*MUSAYAR ZUCIYA:- Hak'ik'a banyi zato ko tsammanin makaranta labarin nan sunkai yawan haka ba sai da akazo page 21, a hak'ik'anin gaskiya naji matuk'ar tsoro na razana da ganin millions of people's da suk'e matuk'ar son Dr Abubakar da Aishatul humaira a ranar da waya nata tarwatsewa toh da tuni an wuce babin wayata, everywhere MUSAYAR ZUCIYA Hajja karki kashe Dr becan-canci haka ba, idan kikai hakan kin sakamu cikin tashin hankali INdo kuma baki kyauta mata ba. Karku manta Allah babu ruwansa da lokacin da zaka farajin dad'in rayuwa ya d'aukeka, anytime kowane irin yanayi kake ciki idan lokacinka yayi dole ka barshi katafi ba tare da kashiryawa hakan ba. A yanzu haka nasan wad'anda suka tanadi likaffani na mutuwarsu sabida suna ganin sun tsufa rayuwa ta k'are musu amma har yanzu basu mutuba sai 'ya'yansu da jikok'insu wad'anda ba'a saka musu ran mutuwa sune suke mutuwa. Dan Allah badan niba kuyi hakuri ku d'auka a cewar kuma akanku hakan zata iya faruwa sannan kuma kowacce zata yiwa Abubakar addu'ar Allah ya sadashi da rahamarsa. Labarin gaske ne domin da Ummi Aisha itace zata yishi so bansan Stylish Bch ta bata labarin ba sai jiya. Kuyi hakuri harda masu cewa sundena karantawa sabida sunsan karshe dai Sadeeq zata aura suzo suna kishi da fateema🤭toh duk kuyi hakuri kuma sannan ku yafewa 'yar uwarku, da ace tun farko bansa muku true life ba wallahi akwai yadda zanyi na sauya salon amma yanzu kona sauya toh araina zan dingajin abun tunda nasan ba haka yake ba, duk wanda na 6atawa tundaga kan fara novel din har zuwa wannan pagen kuyi hakuri ku yafewa Hajja ce👈 'yar Adam ce kamar ku sannan kuma meyin kuskure a duk inda ta samu kanta, wallahi dana dinga ganin comments d'inku dakyar nayi bacci zuciyata na rawa Ina ganin ban kyauta muku ba ciki rayuwarku. Nasan da yawanku zaku dena karantawa toh Ina fatan duk wanda ya tsaya iya nan ya d'auki wani darasi a ciki amma Zan samu na k'arasa shi a WATTPAD dan nima na samu nutsuwar Zuciya. Nagode gaduk wanda suka karanta farkon labarin Allah ya sadamu da rahamarsa a cikin kabarinmu Amin Love you all m fan's❤🤝❤*
Page *22*
Hark'asa INdo ta tsugunna tana gaida shi idanta akan fuskarsa tace,
"Abba ina wuni?"
Ya zura wayar cikin aljihunsa yana kallonta ya amsa.
"Lafiya lau Aisha tashi kishiga daga ciki."
"Toh adawo lafiya."
Tafad'a tana mik'ewa ta nufi cikin gidan, tana shiga sallama tayi tana k'iran Haleema kamar yadda takeyi idan suka zo gurin da zasu had'u. Haleema dake zaune a falo tajiyo INdo na nemanta da sauri ta mik'e ta shige d'akin su dan bata son su had'u a cikin wannan yanayin. Mata tagani a zaune a falo wasu sunzo wasu kuma na shigowa Mama a gefe gurin kujera ta takure Umma kuma a bakin k'ofa INdo ta dinga binsu da kallo kafin ta k'arasa kusa da Fateeman Sadeeq ta zauna itama ta takure tana gaida su, suka amsa mata a sanyaye. Juyawa tayi tana lek'an fuskar Fateema wadda take faman hawaye a dai-dai fuskar tata tace.
"Kai amaryar malam menene kike kuka? Ko malam Sadeeq ne,dan nasan shi sarai tun a makarantar mu meh yayi miki..?!"
Zame jikinta tayi daga na INdo ta juya tana kallon Mama sai taga itama ta d'auke kai Fateema ta rasa yadda zatayi gashi INdon ta takura mata akan sanjin abinda takewa kuka,mutane dake shigowa ne ya k'ara sanya INdo cikin wasi-wasi kuma da sun shigo zasu samu guri su zauna a cigaba da zaman shiru sai kuma kallonta da ake yi. Mama ce tayi k'arfin halin yin magana tana kallon su fateema tace.
"Fateema jata kushiga cikin d'aki mana."
Hakan akayi kuwa suka shiga ciki nan INdo taga Haleema a mak'ure jikin gado sai shashekar kuka takeyi, cikin sauri ta k'arasa wajanta dayake Allah ya had'a jininsu da ita ta janyo ta da sauri cike da damuwa da nuna kulawa tace.
"Haleema Hali dubu kyakyawa, me kikema kuka kema?!"
Rungumeta Haleema tayi yayin da INdo tayi shiru tana rik'e da ita, ita INdo ba komai yake sanyata saurin kuka ba har sai abin yakai mak'ura sannan batada tsoro musamman a fagen magana kafin Haleema tayi magana Mama tashigo d'akin Fateema na zaune fuskarta cikin hijjab Mama ta rik'o INdo ita kuma jinta ajikin Mama yasa tayi murmushi sai taji tamkar Abubukar d'inne ya rik'ota.
A bak'in gado ta zaunar da ita can suka jiyo muryar Wata tsohowa mak'ociyar su ta shigo tana fad'in.
"Allahu akubar Garbati ankai sa'i, d'azu-d'azun nan yana fitowa daga gidannan ya lek'a zaurena muka gaisa yace min zai tafi birnin taraiya, Allah sarki kungani ya bani yaci inci goro Allah yajik'anka Garba.."
Ta k'arasa maganar tana nuna musu naira d'ari biyar d'in daya bata, a cikin d'aki INdo ta kalli Mama tana zaro ido tace.
"Mama waye Garba a gidannan da ya mutu?!"
Cikin dakiya Mama ta k'arasa wajan wardrobe tana cewa.
"Anan gidan yake Aisha zakiji ko waye."
Farin hijjab ta zaro tare da mik'awa INdo shi tana cewa.
"Ciro mayafin Aisha a ajiye shi."
Kamar yadda Mama tace haka tayi tasanya hijjab d'in Mama zumbulele sannan Mama tace ta zauna karta fito. Suna zaune zugum sai ta d'akko wayarta number'n sa ta k'ira cikin sa'a aka d'auka cikin zumud'inta tace mai.
"Salama alaikum my key kaje ko kakusa zuwa..?!"
Taji ance "Sorry hajiya me wayar yanzu haka Allah yayi mai rasuwa."
Da mamaki tace "Rasuwa kuma? Toma waikai waye ma tukunna?!
Kashewa akayi INdo ta zaro ido tana kallon wayar tare da furta.
"Rainin hankali toh ko fad'uwa wayar tayi wani ya sace shine zaice min haka. Aniyarka ta bika mugu 6arawo."
Ta fad'a su kuma Haleema dasu Fateema da wasu da suka shigo d'akin suka bita da kallo. Hawwa ce ta shigo tana kuka sosai saida tazo falo ta kuma 6arkewa da wani kukan tana shashek'a tace.
"Allah sarki Yaya Habu yanzu ya gama min waya Mama kinga kiran da yayi min yace gobe insa aje a d'akko min Humairansa... Tazo muyi hira da daddare a maida ita baya son ta zauna it...."
Ta kasa k'arasawa sai kuka, INdo ce ta fito fululum cikin hijjab jin muryarta ta k'arasa kusa da Hawwa ai Hawwa na ganinta ta janyota jikinta kukan ya tsananta amma bakin be fasa magana ba.
"Aunty Humairah kinyi rashi Allah yajik'an Yaya Habu yaso kuyi long life a tare sai gashi Allah ya d'aukesa ya barki...."
Muryar Mama ce ta katsewa Hawwa kukan da takeyi cikin fad'a tace.
"Amma dai ban ta6a sanin bakida hankali ba sai yau Hawwa, wannane wane irin hauka ne daga shigowarki sai kace ba gidan musulmai kika shigo ba. Toh kin gaya mata kinji dad'i tun zuwanta kowa ya kasa gaya mata saike wawuya kawai..."
Da sauri Hawwa ta kalli INdo sai taga ta kura mata ido fuskarta a murtuk'e tun daga nan kuma sai bakin mutane ya fara bud'ewa aka fara zance mutuwar kunnuwan INdo suka dinga jiyo mata ai yana tafiya har ya wuce Kaduna Allah yayi masa rasuwa.
Sosai hankalin Hawwa ya tashi ganin yadda INdo ta kafeta da ido hakan ya bata tsoro tayi saurin matsawa baya INdo ta bita cikin tashin hankali Hawwa tace.
"Aunty Humairah Lafiya? Please wannan kallon fa..?!"
A hankali INdo tasa hannu ta rungume Hawwa cikin rawar murya tace.
"Yaya Hawwa kema sokike Yaya Abubakar ya mutu? Yanzu na buga mai waya wani ya d'auka yace min me wayar ya mutu ashe kema sokike ya mutu? 'Dazu ni narakasu mota suka shiga shida malam Sadeeq amma meyasa kike son yayanki ya mutu? Kinga yana sona dayawa d'azu fa har cemin yayi yana son duk wani mesona kuma zai sani a makarantar abuja..."
"Kiyi hak'uri aunty Humairah nima inason Yaya Habu amma Allah yafimu sonshi shi yasa yayi hatsari..."
Hawwa ta fad'a tana kuma sakin kuka, da sauri INdo ta hankad'a Hawwa baya iya k'arfinta jikake gam..! ta bugu da kujera cikin kukan bak'in cikin maganarta yasa INdo cewa.
"Daga yin bikin mu shine zaki mana addu'ar ya mutu sabida bakya sonmu, toh insha Allahu sai Isyaku ya riga dacta mijina mutuwa fatanki ya biki, ance miki Garba ne ya mutu shine zaki zo kice Yaya Abubakar ne dan bak'in ciki..."
Umma ce tayi saurin toshewa INdo baki cikin rufewar ido ta fara tureta domin ta baya ta rik'ota ta kuma toshe mata. Cikin kwantar da murya Umma kishiyar Maman su Sadeeq take mata magana a hankali.
"Kinga Aisha kiyi shiru kinga mutane sun fara cika gidan yi hak'uri taho muje ki zauna kinji 'yar albarka."
Tana nishi Umma taja ta still bata dena yiwa Hawwa kallon banza ba duk kuwa da cewar ta girmeta nesa ba kusa ba amma cewar Abubakar d'inta ya mutu shine ya d'arsa wata k'azamar kiyayya a zuciyar INdo.
Fateema ce ta fito idanunta jawur ta kama hannunta suka koma cikin d'akin Mama, suna zama amma sai mita INdo takeyi Mama ta shigo ta kalleta tare da cewa.
"Aisha kidinga hakuri kinji ko?"
INdo tace "Toh Mama ki gaya mata bana son wasan mutuwa."
"Toh zan gaya mata tashi muje ki wanke fuskarki da sabulu."
Babu musu ta mik'e suka shiga bathroom saida ta gama wankewa sannan Mama ta kamo hannunta suka wuce, d'akin Abba suka shiga yana zaune yayi shiru yana bud'e likkafani gefe turare ne a kusa dashi suka shiga bayan Mama tayi sallama. Sake gaisawa suka yi da INdo sannan Abba ya kalleta tsawon lokaci ya kasa cewa komai, can dai ya nisa yace.
"Aisha ke musulmace ko?!"
