Da sauri ta shiga gidan su Uwani da Maryam na biye da ita lokacin su duk da yaransu sunyi aure,tana zuwa taga Nafeesah tayi d'aya-d'aya da kayayyakin cikin ledar su Sagiru da shehu sai shan sweet da chocolate sukeyi INdo tayi kukan kura tare da fad'awa kan kayan tana yiwa Nafeesah masifa.
"Dan uwarki wane d'an iskan ne yace idan kin higo ki bud'e min kaya na? Kodan kin rakani hine zaki dinga min hihigi cikin abubawa na, ai danni aka siyo. Bani kayana banza kawai sutofes (stupid)."
"Ke INdon nan wallahi masiffiya ce, ba mubiyu ya siyowa kayancin ba, ai na san kayan sawar naki ne amma ai daya higa shigon nan ya dawo cewa yayi idan mun dawo muhya. Ke wallahi rintoh gareki."
"Ah Kakan cewa yayi mu raba. ke waima wayake son ya dinga yiwa mutunci? Ni ko keh?"
"Oho ba'a sani ba, kuma yasin komai rabahi za'ayi dai-dai."
Sagiru daya hango wata alawa k'ark'ashin k'afar INdo yayi wuf ya d'auke tare da 6arewa yasa baki da sauri dan karta juyo yana cewa.
"Wallahi kuwa Nafi karki sake ta cuceki a raba shi ki fara d'auka."
Da sauri cikin bala'i wanda har rufe mata ido yake yi tace,
"Toh munafiki algungumi zugata, wallahi hekaja ink'i rabawar banza kawai..."
"Oho dai a raba mugani."
Ya kuma fad'a cikin tsokana tayi mai banza tare da maida kayan da jakar kayan kwalliyar ta cikin leda sannan ta kalli Nafeesah tana hararart tace.
"Ki za6a raban Allah za'ayi ko kuma raban gaskiya kike so..?!"
Nafeesah ta murgud'a baki tare da cewa.
"Rainin hankali, toh raban Allah da ma'aiki zaki yi mana babu wani rabon gaskiya 'yar latsi..!"
Suna kallonta saida ta fara ware komai daban sannan ta kwashi me yawan ta turawa Nafeesah kad'an tace.
"Gashi nan."
Nafeesar ta kwaso wata uwar ashariya ta zubeta sannan tace.
"Idan kin isa kice ba uwatace ta haifeni ba kanbala'i..."
Inna na kallonsu tun shigowar INdo k'irjinta ya fara bugawa kanta yana juyawa ganin yadda 'yar tata tadawo sabuwa, Allah yasa dai ba wani abun yayi mata ba ko yake son yimata ya fara kowa mata shiga masu kyau. Duk fad'an da suke yi ta kasa cewa dasu uffan bakinta fal addu'a da fatan Allah ya cire mata wasi-wasin da take yi akan lamarin Abubakar.
"Gaskiya kema INdo kinso kanki dayawa, taya ance kiyi rabo tsakani da Allah sai kiyi yadda kikaga dama dan mugunta..."
Cewar Maryam Aliyu tana bawa d'anta nono. Can Sagiru ma yace rabo beyi ba Nafesah karta yadda ita kuma Uwani tana bayan INdo dankar sai an gama fad'an ta hanata komai. INdo ta matse nata tsakanin cinyoyinta tare da cewa.
"Saida na tambaye ki rabon Allah ko rabon gaskiya kika ce na Allah toh ai Allah baya rabawa dai-dai sai dai yabawa wannan meyawa ya bawa wani kad'an, alal misali kinga ai Maryam ke mijinki yafi na uwani kayan gona kuma dacta Habubakar shima yafi baban mu kud'i ko ba haka ba..?!"
"Oho miki banza muguwa kuma bari ya dawo saina gaya mihi."
"Sai ki fad'a ko'a jikina wallahi."
Ta fad'a tana jan tsaki. d'aya-d'aya ta bamawa su Uwani, babu wanda beji haushinta ba sabida ko 'ya'yansu bata bawaba suka tashi suka tafi. Kallon Inna INdo tayi ganin tayi tagumi yasa tacewa.
"Inna kizo kiga kayan da ya kawo min, ya kaini aka sani a inji mezafi aka gasa min kai aka dinga hyafamin wasu abubuwa akaina Inna jibi yadda gahina ya zama.."
Tana magana tana bud'e kanta, gabaki d'ayansu suka kalleta baki bud'e cikin mamaki Inna tace.
"Nahiga uku ni Maryamu 'yarnan kanki nekuwa?"
"Hehehe kaji Inna da wani batu, toh inba nawa bane jikin kuma nawaye kema dai."
"Ta6 lallai INdo anyi klin kinga yadda aka nannad'a miki gahinki kamar na indiyawa."
Cewar sagiru yana kwakulo chocolate d'in daya mak'ale jikin jajayan hak'oransa. Banza tayi mai taci gaba da nunawa Inna kayayyakin daya siyo mata, Inna tayi godiya cikin rashin nuna kyashi ga uwa a wani bigire da wasu 'ya'yan keyi INdo ta d'akko wani flat shoe tare da janyo k'afar Inna tana cewa.
"Inna saka wannan mugani kozai yi miki."
Tana saka mata kuwa yayi cif-cif a k'afar Inna INdo tayi dariya tare da fad'in. "Inna k'afarmu d'aya Ashe, toh nabar miki wannan innata kema kidinga sakawa idan zaki unguwa ko kauyen ku."
Da sauri Inna ta zare takalmin daga k'afarta tare da rik'o hannun INdo tace. "A'a 'yarnan barshi na gode miki Allah yayi albarka amma bazan k'ar6a ba, sabida ke aka bawa tayaya zan k'ar6e miki ya gansu a jikina a'ah."
"Toh danya gani kuma Inna heme? Zece kibahi ne? Kawai ki k'ar6a nina baki ai yariga ya siya min."
Ganin ta dage yasa Inna ta k'ar6a tare dayin godiya sannan INdo ta shiga da kayanta cikin d'aki ta zuba a cikin Ghana must go d'inta. Tashi tayi tafita zuwa gidan Rukayya, duk inda tayi mutane sai sunyi mata magana, maza kuma su tsayar da iya amma sai hura anci take kanta a d'age tana 6are alawa tana sha hankalinta kwance duniya tayi mata sabunta jinta takeyi tamkar akan iska.
****
Qarfe 2:35pm ya fito daga office d'inshi, sauri yake yaje gida yayi wanka dan yana son zuwa sani a yau. Da sauri yafita yana zuwa gida wanka yayi tare da shiryawa cikin k'ananun kaya white jeans da black shirt me dogwan hannu ya d'ora facing cap dama ya riga yayi sallah yaci abinci a office dan haka ledar d'in kunan daya bawa Hawwa ta d'inkawa INdo su ya d'auka yafita sai bulala k'amshi yake tamkar anyi 6arin turaren.
Passenger seat ya ajiye kayan sannan ya tada motar ya wuce domin yau kwanansa goma sha hud'u rabansa da kauyan Sani, yayi missing d'in INdo ba kad'an ba domin babu waya a hannunta.
Yana shiga unguwar yara suka yayyame shi yayinda suke ta mik'a mai gaisuwa, yau kam suna da yawa harda matasan samari ya ciro 3k ya basu yana mamakin abinda suka maidashi tamkar wani kansilan su ko chairman d'insu. Shehu ne ya k'arasa jikin motar yace.
"Bari a k'irata tana gidan k'awarta."
Abubakar yayi murmushi tare da d'aga kai sannan shehu ya ruga da gudu gidan Sahura kokafin yaje Ashe har an gaya mata suka had'u a hanya shehu na gaya mata irin kyawun da Abubakar yayi yau ita kuma ta k'agara tagani hakan yasa ta yin gudu.
Ta glass ya hangesu ya zaro idanuwansa yana kallonta ganin tun rigar datasa ce a jikinta tayi jirwaye su manja bak'in tukunya ne gashi nan dai ya kifa kansa akan sea-tearing. Ashe babban aiki ne a gabansa na aniyar ganin INdo ta waye, toh meye amfanin wad'ancen kayan na gurinta gashi yau harda k'aro mata kala shida duk atamfofi, yasan ma aikin banza ne yanzu ya zaiyi. Kafin ya nemo amsa yaji tana mai magana a hargitse sai uban nishi takeyi ya d'ago da kansa a hankali tare da zuba mata fararan idanunshi akan nata yana lumshewa cikin wani irin salo.
Bah k'aramin kyau da had'uwa taga yayi mata ba taji k'afarta na rawa zuciyarta na harbawa muryarsa a sark'e yace mata.
"Humayrah ook at you, da alama yau ko wanka bakiyi ba a matsayinki na 'yanmata wadda ta kusa yin aure jibi tun rigar last week meye hakan..?!"
Tana wasa da belt d'in rigar daya fara zarewa tace.
"Wallahi dacta bansan zaka zoba yau danayi kwalliyar."
Tsaki yaja d'an k'arami sannan ya fito daga cikin motar ya jingina yana kallonta. Tundaga sama har k'asa take binsa da kallo yace mata.
"Dena kallo na." Toshe baki tayi tana dariya jin abinda ya fad'a ashe yana kallon yadda take mai ya kuma cewa.
"Tunda naga alamar bakya son yin wanka toh zan canza ki na koma kan Nafeesah domin tafiki wayewa. Ko kuma na dena zuwa tunda abin naki haka ne."
"Wayyo dacta dan Allah kayi hakuri wallahi ko hekaran jiya da salele yazo nayi kwalliya ka tambayi innan kaji, kaima fa dan bansan zaka zo bane."
Tayi maganar tamkar zata rarume dan duk ta rud'e jin cewar zai dena zuwa. Komawa yayi ya zauna sannan ya kalleta yace.
"Toh jeki ki wanka ki kuma saka sabuwar riga ina nan Ina jiranki."
Da sauri ta shiga gida, kafin minti biyar sai gata cikin sabuwar riga yellow da kwalliyar gloden ajiki sai hoda data shafa da lipstick ta fito duk dan kada ya tafi. Kallonta yayi tare da yin murmushi yace.
"Toh koke fa, shiga muje na siyo miki wasu abubuwan ina Nafeesah ta raka mu?!"
Cikin sauri INdo tace "Bata nan taje kai nik'a muje kawai basai ta rakamu ba."
"Toh shikenan." Ya fad'a tare da shiga motar ya bud'e mata ta shiga yaja suka tafi yana janta da hira cikin salo irinnashi. Cikin gari suka shiga yayi mata shopping abubuwa na buk'ata su brush, makilin, sabulun wanka na wanki, mayukan gashi turaruka, pad, cotton balls, panties dadai sauran su sannan suka juyo gida.
Abubakar ya gargad'eta sosai akan yin kwalliya sannan ya bata d'inkunanta INdo ta dinga zuba mai godiya kamar bakinta zai tsinke sannan suka yi sallama zata fita kawai yaga k'asanta duk ya 6aci yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa.
"Humaira kinsan al'adarki tazo?!"
Da sauri ta kalli bayanta domin wannan shine karona biyu data ta6a yi, na farko a saye yakumbo talatu tace mata kowace mace tanayi sunansa al'adah kuma inyaxo ba'a sallah ba'a ta6a kur'ani.
Tace masa "Ban saniba yasin amma ba komai yakumbo ta gayan yadda zanyi."
Hannunta ya janyo karo na farko da hakan ya ta6a faruwa, ledar hannunta ya kar6a tare da zaro pad yaciro guda d'aya yace.
"Kinsan wannan."
INdo ta girgiza kai yayi murmushi tare da zaro pant d'aya ya nuna mata yadda zata yi yace.
"Yanzu idan kinje gida saiki saka a haka kinji? Duk sanda tajik'e saiki cire kiyar kisake wata bye-bye."
Ya fad'a yana d'aga mata hannu, bud'e k'ofar tayi da ledoji a hannunta ta fita shi kuma ya janyo yare da d'ora kyalle agurin data 6ata mai ya bar unguwar.
Bayan wata biyu.
*HAJJA CE*👈
[7/4, 6:39 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
Page *16*
Zaune suke a cikin ajin wanda yawancin su duk matan aure ne da alama makarantar manya ce ta yak'i da jahilci. Gefe guda kuma INdo ce ta duk'ufa tana kallon wani littafi na alifun ba'un sai faman mamul-mamul takeyi da bakinta da alama sotake tasan su ta kuma gane su a haka wata dattijuwar malama ta shigo hannunta rik'e da littattafai idanta sanye da glass fari ta samu guri ta zauna. Bayan ta kammala biya musu littafin ahkdari ta zauna tana kuma yi musu bayani har tazo tana yi musu sharhin isra'i da mu'iraji tana basu labarin ire-iren matan da annabi (s.a.w) ya gani a cikin wuta tace.
"Manzon Allah sallallawa'alaihiwa sallam yana cewa aure sunnah tane duk wanda baya son aure baya tare dani, baya da alkairi mutum ya zauna yayi ta kace nace da mutum musamman idan bata fuskar addini ba. Lokacin da ma'aikin Allah (s.a.w) ya dawo daga isra'i Nana Fateema da megidanta sayyadina Aliyu suka je gurinshi suka tarar dashi yana kuka suka tambaye shi menene yasanya shi wannan kukan, sai ma'aiki yace, yaga mata dayawa daga cikin al'umarsa anayi musu nau'i-nau'in azabobi kala-kala.
Yace yaga wata mata an d'aureta d'auri irinna azaba da gashin kanta, _itace mace baliga wadda take barin gashin kanta a waje dan wasu sugani_ ya kuma ganin wata an zaro harshenta an nannad'eta dashi, yace _itace wadda take d'aga murya idan tanayiwa mijinta magana duk yadda taga dama, duk abinda zai mata ta kushe, ta dinga ganin be'iya yi mata komai_ wata kuma an tsananta d'aurin nononta, _itace wadda bata kula da shimfid'ar mijinta, bata bashi hakk'insa, ko tayi ta garashi dan taga yana buk'ata, sannan tana bin wasu mazan a waje_ wata kuma aka maida fuskarta ta alade jikinta na jaki. _itace wacce ta kassance munafuka, annamimiya me d'aukar magana takaiwa wannan taje can ta kunsa wata maganar_, ita ake yiwa wannan azabar.."
