*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[11...]_*
..............Yau su Jiddah da murna biyu suka tashi, Na tafiyarsu barno gobe da zuwan yayarsu Zulaihat dake aure a huntuwa Katsina state kenan.
Tsaf kowa yagama had'a kayansa, Zarah da walida suka fito cikin shirin zuwa kunshi Wanda Jiddah tace bazatajeba, ko kitso tak'iyi tace saitaje barno za'ai mata irin nasu.
“Umma dan ALLAH kibamu aron dubu d'aya inji aunty Nafisa, tace idan tazo zata baki”.
“Wa? Kunga idan zaku kubar tsayani, idan kuma kunje kubar tunoni, sisi ban badawa, yanzunan zamu Shiga kasuwa nida Maman Sadiq da Jiddah ”.
“Haba Umman mu ta mutunci, ALLAH ya k'ara miki Nisan kwana”. ‘Walida tafad'a tana salute d'in Umma’.
Cikin dariya Jiddah dake janyo ruwa a rijiya tace, “Kumace ta tsiyace mana”.
“Kai Yaya Jiddah dan ALLAH karki 6ata mana tsari mana.........".
“kujimin yarinya, yoni minace? Umma nace karki basune?”.
“Ai koma bakiceba ba bayarwa zanba, kuje taimuku bashi, idan Nafisar tazo Ku k'arata, ai Rashidar zata muku lamuni”.
cikin shagwa6a Zarah tace, “ALLAH Umma sokike kawai girmanmu ya fad'i a wajenta, ga sabon d'inkinmu ki rik'e matsayin jingina, idan munbaki saiki bamu”.
Jiddah ta kwashe da dariya tana mik'ewa, “Umma Na rantse ki kar6a, idan ba a biyakiba kibar gayu susa tsoffin kaya a wajen biki”.
“Gaskiya Jiddah kin kawo shawara Mai k'yau, y'ammata aje a d'akko ga dubu bugun Abuja”. ‘Umma tak'are maganar tana dariya da ciro dubu a jaka’.
Walida data kwaso sabbin kayansu itada Zarah ta mik'ama Umma tana tura baki irin munji haushinan.
Kar6a Umma tayi tabada dubu, suka fuce suna musu sallama ciki-ciki. Dariya sosai Umma da Jiddah keyi harsu Zarah suka fice.
Cikin dariya Jiddah tace, “Umma y'ay'ankifa sun shak'a”.
“Ai gara da suka shak'a, nima Na rama kiramin innata dasukaitayi d'azun da farar safiya”.
Jiddah ta had'iye dariyarta tana zaro ido waje, “Tofa Umma ashe nima ba tsira zanyiba”.
“Oh kinzata kema kinsha banzane? Inanan zuwa kanyi ai”.
“Haba Ummanmu yi hak'uri, kingafa har kud'in saya mata goro na tanada ALLAH kuwa”.
“Ban yarda dakeba Jiddah..........”
Kafin Jiddah tabama Umma amsa Maman Sadiq ta shigo da sallama. Amsawa sukai Umma namata lale. Yayinda Jiddah ke fad'in “Mama ina Rudwan d'in?”.
“Nayi cinikinsa a hanya yanzunan”.
“Haba dai mama, aiko dabaki k'arasoba”.
Mama tai dariya, “Mizai hanani k'arasowa kuwa? Na gamu dasu Zarah ne suka amsheshi”.
“Yanzu naji batu mama, yama huta dashan wanan ranar da turnitsin kasuwa”.
Babu 6ata lokaci suka shirya suka fito domin tafiya kasuwa, sai da Jiddah ta lek'a gidan Rashida tabama su Walida key d'in gidan sannan ta fito suka tari napep zuwa kasuwa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tsaf malam mustafa yagama binciken da malam ya sakashi akan Jiddah, dan haka yau bayan idar da sallar zuhur yasameshi da bayanin komai daya danganci Jiddah da ahalinta.
Malam yayi farin ciki sosai da tarbiyyar yarinyar, saima yaji takuma Shiga ransa fiye da lokacin daya ganta, dukda ya jinjina mamakinsa akan lamarin mahaifinsu na jahilci, inba jahilciba babu wani bawa dazai guji Ni'imar ALLAH saboda tsarinsa na banza, indai kana numfashi kaji Abu iri-iri a duniya, na ban haushi dana ban al'ajabi..
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
“Da gaske kana sonta Alhaji Garba?”. ‘Abba yay maganar yana kallon abokinsa Alhaji Garba mai tabarma’.
“Wlhy da gaske nake maka wannan zancen Alhaji Zakari, inason Jiddah y'arka, danni dai bak'aramin birgrni tayiba wajen taronnan da akayi”.
Abba yay murmushi kafin ya muskuta zamansa ya jingina da bango, “Alhaji Garba daga yau nabaka Jiddah, ko gobe kake buk'atar ganinta a gidanka kazo a d'aura muku aure”..
“Kai amma naji dad'i sosai abokina, ALLAH ya k'ara girma, tabbas inason auren ya kasance kusa, saboda matsalar hajia deluwa ta isheni ainun, ina buk'atar Matar da zata kwantar da hankalina nima, sai dai ba wai gobeba, idan babu damuwa yakai k'arshen watanan”.
“Hakan mai sauk'ine, dama zasuje Barno biki gobe, nima jibi zanje a d'auro auren Dani, saboda k'anin mahaifiyar tasune zai aurar da yarinya, insha ALLAH zan sanar da danginta kai”.
“Ai to indai hakane kawai bara Na shirya muje tare, kaga saisu ganni dak'yau nayi gaisuwar surukai ma”.
Dariya sukad'anyi suna tafawa.
Abba yace, “Lallai kakawo shawara mutumina”.
Turk'ashi🙆🏻, yau munga idi abba zai 6aro mana ai😱.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai kusan k'arfe 5 su jiddah suka dawo gidan, sun iske ko ina ya kacame da hayaniya, dan kuwa aunty Zulai ta iso da y'ay'anta biyu, tabar manyan guda uku acan gida wajen kakarsu, nanfa aka kuma kacamewa murnar ganin juna, dan kusan shekara kenan batazo kano ba, sukuma inba haihuwa tayiba Abba ba barinsu zuwa yakeba, garama Jiddah wani lokacin Umma kan aiketa tayi kwana biyu ta dawo.
Ana cikin Murnar ganin Aunty Zulai saiga Aunty Nafisa itama takasa hak'uri tataho nan ta kwana tunda da sassafe zasu wuce. Gidafa ya kacame tamkar ana biki, babu maijin maganar wani, ga y'ay'ansu Aunty Nafisa dama bajin magana sukeba, Umma dai tasamu ta rufe rijiya 6am saboda tsaro. Ganin k'unshin su Zarah yayi k'yau Jiddah tace dama itama tasani taje.
Dariya sosai suke Mata hardasu Aunty Nafisa.
Yaukam sunsha hira, dan kusan raba dare sukayi ana hirar zuminci.
Washe gari tunda asubar farko suka tashi, ALLAH ya sosu aka kawo wuta, dan haka sukasa ruwan zafi Mai yawa a hita, har suka samu ya tafasa akwai wuta.
Kaf yaran Zarah ce tai musu wanka, yayinda Walida ke shiryasu. Jiddah da aunty Nafisa kuwa sunata k'ok'arin had'a abin Karin kumallo.
Sunsami gudanar da komai akan lokaci har sallah, karfe 6 saura motar bos da Uncle yahaya ya tanadar musu ta iso, dan haka akaita fidda kayansu ana lodawa amotar, bayan angama tsaf, saikuma ga Maman Sadiq da tata gayyar y'ay'an itama. Tuni suka shishshiga mota aka rufe gidan suka shilla Barno.
Saina karaso nima🚗, dan bazan had'a mota da kowaba🥺.
★★★★★
Sun isa barno lafiya, yayinda dangi suka kacame da murnar isowarsu, bazaka ta6a cewa aunty Zulai da aunty Nafisa ba tsatsonsu bane, dan yanda akema su Zarah suma haka ake musu babu wani banbanci. Dan danan aka shiga hidima dasu, bayan sunci abinci sunyi nak kowa yanemi Mai fisheshi, tuni Zarah da Walida sunbar gidan bayan sungama tsokanar Inna hajia (kakarsu mahaifiyar Umma), ta tsufa kam, saidai bazamuce irin tukuf d'inan ba, daka ganta kaga cikakkiyar kanuri, dan harda 6ular hancinta ras, Hausa kam kad'an-kad'an takejinta ma.
Fitar su walida babu dad'ewa saigasu Fannah amare, tuni suma suka janye Jiddah bayan sun gaisa dasu Umma.
Washe gari da Hantsi saiga Aunty Sauda babbar yar su Jiddah tazo itama daga Yola, dan can take aure. Zokaga murna wajen Umma dasu Aunty Nafisa anga y'ar uwa, su Zarah kam basusan tazoba saida sukazo d'aukar kayansu, nanfa suma suka kadandaneta suna nuna murnar ganinta, tare damata tsogumin batazo da yaraba sai wadda take goyo kawai Hanan.
Wajen karfe 3 itama Hannatu ta iso tare da Mamansu (Amina Matar Abba ta farko) dakuma wasu daga dangin Abba da sukazo yima Umma Baici, y'ay'an Ummafa sun had'u, Amina da Umma kam idan kagansu abin sha'awa, tamkar wasu Yaya da k'anwa, dukda basu zauna gidan Abba a tareba hakan bai hana kulluwar zuminci mai k'arfi a tsakaninsu ba, dan sunajin dad'in yanda Umman ta had'a y'ay'an dukta rik'e, (itako aunty Zulai mahaifiyarta ALLAH yamata rasuwa dama) dan haka batada Uwa irin Umma, Abbanma daya haifesu ba damuwa sukai dashiba, dukda suna bashi girmansa kamar yanda koyaushe Umma ke nuna musu muhummancin hakan.
Biki yacigaba da gudana yanda yakamata, yayinda aketa zuba al'adun biki irinna kanuri, Su Jiddah dai anshige ko ganinsu ba'ayi, kuma duk wannan shagali bai hanata saka hijjab d'intaba duk inda zataje, nik'ab ne dai data d'akko zatasaka sai a kwace a hanata, babu yanda zatayi dole ta hak'ura, amma duk saitake jinta a takure, shiyyasa ko yaushe kanta a k'asa batason kallon kowa.
Washe garin d'aurin aure saiga Abba da abokinsa Alhaji Garba, kasancewar tafiyar wuri sukayi wajen k'arfe d'aya suka iso.
Basu sami ganin Umma ba saida aka d'aura aure, amma sun sami tarba ta mutunci daga y'an uwan Umma maza.
Bayan gama d'aurin Aure Umma tasamu da k'yar tafito cikin mutane ta samesu a gidan makwafta da aka saukesu a d'akin soro, ganin dukkan tarbar da zata iya musu an musu sai suka gaisa takoma kiran su Aunty Sauda.
Amina kan duk yanda Umma ta rok'eta tazo su gaisa k'i tayi.
Daga Sauda, hannatu, Zulaihat, har Nafisa haka suka shigo fuskoki babu walwala, kowacce kuma cikin kamalarta, dan duk ALLAH ya kaisu gidan hutawa, babu maishan wahala a gidan aure.