'Dan murmushi tayi alamar kunya tana sunkuyar dakai tace,
"Eh Abba."
"Alhamdulillahi ina son sanar dake Abubakar dai Allah ne ya bani shi, nina raineshi tundaga zanin goyo har girmansa da temakwon Allah, bayan ya girma ya mallaki hankalinsa shida d'an uwansa suka d'auke min duk wani nauyi nasu dana k'annansu, kafin ya aureki ya nemi auran wata yarinya Allah ya k'adarta beyi ba sai dake, toh Allahn daya baki Abubakar Aisha ya k'ar6i abinsa domin yanzu haka suna hanya za'a kawo gawarsa ina son ki daur...."
Bek'arasa ba yaji ta fashe da kuka, kusa dashi ta rarrafo tare da rik'o Hannunsa tana jijigawa tana fad'in.
"Abba... Abba wallahi ba dacta bane, ba shine ya mutu ba shi yatafi abuja k'ila dai malam Sadeeq ne, dan Allah Abba karku ce haka wallahi yace zai dawo ya tafi dani can garan..."
Mama Abba ya kalla alamar tazo ta zanye ta, tana zuwa INdo ta juya kanta tare da rik'o hannunta itama tana cigaba da magana tana basu rabarin abinda yace zai yi mata nan gaba sai kawai itama Maman ta fashe da kuka Abba ya fara mata fad'a amma ina ta kasa yin shiru bare ta bawa INdon.
"Kutashi kuje yanzu suna hanya zasu kawo shi, karku sake kubarta tafita ko'ina kinajina...?"
Mama ta kad'a kai tare dajan hannun INdo suka shiga gidan sai ihu take mutane na kallonta cikin tsananin tausayawa.
Tana shiga ciki ta zu6e ak'asa jikinta sai rawa yakeyi aka rufa a kanta kowa sai nemar mata d'auki yake ta zame jikinta daga na wata mata tana kallon Matan tace.
"Sani zantafi."
Umma ta rik'ota itada Fateema ta fara tirje musu dama INdo yaya lafiyar kura, dacta ne yasanta ya kuma san yadda zai biyo mata gashi babushi dan haka abin nata ya kuma yawa.
Kullesu akayi a d'aki babu me fitowa suna jiyo kukanta har aka dawo daga d'akko gawar Abubakar, d'akinsu aka kaishi Sadeeq tamkar wani zararre fuskarsa fal hawaye idanunsa sunyi luhu-luhu tamkar kurji ya fito ya shiga cikin gida yana neman Mama. Da kyar ya iya tambayarta zani ta mik'e ta bud'e d'akin, suka shiga.
Gaidashi mutanan d'akin suke suna mai gaisuwa, yana furta "Alhamdulillah." INdo tayi zumbar ta mik'e daga ruk'on da Zulaihat tayi mata, lokacin Mama ta mik'a mai zannin ya k'a6a kawai yaji INdo ta mak'aleshi katak'am tamkar ba rik'on mace ba tana kuka tana cewa.
"Dacta ka dawoko? Nasan dama bazaka barni ba dan Allah da manzansa kace min Malam Sadeeq ne ya mutu ba kaiba, wallahi kaga zanyi kwalliyar da kace irinta d'azu, mu koma gidanmu nan kana da mak'iya ciki harda Abba duk fatan mutuwa suke ma..."
"Aisha sakar ni please."
Sadeeq ya fad'a yana 6an6areta daga jikinsa amma tamkar mutum biyu ne suka rik'esa, ya rasa dalilin dayasa takeja masa mugayan alkaba'i tun suna makaranta nan fa su Mama suka k'arasa suna nuna mata bashi bane amma tak'i sakinsa cewa take.
"Duk inda zahi zan bihi wata k'ila akwai masu bibiyarsa basa sonshi toni ina sonsa."
Janta yayi ganin ta mak'ale suka k'arasa bakin gado ya zaune tare da nunawa Fateema alamar tazo ta zauna kusa dashi. Tana zuwa INdo ta kare shi alamar karta ta6ashi Fateema ta toshe baki kuka na shirin kwace mata, haskilowa kawai takeyi tasan da shi ya rasu k'ila da tuni itace a cikin wannan yanayin da INdo take ciki.
Kabeer ne ya shigo ya kar6i zanin domin sam INdo tak'i sakin Sadeeq, Mama kuwa so take ta 6an6areta domin tasan hankan ba dacewa bane kuma INdo tashiga cikin takaba hakan yasa ta fara sanya ta cikin dokokin da musulinci ya tanadarwa ga duk macen da mijinta ya rasu...
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
Page *24*
Koda sukaje kauyan Sani bak'aramin mamaki Fateema tayi ba da ganin gidan su INdo da kuma kauyan da suke, lallai Allah ya d'aukakata daya aura mata Abubakar har kuma tashiga wannan uban gidan wanda yafi nata komai da komai. Basu jima ba Sadeeq yace zasu koma ya bada dubu ashirin Inna da malam Hamza suka dinga yi mai godiya amma INdo fateema kawai tayiwa sallama ta koma gida 'yan garin suka cigaba da zuwar musu gaisuwa.
Rayuwa gaba d'aya ta sauyawa INdo komai yayi zafi tunda ta dawo kauyan Sani komai nata ya canza, tana takaba a gidan su kamar yadda malam Hamza ya buk'ata sai dai itace inzata bayan gida sai abata sanda da wuk'a wai ta tafi da ita ko idan zatayi bacci toh ruwanta a buta da wuka wai mijinta yana biye da ita duk da cewar ba'a gidansa takeba. Sannan ta dinga tafiya a hankali karya tad'iyeta. wayace haka ake zaman takaba?wannan ba musulinci ya koyar dashi ba kawai mutanene suka maidashi al'ada har hakan ya fara zama kamar ibada. Satin INdo biyu a gida lokacin sati uku kenan da rasuwar Abubakar su Mama sukaje garin domin ita sam hankalinta ya kasa kwanciya, a zaure suka tarar dasu INdo suna tsinkar zogale harta fara komawa kalarta ta dah gashi dai jikinta da kaya masu kyau amma babu tsafta tunda ta dawo sau biyu tayi wanka wai ai duk cikin takaba ne. su Hawwah suka dinga kallonta cikin tsananin mamaki ita kuwa ta kasa 6oye farin cikinta da ganinsu.
Bayan sun gaggaisa ne Mama ta kasa yin shiru ta kalli INdo dake tsakiyarsu Haleema tace.
"Aisha ya naganki haka?duk kinyi wani iri anya kina wanka da kula da lafiyar jikin ki?!"
Cikin rashin damuwa tare INdo tace.
"Ai Mama nida nake takaba ai ance ba'a wanka sai dai a sati sau d'aya shi yasa ma banayi..."
"Subahanallahi inji waye ya gaya miki haka?"
INdo tace "Su Inna ne."
Inna nacan tana k'ok'arin had'a dambu ta samu tabasu suci Mama tace.
"Zonan Aisha na shiga uku ba haka ake yi ba a musulunci, ba haka qur'ani ya gaya mana ba."
Tashi INdo tayi zuwa kusa da Mama ta zauna Mama na kallonta cikin tsananin tausayawa ta janyo ta jikinta tace.
"Mecece Takaba Aisha?!"
INdo tayi shiru sai faman wulk'ita idanuwa takeyi Mama tace.
"Aisha Takaba dai itace Zaman da mace zatayi bayan rasuwar megidanta na wad'ansu kwanaki sanannu a cikin gidanta batare da tayi ado da kwalliya ba, ba kuma data kuma yin wani auren ba, ko sanya dukkan abinda zai ja hankalin wani a jikinta ba na tufafi ko kayan k'arau. Aanan Takaba ta sha babban da Iddar saki, shi yasa naso a barki a can domin d'an zaman da kikayi a gidan mu na gano cewar kinada gyara a cikin rayuwarki. Banda iyayanki sun kafe kancewar gara kitafi babu me zuwa ya zauna dake a cikin gidanki sannan kowa yasan mijinki ya rasu gashi idan kikaga Sadeeq wani tashin hankalin ne da bazan bari ba wallahi yanzu gashi kinzo nan sun k'ara dilmiyar dake cikin wani duhun kan.
Wallahi mahaifinki gaddama garesa Aisha ba yadda ba'ayi dashi ya barki ba yace dasun dawo bakwai za'a tafi dake sabida baya son abinda kikewa Sadeeq. Shin kinsan Gwargwadon kwanakin Takaba a musulunci Aisha?"
INdo ta girgiza kai alamar a'a Mama ta d'ago ta daga jikinta tace.
"Alokacin da mutun ya rasu, to zai bar iyalin shi ne a d'ayan hali guda biyu, kodai ta zama tanada Juna biyu ko kuma bata da shi. Idan bata da juna biyu to Takabarta itace tayi Wata hud'u da kwanaki goma Kamar yadda Allah yace cikin Suratul-Bak'ara _Kumma dukkanin mazan dake rasuwa daga cikin ku subar matayan su, to matan zasu zauna wata hud'u da kwana goma aya ta d'ari biyu da talatin da hud'u 234..._
To amma idan ya rasu ya barta da juna biyu a wannan lokacin k'arshen Takabarta shine ta sauk'e abinda take dauk'e da shi koda kuwa ranar da ya rasu ne ma'ana ta haihu ko tayi 6arin cikin. Misali ya rasu 10:00am na safe ita kuma ta haihu 10:05 na safiyar, shi k'enan ta kammala takabarta, idan wani ya gani yace yana so aka d'aura aure 2:30 na ranar aure ya d'auru _(ana k'ar6ar gaisuwa ana d'aurin aure)_ Dalili kuwa shi ne. fad'in Allah (s.w. a) a cikin Suratut-Talak aya ta 4 _Kuma dukkanin mata masu juna biyu to lokacinsu shine su sauk'e abinda suke d'auk'e dashi_ da kuma Hadisin Subai'a Al-aslamiyyah, Ita ta kasance tana auran Sa'ad Dan Khaulah, shi kuma ya fito ne daga gidan Amir d'an Lu'ayy, yana daga cikin wad'an da suka halarci yak'in Badar, sai ya rasu yabarta a halin bankwana tana da juna biyu, bata ko jima ba bayan rasuwar shi saita haihu, a lokacin data kamma biki sai tai kwalliya, sai Abu-Sanabil Dan Ba'akk yazo wurinta, shi kuma ya fitone daga gidan Abduddar, sai yace da ita Lafiya naga kin cancara ado haka, ko kina son ki aure ne? Na rantse da Allah lokacin auranki bai yi ba, harsai kin yi wata hud'u da kwana goma. Sai Subai'a tace Yayinda ya fad'a min haka maraice na yi sai na tattara kayana naje wurin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, na tambaye shi hakan, sai ya ban amsa da cewa ai na kamala Takabata tun lokacin dana haihu, ya ban dama da inyi aure a duk lokacin da naga dama. Yanzu ke Aisha kina da ciki?!"
INdo ta kalli Yayya Hawwah kafin ta maida idonta kan Mama tace "Wallahi ban sani ba nima." Mama ta sake kallonta sannan tace.
"Kinyi al'ada sanda kika dawo?!"
INdo ta sunkuyar da kai sannan tace,
"Ai yanzu ma haka inayi yau kwanana biyu kenan."
"Hazbunallahu wani'imal wak'il, yanzu duk da kina wannan jinin Aisha bakya wanka?!"
INdo tayi shiru jin yadda Mama tayi magana da alama abin mamaki ya bata da haushi ita kuma ya zatayi tunda ance mata haka akeyi. Inna ce ta shigo tana tayi musu sanna tare da kawo musu ruwa a kwanan shin ruwan malam Hamza, tsabtar kyawun kwanon da yadda ruwan ciki yake garai-garai abin sha'awa shine ya sanya su Haleema shan ruwan gidan.
