Ina saka kayana ina mita cewa naga yanda za'ayi wani ƙaton banza ya hanamin nayi rayuwana yadda na tsara abuna , zanje daura dole saina san dalilin da yasa aka yankewa Aunty Suwaiba ƙafa , a madubi na kalli kaina kamar ina ma wani kashedi na nuna da ɗan yatsa duk wanda ya shigo da takura a rayuwata , abuna da nake fesawa na bacci na ɗauko dan yana cikin jakar makaranta na tuni nake neman sa'a akan Dady dan ina da ƙudiri akan shi sosai a zuciyata , ta cikin madubi na fesashi fesss dariya nayi tare da cewa haka zan feshe ka kamar na watsawa sauro magani maimakon kai ka mutu sai kawai ka tafi duniya bacci.....
Ina gama saka kayana na yafa gyalena na ɗauka jakana dan a lokacin har Yazeed yazo wayata na ɗauka da kwalbar abuna na fice daga cikin ɗakina dan ko Kaka ban faɗawa Daura zanje ba kuma ban leƙa mata ban kwana ba !
A harabar gidan na samu hayaniya ya gauraye tsakanin Ashiru da Yazeed kowa sai ɗaga murya yakeyi kamar zasu buga , wurin Yazeed na nufa nace masa ya akayi ne ? Cikin ɓacin rai yace wannan jakin ne zai ɓatamin rai , wai me yace ne ? Nayi tambayar ina kallon Ashiru amma Yazeed na tambaya ,
Yazeed yace cemin yayi ni ɗan iska ne ina leƙe² nazo zan leƙaki , ɗauke idona nayi daga kan Ashiru nace ma Yazeed miye leƙe² ? Duk shiru sukayi , murmushi nayi a raina na kalli Ashiru nace Dikko yace idan ka bari na fita zaka bini ko ? Yace Eh , nace idan Yazeed zai ɗaukeni fa ? Shima sai naje , kallon Ashiru nayi sosai ƙosashshen ƙato ne mai sigar "yan restyling ya ƙoshi sosai Dikko yayi mishi horon ƙarfi ko ina ya cika kamar anbi jikinshi an tsatstsaga mishi dutsina saboda cikarshi ,
Ajiyar zuciya na sauke na kalli Yazeed nace wai miye leƙe² ? Kowa shiru yayi , to tunda baza kuyi magana ba kai Yazeed muje kafin rana yayi , juyawa Yazeed yayi da niyan tafiya Ashiru ya shaƙoshi ta baya , murmushi nayi a bayyane tare da cewa kai yaro sakar mishi wuyan riga kafin inci uwarka , na ƙarasa maganar ina nuna mishi da kaina ,
Ni zaki ci ma uwa ? Ya tambayeni , nace ba kai kaɗai ba hada Dikko naci uwarka naci uwar wanda ya turoka ka zauna dani , gyara tsayuwata nayi sosai tare da nuna Ashiru da ɗan yatsa nace ai saboda so duk za'a sakawa rayuwata ido ko ? Shiru Ashiru yayi yana kallona a nutse baiyi magana ba , naci gaba da cewa ni dama inda na gode Allah ban taɓa cewa ina san Dikko ba , tou wai waye ma zai so mahaukaci ?
Yanzu mutum anjima aljani , a haukan nashi yake tunanin zan iya aurenshi ? Bashi da aiki sai zafin kai da doke² idan har baka fita harkata ba saina tona maka asiri , ke ni zaki tona ma asiri.....? Tabbas nasan ahalinka kaf kuma nasan abinda ya raboka daga gidanku ka dawo rayuwa ƙarƙashin mahaukaci , { kuma ƙarya nakeyi bansan komai game da rayuwarshi ba , }
Ashiru yace ke yarinya bamu da sata bamu da maita kuma bamu gaji iskanci ba duk duniya wannan abu 3n dana faɗa ɗaya daga ciki mutum zai samu kanshi yaji takaici kuma shi ubana baya taushewa....
Nima ban gaji iskanci ba hayenshi nayi kamar yadda kaima baka gaji kwaraka ba kake rayuwa a ƙarƙashin wani , kuma idan ubana ya taushe kaima ai naka ya taushe saboda kunne ya girmi kaka yaro idan baka san asalinka ba yanki fili ka shiga siyasa , Sultana bata siyasa amma rayuwar kowa da labarin gidan kowa yana a tafin hannuna saboda ɓacin rana , kasan duk wanda baisan kanshi ba daya shiga siyasa duniya zata faɗa mishi koshi ɗin waye , nima siyasa ce duk wanda ya shigoni zan warware mishi dan nidai ubana bai taɓa murƙushe surikarshi da ɗiyar maƙocinshi ba , { kuma haka nan kawai na faɗa dan in ɓata mishi rai bansan komai game da rayuwarshi ba , } cikin ɗaga murya Ashiru yace ke...... Ki gyara kalamanki akaina tun kafin in ƙera miki rayuwa , a sanyaye nace malam Ashiru ai yanzu muka fara , zama fa tare dani zakayi anshi wannan kafin in dawo , kafin ya ankara na feshe banza ya ƙame a wurin ,
Da taimakon masu aiki da kuma Yazeed aka sakashi a mota bayan na faɗa musu ciwon farfaɗiya yake , haka ciwon yake taso mishi lokaci² , ina ƙoƙarin rufe motar naji wayar Ashiru tana kuka a aljihunshi , Yazeed nasa ya cirota nace waye yake kira ? Yace mai gida , saida nayi dogon nazari sannan nacewa Yazeed ya maida mushi wayarshi a jikinshi muje ,
Maida wayar yayi jikin Ashiru mu kuma muka shige mota mukai tafiyarmu , tunda muka kama hanya bana tunanin komai sai tunanin irin halin Dikko , ga zuciya kamar kumburƙuma , mema Dikko yayi min na rayuwa wanda ya kamata ace na so shi ? Bashi da aiki sai doke² so biyu yana dukana na farko saida na suma , na biyu dakel aka riƙeshi umm gaskiya bana san namiji da zuciya gashi bashi bada uziri ko kaɗan na rayuwa jiya daga ya kirani na fara bacci kawai ya hauni da masifa , na sake kiranshi ya kashe wayarshi gaba ɗaya..
Dai² saitin zuciyata na dafa a bayyane nace kiyi haƙuri dan Allah dan annabi kiyi haƙuri ki goge wannan mutumin daga cikinki , a sirrance na sake cewa me ma Dikko yayi miki na rayuwa ? Mota ce kawai ya baki sai miliyan ɗayan kuma dan ƙaranta daci baya mahaifiyar shi ta ansa , gashi bata so na , kallon Yazeed nayi da wutsiyar idona , zuciyata tace kalli Yazeed shima dai lafiyayyen matashi ne jini yana motsawa ko ina ajikinshi , yana da ƙirar burge mace kuma shima dai ɗan kwalisa ne , me ake nema na rayuwa ? Idan dai namiji yana da "yan canjinshi kuma ya iya soyayya ai shikenan , kawai ki watsar da Dikko duk da dai badai wata makusa shima dai kyakkyawa ne gashi ɗan gayu uwa uba ya iya magana mai daɗi amma yanayin Dikko yafi na Yazeed nuna gogewa a wurin iya ɗagawa mace hankali ƙwayar idonshi ya nuna haka giraren shi kawai ka kalla kasan zaiyi jarabar masifa duk macen da Dikko ya damƙa zataji a jikinta bare kuma ni da yakeji ma haushi nayi imani da Allah irinsu Dikko sune masu horar da mace da azaba a wurin kwanciya matsawar tayi musu laifi , mace taita ƙarewa a rasa abinda ke damunta , ai dama yama taɓa faɗa min da bakinshi cewa idan harya aureni sai nasan shi ba abokin wasana bane ba bare ga Dikko da ƙeta , umm manta da Dikko kawai ki auri Yazeed na tabbata zakiyi rayuwa mai inganci dan shima jajirtaccen namiji ne tunda har baiji tsoron Dikko ba ya shiga soyayya dake wannan namiji yakai jarumi...
Ajiyar zuciya na sauke na sake kallon Yazeed da wutsiyar idona , kallon siffarshi nayi sosai domin Allah Dikko yafi shi zarrar cika cikakken namiji nesa ba kusa ba , duk baƙar hassadar ka babu yadda ka isa ka kushe Dikko wallahi , domin cikakken namijine jajirtacce yana da zarrar da duk macen data ganshi mai lafiya da sanin duk wasu qualitative na namiji tasan Dikko yakai kuma wallahi babu yadda za'ayi yaba kanshi kunya wurin mace a gado , mutum ɗan tara ne bai cika goma ba , ni gaskiya na haƙura da Dikko dan bansan ranar da zai samu lafiya , idona ya cika da hawaye gaskiya ina san Dikko sosai wallahi idan har nace bana sansa nayi ƙarya , domin duk yadda zan faɗa muku Dikko gani nake baza ku gane ba ,
Da wata irin ƙara ya farfaɗo wayyo Allahna mai gida karka kasheni kayi haƙuri na bari , wayyo Allah ku taimakamin zai kashe ni wayyo............. Wani irin ihu ya sakeyi wanda ya jawo duk hankalin wanda ke cikin asibitin yana cewa gashi nan ku riƙeshi wayyo kakkafawa Al ' Ameen ya sakeyi yana fizge² idonshi a rufe saboda tsabar tsoro , dole tasa akayi mishi allurar bacci dan ya cikawa mutane asibiti da ihu kuma ga marasa lafiya sosai masu buƙatar natsuwa.
Me wannan yaron yake nufi zanyi ta kiranshi baya ɗaukarmin waya ne ? Ƙaton banza kila ma yaje ya miƙa mata fuskar tayi mishi feshi , shi uzirinshi idan ya kiraka so ɗaya baka ɗauki waya ba zai maka uziri har zuwa lokacin dakai zaka nemeshi da kanka , akan Sultana kaɗai yake maimaita kira dan idan ya kirata bata ɗauka ba duk bayan mintuna saiya sake kira yaji ko zata ɗauka , hardai ya samu sa'ar barin nigeria Ashiru bai kira ba bare yasan a ina aka kwana....!
Duk wani shiri daya kamata tayi , tayi ta tattara duk wani abu da tasan idan taje tayi zata tafi da imanin Dikko , duk wani tsafe² saida ta haɗo kanshi , turarenta da man shafawarta da powder har kwallin da zata shafa a idonta duk anbisu an barbaɗesu da asiri , kaya masu azabar² ɗauka hankali ta ɗauka , wai ita zataje jinyar ƙanin mahaifiyarta wato Al ' Ameen , shiri tayo mai kyau da makaman yaƙinta tayo garin katsina bata san sunyi hannun riga da Dikko ba.....
Ni yanzu ina zansa kaina komai ya fara warwaremin kayi wani abu haka nan mana ai bana tunanin akwai abinda ya gagareka , ya ina neman mafita kuma ɗan gwamna zai shigo rayuwarta , yaron nan ɗan iska ne ya raina mutane duk garin nan babu wanda baisan halinshi ba baida mutunci kuma ya raina mutane dan baya ganin girman kowa a garin nan , dan gaskiya idan aka aike ka neman tantirin ɗan iska daka ga Dikko ka tsaya ka samu saboda wannan dalilin ne yasa nasa kayimin aiki akan ya lalatawa ɗiyar Binna rayuwa dan nasan idan har Binna yace zaiyi wani abu Dikko kawai zai iya bi ta kanshi da mota ya wuce , dan na tabbata daba Dikko ne ya farke yarinyar nan ba da har yanzu zaune bai ƙare ba.
Bello ne zaune a gaban bokanshi duk ya koro wannan sharfin tare da fashe mishi da kuka cewa tuni kasa ni nabar sallah azahar da asuba da isha'e amma ka kasa wani abu ? Wata irin dariya bokan yayi cewa akwai sauran mafita ɗaya , jikinshi na kyarma yace wace mafita ce ? Saura la'asar da magrib zaka dakatar , Bello yace na ajiye 3 biyun kake tunanin zai gagareni ne ? Na daina sallah dama ai ba kullum nakeyi ba ni koma miye zanyi amma duk yadda za'ayi nidai a raba yarinyar nan da Dikko ko kuma in aureta kawai kaga sai in ida cika burina tana gidana , hahahahaha bokanshi yayi dariya tare da cewa idan dai kana san ganin burinka ya cika na auren yarinyar nan yanzu sai ka auri mahaifiyar , zaro idanuwa Bello yayi tare da cewa kamar ya in auri mahaifiyata kuma boka ?
Wata irin dariya yayi mai ansa kuwwa gaba ɗaya dajin ya karaɗe da ƙarar dariyarshi bayan ya samu natsuwa yace yarinyar tana da ibada tana sallah akan lokaci kuma tana da karatun littafin Allah babu dare ba rana , kuma kasan munyi² mu rabata da sallah abun ya gagara idan har zaka iya auren uwarka duk daren duniya zaka kwanta da ita ne ka riƙa samun natsuwa daga gareta shikenan Sultana zata aure ka kuma duk duniya babu wanda ya isa ya hana auren , saboda sai mahaifiyar taka tayi bacci zaka kwanta da ita , tou yadda ka sadu da ita tana bacci bataji bata gani ba haka za'ayi aurenka da Sultana mutane bazasu ankara ba bare ayi ta surutu....
Shiru Bello yayi bayan wani lokaci yace wannan kauce hanya tayi yawa da wane idon zan tsaya a gaban Allah uwata fa.......? An zan samu rahama ranar gobe ƙiyama ? Boka yace wanda yayi kisa me ya rage mishi daga rahamar Allah a duniya da lahira ? Bello ga kisan kai ga zinace ² ga caca kawai kayi sai ka tuba idan ka kusa mutuwa tunda kana san rahamar , Bello yace to a rabata da Dikko basai na aureta ba , Boka yace ko ka aureta ko a rabata da Dikko saika auri uwarka , idan haka baiyi ba tou kisanta shine mafita kawai.... Bello yace shikenan zanyi shawara....
Har muka isa Daura ni banyi magana da Yazeed ba sai shi daya kunna wata waƙa ta "yan siyasa yakebi , wannan ta shiga ta fita , nidai hankalina da zuciyata ya tafi yayin da nake jinjina auren Yazeed sai kuma tunanin yadda zanyi ma in cire Dikko daga raina tun farko ma kenan. Haka nan naji gabana ya yanke ya faɗi ina tunano lokacin da Dikko ya sumbaceni a ƙofar gidanmu ranar dazai rabu dani , tashi tsikar jikina tayi yayin dana tuno yadda na kasance a jikinshi da maganarshi da yake cewa zamuyi aure bada daɗewa ba ,
Haukanshi na tuno yadda yake fizge² yana zabura kamar anba doki ƙwaya idan an riƙeshi , kai gaskiya ina san Dikko amma idan har na aureshi ranar da nayi mishi lafiya waye zai riƙeshi idan zai dakeni....? Murmushin Dikko na tuno a ranar da mukayi faɗa dashi hanyar tafiya bakori lokacin da muka tafi da Mardiyya maganar da yayi na tuno ,
Haba yarinya Dikko ne fa ! Kin manta nine na koya miki ? Nine nayi kuma nine na fara baki idan daɗi kikaji ko zafi duk nine dai , ruwa idan da rabon ka a ciki ko ka zubashi a kwando bai maka yoyo , ni ba abin farautarki bane zaki duk jarumtatai yana ganin ƙimar mafarauci a wancan karon suma kikayi wannan karon ma haka zata sake faruwa dake ba suma ba har jinya sai kinyi idan kika dawo ɗaukar fansa zaki gane Dikko ba sa'arki wasanki bane domin saina baki azabar da sai kinyi fitsarin wahala , bayan kin dawo daga duniyar suma tsorona zai shigeki a duk lokacin da kika kasance dani a shimfiɗa ɗaya ,
Wallahi jarumi ɗaya akeyi a ƙarni nine jarumin wannan lokaci , Dikko jarumin maza ne kuma keda kanki zaki faɗa kije ki dawo ina nan ina jiranki , murmushi nayi a bayyane nace wannan gaskiya ne mutumina Allah ya baka lafiya.....
Fita nayi daga cikin motar ina fita da Yayar Aunty Suwaiba na fara haɗuwa muka gaisa da ita take cemin yanzu nan aka tafi da Suwaiba Zaria wai sunje zasuyo wasu aune² , cikin rashin jin daɗi nace yaushe zasu dawo ne ? Tace insha Allah barasu wuce kwana biyu ba , nace tou dan Allah akwai wata waya a hannunta wacce aka bata a asbiti shin ko zan samu wayar ne da Allah ko kuma ta tafi da ita.....?
Shiru tayi irin na masu nazari tace me zakiyi da wayar ne , murmushi nayi ba tare dana bata ansa ba na buɗe jakata na ɗauko kuɗi na bata tare da cewa bani wayar ke kuma ki riƙe wannan , cike da farin ciki ta anshi kuɗi tare da cewa ina zuwa , mota na koma ita kuma ta shiga gidan Aunty , bata wani daɗe ba ta dawo da wayar ta bani , godiya nayi mata sosai tare da cewa zan sake dawowa godiya tayimin sosai har muka tafi tana godiya tare da ɗaga mana hannu har saida muka ɓace...
Har yanzu banyi magana da Yazeed ba amma na fahimci wasu ɗabi'u nashi , ina wani tunanin ne wayar da Dady ya bani ta fara kuka da sauri na fiddo wayar daga jakata na ɗauka tare da cewa Dady barka da wannan lokacin , na nunawa Yazeed yayi parking , yana yin parking na fice daga mota...
Barka dai kin wani manta dani ko ? Haka kin kyauta kenan ? Haba taya zan manta dakai bayan kullum kana raina kamar kuɗin haya kayi haƙuri ban manta dakai ba kullum tunanin ka nake yanzu haka ma tunaninka nake kawai sai ka kirani , dariya yayi cewa tou yanzu kina ina ? Kallon titi nayi tare da cewa ina gida , ina ne gidan naku wai ? Zaka zo ne ? Saidai ke kizo , kana ina ne ? Ina nan Ambasada kinsan wurin ne ? Nace Eh hanyar Shinkafi ko ? Yace Eh kizo to , gani nan zuwa amma zanzo sanye da niƙaf da hijabi wurin ina kake ne ? Kinsan Fesra hotel ? Eh na san wurin tou ina a wajen da Allah karki ɓatamin lokaci , baka da damuwa ina faɗin haka na katse kiran !
Kwanan wata na kalla a wayata nai murmushi cewa hawan ruwan ciki na fa sai mutum ya shirya baka da zarrar da zan miƙa maka linzamina rayuwata , wahalar banza zansha bayan ka haɗamin da "yan dabaru kayan maza , tsoki nayi tare da cewa anya ma muradin kake nema ? Ko kuwa dai......?
Kiran dana ansa a baya da baƙuwar number da akace za'a kashe ni na fara kira a kaina nake cewa zan gane yanayin iskan inda ake magana dani dan ranar dasu Al ' Ameen suka bini da gudu har muka haɗu da Bello naga motar Dady a ƙofar get in makarantarmu , kila Dady ya ganni Bello yana bina daga baya zasu haɗu sai yace meya haɗaka da wannan yarinyar da kake binta ? Kawai zaice ai ɗiyar *BINNA ce...* , ko kuma sunyi magana na shi yasa na ansa wayoyi daga mutane daban² kowa yana so yasan inda nake , tou idan wani abu bai faru ba taya akayi Bello ya kasance a wurin bayan Dady kaɗai yasan zanzo makaranta tunda shine kaɗai na faɗawa ina katsina ? Kuma wurin baiyi hanya ɗaya da majalissar su ba kwata² gidan Bello ba'a hanyar yake ba ? Murmushi nayi tare da cewa haba tsofaffi na gano makircinku amma idan ma nemana kukeyi yanzu zan gane ta hanya mafi sauƙi , a dai² lokacin da aka ɗauki wayar , ba mai maganar nake saurare ba yanayin iskan wurin nake so na fahimci ko a inda Dady yayi waya dani ne yake magana.....? Shi kuma cewa yakeyi ,
Zaki mutu mutuwa irin ta karnuwa wallahi saina kashe , dariya nayi tare da cewa baka iyawa , yace zaki mutu fa , nace ƙarya ne , sai na kasheki wallahi , wallahi kana iya kasheni ? Na tambaye shi , yace Eyyy , nace tou idan ka isa kai jarumin ne a harkar kisa ka kashe ni a Ambasada zanzo wurin Fesra hotel yanzu sanye da niƙa da hijabi bana kasuwa fa , sai kin mutu kuma kafin mu kasheshi sai kowa ya zagaya ki , gani nan ka kasheni in gani , ina faɗin haka na katse kiran na fara kiran wayar Hafsa...
Ba ɓata lokaci ta ɗauka muka gaisa da ita , nace Hafsa kina ina ne yanzu ? Cikin muryarta ta sakarkari tace ina Qerau gidan Amisty , nace kina da hijabi da niƙaf ? Me za'ayi dasu ne ? Nace Dikko ne naji yana maganarki yanzu yace baiji daɗin abinda yayi miki ba da zai ganki da zai baki haƙuri amma sai ya ganki cikin niƙaf da hijabi dan ranar nan ma abinda yasa ya dakeki wai saboda kinzo ko gyale babu shi yasa kika ɓata mishi rai dan kishinki yakeyi sosai ,
Hafsa tace muna da niƙaf mana wanda muke amfani dashi idan zamu shiga wurin da bama so asan mune , nace to ki saka niƙaf da ƙatuwar hijabi ki shiga napep karki tafi da wani ya rakaki kinsan su "yan siyasa basa san surutu shi yasa sukeyin komai nasu cikin sirri , kicewa mai napep ya kaiki Fesra hotel dake hanyar shinkafi idan kinzo wurin ki kira wayar Dikko kinji ko ? Tace to , nace yawwa kiyi sauri kinsan baya san jira , tace yanzu fa , tana faɗin haka na kashe wayata na sake kiran Dady ,
Bayan ya ɗauka nace ya kamata kaɗan sirrinta motarka a cikin hotel in dan wani ne zai ajiyeni a mota ban sani ba ko ya sanka , Dady yace ai dama ba'a mota nake ba ina zaune a ƙarƙashin wata bishiya ne ba da mota ta nazo ba , kashe kiran nayi tare da cewa lallai ka shiryamin zagon ƙasa da yawa ,
Wayar mai cewa saiya kasheni na sake kira bayan ya ɗauka nace wallahi ku dukanku baza ku iyamin fyaɗe ba , na rantse da Allah duk yawanmu sai munyi wasan danbe dake wallahi ׳ sannan mu kashe ki , idan kuma kinyi sa'a kin mutu kafin mu gama kin huta , dariya nayi tare da cewa aiko rijiya ta ƙafe da zaran anyi yasa wasu ruwan ne zasu sake ɓulɓulowa ƙananan kwartaye daku nice uwarku gani nan zuwa...
Kashe wayar nayi na koma cikin mota inda Yazeed keta jirana , ina shiga yaja muka nufo cikin babban birnin garin katsina ta Dikko ɗakin kara , kunya gareku badai tsoro ba ,
A motar Yazeed na saka cajin wayar dana anso a wurin Yayar Aunty dan wayar a kashe take ba caji , bayan na saka naci gaba da sauraren waƙar da Yazeed kebi ta mai girma gwamna ,
A zahiri nake sauraren waƙar amma a baɗinance ina tunanin yadda zan ƙare da masifar da nake san haɗawa dariya nayi a bayyane a zuciyata nace ai basu iyawa dan basu da shedar da zasuyi shara'a dani harkar karuwanci dai kowa yasan anayi ko sunkai ni ƙara kawai zancewa alƙali ni karuwa ce kuma kawaliya ce , inayin karuwanci ne saishi Dady ya kirani yace inzo , sai ince ya mai girma mai shari'a da ya kirani to dama wayata ta kwana biyu kashe babu caji , shine ina buɗewa kiranshi Dady ya shigo bayan na gama waya dashi akan yana da muradi munyi ciniki nace na sallama , bayan na gama waya dashi sai na fara bin kiran miss calls in da aka ajiyemin a wayata bayan ya ɗauka shima dai muradin ne sai naji shi wannan zai bani kuɗi da yawa to kaga tunda ina kawalci kawai saina tura Hafsa taje wurin Dady nace mu raba ƙafa taje can ni inje wurin masu yawan dan danbe zasuyi tunda ni nafita kuzari da kuma daɗewa ana ɓarin wuta a gado ,
Sai Dady yace ya mai girma mai shari'a ai Hafsa ɗiyata ce , sai Alƙali yace ke Sultana me yasa kika haɗa uba da ɗiya sai ince ai ranka ya daɗe ni badashi na haɗa ta ba a tambayeta Dikko nace mata , wata zufa naji ta ketomin duk da a c dake cikin motar , yayin dana hasko har an kirawo Dikko ya fara wannan ihun nashi ana riƙeshi yana wannan zaburar yana saiya kashe kowa... Wayyo Allah ba Dikko ba kai ba ,
Ajiyar zuciya na sauke tare da sake tunanin Alƙali zaice kince Dikko to ya akayi kikace bashi ba kuma ? Shikenan sai inyi shiru inta mazurai banda mafita dan idan an tambayi Hafsa zatace ai cewa tayi Dikko yace in sameshi a Fesra hotel , na shiga 3 , ina cikin wannan jimamin sai Alƙali yace to ya akayi kika samu miss call na wasu kwanaki , sai in nuna mishi miss call in wanda aka taramin ranar da akace za'a kasheni , bayan alƙali ya gani sai kuma yaga nabi kiran babu daɗewa , da sauri na goge wancan tsohon kiran , sai Alƙali yace ya akayi duk kwanakin baki bi kiran ba sai yau ? Kuma kinga miss call , sai ince yamai girma mai shari'a ai nazo zan ɗauki wayar ta mutu saboda rashin caji , idan alƙali ya irga kwanaki sai yace har kwana kaza bakiyi caji wa wayarki ba ? Shafa kaina nayi tare da cewa ai cewa sukayi zasu kashe ni.....? Meye shedar ki kin shigo da wani zance a wani , kai aiko ubana zanci.
A , a bazanci ba tsautsayi sai yasa suce ai ranka ya daɗe ta kirani bayan na kirata , dama ina da record in kiran sai in faɗawa alƙali sai yace in kunno aji , zufa nagoge lokacin dana kunno amma ba m card a wayar an cireshi wani irin ihu nayi tare da cewa Dikko me yasa ka ciremin abuna ? Wallahi Dikko ya cireshi da sauri na zura ƙafata na taka burki tare da kaɗa kan sitiyarin motar kamar sakarai haka Yazeed ya sakar min motar dan mun shigo cikin gari kallo Yazeed yabini dashi tuni na juya kan sitiyari na tun kari goruba road Yazeed ya zuƙe gefe ɗaya dan rabi na a saman jikinshi nake shi tuni ya ɗauke kamar an ɗora kura saman kare , banma san yanayi ba , ina tuƙin nake tunani anya ma Dikko yana garin nan gaskiya baya nan dan daya nan bazai turo min Ashiru ba ,
Ai banma tsaya ba dana isa goruba yadda naga duk an watse gidan ana rusashi aiki ake mishi kuma baya zama , cikin hayaniya nace Yazeed ina Dikko yake zama banda nan ? Banza yayi dani dan baya iya magana , kai tsaye gidanmu na nufa a wurin Ashiru zan samu wannan ansar ,.....
Ilimi ake nema baiwa kuma samunta dace ne.
23/10/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA.....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 62
Tunda na shigo anguwar na danna horn biyyyyi , ina isowa bakin get in gidanmu tuni an buɗe min get na shige ko parking in kirki banyi ba na fito , ina fitowa Ashiru na gani tsaye jikin mota , kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannuna nayi da mamaki ya akayi ya tashi tun yanzu ? Kamar yasan abinda nace yayi dariya yace shi kuma wannan wasan ya kika ganshi ne "Yar mata ?
Ashiru ba wannan ba ina Dikko yake ? Murmushi Ashiru yayi yace mahaukaci bari kiga saƙon daya bari a baki idan kin dawo , wayarshi ya ciro daga cikin aljihu yana cewa bani ɗaya bane nake tare dake irina da yawa mai gida ya watsa kina tunanin kin barni ina bacci tunda kika fita a gidan nan akazo aka dawo dani daga duniyar baccin da kika turani , saboda anga fitar motar Yazeed amma ba'a ga fitowa ta ba wannan dalilin yasa aka zo dubawa ko lafiya , amma abun kunya wai kin mameni na tafi doguwar suma , hmmm
Yadda sukayi tunani kuwa haka ne ina kwance a mota ina bacci kamar wani kolon namiji , irin abinda nake amfani dashi ya ɗauko a mota tare da wurgomin na riƙe yace mai gida yace a ƙara miki dan yasan naki ya ƙare daga yanzu , kinga wannan ya nunamin wani abu a baƙar leda yace dashi aka maidoni hayyaci na , ya kika ga wannan hotunan ya nunamin lokacin dana fita daga cikin motar Yazeed da lokacin dana koma cikin mota , har kuɗin dana bawa Yayar Aunty zuwana goruba , dariya Ashiru sosai tare da cewa kina ja da mahaukaci ne yarinya , tou bari kiji abinda majnun yace......{ mahaukaci }
Record ya kunno na maganar Dikko , "Yar yarinyana barka da hanya fatan kin dawo lafiya ? Ya gajiya ? Allah ya huta gajiya , am An mata nine mahaukaci dai ko ? To wai sai yanzu kika gane mahaukaci ne ni ? Aini tunda nake ban taɓa hankali ba kullum cikin hauka nake kuma wallahi ׳ zan nuna miki ni cikakken mahaukaci ne ina nan dawowa babu jimawa idan na dawo zan nuna miki babban haukana , duk fita ɗaya da kikayi ki sani ko wace da irin azabar dana tanadar miki wallahi saina zane miki jiki tass idan na dawo kinji nayi na rantse kuma wallahi saina rufeki a ɗaki zanga wanda ya isa ya kwaceki a hannun mahaukaci , kinyi ɗaya Allah ya baki sa'a kuma kada Allah ya sanyaya miki zuciyarki ubangiji ya ƙaro miki taurin kai da kangara ni kuma yabarni da fitina na dani dake wanda ya fasa shi ba ɗan baban shi bane , wato maganar dana taɓa faɗa mishi lokacin dana kashe mishi doki ,
Juyawa naji cikina yayi ƙuww maida wayarshi yayi a aljihu yace tou ni zan tafi dan mai gida yace in tafi in barshi dake tunda ke yarinya ce shi da izininshi bai yadda in fitar dake ba , yace kawai inje abuna inyi huɗɗoɗi gabana , har ya shiga mota ya fito ya sake cewa kalli wannan dan ki koyi yadda zakiy faɗa da mai gida ,
Dukan da yayi ma Al ' Ameen ne a wayar Ashiru , abiyar zaman mahaifiyar shi tayi video dan sharri ta turawa Dady , shine Dady ya turowa Dikkon shima dan ya gani Dady yace ina anfanin wannan ? Kaga irin abinda kakeyi Babana miye haka dan Allah ? Ta ɗauka dan tayi ta yaɗashi a duniya ta ɓata maka siyasarka , tou ka kiyaye wannan doke²n , amma nace mata wallahi idanma tasan ta tura ma wani vidio nan tasan yadda zatayi dasu su gogeshi idan har na naji labari ko ganshi yana yawo a duniya tasan abinda zai faru da ita ,
Dakel na haɗi wayun bakin na zufa ta ketomin , Ashiru yace ai finafinan yawa garesu wannan talla ce idan kika kalli cikakken film in fitsari zakiyi tsiii a wandonki , cike da ɓacin rai nace ya akayi banyi ba ? Ashiru yace sauri kike ? Ki fara lissafi daga yanzu duk ranar da mai gida ya riƙeki a hannun shi idan kikayi ni zaki fara tunowa kice ashe Ashiru da gaske yake , dariyar mugunta yayi tare da cewa an kunna wasan mudai Allah ya taimakemu mun fita lafiya , 1 ya faɗa tare da nunawa da ɗan yatsanshi yace ki daure ki fita ko so ishirin ne yarinya kiga yadda zai miki lullusar fitar hayyaci saiya maida ke gari muna gefe muna kallo , na barki lafiya yana faɗin ya shiga motarshi yayo wurin Yazeed ,
Saida ya kalleshi sosai yace kai kuma ni da kaina zanci uwar data haifeka idona idon ka saina baka kashin bala'e saidai in ka daina yawo a cikin garin katsina , murmushi Yazeed yayi tare da cewa nima idan har ka ganni ka gudu ka ɓoye dan sanyi da ruwa bazai hanaa inci uwarka ba , Ashiru yace mu zuba sakaran banza anyi maka rana kana nema kayiwa mutane dare gara ka tuba tun kafin kayi biyu , ko da yake ni nasan yadda nasan mutuwar da zata ɗaukeni mai gida bazai koreka ba danshi ba matsiyaci bane irinka amma nasan saiya ci ubanka cikin farashi mai tsada , sakaran banza butulu kawai mutum mai manta alkairi da akayi mishi a baya jaki ne , ka tabbata jaki , jakinma mai ɗan guntun bindi , kuma wallahi saika bar comparny tunda ba filin tsakar gidan ubanka bane ba , ko mai gida bai koreka ba wallahi da kaina zan kora maka uwa....... Yana faɗin haka ya fice da gudun tashin hankali ,
Wurin Yazeed na nufa nace da Allah ƙyalesu mahaukatan banza daga shi har Dikkon , murmushin ƙarfin hali Yazeed yayi lallai Sultana yarinya ce wato tana ganin wannan abun a rabu dashi ne , idan har yaran Dikko sukaji wannan wallahi sai sun ciccirashi idan har aka bajeshi a saman faranti akace su cinyeshi wallahi wani ma bazai samu inda zaici ba , dan Dikko yana da kirki yana musu hauka da kuɗi kuma shike cidasu sun tirku kamar karnukan turawa kuma an basu horo mai kyau na faɗa , idan har Ashiru ya faɗa musu halin da ake ciki ya tabbatar fita ya gagareshi har gida ma suna iya zuwa su ɗaukoshi kuma basujin yi haƙuri bare ku bari Dikko kaɗai ya isa ya dakatar dasu , Dady ya samo su dan su kula da tilon ɗanshi kuma Dikko baya fita sai tare dasu rabon dai Allah ya haɗashi da Sultana yake fita shi ɗaya zuwa wurin dawakai , kuma ranar daya fara zuwa shi ɗaya Allah yasa ya watsawa su Sultana ruwan dake kwance saman ƙasa ta bishi tana zaginshi zagin da tayi mishi yasa yayi mata mark tun daga wannan ranar bata sake ɓace mishi ba , kuma ai ita Sultana tasan irin yaran Dikko tunda shi Dikkon ya taɓa zuwa da ɗaya anguwarsu lokacin daya taka mata mage , dan Dikko ya tafi dashi yaci uwar Sultana amma yadda tayi magana cikin sanyi cewa da Allah cikinku waye yake tuƙar motar nan ? Ya takamin magena , sai Dikko yaji ta bashi tausayi kuma "yar ƙarama da ita amma ta cika taurin ido shi yasa yace mata itama gobe idan ta tsaya a hanya haka zaibi ta kanta da mota ya wuce , sai ya hana a daki Sultana dan gani yake duka ɗaya zai mata a shafe tarihinta a duniya...