Abba yayi mamakin ganinsu amma saiya 6oye ya amsa musu gaisuwarsu babu yabo babu fallasa, ko tambayar ya yaransu baiyiba, amma su da suka tambayi yasu kalifa saiya hau washe baki da fad'in duk sun a lafiya.
Takaici ya cika zuciyarsu aunty Sauda da Umma, basubi takansaba sukai masa sallama suka fito.
Umma ma sama-sama taimasa sallama ta fito tabarsu, dan anan zasu kwana sai gobe zasu wuce. Aiko bata sake bi takansuba saida daddare data kawo musu abinci, anan ta iskesu da y'an Uwanta maza, haka kawai tasha jinin jikinta da zaman hirar tasu, saidai batace dasu komaiba ta juya tana fatan ALLAH yasa alkairine.
Washe gari Abba yasamu gaisawa da Inna hajia, itama yaymata dukkan bayanin da yama y'an uwan Umma, ta jinjina wannan lamari sosai, saidai batada hurumin hanashi yin yanda yaso da y'ay'ansa, dan haka tabishi da addu'ar ALLAH ya za6a abinda yafi alkairi.
A ransa yace, “ai yama za6a, dan auren Jiddah da Alhaji Garba babu fashi”.
A ranar suka koma shida Alhaji garban bayan angama nunasa cikin dangin Umma da sunan Mijin da Jiddah zata aura.
Kowa dai wannan za6i bai masaba, amma basuda hurumin hanawa saboda dai shikeda iko da y'arsa. Umma da Jiddah da su Aunty Sauda dai basusan abinda ke faruwaba, duk da sunji anad'an maganar sama-sama, saidai basu fahimci wacce Jiddarba.
Kammala biki da kwana biyu suma sukayi azamar tafiya, dama tun jiya aunty Sauda da mama Amina da aunty Hannatu sun koma da sauran dangin Abba.
Abba dai daga Barno Ashe Adamawa ya wuce da Alhaji garba, inda yasanar dasu shine zai auri Jiddah, babu mai hurumin hanashi iko da d'iyarsa, amma wasu sun nuna masa illar hakan, dan Alhaji garba yayma Jiddah Tsufa sosai. Amma ganin ya dage sai suka bishi da fatan alkairi kawai, dan kowa yasan halinsa na kafiyar tsiya.
Da daddare Inna hajia ta kira Umma gefe, cikin tausasa harshe taimata dukkan bayani akan auren Jiddah da Alhaji Garba da Abba ya sanar musu. Take hankalin Umma ya tashe, tace wlhy Sam bazata aminceba, sai dai a wannan karonkam su rabu dashi.
Murmishi Inna Hajia tayi tana jinjina kai, kafin ta nisa cikin dattako tace, “Uhm-uhm Yagana karmu soma haka dake, wannan baikai abinda za'a tashi hankaliba, ALLAH dai shine maiyi, sannan komai da kowa a hannunsa yake, karnaji karna gani ance daga 6angarenki matsala take, kibarshi yayi yanda yaso da d'iyarsa, ALLAH dai maijine kuma Mai ganine, sannan yana tare da masu hak'uri”.
“Hakane Inna, amma ita yarinyar lamarinta za'a duba, wlhy koshi kansa Alhaji ya girmesa, manyanfa y'ay'ane dashi zagada-zagada, dan ko autansa saidai suyi sa'anni da Jiddar, amma dan zalunci irina zakari shine zai had'ata aure dashi? Lallai yanzu nakuma aminta da baya k'aunar yarannan da gaske........”
“Koma dai Miye yagana nidai nace kiyi hak'uri ki saka masa ido, itako mucigaba da Mata addu'a, kokun koma karnaji wani tashin hankali tsakaninki dashi”.
“Shikenan Inna”. ‘Umma tafad'a wasu hawaye masu rad'ad'i Na kwararo mata’.
Washe Gari haka suka baro barno ranta a 6ace, su Jiddah duksun damu da halin da sukaga ta shiga daga daren jiya zuwa yau, amma sunyi tambayar duniya tace babu komai.
Haka dai suka iso kano.
Tamkar Jira Abba yake dama da dawowar tasu saigashi a gidan bayan magriba, aunty Zulai da aunty Nafisa duk suna gidan, Maman Sadiq ce kawai suka wuce gida itada yaranta.
Babu wani 6oye-6oye ko lallashi cikin gadara ya sanarma Umma zancen Auren Alhaji Garba da Jiddah, harma da jadada mata zancen kawo kud'i da zaiyi gobe idan ALLAH ya kaimu.
Uffan batace dashiba harya k'araci hargowarsa ya fice.
Yayida tuni tashin hankali ya dabaibaye su Aunty Nafisa wad'anda Jiddah ta sume musu saboda abinda sukaji daga bakin Abba.
Wannan dare dai yazo musu cikeda k'unci da damuwa.
Washe gari Aunty Nafisa takoma gidanta cikin damuwa da tausayin Y'ar uwar tasu.
Itama aunty zulai kwanata hud'u tak'ara ta koma gidan mijinta.
Gaba d'aya gidan Umma ya canja daga yanda kuka sanshi, babu wani farin ciki ko walwala tartare da ahalin gidan a yanzu, komai ya canja musu, kwata-kwata Jiddah tabar zuwa makaranta saboda damuwa.
Tuni Alhaji garba yakawo kud'i, Wanda Uncle yahaya yayta zabga masifa akan hakan. amma sai Abba ya yayyanka masa magana wadda tai masifar 6ata ransa ya janye hannunsa daga maganar Auren Jiddah.
Kwata-kwata sati hud'u aka saka bikin, koma tunanin Yaya batun karatunta baiyiba.
Su Zarah Kansu duksun fita hayyacinsu tamkar sune Jiddahn.
Ahaka aka cinye sati biyu, ana saura kwanaki 10 cif lefe ya iso, saboda Abba yabama Umma haushi saiyasa y'an kawo lefe suka Kai gidansa da Hindu ke ciki, Aunty Nafisa da Maman Sadiq ne kawai sukaje, sauran kam duk k'awayen hajia Hindu ne. Sai shak'iyanci sukeyi wai tsoho ya iya had'o kayan lefe.
Sosai lefen kam aka kashe kud'i dan komai yaji d'am, kaikace na saurayi d'an shekara 26 ne😑.............✍🏻
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
*_Zaku iya samun RAINA KAMA a audio ta wancan link d'in Na sama, Abban dausayi YouTube channel tv😄🤝🏻._*
Yau babu magana🤫🤐
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[12.....]_*
..............Malam Mustafa yadamu kwarai da rashin ganin Jiddah a makaranta, dan da wahala kaga tayi fashi, inhar kuwa tayi washe gari sai kaga k'annenta sunzo sun fad'i dalili, kokuma idan itace tazo tafad'i abinda ya hanata zuwa.
Madina ma ta damu da rashin zuwan Jiddah, gashi ko gidansu bata saniba, dan duk iyakar shakuwarsu k'awancen iya makaranta ya tsaya, sai a yaumane takejin takaicin hakan.
Da aka tashi Malam mustafa yaso zuwa gidansu Jiddah, amma sai wani uziri ya rik'eshi, dole ya hak'ura akan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.
Saikuma da yamma malam yay kiranshi a waya akan yazo yana nemansa.
Bai samu ganin malam ba sai bayan sallar isha'i, dan ya iskeshi yana da bak'i. Bayan tafiyarsu yasamu gaisawa da malam.
“Mustafa dama akan yarinyarnanne, inaso asamo mana inda mahaifinta yake, dan inason ganawa dashi kafin musan abinyi”.
“To malam, insha ALLAH zuwa gobe zanzo na sanar maka”.
“To ALLAH ya kaimu da rai”.
Washe garima malam mustafa bai samu zuwa wajen Jiddah ba, sai dai binciko Alhaji Zakari dayayi, gidansa da wajen kasuwancinsa.
Duk yanda akai malam mustafa yazo ya sanarma malam.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah dukta fige a tsaye, da kaganta kasan tana tare da damuwa, Umma takan danne tata damuwar tayita lallashinta da nuna Mata muhimmancin yadda da k'addara Mai k'yau ko sa6anin hakan, tareda tunatar da ita amfanin biyayya ga iyaye.
Da wannan shawawar warin ne Na Umma take d'an rage nauyin damuwarta, har yau take d'an ta6a aikin gyaran gidan saboda su Zarah suna makaranta.
Gaba d'aya bikin saura kwana shidda ne ya rage, amma bazaka ta6a cewa za'ayi wani biki bane agidan, dama Abba yace Umma karta sai komai, dan Alhaji Garba yace amarya kawai yake buk'ata, komai ya tanadar mata.
Wannan dalilinne yakuma saka Umma banzatar da zancen auren, tacigaba da yima d'iyarta addu'ar nema za6in ALLAH.
★★★★★
Biki ya rage saura kwana hud'u dangin Umma suka fara isowa, hakama su Aunty Sauda da aunty Zulai, kowa dai kagani babu wani d'okin auren a tattare dashi. Kowa dandai babu yanda zaiyine da lamarin Abba kawai.
✨✨✨✨✨✨.
Yayinda shirin biki keta kankama a gidan su Jiddah ga malam Abdul-ra'uff kam shirin zuwa Neman auren Jiddah suke ga Alhaji Zakari. Alhmdllhi sun sami isowa yana gida bisa jagorancin malam Mustafa.
Dukda Alhaji Zakari baisan mike tafe dasuba yaymusu tarba ta mutuntawa saboda ganin manyan malamai a gabansa, dukda gefen zuciyarsa Na zargin Jiddah ce takai k'ararsa garesu, shiko ya k'udiri aniyar mutuwar Jiddah ce kawai zata Hana ya aura mata Alhaji Garba. Amma duk saiya danne wannan zancen zucin nasa ya fuskanci su malam.
A nutse malam Salis yayma Abba bayanin abinda ke tafe dasu.
Abba dake masifa a zuciyarsa hace, “Ahaf zargina yazama gaskiya, to lallai dagaku har ita zanyi maganinku ne”.
Kwantar da murya yayi a fili tamkar mutumin kwarai yafara magana, “ALLAH sarki malam gaskiya banji dad'in zuwan wannan magana Mai dad'i a k'uarraren lokaciba, dan abin farin cikine ga kowanne Uba yahad'a jini da malam, danasan da wannan kudiri naku daban amshi za6in Jiddah ba, yanzu haka maganar danake muku ranar asabar d'innance d'aurin aurenta wlhy”.
Gaba d'aya jikinsu malam yayi sanyi, amma babu yanda suka iya, dan Neman aure akan nema bashida kyau, balle wannanma da aski yazo Gaban goshi.
Sallama sukaima Abba suka tafi, saidai gefen zuciyar malam mustafa bata aminta da maganar Abba ba. Shima Abban kuma ya tsargu da kallon da malam mustafa ke masa.
Dan haka suna tafiya yanufi gidan Umma, kiran Jiddah yay ya Kora Mata gargad'i akan wlhy idan wani malami a makarantarsu ya aiko koda kiranta taje saiya matuk'ar 6ata ranta sosai.
