parlour suka koma shida inna.
"Mahfus yace inna yau din nan fadi bazata kwamin a gida ba.
"da sauri inna tace sbd me Mahfus?
"Mahfus yace haba inna kamar ba'a gabanki akai komai ba?
"rashin mutunci ya tashi daga kaina ya dawo kanki inna.
"to wlh bazan yarda da haka ko waye daga cikinsu tace xata xaganmu uwa xan rabu da'ita kowaye kuwa.
"murmushi inna tai snn tace babu wanda xaka saka daga cikinsu saidai halinta ya koreta.
"ban yarda ka saketa ba kabari idan ta huce ka lailabeta kaji dalilin yin haka yanxu haka wani abu tagano kuma take xarginka dashi kasan mata da kishi.
"shiru Mahfus yai yana kallon inna.
"gani yanda yake ajiyar zuciya yasa inna cewa tashi kaje ka kwanta.
"mikewa yai yashige dakin amatullah, lokacin tana kwance tana game gani ya shigone yasa ta ije wayar a gefe ta gwara masa ya kwanta.
"gani yadda yace huci yasa bata tankamasa ba.
"itama kwanciyarta tai.
"koda Mahfus ya kwanta ba bcc yakeyi ba idonsa biyu tunani abinda fadi tai masa ne kawai yakeyi.
"shidai a iya tunanishi bega abinda yai mata ba.
"irin kudin ma da yakashe duk haihuwar da amatullah takeyi betaba kashe mata ba.
"amma yau shine take xagi abin ma ya tashi daga kansa ya koma kan mahaifiyatsa.
"itako fadi tanacan tana fadi ai da katsaya kaga tattagaryan rashin mutunci d'an rainin wayo.
"da irin wannan tunani ne har asuba yai Mahfus besani ba amatullah ne da ta tashi sallah snn ta tada Mahfus danyin sallah.
"Kunna light da xatai sai taga idonsa biyu.
"gani hakan yasa bata sake tanka masaba shigewa tai toilet tai alwala taxo ta fara sallah.
"tana fita Mahfus ya shiga yai alwala a daki yai nashi sallah.
"yana idarwa yaje ya gaida da inna tunda yakoma daki be sake fitaba sai misalin 20PM snn yai wanka ya karya ya fita kasuwa.
"itako fadi tunda ta tashi taiwa rukyyat wanka suka karya ta koma ta kwanta bata sake fita ba.
"bayan kwana biyu Mahfus yana dawowa kasuwa biyawa yai ya siyewa su zunnurai da rukyyat kayan sawa masu kyau da tsada.
"yana dawowa yasami amatullah a parlour suna zaune da inna.
"bayan ya gaida inna itama amatullah ta gaida shi.
"mikewa zunnurai yai nashi ya hannunsa snn yashiga dakin fadi da sallama lokacin tana zaune kan cushion rike da rukkyt.
"kusa da ita ya xauna hade da sa hannu ya dafo kafadarta yana cewa my madam kenan aiki kikeyi haka kawo na tayaki mana.
"hannu yasa xan karbi rukkyt da da sauri ta kau da'ita.
"murmushi Mahfus yai snn yace yau harda baby nawane ake fushin?
"idan kuna fushi dani ni bana fushi daku abani baby na.
"hannu Mahfus yasa ya dauki rukyyt hade da dauko pampas xai sa mata.
"dauko yai yasa mata up side dow snn ya dauko riga xaisa mata.
"gani duk shirme yakeyi yasa fadi amsar yarinta ta gwara ta da kanta snn ya sake amsarta yana lailashinta har tai bcc.
"fadi ta kasheta ta kwantar da'ita.
"shima Mahfus xuwa yai bayan fadi ya kwanta mata a jiki yana shafeta hade da cewa haba my wife me nai miki haka kike fushi dani?
"sbd Allah kodan bakisan halin da nake shiga neba na rashinjin dumin jikinki ba.
"my baby kodai kindaina sonane.
"tsareshi tai da ido tana kallanshi.
"gani haka yasa Mahfus juyota ya haye kanta yana kokarin yimata kiss.
"hannu fadi tasa tana kokari tureshi.
"Mahfus na gani haka kara mannewa yai a jikinta.
"daure fuska fadi ta karayi tana fadi ka sauka min ajiki.
"Mahfus yace ba xan sauka ba.
"fadi tasake cewa ka dauka.
"Mahfus yace bazan sauka ba.
"duk mgnr da Mahfus xaiyi saiya yashe mata ido.
"da fadi ta gaji tsayawa tai tana kallonsa.
"Mahfus yace kinaso na dauka?
"kai kawai ta daga masa.
"sai Mahfus yace saikin fadimi laifina.
"hannu yasa ta cikin riganta yana shafeta hade da hura mata fuska a hankali.
"daga snn fadi tafara fadi masa duk abinda yake cikin zuciyarta.
"Saida ta gama tsaf, snn Mahfus yace to kiyi hakuri amma wlh duk abinda kike xargi ba haka bane amma tunda abin yaxama haka kiyi hakuri inda ana dawowa da abin baya dasai a dawo da suna bayan amma tunda wannan yariga ya wuce idan kika sake haihuwa sai nayi miki duk abinda kikeso kinji.
"kai kawai ta daga masa.
"shafeta Mahfus yai tayi hade da tsikaranta' ita kuma tana dariya.
"fadi najin gaban Mahfus ya mike da sauri ta tureshi ta mike hade da cewa tashi katafi nagode haka.
"shiko Mahfus a nashi zuciya cewa yake koda baki koteniba tafiya xaiyi tunda abinda nakeson ji nariga naji.
"hannu yasa zai rungumota da sauri ta kauce.
"dariya kawai yai yafi.
"bayan kwana biyu fadi taji sauki garau amma bata fara sallah ba sbd har yanxu jinin biki be dauke mata ba.
"da yamma lokacin Mahfus ya dawo fitowa parlour tai ta zauna rukkyt na hannu inna anata hira gani goma yayi yasa Mahfus cewa kowa yaje ya kwanta har yamike da sauri fadi tace ina xaka.
"Mahfus yace kwanciya zanyi bcc nakeji.
"sai fadi tace na gaji da xama haka so nake a raba girki daga yau nima inada butarka a tare dani.
"Mahfus yace amma...
"hannu kawai inna ta daga masa alama yai shiru.
"mika masa rukkyt tai hade da cewa saida safe.
"amatullah na gani haka mikewa tai ta shige dakinta.
"Mahfus yana gaba fadi tana baya suka shiga daki.
"itama inna mikewa tai ta shiga dakinta.
"cikin dare sha'awa ya kama Mahfus fadi bata nunan masa batada tsarki ba haka ta barshi yai abinda xaiyi saida ya sauka haska gabansa da zaiyi sai yaga jini.
"a gigice yace fadi badai ace bakida tsarki ba?
"kika bari nai amfani dake ba.
"shiru fadi tai.
"Mahfus yace meyasa kikamin haka fadi bakisan yana kashe mana gaba ba?
"fadi tace to ni ina ruwana.
"da ran Mahfus ya baci xaxxageta yai snn yaje yai wanka.
"tun daga lokacin koda yaxo kwana baya kawo tunani kwanciya da'ita har saida yaga tafara sallah snn.
AFTER SIX MONTH
"ranar amatullah ne keda girki.
"ruwan xafi ta dora tana jiran ya tausa ta xuba shinkafa sbd tariga tayi miya.
"daki ta koma ta xauna hade da daukar waya tana duba abubuwa aciki.
"da sauri fadi ta fito daga dakinta dauko motarshi zunnurai tai wanda duk acikin kayan wasanshi yafison wannan motar shikuma lokacin yana parlour suna wasa da ruyyt sbd rukkt tana rarafenta ko'ina.
