Da marece sosae suka isa garin, sai da aka gama kai kowa sannan ta tafi kai Saude gidan da zatayi aiki, sai kalle-kalle take ta dai daure tace, "Baba haja wai duk nan garine?"
"eeh mana, babban birnin tarayya kenan da kikeji"
"Aini ban ɗauka yakai girman haka ba, wannan ai sai dai a kirashi k'asa guda"
"A'ah shima garine, ai bakiga komi ba a girman garin Abuja,"
"Taɓ! Gaskiya ne Baba haja, kowah da garinsu"
Baba haja na mata daria tace "hakane kam"
Suna tafiya ta k'ara ganin wani ginin bene, shima dai kasa shiru tayi tace "Yanzu baba wannan ma mutanene suka ginashi?"
"tohh saude kin taɓa ganin Aljanu sunyi gini?"
"A'ah baba, anma dai yana faɗowa ko?"
"A'ah ko zaki hau ne?" Baba Haja ta tambayeta cikin tsokana, da sauri ta girgiza kai, "A'ah ni bazan hau ba ya zurma dani ciki"
Baba Haja na mata daria tace "ai bazaki zurma bafa"
"A'ah nidai Baaba"
Ana kiran Sallahr Magrib suka isa gidan da Saude zatayi aiki, Babban gidane sosae anan ma saida Saude ta cika Baba Haja da tambaya, ta ware ido sosae tana kallo, sai tayi tuntuɓe take ɗan kallon hanya sannan taci gaba.
Saman carpet suka zauna bayan an tafi musu iso, sai faman shafawa take tanajin laushi har mai gidan ta fito da fara'arta da yake tasan baba Haja, suka gaisa cikin mutuntawa, Saude ma ta gaisheta, sannan Baba haja ta gabatar mata Saude a matsayin er aikin data nema, saida ta gama k'are ma Saude kallo sannan,
tace, "Baba haja mantawa nayi ban faɗa miki ba, banda en matah indai an samu dattijuwa dai ita nakeso"
"Ai duk ɗayane uwargidanah, duk aikin da dattijuwa zata miki itama zata iya"
"Ba aikin ba ai Baba haja, ina tsoran budurwa da aiki ne"
"tohh ai ita ba budurwa bace, gashi dai harda Goyonta"
Dariya tayi "Haba Baba, wannan ai sai dai ko k'aninta, anma er yarinya da ita da goyo? A daiyi hak'uri a samo dattijuwar Baba, anma dai wannan batayi ba"
"Tohh ai shikenan" Baba ta faɗa a sanyaye, ita kam Saude tuni ta lulluɓe fuskarta a mayafi, tana ta kukanta marar sauti, yanzu aikinma taga samu taga rashi.
Abinci aka kawo musu da drinks, bata wani ci da yawa ba dai duk Baba na lura da damuwar data shiga, ana isha'i suka fito gidan.
Suna fitowa Saude ta fashe da kuka, Baba haja ta kalleta,
"karki kuka Saude, insha Allah zaki samu inda zaki aiki"
"A ina Baba Haja? Nidai Saude naaga rayuwa"
"Haba Saude, ki daina mana, ki barni inyi tunanin gidan da suka sakani neman er aiki"
Shiru tayi sun samu wuri cikin duhun daren sun zauna, Baba haja na tunani ita dai sai shesshek'ar kuka take.
"tohh ni Saude ina zan kaiki yanzu?"
"ki taimakeni Baba don Allah karmu koma garinnan"
"Yanzu tashi muje gidan Hajia, nasan ko bazata ɗaukeki aiki ba zata taimaka miki" da sauri kau Saude ta maida goyon Hafsat, ta saɓi kayanta suka tafi. Tana Addu'ah a ranta Allah yasa ta dace.
Gabanta naa faɗuwa suka isa gidan Hajiyar, harma yafi na inda suka fara zuwa girma, ga motocinan da ma'aikata birjik, duk da darene ko ina Haske yake da fitilu masu launuka sun haska gwanin kyau duk hanyar da zasu bi, tafiya sukayi mai ɗan nisa sannan suka isa hanyar da zata sada su da cikin Gidan, gabanta na faɗuwa sukayi sallama suka shiga.
Dattijuwar macece fara tas kyakkyawar gaske, da jin daɗi da hutu suka ɓoye shekarunta, tana zaune a falo taa gama sallamar bak'i, ta tari su da fara'arta, tana nuna musu kujera su Zauna, Baba Haja ce kawai ta zauna, anma Saude kasa zama tayi.
"Haja Sai yau muke ganinku?" dattijuwar ta faɗa tana murmushi,
"Hajia abubuwanne da yawa, yanzu ma en aiki ne nazo kawowa"
"Ayyah! Wannan ta wajenki ce?"
Tayi dariya "Ta gida daice, anma itama aikin na kawota, ba'a dace ba nace bara muzo ko kina da buk'ata"
"tohh wannan er yarinya ina zata iya da aikin gidannan? Kuma Gaskia ban daɗe da ɗaukar en aiki ba"
"tohh Hajia a duba dai, taimakon da kika saba"
"tohh ai gaskia...." tayi shiru tana tunani, Saude batasan sanda kukan da take rik'ewa ya kubce mata ba,
"tohh ɗiyata lafiya kike kuka?"
Cikin tausayawa Baba Haja tace "Hajia nasan ke kaɗaice zaki iya taimaka mata, rayuwarta tana buk'atar taimako, batasan iyayenta ba tun kafin tayi wayau Allah ya ansa abinshi, gashi babu miji, sai musgunawar dangin mahaifi" nan Baba Haja ta fara bama hajiyar tarihin Saude komai ta faɗa mata sai dai taa ɓoye mata cewar Mijin Saude mutuwa yayi bata da aure, daman Saude taa rok'eta karta faɗa mijinta guduwa yayi ya barta, duk daman Baba Hajar bata sanshi ba.
Tsabar tausayawar da hajia tayi mata har saida ta zubda hawaye, kuka sosai tayi daman macece mai tausayi bama kamar ga mata, "Sannu kinji Saude, gaskia naa tausaya miki, rashin iyaye ba k'aramin rashi bane, Ga na miji kuma, ni naasan zafin rasuwar miji don har yau inajin ta maigidana, shekararshi ɗaya kenan da rasuwa,"
"Allah sarki, Allah yaji k'anshi" inji Saude
"Ameen tare da naki, ai ke keda rashi, da k'uruciyarki babu miji babu iyaye, wallahi na tausaya miki sosai"
Maganganun hajia kuka suke k'arama Saude,
Ta share hawayenta cikin son kauda ma Saude damuwa,
"Ina tsohuwar take? Kawomun itanan in ganta Allah sarki itama tayi rashin mahaifi" Saude ta kwanto Hafsa a goye, cikin tsaftar ta duk da kayanta a koɗe suke, an wanke tas babu k'azanta, kuma bata barinta tayi fitsari a wando.
"Ya sunanta?" hajia ta tambaya tun kafin a mik'a mata ita,
Baba Haja ce tace "Hafsat"
"A'a'ahh ashe takwarah ce, zonan Hafsatul kiram" ta ansheta tana fara'a, itama hafsat ɗin sai washe mata bak'i take.
Cak ta tsaya tana k'are ma Hafsat kallo, yanda take daria da sauran Abubuwa kallonta kawai take, ta kasa hak'uri dai tace "Baba Haja abun mamaki bai k'arewa a duniya"
"Hajia wani abun ya faru?"
"Ke baki gani ba Haja? Wallahi yanayin yarinyarnan Sak na Daddy lokacin yana k'arami, ko zuwan duk da yana babba anma yanayin fara'arsu da dariyarsu ɗaya, ke ni duk yanayinsu ɗaya ma wallahi"
"aikau hajia nima saida kikayi magana na lura, abun mamaki kam da yawa yake, tunda nazo daman ban tambayi mutumin nawa ba, ina mai sunan Baba?"
