*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_©2019_*
*بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ*
_In the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful._
*[1......]*
............Tafe take tana zirar da hawaye masu d'umi da saka k'unar zuciya. Kasantuwar Nikab d'in dake sakaye da fuskarta ya hana bayyanuwar kukan nata ga mutane, dukda dai hakan bai hana wasu kallonta ba, musamman wad'anda sukeda tabbacin itace.
Cikin Nutsuwa da sanyi take tafiya, kanta a k'asa dukda kuwa tana sanye da dogon hijjab da nik'ab. Isowarta inda zata yasa ta tura murfin k'ofar gidan kalar madara ta shiga da sallama.
Dattijuwar da bazata gaza shekara hamsinba ta d'ago daga d'ibar ruwan da take a rijiya ta amsa Mata.
“Wa'alaikissalam, yanaga kin dawo dandanan? Kobaki iskeshi a gidan bane?”
Nik'af d'inta ta yaye, kamilalliyar fuskarta ta bayyana, ta d'an sakin guntun murmushi tace, “Eh Umman mu, na tarar har ya tafi kasuwa”.
Batareda ta jira amsar Umman tasuba ta wuce gaba. Binta da kallo Umma tayi, ko kad'an bata yardaba, tasan ta 6oye mata ainahin abinda yafarune acan kamar yanda ta saba gudun kar ranta ya 6aci. Ta d'an sauke ajiyar zuciya tana girgiza Kai, sannan ta ajiye gugan hannunta ta d'auraye hannun da ruwan data jawo ta nufi d'akin da yarinyar ta shiga.
Zaune ta isketa ta zabga uban tagumi tana cigaba da kukan, amma jin sallamar Ummansu sai tai saurin share hawayenta ta maye gurbinsu da murmushi. Da kallo kawai Umma ta bita tana mamakin zurfin ciki irinna y'ar tata, ita har tausayinta take gameda zaman gidan aure, idan bata sami miji na gariba sai dai aita cutarta........
Maganar budurwar ya saka tunaninta katsewa.
“Umma wai su Zarah basu dawoba har yanzu?".
Zama tayi kusa da ita tana fad'in “Basu dawoba Nafisar ma ta kirani tace sai zuwa yamma zasu dawo, zasuyi Mata wani d'an aiki”.
“Humm ni dad'ina da Aunty Nafisa kenan, baka isa kaje gidanta kafito bata nanuk'a maka aikiba, son jikinta yayi yawa wlhy ita da Zarah Umma”.
Murmushi Umma tayi kawai, amma batace komaiba. Sai da taga budurwar zata mik'ene tace, *“JIDDAH!,* dawo ki zauna muyi magana”.
Babu musu ta dawo inda ta tashi ta kuma zama, “To Umma gani, wacce magana ce?”
Numfashi Umma ta sauke, kafin ta tsare Jiddah da idanu, “Jiddah ya kukayi da Abbanku?”.
“Lah Umma aina cemiki ban iskeshiba, yatafi kasuwa sanda naje”.
“Ban yardaba Jiddah, nifa mahaifiyarku ce, duk d'inku nasan halin kowanne, ki daina k'ok'arin 6oyemin abinda ba sabo bane a gareni da rayuwata”.
“Umma kiyi hak'uri, aganina yawan maimaita magana bashida amfani, hak'uri da mantawa da abinda yawuce shine dai-dai”.
“Duk nasan da hakan Jiddah, kedai fad'amin”.
“Shikenan Umma tunda kin matsa. Na iske Abba a gida yanama Karin kumallo, bayan mun gaisa dashi da aunty Amarya, saina sanar masa nazone ya taimakemu da kud'i su zarah sun koma hutu, gashi kuma basu biya kud'in makaranta ba belle su kuma, gashi su waleeda Jsce zasu zana a wannan shekaran. Wlhy Umma bakiga yanda Abba da Aunty Amarya suka hayayyak'o minba, har Abba yana fad'i bazai gaji da takaicin *HAIHUWAR y'ay'a mata* ba harya koma ga ALLAH, wai mune muka dabaibaye DUNIYARSA shiyyasa yakasa gaba ya kasa baya, shi baiga amfaninmu ba inama laifin ciyar damu abinci da yakeyi, yariga ya rantse sisin kwabonsa bazai ta6a kashewa akan muyi karatu ba, gara ya sayama su kalifa ice-cream yasan duk tsiya nan gaba zai amfana dasu...........” kuka ya sark'eta takasa k'arasa maganar, saima fad'awa datai jikin Umman.
Shiru Umma tayi takasa cewa komai, sai k'ok'arin Had'iye wani Abu daya tsaya Mata a mak'oshi takeyi, yayinda hannunta ked'an bubbuga bayan Jiddah.......
Jiddah takuma katse Mata tunani da fad'in “Umma wlhy Duniyarnan tama fitarmin akai, wataran nakanji tamkar zancen Abba gaskiyane mu Mata bamuda wani amfani acikin wannan al'ummar, kowa gani yake amfaninmu daga a haifemu sai muyi aure mu haihu, babu wata gudunmawa da zamu iya kawowa a duniyarmu, mune muke d'aukar ciki, muyi goyonsa, mu haihu, muyi raino, muyi tarbiyya mutum yakai wani matsayi, amma MACE itace zai fara k'ask'antarwa, MACE itace zai fara d'auka mara muhimmanci, itace zai Fara kira mai k'aramar k'wak'walwa, itace zai Fara kira mai k'aramin tunani, itace wadda yake Fara kallo takalminsa abar takawa ako yaushe, mune jagororin AL-UMMA amma mu ake maidawa MAK'ASK'ANTA, Umma Abbanmu namana haka to yaya Miji zaimana muji haushi? Anya kuwa Umma Abbanmu y..........”
Da sauri Umma ta rufe bakin Jidda tana fad'in “Kul jiddah karna sakeji, koma dai minene shi mahaifinku ne, bai cancanci kowanne irin furiciba, addu'a itace kawai makaminmu da hak'uri kinji”.
Kai Jiddah ta d'aga Mata tana share hawaye.
Umma tace, “Inaga kawai Zan samu Na saida Kujerunnan su koma makarantar, dan duk suna a ga6ar dabai kamata ayi wasa da itaba, kodai karatun secondary d'in suka samu ALLAH ya amfana, mutum dai yasamu abin fidda kai aduk inda ya tsinci kansa, kema da bakiyiba keda y'ar uwarki ALLAH ya baki miji nagari dazai kula dake kamar yanda y'ar uwarki ta dace”.
“Ameen Umma, amma baikamata a saida kujerunnan ba, mudai jira muga kozai biya d'in kokuma Uncle zai dawo da wuri, dan nasan shima hankalinsa Na nan”.
“Humm Jiddah kenan. Kema dai kinsan hali basai nafad'aba indai Abbanku ne, mudai jira yahayan kawai”.
Shiru Jiddah tayi tana had'iye wani Abu mai d'aci daya tokare mak'oshinta, ji take da zata samu wata dama akan MAZA masu irin halin Abba, to lallai shine Wanda zata Fara hukuntawa domin na bayansa su Shiga hankalinsu da koyar yanda zasu *MARTABA Y'AY'A MATA*.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*ASALIN LABARIN*
*Alhaji Zakari yaro* d'an asalin jihar Adamawa ne, amma mazaunin kano, dan acikin kano ya bud'i ido yagansa tun a zamanin k'uruciya, ALLAH yayima Mahaifinsa rasuwa tuni, amma sai mahaifiyarsa taci gaba da zama bata koma Adamawa ba, ita tacigaba da kula da al'amuransa harya kai munzalin aure. Da kanta tabashi damar nemo matar aure, anan kano kokuwa cikin y'ay'an dangi dake Adamawa.
Cikin ikon ALLAH ya za6o matarsa cikin dangi, dankuwa acan Adamawa tushensa ya d'akkota, hasalima auren zumincine a tsakaninsu. Sosai mahaifiyarsa tayi murna da za6insa tai ta sanya masa albarka. Babu 6ata lokaci aka shiga shagalin biki Na y'an gata, domin kuwa su biyu iyayensu suka Haifa, dagashi sai k'aninsa yahaya. Ansha biki amarya Aminatu ta tare anan cikin birnin kano. Zamane akeyi mai cike da nagarta da k'aunar juna, dan kuwa suna son junansu, sai da Aminatu ta shekara uku a gidan miji sannan ALLAH yabata ciki, zokaga murna wajen Zakari da mahaifiyarsa da k'aninsa yahaya, a kullum fatan Zakari Aminatu ta Haifa masa d'a Namijine, wataran har takanji haushi a yanda yake nuna k'iri-k'iri yafison a Haifa masa y'ay'a maza, to idan ta haifi mace kenan bayaso? Idan wannan tambayar tazo mata a rai hankalinta yakan tashi, domin tarasa yanda zuciyarta zata iya kar6ar amsar.
ALLAH da ikonsa ciki ya isa haihuwa, a wani daren lahadi Amina ta tashi da nak'uda, gabannin asuba da taimakon ALLAH dana surukarta ta haifo y'arta mace. Tunda mahaifiyar zakari ta sanar masa abinda aka Haifa saiya canja fuska, murnar da yaketayi takoma ciki, batare da yako d'auki y'ar ba ya buga takalminsa ya fice, bai dawoba sai da daddare, wasa-wasa dai Zakari yak'i d'aukar yarinya, hud'uba ma sai wani makwafcinsu yahaya yakira bisa umarnin mahaifiyarsu akaima yarinya. A kayan shagalin suna da ya saya saiya raba uku yabada kashi d'aya, mahaifiyarsa batasan abinda ke faruwa ba, dan a gabanta 6oyewa yakeyi, sai a daren sunan da taga kayan daya kawo takaici ya kamata, kiransa tai ta nema ba'asi, nanfa yashiga kame-kame, itako ta balbaleshi da fad'a, ta inda take shiga ba tanan take fitaba, yayinda shikuma yaketa bada hak'uri da neman afuwa. A daren yakawo sauran kayan, washe gari akasha shagalin sunan baby dataci suna SAUDA.
Bayan haihuwar Sauda zaman Amina da Zakari ya canja alk'ibla, ya janye mata sosai, dukda ta damu amma saita danne zuciyarta darajar mahaifiyarsa dake k'yautata mata, da gudin tsinka igiyar zuminci. Shekarar Sauda biyu takuma samun wani cikin, nanma dai Zakari yakuma k'wallafa rai ga haihuwar d'a Namiji, yakoma ririta Aminatu. Itadai mamakinsa take ainun, amma bata ta6a cewa dashi uffanba har cikinta yakai haihuwa.
