motsi na kwantar da kaina saman ƙirjinshi na rufe idanuwana , shima rufe nashi idanuwan yayi tare da cewa An mata kiyi haƙuri kinsan ina sanki kuma ba wani abu kikamin ba , zan rabu dake ne dan sadaki da farin ciki na gaba tun ranar rasuwa Baba dana tambayeki Mamanki kikacemin bata nan ta tafi ta barki , tun daga wannan lokacin na duƙufa wurin nemota , bayan wanda nasa sun mun samota dakel suka mata bayanin ki cewa tayi ta yafe ki wa Babanku ,
Da suke nemi ba'asi , shiru Dikko yayi ya kasa ƙarasawa , abinda Inna tace shine taji baƙin cikin lalatamin rayuwa tayi kuka kamar ranta zai fita tun lokacin da abokan zama sukaji Baba ya sakani a wasan caca suka farayi mata gori da habaici suna cikin farin ciki , bayan sun samu labarin abinda akamin aka yadani a ƙofar gida shine kunya tasa ta gudu dan bata iya haɗa ido da kishiyoyi , bayan ta tafi shine Baba ya aika mata da saki har saki 3 yace shi mace bata mishi yaji kuma ba'a kome a gidanshi....
Shine ta nemi ya bata ni amma yace ai bai gagara riƙe Uwar masu gida ba , ko dan tana ganin suna da kuɗi a gidansu take tunanin zai bata "yarshi shi jininshi baya zuwa kwaraka dan su basu gaji kwakwa ba ,
Ko baki faɗa ba nasan kina so na An mata , ina sanki bazan iya zuwa rakaki ba nima cikin daren nan zan bar katsina bansan zamu rabu a dai² irin wannan lokacin ba , karkiyi rashin ji banda yawo kinji ko ? Duk wani bincike ² ki daina kibarma Dikko komai tsaye nake babu dare ba rana akanki An mata ko bacci nake kece a saman idona , kece mafarkina komai na kece rayuwarki kaf a raina take ki natsu dan Allah dan annabi , idan kuma kikayi taurin kai zanzo kuma kinsan abinda zai faru ,
Kwanaki na ce bana zarginki , kinsan abinda yasa nace miki haka ? Shiru nayi banyi magana ba , yace kinga ya nunamin tafin hannunshi yace duk motsinki yana nan ciki kuma na yafe miki abinda kikayi a baya nasan ɓacin rai ne da ƙaddara karki ƙara kinji ya ƙarasa maganar yana ɗagoni daga jikinshi ƙara komawa nayi na kwanta murmushi yayi mai sauti har cikin zuciyata ya soka , yace insha Allah zamuyi aure babu jimawa An mata zan dasa farin ciki a rayuwarki nima ki haifomin wata "yar matan , amma bamai taurin kai irin naki ba ya ƙarasa maganar cikin zaulaya.....
Dakel ya ɓanɓareni daga jikinshi ina kuka ya kamo hannuna muka fito , muna shigowa palon gaba ɗaya abokanshi suka taso suna Allah sarki An mata tafiya zakiyi ? Yazeed ne yake cewa sai munzo zance , ko zaki hau dokin bankwana , dariya sukayi dukansu Dikko yace kadaiji kunya , Yazeed yace kaine kaji kunya daka ɗora An mata a doki har tayi kuka , murmushi Dikko yayi tare da cewa Allah yasa ma banji abinda kace ba !
Har wurin mota suka rakani , Yazeed yace yana zuwa , gaskiya sunmin halakci suna cewa basu san zan tafi ba , yawansu da daloli suka sallameni Yazeed ne ya bani kyautar zoɓen zinari mai kyau amma Dikko ya ƙwace shi ya ƙaryashi tare da cewa suma dan karsuce wani abu na barta ta ansa kuɗinsu sai kai ɗan haɗama zaka bata zobe ? Tou har yaushe ma ka siya ka ajiyeshi ? Wato kana jira idan bana nan ka saka mata ko ? Ko ni na taɓa ba matarka kyautar zobe ne ? Cikin yanayin rashin jin daɗi Yazeed yace aikai ba matarka bace ba kuma dan na bata zobe miye duk su da suka bata kuɗi baka ansa ka zubar ba saini ? Dikko yace kaima ka bata kuɗin kaga idan ban barta ta ansa ba , ai ni ban fito da kuɗi ba , sai zobe ka fito dashi ? Allah dai yasa ta tafiya zatayi ɗan iska ƙaton banza kadaiji kunya wallahi , ashe da anci amanata.....
Dariya sukayi gaba ɗayansu hada Yazeed banda Dikko amma maganar dai cikin sigar zaulaya yayi ta dan dai bai cika dariya ba kawai ke baiyi ba , Yazeed yace ba komai An mata zanzo jibi , Dikko yace Allah ya kaimu , kallona yayi yace An mata Yazeed zaizo jibi idan muna da rayuwa amma idan yazo ya baki zo be a , a , kinji nace tou , to ku tafi muyi bankwana yace , wani ne daban yace to ku tafi tare kawai mana , murmushi Dikko yayi tare da fita daga cikin motar yace sai munyi waya ya ƙarasa maganar yana rufe motar... !
Ashru yaja muka tafi daga gidan suna ta ɗagamin hannu , kukana ƙara yawa yayi ina cike da kewar Dikko , tunda muka hau titi na duƙar da kaina naci gaba da kuka ina maraicin Dikko da duka zuciyata.....
Da malami da karuwa ba abin yadda bane ba dan basu da amana , Al ' Ameen kuwa saida yazo malumfashi ya tsaya wurin wani gahurtaccen malamin tsubbu ya anshi asiri , abinda yasa bai anso wurin boka ba saboda Jiddah taga wurinshi taje tayi mishi ɓarin kuɗi ya kwashe komai ya faɗa mata , asirin farko Jiddah karta riƙa jin maganar kowa sai nashi , na biyu kuma Dikko akayi ma ya maidashi aiki na ukku kuma , Sultana rabuwa ita da Dikko , na huɗu kar Jiddah ta aihu dan so yakeyi duk wannan tulun dukiyar ta Dikko su lasheta idan Mardiyya ta aihu sai su kashe shi su cinye komai nashi....
Bayan yazo katsina ya bawa Jiddah yace inji boka kuma duk ya faɗa mata yadda zatayi amfani dasu hada wanda zata zubawa Dikko a abinci godiya tayi sosai ta bashi dubu ɗari 3 tace yasha maganin gajiya , godiya yayi sannan ya fita...
Dikko kuwa tafiyar Sultana bayan kowa ya tattara abinda yake buƙata government house suka nufa bayan ya shirya ma abokanshi abinda ya shirya dan ya kuɓutar da Sultana daga tarkon Momy ta shafawa An mata lafiya tayi rayuwarta free.
Tare ya shiga da zugar abokanshi da sukayi amfani da motoci huɗu , bayan ya fara bincika Al ' Ameen bai samu ba , daga inda yake tunanin zai samu Al ' Ameen babu kai tsaye ƙofar palon Momy suka nufa bayan sunyi parking ya zame ya rufe idonshi , gaba ɗaya suka fito daga cikin motoci suka fara ƙoƙarin fito da Dikko daga cikin mota , jin tsayuwar mota yasan ƙannenshi mata suka fito dan sun san shi kaɗai ne ke zuwa da irin wannan tuƙin kuma sunji an ɗauki lokaci bai shigo ba suka fito , su dai Allah yasa musu san ɗan uwansu kodan shi ɗaya ne namiji ? Da mamaki sukaga ana fito da Dikko daga mota sai kakkafawa yakeyi , wayyo me ya samu Baban Dady sukayi wurin suna kuka dasu aka fiddo da dikko daga mota aka shiga ciki !
Momy na zaune a cikin ƙaton palon gidan gwamnati tanajin daɗin ta bata da wata damuwa ko tashin hankali na duniya tana shan iska yadda ya kamata taga an shigo da Dikko sai kakkafewa yakeyi , ciwon da bata taɓa ganinshi da irinshi ba gaba ɗaya ta ruɗe cikin tashin hankali tace meya sameshi ne ? Wanda Dikko ya ɗaura a matsayin lawyer n shi yace wai kasashi akayi ne ? Gyara zaman kallabin kanta tayi tace miye kasawa ? Wata yarinya yakeso shine akayi mata aure , cikin hargowa Momy tace wace yarinya ? Yazeed yace muma bamu santa ba kawai dai muna zaune ya faɗi yana cewa An mata , dariya Momy tayi tare da cewa shikenan Allah ya raba faɗa , yaushe akeyin bikin ? Yau aka kaita gidanta , Momy tace babanta yaci uwashi shi yasa yayi sauri yasa akayi mata aure ,
Bedroom ta nufa ta ɗauko magani tazo ta zuba mishi amma saiya watsoshi maimakon ya miƙe , ƙara zuba mishi tayi ya ƙara fesewo , cikin ruɗewa ta koma ciki "ya "yanta suka bita suna kuka , tana shiga Dikko yayi murmushi tare da ɗagawa su Yazeed gira ya kashe ido ɗaya ya koma yanayin da yake kamar baya , a firgice ta sake dawowa da wani maganin tana ni maganinshi kamar yana wurinshi , a ruɗe ta fita dan wannan ciwon ya tadawa Momy hankali da gudu ƙannenshi sukabi bayanta dan sunga mahaifiyarsu tana cikin tashin hankali , tana fita Dikko yace ko idan ta sake zubamin maganin ince bazan tashi ba sai an kawo An mata , wani yace a kawo ta daga gidan ubanwa bayan kace muce an mata aure , zaro ido Dikko yayi cewa innalillahi na rantse da Allah da nasan hankalin Momy zai tashi haka da ba wannan dabarar akayi ba , wayyo Allahna gani gareka , shigowar Momy wata irin zabura yayi tare dayin harbe² danma karta ga kamar yana magana shi yasa ya birkice su Yazeed suka fara ƙoƙarin juyoshi amma duk yawansu suka kasa firgito Dikko , Yazeed yace karfa ƙaramar magana ya zama babba.....
