Aisha wannan kuma books d'in waye kike ta lalatawa haka.?!"
Cikin rashin damuwa tace, "is my own."
"Ooh your own?!"
"Yes..!?"
"Toh zane-zane kikeyi or what.?!"
"Home work nake yi."
Tayi maganar tana sake karkad'a biron hannunta, Sadeeq ya zaro idanuwa yana rik'e da ha6arsa kafin ya matsa kusa da ita yanan kallon littafin da take yin rubutun yana jijiga kai ganin note d'in tamkar tafiyar tsutsa wani yayi k'asa wani tsakiya wani sama ya zauna bakin gadon tare da kallon littattafan gurin ya gansu duk na turanci. Karo na farko daya fara zama kusa da ita duk da cewar ba kusa da jikinta ya zauna ba ya d'an bada gap.
'Daukar littafin kusa da ita yazo zai yi INdo tayi saurin janyewa ta 6oye k'ark'ashin cikinta tana faman harhad'e fuska dan bata son ya kushe mata rubutunta, ya ta6e baki tare da d'aga kafad’a yana cewa.
"Toh furniture's d'in d'akin kike drawing d'insu ko me kike yi hakan?!"
"A'a ba d'aya malam Sadeeq, makaranta nake zuwa kuma acan ake koya min wannan karatu."
"Ooh which school ne suka iya d'aukarki a haka Aisha..?!"
Cikin jin haushin sa INdo ta tashi zaune tana kuma 6oye book d'inta tana rurufe idanuwa tace.
"Dan Allah malam Sadeeq ka kyale ni haka nayi abuna ka takura min, neman ilimi naje yi sai yanzu Allah yayi zanyi, lokacin da marigayi dacta yana da rai bashi da wani buri daya wuce yaga nayi karatu amma kai sai afkin yiwa mutane gori toh nima na shiga school yanzu zan zama tauraruwa wata rana so what.?!"
Sadeeq ya tsaya kallonta, sosai tayi k'iba tayi bulbul da ita tayi fresh, duk da Cewar sleeping gown ce a jikinta kuma me d'an kauri hakan be hana bayyana yadda cikar halittar k'irjinta bayyana ba, Sadeeq ya d'auke kansa tare da ta6e bakinsa yace.
"Kinyiwa kanki gata kuwa Aisha, sai dai nasan zaki sha wahala tunda ba iyawa kika yi ba tun farko sai yanzu ne kika fara, shin waye ya kaiki school d'in and waye yake biya miki kud'in?!"
"I am, kasan ance sa kai yafi bauta."
Ta fad'a tana jin tsoran kartaje ya gwasaleta yace ba haka zata ce I am ba, sai kuma taji yace.
"Good hakan ma yayi kyau, but zan cigaba da biya miki ai ilimin yana da dad'i nan gaba zakiji dad'insa idan kika yi."
"No kabar abunka zanyi abuna da kaina, ko ka manta sabida rashin Ilimi na yasa kace ba zaka tafi dani inda kukaje da Fateema ba? Hmm! Allah yaji k'an dacta na, cewa yayi wallahi babu inda baxai iya shiga da niba dan har gaban Obama zai iya zuwa dani kuma yace matarsa ce. Ka tashi ka tafi ka kwanta ni bacci nakeji."
Tayi maganar tana share hawayen daya fad'o mata. Kallonta yayi tsab yaga ta tsuke fuska bayan ta goge kwallar sannan yace.
"Aisha ki lalla6ani, wallahi Zan iya hanaki zuwa school d'in inga ta tsiya dan dama baki gaya min ba ai kika fara zuwa."
Tace "lallai malam Sadeeq, ai wallahi tallahi sai dai ka sakeni in tafi gida dama baka sona nima bana Sanka kaga sai kaje kaji da matarka Fateema nima inje inyi karatuna so what."
"Wato har yanzu baki da kunya ko Aisha? Wallahi zaki sha mamaki na."
Ya fad'a tare da barin d'akin cikin sauri ya koma falo yana jin wani mugun 6acin rai, ko wane munafikin ne yazo ya gaya mata wannan maganar, wannan yarinyar idan ta kuma wayewa sai tafi k'arfinsa gara ma ya togeta daga makarantar ya sanyata islamiya ko zata dinga rissinawa.
***
Washe gari yana farkawa ya fito yayi hanyar bathroom d'in tsakar gida, yana zuwa yaga kaji gaba d'aya gurin ya zama tamkar dama dansu yayi, cikin tsananin mamaki ya fara tunanin toh kajin waye ta kar6o haka dan wulak'anci ake 6ata mai gida. A fusace ya koma ciki ya nufi bedroom d'inta, tana kwance sai shak'ar bacci take tayi d'ai-d'ai da ita books d'in wasu sun fad'i k'asa wasu kuma ta dannesu ya k'arasa kusa da ita cike da masifa zai tashe ta yaga abunda yasa shi saurin shigewa toilet d'inta yana dafe k'irjinsa.
Ya dad'e a tsaye kafin yayi alwala ya fito beko kalleta ba ya fita falo yayi sallah, yarinyar akwai d'aukar hankali komai nata a wannan stage d'in ya cika yaja tsaki tunowa da yayi sanda take zuwa da yagaggun kaya ya kwanta akan doguwar kujera yana sauke numfashi.
Jiyo motsinta yayi sai da ya d'an dad'e har gari ya fara wayewa sannan ya mik'e ya shiga cikin bedroom d'in nata. Tararwa yayi tana k'ok'arin fitowa suka yi karo da goshinan su INdo ta dafe gurin tare da fad'in.
"Kai-kai-kai..!"
Shareta yayi domin shima sauran k'iris yayi wai-wai-wai sabida tsabar zugi amma ya maze.
"Ke meye wancan a bayin waje.?!"
"Ina kwana?"
Itama ta fad'a kafin ta bashi amsar daya tambaye ta, a ciki ya amsa bata damu ba tace.
"Kaji nane."
"Wai Aisha haka kikeyin duk abinda kika ga dama ne? Yanzu me kikeyi da kaji.?"
"Masu kwai nefa malam, idan suka yi kwai nikuma sai na siyar, ance macen da bata sana'a aurace toh ni Ina yi kuma da kud'ad'an na shiga makaranta nayi kud'in napep. Malam tunda ka dawo baka ce INdo sau nawa kikayi rashin lafiya ba amma sai tambaya ta kakeyi abubuwan k'aruwata."
Shiru yayi domin tafishi gaskiya kuma sam beyi tunanin tambayar tata ba dan haka a wannan maganar yaji kunya, amma dan ya raina ta sai cewa yayi.
"Toh dama ke kina rashin lafiya ne? Naga tunda ban ta6a jin ance kinyi cuta ba, kuma da kinyi toh Abba zai gaya min."
Shiru tayi ta shiga kitchen, indomie ta jik'a sannan ta jajjaga kayan miya ta ajiye tare da komawa cikin d'aki yana zaune a falo yana waya da Fateema ta sharesa dan sam batajin haushi bare ya d'aga mata hankali. Sai da ta dubi lokaci tasan indomie d'in ta jik'u sannan ta shiga kitchen ta soya ta dafa tea ta kawo kan center table ta ajiye da kofu na guda biyu ta zauna tare da cewa.
"Ga abinci malam Sadeeq."
Lokacin sun gama waya yana chatting ya kalleta ya kalli agogon dake kafe a falon yaga k'arfe bakwai sauran minti uku, yanzu ne za'ayi breakfast sai kace ba yanzu aka tashi daga bacci ba yace.
"Tun yanzu ake yin karin kumallo.?!"
"Eh ai garin ya waye malam Sadeeq me zamu jira."
"Aci lafiya toh."
Ya fad'a ta kallesa cikin mamaki sannan ta fara had'a tea d'inta, ta iya cin abincin kuwa kad'an kad'an harta gama ci yana satar kallon ta. Tana gamawa taje ta fara dafa zo6on ta kasan cewar ranar Monday ce batada school ta wanke ayarta tana jiran lokacin da almajirinta zai zo ya kai mata markad'e.
Shima Sadeeq bacci yayi yana jiran lokaci yayi ya tafi gidan Fatima yayi wanka dan zaije lecture. Bata tashesa ba sannan duk batasan zai fita ba domin be sanar mata ba har tara da kusan kwata sannan ya farka yana duba agogo yaga har lokaci yayi da sauri ya mik'e ya d'auki mukullin motarsa, beyi mata sallama ba kawai sai tashin motarsa tajiyo taja tsaki sam malam Sadeeq bashida mutunci a jerin da ta sanya shi kenan.
***
Yana zuwa gidan Fateema yayi wanka ya shirya ya tafi, around 12:30pm ya dawo, cikin murna ta tare sa tare da rungumeshi ya d'agota yana cewa.
"Akwai bayani baby na zauna ki gaya min."
Sakinsa tayi ta k'arasa kan TV stand ta d'akko mai wata takadda, bud'ewa yayi ya karanta tare da zaro idanuwa yana kallonta cikin murna ya kuma rungumeta yana cewa.
"Woww babyna am so much happy wallahi, kin zama malama sai yau Allah yayi."
"Aikuwa baby kaji yadda naji kuwa, anjima zanje gidan Aisha idan zaka tafi please zanje kaga mun jima bamu had'u ba."
"Toh kinsan itama ta koma school fa."
"Kai baby shine koka gaya min sai yanzu danace zani gidan?
Sadeeq yace "A'afa nima sai jiya naji kuma kinga ai ban zauna ba sai yanzu, kinga bani abinci naci."
Tashi tayi ta shiga kitchen yayi farin cikin samun aikinta sosai domin yana son abinda take so, yana kuma son farin cikinta. Egg into egg ta kawo mai tare da kunun gyad'a ta zuba mai yasha madara ya zauna a hankali ta dinga bashi harya cinye yasha kunnun sannan suka ci gaba da soyayyar su tamkar babu gobe har mantawa suke yi da matsayin INdo.
Bayan yaje gidan Mama ya dawo sai ya d'auke ta suka tafi, gidan cike da masu siyan zo6o da kunun aya wasu na fita wasu na shiga inji yana tayi mamaki ya cika ransu sai da suka shiga sannan suka tarar da ita a zaune gaban k'atuwar kula duk wanda ya bata kud'i saita bud'e tabashi ya tafi, Sadeeq ya shiga ciki ransa a mugun 6ace shin yarinyar nan meta maidashi ne, wato ma ashe harta zama big hajiya besani ba Allah ya kaisu dare sai ya 6ata mata rai.
Sosai suka yi hira da fateema ta yadda har ta gano lallai itace star a gurin Sadeeq, anayin magariba ya maida ita gida wajan k'arfe goma yazo gidan INdo lokacin tana zaune a falo tana kallon film d'in Basaja na farko.
"Ke Aisha daman haka kika mayar min da gida tamkar gidan kallo? Maza da mata su dinga min strolling a ciki?!"
Tayi shiru ya kuma harzuk'a ta kuma yi mai shiru ganin yana masifa yasa ta cewa.
"Wai malam me yasa ka tsaneni ne? Nifa kamar yadda bakai kace kana sona ba haka nima bance Ina sonka ba. Yanzu da yake ita Fateema matarka ce ta so ai d'azu tazo ta nuna min takardar fara teaching d'inta kai da kanka ka kawo ta sai ni da nake sana'a a cikin gida da kud'ina amma ka dinga min fad'a kana Sa min ido? Toh ka sake ni dan Allah ka gani idan bazan rayuwa ba."
"Ni zaki cewa na sakeki Aisha? Toh bazan sakeki ba kuma karna sake ganin wani yaro ko yarinya sun shigo min gida."
Yana kaiwa nan ya kuma barin gidan sai dai be fita da mota ba, anya ta d'aura a zuciyarta na cewar bazata denaba tunda taga alamar bakin cikin ganin tacigaba yakeyi. 11:49pm ta d'auki pad lock zata kulle gidan taji sa daga waje jikin gate din yace.
"Malama karki rufemin gida."
"Gidan hayan."
Ta fad'a tana shiga falo yayi kwafa tare da shigowa ya rufe. Tuni ta shiga d'aki ya bita dan sake ja mata kunne kawai ya tarar ta cire riga tana niyar saka ta bacci hankalinsa yayi mugun tashi ya kasa controlling d'in kansa ita kuwa sam batasan yana tsaye ba saida ta gama saka rigar ta tashi tsaye domin da a zaune take ta ta6e baki tare da hayewa kan gadon.
Jikinsa na rawa dama Yaya lafiyar kura domin yana da tsananin buk'ata tun yana saurayi bare yanzu domin fateema harta saba da halinsa.
Cikin rawar jiki ya k'arasa kusa da ita kan gadon ya hau sam bata kulasa ba kawai taji ya janyo ta jikinsa suka fara fad'a Sadeeq yayi nasarar rungumota jinta a jikinsa yasa jikinsa ya kuma narkewa ya rasa abinda yake tunzura shi duk da irin naushin da yake sha a gurinta amma yak'i ya saketa.