Tab an da6a kenan, inji masu iya magana, dan kuwa wannan karonma Aminatu Mace ta sake haihuwa k'yak'yk'yawa San kowa k'in Wanda bai samuba, itadai murna tai tayi da kuma godema ALLAH da wannan k'yauta. Amma ga zakari ba haka bane, dankuwa jiyay yakuma tsanar Amina, wai danmi zataita cika masa gida da y'ay'a Mata. A wannan Karon koda ya takalota da fitina bata d'aga masa k'afaba, tai masa tatas, wannan shine silar guntulewar aurensu, sai a gidansu aka rad'ama jaririya suna Hannatu, dan kuwa Zakari yace yabar mata bayaso. Ran mahaifiyarsa yakai k'ololuwar 6aci, ta tattara kayanta takoma Adamawa ita da yahaya.
Shekarar su d'aya da rabuwa da Aminatu yasake aure, Wanda da k'yar mahaifiyarsa ta amince, saida ma Baban Aminatu ya saka baki.
Saidai wannan karonma auren Zakari da Ai'sha baiyi k'arko ba, dankuwa tun a haihuwar farko suka raba jaha, sakamakon haihuwar d'iya mace mai suna Zulaiha. Itama yace bayaso ya barmata. Ananma sosai mahaifiyarsa ta fusata, amma bisa hak'urin da dangi sukaita batane yasata hak'ura. Zakari yakuma auren Rammah. A haihuwar farko Rammah ta haifi mace itama, tashin hankali kenan, dankuwa Zakari yakai k'arshen fusata da haihuwar Mata da ake masa, a cewarsa haihuwarsu batada wani amfani sai d'orama mutum nauyi (🙁humm).
Itama dai batakai labariba ya 6alleta tareda bar mata y'arsa mai Suna Nafisa tace bazata rik'eba. Dole ruk'on Nafisa yakoma hannun mahaifiyarsa dake Adamawa.
Bayan Aurensa da rammah saida ya shekara hud'u bai k'ara zancen aureba. Sai kuma rana tsaka ALLAH ya had'ashi da Y'ar Shuwa wato Yagana, Zakari ya had'u da Yagana ne a Adamawa, lokacin yazo gaida mahaifiyarsa, yayinda Yagana kuma sunzo biki makwaftansu mahaifiyar Zakarin. Dandanan soyayya ta k'ullu a tsakanin yagana da Zakari, dukda sukarsa Na auri saki da k'in haihuwar y'ay'a Mata da akaita kawo Mata. Ba awani ja lokaciba manya suka shiga magana, akaje har Maiduguri aka d'auro auren Yagana. Saida tayi sati biyu a Adamawa sannan suka taho kano, bisa ga dogon gargad'i da mahaifiyarsa tai masa, takumace inhar ya Saki Yagana ALLAH ya isa bata yafeba koda a bayan rantane...........✍🏻
(*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_Ya rabbi kabani ikon fad'ar abinda zai amfanar da al'ummarka, ka tsare harshena daga fad'ar abinda zai cutar daku da ni baki d'aya._*😭🙏🏻
_Ya ALLAH ka gafartama mahaifina abin alfaharina da dukkan y'an uwa musulmai da suka rigamu kwanta dama🙏🏻😭_
*_Wannan littafi tukuycine a gareku my sweet sisters, ina gidiya da karamcinku gareni, alkairin ALLAH yakai gareku a duk inda kuke._*🥰🥰🤝🏻
_Billy s Fari_
_Ummu Basheer_
_Fareeda Musa sweery_
_Ai'sha Manshat_
_Hafsat writer d'in Hafiz_
__________________________________
*_[2.....]_*
................ Zakari dai yataho da Yagana kano cikeda farin ciki, sunkumazo sun zauna lafiya har ALLAH yabata ciki itama, a lokacinne kuma yahaya shima yadawo kano suka cigaba da kasuwancin atanfofi da shaddoji shida d'an uwansa Zakari.
To a wannan Karon dai Yagana ta Haifa masa Namiji, wayyo zokaga murna da tsalle da shirin suna Na bajinta, ragoma biyu aka yanka kuma manya-manya. Ansha shagalin suna yaro yaci suna Nuhu. Sai dai kash bayan suna da kwanaki uku yarasu, wannan Abu yasaka Zakari takaici, harda kukansa rurus, kaikace wani babban mutumne yarasu.
Babu dad'ewa Yagana takuma samun wani ciki, Zakari ya shiga tattalin ta kamar zai maidata a ciki, dan a ganinsa Namijin za a kuma Haifa masa. Sai dai kuma shi Ubangiji babu mai masa shishshigi a lamarinsa. Koda Yagana ta haihu saiga d'iya mace. Babu kunya Zakari ya nuna tsantsar takaicinsa da haihuwar jaririya, gashi babu damar sakin Yagana. Yarinya taci suna *HAUWA'U (Jiddah)*, ko kad'an Zakari bai damu da Hauwa'u ba, koda ciwo takeyi babu ruwansa balle ya damu, ahaka takai yaye aka yayeta, Yagana takuma samun wani cikin. Nanma Zakari ya saka idon ganin namiji, amma saiga mace, itama kiri-kiri ya nuna bayaso, taci suna Fatima (Zarah), bayan an yayeta saiga wani ciki, a wannan Karo zakari baiwani damuba, hasalima ya maida hankalinsa ga kasuwancinsa ne daketa ha6aka gaba d'aya, ga shirin auren Yahaya da sukeyi kuma.
Ansha bikin yahaya da matarsa Zulaiha, itama ta tare anan cikin anguwar, amma haya ya kama kafin ALLAH yakawo kud'in gina d'an filinsa daya siya. Bayan auren yahaya da kwana ashirin da uku ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa, takuma jaddada wasiyarta ga Zakari inhar ya saki Yagana bata yafeba. Sunsha kuka da alhini rasuwarta, kwananta tsara a k'asa Yagana tafara nak'uda, amma sai Zakari ya nuna halin ko inkula akanta, acewarsa bazai wahal da kansa da dukiyarsa ba ahaifa masa wadda bazata iya taimakonsa da komaiba idan ta girma. Haka Yagana tasha matuk'ar wahala kafin ta haihu dak'yar, wahalar da tasha yasaka jinjirin jigata yazo babu rai. Hankalin Zakari yatashi matuk'a, yakumaji haushin kansa ainun, dan aganinsa sakacinsa yasaka su6ucewar Abu mafi daraja da soyuwa a gareshi, ya rungume gawar yaron yayta hawaye da ALLAH wadai ga abinda yayi, daya kai Yagana asibiti da yanzu d'ansa Na nan a raye.
Baki kawai Yagana ta ta6e ta d'auke kanta, takaici Na kuma cimata a zuciya.
Saida takusa shekara sannan ALLAH ya kuma bata wani cikin, zakari yadage tuk'uru wajen bata kulawa da addu'ar samun Namiji a wannan karonma.
Zan iya cewa Yagana ta haihu kusan lokaci d'aya da Zulaiha Matar yahaya, zulaiha ta santalo d'anta Namiji, itako Yagana mace. Takaicifa kamar zai kar mutumin naku. (😆😝).
Babu wani abun arzik'i dayayi a taron sunan tamkar sauran y'ay'ansa Na baya, ranar suna yarinya taci suna Hadiza (waleeda) saboda sunan mahaifiyar su zakari aka sanya Mata, d'an yahaya kuma Abubakar.
Bayan haihuwar Waleeda Ruk'on Nafisa yadawo hannun yagana, tunda yanzu babu mahaifiyar su zakari. Tsakani da ALLAH yagana ke ruk'on Nafisa, inma ba fad'a tayiba bazaka ta6a sanin ba d'iyarta baceba. Yanda take bama y'ay'anta tarbiyya haka take bama Nafisa, duk abinda ta siya musu itama zata saya Mata.
Zakari kam babu ruwansa da maganar yaransa, tsakaninsa dasu sai hantara da duka, yak'i sakasu boko balle Arabic, daga waleeda ma sai haihuwar ta tsayama Yagana baki d'aya, ita murnama tayi sosai, y'an uwantama suka tayata. Da taimakon yayan Yagana aka saka su Jiddah firamari da islamiyya harma Nafisa, yahaya ma yana bada gudunmawa, dukda a tsorace yakeyi saboda a k'ark'ashin Zakari yake har yanzu.
Matar yahaya kuwa tanata haihuwarta, cikin ikon ALLAH kuma maza taketa haihuwa, shikuma yana masifar son a Haifa masa mace, sai yayta sha'awar su jiddah.
Shekarar waleeda takwas a duniya Zakari yaje makka, a wajen aikin hajji yahad'u da matar aure mai suna Hajia Hindatu. Hindatu irin gogaggun matan nanne masu Ido a tsakar goshi, ta ta6a aure amma haihuwarta d'aya ta fito, bata dad'e da fitowa ba suka had'u da zakari. Tun a Saudia soyayya ta k'ullu a tsakaninsu, suna dawowa Najeriya babu 6ata lokaci akasha biki.
Ko kad'an auren bai d'aga hankalin yagana ba, dan damuwarta itace a gabanta, takuma San wanene Zakari, idan baisamu cikar burinsa ba (haihuwar namiji) to itama hindatun ba k'afa zai d'aga mataba.
A gida d'aya aka had'asu da farko, dukda Zakari yafara ginin wani gida mai k'yau dayafi Wanda suke ciki d'an k'arami mai d'aki uku da kicin d'aya da bayi d'aya a waje.
Sosai Hindatu kema Yagana Ummansu Jiddah iskanci kala-kala, su Jiddah kuwa basu isa su wala a gidansuba zata makesu. A lokacin kuma Nafisa nada shekara 19 dan tama isa aure, Jiddah kuma 14, Zarah 12, Waleeda 10.
Tuni Nafisa tabar zuwa boko dan daga firamari itada Jiddah basu cigaba ba, yayan yagana dake taimaka musu ALLAH yayi masa rasuwa, ganin nauyi zaiyima yagana yawa dukda d'an kasuwanci da takeyi saitace Jiddah da Nafisa suyi hak'uri, k'annensu su Zarah suyi su sai suci gaba da islamiyya kawai. Basu musaba suka amince, Zarah da Walida suka cigaba dayin boko da islamiyya, Nafisa da Jiddah kuma islamiyya kawai.
Zuwan Hindatu saiya kuma harmutsa komai Na gidan, domain kuwa shekararta d'aya ta haihu d'a Namiji, murna da shagalin da Alhaji Zakari yayi 6ata lokacine, bayan shekara biyu takuma tagwaye duk maza. Nanfa likafa taci gaba, dan gidan da Alhaji Zakari ya gina dukda girmansa sai yace Hindatu ce kawai zata koma ciki. Dukda abin ya6ata ran Yagana saita danne, tai masa ALLAH ya sanya alkairi.