Zama Inna tayi suka sake gaisawa Mama tayi gyaran murya bayan tace su Haleema su fita, suna fita tayi murmshi tare da cewa.
"Dama munzo ne mu gaida ku sannan zamu tafi da Aisha za'ayi mata wani gwajin ciki sabida shi marigayi yace yasa mata wani abu wanda koda tana da ciki toh bazata dena jinin al'adaba toh yanzu shine zamuje a duba agani kar abar mata abu ba'a saniba ko yana amfani nan da kwana biyu za'a dawo da ita kinsan likitocin nan da k'ak'ale."
Mama ta kifa Inna domin yanzu so take ta tafi da INdo can. cikin rashin damuwa Inna tace "Allah sarki ai babu komai an zama d'aya bari na aika a k'ira malam dama shine ai ke hanawa da yaji yadda takeyi idan taga shi d'an uwan marigayin."
Fitowa tayi ta lek'a waje ta samu yaro yaje ya k'ira Malam Hamza a gurin sana'ar Sa. Tare da ila suka dawo tunda yaga mota yasan bak'i sukayi yana shiga kuwa Inna tace Maman marigayi ce tazo, d'akin ya shiga suka gaisa da Mama Inna kuma ta kawo mata dambu ta kaiwa su INdo ma. A nan Mama ta kuma tsara malam Hamza yayi jim sannan kamar bazai yadda ba sai kuma yayi murmushi yace.
"Toh ai dama ni hajiya dalilin daya sa na kafe kan cewar saita dawo nan, gani nayi yadda shi Saddiqu suke tsananin kama dashi marigayin. Sannan tun a gurin gaisuwar naji ana zance ta fara rik'esa tana cewa be mutu ba harma sun fara samun sa6ani itada Saddiqun wannan dalilin yasa nace dole abani ita mu dawo nan zaman lafiya hajiya ai yafi zama d'an sarki. Amma yanzu tunda akwai wani dalili wanda kuma kune kuke da hakk'i akai toh saita shirya ku tafi idan an kammala yi mata sai a dawo da ita ai duk an zama guda.."
Wani farin ciki ya lullu6e Mama sai ta share hawaye gani takeyi tamkar Abubakar d'in take yiwa a zahiri. Malam Hamza ya dinga bata hak'uri kafin ya tashi ya fita, gurin su INdo yaje yace ta shirya zasu tafi da ita.
Wanka Mama tace tayi sannan tayi tasa kaya Mama ta girgiza kai domin duk kayan na kwalliya ne babu wanda aka ce na takaba ne dole idan sunje tasa a dinka mata wasu marasa style. Babu wanda yasani don Mama tace kar a fad'awa kowa kawai idan an tambaya tana Ina suce tana gidan su marigayi amma karsu sanar da kowa akwai abinda za'ayiwa INdo suka tafi cikin farin ciki da fatan alkairi.
*****
Tunda suka maida ita Mama ta dakatar da Sadeeq zuwa gidan tace koda itace batada lafiya bata yadda ya shigo ba bare hakan nan. Haka kuka Mama ta cigaba da kula da INdo har aka yi arba'in d'in marigayi Abubakar sannu a hankali kuma Mama tana bibiyar al'amranta na addini tana gyara mata sannan tana k'ara nusar da ita abubuwa wad'anda mafi akasari suke k'ara tunawa INdo mijinta soyayyarsa kuwa bata ta6ajin ta kankare koda d'igo d'aya ne, bata komai sai dai taci tasha tayi bacci, idan kuma su Haleema na nan sai suyi hira d'an turancin da suke yi jefi-jefi itama ta d'an fara tsintar k'ananun tana had'awa da wanda Dr yake yi mata sai dai dakyar take iya rik'ewa dan sai tayi ta rik'e kalma d'aya a kwana biyu ko uku sannan take sake fahimtar wata word d'in.
Kusan kullum sai Malam Hamza ya bugo musu waya tunda suka zo sadakar arba'in ya kar6i number abban su Sadeeq kusan kullum sai ya bugo musu yaji wai ko an cire mata abun sai suce a'a likitocin sun k'ara musu kwanaki da haka har INdo tayi watannin takabar ta wanda har lokacin Sadeeq baya shiga cikin gidan su dan ma Allah ya temake sa yana tafiya k'wara state dan wannan tafiyar tasa da Fateema sukayi sabida yana shan wahala.
Ana sauran kwana biyu INdo ta kammala takaba su Sadeeq suka dawo, Fateema ce kawai taje gidan shi kuma su Mama suka fita parking space suka gaisa ya juya ya tafi.
Ranar da INdo ta kammala takaba Abba ya k'ira Sadeeq yaje ya kaisa Sumaila suna zuwa ya samu malam Hamza bayan gaisuwa Sadeeq na mota a zaune ya bugawa Fateema waya suna hirar soyayyar su dan haka suke tamkar zasu cinye junansu Abba ya kalli malam Hamza yace.
"Toh malam Abubakar dai Allah ya d'auki rayuwarsa a lokacin da yake tunanin ya fara rayuwa, ya tafi yabar matarsa yarinya d'anya yau gashi Allah yasa ta kammala takabarta kamar yadda addini ya tanadar. A zahirin gaskiya ba wani abu da marigayi ya sanyawa Aisha a jikinta, me d'akina ce taga bazata iya barin muku Aishan ba hakan yasa tayi muku dabara kuka bata ita mu kuma duk muka had'e muku kai muka nuna cewar eh lallai haka ne abinda ta fad'a."
Malam Hamza yayi murmushi tare da cewa.
"Ai munyi mamaki har muna tunanin k'ila abin k'in fita yayi ashe soyayya ce tasa kukayi hakan ai bakomi alhaji mune da godiya da baku nuna kyama a garemu ba, Habubakar shine sila hakan yasa bazan gajiya dayi masa addu'ar samun ni'ima a cikin makwancinsa ba, alhaji Allah yajik'ansa yayi masa rahama mun gode madallah."
"Ba komai malam Aisha ma ai 'yata ce, sannan kuma babban abinda ke tafe dani shine. Kaf 'yan uwana da masu d'akina suna tausayawa Aisha, yarinya ce d'anya yau gashi Allah ya jarabce ta idan aka barta zata Shiga layin zawarci, sun had'u sun had'e kai wajan ganin bazasu iya bari matar d'ansu d'an uwansu abokinsu ta zauna a haka ba suna ganin yi mata hakan kamar basu rufawa Abubakar asiri ba hakan yasa ko wannen su yazo min da k'ok'an barar su na cewar mezai hana a mayeta da abokin haihuwar sa, ma'ana mu had'asu aure da Sadeeq domin rufin asirin mu gabaki d'aya sannan munsan Abubakar zai yi alfahari da wannan abun."
Malam Hamza yayi shiru kafin yaje ya k'ira Inna ya kuma k'ira amininsa malam kallah suka zauna, Abba ya kuma maimaita musu zancen auran INdo da Sadeeq Inna dai bata ce komai ba tace sune maza masu d'aura aure dan haka ita addu'a ce kawai tata. Bayan Inna ta koma gida malam Hamza ya amince wasu mutanan suka zo a gurin aka d'aura auran INdo da Sadeeq Abba ya bada sadaki dubu ashirin Sadeeq yana mota a zaune duk wainar da aka toya besani ba har Abba yayi sallama da mutanan garin ya shiga mota Sadeeq d'in ya ajiye wayar suka tafi...
#MZ
#Fan's
#luv-all
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
Page *25*
Har sukaje gida Abba be sanar da Sadeeq ba, suna zuwa Abba ya shiga gida shi kuma Sadeeq daya k'agu yaje gida ya juya kan motar ya tafi. Abba na zuwa fuskarsa cike da fara'a ya cewa su Umma.
"Toh hajiya A'i an d'aura aure yau."
"Alhamdulillah Allah ya sanya musu albarka ya kauda fitina ya basu zaman lafiya."
Cewar Umma nan da nan fa gida ya cika da murna INdo kuwa bacci take a lokacin sai bayan da ta farka ne Mama tace.
"Aisha jeki wanka kizo kuje gyaran kai."
Da sauri INdo ta mik'e cike da murna domin tunda ta dawo gidan bata sake koda lek'awa k'ofar gida ba, sam sun hanata ko unguwa Mama zasu sai ta kafa mata doka akan idan ta kuskura ta lek'a waje, yau gashi zata fita kusan kwananta d'ari da takwas raban da ta kalli waje bare taga abinda yake wakana. Ta yi kyau tayi haske fatar jikinta tayi luf-luf sannan tayi k'iba da yake hankalinta a kwance yake suna kula da ita sosai dan ko 'ya'yan gidan basu kaita jin dad'i ba.
Wanka tayi tana fitowa taga saban d'inki an d'akko mata a can gidan Abubakar da takalmi da jaka da mayafi su d'ankune sark'a da kayan kwalliyar su Haleema. Zama tayi tana kallon kayan tare da shafa jakar da takalmin sai hawaye a fili tace.
"Allah sarki dacta kai ka saimin su.."
Tashi tayi tasa kayan sai ga Mama ta shigo cikin wasa tamkar ba suruka ba tace.
"Toh wa kika tambaya da kika d'auka kika sa? Idan kuma nawa nefa..?!"
Dariya INdo tayi tana rufe baki tace,
"Ai Mama ina ganin jakar na gane su, lokacin da zai kaimu gidan abokanansa da nad'akko zan rataya yace min basu yi match da kaya na ba na ajiye ta."
"Allah sarki Abubakar Allah yayi masa rahama Allah yayi baxaku yi tsawon kwanaki tare ba."
Cewar Mama tana d'akko mata humra ta ajiye mata a kusa da kayan tana cewa.
"Daga yau zaki iya sanya komai Aisha sai dai zaki ci gaba dayin abubuwa irinna matan aure domin yanzu kema Matar aure ce."
Sam INdo bata gano inda zancen Mama ya nufa ba, a tunaninta tunda ta ta6a aure toh zata ci gaba da suturce jikinta da kuma d'ora mayafi aka. Tana gama shiryawa Mama ta bata kud'in gyaran kai tasa suka tafi dasu Haleema.
Lokacin da ta fara zura k'afarta a waje ji tayi tamkar yau aka haifeta. Wata ajiyar Zuciya ta sauk'e tare da kallon ko'ina na wajan taga mutane kowa yana harkar gabansa, wasu kuma da suka santa suna sake yi mata gaisuwa tana amsa musu har suka kai bakin titi Haleema ta tare musu napep suka shiga.
Shagon saloon suka shiga sun d'an jima sannan suka fito suka dawo gida. Da dare bayan Abba ya dawo ya k'ira Sadeeq sannan ya k'ira INdo, Mama da Umma duk suna zaune a d'akin. Cikin muryar ta med'an k'arad'i tayi sallama tare da shiga ta zauna tana gaida Abba.
A hankali Sadeeq ya d'ago ya kalleta sannan ya kawar da kai cikin ransa yana tambayar dama tana da ladabi ko kuwa har lokacin mutuwar mijinta na jikinta ta dai kusa tafiya shima ya samu 'yancin shiga gidan ubansa.
Abba ne ya k'ira sunansa ya amsa tare da kallonsa abban yace.