Da to ta amsa, takoma cikin gida tana hawaye. Umma kallo d'aya taimata ta d'auke kanta, bakuma ta tambayeta miya faruba.
Ana saura kwana biyu hajia Hindu ta maido lefen Jiddah gidan Umma, duk da ta kwashi abinda take so aciki babu Wanda ya gane sai aunty Nafisa da maman Sadiq da sukaga lefen. Amma koda sukai magana sai Umma tace subar zancen, ita ta sani, inma dai dai tayi inma sa6anin hakan kanta taimawa.
Aranar y'an Adamawa suka Iso, hakama y'an Barno, tuni gidan ya kacame da yaren Fulatanci da Hausa da kanuri, dolema sai kusan rabuwa akayi, dan gidan yamusu kad'an, wasu suna gidan Uncle yahaya wasu gidan Umma.
Gaba d'aya Uncle yahya ya kauda idonsa akan bikin dukda takaicin auren da tausayin Jiddah Na damunsa ainun.
Wannan biki dai ana yinsane kawai, amarya ma da k'yar tayarda akai mata k'unshi da kitso, gyaran jiki kam komai akace xa'ayi saita saka musu kuka tace bataso.
Tausayinta ke sakasu barinta. Duk wani shagali irinsu kamu babu Wanda akayi, dama ita bawasu k'awayene da itaba, y'an uwanta sune k'awayrnta da Ummanta.
Ranar d'aurin aure gida yagama d'inkewa tab, Amarya kam nacan karshen d'aki kudundune babu lafiya itadasu walida, kowanne zazza6i yamasa rijib, ko wanka basuyiba balle ai batun kwalliya.
Karfe 12 aka d'aura auren Alhaji Garba da Hauwa'u Jiddah akan sadaki naira dubu d'ari biyu.
Abin mamaki saiga Malam Abdul-ra'uff dasu malam mustafa sunzo d'aurin auren suma, saboda koba komai dai d'alibarsu ce, wadda sukeji da ita da alfahari da ita.
Tunda zancen d'aurin auren ya shigo cikin gida jikin Jiddah yakuma rikicewa, dole aka fita da ita zuwa asibiti.
Amma Kiri da muzu Abba yace wlhy ko suma take yau saita kwana gidan mijinta, shi yagaji da wannan iskancin.
Umma duk tana jinsa amma uffan bata ceba, dan itama tunda aka fara hidimar bikinnan cikin ciwon k'irji take, dannewa kawai take tana daurewa.
A asibiti sai da Jiddah tasha ledar ruwa uku, barcin data samune yasaka sauran y'an uwanta zabga tagumi sukai jigum-jigum, kowa shikad'ai yasan minene damuwarsa.
Anayin Sallar magriba Abba yazo asibitin yace a sallami Jiddah, dukda bayani da likita kemasa nason abarta tasami hutu yace Sam yanzunan yakeso, dan gidan miji za'a kaita.
Badan likita yasoba aka basu sallama suka dawo gida akahauma Jiddah shiri.
Koda akazo batun yimata fad'a Umma ficewartama tayi daga d'akin tana hawaye, amma bata bari kowa ya gantaba.
Dangi dai sun tofa albarkacin bakinsu nayima Jiddah nasiha akan abokiyar xamanta da mijinta harma da y'ay'ansa da danginsa.
Tuni Jiddah tabar kuka masu hawaye sai dai kukan zuci, a haka aka fiddota wajen motocin d'aukar amarya da akalla sunkai 25, dan haka kowa yasamu waje aka shilla da amarya.
Y'an anguwa wasu Na sambarka wasu Na tausayin Jiddah.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*Gidan Alhaji Garba mai tabarma* babban gidane sosai Wanda kallo d'aya zakai masa ka tabbatar da maishi ya tara.
Bayan an wangale musu k'aton gate d'in gidan kusan motoci goma suka sami wajen shigewa ciki harda ta amarya.
Tarba suka samu mai k'yau daga dangin Alhaji Garba, wad'anda suketa fatan ALLAH yasa wannan karon an dace Jiddah tazo kenan.
6angaren Jiddah aka kaita, Wanda ya k'awatu da kayan alatu tamkar suyi magana, komai yaji zam, duk had'uwar gidan Alhaji Garba da dukiyar cikinta hakan baisa dangin Jiddah jin zasu tayata murnaba.
Basu wani jimaba suka juya, akabar Jiddah ita kad'ai kudundune cikin hijjabi daboda zazza6i Mai tsanani daya sake rufeta.
Kusan mintuna ashirin da tafiyar y'an kawo amarya Jiddah tafara jin hayaniya sama-sama, abinda ya dameta shine matsalarta, dan haka bata damu kanta dasonjin mike faruwaba. Zuwa wani lokacima sai taji gidan tsitt tamkar babu kowa a cikinsa.
Tun tana sauraren k'arar AC har barci 6arawo ya saceta a haka, dama Allurar bata gama sakintaba.
*Ango*
Kusan k'arfe sha biyu da rabi ango yashigo gidan, lokacin gidan yay tsit kowa yakama gabansa, Daga y'ay'ansa sai matarsa hajiya deluwa.
Fakin motar yay yafito hannunsa d'auke da k'atuwar leda, Kai tsaye sashen Uwargida ya nufa Wanda yafi kowanne sashe girma a gidan.
Tsit babu motsin kowa sai AC da TV daketa faman aiki, ko ina tsaf tamkar ba taron biki akayiba, koda yake yasan babu wani Wanda ya Isa taka mata sashe da sunan zuwa biki. Ledar hannunsa ya ajiye yanufi corridor d'in dazai sadashi da d'akunan barcinta.
Na farko yafara lek'awa babu kowa, Na biyu ma haka, sai a Na uku ya hangota zaune a saman gado, hamshak'iyar macece wadda ta amsa sunanta Hajia, daka ganta kasan tagama jik'uwa cikin nera, ta girma sosai sanan tanada k'iba dai-dai gwargwado, dan bawata k'atuwa baceba can, Ammafa babu k'arya Y'ar gayuce, dan ko shirin barcin Nata kad'ai ya Isa tabbaatar maka hakan, gata Fara tas masha ALLAH.
Manyan idanunta ta sauke akansa, kafin tasaki wani murmushi cikin kissa tafara fad'in “Kaga ango Mijin Amarya Hauwa'u”.
'Dan Murmushin yak'e Alhaji garba yayi, ya zauna kusa da ita k'asan zuciyarsa Na mamakin canjawarta akan wannan auren nasa, Ada inhar zaiyi aure zata d'aga hankalinta, randama aka kawo amarya bata Barin kowa yayi barci Mai dad'i a gidan, amma tunda yafara maganar auren Jiddah ko kad'an bata ta6a nuna damuwartaba, hasalima lefen Jiddah itace ta had'oshi matsayin gudun mawarta.
Fuskarsa d'auke da murmushi yad'an shafa kumatunta.
“Uwargida ran gida!”.
Fari tayi masa da fararen idanunta, kafin ta furta “Fad'I kanka tsaye alhajina”.
Yad'an dara, “Kinyi k'yau gimbiya ta, sai nakejima tamkar ked'in aka kawomin a yau”.
Wani shegen murmushi ta Saki, “Alhajina rufamin asiri, kaga tashi katafi wajen matarka, kar zumud'in son ganinta yasaka juyemin kalaman daka tanada dominta anan wajen”.
“Haba gimbiyata, aike kin wuce aimiki jirwaye da zancen wani, duk abinda yafito zuciyar Abubakar a kanki to lallai nakine, babu Mai kamanceceniya dake balle kamoki”.
Murmushi takuma Saki tana kamo hannunsa ta sumbaci tsakkiya, kafin yagama dai-daita da shiga sak'on Nata ta haye saman gadon sosai taja bargo da fad'in ”Ango mukwana lafiya, kadai bimusu yarinya a hankali karkai mata irinna hajarah, nasanka yanzu haka kaje ka d'irko magunguna”.
Wata Y'ar dariyar mugunta yasaki yana mik'ewa, “Hajjaju akwaiki da tsokana wlhy, ni sharri kikemin babu wani magani danake sha, Na barki lafiya”.
Cikin watsama bayansa harara da murmushin mugunta tace “A gaida amarya”.
Fita yay yana fad'in “zataji”.
Daga nan sashensa ya nufa Wanda shima ya had'u, sai dai baikai girman Na hajiya deluwa ba ko kad'an, had'uwa kawai zai iya nuna masa.
Sai faman zabga murmushi yake yana cire kaya. Wanka ya shiga kusan mintuna talatin sannan ya fito, ya saka jallabiya bayan ya goge jikinsa, yakawo turare ya fesa. Ledar daya shigo da ita ya bud'e yaciro wata karamar leda aciki, saida ya bud'e firij ya Ciro gorar ruwa sanan yakoma bakin gado ya zauna yana zazzage abinda ke ledar saman gadon, magungunane masu d'an yawa, ya 6alli kusan kala shida ya shanye yana zabga murmushi, sai shafar gemunsa dayasha aski yakeyi, tashi ya kumayi ya d'auki wata gorar da aka had'a tsumin magungunan gargajiya a ciki nanma yasha sosai sanan ya d'auki babbar ledar ya fito zuwa sashen amarya Jiddah.
Lokacin daya shigo sashen Jiddah tsit nanma, dan ita koma TV babu a kashe komai yake, sai k'amshi irin wanda akasan d'akin amarya dashi.
Bakinsa har k'arshen kunne ya Isa bedroom d'in Jiddah, sai wani lasar la66a yake tamkar tsohon maye😏😣............✍🏻
Kuyi manage please, yau banajin typing🤒
Yau dai nasan Naga idi😑🥺⛹♀
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[13....]_*
..............Tunda ya shigo idonsa nakan Jiddah k'yam, duk da a kudundune take da hijjab hakan bai hanashi jin wani farin cikiba, haryay tuntu6e da gado kad'an yarage ya fad'i, yadai samu ya dafa gadon.😂😝
Ledar hannunsa ya ajiye saman dirowan gefen gadon kafin ya zauna a bakin gadon shima yana fad'in “Amarsu ta ango mai dad'in tuwo! Nidai abud'e fuska indai bakine nasayi abuna dubu d'ari kash”.
Jin Jiddah tayi shiru bata amsaba yakai hannu ya janye hijjabin, wani hucin zafine ya bigesa, yayinda sanyin AC kuma ya shigi Jiddah tahau kankame jikinta. 'Dan canjawa fuskarsa tayi, yace, “K Jiddah tashi”..
Jiddah dake jinsa sama-sama tad'an bud'e idonta kad'an ta kalleshi, saikuma ta maida ta lumshe tare da k'ok'arin jan hijjabinta daya janye......
Tsawa ya daka mata, wadda tasata mik'e babu shiri, dama Jiddah akwai d'an banzan tsoro, dan haka jikinta keta k'yarma tana hawaye da karanto duk addu'ar datazo bakinta.
'Dan sassauta fushinsa yayi ganin ta rud'e, ya kwantar da murya yana fad'in “Bakida lafiyane?”.
Kai ta d'aga masa alamar eh.
