Tashi nayi na fito nayi alwallah, bamma kowa magana ba na koma d'akina... Kuma koda na gama sallah kwanciya na k'arayi dan inajin gajiya sosai ga kuma bacci.
Amma k'iri k'iri baccin ga yak'i zuwa, hankalina da tunani na gaba d'aya ya tafi ina tunanin irin yanda Nana ta tozarta mijinta daren jiya a cikin bainannasi, miji da yake da daraja yake da matsayi yake da mutunci abin tattalawa idan Allah ya baka, ubangiji ya rataya ma Nana rigar arzik'i amma tana k'ok'arin yagata ta ratayawa kanta rigar wahala, idan har Nana ta fito daga gidan mutunci ko a gaban d'iyanta batayi wannan iskanci ba amma shine har ta fito tsakar gida kuma gidan ma na haya dan ta nunawa mutanen gidan cewa ita ta hana mijinta hak'k'inshi.
Gaskiya abinda wasu matan sukeyi bai kamata ba, duk yanda akayi a zaman jiya aka rud'awa Nana tunani, ashe kuwa idan har zaki biye ma labarin "yan iskan mata babu ranar da hankalinki zai kwanta a gidan aure, su basuyi auren ba kuma su hana masu zaman auren suyi aurensu, sai su rud'aki da zance babu labarin k'arya a samu a kakkab'oki sai kin fito daga gidan mijin kizo kiga labari yasha banban.....
Maganar Karima najiyo tana cewa jama'an gida ku fito majalissa d'inki duniya ta fara tattaruwa, ga A' i nan ta taho da labari, Nana tace ai bama labari kad'ai tazo dashi ba naga ta shigo da leda duk "yanda akayi daren jiya anci kaza mu ta ragowa sauran, kaji jakka sai kace rainon mayu dan ubanta.
Hayaniyar matan gidan naji da alama kowa tayo waje, agogo na kalla naga duka 6:22am, gaskiya dai hakan bai kamata ba da zasu yadda dana basu shawara amma bara nima na fita wajen mu gani....
Nana na gani tana wanke fuskarta tare da cewa ai ilimi yafi sallah ita sallar bara a jingineta idan na gama d'aukar darasin nayi ta daga baya.....
Kallonta nayi k'asa da sama amma banyi mata magana ba, duk yanda akayi Nana uwayenta jahilai ne, wata zuciyar tacemin karki zargi iyayenta Sultana wallahi kina iya ganin babu laifinsu d'a nawa kake ba tarbiya idan yaga ba idonka ya barbad'ar da ita yayi wanda yake so.
Ina isa inda kowa yake na kalli A ` i, nace gaskiya ki daina yo mana sabko duk fa masu gidan basu fita ba kawai sai ki baro gidanku kizo ki hana mazajen wasu baccin safe ? Irin haka da kukeyi gaskiya bai kamata ba, kallon Nana nayi tare da ci gaba da cewa gaskiya kuma matan gidan nan kuna da naku laifi da kuna zamanku a wurin mazajenku baku fito ba babu wacce zata rik'a dako muku sammako ta hanaku samun ladar kwanciya a jikin mazajenku.....
Nana zatayi magana A ' i tace barta in bata sani ba a fad'a mata, kallona tayi tare da cewa ke Sultana kinsan makaho idan yana kashi baisan ana kallonshi ba sai an tsokalo d'uwawunshi, munsan tal munsan sal abu d'aya yasa bazan gaya miki ko waye ubanki ba da rayuwar gidanku amma yau dana bud'e miki zani cikin kasuwa.
Ke harma kina da bakin da zaki zo ki wani ce an hana mazan wasu bacci , ina kika san wannan keda uban naki ma ko gidan bai kwana..... Murmushi nayi ba tare dana nuna naji zafi akan tabo Babana da tayi ba nace.....
Ai duk ubanda ya ganni yasan ubana zauna gida ne, ko bai kwana ba kinsan yayi k'ok'ari kuma ya fita hak'k'in mata tunda har ga sakamakon mu ya fito, duk namijin daya zauna gida ai soko ne tunda babu k'ashin zuciyar da zaisa ya fita neman abinda zai ba iyali, niko zuciyar ubana tsaye take wurin nema ya nemo aci asha kuma ko bai kwana gidan ba da safen idan ya dawo suma matan gidan zai basu hak'k'insu kinga kuwa dan bai kwana ba ai ba aibu bane ba tunda dai abinda suka aure shi danshi d'in ai yana basu bai hanasu ba.
Saboda mata da yawa wannan abun dake kika raina su sunsan darajarshi, wasu matan kuwa zasu iya hak'uri da talaucin namiji amma wannan abin d'aya da kike magana akanshi basu yadda su rasashi ba, wata macen kuma mijinta ya daketa ya hanata abinci amma idan dai zai kwanta da ita ta samu gamsuwa zatayi hak'uri taci gaba da zama dashi a haka tasan arzik'i na Allah, amma wata ita ba shi take mawa ba rayuwarta da tunaninta ya tafi wurin tunanin neman duniya, kamar dai ni dake kinga ba abun ya fiddo mu ba kasuwanci muka d'auke shi, tou haka matan gidan nan suke su ma, da mazajensu masu kud'i ne ko sunyi wani abun wani sa d'aga k'afa dan duk yanda ka raina d'an tsintsu bakacin shi da gashi, namiji ya sakarwa mace ragamar gida ai dole ta koma mijin shi ya zama matar, amma duk da haka dai ki sani Allah ba ruwanshi da kin nemo kinba miji tunda hak'k'in cida da sha sutura da wurin zama lafiya da ilimantar wa duk saida ya d'auki alk'awarin zaiyi a gaban waliyyanki ,
To tunda anyi auren kin gane bazai iya ba ai sai a raba auren ki huta amma bawai ki zauna kiyi ta yayar ma kanki zunibi ba, zaiyi wuya kiji mace taje gidansu takai k'arar mijinta yana basu abinci so d'aya a rana.
Amma mafi yawancin mata namiji ya hanasu hak'k'insu ko baya gamsar dasu sai kinji sunyi tsegumi, aba k'awaye labari aba mak'ota labari aminiya da duk wanda kike hud'd'a dashi sirrin mijinki fallashshe ne, tou wa kikayi mawa ?
Nidai shawara ce idan ta muku zafi sai kuyi hak'uri, amma ya kamata ku rik'a sirrinta sirrin mazajenku domin dai wannan sirri ba abin yayad'awa bane shi yasa yake rufaffen sirri ko an shiga d'aki sai an rufe k'ofa....
Tsoki Nana tayi tare da cewa mu idan zaki zauna kiji ki zauna idan bakiji ki k'ara gaba, Karima tace da Allah kyaleta tafi ma mill tsayuwa bamu fasa zancenmu, ke A ' i albishirinki ....! Saida A ` i ta harareni sannan tace goro,
Jiya fa Audu yaci ubanshi da gudu ya biyo Nana har tsakar gida, kallon Nana tayi tare da cewa kai jiya fa Nana tayi bala'i gidan nan , can naji gurnanin munafiki kamar an kwacewa mahaukaciya diyarta.....
Ke Nana bada dai labari da kanki kinsan masu iya magana nacewa wak'a bakin mai ita tafi dad'i, mu na waje muka gani bamu kalli na d'aki ba.
Tab'o ledar hannun A ` i tayi tare da cewa da Allah idan dai namu ne ki bamu mu cinye sai miyau na yake tsikewa, mik'a musu tayi "yan iska masu kama da maguna suka rarraba suka cinye, Nana na cewa dan Allah A ` i ki kawo min ice cream rabona da insha shi tun ina budurwa,
Karima ta katse ta da cewa haba da Allah bamu labarin Audu ki daina wani zancen ice cream, lashe hannunta tayi sannan ta fara cewa, in fad'a muku tunda na ganshi ya shigo da leda nasan dole yana buk'ata...
Ajiye ledar yayi a gefe na tare da cewa karfa kiyi bacci, inajin yace kar nayi bacci nasan tafiye yake da damuwarshi, saida na bari ya gama abinda yakeyi tsaf yazo ya hawo ta bayana yana wani shashshafoni na fara mutsirniya, cikin raunanniyar murya magana mai fitar da numfashin wahala yace kar muyi haka dake Nana yau kusan sati biyu kenan kina hanani hak'k'ina bakyajin tsoron fushin Allah ya sauka kanki ......?
Aiko na b'ata rai nace gaka k'atoton wanda fushin Allah zai saukar mawa , ai idan dai har kaga ka kwanta dani tou wallahi sai ka biyani duk bashin da nake binka..... cikin rawar jiki ya fara k'ok'arin juyoni yana cewa kiyi hak'uri Nanata wallahi ba'ayimin biyan bashin ba, kuma banyi ciniki sosai ba yau abinda na samu gashi nan na biya na dafo miki indomie, tsoki nayi tare da cewa ai sai ka cinyeta ka kwanta kayi bacci.
Haba Nana idan dai har kika ga anci ko ansha saida natsuwar ci, ina tare da babbar yunwar da abinci bazai gusar min da ita ba kin sa na zama wani susutacce na zama kamar wani tab'ab'b'e banda natsuwa bare kwanciyar hankali kiyi hak'uri don Allah yauma karki ce zaki hanani....
Ai ban gama jin zancenshi ba na duro daga saman gado nayo waje..... Ni kuma naji tana wannan haukan shi kuma ya jata suka koma d'aki. Murmushi nayi tare da cewa kin burge Nana.... Tou me ya faru bayan kun koma d'akin ne ?
Tunda na lura basa san gaskiya shi yasa nima zan biye musu mu zama riftattun gaba d'ayanmu, Nana tace ai koda ya maidar dani d'aki da k'arfin tsiya babu abinda na yadda ya shiga tsakani na dashi, yayi magiyar yayi nacin kuma ya jaraba ansa ta k'arfin tsiya amma ya gagare shi, dole ya hak'ura ya fita baima kwana gidan ba......
Dariya nayi tare da cewa tou ina kike tunanin ya tafi Nana ? Yo can shi ta matse mawa koma gidan uban waye ya tafi bai dameni ba wallahi saiya biyani bashi na ko zaici gaba da kwanciya dani.
A ` i kuwa cewa tayi kwarai Nana karki sake ki yadda ko gidan haya kake zaune kud'in wata ya k'are idan baka biya ba no uziri tashinka akeyi, ya baki idan babu kullum yaita kwanan hak'uri, gaba d'aya suka bushe da dariya...... Banda ni da nabi Nana da kallon tausayi !!!
Mijin Karima ne ya fito cikin kunya yana san ya shiga bayi amma kunya ta hanashi fitowa dan yanzu mun k'ara yawa, daya d'aga labule ya hangomu sai ya koma, k'arshe dai hak'ura yayi da wanka yasa rigarshi yabar gidan.....
Fira akaci gaba dayi tunda muka zauna har zuwa yanzu babu macen data tashi koda wasa, ganin rashin aikin yin nasu bashi k'arewa yasa na tashi dan ina da wurin zuwa anyi firar dare dani idan banyi baccin wuri ba,
Saida na share d'akina na gogeshi tass na kunna tsintsiyar k'amshi sannan na zuba ruwa naje nayi wanka, ina fitowa na shirya saida na gama shiri na sannan nasha ruwan tea ko biredi babu ina gamawa nayi ma mutanen gida sallama tare da rufe d'akina nayi gaba abuna.....
A zaure na sauk'e nik'af ina na fice daga gidan tare da addu'ar yo babban kamu idan na fita, A ` i na gani tsaye da wani amma bansan ko waye ba, ni mamaki ma ya kamani dan bansan lokacin da A ` i ta fito daga gidan ba...
Har zan wuce naji tace ina zuwa haka Hajiyata ? Yaye nik'af ina nayi tare da rage girman idona na dama nace farauta zanje kinsan sai ka gane girman gida kake sanin ta inda zaka fara shara.... Murmushi A ` i tayi tare da matsowa kusa dani ta d'an rik'o k'uguna da hannu d'aya, sannan tayi min wani irin kallo wanda ni bansan abinda yake nufi ba......
Saida ta wani yi k'asa da murya sannan tace da ganinki zakiyi tunon asiri amma ina gargad'inki da ki rik'awa bakin linzami ta k'arasa maganar tare dayin murmushi, bud'e idanuwa nayi dukansu wanda idan har na d'an ragesu na bud'esu lokaci d'aya nasan ina k'ara kyau kuma mutane sunsha fad'amin haka.
Kallonta nayi da duka idanuwana sannan nace dama tunda kike kin tab'a ganin mazinacin da yayi sirri ? Miya had'a karuwa da sirri dama ? Ai da amana da kunya da sirri da gaskiya duk karuwa bata dasu, kunya tana tasowa ne daga b'oye tsiraici tou ban b'oyeshi ba zan bud'ashi wa duk wani mai kud'i ya gani, kinga nan rashin kunya ta fito, daga inda babu kunya kinga babu imani duk mutumin da baida imani kuma bashi tare da rahmar Allah, ina bud'ewa ga maza, namiji kad'ai ya isa ya gani yasha kuma ya tab'a dan haka sakarmin k'ugu daga yau karki kuskura ki sake tab'amin jiki, idan har na baki sha'awa tou ki zama namiji kizo da dubu dari shidda sai in baki duk abinda kike gani a jikina ya burgeki, na k'arasa maganar tare da sauke hannunta a jikina....
Kallona A ` i tayi tare da cewa ai duk saurin anguwar zoma ta bari a haihu ? Duk saurinki kin bari kiji uzirin da nazo dashi..... Bud'e k'ofofin hancina nayi sannan nace ai tunda har aka tanaji aikin ungozance ansa haihu tana zuwa kinga kuwa duk daren dad'ewa amfaninta zaizo. Tou ni bana jira idan na gani saina tanka na dakatar dake ne tun kafin cikin ya samu bare kisa ran ansar haihuwar....
Na sanki cikinki da waje, duk macen dake gidan nan nasanta kuma tun ranar da na kwana na gama karatun halin kowa, kwalwa ta gane inda mutum ya dosa Allah ya bani amma bai bani kwalwar gane rubutu da karatu ba, ina iya gaya miki duk macen dake lesbian a cikin gidan nan , kuma ina gane duk macen da namiji ya kwanta da ita ba tare da na sani ba, ki kiyayeni ina da had'ari ne mai girma domin nima kaina tsoron kaina nake, ki fita idona tun kafin inyi miki terere.......
Shiru A ` i , tayi ta kasa magana..... Murmushi nayi tare da dafa kafad'arta nace yawwa kisan wani abu gaskiya ni bana gaba da mutum ina so abun nan ya tsaya iya mu biyu, zan wuce ki gaishe min da mijin Nana kuma bazan bata labari ba , ina fad'in haka nayi gaba abuna.....
Cin amana da rana k'iri k'iri wannan fa shine an raka zomo rami an dawo.... A ` i takai Nana ta barota gashi kuma tana tare da mijinta, kila ma jiya da yayi zuciya da Nana wurin A ` i ya tafi ya kwana, tabbas ma can yaje tana nan tana haukan banza mijinta yaje ya siyo ma k'atuwar banza kaza taci ta rago musu....
Zuciya ta ce tace Sultana kiji tsoron Allah zato zunibi, tsoki nayi tare da cewa wannan ai ba zato bane abinda yake filin Allah kowa yana gani dandai kawai gaskiya bata fad'uwa, sudai suka sani amma idan tayi tsami kowa yaji.
Napep na tare na fad'a mishi inda zanje, ciniki mukayi na shiga yaja muka tafi. Yau babu inda zan sauke zango sai wurin Alhaji mai gidan "yanci, wato inda Umar yakai ni da farko ban shiga ba na dawo, dalilina na haka kuwa yanzu zakuji.......
18/08/2019
*JAMILA MUSA Ce* 🤙🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 12
Abinda yasa banbi Umar mukaje gaban Alhaji saboda na shirya lafiyayyar yaudara da zanyi masa, sana'ar karuwanci tayi min kad'an gaskiya dan haka dole sai na had'a da sata, shekaru biyu kacal zanyi a cikin wannan mummunar d'abi'ar, ina so na shigewa Alhaji sosai a rayuwa idan ya saba dani zan kunce dawakan Dikko duk in siyar dasu, nasan duk doki d'aya za'a siya da kud'i masu yawan gaske.
A wancan lokacin da munje tare da Umar Alhaji yaga fuskata tou kud'in Umar da nayi wayau na kwace masa tou Umar zai koma ya fad'awa Alhaji cewa wannan yarinyar b'arauniya ce ayi hankali da ita...
Bani da tabbas kuma bani da alkibla nima kaina tsoron kaina nake bansan abinda yake damuna ba umarni kawai zuciyata ke bani ni kuma ina biye da ita.....
A k'ofar gidan Alhaji napep ya sauke ni, kud'inshi na bashi ya wuce nima na shige ciki, kaina tsaye na tunkari gidan babu wani tsoro fargaba bare kuma jin kunyar kowa amma har yanzun ban cire nik'af ina ba.....
Ko mai gadi baiyi yunk'urin dakatar dani ba domin dai yasan mata abokan hud'd'ar ubangidan nasa ne... Hanyar da Umar yabi dani hanyar nabi naci gaba da tafiya har na shiga cikin palon gida....
Saida na shiga cikin palon na cire nik'af ina, d'an kallon palon nayi sannan na kallo inda hotunan mak'iyi Dikko yake raina ya b'aci sosai tsinan ne duk shine silar rushewar gidanmu kowa ya bazama ya shiga duniya, duk da bai sissiye ba da muna zamanmu cikin farin ciki, idan dai kud'i yasa kayi mana haka nice zan mayar dakai talakan k'arfin da yaji, uhum da kinsan waye Dikko da baki ce haka ba .....
Sallama na kwarara daidai yanda nasan za'a iya jiyoni, daga ciki naji ance shigo mana ! Inda naji sautin maganar ya fito nabi na shiga, kwance mutumin yake saman gado ya wani baje sai kace anyi b'arin asara...
Kallo d'aya nayi masa tare dayin murmushi na zauna a gefen gado, kuma nayi karatunshi tun shigowa ta bakin gwargwado kuma na fahimci wasu d'abi'u nashi, da gani zaiyi sauri fushi kuma yana da saurin sauka, yanayin shi ya nuna abun duniya bai rufe mishi ido ba, amma wannan da ganin idonshi mayen mata ne lallai wannan idan ya dafi mace aradu mai ansarta sai Allah...... !!!
Alhaji barka da yini, cikin sakin fuska ya amsa min da cewa barka dai malama ya kike ? 'Dan gyara zama na nayi tare da cewa lafiya qalau ya aiki ? Kallo na yayi tare da cewa ki ganni kwance kuma kice min ya aiki ? Murmushi nayi tare da cewa ai na kwance kuwa shi yasha aiki Alhaji inba ba'ayi tuk'in zaune ba ai anyi na kwance....
Kallo na yayi tare dayin dariya irin tasu ta gogaggin "yan bariki sannan yace wace ce ke ? Kama kaina nayi tare da tattaro natsuwa ta dan ni nawa ba kalar nasu bane, saida na tattaro class ina sannan na d'an rage yawan fara'a , suna na Maryam Aliyu Binna........ Amma anfi sani na da Sultana.
Talla na kawo maka da fatan zaka siya ? Na k'arasa maganar tare da kashe mishi ido d'aya.... Dariya Alhaji yayi tare da gyara zaman belt inshi sannan yace yarinya me kike siyarwa ne ?
K'addara......... !!! Kasan kowa da irin tasa k'addarar haka kuma kowa da irin k'addarar da yake siyarwa, idan talauci ya ishi mai rai yakan siyar da duk wasu abubuwa nashi daya siya ya adana, manoma sukan b'oye hatsi yayin da sai yayi tsada suke siyarwa, dillalai kuwa sukan adana k'addara ta k'asa sai tayi kud'i su siyar, macen da kud'i suka kama idan tayi ajiyar d'an kunnen zinari zobe ko awarwaro wannan talaucin zaisa ya ziyarci kasuwa, yayin da duk macen da tasan ciwon kanta take k'ok'arin adana tata k'addarar da Allah ya bata kyauta sai taje gidan mijinta,
Ni kuma talauci ya dameni ba gidan zama bare motar hawa, kuma ban ajiye hatsi ba ban aje gold ba, shi yasa na d'auko nawa mutunci zan siyar amma sai na lura babu wanda zai siya da daraja idan ba kai ba, dare d'aya tak zaka more amma farashin farko kuma ba tayi miliyan d'aya ne,
Ka ganni dai a fuska gwanin burgewa, masana sirrin mata sunce duk macen data cika muni zaiyi wuya tayi wani armashi, sai kuma sukace kyakkyawar mace kuma wannan riba biyu ce harda gyara ma, karfa kaga kamar ina yaba kaina ne fuskar gida ba itace take nuna tsarin sa da haduwar sa ba, sai an bud'e an duba ake ganewa....
Duk mota sunanta mota amma wata motar bata kai mota ba, tou haka take ga mata duk mace sunan ta mace amma wata macen muna mata ce..... Na k'arasa maganar tare da kallon Alhaji nayi masa kyakkyawan murmushi mai tattare da jan hankali. Saida na kauda kaina sannan nace amma ina da sharadi d'aya , idan anyi ba'a sake maimaici wannan shine sharad'in kasuwata idan zaka zuba hannun jari bisimillah, na mik'a masa hannu na da niyar mu k'ulla alk'awari....
Gyara kwanciya Alhaji yayi da niyar magana amma na lura da yanayin fuskarshi kamar bai yadda dani ba, dan haka na tare maganarshi da cewa karka cuci kanka wannan harka duk taimakekeniya ce , ka bani gishiri in baka mand'a , kaga masanya ce za'ayi fa ni wannan ba matsalata bace kud'in ne kawai damuwa ta, ka yadda na rana d'aya tak 👌🏻........