"Toh Sadeeq kamar yadda ka sani tagwai d'inka Allah yayi masa rasuwa ya bar matarsa, yau kuma Allah ya nuna mana cikar wa'adin takabar ta kamar yadda addini ya d'ora mata. Sadeeq kaine mutum na farko daya kamata ya rufawa matar d'an uwanka asiri ka dubi halin da zata shiga idan ta koma garin su ka kuma dubi k'ank'antar da tayi a matsayin bazawara bawai munaja da ikon Allah bane a'a duba da yadda rayuwarta zata fad'a yasa muka yanke wani hukunci akai."
"Babu komai Abba ni dama tuni nayi alk'awarin zan dinga tura mata kud'i sannan zan dinga yi mata abinda take buk'ata idan har befi k'arfina ba dama jira nake ta kammala iddar sai na tambaye ta abinda yak'e matsalarta."
Sadeeq ya fad'a ba tare da ya kawo komai ba dan sam beyi tunanin wani aure tsakaninsa da ita ba, Fateema yake so kuma ita ya aura baya tunanin zai yi *MUSAYAR ZUCIYA* da watanta nan gaba bare kuma nan kusa daga yin aure wata biyar.
"Toh Sadeeq ai wannan abubuwan daka fad'a koni zan iya yi mata shi, mu yanzu fatan mu ka rufa mata asiri a matsayin ta na mace me rauni kuma matashiya domin a d'azu da ka kaini Sumaila k'auyan su naje ne mun d'aura muku aure dakai da ita ka maye gurbin d'an uwanka...!"
A matuk'ar razana Sadeeq ya zaro idanuwa yana kallan Abban shi, zuciyar sace take rawa jikinsa na tsuma ya kalleshi yace.
"Abba wani auran zan kuma yi? Abba ko wata biyar ban cikasa ba ace na kuma yin aure? Tayaya zan iya zama da mata biyu Abba bayan yanzu nayi d'ayan? Abba matar twin d'in zan aura? Ya akayi mutuwa tayi min haka..."
"Kai ya isa haka karkayi min sakarci kaji ko? Idan baka aureta ba ya kakeso tayi bayan tana buk'atar temako da kuma mai lallashi da tausayawa a gareta...?!"
"Amma Abba yau yau d'innan fa tayi takaba amma ace ayau za'a aura mana aure ko fuskanta juna bamuyi ba? Abba ya Fateema zataji wannan labarin."
Ya fad'a tamkar wani maraya Abba ya wurga mai harara cikin 6acin rai yace,
"Da kuma ace kaine ka rasu aka ce Abubakar ya auri Fateeman zakaji dad'i ko kafison ta tafi ta auri wani bare..?!"
"Wallahi Abba gara ta auri bare haba-haba sai kace jira, dan Allah Abba kuyi tunani ni wallahi..."
Bek'arasa ba Abba yayi saurin katse sa ta hanyar cewa.
"Toh shikenan sakarta ni sai na aureta shikenan hakan yayi maka.?!"
Cikin tashin Hankali Sadeeq ya kalli mahaifinsa sai zuba uban gumi yake baki na rawa yace.
"Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un Abba ai babu aure tsakanin ku gara nid'in."
"A'ah aini tausayinta nakeji Sadeeq kuma abinda zanyiwa Abubakar kenan yasan nayi mai kara ka sake ta sai na aureta ko kuma uncle d'inku Ahmad."
"A'a Abba dan Allah ka rufa mana asiri na kar6i auran Allah yajik'an m twinnie yasa can tafiye masa nan."
Duk suka amsa da amin banda INdo wadda tunda taji maganar da akeyi tayi kicin-kicin zuciyarta banda bugawa babu abinda takeyi wani rad'ad'i na shigarta. Abba ya maida hankali wajan ta ya kalleta cikin kulawa yace.
"Aisha muna fatan bamuyi miki shishigi a cikin rayuwarki ba, muna fatan zaki yadda da auran Sadeeq gashi nan komai nashi iri d'aya ne dana marigayi..."
Da sauri INdo tace "A'ah Abba wallahi ba halinsu d'aya ba koda can kafin mu saba."
Abba ya kalli Mama itama shid'in take kallo sannan tace.
"Aisha ai shima Sadeeq zai miki abinda marigayi yayi miki kiyi hakuri idan kuma bakya sonshi shikenan ai ke yanzu babu batun yi miki auran dole za6i gareki a wannan karan ma. Dama munyi haka ne dan karki shiga damuwa ko da idan kinga Sadeeq d'in."
Shiru tayi batace komai ba sukayi-sukayi tayi magana amma tayi shiru Umma tace.
"Toh da alama ta yadda Allah ya bada zaman lafiya."
Tashi Sadeeq yayi ya fita Mama da INdo suma suka fita aka bar Umma kasan cewar itace da girki ranar.
Dakyar ya iya kai kansa gida, lokacin daya shiga Fateema na kwalliya cikin bedroom taji shigowarsa amma bata ga ya shigo d'akin ba, shi kuwa guri ya samu a falo ya zauna kan kujera tare da dafe k'irji kanshi na barazanar fashewa ya tarwatse.
Fateema ce ta fito cikin shirin bacci tayi kyau ta kuma fari kai da kaganta kasan tana cikin kwanciyar hankali, k'arasawa tayi kusa dashi ta d'are kan cinyarsa tana k'ok'arin d'ago mai kai. Janyo ta yayi jikinsa da k'arfi tare da sanya ta a k'irjinsa ya matseta da hannuwansa tamkar zai maida ita ciki ita kanta dakyar take numfashi zuciyar ta cike da mamakin yadda taganshi.
"Wayyo Allah baby zaka karya ni."
Ta fad'a tana k'ok'arin kwatar kanta sabida ba k'aramin azaba takesha a matsar ba. A hankali ya sassauta mata rik'on dayayi mata cikin sanyin murya Fateema ta kallesa tace.
"Baby wai meyake damunka, haka kashigo fa ba sallama kuma naga duk jikinka a sanyaye meya faru..?!"
"Bakomai kinci abinci dai ko?!"
Ya tambaya yana shafar cikinta, kad'a kai tayi tana kallon shi ya lumshe idanuwa tare da kwantota jikinsa yace.
"Toh why?!"
"Baby kasan dai bana iya ci harsai kana nan, meyasa yanzu kake tambaya na...?!"
"Kinsan ai bana son kina zama da yinwa, kinga gobe ina da lecture 9 to 11 kuma gashi banajin dad'in jikina ya zanyi ne.."
Fuskar sa ta tallafo sukayi kallon cikin ido ta sakar masa murmushi tana shafar gashin dake ha6arsa tace.
"Yanzu ai lokaci bek'ure ba goma da rabi saura minti uku kayiwa class captain waya kace musu bazaka samu damar zuwa ba suyi hakuri zaka samu wani time d'in sai kuyi musu amfani dashi..."
"Ai kuma baby ban musu lectures bafa tunda aka koma gashi har an fara tambaya na exam questions, zanje ko abu d'aya ne nayi musu tashi muje kici abinci."
"Inci abinci ko dai muci abinci?!"
Ta tambayesa tana sake lafewa a jikinsa, suna zama yana cewa.
"Kinsan Abba neya k'irani so munci abinci tare dashi."
'Dan hararasa tayi tare da cewa "Ai kasan dai nima nawa yana jiranka dan haka sai kaci babu wani batun kunci da Abba ko zakayi amai kuwa."
Shi sam yarasa ma mezai yi yinwar ma bajinta yake yi ba shi yasa yace mata haka amma dan karta shiga damuwa sai yace.
"Toh baby na ya zanyi amma nasan yau babu abinda zan iya tabuk'awa."
Shi dai dakyar ya samu yaci duk tunanin yadda zai 6ullo mata yake yi a cikin zuciyarsa, sai da ya tabbatar taci ta koshi sannan ta rakashi yayi wanka ta bashi sleeping gown ta maza yasa sannan suka bi lafiyar gado. Kamar yadda ya sabar mata koda bazai yi komai ba toh sai sunyi wasa haka yauma har sai da yaga ya kwantar da kanta kan k'irjinsa zata yi bacci ya bud'e baki dakyar ya k'ira sunanta.
"Zarah..."
Tayi jimmm jin yadda ya k'ira tsohon sunan da yake kiranta dashi tun suna saurayi da budurwa, can dai ta amsa mai tana shafar k'irjinsa shi kuma yana shafar himilin gashin kanta domin akwai suma yace.
"For example nine na rasu ba Abubakar ba idan aka ce ki auresa zaki iya..?!"
Ya k'arasa maganar yana d'an d'ago mata kai. Shiru tayi na tsawon lokaci tana tunanin abinda yasa shi yi mata wannan tambayar marar dad'in ji bare sauraro, sai da ya sake tambayar ta sannan ta numfasa dakyar tace.
"Haba baby ya zaka min wannan tambayar tunda dai bakai ne ka rasun ba?"
Yace "Eh so nake naji zaki yadda idan aka ce ki auri twinnie d'ina ya zakiyi."
"Gaskiya bazan auresa ba haba ai bashi na aura ba."
"Toh idan aka tursasa kifa ko aka aura miki shi ba tare da kin sani ba ya zajiyi..?!"
"Ta6 d'i wallahi baby sai ya sakeni uhm'um ni dan Allah ka dena yin irin wannan tunanin please."
Jikinsa ya sake janyo ta yana shafar bayanta, so yake ya sanar da ita yau basai taji a bakin wani ba amma ya rasa hanyar fad'ar ya dai daure yace.
"Toh idan hakan ta faru tunda ni bakya sona mutu aka ce na auri Humairah ya zakiyi?!"
"Bama zata yiwu ba sabida INdo bata sanka har agabana ta fad'a."
Shiru suka yi na tsawon lokaci gashi dare ya tsala ko'ina yayi shiru sai k'arar gen d'insu kawai akeji. Numfasawa Sadeeq yayi tare da janyota yace.
"Kiyi hakuri baby na yanzu dawowar da kikaga nayi Abba ne ya sanar da ni cewar an d'aura min aure da ita ni kaina ba..."
Jiyayi ta mik'e zaune a razane daga ita sai bra domin rigar ta zame Fateema ta bishi da kallo hannunta dafe da k'irji ya kalleta bayan shima ya tashi zaune. Wata shegiyar harara take wurga mai cikin zafin rai ta fara magana jikinta na rawa.
"Yanzu kana nufin har an d'aura muku aure?"
Sadeeq ya d'aga mata Kai alamar eh yasa hannunsa ya janyo ta a hankali ta fad'a jikinsa ta saki kuka me ban tausayi ya fara lallashinta shi kansa ji yake tamkar yaje ya bindige INdo. Babu yadda zatayi ita kuma haka tata k'addarar take daga yin aure sai kishiya suna cikin more rayuwarsu.
***
A 6angaran INdo kuwa wani uban nishi ta dinga saukewa duk iya k'ok'arin Mama na ta gaya mata matsalar ta sam tayi shiru tak'i yin magana har gari ya waye bata yiwa kowa magana ba Mama ta rasa dalili dan ta saki ranta yasa Mama cewa.
"Aisha gobe za'a kaiki gida kije kiyi kwana biyu kafin Sadeeq d'in ya ware yadda zai yi."
Sai a sannan INdo tayi magana tana dariya tace.
"Toh Mama amma dai ba shine zai maida niba...?!"
"Toh ai Aisha yanzu dai komai yana hannunsa sai abinda yace kiyi mai biyayya kedai anan zaki samu aljanna."
Ba zato cikin subutar baki tace.
"Ta6 d'ijam.."
Mama ta kalleta cikin mamaki amma sai taga INdon na mutsu-mutsu da baki alamar magana take a ranta lallai yaran nan da alama zasu basu mugun mamaki sam basuyi zaton INdo zatak'i Sadeeq ba ganin yadda suke kammani da mijinta ba....