Acanma akayi sunan tagwayen hindatu. Bayan suna babu dad'ewa Nafisa tasamu miji, babu bincike babu komai Alhaji Zakari yace yabashi, takaici Yakama mahaifiyar Nafisa da Yagana (dayake mahaifiyar Nafisan suna mutunci da yagana sosai saboda ruk'on gaskiya da taima y'arta, itama tayi aure tuni ta hayayyafa ma).
Haka dai akasha biki, Alhaji Zakari baima Nafisa wani abun arzik'iba, a cewarsa baya zuba jari inda bazai kwashi ribaba. Komai sai mahaifiyarta da yagana sukayi iya k'ok'arinsu, saikuma dangi.
Sosai Alhaji Zakari ke nuna banbanci tsakanin y'ay'ansa maza Na wajen Hindu (wadda suke kira Aunty Amarya) dasu Jiddah.
Hindu takuma saka haihuwar d'a Namiji, yanzu yaranta hud'u duk maza, kalifa, Hassan, hussen, Najib.
Alhaji ya sakasu makaranta mai tsada, komai suke buk'ata an tanadar musu, sun taso y'ay'an Hutu, Ana shagwa6asu ainun.
Yayinda gasu Jiddah ba haka bane, ko Alhaji zakari zai musu Abu saiyayi musu tozarci, bakuma zaiyi yanda ya kamata ba, saiya had'a wata baizo wajen Ummansu Jiddah da sunan sauk'e mata hak'k'i Na aureba, kayan abinci ma saiya gadama, saidai yahaya yakawo, wataran kuma ya hanashi ma.
Jiddah iyakarta firamare itada Nafisa, yanzu haka shekararta 20 dai-dai, tana makarantar islamiyya, hafizace ta alkur'ani mai girma, tayi zurfi matuk'a a fannin ilimin addini, ta halarci musabak'an alkur'ani kashi-kashi, kuma tayo nasara, amma a boko saidai abinda ba'a rasaba da Wanda k'annenta su Zarah ke koya Mata.
Da taimakon Uncle yahaya dana Umma, Zarah da walida ke karatu, dukda makarantar gwamnati sukeyi saida ji6in goshi ake iya kare musu buk'atun yau da kullum, dukda ALLAH yayima mahaifinsu arzik'i gwargwadon hali babu ruwansa da su.
Zarah Na shekara 18, tana aji biyar a makaranta, tasamu Matsala ne a wata shekara aka maidata baya, amma da yanzu tagama secondary, itama babu laifi tana ta6a karatun addini. Walida kuwa tana 16 itako ajinta uku a makaranta, sune zasuyi jsce yanzu. To ankoma Hutu amma gashi uncle yahaya bayanan, yayi tafiya, shine Umma tace Jiddah taje wajen Abbansu kozai taimaka ya bada, amma saita dawo da 6acin ran cin mutuncinsa dana matarsa hindu (aunty amarya).
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*_MUN DAWO LABARI_*
Sai yamma lik'is Zarah da Walida suka dawo nik'i-nik'i da ledoji, Jiddah dake tsakar gida tana tuk'in tuwo akan gawayi tai sagade tana kallaonsu, dukda tasan hakan daga aunty Nafisa ne, kullum cikin k'ok'arin k'yautata musu takeyi da abinda ALLAH ya hore Mata.........
Maganar Zarah ce ta katse ta.
“Kai Yaya Jiddah, irin wannan sakin baki haka? ALLAH sai sauro ya antaya ciki”.
Walida dake dariya tace, “gashinan kuwa yana yawo k'umu-k'umu wlhy, aimu gidannan ALLAH yay mana arzik'in sauro kam tamkar d'angwate da kud'i”.
Dariya sukayi su duka har Jiddah, ta rufe tukunyar tuwon data gama tuk'awa tana d'an yarfama rutsin wutar ruwa danya rage zafi kar tuwon ya k'one. “Y'ammatan Umma ya kuka baro Aunty tamu dasu Affan?”.
“Lafiya lumi wlhy Yaya Jiddah, tamace ace miki ta gode da cika alk'awari”.
Murmushi kawai Jiddah tayi, dan tasan laifinta.
”Wai ina Umma?”. ‘Cewar Zarah dake k'ok'arin shiga bayi’.
Jiddah tace, “Taje gidan Uncle yahaya, Maman Sadiq ce k'irjinta ke ciwo, shine taje dubata”.
Walida da Zarah suka had'a baki wajen fad'in “Ayya ALLAH ya k'ara lafiya to”.
“Amin”, Jiddah ta amsa.
Ledojin walida ta d'auka takai cikin d'aki tana fad'in “Yaya Jiddah mi zamu tayaki dashine? Naga yau aikin yamuku dare”.
“Wlhy kuwa auta, amma nama gama, dan miya na farayi sannan, sai dai idan tsakar gidannan zaki share a kunna maganin sauro musami wajen zaman hira”.
Walida ta amsa da to tana nufar inda tsintsiyarsu take.
Zarah ma koda tafito sai tace bara ta kwashe tuwon ita kuma. Haka suka k'arasa dukkan ayyukan suna hirarsu a nutse, dolene su burgeka, dankuwa akwai shak'uwa da k'aunar juna mai yawa tattare dasu, hirar tasuma duk akan Auntynsu ce Nafisa.
Ana kiraye-kirayen Sallar magriba Umma ta shigo, a lokacin su Jiddah sun gama komai, sai k'ok'arin d'aura alwala da sukeyi, amma banda Zarah dake fashin salla.
Atare suka amsa sallamar Ummansu, yayinda suke mata sannu da zuwa da tambayarta mai jiki.
“Da sauk'i Alhmdllh, y'an yini sai yanzu muke ganinku?”.
“Wlhy kuwa Umma, aunty dasu Affan Na gaisheki, yanata kukama saiya biyomu gashi gobe akwai makaranta”.
Y'ar dariya Umma tayi tana cewa, “Ja'iri yau kuma? Amma ranar dayake yaga babansa ai babu yanda banyi ya zaunaba yak'i. Yaya kuka baromin yarinya ta?”.
“Lafiya lau take Umma, ammafa ni sai naga aunty Nafisa kamar laulayin ciki take?”.
Harara Jiddah ta zubama Zarah mai maganar,
“O ke Zarah, wlhy bakida kunya, yaushe kikai girman gane mai ciki?”.
“Tab lallai, kaji Yaya Jiddah da wani batu dan ALLAH, cikin saikace wani abu........”
Hijjab Umma ta cillamà Zarah tana fad'in “Zarah k'aniyanki kinji, Anya kuwa ba aure zansa ayi mikiba?”.
“Wlhy dama yafi Umma, dan Idonta kullum k'ara fetsarewa yakeyi yarinyar nan”.
Waleeda dake alwala ta kwashe da dariya, yayinda Zarah ta kwad'a Mata harara.
“A'a nikam Yaya Zarah karki huce kaina, bani nakar zomanba”.
Haka kullum suke cikin tsokanar juna da wasa da dariya, hakan kuma baisa raini yashiga tsakaninsu ba, Ummansu ta maidasu tamk'ar k'awayenta, sune abokan hirarta sune shawararta, shiyyasa suma basuda wasu aminai a waje sai ita, saikuma a tsakaninsu su biyar.
Sune abokan juna, sune aminan juna, sune y'an uwan juna.
*_Dare_*
Da daddare suna zaune a tsakar gida sunacin tuwo, yayinda Zarah kema Umma bayani akan kayan da sukazo dasu.
“Umma tsarabar Dadyn Affan ce Aunty tace mu kawo, takuma bamu kud'in makaranta tace gobe muje mu biya mukoma makaranta”.
Umma tace, “ALLAH sarki Nafisa baiwar ALLAH, ALLAH ya saka Mata da alkairi, yamata albarka itada zuri'ar ta daku baki d'aya, ALLAH ya cigaba da had'amin kanku kunji”.
“Amin Umman mu”.suka had'a baki wajen amsawa. Kayan aka shiga bud'ewa, sabulan wanka da wanki, sai man shafawa da omo, kayan shayi da maltina rabin katon, da biredi manya guda uku da kud'in makarantar su Zarah sai kaji biyu gasassu.
Addu'a sukaita zubama yayar tasu, Umma ta kirata tai mata godiya da addu'a, tace aima dadyn Affan godiya shima.
Sund'an ta6a hira zuwa tara na dare suka mik'e domin kwanciya, saboda sauro daya damesu gashi kuma su Zarah zasu makaranta gobe.
✨✨✨✨✨✨✨✨
Da wuri su Walida sukai shirin makaranta, sannan sukai Karin kumallo da d'umamen tuwon jiya da Jiddah ta tashi da wuri ta d'umama musu.
Bayan wucewarsu makaranta tagyara gidan duka da taimakon Umma, dukdama gidan bawani babba baneba. Saida tagama komai itama zuwa tara da rabi tai shirin tafiya Islamiyya.
Tsaf tai shirinta cikin Uniform d'inta kalar ruwan toka, (ash color) yad'au guga sai d'aukar ido yake, turarenta da Aunty Nafisa ke k'ok'arin saya musu ta fesa kad'an, sannan ta d'aura Nikab, saidai bata sakeshiba tafito rataye da jakarta mai d'an tsawo kamar suwaga. 'Dakin Umma tashiga da sallama, tana zaune da alama sallar walha ta idar.
“Umma naga bakiyi Addu'a ba, gashi nakusa makara, nawuce saina dawo”.
Kai Umma ta d'aga Mata batare da tayi magana ba, dan batason katse addu'arta.
Jiddah Na fitowa soro ta Saki nik'ab d'inta tare da gyara hijjab d'inta tai addu'ar fita daga gida sannan tafito. Tafiya take a nutse kuma a sanyaye, kanta a k'asa dukda ta sakaye fuskar tata da nik'af. Kullum haka take cikin suturta jikinta, dayawan y'an anguwar a haka suka Santa, saika Tara mutum goma basu iya siffanta maka kamannin fuskartaba, saidai a tafiya kokuma kwatancen ta da suna mai saka hijjab har k'asa da nik'ab, amma mafi yawancinsu sun manta da kamanninta, dan tunda tafara mallakar hankalinta takoma suturta fuskarta..............✍🏻
*_Yanda kuka kar6i labarin yasakani farinciki matuk'a, ina godiya😄🤝🏻, dan haka kumuje Zuwa my guys⛹♀ ⛹♀_*
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[3......]_*
..............Malam Abdul-ra'uff Maina babban malami ne da akeji dashi cikin Najeriya da wasu k'asashen k'etare makwaftan k'asar, ALLAH ya azurtashi da tarin ilimi, ga tsage gaskiya komai d'acinta a wa'azinsa, yanada manyan makarantun addini sosai a cikin Najeriya da k'etare, dukda bashine kad'ai ya ginasuba, akwai taimakon attajirai da jama'ar gari masu buk'atar d'aukaka kalmar ALLAH.
