Saudat ta gama jere ma Rabi'ah kayan ciye-ciye, Husna sai sannu take mata, sai gata ta dawo daga rakiyan Yasseer.
"Sannunku da zuwa Aunty Rabi'ah" kallonta ta ɗanyi.
"Saudat ko?" ta ɗaga mata kai tana murmushi, "Sannunki kinsha aiki, ya gajia?"
"ai ba wani aiki bane"
Taje zata kama Husna dake k'ok'arin tashi dak'yar, "Sannu Aunty"
"Yauwah Aunty Saudat"
Rabi'ah tace "waih! Sannu kinji, gaskia kina k'ok'ari"
"ai saima yazo kanki zaki sani" inji Husna.
"ni? Allah ya rufamun asiri, wahalan ɗaukan ciki, haihuwa ga raino mutum ya tsofe tunda wuri"
"Miye abun rufin Asiri? Kardai kicemun har yanzu kina da wannan Ra'ayin naki tun muna ckul, wollah garama ki canja kin sanmu dangin miji dai"
"akwai hanyar samun yara da yawa ko ban haihu ba, yanzu dai a barni in gama cin amarcina dan Allah ki dainamun maganarnan kina kadamun gaba"
"Baki ma da hankali wallahi, wannan ba tunani mai kyau bane, inma bazaki haifa mana ba zamu auro mai haifa mana"
Filon kujera ta ɗauka ta jefa mata, "bakinki ya faɗama mak'iyanki, kinsan Allah ko wata naji anyi ma kishia zuciyatah tafasa take" Husna daria kawai take mata, ta k'ara ɗaure fuska, "Allah wannan ba abun dariya bane" bata saurareta ba, dariyarta kawai taci gaba dayi, yanda takeyi dariya take bata sosae.
Da yake Saude da Najib suna waje, Rabiah da ɗan rage murya, "wai da gaske wannan ce Saudat ɗin Najib?"
"itace mana"
"daga ina ya samota?"
"ɗiyar Momie ce, daga k'auye tazo"
"lallai kice kyawawan en matah na k'auye, na birni kwalliya da wayewa zasu nuna musu kawai"
"eeh mana, Yayanmu ma a can zamu samo mishi ta biyu"
"Allah idan bazaki dainamun maganarnan ba yanzu zanbar miki gidanki"
Ta rufe baki tana dariya, "yi hak'uri matar babban yaya, na daina"
"karma ki daina ɗin"
A gidan Husna Rabi'ah ta yini har dare, sai fira suke da Saudat kamar wanda suka saba, da yake taji ita Najib zai aura kuma dai yanzu bazata nuna mata wayewa ba, har abincikan data girka ta nemi ta koya mata, taji sun mata daɗi sosae, nan ta koya mata harma da wanda bata nema ba.
Dare ya fara nisa Yasseer yazo ɗaukan Rabi'ah, bai shiga ciki ba yayi parking wajen gidan sannan ya mata waya ta fito, yana zaman jiranta a mota cikin duhun daren Saudat tazo wucewa, cikin tafiyarta ta nutsuwa a hankali take saka k'afafunta, ta amso ma Husna sak'o mak'waftansu.
Hakanan yaji yanason ganin fuskar kowacece, ya bita da kallo cikin duhun darennan har lek'enta yake gashi ta juya baya, Rabi'ah na tsaye ta fito ga mota a kulle, sai k'wank'wasawa take baimasan da ita a wurin ba, gaba ɗaya taa gama k'ulewa. Saida ta dawo ta gabanshi sannan ya lura ya buɗe mata.
A harzuk'e ta shiga ta zauna sai maida numfashi take, juyawa tayi ta fara dukan k'irjinshi, "matah kake kallo ko, bakama lura ina tsaye ba" rik'e hannuwanta yayi sai k'ok'arin k'wacewa take.
"Waya faɗa miki mata nake kallo? Nifa ginin unguwarne suka burgeni, nake tunanin ko nan zamu gina gida idan mun dawo?"
"mak'aryaci, wallahi saika faɗamun ko wacece kake kallo"
"wa kikaga ina kallo nifa banmasan da wata mace a wurin ba"
"k'arya kake" ta k'wace hannuwanta taci gaba da dukanshi, duk ta hargitsa mishi tunani cikin motar dak'yar ya iya rik'eta, gam ya haɗata da k'irjinshi yana sumbatarta, bai saketa ba saida ta nutsu sannan, saida ta k'ara kai mishi duka a k'irji tana harara sannan ta gyara zama tana maida numfashi.
Kwana ɗaya suka k'ara, suka ɗaga moscow bayan Momie ta mishi gargaɗin ya daina daɗewa bai dawo ba,
Ranar da suka tafi, da yamma a ranar Husna ta haifi jaririyarta mace, ba k'aramin murna sukai da zuwanta ba, sai Saudat hidima ta k'aru, har ranar suna itace mai hidima da bak'i ko kaɗan bata nuna gajiyawarta, yarinya taci suna Maheera, kamar Najib na jira, washe garin suna yazo ya koma da ita, aka samo mata mai kula da ita da jaririn.
Ranar Monday ta koma makaranta SS1, gaba ɗaya hankalinta ta maidashi akan karatunta, soyayyarta da zuciyarta kuma duk ta mik'asu wurin Najib.
A moscow, tun komawar Yasseer abubuwa suka dawo mishi sabo, gaba ɗaya yanzu addu'anshi daya ɗaga hannu Allah ya nuna mishi Saude, yasan yaa cutar da rayuwarta kullum cikin nadama yake, so yake su haɗu kota yafe mishi laifin daya mata, gaba ɗaya ko wurin aiki baida sukunin yin komai, a gida ma yafison ya zauna shi kaɗai yana tunanin rayuwarsu ta baya, tohh idan Saude bata k'auyensu tana ina? Kullum tambayar da yake ma kanshi kenan.
Rabi'ah ta shigo ɗakin da wata irin shiga mai jan hankali, a kusa dashi tayima kanta masauki, ta saka hannu ta shafi fuskarshi cikin shauk'i.
"Yauma tunanin kake? Banson ganinka cikin damuwa, kuma kak'i faɗamun damuwarka"
"Rabi'ah plz, inason hutu" ya faɗa idanunshi a rufe da alama damuwan ta fara fin k'arfinshi.
"Yaushene ka fara korata a ɗakinka? Nifa damuwarka kawai na tambaya, ka faɗamin ko miye saimu zauna mu tattauna"
"babu abunda ke damuna, don Allah ki k'yaleni hakanan"
"bazan tafi ba, saika...."
Wani irin tsawa ya daka mata, "kece damuwatah! Ki fita na..." yanda ta zabura ya sanyashi shiru duk baiji daɗi ba, gaba ɗaya tunanin Saude ya fara zautashi.
Hannuwanta ya kamo ya rik'e, "don Allah Rabi'ah, ina cikin damuwa ki barni in samu kaɗaicewa kona ɗan lokaci ne" duka takai mishi, sannan ta mik'e ta fice daga ɗakin, binta yayi da kallo, ita dai dukan miji bai mata wahala, daya ɓata mata rai sai duka, Allah sarki Saude da ko magana yake mata kanta na a k'asa take saurarenshi.
Su Saude suna samun hutu Momie ta fidda ranar zuwa k'auyensu, Najib kamar ya jawo ranar yakeji, gani yake kamar anma riga da an bashi Sauden.
Daren ranar suna zaune a falo kamar kullum suna fira, kallon Ball yake taa biye mishi itama tana tayashi, gaba ɗaya hankalinshi na wurin.
"wai nida ball ɗinnan waka fiso?"
Aje remote yayi ya maida hankalinshi kanta, "karki k'ara haɗamun soyayyatah da wani abu, nafi sonki fiye da yanda nakeson kaina ma"
"luv uh as much dear, in hakane meyasa ka k'yaleni"
"farin ciki nakeji Saudat, wanda ban taɓayi ba, gobe zamuje k'auyenku kawu ya bani aurenki, idan harya bani ke babu sauran abunda zai min shamaki da mallakarki"
"ka ɗauka ma ya baka fa"
Fargaba ce kawai a ran Saude daren ranar, batasan yanda kawu zai amsa maganarta da Najib ba, tasan ya tsaneta komai zai iyayi don ya k'untata mata, kuskurenta tun farko data faɗa mishi Yasseer bai saketa ba ya gudu.
Ranar batayi barcin kirki ba, cike take da fargabar yanda gobe zatazo mata. Barci bai daɗe da ɗaukarta ba aka kira Sallah, a kasalance ta tashi tayi Sallah, ta jawo Qur'an ɗinta ta fara karatu, tana gamawa dai Addu'anta kawai Allah yasa komai yazo musu da sauk'i wurin kawu.
Bata samu komawa barci ba, Momie ta aiko mata ta fito idan taa shirya don safko zasuyi, Najib ne zai kaisu ita da Momie, da wuri suka kama hanya zuwa k'auyensu Saude.