"Wai meye hakan ne kake yi min."
"Shhhiiii..."
Yace da ita a dai-dai kunnanta, duk k'arfin INdo amma ta gaza kwatar jikinta Sadeeq ya sake rungumeta jikinsa sai karkarwa yake yi, cikin k'arfi da yaji sai da Sadeeq ya samu abinda zuciyarsa take muradi a gurin INdo. Jikinta daya raina yau sun had'u danasa, bakinta da yake ganin koda million d'ari bazai iya ta6awa ba yau sai da suka had'u danata tana ta kuka ya rasa yadda zai yi a ganinsa tunda tayi aure ta riga tasan komai be ta6a tunanin zai jita a yadda yaji yanzu ba (k'ila ya manta suna cikin amarci Allah ya d'auke mata angon domin Abubakar ba kullum yake yi mata ba wani sa'in making romance kawai zaiyi da ita) INdo cikin kuka tace.
"Tun farko haka zaka ce ga abinda kake so dani bawai ka hanani yin sana'a taba. Wallahi malam Sadeeq bana sanka duk da a makaranta ance bakyau a gayawa miji haka wallahi ni bana sonka Allah kuma saiya saka min."
"Please Aisha b..."
"Karka yi min magana tsakani na dakai babu magana daga yau wallahi bazan sake yi maka magana ba ko me zakayi min."
Ya kasa rik'ota domin daya kai hannu zata yi mai wata uwar mahangur6a takai mishi naushi da k'afa da hannu tilas yabar d'akin ya koma falo.
"Innalillahi wa'inna 'ilaihir raji'un why? Why? Sadeeq, Aisha ce fa INdo malam Hamza tsefawa secondary school ita kayiwa haka.."
Da sauri ya mari fuskarsa ya gani wai ko mafarki yake amma sai yaji zafin marin sannan kunnuwansa na jiyo masa kukanta. Rintsa idanuwa yayi tare da toshe kunnansa yana faman girgiza kai dan yadda yaji wata bahaguwar kaunarta na tafasa cikin zuciyarsa yayi saurin tashi tsaye ya shiga d'akin da take kwance ya durkusa saitin kanta gwaiwarsa a k'asa ya......
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
_Alhamdulillah³ naji sauk'i godiya me tarin yawa ga masoya, naji dad'in addu'@r ku gareni gashi Allah ya amsa nagode Allah yabar kauna da soyayya._🤲🤝
Dan Allah duk wanda yayi min magana jiya zai ga ban amsa ba wallahi wayar ce tayi wiping kuyi min afuwa dan Allah, na gode❤
*Today is my daughter’s birthday🎂🔥🎂, Fateema Omar Farooq Pz. Wishing you long life, Allah ya raya min ita ya shirya min ita ya tsare min ita da duk 'ya'yan musulmai baki d'aya love you so much my daughter*🎂🔥🎂
Page *30*
Hannu ya kai zai ta6a ta amma sai ya kasa, kallon bayan ta yake yi kawai zuciyarsa na tsananin harbawa.Tashi yayi ya koma gefen gadon ya d'an zauna a hankali ya kira sunanta cikin sanyin murya a kuma dai-dai kunnanta yace.
"Aisha bari muyi magana kota minti d'aya ce please."
Motsi INdo ba tayi ba bare yasa ran zata juyo ko ta tashi zaune, yana jin yadda take sauke ajiyar zuciyar ta amma ji yake tamkar tashi ake bubbugawa sabida tsananin yadda yake ji. Hannu ya kai ya rik'o kafad'unta ta baya amma ko motsi bata yi ba ta dak'ire mai daga kwancen sai ya samu kanshi da kwanciya a bayan ta ya rungumeta a jikinsa tsam amma still bata motsa ba, ya d'ora kansa a wuyanta yana shafar kitson kanta zanan hannu, nan ma ko gezau INdo bata yi ba.
Duk wani hanyar lallashi da Sadeeq ya sani yabi INdo dasu amma taki motsi duk da cewar tana numfashi hasalima idanunta biyu amma ya gagara ko mirgino da fuskarta gurinshi sabida yadda tayi mai taurin kai ta kafe a guri d'aya tamkar mutum mutumi.
"Aisha me yasa bakya jin maganata ne? Shin baki son matsayina a gurinki bane kike yi min haka? Nace ki tashi dan Allah zamu yi magana kinji ko..?!"
Wayyo Allah..! ko pillow'n kanta be motsa ba bare ta mik'e, Sadeeq yayi ya kad'a ya raya, yayi magiyar yayi lallamin tare da lallashi amma tayi gardama. Ya manta INdo amma yanzu ya tuna ko wacece, ya tuna lokacin da tace ta dena zuwa makaranta kuma hakan aka yi ta dena zuwa sai da taji labarin ana bada kyauta sannan ta fara zuwa, ya tuna lokacin da tazo dan samun kyautar atamfa bata yanke farce ba ya hanata tace ta dena zuwa k'arshe ma ta yi hijira daga kauyan sani zuwa kauyen saye bata dawo ba sai da marigayi yaje ya dawo da ita. Wannan suna d'aya daga cikin taurin kanta daya sani dan haka yanzu ya zai yi mata gashi zuciyar sa na buk'atar kasancewa tare da ita, shin me zai yi mata ta huce gashi tace bazata sake mai magana ba, meya kai shi haike mata bayan duk basu shirya yin hakan ba daga shi har ita.
"Ya ilahi...!"
Ya fad'a cikin zuciyar sa. Har kusan k'arfe biyu na dare yana kusa da ita, haka ya gaji ya mik'e ya shiga toilet wanka yayi sannan yayi alwala yaje falo yana fita ta sakko daga kan gadon ta rufe d'akin tamkar dama jira take yi. Yana shimfid'a sallaya yaji ta rufe ya kalli k'ofar cike da mamaki kafin ya tayar da sallah. A ranar Sadeeq be runtsa ba ya dinga sak'e-sak'e da neman hanyar dazai sassauto da zuciyar INdo, har yayi asuba a gurin sannan ya samu 6arawon ya sace sa bayan ya gama samun mafita.
INdo kuwa tana kulle k'ofar ta hau kan gado sai kuka take yi, tasan yayi mata ne dan mugunta amma tayi alk'awarin ba zai sake ta6a ta ba bare har yayi gigin yi mata wani abun. wata sabuwar tsanarsa ta kuma shiga cikin zuciyarta.
Sai da asuba sannan tayi wanka tayi sallah duk a nan cikin d'akin sannan ta koma ta hau gado dan ta san yana nan kuma idan ya ganta zai iya yi mata magana abinda ta tsana yanzu kenan ko kallen ta bata son yayi.
Misalin k'arfe bakwai na safe ya nufi d'akin ya bubuga mata amma tak'i bud'ewa haka ya hakura yabar gidan kasan cewar yana da lecture da k'arfe takwas. Tana jiyo shi ya fita ya rufe gate tayi saurin hantsilowa daga kan gadon taje ta gark'ame gidan da padlock sannan ta koma falo ta zauna sai zabga tsaki take tana harara-harare tamkar ance mata yana gurin ranar bak'in ciki ya hanata yin zo6o da kunun aya sai gurin kaji da taje ta kwashe kwan da suka yi.
***
Shi kuwa Sadeeq yana zuwa gidan Fateema yasa key ya bud'e, shiga yayi a kwance ya tarar da ita tana ta bacci ya lalla6a ya kwanta a bayanta tare da shiga cikin bargonta ya rungume ta tsam a jikinsa yana cizon lip's d'in sa tare da goga goshinsa a bayan ta.
Yadda taji ya nanik'eta ne yasa ta rik'o hannunsa da ya mak'alota dashi ta d'ora akan k'irjin ta shi kuma ya matse ta jikinsa sai rawa yake yi. Gabaki d'aya ransa INdo ce daya rufe ido zai tuno abinda ya faru tsakaninsa da ita, haka ma daya bud'e idon zai dinga ganinta gashi ya tabbatar da yana da mugun tabo a gurinta. Yanzu ya zai yi wajan ganin ya wanke kansa a gurinta? sam beyi tunanin cewar hakan zata ta6a faruwa a tsakaninsa da ita ba sabida tsananin yadda yake ganinta tun zamanin tana INdon ta ba yanzu ba da ta koma aunty Humarah ko aunty Aisha ba.
Da kyar ya iya shiryawa yaje yayi lecture ya dawo, directly ya wuce gidan INdo, cikin tsananin mamaki ya tsaya yana kallon gate d'in gidan ganinsa a gark'ame. Mota ya koma ya wuce gidan su yana tunanin can ta tafi amma abin mamaki sai yaji su Mama suna tamyarsa ita amma ya maze tare da cewa.
"Tana nan Lafiya lau."
Ya d'an jima a gidan ya mik'e ya fita, Haleema ya k'ira a waya tana d'agawa yace.
"Haleema d'an k'ira Aisha a waya naji ina ta k'iran ta not reachable please yanzun nan amma."
"Toh Yaya bari naji."
Wayar INdo Haleema ta k'ira, tana d'agawa tace.
"Aunty Humaira ina kika shiga ne keda wayar ki?"
INdo ta yatsina fuska tamkar a gaban ta take cikin takaitawa tace.
"Ina gida.."
"Okey tom shikenan."
Haleema ta k'ira Sadeeq yana d'agawa tace.
"Yaya tana gida wai."
"Okay thanks."
Suka kashe wayar, Sadeeq ya dinga mamaki wato ma ashe tana jin motarsa amma tak'i bud'e mai lallai yarinyar nan ta mugun raina sa gashi ya kuma siyowa kansa wani sabon rainin. Juyawa yayi ya koma gidan Fateema yak'i kuma bari ta gano yanayin sa.
Haka Sadeeq ya dinga sintiri a ranar daga gidan Fateema zuwa gidan INdo amma abin mamaki har kusan magariba bata bud'e gidan ba, sannan ya kirata a waya yafi sau ashirin amma bata d'aga ba ya san ba k'aramin 6ata mata rai yayi ba.
Har ya kammala kwanaki biyun sa a gidan Fateema INdo bata bud'e gidan ba haka kuma duk wanda yaje bata bud'ewa. Sadeeq kuma ya rasa yadda zai yi tsoransa d'aya karta mutu a gidan besan mezai ce ba. 10:35pm yana zaune a falon Fateema ya shiga cikin tunani yaji Fateema na shafar sajan sa ya kalleta yana murmushi tare da lumshe ido tamkar ya sha kwaya don sunyi wani iri tace.
"Baby ya kamata ka tashi kaje gidan Aisha dare nayi maka fa."
"Ai bata nan taje garin su."
Ya samu kanshi da fad'ar haka yana kallonta, Fateema tana da kyau sosai domin tafi INdo haske da idanuwa ga gashi amma cikar hallitta gaba da baya INdo tafi Fateema. Ya lumshe idanuwa tare da janyo ta jikinsa yana shafar bayan ta, sai dai cikin ransa so yake yaga INdo kota halin k'a-k'ane amma ya rasa hanya.
Friday morning INdo ta shirya tsab ta tattara littattafanta tasa mayafi ta fita, bud'e gidan tayi sannan ta rufeshi daga waje ta tari napep ta wuce makarantar M.M HARUNA. Submitting d'in books na Home work d'in da aka basu aka yi dan malamin ya duba yana zuwa kan na INdo yaga ba kanta hakan yasa ya kira sunanta da ya gani a jikin littafin yace idan an tashi taje ta samesa a office.
Hakan kuwa aka yi ta sami M.m harunan a office d'insa ya nuna mata guri ta zauna yace.
"Aisha Hamza daga wace school kika taho nan..?"
INdo tace "Gaskiya malam ban gama makaranta bani, ni yanzu ne dai nake son yi sabida gaskiya kaga mijin da aka bani d'an rashin mutunci ne kuma a jami'a yake koyarwa, nidai malam dan Allah kuyi iya k'ok'arin ku wajan ganin na iya nima shida matarsa duk malamai ne shi yana min gori kar nan gaba itama tazo ta fara yi min.."
M.M HARUNA yace "Toh karki damu Aisha tunda dai har kinsa a cikin ranki zaki koya toh nasan ba zaki sha wahala ba, yanzu zaki fara tun daga kan alphabets kije ki kwafe su cikin note book d'inki gobe ki kawo min ki kuma dinga k'ok'artawa wajan yin magana da turanci koda kuwa za'a yi miki dariya dan ni daga yauma ki dena min hausa da yawa understand.?!"
"Toh malam yes."