"fadi ijiya ta dauko saida ta daure da pot din dake kan gas yana tausa snn ta dauko motar zunnurai ta daure ta kasa.
"tayi hakane koda zunnurai yaxo dauka ruwan xafin ya xubo masa a jiki.
"tana gama daurewa ta koma dakinta.
"koda ta fita a kitchen din barai kofa tai a bude sbd yafi hangowa da kyau.
"ita kuma amatullah hankalinta yai nisa akan waya.
"fadi na dauki tana jiran result.
"juyowa yai yanaso ya dauko yabawa ruyyt tai wasa dashi be ganiba.
"yana dube dube kataf idonsa ya hango motar a kitchen.
"da dauki yaje daukowa.
"yana tafe ruyyt na binshi da sauri harda gudu take hadawa gata da xafin nama.
"gani haka yasa zunnurai idan yai tafiya daya biyu sai yatsaya yana yimata dariya.
"ita kuma tariga ta hango motar da sauri ta karisa ciki taje ta jawo motar.
"jawowar da xatai gaba daya ruwan xafin ya kwaro mata ajiki.
"ihu tasa tana juye juye.
"gani hakan shima zunnurai ihu yasa yana kokarin kamota.
"shima duk hannushi saida ya salbe da inda rukyyt ta kankameshi.
"jin ihu yai yawane yasa su amatullah da inna dake bcc suka fito a guje.
"ihun da amatullah tai tana kiran rukyyt yasa fadi fitowa a guje.
"gani gaba daya ta salbe yasa fadi sa wata uwar ihu tana fadin amatullah kin kasheni amatullah.
"duk da kukan da amatullah keyi jin kalmar da fadi ke fadi yasa amatullah cewa me kikace fadi kodai banji da kyau bane.
"fadi tace kamar yadda kika ji.
"inna ce ta daka masu tsawa tace cewa dan Allah karku kawomin xance banxa amatullah dauke su mutafi asibiti.
"har tasa hannu xata dauki rukyyt gani yadda ta koma yasa amatullah ta kasa.
"dankwalin kanta ta cire tabawa inna inna ta dauketa ita kuma amatullah ta dauki zunnurai suka fita.
"suna fita amatullah ta tuna kamar tabar key din mota komawa tai ciki ta dauko snn suka shiga.
"babu yadda inna batai ba fadi ta shiga motar amatullah fadi taki.
"gani haka inna tace su wuce sbd yadda taga rukyyt nayi kamar alamu fitan rai.
"a guje amatullah taja mota suka nufi asibiti.
"suna shiga gate din asibiti rukyyt na cikawa.
"jin salati da inna keyine yasa amatullah tace lpy?
"inna tace rukyyt lokaci yayi.
"jin haka yasa amatullah kokarin jiya motar..
"inna tace aa sushiga ciki sbd zunnurai yana bukatar taimako.
"tanayi parlour shinfida rukyyt inna tai a baya snn ta dauki zunnurai suka shiga ciki.
"suna shiga amatullah ne taiwa nurses bayani snn aka shiga dasu gun doctor.
"ashe fadi tana biye dasu.
"tana isowa gun motar amatullah ta nufa.
"lekawa da xatai ta hango rukyyt kwance an lulubeta da dankwalin amatullah wani irin ihu tasa tana kuka.
"gani anfara yima zunnurai treatment yasa inna tacewa amatullah ta kira Mahfus ta sanar dashi abinda ke faruwa.
"amatullah tana fadi masa nan take yabar kasuwa ya kamo hanyar asibiti.
"itako fadi tanacan ta tarawa kanta jama'a sai faman hauka takeyi.
"sai faman bata hakura sukeyi amma taki hakura wani icce ta hango can gefe a guje taje ta dauko xata fasa motar acewarta xata dauki yar'tane.
"jama'a sai faman rikewa akeyi tana kwacewa.
"amatullah ta inna sunacan basusan abinda ake ciki ba.
"da haka har Mahfus ya'iso asibiti koda ya hango jama'a tare beyi tunani fadi bane amma hango motar amatullah agun yasashi karisawa da sauri dan gani meke faruwa.
"koda ya'isa gun maza yagani ririke da fadi gashi kusan cinyoyota a waje suke.
"wani irin bakin ciki ya taso masa besan lokacin da ya dauketa da mari ba.
"yasake binta da tokari da sauri ta mike Mahfus yacewa mutani sukafi ya gode.
"gefe ta koma ta tsaya.
"leka motar amatullah Mahfus yai can gefe ya hango rkyyt kwance.
"kai kawai ya kada snn ya shige ciki asibiti.
"yana xuwa ya biya kudin treatment din snn yace sukafi gida da kanshi ya dauki zunnurai suka nufi gun mota.
"suna isa gun motar Mahfus ya amshi key din motar amatullah sai yace ita da inna da fadi sushiga nashi, shikuma xaixo da gawar.
"bude bakin fadi tace wa?
"Allah ya sauwake da inshiga ta jani gara na koma a kafa.
"jin haka inna ta amshi zunnurai suka shiga motar Mahfus amatullah taja suka tafi.
"shima Mahfus shiga motar amatullah yai yana shiga ya tada motar.
"gani xaitafi ya barta a guje fadi ta shiga kadan yarage ta fadi sbd Mahfus yaki tsayawa ta xauna haka ya fisgi motar.
"tana shiga taci gaba da kuka Mahfus be tanka mataba har saida sukakai tsakiyar titi hannu Mahfus yasa ya bude motar snn ya igijeta kadan yarage ta fadi.
"wani irin ihu tasa hade da kankameshi.
"duk da haka bedai na tuki ba.
"gani hakan yasashi jawo murfin motan ya rufe da kyau.
"har suka isa ko tari bata sake yiba.
"kafin su isa gida Mahfus ya sanarwa nasir da bbn junior da yaran shagonsa.
"suna isa gida suma suka iso.
"bayan an gama wa rukyyt wanka aka sa mata sutura nasir ne ya dauketa suka fita akai mata sallah snn bbn junior ya dauketa suka shiga mota xuwa makabarta.
"bayan sun dawone nasir ya dauki zunnurai xuwa gun tofi.
"suna isa malami yai masa tofi hade da basu wani a gora wanda za'a rinka yayyafa masa snn suka dawo.
"bayan sun dawone duk suna zaune a parlour nasir na rike da zunnurai shine yake cewa sbd Allah garin yaya hakan ta faru yara biyu a lokaci daya?
"dan ma Allah yasa kwana zunnurai yana gaba ne da shima shikenan.
"cikin kuka fadi tace ba itace ba muguwa...
"da sauri Mahfus yace wlh idan bakimin shiru ba saina xakiga abinda xaiyi miki.
"yar'wala kanci kawai marasa hankali.
"in banda tsabar rainin hankali ace har yara biyu sun kone kuma duk kuna gida babu wanda ya sani.
"wlh banga amfani kuba wlh idan kuka bari raina ya baci duk sai kunji a jikinku.
"amatullah najin haka mikewa tai ta koma dakinta.
"shima nasir jan Mahfus yai xuwa waje.
"itako fadi sai faman guguni takeyi.
"duk yadda taso ta kawo tashin hankali Mahfus kin yarda yai mundu takawo mgnr mutuwar rukyyt sai Mahfus yai banxa da'ita.
"dole yasa ta hakura.
"tun daga lokacin ta kudurci ramawa.