"Aikam saɓani kuka samu Daddy yau ya koma wurin aiki"
"Allah sarki, mun kwana biyu bamu gaisa ba" Hafsat ta kamo fuskarta tana ta k'iriniyarta a samanta kamar sun saba, itama sosae ta fara jin yarinyar a ranta.
Baba Haja ma kallonta take "Gaskia duk da basu kama, anma yanayin harya ɓaci"
Hajia tace "ai daman hakane, sai kiga wani yaa haifa maka ɗa"
"Hakane fa, kama dai komai na babarta ta ɗauko"
Hajia ta nisa bayan duk sunyi Shiru, "Zan ɗaukeki aiki Saude, anma ina da sharaɗi"
Harta farajin daɗi, kafin hajia ta k'arasa maganarta, sai kuma murnarta ta koma ciki, "ki faɗi sharaɗin Hajia, insha Allah ko menene zanyi"
"kin tabbata?"
Ta ɗaga kai gabanta na ci gaba da faɗuwa, "Indai zaki zauna anan, sai dai ki zauna a matsayin ɗiyata" wani farin ciki ne ya kama Saude da Baba Haja ko wannensu sai murna yake,
"Nagode! Nagode Hajia! Allah ya saka da mafificin Alkhairi" abunda Saude kawai ke cewa kenan, tama rasa abun cewa saboda murna,
"Ba komai Saude, hakanan tausayinki ta ɗarsu a raina, zan rik'eki amana, kema ki rik'e amana, zan zame miki gatan da kika rasa, zan baki duk abunda zaki nema a rayuwa indai Allah ya horemun ina dashi, zan baki duk wani farin ciki da zaki buk'atah"
"Na gode Hajia, ki bani iyayen dana rasa ma yafimun komai, na miki alk'awarin bazan taɓa baki dalilin da zaki koka da halina ba"
"Naji daɗi sosai Saude, ki saki jikinki kamar gidanku, ni kaɗaice a yanzu, bara a nuna miki ɗakin yayarki da tayi aure anan zaki zauna"
Ta fara k'wala ma mai aikinta kira, sai gata da sauri ta mata umurnin akai Saude ɗakin ɗiyarta da tayi aure, dare yayi ta huta, hafsat ɗinma cewa tayi ta barta zata bama wacce zata kula da ita tunda an yayeta, Baba Haja ma ɗakin bak'i aka kaita ta kwanta.
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
53
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
Ga Shafinku nan na jiya Masoya littafinnan, ```KISAN KANKI GRP```😜❤ gareku RAZ NOVELLA 1&2 I really appreaciated soyayyar da kuke nunama littafinnan, Rabiat na k'aunarku har k'asan zuciyatah😍
www.babymsh.blogspot.com
Wani k'ayataccen ɗaki aka shiga da Saude, ɗaki ɗayane anma babba sosae, akwai kujeru masu kyau da babban Gado saiti, komai na ɗakin a tsare kalan skye blue, ba k'aramin k'ayatuwa yayi ba, a ciki harda toilet shima babu abunda babu a ciki kamar ansan da zuwan Saude,
Wuri ta samu ta zauna gefen gadon saman lumtsumemiyar katifarta, wai wannan k'ayataccen ɗakin duk nata ne, duk kayan dake cikin ɗakinnan na mutum ɗaya ne, lallai en gayu sunji daɗinsu,
Mai aikince ta dawo mata da abinci sannan ta faɗa mata tanaso tayi sallah, ta rakata toilet ta nuna mata yanda zatayi, ananma duk tasha k'auyanci, dak'yar ta gama kalle-kallenta tayi alwala ta fito.
Tunda tayi sallah ta kwanta barci ya ɗauketa, ko juyi batayi saman luntsumemiyar katifar, sai da asuba aka k'wank'wasa mata k'ofa, dak'yar ta tashi tayi sallah saboda barcin dake idonta, tana idarwa ta kwanta saman carpet ɗin taci gaba da barcin.
Sanda ta farka ta fito har Baba Haja ta tafi, bataji daɗi ba taso suyi bankwana ta mata godiya sosae, er aikin Hajiya ce ta rakata har ɗakin da hajiyar take tace tun ɗazu take nemanta, da Sallama ta shiga ɗakin, ta amsa mata duk da tana kan waya ne, ta ɗan tsaya bata shiga ba.
"shigo mana Saude, ina waya da ɗan uwanki ne"
Allah sarki hajia har yaranta sun zama en uwan Saude, saman cinyarta ta iske Hafsat tana ta wasanta, tana ganinta ta k'ara washe baki tana mik'a mata hannu, anma kunya ta hanata ɗaukarta ta nema wuri k'asa ta zauna tana jiran Hajia ta gama magana.
Cikin nishaɗi take wayar cike da soyayyar ɗa da uwa,
"Yanzu haka kaa gantanan hannuna, sai kallonta nake tana ɗebemun kewarka da kana yaro" bataji mai akace ba ɗayan ɓangaren sai dai hajiyar ta k'ara magana,
"nifa ba kama kuke ba, ita ai kyakkyawah ce kamar mahaifiyarta" dariya ta k'arayi bayan taa gama magana.
"kana dashi, anma dai takwarah ta taa fika kyau"
Tana dariya ta gama wayan "Hmm shak'iyin yaro kawai"
Saude tayi murmushi, "Ina kwana hajia"
"lafiya lau Saude ya kika tashi? ya bak'unta?"
"Alhmdlh"
"gaskia kinsha gajia, har Baba Haja ta tafi kinata barci, nina hana a tasheki gara a barki ki huta"
"uhum" kawai tace,
"Daddy ne muke waya inata bashi labarin Hafsat, yarinya mai saurin sabo, wai harya k'agu weekend yayi yazo yaga childhood image ɗinshi"
"Allah ya dawo dashi lafiya"
"Ameen, ya dawo yaga k'anwar dana mishi" murmushi dai kawai Saude take, taso ta tambaya Hajia sunanshi na gaskia, anma kunya ta hanata, da alama Hajia tanaji dashi sosae.
"kinyi wanka?" ta katse mata zancen zucin da take, girgiza kai tayi
"karin kumallo/kalaci fa?"
"A'ah"
"Har yanzu? Aikam mun tashi ɓatawa, banison bak'untarnan Saude kije kitchen talatu ta haɗa miki abunda zakici, idan kinyi wanka ki buɗa ma'ajiyar kayan sawa akwai na yayarki nanan kafin tayi aure, k'ila suyi miki kafin in fita ayi miki wasu"
"tohh Hajia nagode"
"kuma dai? Idan zakimun Godia duk abunda zan miki a rana dubu nawa zakimun? Kamar mahaifiyarki nake babu godia tsakaninmu, don haka ki ringa kirana da Momie kamar sauran Yayunki"
"Tohh momie Na..." sannan kuma tayi shiru ganin Momie ta ɗago tana kallonta, ta sakar mata murmushi sannan ta fita wurin talatu, cikin sa'a a falo ta ganta, daman tana tunanin inda zata gano kitchen ɗin.
Zaman Saude cikin gidan tana daɗa samun kwanciyar hankali, duk da babu inda take fita kuma shigarta da komai nata na k'auye nanan, sai dai jikinta dake k'ara murmurewa yana kyau ta ɗanyi k'iba jikinta ya fara kyau alaman hutu, kullum Momie zata kirata su zauna tana mata fira, tana k'ara janta a jiki, tsakaninta da Hafsat kuma sai kallo ko idan Momie taa fita ta ɗauketa, koda yaushe tana hannun Momie sai barci take bada ta wurin mai kula da ita, kayan yara masu na mata data gani zata zoma Hafsat dasu, ta washe sosai daman Gata kyakkyawa, kamar ba'a k'yauye aka haifeta ba, ta k'ara zama abun sha'awa ga kowa. Soyayya sosae take nuna musu kamar ita ta haifa Saude.
