*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[18➖19]_*
..............Duk yanda akaso nutsuwar Jiddah abin ya gagara, sai da y'an sanda suka kira Uncle yahaya waje dansuyi magana sai akaga Jiddah ta lafa daga fisge-fisge da k'arar da takeyi. Hakanne yasaka Umma dake kuka son fahimtar wani Abu, amma batace komaiba tajigaba da tofama Jiddah Addu'a.
Bayan kamar mintuna goma Uncle yahaya ya dawo, yana shigowa Jiddah ta tashi aguje zata bar wajen, rik'eta Zarah da walida sukayi da k'yar da taimakon Uncle yahaya suka kaita k'asa.
Cikin kuka Umma tace, “Uncle d'insu ka fahimci abinda Na fahimta kuwa akan yarinyarnan?”.
Kansa ya jinjina alamar eh, idonsa jajur shima saboda damuwa yace, “Maman Nafisa Jiddah batason maza su ra6i inda take, lallai akwai abinda ke faruwa dabamu saniba, dan dak'afa fa tazo gidannan tundaga can gidan. Kuma yanzu y'an sandarnan waifa anturosune su kamata saboda Alhaji garba da d'ansa suna asibiti sanadin kwala musu abu datayi. Amma halin da sukaganta a ciki yasakasu komawa”.
Daga Umma harsu walida kuka suka kuma fashewa dashi, Uncle yahya yace, “Ba kuka zamuyiba Maman Nafisa, bara naje nayi sallah nazo da malam Alfah”.
Da to suka amsa.
Uncle yahya yafice zuciyarsa cikeda tausayin Jiddah. Tunda ya fita sai Jiddah takuma samun nutsuwa, dan haka su Umma suka kamata zuwa d'aki saboda mutane makwafta dasuke shigowa jajanta abin, wasuko gulmace ta kawosu.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A asibiti kam da k'yar aka samu jinin dake zuba a kan Alhaji Garba ya tsaya, shiko bala sunama zuwa ya farfad'o, dan baiwani buguba sosai, allurar barci sukai masa danya samu Hutu.
Ran Hajia Deluwa da Ashir kam yakai k'ololuwar 6aci, musamman ma da y'an sandan sukazo suna Kora musu bayanin wai ai Jiddah ta haukace, suko tayaya zasu Kama Mara hankali. Tamkar Ashir ya makesu haka yaji, hajia deluwa kuwa datasan abinda ya faru komawa tai gefe takira malaminta tace ya warware asirin dayay ma Jiddah, amma yayi wani Abu akan Alhaji garba danya Saki Jiddah, tanason akama Jiddah aimata hukunci.
Da to kawai ya amsa mata, danshifa akwai abin tsoroma dayake hangowa gameda wannan abin da suka aikata, shiyyasama tunkan ta kirashi ya warware Na warin ja6a da jiddah keyi, saurama d'ayan.
Shima Alhaji garba wajen karfe tara aka samu ya farfad'o, alurar barci suka sake masa danya samu nutsuwa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Bayan an idar da sallar magriba Uncle yahya sukazo shida malam alfah, kallo d'aya yayma Jiddah yafahimci akwai sihiri a jikinta, dan indai daga ita saisu Umma ne zakajita luf, da namiji yashigo gidan zata hau ihu da fisge-fisge. Addu'oi yabada kafin safiya asan abinyi.
Tunda aka bata ruwan addu'ar sai barci ya kwasheta, bata kuma sanin inda kanta yakeba har asubahi. Yayinda su Umma suka kusan kwana a tsaye suna Kai kukansu ga ALLAH.
Washe gari Alhamdllh jikin nata, dan dakanta tai alwala tagabatar da salla.
Bayan ta idar ne Umma tabata Qur'an, babu musu ta amsa tana karatu, har wajen awa d'aya kafin ta ajiye tahau yin azkar. Duk wannan abun dake faruwa y'an uwanta na zagaye da ita, saida ta kammala sannan ta gaida Umma, su Zarah suka gaidata suma suna rungumeta danjin dad'in ganinta normal.
Babu Wanda yay Mata magana akan matsalarta, saima itace ke cewa “wai Umma ya akai nadawo gidane?”.
Murmushi Umma tayi tana Kama hannunta, murya a tausashe tace, “Uncle d'inkine ya d'akkoki Jiddah”.
Murmushi ta d'anyi amma batace komaiba. Ana cikin haka sukaji sallamar Uncle yahya, atake jikin Jiddah yafara rawa tashiga matsawa baya.
Uncle yahya yad'an murmushi kawai, cikin k'arfin hali yace, “Haba jiddodona ninefa, ko baki ganeniba?”.
“Na ganeka Uncle”. ‘tai maganar murya a raunane tana cigaba da matsawa’.
“Kinga yi hak'uri karkiyi kuka, amma fad'amin tsorona kikeji?”.
Fashewa tai da kuka jikinta Na kuma tsananta rawa, “Uncle kayi hak'uri, wlhy banason ganin maza ko muryarsu banason jiiiiii!!!!!!!”. ‘Ta k'are magar cikin razananniyar tsawar data gigitasu’.
Dole sai fita Uncle yahya yayi, yana fita kuma tafara dai-daita, a hankali saita dawo normal, jikin Zarah dake kusa da ita tafad'a tana kuka, suma su Zarah kukan sukeyi.
A waje Uncle yahya da Umma suna magana ne akan ya Kira Abba ya sanar masa halinda Jiddah take ciki amma yace wai k'arya takeyi, dan haka shikuma ya faffad'a masa magana akan wlhy koda zasuyi yak'i Jiddah bazata koma gidan Alhaji garba ba, dolene ya saketa koyanaso ko bayaso.
“Kamin dai-dai Uncle d'insu, wlhy a shirye nake da igiyar aurena ta tsinke akan komawar Jiddah gidancan, acikin sati uku kacal an maidata haka inaga nan gaba kuma?”.
“Ki kwantar da hankalinki Maman Nafisa, nima ina dai-dai dashi ai, dan yace gobe zai dawo daga legas d'in”.
“ALLAH ya kawoshi lafiya”. Cewar Umma a zafafe.
*_HARGITSI_*.
Dolene mukira wannan tsakani da suna hargitsi, dan kuwa komai ya rikice, ga jikin Jiddah da yak'i dad'i, dan koda maganar Abba daya dawo washe garin dawowarta gidan Alhaji Garba taji to zata fara fisge-fisge da k'ara.
Tsakanin Umma da Abba da Uncle yahya kuwa anyi barank'an-barank'an, dan Abba yaje ya duba Alhaji Garba a asibiti ya shirys masa k'arya da gaskiya akan Jiddah, yayinda hajia deluwa ke tunzurashi a gefe.
Umma da Uncle yahya sun dage sai Alhaji Garba ya saki Jiddah. Alhaji garba ya kafe akan wlhy bazai ta6a sakintaba. Abba ma yadage sai Jiddah ta koma, dan shima akwai nasa dalilin Mai tada hankaki.
Lamari yayi tsamari sosai, yau kusan kwanaki takwas da Fara badak'alar amma babu wani sassauci, hakanne ya saka Uncle yahya shigar da Alhaji Garba kotu domin raba auren Jiddah.
Alhaji Garba yasamu sauk'i harya koma gida, dan haka gidansa akakai masa sammaci.
Sosai hajia dealuwa ke zubar masa tijara akan ya Saki Jiddah mana, aiba girmansa bane ace yashiga kotu akan wannan banzan maganar.
A zafafe yace, “ke Yahanasu, nifa ba auren wannan yarinyar bane matsalata, kud'ina da Ubanta yaci sune matsalata, kinsan nawa ya amsa a wajena kuwa? To naira miliyan Hamsin, ya amsa yabiya banki bashin da yaci, bisaga wannan ne yabani aurenta akan zai biyani rabi nanda shekara biyu, nikuma nace Na hafe masa rabi, dan haka saiya biyani kud'ina Zan saketa”.
“Humm wlhy Alhaji ban ta6a sanin Kai mayen Mata baneba sai yau, akan mace ka d'auki wannan uwar dukiyar ka bashi? To bara Na fad'a maka, rashin sakin y'arsa ba shine mafitaba, dan dama can bason Y'ar yakeba, kobakaga damuwarsama ta dawoba a kullu? To ka saketa, nikuma Zan baka dabarar da zakayi kud'inka su fito cikin sauk'i a hannun Alhaji zakari yaro”.
Jimmm Alhaji Garba yay yana kallonta, saikuma ya gyara xamansa yana fad'in “kamar kuma Na yarda da shawararki, ke nama yarda, samomin takarda da alk'alami”.
Da hanzari hajia deluwa taje ta d'akko masa, dandanan ya zana Saki a takarda yabata yace tabama driver yakaima Alhaji Zakari.