Kallo na Alhaji yayi tare da cewa tou ai ked'in ce kin tsananta miliyan d'aya fa..... Kin kuwa san girman miliyan Sultana ? Idan na baki ita ina zaki zuba ta ? Waye zai d'aukar miki ita ? Me zakiyi da ita kuma ? Ajiyar zuciya na sauke tare da cewa, wurin zubata da d'aukarta da abinda zanyi da ita duk ba huruminka bane ba, kayi kawai ka bani idan kuma baya yuwuwa in hak'ura inyi gaba kila na dace.......
Tashi yayi zaune tare da tattaro duka hankalinshi gareni sannan yace karki k'i fad'amin, kika sani ko zan iya miki maganin damuwarki ne ? Kuma kike maganar miliyan d'ayan d'aya kika sani ko in baki abinda yafi miliyan d'in ? Ni kud'i ba matsalata bane amma ina san sirri dan duk wannan harkar da kikaga inayi gaskiya banayinta da d'anyar kwalwa saboda gudun b'acin rana.....
Alhaji kenan idan na fahimta kallon yarinya kake min ko ? Tabbas a zahirance ni yarinya ce amma a bad'ini ni mai tunani ce, babu wanda ya koyamin yanda ake bariki ni na koya da kaina, ban yadda da zama k'ark'ashin kowa ba nima saboda gudun b'acin rana, "yanci na, mutunci da kowa yake tak'ama dashi ya siyar akan kud'i k'alilin k'arshen wulak'anci da tozarci mak'iyina da bana k'auna shine ya taka ruwan ciki na, a cikin gidansu ya keta min hijabin da nake ta boyewa shine yayi mata kaca kaca.... Shiru nayi saboda idan dai har naci gaba da magana zan iya kamo sunan Dikko in d'ura wa uwarshi zagi.
Hak'uri Alhaji ya bani tare da jawoni jikinshi yace kiyi hak'uri ku matan ne baku da amana sai a had'a kai daku a cuci mutum, murmushi nayi tare da cewa ai ko zanyi cuta bana tsaya inda aka sanni ba, kana dai da kud'i kusa dakai dan bana amfani da banki danma karka wani ce zaka turamin.....
Cikin raunanniyar murya yace karki damu Sultana d'akin nan cike yake da kud'i, zan sake magana ya had'e bakina da nashi wuri d'aya labari ya fara canja salo.....
Murmushin mugunta nayi tare da bawa Alhaji duk abinda nasan zaisa ya samu natsuwa.... Ya dad'e yana gurje kud'inshi kuma ban waniji wata damuwa ba, har saida ya gaji dan kanshi ya kyaleni.
Sauka yayi daga saman gado ya nufi toilet ni kuma ina nan kwance, yana shiga na zaro wayata dana soke a jikin gado wanda duk abinda mukayi da Alhaji saida na d'auka, dariya nayi bayan na gama kallo sannan na mayar da wayata cikin jaka...
Kafin Alhaji ya fito har na gama saka kayana na maida nik'af ina na zauna bakin gado.... Ina jiran fitowarshi ! Bai wani dad'e ba ya fito da sauri ya nufi wurin wayarshi saboda tun dazu ake kiranshi banyi gigin dubawa ba saboda ko na duba bana gane suna....
Kayi hak'uri mai gida shine dai abinda yake ta maimaitawa, bansan abinda abokin wayar yace mishi ba naji yace Eh an basu ranka ya dad'e , tou insha Allah, Allah ya tsare ubangijj ya k'ara taimakawa. Sallama sukayi dashi Alhaji ya ajiye waya sannan ya kalloni tare da cewa ke yanzu ya zamuyi ne ?
K'afa d'aya a saman d'aya na d'ora sannan na ajiye hannuwa na ta baya nace bani zakayi in wuce marece yanayi, tou baza kiyi wanka ba ? 'Dan girgiza k'afata nayi sannan nace bana sauke najasa a wurin da bai kamata ba ka bani kawai na wuce.....
Tou waike taya zaki d'auki miliyan d'aya ne ? 'Daga nik'af ina nayi tare da cewa karfa ka raina min hankali ka bani in wuce kana b'atamin lokaci kaji.... Murmushi yayi tare da cewa ya zaki d'auki zafi da wuri haka ? Tou ya zakiji idan na hanaki kud'in nan, murmushi nayi tare da cewa kai kuma ya zakaji idan ka samu hotunan vidio abinda mukayi a yanar giza gizo ..... Na k'arasa maganar ina masa kallon rainin hankali.
'Daure fuska yayi tare da cewa sai in kashe ki, murmushi nayi da gefen bakina tare da cewa tou da suka shiga duniya kuma ya zakayi da duk wanda ya gani ? Ta ina zaka bi ko gogesu a cikin wayar kowa ? Akwai "ya "ya akwai surukai ga kuma matanka abinda kake b'oyo tou gashi a cikin wayar "yarka ko d'anka tou ya zakayi dasu.........
Zufa ta keto mishi sosai, dariya nayi tare da cewa tou goge ai haka ma bazata tab'a yuwuwa ba, kawai nima nayi maka barazana ne kamar yanda kake neman hanani kud'ina, kaga abinda bazai yuwu bane bani na wuce,
Ya kama kanshi sosai dan haka yace zan baki dubu dari biyar yanzu anjima ki dawo ki amsa sauran, gaskiya idan na tafi bana dawowa ka bani kawai sai mu rabo lafiya, tou wai babu zan baki ? Nace itama babun idan tana kamuwa ka bani ansa zanyi ba cemin kayi d'akin ka cike yake da kud'i ba ?
Mutum cikakke mai arzik'i kamar ka ai bai kamata ya rik'a d'aga murya ba akan miliyan d'aya kacal ba, miliyoyin da suka tafi babu dalili baka san iyakarsu ba bare wannan idan ka bada ita ai kasan ta inda tabi ta wuce...
Dubu d'ari biyar ya bani yace muje in baki sauran suna cikin mota, cikin jakata na zuba dubu dari3 muka fita dubu dari biyu na hannu na, muna zuwa ya bud'e mota ya bani sauran kud'in, bud'e gaban mota nayi na shiga tare da cire kallabin kaina na d'auresu a ciki nace ka ajiyeni bakin titi....
Baimin magana ba ya tada mota muka tafi, saida muka tsaya inda zai saukeni nace da Allah rubutamin number wayarka, har yanzu baiyi magana ba ya ciro biro a gaban aljihunshi ya rubutamin a jikin takarda ya bani,
Nima ban sake magana ba na bud'e mota na fita, napep na tare dan zuwa gida, a k'ofar gida ya saukeni na shige, da sallama na shiga gidan sannan na wuce d'akina ina shiga na ajiye kud'in na zuba ruwa na tafi dan tsarkake jikina banyi ko azahar ba kuma ga la'asar ta kusa..
Saida na gama sallolina sannan na dafa indomie naci, bayan na gama na zazzage buhun kayana na zuba kud'in a k'asa sannan na d'auki kayan na maida daga sama, fitowa nayi tsakar gida na nufi majalissar matan aure....
Barkan ku da hutawa mata masu duniya, Karima tace wai ke duk yau ina kika shige ne ? Ban bata amsa ba na canja tambayar da cewa yau kuma zawarawan anguwar nan dame suka zo mana ne ?
Karima tace ai gasu nan sai ki zauna ayi dake, zama nayi saman takalmana sannan na kalli inda Nana take kwance a saman cinyar A ` i wai tana kakkab'e mata dandirof,
Karima kuma sai cewa takeyi Allah dai ya tsinewa talauci albarka, kullum a rasa abinda za'ayi ta baka sai tuwo maganar d'aya dai tuwo tuwo babu wani ci gaba kullum zance kenan, shi yasa gani nan kullum sai bushewa nakeyi ina k'armashewa kamar mai cutar kanjamau.
Niko da bani da zuciya nace aiko Karima ki godewa Allah, domin dai Allah yayi miki rufin asiri ke kin raina tuwo ko ? Na tambayeta, bata bani amsa ba naci gaba da cewa yo aike cin tuwo yanzu basai wanda Allah yaso yake ci ba ? Da safe kina dama d'an kokonki da rana idan Allah ya hore zakiyi d'an wanke ko teba wata rana ma har taliya kuke dafawa, da daddare kuyi tuwo kuci ku k'oshi keda "ya "yanki kuma duk daren duniya naga sai mijinki ya shigo miki da fura, tou ina laifi ? Aike tsakaninki da Allah saida kice Alhamdulillah bawai ki zauna kiyi ta tsinewa talauci ba ai ina ganin haka kamar rashin godiyar Allah ne.....
Saudatu tace, { itama ba'a gidan take ba shigowa takeyi } ai rayuwa tana san canji kullum abinci d'aya an kama dindindigau kamar kukan mutuwar uwa, ai ya kama a samu sauyi mana Sultana.
Nace haba Saude ai duk namijin da kikaga ba'aci mai dad'i a gidanshi ba tou baya dashi babu namijin da yake so a tsarewa iyalinshi, Saudatu tace ai wallahi k'arya ne mijin Karima yana da kud'in da ko naman rago saiya ciyar da ita dashi, dandai kawai had'in fad'a baida dad'i amma wallahi dasai na fad'a mata abinda yakeyi da kuma inda yake kai kud'in nashi , ita ya rainawa wayau ya barta nan tana ta sassak'ar tuwo sai kace matar ladar noma.
Daga wannan maganar har Karima ta kawo wuya, ta fara zazzaga luk'a luk'an zagi tana cewa ai da ganin biri yayi kama da mutum tsakanina da Nuhu sai Allah ya isa ban yafe mishi ba, kuma zai dawo gidan ya sameni saina ci uwarshi....
Kallon Karima nayi tare da cewa idan dai kuna biye ma zawarawan anguwar nan wallahi duk sai sun kashe muku aure, baku san maganar d'auka ba baku san abinda kuke fad'a musu ba ku biye musu su kaiku su baroku, su basuyi aure ba kullum suna biye daku suna halakar daku,
Karima tace ai wallahi Sultana na yadda da maganar Saude saboda rabon da muyi kwanciyar aure dani da Nuhu yau anfi k'arfin wata d'aya, dama idan ba neman mata yakeyi ba ai kema kinsan abunda bazai yuwu bane ba....
Tsoki nayi tare da cewa ai wallahi saina fad'a miki ko zatai miki zafi, ba Nuhu ba wallahi koni dakel nake iya zama kusa dake, mace da aka santa da gayu da kwalisa da k'amshi da tsafa da tsaftacewa tou ku matan gidan nan ba haka kuke ba, kullum safiya kunzo kun jibge a k'ark'ashin inuwa ba wanka ba wanke ido babu sallah bare salati, baki cuwai cuwai ba abinda kuka sani saidai inuwa ta k'are ku ja tabarma ku k'ara gaba,
Kun fito tun kafin mazajen ku su fita daga d'akin ku kun rigasu fitowa, yara sun kwana zabga fitsarin kwance baku tsaya kun gyara kun wanke ba, yanda namiji yabar d'aki haka zai dawo ya taddashi, baku iya magana da mazajenku ba kuna ma mazanku magana muryarku ta kere tasu mace da aka sani da sanyi, kina ma miji magana tsawa tsawa kamar yaron gidanki, duk daren duniya idan Nuhu ya dawo sai yayi wanka ya tsaftace jikinshi a haka zai rungumeki ki b'ata mishi wanka ?
Kalli kanki Karima ji k'afafuwanki waike matar aure ! A haka har kike tunanin namiji zai samu kwanciyar hankalin da zai baki natsuwa ? Aini wallahi ko toilet na shiga mara tsafta banda natsuwar da zanyi komai a cikinshi wuta wuta zan fito dan kar in d'aukowa kaina cuta, gashin hamatarki ma kad'ai wallahi abin zubar da yawu n....... Mik'ewa Karima tayi tare da kaimin duka dan uwarki ni kike cewa kazama ce ?
Rik'e mata hannuwa nayi duka tare da cewa saurara kiji ni bance miki k'azama ba kawai dai ina fad'a miki matsalarki ne, amma kiyi hak'uri ni ba'a fad'a dani gaskiya ce baki so kuma daga yau na daina insha Allah, amma duk da haka zan baku shawara d'aya dake da Nana wala Allah tayi muku dad'i wala Allah tayi muku zafi Nana tace ki rik'e banzar shawararki kila ta miki amfani can gaba..... Murmushi nayi tare da cewa tou ba damuwa na gode amma kuma ku sani bazan daina zaman majalissar nan ba, yanzu ma sallah magrib zanyi na dawo...
Babu wanda ya bani amsa dan haka naje na d'auk'i buta ta naje nayi alwallah, saida nayi sallah isha'e sannan na fito majalissar su......
19/08/2019
*NICE DAI...*
*JAMILA MUSA...* 🤙🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 13
Sallama nayi musu amma babu wacce ta amsamin, na maimaita sallamar har sau ukku amma dukansu babu wacce ko kallona tayi bare nayi tunanin zasu amsa min, murmushi nayi tare da cewa aikin banza kare da gudun layya.
Wuri na samu na zauna, ina zama gaba d'ayansu suka tashi suka bar wurin aka barni zaune ni d'aya kamar mayya, banji wani damuwa ba haka banji bak'in ciki ba domin dai nasan gaba d'ayansu nafi su ta ko ina da ko ina, tunda kuwa nafi su ai babu dalilin ni na biye musu muyi gaba, bawai dan ban iya ba na iya kuma idan na fara nawa bashi da kyau....
Ban tashi a wurin ba na haska wayata na fara kwafar lambar Alhaji daga saman takarda zuwa cikin wayata da nayo mishi vidio, nafi minti biyar ina rubutawa karantawa ne dai bana iyawa amma ina kwafar abu, idan kuwa zan kwafa da guda guda nake d'aukarshi, kuma zansa a bud'emin whatsApp amma ya zamar min na "yan gaisuwa saidai duk wanda zanyi magana dashi inyi masa voice note, na ajiye number shi a wayata, abinda na saka mishi shine lamba 1
Mik'ewa tsaye nayi tare da cewa bak'in ciki da fushi ba naki bane Sultana tunda kina da aikinyi, d'aga muryata nayi tare da cewa waye yake san k'amshi mu bashi turare ? Tou tabbas maik'o saidai a barwa balangu ansha gaban mai tsiri......
Kujerata na d'auko na zauna k'ofar d'akina tunda na lura suna neman su haramta min zaman tsakar gidan ne kuma aradu basu isa ba, watsa kunnuwa na nayi ina jiyo firarsu k'asa k'asa bana iya cewa naji abinda akace duka ba amma da yake Saude bata iya maganar sirri ba, bama itama ba duk matan gidan ga haka suke, ji nayi tana cewa ai wallahi ki had'ani dashi in nemi taimako....
Daga inda nake zaune nace hattara dai matar aure, idan dai an ciza a busa, ki kiyayi duniya da rayuwar mutanen cikinta, ita duniya da kika ganta juyi d'an magwaro takeyi yayin daya fad'i k'asa zai kwaso k'asa da tsakuwa, idan kika wanke zak'in zai fita idan kuma kika sha baki wanke ba zaki ci da k'asa duniya tafi karfin kowa, wanda yafiki iskanci yazo yayi ya koma ki kama kanki kuma kiyi k'ok'ari ki koma gaban Allah kina mai kamanta gaskiya, amma na horeki da ki kiyaye darajar aurenki tun kafin duniya ta juya miki baya....
Cikin hayagaga Nana tace ai ba tsoronki akeyi ba a gabanki ma za'ayi maganar dan kutumar ubanki idan kin isa ki hana wani abu in gani, tirr na fad'a tare da cewa kutumar ubana tafi k'arfin kaff zuri'arku wallahi, saboda ko da yake raba kutumar wa mata badai irinku masu tsamin daud'a ba...
Kaina Nana tayo da gudun bala'i kafin ta iso na d'auki kujerata na rik'e nace wallahi kika kuskura kika iso nan saina raba miki kai gida biyu, tsoro ya hanata ta iso taja tayi tsaye, tsoki nayi tare da cewa k'aryar rashin kunya sakarkarin banza daku, insha Allah ko gani nayi zaku shiga wuta saina watsa muku fetir, ina fadin haka na shige d'akina na kyale jahilai, dan gaskiya na lura wallahi jahilci ne kawai yake cizar musu kwalwa, inma banda b'atar basira matar aure za'a kai wurin wani namiji ta nemi taimako.....
*** *** ***
Sati na d'aya kenan bana shiga safgar kowa a gidan da nake haya, ni dama fil'azal magana bai dameni ba, shigowa na ma gidan nan ne naga har na iya surutu idan dai har magana da sune zaisa su raina ni har kowa yake k'ok'orin magana kad'an ya dakeni tou na fita sabgarsu danni ina da wata irin zuciya da idan har na gama da abu tou fa tabbas na shafe labarinsa a babin rayuwata, niko nace hada Dikko Sultana ?
Cikin kud'in da Alhaji ya bani na shiga kasuwa na kwankwaso tsadajjiyar sutura, na siyi kaya na kece raina, gyale takalmi jaka turaruka mayuka na shafawa irin ya wayayyun mata, agogo sark"a da "yan kunne "yan hannu zobuna saida na tabbatar nima na zama gogaggiyar mace ta sahun farko a fanni sutura.
Sannan naje nakai dinki wurin telan da nasan shima yasan hannunshi, kuma da naje kai d'inkin na fad'a mishi cewa irin d'inki karuwai nake so yayi min, nace yamin d'inkin dako tuk'i namiji yakeyi idan na wuce saiya dakaya saiya manta da kan sitiyari yake ya tsaya ya kalleni, mukayi tsada dashi na biyashi kud'inshi tare da sharadin idan fa ya lalatamin kayana wallahi saiya biyani, yace kuma yaji ya yadda.
Na gyara d'akina sosai nasa kayan kallo na sake katifa mai kyau na saka ledar tsakar d'aki na saka fanka amma ta k'asa, na kuma k'ara biyan kud'in haya daga lokacin da suka k'are daga lokacin zan siyi gida haka shine tsarina na gaba... Saina sayi gidan zama sannan zan sayi mota kuma duk zakuji ta inda kud'in zasu rik'a fitowa babu b'ata lokaci....
Hankalina kwance banda wata damuwa, banda rashin ci haka kuma babu rashin sha, cikin "yan kwanaki k'alilan na fara sauyawa, k'oshi babu abinda ya bari dan duk daren duniya sai naci nama abinda nake so ci nake ci kuma duk abinda naga dama shi nakeyi babu mai kwab'a kuma babu mai kyahra, jikina kuwa yasha mayuka gani bana jin wahalar wanka dan ko agwagwa bata kaini san ruwa ba, ya jama'a ku tayani hasko kyau ya had'u da gayu, ku tayani ganin gayu ya had'u da wanka, ku tuno wanka ya had'u da k'amshi...... Wuta Sultana lokacina ya fara...... Kalu bale gareku k"azaman mata.....
Kwance nake saman katuwar katifata da tasha shinfid'a da tsaftataccen zani, { bedsheet } iskan fanka sai kad'ani yake ta ko ina, ga wani ni'imtaccen k'amshi dake tashi daga d'akin har jikina, yanzu tunani na bai wuce in addabi Bello ba abokin Babana.....
Dan yanda ya haramta wa Babana wali a cikin garin shi, inda aka haifeshi ya girma a ciki yayi iyali, amma ya gudu ya bar "yan uwa da "ya "ya da matanshi tou shima katsina zata haramta yayi wali a cikinta, idan kuma yayi iskanci saiya d'aure kayanshi yabar birinin katsinar gaba d'aya....
Hannu na, na saka k'ark'ashin katifa na jawo wata "yar k'aramar kwalba dana anso hannu wani d'an daba, ya fad'amin sunan abun amma wallahi kafin inzo gida har na manta, abun fesawa gareshi kamar na turare, kud'i na bashi ya siyomin nace mishi abinda idan na fesawa mutum kawai zai kama bacci babu b'ata lokaci shine ya kawomin shi....
Tashi nayi na rufo d'akina dan ina so in gwada inga ko abun yanayi, saman katifa na kwanta sannan na fesa shi a fuskata..... Luuu wani bak'i na gani ya gittamin daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba saida 11:30am tayi.....
Salati nayi tare da godewa Allah dana farka na ganni a duniya, d'auko kwalbar nayi tare da sunbatar ta, tabbas kece abokiyar tafiyata, amfani biyu zakimin daga Bello sai Dikko daga nan aikinki ya k'are zan yadaki shikenan.....
Wanka naje nayo tare da d'auro alwalla nazo nayi sallah asuba da ban samu nayi ba, ina gamawa na hau shiri domin yau ba abinda zai dawo dani gida sai nayi ido ido da Bello kuma saina tabbatar da k'udurina akanshi.....
Mai da powder na shafa sai kwalli dana shafawa idona, ban shafa jan baki ba saboda bakina baya buk'atar shafe shafe sai kuma lura da nayi da irin manyan mata mawuyaci kuga sun daddab'awa fuskarsu irin abinda muka shafawa, irinsu jagira aishadow duk basa shafawa shi yasa idan suka shiga wuri suke fita daban, bana buk'atar bilicin koda na kasance ni b'aka ce shima ku lura da kyau bilicin na maciyata ne, d'iyan masu kud'i basa shafe shafe mayuka gaskiya....
Doguwar rigar shadda getzner na saka bak'a, kuma tayi matuk'ar martabani domin dai ta zauna min a jikina ciff na d'aura d'an kwalina coge, na kawo gyale na ida kafe wankan dashi komai dai dana san zai martabo min mutunci na saida na saka a jikina, sannan na yayyafa ruwan turare nayi gaba...
Tun kafin in fito k'amshin turarena yakai tsakar gida, a lokacin dana fito ina rufe k'ofar d'akina kuma gaba d'aya hankalin duk wanda ke gidan saida ya dawo kaina, ina rufe d'aki na saka makulli na a jaka na wuce abuna banma kowa magana ba... Da kallo suka bini domin dai sun gane kura ba sa'ar kare bace ba.....
