*_TASHAR TSAKAR GIDA , AN GAISHE DA MADUGUN SHIRI UMAR MAI SANYI..._*
Wata irin shewa sukeyi tasu ta matan tasha , gaba ɗaya sun haukata gidan da hayani suna ta nuna yadda sukayi maraicin junansu , bayan sun gama murnar haɗuwarsu kuma suka runguɗa sukayo kicin ɗina cike da gadara da nuna isa kamar irin gidan baban nan nasu.
Ina tsaye ina ɓare magi suka shigo dan na daina cin abincin gidan kwata² saboda duk idan na ci sai naji tashin zuciya sai nayi amai hankalina yake natsuwa shi yasa na zage nake girkawa da taimakon Nabeela.
Ko inda suke ban kallah ba naci gaba da abinda ya shafeni tunda nasan iskanci ne ya kawo su dan bama kicin ɗaya da Jiddah kowa da nashi , Nabeela tana zaune gefe saman kujera tana waya da ƙawarta suka faɗo tare da fara buɗe² , ke Mardiyya ƙara ruwa ki ƙara yawan magi ki zuba shinkafa bama cin kuskus naci uwar kuskus naci uwar mai dafa kuskus ɗin yarinya tayi magana in shaƙe mata wuyan uwa , duk inji Jiddah fa,
Hahaha suka gaggaɓe da dariya gaba ɗayansu tare da kashewa aka rangaɗa guda cikin iskanci , wacce tayi hoto dani tace yarinya kuma tace uhum taga yadda zamu naɗa mata shegen duka a gidan nan idan kin isa ki kalleni koda motsin kirki kiga yadda zamu ci uwar ɗiyar ɗan wasan caca , suka sake sheƙewa da dariya a dai² lokacin da Mardiyya zata zuba ruwa a tukunya ,
Jiddah kuma ta kwashe magin gabana tana cewa babu fa a gidan ubanta amma dan wani kilbibi hada wani zuba magi sai kace an saba ci a gida , wacce tayi hoto dani tace tsoho harya karci ƙasa baya gane testing in magi baya gane gishiri , Mardiyya tace taya kuwa zai gane bayan baki ya mutu da giya anzo nan za'a nuna mana ƙaryar rashin kunya dama ɗan talaka bai iya samun wuri ba , kashe waya Nabeela tayi tace ke ya zaki ƙara mana ruwa bayan kinga muna sauri shi yasa muke dafa abu mai sauƙi , kallona tayi sannan taci gaba da cewa matar Yaya ya kina kallonsu bazakiyi wani abu ba ? Kinfa san inajin yunwa a gabanki zaki bari a dawo mana aiki baya.....
Ke karki zuba ruwan nan , Jiddah tace zuba , Nabeela tace idan ko kika zuba su za'a samu matsala , ansar ruwan Jiddah tayi tare da zubawa tace ni na zuba "yar gadon rashin kunya marasa ragowa , ni bana neman suna haka kuma bana neman gindin zama tare da Dikko bare a kaɗamin ganye , masu so asan dasu kuma suke so su zauna su haƙuri ya duba dan gudun kar a korasu a koma cin ƙanzo da garin kwali danni a gidan Babana ban rasa komai ba , hehehehe bafa garin kwali ba garin kwaki , Oh 🤦🏻♀kinsan abinda baka sani ba danni bansan da labarin gari ba saida na haɗu da Caca
Yarinya tayi iskanci ta koma gidansu aje can aci gaba da cin abinda aka fi wayau dashi , Mardiyya tace sai Aliyu ya sake sakata a caca , Jiddah tace ni kuma zan siye gidan in ajiye karnuka tunda shi dawakai ya ajiye , cikin ɓacin rai Nabeela ta taso daga inda take itama dai "yar babbar bala'e ce ni kuma fita nayi daga cikin kicin ɗin cikin ɓacin rai , wani irin mari Nabeela ta zabga ma Jiddah tare da ɓaro ruwan daga saman gas cikin masifa tace shin ba nace karki zuba mana ba ? To zan sake zuba wasu idan akwai wata "yar ƙaramar mara kunya ta sake taɓawa taga idan ban ƙona mata fuska ba banzaye ƙazaman banza duk kun cika mana wuri da tsamin dauɗa.
Jiddah tace ni kika mara ? Nabeela tace an mareki dan ita Nabeela ba Sultana ta shigar ma faɗa ba cikinta take ma yaƙi sake ɗora tukunyar tayi saman gas ta zuba wasu ruwan , itama Jiddah ta sake ebowa ta ƙara zubawa akan wanda Nabeela ta ɗora sannan ta yanka mata mari wai ta rama marinta , sake ɓare ruwan Nabeela tayi suka sake tashar magana zuwa harshen turanci kowa yana faɗawa ɗan uwanshi kalamai masu zafi daga baya kuma suka fara bige².
Kokowa ta rikice tsakanin Jiddah da Nabeela tun a kicin har suka fito waje , Jiddah na cewa ke har kin isa kice muna tsamin dauɗa , Nabeela tace nafa sanki tun baki san abinda kike ba duk ƙaryar shafa turaren da saka suturar waye ya koya miki in ba ni ba ? Wato yanzu kin waye iskancin ki zai sauka a kaina ko ? Mutuncin da duk wani feleƙe ma nice na siya miki rigar mutunci a gidan auren idan na zare hannuna daga kanki kashin ki ya bushe dusar gero dake...
Mardiyya kuwa komawa tayi daga gefe taci gaba da video , duk yadda akayi a raba faɗan ƙin rabuwa sukayi domin Nabeela tsatstsaga gareta itama kafiya kamar na Dikko kuma ƙarfi gareta dan duk ƙawayen Jiddah shigar mata sukayi , faɗa yayi nisa kuma Nabeela taƙi ta haƙura gashi sunyi mata taron dangi dole saida aka kira Babbar ɗakinsu Dikko wacce ke zaulayarshi tana cewa saida tayi aure aka haifeshi , itace tazo kuma ko ita Jiddah bata ragamawa ba saida ta zagate tasss ta uwa ta uba.
Da mamaki ta kalli Jiddah tace ni kike zagi ? Na zageki dangi masifa ahalin rashin mutunci , bana tsoron uban kowa a cikinku duk wacce tayimin sai inci uwarta , haƙuri taba Jiddah tare da cewa ita Nabeela tazo su tafi , Nabeela tace bazata ko ina ba tunda bata jin tsoron kowa kuma idan ta sake ganin yarinya a kicin ɗin sai ta kunna mata wuta , tayi tsoki ta nufi kicin tana gunguni ,
Ina kwance ɗaki ta shigo taita zagina wai nice munafuka nazo da asiri dan na firgita Jiddah na hanata zaman lafiya da mijinta , saida ta zageni tas itama tayimin mari da ƙwanya ta tsitstsinen min albarka tayimin gori sannan ta tafi.
Daga gidan Dikko G H ta wuce taje ta faɗawa Momy sai an miƙe tsaye da addu'a akan Jiddah yau taga aikin asiri dan tunda take da Jiddah tun kafin asan zata auri Dikko tana ganin mutuncinta kuma tana darata ta amma yau saboda aikin asiri ita Jiddah ta zaga wai mune dangi masifa ahalin rashin mutunci bata tsoron uban kowa a cikinmu duk wacce tayi mata sai taci uwar yarinya , Momy ki duba lamarin nan fa duk da dai niɗin ina da zaulaya ina shiga sabgar yara amma ko Dikko da nake masa hawan ƙawara ina masa abinda bayajin daɗi duk rashin mutunci sa yana ɗagamin ƙafa ni Jiddah ta zaga ?
Gaskiya Momy kija linzamin abun tun wuri idan har kika bari Dikko yasan halin da ake ciki zaije yayi abinda bai kamata ba idan ya dakar musu "ya ko ya saketa zuminchie zai lalace , ya saki wannan karuwar tun abun nan ana iya dakatar dashi kafin yakai fagen da bakya iya tsawatawa , Momy tace taje zatayi magana da Dikko kuma zatayi magana da Jiddah.
Mardiyya ta turama Dikko video n faɗa ya gani amma baiyi magana ba kuma bai kira Nabeela ba nima daya kirani ban ɗauka ba , ya kira har ya gaji ya daina kira dan kanshi.
Mardiyya ita ta dafa abinci wa su Jiddah kuma haka ta barbaɗe shi tas da asiri takai ma kidahumar ta lashe , ni kam kafin Nabeela ta gama ta dawo har nayi bacci tsabar ɓacin rai......
Haka dai nake dogara rayuwar gidan Dikko babu daɗi tsakanina da "yan uwanshi sai kyara sai hantara ga gori basa so na ko kaɗan , Momy kuwa sai bawa Jiddah shawara takeyi tana ɗorata a hanya yadda zata zauna lafiya amma tana nan shawarar ke amfani da zaran ta tafi Mardiyya zata warwareta kaf !
Ƙawayenta ma haka suke wulaƙanta ni san ransu yanzu kwata² ma na daina fita ko palo kullum ina ɗaki sai sun gama iskancinsu sun tashi nake fita da sauri naje nayi abinda zanyi na dawo ɗaki bawai dan ina tsoronsu ba saidai dan gudun rayuwar da zanyi dan a halin yanzu idan nabar gidan Dikko bansan ina zanje ba , gidan Kaka yafi ƙarfina saboda gidan ɗan uwan Inna ne kuma ban auri ɗansa Sultan ba an buɗa , gidan Baba ƙarami bazaije gareni ba Dikko yasa an ɗaureshi saboda ni , Inna bata nan kuma har yanzu ban samu wayarta ba kuma babu wanda yace min yana waya da ita , idan na tashi hankali nayi faɗa da Jidda tabbas Momy zata iya korata idan an koreni nikam ina zanje ? Dan haka zaman gidan Dikko shine mafita zanyi haƙuri idan ma na tayar da hankalina Dikko ya sakeni bansan ina zan nufa da rayuwata ba ,
Ga Bello ga Dady suma duk ni suke jira , shin rayuwar bariki zanje inyi ? Shin zan dawwa a harkar bariki kenan ? Haƙuri shine maslaha kuma na haƙura , ina tare da damuwa sosai na rasa wa zan faɗawa inji sanyi dan haka kawai zan faɗawa Yazeed , dan yace mu haɗu a washe garin waccan ranar banje ba amma ina jira idan ya sake kirana zan fita idan har ya yadda zai bani mafita kuma zai zamar min garkuwa kawai zan fita daga gidan Dikko inje in auri dai² ni sai in zauna lafiya....
Kwance nake a gado ina nazari yadda rayuwata zata kasance idan na fita daga wurin Dikko , tsikar jikina ta tashi a dai² lokacin dana tuno ranar da zai tafi , yadda lokacin ya kasance yazo a zuciyata ya tsayamin kukan da yakeyi nakeji a raina sautin kukanshi cikin shagwaɓa Dikko baijin magana dana tuna sai inji hankalina ya tashi tsigar jikina duk ta mimmiƙe bana tunanin komai sai san kasancewa dashi , Dikko jarumin namiji ne a fagen daga ya iya jan linzamin mace a filin wasan danbe cikakken namiji ne mai zanawa mace natsuwa mara gogewa a rayuwa taya zan iya rabuwa dakai ne.....................?
Muna waya da Yazeed kuma har yanzu nace masa zamu haɗu amma banje ba banma fita ba gaba ɗaya , har Dikko yayi wata 3 da sati3 da tafiya kuma har yanzu ƙawayen Jiddah suna nan kuma suna hantara sbd sun nemeni da les naƙi , sun nunamin duk wani karuwanci naƙi yadda , da sukaji haushi sai suke tira Jiddah ta riƙa jamin sharri a wurin Momy , haka zata turo "yan uwan Dikko su wulaƙantani wani lokaci su mammareni , kawayen Jiddah kuma sunyi alƙawarin zasu jamin sharri wanda bana iya fitar dakaina a wurin Dikko wai ya sakeni in koma inda nafi wayau lokacin nice zan nemesu idan na nemi na abinci da wurin zama na rasa , gashi banda lafiya ni bansan abinda yake damuna ba sam bana san hayani kuma bana san yawan magana , Mardiyya kuwa tuni ta cire hoton da ƙawayen Jiddah suka ɗaukeni a wayarsu wanda suka ɗaukeni washe garin da aka kawoni ta turama Dikko bansan iyakar sharrin data faɗa ba ko na kirashi waya baya ɗauka rabon da nayi waya dashi tun ranar data tura mishi hoton ya turamin kuma ya kirani yace shi bazai sakeni ba duk abinda naji ina iyawa inje inyi kaina nayi ma, ba bugu ba zagi amma idan na kasheshi na huta , gashi shi baya tsayawa ya fahimceke idan dai ya sauke nashi shikenan ,
Na rasa wanda zanyi shawara dashi , da na fara tunanin su Amisty sai zuciyata ta gargaɗeni da na fita hanyarsu gara dai na faɗawa Yazeed tunda tun farko shine ya faɗamin cewa idan ina da damuwa na faɗa masa zai bani shawara , wayata na ɗauka na kirashi bayan mun gaisa nace yau zan fito ina zan sameka ne ? Wai yana jibiya , zanzo jibiyar wurin ina kake ne ? Ba'a kai jibiya ba kinsan me mujiya ? Ina ne haka ? Hirji matattara tantirai , yaushe zaka dawo ne ? Sai DK ya dawo , yaushe zai dawo ne ? Gobe idan Allah ya kaimu , zanzo hirjin , sai kinzo yana faɗin haka ya tsinke wayarshi.
Dakel nayi wanka na shirya cikin riga da siket na material cikin kayan da Yazeed ya kawomin wanda wurin kai ɗinkinsu ne Bello ya sossoka min wuƙa , kwalli kaɗai na shafa sai viseline dana shafama bakina kaɗa bayan na shafa mai da powder a fuskata , Nabeela tace nayi kyau kuma saida tayimin hoto , komawa nayi gefen gado na zauna bayan ta gama ɗaukana hoton ina neman sa'ar fita , wato inaji Dikko bai faɗa zai dawo ba kawai zaiyi mamaye ne dan da Jiddah tasan zai dawo ƙawayenta zasu bar gidan kuma dole zatayi gyara na musamman dan taci burin dawowarshi duk kuwa data kira aurenta dashi na ƙaddara ne.
Nabeela tana shiga toilet wanka na ɗauki jakata gyale na da makullin goruba na fice abuna , a bakin get na samu Umar muka gaisa yace Hajiya ina zakije ne ? Goruba na faɗa kai tsaye , yo ke baki san mai gida ya dawo ba ? Yana ina ne ? Yana abuja ai shi yasa ƙawayen hajiya zasu tafi nine na samo musu mota tasha baki ga har an fara fitowa da kayansu ba , waye ya faɗa musu ya dawo ne ? Ni na faɗa musu nima abinda yasa na sani Ashiru yacemin na gyara masa ɗakinshi kila shigowar dare zasuyi gobe idan Allah ya kaimu , daga cewa kayi shara sai kazo kayi ta surutu kai bakinka me yasa baya shiru ?
Dariya yayi tare da cewa tubani neke ranki ya daɗe , murmushi nayi cewa tou bani aron motarka na dawo , bani yayi na wuce na shiga naja nabar gidan cike da damuwa , naso ace Dikko ya samu ƙawayen Jiddah yaci ubansu , amma nasan ba saboda su yayi shiru da dawowarshi ba nasan dan Al ' Ameen ne , saida na fara zuwa goruba na gyara ɗakin na kama hanyar jibiya.
Wata irin zuba Al ' Ameen ya goge da boka ya kirashi a waya ya sanar dashi cewa Sultana tana da ciki , tashin hankali gashi Dikko zai dawo gobe kuma yanzu Zaria bata zuwa gareshi kuma boka ya tabbatar ma Al ' Ameen ita kanta Sultana bata san tana da cikin ba , idan kuma har Dikko ya dawo cikin bazai zubdu ba duk irin baƙin asiri da za'ayi shawara ɗaya yasan yadda za'ayi a zubar da cikin dan wallahi ɗa namiji ne zata aifa ,
Cike da tashin hankali Al ' Ameen ya kashe wayar ya kira Jiddah ya faɗa mata cewa idan har ta kuskura aka haifi cikin nan wallahi ƙaryarta ta ƙare duk yadda za'ayi a zuba mata abinda zata ci cikin ya zube , cikin rashin fahimta Jiddah tace wake da ciki ne ? Al' Ameen yace Sultana mana Jiddah tace yaushe ta samu cikin kuma waye yayi mata cikin ? Al ' Ameen yace mai aurenta mana , Jiddah tace ƙarya ne ai Yaya bai kwana da ita ba , Al ' Ameen yace tou tana dai da ciki kuma ɗa namiji zata haifa idan ko ta haifi ɗan nan na rantse da girman Allah ƙaryarki ta ƙare kisan yadda zakiyi da cikin nan ko maganin zubar da ciki ne ki bata a abinci ko abun shanta , saida Jiddah ta sunsunkuya zagi ta luƙaƙashi sannan tace ta daina cin duk abinci da ba itace ta dafa ba a gidan nan dan uban uwarta , shawara dai Al ' Ameen ya bata akan ta kira Yayyen mai gida ta sanar dasu ya faɗa mata abinda zata faɗa musu , godiya Jiddah tayi tare sa kashe wayarta tana neman mafita , kam ya zata yadda ita bata aihu ba sai wata data zo ɗazu da safen nan.........? Bazai yuwu ba koda duka sai sun fitar da cikin nan.
Da tambaya har na isa inda Yazeed yake tunda ni bansan wuri ba mutane ne sukayi ta ɗorani a hanya har naje , bayan na isa na sanar da Yazeed nazo na faɗa masa inda nake yace yana zuwa , an daɗe sosai sannan yazo ta wata munafukar santa ya fito da mota , gaba yayi nabi bayanshi munyi tafiya mai nisan gaske wanda har na fara tunanin na kawo kaina , wato abun ba'a cikin inda za'a gansu sukeyi ba sunyi nisa da mutane , daga inda yace na sameshi zuwa inda ake wasan tafiya ce mai nisan gaske inajin su kaɗai ne suka san wurin.
Muna isa na samu wuri nayi parking dandazon mata ne kamar ƙasa karuwai da suka ansa sunansu , murzajjin "yan iska da suka sha iskanci har sukayi gyatsa saboda lalacewa , wai ana gabatar da shirin wasan danbe babu jimawa , dan haka maganata Yazeed ya hana na faɗa wai in jira inga yadda ake wasan danbe sai muyi magana daga baya , haka mukayi ta ratsa mutane muna wucewa da yawa a wurin na sansu , Safiyya ɗiyar Baba ƙarami tana gani na ta taho da gudu tana zage² wai nice nasa aka kulle babansu , Yazeed ya dakatar da ita wai ta kiyayi kanta idan ba haka ba zai goge sunanta dama Kaka ta matsa masa yaa saka sunanta , laƙwas ta koma bata sake magana ba , gabana sai faɗuwa yakeyi nake bin bayan Yazeed , wato abinda na lura karuwan kila akwai manya akwai ƙanana domin an kasasu wuri daban² haka muka wuce har muka isa wani ƙaton wuri , tsakar fili ne na gida amma an zagaye wani wuri daban an ɗaga wurin da ciko yayi sama yadda duk inda kake zaka iya hange kamar dai yadda akeyin na restyling daga saman wurin kuma an ƙawatashi da wasu irin manyan katifai da pilaluwa an shinfiɗe da zanin gado ,
Wurin wasu lafiyayin maza ya kaini duk gajeren wando ne a jikinsu wai in gaisa dasu sune mazan da zasuyi wasa , murmushi nayi kaɗan na anshi karka rasa fuskata ɗauke da damuwa , bayan mun gaisa yace musu matar DK ce , DK 😳 suka zazzaro ido da mamaki sannan suka bini da kallo har naji babu daɗi , bayan sun gama kalleni tsaf sukace tou su babu ruwansu suka ci gaba da lissafin kuɗinsu , Yazeed yace taho nan ki kyalesu matsoratan banza ,
A , a , ni tafiya zanyi kawai mayi waya ai bansan haka wurin yake ba , Yazeed yace da Allah ki jira kiga danben dana baki labari kwanaki baki sani ba , a , a basai na kalla ba , wayarshi ya ciro a aljihu yana cewa tsaya ki gani mana kafin na ankara ya ɗaga wayarshi ya kwaso mu hoto solfie , zan masa magana akan me yasa ya ɗaukeni hoto Amisty ta shigo da gudu ta rungumeni cikin farin ciki da sauri na juya amma Yazeed ya ɓacemin , wata irin zuba ta ketomin yayin da zuciyata tace bakiyi zufa ba tukun ƙaryarki ta ƙare......
Amisty tace ai ana cemin kinzo kinji daɗin da naji , cikin tashin hankali na saki Amisty nabi hanyar da zan nemo Yazeed iya dubawa ta ban ganshi ba , tou me yake nufi ko ya ɗauka ne dan ya riƙa hansar kuɗaɗe a wurina kamar yadda na riƙayi a baya ? Kwawalwata tace ya ɗaukeni dan ya turawa Dikko idan ya gani zai sakeki shi kuma saiya ɗaukeki ya sakaki a danbe yana kasuwanci dake dan dama haka ya faɗa a baya.......
Dariya Yazeed yayi a dai² wannan lokacin cewa alhamdulillah nasara tazo haba ina zan bar DK da wannan babbar ƙaddarar ? Yarinya kyakkyawa mai kyan diri da siga mai ɗaukar hankalin duk wani lafiyayen namiji , kai ko mara lafiyar ya ganta dan ubanshi saita burgeshi munafiki ya samu "yar yarinya yana hutawa abunshi ai ba taka bace ba wannan nagartacciyar surar , tunda dai ban aura ba gara kowa ya rasa , ka tsere ma kaf abokanmu a naira riga mota matar ma sai kafi kowa ? Idan mun yadda kenan kai mana wayau , yadda nake ƙarƙashin ka gara na samu ko da macen na tsira , kai sarkin dabara kawai kaje ka ɗauko ɗanyen jini dan ka bamu wahala haka zamuje muna ganinta hankalinmu yana tashi to ni burina kawai ka saketa hankalina ya kwanta dan nan gaba yarinyar nan ta goge bata riƙuwa ga kuɗi ga hutu ga gayu dan yadda DK yake ɗan gaye dole komai nasa ya zama ɗan gayu , gara ni in kwasheta idan kuma bata aureni ba sai kawai in barta a wasan danbe nasan duk lokacin dana buƙace ta zan ɗan rage zafi uwa uba kuma zan linka arziƙi dan duk katsina banga irin mazan da zanba ita ba.
Na nemi Yazeed har na gaji ban ganshi ba , kuma na kirashi bai ɗauki waya ba , dan haka na haƙura na fito daga inda nake dubashi na sake dawowa wurin da ake taron danben a lokacin wurin ya cika taf tsit kake ji babu wata hayani ana kiran sunaye....
Hamida Aliyu Muhammed Binna , shine sunan da naji an kira tsagal² ta tashi ta shiga saman filin aka ɗauki ihu da tafi yayin da wasu ke busa usir , idan mutun ya shiga filin saiya tsaya ya kalli mutane sannan ya tuɓe kayanshi ya tafi da kwarkwasa ya hau saman katifa , sai a sake kiran wata itama haka zatayi duk sai an gama kiran sunayen matan sun hau katifa sai a kira mazajen da zasuyi wasan su jera layi sai aci gaba dakai naushi.
Banda lokacinsu domin ina tare da tashin hankalin daya fi wanda naga Hamida a ciki tunda ita tayi kuma kowa yasan tayi fita nayi daga wurin ina kuka , nifa ? Ina hotona zaije ? Kai nidai jakace.......
Aunty kusan abinyi fa dan Caca ciki gareta kuma wallahi ko ranar da aka kawota Yaya dani ya kwana a ɗakinshi kuma washe gari ya tafi amma tana da ciki , idan har ya dawo ya samu cikin nan zai yadda yace nasa ne saboda ta gama dashi za'a ɓata muku ahali shege ya fito a cikinku , idan kuma aka saketa ta fita da cikin nan shima idan ta haife cikin shima shine zaice nasa ne , gobe zai dawo meye mafita ? Zan shigo idan Allah ya kaimu suka ajiye waya , bata faɗawa Momy ba kawai ta yanke hukunci a kanta....
Sai bayan isha'e na dawo gida a gajiye a waje na bada makullin motar Umar a ajiye mishi idan ya dawo , Nabeela tana gani na tace ke kinji kunya kika shigo da cikin shege a gidan aurenki , kin ɗirka dabkekiyar asara ai Yayan zai dawo zaki faɗa masa a gidan uban waye kikayi ciki...
Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji na wuce ciki ban nuna damuwa ba , ikon Allah ashe ciki gareni ? Allahu akbar sai yanzu ma na tuna da yaushe rabon da inyi jinin al'ada , daɗi naji sosai a zuciyata addu'ata ta farko Allah yasa in haifi mai kama da Dikko komai da komai , tunani na biyu ya akayi suka san ina da ciki bayan ni ban gane ba ? Can su suka sani dai , kuma Dikko zaizo ya faɗa musu shine yayi cikin ba cikin shege bane ba , da farin ciki nayi bacci tare da tunanin Dikko.
Da asuba bayan nayi sallah bacci na koma , ban daɗe da kwanciya ba na tafi bacci yauma ya bayyana a mafarki na , kinga inda ya ajiye ne ko kuwa ? Ya tambaye ni , ban gani ba kuma na tambayeshi yace baya san surutu , tou albishiri na kwakwale amma yau ba'a mutu ba kina da ciki kuma zasu zubar da ciki kiyi ƙoƙari ki samoshi idan ba haka ba haɗuwa ta gaba tafiya ce babu fashi , waye zai zubar dashi , ta inda mutumin nan ya fito a ranar da nayi mafarki a goruba yauma ta wurin ya fito ya kamashi da kokowa , yana cewa waye yace ka faɗa ne ? Kokowa sukeyi sosai har mai cewa ya kwakwale ido ya samu damar cire abunda mutumin ya rufe fuskarshi , Al ' Ameen na faɗa lokacin da aka cire abun daya rufe fuskarshi a dai² wannan lokaci naji saukar bulali a jikina......
A firgice na farka daga bacci Jiddah da Yayar Dikko suke ta dukana babu ji babu gani , da sauri na sauko daga saman gado ina cewa me nayi muku ne ? Jiddah tace dole ki tambaya abinda kikayi tunda kinje kin samu an ɗuro miki ciki ke zakici dukiya tou Allah ya warware miki asiri tun ba'ayi nisa ba , riƙeni Yayarshi tayi Jiddah tayi ta kaimin duka a ciki da bokitin ƙarfe wani irin ihu nayi nunfashina ya tafi sama na kasa kwacewa , saida ta gaji sannan suka danneni ƙasa Yayar Dikko tayi min allura suka fita daga ɗakin bansan inda kaina yake ba.
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Dikko ya faɗa tare da cewa Ashiru An mata wani abu ya sameta , Ashiru yace me kuwa zai sameta mai gida , Dikko yace tabbas wani abu ya faru wallahi dan naji a jikina wanda rabon da inji haka har na mata kiramin ita , duk kiran da akayi ma Sultana bata ɗauka ba , cikin tashin hankali yace kiramin Nabeela itama bata ɗauka ba , Jiddah yace a kira , itama bata ɗauka ba dan tabar wayarta a ɗaki tana ɗakin Dikko ita Mardiyya wai suna gyarawa , Mardiyya yasa aka kira tana ganin wayar Dikko ta fita daga wurin Jiddah sannan ta ɗauka , bayan ta gaishe da Ashiru yace mai gida yace kina gida ne ? Eh , tou meya faru a gidan ? Saida tayi dube² tace nidai naji ana cewa an zubar da cikin Aunty Amarya....