*_SANADI_*
Wannan shine sanadin rabuwar Alhaji Garba da Jiddah.
Su Umma Na tsakar gida zazzaune, Zarah da Walida na wanke-wanke, Umma Na girki yayinda Jiddah ke kwance akan tabarma tayi shiru tana tunanin rayuwa da yanda al'amura suka sauya cikin wata biyu kacal. Sallamar Abba ce ta sanyata mik'ewa zumbur, da gudu ta afka d'aki tajecan karshen gini ta 6uya. Yanzu haka take, ko Uncle yahya ne ya shigo saita gudu ta 6uya, addu'oin da malam alfah ke bata tanasha yasa aka samu rangwame tabar yawan k'ara, amma idan Namiji yacika kusantota tana wannan fisge-fisgen harma ta suma.
Cikin hargowa Abba ya jefama Umma takardar sakin Jiddah yana fad'in “Hankalinki ya kwanta yagana, kin kashema Jiddah aure, saiki zuba ruwa a k'asa kisha kinji ko, itakuma daga yau dan Ubanta saita dainama mutane haukan k'arya, kuma wlhy kinji Na rantse Na zare hannuna daga duk wani lamarin Jiddah, ta nemi wani uban baniba d........”
Cikin katseshi Umma ta d'aga masa hannu ”Ya Isa haka Alhaji, dama baka a lamarinsu, dankuma ka fita yanzu bazanji komaiba, amma ina Mai tabbatar maka, ko watan watarana katina wannan maganar taka, sannan ka fad'ama Alhaji Garba, ina godiya matuk'a ni yagana akan sakarmin yarinya da yayi, kaikuma ka gane TUBALIN TOKA baya k'arko, duk abinda ba'a ginashi domin ALLAH ba to baya k'arko, abinda kuma akaima yarinyata nabar wannan ga ALLAH, shine zai Mata hisabi da koma wanene”.
Umma nagama fad'a tai shigewarta tabi Jiddah, sukam su Walida dama tuni sun shige ai, daga d'aki suke jiyo abinda ke faruwa.
Kwafa kawai Abba yay batareda ya iya cewa k'alaba, sai yanaji a ransa badan ALLAH ya Isar da mamansa taimasa akan yagana ba da wlhy yau itama Saki Uku zai Mata, to amma anriga an saka masa Kara da hakan.
Duk wani masoyin Jiddah ya tayata farin ciki da wannan Saki, washe Gari da aunty Nafisa tazo itakam harda rawarta tasha su Zarah na tayata, Jiddah da Umma sai dariya suke musu.
Tuni maganar sakin Jiddah ya karad'e dangi, kowa yaji dalili saiya tayata murna da hakan, tareda nemawa abba shiriya wajen ubangiji.
A yanzu matsalar Jiddah ta tsoron mazace kawai matsalarsu, dan har yanzu bata shan inuwa da koda sautin muryar mazane, iya kokari kuma ana maganin akan warware sihirin jikinta, amma lamarin ba'a cewa komai sai sambarka.
Abba dai ko sisinsa babu balle tambayar Yaya Jiddah hasalima yabar zuwa gidan gaba d'aya, shi a dole fushi yake, sannan ciwon Jiddah yace k'aryane. Kokad'an hakan baya damun Umma, dan a cewarta wannan matsalarsace.
Alhamdllh jikin jiddah yad'an murmure daga ramar da tayi, saidai kulum tana gida bata fita ko ina, zuciyarta nason komawa makaranta, amma tanajin tsoron yanda zata fiti taci Karo da abokan gabarta maza.
Ahankali kuma farin cikin gidansu ya dawo, sunkoma tamkar da, saima ka d'auka wani tashin hankali bai ta6a ziyartarsuba a kwanakin baya, yanzu fatansu kawai ALLAH yabama Jiddah lafiya ta koma normal.
*_A KWANA A TASHI_*
babu wahala wajen Ubangiji, yau ga Jiddah tagama iddah, har wani d'an walima su Zarah da aunty Nafisa suka shirya Na murnar Jiddah tarabu da alak'ak'ai.
Umma dai dariya kawai suke bata, Uncle yahya harda taya 6era 6ari kuwa shida maman Sadiq.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
“Mustafa yanzu ya kake ganin zamuyi akan maganar wadda zataje musabak'arnan ta Saudia tunda yanzu babu yarinyarnan? Kagafa wasu kwanakine kawai ya rage Wanda bazasu gaza ashirin da biyu ba, a ko yaushe kuma za'a iya buk'atar ganinta ma”.
“Wlhy malam nima abun Na damuna, shiyyasa nake kuma takaicin rashin Jiddah, amma yanzu inaga zamu samu wata d'alibar mukuma horata kawai”.
“Eh to shawararka tayi sosai, ALLAH yasa mu dace”.
Ameen Malam mustafa da Sheikh Aliyu dake zaune yana saurarensu suka fad'a.
Daga nan wani zancen suka d'akko, mafi yawa akan gudunmawar da Jiddah tabama makarantarne Na ciwo musabuk'ok'i kashi-kashi da tayi. Shidai Aliyu na zaune yana nazarin wani littafi yana saurarensu, amma k'ala bai tofa ba, dan ba huruminsa baneba. Sai dai k'ok'arin yarinyar ya burgeshi kamar yanda su malam suke fad'a dukda bai santaba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau Su Zarah duk suna makaranta, gashi Umma nason yin aike shago, Dauda kuma baikai ga zuwaba, rasa yanda zatayi tai, ta lek'a kozata samu yaro amma layin fetal yara duk suna makaranta. Dawowa tayi ta kalli Jiddah daketa hidimar d'aura abincin rana.
“Jiddah koda kanki zaki fita dai siyen yis d'innan, kinga nariga nafara kwa6a fulawar alkubus d'inan, ki lek'a konan shagon sama'ilane, idan kuma kingamu da wani yaron saiki bashi ya sayo”.
“To Umma kawo naje d'in”. ‘Jiddah tafad'a tana d'auraye hannunta data ta6a gawayi'. Tana gamawa ta kar6a naira d'arin hannun Umma taja hijjab a igiya ta fita bayan ta d'aura Nik'ab tamkar yanda ta Saba.
Dukda tsoron dake addabarta da tsumar da jikinta yafara haka ta k'arasa shagon sama'ila, da k'yar ta iya mik'a masa kud'in tana fad'a masa abinda takeso, lokacin daya mik'o mata hannunsa yad'an ta6a Nata kad'an sai kawai tai baya jiki Na rawa, bai ankaraba kawai yaga ta zuba da gudu tabarsa rik'e da yis.
Mamaki da al'ajab suka kamashi, dan haka yabiyota yana kwala Mata Kira, amma ina gudu take iya karfinta.
Umma Na gyara mata wutar sai kawai gani tai ta shigo a guje, tana tambayarta lafiya amma bata sauraretaba ta afka d'aki. Umma na shirin binta Sama'ila mai shago ya rabga sallama daga soro.
Wata razananninayar k'ara jiddah ta fasa tana toshe kunnenta. Tuni hankalin Umma ya tashi, dan ita tashagala Jiddah ta samu sauk'i sosai, dan tadad'e batai irin wannan firgitar mai karfi hakaba.
Jikin Umma na rawa ta lek'a dantaga wake sallama, ganin sama'ila saitake tambayarsa komi yafaru da jiddah?, iya abinda ya sani ya sanar mata, sannan yabata yis d'in ya juya.
Dole Umma ta kira Uncle yahya a waya, babu shiri yabaro kasuwa, tsayawa yay suka taho da malam alfah.
Tunda suka shigo gidan malam Alfah yaga halin da Jiddah take ya girgiza Kai kawai.
“yahaya inaga yakamata mukai Jiddah wani waje, bak'in aljanin da suka had'ata dashi yanada matuk'ar naci, tunda munyi namu ba'asamu warakaba yakamata mu gwada wani wajen kuma nakega”.
“Malam duk yanda kace haka za'ayi, mu mun aminta dakai d'ari bisa d'ari, Kai Ubane a garemu, ko bama kusa zaka iya zartar da komai akan jiddah”.
“Nagode da wannan karamci, yanzu ita mahaifiyar tata saitai k'ok'arin fidda mana ita zuwa mota”.
Da k'yar Umma ta iya fidda Jiddah, daga k'arshema saida taimakon Uncle yahya, aiko Jiddah sank'ame musuma tayi amota.
Tafiya sukayi sukabar Umma a gida............✍🏻
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[20]_*
..............Tunda suka tafi Uncle yahya keta tofama Jiddah addu'a saboda fisge-fisgen da takeyi da wata Y'ar siririyar k'ara maikama da muryarta ta dishe. a cikin wannan halin malam Alfah ya faka motarsa k'ofar wata cibiyar magungunan musulunci. Shikad'ai ya fita yana fad'ama Uncle yahya yana zuwa.