Shiru yay yana kallonta, danshifa gaskiya bazai iya hak'uri ba, yanda yay savise d'innan ace yatashi a banza ai akwai babbar matsala. Gyaran murya yad'anyi yakai hannu zai Kama nata, amma sai tayi saurin janyewa, yad'an murmusa da ta6e baki, “Kinga da safe likita idan yazo dubaki zai had'a yabaki magani, dan nikamdai yau babu fashi saina more sadakina. Maza tashi kicire kaya, koda yake kefa malamace yo alwala mufara salla”.
Kan Jiddah a k'asa ga hawaye na zirara da Uban tsoro fal ranta tamkar zuciyarta zata faso k'irji ta fito.
Harara ya zabga Mata, kafin yay Mata magana ad'an tsawace. Ai babu shiri ta rikito daga gadon, dukta rikice tarasa ina zata dosa, wannan yasaka dukkan illahirin jikinta motsawa saboda babu hijjab, sanye take da riga da zani nawani yadi ruwan goro, kayan sunmata d'as a jiki, dan dai-dai gwargwado ALLAH yayma Jiddah cikakken jiki da sura, danma damuwa da ta sakata ramewane yanzu.
Gaba d'aya sai jikin Alhaji Garba Yakama rawar jaraba, sai faman lasar la66a yake saboda yakai makurar buk'atarta, maganin daya loda sha yanzu magani yanzu ne, sune karfinsa ga mace, inbabusu babu uwar dazai iya daboda shekaru sunja garesa sosai, dak'yar ya iya Mata nuni da hanyar band'aki dake cikin d'akin, ta shiga.
Bata damuba da kallon band'akin, fitsarin da dama ya matseta tun d'azun shita samu ta tsugunna yi cikin kwamin wankan dake bayin. Wata muguwar fad'uwa gabanta yayi lokaci d'aya, ta waro idanu waje tanabin jan abun da ke gudu cikin kwamin Wanda da alama jinine.
A fili ta furta “Jini! Kuma?, ni Jiddah mike faruwa dani haka?”. Ido takuma sakawa sosai dan sake tabbatarwa, lallai da gaske jinine wannan, to amma ai yau kwananta uku kacal dagama period, ina kuma tasamo jini..........”
Bata ankaraba kawai taji maganar mutum a kanta. Alhaji garba daya gaji da jiran fitowarta ya biyota, harya shigo bata saniba, shima bin jinin yay da kallo kafin ya furta “K minene hakan?”.
A rikice ta juyo tana kallonsa, in banda iskanci mizaisa ya biyota band'aki, saurin mik'ewa tayi tana sakin zaninta, dukda jinin dake bin k'afafunta bata damuba. Shiko ya k'urama jinin data zubar ido, sosai ransa yakai matuk'ar 6aci, dan wannan jinin ko kad'an bai masa adalciba, batareda ya tanka mataba yafita fuuuu. Da kallo tabisa harya 6acema ganinta sannan ta lumshe idanu tana sauke ajiyar zuciya. Bata kawo komai a rantaba tahau gyaran jikinta, dan ita duk zatonta ko jinintane kemata wasa, sai dai yanda yake zuba da yawa yabata mamaki. Tsaf ta gyara jikinta da wajen sannan ta fito, dan komai da mace zata iya buk'ata akwaishi a bayin, ganinma an ajiye always da fants abin har mamaki ya bata, saikace ansan da zuwan jinin Nata.
Koda ta fito babu Alhaji babu dalilinsa, bata wani damuba tayi kwanciyarta bayan ta canja zaninta kawai, amma rigar da d'an Kwali duk da abinta ta kwanta. Taja bargo ta lullu6e saboda sanyin ac ya addabeta, itakuma batasan yanda ake kashewaba, har kanta ta saka a bargo. Sai dai yanzu takasa barci sa6anin d'azun, tunanin y'an uwarta da kewarsu tadawoma zugiyarta sabuwa, tuni tafara zirar da hawaye. Ta dad'e tana kuka, dan harkusan karfe uku kafin barci 6arawo ya saceta bayan tasamu tayi addu'a da k'yar.
★★★★★★
Alhaii Garba dai daga k'arshe sai wajen Hajia deluwa Yakoma ya sauke kayan wahalarsa, inda Sam tak'i saurarensa daga farko, dak'yar ya iya shawo kanta bayan sunyi cinikin zai bata dubu d'ari biyar. Atake kuwa yaymata transper d'insu dan hakan shine k'a'idarta Dama, saitaji dumus a hannu ko a asusun banki ( wannan bawai sabon Abu baneba).
Aiko ranar tagane kuranta, dan saida takoma yimasa kuka rurus sannan ya hak'ura ya barta badan yasamu yanda yakeso ba, a zuciyarsa kam sai kuma tsinema jinin Jiddah yakeyi, dayanzu yanacan yana morewarsa, sai sanda yaso barinta, amma ita wannan ta ishesa da shegen raki badan yagama nutsuwaba. (😆😝⛹♀)
*Wanene Alhaji garba?*
Alhaji Garba Mai tabarba kowa ya sanshi dashi, haifaffen cikin birnin kano kuma girman nan, sana'ar tabarma dayakeyi tun yana matashi shine sunan ya bishi, Wanda sanadin tabarmar ALLAH yay masa arzik'in da harya bud'e kamfanin da akeyinta, ahankali arzik'insa yacigaba da bunk'asa.
Matarsa ta farko (ladan noma) itace Yahanasu, wadda tun tana k'arama ake kiranta da suna Deluwa, tuni sunan yagama binta harma an manta da yahanasu gaba d'aya.
Yaransu bakwai da ita, maza hud'u Mata uku. Y'ay'ansa Mata biyu sunyi aure shekara d'aya kenan, mazan kam babban ne yahuza kawai yayi, amma sauran ukun duk sunanan suna ruwan ido, iyayansu kuma babu maicewa basu k'yautaba, duk d'insu sunyi katunema a k'asashen k'etare, yanzu haka autarsu Zaliha wadda zasuyi sa'anni da Jiddah tana Niger karatu.
Tun zamanin kuruciya akaima hajia deluwa shaidar batason zama da kishiya, Dan Alhaji Garba yayi aure-aure bayan ita amma babu mai rufa shekara biyu take barin gidan saboda masifar hajia uwargidansa. Sannan koda ciki kika samu to dawuya ki haifeshi, kodai kiyi 6arinsa kokuwa ma ki haifeshi babu rai, mace d'ayace tahaihu dashi bayan hajia deluwa, yaran yana shekara d'aya da haihuwa ya rasu Alhaji Garba kuma ya saketa.
Dangin Alhaji Garba basu isa su ra6eshiba, wannan yasaka duk sanda zai sake aure cikin d'oki suke, saidai auren baya wani Kai labari.
Hajara itace mace ta k'arshe daya sake aure, wadda a k'alla takai shekara uku a gidan, kowa yafara murna da fad'in Hajarah ta gagari Hajia deluwa sai kwatsam ranar ya dank'ara mata Saki. Tundaga nan kuma bai sake zancen aureba kusan shekara hud'u kenan, yay hak'urin cigaban zama da matarsa wadda tun zamanin kuruciya bata yarda yay kwanciyar aure da ita saiya biya, (wanna daliline yake sakashi yawan aure-aure, harga abin Na binsa har tsufa) ahaka ALLAH ya albarkacesu da haihuwar y'ay'anan bakwai.
Kwatsam ranar sai yaga Jiddah kusan shekara biyu data wuce, to amma kuma yarasa ta inda zai tunkari Alhaji Zakari yaro da zancen, dan shima yasan ba kanwar lasa bane, sannan yasan mafi yawa daga sirrkan gidansa, abokinsane shekaru masu yawa wadda sanadin kasuwanci suka kulle, saidai Alhaji Garba yafi Alhaji Zakari kud'i nesa ba kusaba, dan ko a kwatancema bazasu had'uba. To rana tsaka kuma saiga Alhaji Zakari yazoma Alhaji Garba da buk'ata, wadda itace sanadin daya samu damar sako zancen Jiddah a tsakkiyar hark'allarsu. Shiko Abba domin biyan buk'atarsa saiya amince, yakuma dage saboda Neman biyan buk'atarsa.
Sosai Hajia Hindu ke k'awance da Hajia Deluwa tuni.
★★★★★
Sai k'arfe kusan takwas ALLAH yabama Jiddah ikon tashi, dan barcin dabata samu tayiba shiya janyo mata doguwar makara, da addu'a d'auke a bakinta ta farka, idanunta duk sunmata nauyi luhu-luhu saboda kuka, hakama kanta jingim take jinsa, dak'yar ta iya sakkowa a gadon tanufi bayi tana hawayen kewar ahalinta da bak'incikin wannan auren.
Wani mugun mamakine ya kamata sosai dankuwa k'amas babu ko d'igon jini a jikin always d'in data saka, hakama jikinta normal yake, to kodai jiya ta iske jinin a wajen ne itakuma ta tsugunna? To amma kuma ai tagansa har a jikinta ajiyan kuma? Kai wannan lamari da mamaki, itadai dukma takasa fassara lamarin, dan haka tahad'a ruwa Mai d'umi tayi wanka, irin wad'annan ta6e-ta6en kayan y'an gayun dukta iyasu gidan aunty Nafisa, shiyyasa anan basu zame mata sabon abuba, itadai wankan tsarki tayi saboda kore kokwanton ko jinintane yaymata wasa, koda ta fito saita rama sallarta kamar yanda shai'a tabamu damaryi.
Koda ta idar saman gadon ta koma ta sake kwanciya tana cigaba da kukanta, har kusan k'arfe d'aya bataji motsin kowaba a gidan, ga yunwa tafara addabarta dan batasan iya lokacin data d'aukaba rabonda taci abinci mai nauyi. Da k'yar yanzuma tatashi tayi salla, bayan ta idar ne tasamu zarafin bud'e ledar da Alhaji yashigo da ita jiya, dan itadai har jiri-jiri take gani.
“Alhmdllh” tafad'a saboda ganin kaji dasu ice-creem da sauran kayan kwad'ayi irinsu chocolate mai dad'i dawasu kalolin biscuits dadai tarkacen kayan kwad'ayi. Kazar kawai ta d'auka taci kusan rabi, saida taji tafara zufar k'oshi sannan ta mik'e taje ta wanko hannunta da bakinta.
Handbag d'in datazo da ita gidan ta bud'e tazaro Qur'ani madaidaici a girma tazauna tafara karatu cikin suratul Bak'ara da muryarnan tata mai saka zukata nutsuwa. Har aka kira sallar la'asar tana karatunta, saida taji za'a shiga salla sannan tayi addu'ar ta mik'e ta gabatar da salla.
Yanzu dai ta daure ta gyara bedroom d'in musamman ma gadon. Amma koda wasa batayi tunanin lek'a koda falonba, tana gamawa takoma ta zauna tana tunanin su Ummanta ko misukeyi yanzu oho. Hawaye taji suna kwararo Mata, jin kanta zai Fara ciwo saita maida akalar tunaninta zuwa yin Azkar Na yamma.
★★★★★
Ango Alhaji Garba kam fitace ta gaggawa ta sameshi tunda sassafe, dan haka yafita batareda ya lek'o Jiddah ba, har dare kuma bai dawoba.
Hajia deluwa kam dak'yar yau ta iya tashi tana tsinema Alhaji garba a zuciyarta, tareda zubama likitocin da sukawo maganin dayakesha ALLAH ya isa fiyeda cikin buhu, tasamu nasarar aikinta amma wuyar tadawo kanta....