Kallon Dikko Ashiru yayi tare da cewa mai gida wai bata gida bayan ya kashe wayar , tsoki Dikko yayi cewa tafiya katsina ya kamani yanzu , Ashiru yace ka bari sai anjimar mana , umm umm muje yanzu , kallon agogo yayi yace la'asar tayimin a katsina.
Mardiyya kuma komawa tayi suka ci gaba da aikinsu , Nabeela kuwa bata nan bata san abinda akeyi ba dan tana makarata , su kuma hidimarsu sukaci gaba dayi mai kwalliya ta musamman Jiddah ta gayyato danni taci gayu yadda zata yaƙi zuciyar Dikko , Mardiyya ta tsareta da kallo mai tattare da maganganu.
Sai bayan la'asar Nabeela ta dawo har yanzu ina kwance a wurin da akamin allura na suma har na dawo da kaina na kasa ko motsin kirki wani irin ciwo cikina kammar raina zai fita , cike da fargaba Nabeela ta durƙusa gabana tace waye yace miki ana zubar da cikin shege a gida ? Daga na faɗa miki sai ki kashe kanki tou ni tafiya zanyi wallahi bakija min sharri , tana faɗin haka ta miƙe ta fara tattara kayanta , bata gama haɗawa ba Dikko ya bayyana a ɗakina misalin ƙarfe 4:29pm.
A tsorace Nabeela ta gaishe shi ta fita daga bedroom in , bai ansa gaisuwar ba ya nufo inda nake , hararata yayi cewa wani kuma sabon rashin mutunci ne kwanciya a ƙasa ? Yayi maganar yana ɗan tauna cingom bakinshi a rufe , kifa kaina nayi ƙasa dakel nace banda lafiya , me ya sameki ya tambaya cikin sigar lallashi....
Shiru nayi , da damuwa fa , banda lafiya ga naje wurin Yazeed kuma ban san laifin da nayi ma Dikko ya daina ɗaukar wayata ba , idan kuwa ya gano ni yau idan ya fara dukana waye zai ƙwaceni gashi ban iya tashi.........?
24/11/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA.....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 81
Me ya sameki ne ? Ya sake tambaya a karo na biyu , nayi ɓari ne , kallon ɗakin yayi sannan ya dawo da kallonshi wurina yace wane ɓari ? Yayi tambayar a cikin rashin fahimta , ina da ciki ne shine ya lalace , ɓacin rai kwance a idonshi ya gyara zaman hular saman kanshi ya duƙo inda nake kwance sai yanzu ya lura da jinin dake kwance a wurin , shi bai gani ba amma Nabeela tun shigowarta ta fahimta , cikin tsananin ɓacin rai yace ban gane ba fa....
Ban sake magana ba daga haka dan maganar ta isheni kuma a wahalce nakeyinta , Nabeela........... Ya ƙwala mata kira da sanyayayyar muryarshi , da gudu ta shigo jikinta yana kyarma ta tsaya daga can gefe cewa Yaya gani , bai kalleta ba yace me ya faru ? Cikin rawar murya tace Yaya wallahi , tare ta yayi da cewa karki cemin wallahi² me ya sameta ?
Yaya ina makaranta , karki faɗamin kina makaranta me ya faru.............. ? Idan na sake magana zan kashe ki...... , cikin kuka tace matar Yaya ki faɗa masa abinda ya faru bayan bana nan , ke karki ɗaukeni sakarai ai na ganta na kiraki , nunawa yayi da hannunshi ya fara one , two , three , four cikin rawar murya tace Jiddah........
Ba damuwa na Jiddah ba abinda ya sami An mata nake tambayarki , ƙara fashewa tayi da kuka ta sake kallona tana cewa matar Yaya kiyi magana , tashi yayi yaje gabanta ya yanka mata wani irin mari harsai da ta duƙe yace idan kika sake mata magana saina karya miki maƙoshi me ya faru........?
Yaya wallahi bana nan naje makaranta yanzu na dawo lokacin da zan tafi na barta tana bacci , a ina take baccin ne ? Saman gado , ya akayi ta sauko ƙasa to ? Kila ta tashi ne ta faɗi , jeki palo ki jirani zan fito idan kuma kika kuskura kika bar gidan nan na rantse da Allah saina baki wahala , cikin kuka tace tou sannan ta fita.
Dawowa yayi kusa dani , ya kalleni yanayin shi ya nuna yana nazari ne , bayan wani lokaci yace tashi , a tsorace na fara ƙoƙarin miƙewa amma na kasa , da Allah tashi bana san iskanci , tou na faɗa tare da tashi durƙushe dakel , tsugunawa yayi gabana yace ya akayi ciki ya lalace ? Yayi tambayar da harshe mai tada hankali , fashewa nayi da kuka nace Dikko , An mata ya akayi ciki ya lalace ya tsareni da idanuwanshi masu tada hankali idan yana fushi , kayi haƙuri na faɗa cikin rawar murya , bansan shi ba yaci gaba da cewa wato banda iskancin hotunan da kikayi har ma kike tunanin zan barki ciki ya zube ? Ba zubewar ciki ba yau ko naƙuda kikeyi saina zaneki , tashi kije ki gyara jikinki yana faɗin haka ya fita daga ɗakin.
Gaba ɗaya ji nayi kamar an tsintsinkemin lakar jikina , idan kuma Dikko yasan naje wurin Yazeed wace matsalar zan fuskanta ? Ya zanyi ? Ni ba lalacewar cikin ne damuwana ba rayuwar da zan fuskanta idan ya gano cewa na fita naje wurin Yazeed , dakel na shiga toilet dan wanka ,
Cikin tsananin ɓacin rai yaje ɗakinshi , gefen gado ya zauna ya dafe kanshi , zuciyarshi tana mishi babu daɗi miƙewa yayi ya matsa jikin window ya zuge labile yana kallon yadda rayuwar gidanshi ke tafiya , kowa sabgar gabanshi yakeyi ɗora fuskar shi yayi jikin window ya dafa hannunshi a sama yana kallon waje , a zuciyarshi yake zance cewa An mata baki da lissafi ko kaɗan na rayuwa , ina baki dama ta rayuwa amma baki gane abinda nake nufi dake sai idan bana nan duniyar zaki san ni ɗin na gina miki rayuwa , baki da Baba mahaifiyarki ba take , take ba tana can ta kama sabgar gabanta tana gina sabuwar rayuwarta , baku da ahali mai kyau kwata² , Jiddah ce ta shigo ɗakin da sallama.
Ansawa yayi tare da juyowa ya kalleta so ɗaya ya koma yadda yake yaci gaba da zance zuci "yar rashin kunya da kinsan ina tausayinki iskancin da zaki zazzaga a gidan nan ba ɗan ƙarami bane ba mu zuba dani dake duk wanda ya fasa yaji kunya , tashi yayi a wurin ya nufi hanyar toilet yaga Jiddah zaune a gefen gado , ya akayi ne ? Ya tambayeta cikin kwarkwasa tace ba komai ta ƙarasa maganar tana kakkaɓa ido dan ibar mishi hankali , tou yayi jeki zanyi wanka , tashi tayi tana mummurza tafiya da salo mai ɗaukar hankali ta nufi wurinshi.
Murmushi yayi ya bita da kallo harta iso wurinshi ta shige jikinshi , ajiyar zuciya ya sauke tare da riƙeta sosai yana kallon fuskarta da tasha ado da kwalliya , ɗan shanye idon dama tayi tare da cewa nayi ne ? Sassauta ganinshi yayi tare da ɗauke idonshi baiyi magana ba , gyara tsayuwarta tayi ta fara rattafa bayani kamar yadda Mardiyya ta turota cewa.
Bayan Jiddah da Yayar Dikko sun gama dukan Sultana Jiddah ta kwakwkwaɗa mata bokitin ƙarfe a ciki suka danneta suka ɗura mata allura , suna gamawa suka fita a ɗakin , bata samu Mardiyya a ɗakinta ba data koma tana wurin Al ' Ameen , dan itama Mardiyyar tana gama ɗaukar video ganin zasu fito yasa ta fice da sauri ta ɓoye ƙasan bene , suna wucewa tayi wurin uncle.
Uncle gabana faɗuwa yakeyi fa , da Allah can matsoraciyar banza badai kinyi video ba ? Eh kwantar da hankali yau duk bala'e ni na faɗa miki gaba ɗaya gidan nan zai watse , tabbas idan mai gida yaji labarin ɓarewar ciki ranshi zai ɓaci , da zaran yayi fushi baya iya saita kanshi dan haka zai fara duka babu ji babu gani kuma bazai saurari kowa ba , abinda za'ayi yanzu ki faɗawa Jiddah idan mai gida ya dawo taje ta faɗa masa , murmushi yayi tare daci gaba da cewa zai sakesu gaba ɗaya , ita Sultana zai saketa saboda hoton nan , ita kuma Jiddah zai saketa ne idan ya daketa zatace bana auren duka sai ka sakeni dama mun rufeta da wannan asirin duk wanda yazo zatace bazata zauna ba sai an saketa tabbas saiya saketa , Yayarshi kuma bayanin hukuncinta yana wurin Jiddah dama itace ƙatuwar munafukar kinga sun rabu kawai sai kuyi aurenku ya faɗa yana murmushi , kina shiga sai ki haihu idan namiji ne sai mu kashe shi mu cinye dukiyarshi , idan mace ce sai a bari sai an ƙara , dariya sukayi tare da tafawa....
Bara inyi wanka in fito Dikko ya faɗa tare da fitar da Jiddah daga jikinshi , gefen gado ta koma ta zauna tana jiran fitowarshi shi kuma ya shiga toilet....
Lokacin dana fito daga wanka Nabeela ta gyara wurin dana ɓata tass kuma har yanzu bata daina kuka ba , ina fitowa toilet ta shiga da kanta ta wanke kayan dana cire ta wanke toilet in , bayan ta fito tace matar Yaya tsakaninki da Allah ni ina nan wani abu ya faru dake ? Ko inda take ban kalla ba na fara saka kayana.
Har Dikko ya fito daga wanka Jiddah tana nan , saida ya gama shiryawa yana saka kaya tace Yaya gaskiya abinda Aunty Rabiya takeyi bata kyautawa , Yayarshi kenan , ba tare daya kalleta ba yace me tayi miki ne ? A dai² lokacin da yake ɗaura belt a ƙugunshi , kaga dai ko ni kishirya Caca bana iya yimata irin abinda ita Aunty tayi , a dai² lokacin da yake saka riga , yace kiyi maganarki kai tsaye mana yana kallon kanshi a madubi tare da gyara zaman rigarshi , Caca ce take da ciki shine tace sai ta zubar dashi dan ita ƙawayenta sunce babu aihuwa a tsarin rayuwarsu , tsayawa cak Dikko yayi tare da daina ɓalle botiran rigarshi ya kalli Jiddah ta cikin madubi , data faɗamin zata zubar da cikinta dan ita zatayi gaba , shine na bata haƙuri tace bata yadda sai ta fitar ita ba zata zauna wani rainon ciki da "ya "ya ba taje ta tsufe ta lalata ƙuruciyarta , ni kuma sai nayi ma Aunty Rabiya waya a matsayinta na babba tazo tayi ma Caca magana dan karta zubar da cikin , shine tace ita ai bata so ka haihu dama shine fa tazo tayi mata allurar zubar da ciki....
Shiru Dikko yayi yana addu'a a zuciyarshi dan ya saita kanshi amma ya kasa sarrafawa , yayi ya riƙe yaƙi riƙuwa , a zuciye ya fita daga ɗakin zuciyarshi tana tafarfasa da wurin Momy zaije amma yana kawowa ƙofar ɗakin Sultana yaji baya iya wucewa , shiga yayi Nabeela tana ganinshi ta durƙushe irin gani na miƙo kaina , bai kalleta ba ya kalleni yace nidai ko An mata...... ? Dikko dai ko ? Ya tsareni da ido , kayi haƙuri , kamar jira yake inyi magana yace ke............. Saina kashe ki ya fara wani irin gurnani mai tada hankali , da gudu Nabeela ta fita tana neman ɗauki dan ita a tunaninta itace Dikko ya faɗa zai kashe , cikin sanyi nace ba komai kashe ni na faɗa hawaye na gangarowa daga cikin idona , dan bana iya tashi , nunani yayi cewa rufe min bakin munafuka jaka dake da bakisan inda duniya ta nufa ba na tsaneki....... Bana sanki haka kuma bana san ganin ki ya faɗa tare da kaimin wani irin halbi yana ci gaba da cewa ai baki burgeni ba da baki haɗa hada kanki kika mutu ba , bani kika cuta ba rayuwarki ce , zanje in dawo yau mai kwatarki a wurina sai Allah banza ƙazama.....
Fuuuu ya fita daga ɗakin , a palon ƙasa ya haɗu dasu Ashiru ko inda suke bai kalla ba ya wuce ya fita da sauri ji yayi G H tayi masa nisa wani irin ihu ya kurmama mai tsananin tada hankali ya durƙushe a wurin wai....... Wai , wai Allahna , wayyo , kai.........saina kashe kaina ya riƙe wuyanshi da ƙarfin bala'e , duk yadda akayi a ɓanɓare hannun Dikko daga wuyanshi yaƙi fita , kuma daga durƙushen an kasa kwantar dashi tashin hankalin ya girmi tunanin duk mai tunani , a ruɗe Nabeela ta fara kiran wayar Momy amma bata ɗauka ba , Yayarsu ta kira ta faɗa mata sannan ta turawa Dady text kuma har yanzu Dikko bai kwanta ba kuma bai cire hannunshi daga wuyashi ba har yaji ma kanshi ciwo jini yana fita daga wuyanshi.
A wannan halin Dady ya samu Dikko idan hankalinshi yayi dubu ya tashi , itama Yayarshi haka tazo ta sameshi duk wani mai san rayuwar Dikko haka suka zo suka sameshi har Momy kuma zuwa wannan lokacin ya daina lumfashi gaba ɗayanshi ya ɗauke , Ashiru Dady ya kalla yace me yayi zafi haka ? Cike da damuwa Ashiru yace muna Abuja yacemin yaji gabanshi yana faɗuwa tabbas wani abu ya faru da Hajiya amarya shine yace in kirata dama sun kwana biyu basa waya ni bansan abinda ya haɗasu ba , Momy tace shegiya ɗiyar matsiyata idan wani abu ya samu ɗana itama sai an ratayeta.
Hannu Dady ya ɗaga mata ya dakatar da ita sannan yace ma Ashiru ina jin ka , sai na kirata bata ɗauka ba , yace na kira Nabeela itama bata ɗauka ba itama Hajiya Jiddah shine yace na kira Mardiyya bayan na kirata na tambayeta tana gida tace min Ey nace me ya faru a gidan ne ? Shine tacemin ita dai taji ana cewa an zubar da cikin Aunty amarya ne , bayan na gama wayar nace masa Mardiyya bata gida gudun karya shiga damuwa shine ya matsa muka taho katsina , ni daga haka bansan komai ba.
Dady yasa aka kira Mardiyya bayan tazo ya tambayeta abinda ya faru , tace Aunty Rabiya ce tazo tayi ma Aunty Amarya allurar zubar da ciki , Rabiya zatayi magana Dady yace ta rufe mishi baki , shiru tayi tana kallon Jiddah , Dady yasa aka ɗauki Dikko gaba ɗaya kowa da kowa aka nufi ɗakinshi dashi , a ƙasa Dady yasa aka kwantar dashi sannan ya umarci kowa ya fita har Momy , fita sukayi gaba ɗayansu , magani ya fiddo a cikin wata kwalba ya zuba mishi a kunne dan tun lokacin daya bi Dady ranar da gaya hotunan Sultana zata sha giya idan baku manta ba ai a ranar ya fara faɗa zai kashe kanshi , daga nan Dady yace zasuje saudiyya sai aje da Dikko wurin magani , salati yayi tare da buɗe idonshi , Dady yace Babana ka rufa man asiri ka barni na zauna lafiya.....
Kai......... Saina kashe Rabiya..... Riƙeshi Dady yayi idonshi ɗauke da hawaye yace yi haƙuri Babana , a , a , saina kasheta......... Kuma saina ɗaure mijinta daya barta take fita har tanayin iskanci a gidana birkicewa yayi daga hannun Dady yayo waje da gudu , Rabiya na ganinshi ta sauka ƙasa da sauri amma kafin ta ida gangarawa ya rigata sauka saboda shi ta sama ya sauko , yana ƙoƙarin riƙeta tace Jiddah ce...... Jiddah tana gani kowa yana rugawa amma sai ta tsaya , sokewa yayi saman guyawunshi zuwa ɗaya yayi mata ta faɗi ƙasa somammiya miƙewa yayi da gudu yabi Rabiya Dady yace ku riƙeshi mana , kai......... Karku taɓani idan kuka taɓani saina kashe kaina , daf da zata fita daga cikin palon yayi mata wani irin halbi ta fice somammiya , itama An mata saina kashe ta........... Dady yace wai bazaku kwantar dashi ba , wata irin zabura Dikko yayi bana kwanciya ya nufi hanyar ɗakin Sultana , da gudu su Ashiru suka bishi , kai...... Karku taɓani , wai har so nawa zan faɗa bana so ana riƙeni ne............. ? Ya juya tare da sauke ma Ashiru hannu a ciki ya koma baya ya faɗi ƙasa yana ihu , wurina ya nufo yana zabura cewa saina kashe ki......... Da sauri na jawo lokar bedsite na ɗauko abuna yana matsowa na feshe mishi fuska ya faɗo saman gado ruf da ciki saida ya kalleni sannan ya rufe idonshi a hankali ya tafi hutun taƙin lokaci , haka kawai zan zauna ne aljanu su lahanani ? Sun tsaya bayan fage suna ta iskanci an kasa maganinsu tou ni nice maganin su Allah dai ya bani lafiya.
Dady bai shigo ɗakina ba Momy ce ta shigo saida ta zageni tas tace kuma Dikkon zai dawo daga duniyar suma zata faɗa masa nice na zubar da cikin zaici ubana kuma zai sakeni , a raina nace wane dare ne jemage bai gani ba ? Aini halin Dikko da duk haukarshi saidai in ba wani labari dan nayi imani nice mutum na farko dana fara ganowa shi mahaukaci ne ,
Dani da Rabiya da Jiddah aka tattara aka nufi asibiti damu umarnin Dady bayan an tafi dasu Sultana Dady yasa aka fiddo Dikko daga ɗakin Sultana aka maidashi ɗakinshi ,
Washe gari , duk wani taimako daya kamata anyi mana dukanmu nidai saida akayi min wankin ciki domin likita ya tabbatar da cikin ya lalace saboda allurar ta daɗe a jikina babu wani abu da zasu iyayi , Rabiya kuwa tunda ta dawo batayi ma kowa magana ba , Jiddah kuwa kuka take bata zama da Dikko saiya saketa tana ta ɓaɓɓarka zagi ita ba jaka bace ko a gidansu ba'a taɓa dukanta ba sai wani can ƙaton banza , gaba ɗayanmu dai sallamarmu akayi dukanmu kwananmu ɗaya a asibiti , Yayar Dikko mijinta ya ɗauketa Jiddah Al ' Ameen ni kuma Ashiru muka nufi gida , Jiddah kuma wurin Momy ta tafi sai an saketa.....
A ƙofar shiga ciki naci karo dashi , shi zai fita ni zan shiga ran nan nashi a haɗe yana waya ko inda nake bai kalla ba , gaishe shi nayi ƙaddarawa yayi baiji ba ya wuce , jiki a sanyaye na shiga ciki , Nabeela ta gyara ɗakin ta gogeshi ta sakar mishi ƙamshi mai daɗin shaƙa , sannu da jiki tayimin , kaɗan na ansa na wuce bedroom na kwanta.
Yana shiga mota kiran Yazeed ya shigo a wayarshi , kallo ɗaya yayi ma wayar ya ajiyeta a gefe yana ƙoƙarin tashin motar wani kiran ya sake shigowa , bai ɗauka ba ya fita daga gidan da tuƙin rashin sanin darajar rayuwarshi , ya kusa isa inda zaije text ya shigo , ɗauka yayi ya duba Yazeed ne mai turo saƙon , hannunshi ɗaya riƙe da sitiyari ɗayan riƙe da waya , dubawa yayi ,
_DK An mata ta fita hanyata , kaga dai har yanzu bata daina bibiyata ba sai bina takeyi ka duba a whatsapp na ajiye maka saƙo danni gaskiya bana san mayata...._
Da hannu ɗayan daya riƙe wayar ya tura masa.....
_Wace ce An mata kuma.....?_
_Matar ka.....!_
_Wace.....?_
_Sultana ɗiyar ɗan caca_
_Oh wai An matana......?_
_Eh_
_Me tayi maka ne ?_
_Tana biyoni duk inda naje..._
_Tou yi haƙuri ina driving , amma kana ina yanzu sai inzo in sameka muyi magana....._
Yazeed bai sake turo saƙo ba , ajiye wayar Dikko yayi yana cewa zakaci ubanka idan na riƙe ka , mtsww ko saƙon meye ya ajiye Koma dai miye saina gama zan duba , itama An mata saina sa ta rana kanta tunda bata da wayau bazan sake mata murmushi ba sai tayi nadamar sani na , banda Dady ya bashi haƙuri yace mishi babu mai laifin sai Rabiya tunda taje tayi abinda batayi shawara ba , dan yadda Mardiyya ta faɗa masa ya yadda da hakan shi yasa ya faɗawa Dikko aka ɗorawa Rabiya laifi gaba ɗaga banda haka da saiya tada Sultana aiki yadda ko bata tare dashi ta zama condem bata sake amfanin komai sakara ƙarar yarinya da ita.....
Bayan ya isa inda zaije yayi parking , bai fita a mota ba tunanin jiya ya farayi , duk abinda yayi ya dawo mishi a kanshi , Allah ka yayemin wahala , lallai An mata ni zata ma haka ko ? Wato ni zata feshe ma fuska ? Lallai yarinyar nan duk yadda akayi har yanzu tana da wani kuɗiri akaina , wata zuciyar tace ba haka bane ba , wani sashe na zuciyar shi yace kaima kawai ka yada ƙwallon mangwaro ka huta da ƙuda , murmushi yayi a bayyane yace An mata bata yaduwa kuma ita ba ƙwallon mangwaro bane ba idan na yadar da ita ina zataje ? Wane hali zata shiga ? Idan har na rabata dani banyi mata adalci ba gaskiya zama da ita dole saidai zan bata wahala a daren yau saina zane mata jikinta tasss , zan zauna lafiya na kwana biyu idan kuma zafin ya huce zan ƙara mata tunda ita ta zama doki sai an daketa zata tafi , bayan kwana biyu kuma zamu haɗu a saman bargo Allah ya baki lafiya jarumata.....
Fita yayi daga motar ya wuce ranshi a ɗan sauƙaƙen damuwa , kafin ya isa inda ya dosa su Ashiru har sun bayyana a wurin , a hankali mutane suka fara kawo hankalinsu wurin saboda zuwan su Ashiru , DK ya faɗa tare da riƙo hannun Dikko suka taɓa murmushi Dikko yayi kaɗan , abokin nashi ya cire hannunshi tare da nunawa da hannunshi ranka shi daɗe ya kake ya kyau ya zati ya ƙwarjini ya iko ? Murmushi Dikko ya sakeyi yace hali dai na nan Saminu me kazo yi nan ne.....? Ya tambaye shi yana wucewa abunshi ,
Bin bayan Dikko yayi yana cewa Allah ya kawoni kai ka fito ta can ni kuma na hudo ta nan kaga yauni lafiya lau kenan gani ga mai girma DK , Dikko bai sake magana ba ya wuce ciki saida ya gama dube²nshi yace da yaranshi dake binshi ku shiga ku dubomin shi , sun duba sosai basu ga Al ' Ameen ba , jinjina kanshi yayi yace ku wuce muje , yayi gaba suka rufa mishi baya , abokin nashi ne yace DK sallamarni mana nima in sheda , Dikko yace ni kuɗina basu zuwa wasan danbe , dan girman Allah ni yaushe rabona da danbe ai na bar ma su Yazeed , Dikko yace tunda aka fashe idon ka zakace ya faɗa yana dariya , nidai dan girman Allah DK bani , kai ba abinda zan baka , har wurin mota yabi Dikko yana haɗashi da Allah , Dikko kuwa mamakin yadda Saminu ya lalata ma kanshi rayuwa harya dawo ya fara maula abun bai mishi daɗi ba kuma baiso mishi haka ba , saida sukaje mota ya bashi kuɗin da babbban dumtsiya , cah.... Mutane suka rufo wurin suna maula.
Nidai Momy saiya sakeni , Momy tace ke sakarar banza karki kuskura Dikko ya sakeki ba dan ni na haifeshi ba Dikko miji ne ki riƙeshi wannan lalurar nashi zai zamar mishi tarihi Jiddah ki kwantar da hankalinki ki maido natsuwarki a jikin ki karki kuskura ki bari ya rubuta ko ya furta kalmar saki Dikko da kike ganinshi baida mutunci , haka kuma baida haƙuri kamar amai amma ida kikayi haƙuri komai zai zama dai² amma maganar saki ya fita harshenki ,
Nidai gaskiya bana sansa , cikin rarrashi Momy tace keda ɗan uwanki idan baki so sa dan komai ba kiso sa dan zumunci mana haba Jiddah ina wayanki ina lissafinki ina tunaninki ? Karki ma kuskura kiyi wannan rashin wayan a gaban Dikko dan nayi imani da Allah ko da wasa kikayi masa maganar saki saiya sakeki duk kuwa yadda yake sanki ko zai mutu saiya rabu dake ,
Nifa gaskiya na gaji ko za'ayi tashin hankalin da ba'a ƙara maimaita kamarshi saiya sakeni , Momy tace ji Jiddah karki yi abinda zai baki damuwa daga baya fa , idan ya sakeni duk ranar dana zo nace kisa ya maidani ki tunomin wannan ranar , Momy tace ai bana fata ma yanzu tashi kije kiyi wanka kici abinci ki huta zuciyarki tayi sanyi , ni babu ranar da zuciyata zata huta sai ya sakeni , Momy tace yi haƙuri Jiddah idan kina gidan Dikko waye ya isa ya shiga ya katantane ? Bare idan "yan uwanshi sunje a watsar dasu a palo , idan kina gidan dake da duk wani ɗan dana haifa da "yan uwana gidan bazaku zama a raɓe ba , kuma idan ma dan wannan karuwar sakinta zaiyi kinga daga ke baza sake aure ba , nidai ko ya saketa bana zama , Jiddah kalmar saki ya fita daga bakinki bakisan hakin Dikko ba , tashi kije kiyi wanka kiyi bacci , tashi tayi tana ko za'ayi tashin hankali sai Dikko ya saketa.
Al ' Ameen dake rakuɓe yace Hajiya ki bari yayi mata ɗaya kila ta huce , Momy tace da Allah rufemin baki ɗan iska fita ka bani wuri , Allah ya taimakeki ya faɗa tare da fita , cikin farin ciki yace a gaban mai gida zata faɗa na gama da wannan wasan sauran Sultana..... Lokacin mu ya kusa farawa !
Suwaiba kalleni , Dikko ne zaune saman kujera ya kashe zamanshi da ƙafa ɗaya saman ɗaya , duƙar da kanta ƙasa tayi tana kuka , tunda nake faɗin kisa ban taɓa kashe wa ba amma zanyi rantsuwa kuma kinsan halina na faɗa ma na cika bare kuma na rantse idan har kika kuskura nayi rantsuwa zan kashe ki saina kashe ki , in kashe ki kuma na kashe banza dake da ɓeran gidana babu banbanci yadda zan kashe shi ba'a tuhumata abinda yasa na kashe shi haka zan ɓatar dake cikin mintuna biyar zan shafe labarinki a garin katsina ,
Waye....... ? Na rantse girman Allah ga sunanshi a zuciyata amma bana iya faɗa , Dikko yace duk halakacin da nayi miki dake za'a haɗa hannu na zama lusarin namiji ? Me nayi miki haka don Allah..... ? Ki faɗamin shi kawai sai insa a maida ke gidanki cikin mutunci da mutuntawa , wallahi ranka ya daɗe ga sunan shi a zuciyata amma bana iya faɗa , cikin ɓacin rai Dikko yace ku fiddomin zuciyar ta , ta ni idan na duba zan gane ko waye......