Matan malam Abdul-ra'uff hud'u cif, duk da dai a yanzu uku suka rage, ALLAH yayma matarsa ta biyu rasuwa shekaru kusan 15, ALLAH ya azurtashi da y'ay'an da adadinsu zai iya kaiwa 17 a duniya kuma maza da Mata.
Huwaila itace uwargidansa, yaran gidan suna kiranta da suna Hajia bah-bah, yaranta shidda, maza uku mata uku, Muhammad, Zainab, Abubakar, Adawiyya, Ni'ima, Mahmud.
sai ta biyu da ALLAH yay mata rasuwa, Sunanta Hauwa'u, suna kiranta da Annau, yaranta uku, Ruk'ayya, Aliyu, Siyama.
Ta Uku Habiba, suna kiranta iya habi, yaranta hud'u, Umar, Bilal, Aminatu, Abdul-aziz.
Sai Amarya Mariya, suna kiranta gwaggo, yaranta hud'u itama, Binta, Usman, Asiya, Na'imah.
Agidan malam bazamu ce ba'a kishiba, anayinsa kam sosai, saida ba kishi Na haukaba, kishi akeyi Na matan da sukeda ilimi.
Mafi yawa daga cikin y'ay'an malam ALLAH yabasu ilimi sosai, amma Wanda zai iya bugar k'irji yakira magajinsa Kai tsaye shine *ALIYU*.
*Aliyu* mutumne nutsatstse, ma'abocin zirfafa ilimin addini da yad'ashi, yanada sauk'in Kai sosai, bashida fad'a ko yawan hayaniya, komai nasa zaka gansa a sanyaye akuma nutse, badan bashida k'arfi baneba, a'a sanyi tamkar halittarsace, dan ko maganarsa haka take cikin sanyi da nutsuwa. Tunda ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa sai suka koma kamar an waresu, bakomai Na gidan zakaga an sakosuba sai dai idan mahaifinsu Na kusa, hakan yasaka Aliyu bai damu da sabgogin gidanba inhar bana y'an uwansa biyu ba Mata, gashi yanzu duk sunyi aure sun barshi.
Zurfin iliminsa da yawan maida hankali wajen bama addini gudunmawa yasaka mahaifinsu malam Abdul-ra'uff yawan jawosa a jiki, ga tausayin maraicin da suke ciki. Aliyu ya ziyarci wurare daban-daban domin Neman ilimin addini, kullum cikin ziyartar zaurukan malamai yake, ba a Neman ilimin addini ya tsayaba, yana ta6a kasuwanci dai-dai k'arfinsa, dan yanada shago Na saida kowane irin nau'in littafi na Addini da magungunan musulinci, ko kad'an bai yarda yajira daga waniba, koda kuwa mahaifinsane.
Wannan k'ok'arin nasa da ho66asa yasaka wasu daga cikin y'an uwansa jin haushinsa, dan aganinsu kullum Malam yafison Aliyu fiye da kowa a gidan. Bawai su kad'aiba, hatta da iyayensu suna a kan wannan tunanin.
Saidai kuma bahaka bane ga malam, dukda dama ko cikin y'ay'anka akwai Wanda zakaji yafi soyuwa a gareka shi duk yanason yaransa, dan mutumne Maison y'ay'a sosai, kawai abinda basu ganeba (zuciya na k'aunar mai k'yautata Mata a koda yaushe) wannan shine kawai sirrin da Aliyu yabi wajen samun matsayi ga mahaifinsu dama wasu jama'ar dake zagaye da mahaifin nasu.
Yanada shekaru 27 a duniya ALLAH ya had'a jininsa da wata yarinya y'ar makwaftansu, sannan kuma d'aliba a makarantar mahaifinsu inda shima yake koyarwa idan yana gida.
Tunda malam ya fahimci k'aunar dake tsakanin Aliyu da Asma'u saiya nema masa aurenta, dayawan jama'ar gidansu hakan ya 6ata ransu, dan akwai yayunsa da basuyi aure ba kusan su uku. Dayake babu mai damar magana sai basuce komaiba akasha biki cikin tsari Na addinin islama.
Bayan aure da kamar wata uku matsaloli sukai yawa a gidan Aliyu, dan kuwa tunda akakai Asma'u gidansa yakasa kusantarta, badan bashida sha'awar hakanba, a'a lamarinne kawai ya gagara bisa alamun bashida cikakkiyar lafiya.
A matsayinsa na mai ilimi zaunar da Asma'u ya farayi ya fahimtar da ita akan tayi hak'uri ya fahimci baida lafiya, baikuma ta6a fahimtar hakanba saida yay aure, dan kafinma yay aure yakanji sha'awa, sai dai a jarabawa ta Ubangiji yakasa biya Mata buk'ata, yana neman alfarmar fara neman magani.
A wannan zama tayi masa uziri da fahimtarsa, amma yayinda tafiya tafara nisa sai hak'urinta ya nemi gazawa, dukda k'ok'arin neman magani da Aliyu yakeyi ba'a daceba har kusan watanninsu bakwai da aure.
Yakanyi wasanni da Asma'u, amma idan anzo batun biyan buk'ata sai Abu ya gagara, ita kuma hakan yana tada hankalinta daga k'arshe kuma babu biyan buk'ata.
Tabi ta saka kanta a matsananciyar damuwa, dukda k'ok'arin kwantar mata da hankali da Aliyu keyi. Ahankali sai y'an gidansu suka fara fahimtar akwai Marsala, mahaifiyarta ta turketa da tambaya itada yayarta, amarya dake murjewa danjin dad'i ita sai bushewa take a tsaye.
Bata wani tsaya Jan maganaba ta sanar dasu komai.
Tun daga lokacin komai ya harmutse, sukace sai Aliyu ya sakar musu yarinya. Yanason matarsa, dan haka yayta basu hak'uri da k'arin neman alfarma akan magani dayake nema, amma Sam sai sukak'i saurarensa.
Ganin abun zai tasarma tozarci dan harsun fara yawo da magana a anguwa sai malam yayma Aliyu nasiha da nuna masa muhimmancin hak'k'in Asma'u, tunda ta nuna bazata jureba ya sawwak'e mata kawai, kar nan gaba wata 6arnar ta biyo baya.
Cike da damuwa da tashin hankali yabama Asma'u saki d'aya, har hawaye saida yayi, dan yana masifar son Asma'un.
A ranar dai kam sai a asibiti ya kwana, kwanansa uku ya murmure yadawo gida, lokacin dayaje gidansa saiya iske sun kwashe komai, sai iya kayansa kawai aka bar masa, shima abinda keda muhimmanci ya d'iba ya kulle gidan ya fito zuwa gidansu.
Ganin yana tare da damuwa malam ya shawarcesa kozai koma karatune?.
Babu musu ya amsa. Dandanan aka shiga cuku-cukun nema masa gurbin karatu a k'asar Saudia. Cikin sati biyu komai ya kammala, ya cane cikeda kewar ahalinsa da y'an uwansa Mata biyu, Ruk'ayya da Siyama.
Tafiyar Aliyu Saudia saita zame masa alkairi abin alfahari, dan ya ture komai gefe ya maida hankalinsa ga karatu da addu'oin ALLAH ya bashi lafiya, tunda yakuma jin dad'in zak'in karatu saiya manta da wani batun aure. Ya maida hankalinsa tuk'uru. akan Neman ilimi da zurfafa bincike wajen malamai. Cikar kamala da girman mazantaka irinna nutsatstsun samari ta bayyana a gareshi, yazama cikakken mutum ma'abocin yawan ilimi, dukda shekarunsa kad'an suka haura talatin hakan bai hana masana duniyar ilimi girmamashiba, idan yana zuba maka tafsir da yaren Nasara (English) zaka d'auka baisan komai a yaren Africa ba, hakama idan ya juye Larabci abin ba'a magana, saika d'auka wani cikakken balarabene d'an asalin k'asar Saudia, hakama 6angaren yarensa Na Hausa yana nan daram a harshensa bai manta komaiba, dukda baya cikin Nageriya tafsiransa suncika ko'ina Na k'asar cikin harshe daban-daban, wa'azinsa yana saka zukatan bayin ALLAH nutsuwa ta musamman da k'arajin tsoron ALLAH, idan kaji tafsir nasa dolene ka nutsu wajen saurare da k'arajin tsoron UBANGIJI matuk'ar k'urewa, tsage gaskiya yake komai d'acinta.
Tunda yabar Najeria bai sake waiwayenta ba, saidai idan mahaifinsa yaje Umara ko wani Abu ya kaishi ya ziyarcesa, amma koda yaushe suna tare a Video call da mahaifinsa da y'an uwansa su Siyama dama sauran jama'ar gidansu.
Ganin shekaru sunja malam ya shawarcesa akan ya dawo k'asarsa hakanan, kodan ya cigaba da kula dawasu al'amura nasa, saboda shi girma yafara kamashi, sauran yaransa kuma ba kowa keda makamancin halayya ta Aliyu ba, hasalima yafisu indai a fannin ilimine.
Bisa ga bin Umarnin mahaifinsa ya tattaro ya dawo, kusan shekararsa d'aya kenan, tunda ya dawo malam ke zuba ido yaji kozaiyi batun aure, amma shiru kukeji babu wani motsi, sai harkokinsa Na k'ok'arin yad'a ilimin addinin islama yakeyi ta hanyoyi da dama. Dan ALLAH ya d'aga darajar *_Sheirk Aliyu Abdul-ra'uff Maina_* fiye da zaton mai hasashe a ciki da bai Na Najeria da k'asashe masu mak'waftaka, harma sunansa nason fin Na mahaifinsa dan masu iya magana kance kowa da zamaninsa.
Wannan kenan👌🏻🚶🏻♀.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
K'arfe d'aya dai-dai su Jiddah suka tashi daga islamiyya, kamar yanda ta saba saida tai salla a masallacin makarantar gudun kafin taje gida lokacin salla ya shige, gashi a k'asa zata tafi.
Bayan sun idar da sallar da d'alibai irinta masu tsayawa ta tako a nutse zuwa wajen makarantar, da d'an sauri-sauri take tafiya akan k'ok'arinta na isa gida da wuri ta taimaki Umma da aiki, tasan tana can tana fama da gawayi danyin girkin rana. A hankali ta furta “Anya Abba kana tsoron gamuwarka da mahaliccinka kuwa? Kana gudun tashi cikin masu shanyayyen jiki a jerin raunana wajen gina adalci akan iyalai? Ya rabbi ka shiryi Abbanmu, ka ganar dashi gaskiya kafin ka kar6i ruhinsa”. hawaye masu d'umi suka gangaro a kumatunta, bata damu da son sharewa ba dan tasan babu mai ganinta, da wannan ta k'arasa gida.
Kamar yanda ta saba tai addu'ar shiga gida sannan ta shiga da sallama bayan ta tsaya a soro ta goge hawayenta.