"bayan addu'ar uku fadi ta kira yaran aikinta bayan sun dauka ne ko gaisuwa ba sui ba fadi take sanar dasu cewa xata tura masu number amatullah tanaso su rika kiranta a kowani lokaci hade da text massage idan sunji an daga ba ita ba kowaye suce su abokanan harkanta ne.
"amma duk yadda xasuyi kada subari a san waye su.
"da kar suka amince.
"saida tace konawa ne xata biyasu.
"sukace sai ta biyasu kafin suyi mata aiki.
"tura masu number amatullah tai.
"tun daga lokacin suka fara kiranta har cikin dare text kuwa kala kala na soyayya.
"gani haka amatullah ta fadiwa Mahfus hade da mika masa wayar.
"yana amsa suna sake bugowa.
"da sauri ya kara a kunni hade da cewa hello.
"mutumi yace waye kai?
"dan Allah kabawa mai waya wayarta inaso mgn da'ita.
"Mahfus yace kayi hakuri malam kodai batar hanya ne kai.
"wannan number matan aurene.
"kada bakin mutumi yace ina ruwana da aurenta ita ba tasan tanada aure ba muke harkan.
"dan Allah kabata ko kuma kace mata muhadu a inda muka saba haduwa.
"Mahfus najin haka ihu yasa hade da hurga wayar.
"gani haka yasa amatullah tafiya daukar wayar.
"shakota Mahfus yai yana fadin dan ubanki dama maza kikebi?
"me narageki dashi.
"ihu amatullah tasa tanaso tai mgn amma takasa sbd shakan da Mahfus yai mata.
"gaba daya idonusa sun canxa kamar bashi ba.
"zunnurai dake xauna kuka yasa yana ihu, jin ihu sane yasa inna xuwa da sauri tana tambayar ply?
"gani numfashi amatullah na niman daukawa da sauri tacewa Mahfus ya saketa.
"Mahfus yaki yana fadin ni xakiciwa amana.
"sbd bakin ciki sulalewa amatullah tai ta some.
"kuka inna tasa tana salati zunnurai yana gani mmnshi kwance kamar gawa hayewa jikinta tai yana kuka.
"duk abinda sukeyi fadi na jinsu amma bata fitoba sbd dariya keto harda kwarewa takeyi.
"a guje inna taje toilet ta dibo ruwa ta xubawa amatullah.
"shiko Mahfus babu abinda yakeyi sai huci.
"gani ta bude ido yasa inna dagota ta xauna.
"tana xama ta fashe da kuka tana fadi yanxu Mahfus xargina kakeyi Mahfus?
"ashe a rayuwa bazaka iya shedana ba?
inna tace wai meke faruwa ne Mahfus?
"Mahfus be tankaba mikewa yai ya fita parlour ya koma ya xauna.
"mikewa inna tai ta bishi parlour xama tai kusa dashi snn ta haushi da fadi.
"shiru Mahfus yai har saida ta kare snn Mahfus yake sanar da'ita abinda ake ciki.
"salati inna tai snn tace wlh babu inda amatullah ke fita sbd nike zaune dasu ko kofar gida basu fita.
"amma abinda nakeso dakai shine kayi bincike akai.
"kuma dan Allah koda abu yafaru kadaina irin haka watarai xaka aikata abinda xakai da kasani.
"mikewa inna tai ta koma gun amatullah tai ta bata hakuri.
"amatullah cewa kawai tai babu komai.
"inna na fita Mahfus ya shigo kwanciya tsakaninsu babu wanda ya kalli dan uwarsa duk juyawa juna baya sukai.
"bayan amatullah tai bcc tashi Mahfus yai ya dauki wayar yana duba text massage din da suka yo mata.
"da sauri ya kashe wayar ya koma kallon amatullah.
"saidai a iya sani da yai mata tun tana budurwa amatullah bame kwashe2 bane dagashi sai kamarudee bayan su besata da kowa ba banle yanxu ace tanabin maza.
"xuba mata ido yai yai shiru.
"har asuba yai beyi bcc ba.
"gani anfara sallah ne yasashi tashinta tai sallah.
"saida ta shiga tai alwala snn Mahfus yashiga yai nashi.
"yana fitowa sukai sallah bayan sun idar ne har ta mike da sauri Mahfus ya riketa.
"tai kokarin kwace hannunta Mahfus ya riketa da karfi hade da rusunawa har kasa yace dan Allah amatullah kiyi hakuri ki yafemin wlh sharrin shedanne.
"kuka amatullah tasa tana fadin dama ashe a rayuwa bazaka iya shedanaba?.
"Mahfus yace dan Allah kidaina tuna baya babu abinda yake karawa sai bakin ciki.
"nayi miki alkawarin bazan sakeba, amma yanxu taimako daya takeso kimin.
"amatullah tace name fa?
"Mahfus yace da tai makinkine xamusan ko suwaye suka niman rabamu.
"amatullah idan suka sake kira kidauka inaso ki lailabesu musan ko su wayene su.
"amatullah tace to shikenan.
"bayan kwana biyu lokacin Mahfus beriga ya fita kasuwa ba saiga kirabsu amatullah na gani kiran Mahfus tai suka koma daki sbd akwai fadi a parlour.
"suna shiga tai received call din.
"amatullah na dagawa sukace hello baby ya kike kwana biyu na kira baki daga ba ko lpy?
"murmushi kawai amatullah tai.
"snn yace ko xamu hadu a inda muka saba haduwa.
"mmki ya kama amatullah gira Mahfus ya daga mata sai tace to wani gun kenan?
"shima kanshi mutumi mmki ya kamashi.
"wata area din ya fadi mata.
"amatullah tace to sai naxo.
"da sauri Mahfus ya amshi wayar snn ta fadi masa suna unguwar.
"Mahfus yace ta dauko kyale sutafi.
"suna shiga motar Mahfus yace ita xata tuka motar shikuma yana gefen zaune shine ke gwada mata hanyar da xatabi har suka isa gun.
"koda suka isa Mahfus yaita kiran wayar gashi yana ringing amma ba'a daga ba.
"sunyi jira ko xasu fito amma shiru.
"da Mahfus yaga haka komawa gida sukai saida ya kaita gida snn yafita kasuwa.
"da wayar ya fita kasuwa koda zasu sake kira.
H.S.Z.ce
🌺💦🌺
💦
MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)💦
Fasaha online writes F.o.w.
MMN USWAN
H. S. Z.
41
"su fadi suna fita babban hanya suka dauka na fita daga cikin garin kano.
"gudu suke xubawa kamar wanda xata tashi sama.
"hira ya daukesu fadi dariya takeyi sosae harda kyalkyata garin dariyar ne fadi ta dauke wani tsoho.
"yaxo tsallala titi ne yana rike da sandarshi fadi ta dauke shi.
"da sauri fadi tai parking.
"wanda yake gefenta ya leka ta window gani mutumi baya motsi da sauri yacewa fadi taje motar fadi ja mutafi mutumi ya motu.
"jin haka a guje fadi taja motar suka bar gun.
"mutanin da suke kan mutumi daya daga cikinsu da sauri yaja mashin ya bisu.
"gudu fadi ke xubawa babu arxiki shima mutumi binsu yakeyi.
"tana cikin gudu can ta hango police su fito patrol taxo ta canxa hanya saidai kashhh!!!.... Hanyar oneway ne babu hali.
"gani haka yasa fadi juya kan motar daji ta yanka a guje.
"police gani yadda aka juya kan motar yasa su shiga motar su a guje suka bisu.
"ko kafin police su iso motumi yasha gabansu da mashin.
"da fadi ta gano su yakebi a guje ta daukeshi da motar sannan tayo kansa.
"gani xata takeshi da sauri ya murgina gefe.
"snn yasa ihu, ihu da yai ne yasa police kara wuta.