Akwai nau'ika kala-kala daya sanar dasu wanda ya gani, anan gurin kowacce tasan abinda takeyi na rashin dai-dai dan haka sai kowacce taje ta gyara wanda takeyi kafin tilon ganyenta ya bushe ya fad'o ma'ana kafin ta koma ga wanda yayita. Akwai masu iyaye a raye babanki neko Mamanki kiyi musu biyayya akan abinda besa6awa shari'ar musulinci ba domin sa6a musu babban laifine a wajan Allah dama cikin rayuwar mutum gabaki d'aya, Allah yayi mana kyakyawan k'arshe.."
Duka ajin suka amsa da amin sannan malamar ta fita, kasan cewar ajin duk matan aure ne mutum uku ne 'yan mata yasa INdo bata irin wannan haukan gashi basa kulasu ita kuma karatun ba wani shigarta yake yi ba saidai tana matuk'ar san tarihi domin jinta takeyi tamkar agabanta akeyi wasu abubuwan.
K'arfe shabiyu da rabi aka tashesu gaba d'aya makarantar hijjab suke sawa kuma kala d'aya shine ya zama kamar uniform d'insu. Yau kwanakinta talatin da biyar da kawota makaranta babu abinda za'ace sai hamdala domin ta fara iya yin sallah sai dai sam kwakwalwarta bata d'aukar hadda, a gurin za'a biya tanaji amma kuma ya zauna a cikin kwakwalwar ne wahala.
Tana fitowa itada k'awayen da tayi sababbi Zainab da Hadiza suna maganar littafin k'awa'idi sai ga me mashin d'inta wanda Abubakar ya samar mata yazo d'aukarta, shine yake kawota ya kuma dawo ya d'auketa duk sati Abubakar yake bashi kud'insa sukayi sallama ta hau suka tafi.
Zama tayi a cikin d'aki suna hira da Inna ita kuma tafito da littattafan tana kallonsu taja tsaki tare da fad'in.
"Wallahi Inna karatun nan badai wahala ba, ni wallahi duk makarantar ta iheni dacta Habubakar ya takura min."
Ta k'arasa maganar tana turo baki tare da yatsina fuska, Inna tayi dariya tace.
"Haba 'yar nan ki dubafa kigani zuwanki makarantar nan yanzu sallah bata wuce ki, sannan kina zaune a gida kina k'ok'arin yin alifun ba'un d'inki aini kam naji dad'i wallahi."
"Ta6 lallai Inna, nifa ma wallahi inajin film zan higa dan wallahi dana fara Inna zaki ganni da narkekiyar mota wadda tafima ta dacta."
Tafad'a cikin nuna son yin abinda tace, Inna tace, "Ahir d'inki da wannan sana'ar, yanzu keko cewa akayi kihiga ai bakyaje ba sabida ma tsarinku ba d'aya bane su sunfiki kud'i da karatu."
"Toh Inna bakiga 'yar autah ba me sa bakin janbaki, yanzu kina nufin kice min itama tafini kud'i ko iya film d'in...?!"
"Oh ni maryama nace bana son kiyi amma kuna dagewa."
"Toh kiyi hakuri Inna dan yau anyi mana magana akan yiwa iyaye abinda basa so,malam Hansa'u tace me sa6awa iyaye idan ya mutu Allah ze k'onashi na denayi miki na fasa higa film d'in."
Daga nan suka cigaba da hira duk ranar asabar, lahadi da litinin INdo na makaranta kuma alhamdulillahi duk sanda taje ta dawo akwai abinda zata d'an tuna musamman idan anayi musu k'arin haske akan littattafan. Shi kuma Abubakar idan yazo zai kuma sanar da ita abinda shima ya sani da haka INdo ta fara gane fari da bak'i sannan gashi Abubakar yana iya k'okarinsa wajan ganin yayi mata abubuwan zamani wayace kawai yak'i siya mata sabida yasan ba k'aramin d'auke mata hankali zatayi ba shi kuma yana son yaga ta samu wani abun a Cikin addininta.
*Bayan shekara d'aya DA rabi*
Waya ce kare ajikin kunnansa yana ta faman cike-ciken files sai faman murmushi yake yi sannan yace.
"M twinnie na riga na gaya maka bazan samu damar zuwa gidan su wata Fateema ba gobe sabida akwai inda zani, nifa Fateema ma ta rainani wallahi ko ta d'auka kaine babba dan cewa tayi min wai wasan k'anin miji ta farayi dani."
Sadeeq yayi dariya tare da cewa. "My sweet heart kenan ai tayi min dai-dai kasan wayayyen mutum gashi dama ta shiga college abin ya kuma k'aruwar mata Ina son Zarah M twinnie."
Abubakar ya ta6e baki tare da cewa "Yh I see. Yanzu dai sai goben idan ka dawo ma had'u nima idan naje wajan babyna zan baka ku gaisa da ita."
"Okey no problem Allah ya kaimu."
Daga haka sukayi sallama kowa ya ajiye wayar yana kewar d'an uwansa, har tsawon shekarar nan Sadeeq besan Abubakar yana tare da INdo ba domin duk iya hutun da zaiyi a gida baya ta6a gigin nuna mishi dan ko wayarshi gallery d'insa password d'in a jiki bazaka ta6a tunanin ma cewa yana ajiye hoton mace a cikin wayarsa ko laptop ko wani gurin ba sabida iya taku da d'auke kai irin nasa.
Washe gari Sadeeq ya dawo ranar raba dare sukayi suna hira. Da gari ya waye su Mama da sauran yaran gidan anata shirye-shiryan zuwan budurwar Yaya Habu domin a ranar yake son kawo INdo gidan su ganta itama taga 'yan gidansu.
Sam Sadeeq besan lokacin da Abubakar ya fita ba, sai shiga d'akin yayi ya tarar k'amshin turarensa, wanka yayi ya kwanta tare da janyo waya ya k'ara Fateema lokacin sun fito daga lecture around 2:45pm.
Abubakar kuwa yana shiga kauyan Sani yayi parking a k'ofar gidan su INdo,malam Hamza ya fito suka gaisa sannan yace.
"Ai uwar tawa tace idan kazo kajirasu su dawo taje gidan kwalliya, nace yanzu ita kwalliyar ce bazata yi ba sai anje har cikin garin sumaila. Wai ai waccan tafi kyau nace toh Allah ya kyauta."
Murmushi Abubakar yayi yana shafa k'eya tare da rissinawa yace.
"Ai babu komai baba zanjira."
Fita malam Hamza yayi yana ta shiwa Abubakar albarka yana jin aransa zai iya bashi duk abinda yake so indai yana dashi burinsa ma a yanzu kawai yaji Abubakar d'in yace yana son INdo amma yayi likimo ko ita 6eta6a furtawa kalmar ba sai 'yan gidan su daya dama da zancen Aisha budurwarsa. A 6angaran INdo kuwa tunda ta fara gane kyautatawar Abubakar da karamcinsa a gareta da irin yadda yake nuna kulawarsa gareta yasa ta mallaka masa zuciyarta gabaki d'aya, ta sallami salele jira kawai takeyi taji Abubakar yace yana sonta amma hakan ya gagara, gashi zuciyarta ta riga ta mutu akan sa dan ji takeyi tamkar ta fad'a mishi sai dai yanzu tana da kunya dan a makaranta ana gaya musu cewar kunya adon macene duk macen da batada kunyar gayawa namiji abu toh k'imarta zubewa take yi kuma bazai sota ba hakan yasa ko abu take so yanzu bata iya gaya mai saidai ta hak'ura.
Abubakar na zaune cikin mota ya ziro k'afarsa waje yana danna waya kamar ance ya kalli gabansa yaga su INdo da Nafeesah suna tahowa cike da nutsuwa tamkar basu ba.
"Masha Allah."
Yafurta a hankali yana yana me binsu da ido. Har k'asa suka tsuguna suna gaida ya kasa amsawa INdo sai kallonta da yakeyi. Sanye take cikin les Orange da ratsin green ajiki ta yafa mayafi green tamkar ranar da ake sanyata a alalle, wuyanta yasha sark'a tasa d'ankunne yatsanta da zo6e sai k'amshin turare sukeyi yace cikin fara'a.
"Aishatul humairah da my sweet sis Nafeesatu kunyi kyau."
Nafeesat tace, "Kai Yaya Abubakar ai kafimu nidai bari na shiga na sake takalmi."
Tayi maganar tana mik'ewa daga tsugunnan INdo tayi saurin riko hannunta tare da mik'ewa suka shige gida ya bita da kallon mamaki ganin yanzu kunyar da take nuna Mai tayi yawa ya kad'a kai yanajin wani mugun dad’in yanayi yana ratsa shi.
Suna shiga ba dad'ewa suka fito domin sunsan su yake zaman jira, Inna tayi musu fatan alkhairi da addu'ar Allah ya dawo dasu lafia. Yana jingine jikin mota suka fito a hankali ya juya yana kallon INdo suka yi four eye's ta sakar mishi murmushi da fararan hak'oranta daya kaita asibiti aka gyara mata su le6anta yashi red janbaki ta bud'e gidan gaba ta zauna tare da kawar dakai tana kallon k'ofar gidan su.
Shima shiga yayi yana cewa Nafeesah, "Zamu tafi mubarki fa." Tayi saurin fisge hannunta daga rik'on da shehu yayi mata yana bata sallahun abinda zata siyo mai idan sun shiga cikin kano.
A hankali ya dinga tafiya har suka fita daga sumaila sannan ya fara gudu dan ayau zai dawo dasu, suna ta hira wanda yawanci akan makaranta ne data ke zuwa lesson sai dai abin ayi addu'a kawai amma INdo kam bata fahimtar turancin da akeyi sai 'yan k'ananun words wad'anda basu da wahalar rik'ewa.
A k'ofar gate d'in gidan su ya tsaya, ba wani gidane had'add'e ba sannan kuma ba wai gajari bane dai-dai magidanci me rufin asiri da kuma kwanciyar hankali. Suna tsayawa k'irjin INdo ya fara bugawa taji kamar bazata iya shiga ba Nafeesah ta fito INdo ta kalleshi kamar zata yi kuka ya sakar mata murmushi tare da cewa.
"Ya aka yi naganki haka?"
"Yaya Abbakar jinake inajin tsoro."
"Oh toh ai bama cinye mutane kifito mu shiga."
Dakyar INdo ta iya fitowa 'yan layin sai kallansu sukeyi suka shiga parking spaces sunzo wani d'an corridor ya janyo hannunta tayi saurin kallansa ya kai fuskarsa saitin tata kamar zai yi kissing d'inta yace.
"Idan kina yin haka su Halima zasu rainaki, ki saki jikinki."
Yafad'a tare da sakin hannunta, Nafeesah kuwa har takusa shiga ciki sannan ta tsaya suka k'arasa sannan Abubakar yayi gaba sukuma suna bin bayansa. INdo kuwa abinda yayi mata ba k'aramin sake tsuma jikinta yayi ba hakan kuma yasa ta fara mai wata fassara domin a makaranta ana gargad'in suka akan ta6a namijin da ba aure kukayi ba.
Da gudu k'annansa suka fito suna musu oyo-yo suka rungume INdo suna cewa.
"Yaya Habu itace ko?!"
Ya dinga d'aga musu kai yana murmushi yadda INdo da Nafeesah bazasu gani ba. A k'atan falon gidan aka sauke su an baje musu kayan abinci dana sha kala-kala INdo kuwa kamar ta nutse cikin carpet d'in da aka malale falon dashi.
Su Mama da Umma suka fito su INdo suka gaidasu har k'asa sannan suka huta k'annan su Abubakar sukayi ta janta da hira suna jefo mata turanci haushinsu ya fara cika ta domin baganewa takeyi ba su kuma a tunaninsu kunya ce take hanata yin magana basu san duk taci ubansu a surutu ba. Sun jima kafin su sauka zasu ci abinci domin tunda Abubakar ya shigar dasu ya koma d'akinsu ya tarar Sadeeq sai shak'ar bacci yake yi da alama ma ko sallan la'asar beyi ba Abubkhr yace.
"M twinnie ka kashi kazo mu shiga ciki gashi na kawo maka wadda zan aura kugani."
Da sauri Sadeeq ya mik'e cike da mamaki yace.
"Are you serious?!"
"Yap tana ma ciki gurin su Mama."
Sadeeq yace "wai kana nufin kace min zuwa kayi ka d'akko ta, kuma babu wani labari?!"
Abubakar yace "Ya daman Ina sonayi surprising d'inka."
"Ya nagani toh bari naje nayi sallah sai na shiga, nasan ko wacece wannan toh ta had'u and degree nawa gareta M twinnie?!"
"Idan zaka shiga ka gani toh idan kuma labari kake so toh kaci gaba da baccinka."
"A'a zanso ganin matarka mana M twinnie."
Ya fad'a yana shiga toilet dan shi a tunaninsa Abubakar ya manta dawani batun INdo. Saida ya watso ruwa yayi sallah yana idarwa Abubakar na shigowa Sadeeq d'in ya zura kaya sannan suka nufi cikin gidan, tun daga kan takalma Sadeeq yasan budurwar d'an uwan nasa ta had'u suka shiga tare dayin sallama Sadeeq ya zauna kan kujera ita kuma INdo ta d'an jiya ta kallesa suka had'a ido sam Sadeeq be ganeta har ta kaidashi sannan Abubakar ya kallesa cikin sign ya cewa Sadeeq.
"Ya tayi...?!"
Sadeeq ya jijiga kai yana kallon gefen fuskar INdo yayiwa d'an uwan nasa alamar 👌 yana kashe mai ido d'aya. Dariya Abubakar yayi ganin be ganeta ba yace.