25/11/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA....* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 82
Suwaiba najin haka ta saki wani irin fitsari tare da jan jiki ta matsa kusa da Dikko tana ƙoƙarin riƙe ƙafarshi ya kai mata wani irin halbi saida ta koma baya suuuuuu , ke ni ba'a taɓani duk duniya abinda na tsana kenan wani ya riƙemin jiki shi yasa ko ina cikin yanayin fushi aka taɓani nake ƙara firgicewa , ku fiddomin zuciyarta nace................... !
Cikin kuka tace dan darajar Annabin rahma S. A. W kayi haƙuri ka ƙaramin zuwa gobe dan soyayyar da kake ma fiyayyen halitta idan har ban faɗa ba kayi min duk abinda kaga dama , sannan kuma ka tattaromin kaf yaranka duk wanda kasan ya taɓa zama ƙasanka lokacin da kayi rashin lafiya ko baya tare dakai to a nemoshi a taho dashi tunda na kasa faɗar sunansa idan naga fuska zan gane....
Miƙewa Dikko yayi baiyi magana ba ya fice daga wurin , Ashiru ya kalleta yace an daiji ɓitir shegiya munafuka Allah ya ƙara tona muku asiri gobe iwar haka lahira most go dan mai gida zai kashe ki....... Ya nuna yadda Dikko yake faɗa cewa zan kashe ki........
Sai bayan la'asar Dikko ya dawo , gidan yau shiru ba Jiddah ba Mardiyya Nabeela ma bata nan tunda ta fita bayan na dawo daga asibiti har yanzu bata dawo ba , da sallama ya shigo ɗakina ko inda yake ban kalla ba na ansa naci gaba da kallon wayata da nake ta kiran layin Inna.
Kusa dani ya zauna ya riƙoni jikinshi yana wannan numfashin nashi mai tayar da hankali , kyarma jikina ya farayi nace sakeni , anƙi a sakekinki , cikin hayani nace da Allah ka ƙyaleni ke muguwa daɗi kikeji na taɓaki ga jikinki nan ya nuna , da hayani na ce sakar.... Mmmmmm na ƙarasa saboda haɗuwar bakunanmu wuri ɗaya.
Shiru nayi tare da ƙara riƙeshi , girgiza kaina yayi da yanayin na kalleshi , jiki a mace na saka idona a nashi naci gaba da ansar saƙonshi , saida ya gama luguiguita ni ya cire bakinshi yana cewa me ya haɗaki da ƙawayen Jiddah ? An mata bakijin magana dai ko ? Kwanciya nayi a jikinshi da yanayin kasala nace Ey banajin maganar , ke yarinya zaneki zanyi ki gama ƙaryar rashin kunyar ina dawowa anjima ya ƙarasa maganar yana tashi bayan ya saukeni daga jikinshi , nima sauka nayi daga gadon nabi bayanshi har ɗakinshi.
Juyowa yayi ya kalleni tare da cewa zaki rufe ƙofa ne ? Girgiza kai nayi alamar a, a , tou me ne ne ? Ba komai na faɗa ina ƙoƙarin zama gefen gado , ke ׳ karki zauna koma can ya nunamin gefen madubi , babu wani damuwa na koma na zauna , kayanshi ya fara cirewa yana bani labari wai Suwaiba idan ta bari ya fara ranfa da ita saiya ɓoye halittar ta , wallahi An mata da tausayin matar nan nake amma yanzu na tsaneta ko ganin ta bana san yi shegiya ƙazama...
Zama yayi saman bedsite wai inzo in cire masa takalminshi in samu lada , kallonshi nayi ban tashi ba , taso mana shi yasa matan yare suka more ma matar malam bahaushe da ni mijin bayaraba ne ba'a bari na in cire riga dakai na , za'a ciremin da soyayya ana faɗamin kalamai masu daɗi ana kulawa dani harsai naji kaina ya min girma , ya ƙarasa maganar yana zame takalmin shi ya cire safarshi miƙewa nayi ganin yana kwance belt a tsorace , a , a koma ki zauna ai ba yanzu zan dakeki ba sai anjima , yi zamanki ni wanka zanyi.
Cikin kuka nace kayi haƙuri dan Allah , saida yazo kusa dani ya sumbaci gefen fuskata ya latsa cikina saida na zabura da irin maganata yace aradu bazan haƙura ba me kuka ci ne ? Ya ƙarasa maganar yana tambayata , ni abinci naci , ai nasan abinci kika ci idan akwai saura kawomin yunwa nakeji ,
Miƙewa nayi na fita , bayan Sultana Dikko yabi da kallo a ranshi yace Allah yasa "ya "yana suyi kama da An mata , amma kar suyi rashin jinta , ubangiji ka sake azurtamu da wani rabon mai albarka ka bawa An mata lafiya ni kuma ka bani haƙuri da dangana , ina can ina yawo ni banga irin abin nan da masu ciki keyi ba , ko me tayi ta kwaɗayi data samu cikin Oho , tou amma me yasa Jiddah tace wai An mata tace baza ta aihu dani ba ? Ya taɓa saitin zuciyarshi , murmushi yayi tare da faɗa a bayyane yace ƙarya ne "Yar mata tana san Dikko kuma dole zata so ta haihu dani kodan soyayyar da muke ma junanmu , rigima kenan naga Sultana da baby da farin ciki ya shiga toilet danyin wanka.
Ɗakinshi na dawo da abincin kuma har yanzu bai fito ba , ajiyewa nayi na fice a ɗakin , gaf zan shiga ɗakina ƙanwarshi mai bi mishi ta tareni tayo zugar ƙawayenta saida kowa ya zageni fes a cikinsu sannan ƙanwar tashi ta ansa tare da fara sokamin zagi waini har na isa saboda ni ɗin banza Yaya DK ya daki Aunty Rabiya waye ni bare ubana ɗan caca karuwa da aka saka a wasan caca su waye familynki ? Karuwan banza gaba ɗaya wace ce ke bare kuma ubanki duk cikar faɗin birnin katsina ? Waye ya tsaya miki ya ɗauremiki ƙugu kike iskanci , Dikko dake fitowa yace ni nine na tsaya mata dan hayaniyar su ta fiddoshi daga ɗakinshi jallabiya ce a jikinshi har yanzu jikinshi da sauran lema kuma itama kanta batayi tunanin zata sameshi gida ba , kuma Ashiru yaa fita da motarshi shi yasa ta ɗauka baya nan yaci gaba da cewa kuma itace tasa na daketa kuma kema saina baki kashin bala'e zaki fita gidan nan , ke har kin isa kizo har gidana kiyi ma matata takakkiya ? Kin taɓa ganinta taje cikinku ne ? Matata zaki zaga....... Dan baki da kunya ? Ashe nima zaki iya zagina idan kika samu dama ko ? Ya fara fita yanayinshi yana An mata zaki ga wanda ya tsaya mata ? Tou ni nine na tsaya mata ya nuna kanshi cewa to gani kin ganni ya akayi ne..... ?
Kyarma jikinta ya farayi tace Yaya ..... Daka mata tsawa yayi kafin ta faɗi maganarta yace zanci ubanki kika sake kiran suna na , kayi haƙuri , tou daga yau naji labari ko na sake ganinki gidana saina zaneki bata haƙuri , kallona tayi tare da cewa yi haƙuri cikin ladabi , kallon Dikko nayi ya ɗagamin gira , ba komai na bata ansa , hanya ya nuna musu tare da cewa kuje , da sauri suka gangare babu wanda ya sake magana ko waiwayenmu har suka fita , zo muje ya faɗa tare da wucewa gaba nabi bayanshi.
Har ya gama cin abincin baiyi magana ba bayan ya gama ya ɗauki wayarshi ya fara dube² tare da ɓalle botir in gaban rigarshi ya shafa kanshi da yanayin damuwa kallona yayi sannan ya sake kallon wayar yace da ina da ina kikaje da bana nan ? Dam׳ naji gabana ya faɗi kafin inyi magana harya ƙufule yace bakiji ina miki magana , daburcewa nayi nace naje goruba , daga nan sai ina ya faɗa yana tsareni da ido , ƙyarma muryata ta farayi nace sai ina naje tou ? Ina tambayarki kina tambayata ? Kayi haƙuri , miƙewa yayi yace inyi haƙuri.....? Tou kinma san abinda kika yi kike cewa inyi haƙuri kenan ? Nima miƙewa nayi na fara kuka , koma ki zauna idan kika fita ɗakin nan saina kasheki............
Karka kasheni Dikko , ke......... Rufemin baki wato saboda kin ɗaukeni mahaukaci shi yasa kikaje wurin Yazeed kai............ Saina kashe ki........... Da gudu na fita ya biyoni yana ihu ni zaki tona ma asiri saina kashe ki........ Na kusa shiga ɗakina naga kafin in shiga in rufe ya riƙeni da gudu na hau ƙarfen bene na sulala ƙasa suuuuuu kai............... Saina kashe ki......... Maimakon ta fita waje a taimaketa sai tayi tunanin a dole nan ciki zata sama ma kanta mafaka wata irin kururuwa yakeyi mai tada hankali yana maimaita saina kasheki.............. Yana wata irin zabura , da gudu ta sake komawa sama ya sake binta har yanzu bai kamata ba saina kashe ki........ Kawai yake faɗa , irin na ɗazu ta sakeyi amma sai sautsayi ya gitta......
Wani irin ihu Dikko yayi ke....... Karfa ki faɗa ki mutu , na fasa bazan kashe ki ba , An mata ya nufi inda take tafiya zuwa ƙasa dan riƙeta amma kafin ya riƙota takai ƙasa.......... Kai............... Saina kashe kaina zai faɗa ƙasa aka riƙeshi , riƙe kanshi yayi da duka hannayenshi biyu yace kai......... Wai , wai , wai Allahna wayyo................... Saina kashe kaina.......... Wasu suka riƙe Dikko dake wani irin ihu wasu suka tafi wurin Sultana da ko motsi batayi , An mata........................ Ya faɗa tare da faɗuwa ƙasa somamme.
Nabeela Mardiyya da Jiddah da suka shigo yanzu gaba ɗayansu wurin Dikko suka nufa suna kuka , ita kuma Sultana masu aiki mata ne akanta maza na tsaye kowa yana tunanin abinda yayi zafi har Dikko ya jefota daga saman bene ya kasheta , cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya cika da "yan uwansu Dikko wannan karon har wanda suke Baba ɗaya ba'a bari ba kowa yazo tunda sharri ne ya samu dan duk wanda aka faɗa mishi cewa akeyi Dikko ya jefo matarshi daga saman bene ta mutu , abiyar zaman Momy kuwa cewa takeyi tunda ya kashe shima sai an kashe shi hukuncin wanda ya kashe shima kisa ne , yaro ne yana iskanci ba'a iya hanashi ya zama ɗan ido kar akayi masa magana ya ragu , tou wallahi yadda ya kashe ɗiyar mutane shima sai an kashe shi Allah yasa mun gani da idonmu kuma saina tsaya ma iyayen yarinyar nan shari'a daga nan har a tashi duniya sai na tsaya akan kafafuwana an kashe Dikko tunda ɗa baifi ɗa ba.
"Ya " Yanta mata tace su ɗauko Sultana , Momy ta kalli Rabiya tace karku bari ta fita da yarinyar can tunda babu wanda yake da tabbacin mutuwarta dan ko bata mutu ba zata iya kashe ta yadda ta shirya lafiyayen sharrinta , gaba ɗaya wurin ya gauraye da hayani har bakajin maganar wani yayin da matar Dady ke cewa sai an tafi da Sultana , Rabiya tace ita a suwa ? Dan taga Dikko yana sume har ta samu bakin magana ai zai dawo , jin zance Rabiya yasa ta kira Dady ta faɗa masa Dikko ya jefo matarshi daga sama ta mutu ,
Salati Dady yayi cikin tashin hankali , babu daɗewa shima ya bayyana a gidan , ga Dikko kwance a dai² inda yaso ya riƙo Sultana aka riƙeshi ya suma , ga Sultana a ƙasa kwance kuma har yanzu ba'a taɓata ba daga yadda ta faɗa haka aka barta , Dady bai fara zuwa wurin Dikko ba wurin Sultana ya tsaya ya kalleta cikin tausayi sannan ya kalli "yan ɗayan ɗakin yace su ɗaukota su Ashiru kuma suka ɗauko Dikko suka fita daga palon aka bar Momy da " ya "yanta mata "yan rashin kunya masu irin baƙin haƙin halinta......
Fita Momy tayi tana cewa ina za'aje mata da ɗa ? Cikin ɓacin rai Dady yace ashe kina sansa ? Tio Babana ba ɗanki bane ba nawa ne , ga "ya "yanki nan na ɗauki nawa na bar miki naki wa'anda kike so ni ina sansa kuma bana san abinda zai sameshi insha Allah bazai mutu ya barni ba saina mutu na barshi duniya daga haka bai sake magana ba aka sakasu a mota suka fice daga gidan.....
Wannan ranar ta tuno ma Momy da zuwan Suwaiba gidansu , Dikko yana da rigima haka kawai yaje ya ɗauko musu wannan "yar iskar ya tausaya mata amma ita ta saka masa da sakayya mafi muni a rayuwa ta gudu ta barshi da masifa dake neman kaishi ƙiyama babu gaira babu dalili , ya taimaketa amma ta zama silar warwarewar rayuwashi gaba ɗaya kuma ta gudu ta barshi da hauka shi ba mahaukaci ba , jiki a sanyaye ta dawo palo wuri ta samu ta zauna ta zabgaga uban tagumi tana matse hawaye.
Suwaiba kuwa bayan tafiyar Dikko kuka tasha harta gode Allah , bakin gaskiyarta ta kasa faɗin sunan wanda Dikko yake so ta faɗa masa to ya akayi ta kasa faɗa shine tambayar da take ma kanta bayan a zuciyarta tasan sunan , tana wannan tunanin ne Al ' Ameen ya bayyana , tana ganinshi ta fara kaine kuma saina faɗa masa , dariya Al ' Ameen yayi tare da cewa haba "yar gurgus na kulle zuciyarki bakinki baya iya faɗar Al ' Ameen , kuma idan baki sani ba nine na harbeki kika zama gurguwa , abinda ya kawoni wurinki shine fatan sauka lafiya ayi rayuwar lahira lafiya ina nan saina ga bayan mai gida saina kashe shi na kwashe kaf dukiyarshi sai nayi rayuwar duniya mai daɗi nahau manyan motoci in ƙaro mata 3 masu zafi naje duk sauran ƙasashen da bai kaini ba ,
Waye yace maka ina nan ne ? Ni na sani da kaina dan nasan dama bazaki wuce nan ba , ya baki daga nan zuwa gobe mahaukacin banza yana can yana nema na a gari kamar wani lusari baisan ina tare dashi ba , daga wurin mahaifiyarshi nake na sauke zango na a wurinki , naira miliyan biyu aka bani naje na haɗo sammu nine na bashi a banci kuma a lokacin ni ɗaya nake tare dashi a ƙasar London , kuma nine na kashe matarshi har lahira , ni nayi komai kuma nine zan kulle bakin furta zan kashe ki................... Zan kashe ka.................. Saina kashe ku............... Saina kashe kaina............ Haba mai gida kayi haƙuri zaka mutu saurin me kake ? Mutuwar fa yana gaf da kai da zaran na haɗa auren nan aka samu haihuwa sai mu kashe ka kaga mun hutar da kai faɗar zaka kashe kanka Al ' Ameen zai aika ka zuwa duniyar mutuwa , Hajiya Suwaiba na wuce sauka lafiya zuwa lahira , murmushi yayi tare da ci gaba da cewa zai dawo yana zuwa zaice saina kashe ki.......... Haka zai faɗa Al ' Ameen baya faɗuwa dan haka sai ya kashe ki kinga na ture wata matsalar aiki ya ragemin yana faɗin haka yayi tafiyarshi yana dariya.
Fashewa da kuka ta ƙarayi cewa Allah zai tona maka asiri babu daɗewa azzalimi maci amana , murmushi Al ' Ameen yayi bai juyo ba ya ɗaga kafaɗunshi 🤷🏻♂ ya fice da sauri , kifewa Suwaiba tayi a wurin kuma sunan Al ' Ameen yaƙi zuwa a bakinta ,
Tunanin irin halackin da Dikko yayi mata ya dawo kanta , wurin da take taji yana juyawa yayin da zuciyarta tace ta yanka kanta ta rubuta *AL ' AMEEN* a jikin bango idan Dikko yazo zai gani , wayyo Allahna , ta goge hawaye tare da komawa ta kwanta a wahalce ta fara tunanin rayuwar baya................ !!!
Kuyi haƙuri da wannan don Allah , na farko dai banda caji , na biyunsu kuma ina da hidima wanda ba lallai ne gobe zuwa jibi kuji ni ba , amma idan na samu yadda nake so zanyi ko kaɗanne fatan zaku gafarceni.......
27/11/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 83
Da farko dai Dikko mutumin kirki ne a wurinta , nagartaccen namiji mai zama , tsayayyen namiji mai lafiya da cikar zati da kwarjini , jarumin namiji ba lusari ba , idan akace mutum bashi da mutunci ko rashin ragowa idan dai baiyi maka ba tou kai mutumin kirki ne a wurinka , duk halin mutum na kirki dana banza idan dai bai nuna a kanka ba tou bazaka sheda mugayen halayenshi ba , Dikko yana da mutunci amma shi baya shiga sabgar kowa , ko a baya data sanshi da lafiyarshi tasan baida haƙuri haka kuma bai ɗaukar sakarci da shirme , kayi ta magana yana jinka saidai yayi kunnen uwar shegu dakai , yana da tausayi sosai amma yafi tausayin mata a rayuwarshi.
Baya dariya baya murmushi idan kuma ka cika shi da surutu zai tsare ka da dara²n idanuwanshi har sai kaji tsoro kai da kanka zaka lallaɓa ka tashi ka kama gabanka , baya sabgar mata baida budurwa ko ɗaya amma yana da dawakai masu lafiya da ƙoshi , babu hoton mace a wayarshi amma zaka iya samun hoton doki babu adaɗi a wayarshi , ya yadda da doki sosai kuma bayajin wahalar sayenshi baida magana sai ta doki dan ko yana zaune da abokanshi idan suna fira masu zancen "yan mata sukeyi , masu mata suka labarta nasu shi zaice dokinshi kaza² , sai zancen kayan doki maganar polo kalamanshi dai suna tsayawa akan doki ne kawai da abinda ya shafi dokin , idan ance masa shi baya budurwa zaice shi baya san raini dan yaji yadda su kansu suke magana akan matan , kuma yana ganin yadda matan gidansu ke ranfa da maza , gashi kuma suna faɗar irin halayen da matan ke musu , kanaji da girmanka da shekarunka ƙaramar yarinyar daka haifa tayi maka rashin kunya shi duk sabgar da zata zo da raini ko rashin kunya baya ciki shi yasa bai shiga sabgar kowa saita doki , dan doki idan ya sanka kaine kake cidashi kake shadashi akwai ragowa tsakaninka dashi amma idan ya tashi aure zai auri cikakkiyar mace data san kanta mai shekaru da yawa shi gaskiya bazai auri "yar ƙaramar yarinya ba dan idan ya auri yarinya shi kanshi saiya raina kanshi ƙaramar yarinya mai ƙananan shekaru bata dace da rayuwarshi ba...
Murmushin ƙarfin hali Suwaiba tayi tare da goge hawayen dake kwance a saman fuskarta , a bayyane tace ashe dai da rabon sai ka auri ƙaramar yarinya , yarinyar ma ta ƙasan² shekaru , yaushe kuka haɗu kukayi soyayya har aka kai matakin aure .....? Hmmm koma dai miye Suwaiba ba damuwarta bane ba ,
Marin birich a jahar Lagos , madakata ce ta mutanen da basajin magana ko kuma nace wanda suka gagara , madakata ce ta mutanen da suka fi ƙarfin gida ko suka aikata ɓarna saisu gudu daga jahohinsu sai suyi ma kansu masauki a wurin domin tsira da rayuwarsu , mazauna wurin gafurtacci ne kuma gagararri wanda suka ansa sunansu wurin rashin jin magana ko iskanci.
Duk irin matsalar da kaje da ita a wurin sai kaga wanda ya shafe taka ya burjeta murus , idan kuma zancen iskanci ne da duk wata ƙaramar rashin kunyarka tou fa daga wurin dai an rufe littafi , idan ko ke karuwa ce a iskanci har kika je Lagos kikayi rayuwa a ƙarƙashin gada tou lallai iskanci daga kanki an kashe boss , duk namijin da yaje wurin shima dai abin kwatance ne tou ina ga mace kuma....?
Matsalar iyaye itace ta kaini garin Lagos kuma nayi rayuwa a wurin dana faɗi sunanshi daga sama , auren soyayya nayi dani da mijina wanda ni dai Allah ya sani dama bawai wani cancan nake jinshi a raina ba , na aureshi ne saboda girman dukiyarshi wanda mu a zuri'armu attajiri ne sosai dan talaucin mu , ni bana sansa kwata² amma ina nuna masa soyayya saboda kuɗinshi shi yasa yayi tunanin ina sansa har a zuciyata ,
Tou mundaiyi auren na soyayya kamar yadda mutane suke kallo a zahirance amma a baɗinance ni a wurina kuɗinsa na aura , tunda aka ɗauramin aure dashi iyayena sukayi min huɗuba cewa nadai gansu a gidan haye suke zama tou inyi ƙoƙari na ƙulla musu mazauni kafin mijina ya sakeni dan masu kuɗi basu cika zama da aure ba nayi ƙoƙari na gina kaina kafin yayi min wurgin kashi a shara , a nawa ganin nidai ina kallon anyi ma masu kuɗi fahimta ce mara kyau domin auri saki hali ne , kamar jini haka yake gudana a cikin zuciyar mai irin ɗabi'ar danshi auri saki babu ruwanshi da mai kuɗi babu ruwanshi da matalauci haline ne kuma yana ƙarkashin zuciyar maishi.
Tunda aka kaini gidan mijina duk ƙarshen sati sai an aiko ƙanina daga gidanmu wai in bada kuɗin zubin adashe , akan me zance babu ? Dan ko shi ƙanin nawa idan yazo sai ankai ruwa rana nake haɗa masa kuɗin motar komawa dan mijin dana aura mannanu ne bashi da alkairi ko kaɗan dan ko kuɗin cefane ya bada idan ya dawo sai anyi lissafi saiya ƙwaƙwale canjin shi tass ya barni zero ɗina.
Mahaifiyata data ga kullum ƙanina yana zuwa yana dawowa babu kuɗi satin gaba yana zuwa ta tattaro ta taho da kanta , nasha zagi sosai tace ina nan na shige cikin a c na manta da ita , ina nan kullum sai naci nama nasha ruwan lemu , da safe naci shayi da burodi na barta a daura tana can kullum safiya tana karo da zazafen tuwo , taɓarya zata kasheta saboda daka da wahalar rayuwa , ina shafa ruwan sabulu mai ƙamshi idan zanyi wanka tanayin wanka da garin omo sai Allah ya tsenemin tunda na barta take shan wahalar rayuwar.
Na nuna mata cewa kuɗin bafa a hannuna yake ba nima a ƙarƙashin wani nake sai abinda aka bani , kuma bani nake da alhakin kula da ita ba taje tayi haƙuri taci abinda Allah ya hore mata tace bata yadda ba dole irin abinda naci irinshi zata ci , kuma saina shiga adashen nan duk abokan aure na babu wacce bata mallaki ƙaddarar dabbobi ba dan haka nayi ƙoƙari na samu.
Duk yadda naso na nusar da ita ƙin yadda tayi wai a dole saina samo idan ya shiga wanka in riƙa lalube masa aljihunsa dan wallahi ta aiko satin gaba bata samu kuɗin nan ba kashe wannan auren zatayi dan bata ga amfanin aure babu ci gaba ba , nace tou , data tashi tafiya saida ta tunbiji kayan abinci shinkafa taliya makaroni kuskus ta ɗauke sauran madararmu duk abinda ta gani gidan saida tayi gaba dashi buhu guda ta cika na shinkafa da abinda ta tattara daga gidana.
Bayan mijina ya dawo ya shiga store ya fara dube² dama wannan shine al'adarshi duk daren duniya idan ya dawo saiya duba kayan abinci , idan kuɗi ya bani saiya anshi canji , idan naman abinci ya kawo saiya irgashi , tun daga store ya fara faɗa wai yau yaga abinci yayi ƙasa bayan yabarshi da yawa kafin ya fita , ina na kai mishi abinci ? Nace ina kuwa za'a kai abinci inda ya wuce cikin ciki........?
Karfa na raina masa hankali haka yai ta zazzaga ruwan wulaƙanci karshen film in dai yace min dangi ɓarayi sata kamar ɓere zai maida abincin ɗakinshi duk safiya zai auno min gwangwani ɗaya tunda na zama ɓarauniya ba ruwanshi da baƙo kuma idan taliya ya bani ita zanci daga rana har dare , in shinkafa ne itama haka , ya kwasa rashin mutuncin shi daga baya ya kwashe komai zuwa ɗakinshi , binshi nayi ina bashi haƙuri ya basar ya shige toilet , yana shiga naci gaba da bashi haƙuri ina ɗaga kayan daya cire , kayi haƙuri don Allah , a dai² lokacin dana ƙwale² aljihunshi tas , bazan ƙara ba , a dai² lokacin dana ajiye wando na ɗauki rigarshi , na bari don Allah na kwashe kaf kuɗin masu yawan gaske na fita daga ɗakin , ban nufi ɗakina ba na nufi bayan gidan na tona rami na rufe su na maida busashshiyar ƙasa na rufe nayi ma wurin alama da tsinken tsintsiyar kwakwa.....
Ɗakina na koma naci gaba da kuka ban ƙarawa , a haka ya sameni yana ina kuma kika kaimin kuɗin na , rigima ya kaure tsakaninmu tashin hankali na kada Allah maimaita mana anyi shi , kuma tun daga wannan ranar ban ragawa aljihun mijina ba , ba aljihu kaɗai ba ko wanka ya shiga haka zan bincike kaf ma'adanar kuɗinshi , kafin wani lokaci na ƙware da wurin iya sata , kuɗi kuwa duk satin duniya sai anzo an ansa a gidanmu.
Mijina kuwa sai ya daina shigowa da kuɗi gida ya riƙa barinsu a mota , dana duba naga babu komin dare saina lallaɓa na cire makullin naje na buɗe na kwashe kaf kuɗinshi , koda ya kai ƙarata gidanmu iyayena cewa suke aljannu ne dansu "yar su ba ɓarasuwa suka haifa ba , suka ɗauremin ƙugu naci gaba da tsula tsiyata....