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
66
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
A baya Saude ta zauna, ta koma can gefe ta rakuɓe tanata zullumi a ranta, yana drivin yana hangenta ta mirrow, k'arar shigowan message taji a wayanta, ta duba daga Najib ne.
"Ya dai?" kallonshi tayi ta mirrow, ya ɗaga mata gira yana murmushi.
"Meka gani?" ta mayar mishi.
"Kinyi shiru kamar kina da damuwa, ko duk kunyar Momie ne?"
Sai data murmusa data gama karantawa, sai ga wani text ɗin nashi ya k'ara shigowa, "wannan fuskar nakeson gani har muje, murmushi yafi miki kyau" dariya tayi kawai ta tsura mishi ido ta mirrow shima tana kallonshi, duk Momie na lura dasu, ciki-ciki take musu dariya.
Mik'a hannu tayi ta anshe wayar tashi, "kana wannan gudun kuma bazaka maida hankali a tuk'i ba" da sauri yabi hannunta zai ansa wayan,
"plz momie ba wani abu nake ba, lokaci nake dubawa"
"kana duba na motan tohh"
Ta cikin mirrow ta mishi gwalo tana dariya, ya harareta da wasa, bata daina mishi dariyar ba.
Kwata-kwata ta manta da Momie a wurin, ta kwanto jikin kujerar da yake, suna kallon juna ta cikin mudubin kowanne ya kasa ɗauke idonshi, sak'on soyayyar da suka kasa furtawa a baki saboda Momie na wurin ne suke aika ma juna ta kallo.
Garin kallo sunje shiga wani gari, bai lura da bump ba ya faɗa mishi kawai, su duka saida suka razane banda Momie da daman tana sane dashi, ta wutsiyar ido yake kallonta, saida taga abun nasu bamai k'arewa bane, ta saka hannu ta juya mirrow ɗin, su duka har saurin kai hannu suke su gyara, saida Saude ta lura Momie ce ta koma a kunyace ta zauna.
Saida suka isa garin Katsina suka tsaya sukayi Sallah, wani restaurant sukaje sukaci suka k'oshi, sannan suka kama hanyar k'auyensu Saude.
Da yake akwai nisa daga katsinarma, saida suka k'arayin tafiya mai nisa sannan suka isa k'auyen, Najib dai bin k'auyukan wurin kawai yake da kallo, wai anan Saude tayi rayuwa, nan wurin har akwai halittar dake rayuwa.
Itama bin k'auyen kawai take da kallo, tayi kewarshi da yawa, shekara ɗaya da en watanni ko zagayoshi bata k'arayi ba, ba laifi k'auyensu an samu en canje-canje, anma bazata iya mantawa da k'auyenba, kai tsaye take nuna mishi hanyan gidan Kawu duk da k'auyen ba yawane dashi ba. Yananan inda yake, sai dai yaa k'ara lalacewa, ginin jar k'asar duk ya zaganye sai tsummuna ne aka ɗaure akayi kamar katangar dasu, suma duk sun ciccire, wurin dai babu kyaun gani, cikin zuciyarta tayi mutuk'ar tausaya musu,
Momie tace ta shiga ta fara sanar musu zuwansu,ta buɗa motan ta fita, tana k'ara k'arema wurin kallo.
Cikin gidanma duk ya lalace, k'asan tayi gamsa kuka da ciyayi ko ina, ɗaki ɗaya tal ya rage a gidan, shima rufin duk ya zazzare, tana daga bakin ƙofa sai rangaɗa sallama take babu alamun kowa a gidan, harta fara gajia, saiga Gwaggo ta fito daga bayan gida, can gefen ɗakin aka zagaye wani wuri shima da tsummokara, tana ganin Saude ta washe baki.
"A'a'aah sannu da zuwa, sannu da zuwa" duk ta rasa inda zata sakata don murna, don ko kaɗan bata ganeta ba.
Can gefe ta tillar da gwangwanin ruwan hannunta, ta shiga ɗaki ta ɗauko tabarma da tsintsiya, ta share wuri sannan ta shimfiɗa mata tabarmar ta zauna, ita dai Saude sai binta da murmushi take ganin yanda take ta zakwaɗi tasan lalle gwaggo bata gane ta ba.
"daga ina? Halan bak'in gidan mai gari ne? Sannu fa kunsha hanya"
"A'ah nan gidan nazo gwaggo"
"Gwaggo kuma? Kai gaskia badai ni ba, bansan kowa a birni ba, ki dai tuna gidan da kike nema"
"Gidan da nake nema nazo Gwaggo bilki, gidan Kawo Ado"
"eeh gaskia gidanne kikazo" gwaggo ta faɗa cikin sanyin jiki tana ja da baya, "Allah yasa dai ba wani abunne kikazo dashi ba baiwar Allah"
"ki kwantar da hankalinki Gwaggo, Alkhari kawai nazo dashi"
"tohh wacece ke?"
Kawu Ado ne ya shigo gidan har yana tuntuɓe, yake k'walama gwaggo kira, burki yaja a tsakar gidan ganinta da bak'uwar fuska. Shima dai washe bakin yayi suka gaisa da ita, sannan yaja gwaggo can gefe.
"Ina Mak'era aka faɗamun bak'i sun tsaya da k'atuwar mota k'ofar gidannan, nama ɗauka matsiyacin yaronnan ne"
"bashi bane, bak'uwa ce dai mukayi daga birni"
"gidan mai gari tazo ko gidan sarkin noma?"
"gidannan tace tana nema, anma dai bata faɗi daga inda tazo ba"
"tohh fa, Allah yasa ba sace mana kawuna tazo cikin k'atuwar motarnan ba"
Suka jiyo su duka sunason tambayarta, su duka sun k'ara tsufa, kawu Ado duk gashin jikinshi ya cika da furfura.
"baiwar Allah daga ina? Kuma wa kikazo nema?" kawu Ado ya mata tambayar.
Tana murmushi tace, "Kawu daman Saude...."
"Sauden K'aniya, idan ma nemanta kikazo kinzo gidan da bazaki dace bane, tunda tsohin mijinta ya gudu ya barta itama ta gama gabanta, tun kafin magana tayi nisa tsakaninmu kibar gidannan kije can kici gaba da dubata gidan karuwai"
Rumtse idonta tayi sosai maganar ta soketa
Gwaggo ta tari numfashinshi, "Malam anyi haka?"
Idonta a rufe, tanajin k'una a zuciyarta tace "Sauden ce kawu"
"Saude?" suka maimaita a tare, ta ɗaga musu kai, kunya saita kama kawu ya fara kame-kame.
"Saude kece kika zama haka? Kin tafi birni kin manta damu, munanan muna ta addu'ah Allah ya kawoki, yasa kina cikin k'oshin lafiya, ko bilki?"
"eeh eeh mana"
"Alhmdlh Saude ina kika shige haka? Don bamu muka haifeki ba shikenan kika manta damu, anma dai aimu muka rik'eki har girmanki"
"eeh mana, baki kyautaba Saude kinbar iyayenki cikin fargaba, ni banmasan ta inda zan fara bayyana farin cikin dana shiga da ganinki ba" kawu ya k'arasa maganar yana sharar k'walla.
"kuyi hak'uri kawu, nima kuna raina"
Nan fa suka sanyata gaba, ganin yanda ta koma lallai tayi kuɗi tana cikin jin daɗi, sunma rasa inda zasu sakata.
Saida taga sun ɗan natsa, tace "bani kaɗai nazo ba, harda hajiar da nake gidanta, da kuma ɗanta, kuma dai da maganar da sukazo da ita"
"tare kukazo kuma bazaki shigo dasu ba? Kai Saude kinanan dai da halinki na kawaici" kawu ya faɗa, harda dariya shinan ya faɗa abun kirki.
"tohm malam a shigo dasu bara a musu shinfiɗa"
Gwaggo ta kwaso wasu tabarmun ta shimfiɗa musu kafin ya shigo dasu, su Kawo har kyarmar jiki ake, da hannu bibbiyu suka tarbesu, aka shimfiɗesu saman tabarma.
Gwaggi da kanta ta saka mayafi, bashin ruwan laida mai sanyi an sakashi a randa ta anso musu, ta kawo sannan suka shiga gaisawa, en k'auyen har an fara cika gidan suna murna Saude ta dawo, ta canja ta zama er gayu. Bata k'yamacesu ba ko kaɗan, ta shiga cikinsu suna ta labari, har dare suna tare. Najib dai fita yayi ya basu wuri bayan sun gama gaisawa.
Da yake dare yayi, kuma babu wurin da zasu kwanta a gidan, sai suka koma cikin gari babu nisa da k'auyen, a can suka samu hotel zasu kwana, banda Saude, cewa tayi a gidansu zata kwana.