Ajiyar zuciya Yazeed ya sauke wallahi baisan zai haɗu da Ashiru ba a dai² wannan lokacin da bai shigo ba , da yanayin gajiya ya kalleni yace bara in ɗanje in huta zan dawo anjima , sai ka dawo na faɗa tare da cewa ngode.....🙏🏻 , saida ya tafi na wuce cikin gida a tsorace.
Napep na sauketa ta fiddo wayarta ta fara kiran wayar Dikko wannan layi da ake kira a kashe yake , shine ansar da ake bawa Hafsa , tana tsaye tana ta kiran waya taji an nanɗeta ta baya , kai su waye haka ina zaku tafi dani wayyo Allahna , wani irin mari Bello yanka mata tare da cewa wurin ubanki zamu kaiki , kai ku sakeni mana a , a wai miye kukeyi haka ne ? Wayyo Allah bana so jama'a ku taimakeni masu satar yara , ku buɗemin fuskana kun shaƙeni da niƙaf numfashina zai ɗauke ,
Mota suka danna Hafsa da ƙarfin masifa , tana ihu suka daɗe dai² saitin bakinta dole tayi shiru dan sautin ihunta baya fita , basu dawo cikin garin katsina ba suka kama hanyar kaita da ita ,
Wayyo Allahna me zan gani haka ? Uncle waye zai kashe ka na shiga 3 ƙaryana zai ƙare karka mutu ka tashi don Allah , kallon rainin wayau Jiddah tayi mata cewa ke kuma wacece ? Cikin kuka Mardiyya tace Mardy beb mai dogon zamani , Jiddah tace ke kuma ya kike da majiyancin ne ? Mardiyya tace Uncle ...... Saida tayi shashshekar kuka tace Ubana ne Uwa na ne shine komai nawa , ke kuma wace ce ? Nice Jiddah , Mardiyya tace wace ce Jiddah ? Jiddah tace ni Jiddah Matar Dikko....
Cike da makirci Mardiyya ta rungume Jiddah tana cewa mun shiga 3 Aunty namu ya ƙare Allah yaba Uncle lafiya , Jiddah tace am3n , Aunty Yaya DK yasan Uncle baida lafiya kuwa ? Cikin ɓacin rai Jiddah tace ai shine ya dakeshi , Mardiyya fa tasan Dikko yayi dukan saboda Umar da kanshi ya bugawa mahaifiyar Mardiyya waya cewa Al ' Ameen baida lafiya kuma mai gida ya bashin kashin bala'e , danshi Umar komai da ruwanka ne haka "yan gidan gwamnati suke kiranshi shi yasa ko abu akeyi da an ganshi sai a bari idan kuma magana akeyi da an ganshi sai ayi shiru inba haka ba yanzu zai ɗauketa yayi gaba da ita , ita kuma Mardiyya tanayin magana da Jiddah dan su samu kusanci saboda so take ta zauna gidan Jiddah.
Sai wani shishshige ma Jiddah take , bayan sun gama jimamin Al ' Ameen cikin kuka Mardiyya tace Aunty Uncle yana sanki sosai kuma yana bakin ƙoƙari wurin ganin yayi maganin "yar iskar yarinyar nan dan kinsan ni dashi bama ɓoye ma juna komai , yana ƙoƙarin yadda zaiyi ya raba Sultana da Yaya DK yarinyar tsinanniya ce kuma karuwar ijece ita , karuwa ce mai zaman kanta amma tanayin karuwancin nata da tako ne domin ijin wuta takewa mutane sai ta akisu ta barosu , ƙara fashewa da kuka Mardiya tayi cikin kuka tace harfa girman Dad ina tasa wata matatta ta ɗauko mata ta turomin , kuma duk yadda akayi itace tura Yaya DK yayi ma Uncle dukan nan ,
Cikin rashin fahimta Jiddah tace harda matattu take huɗɗoɗinta kenan ? Ita kuma abinda Mardiyya ke nufi kafin Mamy ta mutu shi yasa tace wata matatta , a fahimtar Jiddah ita kuma wanda suka mutu dasu Sultana ke huɗɗoɗinta dasu , bata gane ba kuma bata tambayi Mardiyya tayi mata bayani ba , sukaci gaba da neman mafita yadda zasuyi maganin Sultana yayin da ita Mardiyya ke tunanin anshe goruba hannun kuturu ba wuya take ba , ita kuma Jiddah ta saki baki taci gaba da rattafawa Mardiyya bayani , ta kasa yadda zata samo sperm in mijinta , Mardiyya taci gaba dai da warware mata tunani tana ɗorata a hanyar halaka....
Wani irin ihu Hafsa keyi yayin da aka fara gabatar da wasan danbe a saman ruwan cikinta , wani gidane suka kaita a can cikin garin kaita yayin da Bello ke cewa ba kince ke jar wuya bace ba , ai zaki iya damu ko ? Ba kince ke rijiya bace ba ko kin ƙafe da an yasa wasu ruwan zasu sake ɓulɓulowa ? Ai kince mana mu ƙananan kwartaye ne ba ? Yau zamu nuna miki mun manyan *KWARATA...* ne , a dai² lokacin da wani ya sauka wani ya taka saman Hafsa Bello yana cewa nine Bello aminin ubanki kiji da kyau yadda kikamin video tsirara haka zanyi miki kema , ni na koyama ubanki iskanci amma dan iskan ya lashe min matata a daren farkon dana shigo ina murna zan buɗe ta a leda amma ɗan iskan ya yage min mata ya gudu saboda kawai nayiwa yarinyar gidan da suke zama fyaɗe ba dangi uwa bana uba , amma banza ina gama dafuwata ya cinye kafin inci yasha ruwa ya kama gabanshi ,
Na saka banzan a tarko na amma ranar dana ɗana masa ɗan banzan ya tsalleke , idan baki sani ba nine nayi asiri wa Babanki kuma na haɗashi yake tarayya da ɗiyar Yayanshi wanda suke uba ɗaya , kuma nine nayi asiri na haɗashi yake iskanci da ɗiyar Yayanshi wanda da Babanshi da Baban yarinyar suke uwa ɗaya uba ɗaya , kuma nine nayi asiri ya sakaki a wasan caca nine na maidake kidahumar ƙarfi da yaji nasa kika antaya a ruɗun rayuwa ,
Wani irin ihu yayi tare da cewa naji baƙin ciki yau da ubanki bai duniya naso ya gani yadda zanyi zazzagar da yayi a saman matata yau zanyi akan "yarshi amma nasan soyayyar da yake miki duk da yana cikin ƙasa yanaji yana kallo yau ni Bello zan cinyye yadda ka kayimin nima zan rama idan zaka iya fitowa daga duniyar mutuwa kazo ka ƙwaci "yarka a hannuna ,
Dady dake gefe tsaye ya kasa gane inda maganganun Bello suka nufa , kamar ya yake nufi yayi asiri ya haɗa ahali ɗaya sunyi wannan gauragaurayar haka ? Yana tunani yaji Bello yace masa kaima Alhaji Binna yabi naka ya lashe baka da burin daya wuce ka lullusa akan wannan tsinanniyar yarinya a dai² lokacin da Bello ya afka magunguna a bakinshi ya kora da ruwa akaci gaba da video shi kuma yaci gaba da sharar fage yana ihu yau shine yake lalata "yar Binna ashe dai muradina zai cika ? Dady yace nifa duk ban gane abinda kake nufi ba , Hafsa jin maganar mahaifinta yasa tayi magana cikin wahala cewa Dady zasu kasheni , Dady jin muryar Hafsa yasa yayi wurin ya yaye niƙaf in bawai yana dan yana tunanin Hafsa bace ta kasance a wurin ba hasashe ne , yana yaye niƙaf in Hafsa ya gani tasha azaba sai zaro ido takeyi kamar ɓera yaci guba tasha kuka harta gode Allah saboda azaba , cikin hayani yace ma Bello dan ubanka ɗiyata ce sauka yana ɓanɓaro Bello amma Bello ya dafe Hafsa sosai yana cewa ba'a buga ƙaraurawa ba ,
Dady yace ƙaraurawar ubanka ince maka ɗiyata kana min maganar ƙaraurawa , Bello yace ai nasan ɗiyarka ce ka koma gefe kaima za'a buga naka zaizo , da ƙarfin bala'e Dady ya fizgo shi amma Bello ya ƙadaddabe Hafsa yana cewa ba so kike kisan su waye *KWARATA* ba ? Tou buɗe kunnenki da kyau , Bello kwarto ne , ubanki Binna shima kwarto ne , Yayan ubanki gashi nan tsaye a gefe yana so na sauka ya hau to shima kwarto ne , kowa kwarto kwarto kema kwartuwa dani dake dasu da kowa *KWARATA...* ne ,
Bello yace ku janyemin mutumin nan kumin baya dashi ni kuma inyi gaba da ita mu ci gaba da fafatawa , kama Dady sukayi suka riƙe suna cewa Alhaji ba haka akeyin wasan danbe ba kaima idan ka hau babu mai saukoka sai ka gaji da kanka ka sauka , Dady yace ba Sultana bace Hafsa ɗiyata ce dana haifa da kaina itace ya akayi kuka kawomin ɗiyata bayan munyi daku ɗiyar Binna shine kuma kuka cuceni kukaci amanata wallahi duk saina tsine muku albarka , cikin kuka Dady yace Allah ma bazai barku ba kuma nima bazan barku ba , da sauri Bello yakai dubanshi ga Sultana amma maimakon Sultana sai yaga Hafsa da tuni suma , shima cikin tashin hankali yace ina Sultana take ne.........?
Misalin ƙarfe 3:12am ƙaran wayata ya farkar dani daga ƙatoton baccin daya daɗe yana morar gangar jikina da idanuwana , dakel na lalubo wayar ba tare dana duba ba na ɗauka na ɗora a saman kunne na , nace hello , Dikko ne ya faɗa kai tsaye , cikin faɗuwar gaba na buɗe idona da sauri na tashi zaune nace ina kwana , lafiya lau ya kike ya rashin ji da taurin kai ? Kayi haƙuri don Allah , ai nayi haƙuri shi yasa na kiraki wannan kiran bana rarrashi bane ko yasa ki nemi afuwa ra'ayi nane yasa na kiraki kuma kiran nan bazai hana na zaneki ba wallahi saina zane miki jiki tass idan na dawo kuma bazanyi kaffara ba , kuma ban kiraki dan ince ki daina fita ba duk ba wannan ya shafeni ba yanzu soyayya ne , haka nake laifinki bazai shafi soyayyarmu ba , na faɗa miki ko munyi aure kikaimin taurin kai saina baki azaba kuma mu koma gado nanma in nuna miki girma na , kinsan mahaukaci baida zuciya...
Tou ya kike ? Fatan kinajin daɗin bacci , faɗamin kinyi missing ina ne ko ya ? Dan Allah kayi haƙuri , cikin muryar shagaɓa yace ke kina san mahaukaci ko ? Nidai dan girman Allah kayi haƙuri wallahi bazan sake ba , ah lallai abu ya girma An mata hada mafarkina ? Nidai ba haka nace ba cewa nayi kayi haƙuri , Ey wallahi ai haka nake so kullum nayi ta zuwa miki a baccinki , a , a ba haka ba cewa nayi kayi haƙuri , duk maganar dana faɗa sai yayi wata magana daban , tsoki nayi shi kuma yace ke karfa ki sunbaci ni yayi maganar yana yin wata irin dariya mai kama zuciya , naja miki gemuna An mata tunda baki gaishe shi ba , ki duba a whatsapp inki zaki ga Dikko yana gaishe ki , ni ina ruwana da gemunka , kai wannan gemu ya tsare miki zuciya Allah dai ya nunamin ina da rabon gani ranar da zaki ritsa uztaz a ɗaki kija gemu , yaƙi ya ida maganar yace bara dai in barki karki kasa komawa bacci , cikin wata irin murya mai saukar da kasala yace ina san ki...... Murya mai kama da raɗa ya maida maganar shi cewa mahaukaci ya barki lafiya , saida yayi muah da yanayi mai shiga zuciya ya kashe wayarshi ya barni da tunaninshi...
Buɗe data ta nayi saƙonni suka shigo , na Dikko na buɗe ina duba hotunshi , duk yayi su a cikin yanayin farin ciki hada Dadynshi ya rumgeshi cikin soyayya duk su dukansu suna cikin farin ciki , murmushi nayi tare da cewa an gaishe da mai kyau , idan yayi murmushi yanayin kyau an sharce gemu yayi kalar ɗaukar hankali , voice note yayomin to ya kikaga mutumin naki ne ?
Nima voice note nayi masa cewa wai kai shakarunka nawa ? Na tura , cikin magana mai haɗe da dariya ya maidomin cewa ke yarinya yo ai da kaɗan kika girme ni , bayan naji na tura mishi nine ma na girme ka ? Ey mana baki ganni ɗan yaro ba , ko gemuna ne yake buɗe miki ido ? Amma ai cewa kake kai babban mutum ne , haba An mata nima fa ɗan saurayi ne ko nayi miki tsufa kike tunani ? Karki ja da baya duk abinda kike tunani a wurin marar gemu a wurina zaki samu yarinya , to daga nan muka koma faɗa saida Dikko ya tabbatar nima ya ɓatamin rai akayi rabuwar baran² yace kuma naja ma kaina bazai sake kirana tunda banda wayau ,
Cike da sanyi jiki na koma na kwanta , nidai ina san halin Dikko ina sanshi matsalarshi saurin fushi , hotunanshi naita kallo kamar banda aikinyi , idan na kalli hotonshi sai in hararo siffar Yazeedu kai gaskiya jirgi yafi mota ko a tafiya ma akwai banbanci , murmushi nayi cikin yanayin ɓacin rai nace mutumina kenan ko harsai zuwa yaushe zaka dawo.....?
Murmushi yayi cikin yanayin jin daɗi yace An mata kenan na hayaƙaki ko ? Saina dawo zakiga yadda zanyi dake saina ɓata miki rai gaba ɗaya , hmm yarinya kin rainani da yawa wallahi , amma duk saina sauke miki duk wata rashin kunyarki dake ɗauwaniya da rayuwarki dole sai kinsan nine gaba dake , idan ba'a share masallaci ba za'ashare kasuwa ko wattuba dan wuya ba lada , kuma saina sake kiranki anjima ki gama fushinki saina hana ma zuciyarki zaman lafiya da tunanina.....!
Mardiyya gidan Jiddah ta kwana suna ta tattauna yadda zasu shawo kan wannan matsalar , yayin da Jiddah ta buɗe baki taita tonawa Dikko asiri duk yadda yake kwanciya da ita take bawa Mardiyya labari wai dole take ɗan haɗawa da kayan mata Dikko fitina gareshi kafin safiya tayi sai ya buƙace sau3 , wai ko wucewa tayi tana ɗan murzawa sai yace wai a likitance idan mace tana irin wannan tafiya tana buƙatar namiji ne , kai wasu matan dai wawaye ne wallahi mijinki ya kulle ƙofa dake yayi sirri ki fito duniya kina barbaɗawa , wacce kike ba labarin duk lokacin data ga mijin naki sai wannan maganar naki yazo ya tsaya mata tana kallonshi da wannan maganar da kika faɗa haka babu kyau kuma zunubi ne mai girma ,
Idan kuma kikayi sa'a da "yan iskan mata idan suka gano logon mijinki suka san yanayin sha'awarshi idan ɗan iska ne can zasu zagaye su riƙe miki wuyan miji suyi ta lalata dashi , ke kuma abarki ki zama hoto sunje sun riƙeshi sun zazzage miki shi ya dawo ya kasayi miki komai ke kuma daga nan zaki fara tashin hankali bayan ya riga ya gama horaki da irin yadda yake kwanciya dake , aikinki surutu daga nan saiki ce ai mijinki yanzu baya gamsar dake , dama sunajin haushin kin samu namijin dasu basu samu irinshi ba , naki ya iya gamsar da mace nakine yasan sirrin kwanciya da mace sunajin baƙin ciki basu samu kamar naki ba sai su koya miki bin mazan waje , daga ƙarshe kuma ya ganoki saiya sakeki kije kiyi auren kuma wanda kika aura yazo ya kasa miki irin wanda mijin da kuka rabu yake miki , kila mijinki ya saba kwanciya dake sau 2 ko 3 yadai danganta da yanayin ƙarfin sha'awarshi sai ya nemiki sau adadin lambobin dana faɗa kafin gari ya waye wasu kuma sai suyi 4 kofin haka kafin safe , kuma zai baki su lafiyayyu masu daɗewa suna miki yawo a zuciya , tou shi sabon mijin sai ya kasa baki ɗaya ƙwaƙƙwara daga nan kiji baki iyawa ki ɓallo , kina dai cin abinci mai kyau kici ki ƙoshi jini yana zagayawa ko ina a jikinki ƙarya kike kice baki buƙatar namiji saidai yanayin sha'awa kowa da irin nashi , haka zaki koma kiyi tabin maza kina ganin ina zaki samo kamar wanda kuka rabu , sai Allah yasa ki kasa samo kamar tsohon mijin naki ,
Itafa mace kamar tanda haka take horar da ita ake horon da namiji yayi mata tun tana toya waina jagwalgwalalla zata fara fiddo mai kyau , dan Allah mata mu riƙe ɓoye sirrin mazajenmu wallahi kanmu muke zubarwa da mutunci , Allah yasa mu dace.....
Jiddah taci gaba da cewa gashi kuma idan nasha magunguna ya sani duk lokacin danasha maganin mata ya kwanta dani zai faɗa , idan kukawa kikaji yana faɗin sunan kaya zakisha mamaki kodan ya tashi cikin mata ne ? Wai shi shine ɗan mai ganye idan ina so wai zai haɗamin wasu sirrika masu kyau inyi amfani dasu kuma duk haɗamata bazan iya ƙureshi ba , a yadda yakemin ma tausayi na yake fa , yana da rauni akan mace sosai , yace ita mace abun tausayi ce kuma abun daratawa ce shi yasa ko da yahaniya baya ma mace magana karta firgita , { amma saida Sultana ta ƙure Dikko harya ke dukanta....} tasha dai rashin wayanta ta ƙoshi Mardiyya kuma ta nannaɗe a haɓar zani ta shirya tayi asibiti dan yau Dikko yace ma Jiddah karta fita yawonta yayi yawa...
Wallahi gaba ɗayanku saina sa an ɗaureku......
24/10/2019👇🏻
*JAMILA MUSA....*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 63
Bello yace kamar ya a ɗauremu ? Dady yace saboda ka lalacemin "ya a gaban idona har ina tsaye inabin layi a doka ƙaraurawa in hau saman ruwan ciki ɗiyar dana haifa , taya kake tunanin bazan sa a ɗaureka ba ? Bello yace gafara can itama ai wacce kake tunanin taka ruwan cikin nata itama "yar taka ce sakaran banza ka lalatamin duk wani tsari nawa ai duk cikar garin katsina da batsewar ta babu ubanda ya isa yasa a ɗaureni , bana ɗauruwu a wurinka kaidai sakaran banza mayen mace , to idan baka sani ba ka sani idan kuma ka sani ka ƙara sani Sultana ɗiyar Binna ce , wani irin juyi Dady yaji duniyar tayi mishi kanshi ya sara , cike da tashin hankali yace wane Binnan ? Bello yace Binna nawa ka sani ɗan uwanka da kuke Baba ɗaya dashi ƙaninka....
Saida Dady ya sakejin duniya tayi mishi ƙundubale yace Hajiyata ɗiyar Binna ce .....? Bello yace tabbas , wani irin haushi Dady yayi hafhaf kamar kare yace shikenan na kashe kaina shegiyar yarinyar nan tazo har majalissa ta sameni wai tana so taga bayan Binna dan wawanci da kidahumanci irin nawa ni idona ya rufe akan mace nace mata ai wani ya rigaki dan tuni an daɗe da tura Binna zuwa duniyar mutuwa , girgiza kai Dady yayi tare da cewa amma shu'umar yarinyar nan tacemin wane mai zarrar ne wanda yafi mace zafin nama....? Tabbas mutuwar ki ta zama dole abun kunya na rungumi ɗiyar ƙanina na farfaɗa mata maganganu masu girma na lashi bakinta na tura hannuna a cikin rigar nononta , na kamo hannunta nakai a girma na kai , idan har duniya taji wannan abun kunya sai tsinuwar mutane tahau kaina........
Wato a wancan lokacin taso na faɗa mata wani abu , tabbas nace mata ni Yayan Binna ne , tana tare da wani ƙuduri a ranta tuni tasan wani abu ko kuma wani abu ya faru ya akayi ta shigo rayuwata ..? Wannan shine abinda ya kamata na sani farko kenan kafin inyi mata hukuncin daya dace da rayuwarta , shiru yayi yana nazari zuwa wani lokaci yace an kira Sultana nan ya akayi Hafsa ta bayyana wurin a maimakon Sultana ? Sultana tace zata zo sanye da niƙaf ya akayi Hafsa ta sako niƙaf tazo....? Mu kai Hafsa asibiti saita dawo dole duk zamu samu ansar wannan tambayoyin namu.
Cikin ɓacin rai Dady ya kalli Bello yace tun can baya boka yayi magana akan Sultana me yace wanda yasa muka toshe kwalwarta a kwalba....? Cikin tashin hankali Bello yace bayan Binna yazo yana farin ciki a gidana an haifar masa yarinya mace yace nasarar rayuwa yazo mishi , na tayashi murna sosai yayin da yake cewa ya samu mai share mishi hawayenshi tabbas nasara ce tazo , sai yace kuma yanaji a jikinshi ko baya raye "yan uwanshi zasuyi alfahari da jaririyar da zai sakawa sunan mahaifiyarshi.
Na taya Binna murna sosai bayan ya tafi daga gidana nazo na sameka na faɗa maka duk yadda akayi , a wancan lokacin sai kace muje a faɗawa boka yayi bincike akan ita yarinyar , abinda boka yace mana bayan yayi bincike shine kawai a toshe kwalwar yarinya shine mafita , Bello yace da muka tambayi dalili boka yace idan yarinyar ta girma zatayi ilimi tunda Binna yana da ƙudirin haka akan ta , yarinya tana kishin mahaifinta idan ta tashi ta ganshi a harkar caca zatayi faraucin fitar dashi a caca ku kukace ya dawwama a caca da zinace² idan yana yinsu ya gama lalacewa a mantar dashi tunanin mahaifinshi bare yayi tunanin dukiyar da aka bar muku na gado...
Dady yace ya akayi tasan Hafsa ɗiyata ce ? Ya akayi tasan cewa nine baban Hafsa ya akayi ? Ya akayi Bello tasan ina tare dakai ? Bello yace bata san muna tare ba gaskiya nidai nine nayi mata waya cewa saina kasheta , shine tacemin idan na isa zan iya kasheta in kasheta a wurin fesra hotel ,
yayin da zata sauko daga napep sanye da niƙaf , muna zuwa sai muka ganka a wurin sai muka tsaya muna gaisawa saiga napep ya sauke mai niƙaf bayan dama wacce muke nema tace mana zata zo sanye da niƙaf bamu tsaya bincike ba muna ganin mai niƙaf muka rufa mata tunda dai ta sauka a inda Sultana tace zata sauka , ka tambaya lafiya ? Sai nace maka Sultana ce , kace wace Sultana sai kawai nace maka ruwana ne , kace kana sha ba tare da sanin ko wace ce ba , ni kuma naga abokin cin mushe ba'a nuna mishi sai nace maka ni kasheta zanyi bayan mun gama morewa kai kuma kace muje bayan ka kira wacce kake jira bata ɗauki wayarka ba , sai muka haɗu gaba ɗaya muka taho nan dan bamu da isashshen lokacin da zamu tsaya muyi magana mun barshi akan sai mun gama zamuyi magana , Dady yace to bana tunanin Hafsa tasan Sultana muje asibitin munyi magana daga baya...
A wahalce yace mai gida... Hawaye ya gangaro mishi daga cikin ramin kwarin idanuwan shi yace na bari kayi haƙuri insha Allah bazan sake ba , tashi Mardiyya tayi ta matsa kusa da Al ' Ameen ta kama hannunshi ta riƙe tana kuka , cikin muryar kuka tace Uncle wallahi tunda har ya dake akan Sultana wallahi kafin in bar katsina saina korata zuwa duniyar mutuwa , dakel Al ' Ameen ya haɗiye yawun bakinshi cewa karki kuskura ki fara tunkarar yarinyar nan dan wallahi idan har mai gida ya sani naki ya ƙare farko ma kenan , gara ki koyi yadda zaki kyautatawa Sultana idan har mai gida yaga kina santa wallahi sai yaso ki har cikin ransa saboda yana ma yarinyar nan soyayyar dashi kanshi baya san kanshi , yana san Sultana fiye da yadda yake san rayuwarshi , ko wane awa ko wane minti ko wane daƙiƙa wutar santa sake ruruwa take a zuciyarshi ,
Batajin magana karuwa ce mai lasi da take karuwancinta cikin tako da ƙwarewa , duk inda bakya tunani sansanin yanki garin nan tayi suna amma a ɓoye take huɗɗoɗinta , tunda ta samu ta dafe mai gida ta watsar da ko wane namiji ta koma zama gidanshi tana kwantalarshi , mafita ɗaya shine mu nemi inda Sultana take sai ki shiga rayuwarta sosai a fili ki nuna mata soyayya , a ɓoye kuma sai muci gaba da ɗirkaka mata asiri har mu samu muga mun shafe babinta daga duniyar masu rayuwa , Mardiyya tace haka zamuyi Uncle Allah ya baka lafiya ya ansa da am3n suka ci gaba da tattaunawa.
Mai gida ina ganin yarinyar nan sai an haɗa mata da roƙon Allah ko zata samu natsuwa sai inga kamar ba ita ɗaya bace ba , Ashiru ne yake magana da Dikko a waya , Dikko yace ita ɗaya ce tsabar iskanci ne kawai da raina mutane ka barta kaga yadda zan dawwarata idan na dawo , Ashiru yace to ai duk dai firgicin da nayi mata jiya wallahi yauma ta fita , Dikko yace ai dama nasan saita fita An mata halinta sai ita amma wallahi nine maganin rashin kunyarta , yau kuma ina taje , Ashiru yace wallahi mai gida tunda duhun asuba yarinyar nan ta tafi sabon layi can wurin one way layi ne na tsofaffin karuwai maza da mata , idan kana neman duk wani feƙaƙƙen ɗan iska daya ansa sunansa a harkar iskanci kaje wurin saika sameshi indai ya cika karuwa mai "yanci , tsofaffin karuwai ne da sukayi karuwanci shekaru da yawa da suka wuce sune suke rainon wasu ƙananan masu tasowa ,
Salati Dikko yayi tare da cewa innalillahi wa'inna ailaihir raji'un , wallahi saina zane An mata idan na dawo , wallahi ko zata mutu saina daketa saina dira kanta , cikin ɓacin rai Dikko yake magana shin mema tajeyi ne a wurin ? Ashiru yace mai gida wallahi ban sani ba , Dikko yace kenan tana nuna itafa duk duniya babu wanda ya isa ya dakatar da ita akan duk abinda tasa kanta, wallahi ׳ nine na isa na dakatar da ita duk duniya baki da mai maganinki iskancin ki saini , kashe waya Dikko yayi bayan yacema Ashiru bara zan kiraka.
Da sauri na kwanta saman gado tare da jan bargo na lulluɓe gyara muryata nayi na maida ita yanayin muryar bacci na ɗauki wayata dake tsuwwa saboda kiran Dikko dake shigowa , ina ɗauka nace kai mai zuciya ya akayi ka sake kirana bayan kace baza ka sake kirana ba tunda banda wayau ,
Murmushin ƙarfin hali Dikko yayi tare da cewa key kina tunanin zan iya fushi dake ne dama ? Wai kamar ya kakejin girman soyayyata ne a zuciyarka , An mata yanzu ba lokacin maganar so bane ina kika je ? Ni ? Na faɗa tare da dafe ƙirjina nace kaji sharri ni kuwa ina zanje bayan saman gadona , ke ina kikaje ? Dikko ina kuwa zanje bayan bacci ma nakeyi kiranka ne ya tasheni , An mata ina kikaje nace , cikin kuka nace wai wannan wane irin masifa ne bayan ɗazu wurin 3 da wani abu na dare ka kirani kuma ka tabbatar ina gida , ke ji nan na rufe idanuwana yanayin fushi ya fara hawa saman kaina kafin in faɗa miki magana mai muni ina kikaje yayi maganar cikin murya mai tada hankali , saida naji wani fitsari²n tsoro ya kamani cikin rawar murya nace ƙofar gida kawai na leƙa na dawo ,
Waye yace ki leƙa ? An mata baki so dai ki zauna lafiya ko ? Dole dai sai kin ɓatamin rai ? Nidai ko An mata ? Dikkon naki ? Haba An matana faɗamin wai meke damunki ne don Allah , duk cikin lallashi yayi maganar , shiru nayi na kasa magana ina shashshekar kuka , cikin murya maisa natsuwa yace dole dai saina dakeki zaki natsu ? Ya tambayeni , cikin kuka nace kayi haƙuri don Allah , wallahi An mata bazanyi haƙuri ba saina zaneki faɗamin ina kikaje ? Sabon layi naje , tou waya aikeki ? Babu , badai zaki kiyaye fushin mahaukaci ba ko ? Idan har kika sabar wa da kanki "yan doke²n nan ko aure mukayi hankalin baya kwanciya sai na dakeki banda kyau ne idan ina yanayin fushi kuma na faɗa miki idan na ɓaci ba nine ba , me yasa kin raini da Allah ?
Ban raina ka ba , wallahi kin raina ni har kin faɗawa duniya kowa yasan kin raina Dikko , kayi haƙuri , hmmm banyi ba kuma wallahi bazanyi ba idan dai taƙamarki taurin kai da kafiya nace miki nine kangara idan har bazaki gaji ba nima bana gajiya tunda kema so kike ki zama kamar doki ko anhauki sai an dakeki ina nan dawowa babu daɗewa...... Yana faɗin haka ya tsinke kiran.
Ajiyar zuciya na sauke tare da goge "yar guntuwar zufar data tsattsafomin a goshina bayan Dikko ya kashe wayarshi , lallai wato duk safko na su a wajen suka kwana , kaje ka dakenin wallahi bazan daina fita ba , kai ƙarewar fitar ma ai barin ƙasar kayi baki ɗaya ko kai nace karka fita ne ko karkaje ? Ɗan rainin hankali kawai ,
Abinda ya kaini sabon layi neman wanda yasan Mamy nakeyi , kuma na samu wanda suka santa , kuma na tambayesu ko akwai wanda yasan wata babbar aminiyarta amma ta ɓace kuma ni bansan sunanta ba amma nasan shaƙiƙiyar Mamy ce sosai shin ko akwai wanda yasan aminanta , lissafi akamin nace to sun san wacece aka kwana biyu bata nan ? Sai sukacemin *Raga* ce , nace tun yaushe basu ganta ba ? Lokacin da suka faɗa yayi dai² da lokacin dana san tamin waya cewa inyi sauri na samu Binna za'a kashe shi.
Ina ne iyayenta suke ne ? Na tambaye su amma sai sukacemin gaskiya Raga babu wanda yasan daga inda tazo , wata tace amma naji ance bata lafiya tana asibiti , dana tambayi asibitin cewa sukayi gaskiya basu san asibitin ba , nace to waye yace musu tana jinya a asibiti ne ? Sai sukacemin gaskiya jinyar sirri takeyi , na nemi sanin asibiti sai sukacemin wani karuwanta ne kaɗai yasan inda take , wato kamar wanda suke iskanci dai , sai anjima zaizo nima kuma anjimar zan koma , matar data tunkari mutuwarta saboda ceto rayuwata saina ganta kuma sai naje babu wanda ya isa ya hanani fita ,
Dikko daga kan Sultana wurin Jiddah wayarshi ta sauka me yasa wata ta kwana gidanshi bada izininshi ba ? Ko an faɗa mata gidanshi gidan gwamnati ne ? Ita har ta isa ta daki ƙirji tayi iskancin data ga dama ba tare da saninshi ba ? Shike aurenta ko itace take aurenshi ne ? Daga yau idan Mardiyya ta sake kwanar mishi a gida sai yaci ubanta sakarar banza wacce ƙwalwata ke ƙallon gusin.....