Daga dai ƙarshe mijina ya samu kwanciyar arziƙi dan haka mahaifiyata ta murje idonta tas ta kashe auren nan mijina yayi kuka ya shiga tashin hankalin rabuwa dani ni dama can bana wani sansa , bayan mutuwar aure na gama iddah na sake auren wani amma baikai mijin dana baro rufin asiri ba , shima haka na taso tattalin arziƙinshi saidai na ƙareshi kaf nayi gaba abuna , kuma har zuwa wannan lokaci iyayena basu sayi gida ba , aure na gaba mijin wayayye ne domin shi a banki yake ajiye kuɗinshi ban wani daɗe ba na kashe auren dan zuwa wannan lokacin nima na goge da idan babu malasa gaba nakeyi abuna , bayan wani lokaci na sake aure na auri wani manomi bagidaje ne dan haka shi amfanin gonar na riƙa siyarwa , shima ya gaji ya sakeni daga haka ban sake aure ba dan duk wanda yazo ce masa akeyi ni ɓarauniya ce , wannan dalili yasa ban sake auruwa ba ,
A gida zaman dai babu daɗi dan banda aure kuma banda inda zan samo kuɗi aka fara hantara ta a gidanmu , dan haka na fara sata da maƙota cikin ƙanƙanin lokaci na zama mashahuriyar ɓarauniya a cikin anguwarmu , ko shaguna naje sayayya danaga ba'a kallona sai inyi sata in gudu....
Duk wannan ƙoƙarin da nakeyi a haka banyi ma iyayena ba dan haka na haɗa dai da "yar bariki ta , ina karuwanci ina sata kuma har yanzu basu sayi gidan zama ba , ganin haka yasa idan na sato na daina basu naci gaba da sata ina ɓoye abuna , wulaƙanci a gidanmu kuwa na dare daban na safe daban , a wurin iskancina na haɗu da wani babban attajiri shine ya ɗauki hayata ya tafi dani Lagos , a ranar daya kwana dani a ranar na ɗauke jakar kuɗinshi na gudu ,
Ban bar Lagos ba na nemi matattarar "yan iska wanda suka gagara shine aka bani tayin marin birich ranar da naje da ƙarfin bala'e aka ƙwace kuɗina , naga iskanci da ƙaryar rashin kunya , naga dabar data girmi irin wacce nake gani a garin Daura , naga karuwancin daya girmi nawa naga salon sata wanda ya girmi tawa , wurin yamin nayi zamana da safe zan fita cikin gari nayo iskanci na dawo , wata na biyar a wurin mai hali baya barin halinshi nayi sata naci bugun rabani da yaro kuma sunce sai sun kasheni haka suka ɗaureni a jikin ƙarfe suka watsamin fetir suka cinnamin ashana dan sunfi ƙarfina ina ji ina gani zan mutu kuma gani ɗaure , a dai² wannan lokacin ne Allah ya kawo Dikko , dashi da abokinshi shima kuma kanshi baisan haka wurin yake ba yayi rakiye kawai ni bansan abinda yakai su shi abokin nashi ba.
Dikko yasha dariya sosai sannan ya ɗauki ruwan wani gahurtaccen ɗan daba daya zuba a bokiti zaiyi amfani ya sheƙamin a jiki wutar ta mutu , tun bai gama zuba ruwan ba ɗan daban yasa yaranshi suyi ma Dikko gunduwa² wanda ya kunna min wuta kuma yasa yaranshi su sake tashin wata wutar amma akan Dikko , saboda wurin gungu² ne na sansasanin "yan iska , kowa da zugarshi kuma kowa yana da yaranshi mutanen dai sun kasu kashi daban².
Wanda Dikko ya rako ya ruga da gudu ya duƙa gabansu yace su rufa mishi asiri Babanshi yake neman gwamna karsu kashe shi , ashe ma basu zama gwamnan ba ? To ko ɗan shugaban ƙasa ne sai sun kunna mishi wuta , su kuma dabar wanda aka ɗaukar ma ruwa suka ce ko gwamnan ne sai sun fyeɗeshi harya isa ya shigo da'irarsu ya haresu ? Shi kuma Dikko yana kwunce Suwaiba daga ɗaurin da akayi mata kuma har yanzu bai daina dariya ba.....
Kawai dai anyi tashin hankali mara kyau dakel aka samu aka fitar da Dikko daga wurin da taimakon wanda abokin Dikko yazo wurinshi , kuma duk tashin hankalin nan da Suwaiba ya tafi , tun a mota Dikko ke kuka wai yanajin tausayin sauran matan da aka baro shi wannan wane irin rayuwa ne ? Me yasa mata zasuyi iskanci wai.......? Ya bani shidai baya so yaga mace tanayin abu da bai kamata ba shi dai zai koma ko zai mutu saiya fitar da duk wata mace a wurin , abokinshi yace tou ka rufawa kanka asiri dan ka sake ka koma wurin nan saidai wani ba kai ba , Dikko da kafiya cewa yayi saiya koma su kashe shi , duk haƙurin da aka ba Dikko ya kafe kai cewa saiya koma a kashe shi.....
Nice na bashi haƙuri nace kar ya koma dan na fahimci shi ma'abocin tausayin mata ne amma yana da kafiya idan ya duƙe akan abu sai yayi , nace kayi ka haƙuri ka ƙyalesu duk wacce ka gani itace taje da kanta take zama , kuma idan ka koma zasu nemeni su kasheni , daga haka yayi shiru dai bai sake magana ba , ni bansan abinda abokinshi yaje yi ba , kuma bansan dalilin da yasa shi Dikko yayi rakiya ba , dalilina na bashi haƙuri nasan idan har tsautsayi ya maidashi sai sun kashe shi har lahira....
A cikin jirgi muka zo kano daga Lagos jikina yana ta raɗaɗin wutar data ci jikina sama² , a kano aka ɗaukemu a cikin wasu irin zafafan motoci har katsina , saida ya kaini asibiti aka dubani.
A gidansu Dikko kuwa mahaifiyarshi tayi tashin hankali akan bazan zauna ba , ta zage shi so babu adadi tunda yace kiyi haƙuri Momy zata zauna bai sake magana ba yaci gaba da sabgar gabanshi , ita irin mutanen nan ne masu ƙyanƙyamin mutane , ankai ruwa rana Dady yace tunda Babanshi yace saina zauna babu wanda ya isa ya hanani zama.
Tunda nake zaune a gidan banda wata damuwa domin Dikko yace duk abinda nake so na faɗa masa , shike ɗauke da duk wata ragama tawa duk abinda nake so zan rubuta a rubuce na bada akai mishi , baida hankali wurin kyautar kuɗi hannunsa a sake yake yana da alkairi sosai amma bashshi da mutunci idan aka taɓoshi duk gidan sai kowa yaji masifarshi yana iya sati yana masifa akan abu ɗaya bai gaji ba dan bai gajiya da fitina gashi da kafiyar bala'e idan ya duƙe kai akan abu babu gudu ba ja da baya....
Tabbas Dikko yamin gata yamin halakci fiye da tunanin yadda mai tunani zaiyi zato , ko tafiya yayi ya dawo haka zai jibgomin tsaraba ta sutura saboda duk yadda zan faɗi gayun shi bama zan iya musultawa ba , yanda yake ɗan gaye saida ya tabbatar ya maidani "yar gayu ta gaban jarida , kuma nayi masa koken rashin mazaunin iyayena shi ya tsayar dani akan ƙafafuwana lokaci guda nasha gaban duk wani mai tayarmin da ƙura ya kulleni da motar hawa ta abun kwatance a idon duniya.....
Amma sai na ƙulla aminci da abiyar zaman mahaifiyarshi , ita tana jawoni a jikinta saɓanin mahaifiyar Dikko dan haka aka shiga neman kai ƙarshen rayuwar Dikko dani , itace take aikena nemo mata asiri tana san ganin ƙarshen Dikko tace yadda itama bata da namiji babu wacce ta isa tayi namiji a gidan , tun da aka haifi Dikko take neman sa'arshi bata samu ba kuma baza ta daina ba haka kuma bazata gajiya ba har sai ranar da Dikko ya daina numfashi.
Ina cikin ƙulun bitar bin malamai da bokaye Al ' Ameen ya saƙo cikin aiki ta hanyar bina da yayi ban sani ba har inda zanje , bayan ya tabbatar da komai yazo ya zayyana min hankalina ya tashi kuma na firgita amma sai yacemin na haɗashi da matar Dady na faɗa mata cewa shima yana san ganin bayan mai gida ne kuma yana shirye akan zai bata taimako ko wane iri take so.
Tayi na'am da haka itace ta bada kuɗi Al ' Ameen yaje ya samo asiri aka haɗa manyan masifa aka binne a wani daji sai iskokai suke gadi ana biyansu da jini duk karshen sati , wanda kuma ake so yaci a abinci shine idan yaci zai riƙa haukacewa duk lokacin da yayi fushi yana maganar kisa , iskokai kuma sune zasu riƙa shafarshi , Al ' Ameen yace zai iya bashi , tou shine maganin daya bashi a London , dan rigimarshi shine suka juya abun da faɗanshi shi yasa duk lokacin da yayi fushi sai ya riƙa cewa saina kashe ka................ Farkon asirin rashin lafiya ya farayi kaɗan² Dady yasa aka dawo dashi nigeria baida lokacin tafiya ya tsaya yana ta siyasa , Dikko yayi ciwo na tashin hankali babu wanda ya bashi tashi a duniya , saida aka saka mishi robar hanci kowa ya haƙura dashi , shine Dady yaita rashin lafiya sakamakon ciwon Dikko har ya samu ciwon zuciya saboda tunani , aminin shi Dady shine ya gano ciwon Dikko asiri ne ya kuma faɗawa Dady ciwon Dikko bana asibiti bane ba dan wasu Allah ya basu lilimin gane sihiri , kuma ya miƙe tsaye ya gano cewa Dikko ana so ne ya mutu ta ko wane hali idan bai mutu da kanshi ba yayi kisa sai a yanke mishi hukuncin kisa kuma shi ya samo duk wannan magungun nan da ake mashi amfani dasu ,
Abinda yasa Dikko yasan ina da sa hannu a rashin lafiyarshi , mai aikin Momy taji muna magana da Al ' Ameen a palo ni kwata² bansan tana nan ba kuma bansan ta shigo ba , Al ' Ameen yana magana ƙasa² yake faɗamin boka yace abokin Dady ya miƙe tsaye akan saiya gano duk wani mai sa hannu a rashin lafiyan mai gida shine boka ya bada wasu layu yace aje a tsakiyar gidan nan a rufe ana rufesu an rufe zancen , zaici gaba da magana aka kirashi a waya ya fita bayanshi na bi muka bar ɗakin gaba ɗayanmu , tou itace taje ta faɗawa Dikko iyakar abinda taji amma bata san da waye nake maganar ba , shine yazo yace min ni bazaimin komai ba amma in faɗa masa ko waye yake da saka hannu kuma waye zai binne layu a cikin gidansu , kafin inyi magana shine ya nufi wurin Mom inshi wai tazo taji da kunnenta an haɗa kai da Suwaiba an cuci rayuwarshi sai idan yayi magana ace bashi da haƙuri ya cika masifa , sanin halin Dikko yasa kafin ya dawo na gudu dan nasan duk da yace bazaimin komai ba nasan sai yayi idan har ya riƙeni mai kwatata a hannunshi sai Allah shine na gudu Dikko baisan daga inda nazo ba kuma baisan ina zan koma ba tsintoni yayi kuma na gudu abuna , ashe Al ' Ameen shine yayi sanadin zamana gurguwa , ya bini ya kasheni gudun karna tona musu asiri , shine ya ɗiɗɗirka min alburusai a ƙafa , wanda na faɗi bansan ina kaina yake ba saidai na gannin da yankakkin ƙafafuwa.
Bansan Sultana ba ina jinya aka ajiyemin kwalba da waya , na kira Malamin na bashi shi kuma malamin ya kira Bello ya bashi bayan sunyi ciniki ya ƙara masa akan farashin da ita matar data bani ya maida ma Bello kwalba , bansan Sultana tana auren Dikko ba , abinda yasa kuwa na koreta daga wurin nace mata bana san matsala ta sake shigowa rayuwata dan bansan ita kuma abinda rayuwarta ta dosa ba..........
Lahaula wala kquwwata illah billahil 'aliyyul azeem Dikko ya furta suna fita daga cikin gidanshi ya dawo daga sumar da yayi , a ɗiymuwance yace ina ne nan ina kuma zamuje ? Kallon kanshi yayi sannan ya kalli inda aka kwantar da kujerar gaban mota Sultana kwance , laluba aljihunanshi yayi sannan yace ina wayoyina ? Ya tambayi Ashiru , ban ɗauko ba , to koma , da rubos Ashiru ya koma har ƙofar get in gidan , yana tsayawa Dikko ya fita da sauri yaje ya ɗauko wayoyin ya dawo , yana shiga mota ya kira waya , bayan an ɗauki waya yake sanar da M D in asibitin yana da maralafiya suna zuwa babu jimawa dan a shirya ma zuwan nasu , ya kuma faɗa masa abinda ya faru , na cikin wayar yayi magana shi kuma bai sake magana ba ya tsinke kiran , kallon Sultana yayi yaga tana ciccire² ko fizge² kawai dai { Convulsion } salati yayi tare da cewa kai bi tacan , da sauri Ashiru ya juya sitiyari yana cewa Dady yace mu haɗu dashi gida , Dikko yace ba gida ba takamin motar nan da gudu kayi ta can yana nuna mishi hanyar da zaibi da hannunshi idonshi yana kan Sultana , gudu Ashiru yake falfalawa amma Dikko cewa yakeyi kaje ׳................ Ƙannenshi "yan ɗayan ɗakin dake binsu suna ganin Ashiru ya canja hanya suma suka bi bayanshi da gudu kamar yadda suka ga Ashirun nayi.
Dikko yana tsinke kiran M D ya kira doctors team on call su tanaji ɗaki a amenity DK yana zuwa da mara lafiya kuma su shirya ma zuwan mara lafiyar da zai kawo.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka iya asibitin ƙashi kuma har yanzu Sultana bata daina fiffizgewa ba , tuni an shirya ma zuwansu a saman ɗan gadon da ake ɗaukar marasa lafiya aka ɗorata aka shiga da ita cikin accident and emergency ,
Taimako na farko da aka fara bata allura akayi mata diazepam dan dakatar da wannan fiffizgewar da takeyi , cikin mintuna 3 gaba ɗayan jikinta ya saki ta daina ciccire² a mintuna biyu da suka sake bugawa ta ɗauke gaba ɗayanta wato ta tafi bacci.....
Daga A & E aka wuce da ita amenity nan aka bata ɗaki , cike da tausayi Dikko yabi Sultana dake kwance a saman gado da kallo mai nuna da yana tausayinta sannan ya juyo ya kalli Ashiru dake bashi waya Dady yana kiranshi , ansar wayar yayi sannan yace ma "yan uwanshi suje waje , tashi sukayi suka fita har Ashiru , magana yayi da mahaifinshi bayan ya gama ya zauna a gefen gado ya riƙo hannun Sultana yana shafa fuskarshi dashi , da hannunshi na haggu kuma yana shafa gefen fuskarta ya tsareta da kallo yana mai addu'a ubangiji ya taƙaita wahala yasa An mata karta samu damuwa , likitoci suma kuma suna jiran farkowarta su ɗauki BP { Blood Pressure } nata sai ansan abinyi........
A hankali ya mayar da hannun nata ya ajiye tare da cewa wannan fa shine wauta bugun mace da mangariba , wayarshi ya ɗauka yana ƙara kallon hoton da Yazeed ya turo mishi shida An mata , yayi rantsuwa kuma ya ɗauki alƙawari da zuciyarshi Al ' Ameen Yazeed da Suwaiba idan ya barsu sun huta bai yafewa kanshi ba , Allah dai ya bawa An mata lafiya............
01/12/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 84
Kiran Ashiru ne ya shigo a wayarshi saida ya sake shafo fuskar Sultana ya ɗauki wayar tare da cewa ku shigo na gama , shigowa sukayi tayi dan duk wani yaron Dikko ya samu damar isowa a asibitin ɗakin baya anshe su , kallon Sultana Dikko yayi sannan ya kallesu yana cewa ku ɗan rage ina fitowa babu jimawa ya ƙarasa maganar yana kallon ƙannenshi yace ku kuma ku tafi gida kunji ngode ,
Yaya ai zamu kwana a nan ne inji Dady munyi waya dashi , murmushi Dikko yayi kaɗan tare da tsareta da ido irin kallon nan na rage gulof yace Dadyn yace ku kwana ? Ah Yaya ta daburce , ɗaure fuska yayi tare da cewa ku wuce ku tafi zanzo gidan anjima kunji ya ƙarasa maganar cikin sanyi.
Tou Yaya kuzo mu tafi tana jan "yan uwanta cikin rashin jin daɗi , har zasu fita Dikko yaga kamar babu daɗi yace Ni'ima zo ita ya kira dan itace babba a cikinsu , dawowa tayi ta tsaya gabanshi tana cewa gani kanta yana kallon ƙasa , me ne ne ? Kinji kamar ban kyauta ba ko ? A , a , Yaya , kun tabbata ? Ya ƙarasa yana kallon inda sauran suke tsaye , gaba ɗayansu suka ansa mun tabbata Yaya , yawwa to ngode ku huta gajiya , yawwa suka faɗa suna Allah ya bata lafiya.....
Momy kuwa bayan Dikko ya ɗauki wayoyinshi ya fita itama bin bayanshi tayi ita da zugar ɗiyanta wai tunda har akan Dikko Dady ya faɗa mata magana ta bar mishi shi kuma kada wanda ya buga mishi waya ya jajanta mishi yayi rashin lafiya sai Dikko ya gane bashi da wayau su mata ne kuma suna da yawa su haɗe mishi kai idan har suka bari ya rinjayesu zasu sha wahalarshi karsu sake zuwa gidanshi kowa yaje yayi rayuwarshi , idan yaji ya takura zai kira Dady ya faɗa mishi a lokacin ita kuma zata faɗawa Dady magana ,
Yazeed kuwa tunda ya tura hoto bugun zuciyar yaci gaba da halbawa ga abokinshi da aka kama wanda yayi ma Dikko magana ya fito dashi zasu shiga kotu , kuma ya daɗe da tura hoto baya goguwa kuma Dikko kaɗai ya isa ya tsaya mishi , matsala ta taho lallai haɗuwarshi da Dikko ba daɗi amma addu'arshi ɗaya Allah yasa Dikko ya saki Sultana.....
Matar Dady kuwa ta shiga ta tsaya tsaff a cikin yinin ranar yau tasa Al ' Ameen ya samo mata lambar wayar Maman Sultana har gidan Kaka yaje ya samota da kanshi , bayan ya kawo mata ta rangaɗa mata kira babu daɗewa Inna ta ɗauka suka gaisa ta gabatar da kanta da cewa ita matar gwamnan katsina ce , Inna tace sai akayi ya kuma ? Dan ita a tunaninta Maman DK ce , ita kuma taci gaba da rattafa mata cewa Dikko ya jefo mata "ya daga saman benen kanta ya daki ƙasa saboda shi ya riga gangar jikinta zuwa ƙasa ta daku sosai idan ta yadda ta ɗauke "yarta kafin ya kashe ta dama tana ta shan wahalar dangin miji tsangwamar kishiya masifar miji ga duka ga zagi ga gori abundai ba kyan gani , bayan ta gama faɗar duk buƙatunta Inna tace tou ngode sosai amma ni bana tare ma Sultana faɗa a gidan aure kuma duk abinda mijinta zai mata ni bai shafeni ba ai ina sane da ita tunda nasan na haifeta , na barta ta gurzu da rayuwa dan dani da ita ba'a san gawar farko ba ta koyi rayuwa ta koyi riƙe damuwa haƙuri da rayuwa dan idan nice yau bani ce gobe ba dan nima kin ganni nan nima nabi mijina dan shine gatana kuma marufar asiri na , Sultana yanzu tabar ƙarƙashin iyayenta ta koma ƙarƙashin aure banda iko da ita kuma ita ba yarinya bace idan taji ta matsu tana da ƙafafuwa ta gudu , Allah ya bata lafiya....... Tana faɗin haka ta tsinke kiranta.... Hmmmm Inna kenan manyan duniya...
Bayan awanni biyu da wasu "yan mintuna Sultana ta dawo , kamar mahaukaciya haka ta riƙa kallo tana motsa kanta kaɗan² tana kallo wurare , Ashiru yace sannu Hajiya , binshi tayi da ido ta kwalalo su sosai , Dikko dake zaune saman abin sallah ya tashi yaje wurinta An mata sannu , shima kallo tabishi dashi duk kamar dai mutane baƙi ne a wurinta sai kace wata sakara ,
Murmushi Dikko yayi tare da duƙawa kusa da ita yace sannu An mata , bata iya magana kwata² ta riƙe wuri ɗaya da ido tana kallo , ke me ne ne ? Baki ganni ba ? Ashiru yace mai gida ai sai a hankali zata ganeka , ƙarya ne ta ganeni mana ke ba kin gane ni ba ? Yayi maganar yana juyo kanta ta yadda kallonta zai dawo wurinshi ,
Kallo ɗaya tayi ma Dikko ta juyar da kanta gefe hawaye yana fita daga idonta , murmushi Dikko ya sakeyi tare da cewa bana faɗa maka ta gane ni ba , ɗan taɓe baki yayi yana cewa haushi na akeji baiwar Allah An mata ai koni saina baki shawara kiji haushin Dikko nima kaina haushin kaina nakeji , Ashiru jeka waje , Allah ya taimaki mai gida ya faɗa tare da fita daga ɗakin ,
Gefen gadon ya zauna yace An mata kiyi haƙuri don Allah na bari bazan ƙaraba ki gafarceni na yadda ni mahaukaci ne ya ƙarasa maganar hawaye yana fita daga idonshi , girgiza kai tayi dan bata iya magana , kinyi haƙuri ko ? Da kanta ta nuna a , a , haba An matana nasan kinyi haƙuri kuma bakiji fushi ba ke mai yafiya ce a gareni ki ƙara yafemin kinji An matana..... Ya ƙarasa magannar cikin yanayin neman gafara....
A , a , ta sake nunawa , hannunshi yasa saman idonta ya shafa ta rufe idon yace haba ƙaramar yarinya yau kuma Dikkon ake ma haka ? Abokin faɗan naki ? Kinyi min adalci kenan An mata ? Kiyi haƙuri mana nayi miki alƙawari bazan sake ba dan Allah ya riƙo hannun ta ɗaya ya soka "yan yatsunshi a ciki ya juyar da bayan hannun nata ya ɗora dai² saitin zuciyarshi ya danne da ɗayan hannun nashi yace kinji yadda zuciyata ke halbawa itama haƙuri take baki kiyi haƙuri An mata badan halin Dikko ba dan Allah ki rufamin asiri ki yafemin , karki yadda wani ya gano kinajin haushi na a gaban idon mutane ki nuna babu wani damuwa na yadda idan mun koma gida duk abinda kika ga dama kiyimin na yadda amma dan girman Allah idan kinga mutane ki riƙa sakin ranki karki wani haɗe rai kinji ko........ ? Shiru tayi batayi magana , kalli ya nuna mata idonshi jifa Dikko yana kuka ke bakyajin ƙunya ina miki kuka "yar yarinya ya ƙarasa yana murmushin ƙarfin hali , kallonshi takeyi har yanzu ba magana , hannunta yasa ya shafa gemunshi tare da ɗaga mata gira yace na bari matar Dikko ya faɗa da wani irin yanayi , duba wayarshi yayi da saƙo ya shigo , ɗaure fuska yayi ya goge hawayen tare da kama kanshi wai likitoci zasu shigo inji Ashiru ya turo mishi a waya , shima ya maida da to....
Hada Ashiru suka shigo , gaisawa sukayi da Dikko suna mishi yamai jiki , alhamdulillah daga haka bai sake magana saidai idan sunyi magana Ashiru yayi magana , bayan sun gama ɗaukar BP { blood pressure } nomal kamar yadda sukace aka wuce da ita C T Scan { Computered Tumography }. Dikko dai baije ba sai Ashiru da sauran tawagar suka bi bayan a can sun gama abinda sukeyi suka buƙaci sa hannun Dikko ya sa ya tafi ansa kiran Dady bayan ya gama sa musu hannun zai dawo kafin su gama abinda sukeyi.
Dady yayi ma Dikko faɗa sosai akan me yasa ya jefo ɗiyar mutane daga sama ko yayi hauka ne ? Waye yace masa ana dukan mace ma tun farko kenan ? Shi me yasa yakeyin abu kamar ƙaramin yaro wai ? Haƙuri yaba Dady shi bafa shine ya jefota ba faɗa yayi mata kawai saita firgita , Dady yace tou waye yace ana firgita mace ? Me na faɗa maka akan mace tun auren ka da Sadiyya ? Tunda baka san ta ka sawaƙe mata ta kama gabanta kafin ka jawomin tashin hankali , Dady ba haka bane , tare shi Dady yayi cewa ka rufe min baki ya faɗa cikin faɗa yana ci gaba da cewa ka saki yarinyar nan , haba Da.... , cikin hayani Dady yace bana san maganarka ka bani takaddar sakinta har sai yaushe zan huta da halinka Babana.......? Hawaye ya zubo daga idon Dikko yace Dady ni banayin saki , sai kayishi Babana sai ka saki yarinyar nan bazan bari ka kashe yarinyar mutane ba , yanzu da , da tsautsayi shi kenan maganar nan bazai rufe ba yana can yana zagawa a gari ka kashe matarka , dama na Sadiyya har yanzu surutu bai tsaya ba akan ka tsafe yarinyar mutane banda hauka kuma zakaje da gangan ka jefo yarinyar mutane kai sarkin zuciya itama ta mutu ka zama matsafin kenan ko................?
Shiru Dikko yayi kanshi yana kallon ƙasa lokaci bayan lokaci yana buɗe bakinshi kaɗan yana jan iska cikin ɓacin rai , Dady kuma ganin Dikko yana kuka yasa ya sassauta maganarshi yana cewa ni ne kaɗai na isa na faɗa maka gaskiya komin rashin daɗinta bana san abinda kake yi kaji ? Ya ƙarasa maganar cikin sigar lallashi , kallon Dady Dikko yayi sannan yace kaima mahaukaci kake cemin ko Dady ? Baban naka ne mahaukaci ko ? Ya faɗa yana ɗora kanshi a kafaɗar Dady yana kuka , tunda kacemin mahaukaci kowa ma zaice ni mahauka ci ne.
Bakajin magana Babana nace bana san halin nan bazaka bari ba ya kake so inyi ? Kayi haƙuri Dady na bari bazan sake firgita ta ba , idan na sake ji kuma fa ? Sai kayi min faɗa ya ƙarasa yana kallon idon mahaifinshi cikin soyayya , murmushi Dady yayi shima Dikkon murmushi yayi tare da rumgume Dady yana dariya........ Aka daina zancen saki.