Tunda na fito gida har nakai bakin titi na zama abin kallo ga jama'a , ban damu dasu ba domin dai duniyar yanzu gaba na bata ba baya ba.....
Napep na tare na fad'a mishi inda zai kaini na shiga muka tafi, cikin "yan mintoci kad'an muka isa, na sauka na bashi hak'k'inshi, majalissar ciki take kamar zata fashe saboda yawan dandazon mazan dake cikinta, ina fitowa napep duk wanda ke wurin idonshi ya dawo kaina...
Banji fargaba ba haka kuma ban daburce ba, banji bazan iya tafiya ba dan ana kallona duk wani bargaba da kunya ko tsoro duk basa tare dani a wannan lokaci, tafiya na farayi zuwa wurinsu na k'addara ma kawai ba maza bane mata ne....
Tsofaffin banza tun daga yanayin kallon da sukemin zaku gane duk sun fad'o rami, kallon tarko suka faramin kamar mage ta ritsa bera. Sallama nayi musu yayin dana isa wurin, kusan gaba d'ayansu saida suka amsa kamar ana biyawa dalibai karatu....
Nima kujera naja na zauna sannan na gaishe su, duka suka amsa cikin sakin fuska, inda Bello yake zaune na kalla tare da cewa Baba wurinka nazo , tou yace amma ban ganiki ba, sadda kaina k'asa nayi sannan na d'an murmusa cikin sigar bariki nace d'iyarka ce ta wurin Aliyu Binna...... Na k'arasa maganar tare da d'ago kaina na kalleshi da kyawawan idanuwa na da suka sha da ado da kwalli nakai karshen maganar tare da d'an sassauta kallo na, sannan na bud'e idanuwan dukansu,
Yashe baki yayi yana dariya kamar yaga wawan zama, sannan yace ahaf tou tou Uwar masu gida ce ? Murmushi nayi tare da cewa Eh, kinyi aure ne ? Ya tambaye ni ? Da kaina na bashi amsa cewa A , a, tou kina ina ne haka ? Ba tare dajin kunyar kowa ba nace ina bariki ne ? Dariya yayi sosai tare da cewa "yar gari kenan yarinya ta gane makoma.....
Nima dariyar duniyanci nayi harsai da kyawawan hak'orana suka bayyana idan dai nayi irin wannan dariya ni kaina nasan tana k'ara min kyau sosai sannan na kalleshi nayi murmushi sai kuma na kama kaina, kallon maita ya bini dashi kamar ya cinyeni a bakin titi sannan yace ina kike zama haka ne ? Ina nan tsohuwar anguwarmu daka sani dai....
Tou taso mana ya fad'a tare da mik'ewa, a raina nace wato tunda na zama karuwa bari a bini a lalace ! Zakaci ubanka domin nima kaina tsoron kaina nakeyi, duk a zuciya ta nayi magana....
'Daukar kujerata nayi muka matsa gaba, zama nayi na d'ora k'afa d'aya saman d'aya sannan nace ya ake ciki Baba ? Am tou aike zan tambaya kinga tunda ga gida ai ba'a kai k'aruwa waje ba....
'Dan gajeren murmushi nayi sannan nace gaskiya kam, amma yanzu kana da mota kuwa ? Eh akwai mota hannuna mana, wace iri ce ? Na tambayeshi yana k'ok'arin fad'amin nace dakata ma barshi kawai kasan ko ka fad'a bazan rik'e ba zan manta ne ,
Duk'owa yayi kusa dani waini zai tambaya yanda muka k'are da Dikko kwanaki, dariya nayi sannan nace ai Dikko ba abinda yayi min kuna tafiya yasa aka dawo dani gida, tsoki Bello yayi tare da cewa kaji sakaran banza wannan tunjumemiyar mace ya bari baisha ruwa ba ?
Murmushin mugunta nayi tare da d'aga girarena nace kila bayajin k'ishirwar ne, tou waike kawai sai kika fara bariki abunki ? Nace sosai ma, tou ya akayi kika zab'i wannan harkar bayan baki san yanda abubuwan suke ba ? Duk zan baka bayani idan kana da wurin saukeni mu tafi kaji komai....
Tou ina zuwa, ya fad'a tare da tafiya wurin abokansu, sallama yayi musu tare da cewa zai dawo da daddare duk zasuji bayani, wani ne daga can yace kayi min register idan ka gama ina layi nima.... D'iyar abokinku maimakon kuyi k'ok'arin d'orani hanya A , a, saidai kuyi k'ok'arin k'ara dilmiyar dani....
A mota ya d'aukeni muka tafi, ko a hanya sai wani kyarma yake yana k'ok'arin kai hannunsa cikin rigata, kallonshi nayi tare da cewa saurin me kakeyi haka ne wai ? Ban bari ya bani amsa ba naci gaba da cewa ko da kayi tunanin yau zaka sameni ? Yace a , a nace tou kasa ma ranka natsuwa har muje inda zamu baje kolin iskancin namu muci karenmu babu babbaka babu wanda yaji kuma babu wanda ya gani...
Kyah kyah kyah ya kyalkyale da dariya tare da cewa gaskiya ne Uwar masu gida, kunji ihu kura ta samu nama, wannan dariya itace yayi shi ya samu Sultanar banza zaije ya gurji banza a tunaninshi, baisan ni nafi shi iya iskanci ba domin dai ni naci uwarshi nasha ruwan kanwa maganin kwarnahin ciki....
Har muka iso ban sake magana ba, horn yayi mai gadi ya yaye mana get muka shige ciki, parking yayi sannan yace muje, kai jama'a kuji rashin kunya don Allah dan kwatawalci d'iyar abokinka, uhum cije lebona na k'asa nayi sannan nace masa rubutamin number wayarka don Allah a takarda, yo baki da waya ne ? Ya tambayeni cikin gatsali, murmushi nayi sannan nace aini ko a cikin kwarin k'arama ce har yanzu da sauranmu kafin mu gama nuna Baba....
Hahaha a haka ma baki nuna ba ? Nace yo dana nuna ka ganni a napep baki da dama yace tare da fara rubutamin number wayarshi, mik'omin yayi bayan ya gama, yana k'ok'arin fita nace ka sallameni kafin mu shiga mana.....
Dubu biyar ya mik'omin , ansa nayi tare da jujjuya kud'in nace ashe gara da bamu shiga ba, yo Baba banda abunka wannan ai ko kud'in fira baka biya ba, zaro ido yayi tare da cewa dubu biyar ? Ke kin raina dubu biyar ? Murmushi nayi tare da cewa tou turaren dana shafa idan akace maka kayi tukwuici ai kasan nafi k'arfin ka bani 5k , koni ai nayi kyautar dubu biyar wallahi, ka bani kud'i masu yawa idan kana bani kaji malam....
Daga gaban motarshi ya jawo wani wuri kud'i na gani kamar in zabgaga ihu saboda yawansu , saida na gani sannan ya maida ya rufe kin gansu nan kud'in da zamuyi caca ne na had'a gobe na k'ara miki ki anshi 5k in mana...
Babu gardama na ansa muka fita daga motar dukanmu muka shiga ciki, saida ya rurrufe ko ina mu kuma mukayi ma junanmu masauki saman gado..
K'ik'iy k'ik'iy ya cire riga ya cire wando, jakata na bud'e na d'auko kwalbata sannan nayo wurinshi cikin karairaya, yana k'ok'arin rungumata nayi ma shege feshin maganin sauro, babu b'ata lokaci ya tafi bacci rik'eshi nayi har yakai k'asa sannan na cire mishi gajeren wandonshi na dauki d'an iska hoto, nayi mishi kuma vidio ko ina saida na d'auka, bayan na gama na janye shi daga saman hanya, saida na lalube aljihunan shi kaf sannan na zauna gefen gado na shigar da numbershi cikin wayata, bayan na gama na ajiyeshi da lamba 2.
Makulin motar na d'auka da jakata na bud'e d'akin na fita, cikin mota na koma saida na kwashe kud'in nan kaff sannan na rufe na maida makullin kusa dashi na ajiye, fitowa nayi na tunkari hanyar fita daga gidan, dubu biyar d'in daya bani itace naba mai gadin gidan kyauta, yana ta godiya na wuce abuna ban tsaya saurarenshi ba na fice daga gidan abuna..........
20/08/2019
*JAMILA MUSA...*
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 14
Saida ma na fita daga gidan nakejin wani irin bak'in ciki ya tokaremin zuciyata, wallahi dana iya mota saina taho da motar Bello, zanje gida na jira zuwan shi domin dai nasan nabar baya da k'ura babu yanda za'ayi ya barni na ci kud'in nan , murmushi nayi sannan nayi magana a bayyane cewa Allah ya kawo ka lafiya Baban kwali Baban tusa.....
Ban tsaya wasa ba haka kuma banyi gigin biyawa gidan kowa ba na yanki santa na fara neman gidan da nake kwana....
Tafiya mai zurfi nayi kafin na fito bakin titi, Allah kuma ya taimakeni ina fitowa na samu abin hawa ban wani b'ata lokaci ba, ko ciniki ban tsaya yi ba na afka nace muje.
Inda zamuje ya tambayeni, ni kuma na fad'a masa yaja muka tafi, raina fes zuciyata dunk'ule da farin ciki na isa gida, ko mai napep 1k na bashi yayi ta zabgaga min godiya tare da jawo addu'o'in samun nasara a rayuwata...
Godiya nayi masa sannan na shiga gida da sallama kamar yanda na saba bawai dan zasu amsa min ba, a , a, inayi ne dan fita hak'k'in musulinci, kai tsaye k'ofar d'akina na tsaya na ciro mukulli na bud'e na shige abuna....
Saida na fara adana kud'ina a ma'adana mai sirri sannan na fara neman abinda zanba baba uban ba'u, { ciki } saida na d'ora girkin abinda zanci sannan na fita nayo alwallah dan ganawa da mahalicci na...
Bayan na fito daga bayi ne naji su Saude suna fira kuma ga dukkan alamu zance Dikko ne sukeyi, da wutsiyar ido na kalli wurin, wata bak'ar cikakkiyar buduwarce na gani tsaye, amma ban tab'a ganinta ba sai yau, kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar tanaji da hutu domin ta huta d'in, duk inda ta fito yarinyar can d'iyar wani attajiri ne...
Fasa alwallar nayi na tashi na koma d'aki na kashe d'an gass d'ina na d'auko asawaki dan inaso inji inda labarin nasu zai tsaya, dawowa nayi na zauna ban kalli inda kowa yake ba kuma banyi ma kowa magana ba na tusa buta a gaba naci gaba da gogo asuwaki a bakina....
A ` i ce ke cewa kai amma gaskiya Hafsat baki da hankali ai da ki nemi d'an mai kud'i da asiri gara ki tafi tsirara kawai ki huta, kina ganin ubanshi banza ne ? Wannan Dikkon da kike gani tun yana ciki an gama dafashi da asiri yanda Babanshi yasha wahala kafin ya samu namiji kina ganin daya sameshi da wahala zai barshi ne yai ta yawo figifigi a duniya ba tare da an bashi dafa'i ba ? Kai wallahi kimayi hak'uri ,
Cikin muryar sakataccin "ya "ya tace no ai da ina kiranshi wani lokaci yana d'aukar wayata amma yanzu ya daina d'auka kwata kwata, da sauri na d'aga kaina na kallesu sai kuma na basar kamar ina kallon wani wuri, wato ita tana ma da number Dikko, tunani na farayi yanda wayarta zata zo hannuna na, ba ansar wayarta zaimin wahala ba yanda zan gano sunan Dikko shine wahala a wurina....
Kawai gaba d'aya tunanina ma har ya tashi daga d'aukar number, kawai harma na hango gani nan na d'auko tsiraicin Dikko na balbad'a a social media, tabbas Dikko saina had'a shagalin partyn wulak'anta mishi rayuwa.... Tunani na ya dawo ne a lokacin da naji Saudatu na cewa aiko ki dage yarinya dan nan da shekara d'aya Dikko baya rik'uwa, tunda shi dama bai dogara da kud'in gidansu ba gaskiya Dikko yana da sa'ar rayuwa idan kika auri shi kin more rayuwa domin dai cikakken namiji ne...
Banyi musu magana ba dai naci gaba da goge hak'ora na, wayau sukayi ma Hafsat suka amshi kud'i masu yawa a hannunta da sunan za'ayiwa Dikko asiri, ci gaba da tattaunawa sukayi amma hankalina baya wurin firarsu ya tafi wurin karatun halayyar Hafsat, tab'e bakina nayi a bayyane nace itama dai "yar mad'igon ce { Lesbian }
Kallona tayi nima na watsa mata mayatattun idanuwana masu sa mutum ya rikice na k'ura mata su sosai domin ina so ta yabani idan har ta shigo hannu na nice zan koya mata barikin da zata kawo min Dikko k'asan k'afaafuwana nima in rama wulak'anci da yayi min dan nayi alk'awari nima sai Dikko ya lashi k'afata kamar yanda yasa na lashi tashi...
Shegiya ta kuwa daskare ta kasa barin kallona, kyakkyawan murmushi nayi mata tare da cewa sannu ko ? Na k'arasa maganar tare da d'an wasa da idanuwana... Murmushi tamin tare da cewa ya kike ? Ban bata amsa ba naci gaba da alwallata...
Ina gamawa ban sake bi ta kansu ba nayi d'aki inajin tana ta magana amma na basar da ita, nadai juya ta ganni maza ma sun gani sun rikice ina ga mata mayun mata kuma ?
Ina shiga na kunna gas ina na kabbara sallah. Bansan yanda suka k'are ba, amma nasan tabbas saita dawo saboda taga ina da irin k'addarar da suke nema...
Bayan na gama sallah na zuba abinda zan dafa a tukunya sannan na zuba ruwa na tafi wanka, lokacin da nayi wanka na dawo har ya dahu, dan haka kashe gas ina nayi sannan na shafa mai da powder, d'aurin gaba nayi sannan na zuba abinci na naci gaba daci....
Bayan na gama duk abinda nake na kunna kallo, sannan na saka kayan bacci na koma saman katifa na kame kamar d'iyar wani shege... Kai gaskiya inajin dad'in wannan rayuwa tawa, saida na kwanta sannan na bud'e data ta, lamba d'aya na gano bayan na ganoshi na tura mishi vidion dana d'auko , tare dayin voice note na tura mishi. Ina turawa na sauka online na kashe wayata gaba d'aya, na kashe kallo na rufe d'akina nayi kwanciyata.......
Tashin hankali shine kalmar da Alhaji ya fad'a a lokacin da yaga vidion dana tura mishi, wata irin gagarumar zufa ta yayyafo mishi a lokacin da ya saurari voice note ina, tashi yayi tsaye cikin tsananin tashin hankali ya rasa gane a wace rayuwar yake rayuwar mutuwa ce ko ta duniya ?
A gefe kuma wayarshi ce take ta kwarara ihu, lambar mai gida Dikko ce keta tsalle babu k'ak'k'autawa amma Alhaji yau kam bata Dikko yake ba, saida kiran ya tsinke sannan Alhaji ya sake kunna maganar Sultana yana sauraro, ga abinda take cewa....
_Ina mai farin cikin sanar dakai wannan mummunan labari, d'abi'a na ne yin albishir da farin ciki yayin fad'ar abu mai munin gaske, kuma nakanyi farin ciki yayin fad'ar abun farin ciki, wannan vidion dai dani dakai ne a ciki kuma kaga irin bad'alancin da muke aikatawa a ciki, nidai banajin komai idan wani ya gani domin ni iyayena tuni sun sallama ma duniya ni, saboda haka ni duniya itace uwata kuma itace ubana, idan na yad'a wannan vidio banajin komai tunda biye nake da mutanen cikinta ina basu, nayi tunanin maidashi faifayin filet na sidi dan in siyar na samu kud'i , sannan kuma in watsashi a yanar giza gizo dan inyi suna, kai kuma kana da dama d'aya tak data rage maka, idan har ka bani naira miliyan d'aya nayi maka alk'awari zan goge shi sai in hak'ura basai nayi suna a duniya ba...... Idan kuma baka dasu in turawa "ya "yanka ko suna da kud'in fansar ka ! Sultana, Sultana ce yarinyar mai dogon zamani, idan kuma kace zakayi gigin sako hukuma a ciki na riga dana turama k'awata nace da taji an kamani firr zakaji su sun watsu a duniya kamar saukar tsuntsaye. Ka huta lafiya habibinah muah_ 💋
Goge zufa Alhaji yayi tare da cewa Allah ka tsinewa yarinyar nan albarka, shegiya tsinanniya ubanta da uwarta basuyi addu'ar kwanciyar aure ba yayin da zasu kwanta Allah ya basu cikin d'ebabbar albarkar yarinyar nan, a daidai wannan lokacin kiran Dikko ya sake shigowa.
Jiki a sanyaye Alhaji ya kalli wayar tare da cewa mai gida kayi hak'uri wannan abun kunya ina za'a dashi na watsu cikin duniya ina zina, abun bak'in ciki da d'iyar da nayi d'iya da ita, garin ciye ciye na har naje na ciwo ma kaina bala'e, kila sai ta k'arar da arzik'ina, kuma tace idan na fad'awa hukuma taba k'awarta vidion zata yad'ashi wannan shine ciwo ya riga ajali zuwa...
Kuka Alhaji yayi tayi tare mitar ya shiga 3 ya bani ya lalace, wannan labarin abun kunyar waye ma zai fad'a mawa bare kuma yasa ran zai samu wata sahihiyar shawara, kai ya bani ya bani ya bani........😰🙆🏻♂😭, a daren nan Alhaji baiyi bacci ba kuma baibi kiran Dikko ba, wayar Sultana kuma ya kirata yafi so adadin yawan dutsinan da ake jifar shedan dasu amma maganar dai d'aya ce cewa a kashe.......
Da safe , tunda nayi sallar asuba na koma bacci, can cikin bacci naji ana dukan k'ofar d'akina, addu'ar tashi daga bacci d'auke a bakina bayan na gama nace waye ? Na tambaya cikin muryar bacci tare dakai idona saman agogon dake lik'e a saman bangon d'akina k'arfe 10:36am, cikin muryar murna Nana tace "yan sanda aka d'auko miki Sultana....
Murmushi nayi tare da jawo wayata na kunna sannan nace ma Nana da Allah kije kice waye ya d'aukomin "yan sanda ? Cikin farin ciki ta koma zaure sannan ta tambayi d'an sanda waye yake k'arata ?
Fad'a mata yayi tayo cikin gida da har yanzu tanajin dad'in k'arata da akayi, a bakin k'ofar d'aki ta tsaya sannan tace wai abokin Babanki Bello, jinjina kaina nayi tare da cewa tou ina fitowa....
Data na bud'e na nemo lamba 2, hotunan dana d'auke shi jiya na tura mishi tare da yin voice note na antaya ma banza, ina gamawa na kashe wayata, saida nayi wanka naci gayuna na watsa turare na d'auku iyakar yanda hankali baya tunani duk wanda ya ganni saina burgeshi, fitowa nayi banma kowa magana ba na tunkari zaure, dan zuwa wurin hukuma a yanayin talauci yana jawo ma mutum raini....
A k'ofar gida na samu d'an sandan nan ya gama shak'e b'acin rai daga gani yana jira muje can yaci uwata, a yangance na fito cikin aji na kalleshi tare da cewa "yar labai barka da aiki......
'Dan sakin fuska yayi tare da cewa yawwa, gaishe shi nayi tare da ce masa nice Sultana, kallona yayi sama da k'asa sannan yace tou hajiya muna gayyatarki zuwa ofishinmu ai anyi miki bayanin mai k'ararki ko ? murmushi nayi tare da cewa babu damuwa muje amma Allah yasa ba'a cikin motar "yan sanda zaka d'aukeni ba, murmushi yayi tare da cewa ai hajiya napep zamu shiga, ajiyar zuciya nayi cikin sigar jan hankali sannan nace tou ai har naji natsuwa.
Napep muka hau muka nufi c p s , kuma nice na biya kud'in 1k ne na bayar kuma daya anso canji nace ya rik'e yasha ruwa, tunda muka fita a napep gaba d'aya wurin saida hankalin kowa ya dawo kaina, na farko dai ga wanka ga gayu ga k'amshi uwa uba kyau Allah yayi min kyawun da mutum baya gajiya da kallona, ga gashina na tik'ashi nayi mishi wani irin parking irin na wayayyin mata, baka isa ka rainani ba ko waye kai domin sitirar dana saka ita kad'ai ta isa ka gane ni ba sa'ar wasan yaro bace ba.....
Ofishin d c o muka nufa, a ciki na samu Bello zaune tare dashi da wasu abokan Babana, sallama nayi sannan na gaishesu dukansu cikin kyakkyawan yanayi, bayan mun gaisa nima na samu wuri na kame kamar yanda naga kowa yayi.....
Kallona d c o yayi bayan ya gama karanta wata takarda dake gabanshi sannan yace Maryam miya had'aki da Bello ne ? Murmushi nayi tare da gyara zamana nace ranka ya dad'e ai Baba Bello abokin kasuwanci ne, halak'a ta mutunci ne a tsakani na dashi bayan wannan babu komai....
D C O yace tou jiya ina kika had'u da Bello ne ? Ranka ya dad'e majalissar su naje gaishe su, bayan mun gaisa kuma ya tambayeni nayi aure nace masa A , a, yace yanzu ina nake zama ? Nace masa ina zama a tsohuwar anguwarmu daya sani, ya tambayeni ko ina kasuwanci ne ? Nace masa Eh yace me nake siyarwa ranka ya dade nace masa karuwanci nakeyi, tsakanin mai saye da mai siyarwa ai babu fushi anan muka daidai suka d'aukeni muka tafi wani gida, nuna yawan duka abokan Babana nayi sannan naci gaba da cewa ranka ya dad'e dukansu nan babu wanda baiyi ba kuma duk saida suka k'ara zagayawa "yar labai, kuma gasu nan ka tambayesu idan nayi musu k'arya. Kuma cikon kud'in ma har yanzu basu bani ba..