Jiddah tace Yaya ni kwalwata ke kallon gusin ? Dikko yace to akwai wacce nake magana da ita bayan ke ? Aike inama tantama anya kina da ƙwalwa a kanki ? Sakarar banza saboda wannan surutun banzar naki sai kin wahalar da rayuwarki , cikin kuka tace Yaya baki zakaimin ? Ba baki zanyi miki ba Jiddah surutunki yayi yawa gaki baki da sirri ko kaɗan , tou wani abu akace maka nayi ? Wallahi babu abinda akace kinyi sanin hali ne yafi sanin kama surutunki na sani zama ɗaya sai kin warwarewa mutum komai na rayuwarki anyi mutum babu sirri ina ma amfanin halinki da Allah ,
Wannan Mardiyya da kike gani sai tayi cinikin ki a gaban idonki ta sayar dake , Yaya wani abu tace wai ? Babu abinda tace nasan ke ba'a sakaki a kwana ba kinyi surutu kamar kamun hauka bare ita kuma mai wayau ta sakaki a lungu taita dukan cikinki kina bata labari , tunda Umar yacemin a gidan ta kwana nasan yau kin kwana ɗimi { surutu } wai anyi mace babu aji haba Jiddah wasu matan kamar ka biya kuɗi ka siya magana a wurinsu ni gaskiya bana san mace ba aji ki kama kanki tun kafin inyo miki abiyar zama....
Kishiya zakamin ? Tabbas wallahi aure zanyi kuma dana dawo zanyi shi in Allah ya yadda , kam bala'en nan ni zaka ma kishi ? Dikko yace tabbas kuma babu gudu babu ja da baya aure fa babu fashi ko a yadda ko kar a yadda idan dai har banyi auren nan ba tou ki tabbata mutuwa nayi......... Yana faɗin haka ya kashe wayarshi.
Dikko yana kashe waya Jiddah ta kira Momy ta fashe da kuka , cikin tashin hankali Momy tace me akayi miki ne ? Momy wai Yaya aure zai ƙara , Momy tace ƙarya yakeyi babu auren da zaiyi , cikin kuka Jiddah tace wallahi da gaske yake duk abinda yayi rantsuwa akanshi ba wasa yake ba Momy tabbas aure zaiyi , Momy tace wace ce zai aura ? Jiddah tace Momy ban sani ba kuma yace min wai kar Mardiyya ta sake kwanar mishi a gida bakiji zagin da yayi min ba har cemin yayi ƙwalta tana kallon gusin , Momy tace gidan banza gidan wofi gareshi har kema baki sake kwana ki tattaro kayanki ki taho , Jiddah tace Momy cewa zaiyi nayi yaji kuma kinsan bazai ce in dawo ba , Momy tace ki barshi dan ubanshi zai dawo ya sami ki taho , kamar dai Jiddah bata yadda ba amma ƙarshe dai ta haƙura Momy ta turo driver ya ɗauketa su Jiddah an sauka a gidan gwamnati.
Misalin ƙarfe 12:30pm na fito harabar gidanmu zanyi aike , Ashiru na gani shida wasu irin tiƙa²n mutane harda waɗanda suka zauna dani a goruba lokacin da Dikko ya saceni a wurin bikin birthday ina , shima ɗayan na sansa Dikko yaje dashi anguwarmu ranar daya takamin mage wanda nace jikinshi har wani mai² yake saboda girmanshi kamar an shafa mishi mai , ashe Ashiru ɗan ƙarami ne ma akansu , nafa firgita da ganinsu amma saina basar na kira mai ba filawowi ruwa na aikeshi , zan juya naji suna cewa aiko mun kamashi ba'a nan zamu dakeshi ba tafiya zamuyi da ɗan iska , ji nai cikina ya juya ƙulululu irin kukan nan da yakeyi idan yaji tashin hankali , da sauri na fara tafiya saboda wallahi basu da kyan gani naji wani yana cewa kun gane karmu daki Yazeed muyi masa kashedi idan mukayi saurin dukanshi mai gida zaice mun daki abokinshi kawai dai mu fara worner shi idan baiji ba sai muci uwarshi kawai.
Da gudu na shiga cikin palo har ina faɗuwa da sauri na miƙe nayi cikin ɗakina a tsorace , Kaka ma kanta da take zaune tamin magana bana jinta , ina shiga ɗaki wayata na ɗauka na fara kiran Yazeed babu ɓata lokaci ya ɗauka babu ko gaisuwa nace masa su Ashiru suna nemanka zasu dakeka fa , murmushi Yazeed yayi tare da cewa ki kira DK ki faɗa masa cewa yaranshi su fita hanyarki dake dani idan ba haka ba zaku samu matsala keda shi , nace ai nima yace zai dakeni ne idan ya dawo , Yazeed yace ba komai faɗa masa haka kawai , ba tare da tunanin komai ba na katse kiran Yazeed na kira Dikko.
Shima babu wani ɓata lokaci ya ɗauka nace Dikko ya ansa da na'am yaja na'am in a cikin murya irin ta sakakkin "ya "ya nace kaga yaranka su fita hanyar ni da Yazeed idan ba haka ba dani dakai zamu samu matsala , murmushi Dikko yayi yace wannan ba tunaninki bane yarinya ashe har yanzu kina wasa da mahaukaci to ki sani da abinda zakiyi da kanki da wanda aka sakaki kiyi komai naki na sani kuma ni halinki da rayuwarki sai in rubuta littafi akanki ,
Cikin ɗaga murya nace to me yasa suke binshi me yayi musu ne ? Murmushi mai sauti Dikko yayi tare da cewa bana cikin yanayin faɗa yanzu amma ki bari idan ina fushi saiki taɓoni ko kuma ki bari idan na riƙeki ina baki wahala ki tambayeni anan ne zan baki ansar tambayar da kikemin zararra kawai dake , kaine zararre , ai ni dama tuni na zare , Dikko yanzu me Yazeed yayi ma yaranka ne ? Duk abar maganar zare².
An mata yarana kenan wanda nakan ɓata musu a ko wane lokaci kuma sukeyin haƙuri dani , na saka baƙin ciki a zukantasu yayin da su sukeyin farin ciki , kuma suyi haƙuri basa zuciya dani , kinga su kansu suna kishina tun kafin ni inyi kishin kaina , suna jin baƙin ciki tun kafin ni inji baƙin ciki , suna tayani kishinki tun kafin ni nayi kishin naki , sunji baƙin ciki na samun kishiya a soyayyarki tun kafin ni mai san naki nayi kishin rabamin zuciyarki da kikayi gida biyu , ni ɗaya nake ko a gidanmu kuma duk zuciyar macen dana shiga bana gogewa har abadan duniya amma ke har kina tunanin jinjina soyayya ta data wani Yazeed , ni zaki ma soyayyata kishiya ko ? Hmmm idan har na barki kin huta dai² da saƙon ɗaya da tunanina kice ba Dikko nake ba. Yana faɗin haka ya ajiye wayarshi.
Cikin tashin hankali na sake kiran Yazeed bayan ya ɗauka na faɗa masa Dikko yace bazaiyi haƙuri ba , Yazeed yace sake kiranshi kice masa yayi haƙuri yaranshi su fita hanyar Yazeed , nace tou , wayar Dikko na sake kira amma sai bai ɗauka ba , nan fa na samu aikinyi ,
Har aka kawomin saƙon dana aika a siyomin ban daina kiran Dikko ba , ganin bazai ɗauka ba yasa na kunna data ta yana online kuwa kenan yaga kirana ɗauka ne bazaiyi ba , voice note nayi masa cewa Dikko kana ganin kirana bazaka ɗauka ba , ya gani kuma na tabbata yaji amma bai bani ansa ba ,
Whatsapp video call na kirashi ya ɗauka yana kwance saman gado yana cin cingom cikin salo mai ɗaukar hankali , murmushi nayi dana ga fuskar Dikko a kusa dani nace mutumina kaine a kwance haka ? Wani irin kallo yayi min amma baiyi magana ba , cikin sakin layi nace Dikko kai kana da kyau sosai wallahi kana burgeni matuƙa , har yanzu idonshi akaina yake amma baiyi magana ba yana kallona cikin wani irin yanayi , Dikko kayi haƙuri don Allah tsoki yayi tare da cewa ai kina so dai yarana su fita harkar Yazeed ko ? Nayi shiru , tunda kina san Yazeed na bar miki shi kuma insha Allah duk wani wanda ke ƙasana bazasu sake rabaki da Yazeed ba , na haƙura dake An mata na fita harkarki kuma ki goge number na a wayarki nima zan goge naki kowa yaje yayi sabuwar rayuwa ,
Dan kinga ina sanki zakiyi tamin wasa da rayuwa to na daina sanki ko diamond ce ke na haƙura dake bana so aje akaima Yazeed , yana faɗin haka ya kashe , wani irin tashin hankali naji kamar an tsinkemin jijiyoyin lumfashina , musulta irin tashin hankalin da naji akan kalaman Dikko bana iyawa , cikin kuka na sake kiran wayar Dikko amma yaƙi ɗauka wayyo Allahna kardai mutumina da gaske yake ?
Murmushi Dikko yayi da yaga Sultana tana ta kiranshi yace haba An mata ai tuni kin faɗa tarkona na , tuni na dana saka miki maitata a zuciyarki , murmushin mugunta yayi cewa bari in barki saina gasaki dayi miki rowar muryata nima yanzu zan ɗana irin iskancin da kikemin idan kikaji azaba dana dawo ke da kanki zakiy ta haɗani da Allah muyi aure , "Yar yarinya kawai dake kin maidani abokin wasanki , da girmana kin maidani kamar ƙaramin yaro in biye miki inta sakin layi ko girmana baki gani haba An matana so hauka ne .....?
Tun wurin 12 da wani abu nake kiran Dikko bai ɗauka ba har zuwa yanzu wurin 3 na kasa daina kiranshi kuma ko tausayina Dikko bayaji yaƙi ya ɗauka wayana ni kuma na kasa haƙura ,
Saida aka kira la'asar na ajiye wayar naje nayi wanka nayi sallah na shirya na fita daga gidan na nufi sabon layi.....
25/10/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 64
Lokacin dana isa sabon layi ban samu ganin matar da tacemin na dawo anjima ba , dana tambayi wacce ke bani ansar inda matar taje cemin tayi wai sun tafi wurin taron siyasa , kuɗi na fiddo a jakata saida na shaƙa mata su dai² hancinta na maidasu a jakata nace zan tafi ni suna na Sultana , kuma ni ɗiyar Binna ce ai kin san Binna ba.....? Zaro ido tayi tare da cewa Binna....? Murmushi nayi da gefen bakina tare da shanye idona na dama nace Eh nice na gajeshi masu iya magana nacewa kyan ɗa ya gaji ubanshi na gaji Binna ban gaji uwata ba na ƙarasa maganar ina yatsina fuska , jinjina kai tayi tare da sake kallona ƙasa da sama tace Binna ? Nace tabbas.
Dariya matar tayi ta zira hannunta cikin breziya ta fiddo sigari ta bata wuta , saida taja ta sosai ta miƙomin , ansa nayi ina murmushi na riƙeta a hannuna , ita kuma taci gaba da cewa lallai ai Binna namu ne , bara a kawo miki kofinshi kiyi mishi nayau tana faɗin haka tayi gaba , babu jimawa ta dawo riƙe da ƙofi a hannunta ta miƙomin cewa wannan da kike gani duk daren duniya Binna goma yake sha , kuma yabar wasiyya cewa duk daren duniya saboda san da yake ma giya koya mutu a zubar da kofin giya goma a saman ƙasa , ansar kofin nayi na riƙe a hannuna na ƙura mishi ido , hawaye naji ya cikamin ido bansan lokacin da suka fara gangarowa ba , ɗaga kofin nayi na kai bakina amma kafin in samu damar shanshi an ɓareshi , da sauri na ɗago kaina dan inga waye amma babu kowa kuma babu matar data bani kofin ,
Da sauri na kalli hannuna saboda sigarin hannuna ta cinye wutar har ta taɓomin hannu , yadawa nayi na duba mutanen dake zaune suna wasan lido nace ina matar dake tsaye a gabana da Allah , wasu ne suka ɗauketa a mota , wannan shine ansar da suka bani kawai , da sauri na rufe idona na girgiza kaina gefe da gefe na kalla ba kowa dan haka na juya na tare napep saboda wurin bisa titi ne na nufi gidan cikin ɗimuwa wato har yanzu akwai sauran masu bibiyar min rayuwata ina da sauran lale.
Kai...............Wayyo Allahna saina kasheta , shine kalmar da Dikko ke faɗa yayin da yaga hotunan "Yar matanshi ta riƙe sigari , watsi ya farayi da kaya yau sai ya koma nigeria , da sauri Dady ya dafe dai² zuciyar shi ya umarci a riƙe Dikko amma duk wanda yazo sai Dikko ya duƙe ya naɗa mishi hannu so ɗaya saiya koma da baya ya kwanta , wani irin gurnani yayi tare dayi ma Dady wani irin kallo kamar zaki ya ritsa mutum a dokar daji , cike da fargaba Dady yace ku kamamin shi , wani irin ihu Dikko yayi tare da halbin wanda yazo gaba shima ya kwanta , idon Dady cike da hawaye yace ku kwantar dashi mana gaba ɗayanku kuje , kai......... Saina kashe ku ya fara wannan zabure²n nashi taron mutane da yawa Dikko ya haukace gaba ɗaya yana saina kasheta....
Dakel aka kaishi ƙasa yana wai... Wai Allahna .... Wayyo idonshi yana zubar da hawaye yake kallon Dady duk wanda ke wurin saida Dikko ya bashi tausayi har a ƙasa harbe² yake yana An mata ni zaki tonawa asiri me yasa kike min haka saina mutu tunda baki san Dikko saina mutu wallahi , shaƙe wuyanshi ya farayi tunda bazan kasheta ba ni zan mutu kawai Dady mutuwa zanyi An matana take taɓa kofin... Sai kuma yayi ihu sosai tare da watse mutane dasu ka danne shi , Dady yace karku barshi ya miƙe danne Dikko akeyi amma abun yana nema ya gagara ,
Da ƙarfi ya miƙe ya watsar dasu ƙasa , Dady yace ku rufamin asiri ku maidashi ƙasa , ƙara kama Dikko akayi dakel aka sake kaishi ƙasa a karo na biyu cikin kuka yace idan har na mutu rayuwarki ta zama walawala duk wanda kike tunanin zaiso ki da gaske ƙarya ne nine nake sanki da gaskiya , nine kaɗai zan riƙeki da amana nine kaɗai bazan cuta rayuwarki ba haba "Yar matana karki kuskura ki bari Dikko ya fita a hannunki , birkicewa yayi yana kallon sama yace idan kina ganin munayin faɗa wannan tafiyar babu dawowa har abadan abada idan na tafi babu waiwaye ki natsu mana An mata gaki "yar yarinya ƙarama kina so ki ɓata rayuwarki wai meke damunki da Allah , surutunshi yayi yawa Dady yasa aka zuba mishi maganinshi a baki lokaci guda ya ɗauke ya tafi baccin wucin gadi...
Ganin har yanzu Hafsa bata dawo ba yasa Dady ya shaƙi wuyan Bello yace ka tabbata idan har ɗiyata ta mutu wallahi saina kashe ka har lahira ya ƙarasa maganar yana tura Bello baya , murmushi Bello yayi tare da matsowa shima ya shaƙi wuyan Dady yace ni kuma idan har wannan tsinaninyar yarinyar ta rayu sai na tona maka asiri kuma saina kasheta dan uban daya ci uwarka....
Kokowa ta rikice tsakanin Bello da Dady yayin da Dady ke cewa kai har ka isa kaci kwalar rigata kai waye ? Nan fa Dady ya ƙwance ya fara aman turanci yana zage mashayin giya ɗan wasan caca Bello ba'asan komai ba irin kan Sultana ne haka nan akai ta wanka ana zuwa makaranta , empty brain.
Rabasu akayi dakel Dady yana kiran stupid , Bello yace kai kaima stupid olowa ƙwaira dakai shima dan dai ace wani shege ne , Dady ya sake shaƙo wuyan Bello saida yayi mishi lullusar fitar hayyaci sannan yace ina Sultana take dan uwarka ? Dariya Bello yayi hihihihihi kamar mahaukaci da bakinshi daya fashe jini yana binshi yace nima nemanta nakeyi , wani irin mari Dady yayi masa tare da cewa ina Sultana take ne ? Bello yace ai kana da numberta ka kirata mana , ganin Bello zai raina masa hankali yasa yayi waya polisawa suka zo suka tafi da Bello yayin da Bello kema Dady kallon idan na fito sai naga bayanka...
Ana tafiya da Bello Dady ya fara kiran wayar Sultana , ni kuma a tsorace na shigo cikin gida gabana sai faɗuwa yakeyi kamar banda lafiya haka naji yanayin jikina suku² da sallama na shiga cikin palon gidan , Kaka tana zaune a palo tayi baƙi gaishesu nayi na wuce har zan shiga ciki Kaka tacemin "yan uwanki ne "ya "yan kawunki ne , murmushin ƙarfin hali nayi cewa sannunsu na wuce ciki da sauri.
Ina shiga na fara cire kayana bayan na gama nayi ɗaurin ƙirji dan har yanzu kiran wayar Dady bai daina shigowa ba , saida nayo alwalla na ɗauki wayar Dady cewa barka dai alawar zuciyata , murmushi yayi maicin rai tare da jinjina kanshi yace Hajiyata kina ta ina haka.....? Cike da iskanci nace ka ganni ina nan hotel tun shekaran jiya wani Alhaji ya tafi dani ana wasan danbe dani...
Shiru Dady yayi ni kuma naci gaba da cewa ko zaka zo ayi dakai ne kaga wata yazo ƙarshe , ciki² yace ummm nace tou kayi sauri ka sameni ina nan hanyar shinkafi a cikin fesra hotel ɗaki na 10 , gani nan zuwa , nace kai saurara ba zafin zuwa ba kazo da kuɗi ai zanzo dasu nace mintuna biyar na baka idan ka wuce babu kai a lissafi Dady yace to ina faɗin haka na katse kiranshi na fara kiran wayar Dikko , bai ɗauka ba kaima kayi fushi da yawa haka mutumina Allah ya sawaƙe , ina faɗin haka na ajiye wayar na kabra sallar magrib.
Mota Dady ya hau ya bata wuta ya ibi hanyar shinkafi gudu yakeyi sosai yanayi yana kallon agogo cikin ƙanƙanin lokaci ya isa dan bashi da nisa da wurin yana isa ya fara kirana a dai² lokacin dana sallame sallah na ɗauki wayar yace Hajiyata na iso , ina ka iso ? Fesra hotel ! Ina ne kuma Fesra ? Inda kika ce na sameki ? Ni ? Ni nace ka sameni a Fesra Dady ? Ashe manyan mutane ma suna ƙarya kai amma kaji kunya , da ciwo ya jinjina kanshi tare da cewa tou kina ina yanzu ? Ƙasa² da murya nayi cewa zaka ganni ne ko kaima zakayi wasan danben ne.....? Na ƙarasa maganar ina dariyar mugunta , Ey tou yi sauri ka sameni ina nan ƙofar ƙwaya mintuna shidda na baka ,
Mintuna 6 daga shinkafi zuwa ƙofar ƙwaya ? Idan ka shirya kawai ka taho idan kuma ka ƙoshi in kakkaɓe zani na in rufe abuna inyi gaba mabuƙata da yawa ai , kallon agogo yayi ya hasko tafiyar dake tsakanin shinkafi zuwa ƙofar ƙwaya yace kidai ƙara zuwa mintuna goma , bana jira , Dady yace aiko baki nemi mu haɗu ba Hajiyata , murmushi nayi tare da cewa tou shikenan indai tayin banza wulaƙanci ne albarka ma amsa ce , dariya Dady yayi mai ciwo cewa gani nan zuwa , yana faɗin haka na ajiye wayar banza na ɗauki wayata da nake kiran kowa da kowa da ita.
Yazeed na kira har ta shiga ta fito bai ɗauka ba , wai meke faruwa ne haba da Allah , shi wannan sarkin zafin kan baya ɗaukar wayana , Yazeedu kuma me ya faru dashi kardai su Ashiru sun dafe shi ? Aiko idan har sun kamashi ni wallahi basuyi min adalci ba.
Haka nan na zauna jigum ina tunanin duniya , gaskiya nima dai wasa² "yar iska ce mai lasisi , tabbas duk wanda ya ganni yasan karuwa ce ni amma har yanzu dai karuwanci bai huda jikina ba dan kunsan akwai karuwar da ka ganta kasan karuwa ce , akwai kuma wacce ko ance maka ita karuwa ce sai kace ƙarya ne nima dai yanayi na kawai zaka kalla farkon kallo zaka kirani karuwa amma sanin fili akayi min sirrin ɓoye kuma ni marowaciya ce ga mazan bariki , nayi danfara wa mazaje da dama na feshe na kwashe kuɗi na gudu , na ɗauki tsiraicin maza nayi amfani dashi wurin ansar kuɗaɗe a hannun su , naɗanyi dai suna kaɗan kasancewar shagon da muka so buɗewa na kafa ƙungiyar kwarata a halin yanzu Amisty ta fini suna a harkar bariki ni kuma nayi suna sanadin tarayyata da Dikko dan mutane gani sukeyi ni karuwarshi ce !
Hmmm nifa na buɗewa Amisty hanyar zaman "yanci , ta daina zaman karuwanci a gidansu ta dawo zama tare dani har tayi gidan kanta amma wai ni zatafi suna a harkar bariki , kiran wayar Dady ne ya dawo dani daga duniyar tunanin dana lula , ina ɗauka yace Hajiyata nazo ƙofar ƙwayar , tsoki nayi tare da cewa wai kai Dady wace irin kwalwa gare ka ne ? Ba tare dana jira ya bani ansa ba naci gaba da cewa me kuma ya kaika ƙofar ƙwaya kai da nace maka ka sameni ƙofar ƙaura ? Jinjina kai Dady yayi cikin tsananin ɓacin rai tare da danne zuciyarshi yace Hajiyata ai tsakanin nan da ƙofar ƙaura na kusa zuwa ma ,
Tou cewa nayi ka taho ? Ai nasan cewa zakiyi mu haɗu wurin shi yasa na taho yanzu haka na iso , Dady kenan nifa ina filin jirgi yanzu haka , me kikaje yi a filin jirgi ? Hoto naje ɗauka yanzu mun gama kawai mu haɗu Qerau , ina faɗin haka na tsinke wayata nayi kwanciyata.
Saida yaje airport sannan ya nufi Qerau ɗan wahalar , duk inda ya duba bai ga Sultana ba , haka ya haƙura ya tafi station yasa akayi Bello jakin duka yace duk a ɓare mishi haƙoran bakin Bello na gaba idan dai har bai faɗa masa inda Sultana take ba , Bello yace shi wallahi baisan inda Sultana take ba , Dady yace suyi ta dukanshi harsai yaje maƙabarta ya dawo... Haka akai ta dukan Bello harsai daya suma kuma basu daina dukanshi ba har ya farfaɗowa , Dady yace ka tuno inda take ? Cikin kuka Bello yace a , a , Dady yace kuci gaba saiya koma ya ɗauko kwalwar inda ya ajiyeta , haka akayi ta ma Bello gwalagwala yana zuwa duniyar suma da duka kuma yana farfaɗowa saboda azabar duka...
Su Ashiru sune suka ɗauki matar data bawa Sultana kofin giya , sune suka tafi da ita bayan sunci ubanta sosai suka ɗauki bayanai a wurinta kamar yadda da suka faɗawa Dikko ya umarcesu , bayan sun gama kuma ba sakinta sukayi ba umarni daga Dikko aka ajiyeta a wurin daya basu umarni , bayan sun gama ne suka tura mishi hotunan da sukayi ma Sultana wanda shine yace duk inda suka ganta da abinda takeyi su ɗauko mishi ita su tura mishi ,
Su Jiddah an samu abinda ake so ana wurin Momy kuma sai ƙara tunzura Momy takeyi yayin da ita kuma Momyn take ta daɗa hawa kamar kashin safe ,
Dady kuwa bayan ƙura ta lafa ya fara doke²n waya cewa a ƙara saka shi da addu'a lamarin Dikko fa gaba yakeyi , yanzu banda furunci zai kashe , shi da kanshi yake cewa zai kashe kanshi kuma yana shaƙe wuyanshi , itama Momy haka ya faɗa mata itama dai tasha kuka kamar zata mutu , kuma haka itama tayi ta doke²n waya tana faɗawa "ya "yanta mata Yayun Dikko su biyu ne wanda suke ma'auri tace su saka ɗan uwansu a addu'a.
Bayan Dady ya gama yake tambayar Dikko meya ɓata mishi rai ? Cikin kuka Dikko ya rungume Dady yace Dady nidai ka yafemin badan halina ba kayi haƙuri kabarni aure zanyi idan kana san farin ciki na da kwanciyar hankali na , Dady yace haba Babana kana ɗan yaronka zaka fara taretaren mata ? Nidai Dady a haka dan Allah , Dady yace Babana kayi haƙuri kar kayi aure yanzu lalurar mata biyu kanka baya ɗauka gaka baka da lafiya ka bari ka samu sauƙi mana ,
Ɗagowa yayi ya kalli Dady cewa amma ka manta fa lokacin Sadiyya kafin ta rasu aka fara maganar auren Jiddah nidai Dady gaskiya aure zanyi kuma saura wata ɗaya kawai na faɗa maka dan in fita haƙƙinka , Dady yace ba umarni na kake bi ba ? Kayi min addu'a dan Allah Dady kuma bana so ka faɗawa Momy tace saidai in mutu bazanyi kishiya wa Jiddah ba ,
Shiru Dady yayi yana kallon ɗanshi daya ɗauki soyayyar duniya ya tattara akanshi , kyakkyawan murmushi Dikko yayi ma Dady tare da ciro cingom a aljihun wandon shi ya cireshi a takardarshi ya rabashi gida biyu yasa rabi a bakinshi rabi a bakin Dady yana ma mahaifinshi kallo mai tattare da tsantsar ƙauna yace ai nasan ka yadda Dady shi yasa nake alfahari dake ya ƙarasa maganar yana ƙara rumgume shi , murmushi Dady yayi cikin yanayin damuwa ya fara tauna cingom in da Dikko yasa mishi a bakinshi yace ina bayanka Babana , tafawa Dikko yayi da duka hannayen shi biyu yace na gode Dady.
Shi kuma Dady shiru yayi amma bai tambayi Dikko dalilinshi na abinda yasa yake so ya ƙara aure ba , yadai ansa kuma har a zuciyarshi ya yadda amma dake bayahude ne Dadyn na bugawa a jarida babu abinda ya dameshi da wani auren Dikko kawai dai yana ganin wani ra'ayi ne nashi na daban tunda bai faɗa ba shima kuma bazai tambayeshi dalili ba , kuma bazai hana Dikkon yayi aure ba , dan sanin da yayi ma Dikko a baya babu abinda yake ɓoye mishi kamar aboki da aboki haka suke faɗawa juna damuwar junansu sakamakon Dikko yanzu daya fara zurfin ciki , ajiyar zuciya Dady ya sauke yabi Dikko da kallo shi baya gajiya da kallon Dikko saboda soyayyar da yake mishi ,
Bayan sati 4,
Abubuwa da dama sun faru , kuma duk cikin kwanakin nan babu ranar da bana fita kullum rana saina fita kuma kullum sai anyi hotuna an turawa Dikko , kuma ni ina kiranshi kullum baya ɗaukar waya , nadaiji babu daɗi kuma inayi tunani sosai nakan tuno masu abubu sai inyi murmushi.
Inna har yanzu basu dawo ba , tana can ita da mijinta sunma bar Dubai sun ƙara gaba abunsu , kullum sai sunyi waya da kaka ni kuma sai lokaci² nake kiiranta mu gaisa dan idan ban kirata ba bata kira tana daiyin kara haka ta fulani saidai ta kira mahaifiyarta kuma idan ta kira bata cewa ina Sultana ,
Al ' Ameen ya samu sauƙi sosai an sallameshi daga asibiti ya dawo gidan gwamnati da ƙudurika da dama a zuciyarshi , kuma har yanzu Mardiyya tana nan bata tafi ba ,
Jiddah ma tana wurin Momy har yanzu bata koma gidanta ba , kuma tuni Umar ya biga waya ya faɗawa Dikko Jiddah tayo yaji tana nan gidan gwamnati ,
Hafsa ma ta samu sauƙi babu laifi an sallamota amma dake kanta irin na Sultana ne ta gagara gane yadda abun ya faru kwata² , Bello kuwa har yanzu yana can ana gana mishi azaba yanki² , Dady kuwa ido rufe neman Sultana yakeyi kuma har gidansu taje wurin mahaifiyar Dady wato kakarsu Hafsa ,
Yau tunda gari ya waye da faɗuwar gaba na tashi , idan abu na ɗauka saidai ya kubcemin ya faɗi ƙasa , ko magana akayi sai in firgita , da sauri na fito wanka zanje wurin Yazeed ne dan ya daina zuwa gidanmu saidai muyi waya kuma duk yawan kwanakin nan bamu haɗu ba dan shima yaje tafiya jiya ya dawo shine yau yayi min waya cewa na sameshi company ,
Saida nayi sallah isha'e na fara shiri , Yazeed sai kirana yakeyi kila na ɓata mishi lokaci , ɗauka nayi yacemin kin taho ne ? Nace a , a yace ni nabar company yanzu ina tafiya zuwa G R A mu haɗu dake a wurin , idan kin hau napep wurin wanki motoci na cikin G R A za'a ajiyeki , nace sai nazo ina faɗin haka na ajiye waya naci gaba da shiri ,
Ina gamawa na fice babu wanda ma yaga fita ta a gidan ina fitowa na samu napep na faɗa mishi inda zanje mukayi ciniki na faɗa yaja muka tafi ,
Da sauri ya sauko daga saman gado jin wayarshi tana ringing kuma ya ajiyeta nesa dashi , kafin ya isa inda wayar yake harta tsinke yana isa wurin a dai² lokacin da wani kiran ya sake shigowa , ɗauka yayi tare da kara wayar a kunnenshi mai gida tana nan cikin G R A , baiyi magana ba ya tsinke wayar , makulin mota ya ɗauka ya fita daga ɗakin cikin tsananin ɓacin rai....
Hajiya nifa na kasa gane inda zan ajiyeki wurin wanki motocin biyu ne ke baki san sunan companyn ba ne ? Kiran Yazeed nayi cewa nifa ban gane ba gashi ina tare da mai napep muna ta yawo , cewa yayi in ba mai napep in waya na bashi ya faɗa mishi inda zai kawoni ,
Baya muka koma muka sha wata kwana mai napep sai masifa yakemin wai tun farko ban iya kwatance ba , da tuni nace masa majalissar Yazeed ai da baisha wahala ba , banza nayi dashi dan bana cikin yanayin fitina yau gabana faɗuwa yakeyi har yanzu ,
Mai gida yanzu napep yayi parking da ita a majalisa , kashe waya yayi har yanzu baiyi magana ba , ya tafi wurin kai tsaye zuciyarshi tana ƙara ruruwa da zafin masifa ,
A gaban wani irin makeken wuri yayi parking an ƙayata wurin da wasu irin fitilu masu ɗan bara'un haske , anyi parking motoci masu zafin bala'e daga waje har cikin wurin da aka zagaye shi da wata irin waya mai kyau amma kana ganin wanda ke waje shima na waje yana ganin na ciki , wurin ya haɗu duk matasa ne zaune a saman fararen kujerun rober wasu da ƙananan ƙofinan nan irin wanda ake shan shayin nan na maza duk shekarunsu bazai wuce kamar su Yazeedu ba , duk wanda ubanshi ya tara wasu manyan kuɗi na tashin hankali gashi ya hallara a wurin.
Mai napep na sallama na tun kari wurin kai tsaye , wurin bashi da banbanci da rana kowa yana ganin kowa haka zaka iya gane duk wanda kuka sake haɗuwa a wani wurin daban , can gefe ɗaya kuma ga "yan mata zafafa suma an parkersu sai sheƙi sukeyi dan ubansu gayunsu irin ɗaya babu wacce tafi wata haɗu suma dai cikakkin "yan iska ne kowa tasha karuwanci ta ƙoshi duk "yan yara ² ne sunsha atach sunci bilicing har sunce wayyo Allah sai jin kansu sukeyi ,
Amma ina shigowa wurin wallahi duk macen dake wurin saida ta shiga taitayinta , gaba ɗaya wurin ya anshi ƙamshina ya fara yawo zuwa cikin ƙoƙofin hanci duk wanda ke wurin , ba mazan ba suma kansu matan na zama abun kallo a wurinsu , wurin Yazeed na nufa amma kafin in ida isa tuni ya shigo a haukace wurin da mota , motocinsu Ashiru a bayan tashi ,
Gaba ɗaya wurin ya karaɗe da hayani haba DK kowa DK yake faɗa yana magana da turanci , ɗan duniya uban Yazeed zaici amma sai yayi murmushi a dai² lokacin dasu Ashiru suka fito daga cikin motocinsu fuskar kowa babu imani ,
Da sauri na juya zan fita amma Dikko yace Ashiru riƙemin An mata karka barta ta fita wurin nan , da gudu na wuce Ashiru cikin hayani Dikko yace na rantse da girman Allah idan har ka barta ta fita zakaji ni da ɗaci , tsoro ya kamani a dai² lokacin da Dikko ya taɓa Yazeed amma ba dukanshi yayi ba yanayin dana ganshi na firgita matuƙa , ga Ashiru ya ɗaure fuska kamar bai sanni ba dole na kama kaina na tsaya nabi Dikko da kallo.