Tana cikin wanna tunanin Kira ya shigo wayarta, kallon wayar tayi a yatsine, amma ganin Mai kiran saita d'auka har jikinta Na 6ari.
“Malam lafiya dai kuwa?”.
Daga can malam na barewa yace, “Dadai sauk'i, amma hajia haka mukayi dake? banace idan an daceba ki kirani tun a daren nasan abunyi? Kinsanfa wannan yarinyar nafad'a miki tanada tsari sosai a jikinta, dan bata wasa da addu'a ko kad'an, wannanma munsami damartane saboda taimakon batada lafiya”.
“Malam kayi hak'uri dan ALLAH, wlhy anyi nasara, nima wahalar daya maido kaina wadda yayma amaryar shiri shine yahanani sukuni, yanzudai zance maka an dace, dan jiya a sashina yadawo ya kwana yana masifa, Dana tambayesa kuma ya sanarmin komai akan jini takeyi wai”.
”Ni dama nasan za'a dace, ammafa aikin tun a daren jiyama ya warware, dan tanayin addu'ar barci aljanin yakasa matsarta, hasalima kasa zaman gidan yayi gaba d'aya saida ya dawomin, ayanzu danake miki magana lafiyarta lau, hasalima babu sallar dabatayiba a yau”.
Sosai hankalin Hajiya Deluwa ya tashi, jikinta Na rawa tace, “Malam yanzu minene mafita?”.
“Mafita kam a yanzu dai babu ita daga gareni, dan saina sake sabon shiri akanta da Neman lagonta, ammafa gaskiya komai zai iya faruwa tsakaninta da mijinki, dan naga hakan a istaharar danayi”.
Rud'ewa sosai hajia deluwa tayi, bata kuma sauraren malam ba ta yanke wayar tana zagaye-zagayen Neman mafita. ta nufi k'ofa yafi sau biyar da nufin tafiya sashen Jiddah saikuma zuciyarta ta gargad'eta ta dawo baya, daga k'arshe dai Kira ta kwalawa bilki Mai aikinta.
Bilki tazo da sauri tana fad'in “hajia gani”.
Kallonta Hajia deluwa tayi tana d'an Huci, “Balki kunbama amarya abincine?”.
“A'a Hajia ai baki bada Umarnin hakanba”.
“Jeki sashenta yanzunan ki kiramin ita”.
Da to bilki ta amsa tana mik'ewa zuwa sashen Jiddah.
A zaune ta isketa tazuba tagumi, sai dai ba tunani takeba Azkar takeyi.
Sallamar Bilki ta sakata d'agowa ta kalleta. Bilki tad'an risina ta gaidata, amsawa Jiddah tayi cikin Y'ar fara'ar yak'e. Bilki tace, “Amarya kizo hajia Na kiranki”.
Ba k'aramin fad'uwa gaban Jiddah yayiba, ta had'iye wasu yawu masu kauri kafin ta d'agama bilki Kai da k'yar.
Fita Bilki tayi domin ta jirata a falo.
Gaba d'aya Jiddah ta rikice a tsorace take, jikinta sai rawa yake ta d'auki hijjab d'inta ta tasaka ta fito, a falo ta iske bilki, dan haka taimata jagora zuwa 6angaren hajiya deluwa.....
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Malam kam ganin burinsa Na farko bai cikaba saiya yanke shawarar aurama malam Aliyu Maimunatu, dan haka babu 6ata lokaci yadsamu Iya habi da maganar.
Shiru tad'anyi tana nazarinsa, kafin zuwa can ta sauke nannauyan numfashi “Malam bank'i wannan had'inba, amma kana ganin Aliyu ya warke daga lalurarsa?”.
Murmushi kawai malam yay yad'an girgiza kansa da mamakin furucinta, “Habiba kenan, wannan shine matsalarki kenan? to gaskiya bamuda tabbas akan hakan, sai dai munada yak'ini da addu'ar samun nasara, duba da yanda yay amfani da magunguna da dama akan lalurar domain Neman waraka”.
“To ALLAH ya datar damu, aishi lamari na aure ba'ai masa shishshigi, Zan Kira Sani muyi magana (kaninta Baban mamuna)”.
Malam yace, “To shiken sainaji daga gareku, dan inason ayi auren kusa, daya dawo da sati biyu, tunda yanzu saura sati biyu ya dawo, kinga nanda wata d'aya kenan”.
“Hakane, insha ALLAH zakaji”.
Bayan kwanaki uku dayin wannan magana iya Habi taima malam maganar sukai kud'i ga mahaifin maimunatun, danshi yayi farinciki kwarai da gaske da wannan had'in.
Sosai malam yayi murna, dan haka babu 6ata lokaci akayi komai aka gama. Koda malam ya sanarma Aliyu cayay ALLAH yasa haka shiyafi alkairi kawai. Dama malam baya hangen matsala daga gareshi, saboda yasan biyayyar Aliyu akan mahaifa.
Kwana goma dayin wannan magana Aliyu ya dawo, d'alibansa da malam sunyi matuk'ar farinciki da dawowarsa dakuma nasarar daya samo.
Kwana biyu da dawowarsa y'an uwansa sukazo yimasa sannu da zuwa, aunty Ruk'ayya da Siyama.
Yana k'aunar y'an uwansa haka suma suna k'aunarsa, hira sosai ta 6arke a tsakaninsu har akazo kan maganar aurensa da Maimunatu, a yanda ya lura duk basuso had'inba, dan haka yashiga kwantar da hankalinsu cikin nasiha da nuna musu muhimmancin yin k'ysk'yk'yawan zato ga musulmi. Hakan ne yad'an saka kwanciyar hankali agaresu, har suka fara jefa kalmar fatan alkairi ga auren nasa, dan koba komai suma sungaji da zamansa haka, kowa yana girmamashi matsayin babban mutum amma kuma bashida cikon rigar kamala Na aure, idan har yay auren koyaya mutuncinsa da k'imarsa zasu kuma bayyana ga jama'a.
Duk abinda yadace su tsara Na al'ada Wanda baishiga hurumin addiniba sun tsarashi aranar, tareda had'a k'arfi da k'arfe wajen burin fita kunya, dukda auren gidane bazai hana ai kananun maganaba idan sun gaza.
A 6angaren malam ma sunata k'ok'arin gyara gidan Aliyu, Wanda tunbayan rabuwar aurensa da Asma'u ya saida wancan gidan ya cika yasai fili, yana Saudia yayta aiko da kud'i a hankali aka gine filin da madaidaicin gida Wanda akai masallaci Mai d'an girma a jikinsa da islamiyya Mai ajujuwa da bazasu gaza shida ba. Iya gwargwado gidan yayi k'yau, sannan duk Wanda yagani yasan ba tsarin zaman mace d'aya baneba, kusan komai angama sai abinda ba'a rasaba, dan haka a yanzu malam ya tsaida malam mustafa akan k'ok'arin kammala komai.
Ahaka aka shiga hidimar biki, ango kuwa kosau d'aya bai ta6a ke6ewa da amarya ba da sunan zance, yace ai gidansa zata, minene abin 6ata lokaci a waje.
Shagali biki yafara gudana tamkar yanda Shari'a ta tanadar, babuwani hayaniyar shed'anci Mara amfani, ranar juma'a bayan sakkowa masallaci aka d'aura auren Aliyu da Maimunatu acan gidansu dake anguwar d'orayi. Taron d'aurin aurene daya samu halattar mutane daban-daban a sassan Nageria, burin kowa ya nuna halacci ga Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff Maina, Alhmdllh anyi cikin nasara an k'are lafiya, bayan d'aurin aure aka gudanar da gagarumar walima wadda malamai suka zazzaga wa'azi akan aure da rayuwar ma'aurata, tareda jan doguwar Addu'a ga wad'annan ma'aurata.
Amarya Maimunatu tana cikin farin cikin mallakar cikar burinta, yayinda ango baka gane nasa yanayin.
Bayan kammala walima aka mik'a amarya d'akinta tareda fatan alkairin ALLAH yasa bad'i adawo suna...............✍🏻
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
_Zaku iya samun RAINA KAMA a audio ta wanann link d'in Na sama, Abban Dausayi YouTube channel tv😄🤝🏻_
*_Bazan 6oye mukuba jiya bak'aramar dariya naci akan Comments nakuba gaskiya, lallai nalura kund'auki aurennan da zafi, Abba zakari da Alhaji garba sun zagu babu k'arya🤣🤣, ALLAH ya taimakeni ba a had'a daniba nima😂⛹♀._*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[16➖17]_*
..............Hannunsa daya kai zai rik'e k'ofar Jiddah ta had'a ta datse, take yasaki wata azababbiyar k'ara, yayinda zufa tafara keta dukkan sassan jikinsa.
Jiki Na rawa Jiddah tasaki k'ofar kafin ta lek'oshi, ganin ya zube k'asan kafet yana sakin wahalallen kuka da yarfe hannu sai hankalinta yay matuk'ar tashi, kamar zata fito saikuma taji tsoro takoma da baya da sauri ta rufo k'ofar....
Hakan yayi dai-dai da shigowar Hajia deluwa da gudu, wadda tundaga sashenta tajiyo ihun Ashir.
“Mami ta kasheni, ta tsinkemin yatsu mami..”
Abinda Ashir keta fad'a kenan yana birgima a k'asa da mik'ama hajia deluwa hannunsa.
Hannun nasa takama ta rik'e jiki Na rawa da fad'in “Ashir! Kai Ashir mitaimaka?”.
“Hannuna ta had'a da k'ofa mami! Mami kikaini Asibiti Karna mutu”.
Gaba d'aya hajiya deluwa tarud'e, da Sauri tafita tana kwala kiran direbansu, da taimakonsa suka fiddo Ashir daga sashen Jiddah zuwa harabar gidan.
Sosai hankalin Jiddah itama yake a tashe, sai faman tsiyayar da hawaye takeyi, jin fitar mota yasata bud'e k'ofarta, tasan kila suntafi asibitin, jinin daduk Ashir ya d'igar takebi da kallo wasu hawayen tausayinsa masu zafi sunabin kumatunta, data sani dabata guduba da waje ta fita, “Amma dakin tsaya ai zai tozartakine” wani gefe Na zuciyarta ya fad'a.
Zubewa tayi saman kafet d'in wajen tana kuma sakin marayan kuka da godiya ga ubangijin daya jarabceta da wannan rayuwa....
Ahaka Alhaji Garba ya shigo ya sameta, daganima sashenta yafara shigowa, dan rik'e yake da babbar rigarsa dawasu tarkace a hannu.
“Jiddah lafiya kuwa?”. Ya fad'a yana ajiye kayan hannunsa a kujerar dake kusa da ita.
A tsorace ta d'ago ta kallesa tana girgiza masa kanta, “Alhaji wlhy ba laifina baneba, bada gangan nayi masa hakaba ka yarda Dani...”
“Ban gane maganar da kike ba Jiddah? Mike faruwa? Jinin menene wanan?........
“Alhaji wlhy Ashir ne ya......”
“Yayi Ubanmi munafuka?”.