Kowansu zaro ido yayi tare da dafa k'irji cikin yanayin mamaki yace ke mune mukayi iskanci dake ? 'Daure fuskata nayi kamar gaske nace aini banajin kunya tunda dai banji tsoron Allah ba nayi zina wallahi banajin kunya gaban kowa in fad'a nayi, kunyi mana ko k'arya zan muku ne ? Lokacin da bakuyi ba nace kunyi ?
Gaba d'aya wurin hayaniya ta tashi har bakajin bakin wani, d c o ya dakatar dasu tare da cewa suyi mishi shiru, bayan kowa yayi shiru ya kalleni sannan yace ke Sultana Bello yana tuhumarki kud'in shi da kika d'auka. Cikin natsuwa nace wasu iri kud'i kuma ranka ya dad'e ?
Bayani d c o yaimin kamar yanda na sani, jinjina kai nayi tare da cewa idan sun gama k'arata nima zanyi k'ararsu saboda b'atamin suna da sukayi, ranka ya dad'e a gaban idon waye na d'auka kud'in ne ? Nifa bana sata amma ina neman maza gaskiya, duk abinda nakeyi bana jin kunyar asan inayi domin dai duk sana'a sunanta sana'a, idan ma na d'auka aka tambayeni idan nasan na sata kawai zan dawo musu da kayansu in basu hak'uri tunda karuwanci da nakeyi ai ban b'oye ba na fad'a tunda ba abun kunya bane....
Tambayar Bello D C O yayi ko yana da wata sheda ne ? Baida ita tunda an tambayi mai gadi yace shidai bai ganni cikin mota ba, duk iyakar binciken da akayi dan asamu wata sheda babu ita, dan haka aka rubuta takarda cewa an janye k'ara, bayan an gama rubutu aka bani na saka hannu da larabci nayi sigining ina, an mik'e za'a tafi nace ma d c o naga fa sunamin wani kallon hadarin kaji sufa fita ido na, d c o yace ai duk an rubuta, nace to ranka ya dad'e cikon kud'ina kuma sai yaushe zasu bani ?
Hak'uri d c o ya bani tare da nunamin tunda anyi masa sata inyi hak'uri inma barshi da ramuwar biyan kud'in mutane, babu kunya ba komai nace kenan ni yanzu ranka ya dad'e sunci banza ? Duk wanda ke cikin office in saida ya kalloni, nace ranka ya dad'e kafa duba lamarin nan gaskiya ni ba'amin adalci ba, shiru wurin yayi wutar kowa ta d'auke, murmushi nayi tunda basu da amsa nace nawa ake yankar sammaci ? Sammaci ma ake cewa abin ko miye ?
A kotu ake yankar sammaci d c o ya bani amsa tare da fad'amin abinda ake kiran nasu da turanci, oho dai da yake kan baya ganewa kasa maimaitawa nayi saidai kawai nace nawa ne ? Kud'in aka fad'amin na bud'e jakata na bada sannan nacewa d c o ga wanda nake k'ara nan Bello ina tuhumarshi akan b'atar mahaifina daya tafi babu wanda yasan ina yaje..........
21/08/2019
*JAMILA MUSA...*
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 15
*_Had'inkai group ina tare daku aminan albarka, Allah yabar so da kauna ubangiji ya k'ara yadda da aminci, HALIMATU SADIYYA {{ Leema }} HABIBA IDRIS {{ Hubbie }} HAUWA'U USMAN {{ Smasher }} MAIMUNA O . G {{ Aunty Munari.... }} muna tare_*
*_Mrs Abdul-aziz ina godiya sosai da dogon sharhi kuma ngode sosai page 14 na baki shi kyauta...._*
Lahaula walakuwata illah billah, kiji tsoron Allah ke uwar masu gida a ina na b'atar da mahaifinki ? Sharri zaki min ? Kiji tsoron Allah in babu nan akwai ranar hisabi duk wanda yaci zalin wani daidai da kwayar zarra ubangiji bazai barshi ba, ki daina ganin kin samu dama ta tak'in lokaci yasa ki manta da rayuwar gaba, karki biyewa zuciya ki kafa abinda zaisa kiyi nadama wata rana.....
Gaba d'aya jikina yayi sanyi tsoron Allah ya kamani nasan k'azafi da sharri ba abu ne mai kyau ba, kuma addini na bai koyar dani haka ba, amma d'an kamewa na sakeyi sannan nace ni rayuwar dad'i baza ta tab'a zama takaitacciya a wurina ba, jin dad'i na d'aura insha Allah daga nan har zuwa ranar da numfashi na zai k'are, ina Babana yake wai ina ka kaishi ne............?
Cikin nadama Bello yace na rantse da ubangiji daya bani aron lumfashi ya bani aron lafiya nake ganinki nake kuma saurarenki ya bani hankali da tunani idan nasan inda mahaifinki yake Allah ya tsinemin albarka. Wallahi Uwar masu gida bansan inda ya tafi ba na rantse miki da girman Allah. Tausayi ya bani yana rantsuwar yana wani kwantar dakai kamar an ritse macen da tayi cikin shege ta haihu kuma ta kashe d'an....
Kallon D C O nayi tare da cewa "yar labai shikenan tunda yayi rantsuwa baiyi ba kawai na janye, zan iya tafiya ? Na tambayi D C O, cewa yayi na zauna zamuyi magana, zama nayi su kuma su Bello aka sallamesu suka tafi ni kuma naci kud'in banza Ehe....
Ta wutsiyar idona na kalli d c o bayan fitarsu Bello domin ina son na gano tashi manufar a kaina, murmushi nayi bayan na gama fahimtar shi, a bayyane nace lamba 3 tazo kenan, ajiyar zuciya ya sauke tare da tattaro duka hankalin shi wurina yace ranki ya dad'e ya hak'uri da jama' a ? Kallonshi nayi ba tare da nayi magana ba domin wallahi tsarin bakinshi kwata kwata bai burgeni ba. Amma ba komai zan hak'ura nayi maleji dashi haka nan saboda idan na taro watan aug zai gina min gada nabi na wuce ba tare dana sha k'ashin ruwa ba....
Wayan cewa nayi tare da gyara zama na nace Allah dai yasa aiki zaka d'aukeni mai girma d c o, murmushi yayi tare da komawa ya kwanta saman kujerarshi irin masu juyawa d'in nan, sannan yace wai gida zan saukeki idan ba matsala, d'an yamutsa baki nayi tare da cewa na gode amma ni ba gida zanje ba...
Ina zakije haka da rana ? 'Daure fuska nayi dan ya fara cika min ciki nace wurin aiki zanje, wane irin aiki ? Tsoki nayi tare da cewa kai komai sai anyi maka b'aro b'aro kake ganewa ko ? Tou abokin lalata zanje nema.....
Murmushi yayi tare da cewa ke bakya gajiya ? Cikin wuta wuta nace ka tab'a ganin inda mutum yake rayuwa babu abinci ? Yace a , a, nace tou ni da kud'i da karuwanci sune abokan rayuwata, domin sai nayi nake samu sannan naci nasha na kuma d'aura har in fito na burge abokan harka , idan kuma kaima d'an hannu ne karka wani cuci kanka kawai kayi magana idan kajira sai an maka tayaki tou fa lallai zaka kwana da yunwa, amma kayi hak'uri da tambayar da zan maka tsakanin ka da Allah nawa ne albashin ka...... ?
Kallona yayi tare da cewa hajiya maryam kenan , miya shafi albashi da harkar bariki ne ? Bai shafa ba amma ni ina duba nasabar namiji da cancantar shi kafin wata sahihiyar mu'amula ta shiga tsakani na dashi, dan duk wanda ya jawo maganar aure a rayuwarshi tabbas ya tara abun hidima, bata yuwuwa na biye maka ka k'ok'ar dani ba tare da ka sake bani kud'in da zan sabon fenti ba, dan kai kanka da ban d'aukar maka ido ba duk yanda nake barikin baza ka taya ba,
Kallon agogon dake d'aure a tsintsinyar hannu na nayi tare da cewa zama wuri d'aya tsautsayi inji kifi, malam d c o zan wuce ka rubutamin number ka a jikin takarda idan ayyuka sukamin sauk'i akwai dawowa......
Babu musu kuma ba tunanin komai ya d'auki biro da takarda ya gwagwad'amin number wayarshi, ansa nayi tare da mik'ewa tsaye sannan nace sai ka jini, baki bari mu tafi in ajiye ki ? Ya tambayeni, juyawa nayi na fara tafiya tare da cewa ban hawa mota sai napep a daidai lokacin dana fice daga ofishin....
Ina fitowa wuri na samu na tsaya, wayata na fiddo nayi saving in no d c o da lamba 3 , sannan na kira wayar Alhaji, babu b'ata lokaci ya d'auka tare da cewa ranki ya dad'e tun jiya inata kiran ki wayarki a kashe ko yau da safe ma na kira a rufe.... Ban bashi amsa ba nace kawomin kud'in yanzu nan ina nan c p s ina jiranka kuma karka b'atamin lokaci, ina fad'a na kashe wayata......
Lambar Bello na kira amma bai d'auka ba, daga kira d'aya nima ban sake kira ba, domin dai nasan idan yaga abunda na tura mishi shi da kanshi zai nemeni, k'ok'arin maida wayata nake cikin jikka naji ana cewa shegiya k'awata kece kika koma wata hajiya haka ? Da sauri na d'ago kaina domin jin muryar Amisty da nayi...
Cikin farin ciki muka rungume juna, bayan gaisuwa sai kuma muka shiga firar duniya, yayin da nake tambayarta wane ci baya ta samu na bariki naga har yanzu bata fara hawa mota ba, ajiyar zuciya Amisty ta sauke tare da cewa kinsan mazan babu kud'i hannunsu kullum tsuwwa da kukan babu......
'Daure fuska nayi tare da cewa waye ya fad'a miki ana hawan jirgin sama bashi ne ? Ai filin jirgi ma baka shigarshi dole sai kana da tikitin tafiya, haka nan kike basu suna hayewa basu baki kud'in mai, tou ina uwar d'akin taki ne ko bata nan bata fad'a miki illar maza ba ? Haba Amisty idan baki ridowa da yawa wallahi bariki kasheki zatayi, niko kin ganni nan ni zanyi gwanjo bariki kafin ta wurgar dani gefen titi, kinsan bariki bata da tabbas d'auka da ajiyewa gareta, ni zan kashe bariki bazan yadda ta kashe ni ba, zanyi amfani da talata ta kafin laraba ta, ta riskeni, wannan uwar d'aki taki k'atuwar jahila ce batayi karatun komai ba haka nan ta tara yawan dalibai, har yanzu kuna da dama ki nemi canji makaranta ki dawo makaranta ta zan baki ilimi akan namiji, kud'i kike so ko suna ......?
Horn Alhaji yayi da mota wanda tun d'azu yakeyi amma magana ta hana na saurareshi, juyawa nayi tare da nuna mishi da hannu ina zuwa, ni kuma naci gaba da magana da Amisty, wata matace ta fito daga ciki tayo wurinmu kuma ga dukkan alama tare suke da Amisty, gaisawa muka yi yayin da Amisty ta fara tambayarta ya aka k'are, basu bani labari ba suna ta maganar ne cikin munafinci, ni na fahimta suna magana ne kamar tayi ciki..
Datsar maganar nayi da cewa keko ya akayi kikayi cikin shege ? Gaki a fuska kamar wayayya taya akayi haka ta faru ? Ita kuma a tunaninta Amisty ta fad'amin dan haka tace kin gane ni bawai cikin bane matsala a, a mijina yau watanshi bakwai baya nan kuma ga ciki wata hud'u, kuma nayi a zubar da cikin shi wanda yayi cikin yace wallahi bazai yadda ba saboda bai tab'a haihu ba, idan wannan abu ya fito ai kinsan akwai matsala.....
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na fad'a tare da cewa ke matar aure kike zina ? Hasbinallahu wa ni'imal wakim, amma kinyi k'atuwar asara, kallon Amisty nayi tare da cewa zance zaune ba na tsaye bane idan kuna neman taimako ku sameni gida, ina nan tsohuwar anguwarmu idan kika shigo ki tambayi gidan da nake haya za'a kawoki, ina fad'in haka nayi wurin motar alhaji ina zuwa na kama na bud'e na shige nace muje...
Har muka isa gida banyi ma Alhaji magana ba domin ni yau naga macen da tafini kafirci kina k'ark'ashin bautar aure amma kina aikata sab'o, wannan wai wane irin zamani ne muke ciki lallai ya kamata nasan ita kuma wane rud'un duniyar ne yaja mata neman mazan waje ga nata mijin da yake hak'k'inta amma ta tsallake shi ta tafi wurin na wasu , gaba d'aya jikina yayi sanyi kuma na dawo daga rakiyar duniya....
Ansar jakar da Alhaji ya zubomin kud'i nayi tare da direwa daga motar, zaiyi min magana nace mishi muyi waya kawai nayi gaba abu na, lokacin dana shiga gida bana ko ganin gabana saboda bak'in ciki da kishin aure, d'akina na bud'e na shiga, saida na adana kud'ina sannan naje nayo alwalla nayi sallah azahar, yinin ranar haka na yini sukuku kamar wata mara lafiya, koda nayi sallah isha'i kwanciyata nayi , duk yau banda ruwan shayi babu abinda ke cikin cikina, haka na kwanta da tunani iri iri, ko bacci nayi na farka abun yakan fad'omin a rai har gari ya waye da tunanin matar nan a zuciyata..
Da safe bayan nayi kalaci na gyara d'akina naje nayi wanka na shirya cikin doguwar riga ta atamfa da tasha d'inki buba, hula mai raga { net } na saka kaina na fice tsakar gidan....
Kujera na sa a k'ofar d'akina na zauna tunda fitowa wajen ya zamar min dole, kallon inda Karima take nayi sannan na maida kallo na wurin Saude dake zaune saman turmi, babu ko breziya jikinta kuma babu kaya sai siket ondie da taja saman kirjinta, amma komai na halittar ta babu abinda ya b'oye duk a bayyane yake.....
'Dauke idona nayi gefe na kallo inda Nana take kwance A ` i tana durk'ushe ta duk'a samanta sosai suna k'ushin k'ushin, jinjina kaina nayi sannan na sake kai idona wurin Saude nace ke Saude wai da Allah in tambaye ki ?
Murmushi tayi tare da cewa tambayarni kanki tsaye, b'ata rai nayi sosai sannan nace nan gidan ubanki ne wai da zaki zo ki rik'a zama mana tsirara dan baki da kunya ?
Gaba d'ayansu dariya sukayi ,sannan Saude tace tou ke mai tambayar gidan ubanki ne ? Ni nan ba gidan ubana bane amma ya zama na ubana tunda na biya kud'in haya, d'aki d'aya na kama amma ina da hurumin da zan sauke ubana a ciki, ke ko fa ? Nana ta anshi maganar da cewa yanda kike tak'amar kin kama haya muma kamawa mukayi kuma muma muna da hurumin da zamu kawo mutanen da muke so su zauna tare damu, kedai kawai kice kina so ayi dake.
'Dan gajeran murmushi nayi tare da cewa duk wanda yaci naman arne tabbas zai iya cin mushen alade , banda abinki miya had'a makaho da ganin wawan zama ? Ni bana iya cin naman jaki amma idan na samu doki zanci duk da an yanka shi nasan wata rana zanyi hazaka, ko banyi gudu ba tabbas nasan zanyi tafiya, magana ce na fad'a miki a jimlace idan kina da ilimi sai ki warwareta banzanye da ku masu wahalallen bariki.....
Gaba d'aya wutar kowa d'aukewa tayi sukayi shiru babu wanda tace komai, murmushi nayi tare da cewa ba'a bariki dole saida ado kuje ku ibi ruwa kuyi wanka kusa toka ku wanke baki ko ya rage k'annin koko, daga haka ban sake ma kowa magana ba kuma suma babu wanda ya sake cewa komai,
Bayan Alhaji ya bani kud'i ya dad'e k'ofar gidanmu ya kasa tafiya, hankalinshi a tashe saboda yaso yayi magana dani na goge vidion nan kuma yaji ina na dosa ? Amma samsam ban saurare shi ba, kuma yasan lallai saina sake tambayarshi wasu kud'in tunda akwai vidio a hannuna ban goge ba,
Rasa yanda zaiyi yayi zuciyarsa ta yanke mishi kawai ya fad'a wa Dikko komai yasan babu mai iya magani na saishi amma fa a nashi haukar , d'aga waya yayi ya kira Dikko kuma har zuwa wannan lokacin yana k'ofar gidanmu bai tafi ba.
Bayan Dikko ya d'auki waya Alhaji ya gaishe shi cikin girmamawa kamar yanda ya saba, Dikko ya amsa shima cikin mutuntawa, dan a haife Alhaji ya haifi Dikko amma igiyar naira tasa yana k'ark'ashin Dikko kuma k'asan k'asa ma, dan ubangidan Alhaji na ainahi shima yaron Dikko ne na biyu, tou abinda yasa Alhaji yake kiran Dikko kai tsaye saboda yanajin dad'in yadda yake kularmishi da dokunan shi, shi yasa shi Dikko da kanshi ma ya anshi number Alhaji ko wata matsala ta taso ga dokunan shi, dan dama ubangidan nashi na farko kafin yasan Dikko wurin kula da dokuna ajiye shi Alhajin....
Alhaji yace mai gida kayi hak'uri don girman Allah wallahi jiya daka kirani ina cikin yanayin da bazan iya magana ba, cikin jimami Dikko yace meya faru haka ? Wato ranka ya dad'e ina cikin tashin hankalin dana zab'i mutuwa ma da rayuwa, salati Dikko yayi tare dayin murmushi domin shi yaji mugunta, sannan yace Alhaji duk dad'in duniyar wato tai maka d'aci ko ? Alhaji yace Eh wallahi ranka ya dad'e, Dikko yace tou Allah ya kyauta...
Da sauri Alhaji ya fara bayani wa Dikko dan yasan daga Allah ya kyauta kawai zai kashe wayarshi ne yasan baya doguwar waya, ranka ya dad'e wato wallahi wata yarinya ce muka d'an keb'e da ita, tou wallahi bansan yarinyar nan ta shirya sharri ba, ashe duk abinda mukayi ranka ya dad'e tana d'auka cikin waya ban sani ba, tou ta rik'e vidion sai wahalar dani takeyi tana ansar kud'ad'ena, yauma na bata kud'i kuma a police station nakai mata kud'in inaji wani ne ya d'aure mata gindi take iskanci a garin nan....
Murmushin mugunta Dikko yayi tare dayin kamar bai gane ba, yace wane irin vidio ne ? Gyara zama Alhaji yayi tare da goge zufa yace wato ranka ya dad'e harka daice irin wadda muka saba, Dikko yace wadda ka saba dai , wato ka samo daidai dakai ko ? Tou turomin vidion in gani ya fad'i maganar cikin sigar zaulaya, Alhaji yace ranka ya dad'e vidion fa irin na kafirawan nan ne masu d'aukar tsiraicinsu suna yayad'awa a duniya.......
Dikko yace tou banda abunka kace taje ta yad'a ba hada ita a vidion ba ? Alhaji yace ranka ya dad'e ina za'ayi wannan abun kunya tsiraicina a yanar giza gizo cewa tayi fa har "ya "yana zata tura su gani, Dikko ya gaggab'e da dariyar mugunta tare da kashe wayarshi, irin wannan abun Dikko kadai yake ma dariya a duniya, duk abin burgewa ko na nishad'i Dikko baya mishi dariya kuma baya murmushi idan kaga murmushin shi ko dariya yaji ko yaga k'eta, amma kai kana iya ganin abinda zai baka tausayi kayi kuka wallahi Dikko sai yayi mishi dariya saboda tsabagen shi cikakken mugune....
Cikin sanyin jiki Alhaji yaja motarshi ya tafi, Dikko kuwa saida yasha dariyarshi ya gaji sannan ya sake kiran Alhaji, bayan ya d'auka yace tou waikai kawai sai tayi maka vidio ? Alhaji yace Eh ranka ya dad'e Dikko ya sake shek'ewa da dariya sannan yace kai amma wallahi yarinyar nan tantiriya ce ta fad'a a duniya,
Dikko yace tou yanzu me kake so nayi maka ne ? Alhaji yace ranka ya dad'e so nake kayi min maganinta, dariya Dikko yayi sannan yace nima so kake ta d'aukeni ? Cikin biyayya Alhaji yace haba ranka ya dad'e kada Allah ya had'aka shegiyar yarinyar nan.....
Dikko yace aini ko ta had'u dani bata da yadda zatayi dani, nidai bana neman mata kuma bana sabgarsu bana shiga huruminsu gudun raini, kayi hak'uri insha Allah zanzo katsina jibi idan Allah ya kaimu zata goge vidion dan wahala, ranka ya dad'e ai tace ta turawa k'awarta ne, Dikko yace k'arya take kadai jira zuwana .....
Godiya Alhaji yayi sannan sukayi sallama da Dikko,
Murmushi nayi a daidai wannan lokacin sannan nace duk mai niyar yin magani na nice zanyi maganin d'an banza, zomon bana shike maganin karen bana, maganin d'an iska kuma karen maguzawa, dani dakai dashi mu zuba duk wanda ya fasa yaci k'aniyarshi.......
Sallamar Hafsa ce da wasu zugar tantiran mata, a ciki kuwa harda Amisty, kila sunzo ne suci min uwa tunda nace uwar d'akinsu k'atuwar jahila ce, oho koma dai miye su shigo ina jiran isowarsu wurina inji su kuma da wace suka zo................???