#MZ
#Fan's
#luv-all
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
*A gaskiya ina alfahari daku masoya, comments d'in ku yana sani jin dad'i both wattpad & WhatsApp. Bazan iya lissafo sunayanku ba sai dai ina yiwa duk wata mai bibiyar labarin nan fatan alkaira Allah kuma yabar kauna da soyayya love you all*❤
Page *26*
A 6angaran su Sadeeq kuwa dakyar ya iya fita lecture, itama Fateema bata fasa yi mai breakfast ba sai dai duk babu wanda ya iya ci. Yana tafiya Fateema ta shiga cikin d'aki taci kuka sannan ta d'auki wayarta ta k'ira Ummanta, tana d'agawa ta fashe da kuka hankalin Umma yayi matuk'ar tashi tana tambayar lafiya.
"Kiyi shiru kiyi min magana dan sai kin min bayani sannan zansan matsalarki."
Cewar Umman ta cikin lalla6ata dan ta gaya mata. Cikin kukan Fateema tace.
"Umma Sadeeq ne ya k'ara aure jiya..."
Tayi maganar muryarta na hard'ewa hankalin Umman ta ya tashi tace.
"Fateema a ina yayi auran bako labari?"
"Umma yazan yi matar d'an uwansa aka aura mai jiya shima be sani ba, sai da Abban su ya k'irasa ya gaya mishi."
Ji tayi Umma ta sauk'e ajiyar Zuciya hankalin Fateema ya tashi tana cikin bargo amma wani irin mugun sanyi takeji yana ratsata, jita yi Umma na cewa.
"Oho Allah sarki, Fateema toh karki damu kinga kema wannan kaddarar batak'i ta sauka a kanki ba, kiyi hakuri ki zauna ki taya mijinki zama da ita ba'a san abinda Allah ya shirya ba akan al'amarin. Ina son ki kwantar da hankalinki karki sake ki nuna masa cewar kina bak'in cikin wannan auran idan kikayi haka nan gaba kezakiji kunya sabida shirin na Allah ne dan da be d'auki Abubakar ba da hakan baxata faru ba, ki kankaro mana mutuncin mu ta hanyar k'ar6ar wannan auran cikin nuna farin ciki koda ba hakan bane a ranki."
Wani irin kuka Fateema ta kuma fashewa dashi wanda da kyar ta iya yin sallama da Umman tata. Kuma k'udindinewa tayi a cikin bargo tana cigaba dayin abinta har zazzafan zazza6i ya sake rufar mata.
Sadeeq kuwa yana kammala lecture ya fito daga school d'in, kai tsaye ya wuce gidansu Fateema ya samu ba kowa sai Umma. Shiga yayi har cikin falonta ya zauna suka gaisa cikin fara'a ba tare da ta nuna mai komai ba.
Cike da ladabi Sadeeq yayi ma Umma bayanin yadda lamarin ya wakana sannan ya dad'a da nunawa Umma ta yiwa Fateema nasiha tare da tayashi bata hak'uri, Umma tayi murmushi tare da cewa.
"Karka damu Sadeeq Allah ne yasan abinda ya shirya har akan ta faru, insha Allahu kuma zanyi mata nasiha kaima sai kayi hakuri kasan irin wannan lamarin sai mutum yana kawar dakai dan zakaga ban-banci d'abi'a akan ta baya da kuka yi."
Sadeeq yana sunkuyar dakai yace,
"Insha Allahu Umma na gode Allah ya k'ara girma."
"Amin a gaida mutanan gidan ace muna yi musu Allah ya sanya alkairi."
Batare daya amsa mata ba yayi tafiyarsa baya tunanin ma zai sake zuwa gidan harsai ya samu labarin cewar INdo bata gidan.
A kwance ya tarar da ita ko gidan bata bud'e ba sai da ya sanya mukulli ya bud'e. K'arasawa yayi tare da yaye bargon da ta rufa dashi ya ta6a jikinta mai d'auke da zazzafan zazza6i nan da nan hankalinsa ya tashi ya hau gadon gabaki d'aya ya d'aga zuwa jikinsa yana k'ok'arin san su had'a ido amma tak'i bari hakan ya faru.
"Baby na kinji jikinki kuwa? Meya sameki?!"
Wani kukan ne ya sake zuwar mata cikin rawar murya tace mai.
"Banajin dad'in jikina kaina ciwo yake."
"Oya tashi muje asibiti Allah yasa ma nayi ajiya."
'Dan janye jikinta tayi ba tare da ta kallesa ba ta koma ta kwanta tana cewa...
"Karka damu basai munje asibiti ba dan yanzu ma haka ciwon mara nakeji."
"Wayyo Allah baby na bana son wannan abun wallahi, nida da yadda za'ayi ma da nasa an tsayar miki ki denayin sa."
Shiru tayi mai batayi magana ba shi kuwa duk so yake yi ta dawo dai-dai yadda suke amma ina sai tashi yayi ya koma falo dan bazai juri ganin yadda take sharesa ba, ba kuma yason ya dinga 6ata mata rai.
Yana zaune a falo yana transfer d'in kud'i a account d'in mutanen daya k'ar6i kaya yaji wayarsa na ruri, d'auka yayi yaga Mama sai da k'irjinsa ya buga. Addu'a ya fara yi Allah yasa kar tayi mai zancen INdo domin sam baya k'aunar yaji sa.
"Hello Mama antashi lafiya?!"
"Eh Alhamdulillahi tunda bakaga damar zuwa ba, mekakeyi yanzu?!"
"Kiyi hakuri Mama bak'in zuwa nayi ba yanzun nan na dawo daga lecture, ina gida nazo?!"
"Eh dama cewa zanyi ka shirya kazo kakai Aisha garinsu ta d'anyi musu kwana biyu kafin ka samar mata gurin zama."
Had'e rai yayi tamkar a gaban Maman ransa na suya baya son kuma komawa garin nan duk da cewar sunyi zaman amana dashi amma a yanzu ga Fateema ba lafiya sannan ance yazo yakai INdo garinsu sabida kawai shi aka sakawa ido komai sai ace shi dama shi ya mutu ba Abubakar ba da duk ba'ayi mai wad'annan abubuwan ba.
"Kayi shiru Sadeeq kona shirya tunda nina d'akkota sai na mayar da ita."
Yaji Mama na fad'a cikin fad'a-fad'a. Lumshe idanuwa yayi tare da shafar sajan sa yace.
"A'a Mama kiyi hakuri bari nayi wanka zanzo."
"Toh shikenan kazo kowane lokaci ne sai ka kaita duk ka gama walagigin naka muna nan muna jiranka."
Tana kammala fad'a ta katse k'iran shi kuma yabi fuskar wayar da kallo, shikam ya shiga uku wannan wace irin kaddara ce ta hau kansa. Ya kasa gane abinda Abubakar ya gani a gurinta har yaji yana sonta, ita ba ilimi ba sannan ba Kud'i ba, ba wani shegen kyau ne da itaba sai shashanci ga6untaka kauyanci da rashin wayewa duk ita kad'ai shikam a takaitashi da auranta da aka bashi.
Tashi yayi cikin sanyin jiki ya shiga d'aki, fuskar fateema ya kalla sannan yaje ya shafa fuskar yana kallonta. A hankali ta bud'e sukayi ido hud'u yace.
"Tashi kisha magani kici abinci zansa su Haleema suzo su tayaki zama Mama ta kirani wai zankai Aisha gidan su yanzu kinji.?!"
K'irjin Fateema ya fara harbawa ganin tun yau sun fara raba abubuwa tsakaninsu, da kyar ta daure tace.
"Toh sai kun dawo amma kabar su Haleema basai sunzo ba babu abinda zasu yi min."
Magani ya d'akko ya fita kitchen ya d'akko ruwa sannan ya zauna kusa da ita, dakyar tasha maganin sannan ta kwanta shi kuma ya shiga cikin bathroom yayi wanka gaba d'aya ma besan abinda zaiyi ba akan INdo.
Fitowa yayi d'aure da towel a k'ugunsa ya k'arasa wajan mirror duk Fateema na kallonsa a sace ta cikin bargo. Sai daya gama goge ruwan jikinsa sannan ya zauna kan stool yana shafa mai. Yana gamawa ya nufi wardrobe ya zaro wata shadda blueblack ya sanya tare da d'akko bak'ar hula zannah ya kafa kan goshi, ya sanya agogon hannu ya zura takalmi bak'i tare da feshe jikinsa da turare ya d'auki comb brush ya kwantar da gashin daya zagaye kyakyawan bakinsa.
Duk abinda yake yine yayi amma da Fateema tasan inda zashi sai taji k'irjinta na harbawa zuciyarta na zafi wani bak'in kishi ya mamaye ciki da wajan zuciyarta bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba tayi saurin maida fuskarta cikin bargon ganin zai juyo.
Sadeeq ya k'arasa gurinta bayan ya durk'usa saitin fuskarta ya kura mata ido.
"Babyna karki dinga sanya ranki cikin damuwa, kece mace ta farko dana faraso na kuma fara aura na fara baiyana mata sirrina na kuma yadda da ita, ina so ki dinga alfahari da hakan kina cikin zuciyata bazan ta6a yadda wani ya 6ata miki rai ba ko ya gaya miki ba dad'i in kyalesa.
Ke ko Aisha da aka aura min idan batayi miki biyayya ba sai na sa6a mata wallahi ke nine nace ina sonki ita kuma mutuwar twinnie d'inane yasa aka bani auranta karki dinga damuwa kinji ko.?!"
Sai a lokacin Fateemah taji sanyi ko ba komai ya kwantar mata da hankali da dad'ad'an kalamansa masu zak'in zuma. Kallonsa tayi idanuwanta duk sunyi jah tsabar kuka sannan ya zuro hannu ta shafi fuskarsa tace.
"Nagode da wannan matsayin daka bani, ka tashi kaje kaga da nisa Allah ya dawo min dakai lafiya, a gaidasu Mama."
Murmushi yayi mata tare dakai bakinsa kan nata yayi kissing d'inshi sannan ya mik'e tsaye yana ce mata.
"Amin babyna sai na dawo."
Fita yayi ya shiga mota yabar gidan.
Kai tsaye gidan Mama yayi, a k'ofar gate yayi parking sannan ya fito ta shiga gida cike da tak'ama dan yau jinsa yake tamkar akan iska. Yana shiga k'annansa suka hau gaidashi ya amsa musu sannan ya lek'a d'akin Umma ya tarar tana sallar azahar ya koma ya shiga d'akin Mama.
Cike d'akin yake da k'amshin turaran humra Sadeeq ya bud'e hanci yana shak'a, tsaye yaga INdo ta gama d'aurin d'ankwali ya kalleta tare da jinjina kai. Idan besan asalin INdo ba da ace yau shine karo na farko daya fara ganinta toh bazai mata hausa ba dan babu abinda zai hanashi d'auka cewar batayi degree ba a boko. Sai dai kashhh shine yasanta yasan ko wacece a fannin dak'ik'anci da rashin son karatu tun batakai haka ba dan haka yana shiga gurin Mama ya nufa yana mai cire hular kansa.
"Mama na ina wuni?!"
"Lafiya lau Sadeeq na d'auka ma bazaka zo yanzu ba, ya gidan ya Matar taka?"
Sadeeq ya koma bakin gado ya zauna yana cewa.
"Haba Mama na isa ink'i zuwa, lafiya lau take tana gida ma batajin dad'i."
Yayi maganar yana kuma karya k'arin hularsa. INdo kuwa ci kanka batace masa ba Mama na ganin ikon Allah taga wazai fara yiwa wani magana sai taga kowa yana harkar gabansa. Kasa yin shiru Mama tayi sai da tace.