Kwananta biyar da zuwa gidan ko tsakar gida bata taɓa fita ba, aka fara shirye-shiryen dawowan yaron Momie, kullum sai momie tayima Saude firan Daddy, shima har gajia yake da labarinta da momie ke bashi, yamafi son firar Hafsat har waya suke tayi ta yi mishi gwarancinta.
Daren Ranar dazai dawo basu kwanta da wuri ba, soye-soye aka dinga mishi kamar ba mutum ɗaya ne zaizo ba, yanda Saude ta dage tana aiki duk da daman kullum bata zama, yasa momie take ta faman ce mata taje ta huta, anma bata tafi ba har aka gama.
Washe garin ranar dazai dawo friday, tunda safe suka farka aka fara girke-girke, momie sai faman kiranshi take tun safe, kaɗan-kaɗan taa cema Saude, ko mantawa take da tayi mata maganar?
"Kinga k'azamin yaronnan yak'i ya dinga barin mukullanshi a mishi gyaran ɗaki, kullum yafison zama cikin k'azanta"
Sai dai kawai tayi murmushi "ai haka ɗakin mazan yake Momie"
"Haba k'azamai dai, koda Husna nanan sun dinga faɗa kenan idan taa mishi gyara bai sani ba, wai tana zubda mishi takardu masu amfani"
"Allah sarki, ai basu cikason hakan ba"
"Hhm bakisan k'azantar Yayannan naki bane, saiya buɗa ɗakin nashi zakiga jibji" dariya tayi sosae, momie ma ta tashi tana dariyar jibjin da tace.
Har marece ana jiranshi baizo ba, momie sai kiranshi take a kashe sai marece sosai ta sameshi.
"wai meya tsaida kai har yanzu baka dawo ba?" ta ɗanyi shiru tana saurarenshi.
"A'ah kasan banson tafiyar darennan, kayi zamanka kai aikinka wani satin kaazo"
"A'ah nace, duka yaushe ka tafi? Ka zauna ka gama duk abunda kake fa"
"Yauwah tohh zan kashe saimun sake maganar" ta sauke wayar fuskarta da alamar rashin jin daɗi.
"kin ganshi ashe aiki ya tsaidashi, wannan satin bazai samu zuwa ba"
"Allah sarki, ai kamar gobene"
"Hakane Allah ya kaimu"
"Ameeen"
Da dare momie ta kirashi tana k'ara tambayarshi aikin, duk yaa lura bataji daɗin rashin zuwanshi ba, Momie taa damu dashi sosae, sai dai yaci gaba da kwantar mata da hankali da firar da zata sakata daria irinna ɗa da mahaifiya harta ware, sannan sukai sallama, lokacin Saude ta shigo mata saida safe, tana kan cewa ya rik'e wayan su gaisa da k'anwarshi harya kashe, ta mata bankwana ta koma ɗakinta.
Washe gari da wuri Momie ta fita, har Hafsat ta saka aka shirya mata ita ta tafi da ita Saude na can tana barci, sai k'arfe 10 ta farka da wata matsananciyar yunwa, ta sauko daga Gadon sannan ta jawo zani ta ɗaurin k'irji dashi saman doguwar rigar barcin jikinta, ta tsira ɗan kwalinta irin style ɗin da suke a k'auye shigarsu dai ta en k'auye, kai tsaye kitchen ta nufa.
Talatu ce kaɗai a kitchen ɗin ta fara aikin rana, ta gaisheta cikin girmamawa, sannan tace "Momie fa?"
"sun fita ita da takwararta"
"Yau safko sukayi kenan"
"aikam da wuri ta fita"
Suna ɗan taɓa firarta tana haɗa break fast, doya da k'wai sai ruwan tea ta ɗauka ta fito tana cema talatu bara tayi break fast ta dawo.
"ai naga alama barcinnan bai isheki ba, yunwah ce kawai ta tasheki"
"wallahi fa, ai hakanan dai zan barshi" ta faɗa tana murza ido da hannun data rik'e tean, bayan taa cika baki da doya. Dai-dai lokacin tana wucewa ta k'ofar da zata shigo da mutum falon.
Ji tayi ta kaima mutum karo, gaba ɗaya tean dake hannunta ya kwarare mishi a jiki, da sauri tayi k'asa dakai ba tare dasun haɗa ido ba, jikinta ya fara kyarma ganin yanda ta mishi a jiki tama kasa bashi hak'uri.
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
54
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Ko kallon inda take duk'e baiyi ba, ya wuce ta kawai ya shiga falon, wata hanyar yabi daban, saida taji yaa wuce sannan ta ɗago tana kallonshi bata ga fuskarshi ba, anma a jiki ma ba k'aramin haɗuwa yayi ba, shigarshi kanta ta dabance, ga k'amshin turaren daya bar mata nan mai daɗin k'amshi.
Sauke ajiyar zuciyah tayi bayan yaa shige, take tambayar kanta shi kuma wannan daga ina? Anma ganin yanda ya shiga gidan kai tsaye ya sanyata gano shine yaron Momie da suke sanya ran dawowarshi jiya. Yasseer ta tuna, da ko dak'ik'a ɗaya bata taɓayi ba tare da tunaninshi ba, hakanan wani lokacin sai dai ta shige ɗaki tayi ta kuka har sai k'uncin ranta yaɗan rage, don wani lokacin kuka ma yana maganin damuwa.
Break fast ɗinma kitchen ta koma dashi tayi, hakanan sukuku ta ringa taya Talatu girkin, har Momie suka dawo bata sani ba tana can suna aiki, sai dai ta aiko ma Talatu kalolin Abincin da za'ama Daddy,
Talatu tace "ashe dai Daddy yaa dawo? Yanzu girkin gidannan zai k'aru"
"cin abinci ne dashi sosae kenan?" Saude ta tambayeta,
"A'a zaki sha mamakin kalolin abincikan da za'a haɗa mishi, anma sai yaga dama zaiyi cokali biyar"
Sadeey tace "tohhh"
"sosai fa, kuma duk ma'aikatannan gidannan idan yazo ni kaɗai nake girki yaci, donshi bai son abincin en aiki"
"Allah sarki, wasu ai k'azantane basu so"
"kamar kin sani kuwa shima haka yake, don ɗan gayune na gaske, ubangidana akwai tsafta, anma idan kika shiga ɗakinshi...."
Tun kafin talatu ta k'arasa Saude ta kwashe da dariya tuna abunda momie tace jiya,
"tunma kafin kiga ɗakin nashi kin fara dariya kenan" ta faɗa taa ɗauka ita take ma dariya, talatu akwai labari koba komai firar da take mata tana rage mata wani tunanin,
"kinga yanzu tayani zakiyi mu ɗaura girkin nashi, rana nayi gashi kuma wannan ban kusa gamawa ba"
"tohh" tace sannan ta tashi ta fara k'ok'arin ɗaurawa, da yake tana koyo a wurin talatu kusan duk girkinma ita tayishi, har suka gama suka jerashi a dinning.
Ɗakin Momie ta shiga, tayi mata sannu da dawowa, harta mik'e zata tafi, Momie da fara'arta tace "Yayanki yaa dawo fa, yanzunnan ya fita dakun gaisa" shiru tayi data tuna abunda ta mishi saida taji tashin hankali, jiki ba k'wari tace, "Barka momie ya iso lafiya"
"Yauwah Saude, kije kiyi wankan kun gama girki ko?"