Kai kawai Uncle yahya ya iya d'aga masa, idonsa yay jajir yana rik'e da Jiddah daketa fiffisgewa har yanzun.
Bud'e motar da a kai ya saka Uncle yahya d'ago kansa ya kalli malam Alfah dake k'ok'arin zama a mazauninsa.
“Baba Malam miya faru?”.
“An samu matsalane yahaya, malam tajudden baya nan, amma anmana kwatancen wani wajen a Gadon k'aya, dukda shi bawai yana bada magunguna bane, yana taimakawa dai idan yaga abun ya tsananta ne, sai dai na rok'i alfarmar d'aya daga cikin almajiran malam tajudden wani ya rakamu, ga shinan zuwa”.
“To baba malam muje cand'in, ALLAH ya saka da alkairi”.
Gosulon da suka fuskanta a hanya yahanasu damar isowa da wuri, Ana sallar la'asar suka iso dai-dai masallacin bisa jagorancin kwatancen Zubairu Almajirin malam tajudden.
Malam Alfan ne kawai da zubairu suka fito, massalacine babba dake jingine da wani babban gida shima, anguwar tayi tsitt sai sautin karatun salla dake tashi cikin wata sassanyar murya. Alwala su malam Alfah sukayi suma suka shiga sallar, amma Uncle yahaya yana wajen Jiddah dan ba'a barta ita kaid'aiba..
Bayan an idar mutane suka fara fitowa d'ai-d'ai, sai da kowa ya fito, aka bar malam kawai da wasu tsirarun mutane a masallacin, su malam alfah suka k'arasa ga malam dake shirin fita shima.
Cikin mutunta juna malam da malam alfah suka gaisa, sosai malam zai iya girmar malam alfah a shekaru, shima zubairu ya gaisheshi kafin ya masa bayanin abinda ya kawosu.
Cikin jinjina kai malan ya amsa sannan suka fito.
Ana k'ok'arin fiddo Jiddah amota za'a shiga da ita ciki malam mustafa ya iso wajen, da mamaki yake kallon Uncle yahaya dake share zufa daya had'a saboda rik'e Jiddah.
“Uh uhm malam yahaya kaine yau a anguwarmu? Injidai lafiya?”.
Juyowa Uncle yahaya yayi damson ganin Mai maganar, shima cikin mamaki yace, “A malam Mustafa dama nan anguwar kake? Amma Alhamdllh nayi farin cikin ganinka, wlhy Jiddah ce babu lafiya muka kawota”.
“ALLAH Sarki, jiddah dai dana sani? Wadda akai biki watannin baya?”.
“Wlhy kuwa malam Mustafa itace”.
“Subahanallahi, ina mijin nata? mike faruwa haka?”.
Murmushin takaici Uncle yahaya yayi, yana gyara tsaiwarsa, “Malam Mustafa labarin maid'an tsawone, amma bara mushiga da ita dan malam Na jiranmu”.
“To ba laifi, amma inaga ad'an matsar da motar gaba saboda idanun jama'a”.
Shawarar malam mustafa sukabi, aka matsar da motar kusada k'ofa sosai ta yanda ko an fito da Jiddah babu mai ganinta.
Tunda Aka shigo da Jiddah cikin falon malam Abdul-ra'uff maina take wata k'ara da jijjiga da fisge-fisgen guduwa.
Tausayin Jiddah da tunanin yaushe tagamu da wannan lalurar ya ishi malam mustafa. Sai dai bashida zarafin neman k'arin bayani a halin da ake yanzu......
Maganar Malam Abdul-ra'uff ta katse masa tunani ya maida hankalinsa gareshi.
Kallon Uncle yahaya dake rik'e da Jiddah malam Abdul-ra'uff yayi yana fad'in “kaga inkaso sakarta kawai”.
“Malam da an saketa guduwa zatayi”. ‘Uncle yahaya yafad'a tamkar zai saka ihu’.
Murmushi malam Abdul'ra'uff yayi yana gyara zamansa, “Karka damu sakarta, babu inda zataje insha ALLAH”,
Sakinta Uncle yahaya yayi ya matsa gefe, yayinda Jiddah keta bige-bige tana wani irin gunji, ga uwar zufa da takeyi tamkar fanka bata aiki a falon.
“mustafa jonamin abin turarennan na gefenka”.
“To Malam”. Malam mustafa ya amsa cike da girmamawa..
Tunda Malam Abdul-ra'uff yafara zuba garin magani Na turare hayak'i ya fara tashi sai bige-bigen Jiddah ya k'aru, hakama gunjin da takeyi, sai dai kuma tak'i magana, kamar yanda malam yake buk'ata. Kusan mintuna goma sha biyar ana Abu d'aya lamari Na Neman cin tura, gadai alamun shaid'anin dake tare da ita yana jigatuwa, amma taurinkai ya hana yayi magana.
Malam ya tsaya daga tofama Jiddah Addu'a mik'ewa yay ya fito yana fad'in su Uncle yahaya su biyosa.
A zaurensa bisa rukunin kujerun ya zauna yana kallon su Uncle yahaya cikin yarce gumi.
“Wato maganar gaskiya yarinyarnan akwai sihiri mai k'arfi a jikinta, bisa alamu kuma anyi ne cikeda makirci mai wahalar fassara, dan shaid'anin dake jikinta ma kunga yak'i nuna kansa, alhalin kuma alamu sun nuna yana jigata da addu'oin dake ratsashi, shin kozaku bani wani haske akan al'amarin?”.
Kafin Uncle yahaya yay magana malam mustafa ya sanarma malama wacece Jiddah. Sosai malam Abdul-ra'uff yay mamaki, danshi ko kad'an bai ganetaba, dandanan hankalinsa Yakuma tashi, ya shiga tambayar Uncle yahaya Yaya akai haka? Miya faru da Jiddah bayan gaba d'aya dayin aurenta bata wuce watanni biyarba.
Kan Uncle yahaya a duk'e yana tsiyayar da hawaye yayma su Malam bayani dalla-dalla akan auren Jiddah da sanadinsa harma k'arewarsa sanadin matsalar da ayanzu Jiddah ke ciki.
Ran Malam Abdul-ra'uff ya6aci sosai, ga tsananin tausayin Jiddah da k'aunarta ke k'ara ratsashi, nawa yarinyar take da mahaifinta zai za6i sakata a gararin rayuwa irin wannan saboda cikar burinsa? Lallai alokacin dayasan irin auren da za'ama Jiddah kenan koda nuna k'arfine dasai ya aurama Aliyu ita. Amma babu komai, ya d'auki hakan a matsarin *RUBUTACCIYAR K'ADDARA* a gareta, babu wani mahaluki daya isa gogeta kuma...........
Malam nacikin tattaunawa da zuciyarsa sukaji sassanyar Muryar Sheikh Aliyu cikin sallama. Gaba d'ayansu amsa masa sukayi suna d'agowa da kallonsa. Sanye yake cikin shadda boyal ruwan k'asa mai haske, sai hularsa itama ruwan k'asa amma tad'anyi duhu kad'an, hanunsa rik'e da waya da key d'in mota daya saya tun bayan aurensa da Maimunatu. Kallo d'aya zakai masa ka fahimci hankalinsa a kwance yake, yad'anyi k'iba kuma yay fayau dashi alamun akwai kwanciyar hankali da nutsuwa a duniyarsa.
'Daya bayan d'aya ya basu hannu suka gaisa bayan ya gaida malam dake kallonsa tamkar zaiga maganin warakar Jiddah a jikinsa.
Kallon malam Mustafa yay yana fad'in “Ashe kana nan?”.
“Eh wlhy, tun bayan sallar la'asar nazo dama Na sanarma malam yarinyar da muka za6a”.
“Masha ALLAH, to bara na shiga cikin gida Na gaidasu, idan kun gama Na dawo”.
Harya mik'e malam ya dakatar dashi ta hanyar kiran sunansa.
“Aliyu!”.
“Na'am baba” ya amsa yana maida kallonsa garesa.
“Ku shiga kaida mustafa Falona akwai yarinya Mai lalura ka dubamin ita”.
A sanyaye yace, “To Baba”.
Malam Mustafa na gaba shi yana baya suka shiga, Jiddah Na kwance tayi ligif kamar matacciya, dan tunda su malam suka fita saita bar abinda takeyi ta nutsu, dama matsalarta maza ne kuma sun fita, amma su Malam Mustafa na shiga tahau fisge-fisge da kwalla k'arar datafi wadda takeyi a d'azun.