"Aisha wai bakiga Sadeeq bane, naga ko gaidashi bakiyi ba!"
Ba kunya INdo tace,
"Mama ai yace idan na sake ganinsa na kusala tom d'ina, har wawuya yace min a ranar."
Baki bud'e Sadeeq ya kalleta, rabon daya ganta tun rasuwar Abubakar sai jiya da Abba ya had'asu sai kuma yanzu amma ji sharrin da tayi mai cikin jin haushin ta yace.
"Karki rainawa mutane hankali yaushe na fad'a.?"
Nan ma ba tsoro bare kunya tace.
"Lokacin rasuwar marigayi sanda nazata bashine ya mutuba Ina murna na rik'eka ka tureni kace karna sake kulaka, a lokacin ne na tabbatar da cewa Kaine malam Sadeeq, shi yasa bazan gaida kaiba tunda kace haka."
Tsaki yaja tare da maida hularsa kansa, gaba d'aya ma besan ya fad'a ba yasan dai lokacin ta bashi haushine. Lallai yarinyar nan akwaita da rik'o toh kar Allah yasa ta gaidashi sai me (so what).
Mama ce ta kalleta cikin nuna mata martabar miji tace.
"Aisha ya kamata ki ajiye komai daya wuce tsakaninki da Sadeeq, yanzu mijinki ne dole zaki mai biyayya kamar yadda musulinci ya gindaya. Yanzu ki gaida shi bana son wani tashin zance."
Babu yadda zata yi domin a haka tana ganin k'ima da darajar Mama, cikin turo baki tace mai.
"Ina wuni?!"
Dan kar shima Mama tayi mai magana yasa shi amsawa a takaice yace.
"K'alau."
Mama ta jijiga kai tare da rik'e ha6arta, Sadeeq kawai zata jawa kunne domin shine miji kuma shine sama da INdo duk abinda ya d'orata akai shi zatayi ta kuma k'ara akan wanda take dashi zama tazo yak'i dad'i suji kunya amma zata bari sai ya dawo daga kaita tukunna.
Tashi yayi ya fita bayan yace su sameshi a waje. Sosai sukayi sallama da mutanen gidan suna mata fatan sauka lafiya INdo na amsa musu. Gaba Haleema ta bud'e mata babu gaddama ta shiga shi kuma Sadeeq yaja motarsa suka wuce INdo sai dariya take tana jin dad'in yadda duk suke sonta.
Tunda suka fara tafiya yake amsa waya duk ya cika mata kunne, hannu ta zuwa ta kunna redion motar dan ta riga ta iya Abubakar ya nuna mata sannan ta kunna A.c ta zuge glass d'in kusa da ita. Sadeeq ya sanya hannu ya kashe redion yana wayar sa itama ta kuma kunnawa tare da cewa.
"Haba Malam Sadeeq kana wayarka mana ni kuma ina jin redio na bashi kenan ba."
Wata muguwar harara ya watsa mata ta ta6e baki tare da juyawa tana kallon hanya. Abinda yake k'ona mata rai da turanci yake maganar sai Hausa da yake d'an cillawa. Wayarta ta d'akko wadda tun Abubakar ne daya sai mata ta fara d'aukar photo tana selfie style kala-kala ko kulata beyi ba harya gama wayar ya ajiye ta.
Gajiya yayi kunnuwansa sun cika da k'arar camera ya warce wayar daga hannuta tare da cilla mata ita kan cinya yace.
"Ke bana san kauyan ci fa."
Kallansa tayi hannunta rik'e da ha6arta tana cewa.....
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
Page *27*
"Malam Sadeeq kenan, ai da kasani ba yanzu ba."
Shareta yayi ya nuna tamkar ma bejita ba ta juya tana kallonsa ta kuma d'aukar wayarta daya cillo mata. Madubin saitin kujerarta ta bud'e tana gyara fuskarta ya girgiza kai dan shi dama yasan da wahala yarinyar tayi hankali sabida babu arabi ba boko yaja tsaki har kusan sau uku sannan INdo ta kallesa tace.
"Babu kyau fa."
Yace "Ni zaki cewa babu kyau? Ko kin fini sanine da zaki cemin babu kyau?!"
"Allah ya baka hakuri, cewa akayi idan kaji wani ko wata sunyi abinda ba kyau ka tuna masa, toni tuna maka nayi."
"Karki i sake tuna min domin tun kafin kisan hakan nasani, ke karki sake yin magana har muje inda zan kai kina jina.?!"
Bata sake kula shiba har sukaje danja masu tallar abubuwa suka dinga d'ago musu taga me alawar madara da sauri ta zaro d'ari biyu ta mik'a masa ji Sadeeq kawai yayi tana cewa.
"Bani ta dika."
Aikuwa ransa ya kuma mugun 6aci Allah-Allah yake kafin a gama mik'o mata ya figi motar amma danja batazo kansu ba harsai da aka bata tasa a jaka sannan aka basu hannu. Leda d'aya ta mik'a masa tace.
"Malam Sadeeq bisimillah."
"Banasha."
Maidawa tayi cikin jaka ta bud'e leda d'aya tana sha har wani kunkuni takeyi irin na zak'in nan idan ya gauraye kunne. Wayarsa ya d'auka yasa earpiece tare da kiran layin Fateema, sai da ta kusa yankewa sannan yaji ta d'aga cikin sanyin murya tayi mai sallama.
"Ohh babyna har yanzu jikin ne?!"
Ya fad'a cike da damuwa, can 6arin Fateema tace.
"A'ah kawai dai bacci nake, kun tafi ne?"
"Eh muna hanya ma yanzu zan dawo insha Allah, amma ki tashi ko tea ne kisha zaki kuma samun relief."
"Toh Allah ya kiyaye hanya a gaida min ita."
Tana kaiwa nan yaji ta katse, ba haka yaso ba yaso suyi hira ta d'ebe mai kewa amma tariga ta kashe ya cire earpiece d'in yana cigaba da tuk'insa ba tare daya sake kallon koda inda take ba.
"Malam Sadeeq dan Allah ka kar6a kasha, wallahi tayi dad'i madara ce zallah."
Yayi shiru ta kuma cewa.
"Inkaji dan Allah sha d'aya kaji."
A fusace ya juya yana kallonta shi har lokacin be manta yanayin ta na baya ba cikin 6acin rai yace.
"Wai dole sai na Shane? Idan dole ne toh sani insha dan Allah."
Ya fad'a tare da d'an kallon gabansa kafin ya juyo yana dank'ara mata harara, d'aya ta d'akko da sauri ta danna mai ita a baki ya yi saurin furzar da ita a k'asa amma duk da haka sai da zak'in ya shiga ko'ina na cikin bakinsa ya samu gefen titi ya tsaya tare da nuna ta da yatsa yace.
"Wallahi tallahi Aisha ki kiyayeni karkija wata rana na 6allaki yasin. Kinga ina shiga sha'aninki ne? Toh ki kuka da kanki duk rashin kunyarki a tafin hannuna take...!"
Jan bakinta tayi ta tsuke bata sake cewa komai ba har suka shiga garin Sumaila, tana ganin barkono dama sund'an tsaya sabida ana bada hannu batare da tayi mai magana ba kawai yaji ta bud'e k'ofar ta fita tana cewa.
"Bari na siyawa Inna barkono da gyad'a ko kwano d'aya-d'aya ne."
Kafin ya harzuka yayi magana ta k'arasa wajan, Sadeeq ya kifa kansa a steering shi kam ya shiga uku wannan wace irin yarinya ce tana ganinsu a tsakiyar titi amma ta 6alle murfin motar ta fita. Idan ta dawo sai ya mareta gobe bazata sake yi mai makamancin haka ba.
K'arasowa tayi wani yaro na biye da ita a baya da kaya ta bud'e gidan baya ya zuba sannan ta bashi naira hamsin ta shiga motar ta zauna tare da kallonsa tana gyara mayafi tace.
"Malam muje na dawo, wallahi kuma da arha shi yasa na siyo mata kwano biyu-biy....."
Bata k'arasa ba taga ya d'ago hannu tayi saurin sunkuyar da kai tare da boyeshi tana sauke a jiyar zuciya cike da tsoro da mamaki. Fad'a ya fara yi mata kamar ya samu student d'inshi har ya gama bata d'ago ba ya figi motar taji sun fara tafiya sannan ta d'ago tana kallonsa.
Kasa yin magana tayi ganin yadda yayi kicin-kicin da fuskarsa dan haka ta share Sa har sukaje k'ofar gidansu. Mutane kuwa aka fara murnar ga INdo ga INdo, wad'an da suka sanshi kuma suka dinga gaidashi yana amsawa da kyar tamkar 6eyi rayuwar garin ba. Kayanta ta kwasa tare da shiga cikin gidan su bata sake fitowa ba, shiru-shiru taji babu wanda ya lek'o shi kuma jira yake su gaida koda Inna koda Malam Hamza amma babu kowa daya fito daga gidan haushi da takaici suka sa shi ya tafi ba tare daya aika ankira wani ba.
A cikin gidan kuwa INdo cewa tayi musu ai ya tafi hakan yasa Inna bataje sun gaisa ba su kuma murnar zuwan INdon yasa basu fita ba bare su ganshi harya tafi.
Har Sadeeq yaje gida be denajin haushin abinda INdo tayi mai ba, lokacin da yaje gidan a cike yake da 'yan uwan Fateema hakan yasa shi juyawa yayi hanyar gidan su ba tare da ya shiga ba dan yasan akwai wad'anda zasu yi mai kallon banza.
Mama na ganinsa hankalinta ya kwanta tace.
"Yauwa Sadeeq har ka dawo?!"
"Eh suna gaida ku."
Ya fad'a yana k'ok'arin zama a kujera, Mama tayi murmushi cikin jin dad'i sannan ta shiga d'aki ta kawo mai abinci, beyi musu ba yaci dan yasan Fateema ba iya yi zatayi ba sabida ciwon marar daya barta tana yi. Yana gama ci ya fita yaje can gidan marigayi ya gano sannan ya wuce gurin abokinsa har sai da aka kira magariba sannan ya koma gidan.
****
Bayan sati biyu Abba ya gaji da sanya mai ido da safe ya kirasa, yana zuwa sai daya shiga suka gaisa da Umma da Mama sannan ya shiga gurin abban. Gaisawa suka yi Abba ya kallesa tare da ajiye magazine d'in hannunsa yace.
"Sadeeq yaushe zaka koma kwaran ne?"
"Abba nan da kwana uku insha Allahu zamu koma."
"Kai dawa?"
Sadeeq yace, "Abba da Fateema mana."
"A'ah Sadeeq ya kamata ka farayi musu adalci tun yanzu, ina son tunda zuwan nan na k'arshe da Fateema kukayi toh wannan karan sai ku tafi da Aisha bana son ta cigaba da zama da auranka acan gidan su ina fatan ka fahimce ni.?!"
Wani irin 6acin raine ya ziyarci ran Sadeeq kansa a k'asa yana danna yatsansa cikin zuciyarsa kuwa abubuwane kala-kala a cikinta. Jin yayi shiru ne yasa Abba kuma yi mai magana Sadeeq yace.
"Abba ai tafiya ta da Aisha garin nan bazai yiwu ba sabida kaga su ba Hausa sukeji ba itama kuma ba yarensu takeji ba dama tanajin turanci ne da sauk'i amma gaskiya tafiya da ita matsala zai jazamin wallahi, nasanta tun kafin Abubakar yasan ta."
"Toh yanzu me kake nufi?!"
"Abba kawai zan samu gida na ajiyeta anan idan yaso sai ta zauna a ciki har mu dawo."