Gatan da bata taɓa tunanin samu ba su kawo suke nuna mata, don gaba ɗaya fita sukai daga ɗakin sukace ta kwanta ita zasu kwana a waje, tace su barta ta kwana inda ta saba anma sukak'i, duk yanda taso, anma a ɗakin dai suka bar mata ta kwana ita kaɗai.
Su Momie sun tafi a zuwan sai gobe zasu dawo ayi magana.
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
67
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Kafinsu tashi barci, an gama haɗa musu break fast, daman da Momie zasu tafi sunsha rok'onsu su dawo nan su karya kumallo, sai gashi sun dawo tunda wuri, sabuwar tabarma aka shimfiɗama Momie ta zauna sannan aka jere mata kayan break fast kala-kala.
Koko da k'osai, fura, ɗan wake, shinkafa da wake, alala, sabon tuwo, da shayi ruwan bunu (marar madara), Momie dai sai godiya take, "wannan kalaci duk mu kaɗai? Ai daa baku wahalar da kanku da yawa haka ba"
Gwaggo tace "haba Hajia, ai babu komi, so muke kici ki k'oshi,"
Ɗan waken kawai taci, don Momie akwai son ɗan wake, ta kora da ruwan koko ko kaɗan bata nuna musu k'yamata ba, zama tayi taci kamar yanda zataci a gidanta, Saude ta ɗauka na Najib ta tafi kai mishi yana cikin mota ya kasa shiga.
Ta ajje mishi, suna gama gaisawa ta tashi zata tafi, ya rik'o hannunta
"wannan kayan break fast ɗin duk ni dawa?"
"kai da cikinka mana"
"wasa kike, sai dai ni dake"
"nawa yana ciki fa yanzu zanje inyi"
"A'ah wannan ya ishemu" ta mak'ale kafaɗa, "shikenan kwashesu ki koma dasu"
"rigima ko?"
Ya kashe mata ido, "mijinki na sonki kusa dashi ne"
Jiranshi dai tayi harya gama, don a waje suka shimfiɗa tabarma, duk da ba mutane anma saita kasaci, shima Fura kawai yasha, qila itama don a gabanta ne, don gaba ɗaya tsantsamin kwanukan yake da ruwan garin, yana sha yanajin tashin zuciya dak'yar dai yasha da yawa.
Tana maida kwanukan, ta kwashi tsarabar Hanne k'awarta ta fito, tare da Najib suka jera suka tafi shima yanaso yaga k'auyen. Nan su Gwaggo suka shiga rabon tsaraba suma, don daɗi bakunansu har kusa da kunne, wai yau sune suke fantamawa haka duk sanadin Saude da suka tsana.
Suna tafiya tana mishi bayanin k'auyen, duk inda sukayi ana nuna su 'ga Saude can tazo da bak'on ɗan birni, Saude ce tazo daga birni taa waye, Saudece ta zama er gayu' kowah dai da abunda yake faɗa.
"mutanen garinku fa ke kaɗai suke kallo"
"A'ah ai kaine bak'o a wurinsu"
Dai dai gidan da suka zauna ita da Yasseer ta tsaya tana kallo, bazata taɓa mantawa da gidan ba, abubuwa da yawa a gidan da bazata iya mantawa dasu ba.
A gidanne aka fara ajjeta a matsayin amarya, a gidanne ta zama cikakkiyar mace, a gidanne ta samu farin cikin da bazata taɓa mantawa ba, a a gidanne ta samu bak'in cikin da har yanzu yakenan mak'ale a ranta, a gidan ta samu cikin Hafsat kuma anan ta haifeta, bazata taɓa mantawa da gidannan ba.
Zagayowa yayi saitin fuskarta, ya ɗan kaɗa mata yatsunshi guda biyu, firgigit ta dawo daga dogon tunanin data tafi, "sau nawa zan faɗa miki banson ganin wannan fuskar a tare dake?"
Murmushi tayi, "idan hakan ya maka mu tafi ko?"
"Yayi anma saikin faɗamun nan inane?"
Hawayen data daɗe tana maidawa ne suka fara kwararo mata, girgiza mata kai yayi, yasa hannu yana share mata hawayen, kama hannunta yayi sukabar wurin,
"ga gidan Hanne can"
"tohm ki fito inanan ina jiranki, kuma bance kiyi sauri ba don kawai kin barni anan, zan jiraki ko yaushene"
Murmushi tayi ta ansa ledar hannunshi. Hanne najin sallamarta da gudu ta fito ta tarbeta, har suna kusan faɗuwa.
"sai yanzu zakizo tun jiya ake kawomun labarin Saude tazo garinnan"
"kuma shine bakizo kin ganni ba? Wai jirama tukunna ya akai kika ganeni"
"inafa na ganeki, yanda aketa kwatantamin kene dai"
"wai kinga yanda kika koma kuwa? Lallai birni taa ansheki, wallahi Hajjaju komai naki ya canja fa" sai shafa jikin Saude take yanda yayi laushi tana ta surutu.
"kemafa kin canja k'awatah, don dai bazan mantaki bane anma dak'yar na ganeki, kin zama wata babbar mace, haba duk ina gayun naki kike nema ki tsofe da wuri?"
"Hmm Saude kenan" ta lura tana cikin matsala, kuma ita bamaison jin sirrin mata da miji bane, bazata manta taimakon da Hanne tayi mata ba, ta kawo tsarabarta ta bata, da kuɗi masu ɗan yawa tace tayi jari, godia sosai take mata har suka fito k'ofar gida.
Wurare da yawa sukaje da Najib a k'auyen, daga k'arshe suka wuce rafi.
"Gaskia yanayin garinnan naku da daɗi yake, bana gajia da shak'ar sanyayyar iskarnan"
"saimu barka anan kayita zamanka ai"
"bazan damu bafa, indai tare dake ne"
"daman ai kawu yace indai zai baka aurena tohm sai dai mu zauna anan"
"ke! A ina? Anma dai da wasa kike ko?"
Babu alamun wasa a fuskanta tace "Da gaske nake mana"
"abincin k'auyennan? In kwana cikin k'auye? Kawu ya taimakamun mana"
Dariya tayi sosae, "Matsoraci, daman nasan duk faɗi ne kawai"
"ba haka ba, nafison na ajeki inda zakiji daɗi ne"
"daɗin baki ko?" ta faɗa tana dariya, sai dai taji tayi tuntuɓe har saida ta faɗa jikin Najib, da sauri ya rik'ota, ta dafe k'irjinta dake faɗuwa sannan ta tashi a jikinshi.
Duk'awa yayi wurin k'afar tata, "Sannu, baki daiji ciwo ba ko?"
"A'ah, bara dai a ɗauke dutsin saboda kar wani ya k'ara faɗuwa"
Ta duk'a zata ɗauke, ya riga ya zauna wurin, kamar dutsin daya taɓa mata ciwo a k'afa sanda ta faɗo daga bishiya, da sauri ta ɗaga kanta sama, bishiyar mangwaronnan ce wacce ta faɗo daga samanta lokacin da zata ɗeboma su Kabiruwa.
Juyawa tayi tana kallon Najib, ta k'ura mishi ido sosae ji take kamar Yasseer ne take gani, bazata manta da haɗuwarsu ta farko ba, duk abubuwan da suka faru jikin bishiyarne suke dawo mata a ranta.
Gatanan Zaune lokacin da ake mata Kamu, tuna rik'on da Yasseer ya mata a lokacin tayi, saida duk tsikar jikinta ta tashi, gabanta ya faɗi taja wani ajiyar zuciya, maganarshi ce ta dawo mata a kunne kamar lokacin yake mata ita, lokacin data mishi godiyar taimakon daya mata.
"ni nake da godia, da kika bani dama harna taimakeki, kuma na samu lada"
Najib ne ya hure mata ido, "kamar dai yau kika fara ganina" lumshe ido tayi, kamar dai Yasseer a haɗuwarsu ta farko.
Tana murmushi mai ɗauke da damuwa ta kalla bishiyar, "wannan ne dalilin haɗuwatah da mijina na farko, ananne na ganshi, kayi hak'uri anma bazan iya tsaida tunaninshi ba duk sanda nazo wurinnan"
"Shi kike tunani, anma ni kike gani domin nine a gabanki yanzu, bazan hanaki tunawa dashi ba, don nasan idan kika sake dawowa, nida shine zakina tunawa"
Ɗaga mishi kai tayi, "Allah yaji k'anshi, yakai haske a kabarinshi"
"Ameen ta amsa tana murmushi"
Sai kusan Azahar suka koma gidan, Momie na jiransu har tayi shirin tafiya, yanayinta kawai suka gani gaba ɗaya hanjin cikinsu suka kaɗa, bama kamar Saude da gabanta ya fara faɗuwa, shikenan kawu ya gama tona mata asiri.
Najib ne ke mata magana a ruɗe, "Meke faruwa Momie? Don Allah karkicemun zan rasa Saudat" ganin yanda duk suka tada hankalinsu, Momie ta kasa rik'e dariyarta, sannan suka sauke ajiyar zuciya.