Yazeed har so nawa nace bana so kana tara mun mata a wurin nan ne wai ? Shima kanshi Yazeed zufa ke zobo mishi kanshi ƙasa ya kasa magana , murmushi Dikko yayi tare da cewa ba abinda zan maka idan har nayi faɗa dakai akan mace ni na zama sokon namiji , salon soyayyata a zuciyarta baya buƙatar dukan abokin takara wurin lashe zuciyarta , gani gaka ga An mata macece ita kuma zuciyarta tana da rauni na baka dama dani dakai kowa yaje yayi fira da ita ta bani lokaci naje kaima ta fitar maka da lokaci kaje na baka nan da wata ɗaya idan har ka samu ƙarɓuwa a zuciyarta na baka ita duniya da lahira amma karka sake fiddota waje , yana faɗin haka ya ciro hula daga saman kanshi irin tashi da kwakwar nan ya goge ma Yazeed zufar dake saman fuskarshi bayan ya goge mishi ya kamo hannunshi ya ɗora mishi hular a hannunshi , Yazeed yabi Dikko da kallo , duk saida yabi abokansu ya gaisa dasu sannan yaja hannuna ya sakani a mota yana cewa muje in baki tsaraba..
Ya faɗi tsaraba yana min kallo mai nuni da kasheki kaɗaine bazanyi ba , zagayawa yayi ya shigo cikin motar ni kuma na fashe da kuka , murmushi yayi tare da cewa baki farin ciki na dawo lafiya ? A dai² lokacin daya fara tafiya da mota , ni kuma naci gaba da kuka yace wallahi ki rufemin baki yayi maganar yana kallon madubi ko su Ashiru shi suka biyo , tsayawa yayi ya sauke gilashi yace Ashiru kuje kawai zamuyi waya , banji abinda Ashirun yace masa ba naji yace a , a barshi kawai amma dai goruba zanje yanzu ,
Yana faɗin haka ya ɗage gilashin yana cewa An mata kinsan bugun rabani da yaro ? Kuka nakeyi har yanzu banyi magana ba , Dikko yace wallahi yau mai ƙwaceki a hannun majnun { mahaukaci } sai Allah kawai miƙomin wayata inga waye yake kirana , ɗauka nayi na miƙa mishi , Jiddah ya faɗa tare da cewa lafiya ita kuma wannan ? Yayi maganar yana ɗaukar wayar yace inajinki , banji abinda tace ba yace Ey naje zance yana faɗin haka ya ajiye wayar yana cewa wallahi An mata yau na raina miki wayau , aini ko mace ce banga ranar da zanbi namiji ba ,
Namijin mi Allah na tuba ina mace ? Namiji ma ya biyoni yana so ai sai yaga yanga da kisisina , macen da aka santa da kwarkwasa da ƙwalisa aji da ɗauka kai ke kuma gaki nan sake dan wawanci kin taho kin biyo namiji sakarar banza dake da baki san namijin so ba , wallahi ni da macece ni dana ba maza azaba ko zance namiji yaje wurina dan ubanshi saina daɗe ban fito ba dan yasan yes wannan tasha banban da sauran mata a cikin mata dubu sai yasan ni ɗin ta daban ne , kuma in fito ina isa ina riƙe aji , namiji yayi magana goma ansa ɗaya zan bashi , nidai a tsarina ina mace ko driver bana yadda Yazeed yayi min bare dan ubanshi harya ɗaukar min jakata , ashe hakanan nake tun ƙaho "Yar mata tana da class nan ma ashe zero kin ban kunya kuma kinci baya , saboda Yazeedun banza da wofi kika hau napep ƙarshe ya wulaƙantaki yayi miki masauki inda suke ajiye karuwai nan yace ki sameshi ke kuma wawiyar kika kama hanya kika taho wallahi ji nake kamar in wurgaki waje in take ki da mota ki mutu in huta da takaici , mtsww haba inama amfanin mace ba aji ?
Gunguni nayi mishi yace me kika ce ne ? Shiru nayi ban sake magana ɗaure fuska yayi cewa bari haushinki nakeji da yawa wallahi , tsoki nayi cewa to ai sai ka kasheni nayi maganar ina miƙa mishi jikina wani irin mari yayi min wanda yasa na ɗauke lunfashina lokaci guda...
26/10/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 65
Jin nayi shiru yasa yace ki sake cewa wani abu mana marar kunya da kika raina mutane , ke "yar mitsitsiya dake nan har kin iya masifa da ƙure rai wanda idan nayi zuciya ina iya haɗiye ki ba tare da nasan naci komai a bakina ba wawiya "Yar matan Yazeed dake,
Tunda na taho daga inda naje wallahi bana tunanin kowa sai ke , na taho cikin farin ciki ina kyarma inzo in ganki amma kika lalata min lissafi , maimakon ki tareni da farin ciki sai kika tareni da hawaye.
Cikin kuka nace ba kawai dai kanajin zalinci kazo ka kamani kana ta dukana babu abinda nayi maka tsabar ƙwarewa da zalinci ai dama ba so na kake ba kullum baka da burin daya wuce kaga kana zalinci na.
Haba An mata ke harni zaki faɗa ma bana sanki ? Idan har bana sanki ke har kin isa ki kalli tsabar idona ki zageni ? Na baki tayin soyayya na maimakon kalami mai daɗi sai mummunan sakamako , kicemin mahaukaci kuma ƙarshen ki wulaƙanta ni ki faɗa a gaban yara dake ganin girma na , duk a bana sanki ne kika ɗaga hannu ki zabgagamin mari na gyaleki ? Na rantse da girman Allah da bake ce kika mareni ba idan basai nabi ta kan ko waye da mota na wuce ba Allah ya tsinemin albarka , tou wai taya ma mutum zai kalleni bare kuma har yayi tunanin faɗar mummuna akaina ? Ko bakya so na ko albarkacin darajar wannan bazanci ba ? Yayi maganar yana taɓo gemunshi yaci gaba da cewa ba'a zagin mutumin daya ajiye shi amma ke sam baki da lissafi.
Shashshekar kuka nayi ina cewa kana so na kake dukana ? Har so biyu ka dokeni , kaji min ciwo a gefen fuskata ka farfasa min jikina wannan duk soyayya ne ? Ai na faɗa miki kema so kike ki zama kamar doki ko an hauki sai an dokeki har so nawa na faɗa cewa bana san kina fita ai ke sai kin fita ki nunamin kunne ƙashi gareki ai dai yau jikinki zai baki labari...
Wayyo Allah dama nasan wallahi ba so na kake ba yauma dukan nawa zakiyi ? Duk duniya zuciyata da kwakwalwata ko Dikko basu sani ba sai An mata , haka wayata ma bata san wani Dikko ba itama kanta An mata ta sani amma Dikko ke amfani da ita , ki ɗauki wayata password ina ki rubuta Dikko wallahi zata ce miki a , a amma kina rubuta An mata saita buɗe miki ,
Banda hoton komai a wayata sai doki amma zuwanki yasa na zama zararre ki duba ki gani babu hotunan kowa a wayata na mace sai naki , duk inda kika shiga a wayata An mata zaki gani amma wallahi yau mai ƙwaceki a hannuna sai Allah addu'a ɗaya zaki dage kiyi shine Allah yasa har in gama dukanki ina cikin hayyaci na...
A dai² lokacin daya shigo kwanar da zata sadashi da gidanshi tunda ya shigo santar ya kwace da gudu na tashin hankali kamar zai tashi sama motar har wani lilo take ya danne horn , gabana sai faɗuwa yakeyi cikina sai juyawa yakeyi hawaye kuma basu daina zubowa ba , koda muka iso har an buɗe get in hancin motarshi ya saka ya raba get in biyu ya sauke gilashin motar cewa kai Amadu zo nan...
Da gudu yazo Dikko yace kai buɗe nan baya ka ɗauki wata foodflarks na nan kaje ka samun murfinta , matsawa yayi ya buɗe ya ɗauka yace mai gida ai ba'a siyar da ware² a idan za'a siyar da murfin tou dole da uwar ake siyarwa ba'a rabasu , ta cikin madubi Dikko ya kalleshi yace ni ba abinda ya dameni murfi kawai nake so ka samomin irinshi.
A tsorace na kalli Dikko murmushi yayi min tare da ɗaga min gira yana min kallon rainin wayau ya taka motar muka shiga cikin gidan da gudu , gidan an ƙara mishi wani irin girma na tashin hankali an maidashi gidan "yan gayu anyi mishi bene hadaɗɗe gidan ya ginu sosai gwanin burgewa amma ba'a gama aikin ba , ko me yasa yake sha'awar sissiye maƙota yayi gini......?
Malam Amadu yace mai gida wallahi ba'a siyar da murfi , da sauri Dikko ya fita daga cikin motar bayan yayi parking ya koma wurin get , Amadu na ganin Dikko ya fito a hayaƙe ya wuce da sauri yabar gidan yana kallon rigima irinta Dikko ya za'ayi wai ya samo murfin wannan abun ne ? Ko a kasuwa ba'asiyar da ware² to kodai mai gida yana so yaɗan sha iska ne da macen daya zo da ita shi yasa ya korashi ? Saida ya kalli kular ya kallo gidan da Dikko ya rufe get in da kanshi !
Cikin tsananin ɓacin rai ya dawo da sauri na fito daga cikin motar faɗuwar gabana ya ƙara tsananta yayin da Dikko ya ɗage but ya ɗauko wata irin zureriyar dorina irin wacce ake bugun dokuna da ita yace wuce muje , cikin fargaba nayi gaba Dikko ya biyo bayana ina tafiya ina waiwayenshi , cikin hayani yace ki kalli gabanki ki daina kallo na ya ƙarasa maganar yana zazzaro min duk iya girman idanuwan shi.
Wata irin kyarma na farayi ta tsoro na shiga cikin palon na samu wuri na rakuɓe kamar asirin mayya ya tonu , shima wuri ya samu ya zauna a gajiye tare da cewa zo nan , ƙin tafiya nayi kamar banji shi ba , bakiji ina miki magana ne ? Basarwa nayi na nuna mishi ƙangara da yarinta , cikin hayani yace idan na sake cewa kizo baki zo ba saina tuɓe miki kayan jikinki zan zaneki ,
Kamar ina iyayin wani abu nace ai sai kazo ka tuɓemin dama tuɓeni kake so kayi shi yasa kazo dani ko ni zaka nuna ma hauka ? Kai kaɗai ne mahaukaci kowa mahaukaci ne ? Naci gaba da zagin Dikko yace dama nan nake so kizo , ajiye dorinar yayi ya cire belt yazo yaci gaba da zabgamin shi kamar yana dukan "yar shi yana dukana yana cewa zaki sake zagina ne ? Cikin kuka naci gaba da zaginshi ina Allah ya isa mugu munafiki azzalimi ,
Yanayin fushi ya fara zuwa ki daina zagina....? Ya ƙarasa maganar yana rufe idonshi daya rufe ido komai zai iya faruwa , cikin kuka na matsa daga wurin da sauri nace yi haƙuri don Allah kayi haƙuri 🙏🏻 kafin in rufe bakina ya fara zabura cewa saina kashe ki.......
Cikin ruɗewa na fara gudu zan fita waje amma kafin in fita har Dikko ya ɗauko wata wayar wuta da aka sauke ƙasa ya wurgota ta naɗoni ya fizgo da ƙarfi na faɗi ƙasa ya jawoni na dawo cikin palon , saina kashe ki tunda kin rainani , dorunar ya ɗauka yaci gaba da dukana zaki sake zagina ko bana nan ? Yaya dan Allah kayi haƙuri zaki sake fita idan nace bana san abu zaki sakeyi ko bana nan ? Wallahi na bari ƙarya kikeyi sai kin sake kawai kasheki zanyi inje in wurgaki a ruwa ,
Malam Amadu kuma ganin Dikko ya rufe gida ya lura kamar baya hayyacinshi sai yanzu ma ya gane Sultana ce bayan yayi dogon nazari , da sauri ya fiddo wayarshi ya fara kiran Ashiru , da farko Ashiru kamar bazai ɗauka ba dan yasan dama Amadu zai ce masa mai gida yana dukan Sultana ne shi kuma yana so Sultana taji yadda Dikko yake yarinyar bata da mutunci kwata² ga raini ga rashin kunya yauko zataci ubanta tunda ta raina mai gida , har wayar ta tsinke bai ɗauka ba Amadu ya sake kira saida ta kusa tsinkewa Ashiru ya ɗauka yace ya akayi ne ?
Amadu yace mai gida ya rufe gida kuma ya aikeni wai na nemo mishi murfin kula kuma kamar yana yanayin fushi yazo da Sultana , Ashiru yasan komai dan haka yace to ka sani ko soyayya sukeyi ne ? Amadu yace duk dai yanayin fushi da farin ciki irinsu ɗaya a wurinshi bana tunanin soyayya da Allah kuzo , Ashiru yace ai kaima namiji ne ka shiga ka bashi haƙuri dan yacemin yau sai saɓa mata kamannu ai ta raina mutane barta taci ƙaniyarta yana faɗin haka ya tsinke kiran...
Bayan Ashiru ya ajiye wayar yace kai gaskiya fa za'a iya samun matsala kunsan mai gida matsalarshi da yake duka yana buga mutum da wani abu , itafa ba namiji bace ba duk da bana tunanin zai bata wahala sosai kai ku tashi mu tafi kada rayuwar yarinyar nan ta samu matsala dai , gaba ɗayansu suka fito suka taho goruba cikin motocinsu ,
Zuwa wannan lokacin ni kuma Dikko tunda ya ɗaga ƙafa zai takamin wuya ya kare in mutu kamar yadda yace na riƙe kafarshi na kalli idonshi cikin kuka nace karka kasheni ina sanka don Allah , murmushi yayi tare da takani da ƙafarshi a hankali yace ƙarya kike , da gaske nake ina sanka wallahi , duƙawa yayi ya ɗagoni daga ƙasa ya rungumeni yace da gaske kina so na An mata ? Cikin kuka na ƙara rungume Dikko kaina kamar zai ɓare saboda ya buga min a bango yayi wasan kura dani ya bani wahala sosai duk jikina ciwo yakeyi kamar jirgin ƙasa yabi takaina ya wuce , kwantawa nayi jikinshi sosai ina kukan wahala.
A dai² wannan lokacin da aka fara dukan gida ni kuma daga nan ban sake sanin abinda ake ciki ba , cire Sultana ya farayi daga jikinshi amma ya kasa , An mata tsaya inje inga waye , ina Sultana ta tafi batajin Dikko dakel ya ciro wayarshi daga cikin aljihu saboda cakumar da Sultana tayi mishi Ashiru ya gani yana kiranshi , bai ɗauki wayar ba yace An mata sakarni in buɗo gida , tuni Sultana ta daina motsi dakel Dikko ya ɓanɓareta daga jikinshi ya kwantar da ita ƙasa har yanzu hawaye bai daina fita daga idonta ba amma gaba ɗaya ta tsaya ,
Fita yayi daga cikin palon yazo ya buɗe gidan , Ashiru ya gani tsaye yace ya akayi ne ? Ashiru yace naji shiru ne nace bara inzo inga lafiya ? Lafiya lau Dikko ya bashi ansa , Ashiru yace mai gida to ina Sultana take ne ? Tayi bacci , Ashiru yace bacci ? Umm ya bashi ansa da kanshi , ɗan gyarawa Ashiru yayi yace tou amma ai kayi haƙuri ko ? Na daketa amma kaɗan yayi maganar yana yatsina fuskarshi ,
Ashiru yace mai gida kuma duk da ka daketa sai tayi bacci ? Murmushi Dikko yayi tare da cewa ko ina cikin yanayin fushi nasan abinda nakeyi naso na bata gwalagwala amma sai tayi sauri tace tana so na , wannan kalmar ya ceceta daga azabata kuje kawai zanzo idan na maida ita gida , Ashiru yace bara dai mu jiraka daga ciki , ba tare da Dikko yayi magana ba ya dawo ciki ya bar musu gidan buɗe ,
Ɗaukar Sultana yayi ya fito rungume da ita a jikinshi ya kaita mota , idan mutum ya suma a wurin faɗa ko duka ba'a fesa mishi ruwa , idan mutum ya suma a ruwa ba'a zuba mishi ruwa saidai a buɗe bakinshi a busa mishi lumfashi idan kuma yasha ruwa sosai sai ake danna ƙirjinshi a hankali , idan kuma mutum ya suma a faɗa ko ana dukanshi firfita ake mishi , idan mutum ya suma haka nan babu gaira babu dalili shine ake yayyafa mishi ruwa.
A mota Dikko ya riƙe ruwa a bakinshi ya fesawa Sultana tunda ita dai ba lokacin daya doketa ta suma ba tana kwance a jikinshi ta ɗauke , ajiyar zuciya ta sauke ta sauke a wahalce , rufe motar yayi ya zagaya ya shigo ya rufe , ba tare da yayi magana ba ya tada motar muka fita a gidan.
A waje yaga Amadu tsaye da kular daya bashi ya samo mishi murfinta , yana ganin fitowar Dikko yayo wurin cewa mai gida ba'a samo ba , ba tare da Dikko ya kalleshi ba yace maidata inda ka ɗaukota , buɗe bayan motar yayi ya ajiye ya rufe mukayi gaba su Ashiru suka rufo mana baya ,
Har muka isa gida babu wanda yayi ma wani magana , fita nayi daga cikin motar dakel banyi magana ba , har zan wuce yace An mata zo , dawowa nayi banyi magana ba na tsaya , baki gode ba ? Nayi shiru , shigo , komawa nayi cikin motar a wahalce na zauna , rashin godiya ba ɗabi'a mai kyau bane dana kawo ki gida ai sai kicemin kin gode waike baki iya irin ɗan makircin nan na mata ba ? Gaskiya aikin yawa zaimin in koya miki hankali kuma in koya miki zaman takewa na rayuwa ya zama dole ki koyi kissar zama dani danni bazanyi haƙuri dake ba ke ya zamar miki dole kiyi haƙuri tunda nine samanki fita ki ban wuri ,
Ƙoƙarin fita na farayi yace kuma tafiyar zakiyi da gaske ? Komawa nayi na zauna , kwantar da murya yayi sosai yace kin yafemin ? Da kaina na bashi ansa Eh , zaki aureni aiko ? Shiru nayi ina nazari , yaci gaba da cewa insha Allah ƙarshe watan nan zamuyi aure kuma idan munyi aure bazan miki ko kallon banza saidai ki anshi hukuncin ki a gado , wannan dukan insha Allah shine na ƙarshe bazan sake ba abinda yasa ma na dakeki nayi rantsuwa so adadin da bazan iya gane ko so nawa na rantse ba, ina sanki har abadan duniya bazan taɓa goge ki a zuciyata ba , kuma ai kema kina so na ko ? Yanzu ma da kaina na bashi ansa Eh , ngode zanzo da safe insha Allah kije , fita nayi ina masa godiya kamar yadda yace na wuce ,
Cike da tausayi Dikko yabi Sultana da kallo a bayyane yace duk wannan ɗa'ar wallahi ta banza ce bazata bar abinda take ba , motarshi yaja ya fita daga cikin gidan yana mai ƙarajin soyayyar An mata a zuciyarshi.
Tsaye nayi a gaban madubi bayan na fito daga wanka ina kallon yadda Dikko ya farfasamin jiki sahun bulala babu inda bai fito ba , a fuskata kuma har yanzu akwai sahun marin da yayi min , murmushin ƙarfin hali nayi tare da cewa saidai ka kasheni wallahi bazan daina fita ba idan har baza ka gaji ba nima bazan gaji ba.
Washe gari da wani irin masifar zazzaɓi na tashi ko sallah asuba kasawa nayi ina kwance a gado na rasa abinda yakemin daɗi har 11:15am , ga gidan namu yau cike yake baƙi "ya "ya da jikoki sai hayani sukeyi ɗan uwan Inna zai dawo daga tafiya shi yasa suka taho tararshi , dan abinda na fahimta shine gaba ɗayan ragamar su bana tunanin akwai wani mai kuɗi idan bashi ba ,
Murmushin ƙarfin hali nayi yayin da naji murya wata mata akan ita babu yadda za'ayi a cuci rayuwata a gauraya mata zuri'a da jinin Aliyu , sunan Inna ta faɗa tana ci gaba da cewa har sukayi aurensu suka gama ni ban taɓa zuwa ko anguwar daya zauna ba bare nayi tunanin taka ƙofar gidanshi , ɗan iska mashayin banza mashayin wofi duk ma wanda yasan kanshi taya za'ayi ya bari a gauraya mishi zuri'a da gurɓataccen ahali.
Maganar Kaka naji cikin rawar murya tana cewa ai hannunka dai baya ruɓewa ka cireshi ka yar ko kina tunanin asalin ɗanki yafi ita Maryam ne ? Cikin bala'e tace nidai babu wanda zai haɗamin ɗa aure da wannan yarinyar wallahi , yarinya "yar iska jahilar banza jahilar wofi , sai cin mutunci takeyi wa Babana , abun yamin ciwo amma banda yadda zanyi ,
Ci gaba sukayi da caccar Babana suna gulmarshi suka tado da tarihin auren Inna ai saboda baƙar kafiyarta taje ta aureshi ta zaɓi namiji tabar iyayenta gashi yanzu taje ta haifo ɗiya ɗaya kwantilkwal ta rasa ubanda zai aure ta , ai tasan a zuri'armu auren zuminci kowa keyi jakkar banza taje ta rasa namijin da zata aura sai ɗan caca , shima ɗayan marar zuciyar dake sakarai ne aka sakota har ya dawo ya aureta , wato mijin da Inna take aure yanzu ko ?
Kaka tace to ina za'a kai rabon Maryam ? Cikin ɗaga murya tace rabon wahala ? Hajiya ku hausawa wani abune daku wai sai kuzo kuyi abu idan ya samu damuwa wai sai ku riƙa dangana shi da rabo ne sai kaji mutum na cewa wai rabo ko na abincine sai kaje kaci ka dawo babu wani maganar rabo tsabar kafiyace saboda haka ai itama ɗiyarta ta tana da ahalin Babanta taje can suyi auren zumincisu su haifo masu bakin hali "yan caca karuwan banza.
Ikon Allah wai waye ma yace musu auren "ya "yan nasu zanyi ? Aikin banza anba makaho kyautar ido yace banso wari yake dan yasan baya samu ne nima bana san "ya "yanku kuje can kuji dasu nayi maganar a dai² lokacin dana sauko daga saman gado ina tunanin wato ita Inna auren Babana tayi "yan uwanta basa so ? Toilet na shiga dakel ina cewa mune karuwan banza karuwan wofi.....?
Ku fiddomin shi Dady ne yake magana a fito mishi da Bello , bayan an fiddoshi Dady yace ina Sultana.....? Bello yace ban san inda take ba , Dady yace wai kunji har yanzu bai tuna inda take ba , tou ku sake markaɗashi muji , saida Bello yasha juyin alalar gero akace ka gano ko tana ina ? A wahalce yace tana tare Dikko ,
Dady yace wane Dikko ? Cikin nishi yace Dikko U DK , Dady yace kai kana da hankali kuwa ? Idan har ka bari DK yaji ma kana danganta shi da wannan yarinya tou ka sani saiya yanke maka harshe wallahi , ko kana tunani DK zai saurare ta ne ? Bello yace wallahi yana tare da ita , kuma tana zaune a gidanshi na goruba road ,
Duƙawa Dady yayi kusa da Bello yace ya akayi kasan yana tare da ita bayan shi kowa yasan baya harkar mata , murmushi Bello yayi ya fara cewa.
Bincike na ya nunamin cewa tana zaune a gidanshi bayan dogon lokaci dana ɗauka ina nemanta , duk inda naje bata nan nasa an kirata da wayoyi da dama daga mutane daban² amma duk wanda ya kirata saita banbanta inda take ,
Da naga rainin wayan nata yayi yawa saina duƙufa wurin ganin na samota ko ta halin ya ya ! Nayi binke a wurin ƙanin mahaifinta bayan nayi masa ƙarya cewa zan haɗa kan "ya "yan Binna ne a wuri ɗaya shine yacemin baisan inda suke gaba ɗayansu ba , Sultana dai da tana nan amma wasu ke memanta saita bar wurinshi ,
Bayan an kwana biyu na sake komawa na tambaye shi ko masu neman nata sun sake dawowa ? Sai yacemin kullum sai sunzo yauma zasu zo ? Ban daɗe da zama ba muna fira da ƙarami sai gasu sun sake dawowa , drivern DK ne a da amma a halin yanzu sun rabu kuma bansan abinda ya rabasu ba ,
Bayan sun gama bincike² n su naje muka gaisa dashi Al ' Ameen nace masa lafiya kake neman Sultana ? Kai tsaye yace matar Dikko tasa a ɗauko ta kuma a halin yanzu sun gano tana zuwa erudite idan ta tashi tana zuwa islamiyya daga nan sai a nemeta a rasa ,
Tunda naji tana zuwa Erudite na ɗanawa wurin tarkon , tun safe nake zuwa ina zama a wurin bana ganinta washe gari dana koma sai naga DK ya kawota da kanshi a mota , daya sauketa ya tafi sainabi bayanshi naga ya koma goruba road mai gadin gidanshi shi ya tabbatar min da Sultana tana zama a gidan.
Tashin hankali shine abinda Dady ya faɗa tare sa cewa wallahi bata taɓuwa a bayyane dole wurin boka zamu koma shine kaɗai ya isa ya kashe mana ita , domin barin yarinyar nan a raye barazane ga dukiyata domun ita kaɗai tasan sirrin komai idan har yarinyar nan bata mutu ba tabbas miliyan 45 na kuɗin gado zasu fito kuma daga cikin dukiyata zasu fito , manyan gonakai dake funtuwa da wanda suke a cikin gari gidajen zama da duk sauran ƙaddarori kai haka bama zai yuwu ba ,
Da kanshi ya ɗauko kayan Bello yace saka ka tashi mu tafi idan har ba haka ba dani dakai ƙaryarmu ya ƙare , zuciyar Bello cike da kudurirrika akan Dady domin dukan da yasa akayi mishi ya saka kayanshi suka fita daga cikin station suka nufi wurin boka...
Bayan nayi wanka nayi sallah na kira Inna muka gaisa nace Inna yaushe zaki dawo ? Tacemin sai bayan wata biyu , tambayarta nayi cewa ina so nasan ya akayi kika auri Babana ? Basar da maganar tayi cewa Dikko ma ya kirani ɗazu da safe kashe wayar nayi na ƙyaleta ni bata bani ansar tambayata amma ita tana so tayi min nata maganar daya shafata !
Ina tsinke kiran Inna na kira wayar Dikko , yana zaune a palon mahaifiyar shi tana ta zageshi ɗaiɗaya akan wai bayayi ma Jiddah adalci baya cin abincin ta yace zai riƙa ci , kuma tayi maganar Mardiyya , yace taje ta riƙa kwana , wato ana sasanci dai tana ta farfaɗo matsaloli kuma akan Dikko , Dikko dai sai haƙuri yake bawa Momy ya ƙagara ya tashi yaje wurin An mata gashi harta fara kiranshi , hankalin shi yana kan wayarshi yaji Jiddah na faɗawa Momy wai tayi ma Dikko magana baya barinta baccin dare ita yana shiga haƙƙinta da yawa maganganun dai babu daɗin ji , kunya ma ta hana Dikko ya iya ɗago kai gaba ɗaya wutarshi ta ɗauke zufa yaji tana tsiraro mishi cikin jikinshi lallai yau ya saki da lamarin Jiddah miƙewa yayi zai fita itama Momy kamar saukar aradu haka taji maganar cikin karyewar murya tace Dikko jirata ku tafi , Momy ba gida zanje ba yana faɗin haka ya fice daga palon ,
A kunyance ya shiga mota kamar wani yana kallonshi a zuciyarshi yake cewa tashin kallabi amma kullu yaci amanar koko yanzu idan har Jiddah ta sameni da wannan matsalar ai zamuyi maslaha basai ta tonamin asiri ba , dakel ya ɗauki wayar Sultana cikin damuwa yace An mata da Allah yi haƙuri ganinan ina zuwa wurinki yanzu in Allah ya yadda,
Karka zo gidanmu , me yasa ? Sunyi baƙi sosai kuma banajin daɗi ? Me ya sameki ne ? Inayin rashin lafiya , sannu bara dai inzo , a , a , nidai karka zo , wani abu ya faru ? Babu , gidan ne bana so kazo , ni kuma ina so in ganki bari inzo in ɗaukeki mu tafi goruba ? Nace tou , riƙe wayarshi yayi a hannu yana tuƙi a ranshi addu'a yakeyi Allah yasa An mata ita dai bata da wannan jakancin ,
Dikko yana fita Jiddah tace ni gaskiya Momy kin barshi ya tafi baki mishi magana ba , basarwa Momy tayi kamar bataji ba tace yanzu dai tunda nayi mishi faɗa saiki tattara Al ' Ameen ya maidaki.
A hankali na fito daga ɗaki na shigo palo kuma har yanzu basu daina zagin Babana ba , shi kuma wanda suka zo su tara har yanzu bai iso ba , cikin sakin fuska na gaishe su babu wanda ya ansa inda Kaka take zaune na kalla tare da cewa zanje in dawo , Allah ya tsare hanya tayimin na fita dan Dikko yamin waya yazo.
A ƙofar gida na sameshi tunda na fito yake kallona cikin yanayin damuwa har na shiga motar , zuciyoyin kowa na ɗauke da damuwa ni ina tunanin yadda zanyi in faɗawa Dikko abinda akayi min akan zagin Babana da aibatashi da akayi , shi kuma yana jinjina yadda zai faɗamin tashi damuwar ,
Saida muka tafi yace An mata babu gaisuwa ? Yayi maganar yana miƙomin hannunshi , kamar jira nake yayi magana na fashe da kuka , murmushin ƙarfin hali yayi cewa Allah ya baki haƙuri danshi a tunaninshi maganar da yayimin yasa nake kuka , ni kuma abun duniya ya dameni ,
Har mukaje goruba kuka nakeyi kuma Dikko bai bani haƙuri ba saida nayi kuka na gaji nayi shiru dan dama da yayi parking bamu fita a mota ba , saida na gama kukan yace An mata meke damunki....? Dakel nace masa damuwa ji nake dama in mutu kawai in huta , ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa kiyi haƙuri dukkan tsanani yana tare da sauƙi , ina tare dake kuma in Allah ya yadda damuwa ya ƙare , kuma kiyi haƙuri dan idan ina damuwa ko kinayin taki zan faɗa miki nawa ki koyi riƙe damuwa biyu a cikin zuciya ɗaya , kuma ki koyi farantamin koda kina cikin damuwarki kiyi ƙoƙari ni ki bani farin ciki.
Yau idan zan faɗa miki abinda yake damuna ke kanki sai kin tayani jin babu daɗi , juyowa yayi sosai yana kallona yace An mata dan girman Allah ki daina tsokana na muna ɓatawa , ina da lalura ƙatuwa ki tausayimin ki riƙa kwantarmin da hankalina , ki kiyaye ɓatamin rai dan Allah , ki koyi riƙe damuwata kuma ki zama mai yayemin duk wani baƙin ciki idan kika ganin a yanayi mara daɗi , ni a rayuwata gaskiya ina san mace "yar gayu wayayya mai aji , wadda ta iya tarairayar namiji mace mai sirrinta sirrin ta da ɓoyemin nawa sirrin , macen da zata anshi buƙata ta kuma yi haƙuri ta biyamin ita cikin soyayya da kulawa ba tare data gajiya dani ba , ina san mace ma'aboci ƙamshi da tsabta danni gaskiya ban haɗa mace da komai ba ki zama mai kula da tsaftar jikinki domin ko wane lokaci zan iya buƙatarki kuma ina so duk lokacin dana zo ya zama na sameki a shirye dan natsuwa bata samu babu tsafta ba ƙamshi.
Har yanzu ke yarinya ce kuma kina magana irin ta yara maganarki tanamin daɗi a haka amma yanayin kallon da kikemin baya ɗaukar hankalina kallon da kikema kowa bada irin kallon nake so ki riƙa kallona ba , dole sai kin zama jajirtacciya ki zama gogaggiya wurin iya sarrafawa da kuma ɗaukemin hankalina ga tunanin kowa saike ,
Kwantar da kujerar mota yayi ya kwanta saitin zuciyarshi ya taɓa yace kinga ni ba mahaukaci bane ba amma ke kina ganin inayin ɗabi'u irin na mahaukata , murmushi yayi yace ina da lalurar aljannu basu a jikina amma suna tare dani suna shafar jikina yayin da na shiga yanayin fushi , shi yasa idan raina ya ɓaci nakeyi abu kamar mahaukaci yadda kika faɗa , amma ana ta addu'a kuma nima inayi kema ki tayani kinji "Yar matana ? Nace to , ba tare daya kalleni ba yace bara inyi waya a kawo mana abinci muci kisha magani sai in madaiki gida...
Wata irin ashariya boka ya babbaka tare dayin wani irin mazurai yana kallon su Bello......
27/10/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...*💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 66
Daga Bello har Dady duk tsoro ya kamasu kowa a ƙagare yake yaji abinda boka zai faɗa bayan sun kora masa bayani cewa sudai duk yadda za'ayi ya kashe Sultana har yanzu basu samu yarinyar ba , kuma a halin yanzu babu wanda yasan inda take ,
Dariya boka yayi sosai sannan yace nace bazan iya kasheta ba , Dady yace me yasa ? Boka yace aljannun da nake tsafi dasu basa san mutum mai cika kamsus salawat dole sai yarinyar nan ta daina salloli biyar a rana kaɗai zasu iya kasheta , ba kuma zasu kasheta ba tana cikin jinin al'ada ba dole² sai ta daina sallah sannan kaɗai su iya kasheta.
Dady yace zan baka miliyan ɗaya , girgiza kai boka yayi cewa bata ansuwa kuma bata ciwuwa kuje kawai kusan yadda zakuyi ku dakatar da ita daga sallolin dana faɗa idan ta daina ni kuma zansa aje a tsige mata wuya , cikin hayani ya ida maganar cewa ku tashi ku bani wuri......