Abba ya kallesa sosai kafin yace.
"Kana nufin ta dinga zama anan har lokacin da zaka dinga dawowa yayi."
Sadeeq yace. "Eh Abba idan ba hakan ba wallahi bansan yadda zanyi da Aisha ba idan mukaje can, gashi ta raina ni sam bata ganin girmana tun sanda na koyar dasu a makaranta."
"Shikenan kafin ka tafi kaje ka d'akkota sai ta tare anan gidan Najib tunda naga ya kammalasa kuma 'yan haya zai zuba gashi dai-dai itane gidan."
Sadeeq yayi shiru tunani yake yana kuma jin takaici, kawai yana zaman-zamansa an d'akko mai wani aikin, yanzu duk shekara sai ya bada kud'in gidan hayar da INdo zata zauna dubu d'ari da talatin. Mtwww yaja tsaki ba tare da yasan ya fito fili ba sai da yaji Abba yace.
"Sorry ko na shiga hak'inka ne??"
Da sauri Sadeeq ya hau kad'a kai alamar a'a sannan yace.
"Toh Abba kuma ni zanje na d'akkota? Na d'auka kawo ta zasu yi.?!"
"Eh toh kuma hakan dai yafi, amma ina son ka k'ara d'aga tafiyar ka har ta tare sannan sai kutafi."
Dakyar ya iya amsawa Abba sannan ya tafi. Yau ya kuma yin Nadamar zuwa tsefawa secondary school domin zuwansa ne yasa Abubakar ya ganta harya aure ta gashi ya mutu shi anbarsa da alak'ak'ai.
Yana komawa gida ya bawa Fateema labari tace Allah ya sanya alkairi, kallonta kawai yayi ya shige d'aki.
***
Cikin kwanaki biyu tal Abba yasa Sadeeq aka kwaso kayan INdo na gidan Abubakar harda wanda duk shine ya siya aka kaisu gidan da INdon zata zauna a matsayin ta na Matar sadeeq. Su Haleema Rukayya da Amina yasa sukaje suka kwaso kayan sawarta suka kai can gidan akajera mata sai dai babu dining area gashi INdo tana matuk'ar sansa dan idan tana kai ji take tamkar tana kusa da sharukhan.
Sadeeq da Umma da Hawwa suka tafi d'akko INdo, hirarsu ce duk ta sashi mance wadda zasu je su d'akko har suka k'arasa k'ofar gidansu INdo wanda yake cike da mutane wai ashe su biki suke yi wannan abun ya k'onawa Sadeeq rai sai kace wani sabon aure mtww.
Sun dad'e a ciki kafin a fito da ita su Uwani sai mata murna akeyi ta baro gidan dad'i zata koma gidan dad'i INdo taja tsaki ita kad'ai tasan gidan da zata shiga dan tasan sam basanta yake ba ta kuma riga ta shirya ma zama dashi a kowane irin yanayi indai vazai hanata abinci da fita yawo ba.
A kusa da Umma ta zauna yayin da Hawwah ta zauna gefensa anata yi musu fatan sauka lafiya bayan Malam Hamza yazo sun gaisa dashi Sadeeq din ya kuma bashi amanar 'yarsa sukaja mota suka tafi.
Tunda suka kama hanyar komawa yaja bakinsa ya tsuke jin INdo ta zage sai subirbid'a hira take tamkar ba amarya aka d'akko ba, yaja tsaki ganin sam babu jan aji a tattare da ita. Suna zuwa a k'ofar gidanta suka sauke ta su Umma suka shigar da ita ganin amarya yasa mak'otanta suka shiga suma dan su ganta.
Har kusan k'arfe shad'aya na dare Sadeeq be shigo gidan ba, gidan yayi matuk'ar yin kyau domin yasha tile's bangon da k'asan ta ko'ina sai dai bekai girma da tsaruwar na marigayi Abubakar ba amma hakan be damu INdo ba domin na iyayanta sam be kama k'afar su ba. Kallon agogo Hawwah tayi tare dajan tsaki tace.
"Wallahi Yaya Sadeeq d'an wulak'anci ne, yasan fa muna jiransa amma bazai zo ba ga mijina can sai waya yake yomin."
"Kinga yayya Hawwah kiyi tafiyarki mu zamu jirashi."
Haleema ta fad'a tana gyara kwanciya akan kujera hannunta rik'e da waya wanda hakan yake nuni da cewar chatting takeyi.
"Ba haka mukayi da Abba ba, cewa yayi karna bar gidan nan sai na tabbatar mai da shigowar Yaya Sadeeq."
"Toh saiki zauna gyara wani auran ke kuma ki 6allo naki ba."
Waya ta zaro zata k'ira Abba sukajiyo sallamarsa a k'asan makoshinsa. Tashi kowanne yayi yana sanya mayafinsa ya zauna a kan kujera.
"Toh Yaya Allah ya bada zaman lafiya."
Yayi shiru yana canza channel Hawwah tace.
"Yaya ina muku addu'a kayi shiru."
"Ke malama ku wuce kutafi gida bana son sa ido."
"Amin yayya Hawwah mun gode a gaida gida da abban siyama sai munzo."
Suka jiyo muryar INdo tana fitowa daga bedroom, hatta shi kansa saida ya kalleta ta gyatsina mai hanci tabi bayansu danyi musu rakiya.
"Amarya kamar karmu barki wallahi."
"Allah sarki Aminatu idan Allah ya kaimu basai ku dawo ba."
"Zamu zo amma da yamma kinga gobe monday akwai makaranta."
Cewar Haleema INdo tace.
"Toh koma dai yaushe ne sai kunzo a gaida Mama."
"Zataji."
Suka fad'a tare da juyawa su shiga mota da driver na jiransu itama ta juya ta shiga ba tare da ta kulle gidan ba. Zama tayi a falon tana wak'ar Nas ya shareta yana kallonsa itama bata kulasa ba domin ba so takeyi ba daman.
"Ke jeki kwanta dare yayi."
Yayi maganar yana gyara kwanciya akan kujera. Itama ta gyara zama tare da d'aukar remote tana murmushi tace.
"Wallahi malam Sadeeq banajin bacci."
Had'e rai yayi domin yana son yin waya da Fateema ya rage mata dare yayi mata alk'awari gashi wannan yarinyar zata samai ido.
"Ke bakya jin magana ko? Kin tashi kosai ranki ya 6aci.?!"
Tashi tayi cike dajin haushi ta shiga bedroom, kan gadon Abubakar datake so shi aka sanya mata a d'aki d'ayan kuma dayake matsayin nata aka sashi a d'ayan d'akin da ake nufin na sadeeq ne. Tana kwance kwai ya fad'o mata ta zura hannu k'ark'ashin filo wayam babu sweet d'insa da yake ajiyewa ta kalli agogo da yanzu suna tare kawai ta mik'e ta koma falon tana k'ik'ifta ido.
"Idan Zan iya zama ni d'aya a d'akin Allah ya tsinen..!"
Sadeeq dake manne da waya a kunnensa yaji da fad'a. A hankali yace.
"Babyna wait zan sake kiranki."
Kashewa yayi tare da juyawa ya kalleta sai kuma ya juya ganinta sanye cikin riga da wando pink and white na bacci sun kuma zauna a jikinta d'as duk da basu kamata ba yace.
"Toh kina son nazo mu kwanta tare ne."
"Malam Sadeeq ko bakazo badai toh kabarni anan."
"No baki isaba ko kuma ki kwanta anan d'in ni saina shiga ciki."
Zama tayi kan kujerar tare da cewa,.
"Tunda waya kakeyi toh ka k'arasa anan idan ka gama sai ka tafi nasan sannan nayi bacci bazanji tsoro ba."
Mtwww yaja tsaki ta kwanta suna kallo duk sunyi jigum har wajan 1:45am duk ya gaji ita kuma sai a lokacin tad'an fara lumshe ido ya zaro wayarsa ya lalibi Fateema amma abin mamaki switch off ya cillar da wayar gefensa yasan haushi taji be kiraba yanzu kila tana can tayi mai fassara kala-kala. A takaice duk anan falo suka kwana, haka har yayi kwanaki biyu a gidanta washe gari Sadeeq da Fateema suka wuce kwara state cike da farin cikin su ita kuma INdo aka turo mata Aminatu ta taya ta zama..
_M fan's kuyi hakuri gobe zakujini shiru zanyi 'yar tafiya insha Allahu dana dawo zamu d'ora I need ur prayers please._
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu
*Godiya mai yawa tare da d'inbin farin cikina zuwa ga fan's, na gode da addu'o'inku garemu munje Lafiya mun dawo lafi na gode sosai da sosai.😍 HAJARAH (MUM ILHAM) godiya mai tarin yawa a gareki domin kin nuna mana soyayya nida 'yar uwata STYLISH BCH da kuma 'yata IHSAN, Allah ya saka da alkairi ya bar kauna da soyayya Allah ya raya Ilham👏UMMUL MEENAL, BILLY S FARI & OLO addu'atw gareku bazata fad'u ba sai dai ince Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira domin kuna nuna min sayayya ta hak'ik'a HAJJA CE na sonku fiye da yadda kuke nunan kauna.💋😍💋*
Page *28*
Tunda suka tafi koda wasa Sadeeq be ta6a gigin k'iran INdo a waya ba, bashi dama phone number d'inta bare yace zai nemeta. A 6angaranta itama bata ko tunaninsa tana gidanta hankalinta kwance babu abinda yake damunta. Ranar da su Sadeeq suka cika sati d'aya da tafiya a ranar INdo ta fara fita, kullum tana gidan mak'ota bata nan layin bata can sam bata zama cikin kwanaki takwas mutanan unguwar sun santa maza da mata yara da manya. Yayin da a 6angaran Sadeeq yana son ya kirata tunda yasan tana da hakki akan sa amma baya kaunar ya kirata tayi mai rashin kunya ko ta gaya mai maganar da zai kasa bacci dan ya lura akwaita da shuka magana ba kuma ta barinta indai harka gaya mai toh zata baka amsa hakan yasa ya shareta.
Misalin k'arfe hud'u ta fito daga wanka tana shafa mai tajiyo me tallah a k'ofar gida, cikin sauri ta janyo doguwar riga a cikin wardrobe ta zura tare da d'aukar mayafi ta fita. A k'ofar gate d'in ta tsaya dan sake tabbatarwa da kunnuwanta abinda me tallar yake cewa still taji yana cewa.
"A sai kajin gidan gona matasa..!"
INdo tayi saurin fita tare da kwala mai k'ira ya dawo baya kasan cewar harya wuce gidan nata. Tsayawa tayi suka fara ciniki zata siya har yace zai siyar mata a yadda cinikin ya tsaya, guda bakwai ta siya ta shiga gida ta d'akko mai kud'in ta bashi ya tafi ita kuma ta shiga da 'yan kajinta sai kuka sukeyi iya-iya-iya tana ta murna taje ta zuba su jikin bathroom d'in tsakar gida dama ba'a shigar sa.
A hankali ta ci gaba da kiwonsu tana bayarwa ana siyo mata abincin su hankalinta a kwance su Haleema idan suka zo suyi ta mata dariya ita kuma tace da tayi kud'i saudiya zata tafi idan ta dawo a dinga k'iranta Hajiya INdo kasan cewar sunan ya bazu cikin gidajen mak'ota k'annan su Sadeeq ne kawai ke kiranta da aunty Humairah kamar yadda marigayi ke fad'a mata.
Rayuwar INdo ta cigaba da canzawa sana'o'i take yi kala-kala kajinta ma sunata girma har ta samu sun fara kwai tana tarawa taci takai gidan su Sadeeq sai da Mama tace ta fara siyarwa sannan ta fara.