Duk wani shaƙe² Momy tayi amma Dikko yaƙi tashi gashi Dady baya nan , ciki ta koma ta kira Dady ta sanar mishi abinda ke faruwa , inda zata samu maganin da yayi mishi amfani dashi a gidanshi ya faɗa ajiye wayar tayi ta fita da sauri ta daɗe sosai sannan ta dawo ana shaƙa mishi ya miƙe yana tari da atishawa Yazeed yace ashe da gaske....?
Momy tace da gaske mana ai dan ubanshi yasan baida cikkar lafiya yake so kashe kanshi , dan anyi mata aure miye ? Ba rabokan bace shi yasa baka sameta ba , nasiha Momy tayi ma Dikko daga ƙarshe tace ai An mata hadari ce kuma tazo ta tafi kawai ya manta da ita ,
Tashi yayi baiyi magana ba ya fita suma abokanshi suka bi bayanshi , suna fita suka fara kai daga wasa sai kawai kayi mana haka ? Ai ka sake ganin mai rakoka kayi ƙarya , bai basu ansa ba suka ga ya shiga mota da gudu , ashe Al ' Ameen ya hango ,
Momy data fito dan taga yanayin jikinshi ko ya warware tana ganin Dikko a mota ta hango Al ' Ameen cikin tashin ta nufi wurinshi ta ciro makullin dakel yayin da Dikko yayi tsalle ya tsallake motar dake gefenshi , tace su Yazeed su riƙeshi suna riƙeshi yayi wani irin ihu yace saina kashe shi , ya watse su gaba ɗayansu suka faɗi ƙasa , cikin ruɗewa Momy tace ku rufamin asiri ku riƙoshi , da gudu suka tashi suka bi Dikko yana wata irin zabura ,
Momy kuwa fashewa tayi da kuka tare da cewa ya Allah kayimin sakayya tsakanina da duk wanda keda sa hannu acikin lalurar Dikko , an maidamin ɗa mahaukacin ƙarfi da yaji , wani irin ihu Dikko keyi yana wani irin gurnani mai tada hankali dasu Yazeed sun riƙeshi saidai ya ɓaresu yana wata jijjiga , yayin da Al ' Ameen ya haye saman wani ƙaton tanki yana fitsarin tsoro , dakel aka kai Dikko ƙasa da taimakon duk wani maiji da ƙarfi dake gidan , cikin kuka Dikko ya ɗaga ido dakel ya kalli Al ' Ameen a hankali idanuwanshi suka rufe Momy tasa aka dawo dashi ɗaki....
Sai 1:30am su Yazeed suka tafi amma har yanzu Dikko bai dawo ba , momy tasha kuka kamar ranta zai fita wasu matan basu da adalci ita ba ita taba kanta Dikko ba Allah ya bata shi dan kawai an nemi namiji a gida ba'a samu ba ita ta aifa sai kawai a hana yaro ya zauna lafiya , tou wallahi bata yafe ba kuma bazata yafe ba duk wanda yayi ma Dikko wannan abun ubangiji ya saka mishi Allah kuma ya bashi lafiya duk da dai tasan yana da baƙar zuciya da rashin ɗaukar iskanci abun yayi yawa , shikenan da rai ya ɓaci sai kawai mutum ya riƙa ɗaukewa kamar wutar nepa , ai kowa yanajin fushi kuma kowa yanayin zuciya su duk masuyi me yasa basa suma sai Dikko so kawai akeyi ɗanta ya mutu kuma insha Allah Dikko bazai mutu yanzu ba...
Bayan ta gama kokenta ta kira mutanen da suka kama Bello tace suyi mishi dukan leƙa lahira ya dawo kuma su faɗa mishi idan ya fita ya nemi dafa'in zaman aure ɗiyarshi ta zauna karta fito daga miji idan kuwa ba haka ba to wallahi aka sake mamoshi na gobe saiya fishi jin daɗi...
19/10/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 59
Uhum wai ashe duk abin nan inna tana cikin garin katsina ita da iyayenta "yan gayu dasu sun wani shige cikin ƙaton gidansu sunayin farin ciki basu da wata damuwa abun su a cikin ɓarkeken gidansu dake cikin anguwar layout , yanzu Inna suna da wannan gidan wace ƙaddara taja mata auren Babana taja mukaje mukayi ta rayuwar cin ƙanzo da garin kwaki , wannan irin ƙaton gida an ƙawatashi da ciyayi ga ma'aikata an baza ta ko ina , amma dan mugunta suka bar Inna tayi rayuwa a gidan haya ina ma amfanin arziƙin da baka samma wanin ka.....
Ashiru da kanshi ya shigar min da kayana har cikin ƙaton palon gidan da aka ƙayatashi da wasu irin azababbin kujeru masu kyau da tsada tayils in palon yasha guga duk dare ne sai ɗaukar ido yakeyi tvn bango da sifiku umm amma yanayin palon ya nuna tsohuwa ce ke rayuwa a gidan , wuri Ashiru ya samu ya ajiyemin jakata ya zauna gefen jakar...!
Nima rakuɓewa nayi ina tunanin Dikko Allah yasa karya tafi yabar katsina tsakanin layout da goruba road ai ba wani tashin hankali bane kawai sai in riƙa zuwa ina yini wurinshi in dawo nan in kwana ! Murmushi nayi cikin yanayin jin kunya na rufe idanuwana tare da kwantar da kaina gefe ina tunanin yadda na kasance a jikin Dikko ,
Hannunshi mai laushi baya da wata wahala a cikinshi kamar ba'a amfani dashi , ƙara sinsina jikina nayi turaren Dikko a jikina kamar nice na shafashi , murmushi na sakeyi ina ƙara tunano yadda ya kamani dakel a jikinshi ya rungumeni , ajiyar zuciyarshi dana tuno itace tasa naji tsikar jikina ta mimmiƙe gaskiya Dikko yayi ya gama haɗuwa tako ina , ga aji ga natsuwa ga kyau ga wayewa ga gayu sai maganarshi mai sa mutum cikin halin tunani babu dare ba rana...
Maganar Ashiru ta dawo dani daga duniyar tunanin dana lula , buɗe idona nayi naga wata dattijuwa mai cikar kyawu da asali kame a saman kujera tasha lulluɓi da gyale mai kyau kanta babu kallabi ta ɗora gyalen a saman kanta ta fiddo kunnuwata waje kodan ta nunawa mutane tasa "yan kunne zinari oho , kila kuma nata ra'ayin ne haka...
Gaisheta nayi yayin da nakeji dama ahalin Babana ne dan duk cikar arziƙi ko asali na uwa tou wallahi na uba ne a sama dan uba dashi ake tunƙaho shine ado ga kowa ɗa , duk cikar arziƙi irin na mutum da duk wani mulki ko sarauta da yake taƙama dashi da bazar uba yake taƙama , da zaran ka rasa ahalin Baba na gari tou ka zama sai a hankali , cikin sakin fuska ta ansa gaisuwa daga nan na kama bakina nayi shiru sukaci gaba da fira da Ashiru , a cikin firarsu ne naji tana cewa wai inna ta tana Dubai kunji fa.....
Sun daɗe suna fira da Ashiru kuma har sukayi suka gama ban saka musu baki ba , da Ashiru ya tashi tafiya saida na rakashi har mota ina cewa ya gaishemin da Dikko sosai kuma yace masa idan na kirashi waya ya ɗauka zanyi magana dashi yace insha Allah , saida ya tafi sannan na dawo ciki ,
Lokacin dana dawo har an shigar da kayana ciki , tsohuwar da nake tunanin itace kakata tayi min jagora zuwa ɗakin da zan zauna tana ta jana da fira cikin soyayya amma ni wallahi banajin maganar kowa saita Dikko domin duk ilahirin hankalina da tunani na yana wurin tunanin shi , abinda yafi tsayamin a rai kawai rungumar da yayi min da kuma fitar sautin ajiyar zuciyarshi...
Gajiya tayi da surutu ta fita dan dai Sultana bata ita take ba , tana fita na shiga toilet nayi alwallah nazo nayi sallah bayan na gama kawomin abinci akayi naci ina gama cin abinci na soke saman gado na fara kiran wayar mai gida Dikko......!
