"da haka Mahfus yai ta bawa amatullah kabari.
"har goma yai snn yace ta hado masa abinci breakfast kafin ya fito wanka.
"mikewa yai yashiga toilet ita kuma tanufi kitchen.
"aris da akwai ta soya masa snn ta hada masa tea.
"tana gamawa dinner ta kai masa snn ta koma daki ta sanar dashi.
"daidai lokacin Mahfus ya riga ya fito wanka mai yake shafawa.
"gani ta shigo ya tsaida shafa mai da yakeyi, amatullah tace ya dai?
"Mahfus yace ke nake jira.
"amatullah tace kamar yaya?
"Mahfus yace mai xaki shafami.
"Mahfus yana mgnr ne babu alamar wasa a tare dashi.
'"amsa kawai tai taci gaba da shafa masa, Mahfus na xauna a ganan mirrow dagashi sai towel a daure a gudunshi.
"tana gama shafa masa yace ta dauko masa kayan da xaisa.
"Mahfus yace daukomin mana.
"amatullah tace wanene xan dauko daga ciki.
"shadda milk colour ta dauko masa, yasa yana gama sawa yace xomuje mu karya.
"rike mata hannu yai xuwa dinner, suna fita sukai karo da fadi itama ta fito.
"hannu Mahfus ya riko mata hade da cewa kema xomuje mu karya.
"da sauri fadi ta fisge hannunta.
"da Mahfus yaga haka be sake bi ta kantaba yana rike da amatullah suka nufi dinner, suna xuwa ta xuba masa a plate snn ta xauna.
"itama fadi ciki ta shaga ta hada nata breakfast din snn ta fito parlour.
"dama dabiar sune babu wanda yake cin abincin d'anuwarsa.
"kowa ta kansa yake.
"Mahfus yana gama breakfast ya mike hade da cewa ni xantafi.
"amatullah tace saika dawo Allah ya tsare.
"Mahfus yace amin nagode.
"fadi na jinshi tai banxa dashi.
"har yakai kofar parlour sai ya dawo hade da cewa amatullah xo mana.
"dakinta ya nufa tana biye dashi suna shiga Mahfus ya bude jakarsa handbag finsa wasu takardu na documents din sa ya dauko saida ya bubude ya nuna mata snn yace gasu ki ije dan Allah ki masu kyankyawar buya.
"tun kafin Mahfus ya fita amatullah tace ya kama mata akwatin dake kan wadrop din, sa hannu yai ya kama suka sauke.
"budewa tai cikin xannuwarta wanda bata dinka ba suka xuba a cikin suka rufe snn suka sake kamawa suka meda sama.
"da fadi taji shiru mikewa tai har tafara tafiya sbd taji mgnr da sukeyi tunani me tai kuma sai takoma.
"tana xama Mahfus suka fito shida amatullah.
"Mahfus ya isa parlour kusa da fadi ya xauna hade da cewa adam babu ko gaisuwa?
"shiru tai taci gaba da cin abincinta.
"gani haka yasa Mahfus mikewa hade da shafan mata fuska yace adam saina dawo.
"itako amatullah tana dinner tana fadi kayan da suka bata, suna hada ido da Mahfus daga mata hannu yai snn yafice.
"Mahfus yana fita amatullah tace fadi mutashi lpy?
"cikin fara'arta tace lpy klau ya kwana zunnurai.
"amatullah tace klau.
"fadi tace ina yakene banganshi ba.
"amatullah tace yatafi school.
"fadi tace Allah ya dawo dashi lpy.
"amatullah tace amin nagade ta karisa mgnr ne hade da kwashe kayan ta nufi kitchen.
"itama fadi duk tana mgnr ne amma bekai xuci ba, mafi yawancin lokuta fadi naso taiwa amatullah rashin mutunci amma haka kawai sai ta kasa.
"amatullah tana shiga kitchen ta wanke duk kayan da tabata tana gamawa takoma dakin.
"itama fadi tashi tai ta shiga kitchen taje ta wanke nata kayan itama ta koma kitchen.
"2-30 nayi Mahfus ya kira bb maigadi ya sanar dashi za'a dawo da zunnurai daga school dan Allah yadan fita daga waje ana daukeshi ya karisa dashi cikin gida gun mmnshi.
"da yamma bayan la'asar fadi ta dafawa Mahfus lafiyayyar abinci tana gamawa ta kwashe takai dakinta.
"snn tadawo ta wanke kayan da tabata.
"bayan ta gama ne itama amatullah tashiga kitchen ta tadafa tuwon semovite da miyar vegetables.
"tana gamawa ita dakinta takai.
"saida tabawa zunnurai nashi yaci yana gama ci tai masa wanka snn tai nata hade da alwala saida tai sallah snn ta rangada kwalliyarta cikin riga da sket dakinta ma duk ta fesheshi da turare.
"itama fadi kwalliya tai cikin doguwar riga.
"harda abubuwan da bata shafawa a fuska duk yau saida ta shafa.
"tana fitowa itama amatullah ta fito xata shiga ciki gani irin kayan da amatullah tasa yasa fadi komawa daki ta canxa kaya tasa riga da sket.
"snn ta dawo parlour ta xauna.
"itama amatullah tana gama abinda xatai a kitchen komawa tai dakinta ta kwanta.
"Mahfus yana sallama da sauri fadi ta mike hade da cewa oyoyo sannu da dawowa.
"rungumeta Mahfus yai hade da cewa adam kenan kinyi kyau fa.
"fadi tace nagode.
"yana rungume da'ita suna tafiya har sukai bakin kofarta sai Mahfus yace ina xuwa.
"betsaya ya saurari abinda xatace ba yashige dakin amatullah.
"lokacin tana kwance tana buga game a wayarsa.
"Mahfus yana shiga da sallama binta kan gadon yai ya rungumeta yana xewa my baby kinyi kyau sosae gaskiya ni dan gatane duk wannan kwalliyar sbd dani.
"lailai na more.
"murmushi amatullah tai hade da cewa sannu da dawowa.
"ya kasuwa.
"Mahfus yace alhamdllh.
"tubewa yai ya shiga toilet yana fitowa yace ta xuba masa abinci.
"Tana xuba masa Mahfus yaci sosae yanaci suna hira hade da tambayar zunnurai.
"duk da rai fadi ya baci dan newa tai taci gaba da xaman jiransa a dakinta.
"Mahfus yana gama ci amatullah ta kwashi kayan xuwa kitchen.
"shima Mahfus mikewa yai ya shiga dakin fadi yasa meta zaune bakin gado tana jinrashi.
"bata nuna bacin rai ba tace kadawo.
"Mahfus yana nadowo xama yai a bakin gado kusa da'ita.
"Jawo karamin table din dake gefe tai hade da cewa ga abinci.
"Mahfus yace nakoshi.
"a take ta bata rai.
"Mahfus yace menene abin bata rai dan nace na koshi?
"matsewa tai tace ba komai.
"hira sukai sosae saida Mahfus yaga goma ta kusa snn ya mike..
"da sauri fadi tace ina xaka kuma?
"Mahfus yace xanje na kwanta.
"Sai fadi tace amma kasan girkinane ko?
"Mahfus yace idan girkinki ne sai me?
"fadi tace wlh Mahfus kwata2 abinda kakeyi babu kyau ya sabawa umurnin ubangiji.
"kuma a kwanar da xakai da'ita kasan xaku iya samu shege?
"Mahfus yace Allah ko?
"bansan dama da malama nake zaune ba, shine tutuni bakimin wa'axi na gwara ba sai yanxu da abin yajuyo kanki.
"Mgnr shege da kikeyi idan har zansamu shege da amatullah a kwanan da xanyi da'ita kema shegene a cikinki.
"da sauri fadi tace aa wlh.
"tafiya yai yaje xai bude kofa da sauri fadi tasha gabansa tana cewa wlh babu inda xaka.
"Mahfus yace wlh idan baki kaucemin a gaba ba sai nayi hurgi dake.
"kafi tai wani mgn hannu yasa ya fisgota daga bakin kofar hade da cewa ke kin'isa ki sami doka bayan nida gidana.
"yana fita Jan kofar yai ya rufeta snn yashiga dakin amatullah.
"yana shiga ya kashe light ya haye gado.
"yauma dai haka aka kuma babu yadda Mahfus beyida amatullah ba amma taki, shafeta yai tayi har yai release snn ya kwanta.
"a lokacin da Mahfus ke released ne ashe akwai fadi a makale tanaso taji abinda sukeyi.
"Mahfus ya kwance akan amatullah tana released gurnanin da yakeyi ne yasa fadi ta dauka ko sex yakeyi hankalinta ya kara tashi tana tambayar kanta wani dadine amatullah kedashi haka da har Mahfus yake sabbatu a kanta?
"a guje ta koma daki taje tasa kuka.
"shiko Mahfus yana gama released ya sauka ya kwanta.
"da haka rayuwar su ta kasace har tsawon sati biyu, Mahfus yana dawowa daga kasuwa yana shiga dakin amatullah ganinta yai zaune ta xabga uban tagumi.
"da sauri ya karisa gunta xama yai hade da tambayar lpy?
"meke faruwa.
"amatullah tace tanajin gani hajiya ne.
"Mahfus yace shine xakisa damuwa haka idan dan sbd wannan ne karki damu.
"da sauri amatullah tace da gaske.
"Mahfus yace kwarai da gaske.
"da sauri amatullah ta rungumeshi tana murna.
"Mahfus yace kamar wani lokacine kikeso kije?
"amatullah tace ko yau ma.
"dariya Mahfus yai hade da cewa da darenga amatullah?
"kidai bari gobe mugani.
"amatullah tace Allah ya kaimu.
H.S.Zce🖊
🌺💦🌺
💦
MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)💦
MMN USWAN
H.S.Z.
33
"su amatullah suna fita wani international school Mahfus ya kaita.
"suna isa Mahfus ya fito ya budewa amatullah mota ta fito snn ya dauko zunnurai, daukar zunnurai yai sama snn ya rikewa amatullah hannu suka shiga har office din principal.
"bayan sun gaisa ne suka fadi abinda ya kawosu.
"principal yai masu bayani yadda school din yake.
"saida principal din ya gama mgn, snn Mahfus ya tabi amatullah da kafa.
"alamun school din yai mata?
"kafa ta karkadi masa alamu aa.
"sai Mahfus yacewa principal xasuje su dawo.
"principal yace babu damuwa.
"suna mikewa Mahfus ya dauki zunnurai snn sawa amatullah hannu a kugu ya rungumota,
"kunyane ya kama amatullah sbd basu kadai ne ba agun.
"Mahfus yana rike da amatullah har sukakai inda motansu yake.
"suna isa Mahfus ya budewa amatullah tashiga snn yasa zunnurai a baya shima ya xaga ya shiga.
"da haka saida suka xaga schools yakai duhu a na hudun ne amatullah tace yai mata.
"a take Mahfus ya cika form yabiya komai.
"akabawa zunnurai class nursery 1 hade da uniform dasu textbooks snn sukai sallama.
"suna fita wani dan kareriyar super market suka nufa.
"suna shiga Mahfus ke gaba amatullah na biye dashi a baya.
"tun daga bakin kofar shiga Mahfus ya fara tsince kaya har suka shiga daga ciki.
"duk uban kayan da Mahfus ya diba babu nashi a ciki daga na amatullah saina zunnurai.
"suna zuwa gun bayan kudi akai masa list yabiya.
"gani kaya yai masa yawa yasa amatullah ta dauki zunnurai, shikuma Mahfus yana rike da kaya.
"har sun fita can gefe zunnurai ya hango keke, hannu yasa yana bubugawa amatullah baya.
"karaf Mahfus ya gani, cewa yai my son ya dai?
"zunnurai yace baba kasiyemin.
"jiyawa amatullah tai sbd taga abinda yake mgn akai.
"sai tace haba Mahfus inace ko sati bekai ba, da kasiye masa keke.
"Mahfus yace babu ruwanki.
"ije kayan yai gefe snn ya amshi zunnurai sukaje saida ya xabi wanda yai masa snn Mahfus suka koma ciki ya biya.
"snn suka hada kayansu a mota a bakin super market din akwai masu saida gasansun kaji dasu fruit.
"koda yaushe suna xama a gun 24 hour, guda biyar Mahfus ya siye yace a raba masa gida uku.
"kashi biya a hada gu daya kashi daya kuma daban.
"bayan sun gama sawa sai Mahfus ya siya su kayan fruit shima ya raba gida biyu snn suka karisa gida.
"itako fadi tana can tacika tai fakil kamar ta fashe.
"tanajin shigowar motarsu da sauri takoma daki ta kwanta kamar me bcc.
"Mahfus yana parking amatullah ta fito, tana fita ta budewa zunnurai shima ya fito, Mahfus ma yafito har amatullah tafara daukar kaya, da sauri Mahfus yace barshi kawai.
"barin kayan tai tashige ciki dakinta ta shiga kai tsaye.
"fadi najin tafiyar amatullah da sauri ta mike taxo tana lekenta.
"Mahfus kwashe kayan yai tsaf yakai dakin amatullah, gani bega fadi a parlour ba saida ya dauki nata ledan kazan snn yaje dakinta.
"fadi najin Mahfus ya tunkaro dakinta a guje ta koma ta kwanta kamar me bcc gaske.
"Mahfus yana shiga ya ganta kwance tana bcc beyi kokarin tada ita ba sbd cikin dake jikinta.
"Ije ledar yai akan durowa ya fita.
"yana fita fadi ta mike zaune.
"kitchen Mahfus ya shiga ya dauko plate da cups snn ya koma dakin amatullah.
"yana shiga jin motsinta yai a toilet shikuma zunnurai yana zaune a bakin gado yana wasa da wayar bbnshi.
"saida Mahfus ya cire riga yarage dagashi sai doguwar wando snn ya xauna a kasa dauko namar kazan yai ya juye a plate juice kuma ya xuxuba a cups.
"gani har yanxu amatullah bata fito daga toilet ba, mikewa yai ya bita koda ya leka ganinta yai rike da pan a hannu tagama wanka xatasa.
"batare da ta ankara ba.
"xubawa halittatanta ido yana kallon.
"juyowar da xatai taga Mahfus yana kallonta da sauri ta dauki towel ta daura.
"murmushi Mahfus yai hade da daga mata gira snn ya koma.
"saida amatullah tasa kayanta tsaf snn tafito.
"tana fitowa Mahfus yace xoki xauna mana.