Ta fad'a tana rufe fuska yayi dariya shima tare da cewa "Good." Littafi ya d'akko sabo ya rubuta mata from A-Z yace taje tayi irinsu duka. Allah sarki da yake tana so ba taji wani girman kaiba ta kar6a tana komawa gida a kwance ta tarar da Sadeeq har ya shigo gidan da yake babu abinsa padlock daga waje, ta wuce cikin d'akin ta yayi saurin tashi ya bita a baya ya tsaya a wajan wardrobe ko kallansa ba tayi ba bare ta gaida shi yace.
"Aisha fitsara.., wato ni kika hana shigowa gidan ko? I think nawa ne, koda yake kin ce gidan hayane amma wayake biyan kud'in gidan.?!"
Ko kallansa ba tayi ba ta zare hijjab d'inta ta ninke tasa a wardrobe taje zata shiga toilet Sadeeq ya fizgota nan ma tak'i yin magana ganin haka yasa shi fita yabar gidan, yana tafiya ta kuma kullewa taje tayo fitsari ta shiga kitchen ta dafa abinda zata ci ta koma falo taci ta k'oshi sannan ta fara assignment d'in ta tana gamawa tayi bacci bata sake bud'e gidan ba sai washe gari da zataje makaranta. kullum haka take yi bata bari su had'u dashi kwata-kwata.
Ranar litinin Fateema ta fara zuwa gurin aiki, damuwa da shiga tashin hankali suka taru suka yiwa Sadeeq yawa ya rasa yadda zai yi da INdo, sam ta dena bari ya kwana a gidanta sabida da anyi magariba zata 6ame gidan har Fateema ta gano suna da Matsala a tsakaninsa da Aishan sai dai bata nuna mai san jin abinda ke faruwa kasan cewar bata son shiga cikin abinda duk be shafeta ba.
****
"Abba wannan karan ina son tafiya da Aisha sai dai tak'i yadda ma muyi maganar da ita."
"Sadeeq kenan yanzu kai da iyalinka ka kasa shawo Kansu waye toh kake son yaje ya shawo maka kanta? Duk tsaya ai kaine kafi mu kusanci da ita ya kamata kasan yadda zaka yi ta yadda har Ku tafi tare."
Shiru Sadeeq yayi ya rasa ya zai yi gashi ranar Thursday yake son komawa, ga Fateema tunda ta fara zuwa makarantar nan yasan itama ba yadda zata yi ta bishi ba kasan cewar ya mata alk'awarin idan har takardar aikinta yafito toh zai barta tayi, gashi bazai iya tafiya shi kad'ai ba tunda ya riga ya saba kasan cewa da mace.
"Sadeeq ya kayi shiru? Idan ita Aishan tak'i binka ba saika tafi da wadda kuka saba tafiya tare ba."
"Abba ai Fateema ta fara aiki dan tun yanzu ma ta fara nuna k'in bina wallahi."
"Toh ya zaka yi da rashin iya yaren su da ita Aishan bata iya ba? Kar taje tana baka matsala fah tun da a baya haka kace."
Kan Sadeeq a k'asa yana goga yatsansa a k'asan carpet d'in d'akin, shi kansa yasan ba zai iya tafiya kwara state ba sai da matarsa a kusa dashi gashi abban da zai temaka mai shima yace yaje su sasanta da d'aya a cikin su.
"Shikenan Abba zanje na kuma tambayar su, sai da safe Allah ya k'ara girma."
Abba ya kallesa tare da cewa "Amin Sadeeq a gaida min dasu baki d'aya.
Fita yayi ya wuce gidan Fateema ranar ma anan ya kwana. Washe gari ta kasance Wednesday bayan Fateema ta tafi gurin aiki misalin k'arfe goma Sadeeq ya shirya cikin wani rantsatsan yadi mai matuk'ar taushi sky blue ya d'ora hula yasa turare sannan ya fita. Gidan INdo ya wuce yayi niyar yau kota halin k'ak'ane sai ya shiga gidan ya kuma nuna mata kuskuranta na rainin da tayi masa.
Cikin sa'a ma yana zuwa ya tarar da gidan a bud'e nan da nan zuciyarsa ta sanyaya, a k'ofar gidan yayi parking sannan ya shiga gida bakinsa d'auke da sallama. Takalma ya gani a k'ofar d'akin hakan ya tabbatar masa da cewar bak'i tayi, ya shiga ciki da mamaki sai yaga su Nafeesa, Sagiru da Shehu sai wani wanda besan ko waye ba amma da alama tare suke.
"Yaya Sadeeq ina kwana?!"
Yaji Nafeesa ta fad'a bayan ta durkusa k'asa, murmushi yayi tare da k'arasawa ciki yana amsa mata su kuma Su Sagiru ya basu hannu suka yi musabuha.
"Yasu Inna da malam Lafiya dai ko?"
"Lafiya lau, sunce suna gaida kai."
"Ina amsawa yaushe zaku koma..?!"
Sagiru yana shafa k'eya kasan cewar yanzu duk sun girma yace.
"Nan da anjima zamu wuce."
"Okey tom Allah ya kaimu."
Yana fad'a ya wuce d'akin INdo a tunaninsa zata biyo shi irin abin nan na tsakanin mata da miji da idan ya dawo zata bishi taji abinda yake da buk'ata ko kuma a sake yin wata special Oyo yon amma yaji shiru sai ma dariyar ta da yake jiyowa ya dafe goshi tare da rintsa idanuwa daga bisani ya mik'e yabar gidan. Tunda ya fita be sake dawowa ba sai da akayi magriba sannan ya shiga gidan lokacin bata rufe gidan ba suna zaune da 'yar mak'otansu Mansura suna kallo suna hira.
Ganin ya dawo ne yasa Mansura tayiwa INdo sallama ta tafi shi kuma ya zauna a falo yana kallonta. Sanye take cikin atamfa me ratsin green, white, brown, da purple d'inkin riga da zani sun cika ta sunyi mata d'as tayi kyau sosai ya kalleta amma ita hankalinta na kan TV, sadeeq ya d'auki remote ya kashe TV d'in tare da kallonta sai yaga tana kokarin mik'ewa ta shiga d'aki yayi saurin rik'ota ta fara fisge-fizge zata kwace ya jingina ta jikin bango bayan ya rik'e mata hannuwa.
Murya tamkar ta marayan daya kwana biyu be samu abin kaiwa baki ba Sadeeq yace.
"Aisha what's wrong with you ne ah? Dani zaki yi gaba? Kin manta matsayi na a wajanki ne? Ko baki san wannan abin da kikeyi min ba kina cikin fushin ubangiji ba? Please Aisha ki bari mu fahimci juna I beg of you please..."
Still shiru tayi Sadeeq yakai fuskarsa saitin k'irjinta yana goga fuskarsa yaji tayi magana.
"Wai malam Sadeeq ya haka ne?!"
"Aure ne haka if you don't know."
INdo ta dinga mai-maita if you don't know cikin zuciyar amma ta kasa gane me if d'in take nufi dan tasan don't know da you dan haka tayi tunanin ko wata maganar ya gasa mata dan haka ranta ya kuma 6aci ta zabga mai harara yakai bakinsa ta kauda kai amma duk da haka sai daya laso idon rashin kunyar da harshensa yace.
"Aisha you don't know me shi yasa kike min duk abinda kikaga dama ko.?!"
INdo ta ta6e baki tare da yatsina fuska ta daddage tace.
"Ta6 I know you're noun, ko banda malam sadeeq kana da wani sunan..?!"
"I know you're noun." Ya maimaita a fili yana kallon gefen fuskarta still yana rik'e da ita a jikin bango ya rasa gane me take nufi hakan yasa shi lek'a fuskarta yace.
"Mene kuma noun a cikin maganar da kika min Aisha.?"
Ta murgud'a baki tare da cewa.
"Sakar min hannu malam Sadeeq, kace ban sanka shine na nuna maka nikuwa na sanka, noun is a name of person, animal, place or tins (things) ko ka d'auka yanzu ma banajin abinda kake fad'a? Never past tense kenan wallahi (Da kenan)."
Sadeeq ya cuno baki, so yake yayi dariya amma baya son yayi taji haushi dan so yake ya lalla6a yayi mata wayo ya samu ta bishi dan haka ya dinga gumtse dariyarsa ita kuma tana k'ok'arin kwatar jikinta yace.
"Very Good Aisha you're trying, but kin san menene? Ki shirya kayanki gobe mu tafi kwara state a can wallahi zaki iya komai domin su basa Hausa sosai kafin kiga bahaushe sai kin dad'e, muje ki shirya kayan ki sai na taya kima."
Ya fad'a tare da janyo ta jikinsa ya rungume ta. Cikin sauri INdo ta fisge tare da cewa....
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
*THANKS ALL FAN'S, baki, hannu bazasu iya rubuta yawanku ba domin kunada yawa wlh. Na gode all grps da sukayi ma ihsan wishes. Allah yabar so da kauna.*
_My wattpad so sorry please wallahi nayi nayi yaki yin update kuyi hakuri wallahi tun safe yak'i yi nasara dalili😪_
Page *31*
"Wallahi ni dai baza ni ba, haba-haba da bakin kafa kace wai ba zaka je dani ba sabida ni banajin turanci, toh wallahi yasin yanzu dakaji na faraji ba zan bika ba Allah kuwa."
"Idan nace kuma sai kinje fa ya zaki yi?!"
"Ai karka ma fad'a dan ba binka zanyi ba, kaje ku tafi da Fateema."
"Aisha...!"
Ya fad'a cikin gentle mood wanda yasa INdo saurin kallonsa cikin ido hudu, hannunta ya janyo yana kallon fuskarta a fili ya fara magana besan ma a filin yake yi ba.
"Aisha My heart is filled with instant joy, you give me everlasting warmth. Aisha your eye's, your nose, your pretty cheeks your mouth, your chin, the whole of you all are sweet and so you are. Please Aisha ki bini wallahi babu abinda zan miki kinji na rantse."
Kallonsa kawai INdo tayi sam duk ta kasa gane abinda yake cewa hasalima dabarbarta ta yayi kwakwalwarta ta fara hasashe kafin tace.
"Dare nayi malam Sadeeq kaje ka kwanta nima kwanciya zanyi na gaji."
"Toh zaki bini mu tafi d'in..?!"
"A'ah wallahi bance ba."
"Wai me yasa kike da taurin Kai ne Aisha.?!"
"Malam Sadeeq wane kai ne me laushi?!"
Mtwwww yaja tsaki tare da sakin mata hannu yaje ya d'auki mukulli ya tafi rufe gidan sannan ya dawo, yana dubawa ya tarar ta rufe d'akin ta ya san ko magana yayi ba bud'e mai zata yi ba kawai ya kwanta a falo. Washe gari yana yin sallah yabar gidan bayan ya ajiye mata 10k ya tafi gidan Fateema.
Yana zuwa ya tarar harta gama had'a mai kayansa ita kuma tana k'ok'arin shirin zuwa gurin aiki. Sai da ta temaka masa ya samu relief sannan suka shirya tare suka fito ta samu napep shi kuma ya Shiga mota yayi gidan su dan yi musu sallama. Suna gamawa ya juya ya d'auki hanya bayan yasawa ransa cewar zai gwada musu shi d'in namijin duniya ne sai sun nemesa musamman INdo da bata ganinsa da gashi aka.
**** ****
Bayan watannin uku.
12:30pm tana tsaye a mak'ale jikin bishiyar darbejiya sai makaka ruwan sama ake yi, ta jik'e tayi sharkaf da ita, ganin tamkar ruwa da iskar yana k'ok'arin jijjige bishiyar yasa ta ci gaba da tafiya sai faman tangad'i take tamkar ana tura ta, sam ba tayi tunanin ruwan zai yi yawan haka ba kafin ta k'arasa gida data fito daga school. Hakan ne ya bata damar tahau napep tayi gidan Asma'u tsautsayi kuma yasa ta fito tace ita gida zata tafi.
Horn d'in mota taji amma bata juya ba sabida ko ganin hanya bata yi sabida k'arfin ruwan. Kuma yi mata horn yayi da nufin idan tana son temako idan kuma yayi mata sau uku toh zai rabu da ita ya k'ara gaba k'ila ba bil'adam bace.
Tana jin ya kuma yi ta fara lalu6en inda taji mutar har Allah ya temake ta ta6ota, a hankali taje wajan k'ofar ta bud'e a she ta saitinsa ce sai ji tayi ya ce.
"Ke daga ina kike haka..? Ki zagaya ba ta nan zaki shigo min ba."
"I am not ke sir..., I am Aishat Hamza by name so please don't call me ke again..!"
Ta fad'a tare da d'an bud'e ido ta kalli motar, da sauri ta zagaya ta d'ayan gefen ta shiga ganin Sadeeq ne jikinta sharkaf ya kalleta baki bud'e ta zauna sai ya kauda kai tare da mik'a mata wani d'an kyalle ta kar6a tana goge fuska dashi kafin shi kuma yaja motarsa suka fara tafiya a hankali kasan cewar ruwa ake yi sosai tamkar da bakin kwarya.