Na kirashi bansan so adadi ba amma bai ɗauka ba , tun inayi daga kwance har na tashi zaune haka kira zai shiga yaje ya dawo Dikko baya ɗauka , faɗuwa gabana yayi shikenan ƙarshe kawai zai kashe wayarshi ne daga nan sai ya manta dani , bansan yadda akayi ba kawai naji hawaye na gangaromin daga cikin idanuwana saida nasha kuka har na gode Allah bansan sadda bacci ya ɗaukeni ba na kwanta da tunanin Dikko a zuciyata ,
Yauma horon safe akayi ma Bello yaci ubanshi cikin farashi mai tsada , yayi kuka harya gode Allah , bayan an mishi kashedi akan karya kuskura ya bari auren Sultana ya mutu saida suka haɗa mishi jini da majina sannan suka sallameshi , yana fitowa ya faɗi a wurin da taimakon wasu tsirarun mutane suka ɗauki banza suka wuce dashi asibiti suna zuwa gado aka bashi dan lalubo mishi sauran rayuwa.
Dikko kuwa sai asuba ya farko kuma da ihun saiya kashe Al ' Ameen ya dawo , dakel Momy ta rarrashi Dikko akan ya fita hanyar Al ' Ameen cikin gamsuwa yace mata ya barshi bazai mishi komai ba , Momy ta ƙara da cewa dan Allah uban masu gida kar na sake jin wani maganar kisa ya fita daga bakinka kar kuma ka sake ka dakeshi , jinjina kanshi yayi alamar bazaiyi ba ya ƙare ajiye kan da murmushi ,
Momy da kanta ta rakashi ɗakinshi , acan yayi wanka ya canja kaya ya fita masallaci , daga masallaci gidanshi ya wuce ko Jiddah bata san ya shigo ba kai tsaye ɗakinshi ya wuce dan har yanzu gajiya ke murzar mishi jiki .
Tunda nayi sallah asuba naci gaba da kiran wayar Dikko amma sam bai ɗauka ba , ganin baya ɗauka na haƙura na kwanta bacci tunda na kwanta kamar jaka ko motsowa banyi ba sai bayan azahar , dan nima ina tattare da nau'en gajiya , akwai gajiyan gudu da jifar dasu Al ' Ameen suka min , dukan da Dikko yayi min sai gajiyan hawa doki...
Ina tashi da wayata na fara na duba ko Dikko ya kira babu miss call inshi , saida na sake kiranshi bai ɗauka ba ni kuma nayi alƙawari daga nan har a busa ƙaho idan ba shine ya kira ba bazan sake kiranshi ba.
Yinin ranar yau dai har dare Dikko bai kirani ba kuma nima na basar da lamarinshi , da daddare kuma kaka ta haɗani da gyatima mukayi waya wai nace Inna ni zata dake ma kashedi kar na sake ce mata Inna , nace gwaggo zance miki ko me ? Dariya tayi tare da canja maganar da wata fira ta daban , mun daɗe sosai muna waya da ita cikin farin ciki daga baya mukayi sallama na maida ma kaka wayarta danni dama ban wani san wannan kakar ba gaskiya sai a hoto nake ganinta dan Babana baya bari ina zuwa ko ina kuma duk inda zanje tare muke tafiya dan abinda na fahimta a can baya akwai "yar tsama data faru tsakanin Inna da iyayenta da kuma Babana ɗan uwan Inna ɗaya kawai na sani shima saboda yana mana hidima ne lokacin muna tare da Inna a gidan Baba !
Bayan nayi sallah isha'e ina shirin kwanciya mai aikin Kaka ta shigo wai nayi baƙo a waje , cikin farin ciki na tashi na ƙara gyarawa na fesa turare gyale na ɗauka da sauri na fita ,
Ina fitowa motar Yazeed na gani parke a wurin da aka tanada dan ajiye motoci , cikin farin ciki na isa wurin dan a tunani na shida Dikko ne kuma jiya da zan taho Yazeed yace min zaizo jibi , kenan sai gobe ne ranar da zaizo , cike da farin ciki na isa jikin motar ina zuwa Yazeed ya buɗe motar ya fiddo ƙafarshi ɗaya waje yana kallona cikin yanayin farin ciki ,
Gaishe shi nayi ina leƙa cikin motar ko zanga Dikko , murmushi yayi irin na wayayyin maza yace An mata ni bada DK nazo , me yasa baku zo tare ba ne ? Nima bansan zanzo ba kawai hanya ya kawoni nace bara in biyo miki da mamaki kafin zanzo gobe , a yatsine nace kazo yau gobe ka dawo ? Yace Eyy mana jibi ma zanzo kullum zanyi ta zuwa har sai bana nan ne kaɗai bazan zo ba.....!
Kallon rainin hankali nayi mishi nace to meye nasabar hakan ? Kula mana , meye halaƙar ka ta san kula dani ? Neman kusanci ! Ta wane dalili kusanci zai ƙullu tsakanin namiji da mace ? Abokanta ka , ai babu abota tsakanin mace da namiji , murmushi yayi tare kauda maganar ta hanyar cewa tou ya kike ya gajiyar kuka da hawan doki ? Ya ƙarasa maganar yanamin kallon ƙarƙashin ido....
Lafiya qalau na faɗa a ƙagare , fitowa yayi daga cikin motar ya jera dani , ja baya nayi sannan na juya mishi baya , murmushi yayi tare da cewa haba An mata miye kikeyi haka ? Babu kyau kinsan yana daga cikin ɗabi'u masu kyau martaba baƙo irin wannan tarbar zakimin haba An mata yadda ya ƙarasa faɗar An matar sai naji kamar maganar Dikko , ba tare dana juyo ba nace yi haƙuri bacci nakeji ne ,
Iyya yi haƙuri na tuna kinayin bacci da wuri to zan tafi zanzo goben fa , Allah ya kaimu ina faɗin haka nayi gaba abuna , da gudu na isa ɗakina cikin ɓacin rai ina shiga wayata na duba dan ganin ko Dikko ya kirani , ya kuwa kira amma miss call ɗaya ne , shine duk kiran da nayi masa bai ɗauka ba ni zaima wannan miss call ɗin ɗaya dan ya maidani bansan abinda nakeyi ba ? Tsoki nayi tare da kiran wayarshi dan da bai kirani ba nayi alƙawari bazan sake nemanshi har abadan abada.
Saida kiran ya kusa ƙarewa ya ɗauka , cikin disashshiyar murya kamar wanda mura ya kama yace An matana ya kike ? Ban ansa ba nace me ya sameka muryarka wata iri , gyaran murya yayi irin dandai maganar ta tafi dai² yace babu daɗi ko ? Murmushi nayi tare da kwanciya saman gado nace da daɗi mana , yace wallahi muryar shaƙewa tayi bansan abinda yasa ba kinga kuma ni bana huɗɗa da abu mai sanyi da sai ince mura ya kamani , sannu nace masa yace yawwa yaci gaba da cewa wallahi wayar a mota na barshi sai yanzu dana fita naga tulin miss calls kuma ke na fara kira An mata... Yayi maganar a sakace,
Murmushi nayi cikin yanayin jin daɗin yadda yayi maganar nace tou amma yanzu ka fasa tafiya ko ? Yace zanyi tafi amma sai wani satin banajin daɗi ne duk jikina ciwo yakemin , ni kuma nace ciwon tunani nakeyi , murmushi Dikko yayi tare da cewa Allah ya baki lafiya saida safe... Yana faɗin haka ya tsinke kiran,
Cikin jin haushi na sake kiranshi amma yaƙi ɗauka , ni bansan abinda yasa yakemin irin wannan abun ba , ko wurina yazo baya so ya daɗe , idan inayin waya dashi a ƙagare yake ya barni anya Dikko zai soni kamar yadda nake sansa ......?
Murmushi yayi bayan ya tsinke kiran yace An mata kenan itafa nan a wayan ta so take ta ganni amma bazata iya faɗa inzo ba sai ta fake wai tana ciwon tunani tou ai sai kisha magani ko kin samu sauƙi.....
Daga G R A kai tsaye tsohuwar anguwar su Sultana ya taho inda gidan da yake kiwon dawakai yake , tunda ya shigo anguwar ya ganta cike da taron jama'a maza da mata kuma duk wadda ka gani kasan cikakken ɗan iska ne maza "yan daudu mata karuwai duk wacce ta ansa sunanta tanaji ita wata shegiya ce a cikin iskanci ta hallara a wurin gaba ɗaya anguwar ta karaɗe da kiɗa ko wane ɗan iska da iyayenshi suka ce jeka ka gani su Amisty sun hallarar dashi a wurin ,
Da gudun bala'e ya shiga cikin santar saboda tsabar gudu motarshi har wani tsalle takeyi , kamar fari haka mutane suka riƙa tashi da gudu dan keɓe rayuwarsu daga faɗawa mummunar rayuwa , a ƙofar gida yayi parking ya fita ya shiga ciki rai a haɗe , shigarshi hayani ta fara tashi kowa dai da abinda yake faɗa akanshi ,
Bayan ya gama abinda yakeyi zai fito Umar ya biyo bayanshi yake cewa mai gida yau kaga anguwar namu cike ? Banza Dikko yayi dashi bai bashi ansa ba shi kuma yaci gaba da cewa wata karuwa ce take ajo na cika shekaru biyu da fara barikinta sai kuma shagalin samun "yan cin kai na zaman kanta watanni bakwai , Dikko dai baiyi magana ba yana fitowa ya shiga motarshi ya fice da ribos har ƙarshen santar yana kaiwa titi ya juya sitiyarin motar shi ya wuce inda suke majalisarsu , Hafsa kuma tabi bayanshi ,
Umar kuma mamaki yakeyi ko akwai abinda yake damun Dikko duk dai haka yake amma kamar wani abu ya taɓashi , ko wani abu ya ɓata mishi rai idan an gaishe shi zaice yawwa , ko lfy ko da kyau ko yayi amma yau duk wanda ya gaishe a gidan nan bai ansa gaisuwar kowa ba kuma baiyi magana da kowa ba har ya shigo ya fita...