"mun gama magana, kawunka ya yarda zai baka auren Saude, da munje kawunanka zasu zo a saka rana, saura ka bani goran Albishir" kafin Momie ta rufe baki ya zaro komai na aljihunshi ya aje a gabanta, saida ya jiyo dariyarsu Kawu ne, ya fita daga gidan a kunyace, donshi baimasan suna wurin ba.
A ranar sukai bankwana suka koma, duk kuɗinta da Najib ke bata harma da wanda Momie ke bata, bata kashewa ta damk'ama Kawu yayi gyaran gida, har mota ya bisu yana godia, harda en k'wallansu shida Gwaggo.
Gaba ɗaya kuɗi sun rufe mishi ido, yama manta da wani auren Saude da Yasseer, don daman shi baida wani matsala da aurenta.
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
68
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Watansu shidda da komawa, suka fara zana s.s.c.e, daman tuni aka saka sunanta, sai karatu ya k'aru, kullum cikin karatu take fiye da lokacin data zana j.s.c.e, tun kafinta fara jarabawar Najib ya biya mata ta rubuta jamb.
Karatun da take da maida hankalinta yasa komai yazo mata cikin sauk'i, babu abunda ya shige mata duhu.
Ranar yayesu sunsha kuka, duk da bata da k'awa ɗaya anma duk ta shak'u dasu, tasha kyaututtuka ba kaɗan ba, duk da bata rik'e wani muk'ami ba, ita ta samu kyautan tsabta, kyautan biyayya, kyautan zuwa da wuri, wacce tafi kowa cin english, maths, har teacher n su mai physic da suka sanyama ido saboda mak'o saida ya mata kyauta, da aka fiddota speach yanda take zuba turanci ba k'aramin burge mutanen wurin tayi ba, en makarantarsu kamar su haɗiyeta don murna, ta samu kyautuka sosai wanda bata taɓa tunanin samu ba.
Da dare kuma Najib ya haɗa mata nashi Partyn, duk wasu Abokanshi da yakeji dasu sun halarta a wurin, tun daga na Abuja har wanda suke aiki a Kaduna, itama ta gayyaci k'awayenta sosae har wanda bata tunani sunzo.
Ba k'aramin haɗuwa Saude tayi a wurin ba, cikin doguwar rigarta fara tas mai kwalliyan duwatsu, duk inda ta saka k'afarta Najib na biyu da ita, sosai suka haske a wurin.
A hankali tace mishi, "nafa lura duk en matan wurinnan kishi suke dani"
"Saboda kinfiso kyau da iya kwalliya ba"
Tayi dariya har hak'oranta suka fito, "Saboda ni nake da saurayin da yafi kowanne dai, kaga dole suyi kishi don nawa yafi nasu"
"laah! Kin nusar dani ma shiyasa su Jabir keta binki da kallo ko, bakinsu ya kasa shiru sai yabawa suke da haɗuwarki, aikam partynnan an tashi hakanan"
"Saboda me?"
"Saboda ina matuk'ar kishinki mana, na gaji ana ganemun matah hakanan"
"haba! Abokankane fa"
"koda en gidanmu ne, bakisan yanda nakesonki da kishinki bane, komai zan iyayi idan wani ya raɓeki"
Shiru tayi don yama rufe mata bakin magana, da yake da wuri aka fara Partyn dare baiyi wani nisa ba aka tashi, abokansu da yawa sunso yima Saude da Najib hotuna a wayansu, anma yak'i yarda, sukace ai indai sun dawo bazai hana suyi mata na biki ba.
Saida aka tashi Ahmad yazo, duk Abokansu sun gama tafiya, tare suka fito da Saude tarbanshi, cikin girmamawa suka gaisa sannan tace,
"mufa da har munyi fushi"
"Haba Matar Aboki, keda nake cewa da zaki tayani ban hak'uri"
"ai kamar nama fishi fushin fa"
"tohh afuwan, wallahi abubuwa da yawa na bari na taho, don dai kawai bazan iya hak'urin nan da sati biyu biki ba sannan inga Saudat ɗinnan data sacemun abokina gaba ɗaya"
Tayi dariya sosae "shiɗinne ma na sace duka ba zuciyarshi ba kenan?"
"ai tunda kina da zuciyarshi, ke kikeda ragamar janshi duk inda kikeso, yanzu banda wani sauran damuwa, don naa tabbatar da abokina ya bada zuciyarshi a inda ta dace"
"anma kinason gulma?"
"inasonji, anma gulma fa babu kyau"
"an gama tunda kinason ji, sirri zan faɗa miki ba gulma ba. Kinga abokina da kike ganinshi, son matane dashi don haka kisan yanda zaki rabashi da kallon mata"
Ta waro ido, "Na shiga daɗi" ya k'yalk'yale da dariya, "yanzu nasan kina sonshi yanda ya kamata, anma maganar gaskia wallahi tunda muka tashi ban taɓa sanin budurwar Najib ba bayanke, bai taɓa soyayya ba, a kanki ya fara, kuma yana matuk'ar sonki, yana tsoran yaudara, don Allah ki rik'eshi amana, kada ki raunana wannan jaririyar zuciyar tashi"
"Insha Allah, kamar yanda nasan shima bazai taɓa barin soyayyatah ba"
"Kai! Wai me kake faɗa mata ne tun ɗazu ka tsayar da matar mutane?"
"abunda basai kaji ba, yau na fara ganinta ma baza'a barni mu gaisa ba"
"nak'i ɗin, komai za'ace ayi gabana"
Mik'ewa tayi, "bara in fara tafiya, barci nakeji"
"tohm masoyiya, kiyi barci mai daɗi" Ahmad ma ya mata saida Safe, anan gidan ya kwana da Najib, washe gari tunda safe ya wuce, duk da Najib yaso ya tsaya sai bayan biki.
Saura sati biyu biki, Momie taje babban wurin sayarda furnitures na Abuja, ta zaɓar mata fitinannun kayan ɗakin masu hegen kyau, gaba ɗaya kayan sun tasarma 3million, koda aka faɗa ma Momie ko ɗar bataji ba ta biya kuɗin.
Kayan kitchen ma mak'udan kuɗi ta kashe wurin haɗa mata su, jin Saude take kamar ɗiyar data haifa, gaba ɗaya taa ɗaukema su kawu duk wani hidima, komai ita takeyi.
Haɗaɗɗen lefe Najib ya haɗoma er gatan tata, faɗan irin haɗuwar kayan da kuma kashe kuɗin ɓata lokaci ne, idan kuka tuna wanda yasai mata a tana Saudenta, akwatinan kansu abun kallone, Momie kanta ta yaba da kayan, don farko jira take kawai ya kawo ta raina saiya ƙaroma Saudenta, sai gashi ma ya wuce yanda take tunani, Saude kam har kukan murna tayi, bazata taɓa mantawa da karamcin dasu Momie suka mata ba, kullum addu'arta Allah ya bata ikon fita kunyarsu, don sun nuna mata gata sosai a rayuwah.
Gyan jiki kam kullum cikin yi mata ake, fatarta tayi kyau sosai sai santsi take, har wani ɗaukan ido take. Ta k'ara kyau fiye da daa, kamar ba Saudat ba.
Sauran sati ɗaya biki su Yasseer suka sauka k'asar, motoci akayi da yawa zuwa tarbansu, banda Saude da Najib suna gida yana tayata aikin tarban babban ɗan Momie. Tana gyaran kitchen bayan ta gama, yana zaune ya kasa ɗauke kallonshi daga gareta.
"kallonnan fa ya fara yawa Masoyi" ta ɗauka plate ta kare fuskarta.
"idan ma na kalla ai MATATAH CE, nake kallo, ki barni in kalleki, hakanan yau naji inason inyi ta kallonki"
"nidai banson kallo fa"
"ni kuma inason inyi ta kallon fuskarki, bazan taɓa gajia da hakan ba" ya janye plate ɗin a hannunta, jin k'arar motocine ya sakashi fita daga kitchen ɗin, ta rakashi da murmushi.
Ɗakinta ta koma, ta sake shek'a wani wankan, ta fito ta shirya cikin wani orange ɗin atamfa, mai zanen yellow da fari, tayi kyau sosai bama kaman data zuba ɗaurin ɗan kwalinta mai kyau, ba wani Make-up tayi ba, anma tayi kyau sosai.
Ɗakin Momie ta wuce, Rabi'ah ce kawai, ta taso da fara'arta ta tarbeta, "Sai yanzu kike fitowa? Har ina shirin zuwa ɗakinki in fito dake"
"waceni in saka matar yaya aiki? Sannunku da zuwa"
"yauwah Amaryarmu, kinga yanda kika k'ara kyau kuwa? Dak'yarma na ganeki"
"ballantana ku Aunty Rabi'ah dake k'asar waje"
"nifa da gaske nake, yanzu dai sai mun zauna kafin hidimar bikinnan ta ida haye miki za'a k'ara koyamun wasu girke-girken"
"tohm Aunty"
Fira suka shigayi da Rabi'ah, da yake Momie bata ɗaki, tana shirin tambayar Rabi'ah Momie sai gashi ta shigo.