"fadi na cikin gudu taje ta buge da wani bishiya.
"wani irin kara motar tasa gaba daya glass din gaba ya xubo.
"wanda take gefen fadi ihu yasa yana fadin waiyo kafana2.
"gani haka yasa police din da suke bayan mota duddurowa sukai batare da motarsu yai parking ba.
"fadi na gani police sub yo kansu a guje ta bude mota hade da daukar hakan kudin xatasa gudu kenan daya daga cikin boys din ya shakota yana fadi ina xaki?
"kukuwa suka kamayi tana kokarin kwace kanta kafin police su iso.
"a guje police suka xagaye motar.
"Wasu kuma tafiya sukai suka kamo wanda fadi ta daukeshi da mota.
"jini ne kace2 a jikinshi sbd kansa ya fashe.
"daukarsa sukai suka sashi a motar su.
"shima wanda yake cikin motar fadi yana kukan kafa koda suka duba gani sukai duk kakafuwan su karye.
"daukarsa shima sukai sukasa shi a motarsu.
"duk da ga police a gun amma fadi kokarin guduwa takeyi.
"gani haka yasa suka hadata da sauri boys din suka sa masu handcuf.
"akan xubasu a mota sai police station.
"suna isa cell akasa su fadi, su kuma wanda sukaji rauni asibiti aka kaisu.
"duk da babu wanda xai iya tashi daga cikinsu amma sai da police suka sa masu handcuf ko wannan aka hada da gado da kafarsa daya.
"fadi na fita Mahfus sai faman juye2 yakeyi yana niman abinda xai kwance kansa snn ya kwance inna.
"yana cikin juye2 ne can gefe ya hango wasu kananu kwalba wanda amatullah tai jere dasu a parlour.
"mulmula ya dunga yi hade da juyi har ya'isa gun.
"cikin dabara yasa kafa ya jayo abin jere duk kwalaben suka xubo suka farfashe.
"juyowa yai ta baya a hankali yasa hannu ya dauko wani banlin kwalban yasa yana gogawa har ya yanke agiyar.
"garin kokarin yakawa duk yajiwa kansa ciwon.
"yana kwance hannunsa ya warware ya snn ya kwance kafarsa.
"da sauri yaje gun inna itama ya kwance ta.
"kuka inna tasa inna ta kuka Mahfus yana kuka.
"jikin Mahfus yai sanyi sosae.
"hawaye kawai ya keyi wani nabin wani.
"wannan karo babu wanda Mahfus ya sanar masa.
"haka ya xauna a parlour mgnr kirki ya gagarayi.
"can station kuwa babu irin tambayar da ba aiwa fadi ta fadi inda ta tasamo kudi masu waya haka amma taki.
"har da duka aka mata amma besa tai mgn ba.
"daya daga cikin boys din ne da yaji wiya shine yace satowa sukai.
"mgnr wasu mutani ne yasa police din fita daga cikin cell din.
"wasu mutanine suka bugeshi da mota ya mutu kuma basu tsaya ba.
"daya daga cikin police din yace a wani hanya ne?
"suka fadi.
"yace ya kalar motar yake?
"nan suka masu described din motar harda number motan suka basu.
"nan suka karici rubuce2 su.
"snn sukace ina gawar yake?
"sukace yana mutuwari.
"daya daga cikin mutani ashe d'an jaridane.
"daya daga cikin police din yace duk yadda aikai shegu motaninan ne suka aikata haka.
"dayan yace kwarai kuwa..
"da sauri dan jaridan yace dama kun san da case din ne.
"police sukace aa amma wasu moka kamo kuma muna xargin suna suka aikata.
"da sauri wanda yake gefe yace d'anko za'a barin na gansu?
"police yace kasansu ne?
"yace aa bansansu ba amma muna tsaye abin ya faru.
"harda mace a cikinsu tana bugeshi ta faka ta fito gani ya cika daya daga cikin wanda yake motar yace tashigo sutafi tunda ya mutu.
"police din yace Idan ka ganta xaka ganeta?
"Da sauri mutumi yace kwarai da gaske.
"shiga akai aka fito dasu.
"dukkansu da handcuf a hannu.
"suna fitowa da sauri mutumi yace wlh sune su suka kasheshi.
"babu kunya banle tsoro fadi tace to meyene.
"kana wani nuna mutum.
"duk abinda sukeyi d'an jarida yana nan yana kwasheta.
"gani haka yasa aka medasu cikin cell din.
"suma mutuni suka wuce.
"yadda Mahfus yaga rana haka yaga dare ko rantsawa beyiba.
"tunani kala2 yakeyi har ya dauki waya kamar ya kira nasir sai kuma ya fasa.
"da haka har asuba yai besani ba.
"inna ce tai masa mgn yaje yai sallah.
"ko masallaci be'iya xuwa ba, a gida yai sallah.
"bayan nasir ya dawo daga masallaci a parlour ya xauna sbd yanaso yai kallon NeWS na karfe shidda.
"yana rike da calbi yana lazumi.
"a karshen news ne ake sanarwa ankama wasu barayi sunyo satan kudin da mota da kuma wanda suka bude sanadiyar haka ya rasa ransa ko Allah xaisa sakon ya kaiga yar'uwansa.
"hotonsa aka fara snn na fadi da sauran boys din.
"cikin gigita nasir yace wannan fadi ce.
"to idan har fadine meya hadata da barayi?
"da sauri ya dauko wayarsa ya kira Mahfus, Mahfus yai mmkin gani number nasir a irin wannan lokacin.
"har ya tsinke be dauka ba saida ya kara kira snn Mahfus ya daga.
"cikin rawar jikin nasir yace Mahfus ka kullin news kuwa?
"Mahfus yace aa lpy?
"nasir yace wata na gani kamar fadi...
"da sauri Mahfus yace fadi kuma a TV?
"nasir yace wlh kuwa, to kodai me kama da'ita ne?
"police suka kamasu wai sunyi fashi...
"da sauri Mahfus yace alhamdllh, yanxu suna ina?
"nasir yace banga ne ba Mahfus.
"Mahfus yace nasir mgnr bata waya bace wlh fadi.
"ce itace nasir.
"wlh itace.
"Mahfus ya sake fashewa da kuka.
"nasir yace Mahfus lpyr ka kuwa?
"Mahfus yace nasir na shiga uku wlh fadi ta cuceni.
"nasir yace pls Mahfus kaimin bayani ta yadda xan fahimta.
"nan Mahfus ya fara fadiwa nasir duk yadda akai.
"nasir najin haka mikewa yai hade da cewa Mahfus gani nan xuwa mutafi station din.
Ciki ya shiga ya dauko key din motarsa snn ya fito.
"yana shiga mota gidan Mahfus ya nufa dama Mahfus yana zaune a parlour yana jiransa nasir ya xuwa Mahfus ya fita suka wuce.
"suna isa nasir ne a gaba Mahfus a baya.
"suna shiga nasir ne yai ma police din bayani abinda ke tafe dasu.
"polices din sukace basusan wanda suke mgn a kanta ba.
"da sauri Mahfus ya fito da wayarsa ya nuna masu pict din fadi.
"duk da haka sukace basu santa ba.
"gani haka yasa nasir ciro kudin masu yawa yabawa police din.
"a take mgn ya canxa saidai suce D.P.O. ya hana bari a ganta.
"mafi sauki idan har sunaso al'amarin yaxoda sauki suka mgn kotu.
"nasir yace babu damuwa amma dan Allah ba'a ganta da wani jaka ba?
"police yace duk sunanan amma yanxu bamuda ikon baku sai abinda shari'a tace.
"sbd yanxu ya riga ya xama criminal case tunda akwai kashin kai.