Har yanzu ban daina kiran wayar Dikko ba , duk kiran daya shigo wayarshi na Sultana yana kallo saida yazo goruba gidanshi sannan ya ɗauki wayar cikin tsananin ɓacin rai da hayani yace wai me ye ne............? Ni bana san maita sai kirana kikeyi kin dameni bansan masifa da kwakwa da Allah mayya kawai , cikin tashin hankali na tashi zaune tare da sake kallon lambar wani abu naji yazo ya tokare min a zuciya nace Dikko nice mayya....? Eyyy kece nace mayya ko ba mayyar bace , nima kamar an sakani cikin ɓacin rai nace kaine maye marar tunani wanda baka san ina duniya ya nufa ba , kamar ƙaramin yaro haka Dikko ya biyemin mukai ta zage² duk abinda yace min saina rama ,
Daga ƙarshe ya zageni tass da turanci , cikin kuka nace Dikko An mata ce fa , tsoki yayi ya kashe wayarshi , wayyo Allahna meke faruwa haka ? Yanzu na gama waya da Dikko lafiya qalau sai kuma in sake kiranshi ya zageni me yayi zafi haka don Allah ? Wayyo Allahna , da sauri na kalli agogo 9:24pm zuciyata kamar zata tsage saboda tashin hankali idona kuwa banda aman hawaye babu abinda yakeyi , da gudu na fito har bakin get , wanda nake tunanin shine driver naje gabanshi a rikice na fara magana cikin rawar baki nace da Allah ka kaini goruba road taimakeni don girman Allah na ƙarasa maganar ina jan hannunshi....
Lafiya ya tambaye ni ? Babu lafiya muje don Allah zan baka kuɗi idan muka dawo yanzu zamu je mu dawo yi sauri don Allah na ƙarasa maganar ina goge hawaye idona , muje ya faɗa yayi gaba nabi bayanshi ,
Ko a mota a gaba na kasance ina ce masa yayi sauri , sauri ׳ malam driver , gudu yakeyi sosai amma kayi sauri kawai nake cewa har muka isa goruba road , a harabar gidan na haɗu da Hafsa Dikko ya bata kashin bala'e ana ta riƙonshi ya haukace gaba ɗaya , cikin tausawa na kalli "yar uwata dake duƙe tana kuka Dikko sai ruwan rashin mutunci yakeyi ana bashi haƙuri kamar ana ƙara tunzurashi yana sai ya tattaka ta ,
Wurin Hafsa naje na kamata na miƙar da ita ina bata haƙuri tare da tambayarta meya faru ? Kallona tayi amma bata ce wani abu ba sai kuka takeyi , sakinta nayi zanyi wurin Dikko aka tareni cike da iskanci yake cewa kizo ku barta tazo yayi maganar yana kirawoni da kanshi , turesu nayi na tunkari Dikko kai tsaye ina isa ya yankamin wani irin mari saida na wurwura kamar ranfa na dawo gaban Hafsa ko gabana bana gani sai duhu , kafin in dawo hayyacina na sake komawa inda nakejin sautin muryar Dikko dan kawai ji nake gara in mutu da masifar da zan fuskanta a gaba dan rabuwa ta da Dikko a halin yanzu na dangana abun kawai da mutuwa ta ,
Riƙeni akayi cikin ihu nace ku sakeni saiya kasheni , ka kasheni Dikko kasheni bana so ka barni da raina gani na matsa gabanshi ina kuka , da ƙafarshi yayi min wani irin halbi saida aka ɗagani sama sannan na faɗo ƙasa ruf da ciki , da sauri na sake tashi cikin kuka na sake tafiya wurin Dikko wani irin tsalle yayi ya ɗaga hannunshi sama rigarshi ta ɗage har kana gani cibiyarshi yace idan taurin kaine ɗabi'arki nine kangara zai kaimin duka saman kai Yazeed ya riƙeshi birkicewa Dikko yayi yana saina kasheta , andaiyi tashin hankali sosai munyi zage² da Dikko abun dai babu daɗi dakel Yazeed ya sani mota muka dawo gida can na baro Hafsa kuma bansan abinda ya haɗata da Dikko ba kuma babu wanda yasan abinda ya jawoma Dikko wannan haukar ba,
Sultana tana tafiya Dikko yace zancen banza zance wofi yau duk wani mai tsohon laifi a wurina an famomin ciwon dana daɗe ina raino a cikin zuciyata saura waccan ɗayan ɗan iska yau duk wanda ya hawoni saina lalata mishi rayuwa , yana faɗin haka ya shiga mota ya nufi gidansu ,
Yau duk wanda yaga Dikko lafewa yakeyi saboda tsoro , wurin mahaifiyar shi ya fara shiga itama da yanayin tsorata ta kalli Dikko tace kai lafiya kuma ? Banda lafiya kuma yau duk wanda yayi gigin shigomin rayuwa ko waye saina mishi babu daɗi ba ruwanki yau saina kashe Al ' Ameen a gidan nan kar wani yayi gigin taɓani ko zuwa kusa dani idan ba haka ba yau zan tara majiyyata da yawa a gidan nan , Dikko badai zaka barni na zauna lafiya ba ko ? Cikin hayani yace da ko wane daƙiƙi na rayuwata shi nake jira yau bana iya bacci saina kasheshi yana faɗin haka yayi waje.....
A tsorace Momy tabi bayan Dikko amma lokacin data fito ko sahun ƙafarshi babu tuni ya ɓace , tsayuwa tayi tana tunanin mafita taji gaba ɗaya gidan ya gauraye da hayani da sauri ta nufi inda take jiyo hananiyar tana zuwa Dikko ta gani shaƙe da wuyan Al ' Ameen ya riƙeshi duk wanda ya matso wurinshi halbi ɗaya yake mishi sai mutum yayi sama ya dawo ƙasa somamme...
Ƙatti majiya ƙarfi sunfi nawa amma sun zagaye Dikko an kasa samun wani da zai sake matsawa kusa dashi , cikin ɓacin rai Dikko yace har so nawa zan faɗa bana san wani ya sake zuwa kusa dani idan akwai mai sha'awar jinya ko mutuwa yazo..... Ya faɗi maganar a dai² lokacin daya ɗaga Al ' Ameen sama ya dakashi da ƙasa , Momy tace ku riƙe minshi mana , wani yabi ta bayanshi dan ya kamashi amma yana isa Dikko ya halbeshi ta baya shima saida yayi sama ya dawo some , cikin ɓacin rai yace har sau nawa zan faɗa bana so azo kusa dani kuci gaba da shigowa duk saina ƙarar daku a dai² lokacin da yayi wani irin tsalle ya dira akan ruwan cikin Al ' Ameen dako motsi bayayi yace zaka fita harkata ne ko zakaci gaba da shiga ? Kun hanani na zauna lafiya yayi maganar yana ɗaukar Al ' Ameen kamar ya ɗauki kaza yayi jifa dashi jikin wani ƙarfen fitila , yanayin jifa dashi gaba ɗaya suka rufa kanshi dan su riƙe shi , wani irin ihu yayi kai...... Wayyo wai...... Yaci gaba da dukansu babu ji babu gani duk wanda ya hawo saida Dikko ya kwantar dashi yau kam saida ya tsamama ma duk wanda ya hawo layin shi jiki ya kama gabanshi.....
Goruba road ya koma a daren yana neman wayarshi , kowa ce masa yake baya kyautawa abinda yake yi , baima kowa magana ba yace ina wayarshi , cikin girmamawa Ashiru yace gata mai gida , cikin ɓacin rai yace kiramin An mata , kallonshi Yazeed yayi yace "Yar matan daka wulaƙanta kake tunanin zaka kirata ta ɗauka , ai saboda wannan lalurar yasa na sakata a tarko , Yazeed yace dan kayi ta zalincin ta kana ɗaukar alhakinta ka ɓata rai kayi ta rashin mutunci warware hannun rigarshi yakeyi yana cewa dole sai tasan fushina kuma ta riƙa kiyayeshi na faɗa mata idan nayi fushi bani ne ba , ɓatamin rai tayi data kama hanya ta taho kuma nace bana so tana yawo ita sarkin soyayya dan nace mata mayya taji haushi tayimin zagin rashin mutinci.
Wani ne yace to kai me yasa kace mata mayyar ne ? Raina ne ya ɓaci a dai² lokacin da fushi ya hau kaina ita kuma taita kirana dana ɗauka na sauke fushin a kanta , tunda har zan zama mijinta dole ta koyi ansar laifin da ba nata ba , domin da zaran nayi fushi tofa ko kaina bana saurara.....