"eeh an ajje komai Momie"
"yauwah tohh idan kinyi wankan kimun magana"
"tohm momie"
Bayan ta fito daga wankan, mai kawai ta shafa ta saka kayanta, milk atamfa ce mai kwalliyan ja a jiki, ɗinkin riga da zani yayi kyau sosae, tayi ɗaurin k'irji da zanin can sama ta tattareshi, ta cukuikuye ɗan kwalin ta ɗaureshi tsakiyar kai, ta fito daga ɗakin ta fara biyawa ɗakin Momie, tare suka fito bayan taa kira Daddy a waya.
Da sauri Saude ta jama Momie kujera ta zauna, ta zuba mata abinci ta duba bata ɗauko miya ba,
"Momie ban ɗauki miyanki ba bara inzo"
Tace "tohh" tana k'ara kiran Daddy a waya ko meya tsaidashi? Da sauri ta ɗauko miyan tana sauri ta kawo ma Momie wurin shiga dinning ɗin sukaci karo shima yana sauri momie tayi kiranshi, kamar ɗazu dai gaba ɗaya ta juye mar miyar a jikin fararen kayanshi. Da sauri ta ɗaura hannu akai a razane.
Wannan karon ta k'ure hak'urinshi da rashin maganarshi, wata irin tsawa ya daka mata "ke jahilan wacce gari ce da bakya kallon gabanki tsabar k'auyanci"
Duk taa tsure hawayene ke bin fuskanta, "Kayi hak'uri"
"Dallah rufamun bakinki, hak'urin banza, wannan ma ai tsabar raini ne, kinga ɗazun ban miki ba kawai kuda kunfison mutum yana ɗaga muku murya"
"kinyi shiru malama saina faɗa miki ki gyara ɓarnar da kikayi?" da sauri duk ta ruɗe ta kamo rigarshi ta fara k'ok'arin gogewa duk wurin ya k'ara damewa, wani tsawar ya k'ara mata,
"ke! Miye haka?" duk ta tsorata taja baya, tama rasa me zatayi, Momie daga can tana jiyo su, cikin faɗa-faɗa tace "Haba Daddy banfason zafin rannan, tunda taa baka hak'uri kaje ka cire kayan mana" ya buɗa baki zaiyi ma momie magana kuma ya fasa, a zafafe yabar wurin bayan ya sakar ma Saude wani dogon tsoki, baiko kalla inda take ba.
Wata miyar taje ta kawo ma Momie, sannan ta gyara wurin duk jikinta a sanyaye, muryarshi nata yawo a k'walwanta, sosae take ratsa mata dukka sassan jikinta, ko kaɗan bataji daɗin abunda tayi ma ɗan lelen Momie ba.
Momie ta kirata bayan ta gama gyara wurin,
"Kinga zauna kici abincinki, ki manta da wannan Yayan naki Zafin rai ne dashi, kina hak'uri da faɗanshi kinji"
"babu komai fa Momie aini na mishi laifi"
"Yauwah tohh zuba abincinki kici" ta zuba kaɗan, tana zama taa gama zubawa sai gashi ya dawo da wasu kayan da alama wankama ya canja.
Bayan yaa zauna Momie tace Saude ta zuba mishi abincin, Momie tace "Me zakaci?" baiko ɗago kai ba ya bata amsa sannan yaci gaba da danna wayarshi, lallai mutuminnan miskili ne, ko magana bai cikason yi ba.
Data gama zuba mishin ma ya daɗe sannan ya ɗauka ya fara ci, yana ci yana danne-dannenshi a waya, sai dai yakai cokali yaji babu komi yaa cinye plate ɗaya, Momie na lura dashi tace "Da alama girkinnan dai yayi maka daɗi" cikin zolaya
"Gaskia ne Momie, talatu bata taɓa girki mai daɗin na yau ba"
"Daman ya za'ayi Talatu tayi girki mai daɗi haka? K'anwarka ce tayi maka"
"K'anwatah kuma?"
"eeh mana, idonka ya rufe da faɗa ko gaisawa bakuyi ba,"
Ranshi ne ya ɓaci, waida wannan cikakkiyar bak'auyarce Sauden da Momie ke bashi labari? Duk da baiga fuskarta ba, shigarta ya nuna ko hasken birni bata saba gani ba. Ajje cokalin kawai yayi ya mik'e zai bar wurin.
"Koma ka zauna nace" inji momie, yaɗan tsaya anma bai tafi ba, ta k'ara cewa "Idan ba so kake raina ya ɓaci ba" da sauri ya koma ya zauna don baison ɓacin ranta.
"Saude baki gaishe da yayan naki ba" a hankali tace "ina wuni"
"Lafiya" ya amsa a tak'aice kaman dole,
"Ya hanya an dawo lafiya?" tsoki ya saki kawai, sai da Momie ta mishi wani kallo sannan ya amsa, har lokacin hankalinshi nakan waya.
"Banson halinnan Daddy k'anwarka ce, ka ɗauketa kamar Husna, banson k'ara ganin wani banbanci"
"naji Momie"
"Yauwah Babanah, Saude tashi ki k'ara mishi abincinnan", don dai abincin ya mishi daɗi, anma kamar yace karta zuba duk da ya k'oshi sai yace "farfesun en cikin kawai" daman shi kaɗai ne baici ba, sai lokacin ta ɗaga kai ta kalleshi.
A tare shima ya ɗaga ido yana kallonta, wani irin faɗuwar gaba taji, da batasan dalilinshi ba, tama kasa ɗauke ido daga kallonshi duk taa zuba mishi manyan idanunta, duk yanda ake cewa suna yanayi da Hafsat bata ɗauka yakai haka ba, har yanayin kallonsu ɗaya, shima kallonta yake ko k'iftawa baiyi, bak'auyah ce, anma ba irin k'auyawan daya saba gani ba, kallonta kawai yake yana k'are mata kallo,
Ya rigata ɗauke ido, gaba ɗaya rikitashi take da manyan idanunta, "ke kallonma k'auyanci kike mishi?" da sauri ta sauke idanunta tana zuba mishi girkin, Momie tayi dariya kawai lokacin taa gama nata launch ɗin.
Ta mik'e zata tafi yace "Momie wai yaa maganar kiwon da nace miki zan fara?"
Tana dariyarta ciki-ciki tace "Kiwon en ciki?" aikam sun bama Saude dariya, shima dariyar yayi, "Nifa Momie ba santi nake ba"
"ai bance ba, daɗin girkin Saude ne kawai kakeji" ta tafi tana dariya, ta barshi daga shi sai Saude a wurin, waya taji an kira shi, abinda kawai taji yace "Eeh Najib ne"
A hankali ta sake maimaita sunan nashi "NAJIBULLAHI" suna mai daɗi.
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
55
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
Wannan shafin sadaukarwane gareki sis AL'EEMAN, naga sak'onki, kuma naji daɗin soyayyar da kikema littafina, nagode sosae da Addu'arki gareni, Allah yabar zumunci, Ameen
www.babymsh.blogspot.com
Tunda ya fara magana a waya ta zuba mishi manyan idanunta tana kallonshi ko k'iftawa batayi, maganarshi cikin nutsuwa hankali kwance yake fitar da ita ɗaya bayan ɗaya, yana cikin magana ya ɗago yaga shi take kallo, wani banzan kallo ya watsa mata, batasan ma yanayi ba, saida ya gama wayan har zai mata magana ya fasa, sai dai yaja dogon tsoki, aikam da sauri ta dawo hankalinta, bata tsaya ganin kallon da yake watsa mata ba tabar wurin.
Abinda ta lura ga Najib (Daddy) baison yawan magana, kuma bai cikason a shiga harkarshi ba, ita kaɗai ke zancen zuci harta isa amsa kiran Momie.