"Aisha ce fa student d'inka ta sumaila kauyan Sani Tsefawa secondary school, idan baka gane ba toh INdo malam Hamza ce..."
Sadeeq dake zaune sai gashi a tsaye yana mata kallan mamaki. Sai yanzu ya gane domin ga fashin gushinta nan sannan ya fara tuna kamanninta cikin kwakwallawarsa zuwa idanunsa cikin tsananin mamaki yace.....
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
*Duk da cewar kinfi k'arfin page amma duk da haka zan bak'ishi ba a matsayin komai ba sai dan kawai naga nayi hakan, I am proud of you My Xoxo (miss Xoxo) Allah ya baki abinda kike so Duniya da lahira.*❤😍
Page *17*
"Wallahi kuwa itace, INdo malam dama zaki iya zama haka? Ikon Allah da...."
Cikiin sauri Abubakar yayi magana ranshi a bace ganin yana neman kwance mata zani a kasuwa yace,
"M twinnie ya isah haka ko ka manta matsayinta a gurina ne ah..? Kake neman cin zarafina."
Sadeeq ya k'arasa wajan Abubakar tare da dafa kafad'arsa ta hagu yace.
"Oh sorry M twinnie ba nufina kenan ba abinne ya d'aure min kai."
Jin-jina kai Abubakar yayi yana kallon yanayin INdo yaga ta cukume ta kasa boye fushinta sai faman cizon le6anta takeyi na k'asa tana murd'e k'asan mayafin jikinta ya kalleta yace.
"Humaira zo muje kiga wani abu."
Kamar jira takeyi yace taje ta mik'e suka fita lokacin Sadeeq na tsaye a parking space tsananin mamaki sun addabi zuciyarsa sai gasu, INdo na hangoshi ta k'arasa gurin Abubakar ya bi bayanta. Tsayawa tayi tana kallon Sadeeq cikin salon raini tace.
"Oh malam Sadeeq kayi mamaki ko? Toh aishi dama Allah ba yadda bayayi da bawansa nasan baka ta6a kawowa ranka cewar zaka ganni a makamancin haka ba sai gashi ta silar d'an uwanka."
"Hakane Aisha nayi mamaki kuma har yanzu ina kanyi, shin wace school kike yanzu.?”
Ya tambayeta ta yatsina fuska tare da gyara mayafi tana gyara zaman d'ankwalinta tana son cewa, ba zamu iya magana anan ba da turanci dan ta bashi mamaki amma ta kasa tana dai d'anjin alamu-alamun zata iya amma batason ko gwadawa ne dan karyayi mata wani kallon (We can not talk here) tayi mata wahala kawai ta maze tace.
"I dant talk." (I don't tell you)
Suka kalli juna Sadeeq da Abubakar fuskar Abbakar a had'e ganin haka yasa Sadeeq girgiza kai yana kallonta yace.
"Oh good Allah ya bada sa'a, Ina su Innar ku da malam..?!"
INdo tace "K'alau suke duk suna gaihe ku."
Tayi maganar tana matsawa kusa da Abubakar,murmushi ya sakar mata itama ta mayar mai sannan tace.
"Kazo ka maida mu gida Yaya Abbakar dare nayi."
INdo akwai dad'in murya saidai ta kasa dena sh da hi musamman idan tana magana cikin fushi.
"Toh kuje ku shirya sai mun fara zuwa gidan su budurwar Sadeeq daga can sai mu wuce."
Abubakar ya fad'a yana kallon fuskarta, wucewa tayi ta koma ciki shi kuma Abubakar ya gayawa su Mama cewar zaije ya maidasu. Nan fa kowa na gidan ya fara k'ok'arin fito da abinda zai yiwa INdo kyauta dashi baga k'annan ba baga su Mama ba, haka suka cika INdo da Nafeesah da tsaraba kala-kala.
Fita suka yi duk 'yan gidan suka rako su mota anayi musu fatan sauka lafiya. Sadeeq ne yake tuk'in yayin da Abubakar ke kusa dashi suka su INdo suna baya har suka k'arasa gidan su Fateema, waya yayi mata dama dawowarta kenan daga gidan suna ta raka Ummanta, fitowa tayi lokacin anata k'iran magrib INdo ta kalli Fateema itama Fateeman ta kalli INdo kowa ya fara sak'e-sak'en abubawa a cikin ransa.
"My Zarah ga girlfriend d'in M twinnie nan kusan juna bari muyi sallah tukunna."
Cewar Sadeeq Fateema ta kamo hannun INdo tana cewa,
"Okey My D sai kun dawo, shi yasa naga mutumin ankasa an tsare ashe-ashe."
Tayi maganar tana kallon Abubakar ya galla mata harara tare da cewa.
"Whatever dai please take care of her, if not.. Hmmm."
Dariya Fateema tayi INdo kuma ta bita da kallo, oh itakam taji abinda yace tunda gashi tana dariya ita kuwa please d'in kawai taji amma raguwar duk bata ganeba shi kuma Sadeeq ya zauna saman motar kafin yace.
"Ki kawo mana ruwan alwala karmu rasa jam'i."
Jan hannun INdo tayi suka shiga Nafeesa na biye dasu, a falo suka zauna Fateema na zuba ruwa a buta tanayiwa Umma bayani kasan cewar itama alwala take a gurin. Bayan takai musu ta dawo suka gaisa da INdo ta kawo musu juice da cin-cin a cikin wanda tayiwa Sadeeq d'inta domin ba k'aramin so itama Fateema takewa Sadeeq ba kowa yasani tana mugun sonshi.
Kad'an suka ci wai na 'yan birni karsuci da yawa duk da cewar yayi shegen dad'i amma haka suka hakura, suna Idarwa Sadeeq yayi mata waya cewar su fita zasu tafi.
A bakin mota suka tarar dasu banda ban-bancin kayan jikinsu da babu wadda zata gane waye nata, suka k'arasa Fateema ta kalli Abubakar marainin wayon nata tace.
"Toh gata na dawo da ita, kaga har 'yar k'ibama saida tayi a gode min."
Murmushi yayi tare da zagawa drive seat ya zauna yana cewa.
"Tayaya zan yadda bayan ni a yadda na baki haka na kuma kar6a, anyway thanks amma kad'an."
Tayi dariya su INdo suka shiga mota bayan sunyi Sallama da Fateeman, a bakin titi suka sauke Sadeeq ya kalli INdo itama tad'ago ta kallesa tana faman had'e rai dan karma yayi mata turanci sai taji yace.
"Aisha sai yaushe?!"
Ta sauke numfashi tare da cewa, "Sai wata rana kuma."
"Okey please send m regards to your parent."
Mtwwww taja tsaki mai k'arfi cikin kufala tace.
"Idan bazakai Hausa ba kayi gaba ai bada yaren annabi kayi min magana ba."
"Lallai Aisha ni kike gayawa maganar nan?"
Sai tayi mai da fulatanci itama shi kuma yayi shiru dan shima baji yake ba ta kallesa tace.
"Ko bakaji abinda nima nace ba? Toh duk sanda zaka ganni kayi min wani turanci nima henayi maka wanda na iya ai kowa Allah ya tsaga ya bahi."
Juyawa Sadeeq yayi yana taran napep yana mamakin INdo, wato yanzu ta koyi rainin hankali gashi yagano cewar tanada d'auke kai akan abinda beshafe taba amma idan ka shiga nata zata yimaka rashin kunya duk girmanka.
"Humairah dawo gaba."
Abubakar ya fad'a ba tare daya juyo ba, fitowa tayi ta koma kamar yadda ya umarce ta. Kallonta yayi ita kuma tana gyara rigarta yaja motar suka tafi. Tun suna hira dashi da Nafeesah hartayi bacci, sai da yayi nisa sosai sannan ya gyara murya yace.
"Humairah meyasa kikewa Sadeeq rashin kunya..?!"
Banza tayi Mai sai kunkuni takeyi ya kuma yin tambayar tayi mai banza sannan yace.
"Baki ga d'an uwana bane? Kuma bakiga ta dalilinsa nasanki ba meyasa kikai mai haka."
Tunda suka saba da juna bata ta6a jin haushinsa ba sai yau, Allah kuma ya k'imsa mata yin magana cikin taushi dan da wani ne k'ila su kwashi 'yar kallo tace.
"Duk babu wanda yafiku sanin wacece INdo daga iyayena heku, meyasa hida yasan bajin turanci nakeyi ba amma heya dinga yi min, wannan ai izgilanci ne. Kuma malamar mu a islamiya tace mana, komai na Duniya jarabawa ce haka tace mana lafiya da Allah ya baka jarabawaci rashin Lafiya ma haka,idan Kud'i Allah ya baka hima jarabawa ce hakama talauci, Ilimi idan Allah ya baka jarabawa ne idan bebaka ba hima jarabawa ce, aure jarabawa ne rashinsa ma haka, amma himeyasa yake min haka kuma yasan ban iya ba? himeyasa baka yi mihi magana ba heni...?!"
Shiru Abubakar yayi yana tuk'i, lallai wannan kad'ai yaci ace angodewa Allah tunda har INdo tasan shi. Murya a sanyaye yace mata.
"Haka ne kiyi hakuri."
Cigaba da tafiya sukayi har saida suka shiga garin Sumaila yayi parking akan kwanar dazata kaisu kauyen Sani ya kalleta ta kalleshi bayan ya kunna kwan cikin motar yace cikin wata irin murya.
"Humairah kina sonah..?zaki iya aure na...?!"
INdo tayi saurin rufe fuskarta da gyale tanajin wani farin ciki da annashiwa suna yawo aduk wani sashe na jikinta. Murmushi yayi shima yana jin tamkar an d'auke mai wani gungumeman abu aacikin k'irjinsa ya kuma tambayar ta INdo ta d'aga mai kai alamar Eh sannan ya furta kalmar Alhamdulillah.
"Thank you Humairah Ina sonki so me tsanani, Zan kula dake iya gwargwadon iyawata, zan kare duk wani hakkinki daya rataya a wuyana zan baki kulawa a cikin rayuwar auran mu sannan zanyi iyayina wajan ganin kin cigaba da samun Ilimi ta kowacce hanya indai alkairinki na thanks again I love you."
Tunda ta rufe Ido bata bud'e ba harya gama magana, ganin haka ne yasa shi rik'o hannunta ta fara k'ok'orin kwacewa murya a sark'e yace.
"Idan kina son na sakar miki hannu sai kin bud'e fuskarki."
Kad'a mai kai tayi sannan kuma tak'i bud'ewa, ganin dare nayi mai ne yasashi sakar mata hannun yana murmushi tare dajan motar suka shiga cikin kauyan har k'ofar gidan su lokacin malam Hamza na zaune zaman jiransu.
Da sauri Abubakar ya fito yaje gurin Malam Hamza yana bashi hakuri, shidai malam Hamzah tunda yaga yaransa sai yaji hankalinsa ya kwanta yace ai ba komai. Sim-sim INdo ta shige gida Abubakar ya tambayi malam Hamza inda zaije ya nemi auranta Malam Hamza yace.
"Ai malam Habu tunda ka tambayeni ai kagama tambayar duk wani wanda zai baka uwata, yanzu kawai kaje duk sanda ka kintsa saika kazo ayi."
Godiya Abubakar ya dingayi tamkar cewa akayi an bashi kijerar president. Kayayyakin su ya ciro musu su Sagiru suka kwashe suka shiga dasu cikin gidan shi kuma yaja mota ya tafi yana mai jin farin ciki da nishad'i.
Washe gari yayiwa abban su magana k'annan abban sukaje har kauyen Sani aka tambayowa Abubakar auran INdo malam Hamza ya tara abokansa suka shaida an bashi, a take a gurin k'anin abban su Abubakar ya bada kud'in nagani ina so dubu Hamsin sannan suka tafi suna mamakin gidan da Abubakar yazo neman aure sai dai sunsan ba yadda Allah baya tsara abinsa dan haka babu wanda yaja da al'amarin.
Labari ya zaga gari an kawo kud'in INdo dubu Hamsin masu bak'in ciki nayi masu murna nayi dama haka lamarin mutane yake. A cikin satin ya siyo mata waya sabuwa tecno sabida anyi mai transfer zuwa abuja sabida haka zasu kuma yin nisa.
INdo ta cigaba da zuwa makaranta duk da tana saka wasa a cikin lamari sai dai fa ta k'ara yin clean domin idan kaganta sai ka d'auka tana a matakin degree program ne nan kuwa ko secondary school bata kammala ba. Ta kuma rik'e alk'awari bata kula kowa duk kud'inka duk kyawunka duk ajinka duk meye d'inka bazata kulaka ba tace bazata yi *MUSAYAR ZUCIYA* da kowa ba Abubakar shine a cikin zuciyarta shi kuma take da burin aura...
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
*Gaskiya ban san me zan cewa masoya maso bibiyar labarin nan ba sai dai nace muku love you all.*
_Shafin naku ne My Shuwa Arab, Dota Fatima, Dota Marok'i, My Shama, My Olo, aunty Jidder_😍💋
Page *18*
*Bayan wasu shekaru.*
Gaba d'aya an kammala yin komai ansa rana da Fateemah ta kammala school za'ayi dan haka ginin su kawai suke yi. Gidane me kyawun gaske kowanne yake ginawa kowa kuma da yadda yake son abunsa. Gidan Abubakar yafi tsaruwa nesa ba kusa ba yafi na Sadeeq sosai kasan cewar shi yana son ya samu wani acan inda yake business dinsa idan sunje da matarsa babu wani fargaba dama yanada gidanshi dan haka biyu ya raba sa6anin Abubakar dashi a abujan ma yana da k'atan gida a quarters d'in asibitin da yake aiki.
*****
Fateema na shekarar k'arshe domin sauran 'yan watanni ta kammala, yayin da a 6angaran INdo itama sai hamdala domin zata iya rubuta wasu kalmomin harma ta rubuta wasik'a da Hausa koda ajimi kuma iya yawancin surorin alkur'ani me girma an samu cigaba sosai.