"nasir yace to amma...
"mgnr wani ne ya katsesu.
"jin muryar mutumi yasa Mahfus juyowa da sauri.
"suna hada ido da sauri Mahfus yace again????? me yakawoka nan kuma?
H.S.Z.ce
"
🌺💦🌺
💦
MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)💦
Fasaha online writes F. O. W.
MMN USWAN
H. S. Z.
43
"Mahfus yana xuwa tasha yai sa'a mutum daya ya rage yana biyan kudi suka tashi.
"tunda hajiya taga amatullah taki sakin jikinta yasa ta sanarwa Anty Frd.
"hakan yasa Anty Frd tace ta shirya idan xataje aiki xata biyo ta dauke ta.
"shiyasa Anty na fitowa daga gida taxo ta dauke ta.
"butik dinta ta kaita tarinka xama itace incharged din shagon.
"Anty taiwa amatullah hakane ko xaisa ta rage tunani.
"shikuma zunnurai tace ranar monday zata kaisa school.
"su Mahfus suna kaiwa kaduna mota ta lailace.
"har Mahfus ya samu wata mota xai shiga sai drave yace subari yanxu xai gwaru.
"shiru2 har la'asar mota be gwaru ba, gani dare xai masa a hanya tsaki kawai yai hade da mikewa daga zaune da yake.
"taxi Mahfus ya samu yace ya kaishi abuja line inda akafi samo motan da xai shigo abuja ko Niger.
"yana zuwa ya samu xuwa Niger amma ba cikin garin Niger ba ne.
"wata garine da ake cemata mangwaro, dole yasa ya shiga sbd ba lailai bane yasamu cikin Niger direct dole sai yabiyo ta suleja sbd itace hanyar da tafi kyau amma ita kuma mangwaro tafi short code saidai matsalar yar'kidnapi.
"haka ya shiga sbd bashi da yanda xaiyi tunda mota ya tashi Mahfus yake addu'ar.
"Anty na tashi daga aiki ta biyo ta dauki amatullah suka koma gida.
"saida ta sauketa snn ta karisa gidanta.
"su Mahfus suna isa mangwaro ya samu motar da xai kaishi cikin Niger.
"basu isa ba sai goman dare.
"gani dare yayi idan yace xai karisa gidan su amatullah lokaci xai kara karewa hakan yasa ya kama hotel ya kwana.
"tun da ya'iso yake niman number amatullah amma yaki shiga.
"da haka ya gaji ya hakura, gani number amatullah baya shiga yasashi kiran nasir ya sanar masa ya'iso.
"amatullah ta kashe wayar tane sbd Mahfus yana yawan damuta da kira.
"shima Mahfus tunda yagano gaskiyar al'amari yake ta kiran amatullah yanaso yabata hakuri.
"gani koda ya kira bata dagawa yasashi yi mata texe massage.
"duk massage din da xai shigo amatullah tana gani sai ta goge batare da ta karanta ba.
"bayan Mahfus yai sallah yaci abinci kwanciya yai yana tunani ta ina xai fara.
"can wani tunani taxo masa na cewa kodai yaje gidan alhji Ibrahim ne yai masa bayani tunda shi namijine kuma ba yaro bane xai iya fahimtarsa.
"da haka ya tsaida mgnr.
"amatullah na shiga gida zunnurai ya tareta da oyoyo hade da rungumeta.
"itama daukarsa tai tana masa murmushi.
"parlour ta xauna hade da bude handbag dinta ta dauko sweet ta bashi.
"zunnurai yana budewa yafara sha yana sha yana yiwa mmnshi tadi.
"dariya hajiya tai snn tace aa maigidan xo karagemin mana.
"da sauri zunnurai yaje bayan mmnshi ya boye yanayiwa hajiya dariya.
"hajiya tace niko?
"gwalo yai mata.
"amatullah tace aa zunnurai idan baka ragewa hajiya ba gobe bazan siye maka wani ba.
"zunnurai najin haka da sauri yaje gun hajiya yana goga mata abaki.
"daukansa hajiya tai ta rungume tana fadin ko kai fa.
"mikewa amatullah tai ta shige ciki.
"bakin gado ta xauna tafara tunani abinda Mahfus yai mata hawaye ne kawai yake xubowa.
"da safe bayan Mahfus yai sallah xama yai kan sallaya yana naxari kala2 har rana yafito ba saniba.
"gani goma yai yasashi mikewa ya shiga toilet yai wanka ya shirya snn yafito gidan Alhj Ibrahim yaje kai tsaye.
"a kofar gida ya tsaya ya kira alhji ta waya.
"alhji yana gani number Mahfus yai mmki ya kamashi sai dai ya daga.
"gani anyi picking call din da sauri Mahfus yace alhji katashi lpy?
"alhji yace lfy klau ya gida ya iyali?
"shiru Mahfus yai.
"alhji yace ina fatan lpy ko?
"Mahfus yace eh to lpyr kenan.
"subbuhalailahi alhji yace snn yace ina to fa.
"jin haka Mahfus yace aima gani a kofar gida.
"alhji yace wani gidan?
"Murmushi karfin hali yai snn yace gidan ka.
"sai alhji yace to bari na fito.
"Mahfus yace ok.
"alhji yace kashe wayar Mahfus ya kira yya khamis ya sanar dashi ga Mahfus yaxo.
"yya khamis yace babu damuwa abba duk hukunci da kayanke akanta daidai ne.
"alhji yace to shikenan.
"alhji yana kashe wayar yya khamis ya kira Anty Frd ya sanar da'ita ga Mahfus nan yaxo bikon motarsa.
"Anty tace yana ina?
"yya khamis yace yana gidan alhji.
"Anty tace yanxu haka?
"yya yace eh xakine?
"Anty tace aa mexanje nayi duk abinda abba ya yanke daidai ne ai.
"yya khamis yace nima haka nagani.
"snn sukai sallama.
"tana kashe wayar mijinta ya fito daga bathroom yace dear naji kamar kina mgn ko?
"Anty tace eh wlh.
"yace keda waye?
"shiru tai tana tunani karyan da xatai masa can ta tuno tace hajiya ce tace nazo tanason ganina sbd mgnr amatullah kasan mijinta yaxo.
"da sauri yace da gaske amma lailai yacika mara kunya me yakawoshi kuma?
"Anty tace maybe yaxo daukarta ne sukoma.
"Allah ya kyau kawai yace snn yace tashi kije kada hajiya tajiki shiru.
"da sauri Anty ta mike hade da cewa nagode baby.
"miko mata kyaleta yai hade da key din mota da handbag.
"da sauri ta bar gidan police station ta nufa direct tana shiga tai masu bayani abinda ya kawota snn ta dauki kudi masu yawa ta basu.
nanda nan suka bata police motar ta na gaba nasu yana baya sai kofar gidan alhji Ibrahim.
"a bakin kofar gidan suka tsaya.
"shikuma Mahfus yana daga ciki yana gani fitowar alhji Ibrahim da sauri yakarisa gun.
"har kasa Mahfus ya duka ya sake gaida alhji.
"alhji ya amsa hade da cewa lpy ko?
"Shushe2 kai Mahfus yai snn yace dama akan mgnr amatullah ne...
"da sauri alhji yace me tai maka?
"ko kuma me xatai maka?
"Mahfus yace wlh alhji kuskure ne amma dan Allah kai hakuri.
"saida alhji yai gwaran murya snn yace na rantse da allah Mahfus na baka nan da 5 minutes kafita kabarmi gida na ko nasa a daure ka.
"kuma nabaka nan da sati dukkani kudin amatullah dake hannunka kadawomin dasu ko nabika har kano nasa a dauramin kai.
dan haka fita ka barmin gidana.