Bayan ta duk'a har k'asa tace "Gani Momie"
"Yauwah ki shirya yanzu Daddy zai ajjeki gidan Husna, yanzu taimun waya batajin daɗi kiɗan rage mata ayyukan gidan"
"tohh Momie" ta tashi zata tafi Momie ta fara magana, "itama dai Husna, tak'i yarda a ɗaukar mata er aiki, yanzu aida taa samu maiyi mata gyaran gidan" Saude ta fita ta barta tana faɗa, daman Momie tana bata labarin Husna itace er Autar ta tana bima Najib (Daddy) shine na biyu, sai kuma babban yayansu yana Moscow shida Matarshi, yaranta uku daman.
Kayan jikinta mayafi kawai ta ɗaura akai, sannan ta dawo ta faɗama Momie taa shirya, ba k'aramin ɓata rai yayi ba da Momie tace ya kaita gidan Husna kawai don bazai iya mata musu bane, wani irin kallo yakai mata sannan ya kalli zanin data ɗage can sama (alaman ta saukeshi) donshi yafi aika sak'o da kallo bai cikason magana ba, bata gane mai yake nufi ba, sai tayi saurin kauda kai.
"A haka zaki fita da wannan zanin?" ɗaga kai tayi bata fahimceshi ba,
"da Allah saukeshi nace" da sauri ta saukeshi, anma still dai saman ciki, kaɗa kai kawai yayi ya wuce gaba ta bishi, yau ne fitarta ta farko harabar, sai kalle kalle take daman an fiddo mishi da mota a wanke sai k'yalli take, ya buɗe ya shiga ya barta tsaye, taa rasa inda zata shiga, batasanma yanda zata buɗe ba,
Tsoki ya k'ara ja saboda yanda take ɓata mishi lokaci, daga ciki ya buɗe mata, da sauri ta tafi ta shiga, ta zauna kamar mai koyon zama, wani sak'on ya k'ara aika mata da kallo, anma duk bata gane ba, sai ta k'ara gyara zama ta rirrik'e kujerar data zauna a gaba,
"Motar ma nizan rufe miki?"
"yi hak'uri" sannan ta saka motar ta jawo motar a hankali ta rufe kamar tana tsoran karta ɓalle,
"bata rufu ba" yace da ita, ta k'ara sanya hannu ta jawota, girgiza kai yayi sai magana take sakashi, "matsanan" ta kwanta sosae jikin kujerar, yakai hannu zai rufe duk da haka saida ya taɓa jikinta, da sauri ya ɗauke hannunshi saboda wani yanayi daya ziyarceshi,
Itama wani abune ya ratsa mata har tsakiyar kanta, ba shine na farko ba, anma bata taɓajin yanayin da taji yanzu ba, kodan an kwana biyu ba Yasseer😉.
Gidan da suka fara zuwa da baba Haja nemar mata aiki taga an buɗe mishi ya shiga da motan, gani yayi sai kokawar buɗewa take, ya shareta kawai ya fita ya barta, a ranshi yace 'sai dai ki kwana a ciki ni ba ɗan buɗe miki k'ofa bane' kamar tayi kuka haka ta dinga kiciniyar buɗewa duk ta haɗa zufa ko ina a rufe, sai mai ban ruwan fulawane ya buɗe mata ta fito tana maida numfashi, ta mishi godia sannan ta shiga gidan, da yake tasan hanya.
Zaune ta iskeshi suna fira da dariya kamar ba shi ba, Husna ta kalleta tanaso ta tuna, ta nunata da hannu "kece Saude?" da sauri ta ɗaga kai,
"Allah sarki, kamar kece kukazo da baba Haja darennan ko?"
"eeh nice"
"Anma dai naji daɗin kasancewarki gaban Momie, kiyi hak'uri da wannan ranar kinji"
"ba komai fa"
"Yauwah" sannan suka gaisa, ta mik'e sukaje tana nuna mata abubuwan da zatayi, share-share ne kawai da goge-goge, tana fita taci gaba da aiki, shima tun shigarsu ya tashi yabar gidan.
Sai dare ta gama mata dukkan ayyukanta, ta haɗo mata mayuka masu kyau na gyaran jiki dana kai, da turaruka masu k'amshi ta bata, Saude ta amsa tana ta mata godia.
"haba banson godiyarnan Saude, ai mun zama ɗaya"
"Tohh Aunty Allah ya saka da Alkhairi"
"Ameen" sai kuma ta kalleta,
"Saude kenan, gaki a birni anma har yanzu k'yauye tak'i barinki"
"Ban gane ba Aunty husna"
"gani nayi har yanzu shigarki nanan ta k'yauye, baki ganin yanda en matan birni keyi? Ki canja shigarnan kinji" ɗaga mata kai tayi har lokacin bata dai fahimtan ba, driver aka saka ya kaita har gida.
A harabar gidan ta iske motan da suka fita da ita tare da Najib, an bubbuɗeta da alamar wanketa akayi, ta zagayeta ta wuce cikin gidan kai tsaye ɗakin momie ta shiga, muryarta ta jiyo da alama faɗa take,
"Yanzu saboda kaa ɗauka k'anwarka a mota ne kake wanketa Daddy?"
"nifa momie wallahi da gaske ta ɓatamun mota, ni kunyama nayita ji kar wanda ya sanni a ganni da ita cikin motah"
"Hinyehh! Ai da cemun kayi bazakaje da ita ba kawai, sai insan yanzu kaa daina jin maganata"
"kiyi hak'uri Momie"
Saida ta share hawayenta sannan tayi sallama cikin ɗakin momie duk yanayinta ya canja, tunda take bata taɓajin zafin kasancewarta er k'auye ba irin yau.
Momie ta nemo fara'a tanajin sallamar Saude "Sannunki da dawowa"
"yauwah momie Sannu da gida" ta zube mata kayan da Husna ta bata a gado,
"Gashi ta bani, tace a gaishe dake"
"Ina amsawa, an gode ma Auntynki Husna, naa gani ki adana"
"tohh" ta tashi zata tafi, Momie duk bata yarda da yanayinta ba tace "kodai wani abu ta miki naga yanayinki yaa canja?"
"A'ah Momie, Aunty tana da kirki sosae, er gajia ce kawai"
Momie ta sauke ajiyar zuciya data tabbatar Saude bataji maganar su ba, tace "Sannu kinji, kije ki kwanta da wuri"
Tace "tohm Momie"
Idanunta k'asa k'asa ta kalla inda Najib yake, yana rungume da Hafsat tayi barci a jikinshi.
Washe gari saboda gajia taa daɗe bata tashi ba, sanda ta tashi Talatu harta kusan gama ayyukanta, ta kama mata dai suka k'arasa, duk sai taji ba daɗi kuma ta zauna bata aiki, ta shiga ɗakin Momie ta mata gyaran kaya, ta k'ara gyara ɗakin.
Ɗakinta ta koma duk batason zaman hakanan, da marece kafin su fara girkin dare ta tashi ta fara zagaya gidan, hanyar ɗakin Najib tabi hakanan taji tanaso taje taga inda ɗakin yake, cikin Sanɗa ta k'arasa cikin Sa'a kuwa a buɗe yake, ta dinga lek'en falon ba k'aramin kyau yayi ba, komai a tsare sai dai kuma ko ina yayi datti, bataga alamunshi a falonba, hakan ya bata k'warin gwiwar shiga bedroom ɗin shima ta labule ta lek'a anma bataga alamunshi ba, shima duk yayi kaca-kaca kamar ba mutum ke zama a ciki ba, saida ta tabbatar bai cikin gidan sannan ta gyara shirinta ta fara aiki, gyaran ɗakin ta shigayi ko ina take kakkaɓewa tana kauda kayayyaki.
Cikin lokaci kaɗan ta gama gyaran ɗakin, ko ina yayi fes yayi kyau fiye da daa, har zanin gadon ta cire ta canja mishi wani, toilet ɗinshi ma ta wanke mar duk da baiyi wani datti ba, ta saka turaren wuta mai k'amshi ta turare ko ina. Ita kaɗai ta tsaya tana kallon ɗakin, ita ma kanta yaa burgeta sosai, yanzu momie zata daina damuwa da dattin ɗakin Najib, ta faɗa a zuciyarta.