Hannu Aliyu yasa ya toshe kunnensa yana lumshe idanu danjin k'arar har cikin kwanyar kansa.
Ganin zata fice malam Mustafa yay saurin zungurinsa, idanunsa ya bud'e yana janye hannunsa daga kunnen, taku d'aya ya fisgo hijjabinta ya maidota baya ta fad'in yaraf tana wata irin jijjiga.
Tuni idonsa yayi jajur da 6acin rai (karku manta tunkan Aliyu yaje saudia yanada wajen saida magungunan musulinci dama), kallon Jiddah daketa faman takurewa a jikin bango tana k'yarma yayi, sai duk'unk'une fuskarta take a cikin hijjab. Yaja kujera ta roba dake gefe ya zauna d'an nesa da ita. Nuni yayma malam mustafa dake tsaye yana kallonsu da yabashi ruwa.
Malam mustafa ya mik'a masa ruwan daya d'ebo a Kofi, kar6a yay yafara tofa addu'a a ciki yana kallon Jiddah dahar yanzu take mutsu-mutsu, sai dai takasa yin k'arar sosai, dan ta k'udundune kanta a hijjab.
Ruwan Addu'ar daya watsa mata a jikine ya sakata zabura tana fasa wani kuka, bai sauraretaba ya cigaba, sai kuma mamuk'e bango take tamkar xata koma cikinsa.
Ransa a 6ace, amma hakan bai hana muryarsa fita da sanyiba yace, “Kai wane irin shaid'anine Mai taurin kai? Kana azabtuwa amma bazaka nunaba?”.
Shiru Jiddah ko nace aljani bai maganaba, k'yalesa Aliyu yayi, ya d'auki Qur'an malam Mustafa ma haka suka Fara karatu cikin suratul bak'ara.
Karkarwa jikin jiddah ya cigaba dayi tana wata irin zufa maiban mamaki. “Babu inda zanje, bazan fitaba, nace bazan fitaba, ni kubar k'onani bazan fitaba.......” wad'annan sune kalamun dake fitowa a bakin Jiddah tana kuka. Hakan kuma baisa su Aliyu dakatawaba, kusan mintuna talatin suna janyo ayoyin Ubangiji cikin surori daban-daban, sosai Jiddah ta jigata matuk'a, muryartama ko fita batayi, daga k'arshe kuma tama kwanta k'asa tamkar wata matacciya, cigaba da karatu su Aliyu sukayi, sai bayan kamar mintuna goma suka dakata saboda jin numfashin Jiddah ya daidaita.
Sassanyar ajiyar zuciya Sheikh Aly ya sauke yana rufe Qur'anin, ya kalli malam mustafa shima dake rufe nasa, “Mustafa wacece wannan d'in wai? Minene kuma matsalarta?”.
Nisawa malam mustafa yayi fuskarsa da tsantsar damuwa yake fad'ama Aliyu komai game da Jiddah, harma yunk'urin had'ashi aure da malam yay da ita tun farko, amma suka iske mahaifinta yamata miji”.
Shiru kawai Aliyu yayi yana kallon wani waje daban, shi mutumne mai tsananin tausayi da shiga damuwa akan damuwar wani, tuni hawaye harsun cika masa idanu, ya zari handkerchief daga aljihunsa yay saurin tsanesu. Batare daya yima malam mustafa maganaba yatashi ya fice.
Inda su malam suke zaune yad'an kalla kafin ya kauda idonsa gefe dan kar malam ya fahimci yayi kuka, “Baba ina zuwa su jirani”.
“To saika dawo Ali” ‘malam yafad'a cikin murmushi’.
Yana fita malam Mustafa ya fito, kallonsa malam yay “Mustafa miya farune?”.
“Malam tasamu barcine, inaga zai had'o magungunane”.
“To Alhamdllh, ALLAH kai mana maganin abinda yafi k'arfinmu, harma wanda muke gani munfi karfinsa”.
Amin malam, suka fad'a gaba d'aya falon harsu Uncle.
cikin zolaya malam yakuma kallon mustafa yana cewa, “Halan abokinka yauma halin ya ta6a?”.
Malam mustafa yay murmushi yana bama malam amsa, “Malam ai wannan wajib ne ga Aliyu, sai dai in Abu bai raunana zuciyarsa baneba”.
“To ALLAH ya kiyaye, Yaro ya maida kansa kamar wani mace, Abu kad'an yafara zubda hawaye”.
Duk murmusawa sukayi har su Uncle yahaya dake zaune suna saurarensu. Sosai Uncle yahaya yakumajin k'aunar Aliyu da samun nutsuwa akan maganar da suka gama da malam yanzu.
*********
Kusan mintuna talatin da fitar Sheikh Ali saigashi ya dawo d'auke da farar Leda madaidaiciya, zama yay yana bud'e ledar, dalla-dalla yayma Uncle yahaya bayanin yanda Jiddah zatayi amfani da magungunan, kafin ya d'ora da fad'in, “Ko kunada damar tura wani can gidan data baro yad'an mana wani bincike? Dan ina zargin kamar akwai abinda aka ajiye ko aka binne dake saka aljanin koda yatafi yake dawowa jikinta, abinda na lura dashi kuma kamar shine ke tsoratata inhar tasamu kusanci da namiji, alamun shine tushen sihirin jikinta, sai kuma mun samu rusa wancan kullin nasu da izinin ALLAH koda komai zai dai-daita, sadai insha ALLAH indai tacigaba da amfani da wad'annan magungunan sannan ta tsare yin azkar da salla akan lokaci, ta kiyaye yawo babu d'ankwali da yawo babu takalmi a tsakar gida, ta kiyaye sauraren wak'a ko shiga bayi batareda tayi addu'a ba, da yawaita kusanta kanta da Qur'ani, to muna fatan dacewa wajen samun sauk'i insha ALLAH”.
Alhmdllh kowa ya shiga maimaitawa da fatan dacewa. Uncle yahaya ya d'ora da fad'in ”Zamuga yanda za'ayi a bincika d'in insha ALLAH, mungode sosai ALLAH yak'ara girma da hak'urin taimakon bayin ALLAH”..
Amin duk suka amsa dashi, Aliyu daya amsa a la66ansa ya mik'e yana fad'in “Zaku iya tafiya da ita”.
Sun amsa da to, shikuma yay yunk'urin shigewa cikin gida.
Da sauri Uncle yahaya yace, “Malam bakai maganar kud'i ba ai”.
Murmushi Aliyu yayi, batare daya juyoba yace, “ALLAH yabata lafiya” kawai ya ida shigewa.
Uncle yahaya ya maido kallonsa ga Malam zaiyi magana. Murmushi malam yayi shima, “Malam yahaya wane maganar kud'i kuma? Tunda kaji yace haka bazai amsaba, kuma ai yima kainema, ALLAH yabata lafiya dai mu shine fatanmu”.
“Amin malam, ALLAH ya saka da alkairi, ya albarkaci zuri'a, ALLAH ya k'ara girma”.
Kowa ya amsa da amin.
Uncle yahaya yakai Jiddah dabatasan mi akeba mota, har k'ofar gidan malam da Malam Mustafa suka rakosu, suna niyyar tafiya Aliyu ya fito, hannu kawai ya d'aga musu ya wuce domin haramar d'aura alwalar magriba dake gabatowa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Su Umma na zaune zugum-zugum itadasu walida da Maman Sadiq da Aunty Nafisa wadda tazo sake duba jikin Jiddah ta iske kuma basanan saita tsaya.
Alkubus d'inma da Jiddah ke k'ok'arin d'aurawa sai Aunty Nafisar ce ta k'arasa, dan Umma ma takasa ta6uka komai tunda aka fita da Jiddah.
Su Zarah kam tunda suka dawo makaranta sukaji halinda Y'ar uwarsu ke ciki sai suka hau kuka, alkubus d'inma tunda aka gamashi babu Wanda yako kallesa.
Jin tsayuwar mota ya sakasu mik'ewa a tare suka lek'a.
Sune suka shigo da jiddah wadda take barci har yanzu. Uncle yahaya ya biyo bayansu da ledar maganin bayan yayima malam alfah godiya sosai.
Shima yana ajiye ledar fita yay massalaci, dan ankira sallar magriba.
Jiddah kam d'akin Umma aka kaita aka kwantar da ita, suma suka fito dan suyi haramar sallar magriba, koba komai hankalinsu yad'an kwanta..............✍🏻
*_🤭jiya kwace kodai Abba zakarine ya biya bashin da ake binsa dani😂😝, wani uzirine ya tasomin batareda Na shirya masaba😄, messages d'in PC ma sai yanzu zanje Na amsa mukusu tun kusan Na kwana uku⛹♀, wad'anda suka turo kumin afuwa yanzu Zan amsa insha ALLAH.🤐_*
Ina fata duk kuna lafiya?.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu._*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[21➖22]_*
..............Bayan Uncle yahaya yadawo daga salla suka zauna tattauna maganar Jiddah, bayani yay musu akan dukkan abinda ya faru, kafin ya d'ora da batun malam Aliyu na bincike a gidan Alhaji Garba.