Maganar Hajia deluwa ta katse Jiddah, gaba d'aya suka maida kallonsu gareta. K'arasowa tai tana cigaba da fad'in “Wai Alhaji munafukar yarinyarnan dan kawai Ashir yazo gaisheta shine ta had'e hannunsa da k'ofa ta murje”.
“Ta murje kuma? Ke Jiddah akanmi?”.
“Akan mugunta mana da mugun hali”. ‘Hajia deluwa takatse Jiddah dake yink'urin yin bayani’.
Duk yanda Alhaji garba yaso jin ainahin zancen hajia deluwa ta hana hakan, dan Kiri da muzu tahana Jiddah yin bayani. Daga k'arshe sai fita sukayi zuwa sashensa akabar Jiddah Na hawaye. Acan hajia deluwa ta shiryama Alhaji garba karyar datakeso saida taga ya aminta sannan tabaro sashensa.
Tana dawowa sashenta malam Na marwa takira, a k'ufule tace, “Malam bazan iyaba, maza kasan yanda zakai da yarinyarnan wlhy, ni dama tuni Hindu ta tsoratani akan uwarsu datace ta nacema Ubansu dukda wulak'antatan da yakeyi, koma miye yazo kanka ka aikata Mata tabarmin gidana, yanzu haka harta gwada nakasamin yaro tunkan aje ko inama kenan”.........
“Kinga kwantar da hankalinki hajia, yinin yau gaba d'aya a aikinki nake, dama kobaki kiraniba ni Zan kiraki, gobe idan ALLAH ya kaimu ki aiko a kar6ar miki sak'o”.
Cike da d'oki Hajia deluwa tace, “Nagode sosai malam, harka saka zuciyata tayi Fari wlhy”.
Dariya yayi shima daga can.
Ashir dai ya bugu kam, dan hardasu karaya a yatsunsa biyu Na tsakkiya, farce d'aya ya fita gaba d'aya. bayan an d'orashi aka nad'e hannun da bandeji aka bashi magunguna da sallama.
Tunda suka shigo gidan yake Harar sashen Jiddah yana kunkuni, kai tsaye sashen hajia deluwa driver ya rakashi.
Sai wani sannu da tarairayarsa takeyi, “Sannu kaji Ashir, amma dai yarinyarnan muguwace wlhy, muna ganinta salaf-salaf kamar bazata iyaba”.
“Wlhy mami bazan hak'uraba saina rama, haka kawai kinsakani aikata Abu naje a banza an nakasani, to ayanzu naratse miki saina aikata Na gaske a kanta, naje da nufin Mata barazana tamin haka, to ta shirya Na gaskiyar kuwa w........”
”Kai wai bakada hankali Ashir! Ba Matar Ubanka baceba, banason halin dabbancifa”.
“To amma mami ai duk kece kikaja ko, dabaki turani mata barazanarba tayaya hakan zata faru? Ni koma kallo da zata ishenine? ALLAH kinji Na rantse saina fatattaka yatinyarnan kuma a cikin gidannan saidai dad ya koreni bayan nayi”.
Dafe kai hajia deluwa tayi, dama tasan Ashir akwai bak'ar zuciyar tsiya, duk maganar da take masa bai sauraretaba yafice fuuuu zuwa sashensu.
Jiddah kam bayan taci kukanta ta more tashitai ta koma d'aki abinta.
Bata sakejin motsin kowaba Na gidan har ta kwanta, sai a cikin barcine tad'anji motsi a d'akin, idonta ta bud'e kad'an saitaga Alhaji zaune yana latsa lap-top.
A tsorace ta tashi zaune, yad'an kalleta yana wani had'e fuska.
“Dama kin kwantar da hankalinki kin kwanta abinki, ni idanma mace Na jini a tsarina ko ta6ata banayi balle tunanin ra6arta”.
Badan Jiddah ta yardaba tazame ta kwanta, saidai dukta takura takasa barci, har kusan karfe d'aya taga yazo gefenta ya kwanta tareda juya mata baya, tun tana fargaba harta farajin saukar numfashinsa cikin gurnani.
A hankali ta sakko k'asa ta kwanta itama barci 6arawo yayta fusgarta har yay galaba a kanta.
*_Bayan kwanaki hud'u_*
Jiddah dukta kuma figewa saboda tunanin su Umma da fargabar halin datake ciki, bata sake had'uwa da Ashir ba balle hajia deluwa, Alhaji Garba kam yakan shigo mata da safe, da daddare kuma anan yake kwana, amma zai raba dare yana latse-latse a laptop, tarasa ubanda yakeyi, zamansa a d'akin yake sakata barci rabi da rabi saboda tsoro, shiyyasa dasafe saitaita zabga barci, ALLAH dai ya taimaketa yau yagama kwana bakwai ya koma wajen uwargidansa itama tasami sukuni.
Da wannan barcin hajia deluwa tasamu damar shigowa sashenta ta saka wani Abu a k'ark'ashin gadon Jiddah tun a randa tacika kwana uku a gidan.
Jiddah dai batasan mike faruwaba, yau bayan tayi sallar azahar tad'an fito falonta ta zauna, gaba d'aya batajin kwarin jikinta, saboda tunda tazo gidan bataci abinciba, kullum sai kayan kwad'ayin da Alhaji garba ya kawo Mata na sayen baki, a kullum kuma Alhaji garba Na tambayarta Ana kawo mata abinci? Itakuma saitace eh kawai. Bai ta6a sanin ba'a kawowaba shidai, dan itama hajia deluwa daya tambayeta haka takecewa ankai Mata. da wannan ya d'auke hankalinsa bai saka idoba. Yau kuma gashi a lissafi sashenta zai kwana, duk fargaba ta isheta
Sallamar Alhaji garba tajiyo cikin nishad'i, dan muryarsa a matuk'ar sake, tasan farin cikin nasa baya rasa nasaba da rutsata tana sallar walha d'azun, dan sai kusan 9 ya fita daga gida yau, yashigo mata sallama ne ya isketa tana sallah, tun sannan yaringa farinciki da tambayarta Ashe tasamu tsarki? Itadai kasama bashi amsa tayi a d'azun......
Tunanintane ya katse jin yace, “hummmmmm!” Yana toshe hanci. Da mamaki ta kallesa, ganin zai juya da sauri tace, “Alhaji sannu da dawowa”.
Hannu kawai ya d'aga Mata ya fice da sassarfa. Yana fita ya sauke numfashi da fad'in “Kai wannan wane irin warine a sashen yarinyarnan?”. Babu Mai bashi amsa dan haka yay gaba zuwa sashen hajia deluwa.
★★★★★
Wasa-wasa dai sashen Jiddah ya gagari Alhaji garba harma da Ashir dake fakon Jiddah yay ramuwar gayya.
Ita kuma Jiddah haka kawai takejin wani masifar tsoron maza, ko maganar namiji taji a TV saita rikice, cikin kwana uku kuma saiya koma ma tana tsorata da ganinsu koda a TV ne, dan dama ananne kawai take ganin nasu, tunda ba fita take konan da canba.
Tashin hankali Na biyu abinda take samu taci komai ya k'are, yauma duk a jigace ta wuni saboda yunwa, sallama ta magrib sai a zaune tayita saboda rashin karfin jiki, babu abinda take d'urama kanta sai ruwa.
Zuwa washe gari ko ruwa tasha sai amai, saboda babu komai a cikinta, ga wani Uban jiri dake d'ibarta.
Cikin ikon ALLAH saiga bilki mai aikin hajia tazo kawo Mata waya inji Alhaji, dan yakai kararta wajen Abba shine abban yace ya had'asu, shikuma bazai iya zuwa sashenba shiyyasa ya aiko bilki.
Ganin halin da jiddah take ciki sai hankalinta ya tashi, dan jiddah da k'yar ta iya fad'a mata yunwa takeji, da hanzari ta ajiye wayar takoma sashen hajia deluwa a sace ta had'o tea da abinci takawo sashen Jiddah. Itace ta taimaka Mata tad'ansha tea d'in cikinta ya warware, sannan tabata abincin shima kad'an taci saboda cikinta ya cinkushe, tanama gamaci sai amai.
Sosai bilki taji tausayinta, itace ta taimaka Mata ta gyara jikinta sannan ta gyara wajen, koda Abba ya Kira sai bilki ta d'aga a matsayin Jiddah, yagama bambaminsa harya yanke wayar bilki dake mamaki da al'ajabi bata tankaba, aiko ko fad'a ma Jiddah yanda akayi batayiba. Tadai koma sashen Alhaji tace masa Jiddah batada lafiya.
“ALLAH yabata lafiya”. Yafad'a a k'ufule yana amsar wayarsa.
Tundaga ranar sai bilki takoma kaiwa jiddah abinci a sace, dukda Jiddah nasamun abinci sai ciwo ya zame Mata jinya, kullum tana a kwance babu lafiya, ciwon baya da k'irji ga wani tsoron maza dake kuma shigarta babu gaira babu sabar.
A haka tacika sati uku a gidan, ranardai Alhaji garba yakasa hak'uri, dan haka ya aika bilki da yamma dayake yadawo da wuri saboda juma'ace ta kirawo masa Jiddah.
Tunda Jiddah taji Mai kiranta saita birkice tahau kuka da rokon bilki taje tace tayi barci.
Bilki tace, “Hajia karama dan ALLAH kizo muje Karna rasa aikina”.
Jin wannan furici Na bilki ya saka jiddah Binta, dan bata fatan bilki ta rasa aikinta ta sanadinta. Sai dai kumafa suna yin ido biyu da Alhaji garba jikinta ya Kama rawa tafara kuka da Neman kofar fita, da sauri yazo ya rufe kofar yana matsota cikin toshe hanci, yayi alkawarin yau ba wariba kominene saiya more dubu d'ari biyunsa Na sadaki.
Yana kai hannu zai ta6a jiddah ta kwala Kara da lalumar filawa dake kusa dashi ta kwala masa akai.
Take anan ya zube a sume, jiddah kuma tayi waje da gudu tana kuka.
A k'ofa sukaci Karo da hajia deluwa zata shigo, ram ta rike jiddah tana tambayarta miya faru? Ina jiddah takasa magana, jikinta sai kuma 6ari yakeyi saboda hango Ashir da Bala dake nufosu saboda jin kururuwar jiddah.
Da k'arfi ta hankad'a hajiya ta nufi fita da gudu, Ashir da bala sukai tara-tarana kamata, Bala Na rik'e hannunta shima ta hankad'eshi da karfin tsiya yafad'i kasa da fasashshen kai ta fice a guje saboda Mai gadi da Ashir da direba da suma ke tara-taran kamata.
Haka jiddah taita gudu, mahaukaciya zam a titi, babu inda take dosa sai hanyar gida kuma, saikace wadda ake control da remote. Mutane da yawa sunyi yinkurin kamata abu ya gagara saboda mazane.
A gidan Alhaji garba kam tashin hankali biyu, Alhaji da bala duk sun sume, hakanne yasa Ashir kiran y'an sanda ya sanar musu su Kama jiddah, yayinda mai gadi da driver ke kokarin saka su Alhaji mota za'a kaisu asibiti.