A k'ofar kicin ta iske Umma nata faman fifita wutar gawayin.
Umma ta amsa Mata tana fad'in “Lale da malama Jiddah, har an dawo?”.
Jiddah ta yaye nik'ab d'inta tana murmushi saboda jin tsokanar Umman tasu, “kai Umma inafa malama, kodai d'aliba, sannu da gida”.
Umma dake dariyar amsar Jiddan tace, “yauwa, ai kuke da sannu”.
Bokitin fenti Jiddah ta jawo ta zauna tareda k'ok'arin kar6ar maficin hannun Umman. Umma ta hanata tana fad'in “A'a baiwar ALLAH daga dawowa, kid'an huta mana ko Uniform ki samu ki cire, nasan dai kinyi salla a can?”.
“Umma karki damu, wlhy banajin wata gajiya, dama saurin danaketa yi kenan, dan jiya gawayinnan Na fahinci jik'ak'k'ene, yau da safema da k'yar ya kama”.
“Aifa naga alama wlhy, sauk'inma nagama miya, dan nasamu sund'an kawo wuta shine nayi akan abincan da Nafisa ta sayo mana, ina k'ok'arin d'ora shinkafar suka d'auke wutar”.
“Ai y'an wutarnan basuda alk'awari, sannu da k'ok'ari Umma, amma ina kika samu kud'in kayan miya harda gatantamu?”.
Murmushi Umma tayi, sannan ta mik'e zuwa cikin kicin d'in tana bama Jiddah Amsa,
“Kud'in adashin nanne hajia Lantana ta kawo, ni harma Na fidda ran samunsu, to naga ga kajin da Nafisa ta bamu sai kawai naba Dauda ya yomin cefane”.
“ALLAH sarki Ummanmu abin alfaharinmu, mai share kukanmu, ALLAH ya saka da alkairi, kingani kuma darajar hak'urin da mukai ga kud'in wajen hajia lantanar sun fito, bayan kowa ya fidda ransa ga samunsu, Umma sai ki koma sana'arki karmu cinye kud'in a ciki mu koma tsugunne-tsugunne”.
“Nayi wannan tunanin wlhy nima Jiddah, shiyyasa tun d'azun Na Kira Nafisa muka kuma shawartawa kafin kuma ku dawo kuji yanda mukai”.
“To shikenan Umma, aimu duk abinda kuka yanke dai-daine a garemu, ALLAH yayi mana jagora”.
“Amin” Umma ta amsa.
Bayan gawayin ya Kama sosai Jiddah ta d'ora ruwan shinkafa, cikin amincin ALLAH dandanan ta gama, tana cikin kwashewa a kula su Zarah suka shigo da sallama, kowa a galabaice yake saboda rana. Sannu Jiddah tai musu, hakama Umma. Walida ta wuce gaban randarsu da suke zuba ruwan sha saboda k'arancin rashin wutar lantarki ta k'asar tamu Tasha.
“Ke kuwa walida ki taimaki kanki da wannan ruwan hakanan kafin ya k'ulle miki ciki”,
Kofin ta ajiye tana had'iye Na bakinta cikin hura hanci, “Umma wlhy k'ishirwa Na kwaso, yau Na manta banje da ruwaba saboda saurin karmu makara, nikuma bana iya shan Na bohol d'innan Na makaranta wlhy”.
“to miye matsalarsa?”. Cewar Jiddah dake shiga falo da kular abinci..
Caraf Zarah tace, “Yo iyayi irin nata dai Yaya Jiddah.......”
“Kai Yaya Zarah kiji tsoron ALLAH, kemafa kinsan baida dad'i wlhy”. ‘ta k'are maganar da turo baki gaba’.
Umma dai tana jinsu bata sake tankawaba, saida tagama kashe wutar da Jiddah ta sauke abinci sannan tace, “Da wannan gardamar mara amfani dama tashi kukai kuka cire Uniform kuka watsa ruwa, dan sai k'aurin rana kuke”.
Duk sai suka kumbura baki, wai danmu Umma zatace suna k'aurin Rana.
Fahimtar hakan ya saka Jiddah da Umma kwashewa da dariya, Umma ta toshe hanci tana ra6awa ta gefensu ta shige d'akinta. Jiddah ma saita shige d'aki tana dariya.
Zarah da Walida suka kalli juna suna jinjina kai irin zamu rama d'innan. Walida tace, “y'ar uwa barsu sunci bashi indai munai, daga Umma har yaya Jiddah kowa munsan lagonsa. Dariya suka kwashe da ita suna tafawa, sannan duk suka mik'e zuwa d'akinsu inda Jiddah ta shiga.
Duk d'insu saida kowa ya samu ya watsa ruwa, Walida tayi salla sanna suka hallara a falo domin cin abinci. A babban faranti Jiddah ta zuba musu suka saka miya da namansu a sama, suduka har Umma suka saka hannu bayan walida ta d'ebo musu ruwan tulu mai sanyi. Dama can haka suke cin abinci su Biyar, bayan auren Aunty Nafisa ne suka koma su hud'u, tunda suka taso a wannan tarbiyar suka tsinci Kansu, harma sun Saba, kowa baya iya sakin jiki yaci abinci shi kad'ai saida y'an uwansa. (Iyaye mu kula wlhy, cin abincin yaranmu a waje d'aya yana k'ara musu k'aunar juna a zukata, dan kowa nacin yawun d'an uwansa, shak'uwa da soyayya na sake shiga tsakaninsu, wannan k'yak'yk'yawar d'abi'ar da muka bari tana taka rawar gani wajen raba kayin y'ay'anmu tundaga tushe. ALLAH yasa mugane🙏🏻).
Babu mai magana har suka gama tsaf, suka koma kan nama, kowa yanaci a nutse babu had'ama balle nuna zalama. Bayan sunyi nak walida ta kwashe kwanikan ta gyara wajen, daganan suka baje a falon suna cigaba da hirarsu mai cike da k'arama juna sani ba surutai marasa amfaniba............✍🏻
Wannan kenan👌🏻🚶🏻♀.
*_Assalamu alaikum, dan ALLAH Zan d'anyi wani tsokaci a fahimceni. Gameda masu turamin massages ta PC wasu suna ganin tamkar wulak'ancine idan sun tura ban amsasuba a lokacin, Ku gane wani Abu, inada aurefa, sannan inada uzirirrika tamkar kowacce mace, sannan duk lokacin da ka gama typing ko sha'awar ta6a waya bakayi wlhy, ji kake kanka ya d'auki zafi, sannan fa bake kad'ai bace, mutum yakan samu sak'onni sama da 200 a rana d'aya, banda Na groups, tayaya kuke ganin Zan iya amsasu a lokaci d'aya😄?, shiyyasa nake barin kamar sak'o Na yau Na amsashi da safe kafin Na Fara typing, dana gama nai posting saisu wuce gaba d'aya, to dan ALLAH kuringa mana uziri🙏🏻. Kuma masu Comments a groups wlhy ina kula da kowa, kuma inajin dad'i matuk'a, amma kunyi yawan da bazan iya binku d'aya bayan d'aya Na amsaba wlhy, dan groups ne sama da 30, dan ALLAH kuma kuyi mini afuwa, amma kuna raina kuma ina kula da motsin kowa wlhy, ngd ALLAH yabar zuminci, inajin dad'in addu'oinku gareni da mahaifina😭🙏🏻🥰🥰🥰👌🏻_*
_Naga an bud'e groups d'in MUTUM DA DUNIYARSA kusan 8 kuyi hak'uri sunyi yawa wlhy, dan haka Zan fita a wasu, kafin Ku had'ama wayata zafi😂, inba hakaba nakoma la6e a WhatsApp aradu😫🤣⛹♀⛹♀._
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[4......]_*
..............Kamar yanda suka saba a kowanne dare bayan sallar isha'i akwai karatun manya magidanta a masallacin k'ofar gidan malam. A da shikeyi, amma dawowar Aliyu sai abun ya rabu biyu, malam Na koyar da dattijai, shikuma Aliyu matasa. Kowacce rana akwai littafin da suke karantawa, yauma kamar kullum Qur'an ne a gabansu, yayinda Sheirk Aliyu Maina ke karanto ayoyi daga suratul An-nisa cikin zak'in muryarsa da sanyin irinna masu nutsuwa. da alama ma yau suka shiga Surar, dan fako yake karantowa cikin kwarewar larabci da taka tsantsan.
Masallacin yayi tsit kowa yana saurarensa, sai da ya maimaita ayoyin daya karanta sau uku kafin ya d'ago idanunsa yana kallon d'aliban nasa da zasu iya kaiwa 40+, fuskarsa d'auke da murmushi mai sanyi.
Cikin nutsuwa suka shiga maimaitawa suma, yayinda yake musu gyara a inda yaji kuskure.
Har k'arfe 9 suna karatu.
Sheirk Aliyu ya kalli agogon fatar dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, ganin har tara da kusan kwata yay d'an gyaran murya alamar su dakata. duk kallonsa sukayi, yad'an murmusa yana fad'in “Masha ALLAH, Inaga yakamata mu dakata haka, domin kowa yaje ya k'arasa Uzirinsa”.
Duk sun amsa masa da to.
Addu'a yay musu kafin kowa yatashi ya fito bayan sunbashi hannu duk sunyi musabaha da bankwanar tashi lafiya.
Bayan fitar kowa ya tattare littatafansa yana zare farin glesses d'in fuskarsa sannan ya mik'e shima ya fito. Cikin gidan ya nufa, inda a zauren farko ya iske mahaifinsu malam Abdul-ra'uff da dattijan d'alibansa. Rissinawa yay ya gaidasu, dan yaga da alama suma sun gama karatun nasu na yau, har zai mik'e Malam yace, “Ali inason ganinka kuwa”.
Kansa a k'asa ya amsa da “To Babah gani”.
“A'a ba ciki zaka shigaba? Shiga ka fito zuwa sannan Na kammala nima”.
“To”. Ya amsa yana mik'ewa.
Da sallama ya shiga gidan nasu da a yanzu babu yawan hayaniya, saboda mafi yawan yaran gidan sunyi aure, wad'anda suka rage kuma duk sun mallaki hankalinsu, sai dai jikoki da wasu ke rik'o a matan gidan. Babu kowa a tsakar gida, sai wutar lantarki data haske ko ina kasancewar ba'a kashe gen... Ba saboda masu karatun dare. Kai tsaye k'ofar hajia bah-bah ya nufa uwargidan malam. Saida yay sallama a k'ofar d'akin aka bashi izinin Shiga sanna ya shiga da sallama.
Hajia Bah-bah da wata matashiyar budurwa da yara biyu suka amsa. Yaran suka taso suna masa oyoyo. Hannayensu ya rik'e cikin murmushi yana fad'in “A'a malam k'arami yau anan za'a kwana kaida Ai'shatu?”.