Kowa ya jinjina maganar, domin wannan abune mai matuk'ar wahala agaresu, dama can babu wata alak'ar dangantaka a tsakaninsu, gakuma wannan batun na Jiddah daya gitta, Abba kam sunsan bama zai basu had'in kaiba, k'ilama idan sun masa bayani ya rusa komai, Hindu kam da ace abokiyar zamace ta kwarai dasai ta taimakesu tunda ita gidan zuwantane.
Sunta tattauna mafita amma basu samuba, duk hanyar da suka k'ulla saisuga bazata 6illeba. Dole dai suka ajiye zancen akan sai sunyi tunani.
Sund'an samu kowa yaci abinci, amma zukatansu dank'are da neman mafita suke.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tunda suka idar da Sallar Magriba sai yayma malam sallama yanufi gida, dan yasan d'alibai nacan na jiransa, fatansa sallar isha'i ta riskesa acan.
Kamar yanda yay fata kam saiya dace, duk da bawani nisabane tsakanin gidansa dana malam d'in, ya iske ana kiran sallar isha'i.
Alwala ya sake ya shiga masallaci. Bayan an idar sukai zaman karatu. Bai samu shiga gidaba sai kusan goma saura.
Cikin Sassanyar muryarsa yay sallama, Maimuna dake kwance cikin kujera tana kallon Sunna tv ta amsa tana tashi zaune, tsaf take cikin kwalliya tanata k'amshi, murmushi suka sakarma juna, yayinda Aliyu ya bud'e mata hannayensa alamar tazo.
Ahankali tataso ta shige jikinsa tana fad'in “Nayi kewarka Annur”.
“Nima haka habibati”. Malam Aliyu yafad'a a hankali cikin kunnenta.
Fuskarta d'auke da murmushi har yanzu ta d'ago ta kallesa, goshinta ya sumbata da la66anta, kafin a hankali yace, “Mikika tanadarmin sarauniya?”.
Cikin kashe ido da murya tace, “Komaima Na tanada maka harda abinda malam ya hana fad'a”.
Dariya sukayi a tare, Aliyu yaja hannunta yana fad'in “Zomuje ki fad'amin, ai bazan fad'ama malam kin fad'aba”.
“Yaya Ali kacika wayo wlhy”.
“Aunty Maimoon kin cika wayo kema al”. ‘Aliyu yay mahanar suna ida shigewa’.
Da taimakonta yay wanka sannan suka dawo falon, kullum dare fruits sune abincin Aliyu, gab da zai kwanta kuma yasha had'ad'd'en shayi irin Na larabawa Kofi d'aya, dan haka Maimunatu take k'ok'arin ganin tamusu nutsatstsan yanka.
Sosai ya maida hankalinsa ga Tafseer d'in da akeyi a Sunnah tv Wanda ya tarar Maimuna na kallo, harta gama ajiye dukkan abinda zai buk'ata hankalinsa naga tv.
“Yaya Aliyu”. ‘Maimuna tafad'a ashagwa6e’.
Juyowa yay ya kalleta batare da ya amsaba, da ido ta nuna masa kayan gabansa. Ajiyar zuciya yad'an sauke kafin ya sauka k'asa saman kafet ya zauna, itama zama tayi, sunashan kayan marmarinsu suna kallon tafseer, lokaci-lokaci sukan jefi junansu da murmushi dakuma magana idan ta kama.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah bata farkaba sai kusan k'arfe goma, lokacin Mijin Aunty Nafisa yazo ya d'auketa, su Uncle yahaya ma suna shirin tafiya, amma farkawar tata saita dakatar dasu.
Alhmdllh normal ta farka, dukda tanata ra6e-ra6e saboda ganin Uncle yahaya.
Zarah ce data had'a Mata ruwan wanka ta taimaka Mata zuwa ban d'aki, bayan ta shiga ta dawo waje zaman jiranta, bata wani dad'eba ta fito ta d'aura alwala sannan ta koma d'aki, bata shafa maiba sai kayan da Walida ta ajiye mata ta canja tahau ramuwar sallolin da bata samu yiba.
Su Uncle yahaya basubar gidanba saida sukaga taci abinci da fara amfani da wasu magungunan ta koma ta kwanta saboda jikinta duk babu k'wari.
Sallama sukaima su Umma suka wuce gida.
★★★
Washe gari normal Jiddah ta tashi, wandama bai saniba bazaice tashiga wani haliba jiya, koda Uncle yahaya yazo dubata d'aki ta shige ta 6uya, bai damuba shidai, dan yasan bawai yin kanta baneba. Sallama yay musu ya wuce kasuwa.
Da d'an k'arfin gwiwa su Zarama sukai shirin makaranta suka tafi.
Tundaga wannan lokaci abubuwa sukaima Jiddah sassauci, dukda har yanzu batasan namiji a kusa da ita, amma bata firgita ko fita hayyacinta danta samu kusanci dasu, magani kuma da ruwan addu'oi daya k'are ake aiko mata wani daga gidan malam, malam mustafa da kansa yazo yaymata maganar komawa makaranta saboda sunason sudai taje Saudia d'in, dan tunda sukaji batada aure sai suka ajiye batun waccen da suka za6a suka maida burunsu akan Jiddahn.
Y'an ajinsu sunyi farin cikin dawowarta, musamman ma Madina.
Kuma himma sukai wajen Trining d'in Jiddah yanda zata kuma samun gogewar ilimi sosai dabin k'a'idojin gasar, kuma tana k'ok'arin maida hankalinta sosai, dukda duk lokacin da malami zai shigo musu karatu Jiddah batada sauran nutsuwa harya fice, amma haka take dakewa da yawan Addu'ar samun kwarin gwiwa harya fice.
Duk dokokin da Aliyu yace ta kiyaye Alhmdllh tana iyakar k'ok'arinta, dama can ita bamai wasa da irin abubuwan nan baceba, zaman sihiri jikinta kawai k'addarace daga ubangji Mai jarabtar Bawa aduk sanda yaso, akuma lokacin fayaso.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Shirye-shiryen tafiya gasarsu ya kankama, dukda duk wannan hidimar da akeyi Abba bai saniba, rabonshi da zuwa gidan kusan watanni hud'u kenan, kuma yana zaune a garin babu inda yaje.
Ganin yarage saura kwana biyu su Jiddah su tafi Uncle yahaya yaje har gida ya sameshi da maganar.
A harabar gidan ya iske su kalifa na ball, kallo d'aya sukai masa suka d'auke Kansu tareda cigaba da kwallonsu.
Murmushi Uncle yahaya yayi kawai shi yana k'arasawa garesu da fad'in “yarana kuna lafiya?”.
Cike da rashin kulawa suka amsa suna cigaba da harkar gabansu. “To ALLAH ya k'yauta” uncle yahaya yafad'a yana kamo hannun kalifa domin tambayarsa. Amma sai yaron yay azamar janye hannunsa yana wani 6ata fuska. Uncle yahaya baice komaiba sai tambayarsu Abba nanan da yay. Muneer kawai ya amsa da eh, amma Hassan da Hussain da kalifa tunima sun koma kan hayaniya akan cin Ball.
Haka Uncle yahaya ya k'arasa ciki yana tausayin yayansa akan wad'annan yaran marasa tarbiyya, acikinma Hajia Hindu yatsine-yatsine taita masa, tana shirin cewa Abba baya gida saigashi ya fito saboda jin muryar d'an uwansa.
Zama yay suka gaisa Uncle Yahaya ya fad'a masa abinda ya kawoshi.
Kallonsa Abba yay rai a 6ace, “Yahaya kace min dama wannan shine dalilin dayasa kuka kashe Mata aure?”.
Uncle yahaya yay murmushin takaici yana gyara zamansa. “Yaya ba wannan maganar bace ta kawoni please, nidai yanzu amincewarka kawai da addu'arka muke buk'ata”.
“Yo inda amincewarsa ake buk'ata Aida tini amfad'a masa basaida lokaci ya k'ureba”. ‘Hajia Hindu tai maganar tana gatsine-gatsine’.
Murtike fuska Uncle yahaya yayi yana watsa mata wata muguwar harara, “Kinji na sakoki a cikin zancena Maman kalifa? To ki Kama kanki wannan ba huruminki baneba, kibari idan mungama Na wuce saikiyi keda shi”.
Harara ta watsa masa tabar falon tana jan tsaki. Shima Uncle yahaya tsakin yayi ya mik'e.