Kyawunta ya fito ta waye ta goge kai in baka cika ishasshe bama bata kulaka bare harkuyi hudd'a tare. Zaune malam Hamza da Inna suka suna tattaunawa akan yadda zasu yi da kayan d'akin INdo gashi INdo tace harda gararta zata tafi batason abin gori.
"Toh malam ya zamu yi, iya abinda Allah ya bamu shi zamu yi mata ai suma sunsan damu dasu ba d'aya bane sun fimu ta ko'ina."
"Hakane Maryamu yanzu dai dole naje na siyar da gonata dake can saye guda d'aya, sannan na siyar da shanuna guda biyu sai ayi mata amfani da kud'in nasan dai bazamu yi mata irin yadda take so ba saidai ai munyi k'ok'ari kuma mani wallahi dandai Dacta Habu zata aura hiyasa zanyi mata duk abinda nasan Zan iya sabida yaron nan d'an k'irki ne, duk sanda na kalli katangar nan naganta da suminti sai naji dad'i."
"Hakane kam malam toh sai a siyar d'in Allah ya bada lada."
Malam Hamza yace "Amin."
Kwana hudu dayin zance ya d'auki abokinsa malam kallah suka tafi Saye bayan rabansa da zuwa kusan shekaru goma sha biyar kenan. Sun gaisa da kowa saidai tsakaninsa da yakumbo tsahare babu ko kallon banza, bayan an gayawa sarkin shanu aka yi cinikin shanun malam Hamza wanda shine ya baiwa yakumbo talatu su yace idan sun haihu ya barmata saidai duk lokacin da yake da bukata toh zai dawo ya karbi guda biyu. Dubu talatin-talatin aka siye su nan aka bawa malam Hamza kud'insa dubu sittin, aka koma kan gona wani mutum ya siya dubu cas'sa'in malam Hamza ya kar6o kudin suka dawo gida da dubu d'ari da Hamsin cas.
Had'awa akayi da kud'in nagani inaso d'inta aka had'a suka zama d'ari biyu cif malam Hamza yace aje ayi cinikin gado madubi da wardrobe, nan aka nuna musu kud'ad'an ko wanne babu ma na k'asa da dubu d'ari a cikin irin wanda INdo ta nuna tana so.
Na dubu d'ari da hamsin suka za6ar mata wata yayar Inna ce da take aure a dawakin tofa sukaje suka tayo. Sai kud'in gudun mawar da aka dinga kawo musu dan su kauye basai ranar biki suke bada gudunmawa ba. Haka dame d'ari d'aribiyu dubu biyu gashinan dai aka dinga vawa inna da malam Hamza suka had'e ya basu dubu hamsin da biyar da naira ashirin. Suka had'e da ragowar hamsin dinnan aka had'a d'ari na kujeru gaskiya INdo taci Kud'i wai...!
Sai kuma masu kawo kayan amfani na kitchen me kofi , me tasa, me plate, gashi nan dai suma aka had'a Inna tasa aka siyar da gonarta itama sai aka sissiya abubuwan da babu a kitchen d'in.
****
Gidan su Fateema kuwa ko shirin basu farayi ba sabida su ba wani case karatunta kawai takeyi hankali kwance.
'Bangaren mazan kuwa, kayan lefe ake had'awa komai iri d'aya Mama tace azuba colors ne kawai suke ban-bantawa da kuma size domin INdo tafi Fateemah jiki ita kuma Fateemah tafi INdo haske da tsawo.
Akwatuna bakwai-bakwai akayi musu kowacce shak'are da kaya domin mazajen ba k'aramin k'ok'ari suka yi ba sun kashe Kud'i over.
Ranar da su Fateema sukayi graduation a ranar aka kai kaya murna biyu ta had'ar mata.
'Bangaran INdo ma ankai kayan tana gidan Rukayya kwance tana waya da Abubakar, cikin salon mak'e muryar data koyo wajan su Zainab da Hadiza tace mai.
"My key wai me kakeyi ne yanzu?!"
"Ina office a zaune tare da frame d'inki inata kallonki."
"Yeeee naji dad'i nima ka tambaye ni.."
"Habibty mekike yi yanzu..?"
Ya fad'a kamar yana cikin maye, dariya INdo tayi me sauti sannan tace.
"Ni tunaninka nakeyi dan Allah yauhe zaka dawo.?!"
Dariya yayi tare da cewa, "Sai ending d'in month d'innan, ya mekika tanadar min?!"
Tace "kana nufin ending k'arhen Month watan nan ko?!
"Eh haka nake nufi madam."
"Toh kenan kana nufin ankusa biki."
Yace "Eh amma ai Sadeeq yana nan ba kuma zai koma ba sai an gama biki kokina buk'atar wani abun nasa ya aiko miki dashi?!"
INdo ta kuma gyara kwanciya domin yarinyar ta iya kar6ar sakwan love tace.
"Eh akwai abinda nakeso."
"Toh madam menene shi..?!"
Tace cikin jan numfashi "Kai nake son gani."
Abubakar saida tsigar jikinsa ya tashi yarrrr ya d'ora k'afarsa kan table tare da jin gina da jikin kujerar dayake kai, hannu yasa a k'irjinsa yana d'an bubbugawa tsawon wani lokaci sannan yace mata.
"Sorry Habibty da ace da yadda zanyi danayi na taho, saidai na riga na k'ar6i aikin wani abokina inason idan na taho ya kar6i nawa sabida idan munyi aure bazan dawo da wuri ba sai na gama shan amarci na."
INdo ta guntse baki jin abinda ya fad'a sannan taji yace.
"Ko kina son da an d'aura aure na dawo."
Da sauri tace "A'a bana son ka koma."
"Toh ki tanadar min kanki a duk ranar da aka kawoki gidana."
Kit..yaji ta yanke wayar ya sauke yana kallon screen d'in yana murmushi bata san wannan zantuttukan baya manta ranar daya fara gaya mata irin maganganun tace mai ita ba 'yar iska bace. Ranar yaci dariya kamar cikin sa zaiyi ciwo, bebi kiran ba yaci gaba da aikinsa yana ta murmushi INdo na bashi laugh yasan idan sukayi aure zai dinga shan dariya.
INdo kuwa bata koma gida ba sai da tayi magariba sannan ta koma gida, wayyo Allah dataga irin akwatinan zamanin da Abubakar ya kawo mata bata san lokacin data fad'a jikin Inna ta rushe da kuka ba. Inna sai faman lallashi takeyi Sagiru da shehu suna kallon kayan kowa sai nuna abinda yake sukeyi da kyar tayi shiru aka cigaba da kallon kaya Inna ta nuna mata dubu hamsin tace,
"Gashi 'yarnan sunce kud'in d'inki ne."
K'ar6a INdo tayi tana godiya, tana gama kallon kayan suka rufe ta fita waje. Unguwar su kezy taje ta samesu zaune sai zuk'ar sugari sukeyi ta toshe hanci tana musu magana.
"Kai kezy aji tsoran Allah dai za'a mutu."
Tayi maganar tana sake toshe hanci, jazuli yace.
"Kefa 'yar rainin hankalice dan kinzama babbar yarinya shine zaki dinga yi mana kallon equal.."
"Kai masifaffe ni gurinku nazo, kunsan ankawo kayan aurena, toh sonake kuzo gida kuyi gadi Allah ma yace tashi intemake ka, idan ma kune 6arayin nidai kuzo gobe he'in baku dubu goma."
"Kai hajiya INdo kin zama hajjaju fa Allah."
Kezy ya fad'a tace "Eh koma dai meye nidai kuyi min."
"Karki damu zamuci uwar hegen dazaiyi gigin zuwa."
"Toh nagode."
Tafad'a ta wuce ta shiga gidan su Sahura, ta dad'e kafin ta koma gida. Haka akayi suka yi gadin gidan Allah kuma ya temakesu babu wanda yaje. Washe gari ta basu 10k suka tafi, ta ciro atamfa d'aya ta bawa Nafeesa tayi ta murna sannan ta ciro tirmi biyar ta bawa Inna tace tasa da biki. Inna tace a'a itama INdo ta dage tace tabar mata. Cikin shaddojinta kuma ta za6o wata ash tace abawa babanta, gaskiya INdo batada kyashi wajan bawa iyaye abunta amma fur taki bawa Sagiru yayi mitar yayi magiyar tace bazata bayar ba yana da kud'i. Aikuwa yaji haushi duk abinda tasashi bayayi mata shima.
***
Kowanne 6angare shiri akeyi ta kowanne side, 6angaran Fateema anje an fara jere haka itama INdo an fara, saidai tsarin gidan yasa bazasu iya cewa sai sun saka mata komai ba domin basu da halin yin hakan. Iya d'akinta kawai suka sawa kaya sai parlon farko dining area kuwa kokalansa basuyi ba gashi gida yayi masifar yin kyau domin yafi na Sadeeq had'uwa.
Ana sauran sati d'aya biki Abubakar ya dawo kano, gidan su harya fara cika da bak'in nesa sai tsiya suke mai da masu nuna cewar ya auro 'yar talakawa ga gida har gida amma babu kaya. Sharesu yayi yana yin wanka Sadeeq yazo suka fita. Gidan Sadeeq suka fara zuwa sai sambarka domin kayane nagani na fad'a aka zubawa Fateema, royal ne furniture d'in sannan babu inda va'a k'awata ba sannan suka wuce gidan Abubakar babu abinda yaji aransa na 6acin rai suna shiga cikin bedroom d'in INdo ya fad'a kan gado katifar ta lotsa da alama sakance kuma ba vita form bace ya ware hannuwa yana cewa Sadeeq.
"M twinnie remain 6days na kwana anan nida Humairah tah."
Sadeeq yayi murmushi tare da girgiza kai gaba d'aya INdo ta rikita mai d'an uwa, shi har yau ya kasa manta INdon da ta baya can domin duk sanda zai tuno ta a k'azamarta yake haskilota har tausayin Abubakar yake idan yaka yana wani abun dominta.
Cikin kwanaki uku Abubakar yasa aka sake zuba mai wasu k'awatattun furniture's a inda ba'a zuba ba aka sanya labulaye da site na dining area ba tare daya sanar da kowa ba sai Sadeeq domin cikin dare akaje akasa komai harda plasma TV. Koda dangin INdo suka dawo gidan ba k'aramin mamaki suka yiba.
Ana gobe kamu/yini da d'aurin aure....
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
Page *19*
Suna cikin d'akin su kowanne yana k'ok'arin k'arasa had'a ragowar kayanshi a cikin trolley domin da daddre idan zasu tafi gidajen su kowa ya tafi da abinsa, Abubakar sai murmushi yake yi Sadeeq na kallonsa amma be tambayesa ba domin yasan dole ya gaya mai tunda abin da alama na farin cikin sune.
Jin yayi shiru yasa Sadeeq yin gyaran murya Abubakar ya sake yin dariya ya ganosa shima sarai hakan yasa shi k'in gaya masa saya wanashi tukunna, Sadeeq ya sake d'aukar towel yana yarfewa amma still Abubakar yayi shiru ganin haka yasa Sadeeq yin magana da cewa.
"Kai twinnie kasani a gaba sai faman smiling face kakeyi, kagaya min muyi tare kak'i."
"Oh sorry ai bansan kana son jiba, kawai tunani nakeyi naga tunda aka haifemu har muka girma bamu ta6a raba d'aki ba indai muna cikin garin nan, amma sai gashi m twinnie kana cikin garin kano Ina ciki amma mata sunsa zamu rabu muje mu kwana kusa dasu."
Shima Sadeeq murmushin yayi yana k'ok'arin zuge zip d'in trolley d'in, shi kansa haskilo hakan yake yana hangosa da Zarahn shi abar kaunarsa. Duk jinsu sukeyi tamkar wasu sababbi a cikin duniyar suna jin wani nishad'i Abubakar yana hango yadda zasu kwashe a daran yau shida INdo ya kuma yin wani murmushin har yana fitar da sauti Sadeeq ya kuma kallonsa tare da mik'ewa yana cewa.
"Amma dai ba abinda ka gaya min kad'ai kesaka wannan farin cikin ba dan abin naka yayi over..?!"
"Ina tunanin yadda zamuyi rayuwa ne da Humairah, ina ganin kamar bazan iya barinta anan ba kafin a gama gyara min gidan danake acan, twinnie advice me please."
Mamaki Sadeeq yake ganin wai INdo Abubakar yake yiwa wannan sambatun tun kafinma suyi rayuwar aure ya kuma fahimtarta. Jan trolley d'insa yayi yakaita saitin k'ofa sannan ya dawo yana k'ok'arin cire singlet d'in jiginsa zai shiga wanka dan sai anfara d'aura nasa auran sannan zasu wuce ayi nashi yace.
"Toh mezai hana idan kagama 2weeeks d'innaka kutafi tare sai ta zauna a gidan haka tana ciki ana gyarawa ai tasaba da rayuwa a irin wannan yanayi bazata damu ba."
Wani banzan kallo Abubakar yayi mai kamar yasan hakan zata faru yak'i kallonsa saima saurin shigewa toilet dayayi yana murmushi ciki-ciki. Kwafa Abubakar yayi tare da zuge tashi trolley d'in sannan ya kira INdo a waya ringing biyu ta d'auka yaji muryarta a dashe tana gaidashi yayi dariya yana cewa.
"Kai babyna tun yanzu.?!"
Tayi dariya murya a dashe tace "Tun jiya da yamma."
Yace "Nikam banajinki amma tunda naji kad'an bari na kyaleki inyi wanka kafin gobe kizo kiyi min.."
Kit.. Yaji ta kashe wayar dama yasan za'arina yayi dariya tare da ajiye wayar ya gama kimtsa komai nashi shima Sadeeq yana fitowa ya shiga kafin ya fito har abokansu sunfara zuwa. K'arfe 11:00am suka fito cikin shiga iri d'aya hatta aikin babbar rigar da agogonan su takalminsu da huluna duk iri d'aya ne sai faman k'amshi suke zubawa lokacin gidan yacika da mutane, waje suka koma inda maza suke suna gaggaisawa kafin a d'unguma a tafi gidan su Fateema bakunan su kaf yak'i rufuwa kai daka gansu kasan suna cikin farin ciki.