"batai musuba ta xauna, daukowa Mahfus yai xai kaimata baki, da sauri ta kauda bakinta.
"hannu tasa da kanta ta dauko tanaci.
"gani haka yasa Mahfus kara matsiwa kusa da'ita.
"sai faman janta da xance yakeyi mgn daya biyu sai Mahfus ya tabeta hade da daga mata gira.
"amatullah daure fuska tai, kwata2 taki sake jiki dashi.
"bayan fitan Mahfus daga dakin fadi itama fitowa tai ta labe a jikin kofa tanajin duk mgnr da Mahfus keyi.
"Allah yasa ma duk mgnr da Mahfus keyi amatullah batace komai ba, daga eh sai aa.
"amatullah tana koshi cire hannu tai daga namar tashiga toilet ta wanke hannuta.
"saida Mahfus ya kara ci snn shima ya mike toilet ya shiga ya wanke hannu yafito.
"yana fitowa daga toilet dauko wayar amatullah yai yamikawa zunnurai snn ya amshi nashi.
"amatullah tana zaune a bikin gado dukawa Mahfus yai kamar xai mata mgn batare da ta ankara ba kiss yai mata a kan goshinta hade da cewa baby saina dawo ko.
"amatullah tace Allah yabada sa'a.
"Mahfus yace amin nagode my wife.
"har xaifita yadawo yace ko akwai abinda kike bukata?
"kai kawai ta kada.
"Mahfus yace to shikenan.
"fadi najin alamar fitowarsa da sauri takoma daki.
"Mahfus yana fita daga dakin amatullah dakin fadi ya koma ganinta kwance da yai ya dauka har yanxu bcc takeyi hakan yasa yatafi kasuwa.
"Mahfus yana fita fadi ta mike xama tai bakin gado tunani kala kala takeyi, yadda hankalin Mahfus yakoma gun amatullah da d'anta.
"bayan matar da take saida mata da maganin mata tace Mahfus baxai taba juya mata baya ba sai yadda tai dashi.
"can wani tunani yaxo mata tace komai amatullah itama tafara amfani da maganin matane shiyasa Mahfus yake niman juya mata baya?
"can kuma tace to ai amatullah batasan irin wannan abubuwa ba, saidai ko mmn junior ne xata nuna mata.
"to ai amatullah bazuwa gidan takeyi ba, itama mmn junior bata xuwa.
"wani tunani da yaxo mata da sauri ta mike.
"ko sallar axahar batai ba haka ta xari kyale da jaka takami hanya ta fita.
"Mahfus yana fita amatullah ta amshi wayarta a hannu zunnurai kamashi tai suka shiga toilet saida yafarayi snn itama tai nasa.
"suka fito suka fara sallah.
"shima Mahfus yana shiga kasuwa saida ya fara xuwa masallaci yai sallah snn ya karisa shago.
"fadi tana isa gidan me magani tai sa'a sbd fita xatai, gu tabata ta xauna snn suka gaisa.
"bayan sun gaisa ne fadi tai mata bayani abinda ya kawota.
"murmushi me magani tai snn tace to ai kece da laifi idan kina amfani da magani ba'aso kabari har saiya kare anfiso kafin ya kare kanada wasu kuma ba'aso kullin kaita anfani da kala daya anfiso yanayi kana canxawa sbd dandano.
"amma idan kina anfani da kala daya kullin haka xai rika jinki babu canji.
"yau yana dakin kikine?
"fadi tace eh.
"a take ta hada mata wasu maguguna sunkai kala bayar tabawa fadi tace tashi.
"gani irin hadin da akai matane yasa fadi cewa inada ciki fa.
"sai mai magani tace babu komai, kyauma kenan kinsan dandano mace mai ciki daban yake.
"karma ace karamin ciki.
"fadi tace da gaske?
"mai magani tace kwarai kuwa.
"a take fadi ta dauki magani ta shanye harda cewa idan da wani kikara hadami.
"mai magani tace aa amma ga wannan da yamma ki hada kamar yadda na hada miki haka kisha.
"wani ta dauko tace wannan kuma kibashi yasha.
"da kanki xaki xakiban kabari.
"sbd murna fadi batasan iya adadin kudin da ta dibaba tabawa mai magani snn sukai sallama.
"fadi tana dawowa gida ije kyale kawai tai tafada kitchen babu mgnr sallah.
"lafiyayyar abinci ta hadawa Mahfus hade da juice ta xuba masa maganin karfin maza a ciki snn tasa a frg.
"ko kafin ta kammala dare yayi bayan ta gamane ta tai wanka daga nan tai alwala tafito.
"tana fitowa tafara sallah hada axahar la'asar magrib da isha, tana idarwa ta tsantsara kwalliyarta.
"yau ko parlour batakai abinci ba, a dakinta ta ije snn ta koma parlour xaman jiran Mahfus.
"bata dade da xama ba Mahfus yai sallama a guje fadi taje ta rungumeshi hade da amsar jakan hannunshi.
"Kai tsaye daki ta jashi suka shiga, shima binta yake babu musu.
"suna shiga ta ije jakar snn ta tai maka masa ya tube yana tubewa yashiga wanka.
"kafin ya fito fadi ta dauki sauran magani tasha.
"yana fitowa komai be shafaba kayan bcc kawai yasa, ita kuma fadi ta bashi abinci hade da juice.
"tana bashi ta shiga wanka, Mahfus yaci abinci sosae amma banda juice.
"fadi na fitowa taga besha juice ba sai tace meyasa bakasha juice din ba?
"Mahfus yace kawai dai.
"Sai fadi tace kuma sbd kai nayishi sbd naga kanaso sosae.
"Mahfus yace ayya kuma yau kinyishi kici rashin sa'a banaji sha, amma ki ije wani lokaci xansha.
"duk da fadi bataji dadi ba amma ta daure kayan bcc itama tasa.
"Mahfus yana gamawa ya mike..
"da sauri fadi tace ina xaka kuma?
"Mahfus yace dakin matana.
"fadi tace kamar yaya.
"Mahfus yace kamar yadda kikaji.
"sai fadi tace amma naga yau a guna kake.
"Mahfus yace eh nasan da haka amma ida xaki duba wata nawa nai a dakinki, banje dakin ta ba?
"kuma bata nuna damuwar ta akan hakan ba.
"Fadi tace to ni ina ruwana wannan matsalarkace sbd kai kaxabi hakan.
"Murmushi Mahfus yai snn yace naji nina xabi hakan yanxu kuma naxabi nakuma dakin matana...
"fadi tace amma Mahfus..
"Mahfus yace dan Allah kina batamin lokaci, d'an abinda xanje nayi saikin cinjemin lokaci ni gaskiya dare nayi xantafi duk mgnr da kike dashi kibari gobe sai muyi.
"Mahfus ya karisa mgnr ne hade da tafiya, har yakai bakin kofa sai yadawo ya dauki jakarsa hade da wasu daga cikin kayan sawarsa snn yace to madam fadi atashi lpy.
"yana fita wani irin kuka fadi tasa, shiko Mahfus dakin amatullah ya shiga.
"yana shiga kan gado Mahfus ya xuba kayan saida ya bude wadrop snn ya fara daukar kayan daya bayan daya yana jeresu a cikin wadrop.
"amatullah tana kwance cikin kayan bccta tana kallonsa, zunnurai dake kwance gefenta tuni yariga yai bcc.
"yana gamawa ya dauki zunnurai har yakai bakin kofa da sauri amatullah tasha gabansa.
"babu yadda Mahfus beyiba akan yakai zunnurai dakinshi amma amatullah taki yarda.
"shikuma Mahfus yace wlh amatullah baxan yarda na kwana da zunnurai a gado daya ba, saidai in xai kwanta a kasa..
"da sauri amatullah tace na yarda.
"bude wadrop dinta tai ta dauko bargo tai masa shinfida akan carpet hade da sa masa pilo.
"Mahfus ya shinfidashi snn yai masa addu'a, yana mikewa ya kashe light.
"hayewa kan gado yai hade da sawa amatullah hannu a jiki.
"amatullah najin haka da sauri ta cire masa hannu, murmushi yai snn yasake sawa ita kuma tacire.
"da Mahfus yaga haka mikewa yai yatube snn ya haye jikinta..
"amatullah taso tai mgn da sauri Mahfus ya toshe mata baki hade da kara bakinsa a gidin kunni ta yace kinga akwai yaro a dakin ko.
"dole yasa amatullah tai shiru.
"jin shiru da tai yasa Mahfus kwace mata ajiyar riganta, amatullah najin haka hada kafarta tai tsaf babu yadda Mahfus beyiba dan tabashi hanya amma amatullah taki yarda.
"da Mahfus yaga haka beyi kokarin tilassamata ba kyaleta yai, sai yasa hannu ya kamo nonuwarta yana wasa dasu.
"shiru amatullah tai kamar bata numfashi sbd ita kanta sha'awa ya kamata amma a yadda takeyi baxa iya bawa Mahfus kanta ba.
"jin shiru da tai yasa Mahfus kamo kan nonarta daya yanasha daya kuma rikewa yai ya murxawa.
"jin sperm yana gangarowa da sauri ya rike gabansa yana gogewa a nata da haka har yai released.
"yanajin sperm din yafara xubowa da karfi ya kankameta har saida ya gama released snn ya dauka.
"yana sauka rungumarta yai suka kwanta.
"duk uban leke2 fadi na yau ya gagareta sbd bakin biki ko bcc batai ba har safe.
"da asuba amatullah ta tashi taje tai wanka hade da alwala tana fitowa Mahfus yashiga yai nashi.
"yana fitowa yajasu sallah, suna idarwa amatullah ta duka har kasa ta gaidashi.
"Mahfus ya amsa cikin fara'asa hannu yasa ya dagota snn yace jeki ki hadawa zunnurai abinda xaije dashi school nikuma xan shiryashi.
"amatullah tana fita Mahfus ya tada zunnurai yai masa wanka snn ya shiryashi cikin school uniform.
"amatullah tana gamawa ta kawo, jallabi Mahfus yasa snn ya dauki zunnurai.
"suna fita saiga school bus yaxo daukarsa Mahfus yana sashi ya juya ya koma ciki.
"dakin fadi yashiga sbd yaga tashinta.
"yana shiga yaganta kwance hakan yasa yajuya ya fita yana fita fadi tace banxa kawai.
dakin amatullah ya koma lokacin tana made bargon da zunnurai ya kwanta shima cire rigarsa yai hade da jawota yace xo mu kwanta mu huta.
"ko kafin tai mgn Mahfus ya riga ya jawota jikinshi suka fada gado.
"rungumarta yai suka kwanta shafeta yakeyi hade da bata labarin yadda har kokin kasuwan cinsa suke tafiya.
"Da kuma yawon ribar da yasamu a cikin shekaranga.
"murmushi kawai amatullah tai.
H.S.Z.ce🖊
🌺💦🌺
💦
MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)💦
Fasaha online writes F.o.w.
MMN USWAN
H.S.Z.
35
"Mahfus yace amin.
"mikewa tai ta dauko masa abinci da ruwa.
"Mahfus yana gama ci ya shiga wanka, yana gamawa towel ya daura ya yaxo ya kwanta.
"yau ko dakin fadi beleka ba.
"itama wanka ta shiga tana fitowa ta meda kayanta ta kwanta tana kwanciya Mahfus ya kashe wuta.
'"yau ko d'an karamin bob bebari ba.
"har bcc ya fara daukar amatullah taji hannu Mahfus ya jikinta.
"tanajin haka da sauri ta cire masa hannu hade da matsawa.
"sake binta Mahfus yai, itama tasake matsawa.
"da haka har saida takai bakin gado gab da faduwa take.
"dagowa Mahfus yai snn yasa hannu ya jawota tsakiyar gado.
"jin haka yasata yukurawa da sauri Mahfus ya haye kanta snn yakai bakinsa daidai kunni ta yace haka amatullah menene kikeyi haka?
"sbd Allah yau kwana nawa kenan nake bibiyarki amma kinki bani hadin kai.
"idan ma wani laifi nai miki na tabbata iya kacin hukuncin da xakimin kenan banle babu kodaya.
"amatullah najin haka tasa kuka hade da fadi masa duk irin walakanci da yai mata..
"kafin ta karisa da sauri ya tushe mata baki, hade da cewa kiyi hakuri kinji in Allah ya yarda bazan karaba.
"duk Mahfus ya mgnr ne yana kanta hana shafeta.
"jin bata bude masa kafa ba yasa Mahfus cin gaba da cewa haka amatullah na lura nike sha'awarki ke baki sha'awta ko my baby meyasa yanxu kika baci da rowa ne?
"bayan da ba haka kikeba.
"hannu Mahfus yasa ya share mata hawaye snn yasa gashin gemunsa yana mata wasa dashi a fuska.
"da maimayi ya dami amatullah da karfi tace kabari mana..
"da sauri Mahfus ya toshe mata baki da hannu yana fadin kinga akwai yaro ko.
"shiru tai daga snn bata sake mgn ba.
"da Mahfus yaga batada niyar bashi sauka yai daga kanta yaja bargo ya rufesu.
"yana rufesu amatullah ta juya masa baya, koda Mahfus ya kai mata hannu yaji bayane.
"cire hannu yai hade da cewa ok tunda kika xabi haka nima na yarda amma a bakacin tafiyarki.
"amatullah najin haka da sauri ta juya tace haba Mahfus wani irin mgn kakeyi haka?
"bayan kariga kasamin rai.
"babu alamar fushi a tattare da Mahfus harda ma dariyansa yace idan mutum yanason xuwa gida to yabani hakkina kawai.
"koda Mahfus ya sake kai mata hannu batai musuba.
"gani haka yasa Mahfus kira motsowa ya shige jikinta.
"tunda Mahfus ya samu ya haye kanta mannewa yai yai ya makale mata abinka da mari jiki.
"tunda Mahfus ya makalewa amatullah saida yai released sau uku duk da haka Mahfus beda niyar sauka.
"mmki ne ya kama amatullah sbd da bahaka Mahfus yake ba, duk da Mahfus bamai hakuri ne akan mace ba amma yanxu yafi da.
"ada bewuce yai sau uku a dare kuma ba'a lokaci daya yakeyi ba, idan har yai released sau daya sauka yakeyi har sai ya huta snn ya koma.
"amma yanxu Mahfus ne har yai released uku kuma be sauka ba, da amatullah taji tagaji kuma shi Mahfus din beda niyar sauka.