Tambayar shi suka sakeyi meya ɓata mishi rai haka da yawa har ya daki Sultana da yake iƙirarin ko wani ya taɓata saiya rama mata , cike da damuwa Dikko yace karuwai ne na gani ƙanan yara wanda shekarunsu bai dace da karuwanci ba "yan kuci²n yara wai su nan har sun giga sun tafasa har sun ƙone sun bushe fitilar idonsu wai sunsan daɗin maza , sun gagari iyayensu abin ne ya tadamin hankali , bansan masifar dake damun mutanen wannan zamani ba , wallahi wata "yar ƙaramar yarinya na gani sai kuma yayi shiru hawaye ya cika mishi ido a dai² lokancin da Ashiru ya miƙo mishi waya Sultana ta ɗauka , An mata miye kike kuka kina tunanin zan iya fushi dake ? Cikin kuka nace shine ka zageni kace min mayya kuma ka dakeni , haba An mata ki riƙa min uzuri don Allah ai kinsa bada gangan na faɗa ba fushi ne , tou nidai kazo in ganka , kallon agogo yayi yace dare yayi ki bari da safe zanzo , nidai kazo yanzu , cikin sansanyar muryarshi yace gani nan zuwa....
Gaba ɗaya kowa yace sai yaje yaga yadda za'a ƙare , yayin da wani yake cewa Allah yasa itama tasa ayi maka shegen duka , murmushi Dikko yayi a dai² lokacin da suka fito daga palon yace An mata bata iya fushi dani har abadan duniya domin wannan lalurar ne yasa na sanya mata maitata a zuciyarta , babban muradin ta a yanzu na aureta kaga idan na aureta ta zama tawa , idan har na auri An mata ba maganar yaji dan babu inda zata iya tafiya tabar Dikko muyi faɗa mu shirya danma tana da ƙananan shekaru har yanzu ta kasa kullema 20 , motoci suka shiga suka nufi gidansu Sultana...
11:52pm a gidan Kaka tayi ma su Dikko kuma duka ciki suka shigo da motocinsu , ba waya yayimin yazo ba kukan motarshi kawai naji nayo waje , saida na gaishe da duk abokanshi na shiga mota yana baya zaune ina shiga Ashiru ya fita , fashewa nayi da kuka na rungume Dikko cikin kuka nace shine kacemin mayya ? Yace ai mayyar ce ko ke ba mayyar Dikko bace ba , nima ai mayenki ne kuma ba kin rama ba , to ai har zagina kayi da turanci , murmushi Dikko yayi da gefen bakinshi yace ni wallahi ba zaginki nayi ba , iyakar mayya dana ce ban wani ɓoye da wani harshe na aibataki ba , gaki kin fara zama jajirtacciya soyayyata ta hana ki gano matsalata , haka zakiyi ta haƙuri dani An mata har Allah ya bani lafiya kinji , ya ƙarasa maganar cikin sigar lallashi. Nace to me kacemin da turanci ? Saida yayi dariya yace cewa nayi "yar ƙaramar yarinya kin hanani zaman lafiya , duk wannan doguwar maganar a "yar wannan kalmar ya tsaya ? Ajiyar zuciya ya sauke baiyi magana ba ,
Shashshekar kuka nayi tare da cewa tou me nayi maka haka da ciwo don Allah , riƙeni yayi da hannunshi na haggu har yanzu ina kwance a jikinshi shi kuma ya kwantar da fuskarshi a saman kaina ya fara magana cikin sanyinshi , yace An mata taron karuwai na gani abun ya gigitani wata "yar ƙaramar yarinya ba zata wuce shekarunki ba kinsan abinda na gani anayi da ita , shiru nayi ba tare dana bashi amsa ba , cikin kuka Dikko yace to maza ke layi akan yarinyar yadda kika san ana ɗaukar mutum a abun hawa a anshi kuɗi haka maza ke hawan yarinyar suna sauka suna bata kuɗi , ɗimuwar rayuwa ta sameni duk taron mutanen da aka tara An mata batajin kunya wai ta keɓe gefe ɗaya tayi ma maza masauki a jikinta , mata basu san illar namiji ba duk mayatar mace da masifar maitar namiji bata iya kashe namiji 2 a bariki , namiji kuwa sai ya kashe mace sama da goma yana nan zamzam , rayuwar mace taƙaitacciya ce amma rashin tunani ya hana su gane haka tunda na shiga anguwar da wanda ke gefe na da wanda ke gabana da duk wanda yake bayana zan iya baki labari , kallo ɗaya zanma abu na gama dashi yanayin mutum na kalla zan iya faɗa miki komai akanshi,
Ni mamaki ma nayi duk wa'an nan "yan iska ina ita wacce ta tarasu ta samo su ? Wai ke kinga taron ? Ya ubangiji ka tsare mana imaninmu ka shirya bayinka daga faɗawa tarkon zina , ina cikin jimami ke kuma kin dameni da kira a lokaci ni kuma ina so na samu natsuwa na kiraki ke kuma kin gagara daina kirana ne ina cikin tashi hankali bana so ban ɗauka kiranki ba kuma kiji babu daɗi ina magana dake raina ya ɓaci nayi ta faɗar maganganu babu daɗi , ita kuma wannan yarinya ta wani kama hanya ta biyoni bayan itama na ganta maza sai rumgumarta suke ,
Ai banma san na cire belt na zaneta ba ina cikin wani fushin ke kuma kika zo , ƙara riƙeni yayi sosai a jikinshi hawayenshi ya ɗigo a saman wuyana ya sassauta murya yace dan Allah An mata idan kika kirani ban ɗauka ba ki daina zuwa wurina kuma ki daina kiyi ta kirana idan kin kira sau ɗaya ban ɗauka ba kinji ko ? Nace tou haƙuri ya bani saida ya tabbatar na samu natsuwa ya gogemin hawayen fuskarta nima ya umarceni da in goge mishi nashi da hannushi yayi min nuni goge mishi nayi tare da shafa gemunshi najashi dan yana burgeni , murmushi yayi mai kyau tare da gogamin gemun a fuskata , a kasanlance na sake komawa jikinshi na kwanta , dariya yayi cewa jeki zanzo gobe insha Allah , dakel na iya fita daga cikin motar na wuce ciki kamar wacce bata da lakka a jikinta , cike da tausayin Sultana su Dikko suka bar gidan....
Bayan Dikko ya gama ci musu uwa motarshi ya hau yai tafiyarshi , haka akayi ta ibar mutane ana tafiya dasu asibiti , Momy bata faɗawa Dady ba amma dan sharrin mata aka samu wacce ta sulalewa Dady waya ta fesa mishi komai , shima daya tashi bai kira Momy ba ya kira Dikko bayan sun gaisa yace Babana duk abinda kakeyi ka barshi zuwa jibi ka sameni , wato kaga bana nan shine kake duk abinda kaga dama ko ? Na taho ganin likita ban dai tsira ba saidai ka kasheni hankalin ka zai kwanta ? To ka taho ka sameni zuwa jibi na baka yana faɗin haka ya kashe wayarshi.
Tunda na shigo ɗakina nake tunanin wannan wace yarinya ce ? Bansan mutanen su Hafsa ba amma naji a raina inasan sanin yarinyar da Dikko yayi ma kuka saboda tausayin ta , kuma inasan nasan dalilinta na shiga karuwanci , Dikko yana da tausayi amma baida mutunci ko kaɗan da wannan tausayin nashi Allah ya kamamin zuciyarshi akan abinda yayi min a baya , tabbas ina san sanin ya rayuwarsu Amisty take yanzu , ina san sanin a wane hali Ummu Affan take matar auren da nayi silar zuwanta bariki , ina san sanin abinda yasa matar Baban Babana ta korasu daga gidan mahaifinsu , ina san sanin labarin Aunty Suwaiba , ina san karatu kuma ina san Dikko sannan ina san sanin abinda ya kashe matarshi ko da gaske tsafetan yayi ?.... Kuma gaba ɗaya sai nayi babu wanda zan fasa a ciki !
Sai kuma rashin lafiyar Dikko da abinda yake sashi cusa ɓacin rai a cikin farin ciki wani , tabbas saiya faɗamin meya jawo mishi wannan lalurar da fushin wani yake shafar wani...
Asibiti mai kyau aka kai su Al ' Ameen duk wanda Dikko ya daka babu wanda baima rauni ba , ya gota wasu ya karya wasu Al ' Ameen duk yafi kowa shan wahala dan har safiyar yau bai dawo ba , amma likitoci suna ta bakin ƙoƙarinsu wurin ceto rayuwarshi...
Duk azabar dake damun Bello bata barshi ya zauna a asibiti ba guduwa yayi domin ya kudiri ganin bayan Sultana , dan haka yabar asibiti ya koma gida ,
Da sauri ya fito daga toilet yasha wanka a gaggauce ya saka kayanshi bayan ya shafa mai ya wanke jikinshi da ruwan turaruka dan yanzu yake so ya wuce akwai abinda zaiyi Abuja kafin yabar nigeria , cike da kissa ta shigo ɗauke da kofi ta haɗoma Dikko tea data barbaɗeshi da garin maganin da Al ' Ameen ya kawo mata , cike da kwarkwarewa tace my excellency kasha wannan kafin ka tafi , da sauri ya ansa ya ajiye a saman madubi yana ɗaura agogo bayan ya gama ya saka takalminshi wurin ɗaukar wayarshi kofin ya biyoshi ya faɗo ƙasa ya watse , cikin kyarmar jiki Jiddah ta dafa goshi tace bara in kawo maka wani , kallo ɗaya Dikko yayi mata yai murmushi yace haka nake ni da zaran gishiri yayi yawa abunsha ko abinci ɓarewa yakeyi haka rayuwata take tunda safe kina so ki ɗuramin masifa babu gaira babu dalili , yana faɗin haka yayi gaba ,
Ko wurin Sultana bai biya ba kuma bai kirata ba haka kuma baije gidansu ba danyi ma Momy sallama suka kama hanya daga shi sai Ashiru...