Abba yace, “Ni wlhy ina mamakin yanda kokad'an kaida Hindu bakwa zama inuwa d'aya, nasan dai yagana ce kawai ke rura wutar k'iyayya a tsakaninku kullum tamkar kuna ganin hanjin juna”.
Baki Uncle yahaya ya ta6e kawai, “Yaya nawuce ni”.
Uncle yahaya bai sakebi takan Abba ba tundaga ranar har yau dasu Jiddah ke shirin tafiya k'asa mai tsarki, jirginsu zai tashi k'arfe tara Na darene.
★★★*
“ALLAH Yaya Jiddah harna Fara kewarki tunma da rana”.
Harara Zarah ta zubama Walida Mai maganar, ta d'auki kwandon wanke-wanke data gama tana nufar kicin, “To Uwar iya, kema kad'ai kike kewarta kenan?”.
Dariya Umma da Jiddah dake zaune kan tabarma sukayi, Jiddah ta janye albasar datake yanka wadda zasuci awara tana fad'in “Oni Hauwa, wlhy Zarah yanzu kinzama jarababbiya, wannan harar da kike Mata ai saikisa ta rud'e ta tsulma cikin rijiyar”.
Daga kicin Zarah tace, “Yo Yaya Jiddah abunne da haushi, inama laifin tace munfara kewarki, amma saita wani ware kanta”.
“Kishi kike da autata kenan Zarah?”. ‘Cewar Umma tana dariya’.
“Umma barta ai Zan rama wlhy”.
Zarah da Jiddah suka sanya dariya, yayinda Walida ta kwa6e fuska tana dangwarar da gugan hannunta tadawo kusada Umma ta zauna tana kumbura baki.
Jawota Umma tayi jikinta itama tan danne dariyarta dak'yar saboda baki da Walida ta kumburo. “Kinga auta barsu kinji, saina rama miki nima bazan bar saita kwanaba”.
“Yauwa Ummana shiyasa nake sonki”.
Ha6a Jiddah ta rik'e tana fad'in “To a'a mu tsintomu akai madam, wato Ummanki ma ke kad'ai”.
Gwalo Walida tai musu, yayinda Zarah takai Mata dundu Umma ta tare. “ALLAH Zarah kika dokarmin yarinya saina rama mata”.
Jiddah tace, “Umma harda fad'in ALLAH?”.
“To tadaketa tagani”.
“Yaya Jiddah barsu, badai an waremu ba, yau kina tafiya gidan Uncle yahaya Zan koma nima”.
“Haba dai y'ammatan Umma wasa muke muku”. ‘Umma da walida suka had'a baki wajen fad'a’.
Dariya suka sanya suduka.
Haka suka cigaba da hirarsu har bayan isha'i bayan sungama cin Awara, daga nan Jiddah tahau shiri dan Uncle yahaya yakura Umma yace ta shirya malam mustafa yace zaizo d'aukarsu.
Karfe takwas da rabi kuwa sai gashi shida Uncle yahaya, alokacin kuma kuka yatashi a tsakanin su Jiddah, Umma ma dai tana dannewa ne kawai, suduka gidan sukai mata rakkiya har airport.
Wannan dai shine Karon farko na zuwan Jiddah da ahalinta airport, dan haka sukaita zuba k'auyanci, Jiddah dai tanata kalle-kalle amma bata cewa komai sai dariya da take musu itada Uncle yahaya da malam mustafa.
Saida kuma aka fara shelar matafiyan jirgin Saudia sannan jikinsu yay sanyi, su Zarah aka fara matse hawaye. Sunaji suna gani aka kira sunan Jiddah a bayan Na Uncle yahaya da malam mustafa. A d'arare ta shiga jirgin ga wani tsoro daketa kuma mamaye zuciyarta, Addu'a tafara karantowa a zuciyarta, indama ALLAH ya taimaketa kusada wata Mata malam mustafa ya nuna Mata ta zauna.
Cikin k'ank'anin lokaci sabo ya shiga tsakanin Jiddah da Matar Mai yawan fara'a, da taimakonta Jiddah ta dake kewar y'an uwanta ta ragu Mata a zuciya.
Ubangiji ya saukesu lafiya, inda Jirginsu ya sauka a Jidda, itadai Jiddah tanata tsarkake sunan ALLAH a zuciyarta, lallai duniya akwai abubuwan kallo, gaba d'aya saita koma cikakkiyar bak'auya zam, shi kansa Uncle yahaya sai tsarkake sunan ALLAH yakeyi, yau gashi sanadin d'iyar zumu yazo inda baiyi tunaniba (danshi baita6a zuwa makka ba) jiyay yana k'ara k'aunar Jiddah har k'asan ransa, wato zuminci babban abune da mutane ke wofantar dashi bisaga son zuciya, da mutane zasu nutsu su fahimci muhimman zuminci da sun rik'e, shidai babu abinda zai cema ALLAH sai godiya...............✍🏻
Kuyi maleji da wanga🤐🚶🏻♀
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSO...._*
*_💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_[23➖24]_*
..............Abinda yabama Jiddah mamaki ashe Matar da suka had'u a jirgi tafiyarsu d'aya, sai da suka shiga motar datazo d'aukarsu sannan Jiddah itama taga ta shiga.
Cikin Murmushi matar tace, “Kinyi mamaki ko? Na 6oye mikine dama danna baki mamaki”.
Fuskar juddah ma d'auke da murmushin take fad'in “Aiko aunty kinbani, nakuma gode”.
Y'ar dariya sukayi, wadda tasaka su Malam mustafa kallonsu. Jiddah datun d'azun dauriya take da zamansu kusa da ita tai k'asa da kanta, tana karanto sunayen ALLAH domin Neman sassauci da k'arfin zuciya.
“Kufa Mata inda kuke birgeni akwai saurin sabo”. ‘cewar malam mustafa idonsa akan matar’.
Matar tai murmushi cikin wani salo Mai nuna tsantsar so da k'auna tace, “Shiyyasa kuma zumincinmu keda k'arko”.
Jiddah dai dasu Uncle yahaya suna jinsu.
A haka suka k'arasa Makkah.
Sun isa wani k'ayataccen waje Wanda Jiddah ke k'autata zaton Hotel ne, dan yanada matuk'ar girma, Wanda ya d'akkosune yay musu rakkiya har ciki inda aka tanada musu masauki tunkan su Iso. Abun yak'ara birge Jiddah sosai.
Itada matarnan d'akinsu d'aya, Uncle yahaya da malam Mustafa ma d'akinsu d'aya.
Gaba d'aya Jiddah tama kasa cewa komai gameda had'uwar d'akin, sai kalle-kalle take. Matar tai murmushi tana kallonta “Dukda nima wannan ne zuwana Saudiyya na farko, na Lura kinfini k'auyanci k'anwata”.
Hannu Jiddah ya saka tana rufe fuskarta dan taji kunya, a haka tace “Aunty abunne akwai k'ayatarwa, gaskiya mahaifar Manzon ALLAH ta had'u, duk iya hasashenka saidai kayi amma tabbatarwa saikazo ciki”.
“Wannan gaskiyane k'anwata, ALLAH dai yasa mudace. Yanzu jeki fara shiga wanka dai”.
“To aunty”.
Sosai Jiddah kejin dad'in kasancewa da Matar, dukda kasancewarta Y'ar gayu hakan baisa ta nuna ta fitaba, gashima ta girmeta, dan ko aunty Nafisarsu ma zata iya girma, amma aunty Zulai itama zata iya girmarta.
“K'anwata Muna tare awanni masu yawa amma bamusan sunan junaba, ni sunana Siyama, Matar malaminku Mustafa”.
Sosai Jiddah tad'an waro ido waje, “Lah Aunty dama ina tare da Matar malam ce? Amma kinada kirki wlhy”.
Dariya sosai Siyama tayi (ina fata kun gane, k'anwar Aliyu) kafin tace, “Kanwata kinada abin dariya wlhy, k ya sunanki?”.
“Sunana Jiddah Aunty”.
“Masha ALLAH, ashema mamanace ni”.
Murmushi Jiddah tai kawai batace komaiba.
Kasancewar Siyama da Jiddah sai ya d'auke Mata kewar y'an uwanta da Ummanta, dukda k'asan zuciyarta Na begensu, dandanan suka Saki jiki da juna, harma hakan yabama Malam Mustafa da Uncle yahaya mamaki.