A hanzarce ta gama ta fito, a hanyar da zata fiddata gaba ɗaya bangaren nashi ta haɗu dashi yana niyyar shiga, a ruɗe ta k'ara sauri tabar wurin, binta yayi da kallo kamar ya mata magana kuma ya fasa, ya wuce ɗakinshi.
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
56
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Tun a hanya yake jiyo tashin daddaɗan k'amshi daga ɗakinshi, bai ida yarda a ɗakinshi bane saida ya shiga, tsayawa yayi yana mamaki fitarshi har an gyara ɗakinnan yayi kyau haka, tohh waya shigar mishi ɗaki? Dubawa yayi duk wani takardunshi daya ajje inda zai ɗauka baiso su rikice mar, da kayanshi dayake ajjewa inda zai buk'ata, duk dai wani abu mai amfani bai gani ba, ranshi ya ɓaci ya juya kai tsaye ɗakin Momie ya shiga.
Tun bakin k'ofa yace "Momie kin saka aimun gyaran ɗaki ne?"
"A'ah kaida kace bakaso a shigar maka ɗaki kuma"
Saude ta faɗo mishi rai yaga tana fitowa, lallai itace ta mishi shisshiginnan, Momie tace "Lafiya meya faru?"
"Ba komi Momie" ya juya da hanzari yabar ɗakin, dubata ya shigayi har kitchen bai ganta ba, can ya hangota tana tafiya ita kaɗai, da sauri ya tardata ya kama kunnanta sosai, ya ruɗe ta juyo harta buɗa baki zata kurma ihu, ya saka hannu ya rufe bakin.
A kunne ya raɗa mata "idan kika sake kikamin ihu kunnan naki zan cire" aikam ta nutsu don ba k'aramin rik'o ya mata ba, idanunta sunyi jajir don azaba kamar tayi kuka.
A tsakiyar falon ya tsaya da ita, anma bai saketa ba cikin kakkausar murya yace "waye yace kizo kimun gyaran ɗaki?"
"ba kowa"
"Dakyau isassa, idan baki maidamun duk kayana inda suke ba sai kinyi mugun shan wahala" kai ta ɗaga mishi, itadai Addu'anta Allah yasa ya saketa, yana sakinta ta fara tafiya inda ta ajje takardunshi, kamar wacce tayi harda kowanne saida ta ajje inda ta ɗauka cikin tsari,
"Na gama" ta juya zata tafi, "Dawonan" ya tsayar da ita sannan ya tafi ya fara dubawa, ko takarda ɗaya batayi kuskuren ajjewa ba, yasha mamaki sosae, sai yama rasa mezaice mata.
"Tohh maidasu inda suke" yace ba tare daya kalleta ba, ta maida kowanne tana mishi bayanin inda yake, tana gamawa ta k'ara juyawa zata bar ɗakin duk a takure take.
"Wannan ya zama na k'arshe da zakimun shisshigi a abunda ya shafeni, zanfi jin daɗin zaman ɗakina yanda yake da, don yanzu k'yank'yaminshi ma nake da kika shiga cikinshi, Momie ta kawoki gidannan, don haka indai zuciyar mutanene a jikinki karki k'ara nunamin fuskarki" ɗaga kai kawai tayi ba tare data ce komi ba, ta tafi kawai tana hawaye, sai yanzu taga wautarta ma na shige mishin da takeyi.
Tunda ta shiga ɗakin bata fito ba, ranar monday tunda safe yabar garin ya wuce Kaduna inda yake aiki, saida ta fito Momie take faɗa mata yayanta ya tafi basuyi bankwana ba, murmushi dai kawai ta mata. Saida ya tafi ta fara samun sakewa a cikin gidan, Hafsat kullum da gwarancinta saita tambaya ina Daddy, saboda shak'uwah ce sosae tsakaninsu, yanaji da Hafsat sosai kamar shi ya haifeta.
A wurin aiki kullum Najib ba sukuni, ko yaushe cikin tunanin Saude komai yake fuskarta ce ke mishi yawo, hakanan inya tuna wani abun da tayi shi kaɗai yayita murmushi, saiya gane tunanin Saude ne fa yake yayita jin haushin kanshi, duk yanda yaso ya yakice tunaninta a ranshi ya kasa.
Abokinshi Ahmad ne ya k'wank'wansa mishi kujerar da yake, ya dawo a ɗan razane, "Yadai?" ya tambayeshi, "Dai-dai, naga alamun kwana biyunnan tunani yaa aureka"
"ba wani tunani, abubuwanne da yawa"
"Ka faɗama abokinka hakan, bawai Amininka ba daya gama sanin duk wani motsi naka"
"kuma laifi ne idan mutum yayi tunani?"
"babu laifi, anma kamar kana da damuwa kuma kak'i ka faɗamun"
"nifa babu abunda ke damuna"
"Ok daman shigowa nayi, naga an tashi ko anan zaka kwana?"
Dariya yayi, "A'ah yanzu nake shirin fitowa" ya mik'e bayan yaa gama tattara takardun gabanshi, "ban baka labarin Saude ba? Da tana wurinnan zaka ga yanda zata tattara takardunnan bazakace batayi makaranta ba"
"Saude er k'yauye?"
"ita fa"
"kai kam kana son labarinnan Saudennan"
"Haba ni mezai sakani maganarta"
"Muje ko?" suka jera a tare suka fito, kowa ya shiga motarshi suka tafi.
Da dare Ahmad yaje ɗaukoshi gida zasu fita restaurant da yake shima baida aure, ya buɗe motan ya shiga, ya jawo zai rufe kenan ya fara dariya harda rik'e ciki,
Ahmad ya fasa tada motan ya tsaya yana kallonshi, donshi kanshi wani lokacin mamakinshi yake idan yana dariya don bai saba gani ba,
"wai kai lafiyanka?" bai tankashi ba yaci gaba da dariyanshi "dakai nake fa, kai daman indai anga kana dariya mugunta ne, Allah ya taimakeka bani kake mawa ba"
"nida bak'yauyarnan mana, idan kaaga yanda tayi zata rufe mota randa zan kaita gidan sista Husna, naa tabbata saika fini dariyarnan"
"Sauden dai?" Ahmad ya faɗa da cikin fara k'osawa da zancenta da Najib ke mishi,
"ita mana" kaɗa kai kawai Ahmad yayi yaja mota suka tafi don haushi ma ko magana bai k'ara mishi ba.
Suna cin abinci anma shi dak'yarma yayi cokali Uku ya ajje, sai zancen zuci yake, yadai fito fili yace "kuma kasanme?" Ahmad ya girgiza kai, "wlhy zakasha mamaki idan kaci girkin da er k'yauyennan tayi, ko a restaurent ban taɓa cin mai daɗinshi ba"
Ahmad yace "Ita Sauden ba?"
"Kaa canka dai dai" inji Najib.
"Yanzu kana da magana ne bayan tata? Tunda labarinta ne kam yanzu za'a fara jinka kana dogon surutu"
"Kamar yaya?"
"kamar yanda kake shirin bani kunya mana, duk haɗaɗɗun babies ɗin da suka rikice ma soyayyarka, ka rasa wacce zaka so sai wata er k'yauye can Saude, kullum kana cika bakin bakaga macen da ajinka zai kai ka sota ba"
"Haba! Banson iskanci fa, er k'yauye fa kuma zawara, ta inama kake tunanin dacewarmu?"
"kai ke wannan tunanin, anma a yaren So shi babu ruwanshi da wani dacewa"
"ni don Allah daina tayarmun da zuciyah, tayaya ma zanso wannan yarinyar? Ko kaɗan bata dace dani ba wallahi"
"ka daina yaudarar kanka, don tuni zuciyarka ta faɗama soyayyar Saude"
"nida nake da zuciyar ban sani ba sai kai?"