Bayan la'asar Yazeed yazo ciki muka shiga suka gaisa da Kaka aka kawo mishi ɗan abun taɓawa bai taɓa komai ba muka shiga firar duniya , ya daɗe sai gab magrib ya tafi bayan na faɗa mishi zanje daura gobe idan Allah ya kaimu yace zaizo ya akaini , yayi hauka da kuɗi wa duk wani ma'aikaci dake gidan itama Kaka ya bata kuɗi masu yawan gaske , ni kuma wasu irin jikkuna yasa aka shigo min dasu masu ɗauke da kaya iri daban ² kuma nima ya bani kuɗi gaba ɗaya ma'aikatan gidan maganar Yazeed sukeyi da irin kuɗin daya bada , tou wai me hakan yake nufi........?
20/10/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 60
Ɗan bubbuɗawa nayi na lalleƙa gaskiya Yazeed baida hankali wannan irin haukan duk me ya jawoshi ? Duk abinda ya shafi na sakawa a jiki babu abinda Yazeed bai sako ba , turaruka mayuka gyaluluwa takalmi jikkuna materials masu kyau da tsada lessess shaddoji masu tsada atamfofi ƙarshen iskanci hada breziya da fants ondy da sabuwar waya cikin kwalinta mai tambarin apple a bayanta , nima dai ya zubo kuɗi wanda saida suka bani tsoro ,
Salati nayi naja baya da sauri banma sake gigin ko kallon inda kayan suke ba bare na sake tunanin taɓasu , ɗakin Kaka na nufa na samu tana waya da Inna wuri na samu na zauna cike da mamaki , ina zama tace ga Maryam nan ta faɗi maganar tare da miƙomin wayar ,
Ansar wayar nayi tare da kallon Kaka ita tana san lulluɓi bata san ɗaura kallabi sai a wani fiddo kunne waje kome hakan yake nufi oho , Hajiya Inna haka na faɗa a dai² lokacin dana kara wayar a kunne na , ya kike ? Lafiya qalau wai yaushe zaki dawo ? Idan na dawo me zan miki ne ? Haba kema da Allah ki dawo Inna , zan dawo ai bai gama abinda yakeyi ba , waye ? Mijina mana , cikin in ina nace Inna miji......? Ey mana yanzu aure kikayi saboda Allah ? To kar inyi ? Wani irin kishin Babana naji ya kamani nace kawai sai kikayi aure haba Inna ke me zakiyi da aure da Allah ? Dariya tayi sosai naji tana cewa Sultana ce ,
Sultana zaku gaisa da Alhaji , nace ki gaishe shi sallah zanyi , ina faɗin haka na maida ma Kaka wayarta na shige toilet nayo alwallah sallah magrib bayan na fito ɗakina nai tahowa ta , ina shigowa naji wayata na tsuwwa da sauri na isa wurin wayar , murmushi nayi tare da ɗaukar wayar cikin farin ciki,
Na koma saman gado na kwanta cike da shaƙun so zuciyata nata tsumama da soyayyarshi nace hello , ke yarinya me kike nufi ne yau baki kirani ba ko kinyi fushi da nine ? Murmushi nayi tare da ɗan murginawa na lumshe idanuwa na gaskiya ina jin daɗin muryar Dikko tana sakani ciki wani irin yanayi dani kaina bana iya ganewa , nima irin abunda yakemin nayi cewa zanyi sallah idan na gama zan kiraka , tou kimin addu'a , nace me zan roƙar maka , ki roƙarmin Allah yasa miki soyayyarta wadda bata gogewa har abadan duniya , ubangiji yasa nine mijinki , duk wanda baya san aurenmu Allah ya sanyaya masa zuciyarshi shi da kanshi yace Dikko ka auri yarinyar nan kana santa tana sanka ,
Nace zan maka amma ni bazan aure ka ba , murmushi yayi yace ni ko zan aureki in Allah ya yadda kuma inaji a jikina lokaci yana kusa , ai nace bazan aure ka ba , Ey dama ai nine zan aureki bake ba , kinsan Allah ki daina min abinda bashi da kyau idan ba haka idan na aureki duk abinda kikai min saina rama , ka rama idan na aurenka mana...
Haka kika ce ? Nace Ey , aiko yarinya zaki ga ramuwa hada ta gayya kice zaki je gida in koma daga gefe in haɗe rai ince baza ki ba , kice dan Allah...... Wata magana yaso yayi amma ganin nayi masa "yar ƙarama kamar yadda yake faɗa saidai yayi dariya yace An mata Allah dai yasa ke rabona ce , a cikin zuciyata nace amin tare da tsinke kiran....
Wani irin ihun jin daɗi nayi na miƙe saman gado nayi rawa Allah yasa haka mutumina Allah yasa muyi aure , ina sanka ׳.............. Da tsalle na sauko daga saman gado ina rawar jin daɗi , rumgume hannuwana nayi nai juyi An mata.... Wai me yasa kake cemin An mata......? Banda mai bani ansar wannan tambayar....
Murmushi Dikko yayi tare da gyara kwanciyar shi yace An mata kenan kinga irin yarintar taki wai zakimin addu'ar amma baza ki aureni ba , hmm yarinya kenan kinaji da ƙuruciya sosai har yanzu kanki ɗanye ne amma zan dafa miki shi gaki ga Dikko ubangiji yasa nine mijinki am3n ,
Har yanzu Al ' Ameen bai dawo ba , likitoci suna ta bakin ƙoƙarinsu amma shiru kake ji kamar an aiki karuwa ɗakin kwarto , yauma abiyar zaman Momy ta kira Dady ta faɗa mishi har yanzu fa Al ' Ameen babu wani ci gaba sai ƙasa yake ƙarayi kuma Momy ko ganinshi bataje ba , kuma ta sani sarai ɗan ta yayi wannan iskancin tunda a gaban idonta ya doki Al ' Ameen bata ce komai ba tunda daga wurinta ya fito duk yadda akayi ma itace ta tiroshi sai Dikko ya zauna yaita iskanci amma ba'a iya ma yaro magana kamar ɗan ido ,
Tuni nace ka kaishi gidan mahaukata sai kace ɗanka lafiyarshi qalau yanzu mai hankali zaiyi abinda Dikko yayi ? Cikin ɓacin rai Dady yace ni ban haifi mahaukaci ba , lafiyar Babana qalau kuma Maryam babu yadda za'ayi tasa Babana ya daki wani tunda tasan abinda yake damunshi , duk dai abinda mutum yayi shida Allah kuma ba Maryam aka cuta ba ni aka zalinta duk mai sa hannu a lalurar Babana nakai ƙararshi wurin ubangiji kuma sai Allah yayi min hisabi dani dashi wallahi ban yafe ba kuma bazan taɓa yafewa ba , yana kaiwa nan ya tsinke kiran ya fara kiran Dikko.
Gaisawa sukayi bayan ya ɗauka Dady yace Babana har yanzu me kakeyi ne ? Dady ni ina Abuja , tou duk abinda kake ka kasance tare dani idan Allah ya kaimu gobe na faɗa maka , insha Allah , me ya haɗaka da Al ' Ameen kayi mishi duka haka ? Wai bana hanaka wannan doke²n ba ? Badai zaka zauna da rayuwarka lafiya ba ko ? Sai kayi ta abu ana dan ganaka da zararre ,
Cikin kwantar da murya yace Dady kasan bana iya sarrafawa , tsohon laifi ne na daɗe ina ba zuciyata haƙuri jiya ne taji bata iyawa shi yasa haka ya faru , Allah ya kyauta ya baka lafiya , ubangiji ya yaye maka abinda yake damunka , da am3n ya ansa saida Dady yayi mishi nasiha sosai sannan yace kuma karya zo da kowa yazo shi ɗaya yace insha Allah , cike da soyayyar Dikko Dady ya ajiye waya yana mai tausayin ɗanshi da lalurar dake damunshi , gashi cikakken mutum mai cikar zati da ƙwarjini amma saboda haukan kishi na mata an birkita mishi kwalwar ɗa , matsalar dai kawai yayi fushi idan har yayi fushi tofa nan ake samun matsala danma ana ta roƙon Allah , kuma roƙon Allah gaskiya ne baya faɗuwa ƙasa dan ubangiji maji roƙon bayinsa ne....