Daga Dady har Bello da sauri² suka fito daga wurin boka bayan sun fito ne Dady ya kalli Bello yace duk yadda za'ayi ka samo mana yarinyar nan mu kasheta da kanmu idan har ka samota zan baka zunzurutun kuɗi har naira miliyan 20 , murmushi Bello yayi ya kalli Dady a ranshi yace haba ai kafin Sultana ta mutu kaine mutum na farko da zan fara kashewa , yadda ka wulaƙantani a ofishin "yan sanda kana tunanin ka wulaƙanta banza.....?
Amma a fili sai yace zan iya Alhaji amma ba zanyi aiki bashi ba , Dady yace dama ka taɓamin aiki a bashi ne ? Bello yace har yanzu ina binka cikon kuɗin shiga rayuwar Binna da nayi tun muna matasa , ina binka kuɗin asirin da nayi masa ya shiga caca ya shiga harkar mata sannan kuma har yanzu kuɗin lalata rayuwar Sultana sisi ma baka bani ba ,
Dady yace to wannan zan baka dai , Bello yace tou idan ka haɗo kan kuɗaɗen saika kawomin ni kuma a ranar zan shafe lissafin sunan ta a cikin jerin sunayen masu lumfashi a duniya , Dady yace karka damu zuwa ƙarshen satin nan zan baka , haka dai suka shiga mota suna tattaunawa....
Auntyna ga wasu kayan mata na kawo miki suna da kyau sosai kuma zakiji daɗin amfani dasu masu kyau ne jarababbu ne , Mardiyya ce a gaban Jiddah take korata mata bayani akan kayan matan data haɗo take mata bayani cewa kinga wannan sunansa babu sauran kallo , wannan kuma rantse baki da kishiya , Jiddah tace ya rantse baki da kishiya.....?
Murmushi Mardiyya tayi cikin kwantar dakai mai nuni da salon yaudara tace ai Aunty idan kikaje sayen maganin sai kinyi rantsuwa baki da kishiya ma sannan a siyar miki dashi , dan idan har kina da kishiya ba'a baki shi dan Yaya DK bazai sake zuwa wurin ta kullum yana tare dake manne kamar hanta da jini , dariya Jiddah tayi ta ɗauki maganin tace Mardiyya ina kika samominshi ne ?
Mardiyya tace ni na samo miki shi a Banbaɗawa kuma Aunty da tsada na siyo shi fa , shi kuma babu sauran kallo Yaya baya sake kallon ko wace mace saike domin kece sarauniyar zuciyarshi , dariyar jin daɗi Jiddah tayi cewa kuma kamar kinsan aure zaiyi , wata irin faɗuwar gaba Mardiyya taji lokaci guda taji wutar ganinta ya ɗauke , Jiddah taci gaba da cewa ance ma Momy yana aiki gidanshi na goruba road wai acan zai ajiye matar , gidaje biyar ya siya ya haɗe yana tayi ma amarya gyara , amma Momy tace masa ko waye ya tsaya masa bazaiyi aure ba sai yace mata dama ai ba aure zaiyi ba , kuma da tace masa ance mata yana gyaran gida idan ba aure zaiyi ba me yasa yakeyi ? Shine yace mata masu gidajen ne kawai zasu siyar shine sukace da Allah ya siya shine fa ya siya.......!
Amma ni wallahi inaji a jikina Yaya aure zaiyi , gyara zama Mardiyya tayi tare da cewa Aunty taya zaiyi aure bayan ya faɗawa Momy bazaiyi ba ? Murmushi mai ciwo Jiddah tayi sannan tace idan har Yaya yace zaiyi abu to wallahi duk duniya babu wanda ya isa ya dakatar dashi sai yayi , idan kuma yayi rantsuwa akan abu shima ko za'a mutu sai yayi , kaifi ɗaya ne shi kafin ya furta yake da wahala amma da zaran ya furta tofa ko kanshi baya saurara ,
Mardiyya tace amma me yasa baki faɗawa Momy auren nasa da gaske ne ba ? Jiddah tace Dady tayi ma magana akan ya dakatar da Dikko maganar aure ba zata yadda ayimin kishiya ba , sai Dady yace mata Babana zaiyi aure shine bai faɗamin ba yayi faɗa sosai sai Momy tace itama hasashe ne takeyi , sai Dady yace shirme kenan yama ɗauka gaske ne da yace me yayi ma Babansa aure haka babu shawara ?
Cikin kwantar da murya da ladabin munafirci Mardiyya tace to aike ma Aunty ance ki samo sparm inshi kin gagara , Jiddah tace tunda bai bani ba wai ya zanyi ne ? Tayi maganar cikin hayani , ganin haka yasa Mardiyya ta sake kwantar da kanta tace akwai wani magani da zan samo miki a tea zaki zuba mishi ko a lemu amfanin maganin nan shine yana sa sha'awa na masifa kin gane ki bashi shi da safe zaiyi ta nemanki ya kwanta dake saiki ƙi yadda kiyi ta ja masa rai , zai kasa fita ke kuma kinayin abubuwa irin wanda zasu na tayar mishi da hankali kuma ba zaki kwanta dashi ba , zaiyi ta roƙonki idan kikaji nacin nasa yayi yawa sai kice zakiyi amma da sharaɗin zai baki.....? Zai ansa kai tsaye dan yana bisa matakin da bazai iya miki gaddama ba , haka dai sukaci gaba da tattaunawa taron wawayen...
Ko da aka kawo abincin a mota mukaci saboda gidan akwai taron ma'aikata sosai sun wasu ta ko ina kowa yana aikin daya shafeshi , bayan mun gama cin abinci ya fita yacemin yana zuwa , nima ta cikin madubi na leƙa na gani an ɗaukeshi a mota sun fita daga gidan , ina ganin ya fita kuma ga mota nima na koma mazaunin matuƙi na fice daga gidan na nufi sabon layi ,
Lokacin danaje sabon layi ban fita daga cikin mota ba saboda banajin daɗin jikina , ina zauna na kira wata mata nake tambayar matar nan ko ta dawo ? Tacemin ta dawo amma yanzu bata nan taje Qerau , ni da kaina na buƙaci tayi min kwatance ina taje a Ƙerau tacemin gidan Kaka , nace wacece Kaka ? Tacemin baki san Kaka ba ? Nace ban santa ba , tacemin aiko kowa yasan Kaka garin nan , wayarta ta buɗe ta miƙomin bayan ta nunomin hoton Amisty tana cewa wannan itace Kaka , murmushi nayi tare dayi mata godiya na maida mata wayarta bayan na bata kuɗi na tunkari Qerau kai tsaye....
Ina tafiya ina tunanin Amisty har ta zama Kaka bama uwar karuwai ba Kakarsu fa ? Lallai Amity tana da sa'ar rayuwa , babu wani nisa tsakanin sabon layi da Qerau cikin ƙanƙanin lokaci na isa ƙofar gidan Amisty , taron karuwai da "yan daudu duk wata tsinana da bakin iyaye ya kama gata nan tana wurin karuwai burjik , hada wasu daga cikin "yan gidanmu suma dai duk anyi musu sign in karuwanci , Hamida na gani naga Fa'iza naga Farida naga Zainab ni da yake dai ban san sunansu ba amma duk fuskokin "yan gidanmu na gansu sunkai su goma sha wani abu ashsha...
Inayin parking na sauke glass Hamida ta fara gani na ta rugo wurina cikin farin ciki tana Sultana kece ? Murmushi nayi kaɗan tare da cewa ya gda ? Lafiya qalau me kukeyi anan naga an taraku ? Kallon taron mutanen tayi sannan ta kalleni tace ƙuru'a akeyi , wace irin ƙuru'a ne ? Gasa za'a tafi ta wasan danbe ? Idona naji ya cika da hawaye na kalli Hamida sosai nace kema hada ke a zuwa gasar ne ? Dariya tayi mai nuni da nama raina ta , murmushin ƙarfin hali nayi cewa uhum ? Tace ai nima ina jagorantar team guda ne bayan anyi ƙuru'a idan mutum yaci sai ayi masa interview idan yaci sai ayi training.
Ina ne zakuje gasar ? Na tambayeta , tacemin a gabi za'a gabatar da gasar , bin taron matan nayi da kallo na hango Safiyya yarinyar Baba Ƙarmi itama ta samu isowa Maman Affan da Maman Sadiq kallon Hamida nayi na tambayeta suma wa'ancan hadasu za'aje ne ? Tace suma suna da yaransu , amma ba matan aure bane ba ? Murmushi Hamida tayi cewa ai matan aure ma sunyi kowa yawa a ciki , to me yasa suka shiga harkar danbe bayan suna da mazajen su ? Hamida tace kowa da matsalar data kawoshi kedai bar kowa yayi rayuwarshi , jinjina kaina nayi a lokacin dana hango matar da nake nema dan haka nacema Hamida ta kiramin ita.
Tafiya tayi dan kiramin ita yayin da ni kuma nabi taron dandazon mutanen ina kallo , hankalin duk wanda yake wurin akan motar da nake yake amma tunanin kowa dai Dikko ne shi yasa babu wanda yazo , turomin matar tayi ita bata dawo ba , bayan mun gaisa nace mata kin kuwa gane ni ? Murmushi tayi cewa ya kuwa za'ayi na manta Binna ? Nace yawwa , tou wai ya akayi ranar muna tsaye sai kawai kika ɓace abunki ? Cikin damuwa tacemin wallahi yaran Dikko ne suka ɗaukeni sukaje dani sukamin tambayoyi akan abinda na sani game da Binna da rayuwar ahalinshi , abinda yasa ya shiga harkar caca da kuma bincike akan mutuwarshi , yana da wasu abokan hamayya wanda suke takon saƙa nace musu babu , sundai bincike sosai kamar an bajewa uwar san banza dilar gwanjo.
Kallonta nayi sosai sannan nace to me yasa baki dawo ba ? Riƙeni sukayi a wurinsu har sai da DK yazo da kanshi , da yazo , shi me yace miki ne ? Shima dai tambayoyi yaimin , a tambayar me ya tambayeki ? Hankalinta yana wurin taron su dan haka tacemin ki bari kawai zamuyi magana daga baya , nace a , a ki saurareni mana , dan Allah kiyi haƙuri ko kuma ki bani number wayarki idan na gama abinda nakeyi zan kiraki , wayata na miƙa mata tare da cewa kisa taki a ciki sai ki kira dan kiga nawa , haka tayi bayan ta gama ta miƙomin ta wuce ,
Fita nima nayi daga cikin motar ina tunani kafin Dikko ya gama yin bincikenshi insha Allah ni na gama da matsalata , domin ni nasan abokan takon saƙar Babana, babu wanda ya sani saini ɗaya kuma saina kwatarwa kaf ahalina kuɗin gadonsu sannan kuma da hannuna zan ɗauki fansar mutuwarshi , nayi maganar ina kallon tafukan hannaye na ,
Fitowata daga mota yasa wurin ya ɗauki ihu mutane sukayo wurina suna ta runguma ta , yayin da wasu ke tambayata inda na shige , Amisty Hafsa da duk wanda na sani babu wanda bai rumgumeni ba haka nayi ta gaisawa da mutane cikin riƙe aji da kamewa sosai yayin da wasu kuma suke tambayata inda nake zama , babu wanda naba ansa saidai nayi murmushi kaɗan ,
A wayance Amisty ta fara gabatarmin da sabbin karuwai da irin jajircewar su a harkar bariki , saidai in jinjina kai , su Nana da A ` i Karima da Saude har Asma'u babu wanda babu a wurin domin naga suma sun ƙwace da yawa , Amisty ta zama gogagga sosai a bariki ta anshi takaddun gaba da degree a wurin karuwanci taci bilicin an saka haƙorin makka ƙasa da sama , anyi hujen hanci duk dai inda kake neman karuwar data ansa sunanta a harkar karuwanci kana ganin Amisty ka tsaya , domin kallonta kanshi shima abin burgewa ne , tadai zama Kakar da gaske.
Kallon Hafsa nayi nace ke kuma kinje wurin Dikkon ne ? A sakace tace ni naje wurin daga nan bansan yadda akayi ba , nace kamar ya ? Wasu suka saceni suka kaini wani gida sukayi danbe dani , keda baki san yadda akayi ba ya akayi kika san anyi dambe dake ? Na faɗi maganar ina dafa kafaɗarta muka fara tafiya muna fita daga cikin mutane ina mata tambayoyi kamar haka , su waye suka kamaki ? Ni bansu ba kawai napep yana sauki ni a fesra suka cakumeni , me yasa bakiyi ihu ba ? Nayi ihu dan a kawomin ɗauki daga baya sai suka toshemin bakina , me yasa baki ƙwaci kanki da karfi ba ? Bana iyawa saboda suna da yawa , da suka ɗaukeki ina suka kaiki ne ? A mota suka sakani suka tafi dani wani gida , da sukaje dake ko kinji suna cewa wani abu ? Eh bana iya tunawa dai amma naji mutumin dai yana ta maganganu kuma sunanki yake kira kawai dai na manta abinda yake cewa ,
Kiyi tunani mai kyau idan har kika tuno ni da kaina zan ɗaukeki a mota na kaiki wurin Dikko kuma tsaya ki gani , wayata na fiddo na fara kiran wayar Dikko , ashe Dikko harya koma gida ya samu bana nan , ƙin ɗaukar wayar yayi na sake kiranshi tuni Dikko ya gune yana jira in dawo ya saukemin rashin mutunci.
Ganin Dikko bazai ɗauki wayar ba nace yawwa kin gane ki tuno idan har kikamin gamsashen bayani wallahi sai na kaiki wurin Dikko , murmushin jin daɗi Hafsa tayi cewa , bara in tuno muji , dafe kanta tayi tare da ƙurawa wuri ɗaya ido , tunda taji maganar zan haɗata da Dikko dole nasan zatace wani abu.
Bayan wani lokaci tace yawwa , ni kuma nace dana kiraki kince min kina Qerau , nayi maganar niƙaf da hijabi nace Dikko yana jiranki a fesra ki fara tunani tun daga lokacin da kika hau napep.
Hafsa tace bayan na sauka a napep na fiddo wayata na fara kiran wayar Dikko sai akacemin a kashe yake , ina tsaye a wurin ban tafi ba ina ta kiran wayar kawai naji an nannaɗeni ta baya , nace su waye haka ? Ina zakuje dani ? Sai wani ya mareni yace wurin ubanki zamu kaiki , na nemi a kawomin ɗauki sai suka shakeni da niƙaf suka sakani a mota ,
Sun kaini wani gida bansan ko ina ne ba , wani ne ya fara zuwa a kaina yana danbe dani , sunyi maganganu dai , tayi shiru , ƙara dafeta nayi sosai nace waccan motar kinsan ko ta waye ne ? Hafsa tace ta DK ce , nace tunda har nahau motarshi ai kinsan kusanci yakai ko ? Tacemin Eh tana kallona , nace tou duk cikar faɗin birnin katsina Dikko baida aminiyar daya wuce ni , idan nace yayi zaiyi idan nace ya daina zai daina ya yadda dani fiye da lissafinki , me kike so na roƙar miki a wurin Dikko ? Cike da zumuɗi tace ni ya aureni kawai , nace Dikko ya aureki ya gama idan har kika bani labarin komai baki ɓoyemin ba saina sadaki da Dikko faɗa ina saurarenki , saida ta sake tunani taci gaba da cewa !
Tabbas naji wani yace nine Bello aminin ubanki , kiji da kyau yadda kikamin video tsirara haka zanyi miki kema , ni na koyama ubanki iskanci amma ɗan iskan ya lashemin mata a daren farko , yace na ɗana masa tarko amma ɗan banzan ya tsallake , idan baki sani ba nine nayi asiri wa Babanki kuma nine na haɗashi yake tarayya da ahalinshi ,
Kuma yace nine nayi asiri wa Babanki ya sakaki a wasan caca nine na mayar dake kidahumar ƙarfi da yaji na sakaki kika antaya a ruɗun duniya , bayan ya gama magana yace ni Bello zanyi iskanci da "yar ka idan ka isa ka dawo daga duniyar mutuwa ka ƙwaci "yar ka a hannuna ,
Ya kira Binna daga baya kuma yadai yi maganganu sosai kuma Dadyna yana wurin , kuma mai maganar yace yayi asiri ahali ɗaya sunyi gauragauraya suna iskanci badai zan iya ganewa ba domin ina cikin wani hali a dai² wannan lokacin.
Sakin Hafsa nayi tare da juyawa nace wane irin hali kike ciki ? Juyowa nayi na shaƙe wuyan Hafsa ina cewa wane irin hali kike ciki ? Wane irin haline wannan ? Me Dadyn naki yake faɗa......? Me yace ? Nayi maganar cikin hayani sosai tare da cewa na rantse da Allah idan dai harni ɗiyar Binna ce ɗaya daga cikinsu idan ya sakeyin rayuwa mai daɗi ni ba ɗiyar Babana bace , sakin Hafsa nayi tare da turata baya da ƙarfin bala'e ta kusa faɗuwa Amisty ta riƙeta tana lafiya Mother , idona cike da hawaye nace dake da Hafsa dani gaba ɗayanmu ahali ɗaya ne ,
Gaba ɗayansu babu wanda baiji faɗuwar gaba ba , cikin tashin hankali Amisty ta cire gilashin dake saman fuskarta tana kallona , saida na goge hawaye sannan nayi murmushi mai ciwo nace kunji wani iri ko ? To nima haka naji lokacin da aka faɗamin ku "yan uwana ne , nayi kuka kuma nayi baƙin ciki kasancewa ta a cikin gurɓataccen ahali , cikin ɗaga murya sosai nace tou ku sani ni ɗin ɗiyar Binna ce kuma nima jikar gidan su Hafsa ce dani da "yan uwana da kowa na nuna Hafsa cewa tou idan baki sani ba Kakarki itace silar roshe komai , duniya ya ruɗeta yasa ta kora "ya "yan kishiyarta saboda san duniya wanda basu ji basu gani ba , ni ɗaya tak nake a wurin uwata kuma soyayyata a zuciyar Babana ba ƙarama bace ba , fashewa nayi da kuka ina cewa amma shine suka kashe Babanan, me yayi musu ne ? Cikin musulmar murya na sake cewa me yayi muku ? Mu kuma me mukayi musu suka mayar damu marayun ƙarfi da yaji ?
Inda taron "yan gidanmu suke na kalla tare da nunasu nace su kuma wa'ancan me sukayi muku ne ? Me suka tsare muku ? Shine kukayi silar maida ahalina karuwai........? Cikin ɗaga murya na cire gyalena na wurga saman mota ina cewa na rantse da Allah , na daki kaina , dai² zuciyata nakai ma duka cewa na rantse da soyayyar mahaifina idan nabar ubanki da kakarki sun huta Hafsa kice ni ba MARYAM ALIYU MUHAMMAD BINNA nake ba , ni ba ɗiyar BINNA bace ba.
Cikin tashin hankali Hafsa ta rugo da gudu ta riƙeni tana cewa Uwar ɗaki me yayi zafi haka ? Ki goge ƙudirin ɗaukar fansa a zuciyarki , cikin hayagaga nace ke ji nan kije ki tambayi wannan ruɓaɓɓiyar tsohuwar meye dalilin da yasa ta kora Binna da ɗan uwanshi daga cikin gidan ubansu , murmushi nayi mai kyau ina kallon Hafsa cikin tsananin ɓacin rai nace to ki sani nice na shirya komai ta yadda aka saceki akaje akayi wasan danbe dake , nina shirya komai kaidina da sharrina yafi alkairi na yawa , idan har kina so na goge babanki daga siraɗin ɗaukar fansa na baki daga yanzu zuwa gobe da safe kije wurin kakarki ki tambayota dalilinta na kora iyayena daga cikisu kizo kuma ki faɗamin idan kuwa ba haka ba kema zaki zama marainiya kamar yadda mu "ya "yan Binna muka zama marayu , ina faɗin haka na wuce na shiga mota nabar wurin cikin ƙunar rai.....
Daga Hafsa har Amisty sun gagara gane abinda Sultana ke nufi saboda toshewar tunani , Amisty tace taya ma zamu zama ahalinta ne wai ? Hafsa kuma tace kinji wata sabuwar barazana wai itace tasa aka saceni akayi danbe dani bayan babu abinda ta sani nice fa na bata labari yanzu bata san komai ba , tana ganin dan na bata labari zatayi amfani da wannan damar ta tayar min da hankali , can ita ta sani da ita dasu wannan ba damuwa na bane ba ,
Ina fita bakin titi wuri na samu nayi parking a gefen titi na fara kiran wayar Dady da wayar da Dikko ya bani ba tashi wacce ya bani ba , babu ɓata lokaci ya ɗauka , cikin wata murya daban nace bawan Allah sannu Allah ya ƙetare "yar ka daga hannun azzalimai , ai dama nace duk yadda za'ayi saina samu number ka na faɗa maka gadar zaren da ake gina maka na ƙarasa maganar ina fashewa da kuka ,
Dady yace wace ce ke ? Cikin kuka nace masoyiyar ka ce , wata ce take neman ganin bayan ka shine ni kuma zan tona mata asiri , dani da ita duk a bariki muka haɗu ƙawata ce kuma itama karuwa ce ana ce mata Sultana ko ka santa ? Murmushi Dady yayi yana cewa tana ina ne ? Tana ɓoye a halin yanzu domin tana nan tana nemanka ta kashe ka shine na sace numberka daga cikin wayarta dan in faɗa maka cewa ka ankare dai dan yarinya bata sanka da yawa , cikin rashin lissafi kawai Dady yace ai har yanzu Binna baida ɗiyar da zata ga bayana ke wace ce ? Nace zan bayyana amma sai ƙura ya lafa kuma karka faɗawa kowa domin da wani abokinka ta haɗa kai suke san ganin bayanka , Dady yace waye abokin nawa ? Nace bansan sunanshi ba saina siffanta masa kamanin Bello na ɗora da cewa wata rana kayi ma Sultana waya zaku haɗu a fesra hotel ita kuma ta kirashi ta faɗa mishi shine shi kuma ya bugama "yarka waya yace su haɗu a wurin dan yana jin haushinka sosai shine yasa yakai "yar ka sukayi danbe da ita kuma kaima yaso sai kayi danbe kaga "yar kace , wata irin ashariya Dady ya dandanƙara cikin jin haushi yace ni Bello zai cuta ? Amanata zaici ? Tabbas biri yayi kama da mutum domin idan ban manta ba ita Sultana tace min wai na ɗan ɓoye mota ta daga ciki dan wani ne zai sauketa , wato tayi haka ne dan kar Hafsa tazo taga mota ta ne , amma a cikinsu waye ya gayyato Hafsa , tsakanin Sultana da Bello........?
Bello ne domin shine ya shirya komai yana jin haushinka fiye da yadda baka tunani , amma Alhaji ina ganin shawara ɗaya me zai hana kawai kasa a kashe Sultana kafin ita taga bayan ka , Dady yace haka muke ta ƙoƙari mun faɗawa bokanmu amma yace sai ta daina sallah kaɗai zata iya mutuwa , shin ko zaki iya dakatar mana ita daga sallah ? Wannan ba abu mai wahala bane kauda ita daga duniya ni kaina idan ka bani izini zan iya shafe maka labarinta daga duniya guba kawai zan zuba mata a abinci taci ta mutu amma sai ka farayin wani abu akan Bello , Dady yace bari in fita daga Office sai muyi magana , godiya nayi masa tare da kashe wayata , bayan na gama na cire layin da Dikko ya siyamin na ciro layin da Dady ya bani na saka a cikin wayar da Dikko ya bani na fara kiran wayar Bello da layin da Dady ya bani , wato number da ake kirana ana cewa za'a kasheni , dan ina so nayi recording ita wayar da Dady ya bani ƙarama ce.
Tana shiga ya ɗauka sai yayi shiru dan abinda na fuskanta number da yake kiran nawa kila daban yasai layin , nace ka gudu daga inda kake ni ina san tseratar maka da rayuwar ka ne , cikin muryar shi dana sanshi da ita yace wace ce ke ? Sanin ko wace ce ni ba shine ba ina san tseratar da rayuwarka ne domin a halin yanzu suna san ganin bayanka , su waye ? Kamanun Dady na faɗa nace shine yake san cin amanarka , kun haɗa kai akan zaku kashe wata yarinya amma shine naji yana cewa sai ya kashe ka , dariya Bello yayi ni kuma na dannan record bayan nayi shiru shima cikin rashin lissafi yace wannan shine ƙudirna da ko wane wata da ko wane sati ko wane yini da ko wace awa kowace daƙiƙa saƙo da lungu rana da dare neman sa'ar mutuwarsa nake , saina kashe shi.
Yana faɗin haka na tsine kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya na nufi goruba road , zuciyar Dady tana ɗauke da gudirin ganin bayan Bello , danshi a ganinshi idan ya kashe Sultana sai ya kashe Bello sune damuwarshi kuma sune suka san komai , idan ya kashe su gaba ɗaya babu wata sauran barazana a dukiyarshi , yayin da Bello shima yake ƙudirin ganin bayan Dady zaisa Dady ya kawo kuɗin da zai kashe Sultana yana bashi kuɗin zai burma ma Dady wuƙa a ciki ya mutu shi kuma saiya ɗauki kuɗin yaje ya kashe Sultana shikenan ya rufe wannan matsala....
Tunda na shiga gidan wani irin kallo Dikko kemin fuskar nan a haɗe yana zaune saman bayan motar abokinshi , su Ashiru suna tsaye kusa dashi , jikina yana kyarma nayi parking na fito da sauri na nufi wurinshi , abokinshi na gaida sannan na matsa kusa dashi ina bashi makullin motar , bai ko kalli inda nake ba dan haka na ajiye makullin kusa dashi na koma gefe nima na tsaya kamar yadda naga kowa yayi ,
Hmmm yayi tare da ƙuramin idanuwa yana kallona cikin ɓacin rai , yakai kusan minti 3 yana kallona kuma ko ƙyabtawa bayayi dole na shiga taitayina jikina ya fara tsimama da ƙyarma tuni na sauke kaina ƙasa dan kallo ya firgitani , bayan wani lokaci na sake ɗagowa har yanzu ni yake kallo , da sauri na sake sauke kaina banma yi gigin sake kallon inda yake ba dan bana iya haɗa fuska dashi , tafiya na farayi dan komawa bayanshi ya daina ganina ta gabanshi saboda banajin daɗin kallon ,
Robar ruwa ya ɗauka a gefenshi da magani yace zo ki ansa , ban koma ta gabanshi ba na tsaya daga bayanshi na miƙa hannuna na ansa , robar ruwan ya bani maganin kuma ɓallomin yayi ya miƙamin , ansa nayi nasha bayan na gama na maida mishi robar da sauran ruwan dana rage , ansa yayi ya maida ita a inda ya ɗauka yace tafi Ashiru ya maidake gida , kwantar da kaina nayi saman motar nace ngode , baiyi magana ba Ashiru ya ɗauki makullin yace muje ,
Bin bayanshi nayi ya buɗemin gidan baya na zauna ya rufe ya zagaya ya shiga mazaunin matuƙi yaja muka fita daga gidan , tunda muka fita Ashiru kemin nasiha yana cewa wallahi yau Allah ya tsareki irin dukan da yaso yayi miki Allah kaɗai yayi iyaka dashi haƙuri mukayi ta bashi kafin ki dawo , dan Umar ya kirashi waya yace ya ganki Qerau , mai gida yace ya barki goruba saida ya turo mishi hotunanki sheda ya gani ya yadda kuma ya dawo bai sameki ba , lokacin da kike kiranshi waya tou lokacin ya hau muna ta ƙoƙoarin saukeshi , wai kema ranki ya daɗe dole sai kin fitar wai ? Murmushi nayi amma banyi magana ba , har muka iso gida nasiha Ashiru yakemin , fita nayi tare dayi masa godiya kawai na wuce ciki....
Wasu irin motoci ne parke a harabar gidanmu masu kyau da tsada , kila ɗan uwan Inna ne ya dawo , tunda na tunkaro hanyar da zai sadani da palon naji maganar shi yana cewa ƙaddara babu wanda ya gagara yahau , ni banga abin ƙin wannan yarinya ba , matar ɗazu take cewa wallahi nidai jinina idan dai ni na haifeshi bazai auri yarinyar nan ba , idan kuwa ba uwarshi bace ni tou yaje ya aureta nayi bare duniya dashi ko lahira kada Allah ya haɗani dashi , yarinya karuwa kowa yasan karuwace a garin nan gata ɓarauniya kuma daƙiƙiya kidahuma gata bata fito daga tsatso mai kyau ba , haba duk iyayen mutunci sun haɗa ɗiyansu aure da ita ?
Ɗan uwan Inna yace tunda duk kowa ya hana ɗanshi ya aureta ni zan bada ita , cikin hassada tace ai kasan ɗan tsiya bai gaji arziƙi ba kana tunanin ka haɗa ta da ko driver n ka ko mai gadinka ai ƙarshe watsa maka ƙasa zatayi a ido tace bata sansa kaga kuwa ai ba haka kaso ba , ni ba cikin su zan bata ba , Sultan ɗana zan haɗasu aure a cikin satin biyu masu zuwa , Sultan kowa ya faɗa ɗanka mai mutunci da daraja shi zaka aurawa karuwa ? Gaba ɗaya palon ya gaurare da hayani har bakajin abinda wani yake cewa ,
Hawaye naji ya ɗigomin daga cikin idanuwa na , wayyo Allahna , kila sunyi tunanin zai haɗani da mai gadinshi ko driver ko wani dai mara galihu , ɓarauniya , karuwa , daƙiƙiya , kidahuma ban fito a tsatso mai kyau ba , yace yaji kuma ya gani ɗanshi zai aureni , ya zanyi da Dikko ? Idan har kuma ban amince da maganar ɗan uwan Inna ba ance dama zan watsa mishi ƙasa a idanuwa saboda ban gaji arziƙi ba ni ɗiyar tsiya ce , jinjina soyayyar Dikko nayi a zuciyata gaskiya Dikko yana min soyayya mai girma , a bayyane nace tabbas haƙuri zanyi dakai kodan in nunawa ɗan uwar Inna na fito daga ahalin masu mutunci zanyi haƙuri da soyayyar Dikko in anshi Sultan ko baimin ba , tou tayama zan iya rabuwa da Dikkon wai ? Tun ma farko kenan wayyo Allahna......
Ji nayi gidan yana juyamin yayin da zuciyata kece cewa *DIKKO KO SULTAN...?* cikinsu wa zan zaɓa......?
30/10/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 67
Biyu zuciyata ta kasu yayin da wani sashe yake cewa Sultana kada soyayya yasa ki manta da irin halakcin da Kawu yayi muku , kuna banzace a gidan Baba babu cin yau babu na gobe bare na anjima kaf ahalin Inna sun watsar daku basa shiga sabgarku amma Kawu ya shigo rayuwarku yana taimaka muku , Sultana ya sakaki makarantar boko da islamiyya , yana tare daku yana tsotse duk wata damuwarku yau rana tsaka kwatsam sai ya nemi alfar wurinki kice a , a ? Yaga kina tangaririya rayuwa tana ta wurgel dake ance miki karuwa ɓarauniya kidahuma jahila baki fito tsatson mutunci ba amma yace yaji ya gani a hakan yana so ma ɗansa ke , ga "yar uwar Innarki sai tada jijiyon kai takeyi nata bazai auri na banza ba haba Sultana ki so sa don Allah ,
Ajiyar zuciya na sauke yayin da wani sashe na zuciyata ya fara haskomin rashin mutuncin Dikko kai tsaye yake gargaɗina da ke Sultana ina hankalinki yake so ya tafi ? Dikkon me ? Mutumin da bai san komai ba sai rashin mutunci duka zafin kai , babu dariya bare fara'a kullum fuska a haɗe yanayin fushi da farin ciki iri ɗaya , ga matsalar aljannu yanzu ƙarshe ki zaɓi Dikko wani abu ya haɗaku yayi miki tsinannen duka yace ki bar masa gidansa ina zakije a lokacin ?
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un sam Dikko bazaimin haka ba , taya ma wai zai fara korani ? Yama zauna dani babu aure kuma yayi haƙuri dani bai koreni ba sai da yake aurena zaice na tafi ? Zuciyata tace ai wancan zaman bana aure bane ba yasan zaki iya tafiya ko wane lokaci amma zaman aure daban ne haba Sultana yaufa da gobe ake magana , raba kanki da yau da gobe zama ne zakuyi daga nan har mutuwa , kifa tuno rashin mutuncin Dikko babu imani a rayuwarshi duk sissiye gidajenku da yayi har kin manta Sultana ? Babanki da kika fi so fiye da komai a duniya Dikko ya watse shi da ruwan dake kwance saman ƙasa , Babanki mai sanki ya mareki saboda Dikko ? Me ake da Dikko ...?
Zuciyata ta kasa bani mafita , alkairin Dikko ɗaya ta kasa haskowa rashin mutuncin Dikko kawai take gani yayin da take harzuƙa ni tana tambayata ina maganar ɗaukar fansar budurcinki daya kece miki ? Kin fasa ramawa a shekara biyun ne ? Abinda ya faru dani dashi a ranar daya ɓanɓare min budurci ta ƙarfi da yaji ya dawomin kamar yanzu ne yakeyin abun dani , da sauri na rufe idanuwana naci gaba da kuka zuciyata tana ci gaba da huramin wutar ƙiyayyar Dikko ,
Da sauri na goge hawayena na shiga cikin palon da sallama , gaba ɗaya na gaishe su nayi ma Kawu sannu da zuwa na wuce , Maryam yaki , kawu ya kirani , gabanshi naje na durƙusa a saman ƙafafuwana cikin ɗa'a da ladabi , Maryam ai kin sanni ko ? Murmushi nayi ba tare dana kalleshi ba nace na sanka mana sosai , idan na baki guba zaki iya ci ? Cike da ƙwarin guiwa nace me kuwa zai hana Kawu ? Ai ba guba da zanci a abinci ko abun sha ba wuta idan ka hura kace na shiga sai nayi maka godiya zan shiga cikinta cikin aminci da salama Kawu , kallona yayi sosai cewa shin wani irin soyayya kike ma "yan uwan mahaifiyarki ? Goge hawaye nayi tare da cewa ina musu soyayyar da bana iya fasalta irinshi domin su ahalin uwa jigo ne mai girma ko soyayyarsu daban yake a zuciyata , tun kafin na sansu na gansu kullum mafarkina na gansu ina alfahari dasu kuma dana kasance a cikinsu inayin farin ciki bana fatan rabuwa dasu har abada dan su ɗin mutane ne masu mutunci da nuna soyayya akaina...