Washe Gari Malam Mustafa da wasu manyan malamai y'an Najeriya suka zauna da Jiddah, abin yabata mamaki dan tazatafa sukad'aine sukazo, Ashe harda malamin nan data ta6a gani a taron k'arama juna sani Na Abuja (Malam Abdul-ra'uff), tsuma jikinta yaytayi ganinsu duk maza a wajen, amma haka ta dake tana karanto duk addu'ar datazo gareta, sauk'intama d'an nesa dasu ta zauna, dukda AC dake wajen sai zufa takeyi, Malam Abdul-ra'uff ne kawai yalura da halin da Jiddah ke a ciki, dan haka saita bashi tausayi sosai.
Tambayoyi sukaita Mata domin k'ara tabbatar da nagartarta, inda tai kuskure suyi Mata gyara da fad'ad'a Mata bayani akan abun, duk kuma yanda abun zai iya kasancewa sun Mata bayani, tareda Addu'ar Neman dacewa.
Jiddah ta nutsu sosai domin kuma fahimta, Alhmdllh kuma ta fahimci kaso mafi yawa a ciki, inda kuma bata fahimtaba sosai takan kuma tambaya. Sunyi zama kusan Na awa biyu da Jiddah, Wanda ikon ALLAH ne kawai yabata damar kasancewa zuwa wannan lokacin batareda samun matsalaba, danma Malam Abdul-ra'uff dayaga sosai take a takure yay Mata addu'a cikin ruwa yabata Tasha, shinema takuma samun nutsuwar zaman wajen, bayan sun kamala zaman akad'anyi hotuna kafin su fito suka rankaya Massalaci.
Ai tuni Jiddah tafara hawaye ganinta gaban ka'aba, tashin farko Addu'ar shiriya ta farama mahaifinta, sai Ummanta da Uncle yahaya, kafin nan y'an Uwanta, ta d'ora da addu'ar fatan ALLAH yabasu mazaje nagari itada y'an uwanta da dukkan al'ummar musulmi.
Basubar massalaci ba sai la'asar, dan acan suka had'u da Siyama da Uncle yahaya.
*_Ranar Musabaqa_*
Yau dasu Jiddah suka cika kwana biyu a saudiyya ne ta kasance ranar musabaqar data kawosu, tunda safe suka tafi *Riyadh* inda taron zai gudana, duk yanda Zan fasalta muku abin bazaku fahimtaba, amma kowa ya k'iyasta a ransa.
Tarone Na taurarin al'ummar musulmai, dolene kaganka a wajen kaji kwalla ya cika idonka, Addinin isalama addini Mai nagarta da aminci, duk Wanda ya tsinci kansa a ciki ya godema ALLAH.
Sai Jiddah taga mu bak'ak'e y'an tsirarine a wajen, saima kayi duba na tsanaki zaka iya zazzak'ulomu, babu yaran da kakeji a wajen yana tashi sai larabci, Su Jiddah Matan an killacesune awani glass da zasu iya kallon komi ke gudana a wajen, ankuma kaimusu abinda zasu rimgajin magana shima, babu ruwansu da mazan. Hakan ba k'aramin farin ciki ya saka Jiddah ba, dukda dai tsorone fal ranta, dan ita yaran larabawannan sun tsoratata, tana tunanin Anya kuwa zata iya Kai labari a gasarnan?.
A k'asashen Africa gaba d'aya k'asa kusan biyarce ta halacci taron, sauran duk yankin fararen larabawane dawasu d'aid'aikun kasashen turawa..
Tun Jiddah Na d'ari-d'ari da y'ammatan kusa da ita har suka janye ra'ayinta tafara tanka musu, dukda larabcinta baikai nasu kwarewaba tana k'ok'ari itama. tuni hirar ilimi ta 6arke tsakainta dasu Ummusulaim. Sai hotuna suke musu, Jiddah bata ta6a damuwa da rashin wayaba sai yau, saitaji inama itama tanada ita ta d'auki hotunan domin tarihi........
Tunanintane ya katse jin an Kira sunanta, d'ago kanta tayi ta kalli Aunty Siyama, Aunty siyama ta mik'a Mata wayarta.
“Aunty miya faru? Ajiye miki zanyi?”.
“A'a kema ki d'auki hotunan kodan tarihi”.
Godiya Jiddah taimata sosai, yayinda tuni Aunty Siyama ta juya ta fita wajen da suma aka tanadar musu kusada su Jiddah.
Suna tsaka da hotunansu wata sassanyar murya data fara jan k'ira'ar Al-Quran ta daki kunnuwansu. Kusan duk a tare suka kalli wajen, dan da hankalinsu duk baya wajen, shiyyasa basusan hidimar da akeba.
Mamaki al'ajabi mai girma ya Kama Jiddah, ganin mamalakkin wannan murya ya fitone cikin jinsin bak'ak'e irinta, sosai ta shagala da kallonsa karatunsa Na ratsata da k'ara Mata nutsuwa, batama San sanda tafara masa video recording ba kamar yanda sauran mutane ketayi, ga wajen yayi tsit bakajin sautin komai saina fitar muryar *Sheikh Aliyu Abdul-ra'uff Maina*, abin birgewa da alfaharin duk wani Mai alak'a da wannan *TAURARO*.
Saida ya kai har k'arshen Suratul Al-Ahazab sannan ya dakata yana share kwallar data cika idonsa saboda yana karantawa zuciyarsa Na fassara abinda Surar ta kunsa, hakama masana aduniyar ilimi suna saurarensa da fashin bak'i a zukatansu.
Saida yaja doguwar Addu'a kafin yakoma ma zauninsa, Mutane dayawa ya birgesu dajin k'aunarsa, mahaifinsa kam shikad'ai yasan yanda yakejin d'unbin k'aunar Aliyu a ransa, dukkannin burinsa akan ilimin y'ay'ansa Aliyu ya cika masashi.
Taro yacigaba da gudana bisa bigiren abinda ya tara mutane, dan anfara gudanar da gasa cikin nutsuwa. Wajen tsit yake bakajin komai sai sautun karatu dakuma gyara dasu Aliyu keyima yaran dan sune alk'alan Musabaqar.
Lokacin da aka ambaci Nigeria sosai cikin Jiddah ya juya, dak'yar ta iya janyo numfashi da karanto addu'a sannan tasamu mik'ewa zuwa inda kowa ke zuwa ya zauna.
Tunda ta fito ya kafeta da kallo ta k'asan ido, tashin farko yabata maki d'ari bisa d'ari a 6angaren tafiyar Nutsuwa, harta k'araso wajen yana kallonta, amma bazaka ta6a fahimtar hakanba saishi da yakeyi.
Cikin hashen larabci balaraben malamin yafara Mata tambayoyi kafin yabata izinin tsunduma ga abinda ya ajiyesu.
Sura kawai ya za6omata a cikin Al-Qurani tunda tace ta sauke a hadda ma sai abinda ba'a rasaba.
Aliyu daya d'auke kansa kamar bashine kemata kallon k'asan idoba d'azun yana saurarensu, jin Surar da Sheikh Mohammed Ali ya cafko mata saida yad'an d'ago kai ya kallesu, aransa kuwa yana ayyana shikenan sun fad'i, danshifa bai tabbatar da yarinyarnan zata iya wani abun kwarai ba, dan sanyinta yayi yawa..........
Tunaninsa ya katse lokacin da nutsatstsiyar muryarta mai zak'i da sanyi tafara karatu cikin Suratul Al-Furqan kamar yanda aka bata Umarni.
Wani irin sanyi da nutsuwa suka ratsa zuciyar Aliyu, ya lumshe idanunsa yana mai fassara Ayoyin daki-daki.
Gurin yay tsit ita kawai ake saurare.
Itadai Jiddah kanta na a k'asa bata kallon kowa a cikinsu, karatunta kawai take idanunta na zurarar da hawaye. Bata tsayaba sai da aka dakatar da ita, aka kuma d'akko mata wata surar.
Hawayenta ta share jikinta Na cigaba da tsuma tafara karanto suratul Al-Hujurat, nanma tayi nisa sosai aka kuma tsaidata takoma Suratul Al-Mutaffifin, aka sake maida Suratul Al-Ma'arij, ayanzukam sosai Jiddah take kuka a wannan sura ta al-ma'arij, saboda abinda take magana akai Na azaba ga wad'anda suka bijirema gaskiya da Ni'ima ga masu ruk'o da gaskiya, tsoratarwa da ranar hisabi da sakamakon kowa, saida takai har k'arshenta sannan aka maidata suratul Al-Zumar, nanma tayi nisa aka tsaidata aka dawo da ita Suratul Al-Ibrahim, tanayidai tana shartar kwallanta aka kuma maidata Suratul Al-'Imran.