"hannu tasa tafara tureshi, Mahfus najin haka kara mannewa yai ajikinta.
"da amatullah taga haka hannu tasa tafara muntsileshi da Mahfus yaji haka hakura yai ya sauka sbd yasan tagajine yasa haka.
"yana sauka yace I'm sorry my baby.
"shiru amatullah tai bata tanka shiba.
"ko minutes goma Mahfus beyi da sauka ba bcc ya dauki amatullah, bayan twenty minutes Mahfus ya sake komawa.
"da haka Mahfus yai tayi har safe ko sallar asuba Mahfus be samuba da daki yai shida matarsa suna idarwa yace ta fara hada kayan tafiya.
"sbd gajiya kamar tace abari sai gobe duk jikinta a mace yake ga kuma bcc dake addabanta.
"gani haka yasa Mahfus tayata shirya kayan a cikin akwati.
"suna gamawa ya dauki zunnurai yai masa wanka snn shima yai nashi.
"ita kuma kitchen ta shiga ta hada masu tea.
"Mahfus yana gama karyawa yace ta shiga tai wanka ta shirya kafin yadawo.
"daukar zunnurai yai suka fita tare yana fita dakin fadi ya shiga duk mgnr da yai tanajinshi amma tai banxa dashi.
"da yagaji da mgn ya fita yai tafiyar sa.
"kasuwa ya nufa kai tsaye ya sanarwa manager xaiyi tafiya amma ba dadewa xaiyi ba gobe xai dawo.
"manager yace Allah ya kiyaye hanya ya tsare sukace amin.
"suna gama mgnr da xasuyi Mahfus yacewa yaran shago su samasa four bag of rice a mota.
"bayan sun gama xubawa ne ya dauki kudi yace su siye masa katon din taliya guda biyar da vegetables oil jarka biyu da dai abinda baxa'a rasaba.
"yaran shagon Mahfus sai faman wasa da zunnurai sukayi.
"Mahfus yana gama hada kayan ya dauki zunnurai sukai gida inna yaje sallamarta.
"gani zunnurai inna ta amsheshi tana fadi maigidana na kaina yau auren ne ya tashi?
"shima zunnurai dariya yakeyi dauka yai daga jikin bbnsa yaje ya hau kafar inna.
"bayan sun gaisa ne Mahfus yace inna dama naso sallamarki ne xamuyi tafiya.
"da sauri inna tace ina xaka kuma Mahfus?
"Mahfus yace xankai amatullah gida ne.
"a take inna ta daure fuska hade da cewa yanxu amatullah din ne sai kakaita gida kamar wata karamar yarinya.
"ita ba xata iya xuwa da kanta bane sai ka kaita.
"idan katafi da'ita ita kuma fadi dawa xaka barta?
"murmushi Mahfus yai snn yace inna kenan to ai ba dadewa xanyi ba gobe xandawo.
"shiru tai fuskan nan daure, gani haka yasa Mahfus ciro kudi dubu biyar yace inna gashi asai goro.
"jiki na rawa ta amsa hade da samasa albarka da kuma fatan adawo lpy.
"ko kafin yakoma gida amatullah ta riga ta shirya shi take jira.
"mikewa Mahfus yai hade da cewa inna xamu tafi zunnurai najin haka da sauri ya mike.
"Mahfus yace zunnurai baxaka xauna a gun inna ba?
"girgixa kai yai.
'"inna tace Allah ya raka taki gona, nima na huta.
"dariya Mahfus yai hade da rike hannu zunnurai.
"inna tace Allah ya kiyaye hanya kadawo lpy.
"dukawa Mahfus yai hade da cewa amin inna nagode.
"Mahfus yana isa gida yashiga dakin fadi sbd sunyi sallama duk mgnr da yai mata bata tanka ba.
"da yaga haka yasa nasan kina jina dama na shigo ne muyi sallama dake sbd xamuyi tafiya da amatullah amma in Allah ya kaimu gobe xandawo.
"da sauri fadi tace ina xaku?
"Mahfus yace amatullah ne xata gida.
"duk da ba haka tasoba amma wani irin dadi ne taji mikewa tai hade da cewa bari naje muyi sallama.
"ta suka fita a parlour ta tsaya tana jiransu Mahfus yana shiga yace dauki jaka ita kuma amatullah ta dauki zunnurai suka fita.
"suna fita tasa key ta rufe dakinta duk da haka bewa Mahfus ba saida ya kara amsar key din yasake rufewa da kyau.
"suna isa parlour fadi ta taresu da ashe tafiya xakuyi?
"amatullah tace eh wlh.
"fadi tace Allah ya kiyaye hanya ya tsare.
"amatullah tace nagode.
"Mika hannu fadi tai xata amshi zunnurai...
"da sauri amatullah ta kau dashi hade da cewa barshi kawai.
"da sauri amatullah tabi Mahfus fadi na biye dasu a baya.
"har Mahfus ya bude but'din mota gani fadi na xuwa da sauri ya meda ya rufe, dauko jakar yai yasa a baya yarufe snn yaxo ya shiga.
"Itama amatullah shiga tai ta xauna fadi ne ta rufe mata murfin mota Mahfus yana jin motar fadi ta fara daga masu hannu tana bey bey.
"ko kallonta amatullah batai zunnurai ne yake daga mata hannu.
"saida zunnurai ya daina hangota snn ya sauke hannu.
"ko cikin garin kano basu bariba bcc ya dauki amatullah.
"mgn Mahfus yai yaji shiru juyowa yai yaga har tai bcc, murmushi kawai yai sbd yasan shine ya hanata bcc da dare.
"zunnurai hannu yasa yana bubuga mmnshi, Mahfus yace ka kyaleta baka gani tana bcc ne.
"shima be dade ba yai bcc.
"gani shi kadai ne yasa Mahfus ya kaset din sheikh jafar yana ji.
"suna shiga kaduna amatullah ta falka, Mahfus yace me bcc har kintashi?
"murmushi tai hade da cewa sannu da tuki.
"murmushi yai yace yauwa sarkin bcc.
"amatullah tace kaine...
"Mahfus yace nine me?
"amatullah tace kaine ka hanani bcc da dare ai.
"dariya Mahfus yai yace idan banda abinki tafiya fa zakiyi, kinga yanxu da nasamu nai haka ya kikaji.
"murmushi amatullah tai.
"Mahfus yace idan kika dawo kuma na sake haka koma yafi haka.
"dukkansu dariya sukasa.
"tunda su Mahfus suka tafi wani sabon duriya ta bude na bincike duk kayan Mahfus dake dakinta saida ta bincika amma bstaga abinda takeso gani ba.
"Wasu takardu ta gani koda ta karanta ba sani ma'anarshi tai ba da haka tagaji ta hadura.
"su Mahfus suna isa ana kiran sallar magrib saida yai parlour snn duk suka fito shida amatullah Mahfus yana rungume da zunnurai sbd yana bcc.
"har parlour suka shiga lokacin hajiya na daki jin sallama ne yasa ta fito gani su amatullah tai kamar a mafarki.
"hajiya tai mmkin gani su amatullah sbd babu wanda ta sanarwa suna hanya.
"a gefe Mahfus ya tsaya gani haka hajiya tace bissmill snn ya xauna.
"amatullah ta amshi zunnurai ta kwantar dashi.
"saida Mahfus ya cire hula snn ya duka har kasa ya gaida hajiya.
"itama amsawa tai da fara'arta hade da tambayarsa iyali.
"Mahfus yace duk suna lpy.
"Amatullah na kwantar da zunnurai ya bude ido gun bbnshi ya koma ya tsaya.
"Mahfus ne yace zunnurai ga hajiya jeka ka gaida ta.
"zunnurai tsayawa yai ya xubawa hajiya ido ya kallonta.
"amatullah ne tasa hannu ta jawoshi jikin hajiya snn hajiya ta daukeshi tana dariya.
"mikewa amatullah tai tashiga kitchen ta daukowa Mahfus ruwa da lemo ta kawo masa.
"dukawa tai ta xuba a cup snn ta mika masa.
"hajiya na gani haka ta mike ita da zunnurai suka shige ciki.
"hajiya na shigewa Mahfus ya dawo kusa da amatullah ya xauna.
"sai amatullah tace bari na kawo maka abinci.
"Mahfus yace aa xanje nayi sallah na dawo.
"mikewa yai ya nufi masallaci.
"ita kuma amatullah kitchen ta shiga ta bude tana duba wani irin abinc ne hajiya ta dafa.
"tuwun shinkafa da gani da miyan agushi da yasha nanan rago.
"dibawa Mahfus tai a wani kula da miya ta kai masa dinner snn taje nata sallah.
"tana idarwa Mahfus yakirata ta waya yace gashi a parlour.
"mikewa tai taxo tana xuwa tace suje dinner yaci abinci.
"yana xama ta xuba masa a plate yaci suna hira har ya koshi hajiya na daki ita da zunnurai amma duk mgnr da sukeyi tanajin su.
"yana gamawa suka dawo parlour sukaci gaba da hira, zunnurai yanajin muryar bbnsa yace saidai a kaishi.
"hajiya ne ta rakoshi parlour tana shiga parlour Mahfus ya duka suka sake gaisawa snn ta xauna.
"xama tai suna hira tare tun Mahfus najin kunya har yasaki jiki suka kama hira.
"suna cikin hirar ne yya khamis da yazed sukai sallama. yazed na gani amatullah a guje yaje ya rungumeta yana murna.
"mikewa Mahfus yai saida yya khamis ya xauna snn shima ya xauna yya khamis ya mike masa hannu su gaisa amma Mahfus yaki miko nashi hannu gaisa wa kawai sukai.
"yazed ya dauki zunnurai yana cewa kai me kama da bbnshi.
"dariya Mahfus yai.
"yya khamis jawo zunnurai yai hade da cewa kai xo mugaisa.
"saida suka taba hira snn yya khamis ya mike hade da sallamarsu.
"bayan ya fitane Mahfus ma ya mike hade da kiran yazed suka fita.
"suna fita Mahfus ya bude mota yacewa yazed ya kama masa, hannu yasa suka sauke Mahfus yace su dauka sukai ciki.
"yazed yace yabari kiran mai gadi yai yaxo ya kwashe xuwa cikin parlour a gefe guda aka xuba.
"tsayawa Mahfus yai a waje yace yazed ya kira masa amatullah, tana fitowa Mahfus yace shi xaitafi kwanciya.
"Cewa to kawai tai snn tace ina xuwa, da sauri ta shiga ciki ta sanarwa hajiya, tare suka fito hajiya ta haushi da fadi tace cewa menene kakeyi kamar bako sbd Allah.
"kai daban ne amatullah da ban?
"dakai da amatullah duk daya na dauke ku.
"Mahfus ya duke yace kiyi hakuri hajiya.
"hajiya tace babu komai ya wuce taso mu shiga ciki.
"mikewa Mahfus yai suka shiga ciki, suna shiga hajiya ta shige bedroom dinta hade da kiran amatullah.
"amatullah na xuwa hajiya ta dau key ta bata hade da cewa key daki ne ki bude wa Mahfus ga bargo ki hada masa dashi.
"tana xuwa ta bude masa dakin ta gwara masa gado hade da ije masa bargon.
"parlour ta koma da sanar dashi mikewa yai ya biyota suka koma cikin dakin tare.
"toilet ta shiga ta hada masa ruwan wanka tana fitowa tace masa xantafi saida safe.
"da wasa Mahfus yace kixo mu kwanta mana..
"bude baki amatullah tai hade da dariya snn sukai sallama.
"tana fita ya shiga wanka yana fitowa ya kwanta.
"itako amatullah hira sukai sosae da hajiya, duk hiran da sukai koda wasa amatullah bata aibanta Mahfus ko danginsa a gun hajiya ba, saidai ta fadi alkairinsa.
"duk da hajiya tasan akwai matsala a kasa amma taji dadin ganisu haka da tai.
"basu kwanta ba sai shabiyu, asuba nayi hajiya ta tada amatullah akan taje ta tada Mahfus sukafi masallaci dare sukaje da yazed.
"itama ta koma tai nata,tana idarwa hajiya tace tashiga kitchen ta hadawa Mahfus abin breakfast.
"arish ta soya masa da kwai hade da tea tana gamaawa a kula ta xuba saida tai wanka snn taxo ta dauka takai masa.
"shima lokacin ya gama nashi wankan ita yake jira tana shiga bayan sun gaisa ne ya bata key din motarshi yace taje ta dauko masa kayansa kuma ta meda wanda ya cire.
"tana dauko masa yasa snn ya karya yana cikin karyawa ne a cikin hira amatullah take tambayar sa wata nawa xatai?.
"😳 ido Mahfus ya bude hade da cewa wata fa kikace?
"nikuma na xauna dawa?
"dariya amatullah tai.
"Mahfus yace ina laifin kwana uku?
"shidinma a takure xankai.
"amatullah tace haba Mahfus kwana uku fa kace.
"Mahfus yace to hudu.
"amatullah tace aa.
"Mahfus yace to sati.
"amatullah tace biyu ko uku.
"wani mugun harara Mahfus yai mata hade da cewa sati.
"amatullah tace haba Mahfus...
"da sauri Mahfus yace ke wlh bazan kara miki koda yini daya ba.
"da haka sukai ta hira har yakare, yana gamawa tare suka fito parlour amatullah taje ta sanarwa hajiya Mahfus xai tafi.
"tana fadi mata tare suka suna fitowa Mahfus ya duka yana sallamar hajiya.
"hajiya tai masa fatan sauka lpy.
"hajiya na juyawa Mahfus ya mike suka fita a bakin motane Mahfus yasa hannu ya dauko kudi hundred thousand yabata yace tabawa hajiya snn yasake dauko wasu ya bata koda xata bukaci wani abu.
"amatullah tai masa godiya da fatan sauka lpy.
"har Mahfus ya bude mota xai shiga hannu yasa ya jawo amatullah jikinshi rungumarta yai hade da kiss yace dan Allah ki kulami da kanki da yarona.
"murmushi tai snn tace in Allah ya yarda.
"snn Mahfus ya shiga mota yaja dagawa amatullah hannu yai har yashige.
"itama daga masa takeyi.
"saida taga shifiyarsa snn ta juya ta shige ciki.
"basusan duk abinda sukeyi hajiya na hangosu ta window ba.
H.S.Z.ce🖊
🌺💦🌺
💦
MATAR RAFI
(THE FIRST WIFE)💦
Fasaha online writes F.o.w.