"Ke wai daga ina kike haka cikin wannan ruwa?"
"Please sir I told you am not ke, kace min Aisha and daga school nake.."
"K'arya ne ya aka yi banga students ko d'aya ba sai ke kad'ai zaki tsaya yi min wani turancin banza."
"Hmmm oga Sadeeq you don't know justice is the best policy ko?!"
"Kut..!" Ya fad'a ba tare da ya san ya fito fili ba sabida tsananin mamakin ta da d'aurewar kai jin abinda take ce mai. Juyawa yayi yana kallonta tana goge fuska ya cije lips d'insa na k'asa har suka k'arasa bakin gate d'in gidan ta, tayi niyar fita taji motar a kulle sai ta kallesa tace.
"Malam Sadeeq we are here fa, please ka bud'e min zan fita thanks for the help."
"Karki fito ki zauna a ciki na gaya miki."
Yafad'a tare da zarar mukullinsa na gidan ya fita da kanshi. Kallo tabishi dashi sai tayi murmushi lokacin ta tuno da Abubakar sam baya d'aure mata fuska tun lokacin da ya d'akkota daga Saye, yakan yi mata duk abinda zai satayi dariya ko tayi farin ciki amman wannan gadai kaman nin sak amma zuciyar ta banbanta.
Dawowa yayi cikin motar shima duk ya jiki, shigar dasu yayi har parking lot da yake k'arami ne dai-dai mota d'aya INdo ta bud'e ta shige d'aki kasan cewar babu nisa befi taku hudu ba. Shima yana gama parking ya shiga falo bata nan ya wuce bedroom d'inta, tsaye ya ganta d'aure da zani ta juya baya wanda da alama da taji motsinsa ne tayi saurin yi.
A hankali ya taka yaje har kusa da ita ya tsaya, matsawa yaga tayi gaba shima ya matsa har takai k'arshe sannan yace.
"Go on.."
"Aisha you're beyond my control ko meye dalili ne?!"
"Because we don't love each other."
"You dai but me...."
Yayi shiru yana kallon keyarta don har lokacin bata juyo ba sabida wani dalili nata da bata son ya gani. Ji tayi ya rungumeta ta tayi saurin rintse idanuwa jin yadda tsigar jikinta ta tashi yarrr yana k'ok'arin d'ora hannun a saman cikinta tayi saurin rik'e mai hannu.
"Please don't touch me."
"Akan wane dalili? Shin Aisha an hanaki yin yaren Hausa ne?"
Tayi shiru tana kauce mai da sauri ya finciko ta suka fad'a kan gado har zanin da tayi d'aurin k'irji dashi yana zamewa tayi saurin tashi a firgice shi kuma yasa hannu ya dawo da ita duk da cewar kayan jikinsa a jik'e suke.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un malam Sadeeq ka tak'aita ni k'il...!"
Da sauri ya mik'e zaune jin abinda ta fad'a, itama ra mik'e cikin kid'ima ta sauke zanin k'asa ya zamana bra ce kawai tayi saura daga cibinta zuwa sama, hannunta a saman cikinta daya d'an fito wanda ba kowa yake gani ba idan ba kwance pzani tayi ba ko kuma tasa t.sheet yaga tana shafar cikin bakinta a cune tana shirin yin kuka yace.
"Aisha what's going on.? Ciki gare..Ki..ne...!"
Bata lokacin da ta d'aga mai kai ba sabida Asma'u tace mata kar tayi abinda zai sa cikin ya samu matsala yau gashi Sadeeq zai nakasa mata shi. A zabure ya dawo k'asa idanuwa waje INdo na hawaye ta narkamai harara mai tattare da tsananin bak'in ciki ya kalleta k'irjin nan fam ya kuma yin kyau cikin in'ina yace.
"How come's daga yi d'aya...?!"
"Ka kaini asibiti nidai, idan ba bakayi ba yau ai gashi ka dauje ni."
Ya akai haka daga one day wanda yasha matuk'ar wahala ace mai tana da ciki ga Fateema da suka dad'e tare ko 6atan wata bata ta6a yiba amma INdo nada Ciki.., ya kuma kallonta sai hawaye take yi bayan ta gyara d'aurin zaninta gashi har lokacin ruwa ake tsugawa Sadeeq ya koma kan gadon tare da zama a bayanta a hankali ya rungume ta tare da rintsa idanuwansa yana jin wani feelings har cikin k'ahon zuciyarsa.
"Aisha Allah ne ya baki Abubukar a lokacin da zaku fara sabuwar rayuwa sai ya d'auke sa ba tare da kowa yasan manufar yin hakan ba, an had'a mu aure ba tare da muna so ba sai dai ko wannen mu ya d'auki hakan a matsayin kaddara. Aishi kiyi hakuri ki gafarce ni wallahi ko wanne tafiyar dani nayi tane cikin damuwa da tashin hankali amma ke babu abinda ya dameki why."
"Nidai ka kaini asibiti kawai dan Allah."
"A cikin ruwan nan? Dama gashi kinje kin kaimin shi ruwa ya jibgeshi k'ilama kinja mata/masa mura."
Sake rik'ota yayi sosai a jikinsa yana yawo da hands d'insa tayi d'if, ganin haka yasa Sadeeq matsawa ya kwantar da ita kan gadon ya kura mata kyawawan idanunsa yana shafar cikin ta a hankali saitin kunnanta yace.
"How many months."
INdo ta kawar da kai tace "Ai bakaso ka dawo ka tarar dani a raye ba malam Sadeeq, sabida tunda ka tafi ko please call me baka ta6a gigin yi min ba. A gabana kasha yiwa Fateema waya sabida ita *Son ranka ce* ni kuma *Za6in iyayanka* hakan yasa baka san komai daya danganceni ba. Duk surutuna wallahi danaga kana yin haka ka watsar dani yasa nak'i nunawa kowa ina da ciki sai Asma'u da Mama sune kawai suka sani, sai gashi Allah ya raya ni da abinda yake cikina cikin k'oshin lafiya. Baya sani wani laulayi yadda neke komai a baya haka nake yi har yanzu.
Malam Sadeeq baka sona sabida kasan cewa ta 'yar kauye, matalauciya, marar Ilimi. Karka manta Allah dayayo ka cikin wadata bawai yafi sonka bane, Allah dayayo ka hazik'i fasihi mai d'in bin basira bawai dan yafi sonka bane ko kuma dabarar ka da iyawarka ba kawai hakan ma jarabawa ce sai gashi kana min gori akan hakan. Shin ka manta twinnie broth d'inka duk ya fika wannan felek'an amma da Allah ya tashi sai ya bashini, ya zamto a duniya ni yake so har ya koma ga mahaliccinsa. Shine mutum na farko daya fara tsamoni daga k'angin wahala da toshewar kwakwalwa Allah ya gafarta mai haka kuma har cikin zuciya ta yana nan I will never forget him..never..never...."
"Kiyi hakuri Aisha."
Yayi maganar jikinsa a sanyaye, INdo ta share hawayen fuskarta tana cizon lips, ruwan da akeyi ne ya haddasa wani sanyi me ratsa cikin tsokar mutum hakan yasa INdo takure guri d'aya, Sadeeq na ganin haka ya xura kansa cikin wuyanta idanunta a lumshe yace.
"Aishi kinyi hakuri kin yafe min? Namiki alk'awarin maye miki wanda yafi Twinnie d'ina, bazaka sake yin kuka dani ba har nima lokacin da tawa zata kasance. Ina son ki bani dama na shiga cikin rayuwarki nima na d'an yi miki koda rabin abinda Marigayi yayi miki ne, ina rok'onki alfarma ko yaya ne ki bari muyi rayuwa tare."
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
_Na baku page d'in nan kyauta danjin dad'in ku, *Home of novel, Tsakar Munay, Zauren Sadeeya, Khadija candy, Rano online, Feedohm novella, Dandalin Billy bilya, Basma elr Lele grp,* Tnxs n I really appreciate ur love's care's of d comment's_😍👍
Page *32*
'Dan zame jikin ta tayi daga nasa ta kallesa, "shin da gaske ni yake so ko kuma cikin dake jikina? Anya malam Sadeeq kana sona kuwa? Amma zamu gani idan gaske ne."
"Kin yi shiru."
Dariya ce ta su6uce mata ganin yadda yake kallonta tamkar wani mara lafiya, ganin tana dariya yasa shi jin wani farin ciki har cikin ransa ya kuma janyo ta cikin jikinsa yana shafarta, ba zai mata komai ba dan karma tayi tunanin dan hakan yake sonta yanzu gara ya daure ya hakura ana d'auke ruwa kawai ya gudu gurin Fateema tunda Allah ya kasa ya bashi biyu.
"Kana ganin yanzu babu abinda ya samu cikina?!"
"Insha Allahu karki damu, ko kina jin wani ciwon ne?"
"A'ah bana jin komai ni sai yunwa."
"Okay sorry bari ruwan naga ya fara d'an tsagaitawa sai na samo miki wani abun kici. Bafa ki bani amsa ta ba Aisha baki ce kin yadda zaki zauna dani ba."
Dariya da kuma yi tunowa da maganar Asma'u da tace tayi hakuri wata rana sai labari, shi gani zai yi kamar an shiga rayuwarsa ne shida Fateema amma tunda had'in Allah ne wata rana sadeeq zai kulata sai so ta koda bekai na Fateema ba tunda har Allah ya kuma had'a su a bed gashi harda rabo.
"Aisha me kikema dariya ne? Ko gemun dana tara kikewa dariya.?"
"Kai a'ah wallahi ni ina ruwana da wani gemu."
"Toh kina so kenan in barshi yamin kyau?!"
"Lalalah bance ba yadda kagani kai dai, kuma tunda ka barshi ai kowa yasan so kake yi taya za ai nace beyi maka ba ni INdo."
Tayi maganar tana rik'e ha6arta cikin nuna k'ask'anci dan ta san bata kai wannan matsayin ba da har zata bashi umarni yabi ba. Yatsansa yasa a goshin ta wajan billenta yana shafawa ta lumshe idanuwa tana tuno Abubakar sabida duk sanda zai ganshi sai ya ta6a mata shi, sai dai idan ta d'aura d'an kwali ta cukaro shi ya rufe shine kawai ba zai ta6a ba.
"INdo malam Hamza...! Wai me yasa ake ce miki haka ne, a memakwan Aishat Hamza."
Ya fad'a cikin wani irin style wanda yasa ta kalli cikin idanunsa shi kuma ya kanne mata nasa tayi murmushi tare da cewa.
"Haka mutane suke kiran baban mu, toh lokacin da aka sani a makaranta dama kowa INdo yake cemin banda Inna ita sai dai tace min 'yar nan, shi kuma baba yace min uwata shine da aka kaini sai aka tambaye ni sunana baban mu yak'i fad'a ni kuma karna fad'i sunansa sai nace INdo Malam Hamza shine kawai sunan ya zama haka."
"Ummm! Good, toh yanzu kuma fa a school? Ko har yanzu kina nan a INdo malam Hamzan?"
"No..no..noooo, Aishat Hamza tun lokacin da Mubasheer yaje yamin registration ya saka min haka shikenan nima na cigaba da sawa."
Kallonta yayi yaji wani mugun tausayinta sai dai shi kansa yasan ya makaro, tun a baya ya kamata yaji tausayinta amma beji ba ganin batada nutsuwa a memakon ya tallafa mata sai ya k'ita sam baya k'arfafa mata gwiwa akan sha'aninta amma ya zai yi da sharrin zuciya dana shed'an, yasan dai marigayi shine ya kwashe ladan gashi har yau da baya duniya ta kasa manta shi. Yana fatan shima wata rana tayi mai irin wannan abun ko yana da rai ko kuma lokacin yabi d'an uwansa.
Uban ruwan daya jibgeta ne gashi kuma ya rungemata a jikinsa ta takure yasa wani daddad'an bacci ya sace ta ba tare da tasani ba. Shima sai da ya janyo ta yaji jikinta ya saki hakan yasa shi leken fuskarta kawai sai yaga ashe har tayi ya bacci, ya juya yadda zai dinga kallon fuskarta ya kura mata ido.
Ya dad'e yana kallon kyawunta mai kwantar da zuciya kafin yayi murmushi tunowa da yayi sanda ta d'auke mai naira d'arinsa daya je siyayya. A hankalli yaka sanya hannunsa saman cikinta yana shafawa zuciyarsa na tsananin harba mai cikin wani masifaffan son kasancewa tare da ita ya kai lips d'insa kan nata ya sumbace shi sannan ya mik'a a hankali ya sanya mata pillow a inda ya tashi tare da rufa mata lallausan bargo ya mik'e da sauri kasan cewar an tsayar da ruwan har an fara k'iraye-kirayan sallar juma'a.