"mari mutunci kawai.
"juyawa alhji yai yashige ciki.
"jikin Mahfus yai sanyi a sanyaye ya mike ya fita.
"yana fito Anty Frd tai masu sigina da sauri suka fita suka kamoshi suka sashi a motar su sai station.
"shiko Mahfus sai faman tambaya yakeyi me nai maku?
"banxa dashi sukai babu wanda ya tanka masa har suka isa.
"suna isa cikin cell aka sashi.
"saida suka amshi wayarsa da agogonsa kuma ya tube dagashi sai gajeran wando.
"lekowa Anty tai suka hada ido da Mahfus.
"da sauri Mahfus yace dama kece kikasa aimin haka?
"Anty tace kadan ma kagani snn ta juya gun police.
"kudi me yawa ta kara masu hade da cewa ijiyarshi na baku.
"snn ta fita.
H.S.Zce
🌺💦🌺
💦
MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)💦
Fasaha online writes F.o.w.
MMN USWAN
H. S. .Z.
Godiya mai tarin yawa gareku masoyana masu bina ta private da masu kirana duk nagode allah ya bada lada ameen.
42
"malam meya kawoka nan?
"mutumi yace abinda ke tafe da kai nima shike tafe dani.
"nasir dake tsaye yace Mahfus dama snn shine?
"Mahfus yace wlh nasir kwanakin baya lokacin fadi nada ciki na kaita asibiti antenatal tana fitawa shine wannan mutumi ya tsareta a cewarsa wai fadi matarsa ce.
"himm kawai nasir yace.
"da sauri mutumi yace wlh Fatima matata ce.
"Guduwa tai da igiyar aurena a kanta batare da na saketa ba, kuma bata guduba saida ta kwashe min dukiyata kab.
"yanxu da haka a TV na ganta annunota shine nazo.
"nasir yace ta yaya akai tagudu da igiyar aurenka batare da ka saketa ba?
"Kasan da cewa fadi matar aure ce kuwa?
"mutumi yace kwarai da gaske abinda yafi haka ma fadi xata aukata.
"ni kaina na auri Fatima a matsayin budurwa ce ban taba sanin Fatima ta taba aure ba sai bayan rabuwarmu.
"ashe Fatima ta taba aure harda yara uku acan barno din, bayan rabuwarta da uban yar'yar'ta ne muka hadu har Allah yasa na aureta.
"lokacin inada matana biyu itace ta uku da kuma rufan asirina daidai gwargwado amma sanadiyar aureata saida ta sani na rabu da matana bayan rabuwarmu dasu ita kuma ta kwashe min dukiyata kab ta bar garin.
"bayan shekara uku da tafiyarta lokaci daya na ganta da wannan mutumi tana dauke da ciki su fito asibiti.
"nayi iya gwargwado nai masa bayani amma yaki saurarona sbd Fatima tace bata sanni ba.
"sai kuma jiya da naganta a TV annunota shiyasa naso tabani kudina ni kuma na bata takardanta hade da yi mata Allah ya'isa.
"sbd ta rabani da matana masu rufamin asiri da akwai da babu muna tare, gashi tunda narabu dasu bansake wani aureaba sbd bani da kudin wani auran.
"ajiyar zuciya ne kawai nasir yai hade da mmkin fadi.
"shiko Mahfus shiru yai sbd yarasa abin cewa.
"allah ya kawai nasir yace hade da kamo hann Mahfus su tafi.
"suna ciki tafiya ne nasir yake cewa Mahfus kamata yai daga nan mutafi kotu kawai muyi kara sbd police basu da gaskiya kada suxo su tabi kudin ne.
"koya kagani?
"Mahfus yace hakane.
"kai tsaye kotu sukaje bayan suyiwa alkali bayani abinda ke tafe dasu.
"alkali yace babu komai su hadu jibi.
"nasir yace Allah ya kaimu.
"suna barin gun gida suka koma saida nasir ya sauke Mahfus snn shima yaje gida.
"Mahfus yana shiga yasami inna a parlour zaune shima xama yai snn ya gaida inna.
"inna ta amsa hade da tambayar yadda akai.
"Mahfus ya kwashe komai ya sanarwa inna.
"inna salati tasa hade da mmkin fadi tana fadin Allah yai tsinanniya ashe muna zaune da yar'daba ne bamu saniba.
"garama da Allah yasa rukyyt ta mutu sbd banga amfani hada zuri'a da irin w'yar nan mutani ba.
"Mahfus yace wlh inna babu abinda yafi damuna kamar sakin amatullah da nai.
"ashe kenan duk sherine.
"kai amma fadi ta cuceni ta rabani da mai sona Allah ya'isa tsakanina da'ita.
"hannu Mahfus ya kwashe yasa akai hawaye kuwa wani kebin wani.
"gani haka yasa inna matsowa kusa dashi tana bashi mgn da hakuri.
"fashewa da kuka Mahfus yai yana fadin wlh inna inaso matata gashi bansan yadda xanyi ta dawo guna ba.
"wata kila narasa amatullah kenan.
"amatullah tariga taimin nisa inna shikenan inna.
"inna najin haka ta haushi da fadi tana fadin dan Allah karufewa mutani baki meye kakeyi haka kamar mace?
"sai kace ita kadai ce mace a duniya, baga mata nan bila adadun ba.
"Mahfus najin haka mikewa yai yashige dakin amatullah kan gado ya fada yaci gaba da kuka.
"washe gari da xuwa amatullah hajiya takira duk yaranta tace tanaso ganisu.
"shima alhji Ibrahim ta sanar dashi.
"shima yana yin breakfast yaxo shida yya Abdul, sun shigo ba'a dade ba su Anty Frd da yya khamis suka shigo.
"har kasa suka duka suka gaida alhji Ibrahim da hajiya snn suka xauna.
"lokacin amatullah tana daki kwance.
"hajiya tacewa yazed ya kira mata amatullah.
"yana xuwa tare suka fito amatullah na ganisu yasa ta duka har kasa ta gaidasu snn ta samu gu ta xauna.
"zunnurai yana jikin yazed yana wasa.
"hajiya ne ta kwashi abinda ya faru ta fadi masu.
"salati alhji Ibrahim yasa hade da cewa yanxu shi Mahfus din ne yai mata haka?
"karab Anty Frd tace himm Abba kenan idan akwai abinda yafi hakama Mahfus xai aikata.
"yya Abdul da yya khamis cewa sukai kawai Allah ya kyau ta.
"alhji Ibrahim yace naji saki dai ta saku amma wlh sisi baxan yafe masa ba, gaba daya kudin amatullah saiya dawo dasu ko kuma nasa a daureshi.
"Anty tace kwarai da gaske Abba tunda beda mutunci.
"amatullah na zaune babu abinda takeyi sai kuka.
"murmushi kawai hajiya tai hade da cewa a dai bi abin a hankali alhji.
"alhji yace barni dashi kawai hajiya , besan koni waye ba amma xai sani.
"nan dai sukai ta tattanawa yadda xasu bullowa al'amarin.
"bayan kwana biyu su Mahfus suka hadu a kotu nasir da Mahfus sai fadi da boys dinta da kuma tsohon mijinta.
"bayan alkali ya shigo kowa ya gabatar da kansa snn alkali ya juya gun fadi yake tambayar ta.
"batare da tabawa kotu wiya ba duk ta amsa laifinta.
"suna areas boys din su amsa laifinsu.
"hakan yasa alkali ya dauki kudin Mahfus ya bashi.
"Mahfus yana amsar kudinshi yace ta tafi ya saketa saki uku.