Daga wurin Dady wurin Momy ya wuce duk sallamar da yayi bata ansa ba daga ita har "yan uwanshi kuma babu wanda ya kalleshi , Rabiya sai haɗe rai takeyi tana hararar bango , cikin rashin jin daɗi Dikko yace Momy meya faru ? Fuuuu ta tashi tayi ciki suma suka tashi suka bi bayanta , cikin yanayin damuwa Dikko yabi bayanta tana zaune a gefen gado sai ɓata rai take , wurinta yaje ya duƙa gabanta ya riƙe hannunta cikin lallashi yace baki lafiya ? Cikin faɗa tace lafiyata qalau , tou me yayi zafi haka ? Ya faɗa yana tsareta da ido , ban sani ba tunda kaje ka haɗani da ubanka kai ɗan zinari , me nace masa Momy ? Kace masa ni bana sanka , Rabiya tace Momy ji har kin manta kina masa magana shi yasa yake iskancin daya ga dama , cikin ɓacin rai ya leƙa ta gefen Momy inda Rabiya take zaune yace ki fita hanyata kafin in kwantar dake , Momy tace kwantar da ita Iliya ɗan mai ƙarfi , ƙannenshi ya kalla tare da cewa da Allah ku fita kuba mutane wuri , tashi sukayi suka fita wurin ya rage daga Dikko sai Momy sai yayyenshi , Rabiya tace to ka kwantar dani mara kunya , bai kalleta ba yace Momy me nayi miki ? Dikkon ne mai laifi a wurinki ? Haba Mamana waye zai haɗani dake ? Cikin sansanyar murya tace Dadynku ne yayi min wulaƙanci a gaban kishiya abin baimin daɗi ba , Rabiya tace ki kyale shi Momy ai duk shine munafukin , dunƙule hannunshi yayi tare dakai zamiya taja baya da sauri yace zan...... Riƙeshi Momy tayi tace ya isa ta faɗa tare da miƙewa taja hannunshi suka fita waje ,
Wurin motarshi suka tsaya tana masa magana wai yanzu ya daina santa a gaban idonshi ake mata iskanci a gidan nan yana kallo bayayin komai , yace Momy tou yanzu kuma me akayi miki wanda nayi shiru ? Ɗan ɓata rai tayi cikin rashin san zaman lafiya tace yanzu ba a gabanshi Bilki taje take faffaɗa mata maganganu marasa daɗi ba shine yayi shiru { abiyar zamanta } Dikko yace Momy dan girman Allah kiyi haƙuri babu yadda za'ayi ta faɗa miki maganganu kedai ki bari a zauna lafiya , sai kice anyi miki laifi kullum inyi ta hauka har an fara cemin mahaukaci , tou Dikko ƙarya nakeyi ta juya zata koma ciki da ɓacin rai tana gunguni , da sauri yasha gabanta yace shikenan zan mata magana , dariya tayi irin ta ƙasaitaccin mata , duƙawa Dikko yayi ta dafa kanshi tana cewa Allah yayi maka albarka , amin ya faɗa ta koma cikin ɗaki ,
A gajiye ya koma mota ya kifa fuskarshi a saman sitiyari shidai baisan abinda yasa gidansu akeyin bahaggon zama ba , sai zafin kishi da nuna "yan ubanci "yan wancan ɗakin basa san "yan wancan ɗakin , kowa ɗan ɗakinsu ya sani kuma shi yake so , sai kuma wani babban shirme idan ana faɗan kishi sai kowa ya shigar ma mahaifiyarshi wai me yasa mata sukeyin haka ? Shifa a tunaninshi matar uba uwa ce , ita kuma "ya "yan mijinta kamar itace ta haifa , gaskiya gaba ɗaya babu kyautawa su kuma wanda iyayensu basa gidan an ɗauki masifar duniya an ɗora akansu ga masifar aiki ga aike² kamar ba "ya "yan Dady ba sunayin wata irin rayuwa kamar "yan aiki kuma a hanasu ganin Dady saidai shi idan yana nan yake musu jagoranci zuwa wurin Dadyn , kuma shima Dadyn ya kamata idan baya nan ya dawo yaga kowa suma ya nemesu tunda ai yasan ya haife su , haka ya siyama kowa sabuwar mota amma duk wanda babu uwarshi a gidan babu rabonta , dole shine ya siya musu motocin da suke hawa Momy kuwa tace ina wuta ta jefa Dikko tayi tashin hankali saida aka kai ruwa rana suke hawan motoci , su Momy basa tunanin idan Dady ya sakesu ko suka mutu suka bar nasu "ya "ya wace irin rayuwa zasuyi ? Ya kamata a riƙa adalci a rayuwar "ya "yan da basa tare da iyayensu a gidan miji dan babu wanda yasan abinda gobe zatayi haka kuma babu wanda yasan maci tuwo sai miya ta ƙare , shi kuma yayi bakin ƙoƙarinshi wurin ganin Momy ta jawo yaran jikinta tana basu kulawa tarbiyya da tsaro kamar yadda take ba nata "ya "yan amma tace sam bata ƙaunar ɗan kishiya , tsoki yayi a dai² lokacin da text in Umar ya shigo Al ' Ameen ya shiga gidan gwamnati yanzu , dan yadda yasa aka sakawa duk wani motsin Sultana ido a baya haka yasa a sakawa Al ' Ameen.....
Yana tashin mota wani text in ya shigo amma yanzu ba Umar bane Al ' Ameen ya shigo yana ɗakin Aunty , kai tsaye wurin Dikko ya nufa da gudun tashin hankali ɓacin rai yana hawa , tunda motarshi ta tsaya gaba ɗayansu sukayo waje hada Al ' Ameen da matar Dady ita tana cewa wannan wane irin iskancin tuƙi ne zaka zo ka tashi hankalin mutane , wani irin kallo Dikko yayi mata sannan ya kalli Al ' Ameen yace me kazo yi nan ne ? Shiru yayi baiyi magana ba , fitowa yayi daga cikin motar ya taka ƙafarshi ta baya ya dafa murfin motar da hannun damarshi na haggun kuma riƙe a ƙugunshi yace da kai nake me kazo yi nan ne ? Aike na tayi , zuwa ina ? A daburce yace ca ca can..... Ya nuna da hannunshi , har yaushe aka fara aiken ni ban sani ba ? Yanzu ne mai gida , tou ya akayi ka shiga ɗakinta ? Kai Dikko bana san iskanci ni zan aiki yaro kazo kana mishi tambayoyi , hannun daya dafa murfin mota ya ɗaga mata ba tare daya kalleta ba yace hajiya ba dake nake ba yanayin fushi yana gaf ki kama gabanki ko kimin shiru , sakin murfin yayi ya matsa kusa da ita ya riƙe ƙugu yace ai nima a cikin matan na tashi kuma duk wani makirci na iya kuma duk a wurinku na koya ki bari kafin in gigita miki tunani , wurin Al ' Ameen ya koma ya riƙe wuyanshi amma bai matse ba yace tunda kake ka taɓa ganin wani mai aikinta yaje ɗakin Momy ?
Kafin Al ' Ameen yayi magana ta ɗaga murya tana salati cikin kuka wai ita Dikko ya daka ? Ta shiga 3 ta lalace , Dikko yace tou tunda sharrin kike so bari ki tara man mutane idan Dady yazo zance Al ' Ameen na kama ɗakinki , ta ɗage baki bata ƙara ihun ba kuma bata rufe bakinta cikin tashin hankali ta kalli Dikko tace ummmmmm , murmushi Dikko da gefen bakinshi yace ummmm a dai² lokacin da yayi ma kan Al ' Ameen kyakkyawan riƙo da duka hannayenshi ya buga shi da bango yayi mishi fashin kwakwa , amma ba fashewa yayi biyu ba , take a wurin Al ' Ameen ya ɗauke , dariya Dikko yayi ya kalli matar Dady har yanzu bata rufe bakinta ba , but ya buɗe ya jefe Al ' Ameen ya rufe yaja motar da gudu ya barɓaɗeta da hayaƙi bata matsa ba tana tsaye wurin , Goruba yakai Al ' Ameen ya cire wayar jikinshi ya nufi asibiti dan dare yayi.
Satina 3 a asibiti bayan nasha doguwar wahala dan bayan an haska ƙwalwata likitoci sun tabbatar da jini ya shiga brain ina saida akayi min borrhole surgery kuma kullum Dikko ne yake jinyata komai shi yakeyi min yana bani haƙuri akan abinda ya faru bazai ƙara ba , amma na daka kaina ƙasa bazan komai zama dashi ba.
Inna kuwa Dikko ya kirata ya faɗa mata banda lafiya tace Allah ya sawaƙe itama tasha fama da rashin lafiyar wai tayi ɓarin ciki , da yace mata gani cewa tayi tana gaisheni itama zata dawo kwanan nan ,
Dikko kuwa ya ƙufule akan duk wanda baizo ganin Sultana ba shima saiya rama , zama dai cikin mata yasa shima ya iya tsegumi da irin halinsu ,
Bayan an gama kai magunguna a mota da dai abinda ya kamata yace muje , fashewa nayi da kuka ni bazan zauna ba , haba An mata wai meye kikeyi haka don Allah ? Nifa gaskiya bana sanka saika sakeni da , da ƙarar kwana dana mutu an fara kiran marigayi Sultana , yi haƙuri bazan ƙara ba , nidai bazan zauna dakai ba mahaukaci , ba komai idan ma kince mahaukacin ne ai banji wani damuwa ba na yadda ni mahaukaci ne kiyi haƙuri dan girman Allah An mata , nifa bana zama dakai saika sakeni , daka min tsawa yayi tare da cewa anƙi a sakekin kuma tunda ke yarinya ce ta tashi mu tafi bara ki sake magana kiga yadda zanyi dake dan kiga ina lallaɓaki kike tunanin na warke ? Tou ina nan yadda kika sanni tun farko ban canja ba sai abinda yayi gaba ya ƙarasa maganar yana min kallon da bana so.
Naji tsoro amma saina kalli ƙasa na sake cewa saika sakeni , zama yayi kusa dani yace An mata kalli ya nunamin cikin ƙwayar idonshi da kallonshi mai ɓatar da damuwa yace yanzu ko dan albarkacin wannan bazanci ba ? Haba ƙaramar yarinyar Dikko cikin sigar lallashi ya ƙarasa maganar yana murmushi tare da rungumoni jikinshi ,
A wahalce na sauke ajiyar zuciya cikin shashshekar kuka , dafe ƙeyata yayi da hannunshi yace ai na sani kiji natsuwa daga jikina An mata yayi maganar yana jawo numfashi daga cikin cikinshi saiya ɗan riƙeshi a ƙirjinshi kamar shashsheka haka da ɗan sauri² mai tayar da tsikar jiki cikin salo mai tada hankali , shiru nayi ban sake ko motsi ba na ƙara lafewa a jikinshi , murmushi yayi a zuciyarshi yace haba An mata ina zaki tafi kibar mahaukaci ? Ai muna tare harsai hauka ya ƙare.
Saida ya tabbatar ya ladabtar da jikina ya fara ƙoƙarin sakina , ƙara riƙeshi nayi ina kuka , me ne ne kuma ? Ba komai na bashi ansa , tou sakeni , anƙi a sakenka na faɗa da irin ansar daya bani aa farko ina ƙara lafewa a jikinshi kamar ƙadangare ya lafe jikin bango idan yaga mage , murmushi Dikko yayi cewa tou tashi muje gida sai ki rufe ƙofa ga makullinma tun yanzu ya bani a dai² lokacin daya ɗagoni yana kallona yace kinga sai muci karenmu ba babbaka ko......? Ya ƙarasa yana ɓata fuska a sakace , Murmushi nayi banyi magana ba ina kallonshi , yace yawwa jarumata muje ya ƙarasa maganar yana saukoni daga saman gadon....
Ashiru ne ya ɗaukemu , dani da Dikko muna baya kuma tunda muka baro ɗakin har yanzu bai sake magana ba sai haɗe rai yakeyi kamar bai sanni ba , ko magana nayi mishi saidai yayi min wani irin gittaccen kallo , ni na kasa gane inda ya dosa wani irin birkitaccen hali yake dashi yanzu mutum anjima ba mutum ba , tsoki nayi ban sake magana har muka isa goruba road , ajiyemu Ashiru yayi ya tafi da motar ledar magungunan ya bani wai inje ciki yana zuwa kuma inyi wanka....
Banyi magana ba na shige , na daɗe sosai har nayi wanka na fito bai shigo ba , jikin madubi na matsa ina duƙar da kaina inda akayi min aiki , taƙaitaccen murmushi nayi tare da komawa da baya na zauna saman gado ina kallon kaina a madubi nace ina Amisty ? Kizo kiga ranar da nake faɗa tazo ,
Nace miki naji a jikina zan rasa wani babban abu mai muhinmanci a rayuwata , ni kuma zan shiga wani babban tashin hankali wanda bansan ranar zuwanshi ba , ashe abinda zan rasa ba komai bane sai Babana , tashin hankali kuma ashe shine wannan na taɓa kaina yau itace ranar wayyo gani anyi min aiki cikin kai niba mahaukaciya , fashewa nayi da kuka gaskiya rayuwata ta cika tsalle² a dai² lokacin nan ya shigo yana cewa kin fara ko ? Kedai kika sani An mata kiyi duk abinda kikaji kina iyawa , da gudu na tashi naje na rungume Dikko cikin kuka nace wai me yasa rayuwa take tsanantawa ne ? Ba tare daya riƙeni ba yace An mata duk yadda rayuwa ta baki kawai ki ansa , ya ƙarasa maganar yana jana zuwa gaban gado ya zaunar dani , wayata ya ciro daga aljihunshi Hafsa ke kirana , shine ya ɗauki wayar yace ya akayi ne ? Bayan wani lokaci yace lafiya , kila gaisheshi tayi nadaiji yace lafiya , ........, tana bacci , ........ Wane wuri ne ? ........ Tou bata da lafiya idan ta samu sauƙi zan kaita yana faɗin haka ya tsinke kiran !
Ajiye wayar yayi da nashi ya ɗauki kofi zai fita , tun kafin ya fita cikin kuka nace bazan sha ba , baiyi magana ba ya dawo ya ajiye kofin a inda yake ya nufi toilet , kuka naci gaba da yi ina maimaita bana sha kuma bazan sake sha ba mugunta kawai , har ya fito wanka ban dai tsegumi ba , ko inda nake bai kalla ba yaci gaba da huɗɗar gabanshi , ganin zai saka kaya nace nayi wankan na faɗa a tsiwace , tou ina ruwana da wankanki , ai kaine kace nayi wanka , rigarshi yake ƙoƙarin sakawa yana cewa tou ki kwanta kiyi bacci idan kuma kina zuwa tashi mu tafi G R A zanje Jiddah bata da lafiya , banyi magana ba na tafi inda ya ajiye kofin na ɗauka nace zansha , ai babu ya ƙare ki saka kayanki kawai mu tafi , yi haƙuri , a , a , dan Allah Dikko ai nace babu ya ƙarasa maganar yana kallona , na bari , zaki sha ne ? Ey tou jeki ibo ya faɗa yana cire rigar daya saka tare da cewa dandai baki lafiya amma yau dasai nayi miki rowa ƙaramar yarinya dake , murmushi nayi tare da juyawa na murza ƙuguna cikin salon jan hankali da neman faɗa , murmushi yayi ya biyo bayana yace bakijin magana ko An mata ? Nima yadda naga yana ɗaga gira nayi nace kai ka koyamin rashin jin ai...
Ah ni ƙarya kikemin , tare dashi mukaje wurin firij ni na riƙe kofin ya zuba yana kallona yace An mata nan gaba kodai nine zan riƙa riƙe makulli , hmmm idan ya ƙare bana sake siyowa inba haka idan kika kamani a ɗaki saina ci ƙaniyata yayi maganar yana riƙoni jikinshi bayan ya maida "yar jarkar a firij , ɗaga hannuna nayi da niyar shafa gemunshi amma saina ɗorashi a goshinshi , dan shima haka yakeyi baya yadda mace ta gane abinda yake tada mishi hankali a jikinta kuma ko yana kwance da mace yana warwarewa yana saiti baya surutu shiru yakeyi sai wani munafikin kukan kissa mai tsayawa a rai da tada hankali idan ka tunoshi , kome nake abun yana yawan zuwamin a rai , idan na tuno abun sai hankalina ya tashi sai naji maganar Dikko ko na ganshi ko naji ni a jikinshi nake samun natsuwa , Hmmm Dikko duniya , amma ban sani ba ko ni ɗaya yake ma haka ......?
Saifa na taɓo dan haka na ɗan basar na taho da hannu ina kawowa saitin bakinshi ya sumbaci hannun muah yana sauke wani irin nishi , tsikar jikina ta tashi yarrrrr da sauri na shanye maganin nace ngode , murmushi yayi ya jani zuwa ɗaki..... An danbace cikin tsari da sabon salo ba irin wancan ba...
Sai bayan isha'e muka isa G R A kuma an sauke bene anyi ma palo gyara na bada mamaki idan baka san wurin ba zaka rantse bene bai taɓa zama a wurin ba a cikin sati 3 , binshi nayi har ɗakin Jiddah ina ƙara kallon palon , ɗakin cike yake da mutane da "yan uwan Jiddah da mahaifiyar Dikko da danginshi , sai wata mai kama da maman Dikkon kila itace maman Jiddah , wani irin kallon tsana Momy ta bini dashi har naji babu daɗi jikina ya fara ƙyarma , kusa da Dikko na zauna idona ya cika da hawaye kuma har yanzu jikina bai daina ƙyarma ba dan ni a halin yanzu bana so nayi wani abu da zaisa nayi nisa da Dikko wallahi bana iya rabuwa dashi , cikin rawar murya nace Momy ina yini ɗauke kanta tayi bata ansa ba , kallona Dikko yayi yace me ne ne kike kuka ? Dakel na haɗiye yawun bakina nace ba komai , kallon Momy yayi sannan ya sake kallona , tana ganin Dikko ya kalloni ta nunamin saita kasheni , da sauri na ɗauke idona na gaishe da Maman Jiddah , itama ɗayan mara wayan ɗauke kanta tayi in banda rashin wayau abiyar zaman ɗiyarta aida da wayau ko ba daɗi tayi ta "yan bariki tace lafiya lau Sultana badai wayau "yan mata sunma makaɗi tusa.....
Duk basar dani sukayi sukaci gaba da firarsu ita Maman Jiddah babu ɗan kawaicin nan irin na sarakuta da Dikko ta saki baki sai ɓarin maganganu takeyi na rashin lissafi a gaban Dikko abinda na fahimta wurinta Jiddah ta gado surutun tsiya kamar akku , ita kuma Maman Dikko bata da yawan magana kuma bata cika dariya ba tana da natsuwa sosai tanayin magana cikin aji da kamun kai amma bata da mutunci "yar masifa ce wato mafaɗaciya su kuma su Dikko a wurin uwarsu suka gaji rashin mutunci , suna da sakin layi idan mutum ya shiga jikinsu dole zai raina su dan basu da sirri ga Mardiyya amma sai sakin layi suke suna maganganu.......
Dikko kuwa bayan ya gaisa dasu Momy wurin Jiddah ya koma yana ta jera mata sannu haushi abin ya bani kuma na ƙufule har a wuya ji munafurci ɗazun nan yake nuna ba wata bayan ni amma yanzu yaga Jiddah harya manta da Sultanar banza , kallon Jiddah nayi sai wani kwarkwasa takeyi tana kashe mishi ido shi kuma yabita da kallo , komi ya sameta ? Oho ma banza , miƙewa nayi na fita dan abune nasu na "yan uwa ni kuma a cikinsu bare ce ba "yar uwa ba dan haka na tattaro mutunci na nabar ɗakin ,
Palo na dawo na zauna , shiru² ba Dikko ba inuwarshi har 9:13pm gajiya nayi na kirashi a waya , ya akayi ? Ya tambayeni bayan ya ɗauka , bacci nakeji , kashe wayar yayi ya fito saida yazo inda nake zaune yace ai na ɗauka kin tafi kin kwanta , jeki ki kwanta fita zanyi yayi maganar yana miƙomin wayoyinshi , cikin ɓacin rai nace ai dama dole zakace naje na kwanta tunda kaje ka kasa ka tsare kai tattabara sarkin aure , yarinya kenan idan kinga dama tashi muje , nifa bana kwana gidan nan a ina ma zan kwana tunda an rushe ɗakin na ? Bai bani ansa ba yace tou naji baki kwana tashi kije Ashiru ya maida ki goruba , ai ni tsoro nakeji saidai mu tafi tare idan nayi bacci kaje inda zaka je , duk in fasa abinda zanyi sai kinyi bacci kammar sakaran namiji ? Ke zaki koyamin yadda zanyi rayuwa ma kenan ko ? Idan kinga dama ki bishi ni kinga tafiyata kuma karki zubar min da wayoyi yayi gaba abunshi............
02/12/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 85
Da sauri nabi bayanshi har an buɗe mishi mota ya shiga , yana shiga nima na shiga kafin a rufe , kallona yayi baiyi magana ba sai tsoki tare da matsawa daga kusa dani yana hararata , murmushi nayi kamar sakarai ina yaƙe haƙora , yadda nayi abun na bashi dariya yace hmmm Yarinya , tafiya aka farayi da motar ni kuma na miƙa mishi wayoyinshi yace in riƙe mishi zasu ajiyeni gida shi Kano zaije , cikin rashin jin daɗi nace haba Dikko Kano kuma yanzu na ƙarasa maganar kamar zanyi kuka , yi haƙuri An mata zan dawo ai ba kwana zanyi ba yayi maganar yana jawoni jikinshi , kwace jikina nayi ina cewa ai saika kaje kayi ta tafiya , yi haƙuri , ban sake magana ba har muka iso gida ,
Anayin parking na fita cikin ɓacin rai , kirana yayi nai banza dashi kamar banji ba , cikin fushi yace kije kiyi ta zuciyar ƙaramar yarinya dake , ban juyo ba na shige ciki da gudu ina kuka nidai bana so ya tafi da daren nan shine zai tafi ya barni , har sun fita daga gidan Dikko yaji kamar babu daɗi suka dawo , palo ya sameni kwance saman kujera ina kuka , cikin rarrashi yace An mata zo nan , dan bai shigo ba daga bakin ƙofa ya tsaya , ina tashi nayi bedroom , da sauri ya biyoni na kusa shiga ya riƙeni cikin disashshiyar murya yace haba An matana meye na fushi tou ? Yi haƙuri bazan daɗe ba maganina zan anso kinsan banajin daɗin tafiya da rana kafin ma kiyi bacci zan dawo insha Allah kinji An matan DK ya ƙarasa maganar yana rungumeni , banyi magana ba , ina shashshekar kuka , kinyi haƙuri ko ?
Ey , hannunshi yasa a aljihunshi ya ciro cingom saida ya saka a bakinshi yace kallar ni , tashi nayi daga jikinshi ina kallonshi , murmushi yayi da kallo mai kwantar da hankali tauna cingom in yayi sannan yace idan miji zaiyi tafiya ba'a mishi haka kinji ko ? Tom , ba'a yin abinda zaisa ya tafi da fushi kinji ? Tom , idan miji zaiyi tafiya addu'a ake mishi sai a rabu cikin soyayya da nuna kowa zai shiga taitaiyin shi idan abokin rayuwarshi baya kusa ki nunamin girman yadda zakiyi maraicina idan bama tare , zan tafi da soyayyarki kuma zanyi kewayarki zan dawo gareki ina mai farin ciki darajar waccan kulawar , kinga na baki wayoyina nace kije Ashiru ya maidake gida ni zanje na dawo ko ba daɗi sai kimin fatan alkairi ,
Kalli idona ki gani , kallonshi nayi cikin yanayin jin kunya , da nace zanje in dawo sai ki kalleni da irin wannan kallon ya nunamin cikin wata irin murya da shagwaɓa ina zakaje haka ne ? Kin gane ? Zanji wani iri a zuciyata kinyi min magana da salon da dole saina kalla , sai ya saki muryarshi yadda yake magana yace sai ince hajiya kano zanje , sake shagwaɓewa yayi ya nuna yadda zanyi idan zan bashi ansa , amma sai kiyi ta abu da Allah na yarinta ba lallashi komai maganarki a tsaye baki lanƙwasamin harshe nace miki bana san yadda kikemin magana saiki tayi min kallon da bana so , daga nace zan tafi kano ba addu'a ba komai fuuuuu ke ƙaramar Yarinya , kinsan Allah idan kikayi wasa saina ƙara aure ,
Tou kaje ka ƙara mana na hanaka ? Kinji yarintar ko ? Ji abinda kikeyi kina magana da miji kina ɗaga mishi murya , ba abinda kika iya sai kwanciya jikina shine kaɗai aikinki saina raba wurin kwanciya dake tunda ke Yarinya ce , kaje ka raba , murmushi yayi yace nasan ciwonki , yadda nayi maganar ya nuna dole zakace naje na kwanta tunda kaje ka kasa ka tsare kai tattabara sarkin aure , murmushi yayi tare dayin wasa da idonshi yana ci gaba cewa yes haka kishi ne , kishi kuma so ne , da hannunshi ya rungume kanshi yace wayyo An mata na kishi na ci gaba sabo ,
Da wata irin tafiya mai taɓa zuciya ya fita yana cewa ko bakimin addu'a a gabana ba nasan zakiyi a zuciyarki kuma saina yo miki tsaraba tunda kikaji kishina a zuciyarki saina sa kinyi farin ciki mage zan samo miki , ya fice , murmushi nayi da farin ciki na shige ɗaki da gudu na hau gado ina tsalle Allah ya tsare hanya mutumina.
Bayan na kwanta na ɗauki wayata na kira Amisty , babu wani daɗewa ta ɗauka bayan gaisuwa nace Amisty don Allah rubuto min An mata ki turomin , kamar ya ? An mata haka zaki rubuto min , tou ta faɗa tare da ajiye waya , burum ta rubuto ta turomin , gyara kwanciya nayi na rubuta An mata , wayar Dikko ta buɗe , Allah sarki Dikko ashe da gaske yake da sunan da yake kirana ya kulle wayarshi , ba wani ruwana da saƙonni wayarshi dan bana ganewa , ma'adanar hotuna na shiga ina kallon Dikko da "yan uwanshi , haka dai nayi ta zaliƙe² a wayarshi har na shiga inda nakejin maganata da tashi duk wayar da nakeyi dashi yana record kenan , Allah sarki Dikko , saida nayi filla² da duk inda nake iya shiga a wayar amma banga hotuna na ba , tou ina suke ai yacemin wayarshi bata san kowa ba daga An mata sai Doki , tou naga dukuna babu iyaka a wayar amma ina An mata tou........ ?
Tashi nayi zaune na ciji ɗan tsayana cikin yanayin mamaki to dama masu gemu sunayin ƙarya ? Tsoki nayi tare da ajiye wayar , ina ajiyewa kira ya shigo , kamar ansa ni na ɗauka tare da cewa waye ? Caca , Oh Jiddah ce kenan ko ? Zuciyata ta fara turani inyi abinda zan ɓata mata rai amma sai wani sashi na zuciyata yace bari suja miki sharri Dikko ya sakeki , da sauri na kama kaina nace yana wanka , uban waye yasa kika ɗaukar mishi waya tou ? Ina da ansar bata amma nidai bana so naje nayi abinda zai jawomin tashin hankali har Dikko yayi fushi dani , tsinke kiran nayi , haka kiran yaita shigowa amma ban ɗauka ba , tunda kiran Jiddah ya shigo kira yaci gaba da shigowa , ita kuma ɗayar wayar naga hoton jirgi daga sama ita kira baya shigowa kenan ?
Da naji kiran yayi yawa zasu hanani bacci kawai na kashe wayar , nayi kwanciyata naci gaba da bacci abuna....
Yau kwanan Al ' Ameen 22 babu wanda yasan inda yake , duk wanda yasan yana da haɗin guiwa da Al ' Ameen akan "yan tsirkulle² hankalinshi a tashe yake danjin Dikko ya tafi dashi tun daga ranar da Dikko ya tafi dashi har zuwa yau basu da nutsuwa , su basu san ba'a kan matsalarsu Dikko ya riƙe Al ' Ameen ba shi Dikkon ya ɗauki Al ' Ameen dan yasan abinda ke tsakaninshi da Jiddah ne , wanda har ba'a magana sai tsakar dare , shi bai wani san akwai wani abu tsakaninshi da matar Dady ba.....
Zaune take ta wani kame abunta a saman kujera ta ɗauke kanta gefe gudu ba kajin wani lafiyayyen motsi sai ƙarar cingom in ita ƙasa×⁴ , kallonta Dady yayi yace wai meke damunki ne ? Duk kinbi kin tashin hankalinki akan wani dalili naki na daban , akan me fushin wani ni zai shafe ni ne ? Saida ta ƙara ƙaras² sannan tace haba mai girma gwamna ya za'ayi ace duk inda Dikko yake ajiye mutane ace an kasa samo Al ' Ameen ? Kafa san halin Dikko kila ma yaje ya kasheshi ya jefar dashi ruwa , tou ni gaskiya bazan daina fushi da tashin hankali ba sai an samomin Al ' Ameen a daren nan.....