Shad'aya da rabi dai-dai dubban mutane suka shaida auran Sadeeq Salman Harun da Fateema Idris yahaya. Sadeeq murna kamar zuciyarsa zata fito sai gaisawa suke da mutane wanda yawance basu gane waye angon yanzun sabida kowa akayiwa murna saiya amsa. Bayan sun shiga gidan su Amaryar sun gaisa da iyaye amarya ta fito cikin makeup tayi masifar yin kyau cikin farin les riga dazani tazo ita kanta kasa gane waye nata tayi saida aka ce za'ayi musu su biyu sannan aka musu su uku itace a tsakiya, ana gamawa suka fita.
Bayan an koma gida mutane sunci abinci sukuma suka kumayin wanka suka sa wasu fararan kayan wanda suma babbar rigace kalar surfanine ba irin wanda suka cire ba nan ma sunyi masifar yin kyau Abubakar yayi ma INdo text message cewar gashi nan zasu taho.
Motoci ne reras sunfi ashirin aka tafi Sumaila kauyen Sani unguwa kuwa unguwar su INdo akayi parking motocin, ana gayawa su INdo jikinta ya fara rawa hankalinta ya tashi tsoro ya fara shigarta suna zaune a gidan Rukayya ta kule cikin uwar d'akinta tayi shiru domin su Uwani su Rukayya duk suna bata labarin aure Abubakar nata kiran wayarta tana gani tak'i d'auka shi kuma befasa kiranta ba. Sai da su baffajo na saye suka shigo zauran gidan sukace a fito musu da ita sannan ta fita jikinta ya kuma yin sanyi. Hannayenta suka kama sanye take cikin shadda maroon color sai hijjab datasa fuskarta tashi kwalliya kaida kagani kasan amarya ce su Baffajo suka wuce da ita wajan masu d'aurin auran Abubakar na zaune aka zaunar da ita a kusa dashi ga uban maza waliyin amarya ya tambaye ta.
"Aisha kina son Abubakar wanda za'a d'aura muku aure yanzu..?!"
Kan INdo a k'asa jikinta sai uban rawa yakeyi Abubakar hankalinsa yayi mugun tashi ganin tayi shiru, ana k'ok'arin sake tambayarta ta d'aga Kai alamar Eh sai a sannan ya sauke wata uwar ajiyar Zuciya yana dafe k'irji shima wakilinsa ya tambayesa.
"Abubakar kana son INdo zaka aureta da yardarka ba takurama akayi ba ko..?!"
Yace "Eh uncle." Sannan akayi kabbara aka fara addu'ar d'aurin aure a gurin aka damk'awa INdo kud'in sadakinta naira dubu tamanin lakadan kowa ya shaida sannan su Baffajo suka shiga da ita cikin gida, fuskarta kunshe da murmushi ganin yadda Abubakar d'inta ya tsure taji ta k'ara sonsa cikin zuciyarta.
Shigowa ango yayi da abokansa cikin gidan aka fara hotuna wasu sun tsaya sun shiga cikin matan yayin da wasu abokan da girman kai yayi musu kwaliya suka ja baya cewar mutanen basuyi musu ba wata ma mata tukin tuwo sukeyi suka saki dan ayi hutonan dasu, hatta Sadeeq buya ya dingayi a bayan Abubakar.
Shikuwa babu ruwansa duk Matar data matso zai matsa suyi tare za'ayi musu shida INdo yayi k'ok'arin cafko hannunta ta cikin babbar rigarsa, da sauri ta kallesa cikin sa'a akayi musu hotuna sai hakan ya bada style zata yi magana yayi saurin sakin mata yana dariya Sadeeq yazo akayi musu su uku sannan suka tafi sam an hanashi amaryar su ke6e har suka kammala komai aka bar motocin da zasu tafi da amarya sukuma su Sadeeq suka wuce.
Duk zaman dasu Abubakar sukayi a garin an hanasu ganin amarya sunyi magiyar sunyi duk iya yinsu amma mutanan bikin nan suka hana. Sai bayan la'asar an shirya amarya za'a tafi sannan Abubakar suka tafi yabar abokansa da zasu d'akko su duk da yasha wulak'anci wai yaja zasu d'akko 'yan kauye a motarsu.
INdo na lullu6e su Inna nayi mata fad'a idanta har’wayau hawayen sunk'i zuwa sai Innace keyi dan tama kasa tsayawa sosai tayi mata fad'a sai faman cewa takeyi. "Tabi mijinta tayi zaman aure." Sune kawai kalaman Inna, haka ma malam Hamza shima abinda yace mata kenan sai kuma nuni dayayi mata da yadda Inna takeyi mai biyayya. 'Yan uwa duk sunyi mata fad'a ana k'ok'arin fita da ita saiga malamarsu ta islamiya malam Hansa'u tazo yi mata Allah yasanya alkhairi ta jata d'aki suka zauna ta Fara mata nasiha.
"Toh Aisha yau dai gashi Allah ya kawo ranar da kika koma k'ark'ashin wani ba iyayanki ba, yanzu ya koma shine uwar shine kuma uba shine danginki. Aisha kiyi biyayya yin biyayya ga mijinki shine zaki samu aljanna, karki manta da karatun da ake koya muku duk abinda mijinki yace kiyi toh kiyi indai besa6awa addininki ba, ke ko cewa yayi Aisha ga wuta fad'a karkiji d'ar kifad'a din kawai, Aisha kibi aure karki yiwa mijinki rashin kunya ko gaddama ko kiyi musu dashi yin hakan Allah zaiyi fushi dake fushin Allah kuwa babban had'arine akan kowanne halitta.
Allah ya bada zaman lafiya Aisha ya kad'e muku fitina a cikin auranku ya baku zuri'a masu albarka tashi muje akaiki gidanki mai tarin ni'ima da albarka.."
Sai a lokacin INdo ta fara kuka tsoro ya kuma shigarta har aka shigar da ita jibgegiyar motar abokin Abubakar dayazo daga Abuja.
Su uku suka shiga sai driver da friend d'inshi a kusa dashi, ana gama cika motocin suka d'auki hanya shikenan INdo tabar kauyen Sani saidai tazo da ziyara Allah ya d'agata. Gudu suka dingayi kafin wasu awanni sun k'arasa k'ofar gidan su ango lokacin duhu yafara yi.
Bayan an kaita su Mama sunyi farin cikin shigowarta zuri'arsu sunyi mata nasiha aka sake d'inguma aka kai INdo gidan Abubakar masoyinta farin cikinta abin alfaharinta, fuskarta a lullu6e aka shigar da ita cikin d'akinta.
Ita kuwa Fateema saida akayi sallar isha'i sannan aka kaita gidansu Sadeeq itama su Mama sukayi farin cikin shigowarta cikin su sannan aka wuce da ita gidan Sadeeq farin cikinta abin kaunarta, ta riga ta tsara musu yadda zasu gudanar da rayuwar auransu abinku da 'yar boko wayayya.
Masu kawo INdon kauye sai da suka kwana Abubakar yace abarsu sabida dare yayi kuma duk masu motocin sun tafi wai bazasu koma wannan kauyan ba yadai sha iskancin abokai wanda hakan besa yaji kaunar INdo ta ragu koda da kwayar zarra ba. Sadeeq suka raka gidansa aka yi musu nasiha shida amaryar sannan Abubakar suna k'ok'arin fita yace ma Fateema dake lullu6e cikin mayafi.
"Ke..! Sauran kibawa twinnie d'ina wahala ko kiyi mai rowa."
Tana jinsa ta k'i cewa komai har suka fita Abubakar ya kalli Sadeeq tare da cewa.
"Kai twinnie wallahi kabi yarinyar mutane a hankali, nasanka sarai a mafarki ma kana wuce k'a'ida bare kuma yau gaka ga mace mallakinka. Idan ka kirani da safe ba zuwa zanyi ba ah toh..."
Hannu Sadeeq ya bashi suka tafa suna dariya kafin su rungumi juna Sadeeq yace.
"M twinnie har gobefa kai saurayi ne sorry to you wallahi but zaka iya sato Aishan ku koma wani d'akin fa."
"Nop karka damu zan hakura harsu tafi ai daga yau ne gobe zan samo musu mota ta maidasu."
Kamar karsu rabu haka sukeji amma babu yadda zasu yi yana fita ya rufe gidan ya koma ciki. A hankali ya zauna kusa da ita tare da yaye mayafin kanta cikin kunnanta yasanya bakinsa yace.
"Amarya muje kiyi alwala muyi sallah."
A kunyace ta mik'e ya kama hannunta ya kaita har bedroom d'insa cikin toilet sannan ya fito ya shimfid'a musu sallaya ya ajiye mata sabon hijjab, tana fitowa shima ya shiga yayi alwalan sannan yazo yajasu sallah suka yi raka'a biya ya dafa kanta yayi mata addu'a sannan ya kalleta yace.
"Nasan akwai yinwa a cikin nan tashi muje na baki kici bana son kwana dayinwa."
Ya fad'a yana shafa mata ciki, Fateema cike dajin kunya ta mike yayi saurin rik'ota tare da janta jikinsa suka nufi parlor. Kajine gasassu sunsha kayan had'i da lemuka da fresh milk suka zauna yafara bata, a yangance suka gama ci sannan ya wanke hannunsa ya jata suka shiga d'akinsa.
Kayan bacci yasa ya d'akko wata shegiyar rigar mata ta bacci ya mik'a mata yace tasa, ta d'aga rigar nan ta ganta 'yar firit Fateema aka dinga raba idanuwa ta kasa tashi tasa yayi murmushi tare da cewa.
"Bari nazo na temaka miki."
Ya mik'e daka bakin gadon tana ganin haka tayi wuf ta shige toilet yayi murmushi yana lasar leb6ansa. Fitowa tayi bayan tasawo sai kuma ta nad'e jikinta da mayafi kamar tasa lafaya ta kwanta a kunyace, shi kuma yayi musu light of (kafin naji kici-kicin su k'ila k'ok'arin kwance mata yake yi nidai Hajja nayi kwana dan d'akin badai duhu ba yau su Sadeeq za'a angon ce na fita zuwa gurin Abubakar.).....
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
Page *20*
Around 1:45am Abubakar ya shiga cikin gidan nasa bayan ya gama kulle ko'ina yana son lek'awa yaga yasuke amma yana tsoran yadda zai shiga ya gansu dan yasan matan kauye basu fiye kwanciya da riguna ba dan haka ya koma yashiga d'akinsa ya kulle.
Wayar INdo ya dinga k'ira amma ba'a d'aga ba ya ajiye tare da shiga wanka. Sukuwa su INdo bayan an kawota tafita suka zagaya gidan farin cikinta ya kasa 6oyuwa ganin irin gidan da take ciki gida irinna cikin films had'add'e wanda ko cikin mafarkinta bata ta6a zaton zata ta6a koda jikin gidan ba, tun shad'ayan dare suka barbaje bayan sinci sunyi hani'an ga iskar fanka na kad'a su ai babu wanda ya kuma motsawa munshari kawai kakeji yana fita hahhhussss ta kowace kusurwa.
Tun sallar asuba yafita, su kuma suna tashi suka hau shirin tafiya, saida yaje gida yasa Mama ta bada abinci aka kaimusu sukaci wajan k'arfe goma na safe ya kawo musu buses biyu ya biya masu motar sannan suka tafi sunata yiwa INdo Allah sanya alheri. Saida yaga sun tafi sannan ya shiga gidan, a tsaye ya tarar da INdo tana wajan dining bakinta a bud'e sai shafar kujerun takeyi ya tsaya yana kallonta ba tare da tasan yana tsaye ba.
Yana kallonta ta d'an d'osana d'uwawunta akan kujerar sai kuma tayi saurin mik'ewa tana dariya tana karkad'e gurin, ya shigo a hankali cikin rashin sa'a ta hangosa ta cikin glass d'in drawer flat's na dining dake wajan. Da sauri tayi hanyar shiga d'aki zata gudu yayi saurin cafko ta yana dariya yasanya ta a jikinsa.
Fisgar jikinta takeyi zata gudu amma ya hana hakan faruwa, kanshi ya zura a wuyanta ya fara shin-shina wuyanta yana sanya siririn hancinsa cikin kunnanta iskah na shiga ciki, INdo taji wani irin abu hankalinta ya fara tashi kwakwalwarta ta fara aika mata da wasu bakwannin al'amra.
Jin hannunsa a kan k'irjinta ne yasata kwallara mai wata uwar k'ara, Abubakar yak'i sakinta saima jikin bangon k'ofar da zata kaita bedroom d'inta ya jinginar da ita gaba d'aya ta tsure ya kamo fuskarta da duka hannunsa biyu, bakinsa yakai saitin nata zaiyi kissing d'inshi INdo ta kwalalo mai ido tana bin harshensa da kallo tamkar idonta zai fad'o sai girgiza kai take alamar bata so.
Ganin kamar abinda yake shirin yi mata ne bata so yasa shi sonyi mata dan ta gane cewar ba wani abun aibu bane. Gate yajiyo ana bugawa nan INdo ta fara sauke numfashi dan tasan dole yanzu yaje ya bud'e, ba zato bare tsammani kawai taji ya zura mata tongue d'insa tayi-tayi ta datsa bakin amma ta kasa ya fara tsotsa tare da zame d'ankwalin kanta yana shafar gashinta. Nan da nan jikin INdo ya fara kyarma tamkar shocking yajata yayi k'ok'arin tattarota zuwa jikinsa still mouth nasa na cikin nata idanunta a tamke ta dunkule hannayanta jira kawai takeyi taji zubar fitsari.