MMN USWAN
H.S.Z.
36
"amatullah tana shiga kai tsaye dakin hajiya ta nufa.
"lokacin hajiya na xauna bakin gado tace har kindawo?
"amatullah tace nadawo hajiya.
"Sai hajiya ta sake har maigidan naki ya tafine?
"amatullah tace eh yatafi gashi ma yace nabaki.
"kudi ta dauka tabawa hajiya.
"hajiya ta amsa hade da sa albarka.
"amatullah nawa hajiya kudin mikewa tai takoma dakin da Mahfus ya kwana taje kwaso kayan abincin da yaci.
"amatullah na mikewa hajiya ta bita da kallo tana mmkin Mahfus yadda yaketa shanawarsa da kudin da banasa ba, harda kara aure.
"yanxu hak duk wannan tsarabar a cikin kudine.
"can kuma da tai wani tunani sai tace menene a rayuwar idan zasu xauna lpy ma duk me sauki ne daukar kudin hajiya tai tasa a cikin wadrop ta ije.
"bayan amatullah ta dawo sai tace ta shirya yazed ya kaita gidan alhji Ibrahim ta raba shinkafan biyu ta dauki bag two da jarkan mai ta kai masa.
"idan ta ije ya kaita gidan yya Abdul shima in suka gaisa sai ta wuce gidan kamarudee ta gaishesu dama kwanana matarsa ta haihu na uku.
"da yamma sai takoma gidan alhji Ibrahim ta kwana.
"da safe idan ta dawo sai kuma taje gidan yya khamis shima ta kwana daga nan sai gidan Anty Frd ko?
"amatullah ta eh yayi.
"suna cikin mgn saiga yazed ya shiga bayan su gaisa ne amatullah tace dama yanxu xanje tadaka ko na kiraka ta waya.
"dariya yai hade da cewa abinda koda kin kirani baxaki sameniba.
"amatullah tace sbd me?
"yazed yace wlh Anty wayar tawace ta samu matsala, ni dama xaki bani takice.
"da sauri tace aa baxan bakaba sbd a ciki nake kallon abba, saidai na baka kudi ka siye wani.
"Da sauri yazed yace Anty na kenan shiyasa nake sonki sosae.
"a lokacin hajiya tasa baki tace eh tunda kafita wayo ba, ai ba rasa kudin siya wata wayar karasa ba.
"dariya yai hade da kashewa hajiya ido.
"amatullah bag dinta ta yawo ta ciro fourty thousand tabawa yazed.
"amsa yai hade da godiya.
"suna cikin hira saiga kiran Anty Frd ya shigo ta kira gaida hajiya.
"hajiya na dagawa Anty tace ina kwana hajiya.
"hajiya tace lpy klau ya aiki da kwanan maigida?
"Anty tace ply klau, hajiya kinajin motsin yar'kano kuwa?
"hajiya tace gasu ma sun xo.
"cikin murna Anty Frd tace Allah da gaske?
"yau she sukazo?
"hajiya tace jiya ne maigidanta ya kawota.
"mikawa amatullah wayar tai, amatullah tace Anty ina kwana.
"Anty tace lpy klau ina yarona bashi naji muryarsa kafin nazo.
"Anty tace to shikenan ki gaida min dashi kafin nazo.
"jin tace xata xone yasa hajiya cewa amatullah tabar tafiya xuwa gobe.
"zunnurai yana tashi mmnshi tai masa wanka snn ya karya, yana gamawa yazed ya daukeshi suka fita.
"Mahfus yana isa saida ya biya kasuwa tunku kafin yaje gida, yana isa kasuwa ya kira amatullah ya sanar mata ya'isa.
"baya sun gama snn ya kira fadi itama ya sanar da'ita ya iso amma yana kasuwa.
"suna gama waya fadi ta shiga kitchen hada mata abinci.
"la fiyayyar abinci ta hada masa tana gamawa tai wanka tasha kwalliya ta xauna xaman jiransa.
"Anty bata xoba sai bayan isha tana sallama a guje amatullah taje ta rungumeta tana fadi Anty oyoyo.
"itama rungumeta tai tana fadi mutan kano sannunku da xuwa.
"gani zunnurai ya taso yasa Anty Frd tace matsa na dauki yarona.
"daukar zunnurai tai ta rungume tana fadi oyoyo my son.
"bayan ta xauna ne amatullah ta duka ta gaida ta.
"amsawa tai cikin fara'arta hade da cewa ina mijinki?
"amatullah tace yakone.
"dago fuska zunnurai yai yana kallon Anty Frd.
"tallafo fuskanshi tai tana cewa ina dady ka?
"zunnurai yace dady na yaxo ya tafi.
"dariya sukai hajiya tace zunnurai kenan to ai xaidawo ko.
"kai kawai zunnurai ya daga.
"hajiya tace kodai xata xauna da nine?
"kaga idan bbnka yaxo sai nace ya barmin kai..
"da sauri zunnurai yace aa idan dady na yaxo binshi xanyi mu tafi garinmu.
"mangaran masa kai Anty tai snn tace Allah yasa kowa yanada gari.
"hajiya na gani haka ta daukeshi ta rungume snn tace Frd ga kayan da Mahfus ya kawo.
"kallon kayan Anty Frd tai hade da yamutsa fuska snn tace a kudin mu.
"murmushi hajiya tai snn tace Frd kenan.
"mikewa anty tai hade da cewa ni xantafi dare nayi.
"hajiya tace a sauka lpy.
"amatullah ma tace Anty sai nazo.
"Mahfus yana shiga gida fadi da fara'arta ta tareshi saida ta rungumeshi snn ta amshi ledar hannushi.
"kari sowa yai ta xauna akan cushion ruwa ta kawo masa saida ya amsa yasha snn tace sannu da dawowa.
"yace yauwa ya gida?
"tace lpy klau ya hanya?
"Mahfus yace hanya alhamdllh.
"snn tace ga abinci ka a dinner table ko nakawo maka nan ne?
"Mahfus yace aa barshi kawai.
"Mikewa yai suka tafi tare yana xama ta xuba masa yanaci suna hira saidai ba haka taso tajin hirarba sbd koda ta sako mgnr amatullah a ciki sai Mahfus ya kauce, bayan ya koshine suka mike hanyar dakin amatullah ya nufa.
"da sauri tace ina xaka kuma?
"Mahfus yace wlh a gajiye nake wanka xanyi snn na kwanta.
"Mahfus ya karisa mgnr ne hade da tafiya.
"da sauri fadi tasha gabansa tace cewa haba Mahfus me kake nufi da nine sbd Allah.
"duk da ma babu amatullah a gidan shine saika kwana a dakinta?
"to wlh bazai yuwuba, nima mecece kamar kowa kuma nima matarka ne kuma dan haka wlh daga yau saidai a raba girki kowa yasan ma xaunishi.
"tsayawa Mahfus yai hade da rike kugu yace to yanxu me kike nufi?
"fadi tace ina nufi raba mana kwana xakai.
"sai Mahfus yace to yanxu kibari sai amatullah tadawo duk yadda xa'ayi sai ayi.
"fadi tace to na'amince, amma dai kasan idan har ka kwana a dakin amatullah bakamin adallaci bako?
"nimafa matar kane kuma yau tsawo kwana nawa nake bukatar ka, idan kaida nake xamanka bakaimin magani ba kanaso naje wanine yaimin?
"da sauri Mahfus yace ke wani irin mgn kikeyi haka?
"me kuma yakawo xance wani?
"waya shige muje.
"tasa a gaba yai suka shige, suna shiga ta toilet ta shiga ta hada masa ruwan wanka snn tafito.
"tana fita tai masa mgn yashiga, Mahfus yana shiga wanka ta bubude wasu maguguna tasha kafin ya fito.
"yana fitowa itama ta shiga ta sake watsawa karamin towel kawai ta daura tana fitowa ta kashe light hade da cire towel din.
"hayewa tai jikin Mahfus, duk da gajiyar da yai besa fadi ta barshi ya huta ba.
"da dare har amatullah ta kwanta sai hajiya ta da'ita cikin gigin bcc amatullah ta tashi zaune.
"sai hajiya tace amatullah.
"amatullah tace na'am hajiya.
"hajiya tace dan Allah dan annabi amatullah ki xauna da mijinki lpy, banaso kita da hankalinki akan kudin da yaci miki.
"dan Allah kada kibari wasu su xugaki amatullah ba keba ni kaina nasan kinfi karfin kudi.
"in kuma mgnr motane a gobe nan ni mai siye miki wanda yafi nada tsada.
"shiru amatullah tai tana hawaye.
"hajiya tace dan Allah amatullah inaso ki duba darajan d'annan da Allah ya baku kimai da komai ba komai ba.
"koda da wasane banaso naji ance kin masa mgn banle har sanadiyar haka yasa kusamu sabani.
"sai hajiya tace yataba hanaki abinci?
"amatullah tace aa.
"suturafa?
"amatullah tace aa.
"hajiya tace to kingani kodan darajan haka ma yasa ki kyaleshi.
"idan kuma mgnr auren da yai ne can tamatse masa nasan da xafi amma hakuri xakiyi wataran sai kabari.
"hajiya taci gaba da cewa amatullah duk wanda kika ganshi da mijinshi da kuma yaransu su kadai sukasan irin gwagwarmayan da sukasha a rayuwa snn suka kai wannan lokaci.
"amatullah koda Mahfus yana tutar dakene bazanso ki kashe aure kidawo mu xauna tare ba.
"amatullah nayi miki alkairi duk abinda kikeso in har befi karfina ba ki tambayeni xanmiki shi amatullah.
"ina yimiki hakane dan ki xauna lpy da mijinki Mahfus yana sonki kema kina sonshi dan Allah Ku xauna lpy.
"Amatullah tace in Allah ya yarda hajiya naji kuma na gode.
"hajiya tace gobe da safe idan Allah ya kaimu ki tunami idan yayanku ya shigo nai masa mgn kuje tare ki xabi kalar da kikeso.
"jin haka yasa amatullah fashewa da kuka ta rungume hajiya.
"hajiya tace menene haka kuma?
"ko duk kukan murna ne.
"sa safe Mahfus yacewa fadi tashirya xai kaita asibiti awo antenatal kafin yatafi kasuwa.
"fadi tace to hakan yasa tai sauri tai duk wani aikin da xatai ta shirya suka fita tare.
"da safe hajiya ta kira yya khamis tace yaxo dan haka beyi kasa a gwiwa ba yana fita daga gida yaje.
"yana shiga har kasa yaduka ya gaida hajiya.
"bayan sun gama gaisawa itama amatullah dukawa tai ta gaida shi bayan su gama gaisawa ne hajiya take sanar dashi.
"yya khamis yace babu damuwa idan ta shirya tafito sutafi.
"kyaleta ta dauko suka tafi harda yazed ya rakasu.
"suna isa yya khamis yace taje ta xabi wanda takeso.
"ita da yazed sukaje xaban sai faman ruwan ido sukeyi daga karke saida yya khamis yaxo da kanshi ya xaba mata.
"yace yayi mata?
"amatullah tace yayi.
"motar me kyau ne ga tsada har yafi wanda Mahfus yake hawa tsada.
"suna gama ciniki transfer yai masu, yazed ne ya dauki motar xuwa gida shida amatullah.
"suna ije motar ya rakata gidan alhji Ibrahim.
"Mahfus suna isa asibiti a wajan asibiti Mahfus ya tsaya ita kuma ta shiga ciki.
"tunda sukai parking wani mutum ya xubawa fadi ido, tasowa yai yaxo kusa da motar Mahfus ya tsaya jiran tafito ya gani ita din ne da gaske ko gixo take masa.
"fadi na fitowa har ta bude mota da sauri mutumi ya rike morfin motan yana kiran Fatima dama kina garinga?
"wani irin mugon kallon tai masa hade da daure fuska.
"da sauri Mahfus ya yafito ya xagayo yana fadin lpy malam menene?
"mutumi yace wlh matata ce.
"cikin xafin rai Mahfus ya dauke mutumi da mari.
"Mahfus yace dan ubanka aina taxama matarka?
"mutumi yasake cewa wlh matata ce na rantse da Allah.
"Mahfus yace da aurena a kanta kana kiran matarka.
"mutumi yace wlh nima da aurena akanta idan ma ta aureka to tayi aure akan aure ne.
"cikin tsawa Mahfus yace dan Allah dan rainin wayo tashi kabani gun.
"hannu Mahfus yasa xai tura fadi a cikin mota da sauri mutumi ya rike fadi yana fadin wlh babu idan xaki tsohowar mana fuka wlh hukuma ne zasu rabamu.
"dama na dade ina nimanki wlh yau koni koke.
"jin haka yasa fadi sa ihu tana fadin dan Allah Mahfus karabani dashi wlh mahaukacine.
"mutumi yace kedai mahaukaciya wlh yau saidai hukuma ne kawai zasu rabamu, muguwa azzaluma tsinanniya Allah ya'isa tsakanina dake.
"duk mgnr da yakeyi yana rike da hannu fadi yana faman janta.
"shima Mahfus yana rike da hannunta amma yakasa janta sbd kalaman mutumi ya kashe masa jin.
"ihu karya kawai fadi keyi sbd tasan mutumi yafita gaskiya.
"jama'ar dake kansu ne suka kamo hannu mutumi da kar suka babare fadi daga hannu mutumi.
"fadi na gani ya saketa da sauri tashige mota tana fadin dan Allah Mahfus kazo muje karabani da mahaukacinga.
"shiga mota yai yaja motar a guje.
"bayan Mahfus sukafine mutani da suka rike mutumi suka sakeshi.
"ihu yasa yana fadin Allah ya'isa tsakanina daku kuma wlh daga yau na tunga bibiyanta kenan shegiya kawai.
"watsawa sukai suka barshi yanata xage zage hade da hurta Allah ya'isa.
"tunda Mahfus yaja mota sukabar gun babu abinda fadi keyi sai kukan karya.
"shiko Mahfus shiru kawai yai be tanka mata ba sbd cajin da kansa keyi.
"gaba daya kansa ya daure.
"yana ijeta yatafi kasuwa.
"koda ya dawo daga kasuwa kwanciyarsa yai koda tai mgn baya tanka mata.
"safiya nayi wanka kawai yai yafita kasuwa be tsaya karyawa ba.