Dady bai sake magana ba ya fara kiran wayar Dikko , gaba ɗaya wayoyin a kashe suke , Ashiru ya kira kuma ba tare dashi Dikko ya tafi ba saboda shine yace ya maida Sultana Goruba shi zaije ya dawo sai bata bi Ashiru ba tabi Dikko , cike da girmamawa Ashiru ya ɗauki wayar Dady ya gaishe shi , bayan gaisuwa Dady yace ina Babana ya kai Al ' Ameen ? Har ga Allah Ashiru bai tunanin komai ba yace yana Goruba road , Dady yace ka kawoshi yanzu² , Ashiru yace insha Allah suka ajiye waya ,
Bayan Dady ya gama waya da Ashiru ya kalli Bilki yace tou kinma ji yana Goruba Ashiru zaizo dashi yanzu , murmushin jin daɗi tayi ba tare data kalli Dady ba tayi godiya kusa da ita ya zauna................. !!! | cikin "yan mintuna da basu wuce 15 ba Ashiru yakai Al ' Ameen , kuma lafiyarshi garas dan Dikko bai dakeshi ba tunda ya buga mishi kai a bango ya suma bai sakeyi mishi wani abu yana mishi tambayoyi ne kafin ya gama yaci mutuncin shi ,
Momy kuwa tana can sake da baki tana bacci bata san wainar da ake toyawa ba , dan ita ba ma'abociya sa ido bace da sanin halin da wani yake ciki ba , barta dai da zafin kishi taƙalo fitinar da bata garai bata da dalili dan mafaɗaciya ce ta farkon shafi kuma bata san zaman lafiya ko kaɗan , ko shiru taji gidan kwana 2 ba'ayi faɗa ba haka nan zatace ta fita ana mata kallon hadarin kaji haka zata saka Dikko gaba tace anyi mata an matsa mata ita zata kashe auren nan tayi tafiyarta bata zama hawan jini ya kamata idan kuka bari na mutu kun shiga3 kaza² duk dan dai ayi hayaniya , haka zata haukatoshi ya fito yaita cancara ruwan rashin mutunci dan duk yafi kaf "yan uwanshi fitina bai gajiya da faɗa kuma baida haƙuri kamar amai idan ya fara babu kyau , tou bata tsayar da kanta wuri ɗaya ba bare ta gane inda duniya ta dosa.....
Da inda ya ajiye Al ' Ameen ya fara bayan ya dawo daga kano babu shi babu dalilinshi , agogon hannunshi ya kalla 2:15am jinjina kai yayi ya nufi ciki , wayoyinshi ya ɗauka duk ya fitar dasu a jirgi , kai tsaye Umar ya fara kira , cikin yanayin bacci ya ɗauka , bayan ya ɗauka Dikko yace ina Al ' Ameen ? Kallon Al ' Ameen dake kwance kusa dashi yana bacci yayi sannan yace har kin farka kenan ? Dikko yace kai nine ta farka gidan su wa ? Ai na gane ki ranki ya daɗe Baki daɗe da kwanciya ba a kusa dani kikayi mafarki ? Shiru Dikko yayi yana sauraren Umar daya maidashi mace , Umar kuma yaci gaba da cewa ....... A ina kika ga ɗakin ne ? ....... Tou Allah ya ƙarawa mai girma gwamna lafiya da nisan kwana muyi ta zarce muci gaba da zama a gidan gwamnati kuma kema zan kawoki har sai kin kwana kamar yadda nake kwance dani da mai gidana Al ' Ameen a ɗaki ɗaya yana bacci , kashe waya Dikko yayi tou waye ya tafi da Al ' Ameen wato yana can ma yana bacci yasan zan nemeshi shi yasa bai tafi G R A ba ya tafi wurin Umar , tashin Sultana ya farayi , da sauri na buɗe idona a firgice dan mafarki nakeyi da mutumin nan , An mata tashi na dawo lafiya kuma na samo miki magen kamoni yayi yana sauko dani yake cewa muje ki anso fita zanyi , banyi magana ba kafin in saka takalmina har ya fita daga ɗakin ina fitowa harya fice daga palon da sauri , kafin na gangare daga sama har ya sauka , cikin mota na sameshi kwalin da magen take ciki ya miƙomin tare da cewa jeki saina dawo , ajiye kwalin nayi ƙasa zan riƙeshi a kasalance yace yi haƙuri An mata idan kika taɓani yanzu zaki jawo rigima , nidai dan Allah , tou taho ya faɗa yana kamo hannuna ɗan jirgewa nayi na zauna a jikinshi na kwantar da kaina a ƙirjinshi baimin magana kuma bai taɓani ba shi kaɗai yasan ɓacin raan da yakeji a zuciyarshi saida na gaji na tashi da kaina ya ɗauki kwalin ya miƙamin na wuce ciki shi kuma ya fita......
Yau yazo da wani irin ɓacin ran da babu wanda ya taɓa ganinshi a yanayin , yayi ihu yayi hauka yace ana shiga mishi haƙƙi ya daki kanshi da saitin zuciyrashi yace shi ba mahaukaci bane ba , shi Dikko yasan abinda yakeyi ya rantse da girman Allah a tsautsayi wani ya kuskura yazo kusa dashi saiya kashe shi da gaske yake kisa zaiyi zai kashe ko waye ya kuskura yazo inda yake idan kuma mutum ya taɓashi to tabbas ko gawarshi bazatayi kyan gani ba saidai shima ya mutu ya yadda da wannan , idan da wanda ya gaji da rayuwar duniya yazo yau shine zai kashe ko waye idan baiyi kisa yau a gidan nan ba tou wallahi ya yadda shi ba ɗan Babanshi bane ba ina Al ' Ameen ina wanda yaje ya taho dashi waye yasa aka fito dashi ne............ Ya ƙarasa maganar yana buga kafarshi ƙasa da ƙarfi tare dayin wani irin ihu mai tada hankali da gigita , dake dare ne ihun Dikko da hayaniyarshi ya karaɗe kaf ilahirin girman gidan gwamnati ihunshi na yau yafi na kullum tashin hankali dasa ɗimuwa , duk mai imani saida ya tausaya ma Dikko kuma kowa yasan wannan abu badai mutum ba , kowa yayo waje inda yake tsaye yana hayaniya sun zagayeshi amma an rasa waye zai shiga wurinshi , sunan Al ' Ameen ya kira da wata irin murya yace ba duka ba zagi ba harara bare magana mara daɗi ka fito da kafafuwan ka kazo ka shiga mota kafin in irga 10 idan kuma ka bari na fito dakai da kaina saidai uwarka ta sake haifo wani ba kai ba dan zaka shiga 3n ka kuma zaka bani ka lalace , rufe idanuwa yayi cikin rashin mutunci ya fara kiran numbobi One , Two , Three , Four , Five , Six , Ser..... Da gudu Al ' Ameen yazo gabanshi , Momy tace me yayi maka ? Babu ruwanki kuma nayi rantsuwa duk wanda yazo kusa dani saina kashe shi..............
Waye yaje ya ɗauko ka ne ? Ashiru ne Al ' Ameen ya bashi ansa , bai sake magana ba yayi gaba Al ' Ameen yabi bayanshi wurin yayi tsit kamar babu kowa yana fara tafiya suka riƙa darewa suna buɗe hanya har ya wuce , saida Dikko ya fita da Al ' Ameen hayaniya taci gaba tashi kowa yana tausayin rayuwar da ta samu Dikko gashi mahaifiyarshi bata da ragowa bare a fahimtar da ita yadda lalurar ɗanta take bata ajiye komai ba sai girman kai wulaƙanci rashin mutunci da masifa dama marar mutunci haka ake masa ana ganin kuskure babu mai gyara masa saidai a barshi yaje can yaji da halinshi.....
Uwar Jiddah kuwa data biyo Momy cewa tayi Maryam ashe ɗanki mahaukaci ne shi yasa kika maƙale saiya auri Hauwa'u ? { Jiddah } da yanzu tana can ƙasar waje tana aure yanzu haka ma takarar gwamna zai tsaya Dikkon ma har nawa yake ? Aure babu wani ci gaba ita ba ciki ba sai haƙuri irin wannan haukan yayi ya riƙemin ɗiya yaita bugu ita ba ƙato ba ? Kai ׳ gaskiya abun baiyi tsari ba kila ma bugun da yayi mata ne yasa take rashin lafiya gaskiya an shiga haƙƙina kinci amanata wallahi saida Hauwa'u tacemin bata zama kwanaki daya bigeta tace saiya saketa kika shiga kika fita ta haƙura ta zauna ashe zalinta ake ci , Momy tace aini ban iya neman asiri ba ita tayi ma kanta karatun ta natsu ta koma nidai shawara na bata kuma ta ɗauka , Maman Jiddah tace tou wallahi bana lamunta ni ban yadda da auren bugu ba waye ma Dikkon ? Waye shi........ ? Murmushi Momy tayi mai ciwo a zuciyarta tace Dikko kuwa kowa ne dan ba sakarai bane ba yasan damarshi , bata sake magana ba ta kwanta , Maman Jiddah kuma wayarta ta ɗauka ta fara kiran Jiddah tana ci gaba da cewa aure babu wani ci gaba har yanzu ko ciki babu ina ma amfanin rayuwar Dikko ɗan iska kawai daya raina mutane.
Bayan Jiddah ta ɗauka tace Hauwa'u ashe Dikko hauka yake mara ɗaura zani ? Magana Jiddah tayi , mahaifiyarta taci gaba da cewa wallahi nasan ba komai bane sai hassadar ganin zaki ci gaba shi yasa Maryam tasa kika auri Dikko da yanzu kina can ƙasar waje kina huta .......... Eh da kema zaki zama matar gwamna ........ Wallahi hassada ce kawai tunda taga ita "ya "yanta basu auri gwamnoni ba shi yasa tayi zalinci ta haɗa aurenki da mahaukacin ɗanta , haka dai taita maganganu Momy kuma bata ce ummm ummmm ba......
Inda yakai Suwaiba yaje yakai Al ' Ameen , kuma wuri ɗaya ya haɗasu babu abinda ya dameshi Suwaiba kuwa sai bacci takeyi kamar jakar data kwana tana wahala , saida Dikko yayi ma Al ' Ameen lullusar fitar hayyaci ya ɗora da cewa idan wani ya sake zuwa ya bishi yaga yadda zaibi ta kanshi da mota kuma ya kashe banza , a wahalce Al ' Ameen yace nasan idan ka kashe ni ko bayan bana raye zaka tuno da maganganu na....
3 ta wuce ya koma gida kuma bai sake tashin Sultana ba haka kuma baiyi bacci ba yana zaune a gefen gadon yana nazarin wasu maganganun da sukayi da Al ' Ameen ,
Al ' Ameen miya haɗaka da Jiddah ne ? Wallahi mai gida ba abinda ya haɗani da ita kawai dai tana aike na ne na samo mata asiri tana san ganin bayanka , kamar ya zata ga bayana ? Saboda makirci da sharri irin nashi saiya kawo mishi zanje can baya wanda shi Dikko daga shi sai Allah sai Jiddah suka san wannan sirri na zance sperm , ya akayi maganar yaje wajen Al ' Ameen da wasu zantuka na rayuwar shi da ita a fanni auratayya ? Me yasa Jiddah ta tona mishi asiri ? Me yasa ta faɗeshi a yanayin da duk duniya ko iyayenshi baya fatar su san yana shiga irin wannan yanayin me yasa ׳............... Kai wannan wace irin mace ce ........... ? Hayaniyar shi ta farkar dani daga bacci , takalmin ƙafarshi ya fara cirewa ranshi a matuƙar ɓace kanshi yaji ya yamutsa daya tuno har kwanciyar da yayi a jikin Jiddah da bai sauka ba sai bayan mintuna 20 duk hadashi ta faɗawa Al ' Ameen wani irin ihu Dikko yayi mai tada hankali , da gudu na sauka daga saman gado jikina yana kyarma dan na firgita kuma ban taɓajin irin ihun ba , fashewa nayi da kuka , ke zo ki kwanta mana , maganar shi ta ƙara gigitani dan haka da gudu na fita daga ɗakin ya biyoni yana cewa karki hau bene An mata ki rufamin asiri , tsayawa nayi nace tou me nayi maka ? Da hannunshi biyu yake nunawa na yanayin lallashi bake bace ba yi haƙuri taho ,
A tsoroce naje wurinshi na riƙe hannunshi ina kallon idonshi , murmushin ƙarfin hali yayi tare da cewa wuce muje ciki idan ina ihu ki daina fita da gudu kinji ? Ni bana san ihun tsoro nakeji , kiyi haƙuri na bari bazan ƙara ba An mata , tou ina kakai m card in nan ?
Cikin murya mai kwantar da hankali yace me zakiyi dashi ne ? Wata ɗauka da nayi zan goge , dalili ? Nidai ka bani , ni wallahi bansan inda na ajiyeshi ba , wani abu ya faru ne ? Ey , tou meye ne ? Muje ɗaki , hannu na yaja muka koma ciki gaba ɗayanmu toilet muka shiga ni na wanke fuskata da bakina na fito , duk daren nan saida Dikko yayi wanka shi bansan abinda yasa ya mada rayuwarshi ta dare ba yanayin abu da dare kamar rana , bayan ya fito ya saka kayan jersey ya ɗauki wayarshi ya shiga duniya yace ina saurarenki.....
Gefen gado na zauna shi kuma yana zaune gefen madubi , da farko dai ina baka haƙuri akan maganar da zanyi , baimin magana ba hankalinshi yana kan wayarshi , naci gaba da cewa can² baya na haɗu da wani mutumi muka shiga har ƙallar rayuwa dashi amma babu wani abu daya shiga tsakani , yadda abun ya faru na faɗa masa kaf da zancen maganar recording da nayi masamasa ,
Ranar dana fara ganinshi a bacci da zancen ƙwaƙwale ido da yakeyi kuma yake faɗamin kuma ya zama gaske , ganin Al ' Ameen a baccina ranar dana ga Dikko ya rabu biyu daren ɗaurin aurenmu kenan , yace shine ya turomin tsafinsu a auna nauhin idona saboda naci kuɗin su ban biya da idanuwa na ba za'a ɗauramin aure gobe sai su cire idona , a tsarin tsafinsu basa cin idon wacce babu igiyar aure akanta zanyi aure sai aka zo dubani , shine nayi kuka kake tambayata abinda ya faru , ranar da aka kawoni gidanka a ranar nayi mafarki dashi yacemin ya cire ido saura nawa tunda nayi aure....
Abinda yasa har yanzu basu cire idona ba saboda wannan record in da nayi mashi yana so ya tabbatar babu wata sauran hujja a wurina suna so na basu su goge shi , shin idan na goge ko sun goge zasu fita harkata ko kuwa zasu kaini nima kamar yadda suka kai sauran matar aure ne ? Tsoki Dikko yayi ba tare da kalleni ba ya gyara zaman shi yana cewa ƙarya ne , wannan labari tatsuniya ne , a , a Dikko da gaske ne wallahi , An mata banda ƙaryar bacci to me ya kawo Al ' Ameen a mafarkinki ?
Yacemin Al ' Ameen ya munafurce shi kuma wallahi zai tona masa asiri Al ' Ameen shine jagorar matsalar rayuwarka , duk haukan da kakeyi shine , ni banasan wannan maganar karki sakemin irinta , Dikko wallahi har inda aka binne asirin ya nunamin , cikin hayaniya yace da Allah bana san iskanci in banda iskanci ya za'ayi Al ' Ameen ni yayi min wani abu ? Zan sake magana ya dakamin tsawa yana cewa kwanta kiyi bacci idan na sake jin surutunki saina zaneki , Dik..... Ki rufemin baki karki ɓatamin rai a daren nan............. Ya ƙarasa yana rufe idanuwanshi.
A hankali na koma na kwanta tare da fashewa da kuka nace na rantse da Allah da gaske ne , kuma a ido biyu zan iya gane wurin , ka tsaya na faɗa maka abinda yace Al ' Ameen ɗin yayi masa mana , ke.................. Ki rufemin baki....... Idan kika sake magana saina kashe ki......
Shiru nayi ban sake ko tari ba nabi shi da kallo , dakamin tsawa yayi cewa daina kallona ki juya can ki kalli bango , banyi magana ba na juya naci gaba kallon bango kamar yadda yace , har aka kira sallah asuba ban sake magana ba kuma ban koma bacci ba saishi dake ta ansa kiran waya , ana kiran sallah asuba kuma ya maida wayar jirgi ya sauya kayan jikinshi zuwa jallabiya ya fita masallaci.
Abinda ya faru a baccina kamar yadda na saba mafarki dashi lokaci bayan lokaci , ina ganinsa a wasu kwanaki na baccina wanda bana iya ganewa ko tuna lokacin da yake zuwa a baccin saboda ba kullum yake zuwa ba kuma ranakun zuwan nashi daban ne ,
Ranar da naga sunayin kokowa da Al ' Ameen , wata ranar kuma da yazo a baccina kamar yadda ya saba yace mi yasa ban goge ba ? Nace masa Dikko bai bani ba , shine yacemin inyi alƙawari na samo mishi record Al ' Ameen yaci amanarshi ya yadda dashi amma ya zalinci rayuwarshi , ga yadda ya faɗamin dai , kuma yace abinda yasa zai tonawa Al ' Ameen asiri yana so Dikko ya ƙoreshi daga ƙasanshi shima saiya tagayyara kamar yadda shi mai ƙwaƙwale idon ya tagayyara.......
Dani da Al ' Ameen dukanmu iyayenmu ne sukayi aiki a gidansu Dikko , mahaifinshi Dikko mutumin kirki ne mutum mai mutunci da mutunta kowa kuma yana da alkairi da san kyautatawa wanda bashi da hali haka kuma bashi da ƙyanƙyamin talakawa , lokacin da iyayenmu suke aiki a gidansu shi mahaifin Dikko lokacin yana da mata 4 cas mahaifiyar Dikko itace babba amma yayi aure² dan samun ɗa namiji ,
Dan ya tashi hankalin rashin samun namiji tun kafin haihuwa tayi nisa , haihuwar Maryam 3 a wancan lokacin kullum mata take haihuwa dan haka kawai Dady yaci gaba da aure saida ya tara huɗu gaba ɗaya , ganin haka yasa ita kuma ta dakata da haihuwa kwata² saboda baƙin ciki da kishi , ta tashi hankalin miji ta hanashi zaman lafiya da kwanciyar hankali dan duk yadda zan kwatanta fitinarta ta zarce wurin , ga rashin san zaman lafiya ga wulaƙanci idan ta fara fitina babu wanda ya iya yasa tayi shiru , dan haka itace ta ɓata kaf gidan ya haukace aka shiga sahun kishi da jefe²n juna , a lokacin da take ita ɗaya bata san "yan uwan Dady dan ita Allah yayi mata tsantsani da ƙyanƙyami idan dai ku masu kuɗi ne ko "yan gayu tou kune abokan tafiyarta dan ita "yar gayu ce ajin farko da ƙarshe bata tarayya da mutumin data fi wayewa cewa takeyi zai kidahumar da ita , tasan hannunta kuma tasan abinda take dan duk matan da Dady ya auro babu kamar ta , ga kyau ga gayu ga aji idan ta raina ka ko ƙofar ɗakinta baka taka mata bata da mutunci yadda baki tunani , idan tana sanka kawai tana sanka idan bata sanka bata sanka........
Itace babba kuma itace ta ɓata gidan , ita bata iya neman asiri ba amma tasan logo da kissa na duƙunƙune kan namiji shi yasa Dady ya fifita ta akan kowa sai suke ganin kamar asiri take masa dan haka suka tisota gaba jifa , nan fa gasar haihu ya tashi dan haka akaci gaba da watso ma Dady "ya "ya mata , ganin buƙatarshi bata biya ba ya fara tarawa da ebewa , amma ita Maryam duk rashin kunyarta ba'a taɓa jaraba mata bulalar saki ba.
Ganin ana haihuwa yasa itama taci gaba da haihuwa , tana komawa haihuwa Allah ya bata Dikko , tunda ta haifi Dikko su kuma suka tasashi gaba yadda basu haifa ba babu wacce ta isa itama tayi namiji sun yadda su kashe shi a tashi a tutar babu...
A kanshi aka samu namiji kuma har yau ba'a sake samu ba , bayan Dikko ya girma kuma aka riƙa harin rayuwarshi a waje idan ya fita shine dalilin da yasa aka haɗashi dasu Ashiru , shi kuma Al ' Ameen da ƙarfin bala'e ya shiga ya fita yake tuƙa Dikko kuma bansan abinda ya rabasu ba a halin yanzu amma dai nasan basu tare ya koma tafiya da zugar yaranshi.
Abinda yayi min shine , dani dashi gaba ɗayanmu munyi aure wurin zama da duk hidimar da kika sani anayi a aure Dikko ne yayi mana gaba ɗayanmu , tunda nayi aure na fita daga ƙarƙashin shi domin a lokacin Al ' Ameen ya zuƙeni daga jikin mai gida , amma duk da haka na yadda da Al ' Ameen sosai ganin iyayena da nashi sun tashi wurin aiki ɗaya kuma gaba ɗayanmu a gidan muke zaune , na yadda da Al ' Ameen jinsa nake kamar a ciki ɗaya muka fita , ashe ni mugunta ta yakeyi mugune azzalimi ne ya yaudareni anan inda nake tsaye a nan aka binne sihirin da akayi ma mai gida , abinda yayi min shine zaici gaba da faɗamin ne Dikko ya tasheni yacemin wai in tashi ya dawo , tabbas zan gane wurin amma ta ina zanbi inje wurin ? Ina Dikko ya ajiye m card in nan wai ? Har ya dawo daga masallaci ban tashi ba a yadda ya barni ba , kuma banyi sallah ba , cire jallabiyar shi yayi ya maida kayan daya cire ya kwanta.
Shin wai wannan mafarkin da gaske ne ko kuwa tatsuniya ne kamar yadda Dikko yace , tashi nayi naje nayi alwallah nazo na kabbara sallah , shi kuma Dikko bayan ya kwanta yana tunanin maganar Sultana da zancen Sadiyya sai kuma maganar Suwaiba da tace masa ya tattaro kaf yaranshi duk wanda yasan ya taɓa zama a ƙasanshi ko basa tare yazo dashi , ita kuma Sadiyya tace masa a cikin yaranshi wanda ya kasheta yake , An mata kuma tace masa Al ' Ameen , shin wai me ye gaskiyar lamarin nan ,
Gaishe shi nayi bayan na gama sallah , bai ansa gaisuwar ba kuma bai kalleni ba , nima ban sake gaishe shi ba nayi kwanciyata a wurin , bayan wani lokaci yayi tsoki tare da saukowa daga saman gadon , canja kaya yayi ya ɗauki makulin mota ya fita , tashi nayi na koma saman gadon ina cewa aikin banza adashen tusa.....
Kai tsaye wurin da ya ajiye Suwaiba da Al ' Ameen ya nufa.........
04/12/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 86
Ya za'ayi Al ' Ameen ni yayi min wani abu ? Tou me mutumin ya faɗa mata ? Ina yasan Al ' Ameen ? Me yasa ni kuma Al ' Ameen zai zama jagorar matsalata ne bayan dashi ake nemamin magani , mi yasa dole sa a mafarki zai bawa An mata labari ? Ƙarar wayarshi ya dakatar dashi daga tunanin daya tafi , Momy ya faɗa tare da ɗaukar wayar suka gaisa , Dikko kana ina ne ? Ina nan bisa titi , ina zakaje a safiyar nan ne ? Zanje gida , wane gidan ? G R A , daga ina kake ne ? Goruba , daina tambayar tayi cewa Dikko kazo ina neman ka yanzu²n nan , cike da damuwa yace me kuma akayi miki ne ? Dikko nidai tafiyata zanyi na gaji da zaman haƙuri , kuma fa bata iya tafiya ko ina ta bar Dady , Momy kiyi haƙuri dan Allah,
Ni bazanyi ba , tunda ka tafi da Al ' Ameen jiya Bilki ta hana gidan nan zaman lafiya ta turo "ya "yanta sai rashin kunya sukemin dan taga ba kowa cikin yara duk su Nabeela suna wurin Jiddah ko nice zan fita inyi faɗa da Yara ne ? Nidai nasan nafi ƙarfin Bilki daga ciki har waje wani iskanci saida tasa yara suyishi , cike da damuwa Dikko yace Momy dan girman Allah kiyi haƙuri , wallahi bazanyi ba saidai idan Bilki ta koma uwarka sai in ƙaleka dama kwanaki dana faɗa maka ta zageni kace zakayi mata magana bakayi mata ba sakaran banza mara kishin uwarshi tana faɗin haka ta tsinke kiran.
Innalillahi wa'inna ilahir raji'un ya faɗa tare da samun gefen titi yayi parking , wayar Ashiru ya fara kira , Ashiru kuwa yanaji yana gani yaƙi ɗauka dan Umar ya bashi labarin abinda mai gida yayi a jiya kuma dama yasan tunda ya ɗauko Al ' Ameen saiya fuskanci matsala tou shi ya za'ayi ma yace ma Dady baisan inda Al ' Ameen yake ba taya zaice kuma bazai ɗauko shi ba ?
Yana ajiye wayar zai tashi motar text in Ashiru ya shigo , kayi haƙuri mai gida Dady yasa na ɗaukoshi kuma na kira wayarka a kashe ka gafarceni nasan ban kyauta ba , tsoki Dikko yayi tare da ajiye wayar saida ya fara tafiya ya fara kiran wayar Dady.
Cike da fargaba ya ɗauki wayar yace Babana lafiya ? Dan shi a tunanin Dady ba lafiya shi yasa Dikko ya kirashi a safiyar nan , Dady wai me nayi maka ne ? Babana ba komai , tou me yasa za'a hanani na zauna lafiya ne ? Da sauri Dady ya tashi daga kwanciyar da yake yace me akayi maka ne ? Horn Dikko ya danne ɓiyyyyy , Dady yace a , a Babana , Dady kawai zan mutu na huta , yi haƙuri Babana² dan Allah tashi tsaye Dady yayi cikin tashin hankali yace wai ina damuwar take ne ? Me yasa kasa aka taho da Al ' Ameen ne ? Yadda sukayi da Bilki ya faɗa masa , kashe waya Dikko yayo bai sake magana ba ya ajiye a gefe , me ne ne tsakanin Al ' Ameen da matar uba wai ?
Ko dan yace zaice ya kama Al ' Ameen a ɗakinta ne ? Tou kodai ? Karka yi zargi zuciyarshi ta faɗa masa , to me ya shafeta da lamarin Al ' Ameen haka da yawa ? Dama kwanaki daya dokeshi itace tayi video ta turawa Dady , yanzu kuma shine tasa akaje aka taho dashi ko ? Maganar Sadiyya ta dawo mishi a zuciyarshi an haɗa kai dashi da matan uba an maidakai lusarin namiji , ni kuma yayi nasara akaina yakai min rayuwata ƙarshe , ka tattaro kaf yaranka har wanda suka daina maka aiki ka kawosu idan na ganshi zan ganeshi { Suwaiba } , wallahi mai gida ba abinda ya haɗani da ita kawai dai tana aike na ne na samo mata asiri tana san ganin bayanka , { Al ' Ameen } , a , a Dikko da gaske ne wallahi , { An mata } , banda ƙaryar bacci to me ya kawo Al ' Ameen a mafarkinki ? Dady kuwa sai kiran wayar Dikko yakeyi amma yaƙi ɗauka dan haka ya kira Momy yace mata yasan itace ta ɓatawa Babanshi rai har so nawa yace su daina saka "ya "ya a damuwarsu basa bari , me yasa suke san ɓata mishi gida ? Kullum yana ƙoƙarin haɗawa su kuma suna rusawa ? Wai me yasa sukeyin abu na rashin tunani haka ? Tou wallahi tayi kuka da kanta dan zai mata rashin mutunci idan wani abu ya sami Babanshi.