22/08/2019
Taku a kullum mai san farin cikinku wato .
*MEELAT MUSA*
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 16
*_Bandai ji komai ba , 71 , 29 babu damuwa zamu rama muma..._*
_____```^^=°°--- Basarwa nayi tare da d'auke fuska ta daga dubansu, mutum dai bai isa yazo har gidana ya dakeni ba, kallon banza ko maganar banza mutum yamin wadda batamin ba wallahi ina da Lamba3 d c o zaici k'aniyar mata....
A daidai lokacin da suka iso gabana maganar zuci ya k'are, Amisty ce tace wurinki fa muka zo kina yi kamar baki ganmu ba, saida na gama kallesu tsaf sannan nace sannunku da zuwa tare da mik'ewa zan shiga d'aki dan d'auko musu tabarma...
Gaba d'ayansu rufa min baya sukayi suma suna k'ok'arin shigamin d'aki, ja nayi na tsaya tare da tambayarsu ina zasu je ? Amisty tace ciki zamu shiga ? Murmushi nayi tare da cewa kuyi hak'uri ku jirani ni bana kai mata cikin d'akina...
Hafsa zatayi magana Amisty ta dakatar da ita, kallonsu nayi tare da cewa barta ta fad'i cikinta, Amisty tace barta kawai d'auko mana kedai, munafikin murmushi nayi tare da juyawa na shige cikin ɗaki, domin ita Amisty tasan wace ce ni, tabarma na d'auko nazo na shimfiɗawa banza nace su zauna...
Dukansu zama sukayi lokaci ɗaya, su A ` i da Saude Nana da Karima duk suka taso suka dawo ƙofar ɗakina, nima zama nayi tare da cewa meke tafe daku ne ? Na ƙarasa maganar tare da kauda kaina gefe ɗaya....
Amisty tace Sultana ke kikace mu sameki gida ! Kallonta nayi tare da cewa sai akayi ya ya ? Amisty tace ai shine muka zo ! Kallon tantiran mata nayi sannan na maida hankalina wurin Amisty nace da Allah daga yau idan zaki zo wurina kidai min kwashe kwashe , da sauri Amisty ta kalleni sannan tace haba Sultana mi yasa haka kuma ?
Kai tsaye nace kinsan bana san munafirci kuma ban tare da munafikai, waccan bak'ar yarinyar da kika gani na nuna Hafsa budurwar Dikko sannan naci gaba da cewa gaskiya aminci take da mak'iya na saidai ta zab'a ni take so ko su A ` i , murmushi Hafsa tayi tare da kallona sosai ni kuma na d'an gyara zama yanda zan d'aukar mata hankali sosai, saboda ina so na rabata tarayya dasu A ` i idan ina tare da Hafsa suma suna tare da ita riƙa zugamin ita zasuyi har su hanani na cimma buruni tunda na lura ita Hafsa doluwa ce kuɗinne kawai ba wayau sai tsabar neman matan bala'e. Kwazzaba tasa har bata iya tantance kifi bata gane kwad'o,
Cikin ruɗewa Hafsa ta fara magana irin ta "ya "yan masu kuɗi, kin gane Sultana nifa ba abokaina bane kawai gaisawa mukeyi sai kuma wata huɗɗa tamu data haɗamu amma ba komai tsakaninmu gaskiya,
Ɗaure rai nayi tare da cewa nifa ba abinda ya haɗaku nake so na sani ba cewa nayi kawai ki faɗa ni zakiyi abokiya dani kibar su A ` i ko kuwa su A ` i kika zaɓa, Hafsa tace haba aike tawa ce kuma ina tare dake, murmushi nayi tare da cewa magana ta ƙare mata tacewa mijinta shege...
A ` i zatayi magana nace dakata malama ta bakin gulbi, ki taka sannu da lafiya kafin insa a ɓatarmin dake cikin garin nan, nuna yawan su Amisty nayi tare da cewa nan da kika gansu duk dalibai na ne, zan fara basu karatu daga jibi idan Allah ya kaimu, na kafa ƙungiya ta mai take *kwarata* duk wacce kika gani anan mabuƙaciya ce, zan haɗa ne zanba mace namiji idan an sallami mace zata fiddani, zan haɗa mata da mata amma a tafiyata ban tafiya da taron banza, sabbin ɗalibai ku na ɗaukeku kyauta basai kunyi register ba, amma daga ba yanzu ba duk wacce zata shigo cikinmu saita ajiye dubu talatin kuɗin register haƙƙina neman maza da mata masu abun hannunsu....
Miƙa hannuna nayi tare da cewa duk wanda yake tare dani ya ɗora hannunsa a saman nawa, kowa ɗora hannunshi yayi harsu Nana matan aure ba'a barsu a baya ba, ku ɗauki alƙawari babu cin amana , gaba ɗaya suka amsa munyi alƙawari bazamu ci amana ba, nace kuyi alƙawari zaku zama ɗalibai masu biyayya, munyi alƙawari zamu zama ɗalibai masu biyya nace idan kun samu ina nan ko bana nan zaku ajiyemin nawa kason, shima suka maimaita, sannan nayi addu'a tare da neman Allah yasa albarka a cikin wannan ƙungiya tamu mai albarka wanda nayi ma laƙabi da *KWARATA* saboda dukanmu lalatacci ne ,
Bayan an gama nace tou kowa ya tashi ya tafi nima zan fita inda fuskar jama'a take na samu gida na siya idan kuɗina yakai, idan basu kai ba kuma zamu kama shago, wannan shago zai zama nan ne kowa zataci gayu da safe taje ta zauna, yayin da zamu kafa ƙaton allonmu ya kalli al'umma, za'a rubuta a gaban shagon ko gidan tambarin *KWARATA* idan ma baka iya ba kazo za'a koya maka.
Zamu rubuta a jikin takarda mukai kuma a buga mana su da yawa, ni zanbi manya ofisoshi da kasuwa da kuma kamfaninika da inda "yan siyasa ke zama saina zabo mana manyan alhazawa sai mu raba musu, duk wanda ya gani ya karanta dama ga number wayata nan a jiki, ku kuma kuna shago kunsha wanka kunayi kuna ƙara powder da jagira ina binku ina muku wanka da turare, da mutum yace zaizo zance ya iso akawai kaya a ƙasa, yana shigowa ya ganku wayyo shikenan labari zai canja salo, ni kuma ina da wata dabara ɗaya amma bazan faɗa muku ba saboda karuwa bata da amana,
Nana tace tou mu da muke da aure fa ? Kallon ta nayi ƙasa da sama sannan nace duk iskanci da kukeyi keda A ` i sai yanzu kika tuna Allah ? Tsoki nayi tare da cewa tunda na lura kema kinasan duniyar sai in ɗaukeki aiki ki riƙa sharewa kina gogewa, ke kuma Karima idan mijinki ya barki zan zuba miki kayan mata da maza na gyaran harka duk wata zan baki dubu biyar ko anyi ciniki ko ba'ayi ba, amma idan mijinki ya barki fa.
Tun kafin in rufe bakina Karima tace koma bai barni sai naje wallahi, dubu biyar fa ? Ina nan kullum zaune gida naira hamsin ma wahala take min , kuma Sultana ki rubuta a jikin takarda duk wanda zaizo ya taho da kaza kinga idan anci an rage ai muma zamu maida miyanmu.....
Kallon Karima nayi sannan nace kazar Lbura'uba, an faɗa miki *kwartancin* wahala zamuyi ? Kudai kuyi ta addu'a a samu bakin titi, addu'a sukayi tayi Allah ya taimaka ya bada sa'a, daga ƙarshe dai kowa ya kama gabanshi, nima na kulle ɗakina na fantsa ma cikin gari...
Ina bakin titi tsaye naji wayata tana ta kururuwa dan haka dole na dakata, fiddota nayi na duba dan ganin mai kirana, Lamba 2 wato Bello kenan, ɗauka nayi tare dayin sallama, bayan ya ansa na gaishe shi, bai ansa gaisuwar ba yace ke Uwar masu gida hotuna na gani ?
Amma ai ka gane ko waye a jikin hotunan ko ? Eh nine , tou kuɗi zaka bani naira budu ɗari biyar nan da gobe idan Allah ya kaimu idan kuma kace babu sai ina watsa su duniya kowa ya kalla kyauta.... Ɗanka da matarka da abokanka duk suna kwance a saman gado zasusha kallo abunsu...
Sirikinka da surukarka zasusha kallon siriki tsirara... Tou nabarka lafiya, ina faɗin haka na katse kiranshi, ina duba yanayin samun mutum kafin na yanka mishi haraji, Bello baida ko sisi kuma baida wata sana'a data wuce caca, kuma caca ba kullum akeyinta ba, gashi kuma na sace kuɗaɗanshi kaff da na gani a mota ba damuwa na bane nidai kuɗi kawai, ina gama waya da Bello na kira lamba3 wato d c o, mai girma ɗan sanda yarinyar jiya ce, Maryam Sultana Aliyu Binna, ya garin ? Haka nayi masa bayani bayan ya ɗauki wayata....
Hajiya ya kike ? Lafiya qalau kana ta ina haka ne ? Yace naje ganin gida ne baby, cikin salon cuta na kwantar da murya ƙasa ƙasa nace kuma "yar laɓai maimakon ka kirani inyi rakiya ? Murmushi yayi sannan yace wallahi nima tafiyar bazata ce wife ina ce bata lafiya, tou lallai wannan kuwa da sa'a take wace ce ita, dan bansan abinda wife in take nufi ba, dana dangantata da mace saboda naji yayi magana da sunan jinsin mace ne, yace wife itace ba lafiya,
D c o yace matata nace, danshi yanda yake kallon wayewa ta ya ɗauka wata shegiyar baturiya ce, danaji yace mata nace ai shine nace wannan tana da sa'a, da kaji kuma nace wace ce ita ina tambayarka amarya ne ko uwar gida ?
D c o yace ai mata ta ɗaya ce, nace tou yayi kyau yaushe zaka dawo ne ? Zan dawo amma sai ta samu sauƙi, to Allah ya sawaƙe ya bata lafiya, d c o ya amsa da amin mukayi sallama.....
Lallai duk yanda akayi wannan matar tashi tasan damarta ne, idan ta riƙe d c o sosai taya zamu samu wani abu a wurinshi ne to ? Wato ita munafika nufinta ita ɗaya zataci ? Taci gidansu bari dai d c o in ya dawo bata ƙara ganinshi dan ubanta ba rashin lafiya ba ko mutuwa tayi sai anyi jana'izarta baije ba....
Napep na hau na nufi gidan Alhaji marenin wayau na, tsoho ya tsufa amma zuciyar bata mutu ba, buɗe na samu gidan dan haka na banka kaina tsaye na shiga, babu dawakuna ko guda ɗaya duk an fitar dasu an share gidan ƙwal gwanin burgewa, sai cire yana akeyi ana wani kakkaɓe kakkaɓe get in gida sai wanke shi akeyi ana goge duk inda yayi ƙura....
Cikin masu sharar na tamabaya lafiya ko Alhaji ya tashi ne ? Yace lafiya qalau bai tashi ba ubangidan shi ne zai dawo gobe, tsoki nayi tare da cewa shine ake ta wani share share ? Yace Eh , Dikko ko ? Na tambayi yaron yace Eh ai ance ma ya iso yana Abuja ko zasuyi me ne ne ? Amma dai naji ance jirgin safe zaibi yaje kano akwai abinda zasuyi sannan zai shigo katsina....
Jinjina kai nayi sannan nace tou shi ina Alhajin ne ? Ai sun tafi kano taroshi, daga nan har kano suka tafi su taho dashi saboda tsabar basu da aikinyi ? Yaron yace ai ba rashin aikinyi bane ba hajiya duk abinda kika ga sunayi dan sun san zasu samu, Alhaji fa baya saida fari baya saida baƙi kiwon dokuna yake amma kiji irin dukiyar dake gareshi, sun san suna samu da D ---K ɗin ne shi yasa suke laƙafe dashi, da yana nan da baya nan kuɗi suke samu kamar tashin hankali...
Tou zan tafi kawai mayi waya dashi, jakata na buɗe nayi ma yaron alheri godiya yayi tayi tare da cewa Allah ya kareki ya ƙara arziƙi hajiya ubangiji yasa kifi haka Allah ya ƙara lilka darajarki ngode sosai. Ban saurareshi ba nayi waje abu na,
Gida na koma saida nayi sallah isha'e sannan na fara nazari akan Alhaji abinda zance masa kawai ya bani mota da gida sai in fita daga harkarshi, dan ni duk inda zanji ƙamshi ko labarin sunan D ---K na tsani wurin tsakani da Allah bana san Dikko na tsani rayuwarshi wallahi, amma idan har Allah yayi min cikakken arziƙi saina wulaƙanta ma Dikko rayuwa,
Wani irin baƙin ciki naji yana tasomin hawaye ya cikamin ido na abinda ya faru tsaƙanina da Dikko ya dawomin sabo fil a zuciyata, zuciya ta tace min ƙaryane baza a fita daga harkar Dikko ba sai na halakashi, kamar mai aljannu lokaci guda na burkuce nayi nayi na saita kaina amma na kasa wuƙa na ɗauko tare da kwarara wani irin ihu nace wallahi saina kashe ka........ Na ƙarasa maganar cikin kururuwa.
Duk wanda ke gidan nan babu wanda baiji ihuna ba, da gudu Nana da Karima sukayo ɗakina amma banda su A ` i saboda yau da wuri suka tafi gida. Lokacin da su Nana suka shigo duk na yanyanki wasu wurare na jikina da wuƙa, abin ya tada musu hankali dakel suka riƙeni suna tambayata waye Sultana kallon Nana nayi cikin kuka nace wallahi saina kashe shi gobe zai shigo katsina bana ko ƙaunar jin irin sunanshi a rayuwata....
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, shine abinda Dikko ya faɗa a daidai wannan lokacin tare da janye ruwan dake gabanshi, hankalin kowa yayo kanshi tare da tambayar lafiya ranka ya daɗe ? Dafa ƙirjishi yayi tare da cewa gabana ke faɗuwa babu gaira babu dalili.
Duk kusa dashi suka matsa suna mishi sannu, kallon babban yaronshi yayi sannan yace maza kiramin gida, ɗaukar waya yayi ya kiro dadyn dikko, babu ɓata lokaci dady ya ɗauka D --- K babu ko gaisuwa yace Dady lafiyanka qalau kuwa ? Murmushi Dady yayi tare da cewa mi kuwa zai sameni ? Bayan ina nan zaune cikin iyalina muna farin ciki saboda zuwanka ! Dikko yace Dady karka ɓoyemin dan Allah miye ? Dady yace tsaya ma kaji, saida ya haɗa Dikko da kowa yayi magana sannan yace kaji ko ?
Ajiyar zuciya Dikko yayi kamar wanda yasha kuka ya ƙoshi sannan yace kawai haka nan naji gabana yana faɗuwa, Dady yace saboda zaka ga ganni ne, kayi ta addu'a Allaah ya tsare kuma kayi bacci da wuri, jinjina kai Dikko yayi tare dayi ma Dady sallama suka ajiye waya....
Dakel su Nana suka lallasheni nayi shiru, Karima tace inyi ta addu'a don Allah sharrin shaiɗan ne, nace tou amma har yanzu ban daina baƙin ciki ba, saida suka tabbar hankalina ya kwanta sannan suka tafi bayan sunsha fama na faɗa musu ko waye naƙi faɗa musu...
Suna fita na rufe ɗakina nayi addu'a na kwanta bacci,
Da safe kuwa misalin 12:45pm na fara gwagwaɗawa Alhaji kira, bawan Allah banda zufa babu abinda yake haɗawa, idanuwanshi sunyi jajir saboda tsabar tashin hankali duk wanda ke wurin saida Alhaji ya bashi tausayi duk da babu wanda yasan abinda yake damunshi, amma banda Dikko dakeyin kyakkyawan murmushin dake fito masa da tsananin kyawunshi, da yasan yanda yakeyin kyau idan yanayin murmushi daya dawwama yanayin fara'a, duk da ko baiyi murmushi ba yana da kyau sosai gaskiya, taunar rainin hankali yake ma cingom in bakinshi sannan yace wai har yanzu ta hanaka ka huta ne ?
Kamar Alhaji yana jira yace Eh ranka yadaɗe, Dikko yace bani ita, Alhaji yace ai kiran ya tsinki, ɗaure fuska Dikko yayi sannan yace kirawo min ita...............
23/08/2019
*JAMILA MUSA* 🤙🏻
Ina mana barka da juma'a,
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 17
_Don Allah kuyi haƙuri mu dukanmu mubi labarin nan a hankali, wannan labari na faɗa muku yanda yake, an rage wasu abubuwa ne wasu kuma an gyara su, labarin yana da yawa sosai ba'ayi komai ba yanzun muka fara wasan , kuyi haƙuri muje a hankali, ni jamila musa nake cewa asha karatu lafiya...._
Gajiya nayi da kira ba'a ɗauka ba dan haka na haƙura banyi yunƙurin sake kira ba, ina ƙoƙarin ajiye wayata kira ya shigo a cikin wayata mamaki ya kamani sosai ganin kiran Alhaji, taya zai kirani bayan ni na kirashi da kaina bai ɗauka ba ?
Haka nan naji tsikar jikina ta tashi zuciyata namin wasi wasi lallai akwai wata ƙullallah da ake son ɗaura min, duk yanda akayi wani baƙon lamari zai faru tou amma bansan ko miye ba, kashedi zuciyata tamin tare da hanani ɗaukar wayar, sau biyu aka kira ban ɗauka ba dan haka suka haƙura basu sake kira ba...
Kallon Alhaji Dikko yayi sannan yace yarinyar nan zata kai shekaru nawa ? Saida Alhaji ya kwantar da kai cikin biyayya sannan yace baza ta wuce sha shidda zuwa sha bakwai ba, D --- K yace tou wallahi wannan yarinya tasan abinda takeyi kila shekarunta ya wuce yanda kake tunaninta tana abunta da lissafi, amma baka taɓa kiranta a waya ba ko ... ?
Alhaji yace Eh gaskiya chat kaɗai mukeyi da ita, sai ranar da ta turomin vidion nan shine na kirata, amma daga ranar ban sake kiranta ba saidai ta kirani, Dikko yace tou jikinta ya bata ba kaine kake kiranta ba shi yasa bata ɗauka waya ba, amma nasan zata kiraka zuwa anjima zatayi tunanin wayar ta koma hannunka, ajiye wayar yayi a gefenshi suka ci gaba da abinda sukeyi..
Ina ajiye wayar kiran Bello yana shigowa, ɗauka nayi bayan mun gaisa yace min Uwar masu gida nifa har yanzu ban samu kuɗin da kike magana ba, jinjina kaina nayi tare da murmushi nace kanajin wasa bazan iya tura hotunan ka ba a yanar giza gizo ko ? Tou wai babu zan baki ne ? Cikin faɗa yace tou banda su ko satowa zanyi in baki saboda inajin tsoronki to ki turawa uwar yanar giza gizo dan kutumar ubanki ko an faɗa miki tsoronki nakeji ko inajin tsoron a ganni tsirara, idan baki sani ba har gasar fitowa tsirara nayi daga ƙofar gida na har bakin masallacin juma'a naje ranar juma'a babu kaya a jikina na dawo, ni zaki ɗauka hoto kimin hauka ? Tou bake ba ubanki ma nafi ƙarfinshi ki riƙe kiyi ta kallo mtsw ya kashe wayatshi....
Murmushi nayi tare dabin wayar da kallo, har zan haƙura wata zuciyar tace wallahi ƙarya yakeyi bai wani fita tsirara ba idan kika fahimci maganar shi ta farko a sadudance yayi miki magana, karki sauƙaƙa mishi number wayar matarshi zaki fita ki samo ki tura mata zata bashi labari, idan kin tura mata ni na sani sai ya kiraki, idan ya kiraki sai kice kin turawa ɗanshi ma, shi kuma ɗan ba hoton za'a tura mishi ba voice note za'ayi mishi da wasu maganganu masu zafi zuciya zata tunzurashi yayi ma baban magana, tashi dai ki fita duk ki samo numbobinsu ki dawo sannan musan abunyi...
Bello kuma shida abokinshi suka kashe sannan yace na faɗa mata, abokin yace tou yanzu zata shafa maka lafiya kaga kun rabu lafiya zata gaji da ajiyar hotunan ta gogesu, Bello yace ni tsoro na ɗaya tace ta turawa wata ƙawarta hotunan fa, karka damu sun gaji su goge dan ubansu, dariya sukayi tare da ƙara kashe wa cikin duniyanci....
Ina fitowa daga wanka nace ba'asan tsiyar nasara ba sai zashi ganin gida, zakayi dana sanin hanani kuɗin nan, kila kuma rabona ne yake da yawa kuɗin zasu sake yawa.
Har na gama shiri da abinda nake saƙawa nake warwarewa, Nana na kwaɗawa kira ta kwararo da gudunta tazo, kallonta nayi sannan nace Nana aiki yamin yawa zan fita neman wurin zama sannan kuma zanje wurin wani Alhaji dake tamin rainin hankali, ai kinsan majalissar babana ko ? Nana tace Eh na sani, nace ai kinma san Bello abokinshi ko ? Nana tace sosai ma, tou lambar wayar matarshi da babban ɗanshi zaki kawo number wayoyinsu zan baki dubu ɗaya...
Yashe baki Nana tayi sannan tace godiya nake Sultana, wani sauran biredi da naman da naci jiya na rage na miƙa mata ansa tayi taita kwarara godiya harta fita, tana fita nima na tattara nawa ya nawa na fita nabar gidan...
A ƙofar gidan Alhaji napep ya sauke ni, wasu irin zuƙa zuƙa motoci tun daga ƙofar gida har cikin get in gidan, kuma yauma get ɗin a buɗe yake daga inda nake tsaye ina hango komai na gidan !