"da haka suka cigaba da xama har kwana uku a ran na uku ne bayan Mahfus ya dawo kasuwa dakin amatullah ya shiga xai kwanta har xai rufe kofa kenan saiga sallamar fadi.
"banxa yai da'ita tai ta salamar yanaji amma be amsa ba.
"gani haka yasa ta tura kofa xata shiga ciki..
"da sauri Mahfus yace aa kada kishigo ki tsawa nafito.
"fitowa yai yatsaya a bakin kofa snn yace gani.
"har kasa fadi ta duka tace dan Allah Mahfus kayi hakuri wlh wlh bansan mutumi ba.
"Mahfus yace idan ban sanki ba ta yy akai yarikeki kamar ke ka dai ne mace a gun?
"kuma ba hakaba kinji kalamar da yake fadi akanki kuwa fadi.
"cikin kuka fadi tace wlh karya yakeyi ni bantaba aure ba sai a kanka.
"kaine kawai na mijin da nasani a duniya.
"Mahfus yace ni ban tambayeki wannan ba.
"fadi tace wlh kuwa banida wani a laka da kowa, idan ma kana musune bari na dauko kur'ani na rantse maka.
"Mahfus yace na yarda amma d'an Allah ki kiyaye.
"fadi tace to nagode kuma in Allah ya yarda xan kiyaye.
"hannu Mahfus yasa ya dagota snn ya share mata hawaye yace jeki daki ki kwanta..
"da sauri tace kai fa?
"Mahfus yace aa kiyi hakuri gobe xamu hadu.
"tana shiga daki shima ya shiga dakin amatullah.
"tana shiga daki ta kwashe da dariya tana cewa har yanxu bakasan waye Fatima ba.
"shima bakin shegen maganinshi xanyi sai nasa a manmi dashi a doron kasa, snn kadawo kanka.
"hayewa tai gado ta kwanta hade da dauko wayarta tana dane dane.
"shima Mahfus yana shiga amatullah ya kira suka fara waya basu kwanta ba saida duk kudin wayarsa yakare wuraren 2-30AM snn suka kwanta.
"duk inda hajiya ta lissafawa amatullah duk taje alhji Ibrahim yaji dadi sosae gani amatullah da taxo ganinsu.
"kyauta sosae yabata itada zunnurai.
"su yya Abdul da kamarudee ma ba'a barsu abaya ba.
"yya khamis da motarshi haka.
"itako Anty Frd daukar amatullah da zunnurai tai xuwa shagonta na English wear wanda ake kawo matasu daga India Dubai ummura kayane ta xabanwa zunnurai na gani na fada.
"itama amatullah dike dike irin na manyan mata Anty Frd tai mata.
"ana gobe Mahfus xaixo hajiya ta hada masu kayansu tsaf gu daya.
"ita kuma Anty takai amatullah gun gwaran jiki da kai.
"amatullah ta dawo kamar amarya.
"washe gari ana sallar asuba amatullah ya kami hanya.
"axahar yai masa a gidan su amatullah yana parking yafito daga mota ya karisa ciki.
"karo sukai da amatullah a parlour da sauri suka rungume juna Mahfus yamance kamar gidan surukai ne harda kiss sukeyi.
"gwara muryar hajiya ne yasasu sakin juna da sauri Mahfus ya duka hade da cire hula suka gaisa.
"jin muryar bbnshi yasa zunnurai fitowa da gudu ya rungume bbnshi.
"bayan sun gaisa ne hajiya tace ya xauna a kawo masa abinci...
"da sauri Mahfus yace aa hajiya a koshe nake kaya kawai zasu dauko mutafi.
"hajiya tace da wuri haka?
"susa kai Mahfus yai hade da cewa wlh kuwa.
"a lokacin ne amatullah tace Mahfus.
"dago kai yai hade da cewa na'am.
"amatullah tace hajiya tasiyemi mota.
"Mahfus yace Allah amatullah.
"tace Allah kuwa.
"sake dukawa Mahfus yai yana godiya.
"dariya hajiya tai hade da cewa babu komai.
"snn tace katashi kutafi kada dare yai maku a hanya.
"shiga ciki amatullah tai ta dauko kayansu.
"tana fitowa Mahfus ya amsa yakai mota zunnurai yana biye dasu.
"har sai suka gama sa kayan a mota.
"amatullah tace xataja motar..
"da sauri Mahfus yace be yarda ba.
"gani yasa hajiya tace yazed ya bisu ya kai masu motar gida.
"Mahfus yace yabari kawai.
"fita sukai da yazed tasha sukaje suka samo wani drive sukai tsada da Mahfus ya biyashi.
"suna dawowa Mahfus yace tafito sutafi.
"saida yaduka yasake sallamar hajiya shida amatullah.
"hajiya tai ta samasu albarka hade da fata sauka lpy.
"amatullah da Mahfus da d'ansu suna motar Mahfus shikuma drive yana motar amatullah.
"hajiya da yazed suke daga masu hannu har suka fice.
"drive na gaba su Mahfus suna biye dashi.
H.S.Z.ce🖊
🌺💦🌺
💦
MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)💦
Fasaha online writes F.o.w.
MMN USWAN
H.S.Z.
37
"tunda Mahfus sukabar cikin garin minna gudu suke xubawa kamar wanda zasubar kasan.
"Kusan bibiye suke da juna babu wanda yaiwa d'auwasa nisa.
"gani goma tayi Mahfus be dawo gida ba yasa fadi nimarsa ta waya.
"duk kiran da tai yana kalla amma be daga ba sbd sauri.
"ita kuma besa ta daina kira ba har four miss call.
"gani ta sake kirane ya sashi dagawa.
"ko sallama babu banle gaisuwa Mahfus yana dagawa fadi tace me katsaya yine da har yanxu baka dawo gida ba?
"cewa kawai yai kiyi hakuri na kusan dawowa hade da kashe wayar.
"itama fadi hurga wayar tai hade da tsaki.
"shabiyu da rabi daidai su Mahfus suna shiga gida.
"fadi na zaune a parlour jin shigorwa motar Mahfus da sauri ta mike ta leko ta window ganishi da amatullah yasata barin gun da sauri ta shige dakinta tana fadin dan rainin wayo wanga banxan yaje dauka shiga yake boyemi.
"wlh da nasan ita yaje dauka ko sauraranshi bazan yiba banle har na tsaya jiransa.
"suna parking Mahfus ya fito shima drive yafito gani dare yai yasa Mahfus cewa drive ko xai kwana in yaso da safe sai ya tafi.
"sai yace aa abashi balance dinsa kawai ya tafi.
"Mahfus yasa hannu a aljihu ya ciro kudin ya bashi hade da godiya.
"ya rakashi har bakin gate yana fita Mahfus ya rufe shida bbn maigadi snn ya koma gun amatullah.
"bude mata mota yai ta fito ya amshi zunnurai dake bcc ya kafarta ya rungume snn itama ta fito hade da daukar handbag dinta.
"mike mata zunnurai yace ta jiranshi sa key yai ya rufe duk motocin duk snn ya mike mata key hade da amsar zunnurai yace sushiga ciki.
"amatullah tace kayan fa?
"Mahfus yace barshi kawai da safe xan kwaso.
"yana gaba tana baya suka shiga ciki, gani kofar parlour bude Mahfus ya dauka fadi na parlour ne da sallama ya shiga.
"Yai ta sallama yaji babu wanda ya amsa haka yasashi sa kai ciki, yana shiga yaga babu kowa a parlour kuma ga kofa a bude tsuki kawai yai ya karisa shigewa.
"da kanshi ya bude dakin amatullah suka shige,suna shiga ya kwantar da zunnurai a kan gado.
"gani hakan yasa amatullah bude wadrop din ta dauko bargo tai masa shinfida a kasa saida ta rage masa kayan jikinsa snn ta kwantar dashi.
"Mahfus yacewa amatullah ta hada masa tea kafin yafito wanka.
"tubewa yai ya shiga wanka ita kuma taje kitchen hada masa tea.
"kafin ya fito har tagama hadawa daki ta kawu ta xauna xaman jiransa.
"yana fitowa itama ta shiga xama yai a bakin gado yana shan tea, yana gamawa mikewa yai dagashi sai towel yaje yana yima fadi knocking.
"lokacin tana zaune a bakin gado tana jinshi har yai ya kare bata tanka shiba.
"da yagaji da knocking komawa yai dakin amatullah, gani yashigo amatullah tace na dauka acan xaka kwanta ai.
"ban yai da'ita be tanka mata ba, hayewa gado yai ya kwanta hade da cewa dan Allah ki kashewa mutuni light.
"tana kashe light hayewa tai ta kwanta.
"jin ta hau gadone yasa Mahfus matsowa inda take hannu yasa yana shafe mata fuska yana cewa hajiyata kinga yadda kika kara kyau kuwa?
"xonan matata ki fadin min menene sirin?
"Mahfus yara shigewa jikin amatullah yai hade da sa hancinsa yanayi kamar yana susunarta.
"yana cewa kinji kamshin da kikeyi kuwa na tabbata koda a maryane bazata gwada miki komai ba.
"dan Allah fadimin sirrin mana.
"amatullah na dariya tace wlh Anty ne ta kaini gun gwaran jiki aka gwarani.
"Mahfus yace waishhhh sauke mata numfashi yai a jiki hade da cewa gaskiya Anty ta kyau kuma tana sona da yawa tunda har ta gwaramin matana.
"gaskiya ni d'an gatan Anty ne.
"da maganganu masu dadi ta kwantar da hankali Mahfus yake fadiwa amatullah da haka har yasamu ya biya butakarsa.
"yau ma hakane kusan hana amatullah bcc yai motsi kadan saiya koma da haka har asuba yai.
"da asuba ma har yamike xai kara hayeta kukan zunnurai ne yasashi dakatawa mikewa yai hade da daura towel yashiga toilet yai wanka da alwala snn yaxo ya fara sallah.
"ita kuma kitchen ta shiga ta hadawa zunnurai tea ta kawo masa snn tashiga toilet wanka.
"zunnurai yana gama sha ya mike xai fita.
"tsawa Mahfus ya daka masa hade da cewa dawo ka kwanta.
"dawowa zunnurai yai ya kwanta rage light din dakin Mahfus yai gani duhu a dakin yasa zunnurai komawa bcc.
"amatullah na idar da sallah suka koma suka kwanta, suna kwanciya bcc ya daukesu.
"fadi bata tashiba sai shadaya bayan tai wanka kitchen ta shiga dan niman abinda xataci.
"arish ta soya da kwai snn ta hada tea parlour ta dawo saida ta kunna TV zeeworld volume tasa sosae snn ta xauna ta fara breakfast.
"ita kanta volume din ya dameta amma besa ta rageba.
"suma su Mahfus jin volume din besa sun tashi daga bcc ba saida axahar.
"Mahfus ne yafara tashi wanka ya shiga bayan ya fitone ya tada amatullah itama tashiga nata wankan kwalliya Mahfus yai cikin kananu kaya ba karamin kyau yai ba.
"shima kanshi yasan yayi kyau, suna hada ido da amatullah gira ya daga mata.
"itama murmushi tai masa, bayan ta gama shafa mai ne hade da kwalliya tacewa Mahfus yaje mota ya dauko masu kayansu.
"yana fita ta tada zunnurai tai masa wanka ta shafa masa mai.
"shima Mahfus yana fita suka yaga fadi a parlour zaune tana kallo.
"xama yai kusa da'ita hade da cewa madam kintashi lpy.
"a yamutse ta amsa da lpy.
"dariya Mahfus yai hade da sa hannu ya dago habanta.
"hannu itama tasa ta bude masa nasa hannu.
"dariya Mahfus yai snn ya mike ya fita.
"yana fita ta mike ta lekarsa ta window.
"can gefe ta hango sabuwar mota mmki ya kamata yana kwaso kaya yasa key ya rufe motar snn ya kwaso kayan zuwa ciki.
"gani zai shigo a guje ta koma ta xauna.
"shima be tanka mata ba kai tsaye dakin amatullah ta shiga, itako fadi bin jakar takeyi da kallo sbd taga ba dasu amatullah tai tafiya ba.
"yana shiga amatullah ta tareshi ta amsheshi.
"bayan Mahfus ya xauna ne yake tambayar amatullah ina tasamo wannan jakar?
"itama xama tai kusa dashi snn tace Anty Frd ce ta siyewa zunnurai hade da kaya a ciki.
"hannu yasa ya jawo jakar yana bude kayan yake dagawa daya bayan daya yana duba quality dinsu.
"saida ya gama dubawa snn yace amma kayan suna da kyau.
"amatullah tace eh kasan daga Dubai Cairo India har ma da China tana xuwa siyo kaya gani wasu a kasar akwatin yace wannan fa?
"amatullah tace shima duk ita ta dinkamin.
"daga su yai ya kare masu kallon snn yai godiya, da kanshi ya xaban mata wanda xatasa riga da sket snn kuma ya xabawa zunnurai da kanshi ya sama masa.
"bayan amatullah ta gama shirine Mahfus ya kalleta murmushi yai hade da cewa baby kinyi kyau fa.
"murmushi itama tai hade da cewa nagode.
'"bude mata kofa yai tafita shima fita yai yana rike da hannu zunnurai parlour ya nufa ita kuma amatullah ta shiga kitchen hada masu abin breakfast.
"bayan Mahfus ya xauna ne fadi tace naga sabuwar mota Allah ya kara arxiki.
"Mahfus yace amin amma ba nawa bane, na amatullah ne mmnta ta siye mata.
"shiru fadi tai kamar bataji abinda yace ba.
"tun daga lokacin bata sake mgn ba koda Mahfus yayi kyaleshi takeyi.
"amatullah na gama hada abin breakfast takai dinner snn taxo ta sanarwa Mahfus.
"Mahfus yace aa ta kawo masa nan kawai.
"gani amatullah da sabbin kayan da bata santa dasu ba yasa fadi kallon amatullah daga sama har kasa ta xabga mata harara.
"da amatullah ta lura da haka canxa sallon tafiya tai, dan karin bakin ciki saida ta dawo gaban Mahfus snn tace mema kace?
"Mahfus yace cewa nai kikawomin nan.
"dama riga da sket tasa tun daga gabansa tagansa tafara canxa salon tafiya duk yadda ta juya haka bayanta yake juyawa.
"shiko Mahfus gaba daya hankalinsa ya koma kan amatullah yabar kallon TV da yakeyi.
"itako fadi sai xabga masa uban harara takeyi.