"ka taɓa sanin alamomin So?"
"Na taɓayin Soyayya ne dazan wani san alamomin so?"
"kaji matsalan, bakasan yanda akeji idan an fara soyayya ba shiyasa ka kasa yarda da kanason Saude, uku kawai zan faɗa maka ka yarda da abunda nake faɗa" shirun da Najib yayine ya bama Ahmad damar ci gaba da magana.
"Kana yawan tunanun Saude ba?" ya ɗan tsaya yana tunani, Ahmad yace "ka cemun eeh kawai"
"tohh eeh ina jinka"
"kullum kana yawan yimun maganarta, baka da zance dai saina Saude tun sanda ka dawo, na biyu kenan"
Najib ya gyara zama, tabbas sai yanzu ya fahimci duk maganganun Ahmad hakane,
"Na Ukun fa?"
"Na fahimci Saude duk abunda tayi a baya, burgeka yake yanzu ba?" baki buɗe Najib ke kallonshi yana murmushi yama rasa bakin magana "kuma naa tabbata komai kake kanajin daman Saude na kusa dakai ko babu wani dalili"
Najib na dariya yace "tohh malamin soyayya, darasi yayi daɗi har kaa faɗi huɗu baka sani ba"
"Na biyarma zan faɗa maka yanzu, sai wani murmushin jin daɗi kake ina maka firarta, wannan ma babban alaman kana sonta ne"
Dariya yayi sosae ya bashi hannu suka tafa "Tohh aini malami na dukkaa rikitani ma"
"Hahhah bafa ajin maths muke ba, maganar soyayyah ce"
"ai wani lokacin yaren mathematics ɗinma sai yafi na So sauk'in ganewa"
"ba kamar ga sabon shiga ba"
"hakane, anma fa ni har yanzu ban yarda inason Saude ba, baka ganta bafa, ni haushin shigarta ma nake"
"kana son Saude fa, ka daina yaudarar kanka, kawai ka maida ita kalar macen da kakeso"
"Kayi magana ananma zanyi tunani akai"
"Yauwah kokai fa"
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
57
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
❣Page ɗin yau dai yayi tsawo, musamman don sadaukarwa ne ga Auntiena ```Asma'u musa barah msh``` (Husna a nvl ɗinnan😉) fatan Alkhairi a duk inda kike.
www.babymsh.blogspot.com
Tun bayan tafiyar Najib sai Saude taji gidanma yafi mata daɗi a haka, Hajia na ɗan aikata gidan Husna harsun saba sosae, hankalinta yanzu kwance har mantawa take da wani Najib, tunanin Yasseer ma kullum k'ok'arin yakiceshi take.
Ranar friday sati uku da tafiyar Najib, da aiki suka tashi gidan kamar za'ayi wani manyan bak'i, kuma taa lura Momie na cikin farin ciki fiye da kullum, sai dai bata tambayeta dalili ba don bata faɗa mata ba,
Sai bayan saukowar masallaci suka kammala, a gajiye Saude ta fito daga kitchen ɗin batama jira an gyara wurin da ita ba, tafiya kawai take bata kallon gabanta sai dai ta jiyo sallamar mutum, idanunta akan hanyar shigowarshi, harta buɗe baki zata amsa mishi sallamar ta tuna maganarshi daya faɗa mata.
"Idan har zuciyan mutanene a jikinki, karki k'ara nunamun fuskarki!!!" maganar taa shigeta sosae, kafin ya shigo ta lallaɓa ta koma can jikin bango ta laɓe bayan ta amsa sallamar can cikin mak'oshinta, tana hangenshi ya shigo ya wuce, ya k'arayi mata kyau sosae, anma kamar yaa ɗanyi rama.
Saida ta tabbatar ya shige ɗakin Momie, sannan ta fito tabar wurin, ɗakinta ta shige, bata k'ara marmarin fitowa ba.
Tun shigarshi gidan yaketa hangen inda zaiga Saude anma bai ganta ba, shiyasa ma kai tsaye ya wuce ɗakin Momie yasan zai sameta a can, anma bai ganta ba, Momie ita kaɗai ke maganar ta anma tunanin ta inda Saude zata fito yake. Dubara tazo mishi na tambayan Momie,
"Nifa tun zuwana banga Hafsat ba ko tana wurin Mamanta?"
"A'ah tana wurin lesson ne" shiru yayi donshi ba amsar da yaso ta bashi ba kenan,
"Aina ɗauka tana wurin Mamanta"
"A'ah" kawai Momie tace mishi, baiso hakanba, sai kuma yaga wannan kamar dama ne dazai fara yima Momie tuni akan hakk'in Saude.
"Momie itafa Sauden yaushene zata fara zuwa makarantar?"
"Haba Saude fa, ai ita yanzu tayi girma da zuwa makaranta, nasan bazata so ma tana shiga aji da k'annanta ba"
"A'ah Momie, shi karatu ai baida babba babu yaro, idan har tanaso ko inane zata iya, in kuma bataso sai mu k'yale andai fita hakk'inta"
"Hakane, anma tunda gaka kazo saika nema mata makarantar daya dace"
"tohm shikenan Momie, tana ina?" ya samu dai ya tambayeta.
"k'ila tana ɗakinta ko, gajiyar aiki nasan tana hutawane, tun asuba bata zauna ba" wani irin daɗine yazo mishi,
"Momie Saude ita tayi girki?"
"Kusan ita tayi fa, don yanzu Talatun ma ita ke tayata" fara'arshi saita k'aru yau zaici girkin Saude, har k'agara yayi su tafi dinning cin abinci, anma kuma shiru babu Saude, kuma yaji Momie batayi maganarta ba, sai yanda Momie zatayi maganarta yake anma bata kula ba.
Haka duk ranshi ba daɗi ya yini a ɗakin Momie, sallah kawai ke fitar dashi don karma ya fita Saude ta shigo bainan, har dai Momie da taga dare ya kusa bai fita ba tace "yau kuma bazaka fita ba?"
"A'ah Momie, yau ranarki ce babu inda zanje nan zamuyi ta fira" aikam taji daɗi sosae da maganarshi, ta ɗauka daga sallahn isha'i ma zai wuce ya kwanta, sai gashi har 10:30, yana jiran Saude tazo mata saida safe.
"Naga alaman yau anan zaka kwana, kaga ni tashi barci nake ji"
"Momie yau kuma korata ake?"
"Ya zanyi na kori Babana, barci nakeji gobe ka dawo muyi firan"
"Tohm mu kwana lafia" ya tashi ya tafi yanajin haushin barcin wurinnan na Momie yau, duk da haka a falo ya zauna yana hangen hanyar da zata fito yana kallon dole.
Saude da taga haka saita fasa fitowarma, ta koma ɗaki ta kwanta ko kaɗan bataji daɗin rashinma Momie saida safe ba, barcin k'arya ta ringayi duk sanda ta aika kiranta da rana don batason fita, saida dare ya raba tsakiya sannan ya hak'ura ya kwanta.
Washe gari da asuba taje gaisheta tana gama sallah tasan bai dawo masallaci ba, da yake yaa daɗe baiyi barci ba, sai bai farka da wuri ba sanda ya tashi harsun gama break fast, ta koma ɗaki, yinin ranar ma wasan ɓuya suka ringayi, kota fito bata bari su haɗu.
Ranar asabar kenan haka har dare basu haɗu ba, gashi lahadi yakeson komawa, kusanma haushin kanshi ya fara ji, kenan maganar Ahmad gaskiyane yana son Saude? Shiyasama duk ya damu ya ganta, miye ma a jikin Sauden da zaiso ya gani? Tunaninta ya matsa mishi har baison zama shi kaɗai, tashi yayi yabar ɗakin Momie yama fasa son ganinta.