"shikuma tsohon mijinta hakuri kawai aka bashi sbd tuni ta riga ta salwantar da kudinshi.
"kuka yai sosae hade da yimata Allah ya'isa snn shima ya saketa saki uku.
"bayan duk sun gama alkali yace an yanke mata hukunci xaman gidan yari na shekara talati sbd bada saninta tai ba, matsala daya ne da ta aikata hakan kuma tana gani ta gudu sbd wani manufa nata.
"su kuma boys dinta an yanke masu hukunci xaman gidan yari na shekara goma.
"da haka shari'a ya tashi.
"bayan kwana biyu Mahfus ya sami inna yake sanar da'ita shifa gaskiya yanaso yaje bikon matarsa.
"inna tace yabari tuku sai bayan kwana biyu.
"Mahfus be musaba haka ya hakura amma hankalinsa baya tashi saida dare kusan kasa bcc yakeyi.
'"bayan kwana biyun haka yasake komawa gun inna.
"inna tasake cewa yabari sai bayan kwana biyu.
"tun daga lokacin besake mgn ba.
"washe gari tun da safe yabar gida gidan su nasir yaje ya sallamesa cewa xaitafi yadawo da amatullah.
"nasir bece komai ba Allah ya kiyaye hanya kawai yace.
"Mahfus yace amin nagode.
"a gwurgwuje Mahfus yabar gidan.
"yana fita nasir yace jeka idan rabo wahala ne ke kiranka sai kaje.
"Allah ya kyau ta
H.S.Z.ce
🌺💦🌺
💦
MATAR FARI
(THE FIRST WIFE)💦
Fasaha online writes F.o.w.
MMN USWAN
H. S.Z.
44
"Anty tana fita gida ta xufa kai tsaye.
"tana shiga mijinta yace har kindawo?
"Anty tace eh.
"tunda akasa Mahfus ya cell sai faman tunani yakeyi kala2 gashi babu waya a hannunsa banle ya sanarwa nasir.
"shima nasir din gani safiya yayi Mahfus be kirasa ba yasashi daukar waya ya fara niman number Mahfus koda yai trying sai ya jiya switch off.
"jin hakan sai yai tunani kodai bashi da charge ne.
"daga nan ya hakura be saki kiraba.
"amatullah tana karyawa tai shirya xuwa shago.
"gani ta shirya xata fita zunnurai yasa kuka zai bita.
"itako amatullah tace babu ida xata dashi.
"Sai da hajiya tasa baki snn amatullah ta tafi dashi.
"sashi tai a gefen ta ita kuma tana driving sai faman xuba mata xance yakeyi har suka isa.
"suna isa bayan amatullah ta fito xagowa tai ta fito dashi snn tasa key ta rufe motar ta.
"suna shiga shagon yaran ganita da sukai da zunnurai daya daga ciki ta tambayeta da cewa Anty wannan yaron waye?
"murmushi kawai amatullah tai masu.
"shima zunnurai sai faman kallansu ya keyi.
"daukarsa sukai suna masa wasa.
"bayan alhji ya fito daga gida saida ya biya gidan su amatullah gun hajiya ya sheda mata duk yanda sukai da Mahfus.
"murmushi kawai hajiya tai snn tace nidai gaskiya inda so samune nafiso ta koma dakinta sbd babu amfani yarinya karama kamar amatullah ace tana xawarci, kuma ko ba komai aure shine mutunci diya mace.
"alhji yace haka ne amma gaskiya koda xata koma saiya dawo mata da dukiyarta tsaf snn takoma.
"sai hajiya tace eh baxan hanaka daukar mataki akan hakan ba, amma dan Allah idan har yaxo da niman shiri ne abashi ita su tafi.
"sbd wlh amatullah tana son mijinta shima nayi imani yana sonta kaga idan akace za'a rabasu akwai matsala dan ma Allah yasa ba garinsu daya bane da Allah kadai yasan abinda zasu rinka aikatawa.
"kaga da suje suna aikata alfasha gara suje suyi na sunnah.
"shiru alhji yai yana saurarenta har takare snn yace gaskiya ne kuma kinyi tunani, shikenan nasan abinda xanyi.
"hajiya tace yanxu ina yake?
"alhji yace tun jiya yatafi amma inasa ran xaidawo sbd ce masa nai sati daya nabashi.
"hajiya tace to babu damuwa Allah ya dawo dashi lpy.
"hajiya tace amin.
"har alhji xai mike sai kuma ya dawo ya xauna.
"da sauri hajiya tace lpy alhji?
"gwaran murya yai snn yace kema yakamata a cikin xawarawanki kifito da guda daya daga ciki sbd kinga axumi yana xuwa ina miki kwadayin samu ladan kwatanga mai tsarki.
"murmushi hajiya tai hade da cewa kaji alhji dai inani ina wani aure kuma.
"murmushi alhji yai snn yace a tunaninki kin wuce aure ne?
"hajiya tace aa amma munbar wa yar'baya.
"murmushi kawai alhji yai hade da mikewa.
"gani har dare yai Mahfus be kira nasir ba, da yaran shagonsa yasa nasir ya fara tunani ba lpy koda ya sake trying number har yanxu switch off.
"itama inna rabonta da Mahfus tun jiya hankalinta ya tashi sosae sbd tunda take da Mahfus be taba kwana har ya yini be kirata ba.
"hankalinta ya tashi sosae cikin dare kasa bcc tai sai faman tunani kala2 takeyi.
"washe gari tunda safe nasir yaje gidan inna tambayar ta ko Mahfus ya kirata.
"a lokacin ne inna take tambayar nasir inna Mahfus yaje?
"nasir yace cemin yai xaije bikon matar sane.
"kuma koda ya'isa saida ya kirani ya sanar dani ya'isa.
"Amma kuma tun daga lokacin bansake samu saba.
"koda na kirashi number shi switch off.
"amma bari na kira bbn amatullah naji ko ya'isa gunsa.
"inna tace to kirashi muji.
"nasir na kira alhji Ibrahim ya daga kiran nasir, cikin girmamawa nasir ya gaida alhji Ibrahim.
"shima amsawa yai da fa'arsa.
"snn alhji Ibrahim yace yah mutuminka ya'isa gida?
"shiru nasir yai snn yace wlh alhji dama buguwa nai naji ko ya'iso.
"alhji yace yaxo amma be dade ba yabar gidan akan xai koma gida.
"nasir yace to wlh bedawo ba kuma koda munyi trying number sa baya shiga.
"alhji yace subbuhanallah allah yasa dai lpy.
"nasir yace amin.
"bayan sunyi sallama da alhji ne nasir yake sanarwa inna yadda sukai da alhji Ibrahim.
"kuka inna tasa hade da fitowa da wayarta ta bawa nasir tace ya kira mata bbn junior.
"kira daya nasir yai masa bbn junior ya daga bayan sun gaida ne nasir yake sanar masa inna ce takeso ganisa.
"bbn junior yace ga shinan xuwa.
"suna kashe waya shima nasir sallamar inna yai yakoma gida.
"yaran aikin Mahfus tunda sukaga haka duk cinikin da akai hadawa sukeyi a bawa manager shikuma yasa a banking.
"alhji Ibrahim suna gama mgn da nasir kiran hajiya yai ya sanar mata abinda ake ciki.
"salati hajiya tasa ta sanarwa ubangiji take ta kira yya khamis ta sanar masa shima kiran Anty Frd yai ya sanar mata.
"cikin baraxana Anty Frd tace subbuhanallah Allah yasa dai lpy koda hatsari yai a hanya?
"yya khamis yace to waya sani.
"Allah ya kyauta kawai tace snn sukai sallama.