Cikin sand'a ya fitar da motarsa sannan ya kulle mata gidan ya tafi gidan Fateema da zafi-zafinsa. A k'ofar gida yayi parking motar ya tura gate d'in a kulle, wayarsa ya janyo ya kirata ringing d'aya ta d'aya cikin murna da zumud'i tace.
"Allah yasa dai baby haka zaka cemin ka iso cikin Kano..?!"
Muryasa cikin murmushi yace.
"Fito ki gani ina gate."
Zaro idanuwa Fateema tayi tamkar tana gabansa cikin sanyayya murya tace.
"Baby kadawo kana waje? Please I'm so sorry kaga yanzun nan muka tashi yara sabida ruwa, dan Allah baby kajira ni in k'araso."
"Okey toh kiyi sauri kinga karna rasa sallahn juma'a."
"Toh godiya nake baby na sai na k'araso."
Sallama tayi da sauran malamai matan da suka fito tare, cikin sauri ta tari Napep kafin wani sakannin har ya kawo ta. Cikin mota ta tarar dashi ya ziro k'afarsa waje hannunsa rik'e da wayar marigayi yana kallon pic's d'insa dana INdo wanda yayi mata tun tana INdo malam Hamza ranar da taso cin atamfa Allah beyi ba, dana d'aurin aure harda wad'anda suka yi a Munjibur park da wad'anda yake mata a cikin gida sai dai duk babu hotan banza a ciki Fateema na k'arasawa wajan Motar yayi saurin zura wayan a cikin aljihunsa.
"Oyo-yo baby nah, taho mushiga ciki."
Ta fad'a tana kallonsa cikin murmushi tare dayin gaba ta bud'e k'ofar gate d'in shi kuma ya biyo bayan ta. A parking lot ta tsaya yana shigowa suka rungume junansu cikin nuna kewa kafin yace.
"Bari nayi alwala naje nayi sallah kafin na dawo ki samar min wani abincin kiyi da d'an yawa za'a kaiwa Aisha na biya naga ashe batajin dad'i."
Kallansa tayi tana dariya tace.
"Wai wannan uban k'asumbar daka tara gashi hardasu gemu duk na meye."
Shafar faskar yayi yana tafiya yana cewa.
"Baby wannan gemun na komai ne wallahi, hmmm danma Allah ya temake ku a iya tara gemu na tsaya, bari dai naje na dawo please ki d'ora girkin."
Dai-dai lokacin suka shiga cikin Falo ya shiga toilet ita kuma tayi bedroom d'insa dan k'ara masa k'amshi duk da cewar kullum tana k'amsasa shi. Yana yin alwalan ya tafi masallaci, ana idarwa ya wuce gidan su suka gaisa dasu Mama tana tayin murmushi a tunaninta be fara ganin cikin INdon ba tasan zai yi murna d'an k'aniya da ana bashi yana nuna baya sonta.
****
Yana dawowa ya tarar ta gama dama already tana da miya wadda tayi jiya tasha kifi sai k'amshi takeyi. Rungume ta yayi cikin tsananin so da buk'atuwa domin da k’yar yayi sallah banda ta juma'a ce da bazai yi ba sai ya fara samun nutsuwa. Sannan baya son komawa gidan INdo da wannan matsalar dan kar tayi tunanin hakan ne yasa shi cewa su shirya yanzu yana sonta, ya fison ya fara nuna mata yanzu ita d'in yake so kafin ya fara nuna mata ainihin waye shi.
Bedroom suka koma hakan ya tayarwa da Fateema hankali dan tasan a wannan yanayin ita yak'e muradi gashi ita kuma tana period ya zata yi mai? Ganin yadda yake mata zafi-zafi yasa ta rik'o hannunsa tare da kwato shi saman k'irjinta murya a karye tace masa
"Sorry baby.."
"For what.?!"
Ya tambaye ta yana matsar ta da gashin kanta, nuna mai tayi hakan ya tayar mai da hankali duk iya k'ok'arinta na ganin ya samu nutsuwa abin ya faskar sai da kawai ya nuna mata yayi normal sabida baya son damuwarta yasan da zata iya d'auke blood d'in da yanzu tayi.
"Baby Ina abincin Aishan, kawo naje nakai mata zan biya can gurin Anas akwai abinda zan k'ar6o a gurinsa."
Kallonsa tayi tasan k'ila yaje gurin Aisha, amma a k'a'ida yau itace dashi sai dai baxata so ta ganshi cikin matsala ba, tayi murmushin yak'e tana shafar gashin da ya lullu6e k'ewayan bakinsa tace.
"Yana falo na zuba."
Tashi yayi ya mayar da kayansa ta rakosa ya d'auki basket d'in k'irjinta na bugawa dan tana zargin akwai abinda zai had'asa da INdo amma tasan basa shiri zai iya sharewa ya jira har lokacin da zata samu tsarki.
"Bye-bye baby ina dawowa zanci abinci nayi bacci dan agajiye nake munyi kwanan mota."
"Toh sai ka dawo ayi mata sannu, kona zo muje tare?!"
Kallonta yayi na 'yan dak'ik'a kafin yayi murmushi yace.
"Yanzu kika dawo daga gurin aiki, sannan kice zaki fita bayan mijinki ya dawo daga tafiya me nisa. No ki zauna ki tanadar min dadd'ar hirar da zaki min idan na dawo."
Fateema tayi dariya tare da d'aga mai hannu ya fita tana kallonsa kishinsa fal cikin k'ahon ziciyarta.
Yana fita ya shiga mota yayi gidan INdo, yana zuwa a bud'e yaga gidan yayi parking a gefen gidan ya d'auki kayan abinci ya Shiga. Babu kowa har ya shiga cikin bedroom d'inta bayan ya ajiya abincin a falo. Tararwa yayi ta idar da sallah, ya tsaya a bayanta yau INdo ce take sallah harda su addu'a, lallai Allah buwayi mai sauyin lamari kamar yadda ya sauya salon alak'arsu daga malamin ta zuwa mijin twinnie d'insa daga nan ya sauya zuwa mijinta.
"Humairah."
Taji ya fad'a k'irjinta yayi tsananin bugawa tayi saurin waigawa tana kallonsa ido waje. Murmushi ya sakar mata tayi saurin d'auke kai dacta ya fad'a mata jin muryar data fara kiranta da sunan. Anya ba munafuntar ta akayi ba Sadeeq ya mutu aka raina wayonta aka ce Abubakar ne, anya shima ba yaudararta yake yi ba aka had'a baki dashi zasu raina mata hankali.
Bata gama dai-dai tuwa ba taji ya zauna a kusa da ita har suna gogar juna ya lek'a fuskarta tare da cewa.
"Tunanin me kikeyi haka? Ni ko Abubakar."
Ta zame hijjab d'inta ba tare da ta kallesa ba. Shin me yayi mata a cikin rayuwarta da zata wani dinga tunaninsa, wanda yayi matan ya koma ga Allah ko kuma dan yayi mata ciki shine zai sa ta dunga tuna sa kila haka yake nufi.
"Okey yanzu bazaki kulani bama.?"
"Welcome back malam Sadeeq."
"Sai da na rok'a, ai ba haka kikewa M twinnie ba oya hug me."
"Kitchen zani mafa ko indomie na dafa, nasan dai kai bazakaci ba."
"I said kiyi min Oyo-yo, kamar yadda kika min ranar danaje d'akkoki kika yi tunanin marigayi ne, oya am waiting."
Tura baki tayi tana mamakinsa ganin irin yadda dacta yake mata abubuwa tace.
"Ni a'a, ka kyaleni naje wallahi inajin yunwa."
"Na kawo miki abinci, amma sai kin min oyo-yo sannan zan baki."
A hankali ta juya ganin ya takura mata ta rungumesa bayan ta rintsa idanuwa. Jin k'irjinta a nasa ya sashi jin wani shock ya sanya hannunsa ya mak'alota gabaki d'ayanta jikinsa ya hau rawa tana jin haka ta kwace kanta ya samu da kyar yajata suka fita falo.
Da kanshi yaje ya d’akko plate a kitchen ya zuba mata, tunda taji k'amshin kifi take jin tamkar ta cinye abin miyar ya zuba musu tare sai kallonsa take yi ganin yanzu yana mata wasu abubuwan da marigayi yake mata hakan kuma ya sa ta d'an sakar masa tun yana bata a yangance taji ko abinda ke cikin nata besan ana bata abinci ba yasa ta cewa.
"Kawo ni na dinga baka gaskiya."
A tunaninsa ko ta fara sonsa yayi murmushi tare da sakar mata spoon da pork d'in, idan ta bashi sau d'aya sai tayi kusan spoon biyar sannan zata kuma bashi, ya dinga bin fuskarta da kallo yana jin wani abu tamkar magnet yana fisgarsa. Sai da suka k'oshi sannan ta kwashe kwanukan takai wajan wanke-wanke yana binta da kallo duk da cewar doguwar riga ce a jikinta sai dai komai na jikinta rawa yake yi Sadeeq ya jingina da kujera shi kam bazai iya kwana a haka ba, tunda yasawa ransa idan ya dawo zai samu nutsuwa koda a gurin Fateema ne toh gashi tana off yayi 3mothns a wahale bazai iya kwana haka ba.
"Sir Sadeeq na gode sosai, a cewa Fateema itama na gode ga kwanukanta."
INdo ta fad'a tana k'ok'arin ajiye kwandon akan center table. Shi kuwa tamkar me bacci haka yayi nan kuwa yana kallonta ta k'asan ido yaga tana kallonsa jin yayi shiru yasa ta shiga d'aki ta zauna a bakin gado tare da d'akko jakar makarantar ta ta fito da books d'in wanda duk iya kunshesun da tayi a jiki saida ruwa ya ta6a su ta bubbud'e su akan gado tana turo baki ganin duk sun sha ruwa.
Ta bayanta taji ya rik'o ta, sharesa tayi ta cigaba da hura book d'in hannunta da baki ya sa hannu ya k'ar6a ya ajiye akan gadon ita kuma ya jata suka kwanta akan gado INdo tace.
"Ana k'iran sallar la'asar."
"Uhmm naji Humaira but I need your help please."
"Tofa name.?!"
"I need you, dan Allah humaira karki min wata fassarar karki hanani ina cikin matsala humaira wallahi I love you... I love you Aisha karkiyi tunanin kodan wannan abun ne."
Jikin INdo yahau rawa ta fashe da kuka tana jin yadda yake mata amma ta kasa hanasa domin tana jin hirar matan ajinsu akan mazajen su. Shi kuma jin bata yi masa irin na farko ba yasa shi cikin karyar da kai da nuna tsantsar nadama yasa har ya cinma muradinsa akan ta sannan shima yahau yin nasa hawayen.
_"Twinnie kasan nifa ni bazai yuwu nazo gidana naga matata ba sannan na kyaleta ba no Zuciya ta baza ta bari bama tunda nasan mallakina ce."_
Ya tuno irin hirarrakin su da Abubakar cikin shak'kk'iyar murya Sadeeq yace wa INdo.
"Skukran-laki Aisha Humaira. Do you love me? Please humaira love me as I love koda na iya yau ne kawai."
"Malam S.."
Ya rufe mata baki da nasa cikin son katse ta da sunan da yaji zata kirasa sannan ya cire yace.
"Don't call me malam again. please change my name in dai har kin yadda zaki soni kamar yadda kike son twinnie d'ina."
Hannunsa zagaye da wuyan ta suna had'a numfashi INdo tace.....
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
Page *33*
"Toh mezan ce maka? Kaga kaima Fateema ka fara aura, kuma ita kake so kafin ni. Toh nima ina sonka amma nafison marigayi dacta nima kaga ma an raba kar wani yaji haushin wani."
Fuskarta yakai dai-dai tata ya had'e hancinsu guri d'aya yana rik'e da hannunta yace.
"No Humaira wannan ba magana bane har yanzu ke yarinya ce. Idan nace zan dinga nuna miki soyayyar Fateema a fili zaki sha wahala tunda kinga ina nuna mata itama zata fallasa nata. While ke kuma idan kika ce zaki fifita soyayyar m twinnie a gurina babu abinda zanji sabida yadda muke dashi kuma baya raye bare ya dinga rama miki kamar yadda zamu yi nida Fateema a gabanki. So kidena kawo wannan abun a ranki yanzu ni zaki saka a cikin zuciyarki ba wani ba."
INdo ta juya baya tare da cewa.
"I love him tayaya zank'i fad'a kawai dan ya mutu? Dama haka soyayya da amana take idan ka mutu a shafe babin rayuwarka? No gaskiya nayi mai alk'awarin bazan manta da shiba har k'arshen rayuwa ta."