Hajia deluwa kuwa sai shar6ar majina take tana kuka da tsinema jiddah, ita bazata yardaba inhar mijinta da d'anta suka rasa ransu wlhy saita kashe jiddah itama, shi bala daga dawowarsa kwana biyu kenan Jiddah ta kashe matashi. Haka taita sambatu har sukaje asibiti dasu.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨.
Su Zarah na zaune a tsakar gida kowa nad'an wiki cikin rashin kuzari, dan tunda Jiddah tabar gidan dukkan farin cikin gidan ya gushe, Ga Umma kuma ta hanasu zuwa gidan Jiddah su ganta kwata-kwata, sai Maman Sadiq ce da aunty Nafisa suka shirya zuwa gobe su dubota, shiyyasa Umma tace Subari idan sunje sunga hankalinta kwance suma saisuje.
Da gudu Jiddah ta shigo musu, dan haka suma duk sai suka kwasa da gudu zuwa cikin d'aki, amma k'arar da jiddah ta kwala tana zubewa a k'asa yasakasu lekowa a rikice, ganin jiddarsu ce duksai suka yo waje hankali a tashe, gaba d'aya kanta sukai suna kiran sunanta, amma ina fisge-fisge kawai take tana kwalla gigitattar k'ara......
A haka Uncle yahya yashigo a rikice shima, dan tuni sama'ila Mai shago dasukaga shigowar jiddah anguwar Ana shirin sallar magriba sukaje suka kirashi.
Yana kai hannu zai ta6a Jiddah takuma sakin wata k'arar datafi ta farko.
Kowa saiya kuma birkicewa, ga kofar gida yacika da y'an anguwa, kowa yana tambayar miya sami Jiddah?. Isowar motar y'an sandane yasa kallo komawa Kansu, kutsawa sukai zuwa cikin gida babu ko tsayawa Neman iso.
Babbar magana, y'an sanda dai sunga abinfa yawuce tunaninsu, dan shigowarsma saita kuma kid'ima Jiddah tacigaba da sakin wani ihu Mai fita da gurnani maiban tsoro, sai wata irin fisga takeyi nason guduwa daga rikon da sukai Mata........
Tashin hankali ba'a saka maka rana😿, wayyo jiddah.😣
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A 6angaren Aliyu kam Maimunatu na samun tsarki a ranar yay shirin gwajin lafiyarsa cike da fargaba.
Da farkoma shareta yay kusan kwana goma da samun tsakinta, saida yau yaji yakasa jurewa saboda sha'awar kasancewa da mace yakeji ainun. Dan haka yaymata shiri Na musamman irinna masu ililin da sukasan sirrin yanda ya kamata a tunkari mace, musamman ma budurwa.
Cike da tsoro yayta driving Nata akan abinda yakamata tayi kafin akai ga kwanciya, sunyi salla da tambayoyi dayay Mata akan addini Wanda baisamu Matsala da itaba sai kad'an-kad'an.
Daganan kuma sukai shirin barci.
A farkon Fari da fargaba yake sarrafata, da lamura sukai nisa kuma sai komai ya tafi dai-dai fiyema da yanda yay zato.
A ranar yasamu nasarar Fara bin hanyar cikar burinsa, dan baiyarda yazo Mata kaitsayeba.
Haka yayta Binta a hankali har tsawon kwanaki hud'u kafin yayi Mai gaba d'aya.
Maimuna dai kam tazama Aliyu, Aliyu kuma yazama maimuna. Saidai muce ALLAH yabada zaman lafiya Na har Abadan.
A kwanakin da suka biyo baya sosai yake Nuna Mata kulawa Mai cike da martaba ta, dukda tasan baya sonta bài ta6a Nuna mataba koda a fukane kuwa.
Saima mamaki da yake bata yanda ya iya sarrafa mace a zaman takewa Na yau da kullum da shinfid'arsu. Abin ba'a cewa komai sai sambarka.
Tuni kaunarsa takuma mamaye jini da ruhinta, suk hanyar dazata k'yautata masa ita takebi.
A haka sheikh Aliyu yafara gudanar da al'amuran addini a anguwar, masallacinsa da makarantarsa suka Fara aiki, da dare maza magidanta ke d'aukar karatu, wataran kuma ya gudanar da tafseer.
Da safe kuma matan aure, da yamma yara da y'ammata.
Kafin kacemi makaranta tafara cikewa, dan kowa yaji babban malami sheikh Aliyu maina ne, to baya sanya saiya kawo iyalansa dashi kansa.
Angwanci yayi matuk'ar kar6ar Aliyu, danya murje yayi wani 6ul-6ul dashi, sai wani k'yalli da cikar kamala yake k'arawa.
Kullum yaje gaida malam kuwa saiya tsokanesa akan mirjewar da yayi, hakama malam mustafa.
A yanzukam bashida wata Matsala, komai yana tafiya masa dai-dai saidai abinda ba'a rasaba Na kalubalen rayuwa Wanda ba'a taba raba Bawa dashi musamman ma irinsu dake d'auke da nauyin al'umma.............✍🏻
https://youtu.be/eOU-ju4f6KY
*_Zaku iya sauraren RAINA KAMA a audio ta wannan link d'in Na sama, Abban dausayi YouTube channel tv😄👍🏻_*
*_Humm yau dai nasan ba sauk'i a wajen fans🤭⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀⛹♀🥰🥰🥰😂_*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[14➖15]_*
..............Sosai Jiddah ke yaba k'yawun tsarin sashen hajia deluwa, dan bak'aramin kud'i aka narkaba gaskiya, gabanta ya fad'i saboda hango Hajia deluwa dake hamshak'e cikin kujera, taci kwalliya cikin wani ubansun leshi ruwan ganye, ga wani kamshi Mai kwantar da hankali datake zabgawa.
Tunda Jiddah ta shigo itama Hajia deluwa kemata kallon k'asan ido daga k'asa har sama, sosai Jiddah taimata k'yau fiye da yanda hajia Hindu ta nuna Mata ita a hoto, dukda a yanzu cikin hijjab take kuwa.
Gabanta Jiddah taje ta zauna a k'asa, cike da girmamawa muryarta a matuk'ar sanyaye tace, “Hajia ina yini”.
Cike da yatsina hajia deluwa ta amsa da “lafiya amarya ya kwanan amarci?”.
Shiru Jiddah tayi takasa amsawa, yayinda hajia deluwa keta wani ta6e baki tana gyara zamanta, cikin dakewar murya tace, “To amarya inason muyi magana ta fahimta dake, dan banason biyo miki ta hanyar da zaki gaza 6illewa, da farko dai kisani ina matuk'ar son mijina da dukiyarsa, babukuma wata danake k'aunar tazo ta haihu dashi bayan nawa y'ay'an, kullum burina dagani sai y'ay'ana mu mallaki komansa, a girme Na girmi Mamanki ma balle ke nasani, Alhaji kam inda su Yahuza auren wuri sukayi sun Isa Haifa masa kamarki matsayin jika, inason nabaki shawarar kibar gidannan tunda arzik'inki, Zan baki ko nawa kikeso domin kibarmin mijina, dan tabbas nasan dukiyarsa tasaki aurensa, dan Ku y'an matan yanzu duk inda naira take kuna a nanik'e, abinda yasa duk nake miki wannan jawabin cikin lalama saboda nakula kamar zakiyi hankali, sannan kece mafi k'ank'anta a matan da Alhaji yata6a aura adukkan aure-aurensa. Kifita kisamu saurayi dai-daike ki aure, inma baida kud'in aurenki Zan iya masa komai, ke nama tak'aita miki zance koda cikin su Ashir kikeso ki za6a (yayanta fa🙆🏻).
Duk wannan maganganu da Hajia deluwa keyi kan Jiddah Na k'asa tana mamaki da al'ajabinta, gaba d'aya takasa fahimtar inda surutanta suka dosa, wannan wace irin macece?........
Kafin Jiddah tasamu zarafin amsawa sallamar matashin saurayi dazai iya kaiwa shekaru 29 ta karad'e falon.
Cikeda washe hakora Hajia Deluwa ta amsa masa tana fad'in “Wai ina kashigene haka Ashir?”.
Idonsa akan Jiddah yace, “Mami wlhy ina d'aki kwance abuna, wannanfa?”. ‘Yak'are maganar yana lasar la66a da nuna Jiddah’.
Baki hajia deluwa tad'an ta6e, ”Amaryar gidance”.
Sosai Ashir ya zaro ido waje yana kuma lek'a fuskar Jiddah, “wai mami dama wannan karon karamar kaza Dad ya d'akko mana? Kai dad yana yarfamu wlhy, inma auren zaiyi ya d'akko wadda kowa yagani zai yaba mana”.
Harara Hajia deluwa ta watsa masa, amma batace komaiba.
Jiddah kam gabanta saikuma fad'uwa yake, ga maganganun Ashir na sukar zuciyarta amma batako motsaba.........
“Kinga tashi ki tafi, kije kiyi nazari akan maganata”. Maganar Hajia deluwa ta katsema Jiddah tunani.
Dak'yar ta iya mik'ewa ta fice jikinta Na rawa, yayinda Ashir kebinta da kallo tamkar tsohon maye..
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Ango Ali baisamu damar shiga gidan nasaba sai wajen sha d'aya, Malam Mustafa ne ya kaishi har gida, batare daya shigaba ya juya yana tsokanarsa wai asha angwanci lafiya.
Murmushi kawai yay bai iya bama malam mustafa amsaba, danshi ba mutumne Mai yawan maganaba inhar baisoba, idan kuma yaso zakaji yanayi sosai mussaman ma idan tashafi addini.
Cikin sanyin nan nasa tamkar mara laka a jiki ya k'arasa cikin gidan, a hankali ya furta “Masha ALLAH” akan la66ansa saboda k'yawun da falon yayi, komai yayi cikin tsari dai-dai gwargwado, bai zaunaba ya nufi bedroom d'in Maimunatu.
Cikin sassanyar muryarsa yay cikakkiyar sallama.
Maimunatu dake kwance tad'ago idanu tana kallonsa da amsa sallamarsa akan la66a, sanye yake cikin wani lallausan yadi kalar madara, sai hularsa kube ruwan makuba dad'an ratsin kalar madarar, jikinsa Na fidda wani sassanyan kamshi maisaka zuciya nutsuwa.
Shikam kallo d'aya yaymata ya janye idonsa tareda ajiye ledar hannunsa saman madubi sannan ya zauna a bakin gadon d'an nesa da ita. Tashi tayi zaune tana fad'in “Yaya Aliyu ina yini”.
A sanyaye yace, “Lafiya lau Maimunatu, ya gajiyar hidima?”.
Murmushi tayi kawai amma bata iya bashi amsaba sai wasa da gefen gyalenta da takeyi.
Kuma kallonta yad'anyi kafin yakuma d'auke idonsa, “Ga abinci nan nasan kina buk'atarsa, danku Mata idan kuna hidima nakula bakuda lokacin cikinku”.
Murmushi tayi idonta akan bakinsa dake motsawa a hankali tamkar bashi ke maganarba....
Jin tayi shiru saiya juyo ya kalleta, saurin janye idonta tayi akansa ta amsa da “to, nagode”.