Dikko yana da mutunci kuma yana da kirki Allah yasa mishi tausayi amma yafi tausayin mata a rayuwarshi , kuma tun kafin matsalar nan ta sameshi bai ɗaukar raini kuma da an taɓoshi sai anji babu daɗi bai iya zuciya ba haka kuma sai laifin wani ya shafe wanda baisan anyi mishi ba , dariyar mugunta dama haka Allah ya halicceshi tun fil'azal baya dariya kuma shi bai cika murmushi ba ,
Koda Dady bai samu namiji ba ya tashi hankali sosai kuma duk matanshi kowa addu'a take Allah yasa itace zata haifo , shi kuma a tunaninshi duk wacce ta haifa duk ɗaya tunda suma "ya "yanshi mata baice baya sansu ba kuma kowa tana da , amma tunda aka haifi Dikko sai wutar kishi taita ruruwa sai jefe² har suke ganin kauda Dikko daga duniya shine kawai kwanciyar hankalinsu , tun yana ƙarami suke asirinsu kuma basu gaji ba daga ƙarshe aka tura mishi aljannu su shanye jininshi ya mutu , yasha wahala sosai babu wanda yayi tunanin zai sake rayuwa amma ubangiji yayi alƙawarin rayayye ne ,
Ganin ba'a samu nasarar hakan ba yasa akayi amfani da fushinshi wurin saka wani fushin idan har yayi zuciya sai ya fita hayyacinshi yayi ta hauka bayaji baya gani ya riƙa kiran saiya kashe sai yabi takan mutum da mota , tou kalmar kisan itace ba'aso yana faɗa idan yana fushi dan idan yace zaiyi kawai sai yayi yake samun natsuwa , to idan yace saina kashe ka daga nan yake tafi sai ya ɗauke wuta ya faɗi , tanan ake neman sa'ar sa ake farautar numfashin shi a haka aljannu ke so suyi nasarar raba gangar jikinshi da ruhinshi su shanye mishi jini ya mutu.... Shi yasa ya faɗawa Sultana idan yayi fushi bashi bane ba ta kiyayi fushin shi saboda baya da kyau , tayi ta haƙuri dashi har Allah ya bashi lafiya !
Ana ta neman taimako dai , wannan magungunan da ake mishi amfani dashi na cikin baki dana shaƙawa abokin Dady ne ya nemosu dan ya tausayawa Dady akan lalurar Dikko saboda Dikko ke ciwon amma Dady ke jinyar bawai jinya ta kula ba , jinyar kar Dikko ya mutu shi yasa duk abokanan shi suka miƙe suka tayashi neman taimako , kuma har yanzu ba'ar nema ba , yanzu haka ma idan Dikko ya samu Dady a inda yake idan ya gama ganin likita zai wuce saudiyya suyi umara tare sai ya dawo dashi inda wani amininshi yace mai maganin yace sai an kawo mishi Dikkon , dan da Dady ya bari saiya dawo amma haukan da yayi jiya yasa Dady yace ya sameshi.
Dikko ganin Sultana bata da niyar kiranshi yasa shi ya kirata , har na fara bacci kiran wayar shi ne ya tashe ni , cikin gigin bacci na ɗauki wayar na gaishe shi da muryar wanda bacci yafi ƙarfin shi , cikin murya mai nuna da fushi yace har yanzu baki gama sallar ba ? Bacci ya riga yafi ƙarfina kawai na kashe wayar banma san na kashe ba , ƙara kira yayi har yanzu bacci bai sakeni ba , dakel na ɗauki wayar na ɗorata a saman kunne nace inajinkan , ni zaki kashe ma waya har kin isa in kiraki ki kashemin waya An mata......?
Da sauri na buɗe idona dan namayi tunani ko a mafarki nake wayar wallahi , yi haƙuri don Allah wallahi na fara bacci ne tsoki yayi tare da kashe wayarshi gaba ɗaya , da sauri nabi bayan kiranshi amma har ya kashe wayarshi akace a kashe take....
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un haba ina amfani halin Dikko dan Allah anyi mutum rayuwarshi babu uziri , kwata² bayamin adalci bayan yasan da kaina ina kiranshi , shi so nawa na kirashi bama ya ɗauka tou idan ka kira kai baka cika Dikko ba , kuma nima har abadan duniya bazan sake kiranka ba da Allah can tsamiyar biri dakai mtsww....
Komawa nayi nai kwanciyata cikin ɓacin rai , shi wannan Dikko baida haƙuri ko kaɗan sai zafin kai shi ɗan zafin zuciya ko an faɗa maka bana iya rabuwa dakai , ko zan ragu ne idan na ɓata dakai duk abokanka ma sunfi ka kirki masu haƙuri kaiko komai fushi duk namiji shi ke sarrafa fushin mace amma kai ƙato dakai saini zanyi ta haƙuri dakai ? To bazanyi haƙurin ba kuma an ɓata babu ranar shiryawa.....
Wuri ɗaya ya ƙurawa ido yana kallo , ajiyar zuciya ya sauke mai tattare da ɓacin rai , murmushin ƙarfin hali yayi a bayyane yace wai Allahna , wai..... Wayyo ya ƙarasa yana mai kwanciya dakel cikin yanayi mai nuni da wahaltuwa ,
lumshe idanuwanshi yayi ya ƙara cewa wai........ Wai Allahna , kukan Sultana ya riƙaji a zuciyarshi idonshi ya cika da hawaye yayin daya tuno yadda yayi da ita a safiyar daya anshi budurcinta ta ƙarfi da yaji ya ɓata mata , gangarowa hawayen yayi daga cikin idonshi saida ya sake wai..... Wayyo har yanzu idonshi a rufe a zuciyarshi yace Allah na tuba ׳ , Allah ka ƙaddara aure na da "yar yarinyar nan ya ubangiji kasa An mata rabona ce duk abinda zanma yarinyar nan nidai nafi so kawai na aureta ta samu natsuwa dani , ya Allah kaji ƙaina ka tabbatar da auren mu , zan nunawa An mata tsantsar soyayya mai tsafta zan gatanta ta kuma zata samu natsuwa daga gareni mai sa natsuwa ,
Ashiru ya kwalawa kira bayan ya samu natsuwa , da sauri ya shigo cikin girmamawa yace mai gida , ran Dikko a haɗe yace wani tunani nayi me kake tunani game da Yazeed da yace zaije zance.....? Cikin girmamawa Ashiru yace mai gida kila wasa yakeyi ,
Murmushi Dikko yayi tare dayin shiru yana nazari , bayan wani lokaci yace tabbas sai yaje wallahi sai yaje wurin An mata , nasan halin Yazeed ciki da waje , yanzu nayi wani tunani idan ka fahimci rayuwarshi ya cika leƙe² aiko idan har ya leƙo An mata saina tada katsina da bala'e ,
Tun bansan meye iskanci ba nakejin kalmar iskanci a bakin Yazeed , idan kayi tunani goruba ba majalissar shi bace tunda yaga An mata ranar dana daketa ya dawo da zama gidan nan , jinjina kai Dikko yayi yaci gaba da cewa lallai akwai abinda zai faru , miƙewa yayi tsaye yace zafa a samu matsala ya ƙarasa maganar yana ma Ashiru wani irin kallo , da sauri yaja da baya yana cewa mai gida haka bazai faru ba ,
Dikko yace abun yakemin yawo a zuciya yace An mata ta cika zama ɗaki kamar mai jego , yawan zama da hijabi kamar mai takaba , ya gajiyan hawa doki ko zaki hau na bankwana , kyautar zobe a maimakon kuɗi kamar yadda sauran sukayi mata , duk haka yana nufin wasa ne.....? Me yasa su sauran basuce haka ba ? Mahaifiyar An mata bata nan tayi tafiya zuwa Dubai ita da mijinta da mukayi waya da ita nace sai ta dawo zan dawo da An mata , abinda yasa na mayar da ita shine ,
Washe garin ranar dana bata kashi su Yazeed su suke riƙeni lokacin dana bigawa An mata kai da bango , tayi ƙara sau ɗaya mai tsananin tayar da hankali , ihunta shine ya jawosu suka shigo ciki da gudu a lokacin ita kuma ta suma....
Gaba ɗayansu sun riƙeni , ni kuma ina zabura cewa saina kasheta , kowa haƙuri yake bani hankalin kowa yana kaina amma idon Yazeed yana saman An mata , abinda tayi min suka fara tambaya ina cikin wani yanayi saina ce na hanata fita shine ta fita maza suka daketa to da wani ya daketa gara ni da hannuna in kasheta , ko ina cikin yanayin fushi duk abinda akeyi ina sane kuma kar nake bana mantuwa , tabbas naji Yazeed yace wannan tafassar fa.......?
A dai² lokacin na kwace na fita daga gidan , ranar a gidan ya yini har 1:21am yana nan a tunaninshi zan tafi baisan tunda na dawo da An mata goruba na daina kwana gidana nake kwana tare da ita , ita kanta bata san gidan nake kwana ba saidai kawai ta ganni da safe , Yazeed yace min DK yaushe zaka wuce ne ? Nace masa aini bana fita sai kowa yabar gidan nake fita , sai yacemin tare zamu fita , nace masa bana zuwa da kowa kuma bana fita da kowa , yace zai bini a haka dai saida nayi mishi gatso² ya tafi , misalin 2:09am ya kirani na ɗauka yace wai na wuce ko ina goruba ne ? Nace masa ya akayi ne ? Murmushi Dikko yayi tare da cewa waini za'a ɗauka sakarai bayan har "yan cikin Yazeed ina kallo.