A tare suka amsa da e Kawu! Zamu kwana wajen hajia bah-bah ne, Ammin mu taje Kaduna.
“Masha ALLAH, ALLAH ya dawo da ita lafiya”. ‘ya k'are maganar yana zama a kujerar kusa da k'ofa’
Budurwar tace, “Yaya ina yini? Wad'annan iyayen maganar sun tsareka da surutu”.
Murmushi yayi sannan ya amsa da ”lafiya lau Ni'ima, ya makaranta?”.
“Alhmdllh yaya”.
Murmushi yayi yana maida hankalinsa kan hajia bah-bah dake kishingid'e tana murmushi tun shigowarsa.
Cike da girmamawa yace, “Hajia ina yini?”.
“Lafiya lau Aliyu, har an tashi daga makarantar?”.
“Muntashi hajia, saikuma ALLAH yasa muna cikin masu kaiwa gobe”.
“To ALLAH ya datar damu”. Hajia bah-bah tafad'a tana tashi zaune sosai. Yayinda Aliyu ya yunk'ura zai tashi, amma sai hajia Bah-bah ta dakatar dashi ta hanyar fad'in “Aliyu abinci fa?”.
“Alhmdllh hajia, dan yau nagaji barci zanyi da wuri, idan naci abinci yanzu zai takura min”.
“To shikenan, bandama dai kanason zama babban kwabo ai kawuce cin abincin gidanku saina matarka, yakamata dai a motsa hakanan Aliyu”.
Murmushi yayi yana mik'ewa da fad'in “Za a duba insha ALLAH hajia”.
Bayan fitarsa Ni'ima tace, “Wlhy kuwa hajia yakamata Yaya Aliyu yay aure, yanzufa kaf gidanan shikad'ai ya rage baiyi aureba a maza, gasu yaya Mahmud da Yaya Usman harsun cika wata hud'u da aurensu, shiko ko maganar ma bayayi, yakamata ya cire Asma'u a ransa, tana gidan mijinta hankali kwance harda yara biyu da cikin Na uku shiko ya zauna”.
Hajia bah-bah batace komaiba, amma fuskarta ya nuna alamun damuwa da tausayin Aliyun.
Shikam d'akin iya habi ya shiga itama bayan yayi sallama an bashi izinin shiga, ita kad'aice kawai a d'akin, dan dukta aurar da yaranta, sai yarinyar k'anwarta da take rik'o mai suna Maimunatu, itama budurwace, dan zatakai sa'ar Ni'ima.
Iya Habi ta tareshi da fara'a kamar yanda ta saba, dan ita mace ce mai yawan barkwanci, cikin tsokana tace, “Tuzurun gidanmu har an tashi daga karatun?”.
Fuskarsa d'auke da murmushi ya zauna, cikeda sanyinsa ya gaidata, shi mutumne da bashida yawan magana, shiyyasa ko Ana tsokanarsa bai iya ramawa.
Maimuna data fito a d'aki tawani washe baki, a rayuwarta tana k'aunar Aliyu, amma shi yanda ta lura matanma basa gabansa kokuwa duk malantarce oho.
“Yaya Aliyu barka da dare”.
Idanunsa yad'an d'ago ya kalleta kad'an ya janye sanann ya amsa da fad'in ”Yauwa Maimunatu, ya makaranta”.
“Alhamdllh yaya, d'azun a islamiyya nazo dubaka a office amma saina tarar ka fita ma”.
“ALLAH sarki”. Abinda kawai yafad'a kenan yay shiru da bakinsa, saima ya mik'e yayinda Maimuna ke shirin zama kusa da kujerar da yake zaune.
“Iya bara naje sai ALLAH ya kaimu”.
“ALLAH ya tashemu Aliyu kaji”.
“Amin iya”.
Maimuna da takaici ya isheta kam batama amsaba, tarasa yanda zata shawo kan Aliyu kanta.
Iya Habi Na kula da ita, murmushi kawai tayi ta d'auke kanta, tuni ta fahimci Maimuna nason Aliyun.
Aliyu kam yana d'akin gwaggo itama suna gaisawa, itama mace ce mai yawan sakin jiki da mutane, nanma ya gaisa da k'annensa biyu dasuka rage a d'akinta basuyi aureba, Asiya da Fatima, sanan ya fito zuwa kiran malam.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah dake fitowa daga d'aki cikin shirin fita ta kalli Umma dake zaune a tsakar gida tanajin redio, su kad'aine a gidan, su walida sun wuce islamiyya.
“Umma bara naje Na duba Maman Sadiq daga nan zanje na duba sa'adatu sulaiman ta islamiyyarmu ance batada lafiya yau ko islamiyya batajeba”.
“To jiddah saikin dawo, amma a dawo dai da wuri”.
“To Umma insha ALLAH”.
A k'afa ta taka har zuwa gidan Uncle yahaya, dan basuda wani nisa mai yawa, ta iske gidan shiru, su Sadiq duk sun wuce makaranta, Maman sadiq dake wance a tsakar gida ta d'ago Kai tana murmushi da amsa sallamar Jiddah.
“Yau malama ce a gidan namu?”.
Jiddah ta zauna gefen tabarmar tana yaye nik'ab d'inta, fuskarta d'auke da murmushi ta fara gaisheta. Maman sadiq ta mik'e zaune itama tana amsawa.
“Maman sadiq yanaji gidan shiru?”.
“k'annen naki duk suna islamiyya Jiddah, yasu Zarah?”.
“Suna lafiya, suma idan sun dawo islamiyya zasu biyo dubaki”.
“ALLAH ya dawo dasu lafiya”,
“Amin mama”. Jiddah tafad'a tana mik'ewa tsaye, hijjab d'inta ta cire ta d'auki tsintsiya ta share tsakar gidan. Duk wani aiki daya dace tayisa, ta dafa musu taliya bisa Umarnin Maman sadiq d'in. Bayan ta kammala komai taima Maman sadiq daketa kwarara Mata addu'a sallama ta tafi.
Daga nan napep ta hau zuwa gidansu Sa'adatu sulaiman d'in.
Bata wani dad'e a canba takuma hawo napep zuwa gida kasancewar yamma tayi lik'is, gab ma ake da kiran magriba.
Tunda ta fito a napep d'in gabanta ya fad'i domin ganin motar Abbansu a k'ofar gida, jiki a sanyaye ta mik'ama mai a daidaita hamsin d'insa tanufi k'ofar gidansu, kamar kullum saida tayi addu'ar shiga gida sannan ta shiga da sallama.
Tunkan ta k'asara shiga take jiyo sautin muryar Abbansu Na magana a zafafe.... Batada ikon juyawa dan haka ta ida shiga. Umma Na zaune a kujera y'ar tsugunno, yayinda Abba ke bisa tabarma da Umma ta shinfid'a masa. Yaye nik'ab d'inta tayi tak'arasa gabansa ta durk'usa, cikin rawar murya tace, “Abbah ina yini?”.
Harara yakuma zuba Mata, wadda dama tunda ta shigo yake mata ita. “Daga ina kike k?, nifa bazan d'auki wannan iskancin nakuba, wlhy duk wadda tajawo min magana saidai ya k'arema uwarku, ke ko kunya bak'yaji kiyita yawo gand'an-gand'an cikin anguwa domin kuji dad'in tozartani a dinga nunaku Ana y'ay'an Alhaji zakari ne ko? To lallai bazan lamunta ba, kodai ki fidda Mijin aure kokuma wlhy Na baki duk Wanda yaymin, itama Zarahn tazo ta fidda miji dan banga amfanin wannan karatunba, kuma da kukeyi bazai amfaneku da Komaiba balleni dake wahala daku”.
Cikin share hawaye Jiddah tace, ”Abbah kayi hak'uri, wlhy ba wani waje najeba, gidan Uncle yahaya naje Na duba Maman Sadiq batada lafiya”.
“Wannan kuma ke kika sani, nidai nafad'a miki”.
Umma na zaune tana saurarensu, duk k'ok'arinka baka isa gane yanayin da take cikiba, dan fuskarta gwanace wajen shanye damuwa da 6acin rai. Koda Jiddah ta tashi ta shige d'akinsu tana hawaye da kallo kawai Umma ta bita, bayan shigewarta ta d'auke idonta tana maidawa ga Abba.
“Alhaji nikam inason na tambayeka wani abu”.
Banza yay bai tanka mataba, sai dai ya nuna alamun yana saurarenta.
Bata damuba itama ta cigaba da fad'in “Shin wani yata6a nuna maka illar abinda kakeyi a rayuwarka kuwa? Baka tsoron ranar da zakayi nadama akan wannan ak'idar taka ne? Kokuwa dan kaga dai ina maka shiru akan lamarin yarannan? Lallai Ubangiji adalin sarkine, domin adalcin mulkinsa ne yasa shi fidda rayayye a cikin matacce wlhy, lallai ina jiye maka ranar dana sani”.
Umma Na gama fad'a ta tashi ta shige d'akinta. Cike da tsantsar takaici Abba ya bita da kallo, sai dai kuma ya had'iye abinsa ya mik'e domin bin bayanta.
Umma dake zaune a bakin gado tayi tagumi ta d'ago idanu ta kallesa kafin ta janye.
Zama yay kusa da ita a bakin gadon yana fad'in “ke dad'ina dake Yagana rashin fahimta, to miye Na yankamin wannan maganganun?”.
Murmushi kawai Umma tayi, dan hakan da yayi yakuma tabbatar Mata da zarginta. Ta d'an kallesa a kaikaice, “Halan yau amarya ta murd'a kanbunta na doguwar tafiya? Shiyyasa aka taho ga juji?”......
Da sauri ya saka hannu ya rufe mata baki. “Nidai karkimin sharri, a yaushe na ta6a cemiki juji?”.
Nanma murmishin Umma tai kawai ta d'auke kanta tana had'iye wani Abu mai d'aci. Lallai rayuwar wasu mazan wanan zamanin Na d'aure kanta, mace batada wani kima ko muhimmanci a garesu sai in zasu biya buk'atarsu. Takanyi wata bataga Abba a Idonta ba, badan tayi tsufan da bazata iya amfanar dashi ba, a'a sai dan kawai ita uwace ta y'ay'a Mata wad'anda ba sune tsarinsa ko ra'ayinsa ba, idan harka gansa yana yawan zuwa gidan to lallai yayi fad'ane da hindatu ko tayi wata tafiyar da bazai iya jurewaba shikuma, to lallai a wannan lokacin zai maida gidanta wajen zuwa, abinda ke 6ata ranta da zuwan nashi shine gushewar farin cikin yaranta, dan yata caccakarsu da jifansu da kalamai marasa dad'inji, badan sun masa laifin komaiba, sai dan kawai su ba abin sonsa baneba............