"amatullah tana kwaso kayan da rangwada take tafiya kamar wanda xata karye tana isowa gaban Mahfus da sauri yasa ya tareta gani yake kamar xubewa kayan xaiyi.
"kafin ta zauna saida ta gwara wiyar rigarta gaba daya kusan rabin nonuwarta a waje yake snn ta xauna xuwa nonuwar ido Mahfus yai kallon TV ya gagara.
"gani hakan yasa amatullah narkewa tana xuba masa shagwaba tunda tasan fadi ba turanci sosae takeyi yasa amatullah ta daina mgn da hausa.
"duk mgnr da xasuyi da turanci sukeyi, tana hada tea din kamar ba xatai ba.
"gani haka yasa Mahfus amsar spoon din da kansa ya hada yana gama hadawa ya dauka yasa Mahfus dauka yana bata a baki.
"kaiwa na farko da yai mata ihu tasa hade da yarfe hannayeta tana fadin akwai xafi.
"da sauri Mahfus yace sorry baby.
"tun daga lokacin duk dibawar da xaiyi saiya hura kafin ya bata.
"haushi ya kama fadi hurgi tai da remate din hannunta ta mike hade da cewa wani waka kancin baxa.
"da sauri Mahfus yace aa madam xo mana yaya akai ne.
"ban tai dashi ta shige daki.
"suna gama karyawa amatullah ta kwanta a jikin Mahfus shikuma hannu yasa cikin riganta yana wasa da nonuwarta.
"shikuma zunnurai yana kwance akan cushion yana wasa da wayar bbnshi.
"da Mahfus yaji ba xai iya jurewa ba daukarta yai cak kamar karamar yarinya xuwa daki.
" sai daga baya zunnurai yana juyawa yaga ba iyayensa a parlour da sauri ya bisu ciki.
"ko kafin yaje su riga sunci gari.
"yana shiga ganinsu yai suna hira xama yai yaci gaba da game har bcc ya daukeshi.
"gani yai bcc yasa Mahfus xare wayar daga hannunshi snn ya jawo amatullah jikinshi ya dora daga inda ya tsaya.
"itako fadi tuni ta riga ta yanke shawarar cire ciki baya ya fita sai tasan abinyi.
"su Mahfus basu fitoba sai bayan la'asar suna tashi tare sukai wanka Mahfus yana rungume da'ita baya sunyi wanka ne hade da alwala suka fito sukai sallah.
"suna idarwa wani kwalliya ta sakeyi daya daga cikin kayan da Anty ta batane tasake dauko daya daga ciki doguwar riga wanda ya bata shep tasa shiko Mahfus dagashi sai short nicker suka shiga kitchen tare suke aikin abinci.
"amatullah ne ke daura sanwa Mahfus kuma ke bare su maggi motso daya biyu sai Mahfus ya rungumeta.
"duk abinda sukeyi fadi na kallansu.
"da haka sukai har suka kare, bayan sun karene Mahfus yace amsawa fadi amatullah batai musuba ta xuba masa tace ya dauka ya kai mata daki.
"jikin Mahfus na rawa ya dauka yakaiwa fadi, da sallama ya shiga dakin tanajin tai shiru kamar bata jishi ba.
"bakin gado ya xauna yace madam tashi kici abinci kada kibarmin baby na da yunwa kinjiko.
"cikin kaukausar murya fadi tace uban uban baby yaci ubanshi kuma gobe goben nan xan cire cikin naga ta iskanci.
"mana fiki algungumi wanda besan dokokin aure ba.
"dariya Mahfus yai hade da cewa duk nikadai?
"mikewa tai hade da daukar plate din abincin ta watsa masa.
"da sauri Mahfus ya mike yana fadin fadi ni kika wa haka?
"fadi tace anyidin dan rainin wayo.
"a fusace ya daga hannu zai mata mari ko mai ya tuni da sauri yafita daga dakin.
"dakin amatullah ya shiga lokacin tana zaune tana jiranshi.
"boye damuwar sa yai snn ya shiga amatullah tana gani duk jikinsa ya baci da abinci da sauri tace kayi barine?
"Inda inda Mahfus yai hade da cewa eh aa eh karo nai da karfe gado.
"shiru amatullah tai ta kyaleshi sbd ta riga taji duk mgnr da fadi keyi.
"mikewa yai ya shiga toilet ya wanke jikinshi snn yafito yaci abinci.
"suna gamawa amatullah ta kwashi kayan ta meda ciki.
"ana idar da da sallar isha su kwanta saiga fadi tana masu knocking.
"Mahfus ne ya fito daga shi sai gajeran wando wani kallon banxa fadi tai masa snn tace kace ta fito mgn xamuyi.
"Mahfus yace mgn kuma fadi kibari da safe mana...
"da sauri fadi tace yanxu nakeso ayi ba sai gobe ba.
"lekawa Mahfus yai ya kira amatullah daga ita sai rigan bcc ta fito.
"Mahfus yace ina sauraranki.
"fadi tace girki nakeso a raba yau dinnan sbd kowa yasan ma xauninsa.
"tsaki amatullah tai snn tace baby ni xankoma ciki idan kagama ina jiranka.
"tana shiga Mahfus yace dan Allah kibari gobe da safe sai muyi mgn.
"da sauri fadi tace wlh baka isa ba.
"Mahfus yace nidai baki isa ki hanani abinda nai niya da daren nan ba kinga ma shige wata idan kinga xaki bari sai gobe to in kuma baxaki bariba kekika sani.
"yana shigewa fadi tace dan'iska sai nayi maganinku daga kai har ita.
"dakin ta koma tana tunani ta inda xata bulo masu.
"da safe bayan amatullah ta shirya zunnurai xuwa makaranta Mahfus ne ya kaishi har school din sbd tafiyar da sukai kwana biyu.
"Mahfus yana fita fadi itama ta fita wani chamis tasiye magani cire ciki.
"da kar mai chamis din yabata saida ta xuba masa kudi da yawa snn ya yarda ya siyar mata.
"da sauri ta koma gida kafin Mahfus ya dawo tadawo tana shiga kitchen ta nufa ta hada tea snn ta koma dakinta.
"saida ta karya snn ta dauki magani tasha double dinshi ma tai sbd yai mata aiki da sauri.
"tana gamasha ta kwanta tana jiran result.
Mahfus yana dawowa wanka yashiga sbd yanaso ya fita kasuwa da wuri sakamakon rashin xuwan da yai kwana biyu.
"bayan Mahfus yafita amatullah ta kira Anty Frd bayan sun gaisa ne amatullah take bawa Anty labarin.
"dariya Anty tai snn tace rabu da'ita nidai shawarata dake shine kada ki sake kiyi ciki yanxu har sai kinga kamu ludayinshi.
"kuma duk abinda kikasan yafi so shine zakiyi kada ki saurara masa ko kadai.
"amatullah tace to Anty naji kuma nagode.
"nai dai takara bata shawarwari da yadda xata kara rike Mahfus.
"shiru shiru ko gexau bata jiba.
"ita kuma amatullah tunda tasan babu abinda Mahfus yakeso kamar a rinka nuna masa so a kowani lokaci haka yasa ta xage dantse wajan bashi kulawa da kuma bashi hadin kai a duk lokacin da xo mata.
"kuma yanxu ta daina sauraranshi idan tana bukatar abu saidai tabashi kudi tace ya siyo mata.
"shiyasa gaba daya amatullah ta gama jayo Mahfus a jikinta.
"itako fadi shiru da taji yasa ta canxa shawara Mahfus yana fita itama ta fita gun areas boys dinnan ta koma wannan karo motocin gidan tace su kwashe suna daukawa subar garin.
"tana tafe tana mgn a xuciyarta tana fadi badai kajuyamin baya ba yau xakuga iyakanku a hankali saina kwashe dukiyar da kuke takama dashi snn nabar gari.
"da haka tai yi har takai gida.
"tana shiga suka hadu da amatullah a parlour tana zaune tana jiran zunnurai yadawo daga school.
"da yamma baya mahfus ya dawo daga kasuwa dukkansu a parlour suka xauna suna hira kamar babu komai a xuciyar fadi.
"gani goma yai yasa Mahfus cewa kowa yaje ya kwanta shima mikewa yai yaje ya rufe kofar parlour snn yaxo yashige dakin fadi.
"yau sakar mata jiki tai yai abinda yakeso shiru da tai ya dauka bcc ne tai yasashi shima kwanciya be nimi matsa mataba sbd cikin da yake jikinta.
"bcc na daukar Mahfus a hankali fadi ta tashi taje ta bude kofa snn ta dawo ta kwanta.
"2-30 daidai sukaji ana knocking a kafar dakin fadi.
"Mahfus ne ya tashi yaje ya bude kofa, yana budewa suka sa masa bindiga a kunni.
"da sauri fadi ta taso taxo bayan Mahfus ta boye jikinta na rawa na karya.
"sukace kabamu key mota.
"Mahfus yace banda mota...
"kafin ya karisa daya ya daukeshi da mari yana cewa wanda yake waje na ubanka ne?
"amatullah najin marin da akaiwa Mahfus yasata tafito.
"itama kara mata bindiga sukai.
"duk yadda sukakai ga tsorata Mahfus dan yabasu key din motar amma yaki.
"gani yaki fadi tasa kuka tana fadin dan Allah kuyi hakuri kada ku kashemi mijina dan Allah.
"daya daga cikinsu sukace idan har kuna sonshi to kufito da makulan motocin gidan nan.
"amatullah tace idan akan matane muje nabaku.
"mikewa daya yana biye da'ita suka shiga daki.
""sunna shiga gun wadrop ta nufa budewa tai, tai kamar tana niman key gani kudin da yai yasashi rudewa hannu yasa ya fara diba.
"a hankali amatullah taja da baya kamar tana niman key din karfe rataya handbag ta kwada masa akan.
"a take yasa ihu kansa ya fashe fadi yai kasa yana juyo juyo.
"Mahfus najin ihunsa hannu shima yasa ya nushi wanda yake kansa a gaba shima ihu yasa ya fadi a guje Mahfus yai dakin amatullah.
"ganishi kwance cikin jini yasa Mahfus kamo amatullah suka fito wanda yake kan fadi ya kama Mahfus da danbe hade da cewa katashi mugudu ihu da yake masane yasashi tashi.
"da kokuwa suka shiga dakin amatullah sai faman janshi sukeyi shima Mahfus yana jinshi sbd kada su fita dashi.
"hankali fadi ya tashi cikin dabara ta tai maka masu suka fita tana fadin dan Allah Mahfus kabarsu sufita kada ya mutu mana a gida.
"shi wanda Mahfus ya nusane yatsaya danbe da Mahfus shikuma daya daukar wanda amatullah ta fasa masa kai yai a guje sukabar gidan.
"gani yadda ya rikewa Mahfus gaba yana murdawa yasa amatullah shiga kitchen a guje ta dauko wuka xata caka masa kenan a guje ya saki Mahfus yasa guje.
"a fusace Mahfus ya dauke fadi da mari har guda uku fadi tai kasa tana kuka.
"da sauri suka rungume juna ita da Mahfus.
H.S.Z.ce
🌺💦🌺
💦
MATAR FARI
(THE FIRST WIF)💦
Fasaha online writes F.o.w.
MMN USWAN
S. H. Z.
38
"gani yadda Mahfus da amatullah suka rungume juna yasa fadi sa wata uwar ihu.
"da sauri Mahfus yace ihu uban me kikeyi wlh idan bakimi shiru saina cicci ubanki kibar gani kinada ciki.
"dan tsabar rainin wayo ina kokuma da mutum bantu ki tayani amma har kokarin tayasu kikeyi....
"da sauri fadi tace tayasu kuma Mahfus?
"Mahfus yace banganki bane?
"kodai ma ke kika turosu?
"da sauri fadi tace haba Mahfus wani irin mgn kakeyi haka?
"Mahfus yace wlh na rantse da Allah idan ina mgn kikasake samin baki saina miki duka.
"banxa kawai ubanki ne ya nimomi kudin, ko ubanki ya nimomi.
"ko kuma ke kika turosu da har kike kokarin tayasu.
"tun daga lokacin fadi bata sake mgn ba, a hankali ta xari dakinta da takoma daki.
"tana shiga tace banxa kawai dole kasamu bakin mgn tunda basu kwantarmi dakai ba amma ka kiyayi haduwarmu na gaba.
"ita ko amatullah komawa Mahfus hannu tai suka xauna akan cushion.
"rungumo amatullah ta gefensa yana fadin haba amatullah abu kamar da hadin baki, laifin me mukai masu sbd Allah amatullah?
"amatullah tace gaskiya ya kamata yaiwa police report..
"da sauri Mahfus yace kibarsu kawai.
"amatullah tace sbd Mahfus idan ba'a dauki mataki tun yanxu ba ba fata nakeyi ba amma duk ranar da suka sake xuwa wlh kadan ne xai rage baxusu kashe muba.
"Mahfus yace haka amma dauko min wayata a daki.
"amatullah tace kamance kamar a dakin fadi kake?
"mikewa yai hade da tsaki ya nufi dakin fadi.
"fadi najin tafiyar Mahfus da sauri ta koma ta xauna a bakin gado ta hada kai da gwiwa kamar me kukan gaske.
"yana shiga ko kallon inda take beyaba wayarsa kawai ya dauka ya fita.
"yana fita fadi tace waha lalle kawai.
" parlour Mahfus ya koma ya xauna bbn junior ne ya fara kira ya sanar dashi snn ya kira nasir shima ya sanar dashi.
"cikin dare nasir yaxo tun daga bakin gate yafara gani jini da sauri ya karisa ciki.
"jin shigowar nasir ne da sauri yace amatullah taje tasa xani da hijab sbd kayan bcc ne a jikinta.
"nan danan tasa ta fito.
"nasir na shigowa a parlour ya gansu cikin gigita ya karisa gun Mahfus hade da tambayar suwaye ne suke bibiyarka haka Mahfus?
"Mahfus yace wlh nasir bansani ba.
"nasir yace na uku fa kenan.
"amma ka sanarwa police ko?
"amatullah tace nima abinda nace kenan amma yaki amincewa.
"wayarsa nasir ya ciro daga aljihunshi ya kira police report.
"bayan sun mgn da police ne nasir yace gara da aka sanar dasu ta hakane za'a samu wani informations akansu amma sbd Allah kullin aita bibiyanka haka idan ba'a dauki mataki ba Allah kadai yasan abinda zasu nan gaba.