Yayar Inna tace kunji makirci ko ? Tou mu bama sanki gidan uwar wa muka nuna miki so ? Ke nan "yar tatsiyar alhaki dake har kin iya makirci , bama sanki bakya sanmu amma tsabar ƙwarewa da bariki mu zaki ma bariki ? Tou uwarki ma kanta a gabana aka haifeta ki sani ni nasan kina nan kinaji kamar ki cakamin wuƙa na mutu ,
Murmushi nayi mai ciwo tare dayin magana a zuciyata nace tabbas hasashenki gaskiya ne , amma a fili nace haba Inna aiko da duniya tayi tirr da Allah wadai da dani , magana ce na faɗa mata ita da take cewa bata so na kuma a matsayinta na Yayar mahaifiyata....
Kallona Kawu yayi sosai tare da cewa shin zaki iya auren ɗaya daga cikin ahalin mahaifiyarki kuwa ? Kallonshi nayi tare da cewa me kuwa zai hana idan har ya ganni nayi masa...! Idan ya ganki kinyi masa shi kuma ke bai miki ba fa ? Karka damu Kawu nayi alƙawarin sadaukar maka da kaina duk abinda kake so zan aikata , duk uwa sunanta uwa yayar uwa da ƙannen uwa duk iyaye ne yunwa mai tsanani da kewar abinci ya kamani , tsananin yunwa bana iya tashi ko ƙwaƙwƙwaran motsi bana iyawa ina kwance ina jiran mutuwa tazo , sai ga "yar uwar mahaifiyata tazo da ƙwano riƙe a hannunta sai tace "yata na ganki kinajin yunwa sosai wannan ƙwanon yana ɗauke da abinci mai daɗi na taho dashi na baki sai kuma naji nima ina da buƙatarshi kiyi haƙuri ni naci ke kuma ki jira wani , ita tafi ni jin ƙwarin jiki tunda har tana iya tafiya ni kuma bana ko iya tashi tsaye saboda yunwa ga kuma ƙamshin abinci yana ta dakar min hanci amma sai ta hanani bayan taga ni nafita buƙata , ta san wannan abincin shine rayuwata idan ta hanani zan iya mutuwa a ko wane lokaci amma ina kallonta ta zauna ta cinye abincin nan kaf a gaban idona tayi min ƙwalele sai nayi haƙuri ,
Ina nan kwance na kusa mutuwa sai gata ta sake shigowa da wani kwanon abincin shima sai ƙamshi yake , sai ga ɗan uwa mahaifiyata shi kuma ya shigo da nashi abincin amma sai yace Sultana gashi kici amma kiyi haƙuri ya fara yami naji ance min kina nan yunwa zai kasheki shine naje na samo miki wannan kici dan ki rayuwa , saina ansa zanci sai wannan "yar uwar ta mahaifiyata ta ajiyemin nata kwanon tace kici wannan shine sabo bai lalace ba karki ci nashi zai lalata miki ciki , tou faɗamin wane zanci a ciki tsakanin mai kyau ko mai yami ? Wanda baiji tausayin karka mutu ba saiya tausaya maka saboda lalacewar ciki....?
Gaba ɗayansu shiru sukayi suna kallona babu wanda ya bani amsa , kallon Kaka nayi nace Kaka wane zan ɗauka inci a ciki ? Cikin muryar tsufa tace ai wannan lalataccen shi kawai ya kamata kici , murmushi nayi na kalli Kawu nace abun mamaki shi ɗan uwan mahaifiyata yace abincin yayi yami amma ina dubawa sai naga ya fara tsutsa shin Kaka naci kona fasa ? Kaka tace ci kuwa , Kaka sai ita Yayar uwa ta buɗemin nata kwanon sai naga farfesun kaji ne da zafi ga ƙamshi tana kici wannan ki bar wancan ? Kaka tace kajin nan kuwa basa ciwuwa a gareki , dariya nayi na kalli Kawu nace ina fara cin abincin nan kawai sai ya koma min daddaɗa ina san duk wanda zaka bani ina san sa , ina sanka ina alfahari da kaf ahalin mamana fatan alkairi a gareku iyaye na gari , 🙏🏻 ina kaiwa nan na miƙe nabar palon.
Ina shigewa Yayar Inna tace tou na gane wato habaici tayimin yarinyar can ? Nice na cinye abincin dan ki mutu tunda nace ɗana bazai aureki ba , shegiyar yarinyar makira munafika wannan idan ta auri ɗanka aisai ta rabaka dashi har abadan duniya , Kawu yace babu gudu babu ca da baya sati biyu masu zuwa zan ɗaura musu aure , ƙarshe dai saida rayuka ya ɓaci kowa ya tafi Kawu yana cewa zai turo Sultan idan Allah ya kaimu su gaisa.....
Sai ƙarfe 2:19am na buɗe wayoyina kuma a dai² wannan lokacin nahau online na cire hoton Dikko dake a d p ina na saka hoton fulawa , layin Dady na kira yana shiga ya ɗauka yace baiwar Allah tun ɗazu nake kiranki wayarki a kashe , nace bari kaidai wurin yi maka record in maganar abokinka suka kusa kasheni shida Sultana shi yasa na rufe wayar na gudu dan tsira da rayuwata yanzu na samu wuri na tsaya haka nan na gwada sa'a har ina tunanin idan na kiraka a tsakar dare kamar nayi hauka ma ,
Dady yace ai ni tuni nayi bankwana da bacci matsaloli suna neman kunnomin kai , na yadda da Bello 100% tun yana matashi nake tare dashi amma yau rana tsaka zai tattara wannan mutuntakar ya zubar , Hmmm ai danma bakaji abinda yace maka ba , kuma ya buɗe kaff wasu ɓoyayyin surruka yana faɗawa ita Sultana , Dady yace wai me yake cewa ? Ina zuwa na faɗa tare da tsinke wayar , canja layikan nayi layin Dikko zuwa cikin wayar da Dady ya bani , layin Dady zuwa cikin wayar da Dikko ya bani , bayan na gama na kirashi ya ɗauka.
Da babbar wayata na kunno mishi maganar Bello , yaji Bello yana cewa wannan shine ƙudirina da kowa wace daƙiƙa saƙo da lungu rana da dare neman sa'ar mutuwarsa nake saina kashe shi.....
Dariya Dady yayi tare da cewa shirmen banza shirmen wofi akan kaina dukiyata da iyalina zan iya shafe labarin duk wani banza daga sahun masu lumfashi a duniya , speaker na saka wayar na kara babbar wayata na fara ɗauka , Dady yaci gaba da cewa ganin bayan Bello ba wani abu mai wahala bane a wurina na barshi ne ya rayu na wani lokaci dan kauda min rayuwar yarinyar dake adawa da dukiyata idan ya aika ta zuwa duniya matacci nima saina turashi zuwa can ni kuma inci gaba da rayuwata babu maƙiya sa ido da wata baraza akan komai dana mallaka a duniya domin na kauda matsala a rayuwata....
Ajiye recording in nayi a wayata sannan nace Alhaji Bello yana da hatsarin gaske bana tunanin zaka iya kauda matsala biyu a cikin kwana biyu na mutuwarka daya ibar maka , dariya Dady yayi tare da cewa ki bani zuwa jibi zakiji labari yasha banban yayin da za'a faɗa a gari cewa wani ɗan cacan ya sake , sai kuma yayi shiru ya canja maganar da cewa ngode zan kiraki zuwa safe idan Allah ya kaimu lafiya...! Godiya nayi masa mukayi sallama na tsinke kiranshi na kira Bello.
Cikin maye ya ɗauka kuma daga jin yanayin wurin tabbas yana gidan caca , cikin muryar maye yace ke kika kirani ɗazu ? Ey nice na kiraka , na kiraki wayarki a rufe , Ey na bashi ansa , wai nine ma ɗan ƙaramin ƙwaron nan zai kashe ko ? Nace haka ya faɗa kuma haka yake shiryawa yace gobe²n nan iyalinka zasuyi kukan mutuwarka , amma wai me yasa yakejin zafinka haka da yawa ? Me kayi masa yake san ganin bayan ka ? Saurara kaji abinda yace maka.
Kunno mishi record in nayi yaji Dady yana cewa , ganin bayan Bello ba wani abu bane mai wahala a wurina , na barshi ne ya rayu na wani lokaci dan kauda min rayuwar yarinyar dake adawa da dukiyata idan ya aika ta zuwa duniyar matacci nima saina turashi zuwa can ni kuma inci gaba da rayuwata babu maƙiya sa ido da duk wata baraza akan komai dana mallaka a duniya domin na kauda matsala a rayuwata.
Cikin maye Bello yay dariya yace ni kuma a cikin daren nan zan sakashi a tarko naci gaba da farautar rayuwarshi zuwa ƙarfe 10 dai² na safiyar gobe zan kasheshi na kuma kashe Sultana saina kashe su wallahi , yana faɗin haka ya tsinke wayarshi.
Wai me kike nufi ne ? Ni zakima gwala² ne ? Dikko ne kwance a saman gado yana jawo Jiddah jikinshi tana zuƙewa tanaja baya tasha wando jeans ta haɗa da belt , Mardiyya ta bata shawara ta daina bawa Dikko haƙƙinshi dan tana sakin jiki yana murjeta sosai shi yasa ya rainata ta kame abunta ta rufe a wando , saida ta bari wasa yayi nisa taga ya fara sakin layi ta ƙwace kanta , Dikko yace meye haka ne wai ? Cikin kwarkwasa da salo mai ɗaukar hankali tana yauƙi tace ai mantawa nayi da zakayi aure saboda ni bankai mace ba shi yasa zakayi min kishiya ? Tou kaje wurin waccen zaka aura sai ta baka maganin damuwar ka , murmushi Dikko yayi tare da ƙurawa Jiddah ido yace yanzu me kike so ne ? Saida ta sake girgizawa tace idan kana so ka kwanta dani sai ka sauka ƙasa ka bani haƙuri , ba tare da Dikko ya kalleta ba yace ai gara in mutu da in baki haƙuri danni mace bata ɗagamin hankali wannan abu fa duk taimakon kai da kaine , sauka yayi daga saman gadon yana cewa idan kinji kina muradi sai ki nema na baki danni bana hora mace da tauye mata haƙƙinta ,
Juyowa yayi ya kalli Jiddah yace duk macen data san kanta tasan mutuncin kanta bata tauye haƙƙin mijinta saboda wani tunanin banza nata , ni da mace neni na rantse da Allah duk mijin daya aureni sai yaga bariki na tashin hankali , ko inuwarshi na gani saina ɗage mishi zani na bashi natsuwa , amma ke har kinma samu an nemeki zaki rainawa mutane hankali waye yace miki horon hana namiji haƙƙinshi shine ke nemawa mace mutunci da martaba wurin namiji ? Idan har baki sani ba wannan abun babu abinda ya kaishi zubar da mutum mace wurin namiji , ƙimarki da darajarki sonki yana ƙara samun nakusa a zuciyata duk macen da tayi ma namiji horon hana haƙƙi taci baya a zuciyarshi.
Misali kece kikayi tafiya a cikin tsananin rana ƙishirwa ya kamaki sosai kamar zaki mutu yayin da kikejin wannan ƙishirwar bakya tarar ruwan da zaki sha wurin kashe miki wannan ƙishirwa , kwatsam sai gashi kinga ruwa a gabanki jikinki yana kyarma kika duƙa da niyar sha sai wani ya hanaki shan wannan ruwan ya tareki , idan kina iyawa a dai² wannan lokacin me zakiyi ma wannan mutumin daya dakatar dake daga biyama kanki buƙatar ki.......?
Jiddah tace sai inyi kokowa dashi in karɓa insha , girgiza kai Dikko yayi cewa ni bana iya gudu ina shan ruwa domin nasan baya kashe min kishirwata , haka kuma bana ci idan bana cikin natsuwa domin idan har naci abu ba'a natsuwa ba tabbas zaisa min tashin zuciya ko kuma inyi amai , ni bana danne mace da ƙarfi na kwanta da ita idan har na kwanta da mace ba'a cikin natsuwa ba bana samun natsuwar da nake so , ni a wahalce ita a wahalce me kayi kenan ? Abinda nake so ban samu ba , ni ba sakaran namiji bane da zaki tsuke da jeans da belt in kamaki da ƙarfi in cire miki na afka kanki kamar wani dabba ƙarshe inji miki ciwo kinga kaina nayi ma tunda gobe idan nazo na laɓe bayanki ina buƙata ya zanyi ? Ya ƙarasa maganar yanayi mata kallon ukku saura kwata , yaci gaba da cewa amma shawara ɗaya zan baki shine ki sake masu baki shawara su koya miki yadda ake tattalin miji wannan wacce ta koya miki haka ba ƙawa bace ba tunda har ta koya miki yadda zaki nakasa rayuwar mijinki , mai maimakon ta koya miki yadda ake tattalashi....
Tun asubar farko Mardiyya ce tsaye a cikin kicin ɗin Jiddah tasha wanka tasha jagira ta ranbaɗa powder da kwalli sai zuba ƙamshi takeyi kamar amaryar sarki , ta haɗu a cikin wani dakeken tsadajjen leshi baƙi tasha atacch ta zubo shi har tsakiyar bayanta , tayi kyau sosai , gaba ɗaya gidan ya karaɗe da ƙamshin girkin da takeyi Jiddah nacan kwance saman gado kamar asara dan Dikko tunda ya fita masallaci bai dawo ba gidansu ya wuce saboda takaicin Jiddah , Jiddah tana kwance Mardiyya ta dafo abinda zasu yi kalaci ta barbaɗe da asiri ta kawo mata , jakar ta sauko ta lashe , bayan Jiddah ta gama tace ta ajiye na Yaya a saman tebirin cin abinci bayan shima na Dikko an barbaɗe da magunguna...
Misalin ƙarfe 11:40am ya fito daga wanka yana fitowa wayar shi ya ɗauka ya fara kiran An mata , lokacin da wayar shi ya shigo ina tsaye a jikin madubi dan fitowa na daga wanka kenan ina shiryawa Sultan zaizo misalin 12:20pm kamar yadda Kawu ya kira ya faɗawa Kaka ta sanar dani , a daddafe nakeyin komai dan har yanzu banajin daɗi jikina yadda ya kamata ,
Wayar yana shigowa na tsinke kiran , sake kira yayi na ƙara kashewa , kallon number yayi yana cewa haba An mata me kuma ya faru ? Bayan jiya ban dakeki ba ranar dana dokeki ma ai bakiyi fushi dani ba yi haƙuri ki ɗauki waya An matan Dikko ya ƙarasa maganar yana sake kiran wayar , wayar yana sake shigowa na ɗauka cikin ɓacin rai nace wai me ye ne......?
Ke.... wa kike ma hayani ? Dakai nake , me yayi zafi ne to ? Haba An matana , yayi maganar cikin sanyin murya , natsuwa tazo jikina na nemi haushin Dikko na rasa kamar an tambayeni nace aure zanyi da ɗan Yaya mamana a cikin sati biyu mai zuwa , yanzu ma na fitowa wanka zaizo wurina mu gaisa , wane irin aure haka da rana tsakiya ? Ko dama kun jima kuna soyayya ne ? Cikin kuka nace a , a , ni banma taɓa ganinshi ba sunansa ma ban taɓaji ba sai jiya sunanshi Sultan , murmushin takaici Dikko yayi tare da cije leɓonshi na ƙasa yace to nima gani nan zanzo , a , a ka bari yazo ya tafi sai kazo , Dikko yace idan har nace zanyi babu wanda ya isa ya dakatar dani saina zo gani nan zuwa........ Yana faɗin haka ya kashe wayarshi.
Cikin ruɗewa naci gaba da shiri kar Sultana yazo ya haɗu da Dikko tunda tun jiya Babanshi ya faɗa zaizo idan kuma ya koma yace Babansa yazo ya samu nayi baƙo ai abun babu daɗi ,
Yarinya Dikko zaki tonawa asiri ? Ni zaki faɗa ma aurenki nan da sati biyu ? Duk duniya naga mai aurenki idan ba ni ba , lallai An mata baki da hankali inma banda wawanci da rashin lissafi kai tsaye sai ace za'ayi miki aure da wani kawai kinma yadda kin hankaɗeni gefe ɗaya , naga jakin Sultan ɗin ina fama da matsalar Yazeedu zaki sake tattago wata , yana gama sa kaya kiran Inna ya shigo wayarshi...
A zuƙuwa ya ɗauka , bayan sun gaisa Inna take faɗa masa mutuniyarshi ta faɗa mishi zatayi aure ? Cikin farin cikinta da jin daɗi take bawa Dikko labari cewa ai auren zuminchie ne dake a familynsu auren haɗi akeyi , cikin yanayin farin ciki Dikko yace to kun tambayi ita yarinya tana san yaron ne ? Duk abinda ya faru jiya kamar ansa Inna ta kwashe kaf ta rattabawa Dikko , dan ita bata san Dikko da Sultana soyayya akeyi ba kuma bata san waye Dikkon ba kawai dai tanayin waya dashi dan yayi tsayuwar arfa wurin ganota ya sadata da "yar ta shi yasa ta bashi wani matsayi na musamman a rayuwarta gashi kuma yana ƙoƙarin kiranta a waya yana gaisheta lokaci².
Inna ta ƙara da cewa aiko bata sansa su babu ruwansu haka suke haɗawa a can gidan aure ake fahimtar junan , cikin ƙarfin hali Dikko yace Allah yasa alkairi Inna ta ansa da amin tace itama zata dawo kafin bikin , Dikko ya ansa da a dawo lafiya yana faɗin haka ya tsinke wayarshi.
Ajiye wayar yayi yana cewa An mata da gaske bari zakiyi a rabaki dani ? Haba yarinya Dikko Yazeed Sultan gaba ɗayansu nine zakaran rukuminsu gani nan zuwa a dai² lokacin daya rataya kayan da zai saka a jikin wani ƙarfe ya rungume turare yana bugawa , wani irin turare ne na "yan gayu mai masifar ƙamshi da tsada wanda ni da naji kuɗinsa naji dama kuɗin ya bani na siyawa "yan gidanmu gidan zama , shi turaren ba kaya yana a jikinki kake shafawa ba , sargafe kayan akeyi saman wani abu sai a riƙe ta inda turaren ke fita cikin hannun haggu ana zungurashi da hannun dama turaren yana fitowa , tou idan wani yana wurin akayi feshin shi kanshi turaren saiya bi kayanshi da jikinshi , idan kuma aka sakashi a jikin kaya ko an wanke ƙamshin baya fita kuma haka ƙamshin zai kama jikin wanda ya saka kayan.
Alhaji idan kuɗin nan sun haɗu ka kawomin dan zanba yaran da zasu tayani aiki wani abu a ciki yau nake so na kashe yarinyar nan gata nan na kamota , Bello ne kwance saman kujera ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya yana magana da Dady a waya ,
Dady yace kuɗi sun haɗu kana ina ne kaida yarinyar ? Bello yace ina sabon gidan bayan sabon gidan sarki ai ka gane gidana da nake gini ban gama ba ko ? Dady yace Eh Bello yace to ya taho da kuɗi ka ɗauki gawar Sultana , Dady yace gani nan zuwa ya tsinke wayarshi.
Bello kallon yaranshi yayi yace yana zuwa sai ku rufeshi da duka harsai ya mutu mu kuma mu ɗauki kuɗin saimu gudu ,
Shi kuma Dady yana gama waya da Bello ya kira "yan sanda cewa a bashi jami'ai cikin kayan gida su biyoshi dan zuwa inda wani ya kashe wata yarinya , bayan ya gama waya da polisawa yace haba Bello tunda dai burinka ganin bayana nine nan zan ga bayanka a banza a wofi dani kake zance ko ka manta waye ni ? Muke da gwamnati mu'ahhukuma hannunka dumu² a kisan Sultana "yan sanda na kama sai su kashe ka , Sultana ta mutu Bello ya mutu damuwa ya ƙare.....
Kukan motocin Dikko na jiyo suna shigowa wani irin kuka sukeyi suuuuuu ba ƙara sukeyi ba cikin laushi suke kuka suuuu ina lissafi a zuciyata saida mota biyar ta shigo , wani irin farin ciki naji a zuciyata a bayyane kuma nace barka da zuwa mutumina , a ƙagare na saka hijabi nayi waje cikin jin daɗi.
A harabar gida su Ashiru sun wasu kuma sun hana shiga ko fita harsai mai gidansu ya gama abinda yakeyi ya tafi ikon mallaka kenan , wani ne ya buɗe min mota na shiga inda Dikko ke zaune yana ta soɓaro baki cikin sakata , ina shiga ya rufe murfin motar , kallon Dikko nayi cikin jin daɗi tattare da shauƙin so , ɗan kauda kanshi yayi gefe yayi kyau sosai a cikin ƙananan kaya amma idonshi ya faɗa ma'ana yaɗanyi rama ,
Murmushi nayi tare da cewa kayi kyau Dikko , ba tare daya kalleni ba yace ngode An matana ya ƙarasa maganar yana murmushi tare da ɗaga girarashin duka amma bai kalleni ba , sai yayi shiru , ni kuma na sake cewa baka da lafiya ne ? Lafiyana qalau yayi maganar yana duba wayarshi , to kayi shiru ina magana kana kallon waya ,
Ey amma kuma kallon wayana bai hana naji abinda kike cewa , Dikko na faɗa maka , kin faɗamin zakiyi aure kin cire hotona a d pn ki , na sani ai , kayi haƙuri haka Allah ya tsara , ajiye wayar yayi tsakanin ni dashi ya juyo yana kallona yace ku mata kullum tunanin ku ɗaya ne , daga aure sai ku haihu bakwa gina rayuwar zaman auren da soyayyar junanku , bata yuwu kawai magini ya fara gino katanga daga sama baza ta zauna ba saboda a saman iska yake ta ɗora buloluwanshi , ni kuma ta ƙasa na fara nawa nayi foundation mai kyau bayan na zuba masa siminti tsaƙƙuwa da yashi na bi a hankali na ɗora buloluwa na da ko wace daƙiƙa cikin salon iya gini , na bashi ruwa katanga ya zauna dai² da dai² cif da cif faɗamin taya wannan katangar za'a iya ɗauketa a sake mata wurin zama ne ? Sai a sauke bololuwan ai , bulo dubu ne Dikko ya jera taya zasu sauko duka ba tare da wani ya roshe ba ? Kallon shi nayi cewa aiko wasu sun roshe dole a samu rayayyu , bulo dubu ne aka cire kuma ana so a sakeyin irin katangar da ake so a sake ma wurin zama shin gini zai kai kamar waccan da wurin cire bulo wasu suka rushe ?
Sai ayi dashi da fasassun , taya zasu zauna bayan babu dashi a cikin wacce aka rushe , sai a siyo sabo a ɗora , taya za'a haɗa sabon bulo da tsoho ? Ai gini dai ake buƙata abinda tsohon ya bada sabo zai bada irinshi , bolo ina 9incis ne sai akaje siye sai suka ce babu 9 sai 6 , sai insa su bugamin wani inci 9 idan aka samun banbancin siminti fa , wancan yaji suminti sabon kuma yashi yayi yawa...........? Sai ayi filester , ai bana buƙatar filester An mata wato kina tunanin zaki iya rusa soyayya ta ki gina ta Sultan akan tawa ko ?
Ai idan kayi tunani da babu kai zuwa kayi , tabbas babu ni zuwa nayi kuma nazo kenan bana tafiya , Sultan zaizo yayi ta gininshi a saman iska ne domin nasan zuciyarki ta gama ginuwa da soyayyar Dikko rabaki dani a halin yanzu tamkar raba bawa da mutuwa ne , kinkuwa ga abinda baya yuwuwa ne duk wanda yazo saiya koma idan har kina ganin baki mutuwa to na yadda soyayyana zai goge a zuciyarki yarinyar kirki kawai kin shigemin zuciya yayi maganar yana sauke gilashin gefenshi saboda Ashiru yana magana ,
Mai gida wai wani daga ciki akace zai shigo yana ƙofar gida , Dikko yace a , a ya bawa Ashiru ansa yana ɗage glass in , nace kaji mulkin mallaka gidan ubanshi ne fa , ai ni kuma katsinar gaba ɗayanta a hannunmu take ko ina namu ne , banda nan dai ke yarinya shima nan ɗin nawa ne idan kuma kince a , a yanzu in nuna miki ki gani ,
Shiru nayi shi kuma yaci gaba da rattafo kalamai masu girma zuwa zuciyata kaina kwalwata da tunani na , yaci gaba da ginawa kamar yadda yace , karatunshi mai wahar gogewa ne , kalamanshi na da daɗi , soyayyarshi tana da girma , yaci uwar awa biyu yana ɗorani a inda bana iya saukowa , saida ya tabbatar na hawo sosai yace inje zaizo anjima idan Sultan ya tafi , saida na rungumeshi na fita , shidai baya san yana taɓani kona rungumshi zai ƙyaleni saina sauka a jikinshi da kaina , ɗan gayun namiji kenan ga kyau ga tsafta ga wanka ga ƙamshi saboda yawan wankanshi idan ka taɓa jikinshi sai kaji wani irin laushi kamar ka taɓa bayan zomo , ina nan tsaye har suka fita jikina sai ƙamshin shi yakeyi gaskiya Dikko na daban ne.
Saida motocinsu suka ɓace daga wurin ko ɓushi²n ƙurarsu babu sannan motar Sultan ta shigo......
31/10/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 68
Wuri ya samu yayi parking ya fito a nutse yana murmushi , hannu ya fara bawa mutane suna gaisawa duk wani ma'aikaci dake wurin saida Sultan ya miƙa mishi hannu suka gaisa cikin sakin fuska , shima dai wankakken matashi ne wanda shekarun shi bazai wuce kamar na Dikko ba ,
Wurina ya nufo yana murmushi , nima murmushin nayi masa cewa takwarana barka da zuwa , da yawwa ya ansa yayi gaba nabi bayanshi muka shiga ciki , a palo muka samu Kaka gaba ɗayanmu wuri muka samu muka zauna , bayan mun zaune Sultan ya gaishe ta , ta ansa cikin sakin fuska da ɗan barkwancin hakan nan dai.
Fira sukaci gaba dayi da Kaka ni kuma na miƙe nayi ɗakina , ina zuwa alwallah nayi na gabatar da sallah azahar bayan na gama naci gaba sabgogin gabana a cikin ɗakina , kayan da Yazeed ya kawomin na buɗe ina gani , wanda sukafi burgeni suka tafi da tunani na fara zamewa gefe ɗaya zan kai ɗinki.
Ina ta ciccire kayan ne Sultan ya shigo , kamar ya saba dani ya duƙa wurin kaya shima yana fiddowa yake tambayana me za'ayi dasu ne ? Ina murmushi nace ɗinki zankai na taɓa wanda zankai ɗinki da hannuna , ɗan murmushi yayi kaɗan ya fara ciro wasu daga cikin wanda na fitar zankai ɗinki yana cewa gaskiya wannan bama sanshi , tou wai har an kawo lefen ne ni ban sani ba .....?
Dariya nayi nace bafa lefe bane ba , dani dashi gaba ɗayanmu kallon juna mukayi lokaci ɗaya , kyakkyawan murmushi yayi min yana cewa waye ya baki ? Wani ne ya kawomin , wayyo mun kuwa gode ya faɗi maganar yana komawa gefen gado ya zauna.
Sultana ya kira suna na , ba tare dana juyo ba nace na'am , Abba yace nazo na ganki na kuma gaisheki ni Abubakar Sadiq nake suna kirana Sultan ne sunan Baban Mami na ne , ina da mata ɗaya yarana biyu , auren zumunci shine al'adar wannan ahali , amma ni aurena na farko banyi auren zumunchie ba saboda babu wacce zan aura a lokacin yaran duk basu girma ba ni kuma na tashi aure Abba yace inyi kawai daga baya idan yaran sun girma sai in kulle ta biyu da auren zumunchie , kin ganni na ganki ni kinmin a haka Allah yasa nayi miki.....?
Ba tare dana juyo ba nace Ey mana kamin ina sanka , amma fa ni karuwa ce shin zaka aura karuwa ? Yi yayi kamar baiji abinda nace ba yaci gaba da cewa Mami ta bada shawara a ɗaura aure sati mai zuwa sati na gaba kuma sai ayi shagalin biki , nace tou Allah yasa alkairi ya bamu zaman lafiya fita da sharrin dake ciki ubangiji ya kauda shi ya tsinkule idanuwan maƙiya , am3n Sultan ya ansa tare da miƙewa idan kin gama haɗa kayan ki sameni a waje sai in kaiki , na ansa da tou shi kuma ya fice...
Yana fita naci gaba da fiddawa bayan na gama haɗawa na zuba a lader na ɗauka na fita , a mota na samu Sultan na buɗe na shiga saida na zauna na rufe yace ina zamuje ne ? Nace masa goruba road , murmushi yayi tare da kallona yace kice dai amaryar tawa mai kuɗi ce goruba kike kai ɗinki ? Murmushi nayi ba tare da nayi magana ba , jinjina kai yayi bai sake magana ba ya taka mota muka fita daga gidan , muna fita wayarshi ta fara ringing ɗauka yayi banji abinda abokin wayar yace ba shidai yace zanje goruba ne , a , a kayi haƙuri don Allah jirani yanzu zan ajiyeta nazo don Allah , babu damuwa bara na fara zuwa tou yana faɗin haka ya ajiye waya , yana cewa yi haƙuri da Allah na anshi saƙo , babu damuwa na bashi ansa.
Hajiya wai bayan su Dad inmu shi Malam kafin ya mutu yana da wasu "ya "yane don Allah ? Hafsa ce zaune a gaban Kakarta take tambayarta shin ko Dad inta yana da wasu "yan uwane bayan wanda ita ta aifa da cikinta ? Hajiya dake kwance tana gab da ramin mutuwarta tace Hassatu me yasa kikai min wannan tambayar ne ?
Gyara zama Hafsa tayi cewa ba komai kawai dai ina so na sani ne , cikin yanayin wahaltuwa ta majiyyacci Hajiya tace yana da yara biyu amma basa tare damu a halin yanzu ? Hajiya suna ina ne haka ? Fashewa da kuka Hajiya tayi cikin kuka take cewa haƙiƙa ita rayuwa taƙaitacciya ce kuma ƙarewa takeyi ba tare da tayi shawara dakai ba , duniya da komai zaka ajiye kaje ga Allah , babu wanda yazo da arziƙi kuma babu wanda zai koma dashi , ruɗin duniya da shaiɗan yasa na tabka kuren da bashi da gyara kuma rayuwa ta riga ta ƙuremin , cikin kuka sosai taci gaba da cewa yau da zanga Aliyu da ɗan uwanshi dana roƙi gafararsu su yafemin , ni nake kwance ina ciwo amma duk lokacin dana kwanta da sunan bacci sai nayi mafarkin ina faɗawa cikin wani irin tsukakken rami kuma wuta yake ci a cikin sa ,
Hassatu duk arziƙin ka baka isa kayi ma wani arziƙi ba , haka kuma idan ubangiji ya arzurtaka kai bawa baka isa ka talauta wanda ubangiji ya azurta ba , kowa tsirara yazo babu wanda aka haifa da wando ko riga kowa haka ya faɗo kuma kowa haka zai koma daga shi sai likafanin shi , duk abinda kazo duniya ka tara kanaji kana kallo kana sanshi zaka tafi ka barshi magada suci gadonshi , ka bar musu dukiya sunajin daɗin duniya kwana kaɗan sun manta dakai sunci gaba da sharholiyar duniya sai ɗaiɗaiku a "ya "yan naka zasu riƙa tunawa dakai har ka samu suyi maka addu'a.
Haka take ga mace , idan mijinta ya kwanta ya mutu kuka na wani lokaci zatayi daga inda aka raba gado aka bata shikenan ta mance da shafinka a rayuwarta , ga dukiya ka mutu ka bar mata gidanka taci gadonshi tanajin giyar kuɗi yana motsa ta taci abinda ranta yake so tasha wanda take so idan za'a nemi shawararta a misali za'a ce mata Hajiya ko a dawo da Alhaji daga duniyar mutuwa cewa zatayi a , a , a ƙara kwaɓa ƙasa a zuba a saitin kanshi , bayan wasu watanni tayi takaba ta gama tuni ta manta dakai namiji zata samu ta aura kana lahira wani yana kwana a gidanka...
Idan kana da "ya "ya da ita kila idan tana da sauran imani ta kallesu ta tuna dakai , dan ba duka aka taru aka zama ɗaya ba , to ni ba auren nayi ba Hassatu dukiyar nake mawa wannan dalili yasa na fasa gidan na kora "ya "yan malam biyu suka shiga duniya yayin dana kashe uwarsu saboda san duniya kuma duk saboda "ya "yana nayi haka dan ina so suji daɗi kuma sufi na kowa , amma kaico duk wannan yaƙin da nayi Hassatu ubanki sai yayi ruf da ciki akan kaf wannan dukiya shi ya cinyeta duka ya hana "yan uwanshi komai nima mai yaƙin sisi bai bani ba duk abinda nace masa ina so , ko ya kawo abu ya ƙare sai yayi masifa sosai sannan ya ɗauko ya bani kamar zai dokeni. Ki gayamin ɗan da bai ma idonka ba bayan idonka zaiyi ne ? Hafsa tace a , a , murmushi mai ciwo Hajiya tayi sannan tace...