Rintsa idanuwa Sadeeq yayi, sam
Baiyi tunanin zaiji kishi haka ba amma yaji ransa na sosuwa jin yadda take cewa tana son wani mamaci ba shiba. No wonder mutane suke tsoron auran matar mamaci sabida koyaya zaka yi mata abu sai ta fad'esa ta nuna maka yafika, shi kam ya shiga uku gashi wani sanyayyan sonta sai sake shigarsa yake. Ba shakka indai haka Abubakar yaji a baya dole ya rikice yace yana sonta a duk yadda take, dole ya kira ta zuciyarsa sabida yadda a yanzu ta kuma shiga cikin tunanin Sadeeq d'in.
"Juyo toh kiji."
Yayi maganar yana kallon bayanta, a hankali ta juyo sai dai idanunta a kulle suke gam yace.
"Zaki bini idan zan koma kwara state? Karki ce min a'a kinga ina son hakan so nake na shirya yadda zanyi tun daga yanzu."
"Kai karatuna fa?!"
"Karki tashi hankalinki kina dani zan dinga yi miki wannan makarantar duk k'aryar banza ce. Ki bini kigani zaki sha mamaki in a few days."
(Kunji wayo... Wai makaranta ce karyar banza dan kawai yana son yi mata wayo maxa..maza mutanan mu).
"Amma kuma fa malam Sadeeq..."
Yayi saurin katseta bayan ya janyo ta jikinsa yana zagaye hands d'inshi a k'irjinta yace.
Shhhii “ba anan zaki dinga kirana malam ba sai munje teburin d'aukar darasi but wannan gurin kam ki dinga kirana da wani sunan special da zai zama kene kike k'irana dashi”
“Kamar irin su honey, sweetie, heartbeat, July juice, mango, touch light, tomato, vest....."
"Ke.. Ke..! Uhm..uhm duk wannan sunan fa, na waye ne.?!"
"Toh ai lissafo maka nakeyi sai ka za6a a ciki."
"Shine harda su July juice, vest, tomato? You ko.."
Ya fad'a tare da ja mata hanci tayi dariya har hak'oranta suka fito murya k'asa-k'asa tace.
"Ashe kaima wata ran kanada kirki..?!"
"Eh dama kece bakya lura but yanzu ai kin fara gani, tashi muje muyi wanka gashi bamu yi sallah ba."
"Toh amma ka fara yi."
"A'a tare xamuyi tunda komai tare muke yi."
"Innalillahi nidai gaskiya ka fara zuwa ka yi."
"Yauwa kin tuna min ma, baki gaya min ba zaki bini muje? Kinga a lokacin nake son dana koma na sake bud'e wani gurin kema ya kasan ce idan muje kina da naki d'akin, bana son business a nan sabida sa ido da nan kawai zan dawo gabaki d'aya."
Shiru INdo tayi dan a gaskiya bata son zuwa garin tunda yanzu ta fara iya turancinta, itada ba kwarewa ta gama yi ba kawai ya jata su tafi sai sun je shima ya sauya mata tana tsoron Allah tana tsoron butulcin d'an Adam.
"Tunda ba gobe zan tafi ba zan kyaleki kiyi shawara kinji?!"
"Toh."
Ta fad'a ya mik'e ya shiga toilet ya tarar musu ruwa ya dawo, da kyar ta bari suka je wanka suka yi tare duk da dakyar ta tsaya.
Sai da suka d'auro alwala sannan suka fito yana rik'e da ita duk asan samunsa na ganin ta aminta dashi ta saki jiki ta kuma yadda da shid'in me sonta ne da gaskiya. Riga tasa ta atamfa da skirt sannan ta shimfid'a musu sallaya ta bishi da kallo ganinsa a zaune bashi da niyar sa kaya tace.
"Sallan fa, kona yi tawa?!"
Ido ya lumshe tare da hura iskar bakinsa yace "wane kayan zansa.?!"
"Lallai ni ina na sani, ai kasan fa ko hularka babu a cikin gidan nan. Nidai bari nayi tawa sai ka tafi gidan Fateema kayi acan."
Tana fad'a ta fara k'ok'arin tayar da sallah ya mik'e tsaye tare da tsayawa a gabanta yace.
"A'a bari nasa riga ta ai doguwa ce ta rufe min gwiwa."
"Nashiga uku haka zaka yi babu wando ji kafafuwa a waje a haka zaka yi sallan? Oh ni INdo..."
"Eh aini an hallarta min yin hakan kune dai aka haramta muku yin sallah idan baku lullu6e jikinku duka ba, Allahu akubar²."
Taji kawai ya tayar. A ranta kawai ta barsa dan tasan sallar malam Sadeeq bata kar6u ba. Suna idarwa sai ga su Haleema tayi sauri zata mik'e ta fita Sadeeq ya rik'ota suka yiwa juna kallon ciki ido.
"Ina zaki?"
"Su Haleema nefa ba kaji muryar su ba."
"Naji amma ai baki tsaya kinyi addu'a ba kamar d'azu, zo kiyi addu'a sai ki fita gurin nasu."
Komawa tayi ta zauna su kuma sai rangad'a sallama suke yi jin shiru yasa Aminatu lek'awa d'akin.
"Au ashe sallah suke yi Yaya ma nanan."
Guri suka samu a falon suka zauna suna jiran fitowar su. Matsawa yayi kusa da ita tana addu'a saitin kunnanta yace.
"Kiyi mana addu'a, amma dan Allah karki rok’ar min mutuwa da gaggawa."
Bata juyo ba tayi murmushi jin abinda ya fad'a. Shi kuwa tsoran irin addu'o'in da takeyi mai a baya ne yasa shi fad'ar haka yanzu tunda sun fara shryawa . Kuma mik'ewa tayi ya janyota tare da waigawa yana kallon k'ofa sannan ya sumbaci saman lip d'inta ta fita.
"Aunty Humaira ya gida??"
Ta zauna tana kallon Haleema sabida itace me kallonta tunda ta fito, INdo tace.
"Ke wai meye ne? Sai wani kallon tuhuma kike min."
"Kai aunty Humaira, missing d'inki nayi fa kinsan kwana hud'un nan duk a cikin hostel nayi su, bama haduwa sai naji kamar shekara nayi ban ganki ba."
"Oho ni kuwa banyi wani missing d'inki ba sabida kullum idan baki zoba bacci na nakeyi."
"Aisha.."
Sadeeq ya kira ta ta mik'e taje d'akin. Tsaye ta gansa yana gyaran hular kansa ta d'an tsaya nesa dashi ya janyo ta yace.
"Zan fita anjima zan zo muyi sallama."
Tace "Toh sai kazo."
"Is this all abinda zaki ce min?!"
INdo ta d'an kallesa kafin tace.
"Toh kayi shaving wannan gemun yayi ma yawa."
"Sunnah ce fa cutie amma tunda bakya so zan cire."
"Toh sai ka dawo."
"Kin gaji ne? Na tafi na baki guri ko?"
"Ah kawai kaga dai su Haleematu na nan."
"Okey bari naje na dawo, give me good bye hug."
Ya fad'a yana bud'e mata hannuwa, ya zata yi dole taje ta rungumesa ya matseta a jikinsa kafin ya sake ta suka fito tare, 'yan k'annan nasa suka gaidashi sannan ya fita ita kuma ta zauna gurin su suka sha hira har Aminatu ta dafa musu Indomie suka ci.
Sadeeq kuwa gidan Fateema ya koma, tare suka yi sallan isha sam be nuna mata cewar gidan INdo yaje ba nuna mata yayi yana kai abinci gurin Anas ya wuce. Suna idar da sallahn isha'i yace mata.
"Baby na bari naje can gidan nayi mata saida safe, daga can zan tsaya nayi aski ki dafa min tea kafin na dawo."
Fateema da shagwa6a tasan yana son shagwa6a tana jikinsa a tsaye tace.
"Gaskiya Baby karka yi aski ni dai ka barshi ina son shi yayi ma kyau."
Idanuwa Sadeeq ya zaro jin ita kuma abinda tace, INdo tace bata so ita kuma tace ya barshi tana so ya shiga uku.
"Menene naga ka zaro idanuwa haka? Shikenan jeka aske tunda baka son ka barmin kuma ina so."
"Ah baby na isa, tunda kina so ai dole na barshi uwar gida sarautar gida. Bari toh naje na dawo."
Fateema tayi murmushin jin dad'i ganin yana yi mata duk abinda take so. Sai da ta raka shi har gate ya juyo yana kallonta bayan yayi kalar tausayi yace.
"No bye bye kiss ko? Shikenan nayi fushi."
Da gudu ta rik'osa ganin zai fice tana dariya ta kamo wuyansa ya sunkuyo da kansa tayi kissing d'inshi tare da cewa.
"Sai ka dawo karka dad'e."
"Okey as you wish baby."
Sannan ya fita yana tunanin yadda zai yi musu. Su Haleema kuwa Sai wajan k'arfe takwas na dare sannan suka tafi gida ya rage sai INdo kawai tayi sallahn isha'i ta cigaba da gyaran littattafanta.
Jam-luck tasa hakan yasa yana sanya mukulli k'ofar ta bud'e. Shiga yayi tana jin motsinsa tayi saurin kwanciya tayi baccin k'arya. Kallonta yayi ganin yadda ta kwanta akan books d'in gashi ta kudindine fuska cikin bargo, ya k'arasa kan gadon tare da sanya hannu ya cire mata shi daga fuskar ta.
"Oh harma bacci kika yi bayan nace miki zan dawo ko?!"
Yayi maganar cikin kunnanta, INdo tayi mik'a alamar wai ya tashe ta sannan ta fara mistsike idanuwa murya a shak'e tace.
"Au ka dawo?!"
"A'a ina can."
Ya bata amsa yana kallon fuskarta ta wani maze tamkar daga baccin gaske ta tashi.
"Shikenan sai da safe in tafi..?!"
"Eh sai da safe amma 8:00am zan tafi makaranta fa."
"Ba nace kin dena zuwa ba?!"
"Kai malam Sadeeq weekend fa nake zuwa ita kuma Fateema yau da gobe bata da aiki kuma dama acan kake toh kaga ai ba abin hanani zuwa, ni dai gaskiya zani Ina son school d'in gashi malamin shima yana son yaga na iya wallahi yana da k'irk'i yana sona."
"Yana sonki kuma?!"
Cewar Sadeeq a mamakance, cikin rashin fahimtar fassarar dayayi ma maganar INdo tace.
"Eh wallahi har extra lesson yake min."
"What...!"
"Kai malam Sadeeq dafa ace bankai kaina wannan makarantar ba da nasan wallahi har yanzu baxakai marmarin so naba. Toh meyasa yanzu na shiga kake kuma k'ok'arin rabani da ita bayan akan rashin iyawa t...."
Be bare ta k'arasa magana ba taji bakinsa cikin nata. Irin deep nd passionate kissing d'in nan ya dinga tura mata har jikinta ya kasa d'aukarta ta shiga biye mai ba tare da tasan ta iya hakan ba. Cikin rashin sani suka sake kasan cewa da juna musamman Sadeeq da sai da ya jima sannan ya gano da tabbacin abinda ya sake faruwa.
"Na barki... Na barki Humaira kiyi karatunki zan cigaba da baki nawa gudun mawar insha Allahu. I love you with all my heart and soul Aisha please say you love me dan Allah...."
Shiru INdo tayi ta kasa fad'a ji take yi tamkar idan ta fad'a tayi k'arya dan bataji wani love dinsa ba dazai iya sawa ta gaya masa.
"In tafi bakya sona ko?!"
"A'ah ni bance ba, amma ka tafi dare nayi Fateema na jiranka."
"Aisha bakya sona ko? Shikenan."
"Toh ina sonka, aini bance bana sonka ba."
Agogo ya duba yaga sha biyu saura minti goma, da kyar ya tashi ya sa kaya INdo na kwance idanunta a rufe yaje ya sumbaceta sannan ya tafi ya kullo mata gidan da mukulli.
Yana zuwa ta dinga kallonsa wanda yasa shi tsarguwa yayi murmushi tare da d'aukar ta suka wuce bedroom. Romance d'inta ya dinga yi har sai da ya nuna mata shima fa yana buk'ata yasan hakan ne kawai zai wankesa da zargin da ya hango a cikin idanunta, ganin ya fita birkicewa ne kuma ya tayar mata da hankali ta koma bashi hakuri tana lallashinsa sannan yace.
"Toh baby ya zanyi bari kawai naje nayi wanka amma kwanakin da kikeyi sunyi yawa har 7days."
Tana nan kwance yaje yayi wanka ta had'a masa tea yasha sannan suka kwanta bacci bayan sun nanik'i juna kamar za'a sace d'aya.
Sai da yayi kwana biyu a gidan Fateema sannan ranar lahadi da daddare ya koma gidan INdo wanda a lokacin sai da tayi rok'on zuwan period amma ina sabida cikin jikinta gashi a gurinta kawai yake hucewa tunda ya dawo har ta fara jin haushinsa amma baya damuwa bare ya nuna ya gane nufinta.