Matashin jiya daya faɗa min cewa Alhaji yayi tafiya shine yazo wurina da sauri ya gaisheni cikin girmamawa ansawa nayi cikin sakin fuska sannan nace gidan naku lafiya naga taron motoci ?
Lafiya qalau ubangidan nasu ne ya dawo ko gida ma baije ba ya fara da ganin dokuna, jiya da aka fidda dawakunan doki ɗaya ya kare a ƙafa shine ya fara da ganinshi kafin ya wuce.
D --- K ne ya fito daga cikin palon yana magana daga ganin yanayin maganar shi faɗa yakeyi, saida ya fito tsakar gidan sannan ya riƙe ƙugunshi da duka hannuwan shi biyu yaci gaba da magana amma bana iya jiyo abinda suke cewa saboda tazarar dake tsakaninmu.
Zubinsu da yawansu ya bani tsoro gasu ƙosasshi, inda Dikko yake tsaye na kalla, gaskiya Dikko ɗan gayu ne wankakken namiji yasha wanka ya ƙoshi tsaftatacce dashi ya cika ya fito cikakken namiji har wani gemun rainin hankali ya ajiye kamu ɗaya gaskiya duk da bana ƙaunar shi jarumin namiji ne duk inda mace take san namiji Dikko yakai tsakani da Allah zan faɗi gaskiya, domin Allah Dikko yana da kyau mai burgewa da ɗaukar hankali , sauke hannunshi ɗaya yayi daga riƙon da yayi mishi ya saka a aljihu ya ciro ibadar tashi, ya ciro cingom in daga cikin takardar shi ya jefa a bakinshi sannan suka fara taho wurin motocinsu...
Murmushi nayi kaɗan yayin da wani sashe na zuciyata yake cewa kira sunanshi idan ya juyo ki caccakawa uwarshi zagi komai zai faru ya faru idan ma ta tafasa ta ƙone, yayin da wani sashe na kwalwata yake bani shawara cewa duk abinda zakiyi kisa nazari da lissafi kiyi ma takonki linzami mai kyau duk daren daɗewa Dikko sai kinci ubanshi.
Zuciyata tace kiyi masa magana dan ya tunaki kuma yasan kina nan kuma ki faɗa masa cewa zaki ci ubanshi idan babu yau akwai wata rana....
Sallama nayi da matashin daya faɗa min Dikko ne yazo sannan na wuce ciki, a lokacin dana isa wurinsu tuni D --- K ya zauna cikin mota ana ƙoƙarin rufe masa mota na riƙe murfin motar ,
Kowa kallo wurin hannun daya riƙe murfin mota yayi dan ganewa idonsa ɗan rainin hankali daya isa yayi wannan iskancin, kwantar da kaina nayi saman murfin motar cikin tausasashshiyar murya nace Dikko, kallo na yayi tare da cewa na'am ya tsareni da idanuwa, shiru na wani lokaci ya ratsa wurin bai daina kallona ba kuma nima ban daina kallonshi ba haka kuma babu wanda yayi mana magana...
Nice na fara cire idona daga kanshi dan idan har ina kallonshi tou lallai babu abinda zai hana in burma mishi wuƙa, kaina yana kallon ƙasa nace ka kuwa gane ni ? Na ƙarasa maganar tare da ɗago fuskata amma ban sake kallon idonshi ba...
Cikin ɓacin rai yace Al ' Ameen mtsww muje ya faɗi maganar tare da jan murmufin motar da ƙarfi ya rufe, zuciya bata da ƙashi ganin Dikko zai maidani sakara yasa na dunkule hannuna na kaiwa gilashin motar duka saida ya tarwatse , jini kuwa yace gashi nan zuwa...
Duk da haka Dikko baiyi niyar tsayawa ba saida nace kai ƙaramin ɗan iska yau itace rana ta ƙarshe a gareka kamar yanda na dasa lissafin kwanaki mutuwarka , idan har kayi nasarar guduwa ina nan tafe gareka sai ka ɗanɗani azaba kwatankwacin irin wacce ka ganamin baka da aiki sai cin cingom kamar wata karuwa sakaran banza daƙiƙi ɗan gidan matsiy......
Wanda aka kira da Al " Ameen shine ya ɗaga hannunshi da niyar kwarara min mari Dikko ya riƙe hannunshi tare dayin murmushin mugunta yace waye yace maka irinsu ake duka ? Tsaya daga gefe kaga maganin ta, Allah ɗaya nake tsoro amma yau dasai nayi mata allurar natsuwa, amma ka barta nayau zan mata kaɗai idan na sake ganinta tou nasan abinda take buƙata, Al ' Ameen yace mai gida ka sakeni in koya mata hankali, murmushin mugunta Dikko yayi tare da cewa bari in bata abinda ta roƙa...
Sakin hannun Al ' Ameen yayi sannan ya matso kusa dani, ɗan kauda kanshi yayi gefe kamar yana nazari fuska a ɗaure ya juyo ya kalleni ni juyowar da yayi gaba ɗaya wurin kowa ya juya baya, hannuwana ya haɗa duka biyun ya maidasu ta baya ya riƙe, hannu ɗayan kuma ya riƙe fuskata, ƙasa ƙasa yayi magana cewa.
Naga dai kina san cingom in nan kinsan kwanaki da muka haɗu ban "yan maki shi ba, kuma sai kiyi ta abu babu kawaici a gaban jama'a sai kiyi ta wani zalamar Dikko kuma ko an baki ni nayi miki yawa ba inda zaki je dani dan ruwa ba sa'ar kwando bane, kina da daraja ɗaya a wurina kuma albarkacinta kike ci amma wallahi dasai na nuna miki ni tantirin ɗan iska ne, darajar tasa kawai bazan wulaƙanta ki ba, amma idan kina neman rainin hankali da tsantsagwaron rashin mutunci daga kaina an rufe littafi.
Tattaunawa yayi cingom in cikin salon jan hankali saida ya busa cingom in yanda ake cewa kwai, sannan ya kalleni da wani iri salo sai kuma yayi murmushi da gefen bakinshi, hannun daya riƙe min fuska ya ciro cingom in sannan ya tura minshi cikin bakina, tuf tuff na fara tofar da cingom in , murmushi yayi tare da rufemin baki yace ai ƙarya kikeyi sai kinci....
Iya ƙoƙari nayi na tofar yaƙi fita ga kuma ya riƙe min hannuwa duka, daidai saitin maƙoshi na yayi min wani duka wanda yasa dole saida na haɗi cingom in, dariya yayi sannan ya sakeni tare da turani baya yace sai mun sake haɗewa an mata....
Tangal tangal na tafi kamar zan faɗi su kuma suka shige motocinsu suka tafi aka barni a filin tsakar wurin daga ni sai Alhaji, dakel na iya haɗiye yawun bakina saboda azaba da raɗaɗin da maƙoshina yakemin saboda nushin da yayi min.
Kallon hannu na nayi da jini yake ta ɗiga sannan na kalli Alhaji nace kaini asibiti, cikin damuwa yace muje, dani dashi muka nufi wurin motarshi muka shiga gaba ɗayanmu muka nufi asibiti,
Muna zuwa babu wani daɗewa akamin diresin , bayan an bincike hannun kaf ko akwai wani gilashin a ciki, magunguna aka bani sai kuma allurai da akayi min duk Alhaji ne ya biya kuɗin bayan an gama komai ya ɗaukeni muka tafi gida !
A ƙofar gida yayi parking duk muna cikin mota daga ni harshi, shiru mukayi na wani lokaci sannan Alhaji yace hajiya dan girman Allah ki goge wannan vidio dan darajar manzan Allah S. A. W, ki taimaki rayuwata ki goge don Allah, badan halina ba,
Ajiyar zuciya nayi sannan nace tou nima ka taimakeni dan darajar manzan Allah S. A. W dani dakai duk mu taimaki juna daga yau nayi maka alƙawari zan goge vidio sannan kuma zan fita rayuwarka babu dawowa...
Tattaro hankalinshi yayi wurina sannan yace faɗamin me kike so idan har ina da hali zan miki ! Ba tare dana kalleshi ba nace mota kawai zaka bani daga ita na rantse maka da Allah na fita sha'anin ka vidiwo kuma zan goge...
Goge zufa Alhaji yayi sannan yace wace iri kike so ne ? Ni bansan mota ba amma dai mai kyau nake so, kallon motarshi yayi sannan yace kina san wannan ? Ba tare da ɓata lokaci ba nace Eh tamin kuma ina santa,
Alhaji yace tou na baki ita, kina da wurin ajiyarta ne ? Yanzu ma zan ajiye miki ita insa azo a tafi dani amma ki goge hotunan nan dan Allah, karka damu zan goge wallahi, a , a nidai ki goge a gabana don Allah, tunda nace zan goge ai zan goge, Alhaji yace tou bayan wannan sai me ?
Abu na gaba ina so ka faɗamin waye Dikko ? Miye asalinshi waye babanshi a garin nan ? Wane irin matsayi gareshi kuma wane dalili ne yasa yake ɗagawa ta rayuwa ina san ka faɗamin asalin Dikko da kuma tarihin rayuwarshi.....
Gyara zama Alhaji yayi sannan yace fara bani mazaunin motarki na ajiye ki goge vidio sannan sai muyi magana kinga lokacin ina cikin natsuwa, ba damuwa na faɗa tare da buɗe mota na fita na shiga cikin gida !:',
Kuyi haƙuri don Allah yau ina can gidan uwar ɗakina nima inacin shagali da miyar mutunci, wurin uwar ɗakina wato *RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE* ina alfahari dake uwar ɗaki ɗaya tamkar da dubu banda kamarki kuma kina da matsayi na musamma a zuciyar *MEELAT MUSA*.....
24/08/2019
*JAMILA MUSA CE...*
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 18
*_KOMAI DADIN DUNIYA KIYAMA TA FISHI , daga alƙalamin Ummerherny Nerserllerh idan kika bari aka barki baya bazan baki labarin wannan ƙayataccen labari ba wanda ya fito daga alƙalamin haziƙar marubuciyar zamani, Allah ya taimaka surukuta yasa a kammala lafiya amin..._*
Ina shiga gidan ko sallama banyi ba yaro ya shigo da saurinshi wai ance Sultana tazo Alhaji yana kiranta , Nana ta fara miya sameki naga hannunki a ɗaure ... ? Duk hankalin su A ` i ya tashi sunga uwar ɗakin kwarata hannu da ɗamara, murmushi nayi tare da cewa yawwa A ` i da Allah inda zan ajiye mota nake so nayi maganar dan kauda tambayar abinda yaji min ciwo, Hafsa tace ina motar take ne ?
Ba tare dana kalleta ba nace tana waje, dan haushin Dikko ya fara shafar Hafsa saboda soyayyar da take mishi bana san Dikko haka kuma bana soyayya wa duk wanda yake ƙaunar Dikko, Hafsa tace sai in ajiye miki a gidanmu, ban bata amsa ba nabi yaron muka koma waje...
Motoci biyu na gani a ƙofar gida , wurin motar Alhaji na tsaya daidai saitinshi sannan nace gani, wani wuri ya buɗe ya tattaro wasu takaddu ya bani ansa nayi naɗan basar ina kallo a zahirance karatunsu nakeyi amma wallahi a baɗinance bansan ko na miye ba...
Fitowa yayi daga cikin motar ya bani makullin tare da cewa ga motar nan zanje mai gida yake kirana dana gama zan dawo insha Allah amma ki rufamin asiri Sultana ki goge vidion nan don Allah, wallahi karkaji komai Alhaji zan goge amma kaɗan bani na kati plz, yace ina zuwa bara in gama tattara tarkacena a motar nan...
Komai nashi ya kwashe a mota ya zuba cikin motar dana gani, bayan ya gama ya ciro wayarshi yace kalli ki gani, kallon wayar nayi yace kinga na goge nawa ko ? Nace Eh nima zan goge insha Allah, godiya yayi sannan ya bani kuɗi amma basu da yawa yace idan ya dawo anjima insha Allah zai bani tukuicin goge vidio, godiya nayi masa sannan mukayi sallama ya shiga mota tare da cewa karfa kiyi wasa da takardun motar nan ki adana su kinji ko ? Sai yanzu na gane abinda takardun suke nufi godiya nayi masa suka wuce ni kuma na koma gida...
Ina shiga gida Hafsa na ba makullin nace kije ki ajiyemin zan ɗauko ta ƙarshen satin nan insha Allah, ansar mukulin tayi taci gaba da maganar ta, kallonta nayi sannan nace saurara kiji, kije ki ajiyemin mota ki dawo, tashi tayi ita dasu Saude suka tafi ni kuma na shiga ɗakina, ban daɗe da shiga ba Nana ta shigo tare da bani number matar Bello amma bata samo na ɗanshi ba , ansa nayi da nayi niyar bata 500 sai wata zuciyar tace kawai in bata 1k in ka nema ma ka samu ai arziƙi ne...
Jakata na buɗe na bata 1k nayi godiya, itama godiya tamin ta fice a ɗakin, tana fita na kulle ƙofa na kwanta saman katifa na fashe da kuka mara sauti , duk duniya babu wanda ya taɓa wulaƙanta ni kamar Dikko nice zai bawa cingom in bakinshi da yawun bakinshi na haɗe a cikin cikina , duk duniya babu abinda yakai miyau saurin sadar da shaƙuwa, shi yasa masu wayau ko bariki suke basa yadda suna haɗa bakunansu da na wasu, waccan ranar bai haɗa bakinmu ba amma shine yau ya ciro abu daga cikin bakinshi ya bani, yana da wata manufa ta daban shine dalilin da yasa yace ma Al ' Ameen bara suga magani na, wato wannan dalilin ne yasa kowa ya juya mana baya ko ? Saida na goge hawaye na sannan nace ƙarya kakeyi yawun bakin ka bazai taɓa zama hukunci a gareni ba...
Nayi kuka har na gode Allah daga baya kuma bacci ya kwasheni wanda bansa lokacin daya zo ba kuma baiyi shawara dani ba,
Washe gari koda na tashi nayi sallah bacci na koma bayan na gama kwashewa Dikko karama , misalin 09:30am Alhaji yasa aka kirani a waya, bayan na ɗauka nayi sallama dakel Alhaji ya amsamin sallamar cikin nishi yace Sultana ina federal medical center { F M C } saida ya sake yin nishi cikin yanayin wahaltuwa sannan yace ina nan Accident & Emargency kizo yanzu don Allah inasan zanyi magana dake....
Har a zuciyata banji daɗi ba cikin muryar tausayi nace kayi haɗari ne ? Hawaye ya gangaro masa daga cikin idonshi yace kizo dai dan bana tunanin zan ƙara awa ɗaya a cikin duniyar nan....
Subahanalla da Allah ka daina wannan maganar gani nan zuwa insha Allah, cikin rawar jiki na kashe wayata, da sauri na sauko daga saman katifa na zuba ruwa, a gaggauce naje nayo wanka tare da wanko bakina, mai fauda da kwalli kaɗai na shafa, baƙar riga ta jallabiya na saka na yana gyalen a saman kaina na zagoyo dashi har gashin kaina saida ya fito ta ƙasan gyalen jallabiyata, gilashi mai saukin duhu na saka sannan na wanke jikina da turaruka masu sanyi ƙamshi, masha Allah na faɗa a lokacin da naga kaina a cikin madubi, nayi kyau sosai na fito kamar baƙuwar balarabiya a nigeria,
Wayata na ɗauka da jakata, na fito ina tsaye ina kulle ɗaki Hafsa ta shigo, ita ɗaya ce babu abokan nata su Saude, su Nana ma duk basa tsakar gida, ɗan gangarowa tayi da wani irin salon tafiya, ta wutsiyar idona na kalleta sannan na ɗaure fuskata na kallota dukanta a daidai lokacin dana gama rufe ɗakina...
Wow uwar ɗakin karuwai kinyi kyau fa kamar dai ba'a mutu ba, share maganar nayi tare da cewa da mota kika zo ne ? Eh ta faɗa tare da bina da kallon cin wanka , gaba nayi tare da cewa muje ki saukeni f m c biyoni tayi muka fito a tare, a ƙofar gida muka haɗu dasu A ` i hada Amisty da Saudatu....
Amisty tace wurinki zamuje munji shiru har yanzu, kuma mun rubuto takarda an tsara jaddawalin yanda zai ƙawatar ya kuma tafi da hankalin maza gaki kuma zafi fita, buɗe gaban mota nayi na kame sannan nace ku shigo muje kuma, baya suka shiga, Hafsa kuma ta zauna mazaunin tuƙi taja muka tafi....
Saida muka fara tafiya sannan nace karanto min ina saurarenki, Amisty fa tasan komai tasan bana ganewa bana rubutawa kuma bana iya karantawa amma sai tace kidai duba ki gani Sultana, basar da ita nayi tare da miƙa hannuna ta baya na anso takarda ko buɗewa banyi ba na ajiye shegiya ban sake bi ta kanta ba kuma ban sake magana ba har muka isa asibitin...
Wani irin tuƙin ganganci Hafsa tayi tare da sakin sitiyarin saboda taga D --- K , a tare muka iso dasu sai leƙawa take tana kiranshi, wato abinda na fahimta idanma ka nunawa mutum ka damu dashi sai yayi ta ɗagawa, kallon Hafsa nayi tare da cewa ke kuwa baki da aji a haka kike tunanin zan riƙa haɗaki da zafafan mata babu class, raina ya ɓaci sannan nace uban waye Dikko da kike ta hauka kina kiranshi mutane suna kallonki kamar wata zararriya....
A daidai lokacin da muka fito mu dukanmu daga mota shima Dikko ya fito kuma yaji zagin da nayi masa , bai kallemu ba yayi gaba ana take masa baya nima gaba na shiga su Hafsa suka rufomin baya, murmushi Dikko yayi a daidai lokacin da muka tsaya bakin ƙofar ɗakin kowa da muƙarrabenshi a bayanshi, kallona Dikko yayi tare dayin murmushi sannan yace zaki ci ne an mata yayi tambayar tare da ɗaga gira ? Ya ƙarasa maganar tare dayimin wani irin kallo mai tattare da mugunta, yaci gaba da cin cingom inshi cikin salon jan hankali gemunshi yana motsawa a hankali cikin salon ɗaukar hankali , murmushi nayi saboda gaskiya yanayin da yayi ya burgeni, ƙarshen harshenshi ya kawo cingom in yayi wasa dashi a daidai lokacin da aka buɗe mana ƙofa duk muka shiga, daga waje bai sake kallona ba kuma bai sake murmushi ba babu magana har muka isa gaban gadon Alhaji...
Duk matan da muke tare ihu muka farayi saboda tsoron yanayi da Alhaji yake ciki yayin da wasu suka nufi hanyar fita, dani da A ` i aka bari yayin da A ` i ta duƙushe tana kuka ni kuma na cire gilashi na wurgar a gefe na rufe idanuwa na naci gaba da dire dire ina kuka saboda na kasa gaba na kasa baya....
Shi kuma Alhaji burinshi inje wurinshi in taimaki rayuwarshi na goge vidio sai kirana yake cikin dasasshiyar murya da yayi magana sai jini ya kwararo , Dikko yace ya daina magana amma yaƙi saurarenshi Sultana kawai yake kira,
Kusa dashi Dikko ya ɗuka sannan ya tambayashi me zan mishi ne ? Hawaye na zuba a idon Alhaji yace ma Dikko ya rufa mishi asiri ya kawoni wurinshi magana zamuyi ta sirri, Dikko yace faɗamin na faɗa mata kaga ta firgita wani abu zai samunta, cikin wahaltacciyarar murya Alhaji yace kayi min wannan arziƙin na sauran mintunan da suka ragemin a duniya lokacina yana tafiya zan iya mutuwa ko wane lokaci, yanda yayi maganar ne yasa Dikko ya kallo inda nake tsaye ina ta direre kamar anyi ma lafiyayyan diko allurar hauka.
Ɗauke idonshi yayi daga kaina sannan ya kalli zugar daya zo da ita, Al ` Ameen ya faɗa cikin wani irin yanayi kamar bashi ne yayi maganar ba, gaba ɗaya waje suka fita harda A ` i aka fita, inda gilashina yake Dikko yaje ya ɗauko sannan yazo kusa dani, ta gaban rigata ya jawo ya sagala gilashin sannan yace buɗe idonki, jikina yana kyarma na buɗe na kalli Dikko, dakel ya haɗe yawun bakinshi sannan ya tofar da cingom in bakinshi gaba ɗaya yanayin Dikko ya canza ɗaure fuska yayi sosai sannan yace miye tsakaninki da mara lafiyar nan ? Miye dalilinki na zuwa ganinshi ? Me kikaje yi gidanshi ? Kema "yar iska kike so ki zama ko ?
Cikin gatsali nace Ey "yar iska zan zama ina ruwanka da iskanci na ne ? Jinjina kai yayi tare da cewa Allah ya sawaƙe wuce muje yana kiranki, tirjewa nayi tare da juya zan fita da gudu ya riƙoni yace ai ƙarya kike sai kinje, har gaban Alhaji ya jani ya kaini sannan ya zaunar dani saman kujera ya tsaya ta bayana yace gata nan me tayi maka ne ? Ko kaima taci kuɗinka kamar yanda taci na Umar ?