Sake bugun gate d'in ake da k'arfi amma yak'i kulawa hankalin INdo ya kuma tashi, sai da yayi mata ya tabbar da sakon salonsa na farko ya shigeta sannan ya cikata aikuwa ta zandama d'aki da gudu hartana bugewa da bango yayi dariya yana kallonta harta shige sannan ya gyara wuyan rigarsa ya fita yana bud'ewa yaga sisters d'in Mamansu ne da yaransu ya fara sosa k'eya aunty Shafa'atu ta kallesa dakyau sannan tace.
"Doctor ko baku tashi bane ba tun d'azu sai faman bugu mukeyi..?!"
"Ah mun tashi mana aunty yanzu ma na koma ciki da 'yan uwan Humairan suka tafi."
"Oho toh." Suka fad'a tare da shiga ciki suna kiran sunan INdo.
Shiru tanajin su tak'i fitowa sabida gani takeyi kamar idan ta fito zasu gane, yana zaune a gurinsu yaga tak'i fitowa yasan dalili hakan yasa shi ce musu yana zuwa. Kwance ya ganta kan gado ta yaye bedsheet d'in ta cukwikuye jikinta gabaki d'aya ta kudindine ya tura d'akin yana murmushi da mamaki ya hau kan gadon.
Qarah curewa tayi Abubakar ya janyota gaba d'ayanta ya fara warware bedsheet d'in amma sai sake nad'ewa take cikin kasalalliyar murya domin wannan kokawar da sukayi wani shauk'i ne ya dinga saukar mai yace mata a hankali.
"Please Humairah tashi kizo muje sisters d'in Mama ne suka zo, bana son naji sun fara yin k'orafi dake kinji...?!"
Tana cikin zanin gadon tace mai.
"Toh amma kafita sai na fito.."
"Toh nafita kixo yanzo sai ki kawo musu lemo da ruwa."
Yana fad'a ya fita daga d'akin sai dai yana la6e, tashi tayi ta sakko a hankali ta k'arasa gurin madubi tana shafa bakinta ta kuma bud'esa ta kallesa a cikin madubin a fili tace.
"Kai likita da k'azanta kake wallahi irin na film yayi min, amma fa kamar da dad'i hi har wani lumshe ido yake yi."
Dariya ce ta kusa tona mai asiri hakan yasa shi juyawa ya fita falon yana yi gashi ya kasa denawa mutanen dake falon suka bishi da kallo suma suna murmushin kowa da abinda yake kisamawa wanda yasa shi dariyan.
"Abin na masoya ne me ta gaya maka haka kake 6a66aka dariya."
Shafa k'eya yayi yana shirin yin magana sai ga INdo ta fitoh hannunta a saman bakinta sai faman rarraba idanuwa takeyi aunty Siyama tace.
"Aunty amarya taho nan ki zauna."
A d'ard'ar taje ta zauna kafin ta fara gaidasu k'ananun kuma suka gaida ita, had'a ido suka yi da Abubakar yayi mata alamar ta kawo ruwa cikin sa'a ta mik'e taje inda taga an ajiye lemukan da ruwan ta d'ako ta kawo da yawa sannan ta koma zata zauna Abubakar yace.
"Hunairah baki d'akko musu kofina ba."
"Au dan Allah kuyi hakuri kunji bari na d'akko."
Ta fad'a tare da shiga tsalelen kitchen d'inta, kalle kalle ta farayi domin gabaki d'aya ta hargitse ta shagala da kallon dukiyar da aka kashe har ta manta da cewar aikota akayi. Itace ta6a nan shafa can shinshina nan haka ta dinga yi, shirun dayaji ne yasa shi mik'ewa yabiyo bayanta.
Tsaye ya tarar da ita tana ta6a electric oven taga hotan kaza a jiki ya bita da kallo, sam baya ganin aibunta domin yasan dole tayi haka tunda ba ko ina akeda irin abubuwan ba dan ko gidansu Abubakar d'in babu wasu abubuwan da ya zubawa INdo. K'arasawa yayi ta kallesa tare da juya Mai baya yayi dariya yace.
"Ohh su Humayrah daga zuwa d'akko cups sai mukaji shiru."
"Lah wallahi mantawa nayi bari na kaimusu, amma wanne zan d'auka..?!"
Ta fad'a ba tare da tajuyo ba, ya k'arasa tare da janyota jikinsa yace,
"Kibar shi sun ma farasha da jarkar."
"Toh sakarni na fita gurin su."
"Nak'i d'in da wayace kik'i komawa..?!"
Jin ya fara shafar jikinta ne yasa ta faraturesa ya juyo da ita ta kawar dakai sai ji tayi bakinsa a saman k'irjinta INdo ta zabura ya saketa ta ruga falo nan ma suka bisu da kallo ita dai INdo harta zauna jikinta be dena rawa ba a haka har suka gama zamansu sukayi musu fatan zama lafiya sannan suka fita suna tafiya wasu suka zo ranar ma dai haka suka wuni da baki.
Misalin k'arfe goma na dare Abubakar ya shigo gidan, tsit ba kowa sai k'arar inji ya rufe ko'ina sannan ya shiga falon, zaune ya ganta tana kallo ta kurawa TV d'in ido sai dariya takeyi da alama film d'in yayi mata kyau.
Duk sallamar da yakeyi bataji ba sai daya shigo har tsakiyar falon ya kare mata TV d'in sannan taganshi tana dariya tace.
"Kai dacta dan Allah ka matsa kana kare min."
Hannu ya bud'e mata alamar tazo suyi hugging amman tak'i sai ya kashe kallon gabaki d'aya tare da k'arasawa dining ya ajiye ledojin hannunsa. Tashi tayi tana turo baki ganin ya kashe mata gashi bata iya kunnawa ba dama su Hawwa ne suka kunna dasuka zo ya juyo ya kalleta tare da cewa.
"Kin manta ko, da bakinki kika cemin malama ta baku labarin matar da bata bin umarnin miji da abinda akayi mata ko? Shine yanzu nace kizo kiyi min oyo-yo kikaki ba ruwana dake."
INdo ta tuna tayi saurin zuwa gurinsa ta tsaya, ganin haka yasa shi kuma ware mata hannunsa a hankali ta shige bayan ta rintsa idanuwanta ya rungumeta shima. A saitin kunnanta ya tambayeta.
"Kinyi sallah..?"
Kad'a kai kurum tayi sannan nan yace.
"Zo muje muyi wata mu yi addu'a alkairin dake cikin auran mu Allah ya tabbatar dashi."
Tunawa INdo tayi da labarin dasu Uwani suka bata cewar indai taji miji yace ayi sallah akuma ci nama toh ranar aikwai aiki musamman ranar da aka kaika. Janta yayi suka nufi bedroom d'insa dama bata ta6a shiga ba, taga wani shegen gado me shegen kyau bakin ta yak'i rufuwa yace.
"Zokije kiyi alwala."
Tace "Dacta tsaya na gama ganin gadonka wallahi yayi kyau Allah sanya alheri."
"Amin Humaira amma ai shima nakine, duk abinda kika gani na gidan nan nakine ko mutuwa nayi baza a raba gadona dasu ba."
Cikin tsananin murna INdo tace tana kallonsa.
"Dacta da gaske kake nawane.?!"
Kai ya d'aga mata ta fara murna tana godiya sannan ta shiga bayin tayi alwala, tana fitowa shima yayi lokacin ta dawo daga d'akko hijjab, kar6a yayi ya bata sabo tasa sannan yajasu sukayi 2raka'at sannan ya dafa kanta yayi mata addu'a suka shafa. Hannunta ya kama suka koma falo ya kunna musu kallo suna dining suna kallo ya dinga feeding d'inta sai da taci ta koshi ta kora da madara sannan tace ta koshi.
12:49am suka shiga d'akinsa INdo sai hamma takeyi najin bacci, saida ya had'a mata ruwa tayi wanka sannan shima ya shiga ya fito sanye da boxer tayi saurin kawar dakai tana zaro ido gashi ya kulle d'akin itama daga ita sai towel ya kwashe mata kayan ta nema ta rasa.
Turare ya shafa kawai sai na mouth sannan ya nufi gurinta dasu, zama yayi a kusa da ita tayi saurin matsawa shima ya matsa tare da rik'ota da sauri tace.
"Na higa uku ni INdo dan Allah dacta kayi hakuri."
"Shhhh." Yayi mata tare da matsa mata turaren ya ce ta bud'e bakin ya fesa mata da sauri ta tufar da yawu a k'asan bedside carpet yace.
"Humaira ya haka.?!"
INdo kamar tayi kuka tace "yo toh ai ba dad'i."
Dariya yayi tare da girgiza kai sannan ya tashi ya mayar tare da d'akko handkerchief ya goge gurin. Light off yayi musu sannan ya kuma kunna bedside lamp bulb d'in green light ya haske d'akin yayi kyau INdo ta kalli d'akin ta kuma sakin murmushi ita dai yau tana ganin ikon Allah a gidannan. A hankali ya sargafota ta fara zillo towel ya fara kwancewa tace.
"Wai kai bazan sa kaya bane.?"
Cikin sanyin murya Abubakar yace "Eh a haka zaki kwana ko kina son nace bana so amma kuma kisa...?"
Ya tambaya yana shafa gashinta, wani kakkawar yawu ta had'iya tana kad'a kai, ya janyota kan gadon towel d'in ya yaye daga k'asa INdo ta saki k'ara jikinta na rawa. A hankali ya kuma janta jikinsa sannan ya zare mata towel d'in gabaki d'aya ai INdo sai kuka tana cewa.
"Yaya Abbakar karka kalleni in kanawa iyayenka, ni wallahi ka dena ta6ani banasan iskanci..."
Sam bazai iya yi mata abinda take so ba, shi amatsayinsa na likita yasan idan ya barta besamu nutsuwa ba zai shiga tashin hankali ya kuma San akwai illah hakan. A hankali cikin wayewa da iya *TATTALIN MACE* Abubakar ya dinga hillatar da ita yana kuma nuna mata illar hanashin da takeyi a haka ya samu INdo ta yadda dashi ta bashi kanta duk da tasha kuka hardasu majina.
Yana daga kwancen yace,
"Ohh so sorry my wife, please zoki rama kema."
Tana kukan ta k'asa-k'asa tace.
"Meh...?!"
Ai Abubakar besan lokacin daya kyalkyale da dariya ba haushi ya sake zuwar ma INdo ta juya ta fara dukansa yana karewa da hannu...
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
Page *21*
Ganin yak'i denayi mata dariya yasa ta lalubo towel d'inta ta d'aura ta kwanta tare da janyo bargo ta rufa sabida wani sanyi dataji yana shiga cikin jikinta. A hankali ya matsa kusa da ita tare da zura hannunsa ya rungumeta tana jinsa ta kasa yin koda kwakwaran motsi sabida jikinta duk ya lafe a haka bacci ya d'auketa shi kuwa kasa yi yayi se tashi mayayi yaje yayi wanka sannan yayi sallah ya d'auki sallayar ya maida ita inda zai dinga kallon fuskarta. Yana jan carbi yana shafar gashinta tare da shafar fashin goshinta wanda yake d'ansiriri.
Har aka kira asuba INdo bata koyi juyi ba bare asaran zata tashi ya mik'e daga kan sallayar yashiga bathroom ya tarar mata ruwa sannan ya fito, a hankali cikin nutsuwa ya fara tashinta amma babu alamar zata motsa sai ya yaye mata bargon ya fara k'ok'arin kwance mata towel tayi saurin tashi tana rarumarsa tana furta "6arawo..!" ta d'auka 6arawo ne sabida a tunaninta wannan uban gidan baza'a rasa 6arayin dazasu shigo yi musu sata ba. A mamakin ce Abubakar ya kalleta ganin yadda ta cakumeshi tayi saurin sakinsa tare da saurin komawa ta kudindine a bargo yace mata.
"Humairah a mimakwan yin auziya sai ki furta 6arawo? Toh ina 6arawon tashi ki gaya min ko mafarki kikayi..?!"
Tana cikin bargon tace "Allah mafarki nayi kayi hakuri."
"Toh tashi kiyi wankan tsarki sai kiyi sallah."
"Wane iri kuma dacta?!"
Ta tambaya da mamaki yace "na janaba ko bakisan anayi ba?"
Sai yanzu ta gane kenan a makaranta da aketayi musu bayanin wanka haila, wankan janaba da wankan bik'i shi yanzu wanda zata yi shine na janaba ikon Allah dan ita a karatu idan ba practical ba toh theories dakyar suke shigarta.
"Kin iya ko..?!"
Ya tambayeta tayi shiru ya kwanta a bayanta tare da janyota ya matseta, ihu ta farayi sannan tace.
"Toh sani nayi ne, ka gaya min mana."
Yace "Okey kin iya wankan tsarki na haila?" 'Daga kai tayi yace "tashi ki nunin in gani ko dai-dai kikeyi?"
Dakyar ta tashi zaune tana gwada mai ya gyagyara mata sannan yace taje tayi amma ta canzaxani.Ta shiga bathroom d'in da sauri wai dan yana kallonta, tana fitowa sukayi sallah sannan yace tazo su yi karatu, tundaga Nasi ya fara mata har akazo inda ta iya sannan yace toh zai dinga koya mata kullum da asuba indai yana gari.
Gadon ya sake janta ita INdo bata sabayin baccin safe ba hakan yasa tace mai ita kallo zataje tayi ya hanata dole taje suka kwanta, romance d'inta kawai yayi mai tsayawa a wuya dan tana k'ar6ar sakon yadda ya kamata kafin kace mene tuni INdo tayi baci shima ya samu yayi har kusan 9:16am sannan ya farka yana zare jikinsa itama ta farka a kunyace dan ko kallonsa bata iya yi.
"Muje kitchen yau dakan mu zamuyi breakfast."
Kama hannunta yayi suka fita suna zuwa kitchen ya sargafe hannu a k'irji yana jiran yaga ta ina zata fara, itama tsayawar tayi tana kuma bin kayayyakin kitchen d'in da ido.
"Jiya na shigo da slender bari na had'a sai ki soya kwai da tea."