Daganan aka tsaidata, Handkerchief d'in gabansa ya mik'a Mata ta Y'ar k'ofar gilas d'in data raba tsakaninsu, ta kar6a yayinda idonsu ya shiga cikin Na juna, cikin fad'uwar gaba tai saurin janye nata tana jawo numfashi dak'yar, wani k'amshi mai dad'i yadaki hancinta lokacin datakai handkerchief d'in kusada fuskarta, idanu ta lumshe ahankali ta furta “Masha ALLAH”. saida ta goge fuskarta fes dukda hawayen nacigaba da zubowa kafin ta mik'a masa. Kansa ya girgiza mata yana d'auke kansa, a kan la66anta ta furta “Jazakallahu khairan”, ya amsa da “Amin” shima a saman la66ansa, dan yana kallonta ta gefen idonsa.
Anfara Mata tambayoyin daduk suka kamata, harma acikin wasu littatafan daban, cikin amincin ALLAH tana bada amsa yanda ya kamata. Duk sanda Sheikh Aliyu zaima Jiddah tambaya sai idonsu yashiga na juna, saidai kowanne yay saurin janyewa.
Dad'i sosai yacika wakilan Nageria irinsu Malam Abdul-ra'uff da manyan malamai, Sarkin Musulmai da sauransu, saboda jin yanda Jiddah ke amsa komai daki-daki, kurakuran da ake samu daga gareta k'alilanne wad'anda ba'a rasaba.
Bayan an gama da Jiddah aka cigaba da kiran d'alibai.
Saida kowa yayi sannan aka tashi saikuma an tantance wad'anda suka tsallake.
★★★★
Washe Gari Jiddah tasamu nasarar shiga cikin k'asashe bakwai wad'anda suka tsallake, a ranarma Jiddah tasha kuka wajen yin nata.
Washe gari again nanma aka kuma fafatawa da k'asashe uku da suka tsallake, ciki harda Jiddah mai wakiltar Najeriya.
Randa akai Na k'arshe ba k'aramar cika wajen yayiba, dan harda Sarkin Saudia da wasu manya-manyan mutane da duniyar Musulinci ke ji dasu, wad'anda mukeji sunayensu a bakunan malamanmu da litatafai Na Addini da suka riskemu.
A yau kam bak'aramin rud'u Jiddah ta shigaba, saboda tambayoyi su Aliyu ke zak'ulo musu masu wahala da tsunduma kwakwalwa cikin dogon nazari. Kasancewar an Fara da wuri kuma kasashe Uku ne kawai suka fafata sai aka gama da wuri, Nageria ita kad'aice takai wannan mataki a yankin Africa.
Bayan kammalawar su Jiddah manyan malamai suka koma bayan fage domin tantancewa, yayinda a wajen taro aka cigaba da gudanar da lectures masu ratsa jikkuna da duniya gaba d'aya.
Ba'a samu nutsuwar sanar da sakamako ba sai bayan salar zuhur.
Kowa dai kunnensa a bud'e yake da fatan k'asarsa tazo Na farko.
Wajen yay tsit an zubama Manyan wajen idanu dake Magana k'asa-k'asa.
An Kira *Azra Asen* Mai wakiltar k'asar *Turkiyya* wadda itace tazo Na uku.
Gaba d'aya wajen yad'auki kabbara, Azra ta fita inda ake buk'atar ganinta, bayan jinjina da yaba Mata da addu'ar fatan alkairi agareta aka bata k'yautar data samu da k'yautar Nasarar datasamoma k'asarta.
Gaban Jiddah nata fad'uwa da wasiwasin ta farkoce ita kota biyu....
Tunanintane ya katse lokacin da ake shelanta kiran sunan *Arwa Saiyyad* Mai wakiltar k'asar Saudiyya, wadda itace ta biyu. Itama dai tasamu k'aututtukan dasukafi Na Azra tareda fatan alkairi, inda y'an saudia sukai murna, dukda sunyi burin zuwa Na d'aya suma.
Jikin Jiddah duk yay sanyi, azatonta ko ancire sunantane, sai tajiyo Ana kwala kiran sunan *Jiddah Zakari Yaro* *Najeriya* sosai jikinta yahau rawa, saida taimakon Ummusulaim dasuka zama k'awaye ta iya mik'ewa, tafiya take tamkar zata fad'i saboda sassarfa da idanun mutane, ga lalurarta ta tsoron kasancewa muhali d'aya da maza, danma Ubangiji ya sauk'ak'a lamarin..
Dak'yar ta iya k'arasawa garesu. Doguwar Addu'a da jinjina ga Jiddah da iyayenta da malamanta da k'asarta sosai akayi, kafin a damk'a Mata k'autar nasararta dakuma k'yaututtuka da malamai daban-daban wad'an suka fito a k'asashe daban-daban, da manyan attajiran da suka halarci wannan gagarumar Mubabaqa. Kuka kawai Jiddah ta sakamusu harda sheshsheka, inda mutane dayawa suke tayata musamman ma mu y'an Najeriya damuke cikin farinciki.
Aliyu dake murmushi yasaka handkerchief ya d'auke hawayen da suka cika masa idanu, hakama Uncle yahya, su malam mustafa malam Abdul-ra'uff, Sarkin musulmai da sauran malamai dasuka halarci taron y'an Nigeriya duk suna tare da tsantsar farinciki, Aunty Siyama jitake tamkar k'anwarta ciki d'aya, dad'i dukya lullu6eta.
Abubuwa sunciga da gudana kafin taro ya tashi lafiya, masu murna nayi masu kuka nayi.
A ranar su Jiddah suka baro birnin Riyadh zuwa Makkah.
Kowa saiji yake da Jiddah, sai nan-nan su malam Abdul-ra'uff sukeyo da Jiddah, yayinda dad'i ya cikata, gata ga Sarkin musulmai da manyan malamai Na k'asarta da takejin labarinsu kojin wa'azinsu a redio ko TV.
Saidai abinda yabata mamaki bataga malam Aliyu ba tun barowarsu Riyadh, dan badashi suka taho Makkah ba, batadai tambayi kowaba tayi shiru da bakinta, amma haka kawai taji tana kwad'ayin ganinsa kodan tamasa godiyar Handky daya bata ranar, dan dataji d'an Najeriya ne kuma d'an mutumin da zuciyarta take kauna da girmamawa sai dad'i ya kamata, ashema tana sauraren tafseer nasa sosai batasan shi baneba sai yanzu.
Uncle yahya kam fad'a muku irin farin cikin daya tsinci kansa ai 6ata lokacine ma.
Labari kuwa yakai Najeriya tuni, sai hotunan Jiddah ke yawo a jaridu da televisions.
Lokacin da zance yakai kunnen su Umma ai kuka kawai ta sanya Na dad'i, tuni labari yagama zagaye dangi, kowa burinsa Jiddah tadawo ya k'ara ganinta. (Saikace sun manta fuskarta🤣), sundake sai sayen jarida suke suk'ara ganinta, su Zarah ma har Umma suka sayomawa, aiko tasaka k'asan gado ta 6oye bayan sungama Karantawa, wai zata adana tarihi😂🤭. Zumud'in dawowar Jiddah garesu dukya cikasu.
Lokacin da aka nuna Jiddah a labarai Abba da Hajia Hindu suka gani Hajia Hindu rud'ewa tayi, shikansa Abba yau saiyaji wani iri, yarinyarsace a tsakkiyar manyan mutàne da duniyar musulinci ke ji dasu, duk surutan da Hajia Hindu kemasa baibi takantaba yatashi yashige d'akinsa saboda wani jiri dayakeji yana Neman kwasarsa.
hakance takuma kasancewa a gidan Alhaji Garba, dan gaddama suka kwaso suka dire akan ba Jiddah data zauna a gidan baceba, yayinda Ashir keta rantsuwa da ALLAH itace. Alhaji garba yace bai yardaba saiya bincika.
Yayinda wancan cakwakiyar ke faruwa a Najeriya Su Jiddah suna can suna gudar da Umrah a Makkah, tareda zagayen guraren tarihi domin k'arin ilimi, yayin da daga baya kuma suka tattarasukak nufi Birnin Madina.
Kwanansu bakwai a Madina Gari Mai tarin Ni'ima da dad'in zama, Wanda duk muminin daya shiga baya fatan yaga ya fita, kuka dai Jiddah ta shashi yayinda taganta gaban kabarin MANZON ALLAH (S.A.W) da ahalin gidansa.
Ranar jinta take wata iri daban tamkar ba itaba.
Duk inda yakamata suje wajen tarihi malam Abdul-ra'uff shine jagoransu, itadai Jiddah tana k'ara mamaki Ina Aliyu ya shiga?.
Gaba d'aya kwanakin su Jiddah ashirin Cif da tafiya suka juyo k'asarsu ta haihuwa Najeriya cikeda farin cikin d'umbin nasaarorin da suka k'unso.............✍🏻
*_Barkanmu da Juma'a sweet sister's😄😄🤝🏻🥰_*
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
0 comments:
Post a Comment