Momie tace "yanzu na aika kiranki ashe kinanan"
"sannunku da dawowa Momie"
"yauwah sannunki da hidima"
Sai ga Najib da Yasseer sun shigo a tare, suna dariyansu da alama cikin farin ciki suke, Najib yace "Saudat, yau dai ga babban Yayana Yasseer" ya juya kan Yasseer, "Broda, ga MATATAH, Saude na gaji da wannan saɓanin da kuke samu"
Yasseer yace "A'a'tohh karma sai anyi auren mu haɗu a hanya bamusan juna ba" gaba ɗaya ɗakin saida sukai dariya, kowannensu ka kalla yana cikin farin ciki.
Hakan ya sanya Saude ta jiyo cikin ladabi ta gaishe da Yasseer, wani irin shock yaji sauraren muryarta kawai tun basu haɗa ido ba, gaba ɗaya ya kasa buɗa baki ya amsa, jin yayi shiru ya sanyata ɗago kanta, su duka saida gabansu ya faɗi, da sauri ta ɗauke kanta.
Shikam kasa ɗauke idanunshi yayi a kanta, kallonta kawai yake kaman babu kowa a wurin.
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
70
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
💗Whoever forgets to wish you on your birthday I will always be there to wish you.What to do if I forget? Simple come and fight with me as usual.Happy birthday I remember this time. May be we can fight next time.😜 Having you for a sister makes my life more beautiful. I hope that you know that. Happy Birthday. Sis Hauwa'u Sk Msh (Hasma) I love uh so much😍
www.babymsh.blogspot.com
Da Yasseer yayi Sallah yaso ya koma barci abun ya gagara, wani irin azababben ciwon kai ya saukar mishi ko motsin kirki dak'yar yake da kan, gaba ɗaya ji yake kaman duniyar ne duka yake ɗauka.
Hayaniyarsu da yake jiyowa a falonne ya k'ara hargitsashi, daganan yana jiyo dariyar Najib da Saudat, a hankali yake fita zuwa falon ya ɗaura hannuwanshi duka biyun yaa dafe, yana tafiya dak'yar.
Sun baje I.V tana gani, ba k'aramun kyau sukai ba da gani an kashe kuɗi da yawa, ko meya haɗosu? Cikin wasan ta tilla mishi filon kujera, ya tare da hannuwanshi biyu bai sameshi ba yana mata gwalo ta k'ara jefa mishi wani sai saman k'afan Yasseer.
Su duka suka ɗaga ido suna kallonshi, da gani yanajin azabar ciwon kan lokaci ɗaya har ya faɗa, Najib ya mik'e a ruɗe yaje inda yake.
"lafiyanka bruhh? Meke damunka?"
Yak'e kawai ya mishi yace "ba komai" ya raɓa gefenshi zai bar musu ɗakin, Saude ta gaisheshi, hakanan ya tsinci kanshi da sakar mata fuska.
"lafiya lau Saudat ya kika tashi?"
"Alhmdlh" sai kuma ya fita yanajin haushin zuciyarshi da rigimar da take shirin kunno mishi, me yasa zuciyarshi zata mishi haka? Da gani basai an faɗa ba Saudat da Najib masoyane da suke matuk'ar son junansu, tayayama zaiyi nasara?
Yana fita Najib ya zauna jikinshi a sanyaye, damuwa ce bayyane a fuskarshi, "gaskia bruhh yana da damuwa, kuma nasan zurfin cikinshi bazai taɓa bari ya faɗamun ba, koma menene tunda kika ganshi haka yana matuk'ar damunshi da yawa, shi mutum ne da bai ajje damuwa a ranshi"
Itama sosai ta tausayama halin da Yasseer yake, "Allah sarki, Allah yasa dai ba wani matsala bane"
"Ameen"
Ɗakin Momie ya shiga, tana duba zannuwan gadon data saima Saude, da ganin yanayinshi ta maida hankalinta kanshi, zaman dirshan yayi a saman carpet ya jinginar da kanshi a bango,
Momie duk hankalinta ya tashi ta koma inda yake "Baka lafiya ne?" ya girgiza kai kuma ya ɗaga.
"meke damunka?" wasu siraran hawayene suka gangaro mishi, cikin muryan tausayi yace "nima ban sani ba Momie"
"bazai yiwu ba, dole zakasan dalilin damuwarka, sai dai in yauma bazaka faɗamun ba"
Tohh ciki waccema zai faɗa mata? Labarin Saude Matar daya aura a k'auye ya gudu ya barta da har yanzu soyayyarta da tunaninta suka hana zuciyarshi sukuni, har yanzu dana sanin abunda ya aikata yake? Ko kuma matsalar Rabi'ah ta kullum take damun k'wak'walwarshi? Bata rageshi da komai ba, duk wani soyayyar miji da mata tana nuna mishi, matsalanshi ɗaya da ita rashin son haihuwa, kuma Allah ya yishi da son yara, shima yanason yaga k'wanshi a duniya, ko kuma babban matsalan da shi kanshi kunyar kanshi yakeji, wai yanason matar da k'aninshi zai aura!
"ban sani ba Momie, anma inajin kaman duniya gaba ɗaya ta juyamun baya"
"meyasa kace haka?"
"ba komai Momie, anma ina neman Alfarma a wurinku"
"ka faɗi koma menene"
"Don Allah Momie a taimakamun a ɗaga ranar ɗaurin aurennan"
"saboda me?"
"yayi shiru ya kasa bata amsa"
"Karka damu, insha Allah kafin lokacin kaa warware, ka yawaita addu'a akan damuwarka, shi Allah maji rok'on bawansa ne, akwai wata addu'ah a cikin husnul muslim: Allaahumma 'innee 'abduka, ibnu 'abdika, ibnu 'amatika, naasiyatee biyadika, maadhin fiyya hukmuka, 'adlun fiyya qadhaa'uka, 'as'aluka bikulli ismin huwa laka, sammayta bihi nafsaka, 'aw 'anzaltahu fee kitaabika, 'aw 'allamtahu 'ahadan min khalqika, 'awista'tharta bihi fee 'ilmil-ghaybi 'indaka, 'an taj'alal-Qur'aana rabee'a qalbee, wa noora sadree, wa jalaa'a huznee, wa thahaaba hammee ."
"fassarar addu'ar shine: Ya Allah! Ni bawanka ne, kuma ɗan bawanka, kuma ɗan baiwarka. Goshina a hannunka yake, hukuncinka zartacce ne a kai na, kuma k'addararka gareni mai adalci ce. Ina rok'onka da kowane suna naka, wana ka ambaci kanka dashi, ko ka saukar dashi a cikin littafinka, ko ka sanar dashi ga wani daga cikin halittarka, koka keɓance kanka da saninsa a cikin ilmin fake da ke wurinka, da ka sanya Al-Qur'ani ya zama kaka ga zuciyata, da haske a k'irjina, da kwaranyewa ga bak'in cikina, da kuma mai tafiyar da damuwata."
"insha Allah zaka samu sauk'i a zuciyarka, bansan meke damunka ba, anma duk ɗan adam daka gani Allah yana jarrabarshi, kuma imanin mutum baya cika saiya yarda da k'addara mai kyau da marar kyau, komai kaga ya faru dakai k'addarane, idanma matsala tsakaninka da Rabi'ah ne kayi k'ok'arin gyarawa tun wuri, kada ka taɓa raunana zuciyar mace, kada kace zaka juya mata baya don matsalar dake tare da ita na rashin haihuwa"
"kodai matsalan data ɗaurawa kanta?" ya faɗa a zuciyarshi, baison ya faɗama Momie tsakaninshi da Rabi'ah ne, don bazaiso ya haɗasu ta dinga ganin bak'in taba, anma dai duk yanda zaiyi da Rabi'ah batajin lallami ko shawara,
"Na gode Momie" ya furta yana zubar da hawaye, saiga Hafsat ta shigo da gudu Najib ya biyota, baisan sanda ya mik'a hannunta tazo wurinshi ba, ta zulle ko kallanshi batayi ba ta faɗa kan Momie.
"Guje-gujenne ko Hafsa? Bana hana ba?"
Tana shesshek'ar gudu sai dariyarta take "Momie Daddy ne ya biyoni"
"shine kika rugo haka ko ɗayan Daddynki bazaki gaisar ba?"
"ni Daddy na ɗaya mai sona, ban haɗashi da kowa ba Momie"
"Wannan ma babanki ne, ki gaisheshi nace" ta kalleshi tana tura baki, hakanan yarinya da ita gaba ɗaya haushinshi takeji, sai kuma ta ganshi yana hawaye sosai ya bata tausayi.