Da wani irin ihu ya shiga inda ƙannen shi suke kaf dan duk irin wannan lokacin basa bacci zasu zauna sai bayan 6:45 su tashi idan da makaranta kenan haka wannan tsarin yake ko bakya sallah duk idan akayi sallah kaf "yan gidan sai sun haɗu a wurin amma "ya "ya ƙananansu da manyansu idan dai ɗan da Dady ya haifa ne harshi Dikkon , kuma ko aure kikayi idan dai kika zo gida sai kinyi wannan zaman tunin duniya haka suke haɗuwa kuma ba addu'a akeyi ba , ba karatu akeyi ba zasu haɗu dai kawai su zauna a wurin suyi fira ne , idan kuma ranar da babu makaranta sai 7 suke tashi , saida ya zane kowa a cikinsu duka bana wasa ba amma ƙannenshi bai daki yayyenshi ba kuma babu wanda baiji ma ciwo a cikinsu ba ya ɗora da cewa daga yau idan wata ta sake shiga cikin faɗan iyaye saiyabi ta kanta da mota ya wuce "yan iska marasa kunya , dakel aka fito dashi daga wurin yana cewa suma su Nabeelar duk saiya ci mutuncinsu wallahi ba babba ba yaro duk wani ɗan daya sake shigar ma uwarshi faɗa a gidan nan shine zan kawo ƙarshen rayuwarshi............
Sai kuka sukeyi , shi kuma ƙwacewa yayi ya nufi ɗakinsu , a falo ya samu Momy ta kashe saman kujera ta murza wani irin ɗaurin kallabi mai burgewa dan fita zatayi zuwa wurin Dady parking in da Dikko yayi yasa ta koma ta zauna tana ta gunewa , kusa da ita ya zauna ya riƙe duka hannayenta yace Momy dan Allah ki daina damuwa , nuna kanshi yayi da hannu ɗaya ɗayan kuma yana riƙe da hannuwanta yaci gaba da cewa idan ina nunfashi babu wanda zai isa yasa miki damuwa kuma babu inda zakije mu muna tare dake nima ina tare dake Mamana Dady nawa ne shima yana tare da duk abinda nake so kiyi haƙuri baza a sake miki abinda zaisa kiji damuwa ba , cikin sanyin murya tace Dikko ya za'ayi yara su riƙamin rashin kunya idan nayi magana sai ace banda haƙuri , ba tun jiya na faɗawa Dadyn naku ba yace wai bana san zaman lafiya , yi haƙuri Momy fushi yasa ya faɗi haka , me yasa baiyi fushi ya faɗawa Bilki ba saini mareniyar wayanshi ɓacin rai yasa Momy taita maganganu Dikko dai tsareta yayi da ido bai sake magana ba , wato ita dai mace duk shekarunta idan tayi wani abun saidai ace Allah ya sawaƙe ,
A mota ya ɗauketa suka tafi wurin Dady , shima ranshi yayi mishi zafi sai faɗa yakeyi yana kuma ƙara ɗora laifin a wurin Momy itace ta fara koyawa yaranta rashin mutunci kuma ai itace ta fara nuna rashin san zaman lafiya a matsayinta na babba , murmushin ƙasaita tayi tace ma Dikko yaje ya jirata falonta tana zuwa , saida ya gaisa da ya fita , Dady kuwa yabi Dikko da kallon soyayya harya fita , ×××××××.
Tunda Dikko ya fita Hafsa ke kiran wayata naƙi ɗauka ta dameni sosai dan haka na ɗauka bayan mun gaisa tacemin wai na fasa zuwa ne ? Ina ne na fasa zuwa ? DK bai faɗa miki rasuwa ba ? Waye ya rasu ne ? Kakar Babanku duk "yan gidanku suna can yau ake addu'ar 3 muma yau zamuje , wace ce kuma Kakar Babanmu ? Wacce ta haifi Maman Babanku , ke ina kika santa ne ? Kaka Sahura ta faɗa man inda take ni naje na gano wurin nakai "yan gidanku , ranar da mukaje na dawo na barosu can a ranar ta rasu , dan lokacin da zamu tafi na kiraki DK ya ɗauka yace baki lafiya sai muka tafi data rasu kuma na kirashi yace idan kin samu sauƙi zai kawoki , tou Allah ya jiƙanta na faɗa a tsiwace , dan Allah kiyi ƙoƙari kuje yau kuma duk "yan uwa sun haɗu kiga dangi kema , shi yasan wurin ne ? Ey nayi masa kwatance ranar dana kirashi na faɗa masa rasuwar , { wato ranar da aka sallamoni daga asibiti kenan } tou me yasa bai faɗamin ba , zan gani ina faɗin haka na tsinke kiran ,
Gaskiya fa ya kamata naje ko dan nuna soyayya wa kabarin Babana , Allah ya jiƙanka Babana yasa ka huta nayi rashin ka a duniyar nan shi kenan ka tafi inda bazan sake ganinka ba har abadan duniya , ka tafi tafiyar da babu dawowa shikenan ka tafi ka barni........, dole naje wurin ahalinka ko dan jaddada soyayya a gareka Baba na gari , kai sarkin fushi zakaje ko bazaka ba ne ni naje ? A dai² lokacin dana fara kiranshi , saida ta tsinke bai ɗauka ba , sake kiranshi nayi itama saida ta kusa tsinkewa ya ɗauka da abinda bana so wai ya akayi ne ? Dikko koma ya akayi ai zakaji yanzu , dan yadda akayin ne yasa na kiraka , ke karki min rashin kunya kinji , ba wannan ba ni zakaje ko ka fasa zuwa ne ? Ina ? Ba Hafsa ta faɗa maka rasuwa ba shine sai kace saina samu sauƙi bayan ni lafiyata qalau , ni bazanje ba sai kin dawo , tou babu damuwa ngode , ina faɗin haka na tsinke kiran , wayar Inna na kira , cikin hukuncin ubangiji kuma ta shiga amma bata ɗauka ba , ci gaba nayi da kira taƙi ɗauka ,
Dikko na sake kira , bayan ya ɗauka yace ya akayi ne ? Dikko na kira Inna kuma ta shiga amma bata ɗauka ba , da kyau , daga haka bai sake cewa wani abu ba , kaji , naji , tou kace wani abu mana , ai shine nace nace hakan da kyau , nidai baka so na , baka damuwa da abinda yake damuna , ni bansan abinda yasa kake min haka ba na faɗa cikin hayaniya ina kuka , duk saida na safke mai isata sannan yace tou yi haƙuri An mata gani nan zuwa zan miki abinda kike so , tou me yasa ni kake min haka ko ka daina so na ne ? Ina sanki mana tayama zaki fara wannan tunanin ? Bana fata kuma bana tunanin akwai ranar da zanji sanki ya ragu a zuciyata , kiyi haƙuri ki bini da addu'a har ubangiji ya yaye min damuwata dana tuno da abinda yake damuna sai inji raina yana ɓaci shi yasa a ko wane lokaci nake miki magana hayaniya² , kana ina yanzu ? Ina nan inajiran Momy data sallameni zanzo wurinki ai haka yayi miki ko ? Ey , to baki ce kin gode ba , murmushi nayi tare da cewa godiya nake mutumina , yawwa jarumata ngode yana faɗin haka ya tsinke kiran , bin wayarshi yayi da kallo yace mata kenan , ita ba abinda ya dameta shin ina lafiya ? Ko ina cikin yanayin fushi me ya sameni bayan na fito babu ya hanya ba komai itadai burinta ayi mata dai² , zan faɗa mata ba'a kiran miji kai tsaye a faɗa masa damuwa sai an tabbatar da yana cikin natsuwa.
Momy ta daɗe bata dawo ba , har Ashiru ya iso gidan danshi zai maida Maman Jiddah tunda Al ' Ameen bashi nan kuma tsarin nan Momy ce ta tsarashi shi kwata² Ashiru baisan Dikko yana nan ba , ita kuma Maman Jiddah tana gama shirinta ta fito falo dan Momy tayi mata waya cewa wanda zai kaita ya iso itama tana zuwa yanzu , shine tayo parking ta bayyana a falon , cikin girmamawa da mutuntawa Dikko ya gaishe da surukarshi....
Ba yabo ba fallasa ta ansa tana ta riƙe fuska , ko inda take bai sake kallo ba , ita kuma taci gaba da cunkusawa cikinta abinda ta samu an ajiye mata dan karin safe tunda zata ibi hanya ko kunyar sarakuta babu , Dikko kuma fita yayi ya koma mota yana jiran Momy , yana zama yaga Ashiru yasha ta baya da gudu , tsoki yayi tare da kallon agogon jikin waya 8:39am kuma har yanzu Momy bata fito ba shawara ya yanke kawai ya fara ganin Jiddah kuma suma su Nabeela ya zanesu kamar yadda ya zane "yan uwansu zaije ya dawo kafin ta gama ta fito , tashin mota yayi ya nufi gidanshi....
Yana fita Momy ta iso taga babu Dikko kawai ya wani ɓace abunshi , Momy kuwa tana shiga wuri ta samu ta zauna tana ma "yar uwarta magana , amma ke dake gidanki idan kin tanka tou Maman Jiddah tayi magana sai wani cika take tana batsewa , Momy taji ba daɗi amma ta haƙura ta kanne dan abu na "yan uwan taka dole sai an haɗa da haƙuri da kuma kai zuciya nesa , data tashi tafiya duk abinda Momy ta bata cewa tayi ita ba baƙuwar arziƙi bace ba tafi ƙarfin ita ta bata wani abu ta ansa ta riƙe kila zasuyi mata amfani wurin nemawa Dikko rubutun danga na , Momy tace wane irin rubutun dangana kuma ? Maryam gaskiya ni na kashe wannan auren , cikin tashin hankali Momy tace Yaya don girman Allah kiyi haƙuri wai miye matsalar ne ? Kuɗi , banbancin kuɗi ne ke naki ɗan gwamna ne ni kuma gwamnan zata aura gaba ɗaya , zaɓe yana tunkarowa bana tunanin ku zaku sake zarcewa siyasa zata wurgar daku a can tsohon gidanku gidan gwamnati kuwa zai zama na masu rabo ,
Momy tace mu kenan masu rabo ni inaji a jikina munci kuma sai mun sake wannan zaman darajar manzan Allah S. A. W gidan gwamnati sai mun maimaitashi , maganar kuɗi kuma ba damuwar Dikko bane ba saboda shi basu ne gaban shi ba yana dasu yadda tunaninki da ƙwalwarki basu ɗaukar misali dan dayabi izzar kuɗi da mulki wallahi Jiddah bata kai mace ba a wurinshi , Maman Jiddah tace aiko ke kinsan Jiddah mace ce hada gyara gwamna da kanshi yake santa gwamna fa ? Shin ke kin raina gwamnati ko ? Ban raina gwamnati ba amma nima na san nawan tunda ya fara saiya taka matakin da bakya tunani , da haukan zai taka matakin da har ni bana tunani ? Momy tace ba mahaukaci kuma ba hauka Dikko duniya , zamani ɗaya tak a ƙarni matashi mai sa'ar rayuwa , yaro da kuɗi abokin tafiyar manya , mahaukaci da kuɗi kuma mai maihankali babu , gwamnan da kike tunanin kashe auren Jiddah saboda shi tun kafin na ganshi nasan waye shi na tabbata duk kuɗinshi shi 30 baya Dikko ɗaya , yadda baki tunani Dikko ya kafu shi kanshi ubanshi alfahari yakeyi dashi yace yasan ko bayan baya raye zai tallafi "yan uwanshi shi yasa ya dage saida ya tabbatar ya gina Dikko sosai , amma duk da haka shi kuɗi basu ne gabanshi ba shi yasa yake rabar dasu kamar hauka , abinda yasa na kafe sai Dikko ya auri Jiddah dan naga wasu sunci ma bare nawa bana san ya baku² shi yasa na haɗa auren Jiddah dashi , dan nasan Dikko bashi da mutunci idan nice yau gobe bana nan na gina ku ne ku "yan uwana ko bayan bana raye arziƙin Dikko bazai muku wahalar ci ba saboda akwai Jiddah , amma idan har kika kashe auren nan kuka bar bare kuka hana zuminci wallahi gidan Dikko raɓe zaku zama , kuna iya zuwa ma tace muku baya nan kuma yana nan ta hanaku ganinshi , kallon banza ko magana mara daɗi kukayi ma matarshi tabbas nasan saiya ya taka muku burki ko kuma ya ɗauki matakin hanaku zuwa gidanshi ba abu bane mai wahala a wurinshi , ni bana miki hassada kuma bana miki baƙin ciki dan "yarki zata zama matar gwamna shawara na baki dai dan kece ya kamata tun yanzu ki daina tunanin kashe auren , a sanyaye tace kuma kece zaki anshi kuɗin nan ki fara nemawa "yarki rubutun dangana tun yanzu , ɗa ɗaya tak ragamar mata idan dai harya kafa soyayyarshi a zuciyar Jiddah tou sorryn ku ina jajanta muku domin ni kaina bansan a ina Dikko ya gaji zuciya ba , da zaran ya yanke hukunci tou fa ko kanshi baya saurara , karki raba domin yadda mukayi zaman nan zamu sake maimaitashi idan har kika tafi da Jiddah wallahi kuma Dikko yasan dalili tou fa tabbas yadda kika ga kiyi sabon rubutu a saman allo bai bushe ba ki tsomashi ruwa ba tare da kin murza ba rubutun zai sauka to haka Jiddah zata wanke a cikin zuciyarshi ko matalwa batayi , shawara ya rage naki neman rubutun dangana da mafita yana wurinki.....
Tana faɗin haka ta wuce ciki abunta , Maman Jiddah kuwa fita tayi dan Ashiru ya fitar da duk wani abu nata , haka ta fita waje taita tata ruwan rashin mutunci wai Maryam tana mata hassada mai takarar gwamna yana san "yarta take jin zafi , kurar Momy ta riga tayi kuka shi yasa kowa yake ganin Momy bata kyauta ba abu har ga "yan uwanta ashe ba'a kishi ba har "yan uwanta bata raga musu ba , saida ta gaji da tonon sililinta tayi ta tona musu asiri dan wasu basu iya riƙe ɓacin rai ba idan suna fushi sai su manta da abinda gaba zaiyi su kulle idanuwa suyi ta wulaƙanci na rashin lissafi , ko a mota haka ta ci gaba wulaƙanci su "yan gadon rashin mutunci , duk yadda Ashiru yaso ya nuna mata waye Dikko idonta ya rufe ita mai takarar gwamna kawai kuma saita kashe auren , da ɓacin rai suka isa G R A lokacin Dikko harya zane su Nabeela suma ya farfasa musu jiki ya wuce wurinsu Al ' Ameen.
Haka ta tisa ƙeyar Jiddah hada Mardiyya suka kama hanyar Kaduna , Dikko baisan wainar da ake toyawa ba , Momy kuwa tayi kukan baƙin ciki bata nunanin idan bata raye wannan karuwar zata bar Dikko yayi zuminci da "yan uwanshi , dole a sake nema ma Dikko wani auren a cikin familyn Dadynshi......
Lokacin da Dikko ya isa Al ' Ameen ya dawo kuma ya shaƙe Suwaiba tana ta halbe²n mutuwa , halbi ɗaya Dikko yayi mishi a haƙarƙari ya sake somewa , dakel Suwaiba ta nuna Al ' Ameen tace shine , idan baka yadda ba kuma ka tambayi Mustapha zai maka bayanin komai , wane Mustapha ? Mustaphan daka sani kuma saida ya zalinceshi ya munafurce shi yaci zalinshi sos.... Daga haka ta ɗauke Dikko yasa aka tafi da ita asibiti kuma a tsareta , Al ' Ameen kuma bazai dakeshi ba saiya dawo.....
Saida ya sake komawa ta gidansu ya tafi da abinda zasuyi kalaci kuma baije wurin Momy ba , sai 10:15am ya isa gida , lokacin harna shirya , bafa inda zakije yarinya , haba ? Ummm , to me yasa ? Bai sake magana ya zauna a gefen gado sannan yace An mata wai me mutumin cikin bacci yake ce miki ne ? Nima bana san wannan tatsuniyar , to wane iri ne ? Na manta , ke.............. Bana san iskanci ni zaki faɗamin kin manta................. Cikin ɗaga murya da hayaniya ya faɗa , a tsorace nace kamarshi biyu ce duk na faɗa masa sifofinshi dana sani , tashi yayi tare da kwantar dani saman gado yace me yace miki Al ' Ameen yayi mishi ne ? Bai faɗamin ba ka tashe ni daga bacci , danne ni yayi ta ƙarfi yace koma bacci ki tambayoshi abinda Al ' Ameen yayi mishi.................. , kyarma jikina ya farayi cikin kuka nace ai bazaizo ba ranakun zuwanshi daban ne a sati sau biyu yake zuwamin kuma ni bansan wace rana da wace rana bace ba , ke............... Kiyi bacci ko in kashe ki........ Fashewa nayi da kuka nace Dikko ka ƙyaleni don Allah , zaro ido yayi cikin ɓacin rai yace bazan ƙyaleki ba aradu sai kinyi bacci.
Dikko dan Allah , An mata dan Allah , mintuna 30 na baki kiyi bacci kizomin da duk wannan ansoshin , me yasa baya zuwa sai a bacci ? Me yasa baizo wurina ba sai wurinki ? Me Al ' Ameen yayi mishi zai tona masa asiri ? Me yasa yake san ki goge recording ? Me yasa yake kwakwale ido ? Me yasa basu cire naki ba ya kuma nuna miki hanya ta yadda zaki gane zuwa inda kika ce sun binne tsafinsu , me ne ne tsakanin Al ' Ameen da Aunty a cikin mintuna 30 idan kuma kika tashi babu wani bayani zan kashe ki kema kin zama munafukata kenan gawarki zan jefar da ita a cikin ruwa kadojina su cinyeki banza kawai dake , kafin in irga 10 kinyi bacci kafin na irga 200 kin tashi kuma zaki bani ansar duk wannan tambayoyin dana aikeki a wurinshi ki samomin......
Fara kiran nombobi ya farayi tuni har na saki fitsari dan nasan wallahi bazai zo ba , wani irin firgitaccen mari ya yankamin har kin isa kiyimin fitsari a saman gado ? Ni zaki ɓatawa ɗaki ? Da duka hannayena na riƙe kumatuna na runtse idona dan bana san kallon Dikko a irin wannan yanayin , shaƙemin wuya yayi yace me yasa kikayi min fitsari a saman gado ? Saina kashe ki na gano ki kema munafuka ta ce ashe , dama kince min saikin ɗauki fansa akaina shine kika zubar da ciki dama ko ? Duk yana cikin ɗaukar fansa , zuwa wurin Yazeed shima ɗaukar fansa ne , yanzu kuma kin ɗaukeni mahaukaci dake za'a haɗa kai ayi min asiri shine zaki rainamin wayau wai a cikin bacci kike gani dan kin ɗaukeni kidahumi ko ? Tou saina kashe ki..............
Ihu na farayi amma ya riƙemin maƙoshi na fara kakari ina halbe² Dikko yana cewa saina kashe ki tunda kema munafuka ce na tsaneki Sultanar banza Sultanar wofi , faɗowa nayi daga saman gado ni na rigashi zuwa ƙasa daga saman gadon ya ziro hannunshi ya riƙeni Allah ya bani sa'a na tashi da gudu nayi waje ya biyoni yana ihu mai tada hankali , sulɓewa nayi a ƙofar fita falo , wata irin zamiya ya kawo ya riƙeni na tashi da gudu , wuƙa ya ɗauka a saman firij ya jefeni da ita saida ta caki bayana ta sauka ƙasa , hannuna na miƙa ta baya na riƙe wurin , da gudu na gangare falon ƙasa kamar biri ya sauko ta sama ya rigani bayyana a cikin palon , sai ihu yakeyi yana faɗin saina kashe ki........... Da gudu na koma sama ya sake biyoni yana cewa bana sanki na tsaneki kuma saina kashe ki , tunanin yadda zanyi na fita na rufeshi nakeyi dan idan harna fita waje haka zai bini yana ihu , tausayin Dikko ya kamani sosai kuma na rasa yadda zanyi na fita dan ta ko ina ya riƙe hanya , tsayawa nayi tare da durƙusawa na duƙar da kaina ƙasa na rufe idona cikin kuka nace tou gani na tsaya idan dai har mutuwata zaisa kayi farin ciki na baka fansar raina ka kashe ni ,
Wani irin halbi yakai min saida nayi baya suuuuuu nayi ƙundunbala ina birkitowa na tashi da gudu ashe dai da gasken kashe ni zaiyi , saman benen na koma nace zan faɗa in mutu , ai nine zan jefaki da kaina , da gudu na sauka nayi waje kafin yazo naja ƙofar kai............. Saina kashe kaina , nidai bansan yadda akayi ba daga haka........
Fashewa Sultana tayi da wani irin kuka mai tada hankali da gudu mahaifiyarta ta shigo tace kin fara ibadar taki ko ? Cikin kuka tace har abadan duniya bazan daina kukan rashin Dikko ba , ina sanshi ׳ ina ƙaunarka mutumina , saida tasha ihunta harta gode Allah sannan tace Dikko zamani mai zaman kanshi inji Inna , ɗan gayun namiji wayayye ajin farko , mai buɗewar ido da gogewar rayuwa , bazan gaji ba kuma baxan daina kukan rabuwa dakai ba har abadan duniya , saida ta samu natsuwa nace tou ina Jiddah take......... ? Ina Al ' Ameen ? Ina Bello ina Dady ina su Amisty ina labarin sahura , kinyi karatun boko ko kuwa a , a , kin haihu da Dikko ko ah ah ? Dan naji a labarin naki baki min zancen karatu da haihu ba , da kika gudu kika zo gidanku "yan gidan su Dikko sunzo ko kuwa........? Ina Suwaiba ? Ina matar da Mami ta haɗaki da ita wacce ta bawa Suwaiba kwalba ? Ina Mardiyya ? Ina Alajinki ? Ina mutumin dake ƙwaƙwale ido ? An cire asirin ko a , a , Goge hawaye Sultana tayi sannan taci gaba da cewa........
*JAMILA MUSA...*
Mai karatu ina fatan dai ka gane ? Domin farkon labarin zaku kamoshi idan kuka duba ai kunga labari ne bani ce nake faɗa muku ba Sultana ce take bada labarin rayuwatar da Dikko ne , Allah dai yasa kun gane.......
*SULTANA....*
Maman Jiddah suna isa Kaduna da asibiti suka fara saida aka wanke cikin Jiddah tas dan tana ɗauke da ƙaramin cikin Dikko wata3 , Maman Jiddah kuwa bayan ta tabbatar da ciki ya fita ta buga waya ta faɗawa Momy ta zubar da cikin dake jikin Jiddah , hankalin Momy idan yayi dubu ya tashi tayi kuka kamar zatayi hauka taso ace ko cikin ta bari dan idan ka haihu da namiji duk matsayin da yakai da matakin daya taka idan dai kuna da zuri'a ka more mishi , dan duk ranar da aka wayi gari idan Dikko ya ida kicimewa tace ta auri Dikko saima an bata kashin bala'e dan tace tanaji a jikinta Dikko wani babban sa'a ne kuma shi ɗin hatimin nasara ne , idan ta bar cikin ta haihu itace haihuwar zatayi ma rana ba Dikko ba , amma abinda ya faru ya riga da ya faru ,
Dikko kuwa data faɗa masa bai jahilci lamarin ba cewa yayi Allah yasa hakan da tayi shine alkairi a rayuwarshi , kuma ta faɗa masa Maman Jiddah ta tafi da ita akan zata kashe auren shi ta aura mata mai takarar gwamna yace ai wannan ba komai bane ba , idan ita rabonshi ce dasu sake zama idan kuma babu rabo shikenan kawai.
Bayan wani lokaci kuma Maman Jiddah tazo tayi wulaƙancin na ƙarshe saida ta zazzage auren Jiddah hankalinta ya kwanta , da Momy ta kira Dikko akan ya saki Jiddah cewa yayi ai itace ta auro Jiddah , sai kuma ya saketa tazo daga baya idan wani abu ya haɗota da "yan uwanta tace shine yaje ya saketa , ya yadda zai saki Jiddah amma rubutunta ya zama a sama zai saka hannunshi daga ƙasa....
Momy itace ta rubuta saki3 kai tsaye ba tare da tunanin komai ba , ta kuma ɗora da cewa saboda Maman Jiddah ta buƙaci sakin Jiddaah dan zata aura mata mai takarar gwamna , bayan ta gama ta miƙawa Dikko ya saka hannu tare da rubutawa.
_Ni Dikko Umar Dikko na saki matata Jiddah saki 3 , ina mata addu'a Allah ya bata miji na gari wanda yafi ni...._
Tunda Jiddah taga takaddar saki tayi kuka , kamar ranta zai fita dan ita kwata² bata san haka za'ayi ba , uwarta ke cin kuɗin mai takara kuma itace ta tabbatar mishi da zata kaso auren Jiddah ta bashi ita , ita dai Jiddah tasan tana sanshi a da amma tunda aka zo da zance Dikko ta jingineshi a site , bayan auren Jiddah da Dikko ita kuma Maman Jiddah taci gaba da cin kuɗinshi akan zata bashi auren Jiddah ta ci gaba da aske mishi aljihu ta kuma tabbatar mishi da saita kaso auren Jiddah ta bashi ita , shi kuma yaji baƙin cikin kasashi Jiddah da akayi dan haka ya buɗe bakin A T M ya riƙa yayyafa mata ruwan kuɗin , saida aka kaso auren yace baya aurenta shima idan ta ga wani haka zata kashe nashi ta bashi aurenta , kuma ya ƙara da cewa shi babu wata takarar gwamna daya fito yayi haka ne kawai saboda yaga ita mayyar duniya ce ,
Ita kuwa Jiddah haka tayi ta guduwa tana zuwa wurin Dikko kuma haka take tarashi a Abuja , shine ya taka mata burki yace ta daina binshi karta ja mishi sharri , taƙiji taci gaba da binshi yace tou duk ranar daya sake ganinta wurinshi zai kashe ta ne kawai kuma ya kashe banza......
Mardiyya kuwa tana tare da Jiddah amma ba'a gidansu ba itama ta koma gidansu da zama amma suna ƙulle dai tunda ana gari ɗaya , Mardiyya itace take raka Jiddah wurin boka ana ci gaba da neman asiri akan Dikko ya shiga tashin hankali yaji idan baiga Jiddah ba yaji kamar zai mutuwa , idan ta haɗo tsibbunta haka zata zo wurin Momy idan taji Dikko yana gari aita barbaɗe² , Momy kuwa bataji wani komai ba dan ita Allah yasa tana san "yan uwanta , Dikko kuwa ko a ƙwalar rigarshi , itama dai Mardiyya tana ta ƙara gyara nata ƙaimun , amma har yanzu kamar suna tura agwagwa ruwa ne dan Dikko bayajinsu wannan jagwalgwalon sihirin nasu bai zo ba ,
Banda labarin Al ' Ameen haka kuma banda labarin Suwaiba kowa banda labarinshi dan a gidanmu nayi haihuwar farko , na haifi namiji kuma "yan gidansu Dikko sunajin labarin haihuwa suka zo suka ƙwace ɗan wai bazaisha nonon karuwa ba , sunan Dady suka sa mishi { UMAR FARUK } suna kiranshi da Papi , haka Umar ya faɗamin , kuma shine ya bani labarin saukar da Dikko yasa akayimin , ina zuwa makaranta yanzu nayi JSCE kuma tunda naje ban ɗauki position sama da 5 ba , dake kafin na koma saida Inna tayi tsayuwar arfa wurin bani taimako da karatu na musamman a gida , ina js2 nayi jarabawa da "yan js3 , Inna ta siyamin mota nake zuwa makaranta da ita ,
Sahura ta rasu , kuma dani da Inna munje gaisuwa , kuma naje wurin ahalin Babana a can ƙauye dani da Inna , kuɗin gado basu bani ba sun haɗa gaba ɗaya sun cinye , Dady dai shima rayuwar sai a hankali , Bello kuwa yana can yana fama da rashin lafiya ni banje ba kuma bansan abinda yake damunshi ba ,
Tou yanzu ina Dikko ya mutu ko yana raye................?