"aba dade ba saiga police su iso, nasir ne ya taresu yai masu iso xuwa cikin gidan.
"a parlour suka fara tsayuwa Mahfus ne yai masu bayani duk yadda akai.
"sukuma suna rubutawa.
"bayan ya gama bayani ne suka shiga cikin dakin amatullah harda nasir din.
"gani jini kwance a kasa yasa police din daukar photo a wayarsu.
"saida sukasa tissue a hannunsu snn suka dauki wuka da bindigar da suka bari.
"bayan sun gama rubuce2 da xasuyi ne suka fita.
"duk abinda sukeyi a kunni fadi amma taki fitowa.
"nasir da Mahfus suka xauna a parlour harda amatullah suna mgn, gani asuba yayi suka mike zuwa masallaci.
"itama amatullah mikewa xuwa daki dan sallah.
"suna idarwa suka shigo daidai lokacin su inna suma sun iso.
"duk tare suka shigo a parlour bayan sun gaisa ne bbn junior yaiwa Mahfus Allah ya kyauta.
"itako inna fada ta hauyi tana cewa sbd Allah abu kamar da hadin baki?
"kamar kai masu wani laifi?
"nasir yace wlh kuwa ina.
"inna tace na uku fa kenan kamar wanda ya tsare masu wani abu, to wlh ba xai sabuba.
"saukar alkur'ani za'a a gidan duk wanda yakeda hannu akai Allah ya tona masa asiri kowaye shi.
"fadi na daki nanda nan cikin fadi ya juya tarasa yadda xatai da raita.
"tana cikin juyayin hakan saiga kiran yaran aikinta yashigo, da sauri tai rejecting.
"daukar wayar tai a guje taje toilet snn ta kirasu, suna dagawa tace dasu duk abinda suke ciki suyi kokari subar garin sbd ankaiwa police report za'a iya nimansu.
"daya daga cikinsu yace babu inda zasu kuma duk yadda xatayi tayi ta kawo masu kudi suyiwa d'anuwansu treatment yanxu haka kwance yake.
"cikin tsawa fadi tace Allah jacan wawayyu kawai ga yadda nace kuyi kunje kun kawomin harkan shirme shine xan baku wani kudi wlh sisina baxaiyi ciwon kai ba.
"sai yace babu damuwa tunda haka kika xaba amma kisani duk inda kikakai ga iskanci na fiki.
"a yau din nan xanxo gidanku na sanar dashi cewa duk wani satar da ake masa kece domin ke kike turomu.
"da sauri tace dan Allah katsaya wani irin mgn kakeyi haka kamar mara hankali.
"yanxu dai ba zansamu fita ba amma xanyi maka transfer ta account dinka sai kusan yadda xa'ayi kuma kada kasake kirana sbd maigidana yafara xargina.
"lokaci lokaci xan rinka kiranku naji yadda jikin yake.
"a take tai masu transfer kudi masu yawa sbd kada su dameta da toshiyar baki.
"saida gari ya waye tangaran snn inna da kanta taje ta samo malamai tace suxo muyuwa Mahfus saukar alkur'ani mai girma a gida.
"inna tasa Mahfus ya siyo rago hade da kaji.
"bayan ya dawone tasa amatullah tai masu abinci da kajin shikuma rago bayan gama saukarne aka yanka ragon.
"gani duk abinda akeyi fadi bata fitoba yasa inna tambayar lpy kuwa?
"Mahfus ne ya karewa da cewa aa kinsan jiya babu wanda ya rintsa shiyasa nace taje ta kwanta sbd cikin da take dashi.
"Inna tace hakane.
"bayan malamai su gama Mahfus yai masu kyankyawar sallama gaba daya ragon yace sutafi dashi.
"suma sai murna ga lafiyyar abinci da amatullah ta hada masu.
"Malaman suna fita su Zainab suka shigo har kasa suka duka suka gaida inna da Mahfus hade da yimasu Allah ya kyauta.
"Mahfus yace amin.
"suwaiba da fadima suka gaida amatullah.
"cikin fara'arta ta amsa masu hade da mikewa ta nufi kitchen ta xuxubo masu abinci.
"gani amatullah ta fito ririke da abinci hannu biyu yasa suwaiba mikewa xataje ta amsheta Mahfus yace ta xauna Zainab taje.
"Zainab taje ta amsheta bayan ta ije ta koma kitchen daukar nata.
"itama amatullah komawa tai ciki sai xainab tace nifa gaskiya sai kin karami nama.
"cikin wasa amatullah tace baza'a karaba.
"Zainab tace wlh saikin karami.
"amatullah tace ke daban ne su suwaiba daban da xakice saina karamiki nama, to bari jiki babu namar da xankara miki.
"duk sunayine amatullah na dariya.
"bude bakin Zainab tace wlh baki isa ba tunda ba kudinki bane, kudin yyna ne dan haka sai kibarni nayi abinda naga dama dashi.
"murmushi kawai amatullah tai snn tace naji ba kudina bane kudin yynki ne amma ba yynki ya girkemin abinci ba ko?
"bude bakin Zainab tace dan Allah ja banxa kawai.
"ta kariso mgnr ne hade da daukar wani ludayin miya tasa acikin tukunyar miyan xata dibi nama.
"daga hannu amatullah ta wankawa Zainab mari snn tace ko yyn naki da kike takama dashi nafi karfin yacemi banxa banle ke.
"Zainab da kokari daga hannu tai itama xata rama.
"dukka hannaye amatullah ta hada snn tasake wawwa kamata mari, nanda nan Zainab ta kama amatullah da danbe.
"itako amatullah tsayawa tai tana kallonta.
"jin hayaniya a kitchen yasa suwaiba mikewa koda tashiga kitchen gani tai tashake wuyar rigan amatullah tana shirin danbe.
"salati suwaiba tai babu yadda batai da Zainab ta sakewa amatullah wuyar rigaba amma taki.
"komawa tai ta sanarwa Mahfus mikewa yai suka shigo tare duk a lokacin Zainab tana rike da wayar rigan amatullah.
"itako amatullah tsaye take tana murmushi kamar bada'ita ake fadir ba.
"shigowar Mahfus kitchen din yace Zainab saketa.
"Zainab taki.
"Mahfus yasake mgn.
"Zainab taki.
"da Mahfus yaga haka daga hannu yai ya wankawa Zainab mari wanda yasata fadi batare da tasani ba.
"snn yasa kafa ya tokareta.
"a guje taje bayan inna ta boye.
"inna ta mike xatai mgn Mahfus yace dan Allah inna kiyi hakuri.
"hannu yasa ya jawota ta tsuguna a gabansa yace batawa amatullah hakuri.
"Zainab taki ijiyayar wuta Mahfus ya dauko gani xai duketa dashi da sauri Zainab ta juya gun amatullah tace dan Allah kiyi hakuri.
"murmushi amatullah tai snn tace yawuce. Mahfus yace Zainab ta hada kayan da aka bata ta wanke su kama su suwaiba su gwara masa parlour.
"mikewa yai ya shiga dakin fadi, tanajin muryarsa da sauri ta koma ta kwanta.
"wani irin tsawa Mahfus ya daka mata yana cewa dan Allah kitashi ki fita kinxo kin kududune a daki kamar mara gaskiya.
"shiru tai kamar me bcc gaske.
"Mahfus yace banason iskanci ba dake nakeyi ba.
"a hankali ta mike suka fita tare yana gaba tana baya.
"parlour taje ta zauna, shikuma kiran amatullah yai suka shiga dakinta suka fara gwara gun da jini ya bata.
"bayan su suwaiba sun kare xasu tafi gida Mahfus ya basu five five thousand kyauta amma banda Zainab.
"har sun fita sai inna tasa baki snn Mahfus ya bata godiya sukai sosae.
"da yamma inna tace xata koma gida.
"Mahfus yace dan Allah ta tsaya tai masu kwana biyu.
"gani inna xata rinka kwana a dakin zunnurai yasa Mahfus yace amatullah ta kaishi su rinka kwana tare.
"batai musuba tun daga lokacin tare suke kwana da inna.
"Hakan yasa duk ran girkin amatullah Mahfus ko hiran dare bayayi daga yadawo kasuwa suna gama cin abinci sai yace bcc yakeji.
"ranar girkin fadi kuwa dakin inna yake xuwa musamma suyi hira sosae snn yaje ya kwanta.
"da abin duniya ya ishi fadi yanke shawarar kashesu tai gaba daya kowa ya huta.
"ana gobe xata kare girki tacewa Mahfus da safe xataje asibiti sbd batajin dadin jikinta.
"Mahfus yace saidai ta tafi a motar haya sbd akwai inda xaije da sassafe.
"fadi tace babu damuwa.
"da safe bayan Mahfus ya fita itama ta fita babu wanda ta sallama.
"tana fita gidan hawayenta yar'duniya taje xama tai sukasha hiransu snn sukai sallamesu chamis ta nufa kai tsaye dayake sun riga Susan juna da me chamis din shiyasa be bata mata lokaci ba.
"yana mika mata ta nufi gida.
"tana isa sukai karo da inna a parlour tana zaune da zunnurai yana tayata hira.
"inna tace kindawo.
"fadi tace eh nagawo inna.
"bata tsaya jin me inna xata ceba ta shige daki.
"tana shiga tace duk xakuci ubanku yau xa'ayi kwanan lahira.
"amatullah na daki kwance bata fitowa sai bayan la'asar snn tafito dora sanwa.
"koda ta duba kayan miya kadan ne yarage a frg shiyasa tasa sanwa kadan daga inna sai Mahfus.
tuwon shinkafa tai masu da miyar vegetable.
"da yake yau itane da girki Mahfus da wuri ya dawo.
"har amatullah ta gama xata xuba kenan sai taji wayarta na ringing batai ta kanshiba plate ta dauko ta xubawa inna da Mahfus tuwon ta kai masu parlour.
"tana dawowa kitchen kenan tasake jin wayarta na ringing shiga daki tai dan gani me kira.
gani hajiya ne yasa ta daga wayar jin muryar amatullah na waya a guje fadi tashiga kitchen.
"bude miyar tai ta juye Poussin din gaba daya a cikin miyar snn tafita.
"shiko zunnurai dauko handball dinshi yai yana hurgawa bbnshi a jiki.
"shima Mahfus biyeshi yai sukaci gaba da bugawa tare.
"amatullah katse wayar tai sbd batakaiwa su inna jiya ba.
"tana shiga kwanu jiya ta dauko ta juye miyar gaba daya snn ta dauko kananu plate ta fito parlour a gaban Mahfus ta duka ta daga miyar kenan xata xuba a plate zunnurai ya hurga kwallo a ciki miyar yaxube duka a kasa.
"sbd haushi amatullah ta rufeshi da duka.
"gani irin dukar da take masa da sauri Mahfus ya mike ya dauke d'ansa snn ya hauta da fadi.
"yana fadin miyar banxa daga yau kada kisake dukanmin yaro.
"amatullah tace amma sbd Allah..
"da sauri Mahfus yace sbd Allah me?
"gani haka inna tace amatullah ta tafi daki ta kyaleshi.
"daukarsa Mahfus yai yana lailashinsa.
"itako fadi tana daki tana tsinewa zunnurai tana fadin shegen yaro kawai dan. banxa saida na gani tsarina snn kaxo ka wargaxami.
"ta karisa mgnr ne da kwafa snn ta bude kofa ta fita tana fadin lpy me yasamu zunnurai ne yake kuka haka?
"inna tace miya yazubar shine mmnshi ta dukashi.
"a zuciyar fadi tace d'anbanxa ba.
"a fili kuma tace ayya to ai da bata dukeshi tsaursayine.
"inna tace a to.
"kwanci tashi babu fadi ta haifi yar'ta mace Mahfus yai murna kamar me.
"Mahfus yai masu dikuna masu kyauda tsada..
"duk da dikunin da Mahfus yai masu behana amatullah nata dinki ba.
"ana gobe suna amatullah taje tai gwaran jiki da kai.
"ranar suna amatullah ta dauko me makeup duk kayar da ta canxa sai tasake kwalliya.
"ashe fadi na nan na lura da'ita.
"da yamma baya yar'suna sun Mahfus ya shigo dakin fadi lokacin tana zaune a bakin gado kusa da'ita ya xauna hade da dafata yace my madam ya kike?
"taro yatashi lpy?
"hannu tasa ta buge masa hannu.
"murmushi Mahfus yai yace madam kenan ya akaine.
"fadi tace bansani ba, banxa manafiki kawai.
"Allah ya'isa tsakanina dakai.
"da sauri Mahfus yace subbuhanallah kanki daya kuwa?
"fadi tace da kanka nake yawo.
"bakin algugumi mara tsoron Allah wlh bazan xauna da kai ba manafiki yau saika sakeni.
"mikewa Mahfus yai, da sauri itama ta mike hade da shako wayarsa tana fadin saika sakeni.
"Mahfus yasa sakanmi rigana.
"fadi tace baza'a sakeba idan har kaga na saketa kabani takarda ta.
"ta karisa mgn da kuka tana ihu.
"jin kukan da fadi keyine yasa inna shigowa tana fadin lpy fadi meke faruwa?
"fadi tace kinmin shiru tsohowar alguguma.
"Mahfus besan lokacin daya daga hannu ya wankawa fadi mari ba.
"ihu tasa ta kara rikeshi taci gaba da xagin inna.
"shiko Mahfus rufeta da duka yai, duk dukkan da yake mata besa ta sakeshi ba saida ta yayyaga masa rigar jikinsa.
"tana shege tsinanne Allah ya isa kuma sai wutar Allah ya cika.
"algugumi me daukar kwanan wani yabawa wani.
"kamashi inna tai suka fita.
"duk abinda sukeyi a kunni amatullah amma bata fitaba kwanciyarta tai tana sauraransu.
"itako fadi xagi sai abinda ta mance.
"parlour Mahfus suka koma shida inna.
H.S.Z.
🌺💦🌺
💦
MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)💦
Fasaha online writes F.o.w.
MMN USWAN
H. S.Z.
40
"Koda Mahfus ya fita da wayar babu wanda ya sake kira.
"da yaga haka har ya yanke shawara medawa amatullah da wayarta sai kuma yai wani tunani cire SIM card din yai ya sire wani snn yai mata register.
"bayan ya dawo daga kasuwa ne lokacin suxo gun kwanciya Mahfus ya ciro waya ya bata.