Kallon Ashiru yayi sosai tare da buɗe duk girman idonuwan shi masu ba mutane tsoro yace , kawai Yazeed cewa yayi wai "yar yarinyar nan nake tausayi an barta ko yata ƙara jin jikinta ne ? Sakaran banza sai na rubza shi a rami mayen kuma saiya faɗa , { bai faɗi maganar da yayi da Yazeed ba haka kawai yacewa Ashiru } Dikko yaci gaba da cewa ,
Da safe sai An mata ta fito palo ta sameni tana kuka , bata yafe ba duk wanda yaji mata ciwo a gefen fuskarta , na kirata tazo kusa dani na bata haƙuri kuma na lallasheta ta saki ranta mun fara magana Yazeed ya shigo , ni kaɗai nasan fassarar kallon da yayi mata , ta tashi na zaunar da ita saman kujera , kallon da yake mata yasa nace ta ɗauki makullin mota ta ɗauko mana abinci , tana fita ya matsamin muka fita , bayan takai miya ta kwanta yasa na fiddota , nayi niyar zuwa da ita wani wani taron da zamuyi a ranar daka maida ita gida bayan shine ya matsamin naje , na yadda yace inje da An mata nace masa bazani da ita ba , hmmm waini zaima wayau sai ya zuƙe da matarshi kaza ² ya kawo wani makirci ya raɓa , da naga zai maidani wani ruwan tsakar dare kawai na maida An mata gida wurin kakarta bayan na faɗawa mahaifiyarta , yaga gidan shine yace zaizo zance , kawai na ɗauka yana wasa ne amma naji a jikina kamar yaje , ko zaije Allah ya tsallake shi a tarko fitinata ,
Ashiru yace mai gida anya zaiyi haka duk halakcin da kayi mishi , Dikko yace manta da wannan matsayin dana ajiyeshi daban kuma idan ya kuskura yace zai shiga rayuwar An mata zanci ubanshi ne kawai kuma dan naci mutunci shi bazaisa na rabashi daga inda na ajiyeshi ba jeka kawai , fita Ashiru yayi Dikko kuma toilet ya shiga dan yayi wanka.....
Ashiru kuma tunani yake akan maganganun Dikko idan ko har Yazeed ya shiga rayuwar Sultana za'a samu matsala , kuma yayi ƙaton butulci dan Dikko ya suturashi ya farfaɗoshi daga masifar talauci ya kwato mishi "yan cinshi a cikin abokansu , yana zalincin Dikko amma dake shi abun duniya bai rufe mishi ido ba bayajin komai , domin Yazeed yana wulaƙanta dukiyar Dikko da ƙeta an faɗawa Dikko sai yace ai idan Allah ya baka arziƙi tou ba naka bane ba kai ɗaya , yace kuɗinshi na kowa da kowa ne duk yadda Yazeed ke facaka da kuɗin Dikko baya mishi magana kuma ko abokansu da sukayi ma Dikko magana ya kori Yazeed daga dukiyarshi karya talautashi kamar yadda ya lalata arziƙin mahaifishi Dikko cewa yayi ko haka ya tsaya ya daina neman kuɗi nan da shakaru dubu baya talauci....
Ajiyar zuciya Ashiru yayi tare da cewa gaskiya mai gida yana da haƙuri addu'a yayi Allah ya tsare arziƙin Dikko domin shi bangone ga duk wanda ya raɓeshi dan Allah yayi ma Dikko kyauta kuma kyauta mai ɗauke lumfashi hannunshi buɗe yake shi yasa Dady ke cewa yasan koya mutu Dikko zai zama uba ga "yan uwanshi , gaskiya Dikko yana da kirki sosai saidai matsalarshi fushi sai mugunta da ƙeta...
Yazeed abokin Dikko ne , kuma shima Yazeed ɗin babanshi cikakken attajiri ne sai Allah ya kawo mishi karayar arziƙi kuma duk Yazeed shine silar lalacewar komai na ubanshi dan shima yana harkar wasan danbe ya daɗe sosai a cikin harkar , da abokai suka ga bashi da wani kuɗi a hannunshi sai suka cireshi daga cikinsu shi kuma lokacin Dikko baya nan.....
Bayan ya dawo daga tafiya yaga baya ganin Yazeed daya tambaya sai sukace gaskiya DK mun cire Yazeed a cikinmu , bashi da ko sisi zai zama mana damuwa , Dikko yace ba'a rayuwa haka kar a barshi rashin kuɗi yasa ya shiga wani hali na daban gaskiya a ceto rayuwarshi dan duk wanda ya saba mu'amula da kuɗi idan ya rasa yana samun damuwa , a tausayawa duk wanda ya samu ya rasa....
Sai sukace sudai basa zama dashi gaskiya zai rage musu matsayi ne kuma ana ganin girmansu a gari duk wani matashi addu'a yakeyi ya zama kamarsu sai kuma su fara rage zafi gaskiya basa iyawa , amma sai kuma suka ɓoyewa Dikko Yazeed yana wasan danbe.....
Shine Dikko ya farfaɗo da rayuwar Yazeed ya bashi manager a wani companyn shi , yaga kuɗin banza ya shiga daddagar musu uwa , mutane yadda suka ga Yazeed lokaci guda ya zama mutum yana wulaƙanci da kuɗi sai sannan suka cewa Dikko ai yana wasan danbe Dikko yace ai basu faɗa ba shi kuma ya wuce wurin dan idan ya tafi baya dawowa , duk wulaƙancin da yakeyi da kuɗin Dikko shidai Dikkon bai taɓa nuna mishi komai ba , koda ya fara mai gida Dikko yace baya so ya kirashi kamar yadda ya saba tun farko ,
Sai ki haɗa mace 20 zakiji duk sunce su "yan matan Yazeed ne , ɗan neman matane na bala'e , duk macen daya gani saiya lasa ta , tunda yaga Sultana tsutsar masifar jarabarshi ya tashi kuma ya ɗana mata tarko itama so yake ya lashe ya wuce , idan har mace ta kuskura ta faɗa tarkon Yazeed nata ya ƙare......
Cikin farin ciki na wayi gari , a murnace nake ta huɗɗoni na sai shiri nake na tafiya Daura , tun ina wanka ake cemin nayi baƙo a waje , dan gaskiya rayuwar gidansu Inna babu takura zan fita duk lokacin da nake so in dawo babu wani tsanani , idan zan fita Kaka tana nan zatace min Allah ya tsare kuma idan na dawo taga dawowa na zatamin sannu !
Ina fitowa daga wanka hijabi na saka nayi waje , a harabar gidanmu naga motar Dikko , da farin ciki nayi wurin motar ina zuwa Ashiru ya sauke gilashi ya gaisheni , ansawa nayi cikin halin ko in kula , yace ranki ya daɗe mai gida yace inzo in zauna dake harsai ya dawo kuma duk inda zakije nine zan kaiki ,
Cike da masifa nace kamar ya ka zauna dani ? Ko ance neman wanda zai tayani zama nakeyi ni bana san kilbibi kawai ka kama gabanka , Ashiru yace babu inda zanje ko a napep zaki fita yace kawai in riƙa bin bayanki shine abinda yace , to me yake nufi da abi bayana , Ashiru yace nima haka yacemin , aiko sai inga wanda ya isa yabi bayana , Ashiru yace mai gida ya isa kuma sai nabi bayanki saidai ki fasa fita amma ina nan daga nan har Allah ya dawo dashi lafiya ,
Cike da masifa na nuna Ashiru da ɗan yatsa nace kasan sharrina kuwa ? Banza yayi ya ƙyaleni , nace tou bakai ba ko ubangidan naka bai isa ya sakawa rayuwata ido ba dani dakai mu zuba , nayi wanka yanzu zanje daura ka biyoni idan ka isa kuma ta gabanka zanbi in wuce lusari kawai dakai , ina faɗin haka nayi ciki ,
Murmushi Ashiru yayi tare dabin bayan Sultana da kallo , tunanin Dikko yayi da yace masa , An mata tana wayau sosai kuma haɗarinta yawa gareshi tana anfani da wani abu take sa mutane bacci dashi sai ka kula , mai gida ya akayi ka sani , wurin "yan daban da take amfani dasu domin saida nasa aka tattaromin su akan wani binke daya shafeni ka kula tafiyata ta zama dole saboda Dady yana jirana Yazeed sharrinshi yana da ƙarfi na baka amanar An mata Ashiru idan har wani abu ya faru da ita bazanyi kuka da kowa ba sai kai , Ashiru yace mai gida bana tunanin zata fita ta tsorata dakai , Dikko yace batajin tsoro na irin An mata duka baya mata amma zata tsorata dani da zaran na aureta dan irin su An mata hukunci ɗaya ne maganin su kuma dashi zan horata kowa zaiyi mamakin natsuwarta dan yadda nasan zan mutu haka nasan sai An mata ta fita ,
Ashiru yace lallai kuwa gata ita daura zata tafi ma , zanga ta gidan ubanda zaki bi ki fita , fitowa yayi daga cikin mota ya fara duba saman katangar gidan da aka zagayeta da wayoyi masu raba mutum gida biyu su tsisstige masa hanji , zagaya gidan ya farayi ko zai samu wani wuri daya buɗa inda zai ba mutum damar fita ,
Dariya nayi nace ga ɗan boko wanda ya zaga duniya ga jahila wacce ba ilimin boko kuma babu inda taje tana rayuwarta ne a cikin birninsu yau zanga yadda zamuyi wannan wasan dakai malam Ashiru dan wallahi ko min bala'e sai naje daura kuma sai naje na dawo kana nan banza kwance a mota kana baccin asara............
Muyi wasan.....
0 comments:
Post a Comment