Wani irin ihu Sultana ta darkaka daga haka ta ɗauke ashe ba'a tambayarta Dikko ni kuma na tambayeta.......!!!
06/12/2019 👇🏻
*JAMILA MUSA...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 87
*_Wallahi idan kunji haushi na da gangan , inaji dai kun manta yadda labarin nan yake tun farko , masu cewa na gaji na yanke labari kuma dai matsalarku , kamar yadda na faɗa yadda ta tsara abunta dole haka zanyi idan ya miki a haka kibi idan bai miki ba ki barshi babu lallai fa ba dole dan anyi ciwo an warke ai ba'a ba mutuwa haushi ba , nabi tsakar dare nabi rana nayi safiya nayi marece , naji daɗi ko ba daɗi nabi dai ina muku dan kuyi farin ciki amma jiya kawai dan rashin adalci ni hada masu gayamin kalami mara daɗi hmmm aiko idan har kukaimin haka ni baku kyauta min ba kuma ƙullu yaci amanar koko...._*
Inna ce ta shigo cikin ɗakin da sauri inda Sultana take taje ta riƙeta tana shafa mata ruwa take min magana cewa Jamila da Allah kiyi haƙuri da labarin nan haka nan ki tafi sai wani lokaci , Inna ki gafarceni don girman Allah ki barni takai min ƙarshe , Inna tace a , a kije kawai , zan sake magana ta dakatar dani ta hanyar ɗagamin hannu , jiki a sanyaye na fara ƙoƙarin sauka daga saman gadon a dai² lokacin da Sultana ta buɗe idonta dan dawowa daga sumar da tayi wanda ta dawo ta dalilin ruwan da Inna ta shafa mata , cikin kuka tace Inna barta na faɗa mata , Inna tace to karki sakemin wani koke² na faɗa miki , insha Allah Inna , fita Innar tayi ni kuma na koma na zauna ita kuma taci gaba......
Dikko bai mutu ba kuma bai sakeni ba , da na barshi rufe a palo ni bansan abinda ya faru dashi ba tunda ni banyi waya dashi ba kuma ban ganshi ido² ba.
Dikko na kira Inna kuma ta shiga amma bata ɗauka ba , da kyau , daga haka bai sake cewa wani abu ba , kaji , naji , tou kace wani abu mana , ai shine nace hakan da kyau , nidai baka so na , baka damuwa da abinda yake damuna , ni bansan abinda yasa kake min haka ba na faɗa cikin hayaniya ina kuka , duk saida na safke mai isata sannan yace tou yi haƙuri An mata gani nan zuwa zan miki abinda kike so ,
Abinda na fahimta ni a nawa tunanin shine , tunda yana da matsalar fushi da saurin hasala , idan yana fushi kuma baya iya murza kanshi , ban sani ba tunda bai faɗamin dalilinshi naƙin saurere na ba , kila shi zuciyarshi ta tabbatar mishi da cewa lallai ni munafukarshi ce kamar yadda ya faɗa , dole da mamaki ya za'ayi ace sai a mafarki zanga Mustapha , me yasa tunda yasan Dikko baije wurinshi kai tsaye ya faɗa masa damuwarshi ba sai yazo wurina kuma sai a yanayin bacci ? Miye nasabata ko alaƙa ta dashi ? Shi yasa ya warware gaba ɗayanshi ya kasa saita kanshi sai lalurarshi tayi mishi tasiri a dai² wannan lokaci ya alaƙanta abun akan ni dama na zubar da cikinshi dan ina so na ɗauki fansa , kuma na faɗa masa cewa zan ɗauki fansa komin daren daɗewa zansa masa baƙin ciki da damuwa mara gogewa , saiya kira zuwa na wurinYazeed shima yana cikin ɗaukar fansa wato kuma sai yake gani da ni aka haɗa kai akayi masa asiri tunda har nasan Mustapha kenan har yanzu ƙudirin fansa bai goge min daga rai ba , maganar gaskiya ne kenan tunda itama Suwaiba ta kira Mustapha kuma Sultana tasanshi amma sabon rainin hankali wai a mafarki , a ganinshi ina tare da Al ' Ameen bayan shi kuma ya rabu dashi ne saboda ni dan yakai gulmata a wurin Dadynsu Dikko tun lokacin dana zauna gidan Dikko na farko , shine dalilin daya haɗashi da Al ' Ameen ya rabu dashi ya dawo da Ashiru , wanda lokacin da zan koma makaranta a karo na biyu mukayi faɗa da Mardiyya a motar Dikko na dawo katsina su kuma suka wuce Abuja.
Zan faɗa in mutu , ai nine zan jefaki da kaina , da gudu na sauka nayi waje kafin yazo naja ƙofar , kai.............. Saina kashe kaina , da gudu na fita daga gidan jikina yana ƙyarma kuma har yanzu ban daina fitsari ba , gaba ɗaya na ruɗe na rasa abinda yake min daɗi , ina gudu ina waiwaye ko ya biyo ni ne ? Nabar wayata a gida kuma ban riƙe number Inna ba amma tunda har nake kiran wayar a da bana samu yau kuma na kira na samu tabbas zan samu Inna hakan ya tabbatarmin tana nan , kuma lokacin ban lafiya ai ta faɗawa Dikko itama zata dawo babu jimawa , ta dawo kenan shi yasa na samu kiran ya shiga , napep na tare na nufi barhim estate....
Kamar yadda nayi tunani kuwa haka ya tabbata , a buɗe na samu gidan na faɗa da gudu nabar mai napep a ƙofar gida , bedroom na samu Inna kwance tana baccin gajiya da gudu na hau saman gadon na riƙeta ina waiwayen bayana , a firgice ta farka tace ke lafiya ? Me ya faru ne ? Gaba ɗaya bana iya magana dan na firgice yadda tunani baya tunani , bayana na buɗe mata inda ya jefeni da wuƙa sai kuma wasu wurare danaji ciwo wurin guje² , sai gefen kafaɗa ta dake min ciwo saboda halbin da yayi min nayi ƙundunbala , mai napep kuwa mai gadi ya sallameshi ya kama gabanshi.
Meya faru dake ne ? Inna take tambayata , bana iya magana sai kuka , dan haka ta sauka ta ɗauki wayarta ta fara kiran wayar Dikko , amma duk kiran da tayi masa bai ɗauka ba , itace ta taimakamin nayi wanka ta bani kaya na saka , fita tayi ta samamin abinda zanci kamar baƙuwar abinci haka naci gaba da cin abincin a zalamance ina tsare Inna da kallo , kuma har zuwa wannan lokacin kiran Dikko takeyi , ina gama cin abinci na kwanta naci gaba da bacci wahlala.
Inna kuwa kiran Dikko da tayi bai ɗauka ba shine yasa ta fusata ta fara wallahi׳ wannan auren saina kashe shi ni har ya isa in kirashi bazai ɗaukamin waya ba , shiɗin banza shin ɗin wofi me akayi² shi ne ? Ɗan iskan yaro mara kunya daya raina mutane , nan fa ta fara kiraye²n ƙawayenta Dikko ya daki Sultana ya caccaka mata wuƙa yaji mata ciwo , yarinyarta ta lalace kunga yadda Sultana ta koma ? Aure sai kace auren bauta ? Waye Dikko ? Saboda tsabar ma shi ɗan iska ne ya zanemin ɗiya kuma nake kiranshi baya ɗaukar waya , to ni nafi shi kangara da taurin rai naga yadda za'ayi ta koma.
Bayan ta gama kiraye²n waya ta tasheni a bacci ina tashi na ganta da wata irin zuƙeƙiyar wuƙa , cikin magana mai kama da raɗa tacemin idan wani yace miki kina san Dikko dan ubanki kika ce kina sansa saina kashe ki idan mutane suka tafi , idona cike da hawaye na ɗaga mata kai , idan kuma kika kira Dikko ko ya kiraki ni kika ɗauka saina kasheki dan ubanki babu wanda yaji babu wanda ya gani , kaina na girgiza alamar to , sakarar banza Dikko baya sanki ya raina uwarki na kirashi ma bai ɗauki wayata ba , dama matar Babanshi ta faɗamin kullum dukanki yakeyi ga tsangwama ga gori ga masifar kishiya ki zubar da ɗan iska kwandon shara ki fuskanci sabuwar rayuwa , sake kaɗa mata kai nayi , Inna tace sai kin samu wanda yafi shi tunda ubangiji ya halicceki nagartacciyar mace , hawaye ne ya gangaromin daga cikin idanuwa nidai nasan wallahi ƙarya ne babu wani inda zan samu wanda yakai Dikko bare kuma wanda yafi shi.....
Inna kuma taci gaba da cewa idan kuma kika kuskura kika sake zaɓarshi kika koma zama dashi wulaƙancin da yayi miki a baya sai yafi wannan kina komawa gidanshi na cire hannuna a lamarinki , kuma duk ranar daya sake dukanki idan kika je wurin "yan uwana ko ahalin Babanki ko nan gidan da wannan wuƙar zan kashe ki in huta , yanzu ma da kai na bata ansa , saida ta ƙare duk mai isarta sannan ta ɗaukeni a mota muka tafi asibiti.
Tunda muka fita duk idan naga ɓakar mota ta wuce da gudu sai inji kamar Dikko ne a cikinta , tunanin Dikko kawai nakeyi ko yana a wane hali ? Ko ya zaiji idan ya tashi bana nan ? Me yasa nazo gida dama na tsaya a wurinshi gashi yanzu Inna ta ɗauka da zafi harta fara cewa wai ya sossokamin wuƙa , sossakawa fa , jifana yayi fa kawai , yanzu ya zanyi idan na tuna dashi a halin da nake yawan tunaninshi ina gidanshi , wace irin rayuwa zan fuskanta , dandai babu kyau zunubi mai girma ne tsallake maganar Iyaye da kawai saina koma amma ina iya komawa matsallar data fi wannan ta taso ina zanje a lokacin kuma.......? Waye zai ƙwaceni ? Allah sarki mutumina ko kana a wane hali , kana raye ko kuwa ka kashe kan naka kamar yadda ka faɗa......... ?
Har mukaje asibiti muka dawo tunanin Dikko nake , ya wani zo ya tsayamin a rai , ji nakeyi dama kawai zan buɗe idona naga mafarki nakeyi ina buɗe idona sai in ganni a gaban Dikko da nayi farin ciki , koda muka dawo gida bedroom na shiga naci gaba da tunanin da bashi da gaira bare dalili , shashshekar kukan Dikko nakeji a zuciyata yadda yakeyi idan yana kwance dani , yadda yakeyin wata ƙyarma yana wannan kukan nashi , bawai ɓare baki yakeyi yana ihu ba , a , a wani iri dai yakeyi mai riƙe zuciya dasa mutum tunaninshi a ko wane lokaci , nashi daban ne dan Alhaji mai gidan "yanci ba irin na Dikko yakeyi ba , kai na Dikko daban ne salon nashi ma yasha banban , uwa uba ya iya sumbatar mace cikin salon da bashi tafiya har abadan duniya , ko ina kike ko ina kikaje sai kinyi tunaninshi dole ,
Haka nake zaune a gidan Inna tunanin Dikko yasa gaba ɗaya na fita hayyaci na , na ƙara ramewa haske na ya rage ga rashin lafiya ta kunno min kai sai jarabar shan kankana idan na riƙe ƙwallo saina cinyeshi dukanshi , da safe ina tashi dashi zan fara , da rana haka idan zan kwanta bacci , Inna kuma dan na rage yawan tunani yasa ta samanin malami mai bani karatu na musamman a gidan , ina dai tunani sosai amma hakan bai hanani gane abinda ake koyamin ba , itace ta sakani a makaranta kuma ta siyamin motar da nake hawa , ina cikin wannan hali na shigar ƙaramin ciki Inna tabi mijinta sukayi tafiyarsu ta barni a gida dani da wata tsohuwa dan ina tunanin kila mijinta ya sake matarshi dan tafiya da Inna yayi yawa duk lokacin da zaje da Inna yake tafiya ,
A makarantar da nake zuwa a nan na haɗu da Umar bansan abinda yakai shi ba , naji daɗin ganinshi sosai wallahi sai naga kamar zanga Dikko ko zaicemin gashi mai gida zaiyi waya dani , bayan mun gaisa nace masa ko yana koyarwa ne anan ? Yace min a , a wurin wani yazo , ina taso yayi min maganar Dikko ya ƙiya , nace tou ko yanzu ka daina zama Qerau ne ? Nayi haka nidai dan inji an kamo tashar Dikko amma ya ƙiya , tou ina mai gidan naku ne ? Abinda kin guji mai gida sai kuma kice wani ina mai gida? Kamar ya na guje shi ? Ey ai haka kikayi ma Momy rashin kunya dan tazo tafiya dake , Dady yace aje a taho dake kije kiyi jinyar mijinki shine kika ce bakya san mahaukaci sai an sake ki , ai kinsan da rashin lafiyar nashi kika gudu kika barshi , tou haka akayi ? Na faɗa a zuciyata , Umar kuma yaci gaba da cewa mai gida yasha wahala kema Hajiya baki kyauta ba da kika faɗawa mahaifiyarshi baki san mahaukaci , yanzu yana ina ne ? Waye ma yasan a ina yake ? Yana can Dady ya tafi dashi itama kanta uwarshi bata san inda yake ba , a nan yake faɗamin mai gida Dikko yamin halakci da bai kamata koma miye na baɗa masa ƙasa a ido , shine ya faɗamin Dikko yasa anmin sauka da ragunan da aka yayyanka ya ƙara da cewa wallahi da nasan matsayina da yadda mai gida yake so na yake ƙoƙarin kyautatamin da ban saka mishi da muguwar sakayya ba , nasan mutum nawa Dikko ya rabu dashi saboda kawai nayi farin ciki ? Me yasa na tsananta ? Me yayi zafi haka ? Miye dalilin saka sharri akan alkairi , naji dai babu daɗi amma koma dai miye nasan Dikko zai dawo kuma tabbas zaizo , nice na faɗawa Umar inda nake na kuma yi masa kwatancen gidanmu....
Mai ƙwaƙwale ido kuwa na sake mafarki dashi , abinda Al ' Ameen yayi min ni na yadda dashi 100% shi yasa a gidana banyi mishi shamaki dashi ba , ko ina nan ko bana nan zai shiga gidana kamar gidanshi , tunda na fara neman matar da zan aura na faɗa mata cewa Al ' Ameen Yayana ne , tana ganin girmanshi kuma tana girmamashi a matsayin shi na Yayana , idan bana gari ko wani abu matata ke so Al ' Ameen nake turawa yaje yayi mata ,
Hmmm , da Al ' Ameen ya samu sake nidai banda wani ƙarfi kuma iyayena basu dashi tunda na faɗa miki daga ni har iyayena duk a ƙasan baban Dikko muka tashi , Al ' Ameen kuma a wancan lokacin shi yayi ƙutu² ya fitar damu a gidan yaje ya haɗo bala'en dashi kaɗai yasan iyakar irin makircin daya shirya akayi mana rashin mutunci a lokacin Dikko baya nan ya raka Dady ganin likita , amma a cikin rashin mutunci babu Momy a ciki dan ita bata cika surutu ba kawai dai idan tana sanka tana sanka idan batayinka ko sabgar ka bata shiga , matan Dady sune sukayi wulaƙancinsu suka koramu kafin dawowar Dady kinga bamu san abinda mukayi ba kuma Al ' Ameen bai nuna mana komai ba duk dashi muka sha jimamin abun har kuka yayi tare da cewa shima zai bar aikin gidan , Babana ne ya bashi haƙuri yace kada abinda akayi mana ya shafeshi a taƙaice dai ya bawa Al ' Ameen baki akan zai haƙura yaci gaba da aiki.
Fitarmu a gidan yasa muka fuskanci sabuwar rayuwar babu , talauci ya tiso ƙeyarmu gaba , na kira wayar Dikko bayayi danni a lokacin bansan akwai number ƙasar waje ba , kawai na ɗauka duk ɗaya ce , na kira Dikko har na gode Allah wayarshi bata tafiya dan nayi imani da Allah ko kisan kai nayi idan na zaunar dashi nayi mishi kuka zaiji tausayi kuma ko za'a mutu idan yace mu zauna gidan wallahi koshi Dadyn bazai koremu ba dan idan har Dikko yace masa kaza za'ayi tou sai anyi shi , idan Dikko baya san abu Dady duk yadda yake sanshi saiya fita sabgarshi , Dady yana ma Dikko soyayyar da tunda nake ni ban taɓa ganin irin soyayyar ba , amma saboda sharri da makircin Al ' Ameen saida yasa Dady yayi ma Dikko faɗa karon farko a rayuwarshi zuwanki a rayuwarshi kenan.....
Ba'a zagin Dikko ba'a daka mishi tsawa ba'a mishi kallon banza , amma yadda duk baki tunani Dikko yana da tarbiyya dan duk wannan soyayyar baisa ya zama sakaran namiji ba yasa abinda yake kuma Dikko ba ɗan iska bane yana da tausayi amma bashi da mutinci duk yadda baki tunani dan shima ya gaji baƙin hali wurin uwarshi kaifi ɗaya ne idan zaiyi² kawai , idan bayayi babu gudu babu ja da baya bazaiyi ba , yana da halin ko oho kuma yana da mantawa da duk abinda zai ɓata mishi lokaci yana da kafiya ko zai mutu saidai ya mutu ya yadda wani irin hali dai shi kaɗai yasan irin abunshi.
Ban wani ɓoyewa mata ta halin da muke ciki ba , ta tausaya min sosai , Al ' Ameen kuwa shine ya samamin uban gida aka bani mota na riƙa aikin mota ina ɗaukar fasinja zuwa jahohi daban² , da nace bana so yacemin na riƙe motar kafin mai gida Dikko ya dawo sai asan abunyi , haka na haƙura na anshi motar idan na tafi sai inyi wata ɗaya bana nan , idan iyalita tana san wani abu zan aiko direbobi masu yo wa katsina sai a bawa Al ' Ameen yakai ma matata.....
Ina can su suna nan bansan wane irin ɗan wanke suke jefawa ba , matata mace ce mai mutunci mai biyayya mai kawaici da kauda ido akan abun duniya , amma kinsan yawancin mata suna "yar ciwa²r nan tasu ta idan aka baka kuɗin cefane ka ɗan maƙale wani abu , tou haka matata take idan na aiko mata da kuɗi zata ɓoye batayin abinda ya kamata kuma bata cin abinci mai mahimmanci saita maƙale haka kuma ko ruwan da zatayi amfani dashi bata siya saidai idan an dawo da fanfo taje tabi layin ruwa acan ƙofar gidan wani tsohon attajiri da yake fito da tiyo waje mata suke ibar ruwa.
Al ' Ameen kuwa gani yakeyi kamar nine kasashshe wurin kula da iyalita , saiya fara wanketa da ruwan naira dan idan dai kana tare da Dikko tabbas kaima zaka samu bakin gwargwado kayi hidima da rayuwarka cikin rufin asiri kamar dai kaima mai halin ne , haka yake cikamin gida da abokanshi ni ban sani ba yakai cefane yakai abinda za'a dafa tayi girki suci a zauna min a gida har dare ana fira da matata , idan zan dawo gari ya sani dan ina faɗa masa bana ɓoye masa komai , matata kuma bata taɓa faɗamin Al ' Ameen yana zuwa shida abokanshi ba tunda dai na faɗa mata Yayana ne ta yadda a hakan kawai.
Bansan yadda akayi ba ya ɓatamin mata ba idan ina nan nine miji idan kuma bana nan Al ' Ameen shine mai gida , haka maƙota sukayi ta bugomin waya suna faɗamin abokina fa yana zagayawa idan bana nan , da farko ban yadda ba sai naga tou idan sharri ne me yasa mutane da yawa zasu faɗa ? Ashe neman da yake mata akwai gejin da zai kai yana amfani da ita an bashi kuɗi ana neman idon matar aure amma sai anyi fasiƙanci da ita so adadin kwanakin da suka faɗa mishi sai a zuba mata maganin a idonta ana zubawa shi kuma tsafin zai cire idonta , ni kuma ranar da zan dawo katsina sai ban faɗawa kowa zan dawo ba , da farin ciki na shiga cikin gidana amma saina samu matata ba ido tana ta kakarin mutuwa , dana tambayeta sai tacemin Yayana ne yake nemanta shine ya cire idonta , daga haka ta mutu.
Nasan banda wani Yaya wanda ya wuce Al ' Ameen kai tsaye nayi ƙararshi amma sai ya samu ɗaurin ƙugu wurin manyan da yayi musu aiki sukaje suka baza kuɗi aka kori shari'ar kuma har lokacin Dikko bai dawo ba , haka na ƙara ɗage ƙara duk inda mukaje kuɗi ne suke magana , maimakon inyi haƙuri saina biye sharrin zuciya nima na nemi hanyar tsafi dan nayi alƙawari sainayi kuɗi da gasken gaske , zuciya ta ingizani nima na faɗa sana'ar ƙwaƙwale idanuwa , wanda Al ' Ameen ya haɗani dashi ya bani mota shine aka kaiwa idon matata , dan haka na koma wurinshi nima na shiga ƙungiya kuma da idon nashi matar na fara , na lashi takobin duk matar auren da ta zama makwaɗaiciya saina ƙwaƙwale idonta kamar yadda aka ƙwaƙwale na matata ,
Ƙungiyar ashe tana da wani tsari wanda ni ban sani ba , su zasu baka magani kayi amfani dashi ido kawai zai fita kai zaka zuba magani su kuma zasu turo tsafunsu ya zama maciji kana zuba maganin a idon mace macijin zai tsotse idon ya kuma shanye jinin jikin mace , idan yasha jinin saiya zuba wani a cikin ƙwarin idon daya cire kafin tsafin ya gama tsafinshi shine jini zai riƙa ɗiga a idon mutum da zaran an gama shikenan mutum ya tafi kai kuma sai a baka kuɗinka , tsarinsu shine shekara 3 sai kaima su tafi dakai ,
Mu mune ƙanana su kuma sune manya , mu zasu tura muje mu nemo musu matan aure muyi iskanci dasu sai mu zuba magani , kashe duk yaransu sukeyi bayan shekaru 3 sai suyi sabbin zubi , bansan da wannan tsari ba na faɗa ƙungiya kai tsaye saboda wani muradi nawa , ba wurin gudu babu wurin tsira mutuwa tazo min kuma shima Al ' Ameen zai mutu idan dai kayi musu aiki saika tafi saidai a wayi gari ba'asan abinda ya kashe ka ba , to me yasa sai matan aure suke so ne ?
Wannan tsarin tsafinsu ne shi ya faɗa musu irin wanda yake so bashi ya basu kuɗi , wasu zasu ce "yan mata , wasu matan aure , wasu zawarawa wasu mahaukata wasu jarirai wani tsafin kuma zaice mace mai ciki yake so , wasu makafi wasu guragu ko "yan maɗigo ko mazina ci , mai wasa da sallah ko wacce ta raina iyayenta , tou su nasu wacce ta raina aure suke buƙata , kinga ke ni ban kwanta dake ba amma kinci kuɗi dana tabbatar ke ba matar aure bace ba suka sa na koraki , amma sun matsa akan mutuwarki dan record in da kikayi sun takura sosai akan ki mutu , amma basu samu galaba dake tsafi yace kinyi kusanci da sallah yawan karatun al ƙur'ani da addu'a lokacin kwanciya bacci , cire hular saman kanshi yayi ya duƙar da kanshi gabana yace kin gani bani da sumar kai bansan ranar da aka cireta ba sun bugamin lamba , shima kuma tabbas nayi imani sun bugawa Al ' Ameen irinta gaba ɗayanmu zakiji labarin mutuwarmu.
Tou ta ina ne zanbi nazo inda aka binne tsafin da akayi ma Dikko ne ? Labarin tsafinshi ya goge idan ya dawo zai baki labarin komai banda sauran lokaci wanda aka bani ya ƙare , hankalina kuma ya kwanta tunda shima Al ' Ameen zai mutu , yana faɗin haka ya zama maciji suuuuuu ya gudu da wuce , da tashin hankali na farka kuma tun daga wannan ranar ban sake ganinshi a bacci na ba har yau ,
Inna ta daɗe a tafiya lokacin data dawo cikina ya shiga wata 7 bata sake komawa ba har na haihu , dana aihu ni na faɗawa Umar na haihu ita kuma Momy tazo har asibitin da muke ta anshe jariri wai ba zaisha nonon karuwa ba yazo shima ya zama karuwi , ta tata rashin mutunci dai² iyawarta tayi gori tace kuma tunda bata san zamana da Dikko duk wanda ya tsayamin a garin nan zata ga wanda ya isa yasa na sake zama da Dikko , zai dawo saki 3 zai bani babu sauƙi , idan kuma ina tunani Dadynsu zai tsayamin kamar na aurenmu da Dikko yaƙiji ya aureni Dady ya goya mishi baya yanzu haka bazai goyu ba , shi da kanshi zaisa Dikko ya sakeni , ban santa ba labarinta na keji , nayi kuka nasha hauka bansan iyaka ba , kuma da suka tafi da jaririn Umar yazo ya faɗamin wai Momy tace ma Dady nice nayi waya wai azo a ɗauki jaririn nan yadda bana san Dikko haka bana san jaririn kuma duk jinin da Dikko ya haɗo dashi bana sanshi , idan basuje sun ɗauki yaron nan ba komai zai iya faruwa tunda tun cikin naso na zubar bai fita ba zan kashe yaron , ta dai haɗa da ɗan makircita.
Abinda yasa nake kuka har na tafi shine , Umar yacemin Dady yake faɗa da yana tausayina kuma yana so na tunda Babanshi yana so na , ashe bani da mutunci har na danganta mishi ɗa da mahaukaci kuma nice zan kashe mishi jika daga wurin Babanshi dama na zubar da ciki a farko tunda nice nasa Rabiya tayimin allura , Allah yaba Babanshi lafiya ya dawo saiya sakeni.........
Dana tuna zan rabu da Dikko sai inji dama mutuwa nayi kawai na huta da baƙin cikin rayuwa..............!!! Ga Dikko yace baya zuwa bikon mace , iyayenshi sun ɗauki zafi , nima Inna ta gune akan rashin ɗaukar wayar da Dikko baiyi ba kuma har yanzu bai kirata ba , kuma tace idan har na koma gidan Dikko babu ita babu ni har abadan duniya saidai idan Dikko zai zama uwata , tasa kullum ina kiran wayar Dikko akan ya bani takaddar sakina naje nayi aure , wayoyinshi gaba ɗaya basa zuwa , shin yana ina ? Yana nigeria ? Ko yana ina ?
Me Dikko zaice idan ya dawo ? Wane hukunci zai ɗauka ? Ya zaiji idan iyayenshi suka ce nice na maida musu ɗanshi nace bana riƙewa saboda bana sanhi , shin zai sakeni ko kuwa zai zauna dani ? Ya zanyi ׳.................. ??? Yadda zanyi da mafita da rabuwa , gaba ɗaya na tattara lamarina wurin ubangiji duk abinda ya zartar a kaina dama haka yazo a rubuce kuma bawa bai isa ya goge ƙaddara shi ba ,
0 comments:
Post a Comment