Ta tafi inda yake, ta saka k'asan rigarta tana share mishi hawaye, ya ɗago yana kallonta, murmushi ta mishi, "Mamana taa hana kukan rigima, idan ta ganka kana kuka Momie zata faɗa mawa kuma Daddyna bazai kaika shan ice cream ba"
Murmushi yayi yarinyar sai k'ara burgeshi take, inama ace tashi ce? Lallai iyayenta ba k'aramin Sa'a sukai da samunta ba.
"na daina kuka, anma saikin yarda mun shirya bazaki k'ara guduna ba"
Ta mak'ale kafaɗa "nina daina shiri da kowa, best frnd na ɗaya"
"wanene?"
"Daddy na"
Najib ne ya shigo ɗakin yana nemanta, ganin Yasseer zaune gaban Momie harya juya zaiyi baya, Yasseer ya mik'e yabar ɗakin duk kalanshi ya canja.
Momie ta kalleshi, "yayanka ya faɗa maka damuwarshi?"
"A'ah Momie, kin sanshi dai da zurfin ciki"
"tohm Allah ya kyauta"
"Ameen"
"Ina Saudat ɗin?"
"ta wuce ɗaki tasha maganin ciwon cikinta"
"ni wannan ciwon ciki da tak'i yarda aje asibiti"
"ai tace da tasha magani yake tafiya"
"Allah ya bata lafiya"
"Ameen"
Hidimar biki kawai ake, ranar laraba za'a fara shagulgulan, don ita Saude in yanda takeso nema baza'ayi komai ba, tunda safe take jiran Najib shiru bai fito ba, tana ta mishi waya bai ɗauka ba, ta wuce ɗakinsu a falo ta tsaya tana k'wala mishi kira, taji shiru dai saita shiga ɗakin don bataga alaman Yasseer na ciki ba.
Najib ne kwance shi kaɗai, ganinshi da shirin fita ne ya tabbatar mata ba barci yake ba.
"Masoyi kaifa nake jira" ya mata shiru kawai,
"in tafiyatah bazaka kaini ba?" saima ya k'ara gyara kwanciya.
Ta ɗan saka hannu tana buga filon da yake kwance, yanaso yayi dariya ya rufe fuskarshi da filo,
"daman nasan ba barci kake ba" tayi dariyar mugunta, a ranta tace yanzu zaka tashi.
Ta ɗauko wayanta ta fara mishi video, "idan kana barcinma kafi kyau, tunda bazaka kaini ba bara in maka video, wow! Kaaga yanda kayi kyau kuwa?" duk ta kashe mishi ido da flasher ya kasa rufe idon da daɗi.
"wai da gaske videon kike?"
"ina ruwan mai barci da abunda nake?" ya diro daga saman gado.
"in gani inda gaske ne"
"nak'i fa" ta tashi ya biyota da gudu, suka fara zagaye ɗakin taa hanashi ya gani.
Suna cikin zagaye ɗakin ya samu dak'yar ya kamota ya rik'e, ɗaga wayan yayi, "kinga irin videon da zaki ɗauka nan"
Ta fara k'ok'arin zamewa, shikam hankalinshi kwance yanata mata dariya dak'yar ta k'wace, da gudu tabar ɗakin, yace, "Matsoraciya kawai"
Da yake ba kallon gabanta take ba, tana fita sai dai taji ta faɗa ma mutum, kwance saman k'irjinshi, wani iri takeji a jikinta, gaba ɗaya ma ta kasa ɗagowa, ko ban faɗa ba kunsan ko waye.
Tafe yake shima gaba ɗaya komai nashi ya canja, ko tafiya yake tunani ne kawai. Zuciyarshi, ga tarin damuwa data mishi yawa.
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
71
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
🙋🏻kuyi hak'uri dani Masoyah, naga k'orafinku, kuma naji daɗi da gyaran da kukamun, kunsan dai ɗan adam ajizine, babu wanda yafi k'arfin kuskure, gaba ɗaya na manta na saka Saude bata gane Yasseer, wasu na cewa ya kamata ta ganeshi tunda ita a ɗan birninshi ta sanshi, maganar gaskia daman Saude bata ganeshi ba, ita da tazo Abuja ma taa canja ballantana shi daya bar k'asar, ga matarshi Rabi'ah dake kula dashi😉 kuma idan baku manta ba Saude ma tana yarinya a lokacin daya tafi ya barta, Nagode sosai da tunatarwar da kukamun, wallahi naji daɗi sosae, don Allah ko a gaba kuka k'aracin karo da wani gyaran ina maraba dashi, Nagode sosai Masoyah, Allah yabar k'auna, LYSM😍
www.babymsh.blogspot.com
Gabantane ya shiga faɗuwa, har wani kyarma take k'afafunta suka kasa ɗaukanta, tana shirin faɗuwa ya tafi zai rik'ota, ta kauce kawai ta juya zata tafi.
Zata ita manta kamanninshi, zata iya manta sautin muryanshi, da duk wani abu nashi anma bazata iya manta ɗumin jikinshi ba, bazata iya manta yanayin da takeji a duk sanda jikinta da nashi suka haɗu ba.
Tana shirin tafiya ya rik'o hannunta, ta juyo suka haɗa ido, zuciyarta ce ke cewa A'ah Saudat, don yana da yanayin mijinki da kuma sunanshi ba lallai ne ya zama Yasseer ɗinki ba, kima fiddarai da sake ganinshi a rayuwanki.
Bata taɓa tsayawa ta k'are mishi kallo ba, Yayan Najib farine sosai, yafi Najib tsayi da cikar jiki, ga wani irin k'warjini da yake tare dashi, duk da ko ranshi a ɓace yake ka kalleshi kamar yana murmushi, saɓanin Najib da ko murmushin tsadane dashi, yafi Najib sakin jiki da fira da mutane. Kyakkyawane na k'arshe harta kasa gane shida Najib wanne yafi.
Ji yake kamar ya fito fili ya faɗa mata abun dake zuciyarshi, anma ya kasa koda buɗe bakinshi, idon yana kallonta ganinta yake kamar Saudenshi sai dai ya kasa yarda da zuciyarshi, mezai kawo Saude Abuja kuma gidansu? Kawai dai wata soyayyar ce Allah ya k'addaroma zuciyarshi, a hankali ya saki hannunta, kamar wacce take jira da gudu tabar ɗakin.
Fitar da basuyi ba kenan. Ranar bata samu halartar partyn da Abokan Najib suka haɗa mishi ba, don gaba ɗaya ji takeyi babu abinda zata iyayi, saima ta fake da ciwon cikinta.
Washe gari Momie tayi Mother's day, har ranar Saude bata fitowa ko k'ofan ɗakinta, wani tunanin Yasseer ne yake dawo mata sabo, ta rasa gane tsanarshi ne, haushinshi, ko kuma soyayyarsa, ga wani salon da Yayan Najib kezo mata dashi.
Kowanne ɓangarori anata hidiman biki, su gwaggo ma ana k'yauye anata shagali sai ranar ɗaurin aure zasuzo, Najib ma duk ya damu na daina ganin Saude sai dai suyi waya, anma inya tuna ta kusan zama tashi ma gaba ɗaya sai hankalinshi ya kwanta.
Ranar ɗaurin aure.
Tunda safe da sak'on Najib ta farka.
"Yau burina zai cika na samunki, na tabbatar babu sauran wani garkuwa yanzu tsakanina dake, ke tawace, ni naki ne, ina sonki Masoyiyah"
Murmushi tayi bata maida mishi ba saita kirashi, don a halin yanzu tafiso ta saurari muryarshi fiye da komai, "Masoyi an kusa zama Ango"
"nama zama dai, waɗannan awoyinma duk zasu shuɗene bayan sun sadani da farin cikina"
"Me kakeyi yanzu?"
"tafiya nake"
"Ango daman yana yawo?"
"tohh yana iya tunda kina guduna?"
"hhm" knockn k'ofanta taji anayi, ta sauka tana saka hijabi.
"ana miki knockn fa"
"Gashi zan buɗe"
Tana buɗewa sukai ido huɗu dashi, suka sakar ma juna murmushi, "Yadai?"
"Amaryatah nazo gani" ta tsaya jikin k'ofan bata bashi hanya ba sai so yake ya shiga.
"ko ba'a maraba dani in koma?"
"bak'in naka ka baro ka fito?"
"eeh mana tunda ina son ganinki"
Ya wuce ta ya zauna ɗaya daga cikin kujerun ɗakin.
Dai dai lokacin Yasseer na can ɗakinsu ya rasa meke mishi daɗi, tunanin ta yanda zai dakatar da auren kawai yake, ga wani sabuwar rigimar da Rabi'ah ta ɓullo da ita, ciki ne da ita taa rantse mishi bazata haife ba, ita bata shirya haihuwa yanzu ba, dukiyarshi ma gaba ɗaya ya mata alk'awari akan ta haife mishi ɗanshi anma tak'i jin lallashi, ga damuwan zai rasa Saudat kuma.