Abu d'aya yake mata ya d'auke hankalinta shine zai ce tazo suyi lesson wannan abun kawai yake sawa yaga ta sakar mai jiki har itama takan faranta masa ta hanyar kwanciya a jikinsa.
Sadeeq kuwa ta k'arfi da yaji ya zama mak'arya ci a gurin INdo sabida tace bata son gemun Fateema kuma tana so dole yace wa INdo inda ake mai askin ne suka yi gobara yanzu gyara gurin suke yi sai sun gama, gashi shi baya son zuwa ko'ina idan ba gurin ba. Ita kuma Fateema ya rasa yadda zai sanar mata da cikin INdo domin zata yi mamakin tayaya hakan ta faru shida baya nan har tsawon 3months.
***
Ranar Sunday misalin k'arfe 4:30pm Sadeeq da Fateema suna toilet sai rigima suke yi ya rik'e mata hannuwa yana cewa.
"Bake kika hanani yin shaving d'in ba dan haka yanzu babu abinda zai sa kice sai nayi tunda kina so."
"Nidai to yanzu ka rage please, Allah yanzu ta sake yin yawa."
Ganin ta kafe ne yasa shi k'ar6a yayi ya rage iya yadda yake barinsa sannan suka yi wanka suka fito. Shiryawa sukai ko wannce cikin shigar daya fiso sannan suka fito zuwa gidan INdo dan can gidan su Mama zai kaisu ana kawo kayan sa ranar Haleematu.
"Wait anan inje insa ta fito karku shiga ku shantake."
Tashi yayi yashiga gidan ita kuma ta zaro phone d'inta ta kunna data kafin su fito. Yana shiga zaune ya tarar da ita tayi shirinta tsab mayafinta a kan cinyarta yayi sallama ta amsa tare da kai idanunta kansa, har ya k'arasa bata dena kallonsa ba ya mik'a mata hannu ta bashi nata ya d'ago ta tayi murmushi tare da cewa.
"Ko kaifa da kayi wani kamar tsoho.."
"Okey ko shi yasa ma kallon tsufan da kike min yasa kikak'i kar6ar tayin soyayyata?!"
"A'a nidai ban fad'a ba."
Yana rik'e da hannunta ya durkusa yasa gwiwarsa d'aya a k'asa d'ayar kuma ya ajiye ta kamar dai yadda turawa sukeyi yana faman kashe mata narkakkon eye's d'insa yace.
"Humaira kina sona?!"
Ta kallesa ta tuna ajinsa da matsayinsa da kud'insa da martabarsa tun tana cikin duhun kai amma yazo yana rok'on ta so shi duk da har yanzu bata kai matarsa ilimi ba amma itama ta waye dan duk wanda ya kalleta sai yayi tunanin ko ta kammala degree ko tana kanyi. Murmushin jin dad'i tayi sannan tace.
"Ina sonka amma sai kayi k'ok'arin wajan Musanya Zuciya ta daga kan doctor domin har yanzu yana cikin Zuciya ta bazan munafince kaba."
"Aisha...! Are you in your right sence?I'm your husband but kullum sai kin min zancen marigayi why? Please we should help ourselves in one way or the other. Yanzu dai am asking you kina sona??"
"Eh ina sonka.. I love you."
Yana jin ta fad'a ya mik'e tsaye tare da yi mata alama da ta zo su wuce. Har ya d'an tafi yaji ta rik'osa ya kalleta fuskarta a narke ya tsaya yana zaro ido yace.
"Menene kuma?!"
INdo tace "kayi hakuri nafa ce ina sonka."
Rik'ota yayi yana murmushi sannan ya kar6i mayafin ya yafa mata suka fito ya kulle falon still yaga tana kallonsa yaje ya rungume yana cewa.
"Is okay cutie na yadda but sai kin fara nuna min from now on kinji ko?!"
"Toh.."
Ta fad'a tare da gyara swagger bag d'in hannunta. Itace ta fara fita shi kuma ya tsaya rufe gidan. Zaune taga Fateema tana danna waya a gaba ta yatsina fuska ganin sai dai fa ta shiga baya sannan taje ta zauna suna yiwa juna kallon yake har ya shiga shima ya zauna ya tayar da motar suka tafi.
Suna zuwa tare suka shiga lokacin har an kawo kayan anata gani.
'Dakin Mama suka shiga nan suka ga su Hawwah aikuwa suka had'u suna ta hirar su. Har aka yi magrib suna tare sai da INdo ta cire mayafi ta shiga toilet tayo alwala tana fitowa taga suna kallonta alamar dai sunyi gulmarta Hawwa tayi dariya tare da cewa.
"Su aunty Humaira kuma ashe-ashe...."
INdo ta ta6a baki cikin rashin fahimta tace.
"Ashe-ashe me?!"
"Wallahi matar broth wannan ciki ne, haba shi yasa sai wani shining kike yi sannan kin kuma yin kubul-kubul ga shi kuma ya fita."
"Toh ai ba haramun bane ko kin manta a gidan miji nake. Allah sister Hawwah keda Hali dubu (Haleema) kun saka min ido ya isheku haka."
Tunda suka fara magana Fateema take kallon cikin INdo, tabbas wannan ciki ne ba te6a ba. K'irjinta ne ya dinga bugawa yana mata wani rad'ad'i har tana jin tamkar zai fasa mata zuciya. Lallai no wonder taji Sadeeq yanzu baya mata zance yana son yaga ta haihu ashe tuni yaje ya kunsawa INdo.
Babu wanda beyi magana ba a cikin d'akin face Fateema domin idan tace zata tanka babu shakka hawaye zata yi har a samu wasu suce bak'in ciki takeyi mata, sai kawai tayi shiru dama a kwance take hakan yasa ta lumshe idanuwa har aka kira sallan isha'i sannan ta fita basu sake sanya ta a ido ba har Sadeeq yazo d'aukar su...
*Page d'in naki ne aunty Mammn Mu'aleem. Ina fatan zai sanyaya miki rai kamar yadda naji dad'in kulawarki.*🤩
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
Page *35*
Shirin zuwa Sumaila kauyen sani suke farin ciki ya cika zuciyar INdo har ta kasa 6oyewa, kallonta yayi bayan ta rufo d'akinta ta juyo gashi cikinta ya fito yace.
"Cutie koma d'aki gaskiya mun fasa zuwa."
K'irjin INdo ya shiga bugawa hankalinta duk yayi mugun tashi ta kallesa dan san tabbatar da maganarsa. Gani tayi yana dariya hakan yasa ta yin kansa zata dokesa yayi saurin guduwa cikin shagwa6ar da ta farayi wadda yanzu take neman zame mata jiki tace.
"Ka tayar min da hankali Allah ya dawo damu lafiya sai na rama."
Fitowa suka yi suka shiga mota Sadeeq ya d'auki hanya, wannan karan cikin hira suka ta kai da ka gansu kasan masoyane sa6anin lokacin da aka ce ya kaita garinsu ya dinga kumbura tamkar wanda aka sanyawa yeast. Cikin kwanciyar hankali suka shiga garin sumaila, suna zuwa kan kwanar da zasu shiga kauyen sani adeeq ya kalleta yana murmushi yace.
"Cutie ga barkono da gyad'a bazaki siya bane?!"
Juyawa tayi tana kallon gurin kafin tace.
"Eh wallahi kuwa, dan Allah kaje ka siyo min kwano d'aya-d'aya."
"Ke wasa nake miki ni."
Ya fad'a yana tafiya, kallonsa tayi shima ya kalleta tare da d'aga mata girarsa. Hannunsa yasa ya janyo nata yana matsawa ta lumshe idanuwa tana shafar cikinta da d'ayan hannunta.
A k'ofar gidan su yayi parking, gidan yana nan yadda yake tun lokacin da Abubakar ya gyara musu katangar su ya maida ita ta bulo sa6anin da datake na k'asa. INdo ta kallesa tare da Kama hannunsa tace.
"Wait for me, naje na sanar ma Inna zaka shigo ku gaisa."
"Hmm lalle wariyar launin fata, meyasa ni bazan shiga direct ba sai an wani yi min iso? Ban yadda ba tare zamu shiga kema ai idan mukaje gidan Mama wani sa'inma kina rigani shiga."
"Hehehehe lallaima, toh ai ni macace zan iya shiga direct, kaifa sabida su Mubasheer na zuwa su shiga kai tsaye kasa duk muke kulle gidajen sai an buga munji ko waye sannan mu bud'e."
"Toh ai ni har yanzu saurayi ne, su kuma su Inna sun tsufa toh meye a ciki."
"Kai My super glue, wallahi Inna ta ba tsohowa bace rayuwa ce kawai ta maida su haka amma ka bari na kammala karatuna sannan cinikin zo6o ya kankama zaka sha mamakin Inna da baba wallahi. Kuma kasan dai ai abban ku dasu Mama sun girmi su Innata."
"Kaiii cutie..?!"
"Yanzu dai bazaka barni in shiga ba."
Tayi maganar tana turo baki,janta yayi kasan cewar tinted glass ne yasa ba'a ganinsu. Sadeeq ya shafo cikinta tare da cewa.
"Yau dai ina zata ga k'ok'arina, but dan Allah cutie karki bari ta ankara harsai nazo mun gaisa na fito, wallahi kuma sai naji inajin kunya."
"Kunya kuma? Hahahah ta6 ai aikin gama ya riga ya gama, yanzu wannan abun taya yaya za'aiyi ya 6oyu? Dama hijabi ne ko duguwar riga shine zan iya d'anyin dabara amma ai yanzu kuwa ka makaro hakan nan zan shiga Inna ta gani kuma ka shiga ku gaisa da ita."
Sadeeq ya turo bakinsa tare da dafe kuncinsa yana kallonta yace.
"Toh ya zanyi? Dole na shigo tunda an banike."
Tana dariya ta bud'e k'ofar yaran unguwar da suka zo gurin suka dinga kallon INdo wasu na cewa itace wasu kuma suna cewa ai k'anwar Inna ce dan ga kama nan. Gidan ta shige tana dariya jin abinda suke fad'a, tana zuwa tsab ta ajiye cewa itace 'yar fari ta d'ane Inna dake sharce gurin da tayi wanke-wanke.
"Oh ni Maryamu waike yaushe ne zaki san kin girma 'yar nan.?!"
Inna ta fad'a tana janye jikinta daga na INdo. Dariya kawai ita kuma takeyi tare da kallon Innar tana cewa.
"Kai Inna Oyo-yo fa mukayi, nayi missing d'inku wallahi Inna dake da baba tunda aka kaini baku jeba sai su d'an rainin hankalinnan Sagiru..."
"Ga INdo... Ga INdo, yeeeeee sannunku da zuwa."
Nafeesah ta fad'a tana rungume INdo, murmushi tayi cikin nunawa wayewa da kuma zaman birni tare da nuna zaman teburin class ta kamo hannunta tace.
"Su Feenah 'yan mata daga ina haka..?!"
Ta fad'a tana jan hannunta suka nufi cikin d'akin Inna.
"Kinga Feenah d'auki tabarmar baba ki shimd'a anan sabida Malam Sadeeq zai shigo su gaisa da Inna."
Sabuwar tabarmar malam Hamza aka shimfid'a sannan INdo ta ciro d'ari biyar ta bawa Nafeesah cikin k'asa-k'asa da murya tace.
"Mazaki siyo min lemon roba da ruwa zanba shi yasha."
Kar6ar kud'in Nafeesah tayi sannan ta fita da saurinta, sai da ta kuma tsayawa wajan Sadeeq yana tsokanarta kafin ta wuce zuwa shagon da zata iya samowa mijin yayarta ta lemo da ruwan jarka.
"Sannun ku da zuwa, ke d'aya kika zo ko hardashi me gidan naki?!"
"Inna tare muke dashi zai shigo ku gaisa ma, wai ina baba?!"
"Malam yana can gurin sana'arsa, bari wani ya shigo sai yaje ya kirasa ku gaisa."
INdo dake bakin gadon Inna na k'arfe tace "toh.". 'Dan kuma gyara d'akin tayi sannan ta share shi ta ciro turare a handbag d'inta ta fesawa d'akin da kan tabarmar da Sadeeq zai sauna sannan tace.
"Inna bari nace ya shigo ko? Karya ga an barshi a mota shi d'aya."
"Toh kice ya shigo barina saka mayafi na nima."
Fita tayi suka yi karo da k'awarta Uwani da Sahura da alama sunji labarin zuwanta.
"Ahhhh kaga su hajiya INdo amaryar Malam Sadeeq oh harda su abinga."
Sahura ta fad'a tana d'aga mayafin jikin INdo, kaf d'insu sunyi wani bululumu dasu Uwani ma harda tsohon ciki kai idan ka gansu bazaka ce k'awayanta bane sabida tsabar yadda kalar wayewar ta bambanta.