Da daddare tana kallon arewa 24 Sumayya tana gabatar da shirin tauraruwa taji yadda wata mata da ake hira da ita yadda rayuwarta ta faro tun daga tushe har yanzu da takai wannan matsayin nan da nan INdo tayi sha'awar yin karatu itama tana son ta iya turanci sai dai tayaya zata iya? Sam kwakwalwarta bata gane turanci ba kuma ta iya rubutawa sannan ba ta iya maida hankali wajan koya tayaya zata iya zama tauraruwa kamar yadda taga ana haskilo mata masu aji ana kuma alfahari dasu, tasa a ranta zata fara koyan turanci kamar yadda marigayi yaso tayi kafin mai rabawa ta rabasu.
Sannu a hankali tana jin takaicin Sadeeq nak'in nemanta tun ranar da Aminatu ta guntsa mata cewar ai dan batajin turanci ne yasa Yaya Sadeeq cewa baxai tafi da ita can ba hakan yasa abin ya kuma ba ta haushi tsanarsa ta kuma hauhawa a cikin zuciyarta dama ya saba yi musu wulak'anci tun a tsefawa.
M.M Haruna English academic taji anata tallar makarantar a gidan redion express, ta fara tunanin yadda zata yi ta samu shiga cikin ta.
Tanason zuwa tana tsoron kar da taje ta tarrar da garzazzu wad'anda basa Hausa sai turancin, wai shin ma meyasa aka maida turanci tamkar saukar alkur'ani da komai za'a ce in zaka yi sai ka iyasa? Ga larabci yaran annabi amma ba a dagewa da zuwa islamiyoyi ba'a basu muhimmanci kamar yadda ake baya yaran jajayan farar fatar nan. idan aka kyaro baka iya bama sai ka zama wani hulugu ka zama abin raini da wulak'anci a wajan al'umma.
Zata yi turanci itama za kuma taje ta koya badan wulak'ancin Sadeeq kad'ai ba sai dan wata rana itama ak'irata ayi hira da ita a kuma tambayeta tauraronta tace Abubakar ne,haka zakila kuma a Dama da ita ita duniya wannan burinta ne ba kuma zata canza shi ba koda Sadeeq zai saketa.
"Hello mubassheer, kana Ina yanzu.?!"
"Ina majalisa ya akayi ta samu ne..?!"
"Kai d'an rainin wayo ne, kazo dan Allah zamuyi sirri."
"Toh aunty Humaira gani nan zuwa amma fa zaki ban jarkar kunun aya guda biyu."
"Dallah idan baxaka zo ba sai na kira khaleefa wallahi."
"Sorry Matar broth ina zuwa."
Kashewa yayi yana dariya sannan ya d'auki abokinsa guda d'aya suka tafi gidan a mashin. A falo suka zauna ta kawo musu kunun ayar da zobo da jallop d'in taliya suka ci sukayi dam sannan mubashsheer ya kalli INdo yana cewa.
"Toh meye sirrin Matar broth, tunda kin bamu munci..!"
Sai da ta hararesa sannan tace mai.
"Dallah kaga ni ba surutu na tambaye ka ba, jujun labo store zaka dan Allah ka siyo min farm (form) d'in shiga makarantar M.M Haruna Englihi menene ma d'ayan na gaban ma oho na manta."
"Ah Matar broth wai kina nufin shiga zaki yi..?!"
INdo tace "Eh ya ranka? Zakaje kayi min duk abinda za'ayi na fara zuwa kokuwa wulak'anci zaka yi min Kai ma..?!"
"Ah Matar broth na isa, kawo kud'in toh sai muje muji ya za'ayi, amma tukunna kin sanar da broth Sadeeq d'in zaki fara ne dan karya zo yayi min masifa."
"Kai zaka siyo min ko kuwa na sake wani?!"
"Ah na isa kawo kud'in muje muji ya za'ayi."
"Toh nawa zan baka..?!"
"Haba ki kawo ten thousand muje mu fara manage dasu."
"Kana nufin nawa kenan?!"
"Kai Matar broth dubu goma zaki kawo naga kina min wani kallo."
"Ta6 goma fa kace? Wallahi ku tafi na fasa ai ba dole."
Ta fad'a tana shiga cikin d'aki Mubasheer ya dinga yi mata magiyar ta fara bada ten thousand d'in tace ta yafe bazata ba sai da yace.
"Toh kawo five thousand, dubu biyar wallahi Matar broth kin fiye san Kud'i da yawa, duk sati dubu biyar broth yake badawa a kawo miki ga kud'in zobo ga kunun aya ga gullisuwa da kwan kaji dan Allah mekikeyi da kud'i bayan duk akwai abinci a gidan..?!"
Dubu biyar d'in ta bashi ya kar6a ya k'irga sannan suka tashi zasu tafi INdo tace.
"Dan Allah k'anin miji a rage sa ido, duk lissafin ka yana kaina toh da ba kud'in zaka ci naman dakaci a cikin abinci ne? Ko zaka ci harda vegetables d'in ne d'an rainin wayo."
"Magana ta wuce bari muje mu dawo."
Yana fad'a suka fice ita kuma ta shiga d'aki. Ko Ina tas-tas a gidanta bata barin k'azanta sannan kullum cikin k'anshin turaran tsinke d'akin yake dan haka INdo tana samun customers a rana sai ta dura jarkokin zobo dana kunun aya guda d'ari biyu amma baya kaiwa dare Allah yasanya mata nasibi a ciki.
A ranar bataga Mubasheer ba har kwana biyu sai gashi yazo, tsayawa yayi yace ya gama mata komai zuwa kawai zata farayi domin sai da ya sanar da abban su ya kuma bada goyan baya sosai. Juma'a na zuwa ta fara zuwa cikin tsoro da fargabar yadda zata tun kari malamai da d'alibai dan tasan duk sun fita k'ok'ari.
"Matar broth ga class d'inku nan."
Mubasheer ya fad'a yana nunawa INdo ajinsu. Ido ta dinga kwalowa waje hannun ta na dama dafe da k'irji ta kalli Mubasheer cikin tsoro tace.
"Anya bazan koma gida ba, Mubasheer tsoro nakeji wallahi."
"Kai Matar broth wallahi karkiji tsoro kowa fa da kika gani zuwa yayi a koya mai, idan kika nuna musu kina jin tsoro zasu raina ki kedai karki fasa yin abinda kike so ki shiga kawai."
"Toh bari naje idan mun tashi zan yi maka waya kazo ka maidani gida."
"Toh Matar broth Allah ya bada sa'a."
A hankali INdo ta shiga tashin farko ganin yadda hall d'in yake yasa gabanta bugawa da k'arfi sannan ga d'alibai nan a zazzau ne duk sai ta daburce ta rasa inda zataje cikin sauri ta juya zata fita sai taga Mubasheer a tsaye yana dariya, cikin tsananin jin kunya tace.
"Maidani gida bazan shiga ba."
"Hahaha...! Wallahi babu inda zaki, muje na shigar dake haka kurum dan ayi asarar kud'i sai da aka gama komai zaki wani ce kin fasa."
Yana gaba tana bayansa har ya k'arasar da ita tsakiyar kujerun sannan yayi wa wata budurwa magana cewar gata nan dan Allah ta fara helping d'inta ta wasu abubuwan. Karimatu tayi murmushi tare da mik'awa INdo hannu suka gaisa ta zauna a d'ari-d'ari kamar munafuka sai wulkita idanuwa take a haka Mubasheer ya barta yayi tafiyarsa.
Malami na shiga ta fara sunkuyar da kai, nan aka fara gabatar da lesson kasan cewar ajin masu koyan turanci ne hakan yasa komai ake yi musu dalla-dalla cikin hikima da kuma kwarewar malaman ita dai INdo tayi tsit bata ko kwakwaran motsi dan karma malamin yayi mata tambaya koya saka mata ido. Alhamdulillahi kuma ta tsinto abubuwa kasan cewar sai anta maimaita musu abu anji kowa ya gane an kuma fahimta sannan za'a shiga wani abun haka aka dinga yi musu tana kuma zuwa duk juma'a asabar da lahadi da safe.
****
Wata d'aya da sati biyu su Sadeeq sukayi a kwara state sannan suka juyo suka dawo kano. Lokacin satin INdo biyu da fara zuwa makaranta, sam bata yi wani murna da dawowarsa ba sema haushi da takaici dataji. Sai da yayi kwana biyu a gidan Fateema sannan ya waiwayo yau zaije gidan da INdo take.
K'ofar gidan ta tsaya wajan k'arfe sha biyu na dare, key d'insa na gidan ya zura ya dan bud'e abu ya gagara sai yahau buga mata tana kwance a kan gado da littafi a hannunta tana Home work d'in da aka basu, tanaji saidai batasan kowaye ba dan haka batayi ma niyar tashi zuwa ta gano ba.
Mtwwww yaja tsaki tare da ciro wayarsa ya nemo layin Haleema, mtwww ya kuma jan wani tsakin jin tana amfani da ita ya sake kiran khaleel cikin sa'a ya d'auka murya a shak'e Sadeeq tace.
"Dan turo min da number'n Aisha."
Khaleel yace "Yaya bani da ita sai dai ko yah Mubasheer."
"Cene masa ya turo min."
Ya fad'a a dak'ire sabida babu kowa unguwar sai shi kad’ai ga duhu. Yana tsaye yaji an turo ya kira number'n kamar bazata d'auka ba sai kuma tayi picking tare dayin shiru dan taji me maganar.
"Ke zoki bud'e min gida kinaji Ina bugawa kik'ak'i zuwa ki bud'e min."
Harzai katse yaji tace. "Waye kai d'in? Wa kuma kake nema..?!"
"Au bakima san waye ba dan rainin hankali Aisha?!"
Tace "Kai kaga k'ila wrong number ne go and check."
Kafin yayi magana ta katse kiran ta cigaba da aikin ta, Sadeeq yabi fuskar wayar da kallon mamaki ya sake buga gate d'in da karfi cikin jin haushi amma tak'i bud'ewa cikin 6acin rai ya buga number'n Mama tana bacci Haleema ta d'auka tana dubawa taga Sadeeq dan haka ta d'an janye wayarta daga kunne da takeyi da saurayinta ta kara tare da cewa.
"Yaya lafiya? Mama tayi bacci fa."
"Yauwa Haleema kira number'n Aisha kice ta bud'e min gidan Ina waje."
"Okey tom Yaya sai da safe."
Tana kashewa ta kira layin INdo, tana kwance duk tama rasa yadda zatayi Home work d'inta taga kira ta duba a tunaninta number'n d'azu ce tayi niyar d'agawa tayi mai rashin mutunci sai kuma taga Mmn dacta da haka akayi mata saving sunan tayi murmushi tare da karawa a kunne tana shirin gaida ita taji Haleema na cewa.
"Aunty Humairah Yaya fa yana k'ofar gida yace kije ki bud'e mai nidai sai da safe."
"Dama shine? No wonder naji ya fad'a da gadara zoki bud'e min gida, d'an rainin hankali ai na d'auka harka koma bazaka zo ba."
Hijabi tasa ta d'auki mukulli tayi waje, cire kwad'on (pad lock) d'in tayi ta bud'e mai ya shigo sannan ta juya ta koma, shi ya bud'e gate din yasa motar sannan ya rufe gidan ya shiga ciki. Bata falo ya bita bedroom fuskarsa a had'e yana shiga ya ganta kwance da littattafai a gabanta da biro da alama rubutu takeyi baki bud'e cikin tsananin mamaki yace...
0 comments:
Post a Comment