Lokacin ita kuma Hafsat na wurinta ta matsa sai dai ita zata rakata ta kwanta, ta rik'o hannunta suka fito, tana ganinshi ta juya tun kafin ya gansu anma ta makara saida Hafsat ta mishi magana tanata so ta k'wace hannunta taje wurinshi.
Tsura mata ido yayi duk da yaji daɗin ganinta a zuciyarshi, amma saiya kauda kai, ta saki hannun Hafsat kawai, ta juya tabar wurin, yabi bayanta da kallo harta shige.
Hafsat ce ta kamo hannunshi, sannan ya maida hankalinshi kanta.
"Uncle ina sweets ɗina?"
"Sorry Hafsat kinga yau ban fita ba, gobe zamuje in siyo miki"
Ta washe baki, "gobe zaka fita dani yawo ko?"
"eeh mana"
Harda tsallenta "Yauwah gashi babu ckul"
Ya ɗaga mata gira "Hakane fa, tohh kije ki kwanta da wuri"
"tohm uncle Good night"
"bye karki manta da addu'ah" tun daga nan ta fara kware baki tanayi donma yaji bata manta ba, murmushi kawai yayi, shi yanzu harya daina mamakin surutun Hafsat, shekarunta biyu anma labari kam kamar mai sauke hadda, wayau ne da ita sosae shiyasa tun wuri aka kaita prep.
Yau bai fito ba, break fast ma sai dai yayi ma Momie waya aka kai mishi, na rana ma shiru bai fito ba, Momie ta aika aka mata kiran Saude,
"Shiru bakici abinci ba, yayanki ma bai fito ba duk yau"
"Naci a kitchen Momie"
"Bana hana ba Saude? Ɗauki na Yayanki kikai mishi"
"tohh Momie?"
Bata iya musa mata, anma da akwai yanda zatayi bazata je ba, cikin sanyin jiki ta harhaɗa mishi, ta kwasa ta tafi gabanta na faɗuwa har ta shiga.
Yana kwance abubuwa sun mishi yawa, duk zuciyarshi cunkushe take, haushin kanshi kawai yakeji, tunanin Saude, Soyayyarta, da kuma son ganinta sun rikita mar k'walwa, ya ɗauke wayanshi ya kira Ahmad.
"Masoya! Ananan da Saude an manta damu"
"wace Saude? Bazan iya ba Ahmad, gaba ɗaya na fara tsanar kaina, ita zuciyar daman haka take? Bazatayi shawara dani ba akan wacce ya kamata taso ba sai Saude"
Ahmad na mishi magana Saude ta shiga ɗakin, a falo ta aje mishi saman centre table, sai kuma taga kamar bazai san an kawo ba, ta tafi ta faɗa mishi, ta jiyoshi yana magana.
"Haba Ahmad baka ganta ba, bak'yauyah ce ta k'arshe, ko ɗaurin zane bata ita ba ballantana ɗan kwali, sai afkin wanka anma babu wayewa, ni wallahi haushinma ganinta a haka nake" dafe k'irjinta tayi tuni hawaye suka wanke mata fuska,
"bak'yauyen mutum fa Ahmad duk yanda zaka mishi yananan dai da duhun k'yauyenshi, duk inda zai shiga kuwa...." abunda ta iya saurara kenan, da gudu ta tafi zata bar ɗakin, wurin sauri k'afarta harta zame ta faɗi, ba k'aramin zafi taji ba haka ta daure da sauri tabar wurin.
K'arar faɗuwar mutum da yaji ne ya fito dashi, anma baiga kowa ba sai dai girkin da aka aje mishi, bayanta yabi anma harya fito baiga kowa ba, Momie ya gani da shirin fita ta fito,
"Sai yanzu ka fito?"
"eeh, fita zakuyi ne?"
"eeh anma bazan daɗe ba, Saude takai maka abinci ko"
Ya samu amsar tambayarshi kenan itace ta shiga ɗakinshi, "eeh Momie" rage tsawonshi yayi inda Hafsat take,
"Ba magana don za'aje anguwa?"
"A'ah akwai"
"tohh ina mamanki?"
"tana ɗakinta"
"muje ki rakani" yanda Momie bazata ji ba yayi maganar, ya kama hannunta.
"Momie muna zuwa plz"
"owk ta sameni a mota" tayi gaba su kuma suka tafi.
Hafsat taa rigashi shiga ɗakin da Saude take, da murnarta donta faɗa mata tare suke da Najib sai kuma taga tana kuka.
"Mama kuka kike?"
Ta share hawayenta tana k'ak'aro murmushi, "waya faɗa miki kuka nake?"
"nina gani da kaina Momie, kuma kin hana kukan rigima"
Kuka ne ta k'ara fashewa dashi, a k'alla ta samu damar da zata faɗi damuwarta ko zata samu sauk'in zuciyarta, duk da tasan Hafsat bazata fahimci komi ba,
"ba kukan rigima nake ba Hafsat, inayi ne don in rage bak'in cikin zuciyatah, miye don an haifeni a k'yauye? Ni bani da kyau ne? Ko kuma wani mugun abunne k'yauyenci? Mutane da yawa sun gujeni silarshi, harda babanki Hafsat, nasan shima dalilinshi kenan na barina, Uncle ɗinki Najib ma abinda ya sanyashi tsangwama ta kenan, Momie kaɗai ke sona Hafsat, kawuna ma ya tsaneni saboda maraicina, babu fa wanda na ɗaurama kaina, ko kinsan inda k'yauyencinnan yake a jikina in cireshi in huta?"
Kamar tasan me tace, ta girgiza mata kai, murmushi tayi, "Naji daɗi da baki tashi a k'yauye ba Hafsat....."
Muryar Momie suka jiyo tana k'wala ma Hafsat kira, harta tafi da gudu kuma ta dawo, hannu ta saka ta share mata hawaye, sannan ta koma ta gudu.
Murmushi tayi tabi Hafsat da kallo, kawai sai taga mutum tsaye a bakin k'ofa ya harɗe hannuwanshi biyu yana kallonta, jikinta na kyarma ta tashi tayi hanyar fita don taa rasa inda zata shige a ɗakin, ya k'ara mamammake k'ofar yanda babu wurin fita, ta kasa haɗa ido dashi a hankali tace,
"Kayi hak'uri"
"Dame fa?" ya tambayeta cikin wani irin salo.
"Na saka kaa k'ara ganina"
Ita har yanzu bata manta da wannan maganar ba kenan? Ya shareta kawai.
"menene damuwarki?" ta ɗan ware idanunta duk da bata ɗago fuskarta ba,
"ba komi" ta juya da sauri zata koma, saboda hawayen dake k'ok'arin zubo mata.
"meyasa kike kuka?"
Muryarta na rawa alaman kuka yaci k'arfinta tace "kaina kemun ciwo" ta bashi amsa duk taa matsu yabar ɗakin.
Tohh meya shigo dashi shida yace baison k'ara ganinta? Ko kuma wani wulak'ancinne zai k'ara mata.
"Sanya mayafinki kizo muje" ya katse mata tunani, ta k'asan ido take son kallonshi donta tabbatar koda ita yake magana,
"Dake nake, ki sameni a waje" ya fita kawai ya barta, sannan ta sauke ajiyar zuciyah, ta k'arema ɗakin kallo babu wata sai ita dashi, anma tana gudun ta fita ya mata faɗa ko bada ita yake ba, ko kuma tak'i zuwa tayi laifi.
Saida ya gaji da jira ya dawo don kanshi, yace taje su tafi, ta tashi ta bishi zuciyarta na mugun bugawa, harta shiga motan, tunani kawai take a ranta ina zai kaita?.
0 comments:
Post a Comment