Katse mata tunani yay da jawota jikinsa, tai firgigit Na dawowa hayyacinta, sannan ta janye jikinta tana mik'ewa.
Fuskar Abbah a d'aure yace, “Amma kinsan hakan bakomai bane a gareki sai nemawa kai tsunuwar Ubangiji da mala'iku ko? Dan inada ikon nemanki a duk sanda Na gadama kuma nayi buk'ata.
Wani murmushi. Takaici Umma tayi tana had'iye hawayen dake Neman cika Mata idanu, da k'yar ta iya furta “Salla ake kira”.
Tsaki yayi ya cire hular kansa ya ajiye a saman gadon sannan ya mik'e, babbar rigarsa ya ajiye itama kusada hular ya fita.
Umma ta share hawayen fuskarta da bakin zani kafin tabi bayansa zuwa tsakar gidan. Yana zaune gindin rijiya a kujerar da Umma ta tashi, k'arasowa tayi ta d'auraye butar k'arfe data d'akko a d'aki sannan ta zuba masa ruwa ta rissina gabansa ta ajiye.
Hakan yayi dai-dai da shigowar Zarah da Walida suna Y'ar dariya, amma ganin Abbansu Na alwala sai kowa tai azamar had'iye dariyarta, ko kad'an basu Lura da motarsa ba a waje su.
Kallo d'aya yay musu ya d'auke idonsa, yayinda sukuma suka durk'usa suna gaisheshi.
“Lafiya”. Kawai yace yaci gaba da alwalarsa.
Jiki a sanyaye suka maida kallonsu ga Ummansu. “Umma barka da gida”.
Murmushin kwantar da hankali ta sakar musu tana fad'in “y'an makaranta an dawo?”.
“Eh Umma”. Suka amsa murya na rawa, kafin su mik'e zuwa d'akinsu jiki a sanyaye.
Jiddah dake kuka tun bayan tasowarta gaban Abbah ta mik'e da sauri jin maganar y'an uwanta, bata buk'atar su isketa tana kukan, dan haka tai azamar share Hawayenta.
Yayinda suka shigo da sallama saita tarbesu da fara'a, harda tsokanarsu.
“y'an matan gidanmu yau kun makara, dolene ayi muku bulalar makara gaskiya”.
Duk yanda taso 6oye musu hakan bai hanasu fahimtar tayi kukaba, sai gani kawai tai Walida ta fad'o kanta ta fashe da kuka, itama zaran saita had'asu ta rungume tana sakin Nata kukan. Daman sunsan zuwan Abbansu gidan tamkar zuwan 6acin rai ne a garesu da Ummansu abar alfaharinsu da sonsu.
Umma data d'aga labulensu saboda Abba ya fita masallaci tace, “Kukuma minene haka? Nifa kunsan banason wannan shashancin, kufito kuyi alwala, k Zarah tunda ba salla zakiyiba maza fito ki d'aurayemin kulolin Abbanku Na abinci”. Daga haka ta Saki labulen tabar wajen.
Suma sai suka saki juna kowacce Na share hawayrnta, sunsan ita kanta Umman nasu k'arfin hali kawai takeyi. Umarninta sukabi suka fito waje, walida da Jiddah suka d'auka butocin al'awala, Zarah kuma ta shiga kicin d'akko kulolin.................✍🏻
**_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[5......]_*
..............Gaba d'aya saisu Jiddah suka kasance cikin rashin sakewa, dan koda suka idar da salla basu fito tsakar gidaba, duk da zafin da ake zubawa yau. Itama Umma bata nemesu ba, dan tana idar da salla ta fito ta had'a abincin Abba takai falo, baiwar ALLAH harda kunna turaren wuta da maganin sauro. Tana kammalawa Ana kiran isha'i, dan haka bata nemesuba tawuce d'aki dan yin salla.
Ana idar da sallar isha'i Abba ya shigo gidan, babu batun sallama dama a tsarinsa sai gyaran murya, ada dasu Jiddah Na k'anana dasunji gyaran muryarsa suke guduwa su 6uya. (Humm ALLAH ya k'yauta🙁).
Babu kowa a tsakar gidan, dan haka ya wuce d'akin Umma, kulolin dake a tsakkiyar falon yake bi da kallo, kafin ya maida kallonsa ga Umma dake can wani d'an loko inda ta maida wajen ibadarta a tsakanin kujeru. Addu'a takeyi, dan haka baice komaiba ya zauna a kujera mai zaman mutum biyu.
Su Jiddaha sunajin Abbansu na gyaran murya amma babu wanda yay koda gigin lek'owa waje.
Saima tagumi duk da suka rabga, kowa da irin kalar tunanin da yakeyi.
Jiddah ce tafara d'ago Kai ta kallesu, tausayin y'an uwan nata Yakuma kamata, cikin kauda tata damuwar ta zunguri walida dake kusa da ita. Kallonta Walidan tayi, Jiddah ta sakar Mata murmushi “Haba Autar Umma, irin wannan tagumi haka? Yau kin rik'e karatun islamiyya ko?”.
Kasa magana Walida tayi, sai hawaye da suka fara zarya a kumatunta. Jiddah tad'an zaro ido waje tana kamo hannunta “Walida miya faru da kuka haka? Ko bakida lafiya ne?”.
Kafin Walida tayi magana Zarah tace, “Yaya Jiddah kema kinsan Abbane”.
“Abba kuma? To mi Abban yayi? Naga da kuka shigo baice daku komaiba ai?”.
Shiru duk sukayi, Walida ta d'ora kanta bisa kafad'ar Jiddah tana cigaba da kukanta.
Kamata Jiddah tayi ta tayar zaune, “Kinga kukan ya isa haka to, yanzu dai idan anmuku k'ari kuzo muyi, idan kuma ba ai mukuba muci abinci nabaku wani labari, dan wannan kuka bazai canja komaiba y'an uwana, sai k'arin takaici da saka k'unar zuciya, mukasance masu godiyar ALLAH da samunsa a matsayin mahaifi, wani mahaifinma yafishi munin hali ai, amma masushi basu jefarba, to muma addu'a yakamata mu cigaba da masa kunji”.
A tare suka amsa da to, kowa Na share hawayensa.
Qur'an suka d'akko suka karanto inda akai musu k'ari, Zarah ta fara karantowa, dan haka Jiddah taimata gyara dakuma maimaita mata har saida taji ya zauna a harshenta sannan takoma kan Walida, itama saida ya zauna sannan sukai Addu'a, Zarah ta fita d'ebo musu abinci.
Koda suka zauna zaman cin abincin sai duk suka kasa, sai kad'an sukad'an tsakura kowa yace ya k'oshi. Damma kad'an suka zuba.
Daga Umma har Abba suna jiyo sautin karatun su Jiddah daga falo, shi yanacin Abinci ita kuma tana zaune gefensa, dukda dai ba wata hira sukeyiba, garama shi akan kirashi a waya lokaci-lokaci, wani ya amsa wani ya share.
Itadai Umma ranta cike da farin cikin jin sautikan muryoyin y'ay'an nata Na karatun littafi mai tsarki, saitaji kaso mafi yawa Na damuwarta ma ya ragu.
(ALLAH sarki Umma😿)
★★★★
Da asuba Umma da kanta ta fito ta hura gawayi, dan sanda Jiddah ta tashi harya ruru, lokacin anata kiran sallar farko.
Jiddah Ta fito tana fad'in “Umma kinga yau mun kusan makara wlhy”.
Kallonta Umma tayi tana d'aura tukunya bisa garwashin, “Ai dama yanzu nake shirin zuwa na tadaku Jiddah, halan baku kwanta da wuribane?”.
“Kusan haka kam Umma, yanzu mi Zan miki?”.
“A'a jekiyi alwalanki kawai, suma su Zarah ki tadosu”.
”To Umma”.
Abba ya fito daga d'akin Umma fuska a d'aure, kai kace sak'on mutuwa aka aiko masa, Butar da Umma ta cika da ruwa ya d'auka domin yin alwala.
Su Zarah da Jiddah ta taso harsun lek'o kai zasu fito suka koma saboda ganin Abba atsakar gida, ciki suka koma, idan yagama ya fita sa fito.
Shikam baima San sunayi ba, yana kammala alwalarsa batareda yacema Umma komaiba yanufi hanyar soro, k'ofa ya bud'e ya fita.
Umma ta sauke ajiyar ziciya kafin ta kalli k'ofar d'akin su jiddah tana fad'in “Ku kuma Na la6e saiku fito ko”. Ashe tana kallon su Walida sanda zasu fito suka koma.
Fitowa sukayi, walida ta d'auki butar alwala, Zarah kuma ta matso wajen Umma.
”Umma dan ALLAH nad'an d'iba ruwannan?”.
Umma ta mik'e tana cewa “Ki d'iba mana, Amma ki k'aramin”.
“To Umma Na gode”.
Lokacin da Abba ya dawo su Walida duk suna tsakar gida, bayan sun idar da salla suka fito suna kimtsa gidan.
Umma ta dama kunu, sai Jiddah dake suyar fanke, Walida Na bakin rijiya tana wanke-wanke, Zarah kuma sharan tsakar gidan bayan ta gyaro d'akinsu.
Umma ma tana gyaro nata d'akin, dan inhar Abba Na gidan bata barin su Jiddah shiga mata d'aki.
Da gyaran murya ya shigo kamar kullum, dan haka su Walida duk suka nutsu, Dama bawani hira sukeyiba. Kowacce gaisheshi ta shigayi, ya amsa saud'aya yana harare-hararen Neman kuskuren dazai ci zarafinsu. Saidai kuma baiga komaiba, dan haka ya shige yana fad'in Zarah ta goge masa takalmansa.
Da to ta amsa muryarta Na rawa.
A d'arare su jiddah sukaita komai tamkar jiya da daddare, su Walida dai suka samu sukai shirin makaranta bayan sun cakuli abinci, dan yauma basuci Na kirkiba.
Lokacin da sukema Umma sallama Abba yanaji amma bai tankaba, sai Ummace taimusu addu'ar dawowa lafiya.
Jiddah ma a gaggauce takuma kimtsa gidan tai shirin Islamiyya ta fito, dukda da sauran lokaci ta gwammace tabiya ta gidan Uncle yahaya ta cinye lokacin acan.
Kodà tazo yima Umma sallama bata hanata ba, dan tasan gudun zama suke a gidan.
Bayan duk sun fice Abba ya kalli Umma yana wani cika da batsewa yace “Yagana had'amin ruwan wanka”.
Da “to” ta amsa tana mik'ewa ta fice. Babu dad'ewa ta dawo tace ta had'a.
Fitar Abba wanka babu jimawa wayarsa tahau ringing, Umma batako kalletaba balle tayi tunanin d'auka harta tsinke aka kuma Kira, nanma sharewa tai, ganin anyi kira Na hud'u ta nufi wayar danta duba.