Meya kamata yayi? Yana kwance shi kaɗai yasan azabar da yakeji a jikinshi, yaje juyawa yaci karo da wayar Najib ɗayar daya bari, harya maida zai ajje ya hango hotanshi da Saude mak'ale a wallpaper, su duka suna dariya, wani irin daɗi yaji yana kallonta a hotan, gaba ɗaya kewanta yakeji, tunawa yayi da hotunanta da Najib ya taɓa cewa zai nuna mishi, ya shiga dubasu ba wahala sai gashi ya gansu, ya shiga yana dubawa babu wanda baiyi kyau ba, harya jawo wayanshi zai fara turawa yaci karo da wanda Najib yayi mata a tana er k'auye, wani irin zabura yayi ya tashi zaune.
Zazzafan zazzaɓine a jikinshi, anma ji yayi lokaci ɗaya kamar an yaye mishi shi, "Saude? Lallai kuwa biri yayi kama da mutum, babu tantama wannan ce Saudenshi" wata zuciyar tace 'anma mezai kawo Saude anan? Wannan sunanta Saudat kuma matar da k'aninshi zai aura! Mezai kai Saude yin aure saman aure? Anma kuma ai ance daga k'auye tazo, gani yayi kamar yana ɓatama ma kanshi lokaci, ya diro da niyyar zuwa ya tambaya Momie, don ta bashi tabbacin abinda zuciyarshi take zargi.
Cikin farin ciki yake tafiya kamar wanda akama bushara da gidan Aljannah, anan ya wuce abokan Najib en ɗaurin aure, ya wuce can cikin gida, duk taron matan da kema momie hidima da bak'in dake zuwa idonshi rufe ya shiga yana tambayar Momie, dak'yar ya ganota, ya jawo hannunta cikin zumuɗi, "Momie kizo kiji don Allah"
"Meye zanji? Kai har yau kamar k'aramun yaro, bakaga abunda nake ba?"
"plz Momie maganar nada muhimmanci ne, don Allah kizo kiji"
"Ya zanyi da bak'in dake zuwa? Kasan en ɗaurin aurema duk yanzu zasuzo, kaje ka shirya mana"
Rik'o hannunta yayi duk ya shagwaɓe kaman shine Autan "kizo kiji Momie bazaki daɗe ba"
Can ya jata ɗakin da babu kowa ciki, "ki zauna kiji don Allah Momie" ta ɗanji daɗi da taga ya fara sakewa, k'ila damuwar tashice ya tashi faɗa mata, ta zauna tana saurarenshi anma duk hankalinta ya tafi ga hidimarta data baro.
"Momie don Allah ki faɗamun ina aka samo matarnan da Najib zai aura?"
"lafiyanka kuwa? Wai menene matsalanka da aurennan?"
"zan faɗa miki Momie, wallahi zan faɗa miki ko menene damuwatah, anma ki fara faɗamun Momie" tayi shiru tana ɗan tunani,
"Don Allah Momie ki faɗamun" ganin yanda yaketa gamata da Allah ya sanyata fara bashi labarin Saude kamar yanda baba Haja ta faɗa mata, komai bata rage ba harda cewa mijinta ya rasu da kuma er da tazo da ita.
Cikin farin ciki yake tambayarta shekaran Hafsat nawa sanda sukazo? Ta faɗa mishi harma da sunanta na daa Saude, kamar ya fasa ihu don daɗi yadai daure yace "Momie ya sunan mijin nata?"
"Yasseer" ai baisan sanda ya k'ank'ame Momie ba yana murna, ya saketa ya duk'a har k'asa yayi sujjada, "Alhamdulillahi" kawai bakinshi ke furtawa, tsananin murna ma ya hanashi cewa komi sai dai yaci gaba da zagaye ɗakin.
Kallonshi kawai Momie keyi kaman wani zautacce, saida ya gama murnarshi take kallonshi baki buɗe, ya dawo kusa da k'afafun Momie ya zauna, "Momie ta tabbata dai Saude MATATAH CE, wallahi MATATAH CE dana biya sadaki aka ɗaura mana aure"
Sai yanzu ta ida tsorata da Al'amarinshi, gaba ɗaya kamar k'walwarshi ta taɓu take kallonshi, tausayinshi takeji, kodai damuwar tashi ce ta fara rikita shi?
"Matar k'aninka fa ce da za'a ɗaura musu aure yanzu ba daɗewa kake ik'irarin cewa matar kace, ba tun yanzu na gane take-taken ka ba, tun wuri ka fita idona karma ka ɗaga maganar nan wani yaji, wannan ai hanyar da zaka haddasa rigima ne tsakaninka da ɗan uwanka"
"wallahi Momie da gaske nake, Saudat MATATAH CE, nine mijinta Yasseer, na kasa faɗa muku ne don bansan yanda zaku ɗauka maganar ba, anma k'auyensu ne nayi bautan k'asa kuma a can aka bani aurenta"
"k'arya kake mijinta ya rasu, ka rabani da shirmennan naka ka bani hanya in wuce, sai dai in daman akwai wani abun a ranka"
Kamar yayi hawaye yake rok'on Momie, "Don Allah Momie karki yanke hukunci a rashin sani, wannan auren wallahi gaba ɗaya bai halarta ba, nine mijinta kuma gani a raye, ki yarda dani aurene za'a ɗaura saman aure"
Ita dai Momie ko maganganunshi bata fahimta, gaba ɗaya a tsorace take dashi, kallon marar lafiya take mishi, "Momie ki kirata ki tambayeta, zata faɗa miki gaskia da bakinta, idan harta musa na yarda ba Matatah bace"
"kana cikin hankalinka kuwa? Tun wuri ka dawo da tunaninka, Matar k'anenka ce fa, idan har taji maganar nanma ai girmanka zai faɗi a idanunta, na faɗa maka ka daina maganar nan ko?" ta wuceshi zata tafi.
Ya buɗa baki yanda zata jiyoshi, "Momie kinamun kallon mahaukaci ko" wallahi gaskiyatah nake faɗa, don Allah ki saurareni Momie, ina cikin hankalina" tsayawa tayi.
"ki aika aka kira miki ita, idanta k'aryata abunda na faɗa na yarda da duk wani hukunci da zaku yankemun"
Jikinta duk yayi sanyi da maganganunshi, ta dawo ta zauna, yananan zaune ta buga waya, sannan ya sauke ajiyar zuciyah.
Najib na ɗakin Saudat Abokan wasanshi sun sanyasu gaba suna tsokanarshi, yama kasa hak'urin akai mishi ita zaizo ya mata zaune ko shirin ɗaurin auren bazai tafi yayi ba, shine ma mai k'ok'arin maida musu, don dagashi har ita babu mai yawan magana cikinsu, kiran Momie ne ya fiddasu wurin ya tafi ya rakata. Tsayawa tayi kafin su shiga ɗakin.
"ka jirani karka biyoni kaji me Momiena zata cemun"
"kina da sirrin daya fini ne? Ai duk wani sirrinki nawa ne, don haka daga yanzu duk inda kika sanya k'afarki ina tare dake, bazan taɓa barinki ba"
"Gaskia na more miji dake matuk'ar k'aunatah, kaine sirrina Ya Najib, idanna zama matarka dukkan wani burina ya gama cika"
Maganan Momie sukaji, "Saudat ce anan?"
Da sauri ta shiga, "eeh Momie gani", "keda waye?" sai gashi shima ya shiga.
Sai lokacin suka kula da Yasseer da yayi zaman dirshan a gaban Momie, gaba ɗaya itama yanayinta ya canja, tayi niyyar korar Najib don bai kamata ayi maganar gabanshi ba, sai kuma taga ai shima ɗan uwane,
Cikin hikima don kar Saude tayi saurin gano yanayin da suke ciki tace "kince mijinki ya rasu ko?" Saude ta ɗaga kai ita mai gaskiyarnan,
Momie ta nuna Yasseer, sannan take kallon Saude cikin ido "wannan fa kin sanshi? Ki faɗamun miye tsakaninki dashi" k'walalo ido tayi tana kallon Yasseer, gaba ɗaya hankalinta ya tashi, cikin sark'ewar murya tace "Ya Yasseer, anan gidan na sanshi"
Najib yace " Meke faruwane Momie? Wacce irin magana ce wannan?"
Hannu ta ɗaga mishi alamun dakatarwa, "ki faɗamun gaskia" ta ɗaga kai tana kallon Yasseer, ita tsakaninta da Allah a farko gaskia ta faɗa, toh me Momie ke nufi?