Ina da abiyar zama kuma tana girmamani sosai a matsayina na Yayarta a wurin miji , tana bani girma na yadda ya kamata ko aiki taga zanyi bata barina nayi idan har kika ga ina aiki tou lallai Maryam bata lafiya ne , kuma ko tana ciwo saita daure cikin ƙarfin hali tazo ta kamanin dan dai ta bani girmana da mutuntuwa na ina gaba da ita a gidan aure.
Tunda nake ban taɓa ganin ɓacin rain Maryam ba domin mace ce mai haƙuri kunya kawaici da kara , duk "ya "yana dana haifa bana musu wanka ko tsarkin kashi ko goyo duk Maryam take musu idan har kika ga ɗana a hannuna to wallahi nono yake sha kuma yana gamawa Maryam zata ɗaukeshi ta goye , wankina dana yarana duk itace take haɗawa tayi ,
Duk lokacin da Maryam ta samu ciki sai nayi yadda na lalata cikin nan ya zube nayi ta neman asiri karta aihu amma dake ubangiji yayi alƙawarin biyu sai sunzo duniya Allah ya bata Aliyu da Muhammadu , bana san yaran kwata² ina ta neman hanyar da zanyi na sabauta musu rayuwa dan bana san ace "ya "yana suna da "yan uba ba hangen wata irin ƙatuwar gona da Malam yake da ita tun a wancan lokacin an taya gonar naira dubu ɗari 3 da hamsin bana so ace an raba wannan kuɗi idan Malam ya mutu wasu su samu sai nawa kawai.
Wannan gona duk duniya itace kaɗai Malam ya mallaka bayan ita bashi da komai a duniya kuma gonar itama ba gadonta yayi ba , domin talauci ne ya isheshi shine ta fara harkar tsibbunci kuma Allah ya dafa mishi kasuwa ya buɗe yayi ma wani attajiri aiki da buƙata ya biya shine ya baya da gonar yace ya riƙa noma dan ya cida iyalinshi.
Haka Malam yaci gaba da aiki a ƙauye har manyan "yan siyasa suka ganoshi duk buƙatar da mutum yazo dashi insha Allah Malam yanayin aiki an dace , abinda ya maidomu garin Katsina wata yayi ma aiki tayi mishi kyautar gida muka tattaro muka dawo birni.
Muna dawowa liƙafa yaci gaba sosai a taƙaice dai Malam ya tara manyan kuɗi da ƙaddarori manyan gonaye a garin funtuwa gidaje a cikin gari , ganin kullum Malam yana ƙara ginuwa shine na nemi hanyar da zan kora Maryam , bayan nayi shawara da wata aminiyata itace ta bani shawara mutuwar Maryam shine kawai mafita , idan ba mutuwa tayi ba ko sun rabu da Malam itama zata saka ran zataci wani abu a dukiyar gadon fitina za'ayi sosai shafeta daga duniya shine kawai abinda ya kamata muyi , to itace ta rakani wurin wani boka yayi asiri ya haɗa Maryam da aljannu aka tura mata yace idan ta firgita tayi ƙara aljannin zaiyi tsalle yahau saman harshenta take a wurin zai zuƙe jininta shikenan an rufe littafinta , idan kuma ta kira sunan Allah aljanni bazai iya zuwa wurinta ba , haka kuwa akayi Maryam dai ta tafi.
Bayan mutuwar Maryam kuma nayi makircin da nasa Malam ya korasu Aliyu daga gidan nan , nayi tunanin idan suka tafi za'a sacesu dan nayi zaton kawai zasu halaka a duniya ne , da naji labarin basu ɓace ba shine nayi asirin da zasu manta da gida kwata² , kwatsam sai naji labari wani gida sun ɗaukesu suna zama dasu shine na faɗawa mahaifinki nace yasan yadda zaiyi da yaran nan dan a lokacin Malam ya rasu nace idan har hankin yaran nan ya dawo gida zasu buƙaci a basu gadonsu ,
Wannan dalili yasa Dady ya tura Bello ya shiga rayuwar Binna , saboda Bello baijin magana ko kaɗan iyayenshi ma kansu ji sukeyi dama basu haifi banzan ba , kuɗi Dady yake biyanshi kuma shine yace yana so Bello ya gurɓatawa Binna rayuwa yadda ko ya girma ya zama mara gulihu dan karya nemi kuɗi kuma yanaso Binna yayi wulaƙantacciyar rayuwa karya zama na gari dan baya so kwata² ya tuno da labarin gida , Bello da Dady sukayi ciniki Dady ya bashi rabin kuɗin aiki , shine Bello yayi asiri ya saka Binna ya fara caca shan giya neman mata da sauransu , wannan aikin duk na Dady ne Bello kuma ya biya mishi buƙatarshi , aikin Bello kuma shine ɗaukar fansa akan abinda Binna yayi mishi na ansar budurcin matarsa , Binna ya gudu shine Dady yace ba'a barin maƙiyi ya tafi ka dawo dashi wurinka yadda yayi maka kaima ka rama , shikenan Bello yaci gaba da jifar "ya "yan Binna da asiri...
Duk nice na kawo wannan shawarar amma Ubanki ba "yan uwanshi ba ni kaina sisi ya hana a kuɗin gadon nan , girgiza kai Hafsa tayi tare da cewa har nawa ne kuɗin gadon ? Hajiya tace zunzurutun kuɗi Malam yabar naira miliyan 45 gonaye da kuma gidaje , miƙewa Hafsa tayi tana shafa wayarta tace tou ƙalu bale ga rayuwarku domin ɗiyar Binna ta tiso ƙeyarku gaba dake da Dady ƙaryarku ta ƙare ba abinda ya shafeni kinga tafiya.......tana kaiwa nan ta fice daga gidan.
Da gudu Hafsa ta fita tana kuka innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu Baba Binna ƙanin Dady ne shine yayi iskanci dani......? Wani irin ihu tayi cewa na bani na lalace ni Hafsa ubana ya kwanta dani ya buɗemin jikinshi na gani , da sauri ta rufe idanuwanta ta dafe kanta , yauni na shiga 3 ni Hassatu na lalace Baba Binna Allah ya rufa maka asiri da baka raye yau da wane irin baƙin ciki zakaji idan har kasan ni ɗiyar ɗan uwanka ce ? Wayyo Allahna ƙanin ubana yayi iskanci dani kaico da wannan tsohuwa , tirr da halinki duk kece silar rushewar komai ni naga tsiraicin ƙanin ubana yaga na "yar sa Sultana kuma taga na Dady , itama ita da Dady kenan sunyi ? Tabbas sunyi shi yasa har ta ɗauko videon girmanshi ta turomin , kai mun shiga 3 mun lalace wani irin ihu ta kurmama tare da faɗuwa ƙasa somamiya.....
Kai anshi ka irga kuɗin , Bello yakeyin magana bayan yasa wani matashi ya anso jaka daga hannun Dady , buɗe jakar sukayi amma da mamaki sai suka ga wayam , ce ma Bello sukayi ai babu komai a ciki , ɗago kai yayi da niyar yima Dady magana Dady ya gaggaɓe da dariya yace kana wasa dani kenan ko ? Ai kace idan na kawo kuɗi saika sokamin wuƙa na mutu Bello ka cika tsarabarka da yaji ƙaryarka tasha ƙarya yau nine ajalinka hukuma zata kashe ka da hannunta bayan ta kamaka da hannu dumu² a kisan Sultana ,
Bello yace ai hukuma bazata kashe ni ba ta dalilin kisan Sultana saida ta kamani ta dalilin kisan ka , idan baka sani ba bara na faɗa ma tun daga ranar da kasa akayimin duka a ofishin "yan sanda duk wani abinda ya faru tsakanin ni dakai tun daga ranar dana fara zuwa wurin Binna ya ɗaga wasu takaddu yace to ka sani yana rubuce anan ciki.....
Wannan gurzajjin ne amma na gaskiyar ya tafi zuwa hannunshi , duk halakkacin da nayi maka lokaci ɗaya kasa ƙafa ka shure saboda kai kanaji kana da hukuma a hannunka kai ɗan siyasa tou ka sani nawa siyasar yafi naka , dani dakai yarinyar da muka haifa tayi wasa da hankullanmu lokaci guda wurin ganin ta haɗa mana fitina ta yadda zamu fara muna farautar junanmu ,
Na ganota ne domin kirana da tayi da layin da ita kaɗai na kirata dashi cewa saina kasheta , na yadda da hakan da tayimin maganar ka ta kuma yimin maganar Sultana , tana tsaye ne a saman ƙafafuwanta wurin ganin taga bayanmu dukanmu gaba ɗaya daga ni har kai ,
Shi yasa tayi amfani da wasu sirrika data sani wanda kwalwarta da tunaninta ya bata , sai tayi amfani da wannan sirrinka wurin kirana tace kace kaza² kaima saita kiraka wanda haka yasa yanzu kazo min da jaka babu kuɗi.
Saboda ka yadda da cewa zan kashe ka ne yayin daka bani kuɗi domin tafiya da gawar Sultana , banzo da ita ba kuma ban kamota ba amma ina tare da duk wani motsi nata , ta fita daga gida bayan sallah azahar misalin 2:31 , wani ne ya ɗauketa a mota bayan Dikko yaje gidansu ya fita kuma yasa an tare hanyar fita da shiga harsai ya gama magana da ita ya tafi ,
Mota mai lambar kaduna ta daɗe a ƙofar gidan sakamon hanata shiga da akayi cikin gidan , bayan kimanin awowi biyu da wasu mintuna Dikko ya fita daga gidan mota mai lambar kaduna ta shiga , ta daɗe motar sosai sannan ta fito daga cikin gidan bayan mai tuƙa motar ya fito ɗauke da Sultana ,
Yaje kasuwa central market ya anshi saƙo , daga nan ya wuce goruba road , yanzu haka tana goruba road j ta fita daga cikin mota ta shiga shagon ɗinki a halin yanzu tana cikin farin ciki shin zaka bayar da kuɗi na basu damar kasheta ko kuwa.....?
Dady yace takaddun da kake magana ka tura zuwa gareshi waye shi ? Bello yace Dikko ne nayi haka ne domin kuɓutar da tawa rayuwar shin zaka bada kuɗi nace su dawo dasu karsu isa wurinshi ? Har yanzu kana da sauran dama mutuwar Sultana ko kuma taka wace ce ka zaɓa.....?
Dady yace amma me yasa ka tura shedar takkadu wa Dikko ? Saboda shine mijinta kuma ya zama dole yasan duk wasu sirrika da yake ta faman bincike babu dare ba rana , na yanke kawai na rubuta komai na tura mishi ta hanyar ɓoye sunana amma na bayyana naka , abinda yasa kuwa nayi haka dan kayi min kuri da hukuma shi yasa na miƙa kaina ga hukumar gaba ɗaya ,
Kai.... Dady ya faɗa tare da nufa wurin Bello ta haɗashi da bango yace kana da hankali ne ko kayi hauka ne ? Dariya Bello yayi tare da cewa lafiyata garass amma ka sani matar da Mami ta turo ta ɗauki kwalbarnan munyi dukawa matar sosai ta samu ta kubce bayan mun bita bamu samu ganinta ta ɓace mana a cikin asibiti , taje ta ɓoye tayi jinyar sirri a wani wuri daban bayan ta samu sauƙi ta dawo ta duƙufa neman Sultana bata samu ganinta ba amma a bincikenta ta gano Sultana tana tare da DK shi yasa ta tafi wurinshi domin buɗe mishi duk wani ɓoyayyen sirri kenan kaga faɗan yazo ƙarshe , na kashe ko a kashe ni wannan shine muradina domin ni nasan ƙaryana yazo karshe kuma banda sauran dubara ko mafita tunda case ya koma hannun Dikko.........
Ka saki wuyana kawai kaje ka fara neman shedar da zaka kare kanka , 45miliyans sai aje ayi ÷ ÷ ɗinsu in to su Sultana........ Kowawa sukaci gaba dayi tsakanin Bello da Dady , dariya Bello keyi domin shi ƙarya yake ma Dady babu wani abinda ya rubuta akaima Dikko amma karuwarshi yaji labarin tana ta zuwa neman Dikko ba'a barinta ta ganshi , kuma yana ta farautar ta har yanzu basu haɗu ba , dan ƙawarta wacce ta bawa Sultana numberta tace zata kirata itace ta bata labarin yaran Dikko sun kamata sunyi mata tambayoyi kuma ɗiyar Binna tana nemanta , tace ta anshi number Sultana amma ta manta bata ajiyeta a wayarta ba , data tambayeta inda Sultana ke zama shine tace tana zaune wurin DK a goruba road...
Shi kuma Bello ya girgiza Dady ne dan ya anshi kuɗi a hannunshi amma kamar yadda yace duk wani motsin Sultana yana hannunshi tabbas yana tare dashi...
Saida suka gama cakuwa kowa ya saki kowa cikin wahala , saida Bello yayi nishin wahala yace kuma nine na tura yarinyar ka ta zama karuwar Binna , wani irin gumji Dady yayi da niyar riƙo Bello amma ya ruga da gudu ya hau mota ya nufi goruba road domin ganin bayan Sultana dan lokacin da boka ya ibar masa wa'adinsa ya cika , danshi baya iya auren uwarshi gara kawai ya kashe Sultana magana ce ta shari'a kawai ai tayi ana Sign daga ƙarshe ƙotu tacezaiyi gidan yari , Dady cikin ɓaci rai yace ma "yan sanda da yazo dasu suje zai sake nemansu ,
Hafsa kuwa mutane suka ɗauketa suka mayar da ita cikin gidan Hajiya , aka yayyafawa banza ruwa ta dawo , tana dawowa taci gaba da ihu tana na bani na lalace... Gaskiya Hajiya ke sheɗaniya ce ta bada labari a jarida ina ahalin mahaifiyar shi Ba Binna......? Wato mahafiyar ita Maryam kakar ba Binna kenan wacce ta haifi mahaifiyarshi ina suke...............? Ta tambayi Hajiya yayin data sake tafiya zuwa duniyar suma.
Ina zaune a saman kujera shagon ɗinki ana nunamin style Sultan yacemin bari yaje ya dawo kafin in gama zaiga wani abokinshi a road na gaba , fatan dawowa lafiya nayi mishi ya tafi ni kuma naci gaba da dubawa saboda tun farko nace nidai suymin basai na duba ba amma suka tursasani wai indai duba...
Bayan na gama zaɓa na miƙe ana auna ni juyowar da zanyi naji kaina ya sara sakamakon Bello dana gani tsaye ya raɓa ƙofa biyu yana kallona , wata irin mummunar faɗuwar gaba naji a dai² lokacin daya fara kwaikwayon muryata cewa kun haɗa kai akan zaku kashe wata yarinya amma shine naji yana cewa sai ya kashe ka , shigowa yayi cikin shagon yana cewa idan baki mata ba da kikayi wannan maganar ai dariya nayi miki , na baki ansa cewa ko wace daƙiƙa saƙo da lungu rana da dare neman sa'ar mutuwarsa nake saina kashe shi.
Hihihihihihi yayi dariyarshi ta raini wayau yace zakiyi tunanin banda lissafi shi yasa nayi wannan maganar ? Tou saboda kece kaɗai na siya layin nan , nine nan na kiraki nace saina kashe ki , yasa anata gadinki ya hanaki fita saboda baya so ki mutu shin yanzu yana ina ? Ko ya isa ya tseratar dake daga mutuwa ? Kin taɓajin labarin zafi da radaɗin azabar fita rai ? Hihihihihi ya sake dariya yace ai na manta yarinyar malama ce ba mamaki an baki labari a islamiya yayi maganar dai cikin yanayi na jahilci.
Saida ya sake dariya tare da tafa hannayenshi ya ɗora hannunshi a saman kunnenshi kamar yana waya da irin maganata zanzo fesra hotel sanye cikin hijabi da niƙaf napep zai saukeni idan ka isa ka kamani ka kasheni a wurin hihihihihihihihi ya ƙarasa maganar yanayin dariyarshi mai tada hankali sai kuma ya ɗaure lokaci guda yace a maimakon kizo sai kikayi wa Hafsa waya ke mai wayau kika rufzata a rami sai tazo saida ya sakeyin dariya ya fara matsowa inayin baya yaran shago kuwa rugawa sukayi suka fita daga cikin shagon lokacin da suka ga Bello ya fiddo wata irin shareriyar wuƙa daga cikin rigarshi yana cewa rana dubu na ɓarawo rana ɗaya cif shine na me kaya yau gani gaki bankwana da duniya , ya ɗaga wuƙarshi ya nufo dai² saitin zuciyata dashi...........
Yana cewa ba kin kirani cikin dare ba ni kuma na faɗa miki cewa zan kashe shi misalin 10 dai² na safiyar yau , kina tunanin ina cikin maye ko ? Tou kwalba biyar na shanye a daren amma kaina baya manta komai , idan kin isa barzahu lafiya kicewa Binna zanzo na yayyafawa kabarinshi giya kwalba biyu ta tayashi murnar isowar uwar masu gida wurinshi....
01/11/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 69
Hihihihihihi yayi wannan munafikar dariya da bana so , saitin wuyana ya ɗora wuƙar dai² maƙoshina lokaci guda na ɗauke numfashina zufa ta ketomin hawaye suka ci gaba da gangarowa nabi Bello da kallo , dariyar ya sakeyi tare da jan majina , yace kin tuna kika tuɓeni kika ɗaukeni video ? Ka turo da dubu ɗari biyar idan ba haka ba zan watsa su a yanar giza gizo , yayi irin magana na , dakel na haɗi yawun bakina cikin tsoro nace wai me kake so da rayuwata ne ?
Bana buƙatar komai a halin yanzu sai mutuwarki , bara in faɗa miki abinda kika kasa sani nine nan na kashe Binna da hannuna , kuma nine na toshe miki kwalwa na maidake kidahumar ƙarfi da yaji nine na haɗa Binna da Hafsa da Amisty suka zama karuwanshi , haka yake jerasu a layi ya hau akan ɗaya ya sauka ya hau ɗaya , nine nan na shirya komai ta yadda ya faɗa wasan caca shine kawai zai fita a caca nayi na mayar dashi ya ƙiya saboda kawai yayi miki alƙawari ya daina yaso ya lalatamin tsarina ne ni kuma kawai na kashe banza , to me Babana yayi maka haka da zafi ? Ke matar da nake so ya maida ita zawara a ranar da nake farin ciki zan shiga daga ciki , da farko na barshi ta tafi Yayan Babanki ya zugani na dawo dashi ni kuma na hura wutar ɗaukar fansa a zuciya , zan gama da matsalar Binna dake na koma wurin ɗayan ɗan iskan saina ƙare kaf ahalinku dan bana buƙatar ganin jinin Binna a saman doron ƙasa , kauda kaina nayi gefe ɗaya ina wani irin gumji nace kaine ka kashemin min Babana......? Nine na kashe shi ko in nuna miki irin zamiyar da kikayi a jikin gawarshi ne ? Yadda nayi ya nunamin kina cewa wayyo Babana karka ka tafi ka barni tashi Babana baza ka mutu ba gani nazo , buɗe idonka kar kayi bacci uwar masu gida wayyo Babana yi murmushi hihihihihi yasha majina jeki....... Ya faɗa tare da so kamin wuƙa a kafaɗata wanda ba haka yaso ba zuciyata ya saita kuma a samanta yaso wuƙar ya shiga...
Wani irin ihu nayi tare da haɗa hannayena wuri ɗaya 🙏🏻idona yana tsiyayyar da hawaye nace na roƙeka karka kasheni , wata "yar iskar rawa yayi da ƙugunshi yace ke kina tunanin zan barki ki rayu bayan nace miki nine na kashe Binna ? Cikin kuka nace ai banji ba , hihihihi yaja majina ƙazamin banza yace sai kin mutu......
Ci gaba yayi da yankata ina gocewa yanka 3 yayi min a kafaɗa wuyana da bayana , ta ƙasan sa na sulɓe nayi waje da gudu ina ihu , biyoni yayi da wuƙar tsabar toshewar basira yana saina hallakaki nine ajalinki wallahi baki wuce yau sai kin mutu , masu ɗinki da suka fito suma tuni sun tara taron jama'a dan a kawomin taimako , jini sai zuba yakeyi a jikina ina gudu Bello yana bina , da gudu na shigo titi zan tsallaka road in da gidan Dikko yake fitowarshi kenan zai fita , ina dafe wuyana na fara ɗaga hannu dan motocin suna san su wucemu ne , wani irin ihu nayi nace Dikkkkkkkkow na tun kari motocin da gudu kai tsaye , wani irin burki Ashiru ya taka ni kuma na juya dan jin maganar Sultan shine fa Bello ya samu damar sokamin wuƙa a ciki yana cewa saina kashe ki , wani irin yunƙurin amai nayi kamar raina zai fita na ɗagawa Sultan hannu dan bana iya magana....
Da gudu Dikko ya fito daga cikin mota ya zaro idanuwanshi kamar zasu faɗo ƙasa yace me zan gani haka ? Shima Sultan da gudu ya nufo wurin , wani irin gurnani Dikko yayi cikin wata irin murya yace An mata , tare suka iso wurina dashi da Sultan , Sultan yana ƙoƙarin riƙeni Dikko yayi mishi wani irin halbi ya koma can baya wurin motarshi ya faɗi ƙasa , rumgumeni yayi a jikinshi ya riƙe hannu Bello tare dayi mishi wani irin kallo cikin kuka yace An mata me yasa haka ? Bana iya magana kwata² saboda ina tafiya wata rayuwa daban , cikin rawar murya yace riƙeni An mata riƙe Dikkonki ina tare dake babu abinda zai sameki riƙeni mana , ko motsin kirki bana iyawa Dikko kuwa cewa yakeyi daina kuka an mata ba gani nazo ba , yayi maganar cikin sigar tausayi.
Riƙon da Dikko yayi ma Bello tsabar firgita yasa shi ya suma , jinjina kai Dikko yayi tare da cewa Ashiru ku ɗaukeshi ku shigar min dashi ciki idan na dawo saina tillashi cikin ruwa kada ta cinye shi , ƙasa sukaja banza har zuwa ciki , Dikko kuma ya ɗauki Sultana yayi mota da ita a baya ya zauna yana rungume da ita hawaye yana fita daga cikin idanuwanshi , da gudu Ashiru ya fito daga ciki bayan ya rufe Bello a ɗaki yazo ya shiga mota yaja suka ɓace daga wurin kamar walƙiya.
Sultan kuwa dakel ya tashi ya shiga mota a wahalce yayin da yake tunanin meya haɗa Sultana da Dikko ? Mutumin da baida mutunci ya raina mutane baisan darajar kowa ba , bai damu da halin ƙunci da wani zai shiga ba kanshi kaɗai ya sani bai san kowa ba , tare da cikin wanda Sultana ta kawo ɗinki shagonsu Sultan ya ɗauki ɗaya sukabi bayan motar Dikko amma iyakar kokontonsu motar ta ɓace babu wanda yasan ta inda tabi ta wuce ,
Tunda Bello ya tafi ya koma mota dakel zuciyarshi tana mishi wata irin babbakar babbaka kan ragon layya , yana tunanin maganar Bello { nine na tura yarinyar ka ta zama karuwar Binna } kai...... Yayi ihu tare da kaima sitiyari duka yace Allah ka rufamin asiri wannan labarin ya zama a bacci nakejin shi , na shiga 3 ƙanina ɗiyata ta zama karuwarshi wayyo Allahna tada motarshi yayi ya nufi gidanshi cikin tashin hankali , ko da yaje Hafsa bata nan daya tambaya mahaifiyarta tace tana ƙofar marusa gidansu.
Cikin tsananin tashin hankali ya fito yaci taya ya nufi ƙofar marusa , a halin tashin hankali ya samu Hafsa data farfaɗo daga suma sai tace wayyo Allahna Ba Binna saita koma luww , ita Hajiya bata san suna Binna ba ita Aliyu ta sani , Dady kuma shi yasan Binna , Hafsa na sake dawowa Dady yace Hafsa me Binna yayi miki ne ? Dady me yasa ? Ya akayi kuka bari duniya ya ruɗa Hajiya ? Kun watsa kan gidanku kun gurɓata familynku ƙani yayi tarayya da ɗiyar Yayanshi , Yaya kuma yana neman ɗiyar ƙaninshi kaico da wannan ahali tirr daku , mutuwa kizo ki tafi da Hafsatu ina zamu kai wannan abun kunya , tashi tayi da gudu ta nufi rijiya tana cewa saina faɗa wallahi saina faɗa dakel aka riƙe Hafsa , tana ƙwacewa tayi kicin da gudu ta ɗauko galan ɗin kalanzir ta ɗagashi taci gaba da kwankwaɗa shima dakel Dady ya kwaceshi bayan tasha ta ƙoshi layi ta farayi tana mutuwa kizo taho na shirya taho ki tafi dani wurin Ba Binna ,....
Tun tana layi har ta faɗi ƙasa tana cewa kai waccan Hajiyar ƙarshenki bazaiyi miki kyau ba tsohuwar munafika "yar gadon san abun duniya mai kwaɗayin duniya kuma wallahi saikin mutu mutuwarki bazai miki kyau ba , tirr da hali irin naki azzalimar tsohuwa tari Hafsa ta farayi ƙuhul׳ sannan tace tsabar maitar duniya tou idan baki sani ba Aliyun da kike magana shine yayimin ciki kwanakin baya....
Wani irin juyi Dady yaji duniya tayi masa da gudu , cikin kuka Hafsa tayi dariya kamar mahaukaciya tace da nasan Ba Binna ƙaninka ne idan na bari an fitar da cikin nan Allah ya tsinemin albarka saina haifeshi idan namiji ne sunanka zan saka masa da mace ce sunan mayya Hajiya zan saka , wani irin ihu tayi tana cewa ni nafi san mutuwa dan Allah mutuwa kizo ina nan ƙofar marusa gidan Hajiya kizo ki tafi dani bana san rayuwar gaba , cikin kuka Dady yace ki daina kuka Hafsa bazaki mutu ba , girgiza kai tayi cewa mutuwa itace kaɗai natsuwa a gareni....
Murmushi tayi mai ciwo cewa Ba Binna ɗan gayu wayayye dashi ɗan boko kisan farko amma tsabar mugunta kuka molaƙe tare da tamiƙe mishi rayuwa , bazan manta ba nace masa Ba Binna ciki gareni fa , yayi murmushi yace Doughter ya akayi kika yi ciki ? Ko ƙauye fa an waye a binni sai kawai kikazo kika kwanta kika kwashi ciki , yana cemin Doughter saboda "yar sa ashe ɗiyarshi ce ta gaskiya...........? Nace masa Baba yanzu ya za'ayi nima bansan yadda za'ayi ba , na tursasa masa akan a fitar da cikin ya nuna shifa ba ruwanshi bana san ɓacin ransa dan idan ya juyawa abu baya ya gama dashi ni kuma bana san rabuwa dashi shi , ku kuma gida da kuka gane ina da ciki kukaje kuka zubar dashi , Allah duk mai sa hannu a kisan Ba Binna ubangiji ka tagayyara mishi rayuwa...... Tari ya ƙwace mata sosai mimmiƙewa tayi kamar wacce ake zare ma rai ta sake somewa , ɗaukarta akayi itama aka nufi asibiti da ita.
Wata irin dariya sukeyi gaba ɗayansu suna cikin farin ciki tsakanin Jiddah da Mardiyya Al ' Ameen yake basu labari cewa yaufa an shafe labarinta a duniya , Mardiyya tace Uncle kana wurin ne ? Al ' Ameen yace bana nan Nabeela ta aikeni gidansu ƙawarta ina shiga goruba naga banzar ta fito guje kinji daɗin da naji ? Shi kuma ya biyota da wuƙa ina ta murna za'a kashe ta kawai sai naga mai gida ni kuma na ruga banma tsaya ba kar yace hadani , bayan na dawo daga inda zanje nake tambaya akacemin ai ta mutu...
Cikin jin daɗi Jiddah tace damuwa ya ƙare , Mardiyya kuma tace Uncle mun goge ƙatuwar damuwa danni wannan matsalar ta gabana kallon ciki sati ɗaya nake mata , Jiddah bata san da ita ake ba ta rungume Mardiyya sukaci gaba da murna..
Misalin 9:00pm Sultana ce kwance saman gadon asibiti bayan likitoci sunyi mata duk wani abu daya kamata na bata kariya daga yanka²n da akayi mata , su 3 ne a ɗakin Sultana Ashiru yana tsaye gefen gadon Dikko kuma yana zaune saman kujera gaban gadon ya kwantar da kanshi saman gadon yana tunane² , Ashiru ne ya matso kusa dashi ya miƙa mishi wayarshi cewa mai gida maman Sultana ke kira , ansa Dikko yayi ya kara wayar a kunnenshi bayan ya ɗauka.
Cikin kuka Inna tace Dikko me ya faru ne ? Sai kirana akeyi Sultana bata lafiya ance ɗan gwamna ya tafi da ita me tayi mishi ne ? Me tayi mishi ? yaro mara mutunci tun ina tare da mahaifinta ya addabi rayuwar Sultana yanzu kuma meya sake dawo dashi cikin rayuwarta ? Sassauta kukanta tayi cewa ina Sultana........?
Murmushi Dikko yayi da gefen bakinshi yace Mama waye ɗan gwamna ? Ni ina zansan ɗan iska mara mutunci , kin taɓa ganinshi ne ? Kuma ya akayi kika san ya shiga rayuwar An mata ? Nima ban sani ba , ban sani ba tayi maganar tana sake fashewa da kuka , Dikko yace Mama me kike so ayima ɗan gwamna ne ? Ni ya fita daga rayuwar ɗiyata kawai , idan yace bazai iya ba ya zakiyi dashi ? Saima ya fita tunda ba tare aka haifesu ba dan ubanshi , jinjina kai Dikko yayi cewa to karki damu ina tare da ita a halin yanzu , kana ina ne ? Muna asibiti faɗa mata asibitin yayi tare da kashe wayarshi.
Miƙewa Dikko yayi cewa Ashiru zanje gida zan dawo misalin 1:30am bana san kowa ya zauna duk wanda yazo yaga An mata kace ya tafi kawai asibiti bata buƙatar majinyata , jinjina kai Ashiru yayi alamar gamsuwa shi kuma Dikko ya fice daga ɗakin da sauri....
Ba'a wani ɗauki lokaci ba Sultan ya iso dashi da Kaka da Mami sai Abba su kaɗai suka zo , dan yayyen Inna cewa sukayi Allah ma yasa ta mutu uban kowa ya huta da jinin katafi² , gaba ɗayansu sun tausawa Sultana , sun daɗe a asibitin ganin Abba da Mami zasu tafi yasa Ashiru yace Hajiya ai kin ganeni ko ? Eh na gane ka kaine ka maido Maryam gida , Ashiru yace yawwa tou kuyi tafiyarku gida nan suna da malaman jinya , gaba ɗayansu suka tafi amma nayi imani da ɗiyar wani ce a cikinsu babu yadda za'ayi su tafi su barta da wannan darjejen ƙaton a ɗaki.
Yaya kace idan ina da buƙatarka na sanar dakai , Jiddah ce tsaye a gaban Dikko dake saka kaya take mishi wannan maganar wani irin kallo Dikko yayi mata cewa yanzu kina da buƙata na ne ? Eh , idan mace tana san kasancewa da mijinta ai bada baki take faɗa ba tunda ba magana bace da zaki faɗa na baki ansa , matsawa yayi ya kamota jikinshi yana cewa waye yace da baki ake neman miji ? Murmushi Jiddah tayi shima murmushi yayi dan Allah ya sani dama a takure yake baya so ne ya shiga haƙƙinta shi yasa ya ƙyaleta harsai ta buƙata da kanta , yana riƙeta ya aika mata da takardar neman yarjejeni babu ɓata lokaci Jiddah ta amince gado suka koma Dikko yaci gaba dayi mata sign......
Bayan sati ɗaya !
Na samu sauƙi sai abinda ba'a rasa ba , kuma duk kwanaki bakwai ɗin nan Dikko yake kwana dani Ashiru kuma saiya tafi , idan safiya tayi Ashiru yake dawowa su yini da Kaka Dikko kuma sai dare yake dawowa ya kwana ,
Hafsa kuwa saida aka saka mata wata roba a gefen cibiyarta ake fitar da dattin kalanzir in data sha dan ta ɓanɓameshi da yawa , ita kuma Amisty ke jinyarta idan Amisty ta yini sai Mom inta ta kwana.
Ga hidimar aurena kuma babu abinda aka fasa har an gurzo katinan ɗaurin aure nima na ansa na ajiyewa Dikko nashi idan yazo da daddare zan bashi dan idan Allah ya kaimu gobe lafiya akace za'ayi sallameni kuma Inna itama gobe zata dawo idan Allah ya kaimu muna cikin masu rayuwa.
Bello kuwa yaci duka na bala'e a wurin Dikko saida ya lalata mishi ido ɗaya sannan ya tambaye shi abinda ya haɗashi da An mata ? Bello yace ba komai , Dikko yace jin daɗi kawai kakeji ka kasheta ? Bello yayi shiru Dikko yace tou ko ka faɗamin abinda ya haɗaku har ka yayyakata da wuƙa ko kuma na jefaka cikin ruwa kada ta haɗeye ka banza ,
Munafinci yayi ma Dikko yace wani Yayan Babanta yasa shi ya kasheta saboda tana ta tayar da hankali ta anshi gadon su shine ni kuma ya bani kuɗi yace na kasheta , waye Yayan Baban nata ? Inda Dady yake zama da number wayarshi Bello ya bada , Dikko yace aje a ɗaukoshi cikin mintuna biyar , motoci suka hau suka tafi ɗauko Dady dan tunda Bello ya suma daya farko yaga Dikko sai ya koma yauma abinda yasa bai suma ba Dikko yace kana sake somewa wallahi saina sa an rufe ka da ranka.....