*Matata*
Shine abinda taga an rubuta a jiki, dan haka ta maida ta ajiye masa kayarsa takoma wajen zamanta.
Daga can ba k'aramar harzuk'a hajia Hindu tayiba, dan jikinta ya bata yana gidan matarsa. Shanye damuwarta tayi, saboda tana cikin taron mutanene, k'awarta ce ke aurar da y'a a jigawa shine taje. Dalilin kiran nasa kuwa ta kira kalifa ne taji idan sun wuce makaranta shine yace Mata driver yace babu mai a mota, kuma Abbansu tun jiya da yamma daya fita bai dawoba. Shine ta kirashi taji ina yaje? amma har Kira hud'u babu amsa.
Tana cikin wannan tunanin Kira ya shigo wayarta. Abba ne daya fito daga wanka Umma ta fad'a masa an kirashi shine ya duba, ganin Hajia hindatu ce yay azamar kiranta yana shigewa bedroom yabar Umma a falo. Sai dai kuma har wayar ta tsinke bata d'agaba. Kuma kiranta yayi.
Hajia Hindu dake kallon wayar taja guntun tsaki sannan ta d'aga. Ko sallama babu tace, “Alhaji kana inane?”.
Dukda tambayar tabashi haushi saiya danne, saikace wani yaronta. Amma a fili sai yace, “Haba Maman kalifa ko gaisuwa ma babu?”.
Dogon tsaki taja, a harzuk'e tace, “Kaga malam nifa ba wannan ya sakani kiranka ba, yara suncemin tun jiya baka gida, gashi yau sun tashi motarsu ta zuwa makaranta babu mai........”
Cikin nuna damuwa da 6acin rai yace, “Amma driver d'innan d'an iskane, shine bazai kirani a waya ya sanarminba?, to lallai bazan yarda da wannan iya shegenba......”
Hajia Hindu ta katse masa magana da fad'in, “Aiba laifinsa bane shi kad'ai, inda jarabarka bata motsaba katafi wani waje ka kwana hakan zai faru? Kamayi duk yanda zakayi kakaimin yara makaranta kafin su makara”.
Kafin yayi magana ta yanke wayar. Ya dafe kansa saboda takaicin yanda Hindu ke datsa masa magana tamkar boyi-boyinta. Da hanzari yahau shiryawa, dukda ba zaman gidan yakeba yanada kaya a gidan.
Lokacin daya fito Umma na k'ok'arin had'a masa shayi da kayan tea d'in da Nafisa ta kawo musu.
Ganin zai fice tayi saurin fad'in “Abban Nafisa ina kuma zakaje ga Karin kumallo ina had'a maka?”.
“Kinga barshi Yagana, su kalifa zanje nakai makaranta karsu makara, motar da ake kaisu makaranta babu mai”.
“To”.
Kawai Umma tace masa taja bakinta tayi shiru. Shikuma ya ajiye dubu uku a hannun kujera yay ficewarsa batareda yayi bayaniba.
Ko motsi Umma kasawa tayi a wajen balle tasamu damar d'aukar kud'in. (Nace, “Humm”🙁).
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Lokaci da Aliyu ya fito daga cikin gida malam ya shige falonsa da k'ofar ke a zaure Na biyu.
Sallama yayi ya amsa masa tare da bashi izinin shiga.
Malam dake kishingid'e bisa lallausar dardumar dake wani sashe Na falon ya d'ago ido yana kallon Aliyu bayan ya rufe littafin dake hannunsa. Zama Aliyu yayi a gefen dardumar, malam yaymasa alama daya matso kusa dashi. Matsawa yay yana guntun murmushi.
Saida suka nutsu malam yace, “Aliyu!”.
Cikin sanyinsa yace, “Na'am baba”.
“Aliyu ina muka kwana akan batun aure? Nazata a shekara d'aya da dawowarka yaci ace kazomin da zancen samun Matar aure, amma sainaji tsit, mike faruwane?”.
Kansa a k'asa ya kasa kallon malam, cike da kunya yace, “Baba ai har yanzu......”. Saikuma yay shiru.
“Har yanzun mi?”. Cewar malam yana kuma tsareshi da idanu.
Aliyu yakuma k'asa da kansa. “Baba har yanzun banida tabbas akan samun......”. Nanma ya kasa k'arasawa.
Murmushi malam yay, dan ya fahimci inda Aliyun ya dosa.
“Ali kenan, to ai a ganina auren shine zai banbance mana hakan ko? Zamanka haka babu aure a matsayinka Na babban mutum mai koyar da ilimi da yad'ashi ko kusa bai daceba, aure shine cikar kamala Na kowanne d'an Adam, duk girmanka da mulkinka da addininka saika saka rigar aure kake kuma daraja a idon jama'a. Yakamata ka nemo Matar aure hakanan, idan kuma ni Na nemo maka to shikenan. Ni dai nabaka watanni uku idan ALLAH ya kaimu, daka dawo daga tafiyar nan da zakayi kafara shirin aure, inason kafin azuminnan mai zuwa ka ajiye iyali, kaje kayi shawara, zaka nemo kona nema maka kafin ka dawo?, idan kuma kanada wadda kakeso saika sanarmin, dan nikam nagaji da ganinka haka kana yawo babu aure”.
“Amin afuwa baba, insha ALLAH Zan duba, abinda Na yanke zakaji zuwa Safiya idan ALLAH ya kaimu, ALLAH ya huci zuciyarka”.
“To Alhmdllh, ALLAH ya kaimu lafiya, kenan kanada wadda kakeso?”.
”A'a baba”.
“To shikenan, kaje ina saurarenka zuwa safiyar. Akwai wasu littatafai da Malam Salis keso, nace masa Zan tambaya masa ko kana dasu”.
“To Baba wannene?”.
“Yafa bani a rubuce dama dan karna manta, duba littafincan ko ciki Na saka takardan”.
Mik'ewa Aliyu yayi zuwa inda kantar buks d'in malam take, ya bud'e littafin dake a jiye a k'asa da malam ya nuna masa. A shafin farko yaga k'aramar takarda dan haka ya d'akko yana nuna masa.
Kai malam ya jinjina alamar eh itace.
Aliyu yay masa sallama sannan yazo ya fice domin zuwa makwancinsa..
K'aramun gida dake jikin masallacin malam nanne gidan da yaran malam maza duk suka zauna kafin aurensu, ayanzu haka Aliyu ne kawai a ciki sai idan malam yayi bak'i ai musu masauki anan.
'Dakinsa dake can k'arshe ya bud'e da key ya kunna fitilar wayarsa sannan ya shiga da sallama, d'akine babba dake malale da kafet ruwan makuba (oxblood) sai k'atuwar katifarsa irin wadda ba'a sakawa a gado, sai firij da kantar litatafai da k'aramar wardrobe ta kayansa, d'akin babu wani tarkace dan mazaunin cikinsa ma'abocin tsaftane a koyaushe. Fitilar wayarsa ya kashe ya kunna wadda yake amfani da ita idan babu wuta, dandanan d'akin ya gauraye da haske.
Wata k'ofa danake k'yautata zaton bayice a d'akin naga ya shiga. Kusan mintuna 30 saigashi ya fito da alama wanka yayi.
Bayan malam Aliyu ya kammala dukkan uzurorinsa yazo ya zauna a gefen katifarsa yana jawo lap-top d'insa, yanar gizo ya Shiga domin duba sak'wannin jama'a Na neman fatawa da masu gaisuwa.
Ahankali yake binsu d'ai-d'ai yana dubawa, wata fatawar ta tausayi wata ta mamaki, wanima takaici ne tsantsa a ciki. Wasu yakan basu amsa, wasu kam wucewa kawai yakeyi. Wani sak'o dayaja hankalinsa matuk'a ya nutsu yana kuma dubawa.
*_Assalamu alaikum. Malam barka da warhaka, malam wlhy inada damuwa ne, kuma Na rasa Wanda Zan tunkara da ita. Mu hud'u iyayenmu suka Haifa, mata biyu maza biyu, nice nake bima babban wanmu sai k'anwarmu sai kuma autanmu, to malam yanayin rayuwar da muka tashi ta ak'idar boko saiya zamto ta6a jikin juna irinsu runguma da zama kusa da juna hakan ba komai bane nida y'an uwana, wannan kusancin mai tsanani saiya kaimu ga fara wuce iyaka har yayana yafara kwanciya dani, iyayenmu basu ta6a saniba konace ak'idar data lullu6e zukatanmu bata ta6a kai tunaninsu da zarginmu ba, malam yanzu haka maganar da nake maka inada ciki wata hud'u kuma bansan da shiba sai kwanaki 6 da suka shige, hankalina yatashi na nufi d'akin yayana danna sanar masa saina taddashi yana irin abinda yakeyi da ni da k'anwarmu dake bimin. Malam narasa yazan fassara wannan halin dabbancin namu, sakacin iyayenmu ne? kokuwa d'aukar ak'idar da bata dace da addininmu ba?, wlhy jinake tamkar Na kashe kaina malam, nayi nadamar rayuwata data y'an uwana, malam ka taimakeni da shawara dan ALLAH😭🙏🏻_*
Tagumi kawai malam Aliyu yayi ko yatsansa yakasa motsawa, sai had'iyar yawu yake mai d'aci da k'yar, idonsa ya kad'a yayi jazur, yama rasa yanda zai fassara wannan kwamacalar, anya wannan duniyar kuwa mutane na tunanin barinta?.
Kansa dayaji yana Sara masa ya dafe tare da ture lap-top d'in gefe ya zame ya kwanta a katifar.
Gaba d'aya zuciyarsa ta k'untata, wasu hawaye masu d'umine suka silalo masa a kumatu.
Yaja tsawon lokaci yana jujjuya abin a ransa, har agogo ya nuna k'arfe 1am bai iya runtsawa ba, mik'ewa yay yashiga toilet ya d'auro alwala ya dawo yafara jero nafilfili, a cikin sujudansa yana kuka da jaddada neman gafarar ubangiji. Sai kusan 3am ya idar, jin idonsa ya cika da barci yakoma saman katifar ya kwanta.
Amma maimakon barcin yazo saiya fad'a duniyar tunani akan maganar baba kuma, dukda wancan maganar yarinyar nata cin zuciyarsa a gefe. Harga ALLAH a yanzukam baisan kuma ina zai nemo mataba, dan tun tabon da Asma'u tabar masa har yanzu baigama gogewaba, gashima bashida tabbaci akan ingancin lafiyarsa har yanzu.
Kwanciyarsa yakuma juyawa yana ayyana kodai yabama baba damane kawai, k'ila shi yanada wadda ya hango ta dace dashi, tunda yasan baba bazai ta6a masa za6en tumun dare ba.
Da wannan tunanin barci ya saceshi bai fargaba............✍🏻
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
0 comments:
Post a Comment