Tace "Toh akan slimba d'in Zan d'ora."
"No Humairah slender itace abinda za'a zuba kalanzir toh ba shi za'a zuba ba gas za'a saka ajona na wannan sai da kin kunna zai kawo wuta idan ya k'are kuma zakiga yak'i kawowa."
Jinjina kai tayi tamkar ta fahimta, shi kuma dayake yasan dawa yake tare sai ya kamo hannunta suka nufi bayan kitchen d'in, a kan idonta yasa dan watarana idan ba kowa ya zama na ta iya. Komawa cikin kitchen d'in sukayi sannan ya kunna cooker d'in sai ga wuta INdo ta dinga murmushi kusan duk shi yayi koma tana kallonsa suna yi yana nuna mata amfanin komai na kitchen d'in komai saida ya nuna mata sannan suka kwashi breakfast d'in suka kai dining.
Yauma kamar jiya daddare shi yayi feeding d'inta taci sannan shina yaci suka koma wajan TV lokacin injinsu ya mutu suka kalli juna yace.
"Muje d'aki ki gani."
Yana rungume da ita yace suka shiga ya d'akko laptop d'insa ya kunna mata kallon yaga alamar tana masifar son yin kallo tana zaune a tsakiyar gado ya d'ora kansa a cinyarta tayi dariya tana kallonta. Hannunta ya kamo ya d'ora akansa tare da cewa.
"Sweetie bazaki dinga shafani ba, please inason ki koyi soyayya fa ni Ina son love."
Sosa mai ta fara yi ya dank'e hannun tare da cewa,
"Bafa haka akeyi ba, haka...!"
Ya fad'a yana rik'e da hannunta yana shasshafa kansa, haka Abubakar ya dinga tarairayar INdo yana nuna mata abubuwan da zata dinga mai cikin ko wane irin abu ko yanayi sai da ya nuna mata irin abinda zata yi mai tun tanajin nauyi da kunya harta fara sakin jiki tana yi mai ba tare da ya nema ko ya nuna buk'atar hakan ba.
Cikin sati d'aya INdo ta kuma wayewa da wasu abubuwan tayi kyau abinta ranar da ta cika kwana takwas ya d'auketa sukaje gida su Mama suka dinga shi musu albarka INdo bajin kai k'annansa duk babu wanda bata wasa dashi sun dad'e Kafin su tafi gidan Sadeeq sai INdo tayi mamaki ganin gidanta yafi kyau sai akayi sa'a bata kwafsa tayi maganar ba.
Sosai suka sha hira shima Sadeeq ya sakar mata fuska Fateema taja ta suka kule d'aki, nan ma sun dad'e kafin Abubakar yace tazo suka tafi.
Washe gari ya d'auketa suka jajje gidan abokansa na nan sannan ya kaita har Munjibur park wayyo farin ciki a gurin INdo ba'a musallatawa duk abinda taga anhau sai tahau shi kuma ya biya duk bata san sai ya biya ba sha'aninta kawai takeyi suka yi hotuna wasu tare wasu kuma ita kad'ai. Sun dad'e kafin suka koma gida INdo cike da murna ya kalleta shima cikin shauk'inta da soyayyarta sannan yace.
"Zo kimin tausa tunda yauma kin gajiyar dani."
Zuwa tayi tana shan ice cream tana mai sannan shima ta bashi yasha wani shauk'i yana fisgarta bata san lokacin da ta kwanta a bayansa ba a hankali ta furta mai.
"I love you mijina."
"Oh my God what did you say? Allah yasa ba mafarki nakeyi ba sweetie d'an jijjiga ni."
Cikin dariya INdo da bugeshi a baya ya juyo tare da janyo ta aikuma ice cream d'in ya zube a saman k'irjinshi yace.
"Aikuwa sai kin lashe shi kuma ki gama ki wanke ni ah bazan yadda ba."
"Ah my key nifa bani ce silaba kai kaiwa jikinka haka."
Ta fad'a tana masa cukali tana d'iban na k'irjin nasa tana sha yanzu duk ta waye bata kyama ganin shima vaya nuna mata akan komai na jikinta.
"Nifa inajin zafin na cukalin nan ki ajiyeshi."
"Toh baki zansa?!"
Ta tambaya kai tsaye shima kai tsaye yace mata "Eh shi nake so."
Harshe tasa ta fara lasa har sai data sud'e tass sannan shima ya faki idonta ya d'akko ragowar na rubar ya 6arar mata a k'irji yace.
"Ashhh sorry bari na ramamiki kema."
Dariya suka saki tare cikin dariyar tace.
"Kaifa kana sane."
Ya rik'ota yasa baki tass shima ya lashe mata daga nan kuma al'amra suka canza. Ana gobe zai koma abuja suna kwance duk sun mak'ala juna suna sauk'e ajiyar Zuciya kad'an-kad'an Abubakar yana shafar kanta yace.
"Humairah banson tafiya na barki anya bazan tafi dake ba?!"
Shiru INdo tayi babu amsa ya kuma janta jikinsa yana d'an shafarta tana biye mai ya kuma cewa.
"Kinyi shiru Humaira ko dama kin k'agara na tafi.?"
Tace "A'a bansan abinda zance ba nima shi yasa nayi shiru fa."
"Okey kema kina son ki bini ko?"
Tace "Eh mana."
Hannunta ya rik'o ya d'ora a k'irjinsa tare da cewa.
"Ina sonki Humaih ina kaunarki ban ta6ajin Ina kaunar mutum ba kamar yadda nake sonki, please kema ki soni koda bekai yadda nake miki ba kinji..?!"
"Toh ai Ina sanka nima."
Ta fad'a cikin sanyin jiki suka rungumi juna da haka sukayi bacci, washe gari tunda asuba suka yi wanka INdo tayi kwalliya irinta kauye tasa zani daban riga ma haka da d'ankwali. Abubakar na shigowa d'akin daga shi sai boxer da singlet ya kalleta yana murmushi yaga kwalliyar tayi mata kyau ya k'arasa ciki yana cewa.
"Woww sweetie gaskiya sai na biya wannan wanka I like it."
"Toh nawa zaka biya domin da tsada...?"
Ta tambayesa tana jan hancinsa, bakin gado ya zauna yana rik'e da kugunta yace.
"Bari kigani."
Kissing d'in bakinta yayi duk ya kwashe janbakin datasa ya matseta a jikinsa yace.
"Allah ya miki albarka matata kafin in dawo Zan samar miki makaranta damun koma saiki shiga."
"Kanason nayi karatu da yawa, nikuma kaga ban iya turanci ba."
Ta fad'a tana shafar sajansa ya sanya kansa tsakiyar kirjinta yana goga fuskarsa a jiki yace.
"Zaki iya kema sweetie ai da koyo akasan gwani, abaya ma dandai baki tsaya kin koya bane amma yanzu kisa aranki cewar kema zaki iya turanci kinji ko..?!"
"Allah yasa toh.."
Ta fad'a yace "Amin sai kuma abani bye-bye dan bazan tafi haka ba"
Rufe fuska tayi ta zauna kan cinyarsa wannan karan itace ta fara sanya mai mouth nata cikin nashi ya k'ara tabbatar da lallai tana d'aukar naganar tana kuma jinta tare da aikata ta a aikace. Sai da ya samu nutsuwa sannan sukayi wanka kamar karsu rabu duk da yace mata kwana biyar zaiyi yaxo yayi weekend amma gani yake tamkar rasa ta zaiyi, itama haka ta dinga cewa ya barta su tafi abuja tare dama bata ta6a zuwa ba amma ya dinga kwantar mata da hankali yace kila ma jibi ya dawo idan yaje ya rage wasu abubuwa.
'Dakinsa saka koma ya shirya duk ta nanik'e mai ya kalleta yace.
"Idan na tafi kiyi tafiyarki gidan Mama ko gidan M twinnie ki zauna kuyi hira zuwa yamma sai ki dawo dan nace dasu Haleema suzo su zauna a nan harna dawo kinji.?!"
"Toh.."
Tabashi amsa ta fesa mai turare sukaci abincin daya dafa musu suna gamawa sadeeq na yin knocking .
Sai data fara sanyo hijjab sannan Abubakar yaje ya bud'e masa kasan cewar ya hanata zama a haka idan wasu suka zo.
"Aishatu Hamza..."
Cewar Sadeeq cike da zolaya tayi murmushi tare da cewa.
"Malam Sadeeq ya gida..?!"
"Kalau."
Yabata amsa Abubakar yace.
"Twinnie gidana a hannunka please ka kular min da babyna."
"Au wai kana nufin sai an kula da ita? Ta6 Aisha ai ta iya haura katanga bakada case da ita ka kwantar da hankalin ka."
INdo ta turo baki haushinsa ya cika ta Abubakar ya janyo ta tare da cewa.
"Kabari twinnie ai dane kuma kaima ai kayi kana yaro."
Ya kalli INdo tare da cewa "Sorry sweetie karki kulasa Zan dawo na d'aukeki."
Suna dariya dukansu suka fita Abubakar ya shiga mota shida Sadeeq zai saukesa gidan Mama idan yaje, INdo ta zagaya 6angaran Abubakar idonta yayi ruwa murya na rawa tace.
"Allah ya kiyaye hanya."
"Amin." Ya fad'a yana zuro hannu sukayi musabuha yaja motar suka bar gidan, tana share hawaye ta rufe gate d'in tare da shiga cikin gidan. Suna hanyar zuwa gidan Mama Abubakar ya dinga ba Sadeeq hakkin lurar mai da gida musamman ma INdo abin ya dinga bawa Sadeeq mamaki wai yau INdo ce take da matsayi a zuciyar d'an uwansa, koda yake yafishi sanin INdo tun a kauyan Sani.
Bayan sunyi sallama da mutanan gidan ya kama hanya ya tafi bayan ya bugawa INdo waya yace mata ya tafi tayi mai fatan sauka lafiya.
****
K'arfe 11:36am tana zaune a falo tana kallo bama taje gidan Maman ba ganin an kawo wuta, shigowa yayi kai tsaye gidan tana ganinsa ta mik'e da gudu raje ta rungume shi kamar yadda ya sabar mata. Jin jikinsa yana rawa ne yasan ya INdo d'agowa tana kallon kafin k'irjinta ya fara bugawa sam bata gane bashi bane ta sha'afa da kayan dayasa tace.
"My key menene? Inzo mutafi?!"
Wani kallo dataga yayi mata ne yasa hankalinta dawowa jikinsa ta zaro ido tana kallon fuskarsa tace.
"Malam Sadeeq kayi hakuri na d'auka Yaya Abubakar ne."
Da kyar Sadeeq ya samu ya bud'e baki yace.
"Aisha jeki d'akko hijjabinki zamu gidan Mama."
INdo ta kallesa cikin sauke numfashi tana warware d'ankwalinta tayi mayafi dashi tana cewa.
"Ah ai inajin sai anjima zani idan ma banjeba ai yace su Haleema zasu zo."
"Ki d'akko hijjab nace miki kenake jiya bawai surutu ba."
Juyawa tayi tana kunkuni ta d'akko ta fito shi kuma ya juya ya fita. Saida ta fito sanye cikin atamfa blue da zanen ganye fari ta sanya blue d'in mayafi suka fita ya rufe gate d'in suka shiga mota. Kasa tukawa yayi jikinsa sai rawa yake yi INdo ta bishi da kallo cikin mamaki k'arshe ya fito daga motar yace.
"Fito muje."
A k'afa suka taka har bakin titi ya tarar musu napep suka shiga aka kaisu gidan Mama lokacin har mutane an fara taruwa a k'ofar gida Sadeeq ya cewa INdo.
"Shiga ciki gurinsu."
Yana dad'a ya juya yabarta ita kuma ta nufi ciki tana bin mutanan da kallo. Tana shiga parking space taji abbansu yana waya yana cewa.
"Eh wallahi Abubakar d’inne....
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
*MUSAYAR ZUCIYA:- Hak'ik'a banyi zato ko tsammanin makaranta labarin nan sunkai yawan haka ba sai da akazo page 21, a hak'ik'anin gaskiya naji matuk'ar tsoro na razana da ganin millions of people's da suk'e matuk'ar son Dr Abubakar da Aishatul humaira a ranar da waya nata tarwatsewa toh da tuni an wuce babin wayata, everywhere MUSAYAR ZUCIYA Hajja karki kashe Dr becan-canci haka ba, idan kikai hakan kin sakamu cikin tashin hankali INdo kuma baki kyauta mata ba. Karku manta Allah babu ruwansa da lokacin da zaka farajin dad'in rayuwa ya d'aukeka, anytime kowane irin yanayi kake ciki idan lokacinka yayi dole ka barshi katafi ba tare da kashiryawa hakan ba. A yanzu haka nasan wad'anda suka tanadi likaffani na mutuwarsu sabida suna ganin sun tsufa rayuwa ta k'are musu amma har yanzu basu mutuba sai 'ya'yansu da jikok'insu wad'anda ba'a saka musu ran mutuwa sune suke mutuwa. Dan Allah badan niba kuyi hakuri ku d'auka a cewar kuma akanku hakan zata iya faruwa sannan kuma kowacce zata yiwa Abubakar addu'ar Allah ya sadashi da rahamarsa. Labarin gaske ne domin da Ummi Aisha itace zata yishi so bansan Stylish Bch ta bata labarin ba sai jiya. Kuyi hakuri harda masu cewa sundena karantawa sabida sunsan karshe dai Sadeeq zata aura suzo suna kishi da fateema🤭toh duk kuyi hakuri kuma sannan ku yafewa 'yar uwarku, da ace tun farko bansa muku true life ba wallahi akwai yadda zanyi na sauya salon amma yanzu kona sauya toh araina zan dingajin abun tunda nasan ba haka yake ba, duk wanda na 6atawa tundaga kan fara novel din har zuwa wannan pagen kuyi hakuri ku yafewa Hajja ce👈 'yar Adam ce kamar ku sannan kuma meyin kuskure a duk inda ta samu kanta, wallahi dana dinga ganin comments d'inku dakyar nayi bacci zuciyata na rawa Ina ganin ban kyauta muku ba ciki rayuwarku. Nasan da yawanku zaku dena karantawa toh Ina fatan duk wanda ya tsaya iya nan ya d'auki wani darasi a ciki amma Zan samu na k'arasa shi a WATTPAD dan nima na samu nutsuwar Zuciya. Nagode gaduk wanda suka karanta farkon labarin Allah ya sadamu da rahamarsa a cikin kabarinmu Amin Love you all m fan's❤🤝❤*
Page *22*
Hark'asa INdo ta tsugunna tana gaida shi idanta akan fuskarsa tace,
"Abba ina wuni?"