Ɗaga kaina nayi na kallo Dikko ɓacin rai kwance a cikin idonshi zare min idanuwa yayi tare da cewa bari kallona kar fashe miki kwayar ido wallahi, jiki a sanyaye na sauko kaina daga kallon da nake ma Dikko naci gaba da kallon Alhaji ina kuka, dafo kujerar yayi ya duƙo kusa dani sosai saitin kunne na yace na rantse da girman Allah idan na gano akwai wani abu tsakaninki dashi saina kashe ki, ya faɗi maganar tare da shaƙemin wuya sosai na fara ƙoƙarin ƙwalƙwale hannunshi na kasa, tun ina iyawa har nasa wani abu na fara halbe halbe har na faɗo daga saman kujera Dikko bai saki wuyana ba naci gaba da halbe halbe, yanda nake halhalbe ya jawo hankalin mutane suka yo kanmu amma an kasa cire hannun Dikko daga wuyana,
Hayani tayi yawa sosai wanda yasa su Al ` Ameen suka shigo ciki da gudu amma wallahi duk yawan mazan nan suka kasa ɓanɓareni daga hannun Dikko harsai dana suma, riƙe Al ` Ameen yake da hannun Dikko yana cewa don girman Allah mai gida ka ƙyale yarinyar nan karta mutu, zaro jajayen idanuwan shi yayi kamar yaci mutuwa yace fita idona Al ` Amenn ya faɗi maganar yana fitar da wani irin lumfashi kamar ranshi zai fita, Al ` Ameen kuwa ƙin sakin hannun Dikko yayi saboda tunda yaga Dikko a wannan yanayin yasan komai zai iya faruwa....
Yace mai gida karta mutu, Dikko yace ta mutu idan ta mutu kaine ka kashe ta ko kaine zakayi azumi ? Ya ƙarasa maganar tare da kwalalo idanuwanshi waje , sannan yace duk abinda ya faru da ita nine ya ƙarasa maganar tare da nuna kanshi, haƙuri akayi taba dikko dakel aka samu ya sakeni ,
Bakin gadon Alhaji ya koma ya ɗauki wayarshi iyakar bincike Dikko yayi bai samu komai ba, kuma number na dama Alhaji baiyi saving ba, jerin kira ya dawo yaci gaba da binke, saida ya gama sannan ya ajiye wayar , kallo gadon da nake kwance yayi har an sakamin ƙarin ruwa da taimakon Al ' Ameen dayayi tsaye yace a bani taimakon gaggawa,
Kusa da Al ' Ameen yaje tare da cewa bani makullin mota, cikin girmamawa ya ɗauko ya bashi baiyi mishi musu ba saboda yasan Dikko baya san gardama idan yace ayi kawai ayi mishi idan yace a bari barin kawai za'ayi sai a zauna lafiya,
Cingom ya ciro daga aljihu ya ɓanɓare ya saka bakinshi yaci gaba daci, Al ' Ameen kuwa bin Dikko yayi da kallo harya fita daga ɗakin yana mamakin hali irin na Dikko zuciyarshi tayi yawa idan ya burkuce wani lokaci kamar bashi ne yakeyi wasu abubuwan ba...
Ta jikin window ya leƙa Dikko, har ya shiga motar yaja ya tafi cikin tuƙinshi na ganganci wanda baya kaucewa kuma baya ɗagawa kowa ƙafa idan ya tafi sai yakai inda zaije hankalinshi yake kwanciya, Allah ya tsare hanya Al ' Ameen ya faɗa tare da dawowa wurin gado na ya tsaya, su Hafsa da Saude da A ` i da Amisty sunyi jigum kowa yana jiran farfaɗowa ta yaji abinda ya haɗani da D --- K......
Dikko kuwa tuƙi yake amma yana tunanin maganar Alhaji ranka ya daɗe wato wallahi wata yarinya ce muka ɗan keɓe da ita , tou wallahi bansan yarinyar nan ta shirya sharri ba, ashe duk abinda mukayi ranka ya daɗe tana ɗauka cikin waya ban sani ba....
Dukan sitiyari Dikko yayi tare da cewa tabbas yacemin yarinyar nan shekarunta bazai wuce 16 zuwa 17 ba daidai saitin zuciyarshi ya daka tare da cewa kece .... ?
Akan titi duk ƙurewar wuri Dikko ya juya kan sitiyarin mota ya koma baya ba abinda ya dameshi da halin da wani zai shiga kanshi kawai yakeji amma baya sauraren talakawansu, da gudu ya ibi shararra ya komo asibiti, a lokacin su Al ' Ameen sun fito zasu tafi ganin Dikko ya dawo yasa Al ' Ameen ya dawo cikin ɗakin da gudu yasa aka ɓoyeni, danshi Alhaji tuni Allah ya anshi rayuwarshi har an tafi da gawarshi, duk zunubin da Alhaji ya cacumar ma kanshi an samu wani marar rabo a lahira ya dira gidanshi yayi mishi caccakar wulaƙanci aka kawoshi asibiti dan ceton rayuwarshi Allah yasa ikar ibar da yayo kenan, Allah ya jiƙanshi yasa mu cika da imani ubangiji ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo...
Ana ɓoyeni su Al ` Ameen suka fito, a waje suka haɗu da Dikko yana ƙoƙarin shiga suka faɗa mishi mutuwar Alhaji ni kuma an canja min asibiti, Allahu Akbar Dikko ya faɗa tare da cewa ubangiji ya ƙarɓi baƙuncinka Muntari Allah ya kyautata tamu bayan taku, da Amin kowa ya ansa sannan suka tafi a tattare baki ɗayansu...
25/08/2019
Taku a kullum
*MEELAT MUSA...*
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 19
Har yanzu kalar idon Dikko bai koma fari ba, idon nan jajir kamar yaci bala'e, amma a hankali yake washewa zuwa kalarshi ta ainahi, fuskar nan a murtuke ya jingina bayan shi da kujerar mota kana kallonshi kasan yana tattare da tsantsar damuwa.
Ɗan gajeren tsoki yayi tare da gyara zamanshi, hannunshi yakai ya shafe gefen fuskar shi, tunanin safiyar haɗuwarshi da Sultana ya fara dawo mishi sabo fitikil kamar yanzu ne abun yake faruwa, da sauri ya rumtse idanuwan shi tare da haɗe leɓunan sa wuri ɗaya ya danne su da haƙoranshi ta ciki, buɗe ƙofafin hancin shi yayi saboda lumfashin da yake shaƙa yayi mishi kaɗan ya buɗe ƙoƙofin hancin ne dan iskan ya yalwace shi.
Har suka isa gidan rasuwa Dikko bai sake ma kowa magana ba, tunda dama shi ba ma'abokin surutu bane, mota nayi parking ya fita cikin damuwa danshi dama kullum haka yanayin shi yake , farin ciki da ɓakin ciki duk yanayin iri ɗaya ne a wurin shi, babu wanda ya isa yasan lokacin farin cikinshi kuma babu wanda ya isa yasan lokacin da yake damuwa.
Tunda ya fito aka fara gyara mishi wurin da zai zauna dan zamanin ga mutane basa abu domin Allah basa darata girma shekaru da mutumci amma suna ba naira matsayi na musamma, Dikko yana da rashin mutunci amma alherinshi yasa mutane basa ganin rashin mutuncin nashi dan Allah yayi masa kyauta idan dai kukayi ido ido dashi tou tabbas zai baki kuma baya da kwauro idan zai bayar mai yawa yake baka, tou kyautar itace ta danne rashin mutuncin shi ga idanuwan al'ummar gari...
Sabuwar tabarma aka amso daga cikin gidan aka shimfida mishi, takalman shi ya cire ya taka tabarmar da safa, saida ya zauna sannan kowa ya zauna kuɗi suka fara nuna ikonsu domin masu neman asan dasu sukayi ta zubewa suna bada gaisuwa, saida ya jinjina kai dan shi kaɗai yasan tsutsar baƙin cikin dake lasar masa zuciya...
Wanda suka bawa duniya gaba ne suka fara bawa Dikko labarin yadda abun ya faru amma a zahirance yana jinsu amma a baɗinance hankali shi yana wurin Sultana so yake kawai a dawo jana'iza yaje ya ganota wallahi sai ta faɗa mishi miye tsakaninta da Muntari, inma banda take daƙiƙiya dan ta tona mishi asiri shine zai haɗa kirji da ita taje ita kuma ta haɗa da yaronshi...
Wayarshi ya ciro yayi "yan rubuce rubuce bayan ya gama ya tura, wayar shi ya maida aljihun gaban riga a zuciyarshi kuwa yana tunani Sultana ta gama barbaɗashi a duniya kowa kallon ɗan iska yake mishi,
Mikewa tsaye sukayi gaba ɗaya dan an fito da mankara, sai yanzu wasu keyin alwalla shidai yana da ita takalmin shi ya saka suka fita sarari dan sallatar gawar Alhaji Muntari , Allahu Akbar ubangiji kayi mana kyakkyawan ƙarshe hanyar dai ɗaya ce duk wanda yazo sai ya koma Allah kasa mu cika da imani idan ajalinmu yazo ameen....
A asibiti kuwa ina kwance cikin tsaka mai wuya, ina tafiya ne tsakanin rayuwa da mutuwa, duk wanda ya ganni saiya tausayamin ga hannu na naɗe da bandej wanda na fasa shi a jikin gilashin motar Dikko, su A ` i kuwa suna bani kulawa ta musamman tare da tattalina kamar mun fita ciki ɗaya !
Tsaye suke zagaye jikin gado na hankalin kowa tashe, jami'an tsaro ne suka shigo gaba ɗaya suka fatattaki su A ` i , kujerar da ake tura marasa lafiya aka ɗauko aka ɗorani a samanta suka tun kari hanyar fita dani daga cikin ɗakin, wani irin ihu Saude tayi tare da cewa ina zakuje da ita ne ?
Basu saurari kowa ba suka fito dani, cikin mota aka sakani mazaunin baya sannan aka rataye ƙarin ruwan a jikin kujera yaci gaba da shiga cikin jikina,
A wurin suka bar kujerar duk suka shiga mota sukaja muka bar asibitin, kuka su Hafsa sukayi tayi tare da tambayar kansu wane irin laifi nayi wanda har hukuma bata ragamin ba ina kwance a gadon asibiti, sunsha kuka har sun godewa Allah daga ƙarshe suka haƙura suka tafi gida...
Daga maƙabarta Dikko basu dawo gidan rasuwa ba gida suka wuce kai tsaye, tun a get na biyu ya sauka tare da cewa zai shiga yayi bacci , Al ' Ameen yace ranka ya daɗe bara muje get in ƙarshe sannan mu sauke ka amma daga nan ai zakasha tafiya, ba tare daya kalli Al ' Ameen ba yace nan zan sauka ya ƙarasa maganar tare da kallon Al ' Ameen , tuba nake ranka ya daɗe Al ' Ameen ya faɗa tare da jan motar yayi gaba...
Saida ya daina hango ɓurɓushin motar sannan ya fiddo wayarshi yayi "yan lashe lashenshi sannan ya kara a kunnenshi , bayan wani lokaci yace kuna ina ne ? Magana na cikin wayar yayi sannan Dikko yace ku shigo ta get in baya, yana faɗin haka ya kashe wayarshi tare da kiran wata wayar kuma.
Ta baya ya dawo ya bi wata hanya daban , tafiya mai nisan gaske yayi wurin tsitt bakajin ƙarar komai sai motsin tafiyarshi tunda tsakuwowi ne baje a wurin irin wannan fararen wanda idan ana rana har kashe ido suke, idan ya taka sai kaji tsus tsuss ƙarar tafiyar shi ,
Wata hanya ya bullo sai gashi jikin wani makeken get, masu gadi yayi ma magana suka buɗe motarmu ta shigo cikin gidan, gaba yayi motarmu tanabin bayanshi saida mukayo nisa da get in sannan ya tsaya, shima matuƙin motar tsayawa yayi tare da fitowa Dikko bai mishi magana ba ya shiga mazaunin dirver yaja motar yayi gaba.
A bakin ƙofar falonshi yayi parking sannan ya fito yaje ya buɗe ɗakin, dawowa yayi ya buɗe baya inda nake kwance rai hannun Allah, ciro robor ƙarin ruwan yayi ya fara riƙewa sannan ya ɗaukeni ya shiga ciki, a falo ya kwantar dani saman kujera 3sieter saida ya gyara ruwan suka ci gaba da shiga sannan ya fita tare da rufe ɗakin ta waje...
Motar ya ɗauke daga bakin ƙofar falon sannan ya ajiyeta a inda suke ajiye motoci, motar ta gidansu ce kuma jami'an suma na gidansu ne yayi amfani dasu...
Dawowa yayi tare da rufe ɗakin sannan ya wuce ciki, wanka yayi ya cire manyan kaya zuwa ƙanana, falo ya dawo ya zauna yana jiran lokacin da zan buɗe idona ya haɗa partyn shagalin wulaƙantani,
Zama yayi saman kujera wacce take kallona, ba abinda yake tashin shi a wurin saidai yaje yayi sallah ya dawo, idan yazo ya zauna kuwa lokaci zuwa lokaci yakan kalli agogon hannushi sannan ya kalli inda nake kwance, waya kuwa idan an kishi saida ya duba kawai ya latse,
Ruwa ma daya ƙare shine ya cire min, bai daɗe da zama ba aka fara dukan ƙofar ɗakin, ɗan latse baki yayi tare da cewa waye ? Dikko buɗe nice, muryar yayarshi yaji miƙewa yayi yaje ya buɗe ƙofar suka shigo cikin falon tare,
Salati nayi a daidai wannan lokacin jin muryar Dikko da sunanshi da aka kira, wani irin abu naji ya daki zuciyata, na ƙara lafewa bamma yi gigin tashi ba haka kuma ban kuskura na buɗe idona ba, amma jikina ya mutu murus , zama yayi a saman kujerar da yake itama kusa dashi ta zauna saman hannun kujera sannan tace ina ka samo larabawan daji ? Ta faɗi maganar tare dayin dariya...
Banza yayi baice mata komai ba, dariya ta sakeyi tare da jan gemunshi sannan tace dan ubanka bakaji ina maka magana, tayi maganar cikin sigar zaulaya, tsoki yayi tare da cewa ni bana san irin abinda kikemin yayi maganar cikin haɗe rai kamar dai yanda ya saba, kaiji ɗan iska ni zaka ɗaure ma fuska ko mutuwa zakayi na faɗa maka bazan daina janka ba, duk wannan haɗe haɗen fuskar gabana aka haife saida ma nayi aure dan ubanka kazo duniya wane girma zakayi gabana, ko inda take bai kalla ba, kuma baiyi murmushi ba bare tasa ran zaiyi dariya, sansar wauta dai tayi ta nunawa da sakarci amma Dikko tunda yace mata baya san abinda take mishi bai sake magana ba saida ta ƙari rashin wayanta sannan ta taho inda nake kwance...
Ko kallonta baiyi ba dan hankalinshi ma yana kan wayarshi amma yana kallonmu da zuciyarshi, tsaye tayi gabana idona da jikina suka ɗauki kyarma da sauri na buɗe ido na kalleta a tsorace sai kuma na kallo inda Dikko yake zaune amma yanzu bayacim cingom maido kallona nayi wurinta kawai sai na fashe da kuka....
Sai yanzu ya ɗago kanshi cikin tsawa yace ki rufemin baki, da sauri na haɗe kukan tare da rufe idona dan wallahi a halin yanzu tsoron Dikko nakeji dan na fara tunanin kila mahaukaci ne amma har yanzu jikina bai daina kyarma ba.
Juyawa yayar tashi tayi tai mishi magana da yaren arna { turanci } bansan abinda sukace ba, ɗan ɓata fuska yayi sannan ya ajiye wayarshi shima yayi mata magana cikin irin harshen da tayi masa, Allah ya bata lafiya ta faɗa tare da cewa zan koma wurin momy da Allah kayi ƙoƙari ka shigo, da kanshi ya amsa mata, saida ta ƙara kallona sannan ta kalli Dikko ta sakeyin magana da yaren ɗazu, kyakkyawan murmushi yayi sannan yace ngode ya faɗi maganar tare da ɗauko cingom ya fara ci, abinda na fahimta cin cingom in kila yana da ƙa'ida domin yafi amfani dashi a wasu lokutta wanda shi kaɗai yasan su...
Fita tayi daga ɗakin tare dajan ƙofar garam, har yanzu idanuwa na a rufe suke jikina kuma bai daina kyarma ba, tashi yayi yaje ya kulle ɗakin sannan ya dawo ya zauna, cikin kujera ya tura hannunshi ya zauro wata irin zureriyar wuƙa sai kyalli takeyi saboda sabinta,
Ke zo nan , kamar ina jira na tashi dan nasan babu wata ke a ɗakin sai ni, da sauri na isa gabanshi na durƙusa cikin tsoro na sauke kaina ƙasa, cikin natsatstsiyar murya yace kalli , ɗago kaina nayi na kalleshi amma ba ido cikin ido ba, cikin murya maisa natsuwa yace mi yasa bakijin magana ? Shiru nayi naci gaba da lissafin "yan yatsu na, bana san ina magana ina maimaitawa, raina yana sauri ɓacin ne , banda haƙuri zuciyata a kusa take ina tambayarki kawai ki bani amsa...
Mi ya haɗaki da Muntari kikayi mishi vidio ? Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji kardai Alhaji ya nunawa Dikko vidion nan, Dikko kuwa ɗoro tsinin wuƙarshi yayi daidai saitin maƙoshina, wanda ya shaƙeni a gaban mutane lallai zai iya kasheni tunda babu mai ganinmu sai Allah, ina san ganin idonshi domin ta nan ne kaɗai zan iya gano idan Alhaji ya bashi labarin vidio,
Ɗan kartar min wuya yayi da wuƙar tare da cewa ke nake sauraro, cak na ɗauke numfashina tare da kallon kwayar idonshi sannan nace waye Muntari ? Na tambayeshi ne dan san gano ko gaskiya ne ? Da ƙafarshi ya takamin baki sannan ya halbi daidai saitin hancina har saida jini ya fita.
Ƙasa ƙasa yayo da wuƙar daidai saitin ƙirjina inda daya burma min ita tawa ta ƙare, cikin kuka na riƙe wuƙar tare da cewa to yanzu kuma laifin me nayi maka ? Na ƙarasa maganar hawaye na kwarara daga cikin idona, shima hawaye ne kwance a cikin kwayar idonshi cikin damuwa yace saki wuƙar kinji, sakin wuƙar nayi sannan yace zaki iya kasheni ? Cikin rashin fahimta nace kamar ya zan iya kisa bayan nasan ba abune mai kyau ba ?
Dikko yace tou mi yasa kika zaɓi zunubi mafi muni a rayuwarki ? Kin kuwa san illolin dake tattare da zina ? Kinsan bala'en ta kinsan matsalolin da take haifarwa ? Kina ƙaramar yarinyarki ki tunkari mazan bariki, kinsan bala'e kuwa irin na mazan bariki ? Kinsan haɗarinsu ? Mazan bariki basa taɓa jin tausayin macen bariki kuma basa tattalata basu san darajarta ba haka kuma bazasu taɓa raga mata daidai da ɗigon kwayar zarraba bariki ta fito kuma shi za'ayi da ita tunda sunsan idan sun lalataki gobe ma wata zasu nema, kinga kuwa da wannan bala'e da kika bashi gaba kawai gara ki sokawa Dikko wuƙa ki huta ya ƙarasa maganar tare da miƙomin wuƙar....
Kallonshi nayi amma banyi magana ba, murmushi yayi tare da ciro cingom in bakin shi yace na ƙoshi ko zaki ci ne ? Banza nayi kamar banji ba , ɗaga kafaɗun shi yayi tare da cewa kin huta 🤷🏻♂, ya faɗi maganar tare da maida cingom inshi cikin bakinshi yabi ni da kallon rainin hankali,
Shiru na wasu mintoci sannan yace kinsan abinda yasa nazo dake gidan nan ? Keda ke gidanki idan kinyi magana tou na tankawa Dikko, ci gaba yayi da cewa anan kaɗai zanyi magana dake cikin natsuwa, ki daina hayemin kuma ki rage rashin kunya sannan ki taka a hankali duniya taƙaitacciya ce ga kowa amma babu kamar mace,
Ki taka sannu An mata ki faɗamin duk abinda kike so a duniyar nan ko miye zan miki kuma zan baki idan dai zaisa ki kwantar da hankali ki natsu, kuma ba yau kaɗai ba zan ci gaba da kyautata miki daga nan har ranar da numfashina zai bar gangar jikina zanci gaba da kyautata miki dan kiyi farin ciki , ke yarinya ce baki san komai na rayuwa ba, amma zan sake faɗa Allah ya baki sa'ar rayuwa da har kika shigo rayuwata sheɗan kuma ya samu galaba a kaina, tunda ni zina ba aikina bane ban taɓa ba tunda nake wallahi sai a kanki.
Kinsha dani kuma kin gama dani har badan duniya, kina da matsayi na musamman da bazai taɓa goguwa a zuciyata ba kuma kin shiga cikin babban tarihin da bazai taɓa gogewa ba a rayuwata har abadan duniya , duk wacce ta shigo kece farko, ni haɗuwata dake na barshi matsayin ƙaddara kuma bansan abinda ubangiji yake nufi da ita ba.
Daga ni harke babu wanda yasan abinda anjima zatayi bare gobe, amma ina riƙonki da Allah kiyi haƙuri kuma ki yafemin akan duk wani abu daya faru tsakanina dake, taɓe bakina nayi tare dayi magana ƙasa ƙasa amma baiji abinda nace ba, Eye ? Ya tambayani tare da yatsina fuska yace banji me kike faɗa ba ,
Kai tsaye na kalleshi tare da cewa bazan yafe maka ba har abadan duniya, jinjina kai yayi tare da cewa to ba komai Allah yasa rashin yafiyar shine alkairi a rayuwata, kina buƙatar wani abu ne daga gareni ? Ni bana san komai saboda baka da abinda zaka bani ni bakayi kuɗin da zaka taimakeni dashi ba har yanzu, bai sake magana ba, ya ɗauki wayarshi ya kira mutumin daya kawoni yace yazo ya mai dani gida...
Ci gaba nayi da zage zagena ƙasa ƙasa yanda bazai iya juyoni ba, anan nayi ganganci ɗaya kunsan masu iya magana sunce idan mutum matsiyaci ne ko an sakashi a tandun man shanu aka tsamo shi haka nan zai fito jikinshi ƙamas.