Karan farko daya d'an murmusa, ya mik'e yana fad'in “Bara nad'an watsa ruwa, kafin Na dawo kici abinci kiyi alwala...”. Kafin tabashi amsa tuni ya fice.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, tajawo ledar daya ajiye ta bud'e, gasashshen namane sai kayan fruits da abinda ba'a rasaba. Bata wani kwari kantaba taci abinta tayi nak sannan taje tayo brosh tadawo ta zauna.
Kusan mintuna Arba'in saiga malam Aliyu ya dawo, sanye yake da kananun kaya wando dogo fari da riga t-shirt ruwan hanta, abinda tunda maimuna take bata ta6a gani daga gareshiba kenan, saka kananun kaya, gaba d'aya ta shagala da kallonsa saboda wani mugun k'yau dayay Mata, Yakuma komawa yaro d'anye sharaf, a ranta tana ayyana dama yana saka k'ananun kaya haka?......
Malam Aliyu da yaga ta shagala da kallonsa ne yay murmushi yana zama kusa da ita gab tareda kai yatsansa tamkar zai tsokale Mata ido.
Da sauri ta sauke ajiyar zuciya tana rufe fuskarta saboda taji kunya sosai.
Murmushi yad'anyi, yana cewa, “Na canja mikine?”.
“Sosaima”. ‘Ta fad'a har yanzu Idonta a rufe’.
“Humm dama can kallon tsoro kikemin shiyyasa kike ganin Na canja yanzu. Ina fata kinyi Alwalan?”.
Batare data bud'e fuskartaba tace, “Nifa Yaya ina up”.
Baice komaiba sai d'auke kai dayay daga dubanta yana d'an sauke numfashi, kusan mintuna biyu yana mulmula maganar dazai mata a ransa kafin ya gyara zama yakuma fuskantarta.
“Yaushe yazo?”.
Tamkar zata nutse dan kunya haka taji, gyalenta taja takuma rufe fuskarta sosai kafin ta iya bashi amsa, “Yau”.
“Babu k'yau k'arya, yau kwannansa biyu, nanda kwana hud'u zaki samu tsarki”.
Babu shiri ta bud'e fuskarta tana ware idonta a kansa, “Yaya ya akai kasani?”. ‘maganar ta su6uce Mata batare da ta saniba’.
Jikinsa kawai ya jawota batareda ya bata amsaba, cikin kunnenta ya rad'a Mata “Kinason sani?”.
Gaba d'aya kunya ta rufeta, ga jikinta sai tsuma yake saboda jinta a jikinsa, shikansa hakance ke faruwa daga gareshi, amma ya daure kamar bayajin komai.
Kusan mintuna biyu suna a haka kafin ya d'agota zaune sosai. “Tashi muyi magana”.
Gyara zamanta tayi, taja gyalenta takuma rufe fuskarta sosai.
“Maimunatu da farko dai nasan kinada ilimin addini dana zamani, kinkai shekarun da zaki iya banbance dai-dai da sa6anin haka, inaso kisaka a ranki zamuyi tsaftataccen zaman aure tamkar yanda Manzon ALLAH (s.a.w) ya koyar damu, insha ALLAH Zan sauke dukkan hak'k'ok'inki a kaina iya iyawata, kema ina fatan hakan daga gareki. Nasan tunkan ki shigo gidana kinsan inada lalura wadda itace sanadin rabuwata da matata ta farko, to kisanifa har yanzu banida tabbacin samun waraka, sai dai muna fatan dacewa, wannan kuma saikin samu tsarikine zamu tabbatar, idan babu wani canji game da lafiyata to lallai bazan cutar dakeba Zan sallameki insha ALLAH, idan kuma an dace Alhmdllh, zaki zama Aliyu, Aliyu zai zama ke, mallakar Aliyu gaba d'ayansa kuma saikin zama jaruma wajen fahimtar abinda yakeso da Wanda bayaso. Nabaki satar amsa”. ‘ya k'are maganar da yaye gyalen data lulllu6a’.
Saurin kife kanta tayi a cinyarsa saboda kunya, yayinda shikuma yay murmushi.
😂ta gidan Sheikh Ali ina tayaki murna🤭⛹♀.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A gidan Umma kam bayan biki da kwanaki uku kowa ya Kama gabansa, aka barsu su kad'ai, daga ita harsu Walida babu Mai isashshiyar lafiya, kowa damuwa da tausayin Jiddah da kewarsa ta isheshi.
Washe Gari dole Uncle yahaya yanemo likita yazo har gida ya sakama Umma k'arin ruwa saboda batajin dadi sosai.
Bayan la'asar Zarah ta cire Mata saboda ya k'are, ruwa Mai d'umi suka had'a Mata tai wanka, suna tsaka da gyaran gidan saiga Abba.
Kowacce kai a k'asa ta gaidashi.
Bakinsa ya ta6e ya wuce d'akin Umma, dan ya lura yau su Zarah awani yanayin jin haushi suka gaidashi.
Umma na zaune tana cin faten waken da Maman Sadiq ta aiko Mata Abba ya shigo, kallo d'aya taimasa ta d'auke kanta.
Zama yay shima yana wani kumbura. Umma tace, “Ina yini”.
Bai amsaba, sai tambaya daya jefoma Umma.
“Yagana waike aurar da y'arne yasaki maida kanki haka? Lallai aiki ya sameki ashe”.
Wani murmushin takaici Umma tayi kafin ta d'ago ta kalleshi ido cikin ido, “Koma minene ya maidani haka wannan ba matsalarka baceba, saidai inason maka tambaya d'aya. Shin nawa Alhaji Garba yabaka kabashi Jiddah?”.
Gaban Abba ne ya fad'i, bakinsa Na rawa yace, “Yagana ban gane wannna maganar banzar takiba? Dan Zan bada auren y'ay'ana sai an biyani kud'i?”.
“Humm Alhaji kenan, bar ganin ka fini shekaru wlhy kar nake kallonka, a ina kasamu kud'in biyan banki bashin da kaci musu?”.
Harara ya watsa mata yana huci, “Shak'eni Na fad'a miki mana yagana?”.
“Aiba saina shak'eka bama, zaka fad'ane cikin kwanciyar hankali. Wlhy Alhaji ka farka daga nannauyan barcin daya d'aukeka, wato ka ciwo bashin kud'i a banki lokacin da suka baka Na kar6a yayi bakadashi ko? Saboda kakashe kud'in akan matarka da y'ay'an Sonka yanzu anema kabada kud'in ko kaddarorinka hankalinka ya tashi ko? Karasa ina zaka nufa matarka tabaka shawarar Neman bashi wajen Alhaji Garba. Shikuma dayake tsohon banzane kaje da buk'atar kud'i yabuk'aci musanyarsu da yarinyata saboda ta tsole idonsa, wlhy danasan auren manufa kayi da Jiddah ko sama da k'asa zata had'e baza'ayi aurennanba. Amma ko yan.............”
Wata razananniyar tsawa ya daka Mata yana mik'ewa a zabure, “Daga bakin wane mak'aryaci wannan zancen ya fito? Ko rantsuwa nayi babu kaffara nasan yahaya ne........”
“Kwarai kuwa nine?”. ‘Cewar Uncle yahya dayake shigowa yanzu’.
Daga Umma har Abba juyawa sukai suna kallonsa, fuskar Uncle yahya a matuk'ar d'aure yacigaba da fad'in “Wlhy ko'a mafarkina ban ta6a zaton rashin son gaskiyarka yakai hakaba Yaya, yanzu dan ALLAH har nawa Jiddah take da zakayi wannan kulla-kullar akanta? Ashe har mutane masu mutunci sukazo Neman aurenta amma ka shirya musu k'arya? Namaka magana ka gaggayamin son ranka, Anya Yaya kana tsoron gamuwarka da ubangiji kuwa?”.
“A'a bana tsoro dan Ubanka, shin komadai kaine Ubansu Jiddah ban saniba?”.
Daga Uncle yahya har Umma a tsorace suke kallon Abba.
Muryar Umma Na rawa alamar tahowar kuka tace, “Alhaji kana cikin hankalinka kuwa? Mu kake jifa da wad'annan munanan kalamin?”.
Shiru yay yakasa bata amsa saboda ya fahimci 6acin rai ya sakashi yin kato6ara.....
Uncle yahya yay murmushin takaici yana fad'in “Karki wani damu kanji da kalamansa Yagana, idan yamana sharri wannan yarage tsakaninsa da Ubangijinsa, dan shine zaimana hisabi, wannan kuma ni bazaisa naji komaiba saboda ban ta6a kwatanta aikatawaba koda a zuciya balle zahiri, ka saka a ranka kuma alhakin wad'annan bayin ALLAH kawai ya isheka ishara inhar baka rok'i gafararsu ba ka gyara mu'amularka dasu. Maman Nafisa ga magungunanki nan, ni nawuce gida”.
Uncle yahya nagama fad'a ya fice abinsa.
Umma ma tashi tai ta shige uwar d'aka abinta. Da sauri Abba ya bita.
Da sauri tace, “kaga fitarmin a d'aki zakari, idan kuma ni kake buk'atar nafita to lallai yanzu Zan barmaka gidanka tafiyarda har abada bazan dawoba koda hakan yana nufin Zan mutu da igiyar aurenka a kaina”.
Baki ya bud'e zaiyi magana tai saurin janyo hijjab d'inta “ALLAH ya baki hak'uri nizan fita”.
Bai jira amsartaba ya fice.
Duk abinda ke faruwa su walida naji, dan haka suka had'e kai a tsakar gida suna dirzar kuka.
Itama Umma yana fita tafad'a kan gado ta fashe da kuka maiban tausayi.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tunda Jiddah ta koma sashenta taketa juya maganar hajia deluwa a zuciyarta, da mamakin kalamun saurayi da hajia ta Kira da Ashir Wanda take kyautata zaton d'ansune kenan. Lallai ita taga takanta, mutanan gidan kowanne da nashi matsalar....
Motsin dataji a bayantane ya sakata saurin juyowa, gabanta yay mummunar fad'uwa saboda ganin Ashir. Murmushi ya sakar mata yana matsowa gab da ita, “Auntyn mu gaisuwar bangirma nazo kawowa”. Yay maganar yana d'aga Mata gira d'aya.
Baya Jiddah ta matsa sosai jikinta harya Fara tsumar tsoro, Ashir ya kuma kwantar da murya tamkar yana gaban matarsa ko budurwa yace, “Wani ya ta6a fad'a miki kinada k'yau kuwa babie? Da sabon jini kika dace babie ba dad ragowar basirba, kizo nabaki dukkan farin ciki dan nine dai-daike nasan dad babu abinda zai iya miki wlhy, shegen aure-aurensane kawai da basa k'arewa......”.
Duk maganarnan da Ashir yake jikin Jiddah 6ari kawai yake, dan tsaf tagama fahim manufar Ashir a kanta, babu abinda takeyi sai Addu'ar Neman tsarin ALLAH daga shed'ancinsa, yayinda tuni hawaye sun cika Mata idanu. Ganin Ashir yamatso zai kamata yasata afkawa d'aki a guje Ashir ya take Mata baya..............✍🏻
🙆🏻turk'ashi, Uban ko d'an?.
*_Ammafa kun iya buk'ulu, irin wannan addu'a da kuke jama Maimuna kar Sheikh Ali ya angwance_*🤣🤣🤭
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
0 comments:
Post a Comment