Ya zura wayar cikin aljihunsa yana kallonta ya amsa.
"Lafiya lau Aisha tashi kishiga daga ciki."
"Toh adawo lafiya."
Tafad'a tana mik'ewa ta nufi cikin gidan, tana shiga sallama tayi tana k'iran Haleema kamar yadda takeyi idan suka zo gurin da zasu had'u. Haleema dake zaune a falo tajiyo INdo na nemanta da sauri ta mik'e ta shige d'akin su dan bata son su had'u a cikin wannan yanayin. Mata tagani a zaune a falo wasu sunzo wasu kuma na shigowa Mama a gefe gurin kujera ta takure Umma kuma a bakin k'ofa INdo ta dinga binsu da kallo kafin ta k'arasa kusa da Fateeman Sadeeq ta zauna itama ta takure tana gaida su, suka amsa mata a sanyaye. Juyawa tayi tana lek'an fuskar Fateema wadda take faman hawaye a dai-dai fuskar tata tace.
"Kai amaryar malam menene kike kuka? Ko malam Sadeeq ne,dan nasan shi sarai tun a makarantar mu meh yayi miki..?!"
Zame jikinta tayi daga na INdo ta juya tana kallon Mama sai taga itama ta d'auke kai Fateema ta rasa yadda zatayi gashi INdon ta takura mata akan sanjin abinda takewa kuka,mutane dake shigowa ne ya k'ara sanya INdo cikin wasi-wasi kuma da sun shigo zasu samu guri su zauna a cigaba da zaman shiru sai kuma kallonta da ake yi. Mama ce tayi k'arfin halin yin magana tana kallon su fateema tace.
"Fateema jata kushiga cikin d'aki mana."
Hakan akayi kuwa suka shiga ciki nan INdo taga Haleema a mak'ure jikin gado sai shashekar kuka takeyi, cikin sauri ta k'arasa wajanta dayake Allah ya had'a jininsu da ita ta janyo ta da sauri cike da damuwa da nuna kulawa tace.
"Haleema Hali dubu kyakyawa, me kikema kuka kema?!"
Rungumeta Haleema tayi yayin da INdo tayi shiru tana rik'e da ita, ita INdo ba komai yake sanyata saurin kuka ba har sai abin yakai mak'ura sannan batada tsoro musamman a fagen magana kafin Haleema tayi magana Mama tashigo d'akin Fateema na zaune fuskarta cikin hijjab Mama ta rik'o INdo ita kuma jinta ajikin Mama yasa tayi murmushi sai taji tamkar Abubukar d'inne ya rik'ota.
A bak'in gado ta zaunar da ita can suka jiyo muryar Wata tsohowa mak'ociyar su ta shigo tana fad'in.
"Allahu akubar Garbati ankai sa'i, d'azu-d'azun nan yana fitowa daga gidannan ya lek'a zaurena muka gaisa yace min zai tafi birnin taraiya, Allah sarki kungani ya bani yaci inci goro Allah yajik'anka Garba.."
Ta k'arasa maganar tana nuna musu naira d'ari biyar d'in daya bata, a cikin d'aki INdo ta kalli Mama tana zaro ido tace.
"Mama waye Garba a gidannan da ya mutu?!"
Cikin dakiya Mama ta k'arasa wajan wardrobe tana cewa.
"Anan gidan yake Aisha zakiji ko waye."
Farin hijjab ta zaro tare da mik'awa INdo shi tana cewa.
"Ciro mayafin Aisha a ajiye shi."
Kamar yadda Mama tace haka tayi tasanya hijjab d'in Mama zumbulele sannan Mama tace ta zauna karta fito. Suna zaune zugum sai ta d'akko wayarta number'n sa ta k'ira cikin sa'a aka d'auka cikin zumud'inta tace mai.
"Salama alaikum my key kaje ko kakusa zuwa..?!"
Taji ance "Sorry hajiya me wayar yanzu haka Allah yayi mai rasuwa."
Da mamaki tace "Rasuwa kuma? Toma waikai waye ma tukunna?!
Kashewa akayi INdo ta zaro ido tana kallon wayar tare da furta.
"Rainin hankali toh ko fad'uwa wayar tayi wani ya sace shine zaice min haka. Aniyarka ta bika mugu 6arawo."
Ta fad'a su kuma Haleema dasu Fateema da wasu da suka shigo d'akin suka bita da kallo. Hawwa ce ta shigo tana kuka sosai saida tazo falo ta kuma 6arkewa da wani kukan tana shashek'a tace.
"Allah sarki Yaya Habu yanzu ya gama min waya Mama kinga kiran da yayi min yace gobe insa aje a d'akko min Humairansa... Tazo muyi hira da daddare a maida ita baya son ta zauna it...."
Ta kasa k'arasawa sai kuka, INdo ce ta fito fululum cikin hijjab jin muryarta ta k'arasa kusa da Hawwa ai Hawwa na ganinta ta janyota jikinta kukan ya tsananta amma bakin be fasa magana ba.
"Aunty Humairah kinyi rashi Allah yajik'an Yaya Habu yaso kuyi long life a tare sai gashi Allah ya d'aukesa ya barki...."
Muryar Mama ce ta katsewa Hawwa kukan da takeyi cikin fad'a tace.
"Amma dai ban ta6a sanin bakida hankali ba sai yau Hawwa, wannane wane irin hauka ne daga shigowarki sai kace ba gidan musulmai kika shigo ba. Toh kin gaya mata kinji dad'i tun zuwanta kowa ya kasa gaya mata saike wawuya kawai..."
Da sauri Hawwa ta kalli INdo sai taga ta kura mata ido fuskarta a murtuk'e tun daga nan kuma sai bakin mutane ya fara bud'ewa aka fara zance mutuwar kunnuwan INdo suka dinga jiyo mata ai yana tafiya har ya wuce Kaduna Allah yayi masa rasuwa.
Sosai hankalin Hawwa ya tashi ganin yadda INdo ta kafeta da ido hakan ya bata tsoro tayi saurin matsawa baya INdo ta bita cikin tashin hankali Hawwa tace.
"Aunty Humairah Lafiya? Please wannan kallon fa..?!"
A hankali INdo tasa hannu ta rungume Hawwa cikin rawar murya tace.
"Yaya Hawwa kema sokike Yaya Abubakar ya mutu? Yanzu na buga mai waya wani ya d'auka yace min me wayar ya mutu ashe kema sokike ya mutu? 'Dazu ni narakasu mota suka shiga shida malam Sadeeq amma meyasa kike son yayanki ya mutu? Kinga yana sona dayawa d'azu fa har cemin yayi yana son duk wani mesona kuma zai sani a makarantar abuja..."
"Kiyi hak'uri aunty Humairah nima inason Yaya Habu amma Allah yafimu sonshi shi yasa yayi hatsari..."
Hawwa ta fad'a tana kuma sakin kuka, da sauri INdo ta hankad'a Hawwa baya iya k'arfinta jikake gam..! ta bugu da kujera cikin kukan bak'in cikin maganarta yasa INdo cewa.
"Daga yin bikin mu shine zaki mana addu'ar ya mutu sabida bakya sonmu, toh insha Allahu sai Isyaku ya riga dacta mijina mutuwa fatanki ya biki, ance miki Garba ne ya mutu shine zaki zo kice Yaya Abubakar ne dan bak'in ciki..."
Umma ce tayi saurin toshewa INdo baki cikin rufewar ido ta fara tureta domin ta baya ta rik'ota ta kuma toshe mata. Cikin kwantar da murya Umma kishiyar Maman su Sadeeq take mata magana a hankali.
"Kinga Aisha kiyi shiru kinga mutane sun fara cika gidan yi hak'uri taho muje ki zauna kinji 'yar albarka."
Tana nishi Umma taja ta still bata dena yiwa Hawwa kallon banza ba duk kuwa da cewar ta girmeta nesa ba kusa ba amma cewar Abubakar d'inta ya mutu shine ya d'arsa wata k'azamar kiyayya a zuciyar INdo.
Fateema ce ta fito idanunta jawur ta kama hannunta suka koma cikin d'akin Mama, suna zama amma sai mita INdo takeyi Mama ta shigo ta kalleta tare da cewa.
"Aisha kidinga hakuri kinji ko?"
INdo tace "Toh Mama ki gaya mata bana son wasan mutuwa."
"Toh zan gaya mata tashi muje ki wanke fuskarki da sabulu."
Babu musu ta mik'e suka shiga bathroom saida ta gama wankewa sannan Mama ta kamo hannunta suka wuce, d'akin Abba suka shiga yana zaune yayi shiru yana bud'e likkafani gefe turare ne a kusa dashi suka shiga bayan Mama tayi sallama. Sake gaisawa suka yi da INdo sannan Abba ya kalleta tsawon lokaci ya kasa cewa komai, can dai ya nisa yace.
"Aisha ke musulmace ko?!"
'Dan murmushi tayi alamar kunya tana sunkuyar dakai tace,
"Eh Abba."
"Alhamdulillahi ina son sanar dake Abubakar dai Allah ne ya bani shi, nina raineshi tundaga zanin goyo har girmansa da temakwon Allah, bayan ya girma ya mallaki hankalinsa shida d'an uwansa suka d'auke min duk wani nauyi nasu dana k'annansu, kafin ya aureki ya nemi auran wata yarinya Allah ya k'adarta beyi ba sai dake, toh Allahn daya baki Abubakar Aisha ya k'ar6i abinsa domin yanzu haka suna hanya za'a kawo gawarsa ina son ki daur...."
Bek'arasa ba yaji ta fashe da kuka, kusa dashi ta rarrafo tare da rik'o Hannunsa tana jijigawa tana fad'in.
"Abba... Abba wallahi ba dacta bane, ba shine ya mutu ba shi yatafi abuja k'ila dai malam Sadeeq ne, dan Allah Abba karku ce haka wallahi yace zai dawo ya tafi dani can garan..."
Mama Abba ya kalla alamar tazo ta zanye ta, tana zuwa INdo ta juya kanta tare da rik'o hannunta itama tana cigaba da magana tana basu rabarin abinda yace zai yi mata nan gaba sai kawai itama Maman ta fashe da kuka Abba ya fara mata fad'a amma ina ta kasa yin shiru bare ta bawa INdon.
"Kutashi kuje yanzu suna hanya zasu kawo shi, karku sake kubarta tafita ko'ina kinajina...?"
Mama ta kad'a kai tare dajan hannun INdo suka shiga gidan sai ihu take mutane na kallonta cikin tsananin tausayawa.
Tana shiga ciki ta zu6e ak'asa jikinta sai rawa yakeyi aka rufa a kanta kowa sai nemar mata d'auki yake ta zame jikinta daga na wata mata tana kallon Matan tace.
"Sani zantafi."
Umma ta rik'ota itada Fateema ta fara tirje musu dama INdo yaya lafiyar kura, dacta ne yasanta ya kuma san yadda zai biyo mata gashi babushi dan haka abin nata ya kuma yawa.
Kullesu akayi a d'aki babu me fitowa suna jiyo kukanta har aka dawo daga d'akko gawar Abubakar, d'akinsu aka kaishi Sadeeq tamkar wani zararre fuskarsa fal hawaye idanunsa sunyi luhu-luhu tamkar kurji ya fito ya shiga cikin gida yana neman Mama. Da kyar ya iya tambayarta zani ta mik'e ta bud'e d'akin, suka shiga.
Gaidashi mutanan d'akin suke suna mai gaisuwa, yana furta "Alhamdulillah." INdo tayi zumbar ta mik'e daga ruk'on da Zulaihat tayi mata, lokacin Mama ta mik'a mai zannin ya k'a6a kawai yaji INdo ta mak'aleshi katak'am tamkar ba rik'on mace ba tana kuka tana cewa.
"Dacta ka dawoko? Nasan dama bazaka barni ba dan Allah da manzansa kace min Malam Sadeeq ne ya mutu ba kaiba, wallahi kaga zanyi kwalliyar da kace irinta d'azu, mu koma gidanmu nan kana da mak'iya ciki harda Abba duk fatan mutuwa suke ma..."
"Aisha sakar ni please."
Sadeeq ya fad'a yana 6an6areta daga jikinsa amma tamkar mutum biyu ne suka rik'esa, ya rasa dalilin dayasa takeja masa mugayan alkaba'i tun suna makaranta nan fa su Mama suka k'arasa suna nuna mata bashi bane amma tak'i sakinsa cewa take.
"Duk inda zahi zan bihi wata k'ila akwai masu bibiyarsa basa sonshi toni ina sonsa."
Janta yayi ganin ta mak'ale suka k'arasa bakin gado ya zaune tare da nunawa Fateema alamar tazo ta zauna kusa dashi. Tana zuwa INdo ta kare shi alamar karta ta6ashi Fateema ta toshe baki kuka na shirin kwace mata, haskilowa kawai takeyi tasan da shi ya rasu k'ila da tuni itace a cikin wannan yanayin da INdo take ciki.
Kabeer ne ya shigo ya kar6i zanin domin sam INdo tak'i sakin Sadeeq, Mama kuwa so take ta 6an6areta domin tasan hankan ba dacewa bane kuma INdo tashiga cikin takaba hakan yasa ta fara sanya ta cikin dokokin da musulinci ya tanadarwa ga duk macen da mijinta ya rasu...
0 comments:
Post a Comment