"snn yace mata ya canxa mata sim card.
"itama da yake tasan da matsalar batai tambayar me yasaba.
"wayarsa ta dauka tana kwashe number yar'uwanta.
"wanda kuma take dasu akai duk tasa.
"hakura sosae Mahfus ya bata dare da yimata alkawarin baxai sake ba.
"sbd kuka amatullah kasa mgn fadawa tai kan gado taci gaba da kukanta.
"da sauri Mahfus ya bita kan gadon dagota yai ya rungumota snn yaci gaba da bata hakuri.
"fisge jikinta tai ta sauka kasa.
"binta Mahfus ya sakeyi, da sauri ta mike tabar masa gun.
"da Mahfus yaga haka inna yaje ya kira.
"tare suka shigo inna ta hau amatullah da fada tana fadin dama baki hakura ba amatullah.
"to yanxu menene amfani kukan da kikeyi?
"dan Allah kiyi hakuri komai ya wuce, idan har xaki irin tuna baya babu abinda xai kara miki sai bacin rai.
"dan Allah amatullah kiyi hakuri kinji.
Mahfus yace wlh inna in Allah ya yarda bazan karaba.
"wannan ma kuskure ne..
"tsawa inna ta daka masa hade da cewa kaimi shiru sai abu ya faru ku rufe ido ku aikata abu daga baya kuma kukoma kuna nadama.
"gashi yanxu kenan kazo kana nadama.
"shiru Mahfus yai saida inna ta kare mgn snn yace inna kiyi hakuri..
"inna tace ni bakaimin komai ba, matarka ne xakabawa hakuri.
"a gaban inna Mahfus yace dan Allah amatullah kiyi hakuri wlh baxan sake ba.
"shiru amatullah tai tana kallon sa.
"inna ta sake cewa dan Allah kiyi hakuri amatullah.
"gani tai shiru ne yasa Mahfus cewa jeki kawai inna ta hakura.
"inna tace to dan Allah kurinka hakuri da junan ku.
"Mahfus yace to inna naji kuma na gode.
"inna na fita gaban amatullah Mahfus ya rusuna yanata bata hakuri.
"har saida ta hakura snn ya mike hade da kamota suka kwanta.
"duk abinda sukeyi fadi na makale tanajin su, da taga haka yasa ta canxa wani sabon salo.
"tun daga lokaci ta hanasu kiran kuma.
"gani Mahfus be samu isassashen lokaci da xaikai zunnurai tofi yadawo yaje kasuwa yasashi cewa amatullah tarinka kaishi.
"itama tunda taga abin yaxama haka duk lokacin da xata sai tace saidai suje taxo da inna.
"da Mahfus yaji labarin hakan yai fada har yagaji amma amatullah takiji.
"narar Mahfus yana dakin amatullah ne da safe lokaci Mahfus yafito xai tafi kasuwa bayan ya gama sallar matanshi dakin inna ya shiga sallamarta.
"fadi na makale jikin kofa koda Mahfus ya fita tana kallansa jin tai kamar tai masa mgn wani zuciya kuma yace barshi kawai ya tafi.
"tana kllonsa yafito ya tafi.
"yana fita ko minti goma beyi da fita ba itama ta xari kyale ta fita batare da sani kowa ba.
"gun areas boys dinta taje ko gaisuwa basu yiba sbd tace sauri takeyi.
"sai ogan yace fadi abinda ke tafe dake.
"fadi tace aiki nakawo..
"da sauri yace idan asake komawa gidan ku babu wanda xaije.
"fadi tace bashi bane.
"yace ina sauraranki.
"fadi tace so nake kai da kanka xaka bishi kasuwa kace duk satar da ake masa kune kuma amatullah ne ke turaku.
"idan kun sato sai kuraba 50-50 yanxu kuma kai katuba shiyasa kazo bashi hakuri da alkairi bazaka kara ba.
"ido😳 ya bude hade da cewa kinsan abinda kike fadi kuwa?
"fadi tace ina sane.
"yace kinsan irin wannan abu risking ne kuwa?
"fadi tace ina sane karka damu babu abinda xai faru.
"shiru yai snn yace wlh da badan muna bukatar kudi ba babu abinda xaisa nasake miki aiki.
"amma yanxu sai kin bamu kidinmu cash kafi muyi maki aiki.
"nan take suka tsadance tabiyasu.
"fadi tace kada suje yau subari sai gobe.
"da sauri ta koma gida haka tasake shiga a sace babu wanda ya ganta.
"Mahfus yana dawowa siyayya yai masu sosae na kayan sawa har da inna da zunnurai.
"kowa da nashi ledar.
"saidai kayan amatullah yafi yawa da tsada shiyasa daki yabi kowa dashi sbd kada wani yaga na wani.
"koda amatullah ta bude taga kayan godiya tai masa sosae.
"ita ko fadi koda ta bude tagani cewa tai kayan amatullah yafi nata yawa nan ta haushi da bala'in.
"shidai Mahfus shiru yai beci komai ba.
"gu yasamu ya kwanta be tanka ta ba har bcc ya daukeshi.
"washe gari da safe bayan sun karya ya sallamesu yafita kasuwa.
"misalin 12PM fadi tai masu waya, yana dagawa tace yaje yanxu.
"beyi kasa a gwiwa ba suna gama mgn yatafi har cikin shago yashiga yaran Mahfus sunyi kokari tsaidashi amma ina cewa yai ogansu yakeso gani.
"daya daga cikinsu ne yace to yatsaya aje a sanar dashi tuku.
"da sauri yaran yashiga gun Mahfus ya sanar dashi.
"Mahfus yace babu damuwa abarshi ya shigo.
"yana shigowa har kasa ya duka, babu yadda Mahfus beyi dashi akan ya xauna akan kujera ba muyumi yaki harda kwallansa.
"yafara da cewa dan Allah dan annabi dan soyayyar ka da shugaban halinta shugabanmu annabi Muhammadu (S.A.W.)kayi hakuri ka yafemin wlh nayi nadamur abinda na aikata maka kuma in allah ya yarda bazan karaba.
"gaban Mahfus yai mummunar fadi tasowa yai ya xagajo yaxo inda mutumi yake duke hade da sa hannu ya dago mutumi.
"mutumi yaki yarda ya dago wani sabon kuka yasake rusawa Mahfus.
"Mahfus yace dan Allah kafadimin menene ya kawoka ko nasamu natsuwa.
"cikin kuka mutumi yace sai kamin alkawarin ba xakaimi komai ba idan na fadi maka.
"Mahfus yace naji babu abinda xanmaka.
"mutumi yace wannan ba alkawari bane.
"Mahfus yace nayi maka alkawarin babu abinda xanyi maka.
"snn mutumi yasake fashewa da kuka yana fadin dan Allah kayafemin wlh baxan sake aikata hakan ba.
"nayi nadama nayi nadama sosae.
"wlh duk barayin da suke shigowa gidanka ba kowa bane mune muma samu akayi.
"ba kowa bane ya samu uwar gidanka ne sbd tace duk kudin da kake wadaka kake fancamawa dashi natane ita kuma tarasa yadda xatayi ta kwace kayanta shiyasa ta turomo tace idan har mosamu nasara xamu raba 50-50 in kuma bamu samu nasara ba duk hanyar da xatabi saitabi ta kasheka.
"dan ta kwato dukiyar ta.
"wani irin tsawa Mahfus ya daka masa hade da cewa bacemi da gani kafin kai na kashe ka.
"jin haka yasa mutumi fita a guje.
"a fusace Mahfus ya fita shiga mota yai ya fisgi mota da gudu sai gida.
"yana shiga fita daga motar yai ko rufe murfin motar beyiba ciki ya shiga hade da kwadawa amatullah kira.
"jin muryar Mahfus mmki ya kamata sbd lokacin dawowar sa beyiba.
"da sauri tafito tana fadi lpy kadawo yanxu?
"Cikin fushi Mahfus yace bansani ba manafuka azzaluma Allah ya tuna miki asiri dan haka fitamin a gida na sakeki.
"jin kamar saki a gigice inna tafito daga dakinta tana fadin Mahfus me xangani haka.
"amatullah najin haka tace innalillahi'waiina'ilaihim raju'un.
"Mahfus kanka daya kuwa?
"kuka amatullah tasa.
"kamo hannunta Mahfus yai yana fadin fitami a gida kitafi na sakeki.
"fisgo hannunta tai takoma ciki dakinta ta shiga jaka ta dauko ta kwashi kayanta dana zunnurai snn ta dauki kyaleta hade da key din motar ta tafito kamo hannu zunnurai tai zasu fita.
"da sauri Mahfus yaje ya fisgo dinsa yana fadi babu inda xaki kaimin da'na.
"amatullah sake kamoshi tai Mahfus ya sake fisgoshi.
"nan suka kamajan yaro amatullah naja Mahfus naja.
"shiko zunnurai sai faman ihu yakeyi.
"inna tayi tayi Mahfus ya sakeshi amma yaki, gani xasu karya yaro wankawa Mahfus mari tai da sauri ya sakeshi.
"da sauri amatullah ta dauki d'anta suka shiga mota.
"itako fadi tana daki duk abinda sukeyi a kunni ta sbd murna harda rawa takeyi.
"sai daga baya snn tafito hade da murxa ido kamar me bcc gaske tana fadin inna lpy?
"banxa inna tai da'ita.
"daki inna ta shiga sbd ranta ya riga ya baci.
"shima Mahfus kan cushion ya xauna hade da kwashe hannayesa ya xuba aka hawaye ne kawai ke gangaro masa.
"da fadi taga haka dakinta ta koma.
"kasuwar da Mahfus be koma ba kenan.
"amatullah na fita hanyar garinsu ta nufa kai tsaye.
"babu abinda takeyi sai addu'a sbd ji takeyi kamar kirjinta xai fashe.
"bayan isha inna takira Mahfus dakinta ta hannayeshi abinda ya faru.
"kuka Mahfus yasa kamar yaro karami yana fadi yana kuka.
"gani irin kukan da yakeyi yasa inna tace yabar mgnr haka.
"fadi na makale tanajinsu cewa tai dan banxa bakaga komai ba ma.
"lailashinsa ta komayi hade da bashi hakuri.
"amatullah bata isa gida ba sai shabiyun dare.
"jin bugu kofa kamar mahaukata har hajiya taji tsoro.
"amatullah tace nine hajiya kibudemi.
"a gigice hajiya ta bude kofar.
"hajiya na budewa amatullah tasa wani irin ihu hade da fadiwa kasa.
"da sauri hajiya ta dauki zunnurai saida ta kwantar dashi snn tadawo ta kamo amatullah suka shiga ciki.
"amatullah tana fadi na shiga uku hajiya Mahfus ya sakeni..
"da sauri hajiya tai salati ta sanarwa ubangiji.
"amatullah taci gaba da cewa hajiya yaya xanyi da raina Mahfus ya sakeni.
"rungumota tai snn tafara rarrashinta hade da bata baki.
"har saida ta numfasa snn hajiya ta jata xuwa cikin daki.
"cikin dare zazzabi mai karfi yakama Mahfus sai faman juyi yakeyi.
"gani haka yasa inna tace fadi ta kira nasir, ana kiransa gani number Mahfus ne yasashi dagawa.
"inna ce ta amsa tai masa mgn, cikin daren nasir yaxo ya dauki Mahfus xuwa asibiti.
"doctor yana dubashi yace maleriya ne da kuma tunani.
"ruwa suka sa masa hade da allurai.
"gani yasamu bcc ne suka fita waje da inna shine inna take sanarwa nasir abinda ya faru.
"salati nasir yai ya sanar da ubangiji hade da cewa meyasa ya aikata haka betsaya yai bincike ba?
"wlh inna amatullah bazata aikata haka ba.
"to tace to aikin gama yariga ya gama.
"washe gari bayan ruwa ya kare aka sallamesu suka koma gida.
"ita kuma hajiya kiran Anty Frd tai ta sanar mata.
"a fusace Anty Frd babu komai kyaleni dashi sai nayi maganishi.
"dan ubanshi kuma gaba daya dukiyarta saiya dawo dashi.
'"tun daga lokacin Mahfus baya xuwa kasuwa yana zaune a gida ne.
"yau yaran shagonsa kafin suje bank an riga an rufe gashi kuma kudin da yawa shiyasa manager yace bari ya kawowa Mahfus kudin gida dan yaso da safe sai yaxo ya dauka yakai bank.
"Cikin tawa jaka yasa kudin snn ya kawowa Mahfus.
"Mahfus yace inna ta ije masa kudin da safe xai amsa.
""ashe fadi taji haushi hakan.
"a fusace ta koma daki wayarta ta dauka kira daya suka dauka fadi tace yau din nan suxo da shadayan dare kuma idan xasuxo su tabbata su kawo mata igiya.
"tana gamawa parlour ta koma ta xauna lokacin Mahfus yana kallon news.
"daga nan bcc ya daukeshi ita ko fadi idota biyu.
"jiransu kawai takeyi.
"ita kuma inna tana dakinta kwance.
"shadaya da rabi suka iso fadi da kanta ta bude masu kofa.
"suna shigowa da kanta ta tada Mahfus daga bcc.
"gani mutani akanshi yasashi tashi a gigice kafin yace komai fadi tace ku daure minshi.
"Mahfus najin haka kamasu yai da danbe.
"tokari sukai masa a gaba yana fadi sukasa kafa suka takeshi snn sukasa igiya suka daureshi tsaf.
"inna na fitowa itama igiya sukasa suka daureta.
"inna najin haka tasa ihu.
"daki fadi ta koma saletaf ta dauko suka rufe masu baki dashi.
"dakin inna ta shiga ta dauko jakar kudin hade da key din motar Mahfus snn tace sutafi.
"har tasa kafa saidai tadawo ta bude masa baki tace ko kanada mgn.
"Mahfus yace fadi ina xaki kaimin kudina?
"kuma karfa kimance akwai igiyar aurena a kanki.
"dariya fadi tai snn tace igiyar aure fa kace?
"Mahfus kenan inda ana cirewa a bada ijiya da nacire na kaina na baka kahada da naka ka'ije.
"nidai kaga tafiya ta ta karisa mgnr da cewa banxa idan iska ka dai kagani.
"bakasan waye niba shiyasa.
fita sukayi fadi da kanta taja motar Mahfus suka fita.
"Mahfus najin fitarsu ihu yasa
"yana fadin knoooooo.
0 comments:
Post a Comment