Babu wani ɓata lokaci mutumin ya iso, Dikko yana jin tsayuwar mota yaje ya buɗe ɗakin ki ya dawo ya zauna, da sallama mutumin ya shigo tare da kallona yace muje, tashi nayi tare da ƙara kallon Dikko har yanzu bakinshi yana motsawa cikin salo mai burgewa da ɗaukar hankali yana cin cingom inshi cikin kwanciyar hankali , gaskiya nidai yanamin kyau idan yana cin cingom, amma fa bana ƙaunarshi, bai kallemu ba kuma baiyi mana magana ba hankalin shi yana saman wayarshi,
Nayi tunanin DK zaiyi ta haɗani da Allah ko kuma idan yaga zan tafi zai kirani amma ko ɗaya ba abinda ya faru, haka nan naji babu daɗi haƙura kawai nayi na shiga mota muka tafi, 11:30pm a cikin ɗakina tayi min, daga Nana sai Karima kawai a gidan sunata jajantamin.
Kuma sune suka faɗamin mutuwar Alhaji, nayi kuka sosai musamman ma a lokacin dana ga vidion dana ɗauka muna ai kata saɓon Allah wani irin imani da tsoron Allah ya tsargamin zuciya tare da ganin kamar mutuwa zanyi yanzu yanzu,
Na daɗe ina kukan mutuwar Alhaji a cikin kwanaki ukku daga nan kuma na ɓarar da lamarin zance mutuwarshi muka fuskanci rayuwar bariki.....
Bani canzawa, kuma yanzu aka fara....
Muje zuwa....
26/08/2019
*JAMILA MUSA...* 🤙🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 20
*_Shafin ga gaba ɗayanshi kyauta ne ga group mai albarka da mutanen cikinshi masu mutunci MEELAT MUSA FANS kuna fa sakani nishaɗi idan kuna sharfi nakanyi dariya sosai domin kuma ilimi ne na musamma ngode sosai Allah ya ƙara haƙuri da juriya, wata ma dai wai cewa tayi Oga Dikko ! Star Dikko ubangidan KWARATA , nafa gode Allah ya baku wayoyi masu riƙon caji da caja mai saurin cika hand set amin... Ni Meelat ko ince JAMILA MUSA nake cewa asha karatu lafiya...._*
*_Ina miƙa saƙon ta'aziyya ga "yar uwa kuma abokiyar aiki haziƙar marubuciya Fadeela Lamiɗo ina tayaki jimamin rashin ɗan uwanki Allah ya jiƙanshi ubangiji ya amfani zuri'ar daya bari , Allah ya baku haƙurin rashin sa annabi yasan da zuwanshi, mu kuma Allah ya kyautata namu zuwan bayan nasu ubangiji yasa mu cika da imani idan ajalinmu yazo..... Am3n ya Allah..._*
Duniya sabuwa inji masu iya magana yayin da wani yake kuka a lokacin wani yake farin ciki, kukan mutuwa da jimimmamin rayuwa yana gidan Alhaji Muntari yayin da a gidan da muke haya yau muke shagalewa muna raƙashewa muna cin duniyar mu da tsinke...
Zaune muke a saman tabarma yayin da ni nasha riga da zani na atamfa nayi ɗaurin ɗan kwali na irin na sabbin karuwai, na nemi bakin kwalli na daddaɓawa bakina, ga kitso na matan bariki da aka yanyaramin ɗinki rigata ya kameni sosai duk rabin halittun jikina sunyo waje, kallo ɗaya zakamin kasan ni tantiriyar karuwa ce wacce ta anshi lasisin iskanci bada jimawa ba, yanayi na ya fita a cikinsu kana gani na zaka gane nice uwar gidan *kwarata...*
Miƙe ƙafafuwa na nayi a saman tabarma nayi zama irin na matan da basu da kamun kai, a gefen damata Amisty ce zaune da jaddawalin sabuwar bariki mai fara aiki a cikin satin nan..
Nana , Karima , Hafsa , Amisty , A ` i da Saude duk suna wurin daga gabana suna ta bani wani irin matsayi na musamman sai kace nayi musu asiri zakayi mamakin yanda suke darajani, yaran nawa dai su shidda ne duk dani mun zama bakwai mune sabbin *kwarata* a cikin wannan zamani kuma nice shugaba kuma zanzo da salon da tarihina bazai gogu ba a cikin tarihin birnin garin katsina...
Juyawa nayi gefen hagguna zuga ce ta "yan daba dana ɗauko su haya zan riƙa basu albashi duk ƙarshen wata, dalilina kuwa na ɗaukarsu duk yana cikin labarin, sunsha kitso irin na ɗiyan kafirawa kallo ɗaya dai zakayi musu ka tabbatar sunsha iskanci sun ƙoshi...
Saida na gama kallesu tsaff sannan na fara nazari da tunani , na farko dai zamanin ga ya canja rayuwa bata tafiya dole saida ilimi, waye zan samu mai amana da zai riƙa karantawa rubutuwa da fassarawa idan anmin turaci, babu shi zuciyata ta bani amsa tare da cewa karki sake ki yadda da matan bariki dan basu da amana...
Kallon Amisty nayi tare da cewa karanto min ina saurarenki, miƙomin takardar tayi , murmushi nayi bance komai ba na ansa, biro na ɗauka na juya bayan takardar nayi rubutu da labarci kamar yanda nayi a police station miƙa mata nayi bayan na gama rubutawa sannan nace haɗa dukansu ki karanto ina saurarenki...
Zazzare ido ta farayi ta ƙurawa jaddawalin ido, alifun kanshi idan zaki kasheta bata iya karantawa ba, ganin ta kasa nace tou ki kiyayi kanki da duniya duk baiwar ki wani yafi ki, kece kika rubuta kuma kece zaki yaɗa ba kowa ba, karki damu basai naji abinda ke ciki ba, kije kawai....
Ku tashi muje na faɗi maganar tare da miƙewa tsaye, ɗaki na koma na ɗauko gyale na sannan na fito, gaba nayi zugar daba ta da tasha suka biyoni baya harsu Nana ba'a bari ba, ina gaba suna bayana "yan daba kuma suna gaba cikin siga mai kalar bada tsoro,
Gidan da zan siya a cikin anguwarmu mukaje dubawa, ƙaton gida ne sosai akwai ɗakuna birjik ɗaki yakai goma sha ukku, sai bayi guda biyu sai baranda inda ake dafa abinci, amma gidan gidan ƙasa ne irin tsufin ginin da can can, akwai yalwataccen filin tsakar gida...
Nidai gidan yamin sauƙi gaskiya ko dan ina matse na siya ? Miliyan biyu aka masa kuɗi babu gudu babu ja baya gaskiya yayi arha dan da a bakin titi yake bazan iya siya ba , daren jiya na bada miliyan ɗaya da rabi, nace zan cika sauran yau idan Allah ya kaimu....
Shine muka zo gani da kowa , gaskiya sun nunamin farin ciki sosai kuma basu nunamin hassada ba, bayan mun gama dubawa muka fito, tunda muka fito yanayin yadda naga anguwar tayi shiru ya taabbatar min Dikko ya shigo...
Shine kuwa ɗan iskan , ya fito daga gidan dokunan shi na anguwarmu da yake daga get in gidan zaka iya hango komai na cikin anguwar idan aka shigo santar kuma gidan dokunan Dikko yake kallonka,
A tsiyace ya fito kamar yadda ya saba, duk tawagata suka koma da gudu baya suka kauce daga saman hanya yayin da ni kuma na shigo hanya hankali kwance Amisty ta taho da gudu zata jawoni wani mutum ya riƙeta dan a ganinshi biyu babu za'ayi tunda dai ni na tafi sunamin addu'a Allah ya jiƙana, ihu Amisty ta farayi tare da cewa Sultana don Allah karki biye wa zuciya ki dawo ko ki gudu bana so ki mutu yanzu wayyo Allahna, kowa duƙar da kanshi yayi yayin dana tsaya cas kuma Dikko ya sheƙo da gudun tashin hankali, wallahi da bani bace ko wacece sai Dikko yabi ta kanta ya wuce babu abinda ya dameshi...
Gab dani ya taka wani irin wawan birki ya fito cikin tsananin ɓacin rai ko mota bai tsaya rufewa ba , hannushi ya ɗaga da niyar marina kuma ko meye ya hanashi ya mareni Oho, ganin ya juya zai koma mota nace Allah ya auna maka arziƙi yau dasai nasa anyi maka fiɗa irin wacce akewa raguna, daka takani ko ka bigeni dasai naga ko waye ubanka a garin nan...
Uhum yace tare dayin gajeran murmushi da gefen bakinshi sannan yace ake yarinya ce a tunaninki kama nayi miki da ɗan wa a garin nan ? Dake da babanki da kowa naki da kike taƙama dashi talakawan mahaifina ne , ni kuma abinda na ɗauki talaka takalmi na ne zan takashi yayin da nake sha'awa in kuma cire na jefar a duk lokacin dana gaji da ganinshi, ke abinda na ɗaukeki baki da banbanci da dabbar layya a wurina ina kiwonki ne kafin ranar da zan yanka ki , abinda yasa kuma banbi takanki na wuce ba idan na kamaki zaki basu labari...
Murmushi nayi tare da cewa duk takalmi takalmi sunanshi amma ko a cikin takalmin wani baka sakashi yayi maka daidai, talakawa suna taku amma kai da mahaifinka bata tasu kuke ba, duk wadda yace kayi takanshi ne baka zo ba, ba'a saka ka kayi ba'a saka ka daina zakin roba dana sanin mafarauta mugu ɗan gidan mugaye kana mugunta amma kana daɗa suna azzalim baƙin cikin talakawa, kafin ka gama ciwo na ni na gama naka ka saurareni ina dawowa ƙarshen shekaru biyu masu zuwa nan gaba nice maganin tsagerancinka....
Ina faɗin haka ban saurari abinda zaice ba nayi gaba na shige cikin gidanmu da muke haya , tafiya nayi irinta in ka isa wannan ma ka sayeshi....
Murmushin mugunta yayi mai nuni da na gama dake yarinya zaki nemi Dikko ruwa a jallo, juyawa yayi ya koma mota ya fita daga cikin anguwar...
Ban daɗe da shigowa gida ba su Nana suka shigo harda ƙawar Amisty wacce muka haɗu da ita police station tayi cikin shege da aurenta, ɗaki suka sameni ina waya da Bello dan tunin duniya na turawa matarshi hotuna anyi tashin hankali na idon duniya kuma shima hankalinshi ya tashi ya yadda zan iya turawa media hotunan, ya yadda zai bayar da kuɗin anjima bayan sallah isha'i.
Sannu nayi ma kowa bayan na gama waya nace ku zauna mana, wuri kowa ya samu ya zauna, kallon ƙawar Amisty nayi mai cikin shege sannan nace sannu hajiya, murmushi tayi tare da kallon ƙasa cikin yanayin jin kunya,
Ɗan kauda kaina nayi gefe tare da cewa ya akayi da cikin ne ? Ba tare data kalleni ba tace... Wallahi har yanzu bai yadda ba, murmushi nayi tare da cewa bariki da ciki ko goyo wahalalliyar bariki kenan , bariki da tsarin iyali magani ko allura halaka ne saboda baki gwada mahaifarki ba kika tabbatar kina aihuwa ko bakyayi , kallon su Amisty nayi sannan nace tashin farko dai kowa ta nemi gishirinta ta saka a jaka yayin da buƙatar namiji ta gama kammaluwa akanki ki zuba gishiri a bakinki sai ki kora da ruwa,
Nana ta tambayeni maganin me ? Kallonta nayi ido cikin ido sannan nace maganin hana ɗaukar ciki, waye ya faɗa miki haka ne ? Murmushi nayi tare da cewa wani feƙaƙƙen dan bariki mai bariki cikin gidan iyayenshi , tunda kuwa har yasan gishiri yana hana ƙaramin ciki zama a cikin mahaifa ai kinsan ya gogu a harkar bariki.
Dariya kowa yayi tare da cewa wannan dai ai mugunta ce gishiri ai saida yasa maka cuta , ba tare dana kallesu ba nace shigar wata cutar itace take kore wata, Allah dai yasa mu fita bariki lafiya , kowa ya amsa da amin...
Fira dai mukaci gaba dayi daga baya A ` i tace bara suje ita da Saude su anso mukullen shagon da muka kama haya tasan zuwa yanzu sun kammala fenti , sai sun dawo nayi musu suka fita daga ɗakin yayin da Nana da Karima suka fita suma, aka barni dani da Amisty sai Hafsa da ƙawar Amisty matar aure...
Kallona Hafsa tayi tare da cewa uwar ɗakinmu idan babu damuwa nikam ina so na tambayeki. Hankalina yana kan wayata ina ganin rubutun da d c o ya turomin nace ina saurarenki yayin dana kanga wayana daidai saitin bakina nace ni aiki nakeyi ko ka kirani a waya, ko kuma kayomin voice note idan na kunna saina saurara , ina faɗa na tura , yayin da Hafsa tace wai miye tsakaninki da DK ?
Ajiye waya nayi a gefe na sannan na tattara duk hankalina da natsuwa ta wurin Hafsa nace idan na faɗa miki abinda DK yayi min ke kanki sai kinci ubanshi da yake taƙama dashi yana ma mutane iskanci saboda shi , yau ya taɓo ubana yace talakan babanshi ne , nima kuma na taɓo babanshi a cikin magana na, nuna Amisty nayi tare da cewa duk wanda nace ya faɗamin waye uban Dikko a garin nan ba'a bani amsa idan zaki faɗamin Dikko ko waye ubanshi zan faɗa miki abinda ke tsakani na da Dikko....
Hafsa tace Gwamnan garin nan shine uban Dikko, shiru nayi banyi magana ba Hafsa taci gaba da cewa dole sai kunyi haƙuri sannan kuma kunyi ma Dikko uzuri soyayyar da ake nuna masa a gidansu da yadda ake tsoron mishi faɗa yasa yake ganin duk abinda yayi daidai ne a rayuwarshi , wallahi ba'a dakawa Dikko tsawa ba'a masa kallon banza domin mahaifinshi gani yakeyi kamar duk idan akayi masa zai mutu ne , ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗora akan Dikko yana mishi soyayyar da duk duniya babu wanda yake ma irinta a rayuwarshi , fitar da Dikko yake yi da duk wannan iskanci da wulaƙancin da yakeyi ubanshi baisan yana fitowa ba , yasan dai ya baro ɗanshi gida...
Cikin jin haushi na kalli Hafsa tare da cewa nikam bazanyi haƙuri ba kuma bazanyi masa uziri ba , can gidansu ya zama dole suyi masa duk abinda kika lissafo amma badai ni ba , wallahi ko Dikko zai mutu saina tozarta shi , saina wulaƙanta mishi rayuwa a garin nan , ki jira zaki ga yanda zanci uban da ya haifi Dikko saina maida shi abun tausayi da kwatance uban nashi kuma duk daren daɗewa saiya gama gwamna ya sauka tunda gidan gwamnati ba gidan ubanshi bane ba...
Shiru Hafsa tayi bata sake magana ba , bayan wani lokaci tacewa Amisty ku tashi mu tafi , gaba ɗayansu suka fita tare da cemin sai Allah ya kaimu , ban basu amsa ba na ɗauki wayata naci gaba da abinda ya dameni.
Hafsa kuwa kamar ubanta na zaga , tana shiga mota ta fashe da kuka tare da kiran wayar Dikko har ta gaji ta haƙura bai ɗauka wayar ba , daga baya ta yanke shawarar tura masa text duk zagin da nayiwa Dikko komai dana faɗa saida Hafsat ta rubuta ta ƙara da nata dan sharrin ya tafi daidai , bayan ta gama ta tura mishi. Sannan taja motar ta suka bar ƙofar gidanmu...
Su Hafsa basu daɗe da tafiya ba su A ` i suka dawo kuma sun tabbatar min cewa shago yayi yanda ake so an tsara shi gwanin burgewa , naji daɗi sosai suma sunyi farin ciki idan Allah ya kaimu gobe lafiya zamu fara fita aiki , saida akayi sallah magrib sannan suka tafi gidajensu.
Bayan sallah isha'i kamar yanda Bello yayi alƙawari ya kawo min kuɗi , a gurguje ya bani ya tafi dan yacemin suna da wasa jiranshi akeyi , a daren nakai cikon kuɗi kamar yanda nayi alƙawari zan bayar a gaban shedu aka rubuta takarda aka bani ....
Umar ne durƙushe a gaban Dikko cewa mai gida kaga dan Allah tunda kazo gashi har zaka koma gobe don Allah kafin ka tafi ka taimaka ka siya gidan wallahi matar tana buƙatar taimako,
Umar yana magana amma hankalin Dikko yana kan saƙon Hafsa , a fili yayi dariya tare da cewa rigima kenan Allah ya baki sa'a akan duk wani kudirin ki akaina An mata , murmushi yayi sannan yace Umar ni babu abinda zanyi da gida , amma nawa ne kuɗin sai in bashi ayi mata aikin...
Ba'a mugun sarki sai mugun bafade , kuma wani abu za'a bashi a cikin kuɗin gidan idan an siyar dashi, dan haka ya gyara zama tare da cewa mai gida dan Allah tunda dai yafi so ka siya ka siya ɗin kawai , kila gidan ne ya gaji dashi tunda da taimakon yake so da zaice ka taimaka mishi.
Dikko yace tou tunda yanzu yayi maganar siyar da gida ai kowa yasan taimako yake nema insha Allah kafin in tafi zan baka ka bashi , Umar yace mai gida abinda yasa nace ka siya gidan kusa da gidajen daka siya ne kaga idan ka siya sai shima a rushe maka a haɗe wuri ɗaya,
Baiyi magana ba sai ƙara kallon text in Hafsa yake yi yana mamakin ɗabi'u irin na An mata da ba gobe zai tafi ba dasai ya ƙara zuwa ya jawota faɗa kuma yanzu dare yayi dasai ya firgito mata hankali , lallai zai haƙura ya riƙa waya da Hafsa dole kodan dan ya riƙa jin halin da Sultana take ciki.
Umar yace mai gida kayi shiru baka ce komai ba , kallonshi Dikko yayi tare da ajiye wayar shi gefenshi yace wato so kake in ƙara baƙin jini ko ? Cikin rashin fahimta Umar yace wurin wa zakayi baƙin jinin ne ? Ajiyar zuciya Dikko yayi tare da kwantar da bayanshi jikin kujera lumshe idanuwanshi yayi cikin shauƙi sannan yace wai An mata ne tace zataji min mutunci bayan shekaru biyu masu zuwa,
Ya ƙarasa maganar yana murmushi , Umar yace haba ranka ya daɗe ina ma zata ganka ? Kafin shekaru biyun masu zuwa kayi mata tazarrar da baza ta sake ganinka ba har abadan duniya , kai babbar ƙaddara ce da kayi nisa da tazara ga duk wani ɗan ƙaramin sakarai , ka siya gidan kawai ka manta da sha'aninta me zata iya maka ne ? Buɗe idonshi yayi tare da cewa baza ta iya min komai ba kuma badan inajin tsoron tayimin ba kawai dai tana bani tausayi ne...
Umar yace bata da kunya ta raina hankalin mutane ka daina tausayinta shegiyar kanta ce , Dikko yace ba itace shegiya ba nine shegen barni dai da Dikko take wasan , zan bada kuɗin gidan na siya , wani irin farin ciki Umar yayi tare dayi ma Dikko godiya saida ya koɗashi sosai sannan ya fita,
Fitar Umar Dikko ya ɗauki waya ya turawa Hafsa saƙo cewa shifa baima gane yarinyar da take magana ba , tayi masa bayani na yadda ya sani ta tuno masa asibiti da dai duk wani abu daya shiga tsakanina dashi Dikko yace sam bai ganoni ba amma idan tana da hotona ta tura mishi ,
Hafsa tace bata da hotona amma zamu haɗu da safe insha Allah zata ɗauko masa ni ya kwantar da hankalinshi , Dikko yace ai dama hankalinshi a kwance yake amma ya zama lallai zai koyamin hankali ,
Tunda gari ya waye muka sha gayunmu kamar yanda muka tsara , motoci biyu aka ajiye a ƙofar gidanmu ɗaya ta Hafsa ɗayar kuma tawa ce sai kenap ɗaya wacce "yan dabana zasu riƙa amfani da ita kuma ni na siyi ,
Dukanmu a ƙofar gida muka fito , muna ƙoƙarin shiga mota mai gidanmu da muke haya yazo bayan mun gaisa yace ya siyar da gidan nan saboda haka duk abinda muke so zuwa jibi mu kwashe kayanmu,
Cikin ɓacin rai nace wai miya sa kuke abu babu adalci a rayuwarku ? Kai kuma nawa ya baka ya siyi gidan dan nasan za'ayi haka tunda har yaga gidan dana shiga nasan wallahi saiya siya , sakaran banza matsiyaci dashi tou idan ka ganshi ka faɗa mishi nayi gidan zama idan yanajin shi wani mai kuɗine yazo ya sayi anguwar nan duka...
Ina faɗin haka nace ku shige muje , gaba ɗayanmu kowa ya shiga mota , Hafsa ta tuƙa nata , tawa kuma driver na samu saboda har yanzu ban iya mota ba , zugar daba ina kuwa suka shiga napep muka tafi, ashe duk abinda na faɗa Hafsa vidio tamin ta turawa Dikko dan ya gani da idonshi ya kuma ji ina faɗa da bakina , ni kuma bansan anyi ba tasan idan ya gani da idonshi dai zaici mutunci na yadda ya kamata bansan abinda ke cekin zuciyar Hafsa akaina ba...
28/08/2019
*JAMILA MUSA* 🤙🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
0 comments:
Post a Comment