"hajiya ta hana a sanarwa amatullah cewa ba'aga Mahfus.
"tun daga lokacin hajiya ta amshi mine line din amatullah kuma koda mgnr Mahfus takeyi da zaran taga amatullah ta fito canxa mgnr takeyi.
"Mahfus nada kwana uku a cell Anty Frd taje station din sawa tai aka fito dashi.
"suna hada ido Mahfus yace dan Allah Anty mai nai miki kikasa akaimin haka?
"dan Allah ki taimake ni kisa a fitar dani wlh nasan dangina sunanan suna nimana.
"dariya Anty tai snn tace idan har kaimin abinda nakeso wlh ko yanxu ma xansa a sakeka.
"da sauri Mahfus ya idan har besabawa shari'ar musullumci ba xanyi.
"takarda da biro ta dauko hade da mika masa snn tace shedar saki amatullah da kai shine nakeso ka rubuta min anan.
"da sauri Mahfus yace Anty me kikace.
"sake memeta masa tai.
"Mahfus yace wlh Anty koda shekara xanyi a rufe baxan rubuta takardan sakin amatullah da hannunaba.
"babu yadda Anty batai ba amma Mahfus yaki, hakan yasa Anty tace a medashi ciki.
"shima beyi musuba mikewa yai ya koma ciki.
"da yamma bayan sallar isha alhji Ibrahim yasha wankarsa hade da kwalliya cikin manyan kaya yacewa hajiya motarsa xai tafi wani dubiya ne.
"hajiya tace a dawo lpy.
"alhji yana fita sai gidan su hajiya mmn amatullah.
"itama tai mmkin ganisa cikin dare haka.
"har parlour ya shigo ya xauna.
"itama hajiya fitowa tai parlour ta xauna snn suka gaisa.
"hira alhji Ibrahim yaja hajiya tashi sosae harda mgnr Mahfus da amatullah.
"alhji yayi kokarin baiyana abinda ke tafe dashi amma yakasa saidai hausawa sunce labarin zuciya a tambayi fuska.
"mmki ne sosae ya kama hajiya sbd yadda taga alhji Ibrahim ya canxa salon mgnrsa ba yadda ya saba ba.
"Da haka har goma yai yace xai tafi gida nan sukai sallama.
"gani kwanan Mahfus hudu kenan yasa nasir cewa xaixo Niger din da kansa ya dubo Mahfus.
"bayan ya shirya xai tafi saida yaje sallamar inna, inna najin haka kuka tasa tace itama xata.
"nasir be musa ba yace babu damuwa.
"Kaya kawai ta canxa ta fito mikewa nasir key din gidan tai.
"nasir yasa key ya rufe snn suka dauki hanya.
"su nasir basu isoba sai bayan la'asar har gidan su amatullah nasir suka tafi.
"a bakin gate yai parking snn suka fita suka shiga ciki.
"a bakin kofar parlour suka tsaya snn nasir yai sallama.
"yazed ne yafito hade da amsawa gani nasir ne yace sushigo ciki.
"a parlour suka tsaya snn yaje ya kira hajiya.
"tare suka fito, hajiya na gani mmn Mahfus ne da nasir da sauri ta kariso gun cikin fara'arta ta gaidasu.
"shiko nasir har kasa ya duka ya gaida ta.
"hajiya tace yazed ya kawo masu ruwa da lemo.
"kurban ruwan kawai inna tai, gani yanayin inna yasa hajiya cewa badai ace har yanxu ba'aga Mahfus ba?
"inna najin haka tasake fashewa da kuka.
"salati hajiya tasa tace Allah yasa duk inda yake yana cikin koshin lpy?
"hajiya bata rufe bakiba zunnurai yafito a guje ya fada jikin hajiya.
"hajiya tace jeka can ga bbnka nan.
"juyowa zunnurai yai yana gani nasir da sauri yaje ya rungume nasir.
"shima nasir daukar sa yai ya rungume.
"waya hajiya ta dauko ta sanarwa alhji Ibrahim da yya khamis da Anty Frd cewa har yanxu ba'aga Mahfus ba kuma ga mmnsa taxo.
"alhji yace da yamma xaixo, shima yya khamis cewa yai saida yamma xaixo.
"itako Anty Frd cewa tai sai gobe xataxo.
"da yamma amatullah na shigowa parlour karo tai da inna da nasir da sauri taje ta rungume inna.
"inna na gani haka kuka tasa hade da cewa ya mukaji da juyayi?
"amatullah tace name inna?
"da sauri hajiya tace tashi kishiga ciki.
"gani kukan inna ya karu yasa amatullah fashewa da kuka hade da tambayar lpy inna?
"Kodai Mahfus ya mutune?
"shiru inna tai.
"gani haka yasa amatullah kara volume din kukanta tana fadin na shiga uku hajiya shikenan Mahfus din na yatafi ya barni.
"jikin hajiya amatullah ta fada taci gaba da kuka.
"gani irin kukan da takeyi ne yasa hajiya cewa ke bafa mutuwa yai ba, ba'a ganshi bane dai.
"wani irin ihu amatullah tasa da sauri ta dauko wayarta tafara trying number Mahfus duk da haka switch off.
"gani irin kukan da takeyi ne yasa inna barin nata kukan takoma lailashin amatullah.
"koda alhji Ibrahim yaxo duk dai mgn daya ce basusan inda yake ba amma, da safe zusuje police station suyi report da kuma hospital dubawa ko hatsarine yasamu a hanya.
"dare ranar haka amatullah ta kwana buba ci babu sha sai kuka.
"amatullah na idar sallah asuba ta shirya jiran su alhji Ibrahim kawai takeyi.
" su alhji Ibrahim da yya khamis basu xoba sai bayan goma.
"suna zuwa kyaleta kawai ta dauka yya khamis da nasir sukace ta bari kawai su xasuje su duboshi.
"kuka amatullah tasa.
"gani kukan da tasa alhji Ibrahim yace taxo sukafi.
"asibiti suka fara xuwa duk dakunan yar' hatsari saida suka duba amma babushi suka koma gun wani doctor shine yace yau kwana hudu kenan da aka kawo wasu yar'hatsari kuma duk sun mutu ko xasu iya dubawa.
"da sauri amatullah tace eh.
"alhji yace tayi hakuri su zasu shiga su duba.
"amatullah tace itama xata iya.
"tare suka shiga daya bayan daya ake bude masu fuska gawar kowanne saida amatullah ta duba amma duk bashi.
"gani bashi a gun kuka tasa.
"alhji yace ta daina kuka yanxu sai kuma suje police station ko Allah xaisa a dace.
"kai tsaye police station suka nufa saida suka xaga biyu a na uku ne sukaje wanda Mahfus yake nan.
"da hotonshi suke yawo koda suka tambaya police din dake gun sukace bayanan.
"har su alhji sun juya daya daga cikin police din yace suxo gaskiya yana nan amma baxasu ba da belinsa ba sai wanda ta kawoshi taxo.
"alhji yace waye ta kawoshi?
"Police din yace sunanta Frd.
"da sauri alhji ya dauki waya ya kirata.
"Anty na gani number alhji da sauri ta daga.
"ko gaisuwa basuyi ba alhji yace da'ita maza ta bada ixini a saki Mahfus.
"mikewa police din wayar alhji yai sukai mgn bayan sun gamane alhji ya biya duk wani kadin da suka lisafa masa ya biya snn aka fito da Mahfus.
"ana fitowa dashi a guje amatullah taje ta rungumeshi tana kuka.
"shima rungumeta yai hade da share mata hawaye.
"alhji na gani haka barin gun yai ya koma mota.
"shiko nasir dariya kawai yake masu.
0 comments:
Post a Comment