"Kai sahura kina nan da gulmarki, ku shiga ciki ina zuwa."
Ta fad'a tare da dukan bayan Uwani ganin yadda ta rik'e ha6arta tana kallonta. Cikin gidan suka shiga ita kuma ta shiga motar Sadeeq wanda ke jingine jikin kujera ya sanya hularsa a fuska yana kuma zagaye kwantaccen quarter million d'in fuskarsa.
Jin an bud'e k'ofar motar ne yasa shi cire hularsa ya kalleta, zama tayi tana kallonsa da murmushi a fuskarta yace.
"Uhmmm wato anzo gida harma kin manta tare muka zo ko?"
Hannunsa ta kamo cikin nata cikin kalar jimami tace.
"Ni na isa, tunda na shiga mafa koda Inna bamu gaisa ba kuma babu kowa duk basa nan amma ni banajin zan iya mantaka a yanzu domin ka zama ni na zama kai kadena sawa ranka cewar duk inda zan shiga wai Zan manta dakai no, idan nayi haka toh Zan iya mantawa da kaina nima."
Sadeeq ya lumshe idanuwa tare da jan hannunta murya a shak'e cikin wani irin salo yace.
"Kina nufin kenan munyi *MUSAYAR ZUCIYA* dani dake a yanzu? Ba kamar da ba yadda kike nuna min cewar zuciyarki ta M twinnie ce shi kad'ai yanzu zaki iya mallaka min ita...?!"
"Sosai ma kuwa na baka ita ina fatan ka rik'eta amana. Anan aka d'aura mana aure dan haka anan na kuma baka amanar kaina da duk abinda ya shafeni."
"Na kar6a cutie Allah kuma ya bani ikon rik'ewa gam-gam, a baya ma *Illar Zuciya* ce tasa nake ganin kamar anyi min ba dai-dai ba amma a yanzu..."
Yakai bakinsa kan hannunta ya sumbace shi yana kashe mata idanuwa tayi saurin kawar da kai tana dariya. Nafeesa ta hango hakan yasa INdo fitowa da sauri. Amsar aikenta tayi ta shiga ciki Nafeesah kuma ta tsaya a gurinsa suka dinga hira har su Shehu suka dawo suma suka gaida shi. Cikin gida kuma INdo ta gama jerawa Sadeeq abin tarba dan inna ta gama dafa wake da shinkafa Allah sarki harda yanka mai lawashin albasa kuma duk INdo bata hana ba domin ta haka ne zata iya kuma tabbatar da kaunar da yake cewa yana mata dan marigayi baya kyan-kyamin duk abinda zata bashi bare yanzu tasan kanta tasan me takeyi ta kuma san waye mijinta.
"Lallai INdo wai duk malam Sadeeq d'in kikewa wannan tanadin?!"
Uwani ta tambaya tana ta6e baki, gani take kamar INdo ta zurma da yawa duk miji akewa wannan hidimar.
"Toh Uwani bakin ciki kikeyi ko me? Ina zan samu kifi ma dan yana son wake da shinkafa da kifi ko dafaffen kwai."
"Ta6 lallai INdo Hamza, toh k'ila dai yana baki kema ba irin muba da sai dai komai kayiwa kanka."
"Kwaji dashi gulmammu, Inna bari naje nace ya shigo."
Tana fad'a ta kuma fita tace ya shigo. Jerawa suka yi shida Nafeesah yana kallon INdo daga baya. Gaskiya ikon Allah baya k'arewa a duniya ko kana menene sai ya nuna ikonsa akanka yau shine da INdo harda kunshin cikinsa a jikinta "Allah astagfurullah."
Ya fad'a cikin ransa tare da shiga gidan yana sallama, su Sahura da Uwani suka amsa bakinsu a washe yayin da Inna ke tsaye kanta a k'asa sam bata iya kallonsu tun zamanin Abubakar. Cikin d'aki Nafeesah ta shigar dashi ya zauna yana sosa keya yana shafa wuya.
Daga bak'in k'ofa Inna ta tsugunna suka gaisa da Sadeeq sannan su Uwani ma suka sake gaidashi duk da cewar sun gaidashi a cikin mota INdo ta kallesu tare da makewa Sahura hannu ganin yadda take leken sadeeq tana wangale baki.
"Kedallah can malama kina da miji kina kallon mijin wasu haba."
"Kai INdo bana san herri."
Tashi Inna tayi ta shiga rumfar malam Hamza bayan ta tura Nafeesah tace ta kirasa. Kallonsu tayi tace.
"Zan shiga daga ciki, karku ce na barku anan."
"Lallai ma INdo toh ba abinci zaici ba? Toh ki zauna muyi shira mana kafin ya gama."
Uwani ta fad'a tana hararta cikin jin haushin yadda take wani nan-nan da malam Sadeeq sai kace su basuda mijin.
"Toh kuje ku gama muna nan hajiya INdo."
"Toh hajiya Sahura."
Itama ta fad'a tare da shiga cikin d'akin. Kallonta yayi ta zauna kusa dashi tare da d'akko Coca-Cola ta bud'e mai cikin halin damuwa tace.
"Kayi hakuri kasha a haka da bakin jarkar, nan gidan bamu da kofuna kaji my super glue ka daure."
"INdo Aisha ta zaria med'an kallabi..!"
Ya fad'a tare da matsawa kusa da ita. Lek'awa yayi k'ofa aikuwa karaf suka had'a ido dasu Sahura da Uwani suna lek'owa yayi dariya tare da Kai bakinsa saitin kunnen INdo yace.
"Gaskiya d'aliban nan nawa gulmammu ne, sai lek'en mu suke kamar a gidan zoo."
Itama dariya tayi cikin hillata da shagalta yaci wake da shinkafar nan dan sai da suka cinye ta cikin kwanon silbar da Inna ta kawo musu. Suma su Sahura da suka kasa suka tsare aka zuba musu sukaci lokacin malam Hamza ya shigo fuskarsa kunshe da fara'a Sadeeq yayi saurin tura kwanon gaban INdo da ragowar lemonsa da ledar yajin ya maze sai wani danne-dannen waya yake shi a dole beci da yawa ba.
INdo kuwa banda dariya babu abinda takeyi mai amma still ya maze su Uwani na jiyo ta sai mamakin abinda yasa ta dariyar suke yi.
"Sadeequ ashe kunzo? Sannunku da zuwa. Ah kaga uwata an zama manya."
Sadeeq ya fara motsi yana gyarawa malam Hamza guri dan ya shigo. Gaida shi suka yi sannan yayi ta sanyawa Sadeeq da marigayi albarka ganin yadda INdo ta canza tamkar ba 'yarsu ba.
Tare da malam Hamza Sadeeq suka fita ita kuma INdo ta koma tsakar gida gurin su sahura Inna ma taje ta zauna. Suna zaune Rukayya ta shigo murna ba'a magana sabida ganin INdo da ciki, nan fa suka shiga hira baji ba gani amma duk da haka zuciyar INdo bata manta da Sadeeq a mota ba. Nafeesah ya d'auka suka shiga cikin garin har sai bayan sallan la'asar sannan ya dawo dan su tafi.
"Gaskiya Inna zan baki kud'i a hannunki a samu dan Allah a gyara band'akin nan, habba wallahi za'a iya d'aukar larura tunda aka haifeni a haka yake. Ga dubu sha biyar nan ita kad'aice a hannuna nasan k'ila malam Sadeeq zai bawa baba ma wasu amma idan be bayar bama dan Allah Inna a fara da wannan kud'in ko buhu d'aya ne na siminti a siyo a malale k'asan band'akin can kosu Sagiru ne da Shehu sai suyi ai sun iya."
Kwallah Inna ta share tare da yin godiya sam bata ta6a tsammanin akwai ranar da 'ya'yanta zasu yi mata wani abunba ganin itama ba tayi wa nata komai sabida rashi gashi ance sai kanayi za'ayi maka.
"Inna ya kike kuka? Karki bari na tafi haka dan bazan yafewa kaina ba bayan na barki cikin kuka."
Murmushi Inna tayi tare da cewa.
"Allah nakewa godiya 'yar nan domin ban ta6a zata zanga irin wannan ranar ba musamman akanki, sai gashi Allah ya shirya minke ya kuma azurtaki gashi har kina tallafa mana da abinda kike dashi, Allah yayi muku albarka dukanku."
"Amin Inna ta, karki damu dana gama karatu na kware insha Allah zanyi kud'i duk gidan nan sai an gyarasa."
"Toh Allah ya yassare miki."
"Feenah dan Allah idan ya koma kwara state zan cewa Sagiru ya kawoki mu zauna tare ko bakya so?!"
"Ke! Ina so mana ai wallahi kin more gidan miji INdo."
Mtwww "Ban hanaki cemin INdo ba gatsal? Ki kirani yayya Aisha ko Yaya INdo karki sake cemin wani INdo mara kunya."
Kallonta Nafeesa tayi tana ta6a baki kafin ta kad'a kai tabar d'akin. Har zaure Inna ta raka ta tana yi musu fatan alkhairi bayan Sadeeq yazo sunyi sallama. Dubu d'aya ta kar6a gurin Sadeeq ta bawa su Sahura su raba d'ari biyar-biyar suka dinga godiya suna k'ara jinjina arzikin da INdo ta samu sannan ta shiga mota suka tafi cike da farin ciki.
***
Kwanaki biyar yayi bayan sunje kauyan Sani sannan suka d'aga suka tafi kwara state da Fateema bayan yayi yayi da INdo ta bishi tak'i sabida karatunta. Yana tafiya da kwana biyu tasa Sagiru ya kawo Nafeesa duk ranar school d'inta zasu je tare ta zauna a barandar ajinsu INdo idan sun tashi su koma gida ta koya mata abinda ta iya itama hakan ya k'ara bud'e brain d'inta ga cikinta yana ta girma cikin kwanciyar hankali.
Duk wata Sadeeq suke dawowa kuma INdo bata nuna damuwarta duk da bata son tafiyarsa amma bata son nuna mai dan karya kansile mata karatunta, gashi dama ya sanyata a makarantar dare ta islamiya ta matan aure anan unguwarsu hakan yasa ta kuma zama busy tana kuma wayewa ta fannoni da yawa a cikin rayuwarta.
Cikinta har ya shiga 10months bata haihu ba sai dai yayi girma har bata iya zuwa ko'ina. Ranar wata laraba cikin dare ta farka lokacin Sadeeq na mak'ale da ita duk da girman cikin jikinta hakan baya hanashi nanik'arta. Kallonsa tayi tana faman rintsa ido cikin wani irin mugun rik'o yaji ta rik'e mai hannu hakan yasa shi saurin farkawa.
"Cutie what happen?" Shiru sai cizon lips d'inta takeyi tana matse idanuwa ya mik'e tsaye ya sakko yace.
"Cutie kodai haihuwa ce? Bari nazo muje asibiti."
A gigice ya sanya jallabiya ya zari mukulli yayi parking lot. Motar ya fitar da ita shiru garin babu kowa ya kuma komawa gidan da kyar ya kimtsata ya fito da ita mota lokacin mak'ocinsa ya leko sabida yaji k'arar mota. Ganin halin da ake ciki ne yasa shi taso matarsa ta bisu zuwa asibitin.
Duk ya rud'e ya bugawa Fateema ya gaya mata itama hankalinta ya tashi gashi babu abin hawa bare tabisu gata mace. Ganin abun yayi yawa ne yasa suka kira Sadeeq d'in ciki INdo tana ta kuka ya rik'e hannunta zuciyarsa na bugawa da k'arfi da k'arfi tace.
"Dama a makaranta malama tace idan mace zata haihu k'afarta d'aya a duniya d'aya kuma a k'abari. Malam Sadeeq kayi hakuri nasan nima yau dacta zan..."
Sadeeq yayi saurin rufe mata baki yana kad'a kai, da k'arfi ta fizge kanta ta juyar da kai tana ci gaba da magana.
"Sai na fad'a d'in ka bari in gaya maka mana, dacta zanbi nima yau amma dan Allah tunda ance namiji zan haifa dan Allah koda na tafi malam Sadeeq ka sawa d'an suna Abubakar Sadeeq kar kuma a 6oye mai suna dan Allah."
Jikin sadeeq ya dinga rawa gumi gaba d'aya ya gama jik'asa, tana gama yin magana kawai nurse d'in dake gurin tasa hannun zureren jariri ya santalo kan hannun nurse d'in INdo na kwance tayi shiru yayin da Sadeeq ya bud'e baki yana kallon fuskarta gumi na d'iga akan hannunta na jikin fuskarsa....
*Fatan alkairi gareku masoya, a koda yaushe Ina alfahari daku cikin labarin MUSAYAR ZUCIYA. Hajja ce take muku fatan alkairi tare da d'in bin godiya marar adadi*💘
0 comments:
Post a Comment