Bayan masu tafiya ɗauko Dady sun tafi Dikko ya kalli Bello yace dama kai ba wani ba inajin haushin ka dan ubanka yayi maganar yana yankawa Bello wani zaburarren mari harsai da haƙorinshi na ƙurya ya fita , Dikko yace ka ganeni ko ? Yayi maganar yana kai mishi wani irin halbi harsai daya fitar da jini daga bakinshi , duk kaine matsalata wai meme yasa bazan kashe ka ba.......?
Da ido ɗaya ya kalli Dikko dan ɗayan ya daina gani kwata² cewa kayi haƙuri , Dikko yace ai dama ba yanzu zan kashe ka ba kana tunanin zaka mutu cikin sauƙi ka sokawa "Yar matana wuƙa ? Kayimin tabunna a jiki matata ? Ka san irin mutuwar da zakayi ? Bello yayi shiru , Dikko yace to kullum saina reɗi sokar jikinka ina ba karnuka harsai ka ƙare.
A dai² lokacin da aka shigo da Dady , bayan an fiddoshi ne Dikko yaga mijin ƙawar Momy ne , ƙasa da sama ya kalleshi cikin kallon rainin wayau sannan yace ku tattarsu ku tafi dasu , jan Bello akayi aka sakashi a mota shima Dady mota ya koma suka tafi dasu daga gidan , shi kuma Dikko ya nufi asibiti....
A asibiti ya samu Sultan , fuskar nan a haɗe ba ɗan sakin fuska ni bana san wannan ɗabi'ar kullum ran mutum a haɗe kamar an aiko da saƙon mutuwa gareshi , wani irin ƙazantaccen kallo yayi ma Sultan dole tasashi ya tashi daga saman gadon ya nufi kujera zai zauna amma Dikko ya janye kujerar da ƙafa ya matso da ita kusa da gadon ya zauna yana cewa kinsha magani ,
Banza nayi dashi ban bashi ansa ba na kalli Sultan nace kazo ka zauna mana , murmushi yayi tare da cewa ai tafiya ma zanyi , nima murmushin nayi cewa karkaje yanzu ka tsaya , kallon agogon hannunshi yayi yana cewa dare yayi bara inje sai Allah ya kaimu Allah ya tsare hanya nayi masa yayi ma Ashiru saida safe ya fita , yana fita Dikko yace Ashiru saida safe , fita Ashirun yayi bayan yamin saida safe...
Ashiru yana fita yaje ya rufe ƙofar da makulli ya dawo ya zauna kusa dani yace idan ina miki magana baki bani ansa saina ɓata miki rai "yar rainin hankali kawai , gyara zama nayi cewa ai dama saboda baƙar zuciyarka yasa bazan iya aurenka ba nayi maganar tare da ciro katin ɗaurin aurena daga ƙasan pilo na miƙa mishi cewa wallahi Dikko ina sanka amma bazan iya aurenka ba har abadan duniya ,
Ansar katin yayi yana murmushi , ni kuma naci gaba da cewa kai a rayuwarka babu abinda ka sani sai zafin kai , doke² , ɗaure fuska gaka mahaukaci ga aljannu kamar iccen tsamiya ni taurin kai , kai kuma zuciya talauci da arziƙi basa zama wuri ɗaya dole idan ɗaya yazo ɗaya ya tafi , idan arziƙi yana nan talauci zai tafi , idan talauci yana nan arziƙi yazo dole talauci zai kama gaban shi , naji shi wannan ɗin kina sansan ne ? Eh ina sansa , tou ai ba akomai An mata nima da kika ga na kafe kai da fata na aureki bawai dan ra'ayina bane ba a , a muradin zuciya ne itace ta tirsasa amma farin cikinta a kullum bai wuce ta ganki cikin farin ciki ba , duk yadda take sanki dole zata kulle ne idan taga kin samu inda zakije kiyi farin ciki , kin gane ko ?
Kallona yayi da kallonshi mai tayar da tsikar jiki yace ina miki fatan alkairi ubangiji yasa alkairi ya baku zaman lafiya ai da kin faɗamin tun a gabanshi dana mishi Allah sa alkairi kuma saina riƙe hannunshi in jinjina masa cewa ina tayaka murna namiji mai sa'ar rayuwa.
Faɗamin yanzu me kike so na baki gudumuwa a matsayina na babban abokin amarya ? Yayi maganar cikin ƙarfin hali damuwa kwance a idonshi , bana san komai domin babu abinda ba'ayimin ba a gidanmu , murmushi mai ciwo ya sakeyi cewa yi haƙuri ai badan sun gaza ba abokin amarya fa.....?
Nace bana so , da hannunshi ya nune cewa to , to yi haƙuri ya canja maganar da cewa maganar wasu kuɗin gado da kike ta wahalar da kanki ba dare ba rana kiyi haƙuri ki daina maganar kuɗin ki faɗamin adadin miliyoyin da kike buƙata na baki ki bawa "yan gidanku a rufe matsalar , kallonshi nayi cikin idona nace ko naira ɗaya ne saina ansa domin wannan gadon shi zaisa na tabbatar cewa shima Babana yana da galihu , ganin na hasala da yawa ya miƙe yana warware kafet cewa bazance komai ba amarya tsautsayi gareta lallaɓa ta akeyi , a dai² lokacin daya dawo ɗaukar wayoyinshi na watsosu ƙasa ina kuka , baimin magana ba ya duƙa ya ɗauka ya koma saman kafet ya kwanata yana latse²nshi a waya.
Da gudu na sauko daga saman gado na koma wurin Dikko ina kuka , juyamin baya yayi ya sargafa bluetooth a kunnenshi fuskar nan babu wasa a cikinta yaci gaba da abinda ya shafeshi , gabanshi na koma cikin kuka nace bana sanka , murmushi yayi da gefen bakinshi hawaye kwance a idonshi yana kallon wayarshi amma baiyimin magana ba ,
Gemunshi na fizga cikin ɓacin rai , wata "yar ƙara yayi kaɗan cikin salon ɗaukar hankali wani abu naji yanamin yawo a jiki , gyara gemun yayi yana cewa saina dakeki zakije kiyi bacci ko ? Cikin kuka nace ka dakeni da Allah dakeni Dikko na ƙarasa maganar ina shiga jikinshi , da sauri ya fizgi wani irin numfashi ya fitar dashi ta bakinshi tare da lumshe idanuwanshi ya sauke ajiyar zuciya a wahalce cikin murya mai sa mutum ya shiga yanayi yace An mata fita daga jikina don Allah , bazan fita ba , yi haƙuri An ma fita kinji "Yar matana yayi maganar cikin sigar lallashi ƙara riƙeshi nayi ina kuka da ƙarfin bala'e ya ɓanɓareni daga jikinshi ya mareni , da sauri na tashi na koma saman gado na kwanta ina kuka , tsoki yayi ya koma ya kwanta cikin ɓacin rai yana magana ƙasa².
Kuka naci gaba dayi ni ba kukan marin nake ba kukan rabuwa da Dikko ne jibi kamar yanzu ina gidan Sultan , cikin kuka nace kuma ko rarrashin mace baka iya ba , ban iya ba kuma bazan iya ba , tunda kin samu wanda zai lallashe ki sai kije ya lallasheki , ai dan bayanan da kaga yadda ake tarairayar mace , waye yace namiji sai a gaban mace zai tarairayeta ki kirashi a waya yanzu ba kina da number shi ba ? Kirashi yasa ya miki natsuwa sakaran banza mai baƙuwar soyayya , bazan kira ba , sai Dikko da kika raina.......? Mtsw kimma ja ma kanki bara in sake jin ko tarinki kikaga yadda zanyi sukuwa samanki "yar yarinya kawai dake.
Shiru nayi tare dajan bargo zan lulluɓe yace sauka ki kashe mana waccan fitilar da kika kunna ma mutane , murguɗa bakina nayi ban sake ko motsi ba har bacci ya ɗaukeni kuma ban kashe fitilar ba , shi baya san kwanciya da fitila yace idan fitalar ɗaki yana a kunne wai ƙwalwa bata daina aiki , idan aka akashe shine itama kwalwa zata huta , Dikko kuwa jin Sultana tayi shiru ya tabbatar mishi da tayi bacci tashi yayi cikin damuwa yazo gaban gadon ya ƙurawa An mata ido a zuciyarshi yace wannan "yar yarinya Allah yayi mata tsatstsagar masifa , Allah yasa mijin naki yayi haƙuri da yarintarki ubangiji yasa ya riƙeki da amana Allah ya wadata mishi zuciyarshi da tausayinki An mata , haka Allah ya hukunta bani ne nake da rabo akanki ba saboda rashin haƙuri na cinye nawa rabon tun bisa titi...
Ina sanki ׳ Allah ka bani haƙuri da dangana akan rashin An mata , a bayyane yace haƙuri ma ai ya zama na dole haka Allah ya ƙaddara yadda da ƙaddara kuma imani ne , kashe fitilar yayi ya koma ya kwanta yana ta maimaita kalmar Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un , a wannan dare har garin Allah ya waye Dikko baiyi bacci ba yana cikin tashin hankali.
Misalin 11:09am aka bamu sallama , Sultan yazo ya ɗaukeni Dikko yayi mishi fatan alkairi tare dayi mishi nasiha wai An mata yarinya ce ya lallaɓata idan kuma tayi mishi laifi yazo ya faɗa mishi shine kaɗai maganinta , murmushi Sultan yayi yace ai baza tayi ba , Dikko yace ina san haka kuma a kula ta riƙa shan magani akan lokaci Sultan yace insha Allah har zamu tafi Dikko ya dakatar da Sultan yace inzo fita nayi naje wurinshi gefe muka matsa wurin motarshi yace An mata nasan kina da rufin asiri kuma duk wanda ya rufawa wani asiri Allah zai rufa mishi duniya da lahira dan Allah karki sake kiba kowa labarin abinda nayi miki ki rufamin asiri don Allah kinji ? Fashewa nayi da kuka ina ƙoƙarin rungumeshi yaja baya yana cewa mijinki yana kallonki jeki Allah yasa alkairi ngode.
Cikin kuka na koma mota Dikko ma ya shiga tashi yaja shine gaba mune baya , yana fita ya ɗauki hanya da tuƙinshi na ganganci kafin na ƙetfa ido tuni ya ɓace ko ƙurar motarshi babu , ci gaba nayi da zubar da hawaye yanayin Dikko yana burgewa komai nashi nidai yayimin Dikko yana da shiga rai sosai yana da farin jini amma matsalarshi zafin kai.
Har muka isa gida kuka nakeyi , ina fita daga mota nacema Sultan ya bari inyi wanka in dawo yace to....
02/11/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 70
*_Shafin nan gaba ɗayanshi sadaukar wane ga masoyan DIKKO a duk in da kuke a faɗin duniya , DIKKO na gaishe ku , ni kuma JAMILA MUSA nake muku fatan alkairi ku kasance a farin ciki , ina gaisuwa gareku domin ni kune maudu'una , farin cikina , gishirin rayuwar littafin KWARATA..._* 🤝🏻
*_na kuma miƙo gaisuwa gareku_* 👇🏻
*AMINA UMAR* _{ Ummieter }_
*HANEEY* _{ MRS KB }_
*HAWWA MUSA*
*RABI MUSA*
*AUNTY MUSA*
*HAFSAT NASEER*
*FADEELA LAMIƊO*
*HAJIYA A' I QERAU*
*SAFINA ALIYU KAROFI*
*ASIYA ILU BARDE* { MMN SUDAIS }
&
*ZALIHA GAMBO RAƊƊA...*
A rayuwarka babu abinda ka sani sai zafin kai , doke² , ɗaure fuska gaka mahaukaci ga aljannu kamar iccen tsamiya ni taurin kai , kai kuma zuciya talauci da arziƙi basa zama wuri ɗaya dole idan ɗaya yazo to ɗaya zai tafi , hawaye ne ya gangaro daga cikin idon Dikko bayan ya tuno maganganun da An mata ta jefeshi dasu , murmushi mai yagar zuciya yayi tare da kallon kanshi a madubi yana mai sakeyin murmushi wanda har saida kyawawan haƙoransa suka bayyana.
Wai nine mahaukaci ? Duk dana faɗa miki lalurata amma shine kikemin gori wai aljannu kamar iccen tsamiya kwantar da fuskarshi yayi saman sitiyarin mota a bayyane yace bani ne na ɗorawa kaina ba ƙaddara ne kuma haka yazo rubuce a cikin ƙaddarar rayuwata , ɗago kanshi yayi yaci gaba da kallon gabanshi dan tuƙi yake kuma har yanzu baije inda zaije ba , yaci gaba da addu'a ya ubangiji ka bani lafiya ka yaye min wannan lalurar ka bani haƙurin rashin An mata , goge hawayen daya zobo mishi yayi yana ci gaba da cewa wai duk girmana ni nake kuka wa mace , macen ma An mata ashe dama bata so na , wani irin duka ya kaima sitiyari a hayaniyance yace ni kika yaudara ? Nidai kika yaudara bazan taɓa yafe miki ba An mata kuma Allah bazai barki ba saiya min sakkayya ya ƙarasa maganar hawaye na rigangato wurin fitowa daga cikin kwarin idanuwan shi.
Har ya isa goruba ranshi a ɓace addu'arshi ɗaya Allah yasa kada wani ya hawoshi a dai² wannan lokacin da yake cikin ɓacin rai dan duk wanda yazo yana cikin wannan yanayi zafa a samu matsala , aljannu kamar iccen tsamiya ya maimaita a dai² lokacin da yayi parking , yanayin parking Yazeed ya fara gani ,
Fita yayi daga motar cikin tsananin ɓacin rai fuskar nan a haɗe , Yazeed yana ganin Dikko ya taso cikin girmamawa ya miƙawa Dikko hannu , bai anshi hannu ba yace ya akayi ? Cikin rawar murya Yazeed yace DK don Allah wani abokina ne aka kama wata ƙawarshi ta gayyaceshi zuwa gidanta sai mijin ya dawo ya ritsatsu dan Allah kayi magana yana sabon gari police station ,
Wani irin munafikin kallo Dikko yayi ma Yazeed , a hanzar ce Yazeed yaja baya yana kallon Dikko , tsoki Dikkon yayi ya fara tafiya Yazeed yabi bayanshi Dikko kuma yana magana cewe , baku da aiki kullum an kamaku wurin neman mata , nima yau an kamani na kasa fitowa , banyi maganin damuwa na bare inyi ma wani nashi , ina cikin ɓacin rai ka kama gabanka tun kafin in fara ƙwallo dakai....
DK ka duba lamarin nan don girman Allah kayi wani abu akai matsalar babbace , da sauri ya juyo yace kai........... Ka wuce fa , ganin idanuwan Dikko ba'a launin daya saba ganinsu ba yasashi juyowa da sauri ya dawo baya yana tunanin halin da abokinshi yake ciki.
Matsala ce ta neman duniya shi abokin nashi yana da wata buƙata akan wasu harkokin shi nayau da kullum shine malaminshi yace sai ya samo maniyin matar aure kuma saiya nemi matar a gidan aurenta a saman gadon da mijinta yake kwanciya da ita , a jikin hankicif kawai ake so a gogo sperm in shikenan zance ya ƙare , amma zai dawo zuwa anjima idan Dikko ya sauko , zuciyarshi tace a , a kawai kaje wurin Sultana a gabanka zatayi masa waya a wuce da damuwar nan , kai tsaye Yazeed gidansu Sultana ya nufo !
A halin yanzu zuciyata ta cika fal da Dikko , muradina shine naga na haɗu dashi maganar gaskiya so nake na kasance dashi domin inajin Dikko kamar wata runduna ta tsagin rayuwata idan har na bari Dikko ya tafi na shiga3 na tawa ta ƙare , fashewa nayi da wani irin kuka a toilet nace ina sanka ׳ mutumina.....
Sai ihu nakeyi a toilet babu mai jina saboda gidanmu cike yake da mutane "yan kawo lefe , kuma gashi gobe idan Allah ya kaimu ɗaurin aurena wanda za'a ɗaura 2:00pm idan Allah ya kaimu , saida nasha kukana har na gode Allah na fito daga toilet ko mai ban shafa ba na saka kayana , wayata na ɗauka na fara kiran wayar Dikko ,
Ɗauka yayi amma baiyi magana ba , cikin kuka nace Dikko gobe ne fa ɗaurin aurena , Ey ai kin faɗamin jiya da daddare ko kin manta , a , a ban manta ba ƙara tuna maka nayi fa , ina sane ban manta ba , to baza kayi wani abu ba ? Wani abu kamar me ? Shiru nayi ina kuka na kasa magana , Dikko yace Allah yasa alkairi ya baku zaman lafiya ina tayaki murna sosai yana faɗin haka ya tsinke wayarshi....
Wani irin ihu nayi wanda ya jawo hankalin duk wanda ke cikin gidan sukayo ɗaki wurina kowa yana tambayata lafiya ? Kamar baƙuwar mutane haka naci gaba da kallon mutane ɗaya bayan ɗaya cewa ya akayi ne ? Munji kina kuka ne , murmushin ƙarfin hali nayi cewa ba komai ni ba kuka nake ba wani abu ne ya faɗamin a ido , kowa Allah ya sawaƙe yayimin sannan suka fita.
Hijabi na saka na fita wurin Sultan dana baro a mota yana zaman jirana , dakel na ƙaƙaro farin ciki na isa wurinshi amma yanzu ban shiga motar ba a waje na tsaya , ki shigo mana , a , a , haka yayimin , bawan Allah ko murmushi baya gajiya dashi yace kodai naje na barki ki huta ne ? Cike da zumuɗi nace Eh , tada motar yayi yana cewa zan anso miki kayanki kinsan jiya mukayi dasu , godiya nayi masa tare da mishi addu'a Allah ya tsare hanya dan na matsu ya tafi wurin Dikko nake so naje , ina tsaye a wuri harya fita daga gidan yana fita motar Yazeed yana shigowa .{{{}}}
Inda Sultan ya ɗauke motarshi a wurin Yazeed ya ajiye nashi tare da sauke gilashin gefenshi An mata wurinki nazo , ai na sani tunda na ganka gidan nan dama nasan saboda nine kazo , to dan Allah ki shigo wani wuri zamuje muyi magana naga gidanku cike da mutane , babu wani jayayya ko tambayar ina zamuje na zagaya na buɗe mota na kame a gaba Yazeed yaja muka bar gidanmu!
Iyalin Dady suna cikin tashin hankali da damuwa dan tun jiya suke neman Dady babu shi ba labarinshi kuma wayayonshi duk a kashe suke , saƙo da lungu nemanshi ake amma babu wanda yaji ko ɓirɓishin inda yake , cikin kuka Momy tace saika tafi ka saƙe duk ka tashi hankalinmu ? Ka tafi babu bankwana shin wai kana ina ne ?
Wani irin gumji Dady keyi bayan an ɓanɓare Dikko dakel daga jikinshi yace baza ku faɗamin gaskiya ba ko ? Bello da wahala tasashi ya koma wata siffa daban tsakanin ranar daya yayyanki Sultana da wuƙa zuwa yau yace ranka ya daɗe wallahi shine yasa ni , yayin da shi kuma Dadyn yake cewa ƙarya Bello ke masa shine Dikko ranshi ya ɓaci yacicci ubansu yana cewa bazasu faɗa masa gaskiya ba suna masa wasa daa hankali ko ? Ya ƙarasa maganar yana ƙara kaiwa Bello halbi a baki.
Cikin kuka Bello yace wallahi bani bane shine , Dady yace wallahi ƙarya yakemin shine tunda shi ka kama da wuƙa kuma shi idonka ya gani ya yayyaka mata a jiki ni misali idan ma har zanyi kisa zan faɗawa wani ne ? Koshi sakaraine baisan shari'a ba ? Me yasa da nace yaje ya kashe ta baije ya faɗawa hukuma ba ? Ko zan hura wuta nace masa ya shiga yaje ya faɗa ? Idan har ka duba wannan abun kasan duk ƙarya ne sharri kawai yake nemana dashi bansan abinda nayi masa ba !
Bello ganin Dikko yaɗan so karɓar uzirin Dady yasa yace to ranka ya daɗe tunda naga kanshi ya sani baisan nawa ba kuma naga yana ƙoƙarin fita ni ya barni a ruwa bara na buɗe maka gaskiyar abun yadda shike....
Labari tiryan² Bello ya zayyanawa Dikko kuma ya ƙara da cewa kuma kwalbar da ita matar taje ta ɗauko yanzu haka tana hannun shi , wani irin ihu Dikko yayi yace saina kashe ku.............. Wayyo , wai...... Wai , wai Allahna , kai........... Wai , saina kashe ku wallahi kaine ka mayar min da matata daƙiƙiya ko ? Zai fara duka su Ashiru suka danneshi ƙasa dakel saboda ai har yanzu akwai munafirci a maganarsu abinda su suka fahimta kenan , ya akayi kwalbar ta dawo hannun Bello bayan shi yace wata tazo ta ɗauki kwalbar kuma an bada ita wa wani malami ? Shi malamin ya akayi yasan Bello kuma ya bashi kwalba ? Dole bazasu bar akashe su Bello ba Sultana ya kamata a nemo kuma a nemo inda matar data ɗauko kwalba take , bayan ankai Dikko ƙasa Ashiru ya koma mota da gudu ya ɗauko magani har yanzu Dikko zubar da yaranshi yake duk girmansu duk ƙarfinsu tuni tsoro yasa Dady suma shiko Bello yayi fitsari baisan adadi ba , sunga bala'e da masifar daya girmi nasu , dakel aka sake kai Dikko ƙasa aka zuba mishi magani dole tasa ya ɗauke....
Fiddoshi sukayi suka kaishi mota aka sake kulle su Bello sai mai gida ya dawo , Bello kuma maimaita kalmar matata kawai yakeyi , har yaushe Dikko ya auri uwar masu gida ? Lallai akwai bala'e ɗiyar Binna zata zama matar ɗan gwamna ? Surukar gwamna ? Sam wallahi abinda bazai yuwu ba kenan an ɗaura auren ko kuwa ? Wannan ansar ita ya kamata na fara sani farko kenan ,
Kwance zariyar wandon shi yayi ya matsa kusa Dady yayi masa fitsari a fuska , nan take ya farko , ɗaure wando yayi yana cewa zaune fa bata ƙare ba matarka ba ƙawar matar gwamna bace ba ? Cikin jin haushi Dady ya tashi ya kama Bello da kokowa yana cewa ni zaka zubawa fitsari ? Bello yace kai da Allah dan ka farfarɗo akwai sauran rina a kaba fa , saida suka caku suka rabu da kansu , cikin wahaltuwa Bello yace kaji wani aikin kuma ko ? Tou idan baka sani ba ɗiyar Binna ta zama matar ɗan gwamna ,
Da sauri Dady yasa hannunwan shi biyu ya goge fuskarshi tare da yarfarwa , yace aure ? Ta auri Dikko ? Yayi maganar yana fiddo duk girman idanuwanshi , Bello yace ba kana can ka suma ba yace matata kuka mayar min daƙiƙiya yace duk saiya kashe mu , Dady yace sam ba'ayi aure ba , Bello yace idan ba'ayi ba kenan ai zaice budurwarshi , tunda kuma anyi sai yace matata , Dady yace idan anyi auren nan saina rabashi idan kuma ba'a ɗaurashi ba babu ubanda ya isa ya daurashi duk cikar faɗin birnin garin katsina....
An mata kin fito da wayarki ? Yazeed ne yake tambayar Sultana ko wayarta yana hannunta bayan ya samu ƙofar wani gida yayi parking , E na fito da wayata na bashi amsa , An mata dan Allah ki kira DK kice masa yayi waya a sakar min abokina , daga ina za'a sakeshi ne ? Yana sabon gari police station kamashi akayi , laifin me yayi aka kamashi ? Gonar wani ya aura kuma ya samu damar tattare kaf amfanin gona , to ya akayi harya tsaya aka kamashi ? Yankin ya shiga ba ita matar tazo nashi yankin , kaima Yazeed wannan ai ganganci ne , Eh An mata amma dan Allah kiyi ma DK magana yasa a sakeshi , murmushi nayi mai ciwo nace Yazeed zanyi masa amma me yasa wai suke san fasiƙanci da matan aure ne ?
Mafi yawancin matan auren sune suke miƙa kansu wa mazajen waje ta hanyar ɓoye kawunansu su masu aure ne , kowa da irin matsalar dake shigar da ita bariki da aurenta , wasu rashi ne na talaucin abinda zasu ci ko sha , wasu kuma rashin basa samun gamsuwa ne wurin mazajensu , wata kuma tana da komai babu abinda ta nema ta rasa kawai ra'ayi ne ,
Tou su mazan me yake sa suna neman matan waje bayan ga nasu matayen a gida , gyara zama Yazeed yayi cewa mafi yawan mazan waje masu neman matan aure suna nemansu ne saboda matsalolin matansu na gida , wasu kuma suna neman matan aure ne saboda neman wani abu na samun duniya , me yasa dole sai a matan aure ake san samu ne ? Duba girman aure kuma ki tuno daraja wacce Allah yayi masa duk wanda ya ɓata matsayi da darajar aure ya halaka , nidai kira DK a fiddoshi , kayi haƙuri Yazeed gaskiya ni halin yanzu bana tare da Dikko , me yasa ? Haka nan na fita daga rayuwarshi ne dan ina so nima ya fita tawa rayuwar , wai miye tsakaninku ne ? Murmushi nayi a zuciyata nace anzo wurin , kallon Yazeed nayi cewa to kai a naka tunanin meye tsakaninmu ?
Wata "yar munafikar dariya yayi yana cewa muje kawai na maida ke gida yanzu banda lokacin magana dan hankalina baya kwance amma zamuyi magana daga baya , yayi maganar yana taka motar muka tafi , saida muka isa gida sannan mukayi magana dukanmu , Yazeed yace zai kawomin wata ƙawarshi matar aure ce amma tana wasan danbe , kinsan miye danbe ? Ya tambayeni ? Nace masa a , a , Yazeed yace aiko yadda kike hakan nan kika shiga harkar danbe abin zai miki daɗi zaki taka matakai masu girma zaki fito duniya zata sanki kuma sai kinfi ƙarfi DK wallahi ,
Murmushi nayi tare da cewa in banda abinka taya zan iya raba fili inyi wasan danbe da ƙatti majiya ƙarfi ne ? Murmushi Yazeed yayi cewa ba irin waccan danben ba , kawai kidai kije zan turota tayi miki bayanin yadda danben yake , fita nayi daga motar ina cewa Allah yasa tazo lafiya , da amin ya ansa ya fita gidan da gudu lallai yana tare da damuwa , bin bayan motar Yazeed nayi da kallo nace ɗan raini kenan kamar yadda nake kallon kaina a madubi haka nake kallon inda ka nufa , murmushi nayi tare da tinkarar hanyar shiga cikin gida da sauri.
Ina shiga palo Inna na fara gani ta kame saman kujera an wani waye an goge ta fito cikakkiyar hajiya ga haƙorin makka tasha kuma wallahi yayi mata kyau sosai , da gudu na ruga na rungumeta na fashe da kuka , cikin jin kunya take ƙoƙarin rabani da jikinta tana kallon idanuwan mutane ita a dole sai tayi alkunya irin tasu ta fulani , ke saukar min a jiki cikin kuka na sauka ina kamo hannunta cewa Inna zo kiji , da yanayin tausayi ta kalleni ta taso kuma ta biyoni , ɗakina muka shiga muna shiga na rufe ƙofa na sake ɓarkewa da kuka nace Inna nidai tsakani da Allah bana san auren nan.....
Cikin tashin hankali ta kalleni tace Sultana ki rufamin asiri wannan maganar ma ki barta tun farko , ni gaskiya bazan barta kawai kice wani abu na rantse da Allah bana aurenshi nidai bana sansa kawai biyayya nayi ma Kawu nayi tunanin zaicemin ko ina da wani da nakeso amma sai bai tambayeni ba , Inna tace aiko dai ko zaki mutu wallahi auren nan babu fashi ni zaki tona ma asiri dan ubanki , kinsan bakya sansa uban wa yace tun farko kika amsa musu , bakisan halin mutanen ba kina wasa da sha'aninsu ko ?
Cikin hayani nace nima kina wasa da nawa sha'anin bari in fita na faɗa musu bana san Sultan , Sultan in banza Sultan in wofi , wani irin wawan mari Inna tayimin , kamar zan hau bori nace wallahi bana auren Sultan saidai ki kasheni , to na yadda saidai ko ki mutun , aiko bana mutuwa zanje na faɗa musu bana san Sultan tunda ni ba tsoronsu nakeji ba na tunkari hanyar fita zan buɗe ƙofar ɗakin , fizgoni tayi ta maidani saman gado ita kuma cikin damuwa ta buɗe ɗakin ta fita ta kulle da makulli ta waje , da gudu na sauka daga gado naje jikin ƙofar naci gaba duka ina cewa bana so ׳ wallahi ,
Inna kuwa palo ta koma ta ɗauki wayarta ta kira Dikko , yana ɗauka ta fita waje bayan sun gaisa tace da Allah na dawo kazo ina san ganinka idan baka komai , lafiya dai Mama ? Ya tambayeta , gaskiya ba lafiya Sultana tana so ta sake tado min wata fitina da "yan uwana , bayan an tsayar da ranar aurenta duk kwanakin da suka wuce batace ta fasa ba saboda Allah saida taga gobe²n nan ɗaurin aurenta Dikko tace ta fasa ? Na rasa ya zanyi duniya Allah yayi ma Sultana taurin kai , murmushi Dikko yayi tare da cewa me ne ne matsalar ? Nidai kazo yanzu²n , zanzo idan anyi isha'e , a , a Dikko yanzu dai , gani nan zuwa........
Cikin ƙanƙanin lokaci Dikko ya iso Inna tayi masa jagora har ɗakina , Dikko yana da raini tsabar rainin shi duk mutanen dake palon ko ɗaya babu wadda Dikko ya gaishe da , haka ya wuto su yana musu kallon ƙyankyanmi fuskar nan haɗe kamar hadarin tsakar dare har ɗakina , ina kwance saman gado ina ta kuka dan na gaji da bugun ƙofa har na koma na kwanta.
Bayan sun shigo ne naji Inna tace ina zuwa ta fita , shi kuma ya shigo cikin ɗakin har bakin gadona kuma bai cire takalmin ƙafarshi , kallo ɗaya nayi masa na juya mishi baya naci gaba da kuka , jawoni yayi daga saman gadon na fizge na koma na kwanta , cikin rarrashi yace zo inji waye ya taɓamin An matana ? Taho ya miƙo hannunshi , saukowa nayi daga saman gado naje kusa dashi na tsaya , kallona yayi sosai sannan ya kamo hannuna na dama ya ɗora saman kafaɗarshi ya riƙe tsakiyar bayana yace kallarni yayi maganar yana murmushi , kallonshi nayi ina kuka , wai me ne ne ? Dikko ya tambayeni , kwanciya nayi saman ƙirjinshi nace bana sansa , ke yar raini bana so kinaji na ? Kinga zaki tayar da hankalin Mama kiyi haƙuri kinji jaruma ta ?
Dikko nidai bana sansa don Allah nayi maganar cikin kuka sosai ina mai ɗagowa na kalleshi , ƙarya kikeyi da bakinki kika faɗamin kina sansa kuma na tambayeki yayi miki kika ce min yayi sai yanzu kice kin fasa ? Baya yuwuwa wallahi duk wanda ya tsaya miki sai an ɗaura auren nan kuma babu gudu babu ja da baya , wallahi ko na tafi kika sake cewa bakiyin auren nan zanzo in tafi dake goruba jawoni yayi a jikinshi sosai sannan ya shafa bayana da lallausar hannushi yana cewa zakiji a jikinki , da sauri ya ɗagani jikinshi jin ana shigowa.
A dai² lokacin da Inna ta shigo tana ta faɗa cewa ai dama nasan duk yadda akayi Sultana tana da maziga ashe wai wani tsinan yaro ne ɗan mara mutunci take tare dashi , kusa dani ta matso ta yayyanka min mari tana cewa meya haɗaki da Dikko ɗan iska yaron da baya ganin kowa da mutunci garin nan , ke banda kike jaka marar tunani duk wulaƙanci da tozarcin da Dikko yayi muku kin manta ? Tou idan kin manta ki tuna saida Dikko ya haramta muku mazaunin gida , gararin rayuwa wane ne bakuyi ba sanadin shi ? Ki rasa abokin tarayya sai mutumin da silarshi kika yanki tikitin shiga karuwanci , sassauta murya tayi cewa ban san Dikko na tsaneshi matsashi mai ɗagawa da baisan darajar kowa ba , yau da zanga Dikko dasai na ɗauki wuƙa na soka mishi a ciki ya mutu tsabar wutar ƙiyayyar shi dake ci a cikin zuciyata ,
Kin samu za'a rufa miki asiri wawiyar banza a aureki amma da yake ke jakace har kike tunanin zaki ce kin fasa idan banda ma Allah yasa Sultan ɗin mai imani ne an faɗa miki zai iya aurenki ne ? Tou Allah ya rufa miki asiri ma yaso ki a haka da duk katsina kin rasa mijin aure , wayata taje ta ɗauko ta kawo ma Dikko tace ka duba cikin wayar ka ganomin lambar ɗan gwamnan ka kirashi yanzu²n nan ka rabashi da Sultana...
Daga ni har Dikko kallan kallo muke ma juna , cikin jarumta Dikko yace Mama ke baki san Dikko ba ? Ina fa zanso sanin lalataccen yaron nan , to amma waye yace miki yana tare da ya nuna ni , Sultan yake faɗamin yanzu yace ko rashin lafiyar da tayi Dikko shine yake kwana da ita kirawoshi....
Kallona Dikko yayi sannan ya kalli Inna yace ai ba buƙatar kiran shi , me yasa ne ? Inji Inna , saboda Dikko tuni yazo , yana ina ne ? Nine *DIKKO* kuma nine *DIKKOn* da kike nema........... Gani nazo!
0 comments:
Post a Comment