Yasseer ne ya katse mata tunani, sai dai ta ganshi kawai a gabanta,
"ki faɗi gaskia Saude, ki faɗa musu ke MATATAH CE, nine Yasseer mijinki, nasan laifin dana miki fiye da mutuwa saiki ɗaura mun, ki faɗa musu gaskiya, ki faɗa musu mijinki ba mutuwa yayi ba"
Najib ne ya tureshi daga gabanta cikin hucin zuciyah yace "wannan wane irin abune kakeyi bruhh? Karma ka soma, Saudat MATATAH CE, kuma munan bamusan da wani maganar aurenka ba"
Momie ce ta mishi tsawa, yayi shiru anma sai huci yake.
"Saude kiyi magana don Allah, karki bari ku aikata HARAMTACCEN ZAMA, nine Yasseer naki wanda naje bautan k'asa k'auyenku aka bani aurenki, wallahi nasha wahala nemanki, don Allah ki buɗa baki ki faɗa musu gaskia, kada laifin dana miki ya kaiki aikata zunubi, ni mai laifine, ki hukuntani da duk hukuncin da zaisa kiji sauk'i a zuciyarki, anma karki aikata saɓon ubangiji, karki bari a ɗaura aurennan, don har yanzu ke MATATAH CE!"
"Ya isa haka" momie ta dakatar dashi, sannan ta kalla Saude, "ki faɗamun tsakaninki da Allah mijinki yana raye, Yasseer ɗana shine mijinki?"
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
72
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
U're de best dear, so Good to have uh in my life, I love uh My ```waliyya wally```😍
www.babymsh.blogspot.com
A daidai wannan gab'an kam Saude baza ta iya wa momie k'ariya ba kamar yanda zuciyar ta ke zuga ta, amma toh Idan tayi na'am da wannan tambayar me ze biyo baya, wani irin kallo momie zata yi Mata? kallon maci Amana ko kuma mak'aryaciya? "Amsar ki nake jira kuma kinyi shiru Saudat" Momie ta katse mata tunanin da take. Tuni hawaye sun wake mata fuska, ta watsa wa yasseer wani kallo zuciyar ta na tsananin bugawa, Sannan cikin raunannan murya ta ce "Gskia ne momie, yasseer ya Kasan ce miji na a da can baya but not any more! ta karashe maganar da d'an k'arfi tana kallon yasseer da tuni idanun sa suka dawo jaa da jin kalaman ta na k'arshe.
Kafafuwan Najib ne suka kasa d'aukan sa, wani nauyi yaji kan sa na masa kamar ze fad'i yyi saurin zama dirshan akan rug carpet din dake d'akin, ya tallafo kan sa da hannayen sa biyu a hnki bakin sa na furta "innadillahi wa'inna ilaihir rajiun". Wannan shine Kalmar da momie ma ke furta wa, hankalin ta yayi dubu ya tashi ta shiga safa da marwa acikin d'akin.
"Har Yanzu ke MATATA CE Saude! matsayin ki bazai tab'a chanja wa ba agurina, Dan Allah kiyi hakuri Kar kiyi min hukunci me tsauri haka, I know I deserve even more than this but pls kiyi min aikin gafara ko Dan albarkacin 'yar mu da muka Haifa tare".
"Wace 'ya??" ta wurga masa tambayar
"Hafsat mana, ko kina nufin hafsat ba 'ya ta bace?"
"Ae hafsat bata da wani uba daya wuce wannan" ta nuna najib dake zube agurin
"Saboda shi ta sani kuma shine ya yi Mata rik'on mahaifi kuma ya dawo da mahaifiyar ta cikakkiyyar mutum alokacin da kaii ka guje mu"
Yasser ze yi magana momie ta dagatar dashi cikin b'acin rae tace "Duk ku dakata! wannan bashi bane, meyasa kika boye mana wanan BOYAYYEN AL'AMARI Saudat?"
K'afan momie tazo ta Kama tana durkushe cikin muryan kuka tace "Dan Allah momie kiyi hkri, nayi gudun fad'a muku ne kuyi tunanin wani mugun halin gareni yasa miji na ya gudu ya barni, naji tsoron Kar kuki k'arba ta alokacin da bani da wani inda Zan je, shi ya......"
Najib ya katse ta "Sam! wannan ba hujja bace Saudat! I cnt bliv abunda kunne na suka jiyo min" ya Kai hannu ya d'ago ta daga durkushen da tayi suna fuskanta juna kowannen su da rinanne ido
"Idan zaki iya b'oye wa momie then why me! I tout ni dake ayanxu mun zama d'aya da zaki iya fad'amin duk wani Abu naki tunda I'm ur soon to be husband"
"Ya yasseer ba miji na bane ayanxu, yana da matar sa me kaunar sa haka nan nima wallahi Kai nake so ya Najib, Dan Allah karka gujeni masoyi nasan..."
"Ni wallahi duk kun rud'a ni yaran nan, Yanzu ya kuke so mu b'ullo wa wannan sabon Al'amarin, da wani ido zamu kalli mutane kuma me kuke so nayi adaidai wannan lokaci da bai fi awa guda ba a daura aure."
Cewar momie...
"A dakatar da auren nan momie, Dan wallahi Saudat MATATA CE, da aure na akanta har Yanzu"
Najib juyawa kawai yayi zai bar ɗakin, Momie na kiran shi amma ko ya saurareta, sai da Saudat ta sha gaban shi Sannan ya tsaya yana sauke ajiyan zuciya "Pls Kar ka barni masoyi! wallahi ni kai nakeso kuma Kai Zan aure"
wani zafi yasseer yaji azuciyar sa, se alokacin yake k'ara gani wautar sa da yyi abaya.
"Ta yaya Zan aure ki bayan kuma da auren dan'uwa na akan ki, yaya ma Zan yi tunanin rayuwar aure da matar da ta Kasan ce tayi tarayya da dan'uwa na a matsayin matar sa, noo I can't! yana Kai wa nan yasa Kai ya fita momie bata Hana shi ba, ta ma rasa ta inda zata fara tackling problem d'in.
Sai ma tashi tayi itama ta fita zuciyar ta Sam Babu dadi, tana tunanin yanda zata Fara warware wannan matsala data kunno Kai a kurarren lokaci.
Tana fita yasseer ya zube akan gwuiwoyin sa yana ba wa Saudat hakuri data yafe mishi akan kuskuren da tafka a baya, ko kallon shi bata yi ba ta cigaba da rera kukan ta yana taya ta. Gaba ɗaya jin haushin zamanshi gabanta take.
"Ka yi min raunin da bazai tab'a warkewa ba Yasseer, na jima ina jiran dawowar ka garemu ni da 'yar Dana haifan maka but u kept me waiting all dis years, Idan nace a baya ban son ka toh nayi wa zuciya ta k'arya amma wallahi tunda zuciyata ta amshi soyayyar Najib na shafe duk wani Abu da nake ji akan ka wannan yasa nayi pretending kamar ban gane ka ba tun ranar da idona ya sauk'a akan ka"
"Plx Kar kice haka Saude nasan kina fushi Dani ne har yanzu, I know ni ki ke so ba Najib ba Dan nine Mijin ki"
"Baka so na, kama san meye so Ya Yasseer? In har kana ma mutum soyayyan gaskia bazakaji kunyan nunashi koma a ina bane, da kana sona baza ka ji tsoron gabatar Dani ga iyayen ka ba har ka gudu ka barni kaje can ka auri wata ba"
"Wallahi ina son ki, ina kaunar ki Saudat! ya Kai hannu ze rik'e ta, tayi saurin juya wa ta bar d'akin, Kai tsaye ta bi back door ta fita ta can wani b'angare na bayan gidan inda Bbu mutane nan ta had'a Kai da gwuiwa ta kuka na sosae...
Tana fita shima ya fice zuciyar sa na tafarfasa kamar zai fito daga k'irjin shi, Kai tsaye yyi motar sa dake can wani side na parking space d'in gidan, nan ya shiga ya fice daga harabar gidan daya cika da mutane. Ko kad'an Yasseer bai San inda ya nufa ba shi dae kawae yana zuba gudu akan titi kmr ze tashi sama, titin by pass ya dauka wato can ta bayan gari zuciyar sa na tsananin yi masa ciwo, idon sa ya chanja sosae har kamar baya gani sosae, a hnkli ya rufe idon ya sake bud'ewa Bbu abunda yake tunano wa kamar yanda Sauden shi ta chanja, ta murje zuwa had'ad'd'iyar mace me suna Saudat. Tuni yayi nisa da fad'a wa duniyar tunani, wannan yasa bae ga motar da ta sako Kai ba alokacin da yayi over taking....
Momie ba k'aramin ruɗewa tayi da jin labarin accident ɗin Yasseer ba, gaba ɗaya kanta ya ɗaure batasanma me take faɗama taron mutanenta ba, kawai dai tace "an fasa ɗaurin auren, babban ɗanta yayi accident" mayafinta a hannu tabi driver zuwa Asibitin da aka kwantar dashi, tare da wasu en ɗaurin auren, gaba ɗaya gidan yaa rikice.
©Rabiatu sk msh
♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
73
0 comments:
Post a Comment